KUDA WURIN KWADAYI🐝 CHAPTER 1 BY FATEEYZAH MBS - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

KUDA WURIN KWADAYI🐝 CHAPTER 1 BY FATEEYZAH MBS

KUDA WURIN KWADAYI🐝 CHAPTER 1 BY FATEEYZAH MBS

- - Post a Comment

 KUDA WURIN KWADAYI🐝 CHAPTER 1 BY FATEEYZAH MBS

ALHERI WRITERS ASSO.          A.W.A https://www.facebook.com/Alheri-writers-association-100452175039849/


https://chat.whatsapp.com/JcwN25cbC4PB0DUkvu7TtY
*KUDA WURIN KWADAYI🐝* *_Na Fateeyzah mbs✍️_*


 *_Marubuciyar gidan nagoggo da doctor zahrah_* _Tukwuicine ga 'yar mallawa(hasina bammali),marubuciyar jarababban namiji_🥰*_Bismillahir rahamanir rahim🙏_*


 _I am back, after a long break of 1year, wanda nazo muku da wani zafaffen (kuda wurin kwadaya), ku baza kunne tare da bina daki²._ 

_______________________________

 *Page 1* 


 *Monday 23rd Nov.2020* 


 *9:00pm* Yanayin garin shi zai maka nuni da cewa ruwan sama bai dade da gama daukewa ba, saboda yanda ko ina yake a jike, yayin da reshen bishiyu ke motsi saboda iskar da take kadawa, ga kuma wani irin sanyi wanda  ke shiga cikin jiki.


Idan kuma ka kai duba da anguwa, zaka fahimci unguwa ce ta masu hannu da shuni, saboda yanayin gine² gidaje na alfarma da hasken wutar lantarki ya haske ko wani gida, ga fulawoyi na kadawa, sannan ga fitulun bakin titi, wanda suka yi matukar kayata unguwar.


Tun daga nesa zaka ji  karar siren (jiniya)wanda ke na doso wa cikin wannan unguwar, yayin da  na hango wata budurwa nata zabga gudu, kamar ranta zai fita, jiniyar kuma nata  tinkarota, ganin haka ne ya sa ta shige wani  dan tsukun layi, wanda shigewarta kenan, motocin 'yan sandan(police) dauke da jiniya tazo ta wuce da gudu, sai dai ba a dauki  dogon lokaci ba, suka kuma juyowa tare da tsayawa dai² dan tsukun lungun nan.


Ganin haka yasa na tattara alkalamina da littafina na nufi wurin, don ganin kwam😆, domin na samu na tsarabar dawowa ta hanyar fesa muku.


Jin karar jiniyar ta kuma kusantowa gareta, yasa cikin tsoro ta bude wata kofa da take kusa da ita ta kutsa ciki cike da tsoro don samun maboya, wanda Allah ya bata sa'a  ta kasance a bude, kallon mamaki tabi wurin dashi bayan ta shiga ta rufe kofa a hankali, wani wargazaizan parlour ne, wanda ya kusa tafiya da numfashinta saboda tsaruwarsa, bai da wani tarkace, illa Royal chairs(sky blue) set daya dake zagaye da parlourn, sai plasma a jikin bango hade da reciever(GOTv), sai hadadden carpet dake shimfide a tsakiyar parlourn, daga dayan gefen kuma, wata hadaddiyar cupboard ce, wanda ke dauke da wasu manyan littattafai.


Duk cikin  bai fi minti goma ba ta kare ma parlourn kallo, ganin wata kofa, daga jikin parlourn ya sata nufar wurin, sai dai tana daga kafa kafin ta sauke taji taci karo da wani abu, wanda ya fitar da wani irin kara, hakan ya sata kasa motsa dayar kafa, yayin da zuciyarta ta shiga lugude, wanda wani tsoro ya dabaibaye ta.


Jin karar bude kofar ya saka cikinta wani kara, tare da karkarwar jiki, sai dai daga idon da tayi dai² kofar, ya sa ta runtse ido tare da kufcewar wani irin zazzafan fitsari wanda ke rike a mararta tun bayan azahar saboda rashin kwanciyar hankalin yinshi.......... _Ya kuka ji salon nawa?_ 


 _Wace ce ita?_ 


 _Sannan me ta gani ya saka ta wannan kaduwar?_ 


 _Ku biyoni don jin yanda zata kaya._  _Taku a koda  yaushe_ 

 *_Fateeyzah mbs✍️_* *Comment* 

 *Share* 

 *Like*

Post a Comment for "KUDA WURIN KWADAYI🐝 CHAPTER 1 BY FATEEYZAH MBS"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...