LABARIN RAYUWATA CHAPTER 6 BY Ayeshay bee - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

LABARIN RAYUWATA CHAPTER 6 BY Ayeshay bee

LABARIN RAYUWATA CHAPTER 6 BY Ayeshay bee

- - Post a Comment

LABARIN RAYUWATA CHAPTER 6 BY Ayeshay bee                  Www.bankinhausanovels.com.ng Washegarin Dinner in ma ba karamin kayatuwa event in yayi ba. Da farko dai Amaryan wani hadadden lace ta sa su kayi anko da angon ta da ya sha many an Maya, sai daga baya su ka canja I zuwa outfit insu na larabawa. Events yayi dadi sai sam barka, Yanuwa su ka koma in da su ka fito aka bar Amarya da Ango da za suyi honeymoon a kasan.


Kwana biyu su ka jera ita da Faroukh Machina su na kewaya birnin mahe island, ba dai wani magana tsakanin su but it like that are all witnessing the attraction between them. It become intense lokacin da su ka fara fita shopping, suna different games a tare sai kace wasu couples. Sai dai dare nayi kowa ke kama hanyan masaukin shi. Ba ma mahe island kawai ba, ya dauke ts sun je different islands da ke cikin seychelles wanda ta taba zuwa da wanda ma ba ta san su ba, they explore the country sosai a tare, it suvh a bliss for her.


Har hotel in da take Rawan da mijin ta suka kawo mata ziyara, rungume ta Rawan in tayi tana ta faman mata godiya. "I can't believe you make this happen Umayamah you are the best" sun taba hira kafin Rawan In tayi requiring account details inta. Sai bayan ta tafi ta ke ganin alert, she is so shock da irin kudin da ta turo mata, ta kira mata complain ma ce mata tayi its a gift from her dad da kuma Adam.

Da ta sanar ma Faroukh machina kam bai wani yi mamaki, domin shi yasan dukiyan nasu. Ranar da yamma suna zaune a apartment in Faroukh in suna kallon wani movie da ya matukar jan hankalin su ta sanar mishi tana son ta wuce because its getting late.


"But you can sleep here ai" dan zaro idanu tayi tace "No i have to go" dan bata rai yayi, ya cire glasses in da ke idanuwan shi "Kina tsoron am going to do something ne?"


Shaking head inta tayi tace "Aa am avoiding issues ne kawai" ba ta jira cewan shi ba ta mike, dan yanda ta ke ji minti daya ta kara tare dashi, anything can happen and she is done with everything related to boys.

"We shall talk tomorrow" ta fada tana kokarin karasa wa wurin kofan, da azama ya is a gare ta ya jawo hannayen ta duka biyu. Hakan yasa tayi saurin sakin bag inta dake hannun ta, kokarin yake yaga sun hada ido sai dai hakan ya faskara, karshe ma runtse idanuwan ta tayi gam tana ji wani irin abu na mata yawa. Ba ta kwace hannun ta daga nashi ba ba sai dan ba zata iya ba sai dai dan wani irin fadin da ta ke ji yana ratsa ta, it a moment she wouldn't like to end. Jan ta yayi har zuwa kan couch ya made kafafuwan shi kaman wani yaro karami yayi tagumi yana kallon ta. Ba ta dai ce komai ba haka kuma ta kasa yin wani motsi. Sao da ya gaji dan kanshi yace "Umaymah why are you trying to avoid what is between us?"


Mamaki ne ya bayyana a fuskan ta, sai dai kana ganin shi zama san pretense ne kawai "Ni fa ban iya kwana kwana ba Umaymah, when I like something i go for it immediately i get the message and you know we like each other why are you voiding us the right to?" Tsit tayi, tabbas tayi expecting fiye da haka kuma sai dai yanzu da yake faruwan sai ta ke jin rashin jin dadin faruwan shi. He surely have so much effect on her sai dai duk yanda ta ke ji, duk yanda zuciyan ta ke azalzalan ta she is willing to resist everything, willing to resist the urge to fall for him. Runtse idanun ta tayi saboda zafin abinda ta ke niyyan furtawa a gare shi "Am sorry Faroukh if i make you feel that way, ban ce nima ban jin abinda make jin ba sai dai wlh ba zan iya, i just can't do it" hawaye ne su ka fara fita sharara a idanuwan ta.


"But why?" Ya fada da kauraran murya, ba ta amsa shi saboda haka yace "Dan Allah ki daina kuka muyi magana" da kyar ya iya lallashin ta ta dawo hayyacin ta, ita kanta mamakin kukan nata take, she don't know she can still be weak like this, she have been strong for years ba ta tuna sanda tayi hawaye, kai duk nacin Namiji ma ba ta bari wani abu ya shiga tsakanin su.


"Kar ka ga laifina dan Allah ina so kaji dalilina a yanzu" bai tmby ta ta fara bashi labarin. "A Maiduguri na taso, baba na ba laifi yana da kudi na rufin asiri dai dai gwargwada, matan shi uku, mahaifiyata ce ta farko. Nice ta biyu a gidan sannan kuma a gabadaya gidan ma, kanne ko kadan ya rage su cika Ashirin saboda duk mata banana Allah ya basu yara dayawa. Gsky Alhmdlh gidan mu ba wani rashin hankali sosai, sai dan yan kanana nan maganganu da za kaji ana yi kasa kasa. Bsrin ma akan yan dakinmu ko dan saboda soyayyan da mahaifiyar ta ke mana, ita mace mai wa yaran ta wani irin makahon so da a ko ina bata iya boyen shi. Zaka ji ta na Umaymah na, Aisha na, Aliyu na da sauran. Kullum dai kaji ta maganan yaran ta ne a bakin ta. Mahaifin mu kam bai wani nuna banbanci tsakanin mu kuma gidan mu gidan Mutunci ne sai Sam barka. Matsala ta ta fara ne ranar da na dauki kafa na tafi garin Kaduna wurin kanwar mama na. Sauka ne garin Kaduna kenan na jawo trolley na ina Neman taran abun hawa sai ga mota ta tsaya a gabana, loakcin duka duka SS1 nake hakan yasa ko kallon motan ban yi ba. Amma bawan Allahn nan sai da ya san yanda yayi yayi convincing ina na shiga motan shi. A hanya sai dadin baki ya ke min ta hanya gaya min kalamai dada da har mu ka isa gidan da zani. Wayata ya amsa ya samin numban shi, tun daga ranar ya fara kira na a wayan tun ban sakewa dashi har na sake, Barin ma in ina tuno labaran da kawayen na ke bani kan samarin su ni kuma bani da su, tuni na saki jiki na dashi ko bakomai in na koma maid na samu labarin da zan ba kawayena. Zayd maye ne a fagen soyayya, cikin kwanaki kadan sai da ya tabbatar ya kama ni a hannu, sau daya na sha Satan jiki mu fita tare ya kaini shopping, da yake ma a Abuja yake sai da kullum yana hanyan Kaduna saboda ni har na gama hutun. Lokacin kuwa ba abinda na sani bayan shi, komai ma in dai daga gare shi ne to fa ban ganin bakin shi, soyayyan shi kawai na sani, na so zayd fiye da dukkan wani iyawata, na mishi soyayyan da banji zan kara ma wani da Namiji a duniya kuma. Babban dana Sanin da nayi kuwa shine lokacin da zan koma maid, har moto park aka sani a mota sai da na bari ya fara tafiya nayi wayan karya, nan da nan na saki kuwa ina fadin a ajiye ni an mana rashi yanzun nan dole in koma. Ko tsayawa sauraran driver in da yake cewa ya za ayi da kudin ban yi ba. Ina fita na kira Zayd ya zo ya dauke ni sai Abuja. Suka duka lokacin shekaruna sha biyar ne amma haka na sabi jiki na bi zayd hotel saboda ba abinda na sani banda shi. Ba irin soyayyan duniya da zayd bai nuna min, ni kuwa na shgalta gabadaya da irin duniyan da na fada. Abu daya da ya kara dulmiyar dani shine yanda yayi ta kashe min kudi, ba Wai akwai abinda na nema na rasa bane Aa, abin kawa na duniya Wanda na san a gidan ba za ataba siyan min shi ba Zayd ya dinga siya min, ya canja min waya na wullar da waccan saboda kar ma a same ni daga gida. Sai dai dare nayi ya dauki hanyan da ya ke bukata, bai taba sa hannun shi a jiki na ba hakan yasa ko kuma rashin wayau ne ya sani tunanin ba abinda zai min. A daren ya karbi budurcina ya gurza ni son ranshi kuwa, daga baya kuwa ya dinga tarairayata har asibit ya kai ni da ke bakarami wuya na sha ba. Dare nayi ya kara komawa, har yau what am guilty of kuwa shine I enjoy everything he did to me. Kwana na biyu a wurin shi yana nuna min tsantsar kulawa da soyayyar shi da ta matukar shagaltar dani. Ticket in jirgi ya siya min ya raka ni har airport na tafi maiduguri. Sai bayan mun rabu dashi na fara tunanin mai zan fada a gida, lokacin gabana ya fara faduwa,  shiyasa ina isa garin Maiduguri na nufi gidan su kawata,  nan na ajiye duk wani abu da nasan zayd ya siyan min banda waya, ita ta bani tsohon kayan ta nasa duk na firgice sannan na tafi gifa. Ashe wai hankalin su gabadaua a tashe yake, har Anty na da naje wurin ta a kaduna na same su sunyi cirko cirko su ka dinga kallo na,  mamana kawai ta iya min magana. "Sannu" ita ma kawai tace ta fisgi hannu na zuwa daki, abinda ba ta taba min ba iya rayuwar ta tamu,  mari kake ji ko ta ina sai da ta gaji sannan ta fashe da kuka ta bar dakin, to nima dai kukan nake yi. Ba kuma wanda ya kara bina sai da baba ya dawo gida,  salin alin ya kira ni yana tmby na ina yaje, labarin da na shiryo na motan mu tayi hatsari nima da kyar na sha kwana na uku a wani kauye. Dariya ya fara yi sai yace "Au banda iskancin hadda karya kuma kika koyo?" Da farko nayi mamaki sai da naji Antyn kaduna na fadin "Umaymah in kika je? Ba kiyi tunanin zamu je muyi bincike a tashan motan bane? Baki na da driver in mu kayi magana ya sanar min kin sauka bayan kin sanar an muku rashi" Tab! Gabadaya ma ni tunanin bai zo min ba,  daganan kuma banda wani bakin magana duk zagi da fadan da aka dinga min. Ga gori daga abokan zaman mama, suna fadin soyayyan da ta ke nuna mana ne ya jawo komai. zayd ko soyyaya mu ka ci dayi, in takaice ma har zuwa yayi takanas daga Abuja zuwa maid kawai dan ya ganni, haka na kara bin shi hotel mu ka aikata masha'anmu. Kwanan shi uku a maiduguri,  shi da wani abokin shi wai Hafeez,  kullum sai mun hadu dashi. Tashin hankalina ya fara ne bayan two weeks da zuwan shi maiduguri,  gabadaya sai zayd ya dauke min wuta, ko na kira shi bai cika dauka ba wani lokaci ma abokin shin nan Hafeez ke dauka ya na min wasu maganganun banza, na tura text sau da dama,  a cikin har da wanda nake fada mishi ko da ya same ni ne ya ke min hakan. Daga karashe kirana yayi ya wanke ni akan kar in sake kiran shi. Ka tuna nace maka lokacin SS1 nake, gabadaya shekaruna 15 ban sa mai ke min ciwo ba, cigaba da kiran nasa nayi karshe ma sai yayi blocking. I felt so heartbroken to an extend da harna fara fita hayyacina, gida kullum cikin ciwo, tun dawa na daga kaduna iyaye na su ka fita sabga ta hakan yasa ni kadai na ke nukurkusa ko kanne na ba kowa ke tanka ni ba. Duk abinda zayd ya min bai hana na cigaba da kiran shi da duk numban da na samu ba, sai dai kowani kira da irin nashi wulakancin.


