HAMADA BOOK 1 CHAPTER 9 BY ZAINAB KABIR BIROMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 9 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 9 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

- - Post a Comment

 HAMADA BOOK 1 CHAPTER 9 BY ZAINAB KABIR BIROMAN


                Www.bankinhausanovels.com.ng 


MUN TSAYA 

Sabuwan ta san komai ta hadota da wannan jidali har ma ake shirin janyo ma ta asara, ko don kawai sunanta Sarai? Www.bankinhausanovels.com.ng
To kuwa babu shakka bata zamo mai daukan hasara ba. .
Haka al'amura suka ci gaba da faruwa, babu tausayi bare nuna tausayawa, aka barta da ayyukan da komai cikakken Karfi sai yai namijin koKari kafin ya iya cimma rabinsa, balle ita da take dauke da lalura, larurar da babu wani da ya sani Sai ita sai ko Allah da Ya halicceta. A dai wannan Kasa da ta ke cikin Www.bankinhausanovels.com.ng

Ta kode, ta rame, ta fita hayyacinta. A lokacin da Karima tuni duniyar ta gama saisaita a gurinta, tana da ra'ayin Sarai, dama da ra'ayin ne ta iso Kasar ta Saudi, don haka ma sam ba a ma sha wahala akanta ba sai damman take bubbugowa Sarai cikin jin dadi.
Sai ita daya Kwal ce data zame mata Jangwam-gwam! Zako su hadu da Sabuwa

ZAMU TASHI 

ranar da suka yi ido hudu matuKar ta nuna turjiyar biyanta hakKinta. Babbar sana'ar Sarai bai wuce kawalcin ‘yan mata ba. A kawo yara daga Najeriya har da ma _maKoftanta ta fanshesu da damman kudi masu _~ yawa jaka-jaka na Sa'udi, Ya dai danganta da gogewar yarinyar, ta kan musu komai daga bisa sai a shiga cin kasuwa . Inda a Karshe ta kan tashi da babban kaso (riba). Ko da yake a bayan wannan akwai . Boyayyiyar sana'ar da take aiwatarwa cikin sirrri. Tayi aikin da ya zarta Karfinta, aka kuma . kasa ba ta abin sakawa a baka. Ta mike cikin jin zafi, kawai sai ta hankado hamshaKin farantin a gabanta, ta yi mata nuni da idanu, idan taso ta dauka. Yagana ce! . Ta mike tana kwadowa Hajiyar wani kallon biyu-babu. Alal hakika ta gaji, ta gajiya da wanann dabi'ar, an mai da ita tamkar wata karya.

Www.bankinhausanovels.com.ng

A kufule ta ke fadawa Hajiyar sa'ilin da ta shiga daki domin kintsa kiran wani Kasurgumin Alhaji da ya kama kafada da Hayiyar.
Hajiyar na son tankawa a dangane da — abincin da aka baiwa Zalihar, shakkun idanun Yagana ya hana, sai kawai ta bige da hararta.

Ta sha samun afuwa Karkashin inuwar kyakkyawar yarinyar, ta sha ta rabeta donta huta duk cikin albarkacinta, ba ta taba ce mata ba, wani lokaci ma ta dinga dubanta kamar a shake, ita — din ma shakkun ta dubi idaniyarta take. Ta dai lura da wata irin yarinya ce mai murdadden hali, wani lokacin ta zamo sanyi, wani lokacin ta zamo zafi a gareka.

Haka al'amura suka ci gaba da faruwa, ta zamo tamkar baiwa a zamanin BAUTAR BAYI.
Ta kode, ta rame, ta fice hayyacinta, shi ya sa ma Karima take shawartarta ta bi zabin
Hajiyar mana ko ta huta. Rashin wayo da rashin sanin makama Hajiyar ta firgitar da ita daya, ta nunar da za ta
saka Askarawa su kamata su hukuntata su azabtar da ita a Karshe su aike da ita gida, domin kuwa tana zaune ne ba bisa Ka'ida ba a Kasar su, sabanin su da suke da cikakken 'yancin zama a Kasa, idan ma ta yi nufin tserewa a hannunta ne a hanya su kameta a sauki. Idan mata tsere din wa take dashi, ina take da shi, ina ta sani, ina kuma za ta je din?” Abin da zuciyarta ke saKawa ke nan. Tsabar wahala ce ko kuwa Kaddarar al'amari ne? Mararta ta dinga murdawa, baya da Kugu yanai ma ta wani irin ciwo mai radadi, ta wahaltu da yawa, ta fice hayyacinta, abin tausayin ita daya ce Kwal! a gidan, Hajiyar ta yi bulaguro zuwa Dammani (daya ne daga cikin biranen Saudi). Mazauna gidan kuwa kowa ya wuce inda ya ke jin zai fissheshi. .Yunkuri daya, biyu, jini ya tsinke ma ta, ta yi yuuu...ta yi Kasa rikicaaa....a lokacin da take yunkurin shigewa Bayi. Fit! Wani abu ya yi.  tsalle ya fito daga jikinta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Dai-dai da isowarta cikin rawar banjo, ta yi taga-taga. Ta ji tsoro matuka  kamar ta fadi.

