MATAR UBA By Miss_ayusha - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MATAR UBA By Miss_ayusha

MATAR UBA By Miss_ayusha

- - Post a Comment

 MATAR UBA By Miss_ayusha


Www.bankinhausanovels.com.ng 


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€         πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

               ❤❤

                  πŸŽ€


       *MATAR UBA*


   *By Miss_ayusha*


*🌈Kainuwa writer's asso🀝*


Bismillahir rahmanir rahim da sunan Allah nake farawa.


             1⃣&2⃣

Hayaniya ne kawai ke tashi a d'akin kamar ana rigima jin hayaniyar na k'ara yawa yasani kutsa kai na ciki abinda kunnuwa suka jiyo min bai wuce banbamin da matar takeyi ba


  "Alhaji wallahi bazata sab'u ba ya za'ayi komai akayi a gidan nan sai ace Rahina ce da laifi sai kace ita bata da gata to wannan fa sam bazai yiwu ba"+


  "Ke Rakiya in banda abinki Rahina da Heedaya duk ba 'ya ya na bane ko kuma bani da ikon hukun tasu kike nufi,maiyasa kwakwalwarki bata fad'a miki dai dai shin kinga Rahina kawai na hukun ta"


  "Ko ba ita kadai ka hukun ta ba amma cewa kayi laifin tane bayan kuma wanan munafuka mai b'akin aniyar ita ke haddasa komai" jin abinda Rakiya ke fad'a yasa Heedaya kallon mamin ta ganin irin kallon da mamin nata ke mata ne yasa ta yin shiru,


  "Rakiya fita ki bar d'akin nan tun kafin ranki ya baci kinaji ko"


"Ko baka fad'a ba zan fita,ke kuma mu zuba nidake shege ka fasa" nan tasa kai tayi gaba tare da 'yar ta Rahina


   "Ruwan sanyi ta debo mishi yayin da ta mika masa, Alhaji kaji kasha kodan zuciyar ka tayi sanyi"


  "Haba Murja ai ke yakamata ace na baiwa ruwan sanyi ko dan wanan masifafan matar,Murja ina mai baki hak'uri akan duk wani abu da Rakiya take miki ko ba dade ita zata kunyata"1


  "Alhaji kar ka damu mahakurci mawadaci bakomai kaji ana kiran sallah ya kamata ka tafi masallaci" toh ya amsa mata yayin da yayi toilet yayo alwala sanan ya tafi masallacin, su din ma alwalar sukayi dukkan su yanda sukayi sallah bayan idar da addu'an mamin su ta zaunar dasu


"Habiba" na'am mami, "Heedaya" na'am, itama ta amsa


"Heedaya maiyasa baki jin magana maiyasa duk fad'an da nake miki bazaki ji ba,Heedaya miye ribar fad'an da kikeyi tare dasu Rakiya bayan kinsan halin su bazai taba canzawa ba"


  "Mami yanzu dan allah haka kawai muna zaune sai naji wata na fad'a miki maganar banza na kyaleta nikam wallahi sam bazan iya ba,amma kiyi hak'uri in Allah ya yarda na daina kulata"


"Ko kefa yar albarka haka nake son kin kina fad'a kinji ko"eh ta amsa mata,


  "Ai mami ni bansan halin wa ta dauka ba ace yarinya bata da hak'uri ko kadan" kan ki akeji iya abinda Heedaya ta fad'a kenan d'akin mamin su tayi yanda ta dauko mata maganin ta


  "Mami ga maganinki baki sha ba" ohh Heedaya kinga har na manta ma, nikam ina zan mata yanzu dai kisha"haka tasha maganin nan abinsu suna hira kamar ba uwa da yaran ta kai kace kawaye ne, ring ring waya ta shiga ringing ganin Habiba ne ta dauka yasa ni kasa kunne jin mai take fad'a


  "my prince ya kake?"


  "Lafiya lau, ya gidan dasu mami?" Ita din ma lafiyan ta amsa mishi,


"Princess kinsan meye" a'a sai ka fad'a ki shirya yanzu ina zuwa"

"My prince ka dawo ne?" Tun yaushe princess " shine kuma baka fad'a min ba "am swry baby na yanzu baga shi na fad'a miki ba sai ki shirya ina nan zuwa kafin sukayi sallama,


  "Mami wai fa kinsan Ahmad ya dawo shine koya fad'amin sai yanzu wai na shirya yana zuwa"


"Toh habiba tunda ya fad'a miki yanzu ai sai ki shirya ko" toh ta amsa mata

  "Iyye masoya wato ya Ahmad niko ya fad'amin ya dawo ko zai zo ya sameni ai"Kunfi kusa cewar Habiba,


  "Yar kanwata zo kiji dan Allah ki taimaka ki hada mishi orange juice kafin na fito wanka sai ki dan dafa mishi abinda bazai yi wahala ba kinji" toh ta amsa mata itadai mamin su na jinsu ko tak bata ce  musu ba,toilet Habiba ta shiga domin yin wanka yanda Heedaya ta shiga kitchen rasa mai abinda zatayi daya dan tasan kafin tace zatayi abinda take so zai iso kawai ta yanke shawaran dafa mishi jellof na taliya wanda taji uban ganye da hanta a ciki ga kuma juice din da take had'awa tuni wurin ya kaure da kamshi b'angaran Habiba tayi wankan ta tsaf nan ta zauna gaban mirror mai nata da shafa kafin ta danyi makeup wanda bai ma fuskan ta yawa ba wani blue less nata ta saka mai ratsin pink a jiki dinkin riga da skirt sosai kayan ya zauna a jikin ta yanda taci daurin ta sanan ta feshe jikin ta da turare masu sanyin kamshi d'akin ta zata sauke shi ta shiga shidin ma abin kamshi ta fesa yanda duk wurin ya kaure da kamshi kafin ta koma wurin Heedaya, "wow yar uwa kinga yadda kika fito kuwa" da gaske Habiba ta tambaya sosai ma shine amsar da Heedaya ta mayar mata


  "To yanzu dai kin gama girkin ne?" Eh gashi nan komai na jera mishi yanzu fruits kawai zan yanka sai a had'a ko" kiss kawai Habiba ta manna mata a goshi kafin tayi wurin mamin su


  "Mami kiga nayi kyau" sosai ma yar mami kin fito abinki tsaf ina fatan dai Heedaya ta gama shirya komai" eh ta bata amsa "toh ai itama tazo tayi wanka tunda ta gama"to mami bari na kirata" haka ko tayi kitchen dan kiran ta amma me batanan lekawan da zatayi tajiyo hayaniyan ta a waje da hanzari ta karasa wurin


  "Heedaya lafiyan ki daya kuwa mai kuma ya hadak'u"


  "Adda Habi wai fa kawai nafito zan zubar da shara shine wanan banzar yarinyar ta watsa min ruwa ashe uwarta na ganin mu dan na mata magana shine suka hayayako min dukkan su"


  "Ke dan ubanki har zaki yi wani magana to bari nai maganin ki inyaso uwarki ta fito sai ta shigar miki nan fa sukayi kanta ga Habiba sai faman kiran mami take jin kiran yasata fitowa,


  "Inalillahi ke Heedaya mai kike shirin aikatawa haka iyye " me zakiyi da kujeran"


  "Haba mami ya d'aga fitowana kawai Rahina ta zuba min ruwa d'aga magana kuma suka fara balbaleni da bala'i harda wai uwata tayi miye dinta oho"


  "To kiyi hakuri kinji kinga lokaci yana wucewa maza wuce ki shirya Habiba ku wuce mu tafi"


"Shegu dangin munafukai a haka zaku kare matsiyata wanda basu gada arziki ba woo uwa da yarta suka shiga ihu"


  "Mami kinji abinda suke fad'a ko" Heedaya kiyi hak'uri mu tafi" dakin suka koma yanda ta saki kuka da kyar suka lallabata tayi shiru sanan tayi wanka itama, misalin karfe 8 baban su ya dawo a sallah Habiba ke fad'a mishi yau Ahmad zai zo fatan alkhairi yay musu sanan ta tafi kaya iri saya suka saka abinsu kamar yan biyu idan ka gansu dole su baka sha'awa karfe 8:15 Ahmad ya iso gidan.
Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€        πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

               ❤❤ 

                  πŸŽ€


        *MATAR UBA*


     

      *By Miss_ayusha*
*🌈Kainuwa writers asso🀝*

    

            3⃣&4⃣"Heedaya ki tashi dan Allah ki tashi kawai ki kira anty amina kinga jikin mami yana ta tsanan ta"+


"Wai dan Allah adda Habi kamar baki san halin matar nan ba yanzu ko na kirata kinsan bazata zo ba"

  "Dan Allah ki jarraba watakil yau taji tausayin mu tazo tunda baba bayanan" to kawai ta amsa mata,

  "Assalamu alaikum,  ko amsa sallamar bata yi ba tace miye, mayya maiya kawoki d'aki na a wannan lokacin,

  "Anty dan Allah ki taimaka jikin mamin mu ne yayi tsanani ki taimaka mu kaita asibiti"

  "Kaji zancan banza zancan hofi da Allah fitamin a d'aki ta mutu mana miye nawa a ciki gwara ku nemo wanda zai kaita bani ba shashasha kawai"fita kawai tayi tana jin tsanar matar uban ta har cikin ranta, direct waje ta nufa auwal ta tarar a kofan shagon shi hakan yasa ta karasawa wurin shi,

  "Auwal dan Allah ka taimaka mukai mamin mu asibiti baban mu bayanan ga anty amina tak'i saurarana ma"


  "To shikenan maza ki shiga ku fito da ita" da hanzari ta karasa cikin gidan,

  "Adda habi ga Auwal a waje na jiran mu" d'agata sukayi da kyar suka fita da ita motan shi suka kalla a wurin hakan yasa su shiga da ita cikin motan Habiba na gaba sai Heedaya dake tare da mamin su basu tsaya ko ina ba sai GIWA HOSPITAL emergency akayi da ita yayin da suka zauna zaman jiran su dan likitoci sun dukufa a kanta,

   "Heedaya ga waya kira mana Baba yasan halin da ake ciki" wayan ta karba yanda tayi dialing numbern Baban su bugu biyu ya dauka, murya a rikice take magana


  "Baba muna asibiti jikin mama yayi tsanani" d'aga d'ayan b'angaran inalillahi ya shiga ambato "wani asibiti ne mamana" ya tambaya "Giwa Hospital" ganinan zuwa kawai yace kafin ya kashe waya, cikin d'akin likitoci sun bazama a kanta domin ceto rayuwar ta bugun zuciyar ta ya tsanan ta numfashin ta sama sama yake su kansu sun rasa mai zasu mata,


  "Doctor Amir bai kamata mu tsaya kuma ba kamata yayi mu sami wanda suka kawo ta dole sai an sa mata oxygen" sunyi na'am da maganar haka kuwa sukai waje yayi dai dai da isowar Baban su,


  "Doctor tsalha yan mata ina mahaifin ku?" A tare suka nuna Baban su

  "Alhaji ya zama dole sai an saka wa matar ka oxygen dan akwai matsala" Doctor kar a b'ata lokaci kuyi abinda ya kamata cikin d'akin suka koma inda suka saita komai kafin nan aka sa mata,

  "Abba dan Allah ya kace a saka mata oxygen"


  "Habiba ya zama dole tunda suka ce a saka mata hakan ya dace" suna cikin wanan maganr Dr Amir ya fito "Alhaji matar ka na bukatar ganin ka da yaran ta"da gaggawa sukayi cikin d'akin hanun ta gam suka rike,

  "Mami gamunan a gefen ki" ita din ma hannun su ta rike tare da na mijin ta,

  "Alhaji ku saurari abinda zan fad'a muku, " Habiba" na'am mami "ga Heedaya nan ki kula da ita kicigaba da hak'uri da halin ta sanan abu na biyu ina so ku cigaba da hak'urin zama da matar baban ku duk wani abinda zata muku hak'uri shine maganin shi, ke kuma Heedaya nasan halin ki na rashin hak'uri abinda nake son ki sani shine ki daure hak'urin nan shine maganin zaman duniya kinaji " mami dan girman Allah ki daina haka cuta ba mutuwa bace insha Allah zaki tashi,

  "Alhaji ga yarana nan dan Allah ka kular min dasu ka kare min mutuncin su banason wani mugun abu ya same su sanan ka cigaba da hak'urin zama da Rakiya nasan ko ba dade zata gane abinda take ba dai dai bane"


  "Murja banaso kina irin wanan maganganun da izinin Allah zaki tashi mu cigaba da rayuwar mu kamar yadda muka saba" hannuwan su tsaf ta had'e akan kirjinta ta daura su kafin kace me tuni ta fara salati nan ubangiji ya karbi abinsa iya rikice sun rikice da gudu Heedaya ta fita kiran Dr, Dr Amir ne kawai a wurin hakan yasa ta kasa magana sai jikin shi kawai data fad'a,

"Baiwar Allah" bata jira wani magana nashi ba take nuna masa kofar d'akin hakan yasa shi gane mai take nufi janyeta yayi ya rike hannun ta yanda suka nufa d'akin da hanzari ya nufa wurin mamin su nan ya tabbatar musu da cewa ta mutu wani uban ihu Habiba ta saki kafin tayi k'asa a zube da sauri nurses din suka dauke ta aka nufa wani d'akin da ita ita kuwa Heedaya sandarewa kawai tayi a wurin sai da suka zaunar da ita sanan baban su karfin hali kawai yakeyi kafin kace me yan uwa duk sun dauka Murja ta rasu tuni aka cika gidan fam da koke koke ga Habiba datake kwance, gawar aka tafi da ita domin a suturtata ya rage saura Heedaya da kanin baban ta dayake wurin Habiba, bayan mintuna Habiba ta bud'e ido a gadon asibiti sunan mami kawai take ambato nan dai uncle din nata yasa su a mota sukayi gida wanda Heedaya ko a batacewa sai dai ruwan hawaye dahaka suka kai gida.


Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€        πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

              ❤❤

                 πŸŽ€


         *MATAR UBA*
  *Story and written by*


        *Miss_ayusha**🌈Kainuwa writer's asso🀝*            5⃣&6⃣
Sanda suka kai gida a cike suka sami gidan hakan ya k'ara tabbatar musu da lallai Mamin su ta rasu yan uwan ta suka gani hakan yasa aka zaunar dasu a wurin banda kuka babu abinda sukeyi, an kammala suturta gawa yanda aka bukaci suyi mata addu'a akan gawar suka tsaya tuni suka zube k'asa suna wani mugun kuka addu'a ma kasa wa sukayi sai rungume gawar ma da sukayi suna kuka, shi kanshi baban su kukan yakeyi balle ya rarrashe su ganin zasu b'ata lokaci wani bappahn su ya janye su a wurin suka zauna dabas kamar ransu zai fita suma, da haka aka kai mamin su mak'wancin ta na gaskiya suko karban gaisuwa suka cigaba dayi duk wanda yaga Heedaya da Habiba sai ya tausaya musu bama 'ya Habiba gwanin tausayi basu ci basu sha sun zama kamar kurame ta b'angaran baban nasu shima hakan ne,

+

Sauran 'yan uwa basu tafi ba sai da akayi addu'an bakwai sanan gidan ya watse, yayar mamin su Hajiya Aina'u babu yadda bata yi ba ko mutum d'aya a bata amma baban su ya hana dan yadda yake jin yaran a zuciyar shi abin ba'a iya cewa komai, tunda ake karban gaisuwa Murja da 'yar ta suka kaura gidan gaba daya suka bari sai da akayi bakwai ne sanan suka dawo,1

  "Alhaji Alhaji"sai da tayi kira biyu kafin ya firgita ya san da wata a kanshi "Murja lafiya dai ko" aifa dole ka tambaye ni lafiya ka tara yara sai kace wanda daga kanku aka fara yiwa mutuwa to ka taso ina son magana da kai" wani magana ne da baza muyi ta anan ba, indai bazaki fad'e ta anan ba to ki bace min dagani mara hankali kawai"lallai Alhaji wato tunda wanan b'aka mai bak'in aniyar ta rasu ka wani sakalo da mugun hali toh ai bazaka burge ni ba har sai sanda ka dawo da ita duniya,ire ire sunata gaba dama sun addabi jama'a,  Heedaya kallon Habiba kawai takeyi da idonta ya kad'a yayi ja ina bazata iya jure wanan mugayan maganganun ba tsaye ta mike kamar mai shirin dambe,

"Ke Murja kike da suna kowa toh albishirin ki in baki sani ba yau kisani, kar ki manta mamin mu ta samu kyawawan shedu kuma shedar duniya itace ta lahira, ke bakida labarin bayin Allah ne suke tafiya yanzu ai duk wani mara imani mai bak'ar zuciya sai ya jira tashi tazo muji ko za'a samu shedu kamar na mamin mu"


  "Ke Heedaya nice mai bak'ar zuciyar"zata sake magana Habiba tajawo ta "haba Heedaya yanzu har kin manta abinda mamin mu ta fad'a mana"Adda Habiba ban manta ba zan iya jure komai a cikin gidan nan amma banda abu biyu

Na farko naga ana zagin mamina ana muzan tata da mugayan kalamai,na biyu bazan taba bari a gabana wata banza tace zata zagar min babana dan nasan darajar shi watakil ita bata san nata ba" Heedaya har abin naki ya kai da zagi dago hannun ta ke da wuya zata mareta taji an rike shi gam,


  "Ke wace irin dabbar matace yanzu da har zaki daga hannun ki dake ta Murja maiyasa halin ki bazai canza ba maiyasa a koda yaushe kike san b'ata min rai, gaskiya da mahaifiyata tasan abinda zan tarar a auran ki da bata matsa na aure ki ba amma kowa da kaddarar shi na tawa a kanki ne, to inaso ki sani duk wani abu daza kiyi a gidan nan kada ki kuskura kice zaki dakesu dan zakiga fushi na, Habiba ku tashi mu tafi" a wurin suka barta tana ta banbamin da ruga zagi ko kala ba wanda yace mata a cikin su,

Kuka kawai takeyi yau mutuwar mamin ta sabuwa ta dawo mata,

"Mami maiyasa kika tafi kika barmu a irin wanan rayuwar maiyasa mutuwa baki had'a dani ba" haba Adda Habi yanzu dan Allah maiyasa kike haka idan mutuwar ta daukeki ni kadai zan zauna kenan a wanan kuntaciyar duniyar dan Allah ki daina fad'in haka, da kyar suka lallame ta tayi shiru daganan bacci yayi gaba da ita,


  "Babana dan allah kayi hak'urin abinda na aikata dazu" Heedaya

dole zakiji ba dadi akan maganar da take fad'a amma inaso ki dinga kai zuciyar ki nesa kinaji" eh abba "Allah ya muku albarka" amin ta amsa shi abinci kawai ta shiga daura musu dan tasan mahaifin nata bazai wuce jin yunwa ba. 
Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

          

