LABARIN RAYUWATA CHAPTER 3 BY Ayeshay bee - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

LABARIN RAYUWATA CHAPTER 3 BY Ayeshay bee

LABARIN RAYUWATA CHAPTER 3 BY Ayeshay bee

- - Post a Comment

LABARIN RAYUWATA CHAPTER 3 BY Ayeshay bee


                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kwakyawar doguwar farar yarinya da ba zata wuce shekara goma ba na hango, Zaune ta ke gaban famfon gidan su tana Yar wakar ta hade da yin wanke wanken da ke gaban ta Wanda ba wai a son ranta ta ke ba an dai Fi karfin tane ya sa ba yanda ta iya, kwanukan ma dirzan dole ta ke musu duk basu fita. A Haka Mustapha ya yi sallama a kofan gidan har ya shiga ba ta amsa ba. "Ke baki ji ana sallama bane?"+


"To ni Ina ruwana da Kai da zan amsa ba gun Mama kazo" ta fada tana cigaba da wanke wanke kaman ta fashe.


"Kinga ko da ba ki min rashin kunya ba da na taya ki wanke wanken" da sauri ta taso har da durkusawa. "Lah ya Musty Dan Allah kayi hakuri kaga fa wasa nake maka Allah, Amin wa'alaika Salam Yayana na kaina" ta fada tana washe baki ita ala dole yaudara ta ke. Dariya ya dinga kwashe wa dashi har da rike ciki "an ki wayon yarinya baran yi ba"


"Ya Musty Allah daga yau Zan dinga maka biyayya kaga ma fa nace Zan maka zaman dakin in kayi aure" murmushi ya saki sosai "Ashe ko za ki garu yarinya, ba ma Zan dauko Yar aiki ba,


Yanzu dai dube ni na ci kwalliya ta kice in Miki wanke wanke?" Wannan karon turo bakin ta yi kaman za ta saki kuka "toh ba Kai kace za ka Taya ni ba"


"Zan Taya ki sai ran da baki min rashin kunya ba Kinga dai yanzu sauri na ke in Kai wa Mama sako in tafi tadi Kar Mata ta tayi ta jira na"


"Maryam Maryam yanzu har yanzu ba ki gama wanke wanken ba ko ki Zo ki tafi makaranta tsabagen rashin ji ko za ki Zo ki same ni"


"Mama fa na kusan gamawa"


"Ai Naga alama" ta fito tana fada, komawa tayi ta cigaba da wanke wanken shi ko Mustapha  durkusawa yayi ya gaida mama sannan ya bata sakon da Babban Dan nata ya aiko dashi wato Abbah. "To Mustapha an gode ko ka ce mishi an gode sosai Allah ya Kara budi yasu yayar ta ka da faruku"


"Suna lfy lau Mama sun mace zasu Zo Anjima"


"Allah ya kawo su lfy shigo Mana Mustapha"


"Aa mama akwai inda Zan karasa ne"


"A toh shknn sai anjima"


"Toh mama sai anjima Mimi in Zo in Taya kin" harara ta watso Mai shi ko ya dinga Mata dariya yana jin mama na fadin "kyaleta kayi tafiyan ka ni da ita ne yau a gidan Nan" sai da ya Mata gwalo kafin ya bar gidan sai da taci kukan ta sannan ta gama islamiyyan ma latti ta je bayan ta Sha duka gun Mama.


Ai ko ana tashi gun shi ta yiyo Yana zaune a dan karamin shagon da ya ke Zama Yana Saida abubuwan shi. Tun daga nesa ta hango wata budurwa a kofan shagon a tsaye ai ko da sauri ta karasa tana zuwa ko ta rike kugu. 

"Ya Musty dama wannan ce budurwar ta ko toh wlh ba ta da kyau" da mamaki ya bita da kallo sai dai kafin ma ya kwabe ta ta fadi kasa sai dariya ta ke ta yi, yarinyar da ta kumbura kaman ta fashe da ja dogon tsaki da karfi ya fara Mata magana "yi hakuri sadiya Zan aiki da roban tuwon Madaran da kudin anjima" dago ta yayi daga kasa ya matse Mata kunne Sannan ta saki Kara "Ya Musty daga fadan gsky"


"Me ya kawo ki wuri na"


"Tuwon Madara nazo Sha"


"Bayan ki zagi Mai yi ba Zan bada ba" turo baki tayi sai can Kuma ta ja tsaki "ba ma a so ai tunda nata ne" daga kafada yayi alaman ko a jikin shi sannan ta bar wurin tana Yar wakar ta.


Alh ... Shi ne mahaifin SU Mustapha da Anty, Yan asalin garin Kanon ne tun Kaka da kakanni. Zaman makotaka a unguwar Dorayi ya hada su da Su mama sai dai ba wai gidan su na jikin juna bane Aa. Asali su Mustapha ke zaune a layin kafin su Maman su dawo, tun ranar da Abba Usman ya fito ya ga Mustapha ya aike shi shago Kuma ya je ya dawo Yaron ya birge shi Lokacin Yana karami sosai, tun daga nan su ka fara shiri sai dai ba irin na abokantaka ba Saboda tazarar ba kadan bane har ya Kai dacewa Mustapha ya na da kwano a gidan mama sosai su kayi sabo dashi. Ta hakan ne gida je biyun su ka Saba har mama ta ma danta sha'awan Yayar Mustapha mace, ai ko ba musu ya amince Mata ya je su ka gana da Anty har su ka amince da juna, da ke da rabo a tsakani Nan da Nan  aka daura aure, a zagayowar shekaran Allah ya basu Faruk Nan Unguwa su ke zaune sai dai akwai Dan layika a tsakanin su. Shekarar da aka haifi maryam Allah ya wa mahaifin ta rasuwa hakan yayi sanadiyyan tashin su a layin Amma da ke suna son unguwan sai su ka nemi gida Nan kusa layi biyu ne a tsakanin su. Tsakanin Faroukh da Maryam duka duka wata hudu ne.


Dukkan su suna da yayyi Mata da maza sai dai suk sun Zo sunyi aure ya rage sai su biyu auta dalilin Shirin su kenan haka su ke suyi fada su shirya kowa sai ya tsokana Dan uwan shi.


Hakan ta kasance yau ta je gaida Umma kaman yanda su ke Kiran Mahaifiyar tasu ta iske shi da abokin shi bakin rijiya suna hira, ko Kallon su ba tayi ba ta wuce abinta ta shige wurin Umma, sun dan taba hira sannan ta tashi domin debowa Umman ruwa saboda mitan da ta keyi Mustapha ya tsaya bakin rijiya ya ki debo Mata ruwa.


"Keh me zakiyi a nan?" Ya hade rai Yana tambayan ta, Bazan tayi dashi ta karasa bakin rijiyan ta na deba Yana tsokanan ta shi da abokin shi suna dariya kala bata ce Mai ba sai da ta gama deban ruwan ta ta dauki bokitin sannan ta suka a hankali ta Sabi takalmin shi da ke kusa dashi ya cire tsabagen Hira, tsayawa yayi Yana Kallon ikon Allah Bai ankara ba sai gani yayi tayi cille dasu ta katanga Kuma bayan katangan su bola ne da ake cika datti a wurin da gudu Amma Ina da gudu ta je ta boye bayan umma sai da ta Ankara ya sa wani takalmin yasa wani takalmin ya fita sannan ta fito ta bar gidan da gudu maimakon ta je gida sai tayi gidan Anty. A tsakar gidan ta hadu da Faroukh Yana buga ball in shi da sauri ta yi joining in shi suna wasan, wani ihun da ta saki ne a sanadiyyan cin ball in da tayi ya fito da shi daga Falon, Yana fita kafin ta Ankara ya cafko ta ya ja kunnen ta wani Kara ta saki "Ban Kama ki ba yanzu? Ni za ki wullar wa takalmi?" Zuru zuru tayi da idanu alamun ba ta da gsky ba ta Ankara ba sai Jin saukan chaja tayi a bayan ta ai ko ihu ta saki tana Kiran Faroukh ya taimaka Mata. Banza yayi da ita daman Yana jin haushin mace ta ci shi kwalla. Anty ce ta fito Jin ihun yayi yawa, tana ganin Mustapha na faman Kara zuba Mata cajan. Harara ta sakan mishi yayi saurin sake ta "Kai yanzu Dan Allah ba kaji kunya ba Ka Kama gantamemiyar budurwa kana jibga?"


"Kai Anty duka duka fa 11 ta ke Ina ta Zama budurwa Kuma laifi ta min"


"Zo kayan ki Maryam ya Zo ya bige ki a hannu na in bai da kunya" da gudu ta karasa gun Anty ta shige jikin ta tana mishi gwalo "Kuma ma na fasa zaman dakin, Kuma in fada a gida Yan Mata kake tarawa a shagon ka" yunkurin da yayi zai kamo ta ne yasa tayi saurin shige cikin falon Anty, Antyn ko ta kullo kofan tana fadin "daga fadan gsky ai ta gani ne ta fada ko" gwafa yayi sannan ya bar gidan.


Tun daga ranar ya daina shiga harkan ta da ya ganta zai hade rai ko tana son mishi magana kasawa ta ke gashi ko wurin shagon shi ta nufa ba ta ganin fuska kullum Kuma sai ta hango Yan matan nashi biyu ko uku a bakin shagon. Gabadaya ba ta Jin dadin hakan saboda sun matukar sabawa da juna kullum tunanin hanyar da zasu shirya ta ke. Ai ko ranar tazo da solution, ana tashi islamiyya ta jawo kawayen ta Wai su Zo su je shagon yayanta Yana raba sweet ai ko deban jiki su kayi su ka bita ko da ta je Yan matan ta tarar su biyu rike da roban tuwon Madaran a hannun su "Ya Musty fa?" Tace musu Rai a hade "ya je ya dawo Abu zai amso" dayar ta Bata amsa.


"To muga roban naki zamu siya" yarinyar ta dauka abun arziki ne ta Mika Mata roban ai ko tana bude roban ta mikawa kawayen ta tace "ku zo kowa ta dauka Mana" ai ko sa hannu su kayi kafin kace kwabo sun sa Wawa roban karshe sai da ya fashe. Mai tuwon Madara sakin baki tayi tana Kallon ikon Allah, murguda Mata baki Maryam tayi "miye kike kallona za a biya ki abinki hadda roban kinsan mu ba matsiyata bane" wulla Mata roban tayi ganin Yaya mustyn na zuwa ta kwala ihu "Ya Musty kayi hakuri na maka sadaka ka biya malamin ya ce Yana da kyau" kasa fahimtan abinda ta fada yayi sai da ya karasa su ka fada mishi abinda ya faru da gudu ya bita sai dai kafin ya kamo ta tuni har ta Sha kwana. Gwafa yayi ya koma wurin ya basu hakuri sannan ya ce musu su Zo su amshi kudin su gobe.  Kala bai ce mata ba haka ya biya yaran kudin su Bai ba fadawa kowa ba, ita Kuma duk sai ta ji wani iri saboda tayi hakan ne da ya tanka ta at least ko fadan ya Mata yafi akan ya share ta sun Mai sati biyu a hakan daga karshe ta gaji tana dawo daga makaranta ta nufi gidansu. Sai da ta gaida Umma sannan ta tambaye ta Ya mustyn ta sanar Mata Yana daki, dawowan shi daga makaranta ta same shi yana bacci, a hankali ta shiga ta zaune Kan gado gefen shi tana Kallon shi, juye ya Zo ya ci karo da mutum da sauri ya bude idanuwan shi. "Ke lfy? Uban me ya kawo ki daki na?" Narai narai ta yi da Ido sannan ta sauka kasa ta durkusa "kaga fa wlh hakuri nazo ba Ka Kaga ma na kawo maka takalman Nan da kudin tuwon Madarar ka" kallo ya bita dashi ya ga takalman nashi ne kuwa sai kyalli su ke "Ina Kika samo su"


"Bolan na shiga fa na dauko tun washegarin da na wulla su na wanke na bada aka yi polishing, Kai Kuma kana hade min rai shiyasa ban kawo maka ba" daukan takalmin yayi da kyau tabbas su in ne kuwa sai sheki su ke da sauri ya dauko dayan, ba karamin son takalmin ya ke ba sabo ya siye su ba da dadewa ba. Smiling tayi sosai ta ce "am happy because you are ya musty sai kudin tuwon Madarar ka basu su siya roban su" kudin ya bi da kallo duk tarkace ne daga biyar sai goma Ashirin guda Daya ne gabadaya ba za su wuce hundred naira ba.


"Ki bar kudin ki na Riga na Basu"


"To ka hakura?" Girgiza Mata Kai yayi alaman Aa.


"Dan Allah fa nace"


"Ba dan Kinga Ina Wasa dake ba shiyasa Kika Raina ni?"


"Lah wa ya fada maka wlh Wasa nake ma Nima don Allah kayi hakuri" murmushi ya saki Mai kayatarwa "its okay tashi kije bacci na ke ji"


Hannu ta Mika mishi alamun sun shirya shi ma in maida Mata yayi tana dariya da tsalle ta bar dakin. Tun ranar ta daina mishi rashin kunya ko ya tsokano ta sai dai tayimurmushi in ko ya ga fushin ta to ta je shagon shi ta tadda Yan Mata ta dinga kumbure kumburen fuska kenan"


A kwana a tashi ba wuya gurin Allah kafin kace kwabo su Mimi an girma har an shiga SS3 lokacin shekaran ta Sha bakwai, in ka ganta ta natsu tayi hankali tsakanin ta da Mustapha ko in ta ganshi ta dukar da Kai kasa ta gaishe shi cike da kunya shi ko ya dinga tsokanan ta kenan, kala ba zata ce ba zata wuce, shagon shi yanzu ya bunkasa ya bude babba har yaron shago ma ga gare shi saboda makaranta bai cika Zama ba sai dai ya je ya dubo yanayin shagon ya dawo. Yana final year in shi a karatun law time in da ta ke SS3 in, in su na zaune a wuri ya dinga saton Kallon ta kenan farko abun daga mamakin ta ya fara sai da kafin ya Ankara ya fara Jin abubuwa a kanta, daga farko karyata Kan shi yayi Yana tunani abin Kila kawai mamakin nata ya ke. Dukko ranar da tayi abunci a gidaje ukun Nan yaji labari to sai ya je ci ba karamin iya girki tayi ba ya dinga ci Yana Santi Yana fadin ashe "Yar zaman dakin nawa zamu shirya da ita." Iyakan ta murmushi kawai in taso maganan tace "abinda har yanzu ka kasa Samo Matan ya musty"


Tun Yana ganin abun karami sai dai its getting worst by the days har ya zamo babba. Ranar ya je gidan ita Kuma ta fito za ta tafi su kayi kicibus a tsakar gida, gyale ne a jikin ta ta sa rigan atamfa da skirt ya zauna Mata cib cib, bai son sanda ya fara kare Mata kallo ba a zuciyan ya ayyana lallai mimin shi ta girma ta Zama budurwa. Saurin kauda Kai yayi sai a sannan ta gaishe shi kallon ta yayi Yana so ya amsa ya kasa, Kallon kallo su ka soma yi kowa da abinda ya ke ji a zuciyan shi, sauke Kai kasa ta yi da sauri lura da abinda suke  ta yi hanyan waje. Gam ta ji ya ruko hannun ta "Ina za kije Mimi?" He didn't have an ounce idea that Yana da kallan voice in Nan Kuma ma Wai Mimi ya ke ma wa "Gida" kawai ta bashi amsa coz they were all feeling the contact, cikin taushashiyar muryar ya Kara magana "okay ki jira ni in ba Anty sako sai nazo na raka ki ko?" Ba musu ta gyade Kai ta koma gefe. Nan da nan ya fito ya tadda ta tana jiran shi "muje Yan Mata" jiki a sanyaye ta taso gabadaya wani iri ta ke ji, she can feel it Gabadaya jikin ta rawa ya ke yi but she is trying to calm herself. "Wai shin me ke Shirin faruwa da sune?"


"Mimi na Yan Mata manya an girma" smiling ta kakalo kawai "Anya za ki ma iya zaman min dakin yanzu kuwa naga ke ma kin Kai auren yanzu Kam"

"Zani man ka dai yi auren"


"Soon Kar ki damu" gabadaya ji tayi wani iri ba ta ji Dadi ba Amma sai ta fuske. Ba Wanda ya Kara magana illa zuciyoyin su da ke ta kokawa da su har kofan gida ya Kai ta sannan yace "kasuwa Zan je me kike son na siyo Miki and ban son Jin Aa"


"To ka siyo ko menene"


"Kina son turare" nodding ka ta tayi sannan su kayi sallama ta shiga gida. Tayi mamakin turaren da ya kawo Mata, irin hadaddun Nan me Mai da set uku a cikin Babban kwali da spray da perfume daga gani zai yi tsada godiya kawai ta mishi ya girgiza Mata kai.


