LABARIN RAYUWATA CHAPTER 5 BY Ayeshay bee - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

LABARIN RAYUWATA CHAPTER 5 BY Ayeshay bee

LABARIN RAYUWATA CHAPTER 5 BY Ayeshay bee

- - Post a Comment

 LABARIN RAYUWATA CHAPTER 5 BY Ayeshay bee                      Www.bankinhausanovels.com.ng 
A gajiye likis mu ka koma gida ranar, ko kallo na Zayd bai kara yi ba har nayi parking, daukan Amal yayi da ba ta san inda kanta ya ke ba yayi cikin dakin ta. Ni baccin ma ji nayi ba abinda zan iya yi, haka nan na zauna a falo na kunna film duk da hankali na bai wani kai, mutane kawai na ke gani suna ta displaying action. Sautin da ya ke fito daga dakin Amal yasa ni sanin abinda ke faruwa, daman ganin abinda a club in nasan dole hakan zai faru. Its been long sex yashiga tsakanin su as far as i know, they are all louders hakan yasa na ke ganewa.+

Na dade a falon ni kadai ina kallon TV ko kuma ince film yana kallo na dan gabadaya ban sa abinda ake ba. Tunanin kunci rayuwa da tausayin rayuwa irin tawa ya sa naji gabadaya duniyan na neman fice min a kai. Kwallan da na dade ban zubda bane naji suna zuba a idanu na, na dauki lokaci a haka ina jin kaina na juyawa yayin da hawayen ke cigabda da tsiyaya. Ban ji fitowan Zayd ba ko takun shi sai tafun hannun shi da naji kan fuskana, hawayen ya laso da dan yatsan shi manuniya. Yatsan ya koma bi da kallo ya tsaya a kaina kaman mai son gano wani abu, can ya girgiza kanshi sannan ya saman ma kanshi matsugun ni a daf da inda nake. Hannuwan shi ya ratayo ta kan wuya na, sai lokacin na iya daga kai na kalle shi, idanuwan nan sun yi jajur kaman wanda ya sha kuka ya koshi.


Bai dai ce min komai ba har na fauke idanuwa na daga kan shi, kara jawo ni jikin shi yayi ya juya yana fuskan ta na da kyau. "Why are you here?" Na tmby, magana na farko kenan tun bayan fitowan shi.


"Suhaiima please" sauri dakatar dashi nayi da hannu na, a hankali nace "tmbyn ka kawai nayi nd you can only give me an answer" kan shi ya sadda kasa, focus in shi gabadaya na kan yatsun kafana. Ban san mai yake nema a wurin ba. "I want to check on you" more like a whisper maganan ta fito daga can kasan makoshin shi. Siririn tsaki na ja, na janye jikina daga nashi "You can pretend all you want, na riga da na gane komai" saurin girgiza kai yayi yace "pls babe kar muyi haka, ki saurare ni kafin ki yanke min hukunci"


"Wani saurara kuma Zayd? Bayan abinda idanuwa na da kuma idon duniya su ka gani. Ba ma wannan ba, me kuke son in fada wa Mum bayan yarda dani yasa ta amince ma zamana da yar ta, tun dazu na ke ganin miss calls inta" zaro idanu yayi, yace min"dont tell me abun nan yayi yawo?"


"You can check the media ai nd ka kwantar da hankalin ka am not talking about the kiss" ba wani reaction in da yayi sai can yace "am not happy seeing you with Hafeez, kinsan wanene Hafeez? Ta ya zaki biye mai har ki bari ya taba jikin ki bayan kinsan hakan bai dac..." Kaman ya karasa nayi saurin mikewa ina kallon shi cike da mamaki ina jan baya "kai har ka san abinda ya dace da wanda bai dace ba Zayd? Ko kuma kai da kake tabanin muharrami na ne? Fada min yaushe ka fara kokarin kiyaye dokokin Allah" jin yanda na ke magana a fusace ne ya sa yayi saurin mikewa.

"Yi hakuri jewel zo ki zauna Dan Allah muyi magana" tsaki na ja kaman ba zan zaunan ba sai kuma na koma inda nake kafin in mike. Ina jin wani irin tafasan da zuciya na ke fama da, i so much hate my life to the extend na ke jin gwara ayi komai kawai a kare ta cikin kankanin lokaci ko na samu in gina wa kaina sabon rayuwa dai dai da tsari na.


Girgiza kafa nake in hararan shi, hakan ya sa shi yin murmushi. Kwantar da murya yayi ya fara magana "nasan ban kyauta miki ba Jewel but kinsan Amal, kinsan yanda ta sani cikin rayuwar ta abu ne mai wahala kwatsam ace ba ma tare da ita, shi..."


"To mai zai hana ku kasancewan a tare? Kai ma fa na gane kana bukatar hakan. Dan haka please ka kyale min rayuwa tun wuri Zayd"


"Ba zan iya" yayi saurin fada "Zuciyan Amal ni ta ke so sai dai kuma ni nawa zuciyan ke ta hange, ke ce a cikin ta. Ban zan miki karyan ban son kasancewa da Amal ba saboda ita in wata jigone babba a rayuwata, i like her sai dai  i have many reasons da yasa ni kasancewa a tare da ita. Nasan kin san me ya shiga tsakani mu a daki, she wanted to and i can just resist her. Amal mace ce Suhaima sai dai ban mata irin son da ta ke min. Ko da inma tausayin ta yafi son yawa, i befriended because of her eloquence amma sai mu ka tsinci kaman a cimin rayuwan da kika same mu."


Ban ce mishi kala ba har ya gama koro min bayanin shi. "Baki ce komai jewel" kallon shi sannan na juya kai gefe "banda abin cewan ne . kaga it better kawai kaje ku dai dai ta da budurwa ka, i can't stay in this kind of relationship ni dai da daraja ta, i just can't be a second option to someone" tagumi yayi, sosai na ke hango tashin hankali akan fuskan shi "Yanzu me kike so? Suhaiima" kaman zai yi kuka tsabagen yanda muryan shi ke rawa. In ba wai dan na san raggonci namiji akan soyayya ba, da sai ince nayi mamaki yanda mutum hadadde, mai ji da takama kaman Zayd zai tsaye a gabana yana marairai ce min ba. Wlh da farko na dauka yanayin jiki na ne kadai ya jawo min soyayyan Zayd a gare ni, a hankali na ke fuskanta iya gskyn zayd soyayyan gsky ya ke min. Zayd in nan ne dai, da ya san sirrin soyayya, ya afka mata da dama a cikin ta ya kuma juya su son ransa. Har a jiki na ji nake hakkin matan da zayd ya yaudara a baya ne ya kawo shi gare ni har ya kai da afkawa gabadaya, in ba haka ina ni? Ina Zayd? Duk da matsayi da na siyan wa kaina. Dan ko Club mu kaje sai kafi jin tashi na akan na Amal, ita kam kullum da kyar mu ke lallaba wa mu koma.


"Zayd Almansur" na kira sunan shi, bai amsa sai kallon da ya bini dashi da tagumi manne akan fuskan nashi. "If you truly love me ina son ka bayyana wa duniya kowa ya sani, ko nasan matsayi na. Am tired of the hidden game" girgixa kan shi yayi kaman wani yaro karami yace "nikam ai daman ke kika hana ni fada, bara in tashi Amal in in fada" da gaske tashin yayi, sai da na jawo hannun sa sannan ya juyo yana kallo na "a Abuja kaman yanda mu kayi" gyade kai yayi sannan ya koma ya zauna, yana cigaba da nuna min iya gskyn shi sona yake. "Jewel kin san yanda na ke ji akan ki kuwa? I wanted to punch Hafeez so much dana gan shi yana rike min ke. Ina son ki sosai babe ina" yana maganan yana riko tafi hannu na, kallon su ya ke sosai yana maganan. "I've always want to have kid" ba tare da na dago na kalle shi ba nace "you have a wife" tabe baki yayi yace "I don't want her children" idanuwa na akan shi ina shirin yin magana yace "she don't want to have my children either, ko tayi cikin ma aborting ta ke, she is always taking pills ni kuma na gaji na kyale ta. Now she badly wanted the kids ni kuma ban bukata a gareta kuma" suya naji zuciya ta nayi, wasu na neman yaran amma ita wannan gudun su ta ke ma, yanda na ke son ganin jini na ina jin ko dan shege ne, duniya ba wanda ya isa hana ni rainin abu na."Ina son yara kyawawa daga tsotson ki Suhaiima, ai zaki bani ko?" Gyade mishi kai kawai nayi saboda banda interest akan zancen. "Masu kama da ke" ya kara fada, dan zaro idanu nayi nace "masu kama da kai dai, you are more beautiful among the two of us."


"Liar" tsakulan hanci na yayi "i love dark ladies, Suhaiima you are just a dream come true, tun ina saurayi na ke son bakar mace, i love the melanin sai dai am not so much lucky. I like your eyes sosai" hannun shi ya sa ya shafo idanun, a dole na na lumshe su. "Da dan karamin bakin na, i couldn't wait to devour one day" murmushi kawai nayi, ya cigaba da tsaro min kalaman shi masu dadin sauraro amma fa ni kam a kunne kawai ya ke tsaya min. Zayd ya iya soyayya wacce za ta tafiyar da hankalin yan mata, ni kam dai wani ya riga da ya ma tawa illan da bai bar ma wani wurin shiga ba.


Washegari, dole mu kayi postponing flight inmu zuwa next day, ni da Amal ne kawai saboda zayd yace akawai meeting in da za suyi a wani gu tare da ogan shi Hafeez. A daddafe mu ka farka bayan mugun baccin da mu ka sha, cook in Amal ta riga da ta mana abinci. Muna ci Zayd ya zo fita damu wai zai kaimu shopping. Amal tayi tayi ya bar shi amma yana ta insisting. Hakanan mu ka tafi, duk ma kayan ciye ciye ne mu ka dauka daganan ya ja mu beach.

I so much like it in the beach, mu uku mu ka zauna wuri daya muna sharing the best moment, lokaci zuwa lokaci yana satan kallo na duk da Amal da ke like a jikin shi kaman wata mage. Kaman wacce aka tsikala ta mike tsaye har da dan tsallen ta, the girl can be fun and childish. "I have a plan" ta fada tana wani rolling idanun ta "let do a game call Tell us ten things we don't know about you." Duk dariya mu kayi, mu ka hada idanu ni da Zayd, kashe min gira yayi ya juya wurin ta "okay bestie go first, we are all ears"


"Yeah" ta fada da dan saurin ta ta koma jikin shi ta fara magana "No judgement fa" duk amincewa mu kayi sannan ta fara lissafo wa


"1. Nasan ba ku sani but i so much like the name gigi Amal.


2. I prefer Lagos club to Abuja's


3. I like making friends sai dai i always fail in making the relationship work


4. I feel like my relationship has an underneath problem that will unfold

5. I hate taking wines and alcohols


6. I don't really like dark chocolate as i claim to


7. Lagos life isn't as bad as am exaggerating


8. The idea of getting married scared me


9. I don't really like it at my fathers house


10. I don't like been independent on my own“


Ba wanda ya katse ta har ta gama, sai lokacin na yadda ko ya kake da mutum akwai abinda ya boye ma kanshi sanin shi kadai. Imagine, wai Amal hate alcohol and wine, duk yanda ba ta iya dauke idanuwan ta daga kan su, sai dai in bata gani ba kuwa. "Besty ba fa kya son dark chocolate kika ce?" Zayd ya tmby cike da mamaki, like she is always taking them a ko da yaushe. Gyade mi shi kai tayi tana dariya kasa kasa "it just some sort of addiction, at first i pretend loving them and then it turns that way, Love you can go next, asking question isn't part of the rules.


Dariya yayi sannan yace " ni kam ta ina ma zan fara?"


"Ko ina ma" a tare mu ka bashi amsa ni da Amal.