        *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€  *Story and written by*


        *Miss_ayusha**🌈Kainuwa writer's asso🀝*           7⃣&8⃣
Sanda suka kai gida a cike suka sami gidan hakan ya k'ara tabbatar musu da lallai Mamin su ta rasu yan uwan ta suka gani hakan yasa aka zaunar dasu a wurin banda kuka babu abinda sukeyi, an kammala suturta gawa yanda aka bukaci suyi mata addu'a akan gawar suka tsaya tuni suka zube k'asa suna wani mugun kuka addu'a ma kasa wa sukayi sai rungume gawar ma da sukayi suna kuka, shi kanshi baban su kukan yakeyi balle ya rarrashe su ganin zasu b'ata lokaci wani bappahn su ya janye su a wurin suka zauna dabas kamar ransu zai fita suma, da haka aka kai mamin su mak'wancin ta na gaskiya suko karban gaisuwa suka cigaba dayi duk wanda yaga Heedaya da Habiba sai ya tausaya musu bama 'ya Habiba gwanin tausayi basu ci basu sha sun zama kamar kurame ta b'angaran baban nasu shima hakan ne,

+

Sauran 'yan uwa basu tafi ba sai da akayi addu'an bakwai sanan gidan ya watse, yayar mamin su Hajiya Aina'u babu yadda bata yi ba ko mutum d'aya a bata amma baban su ya hana dan yadda yake jin yaran a zuciyar shi abin ba'a iya cewa komai, tunda ake karban gaisuwa Murja da 'yar ta suka kaura gidan gaba daya suka bari sai da akayi bakwai ne sanan suka dawo,

  "Alhaji Alhaji"sai da tayi kira biyu kafin ya firgita ya san da wata a kanshi "Rakiya lafiya dai ko" aifa dole ka tambaye ni lafiya ka tara yara sai kace wanda daga kanku aka fara yiwa mutuwa to ka taso ina son magana da kai" wani magana ne da baza muyi ta anan ba, indai bazaki fad'e ta anan ba to ki bace min dagani mara hankali kawai"lallai Alhaji wato tunda wanan b'aka mai bak'in aniyar ta rasu ka wani sakalo da mugun hali toh ai bazaka burge ni ba har sai sanda ka dawo da ita duniya,ire ire sunata gaba dama sun addabi jama'a,  Heedaya kallon Habiba kawai takeyi da idonta ya kad'a yayi ja ina bazata iya jure wanan mugayan maganganun ba tsaye ta mike kamar mai shirin dambe,

"Ke Rakiya kike da suna kowa toh albishirin ki in baki sani ba yau kisani, kar ki manta mamin mu ta samu kyawawan shedu kuma shedar duniya itace ta lahira, ke bakida labarin bayin Allah ne suke tafiya yanzu ai duk wani mara imani mai bak'ar zuciya sai ya jira tashi tazo muji ko za'a samu shedu kamar na mamin mu"


  "Ke Heedaya nice mai bak'ar zuciyar"zata sake magana Habiba tajawo ta "haba Heedaya yanzu har kin manta abinda mamin mu ta fad'a mana"Adda Habiba ban manta ba zan iya jure komai a cikin gidan nan amma banda abu biyu

Na farko naga ana zagin mamina ana muzan tata da mugayan kalamai,na biyu bazan taba bari a gabana wata banza tace zata zagar min babana dan nasan darajar shi watakil ita bata san nata ba" Heedaya har abin naki ya kai da zagi dago hannun ta ke da wuya zata mareta taji an rike shi gam,


  "Ke wace irin dabbar matace yanzu da har zaki daga hannun ki dake ta Rakiya maiyasa halin ki bazai canza ba maiyasa a koda yaushe kike san b'ata min rai, gaskiya da mahaifiyata tasan abinda zan tarar a auran ki da bata matsa na aure ki ba amma kowa da kaddarar shi na tawa a kanki ne, to inaso ki sani duk wani abu daza kiyi a gidan nan kada ki kuskura kice zaki dakesu dan zakiga fushi na, Habiba ku tashi mu tafi" a wurin suka barta tana ta banbamin da ruga zagi ko kala ba wanda yace mata a cikin su,

Kuka kawai takeyi yau mutuwar mamin ta sabuwa ta dawo mata,

"Mami maiyasa kika tafi kika barmu a irin wanan rayuwar maiyasa mutuwa baki had'a dani ba" haba Adda Habi yanzu dan Allah maiyasa kike haka idan mutuwar ta daukeki ni kadai zan zauna kenan a wanan kuntaciyar duniyar dan Allah ki daina fad'in haka, da kyar suka lallame ta tayi shiru daganan bacci yayi gaba da ita,


  "Babana dan allah kayi hak'urin abinda na aikata dazu" Heedaya

dole zakiji ba dadi akan maganar da take fad'a amma inaso ki dinga kai zuciyar ki nesa kinaji" eh abba "Allah ya muku albarka" amin ta amsa shi abinci kawai ta shiga daura musu dan tasan mahaifin nata bazai wuce jin yunwa ba. 
Miss_ayushaπŸ’‹

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€        πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
               ❤❤
                  πŸŽ€

         *MATAR UBA*

*By Miss_ayusha*

*🌈Kainuwa writer's asso🀝asso🀝*

             9⃣&1⃣0⃣

Kitchen Heedaya ta shiga yanda ta daura musu cous cous da vegetable soup tana kan aikin ne Rakiya ta shigo kitchen din+

  "Ke Heedaya ina fatan dai abincin harda mu kike dafawa saboda Rahina batanan"

  "Sai ki jira ta dawo idan ta dawo zata girka muku amma ba girkin Heedaya zakici ba"

  "Heedaya wa ni kike fad'awa magana saboda ubanki ya daure maki gindin yin abinda kika ga dama to wallahi ki shiga hankalin ki"bata ce komai ba ta rab'a gefenta tai wuce war ta,d'akin su ta shiga jin wayan Addan ta yana ringing ta duba nan kuwa taga Ahmad ne da hanzarin ta ta dauka.
  "Ya Ahmad" na'am Heedaya" ina yini" lafiya kalau ya k'arin hak'uri" alhamdulillahi tace" ina mutumiyar tawa" tana bacci shine amsan data bashi toh ki ce mata ina nan zuwa da yamma ko harda Maryam zamu zo nan tace Allan ya kawo su lafiya sannan ta kashe wayan.kitchen ta koma ruwan girkin ta kara dan harsu zata girka ita bazata iya wani sabon abinci ba anjima haka tayi abincin ta tsaf hankalinta kwance sai mugun ramar datayi kamar ba ita ba d'akin Abban su takai mishi nashi yanda ta ajiye a gefen shi.

  "Abba ga abincin ya sauka" to Heedaya ubangiji Allah ya miki albarka" amin tace dashi .
GIWA HOSPITAL

Tun ranar da su Heedaya suka bar asibiti Dr Amir yake bin duk yadda zaiyi ya sake ganin ta amma bai san ta ina zai fara ba abokin shi ya samu akan suyi magana.

"Aboki dan Allah shin ba wani taimakon da zaka min akan wannan yaran da maman su ta rasu"

  "Dr bansan abinyi ba amma akwai abu d'aya muje cikin file dinsu ko Allah zaisa mu sami numbern wani daga cikin su" haka ko sukayi yanda suka bi file din alhamdulillahi Dr tsalha yace sanda yayi arba da wata number.

   "Aboki ga wata number matsala bamu san numbern waye a cikin su ba"

  "Aboki ai kawai kira zamuyi idan mukaji numbern namiji ne sai mu kashe" da haka suka kira wannan numbern.

  Tana zaune ga hoton Mamin su data saka a gaba tana gani hawaye na zuba a idonta taji wayan Habiba na k'ara ganin sabon number ne yasa taki d'auka sai da akayi kira biyu sannan ta dauka shiru tayi sanda taji anyi magana tukun itama ta amsa

"Dawa nake magana"

"Kina magana da Dr Tsalha"
  "Ayya mai wayan tana bacci sai in ta tashi zan fad'a mata"

  "A'a tsaya kiji bakune wanda kuka kawo maman ku asibitin giwa ba" eh mune" so dan Allah in bazaki damu ba inason ki mana kwataccen gidan ku zamuyi wa Abban ki ta'aziya ne"

  "Gidan mu yana kinkinau wurin masallacin algark'awi"ohk to shikenan sai kinji mu kit ta kashe wayan.

  "Heedaya kedawa kike waya haka?" Hmm wai Dr Tsalha wanda suka karbi Mami a asibiti zasuyi ma Abba ta'aziya ne"Allah sarki sai sunzo.

"Heedaya yunwa nakeji kin dafa mana abinci kuwa"

"eh tun dazu ke nake jira ai ki tashi muci kuma Ya Ahmad ma ya kira ki yana zuwa anjima kinji"to ta amsa mishi.

  Toilet fa fad'a tayo brush sannan ta fito suka ci abinci kafin sukayi d'akin Abban su.

"Abba" na'am Habiba yau Ya Ahmad zai zo toh Allah ya kawo shi lafiya amin ta amsa"

"Habiba kinga lokacin bikin ku bai wuce saura 2 weeks ba dan haka ni inaganin zaki koma gidan Aina'u ko Zainabu in yaso duk abinda ya kamata kuyi kwayi a can ko"

  "Toh Abba"akwai kuma Dr da suka duba mami sanda muka kaita asibiti sunce zasu zo maka ta'aziya" a'a to dama sunada numbern kine, a'a abba inaji dai a file din mu suka dauka toh Allah ya kawo su lafiya Amin dukka suka amsa mishi.

  "Heedaya maza kije ki kiramun Rahina"da toh ta amsa yanda tayi d'akin su Rahina sanda taje Maman ta kawai ta gani da kawarta Falmata.

  "Anti Rahina tazo inji Abba"

  "Badai wani munafurcin aka sake kitsawa ba dai dan nasan hali ansha a nono"hmm kawai tace sannan tayi waje.

  "Ke Rahina ki fito Abban ku na kiran ki"daga ita said leggings red dawani blue body hug a jikin ta tayi wurin Abban nasu ko sallama batay ba balle tace dasu sannu wuri kawai ta samu ta make ba abinda yay mata zafi.

  "Abba gani"

"Rahina inaso ki bani nutsuwarki nan ki ban hankalin ki, kinsan mai nake so dake" kai kawai ta girgiza
"Kinga bikin Habiba ya matso kuma ko ba komai 'yan uwanki ne abinda nake so dake dan Allah ku hada kanku kinji uwata duk wannan fitinan ku bar yinta kinaji" eh Abba insha allah ubangiji Allah yay muku albarka amin suka amsa dukkan su.Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


       *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€*By Miss_ayusha*


*🌈Kainuwa writer's asso🀝*           1⃣1⃣&1⃣2⃣Rahina d'akin maman ta ta koma yanda ta tarar Falmata ta tafi kawai kan kujerar tayi kwanciyarta a kai.+


  "Ke me Abban naku yace miki"


  "Mama kawai cemin yayi mu had'a kanmu bikin Habiba ya matso duk rigimar da mukeyi mu daina"


  "Ohh wato sun sake had'a wani abunko zasuyi bayani tashi mu shiga kitchen"


  "Mama dan Allah kije kinga abu nakeyi a wayana fa"


  "Allah ya shirya min ke" shine kawai abinda maman ta tace.


B'angaran su Habiba suna d'akin Abban su sai hirar su suke sha kiran sallah la'asar ne ya tashe su domin yin sallah.

  Misalin karfe 4:30 Ahmad da Maryam suka zo gidan wai zo kaga murna wurin su Heedaya duk wani b'acin rai jin shi takeyi ya kau nan fa suka zauna zaman hira shiko Ahmad ya tafi domin gaishe da Abban su a cikin d'akin ya same shi kamar yadda ya saba har k'asa ya kai sannan ya gaishe shi kafin kuma ya fita wurin su Maryam ya koma yadda yake tambayar su ina Habiba take kafin ya rufe b'aki ta fito.

  "Habibi gani nan"


  "To ai naga kink'i fitowa ne ina ce sai mun shiga mun dauko ki" dariya kawai tayi kafin suka zauna.


  "Princess me kike buk'ata na bikin"


  "Nikam ba komai dan babu abinda zanyi" bai matsa mata ba dan yasan har yanzu bata bama warwarewa ba.


  "Shikenan kawai yace da ita"nan fa suka hau hira shewar su duk ta cika gid'an kamar wadda ake wani hidima"


Tana cikin kitchen fa taji abun ba mai k'arewa bane hakan yasa ta fitowa direct d'akin su Habiba tayi dan a ciki takejin wannan hayaniyar.


"Ke Habiba wai bakuda hankali ne ya kuke son mayar mana da gida kaman gidan 'yan iska kun cika mutane da hayaniya kawai"


  "Anti kiyi hak'uri" wani uban tsuka taja sanan tayi waje


  "Lallai ma wannan matar akwai 'yar rainin hankali wallahi"


  "Ke dai Maryam haka muke fama da ita" Allah ya kyauta tace sannan suka cigaba da harkan su.

   Sun jima a gidan sosai kafin Ahmad yace da Maryam su tafi haka dai ba da san junan su suka tafi ba bayan tafiyar su ne Dr Tsalha suka zo kiran wayan dazusukayi sanar dasu kan cewa sunzo shiyasa su nufa wurin Abban su.


"Abba wai su Dr din sunzo"Kuje ku shigo da su hakan ko sukayi a tare duk suka fita a bak'in gate din suka gansu.


"Sannunku da zuwa"


"Yawwa" suka amsa wanda Dr Amir ya k'asa dauke idon shi daga kallon Heedaya da take ita kanta duk ta takure wuri daya saboda kallo.


  "Zaku iya shigowa" abinda ya katse kallon nashi kenan.


Jagora sukai musu har d'akin Abban su.


  "Alhaji ina wuni"


"Lafiya kalau"ya aikin naku?"Alhamdulillah suka amsa, ya kuma karin hak'uri alhamdulillah suka amsa duk gaba dayan su ubangiji Allah yay mata rahama amin suka amsa.


  Tuni fuskar Heedaya ta fara zubar da kwallah dama gwanar kuka ce ita bare abin nema ya samu.


  Abban su ne ya ganta hakan yasa shi kiran ta kusan shi ta koma yadd ta daura kanta a kan kafadar shi.


"Mamana miye amfanin kukan yanzu kuma ba na hanaki ba duk sanda kika tunota addu'a zakiyi ba kuka ba hakan ne zai tabbatar da son da kike mata kinji" kai take girgizawa dan hawayen ta yak'i tsayawa har itama idon Habiba ya fara kawo ruwa da kyar Heedaya tayi shiru kafin su Dr suce zasu tafi, maza ku tashi kuyi musu rakiya ko toh suka amsa.


  "Angode sosai ubangiji Allah yayi albarka Allah ya bada lada" amin sh Dr suka amsa mishi.


Har wajen motar su suka rakasu tare da musu godiya.


  "Pls Heedaya in bazaki damu ba ki bani number naki mana sai mu dinga gaisawa ko, kallon Addan tatayi alamu tai musu da ta bashi haka kam ta rubuta mishi contact nata a cikin wayan shi nan yay godiya suka tafi suma cikin gidan sukayi.

"Kai Dr yanzu tayaya zaka fara bullo mata dan naga yarinyar kamar zatayi rigima"


  "Tsalha kar ka damu ni nasan ta yadda zan fara kuma in Allah ya yarda sai ta zama matata"

  "Allah ya yarda amma dai kar ka boye mata kana da mata a duk abinda zakayi"


  "Insha Allah"da haka dai suka karasa yanda Tsalha ya sauki Dr Amir a kofar gidan shi sannan ya nufi gida shima.


Alhamdulillahi duk shirin dasu Habiba zasuyi sun gama shi Abban su kawai suke jira danshi zai kaisu gidan Anti Aina'u aiko sai gashi ya fito boot ya bude musu suka loda kayan su ciki.

  "Kunyi wa Antin ku sallama kuwa"a'a to maza kuje kuyi mata.


Cikin d'akin ta suka shiga tarar d ita tana share d'akin ga Rahina kawai tana kwance tana kallo.


  "Anti munzo miki sallama ne zamu tafi gidan Anti Aina'u"


  "Da Allah ku fita kuban wuri munafukan banza da wofi kawai 'ya'yan banza ku wuce ku ban wuri" kak kawai suka girgiza suka koma wurin Abban su.


  Habiba na gaba sai Heedaya a baya suna tafe sai hira suke abin sha'awa.


  "Yarana zanyi missing dinku fa"


  "Abba ai muma zamuyi missing dinka zan dinga zuwa kaji Abbana"to Mamana da haka har suka isa gidan suna hira.

  Munnira ce ta fara ganin su hakan yasata kwala ihu oyoyo gasu Adda Habiba tuni yaran gidan suka fito da  kyar suka barsu suka shiga.

"Alhaji Hamza yau kaine gidan namu" eh Aina'u ya muka sameku lafiya kalau wallahi to masha Allah.


  "To ga dai 'ya'yan ki sun taho tunda bikin Habiba ya matso shiyasa na tattaro su nakawo miki su" wallahi kamar kasanj nima dazu nake maganar akan zanje gidan na taho dasu tunda uwa Allah ya karbi abinsa" Allah sarki gashi na huta sar dake"bunch na 1000 guda biyu ya dauko sannan yay musu sallama akan zai tafi har bakin motar sukaje suna daga mishi hannu  sannan suka koma cikin gidan.
Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

            

           *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*By Miss_ayusha**🌈Kainuwa writer's asso🀝*            1⃣3⃣&1⃣4⃣
Cikin gidan suka koma zama sukayi dukkan su yanda suka hau hira


  "Adda Habiba ina Ya Ahmad ne" cewar Nabila


  "Ah kaji min yarinya bakina da wayan shi ba sai ki kira shi ai" dariya dukkan su suka saka.


  "Adda Heedaya yakamata muje gidan su Jalila mu kai musu invitation card fa ko baza ayi komai ba ai za ayi walima dai kam"


  "Hakane"cewar Heedaya


Da gudo ya shigo d'akin yana kiran Adda Habiba.


  "Khalil ya akayi ne haka"


  "Kizo Ammi na kiran ki" tare suka tafi wurin Ammin nasu.


  "Anti gani" yawwa Habiba zauna kinji zaman kuwa tayi kusa da ita.


  "Habiba babu abinda zakiyi na bikin ne" eh Anti ni banason yin komai"


  "To shikenan ki shirya anjima Batula mai gyara jiki zata zo zaku fara kinji"eh ta amsa mata zaki iya tafiya wurin su Munnira ta koma banda shewa babu abinda ke tashi a cikin d'akin.

Bayan sallah isha'i duk suna zaune a parlo banda Habiba da take d'aki tana waya Batula ta iso gidan nan suka gaisa da Ammin su Khalil kiran Habiba ta aika ayi sanda sukaje ta gama wayar kenan tare suka fito.


"Habiba ga Batula nan tazo duk abinda ya kamata tai miki zatayi kinji toh ta amsa mata dahaka dai suka shige d'aki.