YAGANACE!

Zaliha ce ta dubeta cikin lumshewar ido.

"Allah Yana son mai taimakon. dan uwansa! Hadisi ne daga bakin Manzon Rahama (SAW)....duk wanda ya rufawa wani Musulmi asiri to shima Allah zai rufa masa asiri a duniya da lahira.Allah na taimakon Bawa matukar bawan_ nan bai gushe ba yana taimakon dan uwansa." Kada ki damu da aibuna, kada ki damu da wannan al'amari da ki ka duba, ki taimakeni domin Allah. :Ba yau ki ka saba ba, bayau ki ka zamo garkuwa a gareni ba....Shi ke nan abin. da ta iya_ furuci. sakamakon murdawar da Mararta take ma ta. Ko cikin barikinta ba ta taba duban irin hakan ba, dan mutum sukutum! guda!! Babu shakka dan mutum ne, duk da kasancewar yana amatuKar KanKanta ba a kuma Karashe halittarsa ba. Wai sai ga jikinta ya shiga Bari, a lokaci guda ta yi JAN HALI tayi tinanin hatsarin da ke tattare da hakan.  Ta hade ta tattare don tayi kana ta cira ta sama ta saki shawar ruwan zafi a bayi ta cika kwanon bam! Kana ta ja Kofar ta bame. Kafin wani lokaci ta gama gayyata komai, ta haKa rami a can bayan gidan da yake da dan rairayl ta tura dan tayin ciki kana ta gyare gidan_ tas A lokacin Zaliha ta gama kintsawa, ta taimaka mata da abinci dana sha har ma da sutturar arziki. "Idan kin so kya iya mai da komai ba komai ba, ki wartsake ki ci gaba da al'amarin Www.bankinhausanovels.com.ng gabanki". Shi ke nan ta fice abinta cikin rawar banjo.
Yana daya daga cikin abubuwan da ba za ta taba mance Yagana ba, har kwanan gobe Yagana ba ta taba bin bahasin al'amarin ba balle ta tuhumeta.
“Aiki ne babu fashi, babu dagi ko KanKani a tsakaninmu, idan ma macewa za ki yi ba ciwo ba ki mace ki wuce ko hakan ya rangwanta min zafin hasarar da kika jazar min". A wani barin ai kin samu Kazamar riba ban da abinki Hajiya?" Yagana ta fada cikin shagube sa'ilin da take shigowa gidan.Hajiyar ta dubeta. Ita kam ta yi tsaye akanta Kerere ba tare da tsoron komai ba. "Babu ko KanKanin tsoron Allah a cikin gudanarwar al'amuran Hajiyar, ta lura da kyau. Ai kin kai ba sai kin ce min ba balle ki nuna min rashin ta ido". Hajiyar ta fada a hasale, don kuwa ta soma gajiyawa da rainin da Yagana_~ ke kawo ma ta. a idan ma ban kai ba-a wannan rana zan kai ne."Wai sai ta shiga umartar Zaliha ma za-ma za ta hada komatsanta, ranar ‘yanci, ranar buwayar saran Jibiya. Daman can ta gajiya da zama karen farauta a KarKashin inuwar Hajiyar, al'amarin na mata ciwo na yadda aka mai da ita karyar dole, don haka ta dubeta da kyau. "Kwarai za mu Kaurace mu kauce miki ko ma samawa kanmu ‘yanci.
Idan ba ki sani ba Hajiya bari in gaya miki, kece Mace guda daya tak! da na tsana, na Kara tsana, na ke matuKar Kyamata Ina miki albishir ba zan taba mancewa da ke ba, domin kuwa ke ce silar gurbacewar rayuwata. Ke nan ba laifi bane don na Kware na kwankware a hannunki na kuma yi haramar samun gashin kai. Anan kam naje nayi mai lasisi
Hajiyar ta hasala, ta Kara hasala. Yagana ta daga mata hannu. : "Kin bari DAN ZAKI YA GIRMA! Ya girma har ma ya tsere sa'ar Babansa! Www.bankinhausanovels.com.ng
Lallai kam akwai abin da Yagana ta taka. Hajiya ta yi sake Yagana ta gama sanin sirninta.
Take ta samawa kanta lafiya, domin kuwa * ta yi barazanar za ta fashe Kwan kowa ya huta duka su yi hasarar zaman su a Saudi, idan ma da hakan za ta faru da sauki, kasancewar suna iya rasa rayuwarsu dungurungum! baki daya. Wulakancin da aka tanadarwa mai Safarar miyagun Kwayoyi ke nan, wanda yake da hannu a ciki wai ko da za ta kwabe ma ta shafe su. Anan Hajiya Sarai ta shiga zubar da gumi. Babu shakka ta debo ruwan dafa kanta. Allah Allah take Yagana ta kauce da Karmashasshiyar yarinyar nan (Zaliha) ko ta sami jini ya gudana a zuciyarta.
Bayan Nuzuha ba cikin gari bane. yanki ne da ke nesa da Kwaryar Birnin Jedda, anan ta kama musu gida sabo da ya danfi rangwame, _ dawainiyar komai da komai har da kudin hayar gidan ita ke musu. Ta yi jinya, ta yi tallafi, ta yi
taimakonta, tayi mata taimakon da komai butulcin zuciya ba za ta taba mancewa da shiba.