Haka suka kasance kullum cikin zulumi da tunanin abinda su ke ji game da junan su, in sun hadu Banda Satan Kallon juna ba abinda su ke yi, tsab Mustapha ya gane tana Jin abinda ya ke ji game da ita sai dai ita Bata gane nashin ba, na tan ma gani ta ke za ta daina.


Wata rana ne ana bikin Yar kanwar mama a cikin gari gabadayan su sun tafi sai ita data tsaya ta gyara gidan ta kulle kenan ta hango shi ya shigo gidan, jiki sanyaye ta gaishe shi Bai amsa ba sai ma Kara matsowa kusa da ita da yayi Yana kare Mata kallo,  fitted gown ke jikin ta na ankon ta Sha kyau abinta ta ci make up da ke ita ba gwanar yin bace ba karamin kyau ta yi ba. "Maryam" ya Kira sunan ta, wani iri taji cause its hardly kaji ya ce Mata Maryam kullum Mimi ya ke Kiran ta. A hankali ta amsa mishi "you know what? Am tired lets just talk and let everything out today" kallo ta bishi dashi feigning to be clueless .


"You have a clue na sani"


"Ya musty Bilkin mama hajjo na jira na fa a gidan su kaga tare zamu tafi Kuma Amaryar ma mu ta ke jira Kar mu bata Mata time" cikin natsuwa ta yi maganan sai dai he can notice it Gabadaya jikin ta rawa ya ke.


"Good kinga ki tsaya mu yi maganan mu Kar suyi ta jiran ki"


Shiru ya danyi sannan ya tsaya gaban ta four eyes su kayi sannan ta yi saurin sadda kanta kasa still Bai fasa Kallon fuskan ta ba ya cigaba da magana.


"Maryam kinga fa ba Zaki fita daga gidan Nan ba sai kin fada min abinda kike ji a kaina" dagowa ta yi za ta saci Kallon shi su kayi four eyes cike da kunya ta maida Kan kasa "eh nasan kin sani, you know my Feelings and yours why not mu yi accepting hakan kawai Ni dai na gaji and am confessing" gabadaya kin dago fuskan ta tayi ganin haka ya tsaya gaban ta sannan ya kalli agogo "kina musu wasting time fa" kaman za tayi kuka ta turo bakin ta "to Wai ni me kake son ji. "Your truth feelings kawai and Zan kyale ki" da mamaki ya ke bin ta dashi ganin idon ta ya ciko da hawaye, kaskanta murya yayi yace "haba Yar zaman daki Haka za ayi abun kina tsoro na kina min kuka? Ko kin fasa ne"


Muryar ta na rawa tace "To ai baka samo Matan ba" da sauri ya ce "wa ya gaya Miki? Na samo Maryam Kinga sai tayi zaman dakin ta da kanta"


"Kinji?" Still dai tayi duk ta kasa motsi.


"Kin amince?" Gayde kanta sama tayi cike da kunya ta rufe fuskan ta ta nufi kofa da gudu matsa Mata yayi Yana Mata dariya. Shi ya kulle gidan ya fita da key. Tun daga nan alaka Mai karfi ya shiga tsakanin su tun tana jin kunya har ta saki jiki dashi. In no time abin ya yiwu kowa ya sani, ji da ita kace kwai tamkar ya lashe ta komai ta ke so zai Mata ko kadan bai son baccin ranta. Ko da su Anty su ka koma Kaduna Abba ya dauke ta ya tafi da ita bayan ya samo wa Maman su abokan Zama Daman Umma Kam tana dasu. KASU ya sa ta bayan ta gama secondary sai ya zamo Mustaphan ma kullum Yana Kaduna. Tana final year aka daura auren su bayan ya je course waje ya dawo ya Zama cikakken lauya Mai zaman kanshi. Farkon auren su komai gwanin ban sha'awa kafin daga baya komai ya fara fading. Ya zamo ba ta Jin maganan kowa duk abinda ta ke so Haka za tayi Bata damu da gyaran gidan ta bama sai dai ta dauka Mai aiki daga baya ta shiga islamiyya daga Nan ta samu hanya yawo. Maimakon da ta haihu abun yayi sauki sai ma ya nunka na da. Shi wani lokacin barr ji yake kaman ba maryam in shi ba Mai gudun baccin ranshi, kaffa kaffa ta ke dashi Amma yanzu shi ne kadai Mai kokarin hakan. Ko Dan over soyayyan da ya nuna Mata ne? A fili ya ke nuna Bai son ganin laifin matar shi. Sai dai yanzu Kam tura ta Kai bango dole ya dau mataki ya Zama Namiji Mai fada a ji cikin gidan shi.Da Anisa, Anty da Suhaima su ka koma gidan Barr, dakin da Suhaima ke zaune Anty da Anisa su ka nufa a tare da ita. Anty tayi insisting dole Suhaima ta dawo nan gidan ta domin ba Yar bauta su ka samu ba Kuma tun an fara samun matsalan dole a kiyaye saboda gaba.+

Maryam dai gabadaya jikin ta yayi sanyi sai bin kowa da ido ta ke ta rike haydar a hannun ta, suna shiga gidan Barr ya nufi dakin Hadiza ya kife Mata Mari ta sa ihu, sai da Anty ta Zo ta sa baki ya kyaleta. Rantsuwa yayi sai ta bar mishi gidan shi tana kuka ta hau hada kayan ta. Daman ko Bai sallame ta ba Anty na da niyyan hakan saboda Abbah ya ce a bar Maryam ta zaune ita kadai ta zauna gyara gidan ta in zata iya.

Ba abin ta da su Anty su ka Bari a gidan komai su ka hada su kayi mota, suna waje Suhaima ta fito daga dakin, gata Nan ne dai kawai ba Wanda zai iya fayyace halin da ta ke ciki don ita kanta ba Wai ta sani bane. A falo ta iske Maryam na zaune Kai a kasa idon ta ya ciko da hawaye. Gefen ta ta zauna sannan ta mika Mata hannu, jiki a sanyaye Maryam in ta Mai da Mata "saduwar Alkhairi Maman haydar na gode sosai Ina fatan Zaki yafe min abinda na Miki Wanda na sani da Wanda ban sani ba"


Muryan ta na rawa ta fara magana "Ehm ehm Suhaima ni Zan baki hakuri akan abinda ya faru, ki yi hakuri pls"


"Ban Zan taba iya rike ki ba Maman haydar, kin min alkhairi a rayuwa ta sosai nake godiya, kwanan Ina tunanin tafiya ma bara naje Anty suna jira na" nodding Kai kawai Maryam ta yi gabadaya ji tayi tana regretting action inta, gashi Barr ko Kallon ta Bai sake ba balle Kuma ta San ran zai Mata magana. Tana ganin ya je book shelf in shi ya dauka littatafai, ko bai fada Mata ta San Suhaima zai ba Saboda ita ce ma'abociyar son karatu.Har Jin jikin motan ya je ya Mika Mata ta sa hannu ta karba hade da yin godiya, idanuwan Nan nashi sun kada sun yi ja, kallo Daya zaka mishi kasan he is hurt sosai, ita Kam Suhaima har wani tausayin ta ke ji. Anty dai ba ta kalle shi ba har ya koma cikin gidan nashi sannan ta ja mota su ka bar gidan.


Dakin Anisa Anty ta Mata masauki ba Wai don Basu da extra ba Aa, a ganin ta za tafi Jin Dadi zaman su biyu akan ace ita kadai ce.

Ko da Dr ya ji labarin komawan ta gidan Antyn, Bai nemi wani ba'asi ba don a tunanin tun farko ma Nan yakama ta ta zauna ba gidan yarinya kamarta ba dole a samu matsala.


Ko da aka fara events In bikin Dr Fahad da Rufaida, sau biyu ta je tare da rakiyar Anisa, faran faran Rufaida da Nabeela su ka Mata karaban hannu bi biyu, Dr kanshi ya ji dadin hakan sosai. Gabadaya he is busy ko da taje gidan bikin duka duka sau Daya ta ganshi shima gaisawa kawai su kayi abokan shi su ka Zo suka ja shi, sai dai ko in ya samu time ya kira ta a waya.


Ranar jumaa ana saukowa Daga Sallah aka daura auren Dr Fahad da Amaryar sa Rufaida hakan yayi dai dai da Lokacin saukan Faroukh daga UK, a Abuja jirgin su yayi landing so gidan su Abokin shi Zaid ya sauka sai da ya jira train in six na yamma sannan ya biyo zuwa Kaduna.


Suhaima da Anisa na shirya warmers Kan table su kaji ihun yaran gidan suna "oyoyo oyoyo ga Yaya Faroukh" Anisa murmushi kawai tayi dan ba wani dasawa su ke dashi ba, ya cika takura Mata komai tayi sai ya kwabeta, at times ji take kaman ya tsane ta ma. Sai da ya fara shiga dakin shi ya ajiye kayan shi sannan ya watsa ruwa. Direct Falon Abbah ya je sanin shi da Anty suna can, zuwa yayi ya gaida su kafin ya nufi wurin kannen nashi.


Suna zaune gabadayan su a Falon wasu na kallo wasu na assignment. Da gudu Kulsoom ta nufi wurin shi Aiko daga ta sama sannan ya ajiye ta, twins Kam sai murmushi su ke suka Mai sannu da zuwa, muhibba ko gefen shi ta koma ta zauna ya riko Mata hannu suna Hira. "Sannu da hanya Ya Faroukh" hararan ta sannan ya ce "ban so rike kayan ki" kala ba tace ba har ta gamawa Arif assignment da ta ke mishi sannan ta Mike ta nufi daki. Good five minutes ba tayi ba Kulsoom ta shigo dakin, Suhaima littafi ta ke karanta wa abinta. "Anty Anee ya Faroukh ki Kai mishi abincin daki" nodding kanta kawai tayi Amma kasan zuciyan ta mamakin takura Matan da Ya Faroukh in yayi ta ke duk da lokuttan da ya so Wasa ya Kan ja ta dashi. Dinning ta nufa ta hado abincin nashi ta nufi dakin.


Sallama tayi ya amsa Mata, waya ya keyi ga dukkan alamu Kuma da budurwar shi ce, ita dai ajiye abincin tayi ta yi gefe don ta San ko ta fita kwala Mata Kira zai. Ka ta hakura har ya gama wayan shi sannan ya juyo gare ta "Zuba min abinci Mana Anee Naga alaman ko murnar gani na ma baki yi right?" Ba abinda ta ce har ta gama zuba abincin ta Mike mishi, ga mamakin ta ko har da godiya ya Mata.


"Da gaske wancan yarinyar ta dawo gidan Nan?" Da mamaki ta kalle shi sannan ta ce "Ya Faroukh wa?"


"Ban sani ba yarinyar da ke gidan Uncle musty Mana"


"Wai Anty Suhaima tana Nan mana"


"Wani daki ta ke Zama?"


"Room Ina"


"You have to leave the room for her then" da mamaki ta dago Kai tana Kallon shi.


"Ko ma da yake bara na bi abin a hankali, Wlh ki kiyaye kanki da ita Kar kice Zaki dinga shishige Mata you never know who truly she is, tashi ki tafi" Bai Bata room in yin magana ba hakanan ta tashi ta Mike jiki a sanyaye.

Kwanan Faroukh biyar a gida Amma ko sau Daya ba su hadu da Faroukh ba sai ranar. Anty was so surprised da Suhaima ta fada Mata she is already a graduate of medicine, tayi tunanin enrolling to islamiyya sai dai Kuma Alhmdlh taji ta San addinin ta sosai, ga girki ma ta iya recipes kala kala and suddenly Anty become interested in knowing her story. Ranar tana tsaye a kitchen tana girki, Anty ta fita Anisa ma Kuma ta wuce computer school unknown to her Faroukh na gidan. Sai dai kawai ji tayi alamun mutum a bayan ta na Kallon ta, karfin halin juyowa Aiko su ka yi four eyes. Ganin yaki dauke idon shi cikin nata ya sa tayi saurin Mai da na ta kasa. "Sannu" kawai ta ce mishi ta juya ta cigaba da aikin ta. As she expected Bai amsa gaisuwan ba instead sai ya fara magana "Suhaima ba ki ji ko? I've warned you kin ki dauka" ganin ba tayi magana ba ya sa ya cigaba da nashi maganan "since ba ki dauki abinda na fada Miki ba let me tell this, am sorry but i have to expose you" cak ta tsaya sannan ta juyo ta kalle shi "I expect to did it soon Faroukh, I don't even understand me ye sa har yanzu ma ba ka dau action"


Tafa hannun shi yayi in an amazing way "Suhaima kenan wato ba Zaki taba canjawa ba Koh?"


Juyowa tayi Wannan karon tsab tana Kallon shi kaman yanda ya kura Mata idanu "a tunanin rashin wurin zuwa ne ya sa na ke zaune da ku F... ? As brave as you are ban yi zaton za kiyi wannan tunanin ba. Let me tell you F... Na tsaya ne saboda ayi ta ta kare, am tired of the game, enough is enough, na gaji hakanan saboda haka Ina Mai rokon ka Dan Allah Faroukh ka shigar da Karan Nan Haka Nan, in ma tausayi na kake ji please ka daina, don't you get it? Am tired of the whole world" ko kadan Faroukh bai yi mamakin kalma daya daga cikin zantukan ta ba because he expects it, sai dai bai tabbatar ba sai yanzu da ta furta da bakin ta.


"Kar ki damu, daman duniya ma ta gaji da mutane irin ki..." Jin da yayi kaman ana Kallon shi yasa yayi saurin juyowa four eyes yayi da Anisa ta kwalalo ido tana Kallon shi. "In ma kinji conversation inmu inji a bakin wani ki gani" ya fada tare da kwafa kafin ya bar wurin. Suhaima ta juya ta cigaba wa Kallon tsoro hade da mamaki, murmushin karfin hali ta kirkiro sannan ta ce "Anee kin dawo?" Nodding Kan ta kawai tayi kafin ta wuce daki.


Anisa kept giving them weird glances, sosai ta ja baya da shigewa Suhaima don gabadaya tsoron ta ma ta fara ji, ita kanta Suhaima ta lura da haka hakan ya sa tayi confronting in ta a daki. "Anee ki daina Jin tsoro na, I don't bite" girgiza Kan ta tayi sannan ta ce "Anty Suhaima me kike expecting Zan yi bayan ji abinda kuka tattaunawa ke da Ya Faroukh? Kin San shi ne Daman"


"I used to live in Abuja, a can na San shi"


Nodding Kan ta tayi alaman gamsuwa sannan ta ce "toh wani Abu ya shiga tsakanin ku ne"


"Kinga Anisa kwantar da hankalin ki ba abinda Zan Miki, you will know my story when the time is due."


Haka dai aka cigaba da rayuwa a gidan, Faroukh na can Yana kulla abinda shi kadai ya sani, Suhaima ko a kullum cikin shiri take Tana sauraron ita baiwar Allah Anisa gabadaya ta daburce Tana mamakin sai dai ganin yanda dukkansu biyun ko a jikin su yasa abin ke kulle Mata Kai. Shin mai Suhaima ta yi haka har yayanta ya ke threatening kulle ta? Ita dai ta San Suhaima is very nice, ga addini ga tsafta gashi Bata kiwuya ko kadan ba kaman ita ba. Da safe bayan sallahn asuba za tayi karatu ta hada breakfast sannan ita zata ma kulsoom da twins wanka ta taya su shiryawa, all these while Anisan ba ta San ana yi ba ma saboda da tayi sallah ta ke komawa bacci. Kyawawan halayen ta ne yasa ta shiga ran Yan gidan gabadaya cikin kankanin lokaci har ma ko da Abbah, Anty ko ji da ita ta ke sosai.