Da ciwo ya cini sosai, dole Mamana ta sani a gaba mu kaje asibitisaboda baba kamya zare hannun shi akaina, barin ma da ya samu labarin naje hotel wurin saurayi. Sai dai duk wani test na typhoid da malaria,  sugar da sauran su anyi amma ba a ganin komai sai kuwa jinina da yayi kasa. Sosai na yi wani mahaukacin jinya duk maganin da ake bani ba sa min aiki, har makaranta dole tasa na ajiye agefe banda karewa ba abinda nake. Nan fa dr yayi shawaran yi min scanning, gwajin farko na Hiv ya nuna positive, shi kan shi wanda yayi test dan rudewan ganin karantar shekaru na sai da ya dinga yin test in da different kits amma it showing the same thing. Gashi lokaci ne da ake mugun kyaman cutan, hmm Faroukh naga rayuwa, takai ta kawo a gidan mu Mamana ne kawai ke iya min magana har ta bani abinci da magani shi ma cup, spoon da plate ina daban a gidan kullum karewa nake. A cikin wannan rayuwan na ziyarci kawata Siyama, da tun farko ita na kai wa ajiyan kayan da Zayd ya bani. Yanda kasan karya haka siyama ta min, sai banyi wani mamaki ba ganin yan uwana ma sun ki ni balle ita. Rayuwa fa gabadaya ta juya min, bayan na fito gidan su ina kuka ne na hadu da wata mata neighbors in su siyaman, a kullum duniya in na ganta ni da siyama mun di ga tsine tsine kenan saboda sanin da kowa ya mata a harkar mata gashi duk na ganta ta dinga bina da wani mugun kallo. Yanzun ma zuwa wuri na tayi tana tmby na lfy? Banda wani mafita sai na tanka ta barin ma da na fahimci ita kadai ke burin min magana ahalin da nake ciki. Jana tayi gidan ta, sai da na natsa ta tmbyn abinda ke faruwa,  na ko fada mata komai. Murmushi naga tayi tace "Ai su daman mutane haka su ke, kar ki wani damu domin kin zo inda za a tarairaye ki" Wani irin kulawa ta bani na musamman, gidan mu kuwa ba wanda ya wani damu ban dawo ba sai mamana ita ma da taji labarin inda nake tazo ta sameni fir na ki binta nace mata zan zauna inda ba a kayamata. Wani irin soyyaya Hajiya safiyya ta nuna min sannan a hankali tana sa min ra'ayin harkan ta tun ina ja da baya amma tarairayan da takebani na yaudarata harna bada kai bori ya hau. Duniya ta dawo min sabuwa,  zayd ko tuni na share shi sai dai na dauki alkawarin rama abinda ya min ko da kuwa ta wani hanya ne, kullum duniya kara goge na ke cikin sabuwan duniyata, ga kudi da su ke zaman min duk lokacin da nake so. Da maganaya fra yawa, ga mamana ta na zuwagidan Hajiya yasa Hajiyan ta kwashinimu kayi kano inda na cigaba da cin kare na babu babbaka sai bayan rasuwan tana koma maiduguri na fara zaman kai na ta duk hanyan da yazo min. Toh Faroukh kaji labarina a takaice, nasan ba za kaso had a zuri'a da mai fama da lalura irin tawa ba da kuma rikakkiyar yar lesbian" Gumin da ya fara keto mishi ya share, still idanuwan shi na kanta.


"Abinda ya wuce ya wuce, but everything is wrong in the way you solve your problem"


Amincewa tayi "Da na koma Kano na koma schl, i study psychology in university kuma nayi realizing duk wani mistakes ina,  i just can't clear them but can you believe yanda yan uwana ke sona a yanzu? Kowa alfahari ua ke da cigaba na wanda da kudin abinda su ke zagi na akai nayi su."


"Ai yanzu an dauki kudi sune mutum Umaymah, but tell me kin dau fansan?"

"Shi ya kawo ni kasan nan" da sauri ya daga kai yana kallon ta"Zayd in na garin nan ne?"


"Aa, there is this girl, daya daga cikin yaran da nake mu'amala dasu ta hada ni da, ina ganin ta nasan cewa she is the one i've been looking. Ta amince da bukata ta, muna gab da cin nasara nayi realizing it can't be good sai aka ci saa ita ma yarinyar ta janye and i don't know what happen but currently tana hannun hukuma ana zargin ta da yunkure kisan shi zayd in" rike kai Farokh machina yayi domin shi wannan kwamacalan ya mishi yawa.


"Amma kina ganin yarinyar za ta aikata?" A hankali ta girgiza kai "Nasan Suhaimaba za tayi ba"


"Amma meye sa ba kije kin kareta ba?" Kallon shi tayi kaman wacce ke shirin dago wani abu tace "Faroukh i have a reputation to save, am a public figure people looks of to me" In understanding ya juya kanshi. Ba su wani kara magana ba ya lallabe ta ta kwana gidan, ta riga da ta san cewa yanzi tunda ya san me ke faruwa da ita ba abinda zai yi yunkurin mata domin a yanda take ji ko ya neme ta bazata iya hana shi but now da ta fada mishi labarinta she feels ease knowing ba ta da matsalan rashin yafe wa kanta da zata yi muddin ta sa mishi cutan nan.


...


Bayan sun rabu da Dr Fahad, Barr daukan hanya kaduna yayi. Gidan Anty ya fara zuwa sai dai yana shiga gidan ya hadu da Anisa banda kuka ba abinda take. Yana cikin tmbyn ta abinda ya same ta sai ga maryam ma ta fito daga dakin, da alamun muryan shine ya fiddo da ita. Sake baki yayi yana kallon ta ita ma kukan ta ke "mimi wha.." Katse shi tayi da cewa "Why why?" Still dai bai fahimce taba,  isa gare ta yayi ya riko kafadun ta "Tell me what is happening Mimi"


A hankaki ta furta "Anty Anty" kwalalo idanu yayi yana fadin "meya samu Antyn mimi,  Anisa tell me what is hapening mana"


"Uncle Musty why not ba za ka ba wani case in nan bane wai? Ba kayi tunanin yin shi zai sa Mom cikin matsala ba?" Anisa ce ke magana yayi da kwalla ke zuba a idanun ta. Juyawa yayi ya kalli maryam tace "She almost had a stroke fa, you are accusing her own child akan wata karuwa Abban Haydar" bai damu da kiran suhaima da tayi karuwa ba yace "My God! Mimi ina Antyn yanzu?"


"Tana asibiti Dad ke kanta,  an hana kowa zuwa wurin ta" zaman dirshan yayi ya zuba tagumi cikin rashin sanin abun yi.Jigum Mustapha ya zama kafin farfadowan Anty, ko bayan ta farfado ma barin ta aka yi a asibiti ba abarin wani ya zauna gun ta. So Mustapha bai samu daman komawa Abuja ba duk yanda ya so hakan.1

Yana nan garin kaduna har aka sallami Antyn sai ranar su ka hadu da Antyn, kallon shi kawai tayi ta dauke kai, to duk sanda ta mishi wannan ya san ba karamin fushi take dashi ba, barin ma yanzu da yake tunanin shine sila. Sai da ya bari a dan natsa washegarin dawowan ta yaje ya same ta its kadai a dakin ta. Ba ta mishi magana ba dai haka kuma bata daure fuska ba. A hankali ya taka har ya je gaban ta ya zauna, kwanciya kuma yayi ya daura kanshi akan cinyan ta. Yayi mamakin sa hannunta da tayi cikin suman shi tana shafawa. "Little drop that case bana ka bane na fada maka kaki ji,  kai ba ka tsoron ba wani abu ya faru da kai?"4


 

Murmushi yayi sannan ya dago yana kallon ta ya dan dukar da kanshi "Anty na ke kike min wa'azi akan taimaka ma duk wanda ya ke cikin halin neman taimako, yarinyar nan looks so innocent i have to help her"


"Looks can be deceiving Little kuma ma in taimakon kake so ai ba dole sai kai za kayi case in nan ba"

"Na riga na fara Anty kuma wlh ba accusing Faroukh nake ba kawai dai ina tunanin akwai abinda ya sani wanda ya boye min" shiru tayi kaman mai wani lissafi "Ba zan ce Faroukh ba zai iya aika ta koma mai kake zargin yayi ba but little Faroukh is my son,  kai kawun shine da kuka matukar shakuwa shin ko ya yi abu kai ba mai iya kare shi bane?"


"Faroukh bai yi ma komai ba Anty, ai muna magana dashi kuma ko bayan zaman court in ba abinda ya dauka na fushi tsakaninmu, min samu kyakyawam fahimta saboda haka Dan Allah ki kwantar da hankalin ki Anty na, i have nothing against my boy" jinjina kai tayi tace "ban son hana ka abinda kayi niyya saboda a ko da yaushe kai mai yin biyyayane a gare ni, ba case in ku bane ya sani a halin da nake ciki little kawai news in yazo min ne a lokacin da nake cikin wahala"

A tsorace yace "me ke damun ki Anty na?"


"Stress little kuma jini na hawa"


"Ya ilahi!" Ya furta sannan yace "please Anty ki ajiye lecturing in nan" da ido ta amsa shi.


...


Abuja, Nigeria.


Dr Fahad da Barr zaune, kokari su ke su saurari labarin suhaima da har ya jawo mata fadawa irin wannan mummunar rayuwan haka. Sai dai abin yana neman ya gagara domin dai Suhaima ta ki basu hadin kai. Ita a ganin ta ko ta rayiwan ma ba wani amfani don haka she want to end everything for good.


"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa,  ta gaji da kukan ne saboda Bai da  amfani a gareta domin bakin tabon da ke jikin ta ba zai taba gogewa ba.


"Karuwan ci? Tabbas nayi shi haka kuma na kasance maci amana ga wadanda su ka bani yarda, shin me kuma kuke so ku sani bayan wannan? Ku barni kawai ayi hukuncin da ya dacen ina ganin nayi deserving komai ma.


"Kin yi yunkurin kashe Zayd" kaman ta daga kai ko za su kyale ta sai dai kalman kisan ya mata mugun nauyin da take jin ba ta ma kanta adalci ba in har ta amince da abinda ba tayin ba.


"Then ki bar mu muyi abinda ya dace" ba wanda yace komai ba har bayan yan mintunan "Suhaima please tell us" Dr Fahad ya fada cikin marairaicewa. Ita kam mamakin yanda su ka dage suna rokon ta akan abinda tasan ita zai amfana. Sai dai tasan duk yanda ta so basu labarin rayuwan ta yana da tsawon da ba zata iya zayyana shi cikin lokaci kankani ba. Ba ma wannan ba tukun, ba taji bakin ta xai iya dauriyan furta wahalolin da su ka mata katsalanda a dukkan rayuwan ta.1


Yanayin rashin natsuwan ta karara su ka fahimta, hakan yasa su ka yanke shawaran barin ta har sai lokacin da ta ke jin za ta iya. "Shknn Suhaima tunda kin zabi kin maganan,  ina so ki sani a kowani hali ni mai iya tsaya miki ne haka kuma yanzu ma ba gazawan zanyi ba. A dan kalilan labaran da kika bani tsakanin ki da Zayd in zanyi fatan samun hujjar da za ta kubutar da ke. Saidai ina so ki sani shi shari'ah yana da wani irin cakwakwiya da mu da ke cikin ta ne kawai mu ka fahimci hakan. Za ki iya ganin ke kina da iya gskyn ma fa in bamu da cikakkiyar hujjan da zai tabbatar da gskyn naki sai kiga kin kwana a ciki. Mutane ke ganin kotu wuri ne da ake fida mai gsky aka kama mai laifi,  sai dai mafi akasari abun ba haka yake bane. Ba kuma na gaya miki hakan bane da kin karaya,  Aa ina so dai ki sa a ranki komai na iya faruwa." Ba suhaima kadai ba hatta Dr Fahad jikin shi yayi sanyi, zai so kadaice wa da Suhaiman ko dan tausasa ta taba barristern abinda ya ke bukata sai dai shi ma he want to respect her decision.