Washe gari aka fara gyaran Habiba inda su Munnira da Heedaya sun bazama gidan kawaye don kai musu invitation card suna hanya wayan Heedaya ya shiga k'ara bata bi ta kan wayar ba saboda ba suna sai number haka kawai ta barshi da niyar idan sun sauka zata kira.


  Sanda suka kai gidan su Jalila basu wani dade ba sukayi gidan su Adama da Bilki sauran catin suka bar musu akan su bawa sauran kawayen nasu da haka sukayi sallama sai gida dan suna da abinyi dayawa.


A gajiye likis suka koma gida ko minti batayi da zama ba sai ga kiran Abban su da azamanta ta dauka.


  "Abbana" na'am Mamana ya kuke?" Abbana muna lafiya ya gida yasu Anti da Rahina" duk suna lafiya Mamana ina fatan bakuda wata matsala ko eh Abba bamu da komai,yayi kyau bani"Habiba da gudu ta ruga ta kai mata.


  "Abba"na'am Habiba ya kike?" Abba ina lafiya ya kowa na gida duk suna lafiya" bakuda matsala ko eh ta bashi amsa to Allah ya muku albarka amin ta amsa nan sukayi sallama.


Wani kiran ne ya sake shigowa wayan ta tana b'ata fuska ta d'auka dan tuntuni ake kiran ta.


"Hello"


"Hi ya kike?"


"Ina lafiya lau"


"Kina magana da Dr Amir"


  "Allah sarki ya gida ya aiki?" Lafiya sai godiya to masha Allah.


  "Heedaya pls inason zamuyi wata magana"


"To amma kaga yanzu bana gida muna gidan Antin mu"


  "Bazaki iya mun kwatancan ba"


  "Unguwan sunusi Prp"owk idan nazo zan kira ki to shikenan da haka sukayi sallama.


Gida fa ya taru makil kannan Ahmad duk sun dawo gidan Aina'u 'yan uwa dadi Heedaya da Habiba dukwani b'acin ransu ya kau da fitinar Matar Ubansu.


B'angaran amarya idan kaga Habiba masha Allah abin sai wanda ya gani babu yadda Ahmad baiyi akan a bari yaga Habiba amma ankj sai dai waya harta Maman Ahmad ta dawo gidan Yayar tata ga 'yan uwan Abban su da ba'a barsu a baya ba su kansu sun bada gudu mawa dan duk abinda akeyi tare dasu ake.


  Yau takama Alhamis tunda suka tashi ake gyaran gidan basu da wani lokacin hutu masu yin lalle nayi masu kitso nayi kowa da abinda yakeyi.


Misalin karfe 4 na yamma Dr Amir ya kira Heedaya akan yazo unguwar hijabin ta kawai ta zura tayi waje da sallama a bakin ta ta karasa wurin shi.


  "Ina yini"


  "Lafiya klau Heedaya ya kike ya gidan?" Lafiya lau ina yayar taki?" Tana cikin gida ohh bazata fito mu gaisa ba" kasan amarya ce ba lallai su barta ta fito ba"au kice hidima kukeyi" wallahi fa shine ko gayyata babu"hmm kawai ta iya ce mishi.


  "To ubangiji Allah ya b'ada zaman lafiya"amin ta amsa mishi.

  "Heedaya in bazaki damu ba akwai wani important magana da nake so muyi dake pls"


  "Ehen inajin ka"


  Nan fa ya fara suburbuda zance ta inda yake shiga ba nan yake fita ba har ya kai aya.


  "To fa" pls Heedaya karkiyi rejecting d'ina hannun shi biyu ya hada wuri d'aya alamun yana rokon ta"


  "Kar ka damu bakomai Allah ya sa tarraya ta dakai alkhairi ne"


  "Alhamdulillahi gaskiya na gode sosai bani da bakin godiya a gareki"


  "Bakomai" tace dashi nan dai yayi mata sallama ya tafi itama ta koma gida.

Washe gari takama friday ranar walima kenan amarya ta hadu iya haduwa gown ta saka na wani pink material mai ratsin ash a jiki idan kaga Habiba bazaka gane itace ba.


  Arewa house angama decorating dukka wurin walima komai dasu tanada sun ajiye shi nan kuma fa 'yan kaisu walima aka tartafi yanda Malama Juwairiya tafara wa'azi mai ratsa jiki dan ya shiga mutane kusan magriba aka watse a wurin walimar.

   "Washe gari ta kama Asabar ranar bata k'arya yau ne ranar da za'a dauran auran Habiba Hamza da angonta Ahmad Hussaini yanda dunbin mutane suka hallarci wannan bikin bakin uban amarya yak'i rufowa kamar gonar auduga 'yan san barka sai zuwa masa akeyi haka dai aka gama taron daurin aure lafiya.


  B'angaran Habiba tunda taji an daura aure ta saki kuka ga Heedaya ma data mara mata baya kuka sukeyi kamar wanda mutuwa zata d'auki d'ayan su da kyar dai aka lallaba su sukayi shiru.


  Misalin karfe 5 'yan daukan amarya suka hallaro ga Abban amarya na jiran har cikin d'akin da Abban nata yake aka rakasu sosai yayi mata nasiha mai ratsa jiki sai kuka har taso ta saka shi kukan shima da kyar aka rabata da mahaifin nata suma b'angaran mata both yan uwan Mamin ta da Abban ta sun mata fad'a sosai ita haka dai suka sakata a mota yanda aka nufi gidan ta dake unguwar rimi.Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


       *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*By Miss_ayusha*

*🌈Kainuwa writer's asso🀝*         1⃣5⃣&1⃣6⃣

Kuyi hak'uri jina shiru da kukayi wallahi school ta sani gaba ga abubuwa sunyi yawa amma da komai yayi dai dai zaku riga jina.

+

  Gid'an amarya yayi kyau 'yan kai amarya sai san barka sukeyi itako banda kuka babu abinda takeyi yau ga ranar da Mamin su taci buri ta gani amma babu ita a wannan lokaci nan fa rasuwar mahaifiyar tata ta dawo mata sabuwa itama Heedaya ba'a barta a baya ba ganin zata rabu da yayarta gashi Matar Ubansu ba kaunar su take ba wannan abu idan ta tuna yana d'aga mata hankali.

Misalin karfe 8 na dare Ahmad da abokan shi suka iso gidan sosai sukai musu nasiha kafin abokan su tafi da sauran kawayen amarya an bar d'aga amarya sai angonta.

Kulle dukka kofofin gidan yayi kafin nan ya dawo yanda ya barta a haka ya sameta umartan ta yayi akan taje tayo alwala suyi sallah tashi tayi kirjinta na bugun uku uku sai da tafara wanka kafin tayo alwala turarukan da Antyn ta ta bata kuwa ta feshi dukka jikin ta dasu kafin kace me har ya dawo cikin d'akin abin sallah ya shimfida musu nan kuwa ya jasu sallah ya dade yana musu addu'a sannan ya matso da abinda ya shigo dashi.


  A cup ya tsiyaya mata sannan ya zuba nashi.


  "Gimbiya sarautar mata bismillah ko" nok'e kafada tayi alamun a'a murmushi kawai yayi da kanshi ya shiga bata tana ci sai da ta koshi sannan yaci nashi shidin ma sai da ya koshi ya tattara su a gefe tana gado can karshe haka ya hau shima tuni ya kashe musu wuta tattara kafana nayi nay waje na basu wuri.


Su Heedaya an koma gida duk kewar 'yar uwarta ya isheta Allah Allah take gari ya waye taje ta ganta.


Washe gari misalin karfe 10 taci ado atampan ta mai purple color ta saka bata yi wani havy makeup ba amma tayi bal'in kyau.


  "Babynah Allah miki albarka" jawota jikin shi yayi yayin da ta amsa mishi da amin maganganun jiya kawai yake tunanowa.


  "Wayyo ya Ahmad zan mutu kay hak'uri bazan iya ba" bugun wasa tai mishi tare da rufe fuskarta.


  "Kaga wallahi kadaina bana so"


  "To zo kiji wani magana"


  Kusan shi ta zauna batayi auni ba ya cafke bakin ta yana kissing dinta ganin abin nashi zae yi yawa yasata fara kuka a hankali da kyar ya raba bakunan su ya saki.


  "Baby yi shiru nine ko" kai ta d'aga mishi "yi hakuri princess kedin ce kinfi zuma dadi" dariya kawai tayi yanda ta daura kanta a cinyar shi suna a haka sai ga sallamar su Heedaya da sauri ta tashi d'aga cinyar shi.


 

Da gudu Heedaya ta rungume Habiba tana hawaye


"Addana nayi missing dinki wallahi" shii kanwata kiyi shiru haka kinji ba zan dinga zuwa miki gida ba kuma kema zaki dinga zuwa min" kai ta d'aga mata "yawwa ko kefa" sai sannan tayi dariya.

  "Ya Ahmad ina kwana" lafiya lau ya amsa musu

  "Ya gidan da kowa ya tambaya yanda suka amsa lafiya lau d'aki ya shiga domin fita dan yasan dole b'ak'i zasu yi ta zuwa mata.


  "Princess zan fita"Tasowa tayi tayo wurin shi kiss ya manna mata kafin tay mishi adawo lafiya ya tafi d'akin ta dawo yanda suka zauna sai hira ga uban mutane da suke zuwa ganin d'akin amarya.


Story continues below

  "Adda Habiba ina ragowar kazar take"


"Ohh Heedaya kwadayi ko" dariya suka kece da ita gaba dayan su abin nema ya samu su Munnira baki yak'i shiru haka dai sukai ta fama.

  Basu sukai shirin tafiya ba har sai da akayi sallah magriba sannan sukai mata sallama akan zasu tafi tsayar da Heedaya tayi.

  "Heedaya kin san mai nake so dake" a'a Adda sai kin fad'a.

 

  "Dan Allah na rokeki duk abinda Anty zatayi maki karki dinga maida mata kinga yanzu ke kadai ce kar tayi miki abinda zai cutar dake so dan Allah ki dinga hak'uri kinji" insha Allah Adda bazan dinga mayar mata ba" yawwa 'yar albarka ki gaishe da Abba kinji" kai kawai ta gyada mata.

  'yan biki fa sai watsewa suke yi gida ya sarara itama yau Heedaya zata koma saboda Abban su yana ta kiran ta, ta gama shirin kayanta tsaf misalin karfe 4 na yamma Anty Aina'u tai mata fad'a sosai akan zama da Matar Baban su sosai ta d'auki shawarwarin sannan su Maryam suka rakata ta hau abin hawa kai tsaye gidan su ya nufa da ita nan kuwa ta biya shi tayi cikin gidan sai sallama take yi amma babu wanda ya amsa ta hakan ya tabatar mata Abban su bayi nan.

Kayan ta ta dire a kofan d'aki sannan tayi hanyar d'akin antyn su amma me kafin ta marasa taji wani uban tsawa.

  "Kada ki kuskura ki shigar min d'aki munafuka Allab yayi kin dawo kenan mai b'ak'ar aniya kawai 'yar mayu dangin maita kin bace min da gani ko sena karaso"


  Tana hawaye tayi maza ta shige cikin d'akinsu tuni ta saki kuka mai tsuma rai anya zata iya cigaba da zama a cikin gidan da halin wannan matar kuwa tunani iri da iri ta shiga yi tana kuka tana kiran Abba jin an dafata ta baya ta zabura juyawan da zatayi sai mahaifin ta data gani ai ba shiri ta rungumeshi tana kuka.


'Yar albarka maiya sameki" Abba ba komai kawai nadawo ban ganka bane" kinga karki boyemin komai keda waye" Abba dagaske bakomai to shikenan Allah yasa hakan ne" kai ta gyada masa kafin suyi waje.

  "Mamana yaya gajiyar bikin" Abba tabi jiki Adda Habi na gaishe ka"


  "Allah sarki Habiba Allah ya mata albarka halin ta na gari ya bita amin ta amsa mishi dashi.


"Mamana kinsan kuwa zanyi tafiya wanda a kalla zan kai kawana goma kafin na dawo"


  "Abba ina zakaje"


  "Kar ki damu akan maganar company din nan ne" toh Abba Allah ya baku nasara ubangiji yasa ayi a sa'a amin ya amsa mata.


"Kuma yaushene tafiyan naka"


"Gobe idan Allah ya kaimu"


  "Allah ya bada nasara" amin yace yana mai binta da addu'a hira sukeyi hankalin su kwance babu wata matsala Antyn su ta kawo abinci.

"Alhaji abinci ya zama ready" to Rakiya bari sai nayi sallar Isha'i tunda kinga masallaci zan tafi.


"To Alhajina duk yadda kace haka za'ayi.


Toilet ya fad'a yayo alwala kafin yace zai tafi fatan alkhairi sukai mishi sannan ya fita.

"Ke bazaki tashi yin sallar bane"


"Anty yanzu zanyi"

"Na aza ai makircin naki zaki cigaba dayi" kai kawai ta girgiza kan ta shiga itama tayo alwala haka ta gabatar da sallar ta duk Antyn nata na kallon ta har ta idar ta zauna zaman addu'a.

  Bayan idar da sallar isha'i a massalaci Abban nasu ya dawo sannu da zuwa duk sukai mishi tare da zama.

  Towon shinkafa tayi miyar ganye zuba musu shida Heedaya suka ci suka yi kat saida suka koshi sannan Heedaya ta fita da kwanunkan.

"Rakiya" na'am Alhaji na kinga gobe in Allah ya yarda zanyi tafiya so ga Heedaya nan ki riketa amana dan Allah.


  "Kar kaji komai Alhaji ai da na kowa ne duk wannan rashin jituwar tamu a baya ne amma yanzu bakomai"


  "Gaskiya naji dadi sosai Allah yayi albarka" amin ta amsa mishi.

  Heedaya da take mak'ale a kofa duk tanajin yadda sukayi taji wani hawaye dazu ta gama zagin ta amma yanzu ta nuna bakomai haka kawai ta danna kanta cikin d'akin.


  "Heedaya kin dawo" eh Abba bacci ma nakeji shine nazo in muku sai da safe"

  "To Allah ya tashe mu lafiya" amin ta amsa yayin da Antyn ta ma tai mata sai da safe sannan tayi d'aki bacci barawo ne kawai ya dauketa.

  Washe gari da wuri ya shirya saboda tun 8 zasu tafi jirgin 9 zasubi sai da ya sake ma Rakiya fad'a tare da danga ma Heedaya kudi a hannu sannan suka tafi.

  Tana da niyar juyawa kenan Antyn ta ta tsayar da ita.


  " dawo nan ina kuma zakije"  Anty fitsari nakeji kafin ta k'ara magana tayi d'aki da gudu.

Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


       *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*By Miss_ayusha*
*🌈Kainuwa writer's asso🀝*


              1⃣7⃣&1⃣8⃣

  Buga k'ofar d'akin ta shiga yi" ke munafukar Allah wallahi ko ki fito ko na illataki a cikin gidan tunda uban naki baya nan"jin abinda Antyn ta ke fad'a yasata fitowa.+


"Gani Anty" maza miko min kudin da ubanki ya baki" make kafada tayi "zaki miko ko se ma taka ki" Allah sarki jiki na b'ari ta mika mata kudin.

  "Maza ki wuce ga kayan wanke wanke ki wanke su fita tsaf" jiki a sanyaye ta fita domin wanke wanke, haka ta wanke kwanukan tsaf sannan ta koma cikin d'aki zubewa kawai tayi tana wani irin kuka mai tsuma rai a wurin bacci yayi gaba da ita.

  Cikin bacci taji wayan ta na kara ganin Amir ne yasata dagawa.

  "Hello baby"


  "Na'am"


  "Ya kike?"


  "Ina lafiya lau"


"Ya gida dasu Abba?"


  "Lafiya lau, Abba yayi tafiya"


  "Masha Allah, pls inaso yau nazo idan har kinada time"


  "Shikenan sai kazo"

  "Yawwa baby bye"nan yayi hanging kiran, jin miryan Rahina na kiran ta yasata saurin fitowa.

   "Rahina" na'am Heedaya ya kike?" Lafiya na lau" ina kikaje ne na dawo baki nan?"


  "Gidan uwarki taje dan ubanki ke kuma shasha sauna da har kike ttambayan ta ya take mara hankali, ina damuwan ki da ita inbanda ke bakida tunani ma wuce kiban wuri a wurin" da sauri Rahina tabar wurin tana kunkunai cikin daki ta shige.

  "Ke kuma ki fito ki daura mana abinci saura na fito baki yi niya ba"


  "Anty amma fa zanyi bako"


  "Ina ruwana da bakon da zakiyi iya abinda na sani ki fito ki daura mana abinci kafin kwarton naki yazo"


  Wani bakin ciki ne ya tirnuke ta jin abinda Antyn nata ke fada kai kawai ta girgiza ta wuce kitchen tuni ta hada duk abubuwan da zata bukata ta daura girkin ta nan da nan ta gama abincin ta juye shi ta ajiye.

Wanka ta shiga ta cancada abinta yanda ta saka abayan ta tay rolling da gyalenta tayi kyau sosai dama abinka da farar mace hakan yasata kara yin kyau.


" Wai Dr ina zakaje ne da kake ta irin wannan shirin haka" Kausar na fad'a miki zani unguwa koko da wani yare nai miki ne?" Da hausa kai min amma naga shirin yaki karewa ne ai" taki akeji matsa min daga hanya"kin matsawa tayi tureta yayi yai wucewan shi wayan ta kawai ta dauka nunbern Salim tayi dialing ringing biyu ya dauka.


"Hajja ya akayi ne"


  "Salim kana inane haka"


  "ina gida ranki shi dade"


  "so akwai abinda nake son kai min yanzu Dr zai fita inaso duk inda yayi ka dinga binshi a baya har ya kai yanda zashi"

  "Angama ranki dade" tuni shima Salim ya hada machine dinshi yabi bayan shi.


  Kai tsaye gidan Dr tsalha ya fara zuwa a parlo ya tarar dashi tare da matar shi.


  "Dr ya kake?" Aboki ina lafiya lau "madam ya karfin jiki?" Alhmdllh Allah ya kara sauki amin ta amsa mishi.


  "Aboki sai ina zuwa haka ne" wurin mutumiyar mana" ahh kace lallai ka samu karbuwa "kai kam ka bari kawai amma ina tunanin ranar da Kausar zata san wannan maganar fa" karkaji komai bari lokacin yaxo toh shikenan ni bari na tafi"nan sukayi sallama ya kama hanya yayi gaba.

  Duk yanda Dr yayi sai Salim ya bishi a haka har ya iso kofar gidan su Heedaya Salim na gefe na kallon shi wayan ta ya buga batafi minti biyar ba sai gata ta fito tun daga nesa yae gifan ta da wani kallo kamar me karasowa tayi fuskarta dauke da murmushi shidin ma hakan ne.

  "Amincin Allah ya tabatta a gareka"

  "Amin babyna"

 

"Ya na sameki fatan kina lafiya"

  "Lafiya lau sai godiya" ya missing din sister

 

  "Wallahi kamar ka sani dan da yau ma zanje gidan ta"


  "Ba damuwa ai ba sai na kaiki ba"

  "Owk durling shikenan"

  Mota ya bude mata suka shiga kafin ya tada mota suka dau hanya.