Anyi three weeks da case in Maryam tun bayan nan Bata Kara zuwa gidan ba sai a Daren ranar Shima a dalilin tafiyan da za suyi Kano washegari da safe ne. Har daki ta zo su ka gaisa da Suhaima gabadaya ta sauya da dukkan alamun kishiyan da aka ce za a Mata ne ya saita ta. Fararan su ka gaisa ta amshi haydar sannan ta fita ta gaida Barr, murmushi ya dinga Mata Yana tambayan ta ya take? Faroukh ko sai harara ya ke aika Mata. Ita Kam Maryam ba yanda za tayi ne yanzu mustapha dai dai ya ke da ita Amma its so obvious he is interested in Suhaima. Sai dai Suhaiman na kokarin kaucewa hakan, musamman ta ke sa wayan ta a flight mode saboda shi in da Kuma Dr, haka kurum duk da auren su su jawo Mata bala'i gun matansu da su ke mutunci, barin ma maryam har gwara Rufaida akwai shariya ko da ta gane hakan. Haka ranar Dr Fahad ya matsa sai ta je gidan shi ba yanda ta iya sai dai da Anisa da Muhibba duka suka tafi a motan gidansu don ba ta yadda ta Kara shiga motan Dr ba tun bayan abinda ya faru a case in maryam, bata wani Jima su ka tafi Dan ma Rufaidan ta amshe su hannu bibiyu, its was so obvious Yana son tattauna da ita sai dai ba dama. Ta San sun Mata mutunci sosai Amma Kuma ba ta fatan tarwatsa musu Family.

Ranar yau ta kasance ranar juma'a. Saboda ruwan saman da ake ta shararawa ya sa ba lallai ka gane cewa juma'an bane. Ruwan ma an dade ba ayi shi ba. Da ke ana cikin karshen october hakan ya sa ake sa ran ruwan bankwana ne ake yi, lokacin kaka na gab da shigowa kenan. Yaran gidan gabadaya na makaranta sai su Anisa da Suhaima kawai. yanayin garin ya sa duk su libge akan gado,  har wurin Goma da rabi sannan su ka mike, shi inma Mommy ce ta musu waya su tashi su ma Baban su breakfast, zai shigo garin yanzu daga Abuja.+


Bai dade da shigo gidan ba su ka gama. Anisa ce ta hada komai ta wuce dashi side in shi.

By 11:37 am, karan siren ya fara tashi. Da ke Unguwa ne da mutane ke hulda akan hanya sosai ba kaman GRA ba, jama'an wurin ne su ka fara mamakin mai ya kawo motocin yan sandan dayawa haka cikin layin? Shin lafiya? Wani mai laifin kuma su ke shirin kamawa. Haka su ka dinga tafiya har kofar gidan Engr Usman alkali, inda duk su ka ja birki. Wani karamin dan sanda ne yayi saurin sauka daga motan farko yayi wurin babban odyssey in da ke tsakiya. Sai da ya sarawa ogan nashi "Sir, how do we get in?"

"Get me the door" ya amsa, dan sanda yayi saurin isa ya bude mai kofan. "Get the boy, dashi za mu shiga" Faroukh ne ya fito daga cikin motan, Yan sandan na bin shi a baya. kai tsaye ya musu jagora zuwa cikin gidan.


Engr na zaune a falon shi yana tsakiyar breakfast ya fara jin siren in Polisawan na tashi. Ba abinda ya kawo a ranshi sai yanzu da ya daga kai, Faroukh ya hango suna faman shigowa cikin gida shi da polisawan kusan biyar. Ai bai san da ya ji kafafuwan shi ba, da kyar ya iya sa takalma yayi waje, domin jin me ya hada danshi da polisawan nan.


Idanuwa ya zuba musu domin gano dalilin shigowar su cikin gidan shi. Faroukh ya zubawa idanu yana kokarin gano wani tashin hankali akan fuskan nashi, sai dai sadda kan shi kasan da yayi bai ba wa mahaifin nashi daman hakan ba.

Hannu babban police in ya mikawa Engr, bayan sun gaisa police in ya gabatar mishi da wani takarda. Engr dai har yanzu a rude yake. Ga faroukh kam har yanzu kanshi na kasa yaki yarda ya kalli mahaifin nashi. Har sanda Engr ya bude takarta, ya ga shaidan kotu ya dauka Faroukh ne ya dauka mishi magana.


Tabbas arrest warrant ne, sai dai ba sunan Faroukh bane a jiki. Suhaima Adam Bello ya gani a rubuce. "An sanar mana cewa tana gidan ka, we need to take her for investigation" Shi dai Engr har yanzu shakku ke ranshi. Shin in ma yarinyar su ke nema me ye hadin ta kuma da Faroukh. Murya ya bude ya kwalla wa Anisa kira. Da sauri ta fito, sai dai tun kafin ta karaso wajen ya ce mata ta kira mai suhaima tazo waje.


Tun daga bakin kofa da ta hango su ta san abinda ya kawo su, ko shakka ba tayi ita su ke nema, balle kuma ma ga Faroukh a tsaye tare dasu. Gabaday jikin ta rawa ya ke, kusan uku ta ke tuntube jiki a sanyaye ta karasa wurin su "Ita ce wannan?" Engr ya tmby, Sergeant maccen da ke wurin ne ta fiddowa Engr hoton da su ka zo dashi domin tabbatar mishi wacce su ke neman ce.

"Suhaimaa" Engr ya kira cike da mamaki a idabuwan shi. Kanta a kasa yake, tana jin zuciyan ta kaman zai fito tsabagen yanda ya ke dukawa da sauri sauri "na'am Baba?"ta amsa.


"Me ke faruwa?" Ya tmby yana kallon ta da kuma yanayin da ta shiga, gabadaya a rikice ta ke sai dai duk da hakan ba ko alaman hawaye a idanuwan ta. Hakan kan shi abun tsoro ne.


Tana shirin ba da amsa taga Ogan nasu ya mika wa maccen handcuff. Kaman a mafarki ta fara jin yanda ake karanto mata marinda right "You are arrested for the suspicion of murder's attempt of Zayd Almansur. You have the right to remain silent. Anything you say maybe used against you in the court of law. You have the right to consult a lawyer, if you can't afford one will be appoint to you if you so desire"


Rayuwa kenan, ashe sa ka wannan abun yana daga cikin kaddarar rayuwa ta, wani irin cunkushe wa taji zuciyan ta yayi lokacin da Yar sanda ke kokarin kamo ta su bar gidan. Kallon fuska Abbah tayi, har yanzu tambayoyi ne a bakin shi, maida idanuwan ta tayi kan Faroukh "Faroukh ban aika ta ba, wlh ban aika ta abinda kake zaton nayi ba, ba ka taba tmby na abinda ke faruwa fa, shine za ka sa a kamani?" Muryan ta na rawa sosai ta ke furucin yayin da yar sanda ke kokarin jan tafita daga gidan. Anisa kam duk ta rude sai faman hawaye ta ke tana kallon Faroukh, taji zancen kuma tasan faroukh in ne yayi abinda ya sa aka kama Anisan, har yanzu dai kasan ya ke kallo. Suna fita daga gidan Anisa ta saki kara ta rushe da kuka,  Kallon ta Engr yayi, tsabagen rudewa sai lokacin ya tuna ya kamata ya san station in da za su kaita. Da azama yayi wajen, kusan duk sun gama shiga motan sai mutum daya ne ya rage.


"Station?" Kawai yace mishi. "Ba case in garin nan bane ba, Abuja za a kaita."

"Station in ina a Abuja?" Engr ya kara tmby.


"Wlh ban sani ba, DIG ne ya turo mu" abinda kawai ya fada kenan ya shige motan su ka wuce.


Daidai sanda su ke fita layin motan mommy ya kunno kai. Sai da ta tsaya su ka wuce sannan ta shiga. Isan ta gida kuwa ta iske Engr na ta faman yi wa Faroukh ihu ya ki magana, Anisa ko sai kuka ta ke ta yi.

"Lafiya? " Abinda bakin mommy ya iya furtawa kenan, sai dai ba ta samu wanda ya iya ba ta amsa ba. Engr kokarin kiran connections in shi ya ke domin jin asalin abinda ke faruwa.


"Faroukh ba zaka min magana ba ko? Me ye hada Suhaima da Zayd Almansur"

"Baba fa..." Kaman zai yi magana sai kuma ya kasa yana bin Anisa da kallon gargadi, girgiza mishi kai tayi ta juya wurin Mommy.


"Ku min magana me ke faruwa? Ina Suhaiman?" Mommu ce ta kara magana tana bin ko wanne su da kallo ganin yanayin kowa ya canja, akan Anisa ta tsaya.


"Mommy sun tafi da ita, Yan sanda, Ya Faroukh yazo dasu" Anisan ta fada tana kokarin kore kwallan da ke zubo mata.


"To me tayi mishi?" Wannan tmbyn kam is more like babu wanda ta ke mawa.


"Mommy daman ranar naji suna magana yana cewa sai ya tona mata asiri, ita kuma tace ya tona in daman me ya ke jira?"


"Ko shine ba zaki fada mana ba sai yau? eh?" Tsawan da Engr ya mata ne ya tsorata Anisa sai da ta ja baya. Mai da idanuwan shi yayi kan Faroukh, yace wa Mommy "ki kira Musty shi ya mishi bayani" yana fadin hakan yayi hanyan dakin shi, dan yanda ya ke ji in ya cigaba da tsayuwa yanzu ya kai kasa.


Bangaren Suhaima kuwa har su ka isa Station zuciyan ta a cunkushe ya ke, ba zafi kuma ba sauki. Ganin abun ta ke tamkar a mafarki, duk da ta san watarana hakan na iya faruwa tunda ta bar Abuja, duk da haka ba ta shiryawa hakan ba. Ba wanda ya hantare a yan sandan, sai dai masu girgiza kai sina kiran "mata akwai iya daukan wa kansu rigima" ba minti talatin ba ta cika a wurin ba su kayi Abuja da ita. Ba wanda tayi wa magana, ba wanda ta ma musu ko kallon banza, ba wanda ta samu matsala dashi har su ka karaso garin Abuja.

A lokacin taji wani nauyi a kirjin ta, Kallon garin kadai yana tuno mata da abubuwa mafi muni da ta aika ta rayuwarta. Shin yanzu kuma wani irin kaddaran rayuwa zai juya mata a cikin garin da rayuwa bai mata adalci ba? Da duk zuciyan ta ta ke jin kiyayyar kasancewa a cikin garin. Ina ma, bai da wani amfani, shiyasa ma ba tayi shi ba tunda mai afkuwa ya riga da ya afku. Sai kuma a fuskanci gaba kawai.


Police headquarters su ka fara zuwa da ita, Wani babban dan sanda ne ya fito suna ganin shi duk suka sara mishi. Kallon ta yayi yace musu "itace wannan?"  "Yes sir" su ka amsa mishi. "Yan mata ke ko wani irin masifa ne ya kai ki?" Bai jira amsan ta ba ya girigiza kai "a wuce da ita station a fara investigation" amsa mishi su kayi, ba wanda da suka taho da ita daga kaduna bane su ka wuce da ita. "Wannan ce Almasur su kayi charging?" Wani ya tmby aka ce mishi eh.

"Tabdijam" kawai yace ya juya.


Suna isa aka tura ta wani cell, ita kadai ce a wurin. Tun daga lokacin kuma ba wanda ya kara bi ta kanta sai wani shegen abinci da su ka kawo mata, kamshi shi kadai ya tada mata hankali balle a kai da ganin shi.


A kaduna kuwa zaune Faroukh ya ke a gaban mustapha yana kokarin mishi bayani "Uncle Musty yarinyar nan munafuka ce wlh, Zaman ta a nan ba alkhairi bane, wlh matsala za ta ja mana shiyasa na tura ta inda ake neman ta kawai" harara shi Mustapha yayi "Faroukh ban sa iskanci za ka gaya min me faru ko kuma ince me ke faruwa?"

"Uncle, Maigida na Zayd Almansur ai ka san shi, Wlh shi tayi kokarin kashe wa ta gudu tazo garin nan, i mean na san ta tun a Abuja" kallon shi Mustapha yayi kaman yana nazari, can ya girgiza kai "Ba zai yiwu ba Faroukh, tayi attempting kashe Almansur kuma ta kwana lfy har tayi watanni a garin nan"


"To ni kuma ai ban san me zance maka ba, investigation dai ake yi an fara neman ta, ni kuma na saukake musu wahala na fada musu inda ta ke da suka zo investigation company inmu" shiru Mustapha yayi yana kara karantar Faroukh in "wai to tsaya ka santa tun a Abujan ne?"


"Na santa, ita ma ta ma Almansur in aiki a drink shop inshi. Kawar Budurwa shi ce kafin ta dawo budurwar tashi, i've seen some of her true colors, zaman ta tare damu hatsari ne Uncle"


"Zan binciko dai" Mustapha ya fada hade da mikewa, kallon shi Faroukh yayi a ranshi yana ayyana ya rasa me yarinyar nan ta ke wa mutane, ko ina sonta ake duk da yana kokarin fahimtar da mutane hatsarin da ke gare ta. Ko ma me ta ke musu shi kam bai kama shi ba.


Ko da Mommy taji abinda Faroukh ya fada wa Mustapha, Fada ta hau mishi sosai akan meyesa tun tuni bai fada musu ba, shin in ma wata muguwan ce da ta musu wani abu kenan. "Amma Faroukh da ta yarana wani abu da ka cuce ni wlh" ta fada tana mai aikawa Faroukh kallon banza. Mustapha da Anisa ko mamakin wannan furucin na ta su kayi. "Mommy Suhaima ba abinda za ta ma kowa,  ni na nasan ba ta aika ta abinda ake zargin ta dashi ba wlh" da kuka ta karasa zancen nata.


"Kaniyar ki Anisa kinji, ba ki da hankali ne? Yarinyar da ake zargi da kisa? Kuma baki ji abinda Faroukh yace ba? Tuntuni daman ba da zuciya daya ta ke zaune da zayd in ba? Wacce aka ce ta kwace wa kawarta Saurayi. Ke baki san dan Adam ba ko? Ba kisan munafunci mutane ba ko? Tun farko meya hana ta fada mana asalin wacece ita?" Yanda mommy ta ke magana da yanayin fuskan ta zai tabbatar ma ka gaskiyan abinda ta ke fadi har ranta, tana jin zafin barin ta da Anisa da ta dinga yi da sauran kannen ta, daman duk karatun da ta dinga koya musu duk pretending ne kawai.


"Bakomai in sha Allahu Anty tunda ba ta musu komai ba. Yanzu dai shari'ah za ta tabbatar da gskyn matsalan." Mustapha ne yayi maganan. Shi inma da hararan ta bishi "Eh lallai yanzu na gane dalilin da yasa ba ka taba gano matsalolin matarka ba sai da ka san yarinyar nan. Gashi nan daman halin ta ne raba masoya ai. Nima ban san meye riban ta ne zama damu ba, tabbas tana da dalili. Ba kaji mai Anisa ta fada ba ranar? Tace wa Faroukh ta san me ta ke, ba hakanan banza ta zauna a gidan su ba?"


"Amma Anty baki ganin shima Faroukh in ya hada da wani ganin dama tun can bai son yariny..."


"Ya ci riban me ke nan? Kaga lil bace  min daga gani, akan macce kana kokarin aiba ta min da ko?" Kwafa tayi sannan tayi hanyan dakin ta ba tare da ta bashi daman kara magana ba. Inji masu magana su kace wai mai da wawa.


Mustapha na fita daga gidan ya kira numban Dr Fahad domin sanar mishi abinda ake ciki. Sanar mishi yayi inda za su hadu suyi magana. Open spaces ne wurin, bai dade da isa ba sai ga likitan nan ya iso. A daddafe su ka gaisa kafin Mustapha ya fara koro mishi bayanin abinda ke akwai.


Shirun dole Dr Fahad yayi, gabadaya ma ji yayi  notunan kanshi sun kwance. Ko da Faroukg ya taba tare shi ya mishi magana bai wani kowa komai ba akan abun. Kawai ya dauka rigima ce tasu ta matasa ko wani banzan ra'ayin shi na daban, shi har ga Allah ma yafi zaton ko al'amarin ne na kishi, yana son ta.


"Me kake ganin za mu yi Dr" Mustapha ya katse mishi dogon tunanin bala'in da ya shiga. "Al'amarin ne da daure kia Barr, barin ma da bamu san komai akan zancen ba"


Wani dan Nazari Barr yayi sannan yace "Ni ina ganin kaman akwai abunda Faroukh in ke boyewa ne gsky"


"Da gskyn ka ma, Amma yanzu ina ganin abunda yafi dacewa shine mu fara sanin inda ta ke sannan mu ji daga bakin Yan sandan. Kotu za a shiga ko miye?"