"I don't know ko zaki ji dadin abinda nayi,  sorry ban fada miki ba munyi magana da Zeenah za tazo ku zauna tare har zuwa agama shari'an" da dan mamaki a fuskanta tace wa barristern "zeenah zata zo? Anya xa ta iya zama a wuri daya kuwa?"


"Ta dai Amince and we are talking with her tana fada min abubuwan da ta sani" da kai ta amsa shi wannan karon a zuciyan ta tana tunanin me zeenah za ta sani da har zata iya fadawa Barrister. Duk ta san akwai ta da dan banzan surutu amma kuma tasan ita ba ta taba fada mata komai ba balle kuma faree'ah da tasu bata taba zuwa daya ba.


Su Dr da Barr ba su dade da tafiya ba sai ga zeenah kuwa da katon trolley inta. Rungume juna su kayi da suhaima,  ba ta san lokacin da ta saki hawaye ba tana fadin "kawa da gaske dai kece" dariya kawai zeena ta dinga yi tana kallon reaction in suhaima. "Ya bayan rabu?" Zeenan ta tmby, dan tabe fuska suhaima tayi tace "gamu nan dai kawai kawa, atleast we are still alive"


"How is your case kuma?" Wannan karon suhaima ba ta amsa tmbyn ba sai ma tashi da tayi da niyyan kawo mata ruwa da abinci. Da dai zeena ta fahimci kawarta ta ba ta son ayi maganan sai ita ma kawao ta share, ta san komai akwai lokacin sa haka kuma ba ta shakkan za su gangaro wannan.


...


Barr kam yana barin apartment in numban El-yas ya kira. Har Company insu yaje ya same shi, sanin wurin is not safe suyi magana yasa ya ja shi zuwa wani restaurant.


"Uncle musty any news ne akan case in?" Girgoza kai barr yayi yace "Ina fatan dai samun news in daga gareka"

"Toh fah" El-yas ya fada, murmushi barr yayi yana dan taba gemun shi. "Ina son any information akan Hafeez, friend in oganka." Dan zaro idanu El-yas yayi kafin yace "Oga Hafeez, i don't really know much about him ai saboda ba wai yana aiki damu directly bane though shi ya ke fidda duk wani tsari da abinda za ayi a company in Al-mansur both telecom da drink shop, he is the director"


"How possible kuma ba za kuyi tare ba? Taya yake sanin duk abubuwan da ke faruwa to?" Kyabe baki El-yas yayi yace "mu ma mun jima muna mamaki, both he always makes it work yana kokari sosai gsky. I think dan uwan oga ne fa ma ko kuma neighbors because tjey have always been together tunda nasan su" da kai Barr ya amsa sannan ya kara tmbyn shi "akwai wani abu da ka taba fahimta tsakanin su da Suhaima?" Shiru El-yas yayi yana tuanin kafin ya tafa hannun shi da karfi "He seems to like her first day in da muka fara haduwa da ita a lagos"


"Daga nan kuma ba wani abu da ka kara gani?"

"Babu gsky" jinjina kai Barr yayi sannan yace "ina son tmbyn ka wasu abubuwa game da abokin ka faroukh, ina ganin kaman akwai wanda ya sa shi aiki akan suhaima, i mean not in a bad way fa amma" dan shiru El-yas yayi dan yatsan shi a bakin shi. Can kuma yayi saurin girgiza kai "Faroukh got the job through me kuma bayan haka ma i was the one that convince him akan aikin. Bayan haka kuma ban tunanin akwai wani wanda Faroukh zai iya ma aiki ya sa mishi ido, bai son shiga harkar da ba nashi ba" da kai Barr ya amsa, sannan ya mai godiya su ka gaisa.


Ya riga ya san next target shi shine nemo waye Hafeez, me kuma yasa Zayd ya bashi ragaman kula da hidimomin shi. He can't do it alone, kuma yana ganin Dr Fahad ya fishi connections a Abuja don haka ya kira shi a waya su kayi magana.


The next target shine ya nemo Faree'ah sannan kuma yana bukatar sanin ina Amal ta ke da Umaymah Amin. Zuwan shi Vows Uku amma an tabbatar mishi ba ta garin Abuja kaman yanda Faree'ah bata nan ita ma. Hakan yasa shi tunanin ba shakka tabbas akwai wani abu a kasa dole kuma ya nemo koma menene sai dai kuma ta ina zai fara? Suhaima, shine kawai amsa da zuciyan shi ta bashi. Bai tsaya wata wata ba ya fisgi motan nashi zuwa apartment in. Ko da yayi Sallama Zeena kawai ya samu a falo, bayan sun gaisa ya mata sannu da zuwa. Bai tmby ina Suhaiman ba instead sai ya nemi magana da ita zeenan.


"Wai shin ina Faree'ah take ne?" Zaro idanu tayi kafin tace "Ai in zaka je gidan yancinmu, ina ni kadai ce ba za a iya tmbyn wani abu akan Faree'ah ba"


"To amma ko meyesa hakan?"


Kai tsaye tace "saboda kiyayya ke tsakanin mu" folding lips in shi yayi,  shi dai yanzu wannan ba shine damuwan shi don haka yace "Amma ya akayi su ke shiri da Faree'ah bayan abindake tsakanin su." Ko dabai fadi sunan ba zeenah ta gane suhaima ya ke nufi "To ai ita ta kawo ta gidan, tare su ke suna shiri sosai ko a gidan ma dakin faree'ah Suhaima ta zauna" jinjina kai yayi yace "Amma na tuna a kaduna da na sanar miki an kama Suhaima kin ce shegiya Faree. Zeenah in akwai abinda kika sani Dan Allah ki fada min kinji?"


Kyabe baki tayi tace "Da gaske Faree'a bata nan sai dai naji ana fadin tabi wani sabon Saurayin ta Dubai" shiru yayi yana wani nazarin da ya ke fatan ya kasance gsky. "Kin san saurayin?"2


"Bansan ko zan iya gane shi ba amma na ganshi da ita a mashaya sau daya" da sauri Barr ya ciro mata hoton Hafeez yana nuna mata. Ta dade tana kallon hoton can tace "ni kam ban gane amma kaman suna yanayi, i wasn't lokacin da na gansu" daga nan pics in Hafeez dayawa ya dingagwada mata sai dai ba wanda ta iya tabbatar wa ko shi dinne.


Ko da Suhaima ta fito ta same su basu wani yi magana sosai ba har Dr Fahad ya kira Barr akan shima gashinan zuwa gidan.


"Hafeez Bature sunan shi, dan uwan makotan Al-mansur in ne tun yaran na kanana lokacin suna unguwan kubwa. Sun yi zumunci sosai da makotan nasu, shi kuma Hafeez lokacin yazo hutu gidan Neighbors in,  a hankali ya fara shiga gidan Al-mansur har ya zama dan gida. Ta haka su ka saba da Zayd tun yana karami, daga haka ma bayan su xayd sun tashi daga kubwa sai ya zamto ko yazo Abujan ba gidan yan uwan nashi ya ke zuwa ba. Yana family house in Al-mansur" Dr Fahad ke bayanin da Barr ke ta mamakin ina ya samo labarin nan cikin kankanin lokaci haka.


Kaman ko ya shiga zuciyan shi yace "Kaman ansan ina neman news in, wlh ina zuwa Restaurant cin abinci naji wani mata na lbrn Hafeez bature dan uwan Al-mansur ya taba cewa yana son ta. Nan fa rigima ya kaure musu akan daya tace sam taji lbrn ko kadan basu da dangan ta nan ne fa ta bada lbrn,  ni kuwa ina ji na ja mota na sai kubwa. Da ma akwai friend ina da mu kayi karatu tare a india,  har layin muka je wurin wani cousin in shi nan fa ya tabbatar mana da labarin"


"Ikon Allah,  yanzu kuma sai sanin yana da alaka da case in nan ko bai da ita"


"Bai kasan yana Dubai" Dr Fahad ya bada amsa, da sauri Barr yace "Dubai?" Sai kuma yayi shiru, he needs someone da zai mai bincike a can Dubai in. Faree'ah da Hafeez na Dubai,  to saura kuma Umyamha sai kuma Amal.


"Dr ko akwai binciken da zaka mana akan Amal Idriss Hayatuddeen nd her suicide issue?" Dan jim Dr yayi kafin yace "Kanwar Saleem ko?" Da kai ya amsa mishi. "Childhood friend in Yusuf ne, da ke kubwan i will try to get something"


Shiru ne ya dau falon kowa da irin tunanin da yake sakawa a zuciyan shi. "Suhaima ina zan iya samun Umaymah ne?" Kallon barr Suhaiman tayi, ko bai fada ba tasan cewa ya dai yi maganan ne kawai. "I don't know"


Dr Fahad yace "Suhaima are you still not willing to say something?" Ba ta kai da amsawa ba zeena tace "Kawa you have to give them the book tunda ba za ki iya basu lbrn ba nasan kin rubuta komai" saurin juyawa Suhaima tayi tana kallon Zeenah kafin tace "Wani littafi kuma kawa?"


Dariya zeena ta danyi kafin tace "Ai nasan kin rubuta littafi about your life, ki basu shi mana may be zai taimaka ma binciken nasu" Da mamaki sosai a fuskan Suhaima tace "to how do you know amma?"


Sosai tayi dariya tace "kawa kenan an gaya miki a banza faree'ah ke ce min magulmaciya?" Kafin suhaima tayi magana Dr Fahad yace "ki bamu littafin to" gabadaya zuba mata idanu su kayi hakan yasa dole ta bude baki tayi magana "Yana kaduna in kuka ma Anisa magana za ta baku"

"Anisa?" Barr yayi saurin fada.


"She knows nothing fa, kawai dai na bata ajiyen littafin ne ba copy bane, manuscript ne"


"Amma ina kika same shi?"


"Nayi saving a wani platform ne, so nayi loghing ne sai na bata ta min printing nace mata ina rubuta novel and she promise me not to read sai na gama gabadaya." Ajiyan zuciya su sake, ba shakka sun san kaduna tayi kira kenan. Sai dai daga karshe sun yanke shawaran Barr ya je ya amso manuscript in Dr kuma ya tsaya domin cigaba da bincike musamman akan Amal.


...


Coocoon apartment


Seychelles


Umaymah Amin ba tayi wani baccin kirki ba taji ana tada ta. Da sauri ta mike ta ganshi tsaye akan ta idanuwan shi gabadaya a kanta.

"Ki fito parlor" kawai yace sannan ya fita dole ta mike ta biyo shi. Tayi mamakin ganin travelling bag ajiye a gefe amma sai ta fuske ta nemi wuri ta zaune. Kallon ta ya ke sosai sai dai wannan ba irin kallon da ya saba bin ta dashi bane mai cike da dimbin so da burgewa wannan kallo ne na tsan tsan tausayi da yake jifan ta dashi.1


"I will be living now" a firgive ta dago tana kallon shi,  da kyar ta iya furta "but why?" Folding lips in shi yayi, a ranshi yana tunanin yanda zancen zai zo mata "Na gama aiki na a nan so yau zan wuce Dubai, i got another work there"


Da mamaki sosai tace "aiki? Nasan an gama bikin su Rawan but still you never mention you are leaving today ai,  is it because of what i told you yesterday?" Tayi mamakin yanda ba ko alamun tantama ya daga kanshi alaman Eh. Zaro idanuwanta tayi tana kallon shi, what is happening again? Abinda ta dinga ambata a ranta kenan.

"Sai dai kuma ba kaman yanda kike xata, am leaving becauee na riga na samu abinda nake bukatar samun" still confuse kallon shi kawai ta ke tana tunanin ina ya dosa?