*********

Da idanun Rahama ta dubeta. "Ina sonki da alkhairi, kusan duka kin hada aiyukan kirki, me zai hana ki tuba ga Ubangijinki ki zamo ta Kwarai?" Ta dubeta da matuKar sanyi. “Al'amarin ya zame min dole. Ban fito _daga yankin mu ba (Barno) sai da wannan nufi, ya zamo wata babbar al'ada a Kasarmu, 'ya'ya mata sukan zamewa iyayensu wata babbar HAJAH! Suna matuKar alfahari da kyawun da Allah Ya baiwa diyansu, don haka ci da sha da . komai na su duka ya ta'allaka ne a wuyansu. Ban cika damuwa .ba da sanin su da yardarsu nake gudanar da wannan sana'a, kawai dai na gajiya da kasancewa a KarKashin inuwar _ bauta ne Www.bankinhausanovels.com.ng
Hakan ya sa na samawa kaina ‘yanci domin samun zarafin gudanar da al'amurana a lokutan da nake ra'ayi ba tare da tilashin wani ba balle ayi KoKarin mai da ni wata karya!"Zaliha ta Kara da yi ma ta nasiha.
"Babu biyayya a cikin sabon Allah. Ki bar wannan dabi'ar ba ta da_ kyaul" "Shi ke nan idan na bari me ki ke son in kaiwa Iyayena da suka dogara kacokam! a kaina?"
Zaliha ta dinga nusar da ita da tsoratar da ita azabar Allah. Sai Yagana ta dinga ganin lallai Zalihar gaskiya ta ke gaya ma ta, kamar ma babu wani da ya taba yi ma ta irin haka, a tun ranar da ta sako Kafafu a Kasar ta Saudi. .
Wasa-wasa sai ga Yagana da kutsawa sosai cikin Jeddah Market, tsoffin kasuwar Jidda inda galibi Ajnabai ke cin Zahama, daman dai ta sani, sai dai ana duban kamar sana'a ce ta wahalar da kai ga tarin KasKancin da ke cikinta. . Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai ga Yagana ta samo dabar tsinto Karafa da tasa a cikin kasuwar Haraj a siyar a sami ‘yan Riyalai
Haka nan ta kutsa sosai cikin tsoffin kasuwannin dai na Birnin Jeddah kamar su Saug al-Asor Sauqg Al-Badi, Bediyus, Sauq_ alBaragheeya, Sawy Al-Alawi. Dukkaninsu tsoffin kasuwannin Jedda ne, kasancewar an gina sababbi na zamani, sai dai kuma ana matuKar samun fa'ida a ciki, kuma sun yi nufin cin Zahama ne ta fannin matarin Kafafu (Takalma).
Anan kam babu inda suke nufa face Soug al-Nada (dew), wani lokaci kuma su mutsa Saugq © Al-Hababa da ke cikin Bab-Makkah, ko kuwa kasuwannin Kauye na Larabawan Saudi wato Balad Market, nan ma ana mutuKar samun fa‘ida, in ta dauro ma wani lokacin a nutsa Banga Fish Market, Kasuwar. Kifi ta mutanen (Kasar Bangaladash, wani lokaci ma kayan Miya da kayan Lambu, Jeddah Fruit & Veg. Market.
"Nan din ma ba a barsu a baya ba suna samun fa'ida sosai su zo su siyarwa da Takari masu sai da Abinci.
A hakikanin gaskiya ana matuKar samun fa'ida a cikinsu sai dai ba kamar Haraj ba. Dalilin ke nan da galibin Ajnabai suka fi yawan nacewa kasuwar ta Haraj.
Zaliha ba ta da Karfin da za ta iya wannan sana'a tana dai bin Yagana ne ba tare da tana wani katabus ba, hasalima Yagana ce ta ke ta yi musu wannan KoKari ba tare da nuna gazawa ba bare nuna bacin rai. .

. Haka al'amuran suka ci gaba da faruwa tsayin wani lokaci har zuwa lokacin da jikinta yai kyau, ta wartseke sarai, ta ga dai zata bari Yagana tayi ta dawainiya da ita ne?  Yau da gobe babu mai iya ma ta sai Allah ko babu komai zamane ba na Kare ba. Zama ne da ake saka ran a Karashe rayuwar da ta yiwa Bawa -saura, ko babu komai akwai lokutan da Yagana zata iya yi ma ta nisa (bata nan).

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "HAMADA BOOK 1 CHAPTER 9 BY ZAINAB KABIR BIROMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...