"Nima nayi tunanin nan Dr, Ina so inyi magana da Engr ne inji yanda zamu fara bullowa abun, saboda zai fi ni connection."


"Ehmm hakan za ayi, ni ma dai zanyi kokarin yi wa Abbah na maganan da ke shi yana ma can Abujan ne" tattauna wan mafita su ka cigaba dayi kafin can Barr yace "abin nan da mamaki, a halin Suhaima da na fuskanta ba alaman za ta iya hallaka ko dabba ma balle mutum. Sai dai ance kar kayi saurin yarda da mutum"


"Tabbas abin akwai daure kai. Amma ni kam ina tunanin ko hakan ya faru to tabbas ba banza ba, Ruwa fa ba ya tsami a kasa. Kila wani abun shi Al-mansur ya mata and she try protecting herself, i mean self defence. Lokacin da accideny in da mai dakin ka ai nayi witnessing. Is like ba ta san inda kanta ya ke ba shigowa titin kawai tayi ita kuma tana gudu"


Barr na shirin responding call in Engr da ya shigo ya katse shi. "Bara nayi picking call in nan please, Engr ke kira" nodding Dr yayi, yana jin gabadayan shi wan iri, labarin da barrister ya bashi ba karamin girgiza shi yayi ba.


Mustaphan kam bayan ya amsa wayan Engr, shi ma dai maganan ce ta Suhaima "na samu daman yin magana da Commissioner of police na nan Kaduna, Ya sanar min bai san kan abun kwata kwata amma tabbas Zayd in bai da lafiya, suna asibiti a indian shi da mahaifiyar shi. In dai ya binciko zan kara waiwayen shi"


"To shknn Uncle, mu ma nan muna kokarin binciken ne. Yanzu haka muna tare da Dr in da yayi treating inta bayan accident in" yanda ya sunkuyar da kai ya ke maganan zai tabbatar ma yanda ya ke ganin girman wanda su ke maganan. Magana daya biyu su kayi kafin yace mai "Antin is so scared, ka san su yan boko halin su daban yake,  tana insisting wai mu bar maganan kawai tunda asirin yarinyar ya tonu. Don haka ka guji maganan a gabatan, we can't just leave the case bayan ta zauna a wurin mu, it can even implicate us balle ma Faroukh is somehow involve ai"


"To shknn Uncle ba wani matsala in sha Allah"


"Allah ya dafa mana" Engr ya fada kafin su kayi sallama akan inda wani abu su nemi juna kawai.


Labarta wa Dr yayi progress in da aka samu akan zance sannan ya ce "Tunda abu ina tunanin kaman court case ne, zan yi kokarin tabo wasu collegeau ina da ke can Abujan


Na'am Dr yayi da shawaran, sun dan jima suna kara tattaunawa akan al'amari. Dukkan su dai abun ya rikita su barin ma Dr Fahad, da su kayi shakuwa na musamman. Duk da ko case in ya shafi yaron babban mutum kaman Al-mansur amma ba su jin za su iya barin shi, sai dai in dumu dumu aka kama ta da lafiya, ba ma sa fatan haka, suna mata kyakyawan zato. Mutum irin Suhaima akwai dadin Zama.


Hatta Maryam da ta ji zancen sai da taji wani iri, barin ma da taji case in da Al-mansur " Hmm ehm in dai sharri ake mata Allah ya fidda ta" ta fada cike da jinjina zancen "Ashe barin ta nan alkhairi ne da kilan harda mu za a kama" hararan ta Barrister "ke dai mimi akwai matsala, ko da ma wani abun ne shin ba gidan yayanki ta ke ba? Kuma ba ke kika fara insisting ta zauna damu ba? Kuma ke kika fara kade ta tun farko. Kinga ko a tsarin shari'ah a ma ke ma suspect ce"


"Ah haba Dan Allah bari mana" yanda ta zaro idanu waje cike da tsoro ne ya ba mustapha dariya, dole sai da ya dara yace "See you mijin ki na lauya kina tsoron shari'a. Yanzu dai kawai mu taya ta da addu'a kuma mu mata kyakyawan zato tunda dai ba ta nuna mana wani kofa da xamu iya gasgata abinda ake zargin ta dashi ba"


"In sha Allah" maryam in ta amsa.


Ita kam Rufaidah ko da aka sanar mata cewa tayi kawai "Allah ya raba mu da munmunar kaddara" da ke ita ba gwanar surutu ba ce.

Dukkan wani bayani da ya kamata ace sun samu sun same shi. Abujan su ka tafi da kansu. Sai dai har yanzu ba su gano asalin abinda ya faru tsakanin Suhaima da Almansur ba. Suna dai fatan ji daga bakin Suhaima, daganan a san yanda za a bullo wa zancen. Duk iya kokarin su a ranar ganin Suhaima hakanan ya gagare su. Dole dai Barr Mustapha ya isa station in a matsayin lawyer mai kare ta, tunda ya samu lbrn sun kai case in court.+

Abin da ya lura shine, kaman ba gsky a lamarin duba da irin kallon da su ke bin shi dashi. Sai kuma su fara kus kus tsakanin su. Wasa su ka dinga mishi da hankali da dai yaga abun da wata a kasa dole ya koma headquarter insu na nan Abuja yayi reporting abinda ke faruwa.
Ko a can inma, shugaban su ce mishi yayi "Barr Mustapha mai ya kai ka amsan irin case in nan? In zan baka shawara ka ajiye wannan case in mana"

"Amma miye dalilin ka na fadan hakan?" Ya tmby, girgiza kai yayi "yace haba Brr kowa ya kwana ya tashi a kasan nan fa yasan su waye Al-mansur, shin kana ganin za ka iya nasara a irin case in nan da ake amfani da kudi da karfin mulki a ci shi? Kai kasan shari'a, Hujjan da duk ka kafa shi shine abin dubawa. Kai ya kamata ka fadawa mutane cewa dayawan mutanen da ake kai prison ba su aikata abinda ake tuhuman su dashi ba,  Aa kawai karfin hujjan akan su ne ya ke kai su inda su ke. Wani irin kudi ma aka yi offering in ka kayi gangancin amsan case irin wannan mustapha?"

Runtse ido Barr yayi, tabbas dukkan abinda ake fada mishi gsky ne. Wannan shi ya ke kara tsorata shi da shari'an. "Ba kudi aka bani ba sir, i personally know the girl ne zan so in taimakeka"

Shiru  yayi alamun nazari, can yace "Shknn Barr tun da ka dage, Allah ya bada nasara. Kaje ka same su, zanyi sending note" godiya yayi ma shugaban nasu, cike da farin cikin nasara ya kara nufan station in.
...

Da constable ya bude mata lock in ta fito, ko kadan ba ta kawo komai a rai ba, binshi tayi kaman rakumi da akala har zuwa inda Mustapha ke zaune. Ko kusa ba tayi tsammani ganin daya daga cikin su ba, barin ma a yanayin da aka taho da ita. Kokarin tsagaita tunanin tayi ta fuskance shi da idanunta da su ke bushe kararau har izuwa yanzu.
Kallo daya ya mata ya ji wani irin mugun tausayin ta na ratsa dukkan jikin shi. Ta tsinci kanta ne a cikin wani irin mawuyacin halin. Ko shakka ba yayi gab ta ke da ta cire buri ga rayuwa gabdaya, shiyasa shi kuma ya lashi takobin taimaka ma ta ko ta halin yaya, ko da kuwa bashi ke da Nasara ba a karshen hankalin shi ba zai kwanta ba in har bai kokarta ba.

"Suhaima" ya kira sunan ta yana kara karantar yanayin ta, shi kam a kwana biyun nan har rama idon shi yaga ta mai. Hannun ta daya ta sa kan goshi ta runtse idanuwan ta, a can cikin ta ta keji wani irin radadi na wucin gadi. "Abban Haydar ka yarda dani Wlh ban aika ta ba"
"Kar ki damu, ba wannan bane matsalan a yanzu" ya fada yana kara gyara zaman shi.

Zaro idanu tayi cike da rashin fahimtar manufar maganar shi. Gane hakan da yayi ne yace ma ta "Kin fa san shi kotu hujja kawai ya ke nema Suhaima, kuma banda wurin ki ban gani akwai inda zan samu hujjojin da ya kamata, shiyasa na ke so ki kwantar da hankali muyi magana" saurin girgiza kai tayi tana fadin "ba wannan bane matsala ta Abban Haydar, so na ke kawai ku yarda dani, ku yarda ban aika ta ba. Amma nasan jayayye dasu ba zai wani haifar da da mai idanu ba, toh in ma na samu fita ina zan nufa? Ban ganin ina da wani abu da zanyi fada domin shi ba, banda komai kuma banda kowa"
Zantukan ta ba karamin illa su ka mai ba, sai dai ba ta cikin halin da za ta fuskanci hakan da ba ta karasa ba. Kaman dai yanda yayi hasashe ne, she is giving up akan rayuwa gabadayan ta. Da kyar ya iya hado kalaman da zai fada mata "Aa Suhaima ki daina maganar nan, ai kina da Allah kuma ba gamu ba? Mu dai ba mu ga wani halin assha a tare da ke iya zaman da muka yi da ke, shiyasa mu ka tsaya miki"
Murmushi mai matukar ciwo ta saki "kasan Almansur a kasar nan kuwa? Kasan karfin shaharan su? Ka san yawan dukiyan su? Za su iya yin komai wurin kwato wa Dan su fada duk ko ta hanyan da su ka ga zai kawo musu nasara, ban san saku hadari dan Allah ka bar zancen nan"
"Suhaima please" ya fada yana dakatar da ita da hannuwan shi. "In ba zaki iya bani karfin guiwa ba kimin shiru" a fusace yayi maganan, kusan sanin ta dashi ba za ta iya tuna lokacin da ya fusata irin haka ba sai lokacin case insu da maryam.

Magana ya fara yi yanzu kuma kaman mai lallashin ta yace "Dan Allah ki bani hadin kai kinji? Wlh hankalina ba zai kwanta ba in na bar ki a haka ba zan iya yafe wa kaina ba." Wani iri kunya taji ya kamata, shin ba matsalan ta bane? Amma kuma shi ke rokon ta ta taimaka wurin kare kanta? Shiru tayi ...

"Shkkn" ta fada a sanyaye, sai lokacin yaji sauki ya mamaye shi yace "Kin amsa wani tmby a nan?"

"Ba wanda ya tmbyn, illa ma nuna wan da suka yi kawai nina aikata abinda su ke tuhumata dashi. Wai meyesa mutane ba su da adalci ne a rayuwan nan?"
Shiru yayi can ya kalli agogo "Suhaima zan tafi gobe za a fara zaman kotu domin gabatar da kara, remember you are pleading guilty,  try to be yourself kawai kar ki yi wani acting. Sannan za muyi kokarin neman bail ko dan mu samu tattaunawa da kyau."
"Kudin bail in bai da yawa ne?" Ta bukata

Shiru yayi kaman ba zai yi magana ba yace "Sai dai gobe in sun bada zamu ji abinda su ka yanke.

Hannu ta mika mishi ta na nuna takarda da biron da ke hannun shi. Kaman zai yi magana sai kuma ya fasa ya mika mata kawai. Phone no ta rubuta mishi da home address na lagos.  Sannan ta mika mishi " Ka kira numban, sunan ta zeenah, tana zaune a gidan yanci a agege da ke garin lagos. Na ma rubuta ma address in, in ka kira kawai kace mata daga kawa Yar baiwa ne. Duk amount in kudin da yakamata ka fada ma ta za ta turo ma ka. In ba ka samu numban ba,  in akwai wanda ka sani a lagos ka aike ta wurin shi. Kawa, Yar baiwa fa za kace mata" kaman a mafarki ya ke jin abun da ta ke fada mishi. Gidan yanci kuma? Mai ya hada suhaima da wannan? Gidan karauwai fa kenan, tab da alamun abun ya fi karfin yanda ya ke hango shi.

Kaman ya share numban da ta bashi, sai da su ka hadu da Dr Fahad a guest house in Abban shi likitan ya labarta mishi yanda su kayi da Suhaiman. Shi kanshi Dr in sai da yaji faduwar gaba amma sai yayi kokarin ba wa Barr karfin guiwa. "Mu neme ta kawai, kilan ta zamo wani hanyan taimaka mana ma bayan kudin" Shawaran ko su kabi. Sai dai kusan sau bakwai suna kira numban ba a daga ba, duk jikin su yayi sanyi. Dr Fahad yayi kokarin daga wayan shi ya kira wani abokin shi da ke garin lagos in kuma ba laifi ya dan yi harka da gidajen kafin daga baya Allah ya shirye shi bayan yayi aure. Bai wani tsaya dogon gaisuwa ba ya sanar taimakon da ya ke nema a wurin shi.
"Haba bokon turai kar ka sa ni jin kunya mana? Kai da kanka yau kuma?" Da shekiyan ci ya mai maganan, Dr Fahad ya gane hakan ne saboda wa'azin da ya kan yi mai lokacin da su ke service.

"Pls mana its urgent, wani case ne" ya fada sounding more serious.

Har wurin magriba suna jiran jin labarin. Sai bayan anyi sallah yayi receiving call in friend in nashi, ba lbr bane mai dadi. Zeenah tayi tafiya yau kwana biyar kenan kuma ba wanda ya san ranar da zata dawo, ba wanda ya san takamaiman inda taje kuma. Ba suji dadin lbrn ba amma sai suka share su ka fara neman mafita, sanin ko an basu bail in tofa ba karamin kudi za su ciro ba. Amma ganin su biyu ne ga kuma Engr is more than ready to help sai su kaji dan dama dama.

...

Safiyar litinin da karfe sha daya da rabi na safe aka shirya sauraron karan. Dukkan su da wuri su ka halarci kotun suna jiran kiran karan su. Ba abinda ya daure wa Barr Mustapha kai sai Jaridar da yaga ana ta sayarwa lokacin da ya isa court house. A young lady charged for murder of the Famous Almansur son. Hoton Suhaima ne a jiki da handcuffs a hannun ta lokacin da ake kokarin shiga da ita police headquarters na Abuja. Abin daurewan kan shine: Atleast case in nan zai yi wata uku da faruwa, shin meyesa ba su taso dashi ba sai yanzu? Sannan a sunan da Almansur su kayi a kasan da mamaki ace dansu yana cikin wani hali na rayuwa mutuwa har na wata uku ba wanda ke da information akai.

  Sha daya dai dai gabadayan su suka gabata cikin kotun. Reporters kala kala Suhaima da police su ka tarar dasu a bakin kotun sai dai ba wanda ta ba wa attention balle yayi tunanin tana da niyyan amsa shi. Tayi kokari sosai gun bin abinda Barr Mustapha ya fada mata, kanta ba a kasa ya ke sai dai duk da haka ba wanda ta ke kallo har a ka isar da ita gun inda ake bukatan ta tsaya. Bakin abaya ke jikinta sai farin baby hijab akai, musamman Barr in ya aika ma ta saboda gabata a gaban kotu. Kana ganin ta kaga wacce ke cikin matsanancin tashin hankali, addu'a ta ke ta fama yi a hankali za kaga bakin ta na motsawa.

Judge Yusuf Ibrahim, shine sunan alkalin da zai saurari karan. Sai da yayi yan rubuce rubucen shi sannan ya dago, kan Suhaima ya fara sauke idanuwan shi. Bai wani dade ba ya dauke ya maida kan lauyoyin da su ke zaune a wurin.

"Lauyan Gwamnati, ina sauraran ka" Alkalin ya fada, idanun shi akan lauyan.

Kai tsaye Barr in ya mike tsaye. Lauyan da ke aiki karkashin gwamnati ma'ana (prosecutor) aikin su suyi proving zargin da ake ma criminal, su gabatar da shaidun da zai nuna guiltiness insu. Irin lauyoyin nan ne da suka yi kaurin suna a sana'ar su kuma suka taka mataki daban daban a fannin shari'ah. Maye ne, dalili kuwa ya matukar kwarewa wurin iya samo hujjoji da kure mutum, ya na yawan samun nasara a dukkan shari'ar da ya sa gaba. da karfin guiwan shi sosai yace "Ya mai girma mai shari'a sunana Barr Sadiq Lawal Funtua. Wacce ake kara tayi yunkurin kisan Zayd Almansur ta hanyan sa mishi guba a abinci,  sannan ta tada gobara a gidan bayan ta tabbatar da yaci abinci. Tayi hakan ne saboda wani tunanin na ta na ganin ba za a zarge ta ba. Bayan ta gama kuma sai ta sa kafa ta bar garin har na wata uku sai a kwanan nan aka samu lbrn ta a jihar kaduna a bakin wani Ma'aikacin Zayd Almansur in. Yanzu haka victim in bai san inda kan shi ya ke ba." Cikin natsuwa ya ke bayanin yana kai kallon shi kan alkalin domin kokarin ganin inda zancen nashi ya ke kaiwa. Yanayin maganan shi kadai zai fahimtar da kai an dade ana damawa dashi.