"Bara dai in miki yanda zaki Fahimta. Like i told you Rawan da Adam duka Friends ina ne tare mu kayi karatu dasu." ID card ya dauko ya mika mata, ba dan ta san menene ba ta amsa tana dubawa. Kaman yabda ya fada mata sunan shi hakan ta gani rubuce a jikin card in,  Umar Farukh machina. Shaidan shi na Detective wanda ke aiki a karkashin Crime investigations department (CID) ta gani, a tsorace ta bishi da kallo. Kai ya daga mata alamun tabbatar mata da zargin nata. "I was hired for an investigation a company in Al-mansur, da kuma shi kanshi Al-mansur in. A nan kuma naci karo da lamarin case inku. Sorry to say Umaymah but you act so selfish gsky. I mean ta yanda zaki bar mutum a cikin case bayan kisan ke ce silan shigan ta duk halin da take ciki. Kar ki manta itan ma fa mutum ce mace kamar ke. I had no intention of coming to seychelles da baki zo bama da bazan zo ba, a safoyyar da zaki taho aka sanar dani in shirya, ina da visa da komai don haka aka dauke ni a private jet zuwa lagos inda na hadu dake a airport. Lokacin ds Adama ya ke sanar min burin Rawan, lokacin nasan na samu perfect solution na yanda zan bullomiki saboda nasan ke Event planner ce mai maida dukkan hankali akan aikin ta, nasan you will make everything work shiyasa na bashi shawaran ayi haka. Am sorry if you may think i used you, this is my job and i have to protect wannan yarinyar da kika bari behind bars" tsabagen shock in da ya kamata maganamai kyau ma kasa hada shi tayi. Key ya ciro da card ya ajiye a gaban ta. "You are so nice to me so taimakon da zan iya miki shine ga key in apartment in nan ki zauna har lokacin da zan neme ki when i think Nigeria will be safe for you" nuna mata katin yayi kuma yace "You can contact duk lokacin da bukatan hakan ya taso,  ko dan nima zan nemeki dole but now i have to go ina da mission a Dubai kuma" a firgice ta dago tana kallon shi, murmushi ya mata yace "Dole in ga yarinyar ki Faree'ah, so ina baran addu'a a wurin ki sannan kuma ki yafe ni kinsan lamarin tafiya" da shu'umin murmushi akan fuskan shi ya fada, daganan kuma bai kara cewa komai ba ya dau luggage inshi ya nufi kofa.1Kaduna+


Yana fadawa Anisa, jiki na rawa ta gaggauta kawo mishi manuscript in kaman yanda ya bukata. Bai yi wata wata ba kuwa ya amsa sannan ya wuce gidan shi da duba iyalin shi. A falo ya iske maryam zaune tana danna waya,  ga gidan duk yanayin shi sai a hankali. Abinda ya lura shine a kwana biyun nan ta fara maido halin ta na da. Tayi farin cikin ganin shi musamman da zuwan nashi ya kasance bazata, amma da ke shu'uma ce ta buga a jarida sai ta basar sannu da zuwan ma da kyar ya fito daga bakin ta. "Au baki ji dadin ganina ba in koma inda na fito?" Hararan ta yayi, dole ta ajiye wayan hannun ta, ta dan turo baki "Mu dai kawai an kwace mana kai wlh" daganan su ka dan sakewa juna, duk can kasan ranshi bai ji dadin irin tarban da ya tarar ba gun masoyiyar tashi kuma mallakin shi.


Sai da ya dan natsa tukunna ya fara bude manuscript in cike da son ganin abinda ya kunsa.


Rayuwata


Babi na dayaDamaturu, Yobe state


Ina tsalle tsalle na shiga layin gidanmu ina cilla jakan Islamiyya ta sama ina cafkewa cike da farin ciki a raina, buri na in isa gida in sanarwa Ummi tabbas yau na bada hadda ta dai dai malamin mu har kyauta ya min. Ina jin kawata Adama da muke dawowa islamiyya tare tana kwla min kira in zo in amshi pencil in da na bata aro nayi mata banza.


Tun a kofar gidanmu na cire hijabi na na ci dammara ina faman kwallawa mahaifiyata kira. "Ummi Ummi Ummi na dawo" da yayata Falmata na ci karo da sauri na matsa saboda saura kiris in buge ta, saurin matsawa nayi a tsorace Sanin halin ta, muddin kuskure ya Sani na buge ta kwana zanyi jiki na na ciwo. Kwafa tayi tana galla min harara "Allah ya rufa miki asiri kuma kar ki cika mu da ihu gantalalliyar uwar ta ki da kike kira tayi gaba tabi duniya" kallon ta kawai nayi domin shekaruna sunyi karanta in fahimci abinda ta ke nufi. ba don na damu da abinda tace ba na nufi wurin mu ina kokarin karasawa dakin Ummi ina cigaba da kwalla mata kira.


Sai dai wasa gaske ba Ummi ba alamun ta haka kuma ba kanwata maijidda. Gajiya nayi na fito na zauna kan baranda ina jiran ta inda za ta fito.  Shin ina Ummi taje? Ni dai nasan in zata unguwa tana fada min amma yau ba ta fada ba. Cikin falon na sake komawa na ga komai na nan yanda ya ke. Don haka nayi saurin nufan dakin ta ina kallon shi. A hankali na duba akwatinan da ke wurin sun ragu ko da na duba wardrobe naga ba kayan ta haka ba na maijidda, ban San lokacin da na saki kara ba na fara birgima a kasa, duk a tunanina tafiya su kayi su ka barni. Ni ko babban bakin cikina shine zan koma wurin Anty Yana. Duk lokacin da Ummi tayi tafiya ta barni a wurin ta ba karamin wahala na ke sha ba wurin Adda Falmata, Anty Yana dai ba za ta buge ni haka kuma ba zata hana a bugen ba, ko kallo ban ishe ta ba, kai ko gaisuwana ba cika amsawa tayi ba.


Wani irin tsawa naji a kai na daya Sani saurin yin shiru ba shiri, jikina har karkarwa yake a sanadiyyan wanda na gani a gaba na yana bina da harara alamun ba wasa akan fuskanshi. Yaya baba ne tsaye a kaina da abokin shi Umar sanda.


"Kukan uban me kike wa mutane? Har da birgima don tsabagen iskanci da samun wuri ko"


Cikin rawan murya da duk ya dishe tsabagen kuka nace "Ummina ban ganta"


Wani irin dariya na ji an kyakyata min, har cikin raina naji bakin cikin dariyan nan mai kama da na mugunta, sai dai ba daga bakin Yaya baba ya fito ba, abokin shi ne Umar sanda da su ke tare.1


"Au ba ta fada miki za ta bar gidan nan bane? To tafi na har abada, ba za kuma ta kara dawo ba har abada. Kin San halina sarai ban son iskanci taso muje Abba na kiran ki" Yaya baba ya fada yana bina da harara.


Daskarewa nayi a wurin, tsabagen rudanin da na Shiga, shin wani irin abu me shirin samun rayuwata?

Ga mamakina abokin Ya baba na gani ya Shiga falon Ummi yana dube dube.


"Kai Faruk fito mu wuce mana, me kake yi a nan?" Yaya baba ya tmby.


Fitowa yayi still da dariya a fuskan shi "Adams wlh side in nan ya hadu, kawai kace wa Abbanku ya maido Ku nan harda Al-lawan tunda mai wurin ba dawowa za tayi ba wlh zai kawo light" wani irin tululin bakin ciki na ji ya sauko min, wai shin shi wannan ma ina ruwan shi da harkan gidanmu ne. Ban San lokacin da na  juya ina kallon shi ba, ido hudu mu kayi dashi, cike da kallon tsana na zabga mishi harara.

Dariyan ya kara yi wannan karon harda rike ciki "calm down little girl, bani na kar zomon ba"

Magana na ke shirin mayar masa duk da nasan ba abinda xai hana Yaya Baba dukana, sai dai shigowan Abbah ya katse ni. Da sauri su ka fita su ka barmu ina cigaba da kukana.


"Keh lafiyan ki?" Naji an fada hankali na dago iddanuwana suka fada kan Abbah. Mahaifina mutum ne Wanda bai iya zama yayi wasa da yaro ba balle yaja shi a jiki hakan yasa dukkanmu tsoron shi mu ke jin har ma da su Anty Falmata. Sauri shiru nayi na kama baki na ina kallon shi jika na na kyarkyarwa. "Dum dume?" Me ya faru? Ya fada cikin kalman Fulatanci, kasancewar shi bafulatanin Ngelzarma. Karamin hukuma a nan Yobe state. Amma sun dade da dawowa jikin damaturu domin mahaifiyar shima a Unguwan Ajayeri ta ke zaune.

Saurin girgiza kai nayi, wani irin kallo naga yana bina dashi mai cike da alamun tausayi. "Ki hada kayan ki maza zaki koma dakin su Falmata" a rikice na dago ina kallon shi sai dai duk tsoron shi da nake ji bai sa na kasa mishi magana ba. "Abbah zanje wurin Goggo ni" kallo na yayi for the first time naji yana lallaban mutum. "Ba kuna zuwa ranar juma'a b?" Gyada kai na nayi. "To ki bari in anyi hutu da kaina zan kai ki dinga mata Hutu"


Ganin ya amsa ni ya bani karfin guiwan tmbyn shi "Abbah ina Ummiy da Maijidda" kallo na ya sake yi nan ta ke kuma naga ya koma bata rai kaman kullum. Don haka ban iya kara magana ba na sa kayana a akwati na bi bayan shi.


Tun daga kallon da yaran Anty Yana ke min na San tabbas ina cikin matsala. Kaf cikin su Al-lawan  ne kadai mai dan sauki da shekara biyu ya girme ni. Shi ne ka dai mai zuwa wurin Ummiy na ya gaishe ta at times ma har yaje mata aike. Adda Falmata tsanan duniya ta dauka ta daura ma Ummiy na to nima ko kadan ba ta raga min, sannan komai za ta min Ummiy ba ta taba daga kai tace mata kala. Ummi na bafulatanar kauyen kollere ne, shima Yoben ya ke. Baffah sunan kani naga da ke bi min, mai sunan baffan Maiduguri ne, hakan yasa yana gama nursey baffan ya bukaci ya koma wurin sa da zama. Maijidda ita ke bi mishi.


A dakin Anty Yana ko Ya baba (mai sunan Abbah) shine babba sai Adda Falmata, Al-lawan sai Sadiya da autan ta Zainab.

Yanzu ma shigana wurin su Al-lawan ne kadai ya min kallon arziki sauran ko duk harara su ke bina dashi sai dai ba daman magana saboda Abbah na wurin, kusan ma sunfi ni tsoron shi don su fini sanin halin shi. Hatta Anty Yana in yana wuri zaka ga tana dar dar duk mulki irin nata sabanin Ummi na da ko kadan ba ta dauka, a wurin Ummi ne kadai za kaga yana raha da dariya har ma yana tsokanan ta. Duk iskanci Anty Yana da Adda Falmata ba su iya taran Ummi su mata, akwai wannan shakkan tsakanin su sai dai ko su sauke a kaina ko suyi habaici shi ma tana kallon mutum zai sha jinin jikin shi. Akwai ta da wasa amma Sam ba ta daukan raini, abinda na ke tunanin ya raba su da Abbah kenan domin har yau ba Wanda ya dube ni ya fada min dalili.


Dakin Adda Falmata na kai akwati na, ita da sadiya ne a dakin. Lungu daya na nemi kayana nasa, a dakin na takure na zauna domin Allah ya gani ina tsoron fita falo.


Nayi mintuna kusan Goma a wurin sai ga sadiya ta shiga tana banka min harara. Na kan yi mamaki domin ita din sa'an Baffah CE ba nawa ba "kizo Anty Yana na kira" abinda ta fada kawai kenan ta fita. Jiki na rawa na nufin hanyan Falon dukkan su suna zaune suna kallo. A hankali na durkasa gaban Anty Yana na ce mata "gani" harara ta bini dashi kafin in ankara ta cakwumo wuya na kaman wata sa'anta sannan ta sake in ta kama kunnuwana duka biyu ta murde da karfi har sai da na saki karan azaba "Warning zan miki domin ba a sona zan zauna da ke, tun can kin sanni ba shiga harkan ki nake ba don haka ban son shishigi ki yi harkan ki inyi nawa, ba zan hana ki hulda da yan uwanki ba amma kar ki sake ko da wasa kice zaki taba min sadiyya da zainab, ba zan dauka ba. Ba zan miki fadan tsabta domin naga uwarki ba laifi akwai shi don haka ki kiyaye ni kina jina?" Da karfi na amsa mata da "in sha Allah" siririyan tsaki taja a hankali tace "in banda ma abun Aeey wa ke tafiya ya bar dan shi a wuri, ni wlh ta bani kunya don da nice maza ne kawai zan kyale" shiru nayi, a raina ina gasgata Anty Yana, ko bakomai tana ma yaranta son da baza ta barsu su wulakanta ba sabanin nawa Uwar da ban San dalilin da yasa ta ke haka ba. Munafunci irin na Anty Yana kasa kasa ta ke yin amma in kana so kaga bala'in ta kama taba mata da. Amma Anty na a gaban ta Adda Falmata da Yaya baba za su min dukan tsiya amma ko dagowa ta kalle su ba tayi. Iyaka in na gama kuka na tace in wuce daki, daganan zancen ya wuce.