  "Baby" na'am durling na tambayeki mana" inajin ka" shin zaki iya tare da matata" kaji ka da wani magana to aini zaman ka zanyi bana matar ka ba ko" hakane baby kinsan halin wasu matan ne ai, wasu kace kuma kasan halin kowa ya banbanta ko" tabbas hakane Allah ya zabar mana mafi alkhairi amin ta amsa hira suke cikin kwanciyar hankali babu abinda ya dame su.

Salim ya kwashe duk wani information ta kaima Kausar hankalinta in yayi dubu ga tashi tsoron ta daya kar Dr neman mata ya fara amma tasan me zata mishi bakomai da ita yake zance.

B'angaran su Heedaya kuwa sun kai gidan Habiba lafiya don har Dr shima sai da ya shiga cikin gidan domin gaisawa da Habiba da Mijin ta haka ko sukayi wuri Habiba da mijinta suka basu yanda suka sha soyayyar su babu abinda ya damesu Heedaya har ta manta duk wani b'acin ran dake ranta domin Dr ya mantar da ita duk wata damuwan ta.

  Sai da aka kusa magriba sannan sukayima su Habiba sallama siyayya yayi mata sosai sannan ya maida ta gida.
Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


     *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*By Miss_ayusha**🌈 Kainuwa writer's asso🀝*


            *1⃣9⃣&2⃣0⃣*


Idan baku manta ba mun t'saya a page 17 & 18 yanda zamu tashi daga 19 & 20.

+

Sai da aka kusa magriba sannan sukayima su Habiba sallama, siyayya sosai yayi mata sannan ya maida ta gida.

Ga yadda muka t'saya nan.


Cigaba.A kofar gidan Dr Amir ya ajiye Heedaya tare da d'aga mata hannu ,cikin gidan ta shiga da sallama a bakin ta bata sami kowa a t'sakar gidan ba hakan yasata fara shiga cikin d'akin su nan da nan kafin kace me bacci yayi gaba da ita.


Bugan kofan tayi ba digon imani a tattare da ita

"Ke munafukar Allah tashi y'ar banzar yarinya kawai tashi nace"

A zabure Heedaya ta tashi

"Anty ya ina bacci kawai zaki min irin wannan tashin dan Allah"

"Dan ubanki tambayana kike iye ,nace tambayana kike ,wato yanzu duk iskancin naki bai isaba har sai kinbi wani gardi waje kunyi lalatar taku saboda kijamana abin kunya ko"

  "Hmm Anty kenan ni banyi wannan gadon ba watakila dai wasu ne zasuyi ba Heedaya ba"

Tas kafin ta gama rufe baki taji an dauketa da mari.

"Wato rashin kunyar ki dawowa zaiyi ko to wahala zaki sha maza ki wuce ki dauramin abinci shashasha kawai"


Jiki na bari Heedaya ta nufi kitchen yadda ta daura ruwan farin taliya dan ta kuduri niyyan da manja zata girka mata.

Gidan Dr Amir

Ya koma lafiya yadda ya tarar da tashin hankali dan Kausar ta tayar masa da hankali ba kadan ba.

"Wlhy Dr sai ka fad'a min wurin wace shegiya kaje idan ba haka ba kaima kasan sauran"

"Kausar look into my eyes am tired of all dis nonsense you are doing to me so dan haka na yanke hukuncin sake aure if you wish ki zauna in kuma kinki you are ready to go the door is open"


 

Tsabar bakin ciki Kausar bata san me zatayima Dr ba.

"Wallahi Dr kaji na rantse inhar ka cigaba da maganar auran zakaga abinda zai biyo baya tun wuri gwara ka barshi"

  "Bazan barshi ba Kausar and duk abinda zakiyi kije kiyi sai dai abu d'aya inhar kika taba Heedaya hmm Kausar you will pay for if dan na lahira sai ya fiki jin dadi"

Tsaki ya buga abinsa ya wuce yanda ya barta a tsaye da bakin ciki anyway she know's what to do, Salim ta kira a waya akan yayi mata binciken yarainyar kafin safiya nan da nan kuwa ya amince.Gidan su Heedaya


Tsaf Heedaya ta kammala abinci ta tace taliya ta soya manja daman sunada yaji rufewa tayi yanda ta kai ma Antyn nata d'aki sanda taje ta sameta tana sallah hakan yasa taji dadi sosai a ranta tuni ta fita daki ta koma key ma ta saka gudun kar Antynta ta shigo.

Wayan ta kawai ga dauka kafin ta fara kira har ya tsinke ba'a dauka ba sai kira akayi.


"Abbana"


Story continues below

"Na'am princess din Abba ya kike ya gida hope all is well? "


"Eh Abba but yaushe zaka dawo i need you by my side i miss you so much "

"Awww princess i miss you to na kusa dawowa kinji"


"Toh Abba"


"Yaya Habiba take kinje gidan kuwa?" da Antyn ki fatan suna lafiya? "


"Eh Abba kowa yana lafiya dazun ma na dawo daga gidan Add a Habiban ai"

"Allah sarki princess Allah miki albarka"

"Amin Abba"


"So akwai wani damuwa ne? "

"A'a kawai gaisuwa ne Abba"

"Owk y'ar albarka sai anjima ko"

" bye Abbana"


Kit ta kashe wayan wani hawaye ne ya fara bin kumatum ta ji take ina ma ace Umman ta nada rai rayuwa kenan haka ta karashi kukan ta ta gaji bacci barawo ne yayi gaba da ita.


"Kan bala'i lallai ma hating at nan ta gama rainani wato ni zatayi ma wannan abincin ko" hanyar d'akin Heedaya tayi jinta a rufe yasata komawa d'akinta banda huci babu abinda takeyi.

Tana haka Rahina ta shigo da wasu 'yan mata da maza kaidai da ka gansu kaga yaran banza d'akin saukan bak'i ta kai su nan duk suka baje sai shewa sukeyi.

Ga wani uban hayaki da yake tashi a d'akin mazan kowa ya kama tashi duk sun maida hankalin su kan lalatar da sukeyi itadai Rahina sun shige d'aki danata saurayin anan sukayi zigidir haihuwar uwar su nan fa suka fara aikata abinda suke so.

Maman ta jin hayaniya yayi yawa yasata fitowa ganin abinda ke faruwa a wurin yasata komawa d'aki dan tasan babu wanda zai aikata haka sae Rahina.


B'angaran Salim duk wani bincike yayi akan Heedaya nan ya sanar da ita komai da komai ba karamin dadi taji ba dan zatayi amfani da Antyn ta wurin cikar burin ta kawai jira take gari ya waye tayi dirar mikiya a gidan.Misalin karfe 10 wayan ta ne ya tashe ta ganin sunan yasata dauka da hanzari.

"Babynerh ya kike ya gajiya"

"Habibi lafiya lau gajiya tabi jiki"

"To ya yaushe Abba zai dawo saboda ayi magana da wuri a shafa fatiha kin  san fa ni na kosa wallahi"

" kai habibi karka damu nan da 4 day's zai dawo"


"To Allah ya kaimu"

"Amin ta amsa"

Sun dade suna magana kafin sukayi sallama sai kuma bacci.Washe gari da wuri Kausar ta shirya dan zuwan gidan su Heedaya sosai taci ado kamar karuwa sannan Salim yazo suka tafi a dai dai kofar gidan ya ajiye ta kafin ya tafi.

Ko sallama babu Kausar ta shigo tana taunar cingum.

"Ke malama lafiya zaki shigo mama gida haka"

" bai kamata ki tambayeni lafiya ba saboda da akwai ta bazaki ganni a nan ba"


" toh maike tafe dake"

"Ba komai ya kawoni ba sai dan na miki gargadi kija wa y'arki kunne ta fita sabgan mijina idan ba haka ba kuma hmm"

"Wacce y'ar tawa d'aya"

"Heedaya take da suna kowa oho"

"Ashh kice min mijin ki wannan tsinanniyar take bi" kafin rufe baki sai ga Heedaya ta fito da bukitin ruwan zafi.

"Ke Heedaya yanzu abin naki har ya kai ki ringa bin mazan wasu saboda la'ana"

"Naga dai ba bin banza nayi ba aure zamuyi to miye a ciki"

Tas Kausar ta dauke Heedaya da mari wai yau an famoma Heedaya tuni suka kaure da dambe ganin ba sarki sai Allah yasa maman Rahina nunawa Kausar ruwan zafi ai tuni ta zubawa Heedaya a kafa tsaban azaba batasan sadda ta saki ihu ba wanda ya tara makotan su a cikin gidan.

"Kinga kadan kikagani kar ki fita hanyar mijina ki gani wai tuni samari anguwa sukayi kan Kausar da Antyn Heedaya amma kafin me sun shiga d'aki har sun rufe ta ciki.

Itakuwa Heedaya direct chemist akayi da ita yadda sukayi treating nata daganan aka samu wasu suka kaita gidan Habiba kafin kace me labari har ya kai ga Abban Heedaya abinda ya faru.Kucigaba da bina jin yadda za'a kaya miye asalin labarin duk zakuji a next page Insha Allah.


Ina jiran naga comment if not typing sae next week.
Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


    *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€*By Miss_ayusha**🌈Kainuwa writers asso🀝*


           *2⃣1⃣&2⃣2⃣*
A cikin gidan Habiba aka dire Heedaya ya Ahmad bayanan wato mijin Habiba sae ita kadai suka samu.

+

"Bayin Allah meya sameta haka? "


"To muma dai a takaice bamu sani ba amma gatanan tai miki bayani mukam zamu tafi"

Godiya sosai Habiba ta shiga musu kafin suka tafi.

"Heedaya yanzu dawa kukayi fad'a haka har da kona kafa"

"Wallahi Adda Habi Anty ta saka ni girki fa kawai sai ga matar Dr Amir tazo toh nikuma fitowana kenan kawai naji sun rufeni da duka muka fara toh ruwan zafin da na fito dashi shine fa suka zubamin"

"Inalillahi to gaskiya Heedaya auran Dr ya haramta a gareki bazaki je ta kashe ki a banza ba"


"Adda Habi wallahi ni kuwa yanzu ne naji karfin son Dr kuma auran gaske zamuyi ki cire komai a ranki ma"


"Heedaya ki rufa min asiri ke kadai kika ragemin baya dake bani da kowa kawai ki hakura da auran shi"

"Adda Habi" kafin ta karasa magana wayar ta ya fara kara ganin habibin tane yasa ta dauka da hanzari.

"Habibi"


"Na"am habibaty kina ina yanzu haka? "


"Ina gidan Adda Habi" kit taji ya kashe waya"


"Adda Habi kiga dai ya kashe wayan"

"To Heedaya ki jira muga ikon Allah me kuma zaeyi"

Wayar Heedayan ne ta sake daukan ruri

"Abbana"


"Na'am princess kina ina haka? "


"Abba ina gidan Adda Habi"

"Bani Habiban"


"Abba"


"Na'am mamana"


"Ya jikin nata"


"Abba da sauki sosai dan Allah ya takai ta"


"To ki kula da ita sai nazo"


"To Abba"

Gidan Abban Heedaya.

Duk iya kokarin na ganin mazan sun buge kofar sun kasa haka suka hakura suka fita.

"Baiwar Allah ki fita yanzu ki barmin gida tun kafin muyi nawa nidake"


"Kedin banza kedin wofi" tsuka Kausar tayi taja gyalenta sai waje.


Sallama ake kofan gidan Habiba mayafin ta kawai ta sako tayo waje ganin Dr ne tare da abokan sa biyu yasa tace su shiga yayi dai dai da dawowan Ahmad.

Duk tare suka shiga gidan kowa nasan yaga Heedaya

"Sister"


"Na'am ya Ahmad"


Kasa magana ma yayi tsaban bakin ciki

"Habibaty"


"Na'am habibi"


"Ya akai haka ta faru"


Nan ta shiga kora mishi jawabi


" lallai Kausar she will pay for it"


Ran Dr Amir a bace suka fita kira Ahmad yakeyi amma ina Dr yayi nisa

Shima Ya Ahmad tambayan meya faru yayi nan Habiba ta maida mishi zance Allah wadaran halin Rakiya yayi nan ya farfarda ma yan uwa tuni gida ya cika anzo gaida Heedaya yan uwan Abban suma ba'a barsu a baya ba suma kansu sunje dubiya.


Gidan Dr Amir

Sanda suka isa yayi dai dai da fitowan Kausar daga cikin d'akin ta.

Tass Dr ya dauketa da mari ji kake tass ya kara bata wani ta dayan gefen.

"Kausar ke wace irin matace wata irin annuba ce ke baki jin abinda na fadamiki ba kenan ko"

Duka kawai Dr ya fara kaiwa Kausar da kyar su Dr tsalha suka banbareshi baiyi auni ba ya shiga kitchen ruwan zafi ya fito dashi take ya watsama Kausar a yanda ta watsama Heedaya.

"Kausar  nagaji na gaji da halin ki kafin na dawo you make sure kin barmin gida na ki tafi can na miki saki daya"


Ihu Kausar ta shiga kwalawa tana kiran Amir amma ina ko ta kanta bai biba ya fita abinshi.

Mamanta kawai Kausar ta kira ta sanar da ita abinda ya faru.

"Jar uba shi Amir din ne yayi miki haka ki jiramu gamunan muna tahowa yanzu tare da yayunki"

"Toh mummy"
Toh anya za'a kwashs yar dadi kuwa ku cigaba da bina jin ya zata kaya.
Bani da charge kuyi manage da wannan dan Allah.


Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


       *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€*By Miss_ayusha**🌈Kainuwa writers asso🀝*
         *2⃣3⃣&2⃣4⃣*
Bayan fitar Dr Amir gidan Habiba ya koma yanda suka tashi suka barmishi wajen.

"Habibaty dan Allah kar kice zaki fasa aure na dan abinan ya faru pls"

"Habibi karka ji komai babu abinda zai hanani auran ka inhar ba mutuwa nayi ba ,yawwa ina fatan dai baka yiwa Antyna komai ba"

"Haba Habibaty ya kike tunanin zan barta haka yanda ta zuba miki ruwan zafi itama haka nai mata"

"Haba habibi gaskiya ni banji dadi ba akan me zakai mata haka daka barta da halin ta ma kadai ya iseta ai"


" tuba nake gimbiya sarautar mata ai min afuwa"

"An maka amma dai ka kula nan gaba"


"Karki samu damuwa sweetheart dina"

Rinring wayar Dr ya shiga kara ganin Abban sa ne yasa shi dauka da hanzari.

"Assalamu alaika"


"Wa'alaika sallam"


"Ina wuni Abba"


"Lafiya lau Amir kana ina ne "


"Abba ina wurin Heedaya"

"To kai maza kazo muna gidan ka"


"To Abba ganinan ina tahowa"

"Allah maka albarka"


"Ameen" ya amsa mishi.

"Habibaty kinga Abba na jirana zan dawo zuwa anjima kinji koh"


"To Habibi"


"Me zan taho miki dashi"


"Duk abinda kaga ya dace dani"

Sallama sukayi kafin ya wuce dan tafiya.

"Lallai Heedaya kunyi nisa bakwa jin kira irin wannan abu haka"


"Kai Adda Habi kinji ki dawani magana ko" yo ai gaskiya me ciwon da bawani mai yawa bane"


Gidan Rakiya


Hankalin Rakiya a kwance sai ma kiran kawarta falmata datayi suka cigaba da bidirin su


"Kawata bansan me yake damun Rahina ba amma fa abin nata yawa yake karayi"


"Kingan ki ko babu komai a ciki yaran zamani kenan ki barta tayi abinda ranta yake so na lokaci ne yawwa Rakiya nikam ya batun maganin Heedaya da za'ayi ne wai"


"Kawata kenan ki bar komai dan yanzu na samo mana mafita wuyar ta daya ayi musu aure da wannan shegen yaron to fa anan zamu samu daman yin abinda mukeso game da ita"


"To ita yar tata fa"


"Share wannan babu wata matsala wannan saunace ita ayi maganin wannan din tukun"


Shewa kawai suka buga yayinda suka cigaba da shege ayar su

Gidan Dr Amir

Abinda yaba Dr mamaki bai wuce ganin Umman shi Umman kausar tare da Abban shi ba


Har kasa ya duga ya gaishe su guska a bace Umman kausar ta amsa mishi.

"Kai yanzu Amir yayi dai dai abinda kai wa yar uwar ka sabida wata banza bare a waje"


Story continues below

"Umma amma kafin ki yi magana kamata yayi ki tambaye mu miye silar abin tunda bakida masaniyar abinda ya faru.

"Babana fadamin meya hadaku da har haka ya kasance a tsakanin ku"

Nan pha Amir ya kwashe komai ya fadama Abban shi wani abu ne kawai ya tsaya wa Abban nasa sanin halin kanwar tasa yasa ya cigaba da magana.

"Yanzu Kausar abinda kikayi ya kamata kenan har kibi 'ya gidan su ki konata a matsayin ki na 'ya mace shin namiji kan ba mijin mace hudu bane"


"Haba yaya wannan sam bayi bane yaya shi yayi mata abu sannan kuma ita za a baiwa laifi kana goya masan bayan yayi auran kenan"

" Adama bani da hurumin da zan hana shi abinda yake so yana da daman da zai auri hudu ma yanzu dai abinda nake so dasu shine kowa cikin nada laifi dan haka kai Amir ka maida matarka dakin ta batun saki ma bai taso ba ke kuma Kausar ci gyara halin ki banda aikata abinda bai kamata ba wannan mijin kine yanada kyau ki bishi sau da kafa kunaji ko"


"Eh duk suka amsa"


"Sannan kai kuma maganar aure idan har iyayen yarinya sun yarda sai ayi komai tunda shi aure Allah ne yake kawo shi, ke kuma Kausar kibi mijinki lafiya ku zauna da abokiyar zaman ki lafiya idan Allah yasa anyi kenan"


"Umman Amir bakida nacewa"


"A'a Alhaji bani da komai fatana su cigaba da hakuri suyi zaman su cikin kwanciyar hankali da nutsuwa"


"Adama fa"


"Bani da tacewa" rai bace tayi maganar"


"To Alhamdulillah ke Kausar zaki bi Umman ki kuje gida sai sanda kika warware sannan ki dawo dakin ki fatan kin fahimta"


"Eh ta amsa tana mai matso kwalla a idon ta"


"Yawwa yanzu sai ku tashi mu tafi ko"


"Rai bace uwa da 'yarta suka tafi Amir ne ke mara musu baya dan shi a rayuwa babu abinda bai san gani yanzu irin Kausar haka dai har wurin mota ya rakasu sannan ya koma gida tare da kwanciya.


Kamar walkiya Rakiya taga Abban Habiba a gaban su ita da aminiyar tata.

"Alhajina dawowa ba sanarwa haka"


Wani banzan kallo da yayi mata ne yasata yin shiru da bakin ta ganin haka pha falmata tace zata tafi nan sukayi sallama tare da fita, ganin Abban Habiba ya fita yasa Rakiya shiga daki domin ganin su Rahina tashin ta kawai takeyi sai da ta buge tane sannan ta tashi.