”Okay:


1. I like kids, as in my own kids.


2. My wife Amina was my first love and i still feel something for her


3. I admire my Mom even though we were never on good times


4. I hate going to work


5. Am eager to have a second wife of my dream


6. I hate publicity, though am always getting them.


7. I like employing people and making friends out of them


8. I wanted to be a Police man


9. I really don't have any friend whom i share my problems to


10. I enjoy having people who raise my status around me" yana gama wa ya saki murmushi, all through maganan da yake focus in shi na wurin ruwa, hakan za ka gane he is saying things directly from his mind.


"You like kids? I never know" Amal ta fada tana kallon fuskan shi, shrugging shoulder yayi yace "i just say things i couldn't avoid ne, no matter how i want to" tafa hannu tayi "It okay, Frnd your turn" annurin fuskana ne ya dauke dan ni ban ma san me zan ce musu ba. They may be saying the right things ni kam ban son in musu karya, domin zamana da su kawai gabadaya karya ne.


"Am feeling hungry" nayi saurin fada "Eyyah sorry" Amal being Amal tayi saurin fada, a cikin ledan shopping bags in da muka zo dasu beach ta dauko wani ledan tana mika min "pepperoni pizza, you gonna like it" amsan nayi ina murmushi na.


"You can still tell us while you eat" Zayd da curiousity ke cin shi ya fada, dan ita Amal har ta manta ma. "Yeah besty please tell us" ajiye pizzan nayi nace "okay kun san is not good to talk while eating"


"Yau kika san rules in kenan?" Zayd ya fada, dariya nayi na fara cin pizza in. To mai ma zan fada musu? They don't know almost everything about me, i don't know the ten to choose.


"Oya tell us" Zayd ne yayi maganan.


"Yayana ba zaka bar wannan maganan ba ko? I have no idea mai zan fada muku"


"Then we can ask you?" Amal tayi saurin fada, duk da tsoron da naji amincewan nayi.


"Do you love somebody?" Ta tmby, sai da mu ka hada ido a sace ni da Zayd sannan na juya nace mata "Yes"


"Who is he?"


"This is the second question and i will answer,   wani ne kuma soon za ki ganshi"


"Frnd wai ke wayau ko? Naji and the next question why are you hiding him?"


"Saboda ina so ya zame miki surprise lokacin da kika ganshi" tabe baki tayi tace "ba dai kyau, next question ur favourite food, you never tell me one" kallon pizzan da ke gabana nayi nace "Pizza" dariya tayi sosai sannan ta kara cewa "Novel or movie"


"Novel" na amsa mata, daga haka tace she is done with her five questions, Zayd yayi sauran. Sai da gabana ya fadi saboda ma irin kallon da ya min tun farkon.


"Kanwata what is your level of Education?" Folding lips ina nayi sannan a hankali nace "Just first degree"


"Degree is not just, a bangaren wani course" kaman ba zan bashi amsa ma sai can kuma nace "Medicine" dukkan su biyun a tare su ka juyo suna bina da kallo "Medicine Friend?" Amal ta fada, da alaman mamakin ma yafi yawa a bangaren ta. "Wow! Housemanship?" Zayd ya tmby. Girgiza mishi kai nayi nace "tukunna dai but soon"


"But why do you choose to focus on something else?" Zayd in ne ya kara tmbyn "I want to enjoy the pleasure of something else, i will get back to it ai" duk mamakina su kayi nit knowing the real truth behind everything.

"Ina ne state of origin inki?" Zayd ya bukata


"Borno" na amsa mishi.


"Ya aka yi kika zo Abuja to?"


"Boko haram crisis" na amsa, yanda nayi sounding so real ya sa ya yarda, it truth though amma partially.

"But Bestie me ya sa kika boye min? Kika ce you are family" kallon shi tayi looking apologetic tace "Dad ina ma fa Dan Borno ne and ina jin Suhaima kaman yar uwa, we are even family now" side hug ta bani, na rungema ta tare da share dukkan wani guntun kwallan da ya taru min, wadan na tuna asalin sirrin rayuwata ne.

"Suhaima is a nice girl, i like her" Zayd ya fada yana kallon Amal, murmushi ta mishi tana kara fadin "sorry for not telling you love" daganan zancen ya wuce bayan Zayd yayi ta insisting inyi Housemanship in mu koma Abuja, duk yanda ya so kin amincewa nayi nace ya barni sai zuwa next year kafin nan am done. "She get a mission here love let her" Amal ta fada.


Sai kusan magreeb mu ka koma gida, a nan ma wani hiran ne ya barke. Daga baya na ja jiki na nayi daki. Ina zaune text in Zayd ya shigo wayana. “babe why didn't you tell me about you before? I want to know every single thing concerning you”  Daman nasan za ayi haka, don haka na tanaji dukkan abinda zan fada mishi in ya tmby. “it wasn't a nice story dear, i lost them both during the crisis due to bomb blast in our house at night, rashin sanin ina zan nufa ne ya sa na biyo makociyan mu wacce ta ke bazawara garin lagos,  unknown to me gidan karuwai ta kawo ni so i have to left” Emojis in kuka ya turo min. Daga baya ko bayan Amal tayi bacci ya zo dakin, da ke shaye shayen ya zame mata addiction duk in bata sha ba ta iya bacci sai taji kaman za ta shide, ya riga da ya shige ta sosai don ko Zayd bai shan abinda ta ke iya kwankwada.

Da ke dan guntun labarin da na bashi ya taso min da tunanin rayuwata, nan da nan na rikide  na zama wata aban tausayi idanuna na sun zama jajawur dau. Ko da ya shigo ya riske ni a haka, he was so touched. Lallashi na ya dinga yi, nan na bashi labarin duk abinda ya fatu dani, yawanci zallan karyane duk da akwai gaskiyan sosai a ciki sai dai ban bada shi a yanda ya kamata ba. Rungumeni yayi har da dan kwallan shi yana min alkawaruruka, akan in na aure shi zai zame min gata a duniya, he will always be there for me, zai zame min duk wani abunda na ke bukata. In short, ba abinda zayd bai fada min ba, ni in ina kallon yanayin shi ma wani irin tausayin shi da ban san dashi ba ke tafiya dani. Nan ya ke sanar min maman shi yar yobe ce, i appear shock saboda ban san wannan in ba. A cewar shi za a nemo yan uwana a bornon sai a je in an tashi neman auren nawa.Karfe 10:00 na safiyar washegarin a cikin garin Abuja ta mana. Driver in gidan su Amal ya zo ya dauka mu daga airport. Kai tsaye wurin mum na fara zuwa. Bacin rai kwance kan fuskan ta tace "Suhaima kun dawo?" Na amsa mata mu ka gaisa. Tace "Suhaima ya akayi haka ne wai? Na ga pictures in Amal na ta yawa a media tare da Zayd" ajiyar zuciya na saki, daman tun juya na shirya abinda zan ce mata. "Mum ba fa wani abu bane, kawai bikin  wata friend inta da su ka yi School tare ne, tare ma muka je. To shi daman Zayd abokin mijin tane. Kawai pics bikin ne ke ta trending. Na fadi hakane dan nasan pic in Amal da Zayd kawai za a turo mata, wanda da gangan ake hakan. Sai dai duk wannan bayanin da na kwasa da Amal ta shigo, kala mum ba ta mata maganan ba sai ma hiran yaushe gamo da suke tayi.+


A ranar na shiga Drink shop, sai dai ban dade ba na fito saboda kiran da Anty Umaymah ta min zuwa blue cabana. Lunch mu kayi da ita, ina bata labarin abinda ke faruwa. " aikin na kyau Suhaima, irin su Zayd su cancanci fiye da haka, Amal ba ta dace dashi saboda gurbata mata rayuwa kawai zai yi. Kema ki kula da kanki please ban son a zo a sami matsala fa" murmushi nayi nace mata "karki wani damu Anty na, duk abinda ya kama inyi to wlh zanyi. Ni kam ko kin San wani abu akan matan shi Amina? Na ji yana fadan ta" tabe baki tayi tace "I don't know much gsky, akwai dai inda na santa. sai dai ita ma yar Yobe ce"


Zaro idanu nayi da mamaki nace "kenan Zayd yana da alaka da Yobe?"


"Mamarshi yar Fika ce, abinda na sani kawai kenan" jinjina kai nayi ina ganin karfin al'amarin, anya shirin mu zai kai labari kuwa?

"Zan iya jawo ta jiki ina ganin daga wurin ta ma akwai burin da zan cin mawa" da kai kawai na amsa ta, a zuciya na kuwa ina tunanin duk abinda za a cewa dauka fansa to tabbas sai an samu gargada a cikin shi. Sai dai nasan she is so determine akan abinda ta sa a gaba, ni kuma alwashi na dauka i will help her out. Sometimes ina jin kaman Dana sani yana min katutu, sai dai a tsari na ba magana biyu. In nace zanyi to tabbas zanyi.


Kamo hannu na Anty Umaymah tayi tana fadin "baby kin dai guje ni Ku?" Daga giran ta tayi tana jiran amsa. Ganin yanayin fuskana ya sa ta murmushi "kar ki wani damu, kinsan tsari na ba takura mutum if you don't want it ba batun dole. Ra'ayi ne kowa na shi ya ke bi" I like this side of her sosai, duk yanda kake kasan ta in ba ka son abu ba ta tilas ta maka.


"Don't you think ya kamata ki bar gidan su Amal hakanan?" Kallon mamaki na mata nace "Anty in na zan je in ba nan ba? In har muna so muyi achieving abinda ke gaban mu then i can't live with you, ai kin san hakan ko?" Da kai na amsa mata tace "am just thinking kar su gaji dake" siririn dariya nayi nace "Su fa basu da damuwa, ko harkan shi yake yi a gidan nan bayan haka kuma na samu karbuwan wurin mum inta sosai"


"Da kyau baby, sai batun karatu when are you ready to continue?"

"Ba yanzu ba tukun"

A ranar, a wurin mu ka kara haduwa da Faroukh. Dashi da wani da ban sani ba suka zo wurin, ban ankara da kusa damu su ka zauna sai da nazo tafiya nace ma Anty Umaymah "bar naje, Kinsan Zayd yau zai dawo ina da wani plan kuma a yau in nan" dai dai nan muka hada ido da Faroukh, sake ido da baki kai har ma hanci nayi ina kallon shi. Na gama amincewa zuciya ta bibiyata ya keyi, in ba haka miye wannan? Kallon banza ya min ya juyar da kai, nima na saki tsaki nace ma Aunty Umaymah "anty akwai matsala zan kira ki" ina fadin haka na ga ya juyo yana kallo na. Murmushin mugunta ya saki yana girgiza kai.


"Har wayau Abban Haydar ban yarda Faroukh ba bibiyan lamarina yake ba" Suhaiman ta fada. tana kallon barrister da faman sauraron ta kawai ya ke yi. Zuwa yanzu shi inma ya fara yarda da Faroukh gsky ya ke yi. Ya kasa hango labarin da ta ke bashi a kanta, ya Riga da ya tabbatar da kokonta da yayi na zaman ta a gidan karuwai, duk da ko ba ta fada mishi kai tsaye a labarin ta ba. Abu daya zuwa biyu ya ke son jin yanzu, shin tana da hannu a kokarin kisan Zayd Al-mansur? Da kuma dalilin da ya sa ta yin abinda ta yi. Shi kanshi ya san karfin halin sauraron labarin ta yake izuwa yanzu, da wani ya bashi labarin ba ita ba to da tabbas ba abinda zai hana shi karyata wa.


"Zan je inyi Sallah Suhaima" ya fada yana dan cizon yatsan shi "zan dawo zuwa yamma, Kinsan dai ranar shiga kotun ya kusa ko?" Da kai ta amsa shi yace "to continue on praying sannan kiyi kokarin karasa min labarin, in min samu baili sauran zai biyo daga baya.