"Wannan case in ba karamin bane, bayan guduwan da tayi ta ba wa yan sanda wahalan bincike" farat daya muryan shi ta canja irin na wanda aka cuca ta "Don haka ina mai rokon wannan kotu mai alfarma da ta hana bailing wannan yarinya, sake ta daga hannun hukuma babban risk ne,  za ta iya kara bacewa wani wuri kuma tazo tana wahalar da shari'ah." Sunkuyar da kan shi yayi sannan yace "ina mai fatan wannan kotu zata fahimci inda na dosa, nagode" ya karasa sannan ya samu wuri ya zauna.

Alkalin ya dade yana rubuce rubuce kafin ya dago yace "lauyan wanda ake kara, bismillah" da izza Barr Mustapha ya tashi ya gabatar da kanshi "Ya mai girma mai shari'a zan so wannan kotu mai Alfarma ta fahimci cewa da wacce ake kara guduwa tayi da yan sanda ba su same ta cikin sauki ba. Ko cikin report insu har cikin gidan da ta ke da zama su ka je kuma su ka same ta, haka kuma ba wani gargada ta mika wuya." Shiru Barr ya danyi na seconds yana kallon yanayin Suhaima sannan ya cigaba "zan so wannan kotu tayi la'akari da cewa wacce ake kara ta san cewa gidan da ta ke zama akwai wanda ke aiki karkashin wanda ake ikirari tayi yunkuri kisa. Da taso guduwa ba zata zauna a wannan gidan ba bayan ta san hatsarin da ke ciki. Ina fatan wannan kotu mai adalci za tayi duba cikin lamarin nan ta ba mu beli, nagode ya mai girma mai shari'ah" shiru kotun ya dauka kafin alkalin ya dago kanshi.

"Muna bukatar hujjoji akan abinda ka gabatar Barr Mustapha. Za a daga wannan karan zuwa 7 ga watan November, nan da sati biyu masu zuwa. Yan sanda na da ikon cigaba da tsare wacce ake kara har zuwa wannan ranar. Kotuu" alkalin ya karasa da bugu yar guduman shi.

Zufan azaba ne ya fara zubo ma Suhaima daga ko ina na jikin ta,  yanzu a wannan kazamin wurin ake so ta cigaba da rayuwa har nan da sati biyu masu zuwa.To kika san inda makomar ki za ta kare bayan shari'an? Wani zuciya ya tunatar da ita. Wani kululun bakin ciki ne ya tsaya mata a makogaro. Shin wannan wani irin mugun kaddara ne rayuwa ke juyi da  ita ta ko wani fanni. Tabbas yanzu kam ta gama yarda rayuwan ta ba ta da wani amfani. Kaman mutum mutumi haka ta ji lokacin da police in ta ja ta zuwa motan su, gab fita kotun ta hadu da Barr Mustapha da Dr Fahad. Police in ba ta wani bata daman kallon su da kyau ba amma duk da hakan bai hana ta hango zallan tausayin ta a idanuwan su ba. Tabbas Allah bai hada ma ka zafi biyu a rayuwa, ita kam haduwan ta da wadannan mutanen ne sanyin da ta ke fuskan ta acikin dukkan wani kunci. Tana ji tana gani su ka kara janta zuwa Cikin tashin hankalin da ta ki jini da dukkan wani nau'i na jikin ta. Hakika an cuce ta a rayuwa, cutan da bashi da iyaka kuma ba mai iya rama mata sai Allah SWT.
...

Su Dr Fahad kam da bakin ciki rashin nasarar da su kayi su ka bar wurin. Barin ma Dr da ke jin kaman ya tsaga zuciyan shi kawai ya fito da ita saboda azaban kunan da ya ke ji a wurin. A cikin yan kwanakin da ya san Suhaima ya mugun sa ta a ranshi da ma rayuwar shi gabadaya, shiyasa duk wani damuwan shi ya ke jin ta kaman nashi ne. Duk wani abinda ya shafe ta ya shafe shi, abinda ya ke fada ma ta kenan kuma har ran shi yana jin gskyn hakan a yanzu.

Tilas Barr ya dau hanyar kaduna saboda a yanzun hakane ya zame mashi dolen dole. Ko Faroukh bai so sai ya sanar mishi dukkan abinda ya sani in details saboda hakan ne kawai zai samo mishi mafitan da ya ke bukata. Gidan Anty ya nufa yana shiga Kaduna, tana ganin shi ta hade rai da kyar ta amsa gaisuwan da ya mata ma.

Marairaice fuska yayi zuwa gare ta, abunda tayin bakon abu ne a wurin shi. Alakar su da ita na daban ne, duk wani matsalolin shi a rayuwa ita kadai ya ke iya tunkara da. Ya santa farin sani don ko mahaifiyar shi bai ma sanin da ya wa Antyn nashi ba. Akwai ta da mugun son ya'ya'nta duk da ta kan dage wurin tsawatar musu. Sai dai ba ko yaushe ta ke karban laifin yaran nata. Yanxun ma ya san matsalan akan furucin da yayi akan Faroukh. "Haba Anty na da lil inki zaki yi fushi kuma?"

Hararan shi ta juya kai "Ka tashi ka tafi kayi abinda ka sa a gaba" ganin dai da gaske fushin ta ke dashi ya sa ya dage yayi ta bata haushi, dolen dole ta sauko tace mishi "ban san ka da taurin kai lil, shin meye sa ba zaka bar case in nan bane wai? Kasan me kake jefa kanka a ciki kuwa? Eh! Akan yarinyar da ba ka santa ba, ba kuma ka san asalin nufin ta ba."

Dukar da kai kasa yayi cike da ladabi "ki yi hakuri Dan Allah Anty. A fahimta ta Suhaima na cikin wani hali da ta ke matakur bakutar taimako. Hakan yasa na ke son yi kokari akan ta. Yarinya ce duka duka amma ba ta da kowa da ya tsaya ma ta a rayuwa, shin ba kya tunanin wani bala'i ne babba ya afku da ita har yasa ta barin kowa nata? Nikam ina tausayin ta sosai wlh haka kuma ina son sanin Labarin Rayuwar ta" shiru Anty tayi tana sauraron shi har ya gama sannan tace.

"Amma ba ka tunanin bala'in da zai raba budurwa kaman wannan da iyayen ta ba karami bane? Ba ka gudun wannan ya shafe mu? Har ga Allah da fari na yarda da ita na bata benefit of doubt amma tunda wannan abun ya faru hankali na ya ki kwanciya da lamarin. Kuma kasan shi Dan adam wani abun kwata kwata ba kama. Amma tunda ka dage Allah ya bada saa" ta na fadin haka ta tashi ta bar falon, bin ta yayi da kallo yana wani nazari kafin ya nemi ganin Faroukh, ba ya gidan don haka ya kira shi ya same shi a gidan shi washegari da safe.Fuskan tan abinda ba ka shirya mai ba karamin rikice ne dashi ba. A kwana biyun nan gabadaya Barr Mustapha ya shiga wani mawuyacin hali. Da dukkan zuciya da karfin guiwan shi ya ke jin son tsaya ma Suhaima. Sai dai, gabadaya ya kasa gane in dai zai fuskanto wa abin. Yayi magana da Faroukh sai dai bai samo wani abin Kirki ba. Yawancin labarin akan abinda ya sani tsakanin Suhaiman da budurwa zayd ne da kuma shi kanshi zayd. Ga fahimtar Faroukh, suhaima na da wani mugun nufi tuntuni akan zayd da ta ke boyewa. Abubuwan dai duk rudani su ka kara mishi, shi da ya ke neman hanyan kare ta gabadaya points in da Faroukh ya bashi is aginst her. Karin karawa yana mamakin a ce wai Suhaima ce ta aika ta wannan abubuwan. Tirkashin fa kenan!+


Yau ya ke shirin koma wa Abuja, yana bukatar ganin Suhaiman su cigaba da tattaunawa kan lamarin. Abinci mai rai da lafiya Maryam ta hada mai, yayi farin ciki sosai duk da bai iya sakin jiki ya ci abincin da kyau ba. Hira ta ke mishi jefi jefi tana sako mishi kishin ta "Mu dai kam Suhaima ta dauke mana kai" za ta fada sai kuma ta waske kaman wasa ta ke. Sai dai ba halin mimin nashi da bai sani ba, a yanzu ba wannan bane matsalan domin bai da karfin guiwan yi mata bayani ba, in har ita da kanta ba ta san ya kamata ba.


Buzz buzz, karan wayan shi ya dawo dashi daga tunanin da ya dan fada. New numba ne hakan ya sa shi sharewa sai dai yanda calls ke ta shigowa wayan ya sa shi daukan wayan dole. Sai ya dauka ya ji muryan mace sannan ya kara duba numban da kyau, sai lokacin ya gane numban da suhaima ta bashi ne.


"Hello" yayi saurin fada gudun ta katse wayan.


"Ehmm ina jinkaaa ai,  na ji kayi shiru ne" ciki da duniyan ci ta ke magana, sai dai daga yanayin sautin muryan ta za ka gane hausa bai gama zama a bakin ta da kyau.


"Dan Allah ina magana da Zeenah ne?"


"Zeenah ke magana amma fa in kana bukatan harka ne dole kayi hakuri zuwa ranar Alhamis, bana cikin lagos" shiru yayi yana mamakin rashin kunya a fila irin wannan, sai kuma wani abu ke gaya mishi to daman kana bukatar ganin kunya gun karuwa ne?

"Amma kina ina ne? Dan gsky a matse na ke kuma ke kadai ce na ke ganin za ki iya kore min kishin ruwa ta" ya mata hakan ne don ya samu hadin kai sosai a wurin ta.


Wani shakiyin dariya tayi tace "toh fa, maza a samu labarin mu kenan. Gsky nayi nesa da lagos sosai"


"Kar ki samu wani damuwa ko ina kike dole ne in biyo ki ai" ya amsa ta cike da kosawa wannan karan, burin shi dai yaji garin da ta ke in yaso daganan ya tattauna da Dr sun san yanda za su bullo wa abun.


"Asuban cin bari garin kaduna zan yi zuwa birnin tarayya gobe in Allah ya kaimu" ai bai san sanda ya saki wani ajiyan zuciya ba, jin komai na kokarin zuwa mi shi da sauki.


"Yana ji kayi shiru?" Ta kara fadi, don har ta fara murnar kamun da tayi.


"Ina garin kaduna yanzu haka, ya za ayi mu hadu"

"Kai kai ina tare da wani mugun ne fa, da zai yiwa da mun hadu a Abujan gobe in za ka iya" ta amsa shi tana faman ya amince ds hakan, wanda ta ke tare dashi in bata ganin zai bata damar fita wuri ita kadai.


"Haba yan mata da dai kin taimaka min mun hadu a yau in, na fada a kagauce na ke fa" shiru tayi tana tunani sannan tace "zanyi kokarin fitowa mu hadun amma fa ba za mu dade, dama za kayi hakurin goben ne"

"Kar ki wani damu ba sai kin daden ba in yaso na kara biyo ki Abujan mu karasa a can. Yau dai a takure na ke wlh" dariya tayi sannan tace "yanda na ke jin ka in nan na san gurzu, ina dai fatan ka tanaji dumus dayawa"


"Kar ki wani damu kinji, ki dai lallaba ki zo in kawai" a marairaice ya ke maganan yanda zai samu tazo in kawai.


"Zan fito nan da yan mintuna bayan mugun nawa ya fita wani meeting, ina zan ganka?"


"Hotel seventeen, in ki fito ki kirani" yana kashe wa ya fara mamakin yanda tayi saurin amincewa dashi, to yanzu kaddara ma ace ba dan yankan kai bane ace wani mugun nufi ya ke dashi akan ta fa. "Allah ya kyauta mana amma karuwanci ba karamin illa ya ke dashi ba" ya fada a ranshi yana jan motan zuwa hotel in, don ya jira ta a can.


Ya kusa cika mintuna talatin a haraban hotel in kafin ta iso. "Muje ko?" Ta fada tana kashe mishi ido, murmushin dole hakan ya sa shi. Sanye ta ke cikin light brown abaya mai stones a jiki, shigan ya mata kyau ba laifi a hakan kaman na kwarai. Daga ganin alamun ta kadai Mustapha ya gane akwai rawan kai da surutu a tattare da ita.


"Kinsan me? Please zauna muyi magana kinji" zaro idanu tayi tana kallon shi tace "ban fa da enough time yana cika zan bar wurin kaga ko yanda na ganka in nan nima raina ya biya" dagowa yayi ya kalle ta, rashin kunya fal idanun ta.


"Karki damu ki zauna muyi magana Dan Allah" ba dan taso ba ta zauna tana kallonshi kamar wata mayya mai niyyar lashe shi. Au'uziyya yayi dan neman sharrin shaidan sannan yace mata "kiyi hakuri in na sa ran ki ya biya kaman yanda kika fada,  gsky na kira ki nan ne saboda ina so muyi magana" da fari mamaki ne ya cika mata idanu sai daga baya kuma jikin ta ya fara yin la'asar. Ita har ga Allah ba ta so hakan ba. Hakuri ya kara bata sannan yace "ko kinsan wata Kawa Yar baiwa?"

"Naam" tayi saurin fada tana kara zaman ta da kyau.


"Na san ta mana, ba dai ita kake nema ba ko? Domin dai ta dade da barin barik... au" saurin rufe bakin ta tayi sannan tace "yi hakuri fa, mun yi kawance da ita a da sosai amma tun da mu ka rabu ban san inda ta ke ba sai dai in ta neme ni, kuma yanzu an kwana biyu gsky banji duriyanta ba" shi dai mustapha gabadaya sauraren ta ya keyi kawai, amma tunda ta danganta kalman barikida Suhaima yaji gabdaya zuciyan shi na dokawa da sauri. Shin me kuma zai ji gaba? Mai ya kai Suhaima bariki? Abin dai sam sam ba kama. Diran mikiya bakin ciki ya mishi a zuciyan shi, ko dai gsky anty ne ke son tabbata? Karuwan ci fa kenan?


Fuske wa yayi kokarin yi yace "Tana hannun yan sanda ne yanzu haka ana kotu."


"Kawa na hannun yan sanda? Shegiya Faree" saurin rufe bakin ta tayi tace "Sorry Dan Allah, gabadaya ban ji dadin abinda ka fada min bane. Duk da ba ma tare yanzu da kawa ina kaunar ta sosai a zuciyata ina kuma yawan kewan ta, kasan haduwan jin..."


Saurin katse ta yayi "Bail mu ke nema, ta bani numban ki in neme ki, tace ko nawa mu ke bukata na bailing in zaki bani" shiru ta dan yi tana kallon wani wuri, gabadaya yanayin ta ya canja "Allah sarki kawa wlh da masharran ta ta hadu da ni na sani. Ka fada ko nawan kake bukata sai in baka, amma babu cash sai a bank. In kuma cheque ne ma toh" hatta muryan da yanayin idanuwan ta sun canja.


"Cheque in mu ke bukata, kudin yana dayawa zai kai millions ba daya ba ba biyu"

"Ko yafi hakan ba matsala" a ranshi tunani ya ke ina su ka samu wannan kudin? Shin na Suhaiman ne ko kuma na ita zeenan? Ba wannan ke gaban shi ba dai a yanzu "Ba kin ce zaki Abuja ba gobe?" Nodding kai tayi, yace mata "tou shknn mu hadu a Abujan zan kira ki,  just make sure kin dauki wayan sannan ina so mu tattauna kan case in amma na ga kaman yanzu kina sauri ko?"

"Mu hadu a Abuja" kawai tace tana shirin mikewa "oh sorry" tayi saurin fada sannan ta koma ta zauna. "Ni fa nayi burin samun wani abu, gashi kuma cinikin mu bai fada ba ya za ayi kenan?"


Confuse look ya aika mata, da ta gane hakan sai tace mishi "ka gane tunda wancan in ba zai samu ba sai a bani wani abu na sa min ran da akayi" dan siririn dariya yayi da yaga gano inda ta nufa "nawa zan baki toh?"