"Dan ubanki ki tashi Abbanki ya dawo"

"Mama dallah ki fita ki bani waje ya ina bacci kawai zaki tashene haka to sai me sannun shi da dawowa idan na fito zanje wurin shi"

Tsabar bakin ciki Rakiya kasa magana tayi sai fita kawai datayi amma tuna maganar kawarta sai taji bakomai bane tayi abinda take so.


Gidan Habiba


Murna wurin Habiba da Heedaya ba'a magana gasu ga abbansu abin kaunar su a gefen su.

"Princess ya akayi haka ta faru pls" bata boye mishi komai ba ta sanar da shi komai da kamai sai da ta kai karshen zance sanna ta tsaya.

"Amma Abba dan Allah karkace bazan auri Dr ba wallahi ina son shi kuma dan Allah karkayi wa Anty komai"


"Princess yanzu haka kikeson mutumin da akan shi za'a illataki"


" eh Abba wallahi ni inason shi"

"Shikenan tunda shine zabin ki Allah yasa haka shine mafi alkahiri"

Tsabar dadi Heedaya batasan sanda kuka ya kubce mata ba take ta rungume Abban nata.

"Abbana inasonka abin alfaharin mu nagode nagode sosai Abbana Allah yajikan Umman mu"

"Amin amin princess to yanzu kiyi shiru hakan nan kinji ko idan har shi dagaske yake to ya aiko ayi komai a gama"

Farin ciki ne menene ita kanta batasan me zata kira yanayin da take ciki ba Allah Allah takeAbban nasu ya tashi kodan ta kira masoyin ta abin kaunarta dahaka dai suka cigaba da lamuran su har yayi musu sallama ya koma gida.

"Add a Habi yau bansan a wani hali nake ciki ba kinji wani farin ciki danakeji wanda tun rasuwar Umma rabo na dashi kenan" Allah sarki Habiba tsabar son da takema kanwar haka yasa ta itama nuna farin cikin akan abinda kanwar tata takeso nan suka rungume juna suna dariyar murna.

"Adda Habi wai yaushe zaki santalo mana baby ne"


" ke Heedaya kunya ce tagama rufe Habiba ko dai Heedaya ta gane tana da ciki ne to Amma ko Ahmad ai be san da cikin ba bare Heedaya da haka dai ta bar zancen suka cigaba da hiran su.


ASALIN LABARIN.

Ku cigaba da bina dai ana tafe.
Misa_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


   *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€*By Miss_ayusha**🌈Kainuwa writers asso🀝*        *2⃣5⃣&2⃣6⃣*
       

TUNA BAYA


Alhaji Hamza Bello shine ainihin sunan shi haifafan garin kaduna ne iyayen shi duk 'yan kaduna ne unguwar sarki kafin Allah ya karbi abinsa .

+

Su hudu ne a wurin iyayan su Hamza shine na farko sai Isma'il na biyu sai Kaltume sai kuma Yunusa a cikin su Allah yayi was mutum daya rasuwa itace Kaltume tun bayan rasuwar iyayan su itama tace ga garin ku.


Alhaji Hamza hamshakin dan kasuwa a yawan kasuwan ci ya hadu da matar shi ta farko Murja wato Umman su Habiba sunyi soyayya ba kadan ba har Allah ya kaisu ga aure amma matsala daya aka samu mahaifiyar mijin bata santa ko kadan dalilin Hamza yaki auran yar kawarta wato Rakiya.


Da haka dai Hamza yake danna zuciyar matar shi duk da Murja mace ce mai sanyin zuciya batada hayaniya ko kadan a haka Allah ya azurta Murja da cikin farko wato Habiba kenan gata babu irin wadda bata gani a wurin mijinta sai dai wurin maman mijin ta.Ciki ya kai matsayin haihuwa Allah ya baiwa Murja 'yar ta mace kyakyawa san kowa kin wanda ya rasa gata kam yarinyar tana shan shi ba wurin Umman ta ba haka kuma Abban ta.


Watan Murja uku da haihuwa mahaifiyar mijin ta tilasta shi akan dole ya sake aure yanda ya auri Rakiya.


Murja dai ita haifafiyar garin yola ce amma sanadin aiki itama iyayanta suka dawo kaduna da zama su uku ne a wurin iyayan su daga Aina'u sai Murja sai zainab.


Tun bayan sanda akayi auran Rakiya da Hamza abubuwa suka fara canzawa dan Rakiya ba karamin shedaniya bace sai data gama yawan barikan cin ta sannan tazo gidan Hamza duk da aikin malami ma.

Murja ta fuskanci kalubale iri iri a wurin Rakiya a haka harta kamo da ciwon zuciya lokacin kuma Allah ya azurtata da wani cikin haka ta cigaba da rainan cikin had ta santalo 'yar ta Heedaya.


Lokacin kuma Rahina 'yar Rakiya tana da wata 10 a duniya haka rayuwa ta cigaba da tafiya har Allah yasa yaran suka girma.

Habiba ta tashi da irin zuciyar Umman su bands Heedaya dan ko a makaranta ita ke karban ma Habiba fada.

Tun Heedaya na karama Rakiya ta dau tsanar duniya ta daura mata dan ta fuskanci yarinyar bata da kunya ko kadan kuma bata da yafiya dan duk abinda kai mata saeta rama.

Ana haka dai yara suka zama yan matan gaske wanda a lokacin Heedaya duk wanda yanemi ya takura wa Umman ta to fa tana dai dai dashi duk da kullum mahaifiyar tana mata fada amma ina Heedaya tayi nisa sanadin mutuwar mahaifiyar tasu ne yasa ta saduda kodan ta cika wa mahaifiyarta burin ta na ganin duk wata fitina ta daina shi.
Waye Amir


Mus'ab Abdulhakim sunan shi suna mishi lakabi da Amir haifafan garin kaduna ne shima Amir ya taso shikadai wurin Umman shi da Abban shi bashi da wa bare kani sai 'yan uwa na jini.

Babanshi Ambassador ne yayin da Umman shi yar kasuwa ce shi kadai ne da a wurin su Amir ya taso cikin gata da kwanciyar hankali iyayan shi sun nuna mishi so ba kadan ba amma duk da haka bai sa ya zama irin wasu 'ya yan ba.

Fari ne yanada tsayi dai dai misali da fadin kirji iya haduwa Amir ya hadu yadda mata dayawa suke kaima hari.

Tun tasowar Amir basa shiri da Kausar wacce ta kasance 'yar kanwar maman shi saboda tana son maza bata da kamun kai hankali bai gama isanta ba itako Kausar a rayuwan ta babu namijin datake so a duniya irin Amir hakan yasa ta matsa wa Mamin ta sai da suka san yadda akayi auran nan shidai Amir kawai dan bin umarnin iyayanshi ne yasa shi amincewa saboda bayi san abinda zai bata musu rai gashi yanzu harta kai abin Kausar gaba gaba yakeyi.

CIGABA


Abban Habiba ya koma gida amma kwata kwata bai nunawa Rakiya komai ba saboda alfarma da Heedaya ta roka sai ma wani rawan kai datake mishi.


"Alhaji na shine zaka dawo bazaka sanar dani ba"

"Dawowan gaggawa ne Rakiya shiyasa amma yanzu ba nadawo lafiya ba"

  "Hakane kaje gidan Habiba ne"

"Eh suna gaishe ki ma"


"Allah sarki nagode sosai"


"Ina Rahina kuma take"


"Tana gidan Anty yalwa wato kanwar ta kenan"

"Owk kawomin abu nadan sa a bakina ko"


"Jiki na bari ta kawo mishi dan duk azatan ta baisan meyafaru ba"Gidan Habiba

Sallama akayi wanda Ahmad ne ya dawo habiba taran shi tayi sai daki anan suka bar Heedaya a zaune.

"Sweetheart sannu da dawowa"


"Yawwa babynerh"


"Amir din bai dawo bane har yanzu"


" wallahi fa gashi ya tafi ranshi a bace"


"Kuma miye idan ya dawo zamuji ai amma gaskiya hankalina bai kwanta da Heedaya ta auri Amir ba"


"Bakasani ba ni kaina banaso amma banason bacin ranta shiyasa nake  tayata son abinda take so dan a halin yanzu ma Abba yace inhar dagaske yake to ya aiko"


" toh Allah sa haka shiyafi alkhairi" amin ta amsa mishi.

"Sweetheart ka kusa zama baba"


Ido Ahmad ya waro waje

"Baby me kike nufi kinada ciki"

"Yes"


Wani ihun murna yayi wanda yasa har Heedaya ta jiyo dagata sama yayi cak yana wuntsulata dan kanshi ya gaji ya ajiye ta


"Babynerh dagaske kike"


"Kasan dai bazan maka karya ba ko"


"Alhamdulillah Allah shine abin godiya babynerh Allah miki albarka" amin ta amsa mishi" yanzu me kike so a rayuwan ki ki fadamin koma miye shi


"Uhmm ni kai nakeso" toh indai nineh kin sameni muje waje kar sister tagaji ita kadai"

Tana makale a hannun shi suka isa parlon ga dayan hannun na kan cikin ta bige hannun tayi duk dan kar Heedaya ta gani.

"Ya Ahmad kun fito"


"Eh matar Dr " kai gaskiya na baka kujerar hajj" laa yanzu sister bakya jin kunyata" haba Ya Ahmad indai ta fanni Habibina ne ba wannan layin lallai kinyi nisa Allah tabbatar da Alkhairi ameen tace.

Kamar daga sama sukaji sallamar Amir hannun shi da uban kaya niki niki ido kawai suka hada sai murmushi.

"Antynmu barka da hutawa" yawwa Dr hannu ya mika wa Ahmad suka gaisa tuni suka barmusu parlon.

"Habibi" ta fada in a serious tone


"Habibaty meyafaru"


"Abba yace sai dai mu hakura da juna amma babu zance aure tsakanina da kai"

Inalillahi shine kawai idon shi duk ya kada


" habibaty dan Allah in wasa kike ki bari dan Allah"


Shiru tai mishi sai da taga yana shirin kuka sannan ta kyalkyace da dariya.

"Habibi wasa nake maka"


"Kai habibaty pillown kujerar ya dauka nan suka fara jefe jefe a tsakanin su.

Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


  *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*By Miss_ayusha**🌈Kainuwa writers asso🀝*             *2⃣7⃣&2⃣8⃣*
Wasan jefe jefe sukeyi dan kansu suka gaji suka bari.

"Habibaty me Abba yace miki"

"Abba yace if you are serious ka turo manya ayi a gama komai"

+

"Dagaske kike"


"Eh mana"


"Wayyo Habibaty can't wait for the day na zama mijin Heedaya ya zanyi ranar"


"And i also na zama Matar Dr that's the most happiest day in my life"


"Habibi meye a cikin ledan ne"


"Ohh dear tsabar kin tsoratar dani a farko yasa na manta da shi ma"


"To yanzu ka miko min nagani"


  "Ledan ya mika mata ido a ware take kallon shi"


"Habibi wani irin kaya ne haka"


" Habibaty kayan jinya ne"

" kai sweetheart diehard soulmate dina muahh i love you so much"

" habibaty all for me"


"Yes"


"So yanzu ya bikin mu zai kasance"


" kai Habibi gaggawa haka don't worry sai lokacin yazo tukun"

" toh Habibaty barin tafi naje na sami Abba ayi komai ba bata lokaci"

"OK dear but i will miss you"


"Same to darling but zan kiraki ina komawa gida kinji"

"Toh shikenan take care of yourself for Heedaya"


"I will Insha Allah love you"

"Love you too bye"

Nan fa yayi waving mata hannu ya fita yana fita ta shiga kwala ma Addan ta kira


"Adda Habi ki fito ya tafi"


Daga ciki ta amsa mata da tana zuwa sai da aka kusa minti biyar sannan ta fito tare da Ahmad sun canza shiga.

"Heedaya irin wannan kiran haka"


"Adda to ya tafi shiyasa na kiraki"


" Ya Ahmad unguwa ne"


" gidan Mami zanje"


" dan Allah ka taho min dasu sister kaji"


"Idan sun yarda mu taho zamu zo kinji"


To kawai ta amsa mishi


"Sweetheart zan tafi"


Har bakin kofa ta rakashi


"To darling Allah ya kiyaye sai ka dawo"


Har ya yi gaba ta tsayar dashi


"Kuma bazaka tuna min ba"


"Mene"


Bata yi wata wata ba yaji saukan bakin ta akan nashi dan kansu suka gaji suka bari


"Allah miki albarka matata"


"Amin mijina Allah tsare min kai"


"Amin"


Cikin gidan kawai ta koma.


Gidan Su Amir

Dr ya sami Umman shi da Baban shi duk a zaune kamar yadda suka saba har kasa ya gaishe su sannan ya fada mishi sakon Abban Heedaya.

"To Amir yanzu ita yarinyar sai ta fadawa Abban nata inyaso gobe sai muje ko"

"To Abba nagode sosai zan fada mata!

"And Amir inaso kasani karkaga dan ka auri wacce kakeso hakan ya baka lasisin wulakanta Kausar"

"Abba insha Allah hakan bazai taba faruwa ba nai maka alkawari"

"Toh Allah yayi muku albarka" amin ya amsa musu.

Tsabar murna Amir bai san sanda yafara kiran abokan shi ba akan suna ina nan suka fada mishi suna gidan Dr Zubair ai ba bata lokaci ya nufi gidan.

Baiwani bata lokaci ba ya isa saboda ba nisa daga gidan su duk wanda yaga Amir yasan yana cikin farin ciki.


"A'a Amir ashe kana kusa" eh ya basu amsa


"Guys kunsan me" no sai ka fada


"Nakusa zama mijin Heedaya gobe su Abba zasu je gidan"

"Wow duk suka hada baki lallai Amir wani irin so kake ma Heedaya haka"fadar Yakub


"Kai Yakub ni kaina ban sani ba all i know shine i love her"


"Allah yasa ayi damu" cewar Dr tsalha" amin duk suka amsa.

Ringring wayar Dr ya kama kara wani murmushi yake wanda suka gane tabbas Heedayan ce.

"Babe"


"Na'am shine kuma baka kirani ba"


"Tuba nake gimbiya sarautar mata yanzu na bar wurin abba"


"To shikenan ya kaje gida"


"Lafiya lau and kinsan me"


"Sai ka fada"


"Ki fadawa Abba gobe fa su Abba zasuzo kinji"

"Wani ihu ta saki wanda yasashi matsar da wayan a kunne"

Sai da tayi me isarta sannan ta tsaya


"Habibi are you there"


"Yes Habibaty ihun na miye"


"Na murna mana"


"So ki fada mishi dai kinji"


"Yanzu ma kuwa"


"Yauwa babynerh sai munyi magana i love you"


"Love you too bye" nan sukai hanging call din.


Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


   *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


  *By Miss_ayusha**🌈Kainuwa writers asso🀝*


          *2⃣9⃣&3⃣0⃣*
          

B'angaran Kausar abin duniya ya isheta ga bakin cikin auran da Amir zaiyi ga kuma har yau baizo ya dubata ba haka yasa ta saka wa Mamin ta kuka akan Amir yak'i zuwa.

+

"Kiyi shiru hakan nan yanzu zan kirashi yazo dama akwai maganar da zamuyi"

"Mami dan Allah yanzu kema so kike yayi auran"


"Kausar shifa mijin mace hudu ne so miye na d'aga hankalin ki kowa zaman ta zatayi ki nutsu kisan me kikeyi fa kinaji ko"


"Yanzu shikenan duk an daina sona a gidan nan amma har ake goyon bayan shi"

"Banda abinki Amir bafa shi ya ganki yake so ba ke kike sonshi kuma sai da na fada miki zaki fuskanci abubuwa da dama amma kika ki to yanzu me kuma zan miki abu daya ne ki kwantar d hankalin ki kuyi zaman ku lafiya"


" wallahi bazata sabu ba har ga Allah"


"Ke kika sani wannan ya rage naki idan kikayi abu ya sakoki gabadaya damuwar ki tunda bakijin magana"

Wayarta kawai Mamin Kausar ta dauka tai kiran shi take yace mata yana zuwa aiko ba'a fi minti shabiyar ba sai gashi a parlon suka zauna dan Kausar tana daki ita.

"Ina yini Mami" lafiya lau Amir ya aikin dai? " alhamdulillah"to masha Allah kasan mesa nai kiran ka" a'a

"Amir so nake ka fadamin duk damuwan ka da Kausar wani irin zama kukeyi"


"Mami lafiya lau muke zaune"


"Kaga bansan shashanci maza inajin ka"

"To gaskiya dai Kausar bata daukeni a bakin komai ba magana ma wannan nayi mata baji takeyi ba hasalima wannan girki batayin shi sai lokaci zuwa lokaci duk dai irin haka"

" ka tabbata irin abubuwan da takeyi kenan" eh Mami to Allah yay maka albarka da har irin zaman da kukeyi kenan baka taba kawo kukan ta gidan ba ita kuma zan sameta"

"To Mami" zaka iya tafiya" saboda kunyar ido yasa shi tambayar ina Kausar din take tana daki shine answer ta Mami ta bashi kai kawai ya saka a cikin dakin.

Tana kwance tana waya da kawarta akan lallaifa tana bukatar taimako suyi gaggawan zuwa ya shigo nan kuma ta katse wayan.

"Amir" tayi kiranshi


"Ya kike ya jiki" bansani ba ai baka damu da sanin ya nake ba sanda Mami tai kiran ka da wancan shegiyar ce ai ka iya nan nakan kafa ka bita aikin banza kawai"

"Kausar ubangiji Allah ya shiryeki Allah ya baki lafiya ni zan wuce" kudi ya ciro ya ajiye mata nan yasa kai yayi waje take ya tafi

"Kausar yanzu dan ubanki har yana tambayar ki ya jiki kina masa gatsali kome yayi miki ai ke kika gawa kanki banza sauna kawai"

"Lallai ma ai zamu hadu ne bari su shafa suzo zasuyi bayani daga shi har ita dan ta kuduri komai zata iya aikatawa akan wannan yarinyar kuma abinma sai an hada da Matar Ubanta fadar Kausar.

Bayan wasu lokaci sai ga su Shafa sun bayyano itada karimatu bayan gaida Mamin Kausar sukayi dakin da take.

"Subhanallahi Kausar meya sameki haka"


Story continues below

"Ku zauna tukun mana" zaman sukayi damas suna jiran jin na bakin ta

"Baki answer mu ba"

"Amir ne ya watsa min ruwan zafi" what Karimatu ta fada duk kina zaune kina kallon shi uban me kika masa? "

Nan ta kwashe komai ta fada musu har karshe.

"Hmm Kausar tun yaushe nayi dake ai maganin dan banza kika ki yanzu wa gari ya waya"

"Shafa naji dan Allah yanzu miye abinyi" abunyi daya ne idan anyi auran mu taru mu mata dan banzan dukan da zamu lahanata" fad'ar Karimatu.