Godiya ta mishi bai amsa ba ya fita daga station in.


Ya so zuwa Kaduna samun Faroukh amma sai Anty ta ke fada mishi ai Faroukh in ya zo Abujan. Saboda haka ya kira shi ya same shi.


" uncle musty i don't want to talk about her again" abinda Faroukh ya fara fada kenan bayan sun hadu da Uncle in na shi.


"Ai ba ra'ayin ka nake nema ba Faroukh, tell me mai ka sani game da Suhaima for the last time. Ta gaya min tana zargin kana bibiyan lamarin ta, saboda duk inda take wani sirrin ta sai ta ganka" dariya yayi hade da tabe baki "To Uncle Musty ita kullum cikin rashin gsky ta ke ai, shiyasa da ta ganin sai ta daburce tun ran da na ganta a vows nasan tana da matsala"


"Ka sha jin abinda ta ke fada kenan" Bare ya bukata.


"Eh na kanji amma ba duka, kuma ni ba bibiyan ta na ke ba kaman yanda ta zargi kawai dai Allah ke kawo ni inda ta ke. Nasan dai na kan sa mata ido, saboda kar taje tayi abinda za ta cuce mutane tunda nasan tana da aim in zaman ta a wurin." Kallon nephew in na shi kawai barr yake. Can yace "to why ba ka fada ma ogan ka ba?"


"Abinda ba ni da tabbaci akai? Bayan haka ma na san yana sonta ko na fada mishi ba ba zai yarda ba illa ma hakan hadari ne ga aiki na." Shiru yayi can yace.


"Uncle Musty kayi hakuri ka daina tmby na akan Suhaima, kar ka manta ni din shaida ne da zan tsaya gaban kotu in bayyana dukkan abinda na sani game da ita wanda naji da wanda na gani, kuma ban nadaman hakan saboda martaban mai gida na zan tsare a kwato mishi yancin shi. Ba a bani daman magana da kai a kanta ba don Allah ka daina tmby na".


"Allah ya kyauta" Barr kawai yace.


...


A wurin suhaima kuwa barr na koma wa ta cigaba da bashi labarin a inda ta bar aya.


Daya dawo a apartment in shi ko ince guest house in shi da ke cikin asokoro mu ka hadu.

"Ya dai babe na yi missing in ki fa" ya fada nayi dariya ba tare da na wani sakar mishi fuska ba.

"Me ke damun ki Jewel?" Kai tsaye nace mishi "Kaine" marairaice wa yayi yana fadin "Ni Zayd, me na miki?"


"Mun dawo Abuja, ina son sanin matsayi na coz na gaji da wannan rayuwan" yanda na ke magana ina ci cijewa yasa ya dauki abun serious.


"We will talk with Amal yau in nan kuma a gidan nan kar ki damu"

"Da dai yafi" na aika mishi harara, dariya yayi ya jawo ni jikin shi yana fadin "to ai ke hararan ma kara miki kyau ya ke, I can't wait ki zama tawa"


"Wife in ka fa? Hope ba zan samu matsala da ita ba?"


Dan bata rai yayi yace "of course no, wa ya isa?"

For the first time ranar yayi kissing ina, mouth to mouth and am surprise yanda na ke iya responding ba tare da naji kowani irin feelings ba.


Kaman yanda mu kayi dashi ina barin gidan ha dade wa ya kira Amal ta zo ta same shi a gidan. Sai da su ka samu natsuwa da muna sannan yace mata "Besty, I want to tell you something, sai dai I don't want you to freak out. Ina so ki dube ni da idon fahimta" kallon shi kawai take, ba su saba hakan a tsakanin su ba like they are always free to each other "wani abu na ke matukar so daga wurin ki"


"Besty be straight mana kasan ba abinda na zan iya baka ba ko?" Murmushi karfin hali ne ya sauka akan fuskan shi.


"Tunda kince haka let me tell you then. Nasan yanda kike sona but am sorry na fada cikin wani irin rikitacciyar soyayya da samun zuciyan wacce na ke so ne kadai zai iya fidda ni daga abinda na afka" at first rasa inda za ta ajiye zantukan nashi da ya sauka a kunnen ta ta yi, tukunna ta fara tunanin gskyn abinda taji. Sai da ta kara duban gaban ta taga Zayd a tsaye sannan ta kara jin sautin kalaman nashi kaman lokacin ya ke sanar mata. Tuni ta rikice ta fara girgiza kanta yayin da jikin ta baki days ya fara shaking sosai "I know am dreaming"

Saurin rike ta yayi yana fadin "calm down lady you are not" da kyar ta ya iya dai dai ta saboda  yanda gabadaya ta firgice cikin yan mintunan da ba su wuce uku zuwa biyar.


"In ba mafarki nake yi ba? Then fada min wannan wani irin wasa ne Zayd Al-mansur" yanda ta kira sunan nashi in full da bai tana ji a bakin ta ba, ya isa shaida mishi akwai gagarumin matsaloli da zai yi facing.


Runtse idanun shi yayi sannan ya bude "Amal kiyi hakuri ba wasa nake miki ba" yanzu kam rasa ma wani reaction da yace tayi. More like a whisper tace "Then tell me kake nufi?"


"I mean I still like you as a friend, sister and ..." Da sauri ta katse shi "cut this off, you know me better i have no time for this nonsense or rather bullshit you are saying. Ka fada min kawai are you dumping me and for what other bitch?"


Abinda ya so daure mishi kai shine, a hankali ta ke maganan yanzu like it no a big deal, dan he seriously expect more. "Am not dumping you Amal, kawai ina son wata daban ne that is not you. Kuma kawarki ce Suhaima" kallon shi kawai ta ke ba kiftawa duk da yanda ta ke jin abun kaman ba gaske ba.


"Suhaima, ta sani?" Da kai ya amsa mata. Dariya ta kara yi wanda kana gani kasan ba tsantsar tashin hankali ne. "Okay" tace still idanuwan ta tsaye a kanshi.


"Okay?" Ya tmby saboda mamakin da yayi, seriously he expects more not even that, worst ma kawai.


"Abinda ka kira ni ka fada min kenan?" Rasa yanda zai amsa ta yayi dan har ya fara daburce wa ma. Ya dauka yau rana ce da zai kwana yana lallashin ta yana fahimtar da ita har ta fahimce ta bawa zuciyan shi salama. But sai gashi ta mishi abinda zai tana tunanin ba, shoulder he be happy? Sad? Like bai ma san wanne ta dace yayin ba.


"Ka gama?" Da sauri ya amsa ta da eh, a tunain shi yanzu ne zata zazzage mishi dukkan abinda yazo kanta. Ya san Amal will do her worst barin ma yanda ta sadaukar mishi da komai ta nuna ma duniya shine a gaba da ko.

Abinda ya bar shi baki sake bai wuce daukan hand bag inta da tayi ba tace "naji, sai anjima" da sauri ya mike ya fara binta. Sai dai duk jiran da ya mata ba ta ko juyo ta kalle shi ba. Har wurin motan ta ya bita yana fadin "Bestie please understand me mana, ko bakomai we have been best friend and we still are, we can't ruin it"

Ba ta ko kalle shi ba tace "to kaji nace wani abu ne?" Tun kan ya bata amsa ta fisgi motan ta in a very high speed ta bar gidan. Ita kanta ba ta da direct inda zata, kawai tafiya tayi tayi har ta kusa barin cikin garin Abujan sannan ta samu wuri gefen titi tayi parking, kife kanta tayi akan sitiyari tana fidda numfashi da sauri da sauri tana jin kaman kirjin nata zai fito. Hannu ta kai idanun ta, ita kanta tayi mamakin rashin ganin ko dikon hawaye. Folding lips inta tayi, jin yanda zuciyan nata ke mata wani irin zafi da ta kasa misalta shi ma. Har yanzu zuciyan ta kokontan maganan Zayd take yi kuma ba ta ganin har abada za ta iya yarda da batun nashi.


Daga wurin aiki take, she is so eager take ta fara bashi lbrn her first day at work. Mahaifin ta ya sama mata aiki a port authority, she is looking forward a amince mata transfer Lagos saboda tafi jin dadin sakewa da Zayd in a can. But now bata jin an ma zuciyan ta adalci in aka ce it broken because her heart is crush, shattered and beyond repair. Har yanzu ta kasa gasgata inda rayuwan ta ke shirin dosa ma tukun. Kara tada motan tayi a sittin ta dau hanyan gidan su, she just want to be home that a lokacin ji take in har ga ta kara sa ba zata iya shidewa.


Cikin yan mintuna ta isa gidan nasu. Ni ko tunda mu ka rabu da Zayd in na yiyo gidan daman. Muna zaune tare da mum a falon ta tana ta ban lbr, wanda ya shafe ni da ma wanda kwata kwata banda Alaska dashi. A wannan lokacin Amal ta shigo a firgice, ba ta ma lura da ni a falon ma ta fada cikin mum tana fadin "Mum am gone, rayuwata ta kare" ba kula ta ke yi sai sai yanda ta ke maganan muryan ta na sarke za ka gane tana cikin tsanin bala'i da har hankalin ta ke neaman gushewa daga jikin ta. Ta ban tausayi a wannan lokacin daga ita har mahaifiyar ta da duk ta rude tana tmbyn ta me ke faruwa. To da yake nasan irin soyayyan da mum kewa yaran ta, makahon soyayya ne da ba ta gani gaba balle kuma bayan ta. Hakan yasa ban yi wani mamaki ba ganin yanda jikin ta ke rawa har tana neman faduwa sai da na kira ta tukunna ta iya zama. "Amal fada min mana me ke damun ki Wai?" Ta kara tmbyn Amal da zuwa yanzu wasu zafafan hawaye su ka fara ambaliya a idanun ta, kaman ta shide. Sun bani tausayi matuka a lokacin har ji nake zan iya janye dukkan kuddirin da na dauka a can baya. They were so happy kafin na shigo rayuwan su, kasa zama nayi a wurin nayi saurin barin falon, nasan yin haka shine mafi a'ala in ba haka ba zuciya ta zata karaya. Duk kan abinda na dade ina yi kuma ya fadi a banza. Anty Umaymah ta min abinda kwatankwatan shi ba su gwada yi min ba ma, she deserves all my sacrifice ko da kuwa a hanya bata ne.

Abu daya da na sani shine wa'adin zama na a gidan su Amal ya kare, in har ba yau to na tabbatar gobe dole zan bar ta. To da amin Koran kare yasa na fara hada kayana gabadaya wuri daya.

Tafi kama da wanda hankalin ta ya fara gushe wa lokacin da ta shigo dakin. Na kasa tantacewa tsakanin ba ta ganni bane a lokacin ko kuwa dai hana gaban ta ne. Fridge in da ke falon ta bude cikin sauri ta ke kwankwadan duk wani abun gushewar hankali da yazo gaban ta. Ganin yanda ta ke ta faman afkawa cikin ta abubuwa yasa nayi approaching inta, wani irin kallo ta min da idanun da su ka kada sosai gashin kanta kuwa har sun fara miikewa. Da sauri naja baya, nasan a yanayin ko kwalban da ke hannun ta zata iya fasa min a kai kuma ta kwana lafiya. Karshe ma da taga abun bai kai mata inda ta ke so ba, alluran ta dauko ta afkawa jikin ta. Komai kawai take yi wanda ta ke fatan zai gusan mata da extreme pain in da take ji, ba kuma tasan hanya banda wanda take bi a yanzu. So she did what she know best.