"Tunda maganan kawa mu kayi i won't charge you much, ko 30k ma ai yayi" dariya yayi wannan karon sosai, lallai kudi sauki ne dasu a wani wuraren, wato ita har tayi aikin dubu talatin. Yanzu akan wannan kananan kudin wai su ke saida Jikin su anyhow? Hmmm! Allah ya kyauta kawai. "Send me your account details" ya fada sannan duk su ka mike a tare.

...

Bayan ya gama dukkan wani abinda ke gaban shi, ya kama hanyan Abuja. Yana tafiya yana tunanin yanda zai bullo wa case in zeenah. Ga na wurin Faroukh, zai so ace Faroukh in ya zame mishi shaida sai dai yana tsoron yanayin Faroukh, duba da har yanzu bai amince da Suhaiman ba. Ba laifi akwai kokarin da Dr Fahad ke mishi, wanda ya ke fatan gabatar dasu a gaban kotu har a samu daman bail in.


Yana isa bai ko tsaya wani hutu ba, police station ya wuce domin samun daman ganawa da Suhaima. Yau kam yanayin ta gabadaya ya baci, ta kara duhu sosai, idanun ta sun shige ciki, tayi wani fayau kaman mai fama da wani babban cuta. Kallon ta Barr ya tsaya yi yana jin wani tausayin ta na ratsa shi.


"Yi hakuri ba mu samu daman bailing inki ba" shine farkon abinda ya fara fitowa daga bakin Barristern.


Ko murmushin karfin hali ba ta kakalo ba, fuskan ta kaman yanda ya ke tace "kai fa kace shari'a sabanin hankali ne ina" daga kan shi yayi alaman tabbatr da maganan shi.


"Kun hadu da kawa" ta tmby, kanta a kasa ta ma kasa focusing mai za tayi. Tunani? Ta gaji da hango abinda ba lallai faruwan shi ba, haka kuma ta gaji da tuno abinda ya riga ya wuve kuna ba za ya gyaru ba. Bakin ciki? Wannan ya zama ita domin sun dade suna rayuwa a tare. Kuka kam ya fi karfin ta tun da fintinkau ya ki zuwa mata har ma a cikin wannan bala'i. Rudu da wasi wasi kam ba wanda ba tayi ba. Shiyasa dai gatanan kawai tana jiran yanda kaddara zai yi da rayuwan ta.


"Ban samu daman ganin ta ba sai jiya a kaduna, zamu hadu amma yau a nan za ta bani cheque in"  da kai ta amsa mishi.


"Ina bukatar jin labarin ki Suhaima, i mean abinda ke tsakanin ku da Zayd Al-mansur na ke son sani in details domin in san yanda zamu bullo wa shari'an nan" shiru tayi bata bashi amsa ba, a ranta kuwa tunani ta ke shin ta ina ma za ta fara?


"Ki daure ki fada min daga ko ina nema" furucin shi kaman wanda ya shigo zuciyan ta. "Na san is not easy but we have to talk" ya kara fadi.


"Labari ne mai matukar tsawo barrister, ban jin zai labartu a nan. In munyi nasarar na fita daga nan zan fada maka komai daki daki" ajiyar zuciya ya saki alaman gamsuwa.


"Shknn but bara na miki wasu yan tambayoyi" ba tare da ta amsa ba ya cigaba da fadin "ranar da abun ya afku kina ina ne?"


"Cikin gidan, daga ni sai zayd in a gidan" kai tsaye ta bashi amsa. Shi kam amsan nashi kara daure ma sa kai yayi, amma duk da haka dai ya cigaba.


"Bincike ya nuna anyi poisoning in shi, shin kinsan lokacin da ya ci abincin na karshe kafin  tashin gobaran?"


"Ni na dafa, yazo yace min yana jin yunwa, in taimaka in sa mishi wani abun, so i cook" ba tare da wani tunani ba ta ke bashi amsa, hakan ya ke tabbatar mishi iya gaskiyan shi kenan.


"Kinyi baki ne a ranar?"


"Mutane dayawa sun zo gidan a wannan ranar, sai dai duk sun bar gidan wuraren la'asar kafin ya dawo bayan magreeb shi daya."


"Kaman su wa kenan?"


"Mostly mutanen da mu ke aiki da su ne a karkashin Al-mansur. El-yas, pat, UK, Faroukh da Mr Bash."


"Kuma ba wanda kike zargi, ko kuma akwai wanda ya shiga kitchen inki a ranar"


"Kitchen is available to all of them ai"


"Amma waye last in tafiya"


"Na fita na bar Zayd da Faroukh tare a gida suna tattaunawa akan wani business insu, ban dade ba na dawo amma sun riga sun tafi by then" nodding kan shi yayi a fili yace "this is really complicated, i have to find all of them gsky"


"Amma kinci wannan abincin da kika dafa?" Girgiza kai tayi tace "ya kawo min snacks da shakes, nafi son su akan normal abinci musamman da dare."


Rike kai Barr Mustapha yayi yana jin kan nashi na wani irin sara wa na wahala. A can kasan ranshi wani abu na fada mishi wahalan banza kawai ya ke, anya Suhaima ba ta da sa hannu a cikin wannan lamari? Saurin koran tunanin yayi, shi dai kam ko ma menene yayi niyyan sai ya ga abunda ya ture wa buzu nadi.


"A cikin wadan da kika lissafo wa kika fi ganin zai bani hadin kai in na nemi magana dashi?"


"El-yas" tayi saurin fada "abokin Faroukh ne, best friends dan naji Faroukh in ya sha fadin El-yas ne ya mishi hanyan aikin da ya keyi" jinjina kai Barr yayi, tabbas ya san El-yas kuma abinda ta fada hakan ne.


"Anya wannan zai bani abin kirki? Alamun shi sun nuna he hardly talks"


"He is somewhat reserve" tace hade da dan yin shiru "amma i trust him ya fadi abinda ya sani"

A nan su ka tsaya sannan Barrister Mustapha ya mata sallama ya wuce. A ranar ya ke son ganin El-yas in.

...


Bai da numban El-yas in, hakan ya tilas ta mishi kiran Faroukh ya amshi numban. "Numban El-yas kuma?" Faroukh ya tambaya yana jinjina maganan bayan uncle in nashi ya sanar mishi bukatan shi.


"Ban kira ka min tmby ba Faroukh, just send the number i ask, okay?" Yana gam fadin hakan ya katse wayar.


Siririn tsaki Faroukh ya ja, kafin ya bude wayan shi domin tura numban. Wlh da ba Uncle Musty bane ba, da ba zai tura numban ba. To wai meye sa shi ba zai fuskanci gskyn Al'amari bane ya kyale yarinyan nan? Shi kam Allah bai daura mishi kaunar ta ko na minti daya, sam ba ta mishi, ko dan ya san asalin wacece ita ne? Amma ya san mai zai yi, Maryam zai je ya samu, ko da ba sa shiri ya san yanda mijin ta ke fifita maganar ta, ta hanyan ta zai cima nasara in har ta iya sa Uncle musty ya bar case in yarinyar nan.


Shi ko Barr yana ganin numban, bai ko kara bi ta kan Faroukh ba ya danna wa El-yas kira.

Bayan sun gama gaisawa ne yace "kana magana da barrister mustapha n..."


"Uncle Musty" El-yas yayi saurin fadi. Hakan ko yayi mishi dadi, ko ba komai maganan da zasu yi will not be formal kenan.


"El-yas ina son ganin ka"


"Okay Uncle, amma ina dan wani aiki yanzu ko bayan magrib ne in ba damuwa sai in sam har gida"


"To shknn ba wani matsala ai" barristern ya fada yana mai fatan El-yas ya cigaba da bashi hadin kan da yake nema.


"Sai ka turo min da address" El-yas in ya fada kafin su yi sallama. Suna gama wayan, barr ya tura mishi address in kaman yanda ya bukata.


A ranar duk yanda ya so ganin Zeenah, hakan bai samu ba. Ta bakin ta dai tace mishi tana cikin garin, amma ba su riga sun rabu da wanda su ka zo tare ba. A cewar ta, ya bari gobe in ya tafi tunda maganan su mai tsawo ne sa yi ta.


Duk gajiya ta dibe shi dayawa, da kyar ya samu ya yi wanka. Hakanan ya lallaba ya sa abu a cikin shi ba wai don yana jin yunwa ko abincin na mishi dadi ba. Aa, ya san yana bukatar hakan ne. Shi da kwanciyar hankali kuma ai sun yi hannun riga,  daga nan har rana da zai ga karshen wannan abu da ya taso mishi kwatsam zaune.


Mimin shi yayi kokarin kira ko zai samu wani dan natsuwa, komin kuwa kalilan shi. Sai dai ba alamun ya samu abinda ya ke bukata in, domin mimin kam banda complain in yayi tafiya bai kira ta ba, yanzu ya daina damuwa da ita kaman da. Banda mita dai da korafi ba abinda tayi mai. Gabadaya ji yayi kwakwalwar shi na neman cukurkude wa, shin wai meyesa mata su ke hakan ne? For once ace ba zata taba lura da damuwan shi tayi kokarin kwantar mishi da hankali ba? Duk da ya san halin matar shi, zallar kishi ke nukurkusar ta. Amma koma yaye ne ai ya kamata ace ta fahimce shi ko? "Mimi banda karfin biyewa rigiman ki please am not so well, ina haydar? Duk kuna lfy?" A hankali ya ke maganan yana jin kanshi na wani irin juyawa. Mutuniyar tashi ko maimakon ta fahimce shi, sai kukan kissa ta sa mai, wai yanzu kwatakwata bai ta ita, ya za ta mishi complain ya nuna ma ta bai da lokacin ta.


Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, shine abinda ya furta cikin ran shi. "Dan Allah ki daina irin wannan mimi, wlh kina daga min hankali. What is your focus kuma? Bayan kin san mijin ki yana son ki, duniya ma shaida ce. I love you so much okay? Ki kula min da ku, da ajiyan da na ke fatan nayi kuma"


Sai a lokacin tayi dan dariya tace "i love you much more better love, duk muna lfy. Ajiyan ka kuma nima ina fatan hakan." Dariya yayi bayan sun gama wayan "mata rigima!" Ya furta a fili, duk dai abun dolen shi ya sauko,  ya kwantar da kai,  ya lallaba ta su ka rabu lfy.


Kiran Dr Fahad ne ya shigo wayan shi, likitan ne ya mishi bayanin duk abinda su ke nema yanzu haka yana kan process. Sun dade daga nan duk suna magana akan case in ne. Its an achievement, da su ke kokarin aiki tare akan case in. Duk da ko kowa ya san zuciyan kowa game da yarinyan da su ke kokarin karewan. Sai dai, sunyi matukar kokari wurin kauda wannan su ka tasa ma abinda ke gaban su a yanzu.

Dr Fahad shi har ga Allah, shakuwa ce da fahimtar juna ya ja mishi duk abinda ya ke ji akan Suhaiman. Ya yarda da ita a cikin lokaci kankani. Yayin da shi kuwa Barr, qualities inta ne da ya gani a bayyane, ya ja ra'ayin shi tun farko akan ta. Duk da bai ta taba furta ma ta ba kuwa, ta hango hakan a wurin shi. Tsakanin shi da matar shi kuwa, soyayya ce daga Allah. Shiyasa duk abinda za ta mishi a duniya ta ke cin riban wannan. Duk fa da haka,  bai hana jin yana kwadayin wannan abubuwan da bai samu a wurin ta ba. Yanda ya ke jin son wadannan abubuwan da ya rasa gun burin zuciyan shi, yana jin zai iya aura kowacece kuwa in dai itan zai samu wannan natsuwar a wurin ta.

Ni ko nace Maryam, kalubale a gaban ki babba ma kuwa.

Zaune ta ke hakimce a kujeran office inta, a hankali ta ke faman juyawa. Ta kura wa news post in da ke gaban wayan ta ido. Wani daci taji ya ziyar ci zuciyan ta, ran ta na wani irin tafasa. "Oh Allah wannan wani irin masifa ne na jefa baiwar nan naka a ciki?" A fili tayi maganan, tana kara jin zuciyan ta na suya. "Allah ya kawo miki mafita, kwarai zan so in cece ki, sai dai hakan nima barazana ce ga rayuwa ta. Asiri na zai tonu, mutane za su daina ganin mutunci na. Duk wani kima da daraja da ake bani zai gushe" ita kadai ta ke magana a cikin rantsatsen office in ta da ya sha haduwa da interiors iya interiors. It looks so serene with simplistic beauty. Yanzu haka dai, tana bukatar wurin da za taje tayi cooling mind inta,  inda za ta samu natsuwa da kwanciyar hankali, tana matukar bukatan hakan. Ita haka zuciyan ta ya ke, in dai taji tana son yin abu to cikin gaggawa ta ke aikata shi. Don haka yanzu ma dole ta biya wa zuciyan na ta bukatar ta.+


Saurin daukan waya tayi ta dannawa PA inta kira, ba jima wa ya dauka "i need a morning ticket to Seychelles tomorrow" dan jim PA in yayi cike da mamaki, kwata kwata bai jin tana da shirin yin tafiya kwana kusa. Amma kwatsam! Ta kira shi.


"Such a sudden trip" ya fada, yana tsimayin ta mishi bayanin tafiyan na ta. Instead, ce mishi tayi "please do as i said" tayi saurin katse wayan. Ba ta cika son binciken ba, barin ma a wannan tafiyan, da ta ke jin dole ma ne ta bar kasan har sai case in nan ya sarara koma an gama shi gabadaya. She can't do anything for Suhaima now, tunda ta san akwai kason sa hannun ta a abinda ke faruwa da ita. Tana dai fatan wani ya taimaka ma ta. She can't say exactly ga abinda ya faru, dan ba ta sani ba ma. Tuni ta dauki jakan ta, bayan shi ba ta kara daukan komai ba. Landline ta dauka ta danna wa secretary inta kira. "Yes madam" mercy ta fada bayan ta karaso cikin office in.


"Am going for a sudden short trip, make sure, you tied of this place" tana gama magana ta sabi jakan ta tayi waje, ba tare da ta amssa sallaman da mercy in ke mata ba. Mercyn ba ta wani damu ba, domin ta san yan mulkin inta tashi haka ta ke musu, sai dai ba ta jin za ta iya daina aiki da madam in na ta, domin akwai arzikin kyauta kam.


A gaggauce ta isa gida, dan abubuwan da za ta bukata ta hada. Ba wani yawa gare su ba, saboda ita al'adan tane in za tayi tafiya ba ta diban kaya da ya wuce 2 sets, duk abinda ta ke bukata in ta je wurin za ta yi shopping insu. Magungunan ta dai ta hada wuri daya.


Banda secretary in ta da PA, ba wanda ta sanar wa za tayi tafiya. Zama tayi duk wani abinda ta ke bukata ayi in bata nan tayi drafting sannan ta tura wa PA ta Email. A lokacin ta yi booking in hotel in da za ta sauka,  a Seychelles in. Bayan nan ne PA in ya sanar mata, an samu flight in amma 6:30 am kuma a airport in lagos. Sannan ba one-way sai round trip. "Its okay, get me a last minute ticket to lagos then"


Karfe hudu na safe driver in ta ya dauke ta zuwa Airport. Har isan ta airport in, fatan ta daya,  Allah ya sa ta bar kasan lfy ba tare da wani obstacle ba. Ba su wani dade ba, su ka daga zuwa Lagos.


A wurin kujerun da aka tanada ta zauna a airport in tana jiran a fara boarding. Don rage time ne ta fiddo magazine in interior decorations tana duba wa, coz akwai aikin da za tayi online very soon a seychelles. Time to time mutane na zuwa su gaisa da ita, wasu har requiring yin photo su ke da ita, perks of being a celebrity, she is an an influencer and blogger online. Cigaba da duba magazine in tayi coz she have to make sure everything is going smoothly.

“What a perfect decoration" ta ji an fada daga bayan ta. Kaman kar ta juya sai kuma kawai taji tana son juyawa taga wanene wannan?


Sanye ya ke da glasses karami da ya matukar amsan shi, frame in gabadaya transparent ne don haka ya hade da lens in ya bada kala daya. Kananan kaya ke jikin, shirt in navy ne ta saman aka yi manya layi ash and red in da aka sa tambarin kamfani. Fari ne sai dai bai yi irin mugun hasken nan ba, kana dai kallon shi kasan harda hutu ya kara mishi hasken da ke gabadaya jikin shi. "Handsome" ta fada a ranta, Kallon ta ya ke da kyakyawan murshi akan fuskan shi "it awesome" ya kara fadi yana mai fadada murmushin shi.