"A'a karima wannan ba shawara bace kamata yayi a sake komawa gidan su yarinyar muji ta bakin Matar Ubanta tunda ba santa takeyi ba daganan za'a samu abinyi.

"Gaskiya ne fa kuma  fadar karima" hakan ma za'ayi" to yanzu yaushe zamu koma ko gobe tunda kafata tayi sauki" to shikenan Allah ya kaimu Ameen duk suka amsa nan fa suka hau wani hira.

Washe Gari

Amir da wuri yayi shirin fita aiki sai da ya biya yay ma Habibatyn shi siyayya sannan yayi gidan Habiba lokaci Ahmad har ya fita aiki gidan sae hayaniya saboda su Munnira sunzo iyayan surutu sai ga Amir ya doka sallama a hade suka amsa

"Oyoyo Habibina"tama manta da akwai Addan ta a wurin"

"Habibaty an tashi lafiya" lafiya lau sae missing naka danayi jiya baka dawo ba" wallahi abu ne yayi min yawa yanzu ma office zan tafi shine na biyo na dubaki"

"Aiko naji dadi Habibinerh yanzu muje na raka ka bakin mota ko"

"To shikenan"har bakin kofar ta rakashi sannan suka tsaya"

"Habibaty kinsan yau ne fa ko" sosai ma nasani" na dauka kin manta ai" da kace zan iya mantawa da abin kaunata kenan"

"Habibaty Allah yasa kar su saka ya wuce 1 month" amin ta amsa mishi

Ledan ya mika mata sannan yace zai tafi

"To Habibi take care of yourself for Heedaya"

"Insha Allah i will bye"

"I love you"

"Love yo too baby"

Nan ya shiga mota ya bata wuta shiganga ba wuya suka hau mata ihu itadai kala batace musu ba haka suka gama abinsu ta fannin Habiba kowa farin ciki takeji wanda sanadin yar uwarta ta samu farin ciki a rayuwarta.

Tsakanin gidaje biyu fa duk an shirya ana jiran ayi a gama komai gidan su Amir basu dade ba sukaje gidan su Heedaya

Tarba ta mutunci suka samu wanda hakan ya tabbatar da lallai gidan su Heedaya akwai mutunci nan dai suka yi abinda ya kamata batare da bata lokaci ba aka sanya auran su wata daya godiya sosai gidan su Amir suka shiga yi daga bisani suka tafi.

Bayan mintuna da tafiyar kowa Rakiya ta shigo dakin

"Alhaji wai wadannan mutanan su waye"

"Auran Heedaya aka bayar wanda za'ayi nan da wata daya" tabdi to abu yayi kyau fa" fuu tabar dakin shidin ma fita yayi.

Sallama takeyi ba gaggautawa

"Wai uban waye ne haka"

"Daallah malama ki fito nice"cewar Kausar

Ba gaisuwa ba komai tahau bala'i

"Kinga yau ba masifa ce ta kawo ni ba neman yadda zamuyi maganin waccan shegiyar yarinyar nazo mu tattauna"

"Ku karaso to" har ciki suka shiga

"Naji abinda kika fada to me kikeso ayi mata ke mahaifiyarta"

"Banida burin da ya wuce naga Heedaya ta wulakanta a rayuwana ta duniya"

"Yauwa nima haka nake sonji dan babu macen data isa ta rabu mijina"

"Yanzu kamata yayi ku amsa numbern juna in yaso ko"

"Hakan ma za'ayi in yaso koma miye sae mu dinga waya" daga haka suka karbi numbern juna tare da sallama suna tafiya Rakiya ta kira falmata ta shaida mata komai itama taji dadin abun ba kadan ba haka suka sallame wayar.

Tana zaune Rahina ta shigo cikin gidan

"Mama an wuni lafiya" lafiya lau yar Mama yau kuma daga ina kike? " dariya kawai ta kece dashi ta nemi wuri ta zauna.

"Mama wai ina Heedaya ne" tana gidan Habiba baki san an saka ranar auran taba" kai amma na tayata murna Allah sanya Alkhairi mtsww uwar taja tsaki dan tana da tabbacin Rahina a buge take shiyasa ta fita hanyar ta.

Gidan su Amir

"Hajiya gaskiya yarinyar nan gidan su gidan karamci ne bakiga irin tarbar da sukai mana ba"

"Allah dai ya basu zaman lafiya yasa ayi damu" amin ya amsa.

Dan nashi ya kira ya sanar dashi duk yadda akayi godiya ya shiga yiwa baban nashi sannan sukayi sallama

"Amir me aka baka haka kake godiya"

"Friends i got her Heedaya an bani ita tazama tawa" bai san sanda yayi sujjada dan godewa ubangijin saba sukan baki suka saki suna kallon shi.

Take ya dauki waya ya kirata

"Baby" na'am kinji ranar bikin mu a'a babu wanda ya fadamin

"To 1 month aka saka" masha Allah ,Allah ya nuna mana Amin habibaty" yanzu dai kayi aikin ka da kyau kar murna yasa ka gagara duba patient da kyau" to habibaty daga haka sukayi sallama.


To gashi dai ansa bikin Amir da Heedaya dayan b'angaran kuma ana shirin yima Heedaya abu wayyo dama ta fasa auran amma muje dai mugani.
Misa_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


    *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*By Miss_ayusha*

*🌈Kainuwa writers asso🀝*

             *3⃣1⃣&3⃣2⃣*


Tsakanin masoya biyu fa abin sai cigaba ake samu soyayya suke ba kama hannun yaro yayinda Amir ya fara gyaran gida bil hakki da gaskiya hatta part din Kausar shima gyaran shi ake ita kuwa tana can tana shirin dawowa.

+

Alhamdulillahi Heedaya  ta warke tas abinta hakan yasa ta bar gidan Addan ta ta koma gida tunda Abban ta ya dawo sosai yake kula da ita dan baya son wani abu ya sake samun princess dinshi.

B'angaran Rakiya kuwa tunda Heedaya ta dawo bata shiga harkarta gudun kar ta sami matsala daga wurin Abban su gashi tunda ya dawo baiyi tozali da Rahina ba hakan yasa yau ya tashi da banbami alla dole sai ta dawo itadai Rakiya har ya gama batace uffan ba ta shige daki wayar ta kawai ta dauka dan kiran Rahina.

"Ke dan ubanki zaki jamin masifa ki dawo Abban ku na neman ki"

" gaskiya Mami yanzu bana kusa amma zan dawo" tsabar takaici kashe wayar tayi nan kuma ta kira falmata.

"Hajjaju ikon Allah"


"Kawata akwai damuwa dan yanzu harta kai Abban su yana neman Rahina kinga fadan da yayi tamin kuwa"


"Karki damu yanzu zan biya na karbo miki wannan maganin ki barbade shi da abinci zakiga aiki da cikawa" godiya Rakiya ta shiga yiwa falmata kaman abin arziki tai mata da haka sukayi sallama.


Wai waye falmata.

Irin 'yan barikin nan ne wanda sun sha bariki har sun gaji bata da yaro ko daya tun bayan 'yar ta data rasu sanadin accident din da sukayi da mijin ta tsabar fitina irin na falmata har mahaifiyar ta ta bar duniya bata daina fushi da ita ba wanda ala dole bakin mahaifiyar tane yake binta a halin yanzu bata da miji sai dai kawayen banza mata da kuma maza wanda suke sheke ayar su tare a ciki kuwa harda Rahina wanda falmata ke bala'in so a rayuwar ta dan tafi kwana ma a gidan falmatan akan wasu wuraren nata wannan kenan.


Batare da bata lokaci ba falmata tayi wurin malamin ta yanda ta karbo ma kawar tata magani domin rufe bakin shi akan Rahina tunda ko ba komai itama tana biyan bukatar ta da Rahina har gidan ta kaiwa Rakiya maganin yadda ta fada mishi a cikin abinci zata zuba mishi dayaci shikenan angama magana.

"Kai kawata gaskiya nagode miki amma yanzu ya batun wannan yarinyar ya za'ayi da ita"

" kedai ki bari so nake sai anyi bikin tukuna tunda yanzu ko me ya faru da ita za a zarge ki gwara idan ta tsallake tabar gidan yawwa kinga ba dan banzan da zai zarge ki kin gane ko" eh ta amsa mata.


Haka Rakiya ta barbade abincin mijinta da magani sannan ta kai mishi bai kawo komai a ransa ba kowa yaci wannan abincin.

Kausar fa tas angama shiri jira kawai take Amir yazo ya dauketa bashi ya tashi zuwa ba sai da akayi sallar magriba sanda yaje ta cika tayi fam kamar zata fashe.

Bata parlon Mamin ta ne kawai a parlon hakan yasa ya duga ya gaisheta sannan ta kira Kausar din gaba dayan su ta hade taiwa fada akan su zauna lafiya daga haka suka tafi.

"Yanzu Amir fisabilillahi muyi da kai tun la'asar zakazo amma sai yanzu saboda baka daukeni a bakin komai ba"


" sae kuma akace miki kar kiyi ma mutum uzuri ko"


"Wani uzuri zan maka wanda ba wurin wacce kaje sai 'yar iskan ka"


"Kausar kisan irin maganr da zaina fita a bakin ki banason iskanci kinaji ko" mtsww kawai tayi ayi dai mugani in tusa zata hura wuta" ko ci kanki bai sake ce mata ba har suka isa gida.

Kwanci tashi ba wuya ranaku nata tafiya lokacin biki na kara karotowa irin kayan da Amir yayi ma Heedaya abin azo a gani ne kowa sai san barka yake mata haka zalika kayan da yayi ma Kausar ma ba laifi sai dai ita da kawaye ke hure mata kunne.

B'angaran su Heedaya ta tattare ta koma gidan yayar Umman su acan ake gyarata wanda take shan gyara iri iri kullum cikin tsokana take wurin su Munnira sune masu raba I.V wa kawayen su dan Heedaya ba fita kuma ga Habiba itama cikin ta ya fito sosai sai san barka

Su kadai suka rage a daki daga Munnira Heedaya sai sauran yaran tare da gyaran jiki wayar ta ya dau kara ganin sunan shi yasata dauka.

"Habibi"


"Na'am habibaty pls ki fito wallahi yau inason ganin ki"


" kasan dai baza'a barni bako"

"Dan Allah kisan yadda zakiyi" to bani minti biyu


Haka Heedaya tai ta rokon Amina mai gyaran jiki ta barta ta fita amma bada sanin Antyn ta ba kawai ganin ta yayi.

"Masha Allah amincin Allah ya tabbata a gareki ma'abociyar kyau da kwarjini"


"Amin abin kaunata sanyi mai sanyaya zuciyar Heedaya fatan kana lafiya"


"Lafiya lau nake sarauniyar yan mata sai kewar ki data min yawa"


"Allah sarki angon Heedaya kwana nawa ne ya rage karka wani damu kanka na kusa zama mallakin ka har abada"


"To amaryar Amir Allah nuna mana ranar da alkhairi" amin ta amsa


"Angon Heedaya ina fatan kagama ganin Amaryar kar aje ana nemanta a gida"


"Ita kanta tasan bazan gaji da ganin ta ba sai dan kawai kar a nemen ta ne zan barta"


" to shikenan yanzu sai munyi magana kenan"


"Eh ya bata answer "


"Love you"


"Love yo too baby" daga haka ta shiga shima ya shiga cikin mota.

"Kai mutumin gaskiya kayi dacen mata inama nice na sami mata mai sona haka"fadar kamis wanda duk abinda suke akan idon shi

"Abokina kenan kaima insha Allah zaka zamu wacce tafi tawa ma kaji" Allah yasa abokina amin ya amsa.

"Yanzu ina zamu nufa? "


" wurin tela" shine answer da Amir ya baiwa Kamis haka suka dau hanya sai kawo dan zuwa wurin tela.


Kuyi manage da wannan banijin dadi ne wallahi idan na wartsake zaku sake jina.


Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


    *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*By Miss_ayusha*
*🌈Kainuwa writers asso🀝*


           *3⃣3⃣&3⃣4⃣*
Kai tsaye wurin tela Amir suka nufa ya karbo kayayakin shi daganan suka zarce gidan.+

Sanda sukaje Kausar ne kawai da kawayen ra a gida bayan gaisuwa da suka mishi yana ajiye kayan yayi gaba abinshi.

"Gaskiya namiji akwai dan wahala" inji karimatu

"Sosai ma kuwa" Shafa ta mara mata baya daga haka dai suka cigaba da tattaunawan su.

Kwanci tashi ba wuya yau gashi har laraba tazo wanda a ranar za'a saka Heedaya a lalle gida fa ya cika makil ba masaka tsinke ba dangin Umman su bana Abban su ba haka duk suka taru ana hidima.

Gidan Abban Heedaya

"Rakiya ki samu ki wartsake kinsan yau za'a saka Heedaya a lalle fa"


"Alhajina ina sane so nake ciwon ya lafa sai na tafi"


" to shikenan ni zan fita tunda ga Rahina zata kula dake na sani sai na dawo"


A dawo lafiya tai masa yana fita Rakiya ta tashi wani makirin dariya ta kece dashi dubeshi wai Heedaya yau ko uwar Heedaya ne ra rayo ake bikin ta ba zuwa zan ba bare 'yar data haifa"


*Tab wannan wani irin rayuwa ne  Allah dai ya shirya masu hali irin na Rakiya*

Haka Rakiya ta karashe banbamin ta tayi gaba dan cigaba da abinda ke gaban ta sai ga Rahina ta dawo


"Mama yanzu bazaki tafi gidan sakun lallen ba"


" dan ubanki ban haneki da min maganar gidan nan ba kinsan Allah idan kika kuma zakiga abinda zan miki banzar yarinya kawai"


Gidan Biki


Mutane an cika makil kawaye da abokan arziki nan fa aka saka Heedaya a lalle kowa na san barka da irin gyaran da Heedaya ta sha ga Habiba ta cikin ta a gaba.


Su uku ne a cikin dakin daga Heedaya sai Habiba sai Munnira Amir yayi kiranta

"Amaryar Amir dafatan kina lafiya"


"Lafiya lau angon Heedaya"

"Ya hidindimu? "

"Alhamdulillahi"


"Muna waje ki aiko wata ta karban miki sako" to kawai ta amsa shi


"Munnira dan Allah kije waje zaki karbamin sako"


Mayafin ta kawai ta zira tayi gaba a kofar gida ta same su


"A'a kaga angon Heedaya ikon Allah"


"Gaskiya Kinci kyauta" rafar kudi ya dauka ya bata nan ta shiga godiya


"Abokan ango yaya kuke? "


Lafiya lau duk suka amsata wanda tunda da fito Kamis yake kallonta


"To ango miye sakon"


Kaya ne ya bata ta kaiwa Heedaya ita dai bata san na miye ba haka ta karba tayi cikin gida dashi

"Abokai nima inaga nayi mata a wurinan"


Dariya duk gabadaya suka kece dashi dan sarai sun san kamis ba kasafai ya cika shiga harkar mata ba


"Kuna ganin kamar wasane wallahi I'm serious" ganin dagaske yake yasa su daina dariya


"Masha Allah ko kaifa amma da kamar wani ba mutum ba" cewar Dr Tsalha

"Amir asan yadda za'ayi a hadani da ita" to aboki karka samu damuwa angama" nan suka tada mota suka tafi.

Cikin gidan Munnira ce kema Heedaya tsiya akan kudin da Amir ya bata nan kuma ta fita dan ana kiran ta


"Heedaya" na'am Adda

"Inaso dan allah inhar an kaiki dakin mijin ki ba ruwan ki da shiga harkar matarshi dan a kowani lokaci zata iya cutar dake kinga yanzu kin tsallake tarkon Anty saura na abokiyar zaman ki"

"Adda in Allah ya yadda bazan dinga shiga harkartaba nai miki alkawari" yawwa sister daga haka hirar tasu ta canza.

Yau take Friday misalin karfe 4 suka gama shirin walimar su a yanda akayi na Habiba anan akayi na Heedaya sosai malama Fatima tai wa'azi mai ratsa jiki sai magriba sannan aka watse daga wurin suka koma gida a gajiye kowa kuma sai bacci.

Washe gari tunda suka tashi Heedaya ke faman kuka lallashin duniya babu irin wanda ba'ayi mata ba amma ina kamar zugata akeyi sai da Antyn ta tai mata nasiha tukun ta saki ranta.

B'angaran Kausar suna zaune da kawayenta wanda suke mata hudubar shedan kafin su koma wurin Rakiya duk da hankalin ta a tashe yake hakan bai hanata nuna damuwa akan maganar da sukeyi ba.


Da misalin karfe biyu aka daura auran Heedaya Hamza ta angota Mus'ab Abdulhakim wai idar har kuka kalli bakin Amir baya rufuwa kamar gonar auduga da haka dai ya samu ya kebe dan kiran abin kaunarshi

Tana kwance kan cinyar Habiba banda kuka babu abinda takeyi taji wayarta yana kara jiki a sanyaye ta dauka shiko ogan yana cike da zumudi

"Alhamdulillahi Habibaty yau burin mu ya cika kin zama Matar Dr"


"Gaskiya ne Habibi Allah shine abin godiya" daga yadda take maganar ta tabbatar masa kuka takeyi


"Habibaty kuka kikeyi" a'a ta bashi amsa kaga Anty na kira na zan kiraka dif ta kashe wayan.


Yan uwa da duk an taru anama Heedaya fada wanda take tuno Umman su kuke ba sassauci takeyi haka Habiba suka hadu suka sha kukan su har suka gaji dan kansu.

Misalin karfe 4 aka kaita wurin Abbanta nasiha sosai shima yayi mata wanda hakan yasa ta makale shi da kyar aka rabasu da Abban nata shima kanshi sai da yayi kwallah daganan kuma aka kama hanyar gidan ta dake rafin guza haka yan kai amarya suka iso gidan kowa sai san barka yakeyi da gidan har part din Kausar sukaje sukayi abinda zasuyi sannan sukayi part dinta.

Anan suka cigaba da zama suna hira banda Heedaya da yau bakinta ya mutu tana makale a jikin Addan ta.

Bayan sallah isha'i ango sukazo da abokan shi nan kuma sabon kuka ya kaure dan Makale Habiba tayi gam taki sakin ta da kyar aka rabasu suka tafi yanda aka barta ita da angonta.


Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


        *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*By Miss_ayusha*

*🌈Kainuwa writers asso🀝*


          *3⃣5⃣&3⃣6⃣*
Kusan ta ya matso kanta ta dafa "haba Habibaty kukan ya isa hakan nan mana yau ranar farin ciki ne ba kuka ba ko kin manta abinda kike buri kenan kin zama Matar Dr yau gashi Allah ya nuna miki ranar so maza dena kukan kinji" jikin ta ya jawo nan ya rungumeta lallashin ta ya shiga yi sai ajiyar zuciya take kamar yarinya da haka ya samu tayi shiru ya janye jikin shi.