A wurin ta zube, na kuma san duk abinda zan yi kwakwal war ta ya mata nauyin da ba zai iya daukan ta a yanzu ba. Sai ya dawo nike cikin tashin hankalin a yanzu ba ita ba, farkon abinda zuciya na ya fara raya min a wannan lokacin shi ne in debi kwamatsai na in bar gidan amma Sam na kasa hakan. Tashi nayi ina sallah ina rokon Allah ya sassauta min lamarin nan, ni kai na nasan Sallan da na rike ne ya kaini e yanzu. Nayi kokarin daura Amal a kai sai dai ance karfe tun tana danye ake tankwara shi, takan kwatantawa dai ba laifi. Karatun Qur'ani kam ni kaina sai ayi satuttuka ban ba duk da haka sau dayawa na kan ce mata ta gwada karantawa in tana cikin gushin maimakon abinda take sha. Ta kuwa gwadan kuma taji dadin shi sai dai yanayin yanzu ya wuce karfin kulawan tunanin ta

da dukkan wani sanin ta.Ina nan cikin zulumi washegari har wurin azahar ba ta farka ba. Ko da naje gaishe da mum ta tmby ni Amal in, nace mata tana baccin har yanzu.


"Ta fadi abinda ya same ta a jiya?"  Sai lokacin na gane Amal ba ta fadawa mahaifiyar ta abinda ya faru ba a jiyan. Dan haka na dan sake. Amal fa har bayan Magreeb ba labarin ta, duk addu'an da na taba sani ba wanda ban jarraba ba amma ko motsin ba ta yi. Ko dana fadawa zayd ce min yayi "she overdose herself ki kwantar da hankalin za ta tashi"+


"Kwanciyar hankali fa kace zayd ina na gan shi? Why are you so selfish ne Wai?" Bala'i na fara mishi a wayan da har sai da ya firgita. "Kai wani irin mutum ne ina fada maka halin da mutum ke ciki kana irin... You know what, I just realize you are not the best person to talk to" ina fading haka na kashe wayan, tsoron kar yar mutane ta mutu da alhakina yasa na gudu cikin gidan na fadawa mum abinda ke faruwa. Ina jin yan matan da ke gidan na ta kananan maganganu akan menene nake damuwa? Ai ba sabon abu bane da Amal ta sha drugs. Ban bi ta Kansu na isa ga mum. Da gudun ta ta nufi side in namu, ganin Amal ya ruda mata tunanin. Da ihu ta fara kiran driver ya fito, ni da wasu daga cikin cousins in Amal in ne mika dauke ta izuwa mota.

Ihun da mum ke yi yasa driver ke ta speeding har zuwa the closest hospital daga gidan. Direct su ma A&E su ka wuce da ita. Ba dadewa likitocin su ka sanr zuciyan ta na neman buguwa za a shiga da ita operation zuciyan ta za iya buguwa anytime soon. Kai wannan ranar na ga tashin hankali, ya guilt da ke ta faman bibiyata. Zayd ma yazo asibitin a rude, sai dai ba wanda ke ta tashi. Mum ta tana ganin zayd tq cakume wuayn rigan shi tana fadin "Duk abinda ya fara da diyata you will be hold responsible zayd, kai koya mata duk wani abinda take in ba haka ba ina Amal ina irin wannan drugs in? In ba kai ke kawo mata ba" da kyar ake raba mum da zayd saboda Marin da tayi ta zuba mishi sai da yayan Amal in Salim ya shiga tsakanin su. It was a terrible day saboda haka mika kwana ni da mum bamu runtsa.

Ko da aka fito da ita daga operation bata farka ba dai amma likitocin sunce it successful. Da kyar aka twankwashi mum mu ka tafi gida. Sai dai da gidan da asibitin kaman abu data ne, don ni a ganina ma asibitin har yafi sauki, at least a nan za ka leka ta ka ganta.

Har safiya Amal kam ba ta farka ba, a takaice dai kwana biyu ba a San tana rayuwa ko mutuwa ba. Gata nan kawai a Raye numfashi ma sai da taimako ta ke shaka, it hurt to see someone in comatose barin ma shakuwa irin namu da Amal, a girl with such a pure heart. A ranar na fizgi mota da kaina na tafi wurin Anty Umaymah, a vows na same ta. Ban tsaya mun gaisa ba ma nace mata "Am done Anty Umaymah"

Da sauri ta zare glasses in da ke idanun ta. Girgiza kai tayi tace "no you can't baby"


Siririn tsaki naja nace "shin kin san irin halin da na ke shiga a duk lokacin da nake abinda zuciya ta bata so, ko kinsan zafin pretending to be nice with people when all you are doing is breaking them? Kin san zafin ganin wanda ya so ka a rayuwa ya baka dukkan yarda da amana a kwance cikin mawuyacin halin da kai kasa shi a ciki. Baki san zafin butulcewa ba" da kuka na karasa zancen nawa. Da sauri ta tashi daga seat in ta ta dan jawo ni jikin ta tana comforting ina, she is so caring in every situation.

With a very cool voice tace "now tell me meke faruwa?" Cikin sheshekar kuka na sanar mata halin da Amal ke ciki a halin yanzu.


"Suhaima kenan to ai butulcewa shine ki kyale ta da zayd yana cigaba da zurmata cikin rayuwan da ba zai taba bata ba."


"He loves her" na fada ina kallon sju'umin murmushin da ke kwance kan fuskan ta.


"He claim so sai dai ke ma yana sonki right? Ga kuma matar shi Aminatu. To ki fada min waye ke so a ciki, kar ki manta fa yana tare da Amal in tuntuni ya gani kuma yace yana so. Ko an gaya miki in yaga wata macen ma bazai so ta bane?"


"He is not bad as you say Anty Umaymah, ni fahimta da zayd mai kyau ce"


"Saboda bai shayar da ke guban da ya shayar dani ba? Da daya wa iri na? Suhaima we need to make a change, and you promise helping in it. So please kar ki rushe abinda muka dade da ginawa, it wasn't easy kema kin sani. Mema ya rage? Abun da ya riga da yazo karshe ma?"


"Amma dai kinsan in ta tashi we are over ko?"

"Ba ita mu ke bukata ba ai, target inmu na hannun ki" tana fadin haka murmushin da ke fuskan ta ya kau. "Alkawari na daukan wa kaina suhaima, sai naga karshen mutum irin zayd. Kinsan irin masifan da ya sani a ciki kuwa?" Kwafa tayi sannan tace "ke dai kawai ki cigaba da alkawarin da kika daukan min. One thing da zaki rike shine you are helping your friend, dole ko ba yanzu ba ta gane zayd bai da wani buri a kanta wanda ya wuce dakawar shi da ta dagawa, she need her for benefit purpose" sauraron ta kawai na ke, sai dai na riga da nasan ba tayi rayuwan da nayi da su ba da har take judgement in nan. He may needs her for benefit but definitely he feels sometimes for her. Akwai mutunci da sanin girman juna kari ma he always try hiding his dirty world from him.


A safiyan mu kayi magana da zayd, he look so pale and worried "za ta warke In sha Allah" a hankali nayi maganan, saboda kawai in dan saman masa da kwanciyar hankalin da na san yana bukata.

"Nasan zata farka Suhaima, matsalan sai shine is she ready to accept my reality? Ina son ki suhaima and I can't risk anything for that" hakanan na ke jin daukan maganan shi na min wani iri a kaina.


"Wai Zayd me ye sa kake sona? Is there something special that I don't know? Na dauka ma damuwan ka akan tuhuma da mum tamaka ne" cije lebe yayi ya fiddo idanun shi waje sosai "Batun mum komai zata ce ba zanga laifin ta na wlh Suhaima, na cancanci haka. Da bani a rayuwan Amal da rayuwan ta bai kai da irin wannan ba. Nasan da haka saboda ita in mutum ce wanda Sam na taji bata gani akan soyayya. Na shayar da ita soyayya ta kuma ta afka cikin shi tsundum ta yanda na ta ganin kowa sai ni. Nasan Amal tana sona but we are better of without each other. Iyayen mu basu taba supporting in mu ba"

Siririn dariya nayi wacce ba ta da kara, tunanin da ya fara zuwa min shine tunda bai san iyayen su ba san son tarayyan su ba sai yanzu? Abu daya dana fara fahimta wurin Zaid Al-mansur shine he is so selfish to an extreme.


"Baka ban amsa ta to ai ni"


"Suhaima, it just happen wlh ina sonki soyayyan da ya fita daban dana kowace mace dana taba tarayya da. Ina ganin ki nasan kece irin maccen da na dade ina burin samu, kinga yanzu da dama ta billo min ba na iya bari ya kwace min ba ai ko?" Daga haka mika var zancen.


Lokacin da Amal ta farka, ni kadai ce a asibitin don haka aka kira ni in ganta. Duk yanayin da ya sa ta sunan shi ta fara kira "Besty Besty" samun wurin zama nayi gefen ta har ta gama farfadowa sannan nace mata "Sannu frnd" kallon da ta min kaman na wacce ba ta taba gani ba, sai kuma na ga ta daga min kai.


"Ina mum take?" Cikin muryan ta da bai gama dawo wa dai dai ba tayi maganan.


"She will be on her way, nace mata kin farka" daganan zaman shiru muka yi sai likitocin da suka kara duba ta. Kwanan kusan uku a asibitin, wani hira dai bai shiga tsakanin mu kaman da amma kuma har yanzu ba wanda yayi ma wani magana akan zayd. Sau uku yana zuwa duba ta in ya daidai ci wanda mum bata nan ko kuma ya biyo Saleem su zo tare. Su inma dai ba wani magana su ke tsakanin su ba.


Ranar da aka sallame muka koma gida, kusan wurin mum muka wuni ni da ita said daga baya mu ka koma daki. Duk ta zama wani irin, na farko saboda tunanin zayd na biyun kuwa dalilin hana ta shan duk wani abu da ta ke sha a baya. Wanda ta ke dashi duk an zubar sannan kuma ba ta daman fita siyan wani. Ta sha roko na in nemo ta, har kusan kuka take min gabadaya duk sai ta zama kaman ba Amal in da na sani mai dakakkiyar zuciya ba.

"Suhaima, can you tell me what is happening?" Cikin sanyayar murya tayi maganan, naga kokarin ta matukar amma duk da sai na fuske nace "akan me kenan"


Tsaki taja sannan tace "Ba maganan wasa bane. Zayd tell me something about you, duk da na yarda da ke ba zaki ci amana ta na so tell me what exactly is happening?" Sai da na danyi Jim, domin duk zama na dasu komai sai nayi lissafi nake yin sa. "Yace min yana sona..."


"Ke kuma mai kika ce masa?" Katse min maganan tayi niko nayi murmushi kawai. Ina ganin anzo kaban da yakamata in mata taimakon da ta min komin kankantan shi. "Ba zan fada miki sai ki min alkawari za ki dauki shawaran da zan baki a yanzu"


Kaman ba ta fahimce ni ba ta Bini da kallon zai can tace "Ehmm hmm"


"Tun muna yaran a islamiyya ana koya mana tauhid. Kuma yarda da kaddara mai kyau da mar kyau yana days daga cikin shishikan Imani. A matsayin ka na musulmi mai addini ya kama ta a San ka da imani. Zan so kin san cewa ba fa komai mutum yake so yake samu a rayuwa ba. Me zai hana ki samawa zuciyan ki hutu ta hanyar kyautatawa Ubangiji da fawwala masa dukkan lamuranki"


Murmushi mai ciwo tayi, kana ganin shi kasan tana cin radadi "Suhaima kin san so kuwa? Kinsan illan shi kin kuma san ciwon rasa wanda kake so kuwa? I can't take it gsky" ni kam har ga Allah a lokacin ma dariya ta so bani, na dai fukse nace "Amal na san fiye da tunanin ki, kuma so ya shayar da ni guban da ko da wasa ba ki dandana ta ba kuma ban miki fatan kin dandanan har abada." Kallo na kawai take amma daga yanayin ta na gama gane ba ta gamsu da abinda na fada mata ba. Sharewa nayi dai na cigaba da cewa "Zan so ki gwada ko da kuwa na kwana biyu zuwa uku ne. Cikin kwanakin kiyi kokarin yin sallah a duk kan lokacin sa, a cikin duk sallan da kikayi ki roki Allah yaye miki musibun da kike ciki. Ki yawan ta abinda kika iya na daga cikin Qur'ani, sannan ki kwatanta yin azkar. In kiyi na kwana ukun nan sai guda hada rayuwar ki ta baya wanda kike daukan barasa da sauran su abun dauke ciwo da kuma sabon rayuwan da nake so ki gwada. Kar kiyi focusing akan jin dadin, ki duba dai yanayin natsuwa da za ki sama wa zuciyan ki"

"Ni ma fa ba son shan wannan abubuwan nake ba, I think na fada miki to amma tsaya tukkunna I thought you also drink" girgiza kai na nayi nace "No, it all fake am just pretending to keep off to your standard amma gsky ni ba abinda nake sha" ta danyi mamaki kafin aka bar zancen ya kau.