She is so friendly so ba za ta iya gwalase shi ba, ballantana ma itan irin mutanen nan ne da su ke entertaining jama'a, ko dan ma business irin na ta ai daman dole sai da farin jina ga jama'a. "It very nice of you to comment, i appreciate" ta amsa shi da kayattaccen murnushin na ta da ke mugun kara mata farin jini ga jama'a.


"You are an interior decorator?" A hankali ta yi shaking head inta tace "am an event planner"


Gyara zaman shi yayi yace "wow! I like your style, if i figure this well you work with interior decorators, photographers, caterers and many different professionals" a natse ya ke maganan, infact ko man shi a natse ya ke.


"You guess right" ta amsa, bai ce komai ba sai ganin da tayi ya mike yana tafiya ba tare da yace ma ta uffan ba har ya dawo gefen ta ya zauna, sai da ya zauna da kyau sannan ya juya ya fuskance ta "am an Architectural Photographer, i don't know ko za mu iya aiki tare? Am going to seychelles nd you?"


Kallon shi ta dan yi sannan ta juya fuska. Suddenly, taji rashin dadin yanda conversation in su ke shirin komawa formal. Girgiza kai tayi tace "am sorry"


Ba tare da ya nuna wani reaction ba yace ma ta "ba damuwa zan iya samu card inki?" Without second thought ta bude hand bag in hannun ta dauka business card inta ta mika mishi "thank you"  ya amsa ba tare da ya duba ba ya sakala a pocket in jeans in shi "see you later" kawai yace da far in ciki bayyana a fuskan shi ya bar wurin ta. Tun tana kallon inda ya bi a cikin airport in har ya bace ma ta gabadaya, tayi tunanin zai yi insisting shiyasa tayi denying offer in shi. Yanzu kam da ya riga ya wuce ji tayi kaman ta je ta jawo domin Sanar mishi she is totally in with the offer sai dai ko kadan ta San ba za ta iya kwatanta hakan ba. Siririn tsaki taja tana mai maida idanuwan ta kan abinda ke gaban ta, duk yanda thoughts in shi ya fitan ma ta a kai hakan ya gagara coz ba ko yaushe ta ke hadu da mutane su yi mata tayin offer tayi rejecting kuma su kyale ta without any persuasion. She pays a lot bayan wannan kuma she is very friendly and accommodating toward duk wani wanda aiki ya hada su, hakan ya sa mutane ke son aiki da ita. Ta fannin ta in dai ka zama mutum mai kula da lura da ai kin shi sosai to ba ka da matsala da ita. Hakanan kawai wani abu ke gaya mata wannan fa ba shi yayi missing offer da ita, Aa, a karon nan alamu na shirin nuna ita ce tayi asaran babban dama da yazo ma ta. Suddenly, sai yaji interest inta ya kara tana son sanin me ya ke bukata a wurin ta. Daga ganin yanayin shi da confidence ya nuna mata shi in ba karamin mutum bane, ba ta bangaren shekaru sai dai ta fannin Naira mai sa mutum suna da daukaka.

Duk yanda ta so ganin shi abun ya gagara, duk da ma ba wani yunkuri da tayi bayan wuce war shi amma ta so kwarai ya dawo ta inda ta ke ta samu daman mishi magana. A haka aka kira boarding, sai a lokacin ta ke tunanin tabbas Seychelles ya ce mata za shi, duk da haka ba ta ganshi ba.

Da ke Ethiopian airline ne flight in, ticket in business class ta siya daman. Settling tayi a seat inta sannan ta fiddo magazines inta tana kara dubawa, a gefe daya tana calculating events in da ke gaban ta duk da ba ta country in. Har aka tashi abinda ta ke ta faman yi kenan, ba laifi tayi progressing sosai. Ajiye su tayi ta dauko English novel in Danielle steel, the cast ta fara karanta wa, it part of her in dai za ta shiga plane to tabbas da novel a hannun ta, tana enjoying karatu sosai a wannan lokacin. She is engrossed in the novel da ba ta ma lura da environment inta, novel like this are so wonderful and lovely to her, sosai novel in ke inspiring mutum. Ba abun da ya dau hankalin ta kaman novel is not centered around budurwa da saurayi, Aa, it talking about babban mace that already yaran ta sun girma sun kama gaban su kowa ya fuskanci future in shi but still the writer got something to share on the mothers life and it amazing.


Kaman an ce ta dago kanta, ta hango shi can gaba da ita. Hankali kwance ya ke operating system da coffee cup a gaban shi a hankali tana sipping.

Seconds ta dauko tana kallon bayan shi sannan tayi saurin dauke kai ta mai da attention in ta kan novel inta.

Awanni masu yawa ya kai su Seychelles international airport da ke mahe island. Aljannar duniya, kirarin da ake ma kasar kenan. Haddaden kasa ne da Allah ya wadata da wadataccen ruwan teku, duwatsuna da tsaunu ka sannan ga bishiyoyi iri iri da ke zama a bakin teku da tsibiri (island) kala kala da su ka cika Kasan. Gabadaya, sai su ka hadu su ka bada wani ni'imtaciyyar ni'ima da annshuwa da ke wadata natsuwa da farin cikin. Sau dayawa za ka iske sabbin ma'aurata da masu yawan shakatawa a kowani sashe na Kasan.

Tun da ta sauko daga cikin jirgin ta ke jin wani natsuwa na daban na mamaye duk ilahirn jikin ta. "Alhamdulilah" ta samu bakin ta da fadi tana mai godewa ni'imar ubangiji ta da ya wadata mutane da wannan Kasa mai cike da albarka. Da lugagges da ba su da wani tawa ta fito daga cikin airport in domin neman taxi in da zai kai ta Victoria, inda za ta karasa Eden island, a nan hotel in da tayi booking ya ke.

Hango shi tayi a can gefe guda shi kadai da camera a hannun shi tana kokarin capturing view in da ke wurin. Murmushi tayi, domin ita kanta ta San da photographer ce ba abinda zai hana ta daukan wurin nan, haka da ita marubuciya ce samun wuri za tayi ta rubuta duk wani yanayi da ta ke ji sanadiyyan ni'imtacciyar Kasan nan kafin ta kara gaba.


Tana cikin wannan tunanin ne ta ga tana kokarin karaso wa inda ta ke, standstill tayi har ya karaso da camera in shi rataye a Wuyan shi yayi folding lips in shi. Irin su ne mazan da mata ba su iya resisting kallo, in kaji ana dream guy, to wannan irin shine gabadaya, wato abinda ake cewa jinin burga, da ka kalle shi zai tafi da kai ga kuma kwarjinin da ke sa ta kasa zuba mishi idanu tana kallon halittan Ubangiji.

"Hey, we meet again" ya fada bayan ya karaso inda ta ke. Siririn murmushi tayi wanda ya kara fiddo da kyan ta, ba fara bace ita amma her skin color is just wow, musamman da ta ke glowing in su da hadaddun creams. Tana kyau iya Kyan ta barin ma in tayi murmushi. Ba siririya bace, sai dai yanayin jikin ta ma kyau ya ke kara ma ta, sai dai kallo days za ka mata kace she is bossy.


Ganin ba tace mishi komai ba yasa yace "Am Faroukh Machina nd you?" Kasa kasa ya ke magana kaman mai rada yana kallon fuskan ta.


"Umaimah Amin" ta amsa tana dan juye juye da kan ta.


" Beautiful lady with nice name, are you heading toward Victoria?" Ya tmby saboda yanda ta ke nuna ba ta son tsayuwan.


"Eden island" ta fada

"Mu je mana, am going there" ba tace komai ba ya kira musu mai taxi su ka shiga. Da farko ba su yi wani magana ba, da ke duk a baya su ka zauna sai lokacin ta ke ganin camera in shi da ya ajiye a kasa da kyau, latest Nikon ce ko shakka babu wannan dan wani kusan ne a Nigeria saboda dai irin harkan sai su.

"Wani hotel za ki" ya kara tmbyn ta.


"Eden bleu" ta bashi amsa, dan cizan yatsa yayi yace "bansan za mu hadu ba da na mana booking a apartment in da zani, nasan you will love it"


"I can come visit" ta fada tana kallon shi alamun is he okay da abinda ta fada. "Sure" ya amsa dukkan suna murmushi cike da annashuwa har su ka karasa destination insu.


...


A daya barin kuwa, kafin safiya. El-yas bai samu zuwa apartment inda Barr Mustapha ya ke ba sai bayan isha'i. Zallan bakin shayi ya iske shi yana sha, suna gama gaisa wa yayi offering in shi shayin, ba musu ya amsa. He looks so calm and cool, shi daman Barr ya mugun yaba wa da El-yas in tun a farkon ganin shi.


"Sorry fa na neme ka kana wani abun" barrister ya fada bayan yayi sipping shayin da ke hannun shi.


"Bakomai Uncle Musty" dan shiru El-yas yayi, yace "naga kai ke kare jewel in mu ai"

Widening eyes in shi mustapha yayi yace "jewel?"


Siririn murmushi El-yas yayi "Oga Zayd calls her that"


"To Amma me ke tsakanin su?" Mustapha ya bukata. Kai tsaye El-yas yace "Employer and employee, then he so much adores her"


"Kana nufin budurwar shi ce?" Girgiza kai El-yas yayi "Probably, amma am not sure. Everybody adores her ai but Faroukh is an exception."


"Kowa ya san tana da halaye mai kyau kenan?"


Gyade kai El-yas yayi "she is so friendly though ba ta cika magana ba, she is kind with everybody. Sai dai wasu na mata kallon mai girman kai, mostly mata ne. amma na fi dangan ta hakan da rashin kula su sosai a zauna ana hira. Faroukh bai taba yarda da ita, ya kan ce min akwai mugun manufa tattare da ita. Bai taba fada min dalilin shi ba kowa da kuwa na tambaye shi" sai dai barr ya gama sauraron bayanin nashi sannan ya fara wani tunani. Ya san abinda zai tmby Suhaima ranar da ya kara koma wa wurin ta.


"Ban san mai ya hada ta da Faroukh ba kam" Barr ya fada, more like kan shi ya ke wa magana.


"On 31st July, wasu daga cikin ma'aikatan ku sun je apartment in da ita Suhaiman ke zama a Asokoro kana daga cikin su?"


"Kwarai kuwa" El-yas ya amsa. "Mun je gidan kusan mu goma a wannan rana bisa ga Umurnin Oga Zayd. Abin da ya faru shine: Suhaiman tayi kwana kusan bakwai ba ta zuwa gun aiki. Oga zayd in ya matukar damuwa da rashin ganin ta a yan kwanakin, to dama a ranar akwai meeting in da za muyi sai ya kira ni, yace min dukkan mu mu same mishi a can gidan. Da ke asali guest house in shi ne. Two flats ne a ciki, daya inda Suhaiman ke zama daya kuma wurin da ya kan hadu da bakin shi. Wato abinda na lura a wannan ranar kaman sun samu wani matsala ne tsakanin su. Ganin mu ya sa ta dole fitowa aka yi meeting in da ita, daganan sai muka zauna hira. To ni dai wani uzuri ya taso min, a gidan na tafi na bar su"


"Ko akwai wanda ya shiga kitchen in gidan ranar?"

Citse lebe El-yas yayi kan shi a sama kaman yana tunani yace "Gsky ba wanda bai shiga ba, ai gidan kitchen daya ne. Tunda na ce maka guest house ne kaga kenan ba lallai kitchen ya zamo daga cikin lissafi ba, duk an shiga, kuma daga masu soya kwai, dafa indomie, sai masu tafasa shayi. Halin Oga Zayd ne haka, he treat all his employers as friends."


"Amma banda Faroukh, ba wanda kake tunanin suna da matsala tsakanin su da Suhaima?"


"Babu ai nace ma ka ba ta cika shiga harkan mutane ba, iya sanina gsky bbu kam."


Banda daure kai ba abinda Barr ya samu wurin El-yas. The more yana kara bincike, the more lamarin yana kara shigar da Faroukh ciki. Kowa ya san Faroukh ya ki jinin ta, to amma miye dalili? Ko da ya san Faroukh in na da baudadden hali amma its unlike him ya dauki tsanar duniya ya daura wa Mutum. Dole ma ya koma wurin Suhaima su tattauna tunda Faroukh in yaki fito mishi a mutum.


"Faroukh yace min asali kawar budurwar shi ce?" Barr ya tmby.


"Eh hakane saboda da ma a gidan su ta ke zama"


Jinjina zancen Barr yayi tayi a zuciya yana mai neman mafita. Sai dai mafita daya ta ke bashi, amsa na wurin suhaima. Kuma in dai tana son fita daga kangin rayuwan da ta ke ciki, ya zama tilas ta buda mishi cikin ta gaba ki daya.

Yana shirin bacci, call in zeenah yayi obstructing in shi. Dole ya dauka, bacci ne sosai a idanun shi, har rufe su ke yana kokarin bude su gabadaya sun mishi wani mugun nauyi ga ya hade mishi da kai. Ita ko zeenah sai faman bashi wani lbr da ba kai ta ke, it doesn't even make sense to him. "Yanzu nan rabuwan dashi, night flight gare shi zai koma jigawa inda iyalan shi su ke. Kaga bakin ciki da ke ranshi? Ga dukkan alamu iyalan na shi ba ma su kula bane kuma ma throughout da mu ke tare dashi ba wani wayan kirki da suka yi, in kaga sun kira to abu ne ya kare a gidan ko kuma suna bukatan wani abu. Ai mata dai..."

"Zeenah please" yayi saurin interrupting saboda shi gabadaya labarin ma ba wai ya wani fahimta bane don bai jin ta.


"Oh sorry, you sound sleepy gobe xan neme ka sai muyi magana, ai kawa tafi karfin komai a wurina kar ka wani damu domin hadin kai..."

"Nagode, zan kira ki goben" yayi saurin fada sannan yayi ending call in. Shi kam bai taba ganin mace  mai surutu ba ma kaman zennan. Ko ta ya ma aka yi su kayi abokanta ka da Suhaima? Bayan itan she is too silent. Shi dai kam wannan sarkakiya na Suhaima na mugun daure mai kai, dole ta samu ta warware mai ko da kuwa itan ce ba ta da gsky ta aika ta abinda ake zargin na ta dashi. Dole daman shi lawyer inta ne ya kare ta ko da cikin wani hali, duk ma bai ganin za ta iya kwatanta aikata hakan.

Shiru tayi tana sauraron shi har ya kawo aya. Sai a sannan ta saki nannauyan ajiyan zuciya tace "zan baka gabadaya lbrn kaman yanda ka bukata. Sai dai ina bukatan wani alfarma in za ka iya min kafin in baka lbrn"

Bai ce komai ba sai dai kallon da ya ke mata ya nuna mata alaman ya yarda ta cigaba, shi dai barr har ranshi ya ke jin farin ciki samun nasaran da yayi a akan ta.

"Ina so Dan Allah in na fara baka lbrn nan kar ka katse ni, kar ka fuskance ni a bai bai haka kuma kar ka min wata tmby har sai kaji bayanin komai daga baki na." Kallon shi ta ke tana bayanin, ido gara rau, shi kam har yau yana mamakin rashin kukan da ba tayi ba duk da tsanin tashin hankalin da ya ke hango wa a idanuwan ta.

"Shknn ba matsala, sai dai kafin ki fara ina son sanin nawa zan amsa wurin zeenah" tabe baki tayi hade da girgiza kai.

"Ko nawa ake bukata za ta baka, kawai ka fada ma ta" kallon ta yayi yana mamakin yanda ta ke da tabbacin za a samu duk abinda ake bukata ko da kuwa yawan su. Kokarin furta hakan yayi.

"In ba za su isa ba fa? Akwai kudin da mu ka hada da Dr da baban su Faroukh ba sai mu hada ba? Sincerely speaking kudin nan na da yawa" ko da ya dago ya kasa karantar yanayin fuskan ta, banda yanda idanun ta su ka fada sosai, tayi wani fayau kaman ba ita ba, har rami kasan idanun ta su kayi, zai iya rantse wa bacci ya dade da kaura a idanun ta. Duk da ana ba ta abinci mai kyau, haka kuma wurin baccin ta ma ba laifi kuma ta tabbatar mishi har wa yau ba wanda yazo da niyyan ma ta tambayoyi.