+

"Habibaty yanzu tashi zakiyi muje muyi alwala muyi sallah dan mu godema ubangiji daya cika mana burin mu" to kawai tace sannan ta nufa toilet shima d'ayan d'akin yayi domin yin alwala kafin ya dawo har Heedaya ta fito shigowan shi keda wuya yasata tashi nan ya jasu sallah har suka idar addu'oi sosai yayi musu tare da dafa kanta haka suka shafa.

"Habibaty tashi muje" ba musu ta bishi suka fita hakan ya tabbatar mata da wurin kausar zasuje" tana wannan tunanin taga sun shiga hannun su na hade da sallama a bakin su sarauniyar taku na kan kujera ta hade daya kan daya fuska a bace ta amsa sallamar.

Wurin zama ya nuna ma Heedaya nan kuwa ta zauna.

"Kausar ina son magana daku gabadaya"


" yo bagani ba ai sae ka fad'a me ke tafe dake"


"Firstly Kausar ga Heedaya nan abokiyar zaman ki kuma kanwar ki dan Allah ina rokon wannan alfarmar daku zauna lafiya babu wani tashin hankali ,kinga kece babba so idan kikayi respecting kanki itama zatayi respecting naki ,ke kuma Heedaya wannan a matsayin yayarki take dan Allah banason wani tashin hankali da fitina pls nake rokon ku"

"Habibi Insha Allah ta wuri na bazaka samu wata matsala ba karka wani damu"


" aikin banza da wofi yo idan kagama fadan abinda ya kawo ka kwa iya fita zan rufe kofa na"

"Kallonta kawai Heedaya tayi ta girgiza kai" hannunta Amir ya kama tare da yima Kausar sai da safe wanda ko ta kansu bata biba sukayi gaba abinsu nan taja kofarta ta rufe.

Sun koma b'angaran Heedaya yadda Amir ya dauko abubuwan daya shigo musu dashi da kanshi yaje kitchen ya dauko cup ya dawo cikin d'akin nan dai ya zuba musu.

"Habibaty matso kici"


"Ni na koshi"


Jawota jikin shi yayi wanda duk ta gama tsorata da kanshi ya shiga bata har ta ture sannan yaci shima ya koshi sauran ya dauke ya kai kitchen sannan ya dawo.

"Habibaty kije kiyi wanka ko sabida kiji dadin jikin ki" kai ta gyada masa sannan shima ya fita.

Toilet ta fada yanda taje tayi wanka ta tsaftace jikin ta tas sannan ta fito turarukan da Addan ta ta shafe jikin ta dashi kafin ta fesa sauran nan fa d'akin ya shiga bada wani kamshi harta kayan wanda Addan ta ta fitar mata ta saka amma ina gani take wallahi bazata iya tsayawa Amir ya ganta a haka ba shiyasa ta dau hijabi ta saka dogowar riga ce wanda bata karasa gwiwaba ma gashi duk komai na jikin ta yana nunawa inama zata iya zama da wannan rigar nan kuwa ta haye gado tai kwanciyar ta.

Bata dade da kwanciya ba sai ga ogan naku ya shigo shima yana barbda kamshi kofar ya rufe yabi gadon shima ya kwanta "Habibaty shiru ba amsa"


"Nasan kina jina sarai kikayi banza dani" itako fannin Heedaya kirjinta kaman ana dukan lugude nan da nan Amir ya jawota jikin shi ba b'ata lokaci ya zare hijabin jikin ta wai nan fa yarasa ma me zaiyi daya shinshinan jikinta tundaga sama har kasa kafin kace me kissing dinta ya fara ta ko ina jin abin nashi ya fara yawa yasa Heedaya fara kuka baimasan me takeyi ba a haka ya samu ya rabata da kayan jikin ta in takai ta muku dai ranar Amir ya miyar da Heedaya babbar mace.

Ganin Amir nayi sunkuceta sai toilet da idanta da ko budewa batayi sun kunbura tsabar taci kuka harta gaji da kanshi ya gasata da kyau wanka ma shi ya mata ya kuma barta ta karasa sauran fitowa yayi ya gyara gadon tsaf sannan yaje yayi wanka har ya dawo Heedaya fito ba da kanshi ya nadota a towel sannan suka fito sai gado matse ta gam yayi kamar wacce za'a kwace mata shi ya nannadeta a jikin shi.

"Habibaty Allah ya miki albarka kinji" kai kawai ta gyada masa nan da nan bacci ya dauke su basu suka farka ba sai asuba hakan ma shiya fara tashi sannan ya tashe ta jansu sallah yayi saida sukayi addu'a sosai sannan suka koma bacci nauyayan bacci ne yayi gaba dasu wanda basu suka tashi ba sai kusan 10 shima wannan sanadin abincin da aka kawo ne ya tashiAmir haka suka shiga sukayo wanka atamfar ta ta saka dinkin dogowar riga wanda yayi ainihin fitar da shape dinta batayi wani havy makeup ba amma hakan bai hana ta kyau ba shima gogan naku shirin shi tsaf yayi cikin riga da wando sai kamshi yake barbadawa a haka suka tafi wurin karyawa.

"Habibtynerh gaskiya ke ragowace"

" oh hakama zakace? "


"Sosai ma bayan duka cizo mitsini da kikai tamin jiya so ya baki mutu ba"


"A'a kam kaika kanka kasan abinda kai ta fad'a ai"


"To ai ke dince kinfi zuma dadi kinji ki kuwa".


"Nikam ya isheni haka muci sai muje na gaida Antyna ko"


Haka suka ciyar da junan su har suka koshe kwanukan ma tare suka wanke sannan sukayi part din Kausar wanda itama ta hade cikin riga da skirt dinta sai baza kamshi take suna makale a jikin juna suka shigo.

Ko kallan gefen su batayi ba bare tasan akwai mutane a wurin

"Antynah ina kwana"

"Daban kwana ba zaki ganni"


"Allah ya baki hakuri" da haka Heedaya taja bakinta tayi shiru" shi drama tasan ba gaishe shi zatayi ba dan Heedaya ta matsa shiyasa ya yarda suka zo haka ko suka juya suka bar mata d'akin.

Gidan duk Amir ya zagaya da ita daga karshe suka koma cikin parlo tana zaune ta daura kanta a cinyar shi shiko hannun shi na cikin rigar ta sukaji sallama ai da sauri Heedaya ta tashi su Munnira ta gani batasan sadda ta saki wani uban ihu ta rungume su ba sai murna gaishe sa sukayi nan shi kuma yayi daki.

"Ke Heedaya kingan ki kuwa" fad'ar Jalila


"Kai kun ganku banasan sharri wallahi"


"Ina kukan yake har ya kare kenan" duka ta kaiwa Munnira a baya nan kuma taji Amir yana kiran ta


"Shi kinyi bakin ma bazai barki bane"


"Ke bansan iskanci fa" da gaggawa tayi cikin d'akin


"Honey gani"


"Abba ne yake kiran ki"


"Wayyo Allah sarki Abbana" wayar zata dauka ya jawota jikin shi sai anan ta dauki wayan tai kiran shi bai dauka ba sai da ta yanke ya kirata duk tana jikin Amir nata

"Abbana"


"Na'am Abba's princess ya kike ya Amir din, hope duk kuna lafiya? "


"Eh Abba lafiya lau muke"


Nan wani fadan yayi mata sannan sukayi sallama rungumeta Amir ya karayi sosai wanda har ya cire mata dan kwalin kanta.

"Habibi ka manta su Munnira na jirana ne wai"


"Tsaya to ai abu zan fada miki Kamis ne yaga Munnira kuma ya kamo so ki mata bayani asan yadda za'ayi kawai su had'e"


"To shikenan zan mata yanzu bari na koma kar suga shiru"


"Haka kike nufin zaki tafi ba tare da kin ban abin dadi da" ido ta zuba mishi batayi auni ba taji bakinta cikin nashi da kyar ta samu ta fita ta barshi da dan kwali a hannun ta.

Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


   *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*By Miss_ayusha*

*🌈Kainuwa writers asso🀝*

        *3⃣7⃣&3⃣8⃣*
Haka ta fito da dan k'wali a hannunta tana dariya.

"Kuyi hak'uri na barku ku kadai wallahi Abba ne yayi kirana"

+

  "Ayya bakomai"

"To ku tashi ku tayani gyara sauran wuraren mana"


Haka suka tashi ba musu suka shiga tayata gyara sai anan ta tuna maganar Amir.

"Yawwa Munnira ga sako daga wurin Amir akwai wani abokin sa daya ganki kuma harga Allah sonki yakeyi bana wasa ba so shine yace nai miki magana idan har kin amince yazo ku daidaita"


"To Heedaya Allah ya kawo shi"


"Amin"


"Yawwa Heedaya nikam ina abokiyar zaman ki? "


"Tana part din ta"

"So dan Allah babu ruwanki da shiga harkartar duk abinda tai miki karki kulata plus"

"Insha Allah"


Haka suka tayata ta gyara ko ina tsaf abin sha'awa sai gab magrib suka tafi itako sai anan ta samu tai wanka Amir na yayi sai soyayyar su da suke zubawa.


Haka rayuwa ta kasance tsakanin masoyanan kullum cikin nunawa junan su so da kauna suke kowa bai san yaga ran dan uwan sa ya baci a b'angaran Kausar ma Amir yana iya bakin kokarin ta dan bata farin ciki amma ina Kausar kullum hudubar shedan dana abokai take dauka.


Kwanci tashi ba wuya auran Amir da Heedaya wata biyu kenan yayinda cikin Habiba haihuwa yau ko gobe.

Yau takama monday tsaf Amir yagama shirin shi dake a d'akin Heedaya yake shi dai bai san meya sameta ba amma kwata kwata kamar ba Heedayar shi ba haka dai ya barta ya tafi office shima dan ta matsa ne bai jima da fita ba sai ga kawayen Kausar sunzo dan tafiya gidan Rakiya


Zaman jiran Kausar sukayi akan ta shirya su tafi dan sun dau alwashi yau sae ta bar gidan nan.


Itako b'angaran ta banda amai babu abinda take kwara ba ta galabaita iya galabaita data ga de abin ba mai karewa bane ta kira Amir


"Habibi"


"Na'am Habibaty"


"Pls kazo gida ba lafiya"


Jin abinda tace yasa shi tashi a firgice ya kwashi key yama manta da Dr Tsalha a wurin

"Frnd lafiya kuwa? "


"Wallahi Heedaya ne wai ba lafiya bansan meya faru ba kaga barin tafi ina b'ata lokaci"


"Allah ya bata lafiya" amin ya amsa haka Amir ya figi mota sai gida

B'angaran Kausar tagama shiri haka kawayen nata suka tasa ta gaba akan sai anje anci ubanta haka kuwa duk suka shiga cikin d'akin ko sallama babu

Daga ita sai vest iya gwiwa dai dai fitowan ta a toilet kenan idon ta yana kallon mutane uku uku dan bawai ta gane su bane kawai dai ta gane maganar Kausar ne.

"La kawata kiga ma ko dai ciki take dashi"


"Kan bala'i lallai dana barar da cikin wallahi kuwa"


"Batayi auni ba taji saukan mari"


"Kausar nayi warning dinki akan Heedaya duk abinda ya sameta a gidan nan wallahi you will pay for it kinji na rantse marar hankali kawai kina biye wannan banzayen frnds din naki stupid kawai ko ki fita ko na tattakaki anan"


" Amir nika mara saboda wannan 'yar iskar"


"You better mind your tongue if not zan gwada miki rashin hankali a wurinan yanzu kuwa"


Kai kawai ta girgiza tabi bayan kawayen nata suna kara hure mata kunne basu dauki hanyan ko ina ba sai na gidan Rakiya a cikin napep din ma maganar suke har dai suka iso gidan suka sallami mai napep itama ta wurin ta sun gama shiri itada falmata dama su suke jira da isansu kuwa ta rufe gida suka dau hanya sai wurin boka.
Kuyi hak'uri wallahi sanda nagama typing tas sannan ya goge.Miss_ayusha πŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


    *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*By Miss_ayusha*

*🌈Kainuwa writers asso🀝*

           *3⃣9⃣&4⃣0⃣*
B'angaran Heedaya banda amai babu abinda take shekawa har sai da Amir yayi mata allura sannan aman ya tsaya daganan kuma bacci ya sunkuceta shiko Allah Allah yake ta tashi yaji abinda yake tunani gaskiya ne ko yaya.

+

Suko Rakiya dasu Kausar an bazama anyi wurin boka a tsorace take dan tunda take bata taba takawa zuwa wurin wani malami ba sai a sanadiyar Rakiya da kawayen ta jeji kawai suke kutsawa harta gaji bataga an iso ba

"Wai dan Allah har yanzu ba'a kawo bane? "

"Daallah idan zaki tafi kizo muje duk badan ke ake tafiyar ba"

"Kema ai da taki bukatar gaskiya Rakiya bakida imani inhar mutum Allah ya hadashi da MATAR UBA irin ki ya shiga uku"

Wani dariyan rainin wayau Rakiya tayi

"Kausar kenan indai akan wannan 'yar iskar yarinyar ce sai yanda karfina ya kare dan sai na hanata jin dadin duniya har karshen rayuwar ta"

"Amma dan Allah me tayi miki haka da kika tsaneta? "

"Ke Kausar tambayoyin ki sun isheni haka mucigaba da tafiya kawai"

Haka suka ringa kutsuwa cikin lungu har daga karshe sukaji an saki wata irin tsawa wanda duk cikin su Kausar ce kawai ta tsorata harda yunkurin guduwa batayi auni ba sai ganin wani mummunan mutumi tagani gaban su daga ganin shi dama kasan ba zaiyi imani ba.


Kirari suka shiga yi mishi yanda daga karshe ya basu izini suka zauna

"Boka gagaraba dau munzo domin neman taimakon ne"

"Akan Heedaya ko? "


"Eh tabbas akanta ne"

"Ke MATAR UBANTA mai kikeso ai mata haka kema abokiyar zaman ta mai like so ay mata"

"Boka babu abinda nakeso ay mata face a rabata da mijina ta bar gidana ta barni da mijina yanda muke a da"

"Ke kuma MATAR UBANTA fa? "

Ai ni boka abu daya nakeso inma za'a rabata da duniya kamar yadda uwarta ta barshi to inaso"


"A'a kawai dai a rabata da 'yan uwanta ta shiga duniya tayi hauka"

Dariya ya kara kecewa da ita na rashin imani wannan aikin me sauki ne surkullan shi ya fara wanda daga bisani ya basu wani abu a hannun su

"Ke MATAR UBANTA wannan zaki samu rami a bayan dakin ta ki birneshi kuma kada kowa ya ganki, sannan ke kuma abokiyar zaman ta wannan a kofar dakin ta kawai zaki barbada data tsalaka shikenan"

Nan fa suka shiga godiya kamar me tare da zabgada mishi kirarinshi wani abu a leda suka ajiye sannan ya bace bat suka tafi.

"Ni yanzu Rakiya tayaya zan birne wannan abu"


"Ba wani abun damuwa bane yanzu mu wuce gidana in yaso da duhu ya shiga sai kije ki birne"

"Yawwa kawata ai haka nakeso shiyasa nake sonki wallahi" daga haka suka rabe Kausar da kawayen ta sukayi hanyar su sai Rakiya da falmata ma hanyar su."Kausar gaskiya wannan Rakiya ta gagara mata ba digon imani"


"Kedai barta ai in Allah ya hada ka da mata irin wannan ka gama yawo"

Gab sun kusa isa gidan ta suka sauka dan bazasu shigaba haka ko ta shiga cikin gidan kai tsaye sai part din ta.Ta wurin su Heedaya kuwa ta farka yanda Amir yay mata wanka tsaf ya gyarata sannan suka zauna

"Habibaty meya sameki haka kiketa amai"

"Habibi nima bansani ba kawai yaune na tashi da ciwon zuciya komai bansan abu mai kamshi da yawa"


"Yaushe rabo da kiyi period"

"Last month ne ai kuma bana fadamaka ba"


Fita yayi ya siyo Pt akan ya gwada fitsarinta bai jimaba ya dawo kuwa

"Habibaty kije ki kawo fitsarin ki a zan gwada abu"


Ba gardama tayo ta dawo ta kawo mishi nan kuwa ya gwada ya tabbatar da ciki gareta tsam ya rungumeta a jikin shi

"Habibaty kin gama min komai a rayuwata ubangiji Allah ya miki albarka na kusa zama daddy"


"Habibi me kace? " ta tambayeshi cikin mamaki


"Yes you are pregnant"


Ajiyan zuciya ta sauke wanda tai hamdala tay godiya wa ubangiji


"Habibaty daga yau kin daina aikin komai me aiki za'a nemo miki duk wani aiki kin daina yin shi"

"Kai Habibi"sai kace wanda cikin yazo haihuwa"


"Koma miye habibaty kin gama duk wani aiki a gidan nan" yanzu tashi zakiyi ki gyara muje wurin Umma"


"Amma dai in mukaje ba cewa zakayi inada ciki ba ko"


"Kedai kawai ki tashi ki shirya" shirin mikewa takeyi wayarta ya hau kara  Addan ta tagani haka ta dauka da hanzarin ta


"Addana"


"Na'am Heedaya na sauka "


"Me kikace ta sake tambaya"


"Na sauka an sami namiji"


Ihu ta shiga kurmawa a wayan ashe bata sani ba har Habiba ta kashe wayar ta

"Habibaty meyafaru"


"Adda Habiba ta haihu namiji kaga sai mun fara zuwa gidan ko"


Eh ta bashi amsa ai da sauri ta shirya tsabar murna zataga baby ma ta manta bata rufe kofar taba suka tafi iyakacin na ciki kawai ta rufe nan suka tafi.


Tana kwance a daki ai tanajin motsin fitar shi dan ta dau shi kadai ya fita yasa tayi part din Heedaya aiko ganin batanan yasa ta barbade dukkan kofan da maganin nan kuma ta kira Rakiya akan yakamata suzo dan basunan sun fita

Ba'a jimaba kuwa suka iso nan ta birne abu batare da kowa ya ganta ba ta bar wurin sai suka tafi zuciyan ta na cike da farin ciki.

B'angaran su kuwa sun isa gidan Habiba yanda sukaga baby boy dinta tsaf mai kama da Ya Ahmad sosai suka mata barka sannan suka tafi sai gidan Abban Heedaya nan ma gaishe sa sukayi yanda yayi musu albarka haka shima suka tafi suna tafe suna hira irin ta masoya har suka kai gidan su Amir din a parlo suka tarar da Umma da Abba har kasa suka kai nan suka gaishe su wanda duk Heedaya takasa sakewa ganin haka Umman Amir tajata sukai daki.

"Ki saki ranki kinji ko ai nan ma gidan kune karkiji komai"


Suna cikin haka Amir ya shigo


"Umma Albishirin ki"


"Goro"


"Kin kusa ganin jikan ki"


Kunyar duniya rufe Heedaya tayi kusan ta Umman nashi ta koma


" yarinya ta wai hakane"


Kasa daga kanta tayi tsabar kunya haka Umman shi ta shiga nan nan da ita harta Abban Amir saida suka fada mishi sosai fa shima ya shiga murna haka Umman Amir ta hada mata komai da zai mata amfani sannan suka tafi.