"Tashi ki bani wuri ni!" A firgice na tashi saboda yanda ihun nata ya sauka a kaina. Sum sum na koma daki, ina shiga naji an jawo ni an hada ni da gini, kafin in ankara naji saukan mari ta ko ina, ba shiri na zube kasa.1


"Taso ko in kara mini" Adda Falmata ta fada tana bina da harara, da sauri na dago a tsora ce. "Kar kiga laifi na kiga laifin Uwarki, kin San mai ta fada min da zata wuce?" Ta fada tana bina da kallon tsana.


Saurin girgiza kaina nayi nace "Aa" nasan rashin amsawan ma wani matsalan ce, ga hawayen da ke ambaliya a idona ba hanyan yin kuka.


" ce min tayi Falmata ga Suhaima nan zan barta a nan gidan. ke da sauran yan uwan naki in kuga dama Ku kashe ta Ku bar min gawan ta, in zo in dauka." A firgice na ke kallon ina kokarin gasgata zancen ta, ni kam na shigo meyesa Ummi zata min haka? Nasan halin zafin ta tsab za ta iya fadan hakan.


"To uwar ki ma ba son ki ta ke ba ta ajiye ki ta shiga yawon duniya don haka duk wani aiki na gidan nan ke zaki dinga yi kama da shara, wanke wanke, gyaran daki ke har ma da mopping." Ni dai ban tanka ba, illa hawayen da ke zubo min. A lokacin na samu kaina da tmbyn shin meyesa Ummi na ba ta jira na dawo daga Islamiyya ba mu ka tafi tare?


Tun daga lokacin kuwa na fara bautan. Kullum na tashi da safe sai nayi wanke wanke, na gyara dakin mu da na Anty Yana. da har dakin su Ya Baba, Al-lawan yace zai dinga yi. Na share tsakar gida da parlor Bayan na gama sannan a bani abincin da aka ga dama In tafi School. Islamic center da ke Yobe mosque a GRA dukkanmu mu ke zuwa, da ke ba nisa a kafa mu ke zuwa, babban titi kawai ake tsallakar damu mu karasa. Hakanan in mun dawo da islamiyya da yamma sai nayi wanki uniform ina da na sadiya sannan ake bari na cin abinci. Aike ko komin dare duk nisan wurin sai naje, Al-lawan ke satan hanya ya raka ni.1

Abbah bai cika zama a gari ba, aikin shi tafiye tafiye su ke hakan yasa bai San abinda ke faruwa ba.

Duk ma ni abubuwan ba wanda yafi daga min hankali kaman debo ruwa. Muddin ruwa ya kare to dole ne naje na debo a gidan su Umar Sanda, da ke suna da dam. Haka zan ta kaiwa da kawowa, in ya hadu dani ya dinga dariya kenan yana "ah su kuka kuka miye na zunburo baki in zaki debi ruwa ki debi ruwa kawai" na rasa me ke mai dariya a jikina. Watarana in naje haka zai sa sai zubawa duk wanda ya zo deban ruwan nan kafin na debi nawa. Maman shi ba ta gida sai Hajja kishiyarta, wanda ta ke aminiyar Anty yana, ita kam daman yar zugawa ayi ce.1


Yau juma'a tunda na tashi ina cikin farin ciki saboda nasan yau za a gidan Goggo. Da murna na dawo daga makaranta kasancewar an bamu script in test in maths da muka yi. L.C.M da H.C.F sai Long division, topics ne da su ke matukar bani wuya amma tunda Ummina ta zauna ta warware min na iya su sosai. Gabadaya test in na cinye, Ummina mutum ce mai hazaka sosai don gabadaya gidan su ita kadai tayi karatun boko har zuwa secondary. Ganin haka Yayan maman ta ya dauke ta zuwa Maiduguri inda ta jona F.C.E. Tana karatun su ka hadu da Abbah har su kayi aure. Bayan ta gama karatun ta samu aikin koyarwa a injiwaju, nan Adda Falmata ta fara yi kuma a nan kiyayyar ta da Ummi na ya samo asali. A cewarta kwata kwata Ummina ba ta raga mata a makaranta, failing inta ta keyi kuma ta dake ta. Ni ko sanin halin Ummi nasan ba tayi dai dai bane, Adda Falmata kuma akwai taurin kai ba za ta yarda ta koya ba. Ni dai nasan ko ni ce ba zai hana ta dake ni ba. Kusan ince akan hakane aka fara jinsu da Anty Yana duk da Ummi na ba ta tanka ta kuma ita Anty Yanan tana shakkan Ummin.


"Kenan ni za tayi farin ciki da abinda naci?" Wani kololon bakin ciki ne ya tsaya tunawan da nayi yanzu Anty bata nan. Kuma har yau ba Wanda yace min ga inda taje. Haka na karasa gida jiki a sanyaye. Ko abinci ban ci ba na kama aiki na kafin lokacin zuwa gidan Goggo yayi.  Tsab na shirya bayan na gama ina zaman jiran su, har mun fito zamu tafi muna ma Anty Yana Sallama naji tana fadin "keh zo ki min wankin su Sadiya, me ake yi a gidan Goggon" wani hawayen bakin ciki na ji ya zubo min nayi saurin gogewa. Ina ji ina gani su ka tafi, ni kuma aka jibga min wankin su sadiya.


"Au wai dan bakin hali shine kike kuka don za kiyi wa kannen ki wankin? Shegiya mai bakin hali irin na uwarta aiko hakanan zakiyi wankin nan" kala bance mata na dauko wankin na fara yi tun ina kuka har na gaji na daina. Abin takaici sai da nayi tsakiyan wanki ta zo ta sa na sake da ga farko, wai basu fita. Hakana libgi wanki jikina duk ciwo har su ka dawo ina wanki, ba Wanda yace min sannu sai Al-lawan da yace "Suhaima har yanzun ba ki gama ba?" Ganin ban tanka shi ba shima yayi wucewar sa.


Wasa wasa har na kusan shafa wata biyu cikin bakar rayuwannan, wahalan yau daban na gobe daban kullum da irin nashi salon. Cikin wata biyun nan kwata kwata ban taba zuwa gidan Goggo ba, tun ana Sani aiki ko kuma Anty Yana ta fita tace ni zan kula da gida, har yazo kiri kiri ko za a tafi nasan bani a ciki.

Ranar tun da yamma bayan na gama wanki na ke jin zazzabi zazzabi, don haka ban tsaya bitan karatu ba kaman yanda na saba sai na kwanta. Da rawan dari na tashi a firgice jin zazzabi ya zuba min sosai, wani irin amai naji ya taso min ko kafin in tashi na zuba shi a kasan tiles in dakin. Na dauka baKowa a daki sai jin muryan Adda Falmata nayi tana fadin "bala'i ke wannan wani irin iskanci ne?" Kafin in bata amsa ta kwashe ni da mari Wanda yayi matukar girgiza ni na zuba kara a wurin. Ban San Abbah ya dawo ba sai jin muryan shi nayi yana fadin "lafiya wa ke kuka?" A firgice Adda Falmata ta kalle ni tana min warning. Da alamun ita ma ta manta yana gida. A tsorace ta fara fadin "Abbah daman Suhaima ce bata da lfy shine ta ke kuka" kallon mamaki na bita dashi, kenan daman ta San bani da lfy in ashe?


Har Dakin Abbah ya shigo, idanuwana sunyi jawur ina kallon kasa ya jawo hannuna. "Falmata gyara wurin nan" ya fada yana jan hannuna muka fita. Sauran kiris ince mai "Abbah zan gyara da kaina" sai dai shima ba zan iya mai musu ba amma tabbas nasan sai na tsani kaina wurin Adda Falmata muddin ta gyara wurin nan.


Zaunan dani yayi a kujera ya taba wuya na. "Tun yaushe ne baki da lfyn?"


"Tunda yamma na fara ji" na amsa mishi.


"To shine zaki zauna kina kuka? Ba ki San ciwon kai zai kara miki ba?"


"Kayi hakuri Abbah" girgiza kai yayi yace "Daga yau in baki da lfy fada zaki dinga yi ba kuka, dauko hijab inki mu je asibiti"


Jiki na rawa na shiga dakin, Adda Falmata ta zuba wa inda nayi Amai ruwa, ta toshe hanci ta. Ban ce mata kala ba na dauki Hijab INA, ina jinta tana kwafa a raina nace, sai dai kin goge in. Ajiko hospital mu ka nufa da Abbah, suna ganina su ka ce banda karfi sai na kwana an sa min ruwa dole. Bayan an min allurori aka sa drip in yace wa nurses in bara yaje gida ya dawo, zai zo da Wanda zamu kwana, a raina na dinga rokon Allah yasa ba Adda Falmata bace domin ni gwara min Anty Yana akan ta sau dubu, ita komin abinta ba duka sai sa aiki da rashin kula da al'amura na. Amma Adda Falmata kaman ta samu jaka, a cewarta tana rama abinda Ummi na ta mata, ni dai na San 90% sharri ne kawai. Kafin Abbahn ya dawo har nayi bacci, sai dai na farka da safe naga Anty Yana ta hada rai sai hura hanci ta ke. Kiri kiri matan nan ba ta taimaka min yin komai ba, a cewarta ita ba ta sa kanta abinda ba hakkin ta bane. sai da Al-lawan ya zo ne ya taimaka min da ke ya riga Abbah zuwa. Shi kanshi Al-lawan in na kan kasa gane kanshi domin wataran kirki watarana kuma ko a jikinshi.Rayuwata

Babi na biyu


Ranar Goggo ta zo duba ni, ita ma ba yanda ta ke dake tana fama da ciwon kafa sosai. "Hala na miki laifi ne tunda mahaifiyar ki ta tafi kika daina zuwa guna?" Goggon ta fada cikin harshen fulanci. "Ba haka bane Goggo" na amsa mata.+


"To kullum na tmby sai ace min baki ce zaki zo ba"


"Goggo akwai abubuwan da nake yi ne"  Harara na tayi tace "abubuwan da yafi zuwa wurina, to ko da wasa kar in kara ji" kallon Anty Yana tayi tace mata "in ma kece ke hana ta zuwa daga yau ya kare kina jina?"1


"Ni ba ruwana" Anty Yana ta amsa tana kasa da kai.


"Yana kiji tsoron Allah dai" nan ta ke Anty Yana ta fara kame kame.


Tun daga lokacin aka fara barina zuwa wurin Goggo, INA son tsohuwan sosai, fata na Abbah ya barni In koma wurin ta sai dai ba daman tmby" Tun asali Goggo ta fito son Ummi na akan Anty Yana. A yanda lbr yazo mana, tun farkon aure Anty Yana da Abba, da kyar Goggo ta amince aka yi auren. Kuma daman ance halinka ke siyan maka mutunci. Tuni Goggo tayi watsi da Anty Yana da ta gano halin ta, don sai ta shekara in ba Abbah ya data ba ba taje gaida Goggo ba. Ko da Abbah ya tashi auren Ummi, sosai Goggo tayi na'am da zancen ganin Ummin bafulatana ce. Sai do Kowa ya shaida halin irin nasu da ya banban ta ne ya sa hakan.