Tun daga lokacin kuwa in har zan tashi sallah ina tada ta tayi haka kuma duk lokacin da naga ta fara shiga yanayin damuwa musamman lokuttan da tsumin shaye shayen na ta ke tasowa, sai inyi saurin mika mata Qur'ani. Sau da dama tana kokarin sharewa amma sai in tunatar da ita abinda muka yi.


A ranar na ukun ne tace min "Wa'adin fa ya aika now can you tell me yanda kuka yi da Zayd?"


"Zan fada miki mana amma yanzu tell me yaya kike ji, akwai wani progress?"


"Tsakiya tsakiya, I like it saboda shi bai dauke min hankali ya hana ni sanin abinda duniya ke ciki even though am living with the pain"


"Kar ki damu a sannu za ki ji daidai. Shaye shayen nan fa Kar ki manta yanzu ma ance ya taba yayan ciki please try avoiding it komai zai faru"


"Nagode now tell me" dariya nayi sosai sannan nace "Kaman yanda na gaya miki Zayd yace yana sona, I try to make see reasons but he keeps insisting ta yanda har sai da ya samu wurin zama a zuciya ta" ido na kyar akan ta, seriously ban damu da duk wani abun da za ta min ba. Wani irin bala'i ne kuma ban gani ba? Ni da naga fadan boko haram ma.

Kallo na take tayi ba kakkauta wa ta ma NASA magana jikin ta ko har rawa yake "You are betraying suhaima ke dashi? My closest people" ban ce mata komai ba, har ta gama kallo na sai kuma ta dafe kai ta fada kan gado weakly tace "nikam na shiga uku"


Na San zaki yi Dana sanin shigowa rayuwanki da nayi Amal, but you will always matters to me. Zan bar gidan Ku tun kafin ki fada min in tafi kuma a yau ba sai goba ba sai dai kuma ba zan iya yiwa Mum sallama ba saboda ban tanaji amsoshin da zan bata ba. Kar ki dauki Sallah da karatun Qur'an in Dana daura ki a kai shima wani daga cikin yaudara na bane, ko daya, ba hanya mafi gsky da yafi wannan Amal. Kina zaune cikin gidan iyayen ki ta ko ina kina samun kulawa da gata sabanin bi hakan yasa na ke ganin nafi bukatan Zayd a tare dani, ina ji a jiki na watarana sai kin gods min na raba ki da nayi da Zayd. Na barki lfy, sai watarana" daga haka na jawo bags Ina Dana hada tun ranar da zayd ya fada mata muna tare dashi. Ba dai tace min komai kuma ba ta hana ni ba har na fita daga cikin gidan daman na Riga da na nemi uber.


Direct guest house in zayd in na nufa. Nawa kaina masauki a days daga cikin dakunan gidan. Kwana na biyu a gidan bamu hadu ba kuma ina zuwa aiki muna haduwa sai dai ban fada mishi ba. Sai ranar kwatsam tashi, da farko yayi mamakin gani ba daga baya kuma yayi replacing mamakin da farin cikin.


"Kin dawo nan ne?"


"Wa nake dashi a garin Abuja bayan Amal?" Da sauri yace "ni mana amma wait ya kuka yi da ita? Ko na kira ta ma bata dagawa" hararan shi nayi nace "Dan Allah ka kyale ta kar rainin hankalin yayi yawa" dariya kawai yayi yace "bakin sani bane dole in shirya da Amal, I need her"


Tabe bani nayi nace "then marry her" rufe baki yayi yana fadin "lallai yarinya ba ruwa na wato kishiya kike wa kanki tun kafin ki shiga ko?" Kai namiji bai da Kunya wlh, hankalin Zayd a kwance mu ka cigaba da zama a wannan gidan. Bai taba nema na kuma da wani abu ba, kaman yanda ya saba hugging ina sai kuma randa tazo mishi he likes kissing me. Ban yarda zayd na so na da gaske ba sai da ya fara min maganan zuwa Maiduguri ina Jan janyewa ba. A lokacin naje wurin faree'ah da ta zo garin na labarta mata, Jana tayi gidan Anty Umayamah mu ka labarta abinda ke faruwa.


"Baki da matsala ai, zan tura Faree ta min aiki akai then you can go" da full confidence inta ta fadi hakan. Ban yi mamaki ba sai bayan kwana biyu da ta kira ni inje in same ta. Daga Office na wuce, kuma duk lokacin nan ina lura da yanad Faroukh ke yawan sa min ido, hakanan zai drink shop ya zauna in bai da ai kin yi. Ni akwai sands kiri kiri na ganshi yana bin bayana a mota daga baya kuma ya bace min. There is more da faroukh bai fada maka ba" jin Barr bai fada mata komai ba yasa ta cigaba.


Tare mukaje Maiduguri, unguwan da ban taba zuwa ba duk zamana a Maiduguri Anty Umaymah ta sa naje. Da tmby muka karasa domin nace mishi unguwan ya canja saboda anyi kone kone dayawa. Da muka karasa gidan da zamu ko, kurmus yake ba kowa a ciki ginin har ya taba fadowa. Ina mishi bayanin karya na yanda aka kona gidan namu be sai ga wani babban mutum yazo da sunan shi makocin mu ne a da. Nima ko nace na gane shi, aka yi ta koke kike sannan na tmby shi yan gidanmu yace har yanzu ba wanda ya samu labari akai. Na ko ci kuka na wanda duk na rayuwa ta nake ma wa da gasken. Da zamu tafi Zayd ya ma mutumin nan alkhairi sosai sannan ya amshi numban shi da sunan ko an samu wani lbr.


"Ba Ku da wasu yan uwane da zaki iya kaini gidan su Suhaima?" Girgiza kai kawai nayi shi ko ganin halin da nake ciki na kuka ya sa ya kyale ni.


"Na so mu tsaya Damaturu wurin kanwar mum inta sai dai ita ce mahaifiyar Mata kar a samu matsala" daga mishi kai kawai nayi amma a batun gsky naji gaba na na faduwa. I mean Damaturun da na sani ada dai kowa yasan kowa.


"Ni ko ba ka cika min maganar ta ba" dariya yayi yace "her story isn't so nice" dai taga banji dadi bane yace min "Okay, but don't judge me. We were so young, mun yi soyayyan da bamu san wani abu mai kirki ba bayan shi a lokacin. Muna ma tare da Amal time in but as my best friend. Lokacin da muka fara dating da Amal kuma da na so barin ta sai aka ki zancen, she is the reason aka hana ni auren Amal da farko. And the worst happen, we were so tempted to each other lokacin, I mean temptation as in sexual ways. To cut the story short, Dad ya ganni da ita a dakina and we are in a very intimate way. Shi ya yanke hukunci duk da mum bata so hakan ba, saboda tasan at young age but Amina is into girls, ta taba kama su da kannen  na mata suna kanana ana tunanin canja kaman sisters in nawa. She is still lnto girls though, kuma ta san nasani amma na yi alkawarin bazan rabu da ita saboda tasan affairs ina and she didn't care"

What a mess! Na fada a raina sai dai kuma a dan labarin da ya bani na gane wacece Amina. Nainah ce, my school mother kuma ita ce ta farko da ta fara bude min idanu a rayuwa. Now, the game will be more interesting.Haka dai na cigaba da zama da Zayd, kullum ya na kara narkar dani cikin salo salo na soyayyan sa duk da ban kai min ko ina, ga kuma wani irin tausayina da yake yi tunda mu kaje maid. Gsky na jinjinawa Anty Umaymah da wannan dabaran.

Ban taba gwada kiran Amal ba tunda na bar gidan su balle kuma in san halin da ta ke ciki. Haka Zayd shi ma duk yabi ya damu ba ta daga wayan shi gashi yanzu bai iya zuwa gidan su saboda tun kwanciyar Amal in a asibiti saleem ya ja baya dashi. Dama dai ba wasu abokanai bane sosai.

+


One obstacle da na kara samu shine oga hafeez. Clearly zayd yace mishi we are dating amma ya ki bari na In sake. Saboda shi zayd ya zuva securities a gidan shi na asokoro ba mai shiga sai da izinin shi. Duk da lokaci zuwa lokaci yana zuwa da mutane daga ma'aikatan mu.


Kwatsam! Wata rana sai muka tashi da munmunar labarin da yabi ya karade garin Abuja baki daya. The only daughter of the famous tycoon, idris hayatudden have attempt suicide. Ko ina ka keta a garin Abuja labarin da ke ta faman tashi kenan. Ina office na gani, a kidime na fita na samu zayd. A hanya mu ka hadu dashi kuma shima zancen ya jiyo. Direct gidan su muka nufa, daga ni har Zayd ba wanda ya iya tuki so El-yas ya kai mu. Abun daure kai ga dai mutane a gidan ga yan media, tension everywhere amma an kasa sanin mutum daya daya san wani asibiti su ka nufa.


"Ke kuma mai ya kawo rasa kunya, after snatching her boyfriend making her to attempt suicide kuma ba kunya kin kwasa jiki duba ta kiyi farin ciki ko?" Wani daga cikin cousin inta namiji ya fada. Ban tanka shi ba haka ma zayd. Karshe ma da muka ga zaman ba amfani zayd ya jani muka wuce. Ranar wuni muka yi neman asibiti amma ba labarin, duk wani connection da Zayd ya san yana dashi sai da aka nema amma ba labarin ta. Ni kuka shi kuka haka muka yi jigum jigum. The worst ba wanda zai ba ka lbrn ga exact abinda ta yi, daga wannan yace daga stairs ta fado sai wanda zai ce Aa poison ta sha. Ba dai mum kuma ba mahaifin ta. Saleem ko zayd ya sha rokon shi ya fada mishi inda Amal take, wanke shi ya ke tas sannan ya kora shi.


To fa tun daga lokacin ne na dauke wa zayd wuta. Abun ya girgiza ni to an extreme da nake tunanin lokaci yayi da zan janye kaina daga kangi da na jefe kaina. Har office said na daina zuwa, saboda dalilin da ke kaini ya kare.


Faree na fara fada ma wa ta min tas tun a waya kafin ta tako har inda nake ta wanke ni. Ni ko na fada mata  ne tunda ni ita na fara kuma ita ta hada ni da Anty Umaymah tunda amma no longer in ai sai a kyale ni "Ba ki san me kike ba Suhaima, yaza ki karya mana burin mu? It can be possible" kiri kiri na nuna mata bazan yi ba. Nan fa ta fara threatening ina ta waya da duk hanyan da ta samu. The worst har da life ina said da tayi threatening ina.