Cikin motan ma sai hira da shewa sukye abinsu har suka iso gida

"Habibaty bari naje na siyo wani abu kinji"


Haka ta fita kawai sai cikin dakin ta dukkan maganin nan sai da ta tsallake su kanta ne yayi wani mummunan sarawa kawai zaman dabas tayi a zaune kafin kace me har tafara juye juye kamar an tsikareta ta tsala ihu nan kuma ta zabura sai waje tana tafe tana sushe sushe.
Wayyo Heedaya ta fada tarkon MATAR UBANTA da abokiyar zaman ta hmm muje dai zuwa *ALLAH ya raba mutum da mata irin su Rakiya*
Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


   *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*By Miss_ayusha*
*🌈Kainuwa writers asso🀝*

         *4⃣1⃣&4⃣2⃣**Wannan shafin nakune duk masoyan wannan littafin MATAR UBA ina jin dadin addu'oin ku Allah ya bar kauna*
+

Haka take tafiya tana sushe sushe alamun sabon kamun mahaukaciyar nan sai dariya take yi gashi dai sai dariya kuma takeyi tana tafiya.


B'angaran Amir yana zaune ji yayi gaban shi na faduwa haka dai hankalin shi bai kwanta ba kawai mota ya dauka sai gida wani irin gudu yakeyi kamar zae tashi sama kitt yaji ya buge mutum inalillahi ya shiga ambato babu shiri ya diro daga motan gashi duhu ya shiga hasken wayar shi ya kunna dan ganin wanda ya bugi

"Habibaty" ya fada da wata irin  murya


Baiyi wata wata ba ya sunkuceta sai cikin motan shi gidan shi ya nufa yadda ya bude part dinta amma me ganin wani gari gari yasa shi shan jinin jikin shi kwantar da ita kawai yayi tare da kulle kofan bansan mai zai yi ba kawai naga ya nufi part din Kausar.

"Kausar ina Heedaya take"


"Bangane ina Heedaya ba ka bani ajiyarta ne" ta fada a irin ko ohon ta


"Kausar inhar kinma Heedaya wani abu toh wallahi zaki fuskanci fushi na ba dan kadan ba"


"Amir pls ya isheni haka ka tafi can kanemi Heedaya a yanda ka ajiyeta aikin banza kawai" wani wawan tsuka taja sannan ta juya masa kai

Fita yayi ya bar wurin amma me ba tafiya yayi ba yana labe yana jin abinda take fada


Aiko Amir na fita Kausar ta dau waya ta kira Rakiya nan ta shaida mata komai da komai duk abinda ta fada kuwa yana kunnen Amir abin karshe dayaji shine dariyan da ta sheke dashi.

Lallai Kausar bazai dau wani mataki yanzu ba dan bashi da evidence din abinda yaji ta fada jiki a sanyaye ya koma part din ta sukutum ya dauketa ya dire ta a mota sai gidan Umman shi duk anan Kausar tana jin fitan shi murna ya gama cikata.


Har sun rufe gidan Amir ya shiga horn haka mai gadi yana tangadin bacci ya fito ganin motan Amir yasa shi budewa da gaggawa bai tsaya sanya ba ya figeta sai cikin gidan a parlo ya direta dan karma tace zata fita ya rufe kofar yana ajiyeta ta tsala uban ihu wanda ya tashi Umman Amir da Abban shi.

"Alhaji mai nakeji kaman ihun mace"


"Hajiya nima kaina naji mu fita mu gani"


"A'a alhaji karfa wani mugun abun ne kuma"


"Insha Allahu ba komai muje"


Haka suka fita duk jikin ta a dadare yake ganin sunyi tozali da Amir yasata karasawa da sauri

"Amir" idonshi wanda ya kada yayi jazur ya dago ya kallesu ga Heedaya da sai shirin yaga kayan ta takeyi dabara kawai da yayi mata ya daure mata hannu.

"Amir magana akeyi bakaji ne maiyasa meta ba dazunan kuka bar gidan nan ba"


"Umma sun haukatar min da ita sunsu ta shiga duniya Allah bai amince ba sunzo rabani da ita amman Allah baiyi ba yanzu gashi Heedaya ta zama wata iri" wani kuka ya yanke da shi wanda sai da yaba iyayan nashi tausayi

"Amir suwaye sukai haka kai mana bayani ka bar kukan hakan"


"Abba Kausar ne tare da MATAR UBAN Heedaya Antyn ta kenan sune da kunne na naji Kausar tana waya suka shaidawa junan su mugun abun da suka aikata.

"Inalillahi wa ina illaihir raji'un yanzu Kausar har rashin imanin ta ya kai tabi boka"

"Umma Abba dan Allah ku taimaka kar kausar ta susuce gabadaya a kira Malam Ayuba ya hada mata magani "


"Amir karka samu damuwa gobe in Allah ya kaimu zan kirashi kai kuma kayi daki da ita dan kar a samu matsala "


Haka Amir ya sunkuceta da cizo da mitsinin da take mishi amman duk a banza dan kwata kwata baji yakeyi ba daureta gam yayi a jikin gadon sannan ya rufe kofar gefenta ya koma yanda take barbaza gashin ta tana kokarin kwance daurin da yayi mata amma ta kasa.

"Habibaty dan Allah hankalin ki ya dawo gareki kar ki barni a irin wannan rayuwar ya Allah nagode maka da batayi wani hannun ba" haka yayi ta surutai daga karshe ya tashi ya dauro alwala sallah ya shiga yi ya dade yana kai kukan shi wurin Ubangiji daga bisani ya shiga tofa addu'a a kofi da ruwa yana zuba mata har ruwan ya kare ya koma tofa mata da baki a haka ranar Amir ya kwana ido a bude abin tausayi.

Da misalin karfe 9 Abban shi ya kira Malan Ayuba nan yayi mishi bayanin komai

"Alhaji insha Allah zata samu sauki bari naje gida sai na hado mata magunguna "


Da haka yayi musu sallama ya tafi can ba'a dade ba ya dawo dauke da galoli a hannun shi


Bayani duk yanda zasuyi amfani dashi yayi musu harda wanda zasu dinga mata hayaki sosai suka mishi godiya wanda suka bashi kudi mai yawan gaske ya tafi.

Amir da kanshi yay mata wanka duk da cizo da dukan da take mishi nan ya bata dukkan wasu magani da yakamata a bata a lokacin duk da da kyar ya bata haka yazo zai saka hayakin tayo kanshi sai da taimakon Umman shi sannan ya saka hayakin a daki har ya gama.

Wayar shine take kara dubawan da zaiyi sai sunan Kausar wani wawan tsaki yaja sannan ya ajiye wayan bayan ta yanke ne Habiba ta kirashi.


"Amir idan kuna tare da Heedaya ka bata wayan na kira nata bata dauka ba gashi tace yau da sassafe zata zo "


"Wallahi Heedaya bata da lafiya wanda a halin yanzu ma bata gane komai sai sun batu ihu da dariya"


"Amir kana nufin Heedaya tayi hauka kenan"


"Kusan haka"


Kuka kawai Habiba ta barke dashi wanda a halin yanzu tana da tabbacin abokiyar zaman ta ne tai mata haka tana kukan ne ta sanar da Abban su iya tashin hankali sun shiga    kafin kace me dukka dangi fa ta dauka Heedaya ba lafiya amma duk abinda akeyi bai sanar da Rakiya ba iyakacin shi yace akan gidan Heedaya ba lafiya haka ta jajanta ya tafi harta Habiba da danyan jegonta suka dunguma sai gidan su Amir.
Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


   *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€*By Miss_ayusha*
*🌈Kainuwa writers asso🀝*      

        *4⃣3⃣&4⃣4⃣*

Basu tsaya ko ina ba sai gidan su Amir yanda sukaga Heedaya abin ba'ace komai Habiba banda kuka babu abinda takeyi yau ga abinda take gudu ma 'yar uwarta ya sameta Abban Amir da Abban Heedaya ne suke magana akan zai tafi da Heedaya gida amma fur Abban Amir yace lallai akwai matsala a komawarta amma kuma bai fada mishi ba maganar duniya yayi akan zasu tafi har Amir shi kanshi sai da ya shiga ba Abban Heedayan hak'uri da kyar ya yarda ta cigaba da zama dasu nan kuma suka Abban Amir suka shiga godiya shi da Amir d'in daga haka yan uwan zasu tafi Habiba fa tak'i tafiya sai da Abban su yay mata magana sannan ta hak'ura ta bisu suka tafi.


+

Tunda suka koma Habiba ke aikin kuka ta rasa mai ke mata dadi a rayuwartar Ahmad yayi yayi amma ina shirun nan bai samu ba.

B'angaran Heedaya fa magani akeyi ba sassauci kuma Ana sauketa mata littafi mai girma shiko Amir wani tattalinta yakeyi ga cikin dake mak'ale a jikin Heedaya sosai yake kula da ita su abokan shi babu wanda baizo ya duba Heedaya ba kullum 'yan uwan Heedaya suna tafe zuwa dubata abin nata yayi sauki ne yayi yawa duk wannan abin da akeyi Kausar bata sani yau ta kudiri niyan zuwa gidan su Amir dan ganin me yakeyi a can dayake tafiya can ita sam wannan abun bai mata dadi ba gashi dai an rabasu da Heedaya amma abin bai canza ba to kodai rashin ganin Heedayn ne yasa shi ya dawo wani iri koma dai miye ae zataje tagani.


Misalin karfe 4 tai shirin ta tsaf ta nufi gidan su Amir a parlo ta tarar dasu gaba daya har k'asa ta kai ta gaida Umma fuska sake ta amsa kamar babu wani abu amma sanda ta kai kallon ta ga Amir wani wawan harara ya watsa mata.


Umma ne kawai ta tashi ta basu wuri dan tasan akwai magana a bakin Kausar aiko kamar jira takeyi ta matsa wurin shi kan kafadar shi ta daura hannun ta.

"Haba Amir yanzu maiyasa ka gujeni dan Allah akan wani dalili ko ba komai nima matar ka ce fa inada hakki akan ka idan Heedaya ne Insha Allah za a ganta"


" kar dai kice min har gida kika biyo ni karban hakkin ki ba damuwa tashi mu tafi"

"Amir is not the matter of that kawai banajin dadin yadda kake min ne"


"Kausar nace miki ki tashi mu tafi"


Aiko ba musu ta tashi suka tafi dan ba karya tana bukatar shi isan su ba wuya Amir ya jawota jikin shi wani zafeffen kiss ya shiga kai mata ta ko ina kai Kausar fa ganin bazata iya jurewa ba ta shiga maida shi dan ba karya tayi missing dinshi.

Nan fa abu ya gagara sai zubewa sukayi a kan gado Kausar nan ta tube ma Amir kaya ganin abinfa zai fi karfina yasa na bar musu d'akin.


Bayan wani lokaci Amir nagani ya fito daure da towel a jikin shi wani kayan ya saka ya feshi jikin shi da turare sannan yayi niyan fita

"Amir ina kuma zakaje? "


"Kausar bana biya miki buk'atan ki ba akwai abinda nakeson yi a gida shiyasa"

"Amir dan Allah ka dawo gida pls"


"Kausar tafiya ma zanyi zamuyi wani aiki a kano kuma zamu kai kwana biyu"

"To Amir Allah ya kaimun kai lafiya yadawo da kai lafiya"


"Amin ya amsa mata"


Har bakin kofa ta rakashi sannan ta koma cikin gida tsabar murna ganin Amir kamar bai damu da Heedaya ba yasa ta kiran duk kawayen ta harta Rakiya sai da ta kira ta sanar dasu halin da ake ciki.Haka rayuwa ta cigaba da tafiya tsakanin Amir da Heedaya kullum sai Kausar ta nemi Amir sannan zai biya mata buk'atan ta duk sanda tace ya kwana uzuri yake bata abin tun bai damunta har ya soma damunta anya bazata koma wurin bokan nan ba tunda dai tasan wurin itama yanzu kai haka dai taita sake sake daga karshe ta hak'ura.


A kwana a tashi ba wuya cikin Heedaya sai girma yakeyi b'angaran Abbanta shima ba'a barshi a baya ba saukan alkur'ani ake mata ba kama hannun yaro.Bayan wata bakwai


Kamar yadda ya saba yana mak'ale a jikinta yana maganganun shi ta shiga ihu tana kurkurwa a'a abu kamar wasa ba Heedaya yak'i sakin ta Amir iya damuwa ya damu Malam Ayuba suka kira nan ya shaida musu babu komai daureta kamar yadda ya saba yayi ya fita a d'akin ma gabadaya tare suka zauna dasu Abbban suna hira kamar daga sama sukaji kukan jariri a firgice Amir suka mike gabadayan su sukai d'akin.
Miss_ayushaπŸ’‹πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


    *MATAR UBA*


πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*By Miss_ayusha*

*🌈Kainuwa writers asso🀝*


πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š


         *4⃣5⃣&4⃣6⃣*

Abinda ya basu mamaki bai wuce ganin 'ya yan da Heedaya ta haifo ba 'yan biyu abinsu a kasa da hanzari Umma ta karasa wurin ta bata bi ta kanta ba sai ta kan yaran daukan su tayi ta fita dasu shiko Amir kusan ta yaje yanda yadan tabata.

+

"Habibaty dan Allah ki dawo hayyacin ki ki dawo kiga babies din da kika haifa mana kuka kuma ya shiga yi kadan kadan"

"Habibi"

A firgice Amir ya kalleta nuskuta idon shi ya shiga yi anya ba mafarki yakeyi ba yaushe rabon dayaji muryar abin son shi


"Habibaty dan Allah kar ki sake komawa wannan halin dan Allah karki sake kinji"

"Habibi ka tashe to ji yadda ka daure ni kamar nayo sata"

"Idan bahaka nayi miki bane guduwa zakiyi ai shiyasa na daure miki hannu"


"Bangane ba"


"It's a long story yanzu ki tashi ki gyara jikin ki"

Da kanshi ya kaita har toilet ita dai tana mamakin ya ta ganta haka amma koma meye zai yi mata bayani ai


Umma ce ta shigo cikin d'akin

"Amir kardai ita kadai ka bari a toilet sai taje taji ciwo ko"

"Umma Heedaya ta dawo dai dai yau Allah ya karba addu'an mu"


Heedaya dake cikin toilet sae anan ta lura da ba gidan su bane sosai take sauraran abinda suke fada tunani ta fara to ko dai hauka tayi ne dan ga dukkan alamu taga haka tunda har daure ta sukayi da wannan tunanin ta shiga yin wanka.


Murna wurin Umma ba'a magana gashi ta gama gyara yaran tas abinsu sai zaman jiran Heedaya kuma da akeyi nan fa Umman Amir ta fada ma Abban shi aiko shi din ma murna ne ya gama cika shi Abban Heedaya da suke hanyar zuwa gidan Abban Amir ya kira yake sanar dashi hamdala ya shiga yi wanda bazai fadu ba.


B'angaran Rakiya abin fa ba sauki hauka takeyi wanda ta fita titi tana tambatse ihu ta da dariyan hauka takeyi haka take tafiya bata tsaya a ko ina ba sai kofar gidan su Amir ta b'angaran  Kausar ma haka abin yake duk kansu abu daya ne yake damun su

Cikin gidan kuwa murna farin ciki ba'a magana kowa sae nan nan yake da Heedaya kamar kwai haka aka maidata ana haka su Dr Tsalha suka zo har bakin gate Amir ya fito aiko tuni suka shige cikin gidan wanda tsaban mamaki ya rasa me zaiyi.

Cikin gidan gaba daya suka dunguma sae parlon anan suka tarar da kowa nan kuwa Rakiya da Kausar suka shiga tunawa kansu asiri kuka a wurin Heedaya da Habiba ba'a magana itakam da bata shiga sabgar ta amma har Kausar tai mata wannan cutarwar haka ko Abban Amir ya kira Umman Kausar nan da nan tazo taji abinda 'yar tata tayi kuka wiwi ta shiga yi kamar me tana ala wadaran da hali irin na Kausar itako Rakiya Abban Heedaya a take ya manna mata red card din ta itako da bata san abinda akeyi ba sai dariya take tuni ta kama hanyar fita aiko ba wata wata mota yayi gaba da ita nan fa mutane suka taru gidan su Amir akayi da ita amma fur Abban Heedaya yace a fita da ita mutane basu fi goma ba wanda suka sallaceta suka kaita.

Itako b'angaran Kausar rufeta sukayi a wani d'aki wanda Maman Kausar ta shiga rokon musu gafara da kyar da lallashi aka shawo kan Heedaya tace ta yafe amma Abban ta ko gefen su bai kalla ba.


Itama falmata ta wurin ta haka take yawo a titi tana sunbatu kowa ya ganta sae yayi wadaran da kalaman da take fadi.

A cikin gidan su Amir aka yayyafe juna inda su Abban kausar suka koma gidan su inda Amir da Heedaya suka cigaba da zama a gidan.

Haka rayuwar su ta kasance yanda akayi taron suna mace taci sunan Umman su Heedaya namiji yaci sunan Abban Amir haka rayuwar su take cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.

Bayan Arba'in


Shiri sosai akai ma Heedaya tsaf Umman Amir ta gyarata da misalin karfe 8 Amir ya dau matarshi suka koma gidan su

Gidan su Rakiya Abban su ya saka Heedaya a gaba nasiha sosai ya mata nasiha aiko har gidan su Heedaya ta daura niyar zuwa da Habiba kuwa.

Ranar fa tsakanin Amir da Heedaya babu kanta ba'a magana sai wanda ya gani nikam ganin abin yafi karfina yasa nayi gaba na barsu.

Fanni Munnira fa abu ba sauki har an kamalla komai na auran ta jira kawai akeyi rana tazo


Ta wurin kawayen Kausar ma har gidan Heedaya suka zo neman yafiyar ta aiko ta yafe musu haka Rahina ma tazo duk sun nemi yafiyar juna daganan kuma zaman lafiya ya samu.


Sosai Rahina ta maida hankalin ta wurin neman mijin aure Abban su ma ya sami matar da zai aura kasancewar ba bikin yara bane yasa su aka daura auran nan babu wani bata lokaci kuwa ta tare.

Itama ta b'angaran Munnira an daura auran su da Kamis abinsu gwanin sha'awa.

Yaran Heedaya sai girma sukeyi wanda kowa ya gansu sai sun bashi sha'awa sosai da shak'uwa kuwa tsakain masoyan ba'a magana sai dai Allah ya kara dankon soyayya.
ALHAMDULILLAHI anan na kawo karshen wannan littafi wurin danayi ba dai dai ba ubangiji Allah ya yafemin.


Godiya gareku masoya wannan littafi a duk yanda kuke Allah ya bar so da kauna sai kuma Allah ya sake had'a mu littafi na gaba mai suna .........


Miss_ayushaπŸ’‹

Post a Comment for "MATAR UBA By Miss_ayusha"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...