Wani ranar juma'a munje wurin ta, tunda mu kaje na lura tana ta kallona, ko dan ganin yanda ban saki jikina cikin yan uwana bane, oho. Sai dai ta bari su Adda Falmata sun bar gun ta jawo ni har dakin ta. "Ke lafiyan kuwa? Ko da wani da ke damun ki ne?" Cikin inda inda nace mata "lfy kalau Goggo kin ga wani abu ne?" Hade rai tayi tace "ke dai Wlh kinji kunya shegen tsoro kaman ba Aeey bace ta haife ki, Allah en shamtata an kam"


Ni dai bance mata komai ba, sai fada ta ke yi a cewarta wai na rame sosai. Ko da mu ka tashi tfy gida cewa tayi ba inda zani. "Bari baban naku ya dawo dole in San abinda ake ciki" wani irin kallo na ga Adda Falmata na bina dashi, ni dai duk tsoron abinda zai biyo baya nake. Har rokon Goggon nayi ta bar ni na koma, maimakon hakan rankwashi na tayi ta maida ni cikin dakin ta.


Ranar ko nayi kwana dadi ba wani fargaba a ciki, ko da na tashi da sassafe na riga na saba da aiki don haka tuni na hau yi wa Goggo aikin gidan ta gabadaya. Ko da ta farka taji dadi sosai sai cewa ta ke "Ayyah ai da kin bari su ..


"Goggo me za a dafa miki?" Na tmby duk ba wai iya girkin nayi ba, banda su jajjage da nake yi sai gyaran kayan miya da su alayyahu. Harara na tayi tace "ke yanzu har wani aiki kika iya?" Marairai ce mata nayi nace "Goggo toh ba sai in koya ba" dariya tayi tace "to ai ni ba ma abun kari a gidan nan, daman dumame ne da shayi. Ke dai bara su Ajiddah su shigo su samo miki Kosai da fanke ko kuma Za kici danwake ko doyon da kowan fulawa"  wai, na manta rabon da naji ana tmbyn me zanci, daman yawanci a garinmu siyan abin karayawa ake yi. Ko kuma a dinga hadawa, kuma ma sha Allahu ma su saidawan sun iya ga arha gashi kuma ba ha'inci.

Ko a gida yawancin siya ake yi sai dai sai abinda sadiya su ka rage ne ake dan bani shima ba kullum ba. In ko anyi a gida, ba wanda ya damu naci ko kar naci, sannan in ana yi ba zan iya zuwa ince a bani ba na jawo wa kaina magana, sai dai in an gama in lallaba inci a kitchen in.


Gidan Goggo gida ne irin na zamani, sashe kusan uku ke ciki daya nata dayan kuma kishiyan ta ke ciki sai dayan autan Aidah (kishiyar Goggo" da yayi aure nan ya kawo matar shi. Dukkan su biyun da yan uwan su su ke zaune, barin ma Goggo da musamman ta ke sawa a kawo mata yaran Yan uwan ta su zauna tare. Yanzu haka mata biyu ne a gidan sai dai dukkan su sunyi aure sun fito.

Sallaman yaran da naji ya katse min tunanin da nake. Yara na mata su ka shigo, ina kallon su su ka gaida Goggo. Dayan ta girme ni amma dayan za tayi Sa'a ta. "Goggo akwai abinda za a siyo miki ne?" Babban ta tmby.


"Ku dai je da shuaima ko akwai abinda ta ke so, maza dauko hijabin ki " da sauri ko na dauka, ta miko naira Dari ina ta murna muka fita dasu Goggo na fadin "a dai kula da titi Mairama" ta nan na gane babban ce mairama.


Muna fita karaman ta matso kusa dani "sannu, ke jikan Goggo ce ko?"


Murmushi na mata nace "eh"


"Ai ina ganin ki kina zuwa da yan gidanku, ina unguwan Ku?"


"Sabon fegi" na amsa


"Lah layin PS" dariya nayi sanin kowa layin PS ya Sani a Sabon fegi ko gidan 530.


"Aa mu layin Ladabi mu ke"


"Oh inda ake saida naman nan ko? Layin Gidan Khadija Bukar matan gwamna" dariya na mata ganin ta gane layin. "Ai muna da Yan'uwa layin ko Yah Mairaman" yayar dai ba ta maida hankalin ta wurin mu ba.


"Ni sunana Ajjidah, ina primary 5 a central, kin ganta can" ta fada ta na nuna min makarantan da ke gaban gidan su Goggo kadan.


"Suhaima, Islamic center mu ke zuwa. Ni primary 4 na ke"

Dariya tayi tace "Ashe ma na girme ki"


A haka mu ka karasa wurin saida abubuwan muka siya, a bakin Ajiddah na ke jin su makotan su Goggo ne, kuma Dadan su yan garin su. Da ke Goggo bafulatanan Kauyen biriri ce.


Su Ajiddah shuwan cikin Maiduguri ne su, in ka gan su Farare, kyawawa ga kuma gashi tubarakallah, kaman labarawa. Mamarsu ce bafulatana na biriri garin su Goggo.


A kwana biyu mugun sabo mu kayi da Ajiddah, ko shago aka aike ta sai tazo na raka ta. Sai da ta kaini gidan su na gaida Dadan su, sannan muka wuni muna wasa. Zan iya cewa Ajiddah ce kawata ta biyu domin duk yaran da ke islamiyya da boko suna shiri dani ne saboda malam yace ina da kokari, ni ko ban iya magana ba balle in shishige musu. Yan unguwan mu ko a shago mu ke haduwa, in kika cire Adama da har gidan tana zuwa tun Ummi na nan. Maman ta kawar Ummi ce sai dai itan wurin kakanta ta ke zaune. Musamman Ummi ke dauka na mu je mu gaida kakan, har yanzu ma ina zuwa amma a sace.


Ranar lahadi har aka yi magriba Goggo ba tayi maganan komawa na ba, ni in banyi ba saboda ban son komawa In har ga Allah. Sai bayan an idar da Sallan isha'i mun tafi wurin Anty Amarya da Anty bilki (bakuwan Goggo) muna kallo sai ga Anty Zulai ta shigo tana Sanar min kiran Goggo. Ban kawo komai a raina ba na fita domin kwata kwata ban kawo maganan tafiyana ba tunda na ga had dare yayi shiru.


Ina Sallama dakin Goggo na ga Abbah a zaune, nan ta ke gaba na ya fadi, da kyar na daure na gaishe shi. "Dauko hijabin ki Ku tafi gida Suhaima. Amma Adamu Dan Allah ka bincika yarinya duk ta rame, sannan kuma duk juma'a a dinga kawo in ta in yaso ran lahadi da Yamma sai kawunta Bukar ya maida ta"


"To Goggo islamiyya fa?"


"Akwai islamiyyan safe da yamma da su Ajiddah ke zuwa sai a sata, yanzu ma dan suna Hutu ne ba su je ba"


"In sha Allahu Goggo" ya amsa sannan ya mata Sallama na bishi a baya har motan shi.


Sai da muka fara tfy yace "akwai abinda ake miki a gidan ne ba ki fada min ba kika fadawa Goggo?" Da sauri na girgiza kai na daman yanzu ma ina tsoro abinda zan tarar wurin Adda Falmata.


"To Goggo tace kina ramewa"


Da sauri nace mishi "daman daman ina so inga Ummi ne" kallona yayi sai na ga ya hade rai dole na ja baki na nayi shiru. Ban San meyesa Kowa bai son maganan Ummiy na ba, ko Goggo da na tmby ta ce min tayi "ban Sani ba ki tmby Ubanki shi da suka samu matsalan"


A haka na shiga gidan cikin wasi wasi.  Sai dai sanin tare da Abbah mu ka taho ba Wanda ya tanka ni sai Al-lawan da yace min "Yar Goggo ashe zaki dawo? Na dauka goggon ta kwace mana ke ne ai" murmushi yake kawai na mai na gaida Anty Yana, domin na kasa tantance habaici ya ke min ko wasa, Anty Yana na shan kamshi ta amsa gaisuwa na ban wani damuwa saboda na riga na saba. Ban zauna sanin dare yayi, ko ba ma hakan ba daman ba son zaman falon na ke yi ba sai ya zama dole. Daki na wuce kaman kullum Adda Falmata na ciki tana waya, duk da karancin shekaruna na kan rasa wani irin wayana ta ke yi haka da saurayin ta rai da rai. Duka duka ma a lokacin ita kanta SS1, Ya baba ne ke SS3 shi kuma boarding School ya ke yi so bai cika zaman gida ba. Adda Amina ne naji ana fadin shekaran nan ta gama makaranta.


"Nyalli jam Adda?" (An wuni lfy Adda?) Na gaishe ta kaina a kasa na ka sa shigowa dakin. Ba ta amsa gaisuwan nawa ba sai tsakin da ta ja "ni fa ban son munafunci in zaki ki shigo" ta amsa sannan ta cigaba da wayan ta. Duk da yawan wayan da take yi nasan bai kamata. Sau dayawa na kan godewa saurayin nata domin duk sanda ta ke wayan kwakwaran motsi bai so ya katse ta. Na rasa zuciya irin na Adda Falmata, tun tana yar kankanuwan ta ta ke da shegen bakin hali da mugun zuciya da sau dama da na ke jin mutane su na cewa ita da ta tashi gadon nikkanwa tayi. Saboda Abbah rashin fara'a kawai gare shi amma bai da mugunta kuma Yana da kirki, Anty Yana ko bakin halin ta da mugun ta na ciki ne sai Wanda ya zauna da ita ke gane hakan.


Washegari, bayan mun dawo daga islamiyyan yamma ina cikin wanke wanke na tsinkayi Sallaman Adama, dariya nayi saboda na San ta ji shiru ne kwana biyu ta biyo ni. Tana ji ina kiran ta tayi banza dani ina ji ta shiga ciki tana gaida Anty Yana. "Anty Yana daman Goggona ne ta aiko ni in kira mata Suhaima amma tace in fara fada miki tukun" shiru Anty Yana tayi kaman ba za ta tanka ba sai can tace "gata can tana wanke wanke in ta gama sai Ku je amma... Ko dan ma barshi kuje in" wani murmushi ne ya subuce min domin tabbas nasan da Anty Yana cewa za tayi kar inyi dare amma tunawan da tayi Goggon Adama ce ke kiran ya sa ta fasa, tasan halin ta tass za ta zo ta sile har inda ta ke. Ita ma kam ko kadan ba ta daukan raini, ko don garin su daya da Ummi na.


Nan Adama ta zo ta same ni ba tace min kala ba sai daurayan da tasa hannu ta taya ni sai har muka gama na canjo kaya sannan mu ka fita da ita. Sai da muka fita na jawo hannun ta naje haba "Aminiyar ke ma kin San ban Unguwan ne shiyasa ban zuwa, na fa je wurin Goggon Ajeyari ne" tabe baki tayi tace "bawani nan Suhaima ko kina nan ba zuwa kike ba sai dai ni nayi ta zuwa"


Hade hannuwana nayi nace "yi hakuri kin fa San ban samun dama ne in dai ina gidan to aiki nake" Ina fadan haka na ga duk tayi wani iri, da alamun tausayi na ba ta, cewa tayi "wai Suhaima ina Ummin ta je?"


Nan da nan idanu na su ka ciko da hawaye "Adama ban Sani ba kuma ba Wanda ya sanar dani"


"Mu je mu tmby Goggo"

Ko da mu kaje wurin Goggo, na samu tayi shinkafa da miya, kaji ne a ciki sannan an yanka salad, hade da ferfesun kayan ciki da kunun aya a gefe. Allah sarki Goggon Adama musamman in ta dafa abin dadi ta ke aikawa a kirani, ban taba fada mata halin da na ke ciki amma ta fuskanci hakan. "Joda nyamu mana Suhaima" (zauna kici mana Suhaima) ta fada bayan mun gaisa. Ban yi musu ba na zauna naci sosai saboda Allah ya gani ina jin yunwa, ranar gabadaya ban ciki abin kirki ba.