Ganin abunda ya zama, gashi kuma ba daman in iya fada ma zayd ya sa na taka kafa office in Anty Umaymah na sanar mata ban yi. Shiru tayi da farko, jikin ta kam yayi sanyi. "Buri na Suhaima shine in saka ma Zayd cutan da yayi sanadiyyan samun duk da nasan shi bai da ita. The plan is in debi jini na in baki ki sa masa ya gauraya da nasa bayan an mai alluran bacci. Bayan nan kuma yaji ciwo da zafin yaudara daga masoyin da kaso tsakani da Allah. Sai dai cikin yan kwanakin nayi realizing a zamanin nan cutar HIV ba wani abu bane da ake daga wuya akan shi ko in har mutum na dashi ya kasa zaune tsaye. Yanzu dai dube ni in ba Ku in ba waya san ina dashi? Ina living healthy life in da masu lafiyan ma ba su ganta ba. Na godewa Allah bai dubi halin da na zabawa rayuwata ba ya daukaka ni. Sannan a kullum yakin neman fansa banda durkusa ni da fama min miki be abinda ya ke. Ko na ma zayd abinda nayi niyya ba zan warke ba haka kuma ba zai ji abinda ni naji ba. I will focus entirely on my carrier yaje shi da Allah" tana fadin haka ta debo magudan kudi ta bani, ban yi musu ba na amsa na turawa Zeena kaman yanda nake tura mata duk wani kudade dana samu ta hanyan zayd ko Amal. Sannan kuma ga wasu makudan kudin da na samu can baya da nake gidan karuwan wanda za kaji a labarin rayuwata tun daga farko. To wadannan kudaden ne na tara har su ka kai yawan yanda su ke a wurin zeenah, na san you will want to know. Shi dai barrister bai ce komai ba ya kosa ta kai inda ya ke so.


Bayan maganan mu da Anty Umaymah nagane matsalan daga wurin Faree take. Ni daman tunda na gane Nainah ce matar Zayd nasan da akwai dalilin Faree na hada ni da Umaymah, shima duk zaka ji in na faro maka labarina kaman yanda nace ma. Na san yanzu you have doubts kala kala a kaina.


To fa daganan ne damuwa ta tarun ma zayd yake tunanin akwai matsala babba tsakanin mu, Wanda shi yayi sanadiyyan kiran ma'aikatan shi guest house in da shi da nake zaune meeting. They all help themselves in the kitchen, daman na fada maka su kan zo gida. Karshe dai shi da Faroukh aka bari suna magana, sun dade suna tattaunawa sannan su ka fita a tare. Ban kuma san meya faru ba daganan ya dai dawo yace min pls yana jin yunwa i should help him with something. Ni kuma na dafa mishi abinda zai bukata, yana cikin ci yana min hira ina amsa shi sama sama sai na lura ya fara sa hannu a kirjin shi. I can remember vividly sanda nake tmbyn shi "chest pain ne?" Yace min shi dai kawai ya ji kaman ana daure kirjin nashi ne, can kuma sai ya fara tari numfashin shi na dan sarkewa. Ganin haka nayi saurin kawo mishi ruwa, da ya sha har abun yayi sauki ya koma yana ajiyan numfashi. Kawai sai naga ya yunkura yayi kasa yana amayo abinda ke cikin shi. Iya rudewa na rude, na rasa ma mai zan mai Ina ta tmbyn shi "zayd lfy kuwa? Ko muje asibiti" daga haka kuma sai ya fara tari mai karfi, sai ga jini ta hancin shi da bakin shi na fita kaman wanda ake korowa. Suman tsaye nayi, nan da nan na rude na shiga daki da sauri ko gyale ban dauka ba sai key in mota dana gani ajiye kan side drawer. A firgice nake sosai, har ya zube a kasa ya jigata dayawa. Hawaye ko ta ina a fuskana na tashin hankalin da yazo min rana tsaka, inda gizo ke sakan kuma ba kasa daga zayd duk attempt ina, ina rokon shi ya tashi na ga idanun shi sun fara rufewa. Ganin haka ya sa da gudu na fita na nufi neighbors, da ke daman na fada maka estate ne ina kokarin kiran wani ya zo ya taimake ni. Ba wanda ya fito har tsawon mintuna hakan ya sa na kara komawa ina rokon zayd ya taimaka ya taso. A lokacin na manta da wani abu Wai shi waya nayi sai da ya fado min na nema sama ko kasa ma na rasa. Ganin yana kokarin rarrafawa ya fito duk da kasan jarumta ne kawai, Yasa na fita nayi saurin tada motan ta yanda da ya karaso ta wurin kofa, zan ida taimakon shi ya shiga. Ganin yana jigata yasa na nufa wurin shi domin in taimaka mishi mu karasa motan, sai dai ina zuwa bakin kofan naga wani irin haske da ban san shi sai kuma ya hade da kara. Ni dai Kawai gani abu nayi da har yau ban cewa ga yanda ya tashi. Ban kara sanin komai ba kuwa saboda wani irin jiri da ya jani ya bugar dani. Daga nan kuwa tashi nayi na tsinci kai na a asibiti, abinda na fara ji shine "Wai karuwan ba ta tashi bane? Na tabbatar ita ta jawo komai ya faru da zayd in"


Dayar ce tace mata "ke dai baki san meya faru ba tunda shi ya zayd in ya farka a na mishi treatment and Mum yanzu haka ta sa a fara shirin fita states dashi" daga nan ban kara jin komai ba har bayan yan mintuna sai kuma kara fitan su daga dakin. ina jin haka nasan da ma tazo min na ficewa Daga rayuwan su baki daaya ko ni ma na samu wani cigaba a tawa rayuwan. Da na bude idanu na tabbatar ina cikin asibitin ne, gashi har da drip a hannu na. Ban tsaya doguwar shawara ba na fisge drip in a hannu na, a hankali na lallaba na fita daga dakin zuwa wajen hospital in bayan NASA dogon hijab in da gani a dakin, hakan yasa ba a wani gane ni ba.


Sai da na fita na fara tunanin yanzu kuma ina zan nufa? Nasan dai ko giyar wake na sha ba zan nufa garin ba a haka, ko bayan hakan ma banda tabbacin ina yan uwana su ke. Kai tsaye na nufi drink shop domin yanda na ke jina dole in bar garin a ranar, kuma dole na bukatan yan kudade Dana tabbatar zan same su a office in. Na kudi a hannu na amma haka na tari taxi zuwa office in da niyyar in naje can in biya shi. A cikin taxi in ne ma hadu da wani kyakyawan saurayi mai kama da Amir, tsohon saurayi nane wanda rabo na dashi tun ina secondary school. Ni aka fara sauke wa dan haka na nemi alfarman driver in ya jira in dan shiga in dauko mishi kudaden shi.


"Muje kawai sauri nake zan biya kudin nata, I have to go Kaduna on time"


"Kaduna!" Na furta da karfi, hakan ya sa saurayin juyo yana kallo na "Kaduna zaka?" Tsintar kaina nayi da yi mishi tmbyn.


"Eh" ya amsa yana bina da kallon son sanin dalilin tmbyn nawa.


"Dan Allah to Yayana ko za ka dan jirani in dauko abu a cikin nan? Ba zan dade ba Nina kadunan zani" baki na kawai naji yana furta hakan. Sama sama naji saurayin na fadin "it okay, Hurry up please" har da gudu na karasa cikin shop in. Gateman in wurin kan shi yayi mamakin gani na, ban wani bashi attention ba nayi requiring key in office ina a wurin shi. Drawer kawai na bude na dauki yan canjin da na gani ban ko kulle ba na fita da dan sauri na, dan bansan wannan saurayin ya tafi ya barni.


A tasha taxi ya sauke mu, ya neman mana mota ba mu kai ko awa daya ba muka tashi. Na so saurayin nan ya bani dama in mishi tmby kan Amir saboda kaman su tayi yawa sai dai ko kala bai ce ba, sai karatun wani papers da ya sa a gaba har mu ka isa aka ajiye mu a tasha.


"Wani unguwa zaki?" Naji ya tmby ni, for some seconds rasa abince mai nayi, ni dai ban san Kaduna ba hasali ma yau na fara tsintar kai na a cikin shi.


"Unguwan rimi" hmm! Wlh ni kai na nayi mamakin tuno unguwa da Amir ya taba gaya min su ke a Kaduna.


Sake tmby na saurayin yayi da "Ta ina"


"Wurin Al-mannar" gabadaya kwatancen unguwan su Ameer in na mai. Ni fa duk a shirmen tunanina jira nake yace shima tanan yake muje, in yaso daganan sai in tmby shi ko yasan Ameer in, sai ya kira min shi muyi magana ko zan samu wani mafita. I realize am so crazy da naji yace "Oh bara in nema mana Bus, na ma driver bayanin in da zai ajiye ki ki samu motan Unguwan rimin.


Haka nan muka cigaba da tafiya, kaman in kurma ihu har muka iso wurin command a ka sha kwana aka cigaba da tafiya. Ban tabbatar da na kade ba sai da aka iso wurin wani barrack wai shi Kalapanzin barrack, nan naji saurayin yana ambaton a sauke shi a nan. Har ya fito ya juyo ya kalle ni sai naji yana cewa driver "Dan Allah ka sauke wannan wurin roundabout in constitution road a nuna mata inda za ta bi hanyan stadium ta hau motan unguwan rimi. bakuwa ce" Gabadaya ya biya kudin motan da NASA, ko godiya ban samu daman yi mishi ba ya wuce, sai lokacin na lura riga military ne a cikin shi wanda ban iya cancan ko na su wanene ba. Ban san yanda aka yi ya gane bakuwa ce ni ba duk da ban fada mishi ba.


Yanda ya fada haka drivern yayi, na mishi godiya na tsallaka titi na nufi hanyan da ya nuna min. Na dade tsaye wurin da tagumi a fuskata, Amal na tuna sannan na tuna yanzu haka ban san wani irin hali take ciki ba, rayuwa ne ko mutuwa? Nobody can tell for now. Nan fa naga wani irin hadari na hadewa sosai gari ya canja, kana ganin yanayin garin kasan ruwa na dab da saukowa. Nan fa naga motoci na ta rafkan gudu akan titin.


Dago tayi yana kallon barrister da jikin shi gabadaya ya gama sanyi "Abban Haydar kayi hakuri da abinda zan fada maka a yanzu" kallon tayi yana mamaki, ta gyada mishi kai sannan ta cigaba da cewa "Ji nayi na gaji da duniyan, ko mai da kowa ya juya min baya hakan yasa na yanke shawaran daukan hanuan da Amal ta yi. Sunkuyar da kai nayi da gan gan na nufi titin ko na samu na daina jin radadin da ke busa min cikin zuci. Daga nan kuma sai tsautsayin ya afka kan Matar ka"


Cocoon apartment

Seychelles


Hausa, origin of sokoto, gargajiya in both theme and outfit. Events: Traditional/kamu and Dinner.


Abinda ta samu daman rubutawa kenan a notepad inta bayan ta gama magana da new bride in da za tayi wa aiki rawan. She seems nice sai dai abinda Faroukh in ya gaya mata akan accent inta gsky ne. Gashi Arabic in ba wai irin wanda ta sani a Nigeria ana koyawa a islamiyoyi ba. Yeah, Rawan is crazy sosai ta dinga sa ta dariya a video call in. "I like ya from ya looks, so let ya be proud pls" yanda ta ke magana duk wani kalma sai abin shi hakkin shi. Ita dai yanzu she got a mission a gaban ta.


Ta wurin da Garden view in take clearly ta zauna tana yan rubuce rubucen ta. Gayyata na musamman faroukh in ya nata zuwa apartment in da ya sauka, she instantly like the place at first sight, the guy must have a very good taste. Sai dai kuma tana iso wa fita ya kama shi zuwa wurin wasu decorator da ya nemi gani. Hakuri ya bata sosai sannan ya sanar da ita she is free to everything in the apartment. Ba ta wani nuna damuwa ita ma, business first saboda haka Orange drink kawai ta saman ma kanta sannan su ka fara magana da Rawan. Already tayi magana da wadanda ta samu gani yan Nigeria in about the catering services and they were ready to tag in.