"Abban haydar" ta fada tana kallon shi tace "kar ka damu, Dan Allah dai kar ku taba kudin ku, akwai more than enough a hannun zeenah, ko da an bar su ba za suyi wani amfani ba da yafi wannan in" iya gskyn ta ta ke maganan, shi kam gabadaya zuciyan shi ya tafi da mamakin shin wani irin kudi ne wannan? A ina kuma ta same su? Sai dai da alaman ta bar ma kanta sani. Katse mishi tunani tayi.

"Zan baka labarin sai dai zan fara daga abinda ya fara hada mu da zayd tunda a yanzu shine focus inmu" gyade ma ta kai yayi kawai ya gyara zaman shi yana mai kara fuskan tan ta. Kan ta a kasa ta fara bashi labarin kaman wacce ta ke karatun jarida ko wani littafi.
...

Uzuri, kalma mai mahimmanci da mutane kwata kwata ba sa wa Dan adam a zamanin nan. In ka ga mutum a cikin wani hali na kazanta a rayuwar nan in ba ka mishi fatan shiriya ba to ko tabbas kar ka zage shi. ba wanda ya san rubutaccen kaddarar shi da ta ke jiran shi a cikin littafin rayuwan shi. Kowa da irin yanda tashi za tazo mishi haka kuma da irin yanda zai kokarta wurin cin jarrabawar shi.
Da can a baya na kazanci masu hali irin nawa a yanzu, na yi Allah tur da wadai dasu. Duk a tunani na ba wani kaddarar rayuwar da za tazo in afka cikin rayuwa irin wannan sai dai ina nayi kuskure, jarabawar tawa dole tazo da hakan.

Lagos, Nigeria.

Yau ma kaman kullum zaune na ke a katafaren gidan rawan (club) in da ke birnin lagos a ikeja. Hankali kwance ba tare da nayi la'akari da daren da ya ja sosai ba. Kaman ba nice Watannin baya da su ka shude kafin yau in na ke dar dar da zaman wurin ba gabadaya na kasa sakewa. Kallo na kara bin gabadaya wadanda ke wurin da ke ta faman rawan su hankali kwance ba tare da an damu da cudanyan da ke tsakanin maza da mata ba kaman yanda ake yi a arewacin Nigeria. Amma nan al'adan su da dabi'un su ya sha banban domin daga musulman har arnan hade su ke hankali kwance suna shan rawan su mai hade da kida da ke matukar tashi,  rawa ne na musamman da ya zama jiki anayi duk dare,  mawakan su dayawa na halattar wurin. Kalolin giyan da ke wurin ko ba a magana balle kuma a kai da irin rawan shafa jikin da ke gudana tsakanin mace da namiji. In har budurwa ba ta zuwa irin wadannan wuraren to ganin mai duhun kai a ke mata shiyasa kowacce ke kokarin halarta wasu ma kawai don su faranta wa samarin su ne. A arewacin Nigeria ne za kaji wai don saurayi yaga budurwa a wurin rawa zai dauke ta yar iska ba zai iya auren ta ba ko da shi in ma yana zuwa. A can ko hankalin su kwance duk abinda zai gudana tsakanin su da mace ba zai hana su auren ta in dai suna son ta. Kawai dai sai dai ace auren ba Albarka sabida ba a gina shi akan turba mai kyau ba. Yau a irin yanda rayuwa ta juya min kenan. Na ruga na sawa raina ba abinda zanyi yanzu in canja hakan, kwalban da ke gaba na na dauka na cigaba da kwankwadan abinda ke ciki. Tunanin kowa a wurin giya ce na ke sha sai dai abinda ba su sani ba har wayau shine na kasa sabawa da shan shi duk barikanci na,  ko dandanon sa tada min zuciya ya ke. Barni dai da duniyanci amma shan giya kwata kwata na kasa iya sa.
Tsit naji wakan ya tsaya a sandiyan salon kidan da aka canja zuwa wani slow motion,  ai ban san lokacin da na mike a hankali na nufi tsakiyan filin ba. Ihu kake ji yana ta faman tashi a wurin yayi da bakin su ke faman furta "Pul-chri-tude! Pulchritude! Pulchritude!" Cike da farin cikin ihun support in da na ke samu na karasa tsakiyan filin. Cikin da natsuwa na fara juya kugu na ina wani irin rawa na daban da ba kowa zai iya shi ba a wannan wurin. Rawan ne na musamman da masu irin jiki nawa kadai ke iya wa,  wanda shi ne asalin sunan da na samu wato pulchritude "physical comeliness"  saboda irin tsarin kyaun halittan jiki na. Tafi ne raf raf ke faman tashi a cikin mashayan nan yayin da na ke ta faman canja salon rawa na na daban kidan na kara shiga na. Ba wanda yayi kokarin shiga sanin yana shiga zai katse min juyin da nake, haka tsari na ya ke ba wai na cika rawa da kowa bane. Carab naji an kamo hannu na ana kokarin juyawa da nayi. A harzuke na dago idanun inga wani ishashen ne ke kokarin min katsalan da a harka na. Ina hada ido dashi duk wani ruwan bala'i da na tara zan sauke mishi ya kau,  sai ma replacing in shi da nayi da wani kayataccen murmushi cike da kunya na dukar da kaina kasa. "Can i dance with you jewel?" A kunne na ya rada min maganan. Ban amsa mishi hakan ya bashi daman kara jawo ni jikin shi, a bisa dole na biye mishi mu kayi rawa. Fahimtan da yayi na kasa sakin jiki in yi rawan da shi ya sa ya jawo ni mu ka bar filin tuni ko wurin ya dinke da mutane "ina kawar ki?" Ya fada yayin da idanun shi ke scanning hall in yana neman Amal. Can na hango ta gabdaya hankalin ta da natsuwar ta zuwa yanzu ya fara gushewa. Da gudu ya isa gare ta tun kafin in gama nuna mishi inda ta ke. Kaman jaririya haka ya dauke ta a hannun shi muka nufi mota. Mika min makullin yayi ya shiga baya tare da ita,  ni kuma na ja motan mu ka nufi Apartment inta da ke banana highland.

Wannan daren shine mafarin komai kuma shine sanadi da ya kawo aya a walwala da farin cikin sabuwar rayuwar da na shiga. Tun a mota na lura da irin kallon da Zaid ya ke jifa na dashi kadan kadan yana dauke kan shi.
Daki na na nufa kai tsaye sanin duk ranar da Zaid ke gari ba a gane kan Amal. Duk wani hiranmu sai ya tafi za ayi shi. Na fito daga wanka kenan da towel a jikina ina goge kaina da head towel naji knocking a kofa. Kusan knocking in da bude kofan duk a tare yake don haka ban samu daman suturta jiki na. "Ouch! Sorry ashe dressing kike" ya fada yana kare min kallo. Kallo na ya ke sosai bbu alamun daukewan idon shi, wuri ya samu ya zauna akan sofa in dakin yana cigaba da karemin kallo. "Ki sa kayan ki mana" ya fada yana maida hankalin shi kan wayan da ke hannun shi yanzu. Da ke gown ne nightie in ta sa ma kawai na sa shi sannan na zare towel in.

"Bestie ta ja min kadaici bayan ta sani zuwa tun daga Abuja" idon shi a saita kan fuskana ya ke maganan. Furucin na shi ya dan so ya bani mamaki,  duk sanda ya iso garin yawanci a irin halin nan ya ke samun Amal don haka shima ya ke biye mata ya sha sosai a haka su ke kare daren. Tun asali ma shi ya daura ta a hanyar duk wani abinda ta ke sha a yanzu haka.

"Eyyerh sorry" cike da duniyanci nayi magana saboda haka yayi kokarin sauya akalan zancen.

"We miss your drinks fa, Ya kamata ki koma Abuja hakanan"

"Next week zamu je da frnd ai"

"Jewel let talk about you mana. Kinsan kina da kyau sosai kuwa? Slowly am realizing how the word pulchritude describes the entire you"

A duniyance na aika mishi da wani irin kallo "Allah koh?"

"Am been serious here Babe Don't tell me ba ki taba lura da irin kallon da na ke yawan aika miki ba" tabe baki nayi ba tare da na juya na tanka shi ba.

"Ina son ki fada min alakar ku da Amal domin ban yarda cewa Ku yan uwa bane kaman yanda ta fada min. Amal ba ta min karya ban san meye sa ta min akan ki ba"
"Ba sanin alakarmu bace abu mai mahimmanci Zaid. Ina ganin sanin dalilin yin karyan shi yafi kamata ka bukata"
Kasa maganan yayi sai dai murmushin da ya ke jifa na dashi ta isa tabbatar min ya fahimci rainin wayau na ke mishi. Kaman wanda aka tsikara yayi saurin tashi daga kan sofa, ido ya kura min sosai sai kace cinye ni zai yi. Sai kuma ya hawo kan gadon da nake zaune yana mai saurin nade kafafuwan shi ya iso gab inda nake. In duniyan ci ne zuwa yanzu ba wanda ban gani da idanuna ba,  Hakan ya sa ko dar ban yi ba na tsaya in ga gudun ruwan shi. Wannan karon direct tsakiyar idanuna ya ke kallo,  ni inma kurawa mishi na mujiyan nayi ina son gano manufar shi sai dai duk yanda na so karantar idanuwan shi na gaza fahimtar me ke damun shi. Ganin abun ba na kare bane ya sa nayi saurin janye nawa idanuwan. Wani rauni naji ya mamaye zuciyata,  Tabbas akwai wani abu da ke cikin idanun dan adam da kallon shi ke haddasa fitina. "Meyesa kika dauke idanuwan ki? They are so lovely" yana maganan ya jawo hannuna yana wasa dashi. Kasa ce mishi komai nayi, ban san dalili ba naji jiki na yayi wani sanyi.

Akwai girmamawa da mutunci sosai tsakanina da zaid Almansur da ba zai barni in aikata abinda na zuciya na ke ayyana min ba a halin yanzu. Sai dai abinda ya min ya zo min kwata kwata a baza ta. Jawo tafin hannuna yayi ya sa yatsan shi yana wasa da shi, pecking yayi a hankali yace "what a skin! So cutee" da idanunwan shi da yayi lum lum kaman mai jin bacci ya dago ya zuba kan fuska ta,  alamun shi ya nuna aminci ya ke nema daga wuri na. Cikin natsuwa na girgiza mishi kai. Kaman dutse haka na ke jin zuciya ta, Sam ban ji alamun tsoro sai dai duk da hakan har raina banji zan iya barin shi aika ta abinda ya ke kokarin yi, ko don saboda Amal,  i so much respect both of them. Kara jawo hannun yayi wannan karon ta gaba, kaman mai karantar wani abu a wurin... "Ya zai..." Sumbar da ya kai wa hannun ya katse min maganar da na ke shirin yi. Kissing wurin hannun ya ke sosai,  kaman an zare min lakka haka na ke jina. Fara kokarin kwace hannun nayi ganin abin ba na kare bane. Sai dai duk iya karfin da nasa na kasa raba hannuna da bakin shi. Daya hannun na sa akan shi ina kokarin dago shi, sai dai hakan ma yaci tura. Kaman karamin yaro ana kokarin raba shi da abin wasa shin haka ya ke claiming hannun yana ciga da kissing. Rau rau nayi da idanuna "Ya zaid please leave me Dan Allah" ganin reaction ina da gaske na ke kin abinda ya ke aikatawa a gare nin ya sa ya dago a hankali.

"Am sorry jewel ba abinda nayi niyyan miki Allah,  wannan inma i couldn't help it ne" harara na watsa mishi "i respect you please kayi kokarin girmama wannan"

"Shknn naji nagode"

"Then get out please" pointing kofan nayi da yatsa na.

"Zan fita But you need to here me out" ganin he is serious ya sa na maida hankalin nawa gare shi.

Hannun shi ya daura kan cinyen shi ya kara fuskanta na da kyau "i have a wife, sunan ta Amina. Cousin ina ce, tun muna kanana aka mana aure a lokacin muna ganiyar soyayyan mu da Amal, na sota sosai sai dai a wannan lokacin fir iyayena su kaki yarda suna nema min auren ta. Daga baya bayan mun kara girma still na nemi auren Amal, wannan lokacin kuma iyayen ta ne su kaki yarda da auren,  ba yanda ba muyi ba still they objected. Su ka raba mu amma as you can see bamu rabu ba. Amma kin san abinda na ke ji yanzu?"

Kallon shi kawai na ke ban ce kala ba shi ma kuma bai jira amsan nawa ba ya cigaba "Wlh yanda na ke ji akan ki,  kaf duniya ba abinda ya isa ya raba ni da ke. Ko iyaye na ko naki ba wanda ke da wannan ikon. Ban taba jin abinda zuciya na ya tafi gabadaya akan shi ba kaman ke. Tun ranar da na fara daura ido akan ki na ke jin zuciya ta na doka miki, ina miki irin soyayyan da ban taba wa wani mahaluki a duniya,  babe i so much love everything about you and i can fight the world for you. No one can stop me not even Amal or Amina"

Garau rau na ke kallon shi. Ko kadan ban yi mamakin abinda zuciya na yaji min ba. A dan sanin da nawa maza wannan ba wani abun rashin kunya bane a wurin. Abu daya na sani tabbas ba za ayi wannan rashin kunyan da ni ba. Wannan karon tashi nayi da kafa na, inajin saukan idanuwan shi a kaina har na isa bakin kofa. A hankali na bude kofan gaba daya. "Please get out" na fada ina nuna wajen. Murmushi mai ciwo yayi sannan yace "kar ki damu am going out"

Amal Idriss Hayatuddeen, diyar wani mashurin mai kudi ne da ya ke zama a garin Abuja. Mahaifin ta ba dan siyasa bane sai dai duk da haka siyasan ba ta damawa sai da irin shi. Mai kudin ne na gasken gasken domin yawancin estates in da ke birin tarayya da ma lagos da sa hannun kamfanin shi a ciki. Yana da kudi na ban mamaki, wanda shi kanshi ba zai ce ga sirrin dukiyar na shi ba domin kuwa ba iya gine gine kadai ya sani ba. Duk wannan dukiyan na shi yara uku kadai Allah ya azurta shi dashi tare da matar shi daya uwar yaran.

Salim ne babban dan shi sai Amal sannan Aliy. Shi jarrabawar ta shi akan yara ta fada mishi. Salim yayi auren har da yara sai dai kuma hakan bai hana shi bin mata, yanda ran shi ya ke so ba. karatun ma da kyar aka samu ya karasa saboda shaye shaye da ya sa a gaba,  an sha koran shi makarantu da dama da kyar ya hada harda masters ba tare da wani result in azo a gani ba. Baban ne ya mishi komai na aure hatta gida da abincin da zai ba iyalan shi shi ke daukan nauyi. Da gan gan ya neman mishi aiki a karamin ma'aikata da niyyan sai yayi hankali zai bashi aiki mai kyau, kiri kiri ya nuna albashin ya mishi kadan yaki aikin, natsuwan ma ya kiyi, har wayau baban nashi ke ciyar da iyalan shi.

Amal ko mace ce mai rauni ga dan banzan kyau mai jan hankali, sai dai ba ta bin mazan bar ta dai da bin club club tana rawa da shan dukkan abinda ya zo gaban ta. A kullum shaye shaye kara karar da ita ya ke. Son duniya Wa Zaid ta ke ma wa duk dai iyayen ta sun sha alwashin ba za ta taba auren nashi ba,  a cewar su halayen shi ba su da kyau ko su ba su yi la'akari da irin nasu yar bane.

Shi kam Aliy kan kat dawowa kasan ne ya gagara,  shi kam ba irin karatun da bai yi ba,  degree kala kala a fanni daban daban. Kusan shi ya biyo baban shi ta fannin iya neman kudi, he is creative on his own yana earning kudin shi sosai, ko da yana shan abu to tabbas ba addiction. He is so responsible sai dai ko kadan bai son maganan dawowa Nigeria, he is so used to the outside countries. Ko kadan bai damu da sha'anin iyayen ba balle yaji halin da su ke. In za ayi watannin in ba su neme shi, he never care to check on them.

Abinda zai baki mamaki shine yanda gidan su ke ciki da mutane,  yan mata da samari,  Yaran yan'uwa da abokai kala kala ba wanda bai zama a gidan nan. Shi kanshi he can't count the no of mutanen da ya ke sponsoring a Nigeria da outside countries. Kai har friends in yaran shi na zuwa su zauna a gidan son ransu.

Post a Comment for "LABARIN RAYUWATA CHAPTER 3 BY Ayeshay bee"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...