Bayan na gama Goggon na ja na da hira Adama sai tabo ni ta ke da kafa da alamun tana so inyi tmbyn ne. Cikin inda inda nace "Goggo daman ina son in tmby ki"


"Me fa?" Ta tsare ni da ido. Nan da nan idanu na su ka cika da ruwa "Goggo daman Ummiy ce ban San inda ta je ba" shiru tayi tsayi lokacin tana ajiyar zuciya kafin tace "Gsky Suhaima ba zan miki karya ba ban San Inda Aeey taje ba, sanin kanta ne ba zan barta ta shiga uwa duniya ba shiyasa ko Sallama ba ta zo min ba. Amma tabbas ba ta can kollere kwata kwata ma ba take ba. Ko don ta ga iyayen ta ba sa raye ne? Hatta Maiduguri duk ba bincika ba taje ba" shiru nayi duk jiki na yayi sanyi. Shin ina Anty ta tafi ta barmin cikin kangi wahala? Cikin rayuwan da ko babba ba kowane bane ya ke iya jurewa, anya Anty ba naso na kuwa kaman yanda Anty Yana ke ji dana ta yaran?


Haka na cigaba da wannan bakan rayuwa, kullum da irin ibtila'in da ya ke fada min, saukin ta ma duk juma'a zuwa lahadi gidan Goggon Ajayeri na ke yin shi. Sai kuma na kanje wurin Goggon Adama, watarana in saci hanya In an aike ni, duk da nasan hukunci da zan fuskan ta in na dade.


A haka muka samun hutun shiga ajin gaba. Adama ke fada min za su je kollere da goggon ta. Don haka ni ma na je na samu Goggo nata ina kuka nace mata zan bita nasan in ta ma Abbah magana zai barta. Ban don ta so ba ta je ta samu Abbah ta sanar mishi, domin a cewar ta Abbah sirrikin ta ne.


Adda Falmata na zagi na tana kirana mara zuciya tunda har uwar da ta haife ni za ta iya tafiya yawon duniya ta barni amma in kwashi jikin in ce zan je in ga yan uwan ta. Ban ce kala ba na cigaba da hada kayana na bi su Adama kollere. Muna zuwa ta kaini gidan Yayan Ummin da ke wazirin garin. 

Muna Sallama a gidan naga duk sun jiyo suna kallona kaman ba su taba ganina ba. Ganina tare da Goggo ya sa su ka gaisa da ita faran faran tace musu "ga yar gidan Aeey nan ta zo Hutu"


Duk cikin su mama Rakiya ne tace "ma sha Allahu sannun ki da zuwa" nan fa Goggo ta tafi ta barni, abin mamaki ba Wanda ya kara daga ido ya kalle ni bayan tafiyan Goggo, sai dai na ji suna ta kus kus. "Eh ai yar Aeey Wanda ta tafi yawon duniyan ta barta" wata tace "to daman mai kuke tsammani da wacce ta yi boko? Ai daman yan duniya ne" wata ta kara cewa "kai amma dai anyi abin kunya"


Mama Rakiyya ce ta sa Altine yar ta ta shigo dani dakin su har ta bani abinci, daman naji Ummi tana fadin ita  in kawar tace tare su ka taso kuma ta auri yayan ta. Abinda ya bani mamaki shine duk sanda mu ka tako kollere da Ummi na sai kunga yanda ake nan da ita kaman za a hadiye "ai ga Aeeyn Maiduguri ta zo" abinci ko kala kala har sai mun ture. Amma yau dan batanan ko kallon arziki ban ishe su sai mama Rakiyya da naci albarkacin Ummi na ta sa aka dauke ni. Kawaye nane dai su Fandau, Hajiya, Aeeshatu da mami su ka zo mu kayi ta labari, sauran kam ce min aka yi iyayen su sun hana su zuwa wai kar na bi halin Ummi na zo na koyawa yaran su. Su wadannan in duk yan uwane shiyasa.


Kawu na da ya dawo da dare musamman ya sa aka kirani, muka ci abinci tare, yayi ta min nasiha game da rayuwa. Tabbas na so gasgata Adda Falmata da tace dangin Ummin ma ba so na su ke sai dai  duk da haka gwara zama a gunsu akan bakin gidan mu.

Kwanan mu biyar mu ka koma, ba ko tsaraban nan da aka saba cika mu dashi in munzo da Ummi babu. Sai kawu na da ya bani naira dari.


A yan kwanakin nan tabbas na ga rayuwa kuma rayuwa ta koya min darussa kala kala masu wuyan mantawa.

Wannan karon ko da muka koma makaranta, sabon aji ne amma ko kadan ban murnar da na ke yi a irin lokaci kaman hakan na canjan aji. Ba sabbin Uniform kaman yanda Anty ke siya min. Na socks, jaka na na makaranta ko saukin har yanzu da kyan shi da takalmina. Sauki na kenan Ummi ba ta siya min abu mara quality sai mai kyau kuma maji gaba. Batun basket daman ba a maganan shi, to in samu inci a gidan ma mana.


Ban kara marmarin zuwa kollere ba amma mu kanje Ngelzarma da Goggon Ajayeri in sha'ani ya taso, ba laifi garin akwai su da son shagulgula. Biriri kam sosai mu ke zuwa da Goggo, gidan dan uwan ta sarkin garin. Fura da nono har sai na ture. In bi yan matan gidan muyi ta yawo gidan yan uwa, kusan duk sa'anin Adda Falmata ne, har babban gida mu ke zuwa da su.1Rayuwata

Babi na uku


Duk wannan farin cikin yana karewa ne a duk sanda na sa kafa cikin gidanmu, gidan da ya ke matsayin na mahaifi na amma ya zame mini wurin da na ke tsoro fiye da ko ina a dukkan rayuwa ta.1

Zaune su ke duk a falo suna kallo niko sai faman mopping in falon na ke. Duk na gaji saboda tulin wanki da wanke wanken da na gama sai haki nake amma ba wanda ya daga ido ya kalle ni balle in samu daman sannu.1


Sadiya ce ta shigo da gudu kafan ta  ba takalmi duk kasa ta taka inda na ke mopping yayi caba caba, idanu nane ya kawo ruwa ban San lokacin da na ture ta ina fadin "haba Sadiya baki ganin nayi mopping ne kin ba..." Wani irin karan da naji ya sauka a tsakiyan kai na ne ya sa na kasa karasa abinda zan fada. Wani irin kallo da Anty Yana ke bina dashi ne ya sa na San yau fa kashina ya bushe. Karan ta cigaba ba kakkauta, Al-lawan ne yazo ya dauke ta yana fadin "kiyi hakuri mana, sai kace wacce za a kashe" kasa cigaba da mopping in nayi nayi turus ina kallon Adda Falmata da Anty yana jiki na sai rawa ya ke. Ban Ankara naji sauka. Bulala a jiki na ko ta ina tun ina muka har murya ta dishe. Sama sama na ke jin Sallama. "Lfy wa ake duka haka?" Naji murya kaman ta ya baba na magana.1


"Au ashe kai ka dawo, duk ta kare sadiya kai tagani ta shigo ta fada wannan Mara imanin ta hankade ta ta fadi" kallona yaya baba yayi, sai faman nishi na ke, harara ya zabga min  "Wai Anty Yana har yanzu wannan bakan mujiyan ta na gidan nan?"


Tabe baki tayi tace "to ya zanyi da ita ta zame min karfen kafa, duk rashin dukana sai da ta sa yauwa na buge ta"


Adda Falmata ce ta zabga min harara  "yarinya sauran nawa ba ke muguwa ba, na fi iya mugun ta kuma ki ta shi ki cigaba da mopping In da kike" jiki na rawa na tashi na cigaban. Adda Falmata ce ta amshi jakan yaya baba ta wuce mai dashi dani ya bita yana fadin "ke in kingama mopping in ki kawo min abinci da ruwan wanka"


Da kyar na samu na karasa sannan na debo abinci na kai mai daki, suna zaune tare da abokin shi Umar Sanda na wuce toilet na dauki bucket na kawo mishi ruwan. Jiki na rawa na ke sanar mishi na gama. Wani kallo ya bini dashi mai cike da tsana yace "ke wai kina yar karaman ki har kin iya mugun ta ko yau zaki Sani, maza fara tsallen kwado" idona duk ya kawo ruwa haka na fara, tun ina daurewa ina yi har na fara kuka. Kallon shi ya ke hankalin shi kwance sai Umar sanda da ke gefe yana ta faman dariya "Adams wai dan wannan abu ta kewa kuka, come on spring ya kamata tayi ma wlh" Ya baba bai juye ya kalle ni sai cewa yayi "ai kinji abinda yace koh?" Ina share hawaye ne na fara spring in, abokin na gefe yana ta faman murmushi ni ko ina zuba mishi Allah ya isa a zuciya ta, da yaga nayi kaman zan fadi sai ya kwashe dariya har da rike ciki.  sai da ya gama alamun numfashi na na neman daukewa sannan Ya baba Ya ce wuce na bashi wuri. Tabbas a lokacin naji wani tsanan Ya baba a raina sai dai na munafukin abokin sa Umar Sanda ya wuce hakan Dan tsananin azaba da kyar na ke iya motsa kafan da dafen bango na karasa dakin, muryata har ya dishes dan kuka har majina ke fitowa, Ranar na tabbatar ya baba ya fi Adda Falmata mugunta.


Sai me? Ina shiga dakin Adda Falmata ta sani kneel down, na daga hannu sama na rude idanu, ko kadan ba ta damu da irin halin da na ke ciki ba. Na rasa wani irin zuciya yaran Anty Yana ke dashi ba, na kanyi takaici duk sanda na tuna yan'uwa nane. Haka ta dinga zabga min mari har sai da ta gaji, fuska na ya kumbura yayi suntum sannan ta kyale ni, wlh tun ina kukan har na neme shi na rasa. Bacci kam Ranar kaura yayi a idona, idona garas har asuba, sai dai sunyi jawur, kai na ko kaman garwashi dan zafi, wani mahaukaciyar zazzabi ne ya rufe ni a nan ta ke.

wan sanyi na dinga yi akan gadon da na ke kwance ni kadai har su ka tashi su ka fara zuwa makaranta, sai dai nasan ko da wasa bazan iya zuwa makaranta ba. Ina ji sadiya na taba ni wai ance na tashi na siyo musu waina da yar yau sai dai ko kwakwaron mosti na kasa yi.

Komawa tayi ta cewa Anty Yana nayi banza da ita. Ina ji tana mita tana shigowa dakin "au wai yau suhaiman dan iskanci kin tashi tayi? Ni zata nuna wa bakin hali irin na uwar ta" wani muhakacin duka ta daka min ba shiri na zauna a firgice. "Ba aika wa nayi a kira ki ba?" Cikin kyarma nace mata "kiyi hakuri banda lfy ne?"


Fuska na tabi da kallo ta zaro idanu "ke lfy wa ya miki haka? Waya mareki?" Ban iya cewa komai ba illa sunan Adda Falmata da na kira mata. Dai dai lokacin ko ta fito daga wanka.


"Falmata ban fa son duka ni kin Sani ko?" In kaji yanda tayi maganan kaman mai lallashin ta.


Galla min harara tayi ta juya wurin Anty Yana tana turo baki "Anty Yana kinfa San munafuncin yarinyan nan, wlh sharri ta ke Min na zo shigowa ne kin San ta ba natsuwa ta kusa cin karo dani shine fa ta buge"


"Ke Suhaima ban San sharri musamman wa yarana" abinda ya fito daga bakin Anty Yana kenan, ba ta karamin magana ba ta fita daga dakin. Ina nan kwance su ka shirya su ka fita school, har itama Anty Yana su ta tafi unguwan. Ba Wanda ya damu da ni balle rayuwata. A wannan ranar zan iya rantse wa tsohon rai ne ya sa ban bi kakanni na da su ka rigamu gidan gsky ba.


Sai da yazo ko kwakwaron mosti kasa yi nayi balle in tashi neman mafita, gashi Abbah bai gari balle in sa hope in taimako daga wurin shi. Ina nan kwance cikin azaban nan naji maganan Anty Yana ta dawo gidan, amma ko ta kaina ba tabi sai ma ji nayi da tana cewa Ya baba "gsky yarinyar nan dole ta fara girki, bazan dauka ba tana kwance in dinga abinci tana ci" sai kace ta taba daukan abinci da hannun ta ta bani, dan tsoro ma ko a gaban ta bana iya diba.