Samples in material ta fara dubawa tana tunanin wannan zai yi suiting Rawan in best? Sai kuma tayi tunanin ai traditional wear ta ke nema kuma na mutanen sokoto, ma'ana dai Hausa/Fulani kenan. Saki or atamfa? Deciding yin duka biyu tayi don haka nan da nan ta tura ma designer da tasan ba zata yi disappointing inta ba. Kafin dai Faroukh ya dawo ta gama duk wani abu da ya danganci outfit, har na dinner ta bada order.


She likes his composure, Faroukh machina kaman yanda ya sanar da ita sunan nashi ba dai natsuwa ba. Kai ita komai yayi ma birge ta kawai take and she is surprise a man affect her in that way. "Sorry fa na barki ke kadai" ya fara yana cire glasses in shi bayan ya shigo gidan, ruwa ya tsiyaya ya dan sha yayi da take bashi amsan "Kar ya damu ai tasan uzurin shi, ya meeting in kuma?


" we talk, he is willing to do it. Only that yace min ba kowani stuff da aka so za a samu ba" Satan kallon shi take yanayin yanda ya ke magana yana dan lumshe idanu alamun ya gaji.


"Ka nuna mishi sample in da na tura maka amma?"


"Yeah" kawai yace yana dan kwanciya jikin kujeran da ya ke zaune.


"Ai da kunyi magana kaga sai musan abinda ake bukata then we can get them together with the clothes" da sauri ya mike zaune yana kallon ta so deeply da dan murmushin da ya tsaya mai iya lebe "Girl you just... So... Wow!"


Dariya ta danyi, a kasan zuciyan ta ko ji tayi wani irin dadin complementing inta da yake. "We are in this together" ta fada tana dariyan kasa kasa.


"Amma kinsan at all tunanin nan bai zo min ba wlh, you are so amazing and creative" wannan karon kam bakin ta kin rufuwa yayi, sai faman blushing take.


"Amma asalin ki yar wani gari ce?"


"Borno"


"Oh Allah sarki kice ma mu makota ne ashe?" Yayi tmbyn yana mikewa "let go outside mana akwai barbecue in da ke going nasan you will like it" ita ma mikewan tayi suna tayi gefe da gefe, tana dan Satan kallon shi tace "Amma ba a Yobe ka zauna ba ko?" Juyawa yayi yana kallon ta "why do you say so"


"I mean your accent and all, ba kayi kama da wanda ya fito daga can" Turus yayi yana kallon ta, sannan ya girgiza kai "kuma daman Yan maidugurin nan kun raina mutane wlh, bansan mai kuka dauke mu yan Yobe ba"


Dariya kawai tayi su ka cigaba da tfy "Banana is from machina amma cikin Damaturu mu ke zaune, yanzu haka yan gidan mu a can su ke" da sauri tace "amma dai kai ba a can kake ba ko?" Zaro idanu yayi yana kallon ta "This woman da gaske dai kike ko? To a can na girma. University ya kaini Egypt, currently ma a can na aiki amma dai a Damaturu na girma"


"No wonder" ta fada, harara ya dan kai mata yace "My people are amazing whether you like it or not dai a can na girma infact ban enjoying Maiduguri at all saboda na kan danje a da can kafin in tafi Egypt"


"Ka dai fada ne kawai dan ka rama nasani" karasa wurin tables in su kayi suka zauna suna facing in juna. "Seriously, kun raina mu wlh. Which tribe are you though?"


"Babur and I know you are Kanuri" dariya kawai yayi, bayan an kawo musu abubuwan da su ka bukata. Daga nan suka koma hiran Yobe da Borno, duk dai kowa so yake yayi defending garin shi. "Kina taba zuwa Yobe ne?" Ya tmby yana tsare ta da idanuwan shi masu sata jin abinda ta dade da cire shi daga rayuwan ta, ita kam wannan bawan Allah ya matukar burge ta.


"Yeah amma fa na fi zuwa Gashua da Potiskum saboda akwai yan uwa na da su ke aure a garin ina ga Damaturu bai fi sau uku naje ba and ban wani dade ba"


"To ki cema ba ki wani san garin namu ba, ina kika yi karatu?"


"Unimaid" ta amsa tana kallon yanayin shi daya dan canja "I've got so many friends da suka gama a can nd a sister also"


"Eyyah, ai daman yawanci yan garin naku can suke zuwa sun san basu da irin shi" murmushi kawai yayi yace "I've been wondering mai yaja attention in ki wurin Event planning"


"People ask the question a lot. Kasan i just realize ina son sha'anin biki dayawa and lokacin da sister ta tayi aure we plan for everything then i know am totally in da ma na dade ina neman business in da ya dace dani"Yau ma kotun a cike ta ke taf, dan har ya kusan ninka zaman da aka yi na farko. Bayan Alkalin ba ya buga a fara sauraron kara, Barr Mustapha ya tashi kaman yanda aka bukata. Da takardu guda biyu a hannun shi ya fito kai tsaye ya mika wa magatakarda.+

"Ya mai mai girma mai shari'ah ina bukatan kotu ta bani daman gabatar ds wannan takarda a matsayin shaida na cewa wacce ake kara ba guduwa tayi kaman yanda lauyan gwamnati yayi ikirari" bayan alkali ya bashi dama ne ya cigaba da cewa "Ya mai girma mai shari'ah gobarar ta faru da ya ritsa da Zayd Almansur ya faru ne a ranar 31st watan july kaman yanda binciken mu ya nuna mana. Wannan takardan da ke hannu na kuma takarda shaidan rike Suhaima da aka yi a asibiti ne 1st August a sanadiyyan hadarin mota da ya gifta da ita a kaduna. A maganan da nayi da client ina, gigicewa ne ya sa ta barin asibitin da aka kai su bayan goboran nan har ta shigo motan Kaduna saboda rashin madafa bayan yan uwan Zayd sun tafi da nasu sun barta ita daya a wurin. Watan Kusan uku tana jinya a asibitin a sanadiyyan karaya da ta samu" nuna takarda yayi a matsayin shaidan record na asibiti "Ya mai girman mai shari'ah bayan ta warke ne ta zabi ta cigaba da zama a wurin wadanda su kayi jinyan ta a asibiti saboda rashin wani na ta a kusa, don haka malama Suhaima ba guduwa tayi ba illa ma nata jinyan tayi a asibiti." Amsan takardan Alkali yayi ya duba sannan ya jinjina kan shi alaman gamsuwa."


"Lauyan gwamnati kana da abince wa?" Girgiza kai yayi nan alkali ya sanar za a fara sauraron karan.


Lauyan gwamnati ne ya tashi sannan ya fara jawabi kaman haka "Ya mai girma mai shari'a in za a bani dama ina da gamsassun hujojin da zasu tabbatar da cewa wanda ake zarhi na da hannu dumu dumu a zargin da ake mata"


"Go ahead and present your witness" alkaline ya fadi hankalin shi na kan court in gabadaya.


"Da farko dai zan so in yi ma wacce ake zargi wasu yan tambayoyi" bayan kutun ta bashi dama ne ta koma sa Suhaiman fitowa gaban witness box, karasa wurin ta yayi yana kallon ta da murmushi dauke akan fuskan shi yace "Malama Suhaima right?" A hankali ta amsa shi. Yace "ko kinsan Zayd Al-mansur? Kuma waye a gare ki?"


"Saurayi nane" ta fada kai tsaye idon ta a kasan domin ba ta iya fuskantan mutanen da ke cikin court in ba.


Dariya prosecutor in yayi yace "Da kyau, Amal idriss Hayatudden fa?"


"Kawata ce" ta amsa a sanyaye, murmushin ya kara yi ganin yanda yarinyar ke bashi hadin kai cikin sauki.


"Da yawan mutanen da su ka san zayd su ka kuma san Amal sun san su a tare, ma'ana a matsayin saurayi da budurwan da su ka debi shekaru da dama suna tare, shin ko zaki iya fada ma kotu ya akayi kika dawo budurwan zayd in? Bayan kuma su in masoyan juna ne?"


Shiru kotun ya dauke, Suhaima kuwa idanun ta na kasa ta rasa ta inda za ta fara amsa wannan tmbyn. Kana ganin yanayin ta kuma kasan jikin ta yayi sanyi ta rasa bakin magana.


"Tou shknn tunda ba ki da amsan wannan amma za ki iya fada min mai ya faru ranar da gobara ta tashi a gidan zayd in" nan kaman tiryan tiryan ta bada labarin duk abinda ya faru.

"Nagode amma ko malama Suhaima za ta iya fada mana me ya zaunar da ita a gidan Al-mansur bayan kuma ba aure a tsakanin su kaman yanda addinin musulunci ya wajab ta"

Da sauri barrister mustapha ya tashi "objection my lord, lauyan gwamnati na kokarin sako addini a inda bai kamata"


"Sustain, Ka kiye lauyan gwamnati, this is not a shari'ah court" amsawa yayi cike da ladabi sannan ya juya gun Suhaima yace "ki cigaba da bamu labarin abinda ya faru a wannan rana har zuwa barin ki Abuja" labarin ta fada kaman yanda aka bukata.


"Wani dalili yasa ki barin asibitin bayan saurayin ki da kike ta kokarin ceto yana kwance baki san halin da yake ciki ba?"


"Ai na fada maka hiran da naji yan uwan shi nayi akan farkawan shi hakan yasa nima na kama gabana"

"In zan dubi labarin nan naki, kina so kice ke kika bawa Zayd abinci yaci kuma ya fara aman jini amma kuma kina so in yarda ba ke kika zuba mishi wani abu ba?"


"Wlh ban zuba mishi komai" ta yi saurin amsawa muryan ta na rawa, yanayin fuskan ta kuwa na cikin rikicewa. Kallon ta Barr Mustapha ya ke ta kokarin yi yana son aika mata tayi calming kanta coz her action is witness by the judge sai dai attention in Suhaiman gabadaya ya karkata gun lauyan gwamnati.


"To waya zuba" ba ta amsa shi ba sai girgiza kanta da tayi tana son tabbatar mishi ba ita tayi. "Am done questioning her my lord" rubutu alkalin yayi sannan ya dago ya kalli Mustapha. "Barr kana da abun cewa?"


"Ban dashi ya mai girma mai shari'a" Daganan lauyan gwamnati ya kara presenting next witness, Faroukh ne hankalin shi kwance ya karasa wurin witness box yana amsa tambayoyin lauyan. Gabadaya zargin da yake a kanta sai da ya fada da kuma abubuwan da ya gani da wanda kuma yaji da kunne shi.


Bayan lauyan gwamnati ya gama tambayoyin shi, kotun ta bukaci ko Barr Mustapha na da nashi tambayoyin. Amsawa yayi da Eh sannan ya mike a hankali ya taka zuwa witness box in da Faroukh ya ke a tsaye. Idanuwa su ka hada na da sakwanni sannan bare Mustapha ya juya kaman wanda bai ma taba ganin Faroukh in na yace "Faroukh, ka mana bayanin abin da ke tsakanin Suhaima da ogan ka Al-mansur gar ka ma kayi ikirarin cewa Cin amanar kawar ta tayi ko miye dalilin ka na fadin hakan?"

Dan tabe baki Faroukh yayi, ya juya kan shi daga kallon Uncle in nashi kafin yace "Ai a fili yake, they were even living together kuma ina jin da bakin ta ta fada cewa saurayin ta ne"


"Haka ne" Barr ya cigaba da magana "Amma ban tunanin hakan zai haka right cewa raba su da kawar ta tayi, in kawar ce tace ba ta son shi fa?" A nan Faroukh bai ce komai ba, sai tunanin da ya dan fara darsu a ranshi, is Uncle Musty going against him? Tabbas Suhaima evil ce.