Addu'a na dinga yi cikin zuciya ina rokon Allah ya aiko da mafita. A cikin hakan baccin wahala ya dauke ni, nafi  kusan awa biyu ina yi sannan na farka a firgice. Ba laifi na dan ji sauki Kadan don haka nayi kokarin lallabawa da dafen bango na isa bayi na dan watsa ruwa, sannan nayi alwala na samu nayi sallah.


Da ke Allah ba azalumin bawan shi bane. Ina zaune naji sallaman Goggon Adama, rabon da ta shigo gidanmu har na manta. A daddafe su ka gaisa da Anty Yana.

"Lfy Suhaima ba taje makaranta ba?" Abinda ya fiddo daga bakin Goggo kenan, in da na cika da mamakin ina taji.


"Ehmm wlh ba ta ji dadi bane da zazzabi ma ta kwana shine nace zuwa makarantan ba zai yiwu ba gwara ta zauna ta sha magani, tunda sai da lfy ake karatun" in kaji yanda ta ke maganan, sai ka rantse da Allah tsakani da Allah ta ke rike dani, Amma Goggo da ke ta riga da San halinta ce mata yi "shine kika baro ta a dakin? Ai da Falmata ce da tuni kuna asibiti" banji amsar da Anty Yanan ta bayar saboda lokacin goggon ta riga da ta shigo ciki.


Tana ganina ta yi saurin iso wa gareni, ina kokarin gaishe ta takai hannun ta wuya na, jin shi zafi radau ya sa tace "kin sha maganin" kaina girgiza ina kara jin azababben ciwon kai na ratsa ni, ni daman ciwon kai ke yawan wahalar dani a rashin lafiya.

Taimaka min Goggo tayi na mike na sa takalmina sannan mu ka fita.


Anty Yana nace ma "Goggo lfy"


"Dallah rufe min baki marar imani kawai, bara Uban nata ya dawo" abinda Goggo tace kawai kenan ta ja ni muka tafi.


Babban chemist muka tafi aka min allura da magunguna sannan mu ka dawo gida "ko mu tafi gida ba?" Goggon ta tmby da sauri na amsa mata. Muna isa ko Adama ta sa min ruwan zafi nayi wanka na samu naci abinci na sha magani, nan ta ke bacci yayi awon gaba dani.


Cikin kwana daya na warware sai dai ciwon kafan da na ke fama dashi har yanzu a sanadiyyan tsallen kwadon da na sha. Da la'asar sakaliya ina zaune muna hira da Adama, daga sama naji sallaman Anty Yana. Nan ta ke gaba na yayi mummunar faduwa na fara addu'an Allah ya sa ba tafiya za tayi dani ba.


Ina jin ta daga daki suna gaisawa da Goggo.


"Goggo jikin Suhaiman nikam yayi tsanani naga ba ta dawo gida ba?"


"Au ashe ba ta dawo ba?" Goggo ta amsa ta cigaba da abinda ta ke ba tare da ta dago ta kalli Anty Yana ba.


  "Ai wai na San tanan, yanzu ma na zo  tafiya da ita ne saboda In Abbansu ya dawo zai yi fada"


Tsaki Goggo taja tace "keh Yana tashi ki tafi ki bani wuri kafin in saba miki, in uban nata ya dawo kice ya zo ya same ni" kasa cewa komai, Anty Yana tayi, sallaman ta da naji cikin sanyin jiki ne ya Sani kyakyawan ajiyan zuciya.


Cikin kwana biyu na warware sosai, ba abinda na ke yi ko zanyi ma Goggo ke hanani, in na musa ta min tatas. Da ruwan zafi ta ke gasa min kafan sannan ta shafa min man zafi. Cikin hikima ta tmby ni mai ya faru don ta San ina jin tsoro. Ban kawo komai a raina ba na fayyace mata.


Ko da Abbah ya dawo, da ke weekend ne sai ya dauka ina Ajayeri bai tmby ba. Sai da yaje gaishe ta take ce mishi "satin nan kuma Suhaima ta guje mune? Ko dai anki kawo ta ne?" Shiru yayi cike da mamaki sai dai don kar goggon ta dago yasa yace mata "ai ni ma bamu hadu da ita ba sai na koma na jiyo miki dalili"


Ai ko yana dawowa gida, ya hau Anty Yana da bala'i. "Wai ni ina suhaima ne, daman tana gidan nan na dawo ba zaki ce mata tazo ta gaishe ni ba"


Cike da in ina tace mishi "ai ba ta gidan nan tana gidan Goggo"


Hararan ta yayi yace "kinsan bana son yawo da hankali ko? Ba daga gidan Goggo na ke da ban gan taba na taho da ita ba"


"Aa Goggon Adama fa na kollere"


"Goggon Kollere kuma? Lfy?"


Nan fa Anty Yana ido ya raina fata ta fara inda Inda. "Eh to wai ciwo tayi shine Goggon tazo ta dauke ta nace mata za kayi fada tace in ka dawo kaje gidan ta ka same ta" shiru shiru yayi yana jinjina zancen kafin can ya tashi ya taho.


Wani tsakar gida muna hira har da yaran Goggon da ke gidan sai ka sallaman Abbah. Zama yayi su ka gaisa da Goggo sosai sannan ta sa aka tashi aka bar mu mu uku kawai. Nasiha ta fara mai sosai sannan ta ce "to bara in sanar maka Yana ba ta kula da suhaima in ma ba ka Sani ba yau ka sani, domin zuwa gidan nayi na same ta rai hannun Allah sun taru sun mata duka, sannan ta tasa yaran ta a gaba ta tura su makaranta ita ko oho, aka sameni aka fada min ni kuma naje naga dahir." Dan Jim Abbah yayi sannan yace "Goggo duka kuma?"


"Kwarai kuwa, ita uwar ta sa bulala ta Zane shi namijin ya sa ta tsallen kwado sannan yar uwar ta kara mata da mari da duka. Shi yasa nace ma ka dole ka farga ka kula da abinda ke faruwa cikin gidan ka don ko gsky da sake"


Godiya ya mata sosai sannan ya Sani a gaba mu ka tafi, ni dai raina bai so ba. Don na fi kaunar mutuwa ta akan wannan gidan. Ta kaina Abbah ya fara "meyesa ana miki abu baki fada min?" Shiru nayi na kasa magana, ai ko tass ya wanke ni.


Muna shiga gida ya hado Anty Yana, Yaya baba da Adda Falmata.


"Yana na dade da Sanin baki son zaman Suhaima a gidan nan sai dai ina so in sanar da ke duk abinda za kiyi wlh sai ta zauna, gida dai na Uban ta me kuma ta fiki iko dashi don haka ki fita idona in rufe, kar ki sake sa hannu ki bige ta, da ba dan kaddara da ya raba mu da Aisha ba ma ina ke ina rike yar ta." Fada sosai Abba yayi  ya zage Anty Yana tasss sannan ya mata kyakyawan warning, Ko kala Anty Yana kasa cewa tayi domin ta san halin Abban, sai dai kana iya hango bakin cikin ta a sanadiyyan sunan Ummin da ya an bata.


Juyowa yayi kan yaran bai fara musu magana ba sai da ya zuba wa Yaya baba mari lafiyayye a fuska. Dawo wa yayi kan kan Adda Falmata, jikin ta har rawa tsabagen tsoro. Wani irin rankwashi ya zuba mata a kai, har ajiyan zuciya nayi don farin ciki. Punishment ya sasu kala kala, sai da yaga sunyi lakwas sannan ya barsu, Adda Falmata har da hawaye da majina tsabagen wahala. Ni kam daki na Shiga na kwanta ko bakomai am satisfied yau an kwato min yanci na.

Bayan ya fita tayi ta muzurai, ni kam ko kallon ta ban yi ba ita kuma ba daman bugu na. Sai dai na sha zagi da habaice habaice, mahaifita ba irin zagin da ba ta sha, duk da ina jin zafi sosai a raina domin Uwa Uwa ce amma wani sashe na zuciya yana gaya min koma mai ya faru ita taja, da ba ta tafi ta barni a cikin kangin wahalan nan da ba za ma su ganin ba balle su zage ta.


Zan iya cewa Alhamdulillah! Tun daga matakain da Abbah ya dauka na samu sauki, duk abin Adda Falmata tana shakkan bugu na, saboda Abbah ya ban daman in har ta buge ni, in fada mishi, in ko ban fada ba to fa kaina zai dawo. Gashi aikin shi yanzun ya dawo cikin Maiduguri saboda haka yana yawan zuwa gida a duk chance in da ya samu.


Ba batun duka yanzu sai dai duk wani aikin gidan nan wuri na ya dawo. Shara, mopping, wanke wanke wani sa'in ma harda girki. Ga wankin su sadiya, wannan kam ko da yaushe ni na keyi.

Haka rayuwan ta cigaban bin, rashin dadi ya fi dadin yawa, tun ina zama in yi kuka har na fara sabawa da rayuwan. Hakan ya sa na natsuwa na maida hankalina sosai a karatu, sau da dama ina tuna huduban Ummina, ta kan ce min, ki maida hankali ga karatun ki sosai domin karatu shine gatan mutum a rayuwa. Da farko har na fara ja baya a makaranta amma da nayi focusing sosai sai na fara komawa dai dai. Ummina mace ce mai matukar mahimman ta karatu a rayuwarta, ko da na taso na ganta tana zuwa, Yobe state university. Inda tayi karatun degree bayan F.C.E da tayi a Maiduguri. Kusan a lokacin na saba da Adama da Goggon ta, a can ta ke barina in ban makaranta.


Sannu a hankali lokaci ya cigaba da tafiya, duk dani ban ganin saurin shi saboda kangin da na ke ciki. A islamiyya a ke koyar da mu addu'oin kala kala, malamin ya kance duk wani matsala da kake ciki to tabbas addu'a ne maganin ta. Hakan yasa na koyi zama in dinga addu'a akan matsalolina, musamman cikin sallah.


Kwatsam! Watan azumi ya shigo, wannan azumin ba karamin wahala na sha ba. Ga makaranta jarrabawa ga aiki kaca kaca a gida, ga kuma azumi. Duk dagewa na dole sai da na ja baya a makaranta, amma still ban karaya ba na kara datse damtse. Duk na je ajayeri musamman na kan zauna inyi karatun duk jarrabawan sati. Mafi yawancin yara kamana ba su San su zauna suyi karatu ba a primary amma ni kam gani na ke shi kadai ne zai cece ni, musamman saboda na saba Muna yi da Ummi.


Ina ganin Anty Yana na ciku cikun siyawa yaran ta kayan sallah amma ni ko oho, ban wani damu ba saboda nasan ba za ta min. Abbah dai ya mana kala bi biyu, har gida aka zo aka gwada mu. Amma kusan yarinta dole naji wani iri, saboda lokacin yara kamana kusan kala shida ko bakwai ake musu, ni ma in haka Ummi na ke min da tana nan. Ribbons kala kala, kitso, lalle, takalma, gyale da hijabin idi. Amma da ke Allah gatan bawa ne ashe Goggo ta min dinki ta ajiye da hijabi to haka Goggon Adama ta aiko min. A lokacin kam na San tabbas su ne gata na.


A ajayeri nayi Sallah, kuma Goggo ce ta sa Abbah ya kawo ni. Muka yi ta yawo da Ajiddah da sauran kawayen mu na islamiyya bayan an sauko idi. Sai wurin la'asar na koma gida. Su Adda Falmata duk suna gidan, ganin su na da yawa na gane harda yaran baffanni na ciki ko harda yaran Baffan maiduguri. Ba wuni saba da su ba saboda haka gaishe su nayi kawai na fita.


"Adda Suhaima! Adda Suhaima!" Na ji ana kwalla min kira ina dab da shiga sashen Anty Amarya. Tsayawa nayi ina kallon mai kirana, ban san lokacin da hawaye mai zafi ya fara zubowa daga idanuna ba.

Post a Comment for "LABARIN RAYUWATA CHAPTER 6 BY Ayeshay bee"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...