"Faroukh kama kotu bayanin sau kusan hudu kana haduwa da Suhaima a lokacin da take kokarin aika ta rashin gskyn kaman yanda kake ikirari to amma ta ya kake tunanin hankali zai dauki cewa a dukkan lokuttan nan ba daya ba ba kuma biyu ba duka coincidence ne?" Sai da Faroukh ya daga kanshi sama sannan ya mai da attention in shi kan Barr "Ni dai kawai nafi yarda Allah ne ya zabe ni saboda ya tona mugun nufin ta"


"Kai dan baiwa ne kenan?" Yanayin da yayi maganan sai da ya girgiza Faroukh Baron ma da furucin ya sauka akan shi, lallai uncle musty is so serious akan case in nan. "Ni bance ba" dan dariya Barr in yayi yace "okay, to ko dai kai waliyyi ne in ba haka ba taya za ayi ce sau kusan hudu kana kama mutum yana aika ta sirrin da ya boye ma kowa? Ba fa kuma a wuraren aiki ka ke ganin ta ba, yawanci ma a waje ne." Nan ma dai Faroukh nai ce komai ba sai takaici da ta mamaye zuciyan shi yana mamakin duk yanda su ke da Uncle musty, duk yanda take girmama shi sai shine yake mishi haka a cikin jama'a kuma akan wata can bare.


"Ka fada min gsky laifin ka kafin binciken mu ya nemo min, You are stalking her ko?"


"Objection my lord" lauyan gwamnati ne ya fada. "Overruled" judge in ya amsa. Idanun Bare Mustapha akan abokin karawan shi, yayi murmushin kana ya juya wurin Faroukh. "Kana iya amsa tmbyn"


Da kyar Faroukh ya hado abinda zai ce "I have a life so i don't think ina da lokacin da zan ta bibiyan ta ta rayuwan bayan bani da wani gami da ita. Haduwan mu a vows El-yas na raka, sai next zasu fita da oga ni kuma naje bashi abu sai sanda naje daukan ta zan kai ta airport naji waya sai kuma randa mu ka hadu a blucabana, restaurant in kusa da apartment ina yake so I usually go there for my meals" jinjina kai Barr yayi. Sai lokacin ya maida idanuwan shi kan Suhaima da kanta ke duke a kasa. Mai da hankalin shi yayi kan Faroukh yace "Amma ya za ayi yarinyar da kake tsammanin tana da mugun nufi ka ganta a cikin gidan Ku tana zauna ba ka dau wani mataki ba? Bayan haka ma meya dauke ka tsawon lokaci kafin kayi reporting zuwa wurin yan sanda."


Kan Faroukh a kasa yace "I try talking to many of my family members, sai dai ba Wanda ya saurare ni saboda wannan yarinya mutum ce da matukar kwarewa wurin Nuna wata fuskan ta daban saboda Munafunci dake cike a ranta da kuma kudirinta"


"Ka gyara kalaman malam Faroukh, kotu za ta iya kama ka akan hakan" dago kai faroukh yayi ya dan juya gefe bai dai ce komai. "Nagode ranka shi dade iya tambayoyin da zan mishi kenan" bayan yan sakwanni Alkali ya bukaci ko lauyan gwamnati na da abince wa.

Mikewa yayi ya tako zuwa gaban alkalin. "Ya mai girma mai shari'a duba da irin bayanin da muka samu daga bakin Faroukh dama ita kanta wacce ake kara nake rokon kotu da ta kama mai laifi domin amsan hukunci da ya dace da ita as we do not need to waste time akan abinda ita kanta ta fada da bakin ta, ita ta bashi abincin sannan kuma ita kadai ne a gidan sai kuwa shi Al-mansur in, kuma a gaban ta yaci abincin ballantana ace wani ya shigo har ya sa mishi wani abun a ciki. Ina fatan kotu ta yi duba mai kyau wa jawabin da nayi"


Komawa yayi ya zauna kafin Barr Mustapha ya taso ya fara nashi jawabin kaman haka "Ya mai girma mai shari'a, kotu na bukatan tayi duba da idon fahimta akan wannan shaidan da aka bayar. Ba ta inda Faroukh ya fito yace yaji wacce ake zargi tayi wani magana akan kashe zayd Al-mansur illa ma sai wasu maganganu da yayi ikirarin yaji tana fada akan wani shiri wanda shi kanshi bai san na menene ba. Zan so kotu tayi watsi da wannan shaidan ba saboda ba ta is a gamsarwa  cewa wacce ake zargi ta aika ta laifin da ake zargi ta na. Da wannan na ke rokon wannan kotun ta daga wannan karam domin mu samu daman gabatar da kyawawan shaidun da za su tabbatar cewa wacce ake zargi ba ta aika ta abinda ale zarhin ta dashi ba, Nagode" komawa yayi ya zaune, bayan mintuna kadan alkali ya sanar cewa ya daga karan zuwa nan da wata biyu masu zuwa.


Tunda Did da Barr Mustapha su ka dauki Suhaima a cikin mota ba Wanda ya samu daman furta wani abu, tsit kawai kake ji sai ajiyan zuciyan da Suhaiman keyi lokaci zuwa lokaci. Ita kadai ce a baya a zaune yayin da ta daura kanta kan cinyoyin ta, gabadaya ta rasa gane wani tunanin ma ya kamata tayi.


"Where are we going?" Dr Fahad da ke tukin ya  tmby Barr Wanda bai amsa shi sai can kuma yace "are you planning on taking her somewhere ne?" Gabadaya sai yanzu su ke tunanin inda yakama ta su wuce da ita, abun ya sha musu kai ne ya kuma hade da basu samu ishashen lokacin sun zauna ba balls sun tattauna.


"Akwai gidan mu a nan, iyaye na na cikin garin ko mu kaita can?"


Nazari Barr ya danyi kafin yace "Ina ganin hakan fa ba mafita bane gsky, akwai apartment in da nake zama in na shigo aiki garin nan, ina ga mu kaita can"


"Its not risky kuwa? Ita kadai fa"


"No zan kira zeenah sai ta zo su zauna" daga haka ba Wanda ya kara magana har su ka is a apartment in da Barr in yake. Sannan su ka fita suka siyo mata dan abubuwan da za ta bukata har da kayan sawa ma. Sai daga baya Barr ya kira zeenah su kayi magana, ta amince zata zo but they needs to compensate her with something.


Seychelles


Din dirin din din din, ga  Amarya ga Ango. Abinda kawai kake jin yana tashi kenan a cikin da ake gabatar da kamun Adam da Amarya sa Rawan. Rashin samun masu busan algaita da kidan kwaryan ne yasa su ka nemi dai dai irin kidan aka sa shi a speaker. Wurin ko ya sha ado da kwarya kala kala manya da kanana da kuma ludayi su ma daban daban sai kilisai da kumbo da aka zuba zuba su ka matukar bada ma'ana. Kujerun wurin ko duk abin an musu kwalliya da tsintsiya na laushi da na kwakwa akai wadan su kuma turmi da tabarya aka sa saboda ya bada tambarin arewa. Akan kowani table akwai side plates da aka sa sa aya mai suga, tuwon madara, iloka, gullisuwa sai kwakumeti. Abun ba zai kara kayatar da kai ba sai kaga ana wuce da cups in zobo, ginger da kunun aya, duk anyi infusing insu da haddadun natural flavours sai kuma goruna fura da nono. Shigowan Amarya kuwa kida saurata na musamman aka sa mata, tana sanye da simple fitted gown na atamfa, plain alkyabba ke kanshi Wanda aka mishi kwalliya silver stones sai ta kasa aka sa patterns in jikin atamfan. Kanta a rufe da hulan alkyabban tana kallon kasa aka haka ta shiga filin zuwa seat inta, kawayen ta da su ma su kayi ankon wani atamfa da yayi matching da outfit in amaryan su na take mata baya har ta zauna su ma suka nemi seat insu. Abun ya kayatar da larabawan sosai, su dai ba so taba ganin irin haka ba balle ma wadanda su ka sa atamfan da basu taba sawa ba. Mc in dai da harshen turanci ya gabatar saboda sanin ba kowa zai fahimci shi ba in yayi Hausa. Kaman a garin sokoto haka yan uwan ango mata su ka feshe Amarya da sanyayyan turare sannan su ka bude mata fuska. Ji kake buda na tashi, ayiriririri ayiririri, banbancin dai kawai wannan speaker ne keyi maimakon mutane. Hotuna aka dinga yi, banda murmushi ba abinda Amaryan nan keyi ganin yawan dagaske ga burin ta na cika, sai rungume kawayen ta take da yan uwan tana farin ciki. Barin ma da aka bide wurin da wakar Hausa na ado gwanja da Naziru sarkin waka. Har kwalla farin ciki ta dinga yi, ana haka aka fara raba abinci lokacin kuma aka samu daman dauke Amarya domin samun daman canja yanayin shigan ta. Abincin da aka dinga rabawa kuwa Waina ne da snacks su samosa, meat pie, spring rolls da sauran su dai aka hada da gashashen naman shanu da na kaza.


Can aka umurci dukkan mutanen wurin su tashi domin shigowan Amarya wannan karon tare da angon ta. Kayatan kuwa A shape gown na saki in navy blue and silver, an mata dauri da silver headtie sai kuwa mayafin kayan da ta ya fa akai to shi ma dai angon ba a barshi a baya ba domin kuwa manya kaya ya sa navy blue ya kuwa sha banban rigan da ya dau aiki. "Wow! Wow! Culture is everything" abinda kawai kake ji yana tashi a wurin kenan wakan aljita na tashi na duba rana da wata suna da haske, har dai su kaje suka zauan. Daganan yan uwan ango su ka zo kaman yanda al'adar su take su wanke mata kafa da hannu da fresh madaran shanu, ba su gama mamaki ba su kaji wakan hausan da ya karade da sunayen su ana ta faman musu kirari. All through the event Umaymah ba ta zauna ba ita da Wanda su ka taya ta aiki said zagaya su ke don tabbatar da komai ya tafi yanda su ka shirya. Murmushi kuwa kin barin fuskan ta yayi ganin abun na tafiya yanda ta ke buri. A haka su ka hadu da Faroukh machina da ya sha jamfan shi fari sal, shima sai washe hakora yake yi da camera kuwa a hannun shi yana duba hotunan da yayi capturing so far.


"You look stressful" ita ta fara magana, yayi dan dariya hakora shi su ka fito kafin yace "it wort ai, it working and see you talking about me when you look exhausted" ita ma dariyan ta yi tace "to ni ai na saba, this my job" da annashuwa ta ke magana, sai ya debi mintuna yana kallon ta sosai har sai da ta gaji tayi gyaran murya, yayi saurin Sosa gefen "God! You are just awesome!" Muryan da yayi maganan dashi ne ya samu effect akan ta, dan sai da ta danyi still kafin tace "And you are superb!" Share zancen yayi "Kinyi kokari fa sosai ko a Nigeria ba a cika yin events yayi kyan haka ba, you are so wonderful, I like people who know their job"


"Thanks" ta amsa da farin ciki sosai ta kalli camera in "can i be a spoiler? I wanna see some pictures"


"You are so welcome then" camera in ya kara kunnawa, bai mika mata said maza da yayi daf da ita sosai ya fara scrolling pictures in. She likes them, irin sosai in nan, talking about people that know their job, he is also an epitome. Ba fuskokin mutane kawai ya daukan ba, Aa har da feelings in da ke kwance kan fuskan da kuma nature in gari. "I love the pictures, hope da su za a musu album in bikin ko?"


"Sosai ma kuwa" ya amsa, har yanzu dai GAF su ke da juna, sai ya zamo ba hotunan kawai su ke kallo ba, Aa har da suakan numfashin junan su da su ke ji. Ita kam ji ta ke kan ta na nema kuncewa, it been long ta bar kanta jin hakan akan wani da Namiji but now zuciyan ta har wani bugawa yake da sauri da sauri.

Post a Comment for "LABARIN RAYUWATA CHAPTER 5 BY Ayeshay bee"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...