HAMADA BOOK 1 CHAPTER 8 BY ZAINAB KABIR BIROMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 8 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 8 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

- - Post a Comment

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 8 BY ZAINAB KABIR BIROMAN


                 Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA 

Akwai wani jami'i mai kula da Kofar fita Sai ya saka hannu (wato ya yi rubutu) a jikin mannanniyar Takardar nan sannan za ka wuce, tabbacin kayanka halastattu ne, wato an cajesu  ba tare da samun kayan laifi ba. Ta dan yi duru-duru bayan ta fita daga Screening room din zuwa farfajiyar da aka _ " tanadarwa Matafiya mai girma da fadi da tarin kayan alatu da isarta ta wuce misali. Tana dai iya halkanta da wasu korayen Kujeru kamar na Karau kamar na Roba, an bi an Kawace kafatannin farfajiyar da ita. Rufin ginin wajen shi ya fi komai jan hankalinta, an bi an kifeshi kamar Laima.
Ko da yake ba siffar Laima ba ce, kwaikwayo ne daga Gizo-gizonda ya yiwa

ZAMU TASHI 

MANZO (SAW) shinge daga kafiran Makkah a cikin KOGON HIRA lokacin da suka yi nufin Ihijirah shi da .SAYYADI ABUBAKAR SADDIK (RA).
Kawai aka dafa kafadunta a lokacin da take wannan tunanin, ta yi mamaki sosai da alamun ta riga isowa.
Ta yi mamaki sosai da alamun ta riga ta isowa. Hajiya Sabuwa ce cike da farinciki sosai ta riKe jakar hannunta tana kuma dafa kafadunta gami da jinjina kai dama dai ba tayi tsammanin fallasuwar al'amuran ba irin shirin da suka yi bana wasa bane, sai dai ko gudun bacin rana don kuwa babu dalilin da zai sa ta iya saka kanta cikin wannan harka.
Kamar Kiftawar ido da bisimillah tuni an yi musayar Jakunkunan tsakanin Hajiya Sabuwa da wani mutumin
Birnin Jedda suka wuce, Zaliha tana ta mamaki tana tsammanin Birnin Makka abar karramawa zasu shiga don gabatar da ibada, har ma ta kasa Boye hakan a ranta. Hajiyar tace ta kwantar da hankalinta kamar tsumma a Randa, tunda ta iso wannan Kasa ko Www.bankinhausanovels.com.ng
Birnin Darul Salama take fatan bida babu shakka za taje ne.Ba ta mance sunan Unguwar ba, Bawadi. Unguwar tana kan hanyar zuwa filin tashi da saukar Jiragen sama na Jidda. Anan suka fara sauka a gidan aminiyar Hajiyar, wato Hajiya Sarai. Duka ‘yan tawagar Hajiyar suka sauka a gidan. Mata

shida, yara biyu, matasa kamarta uku sai mutum guda daya. namiji da yaiwa Hajiyar hidima sosai tun daga shigowarsu. Anan Hajiya ta bashi kudin da ba ta iya_ tantance darajarsu ba, shi ke nan ya kama gabansa yana fadin sai sun hade a Nijeriya. Duk da tarin yawansu haka aka dinga hidima dasu, hidimar da idanun Zalihar bai taba gani ba. A haka har aka sami tsayin kwanaki uku, daga nan aka shiga rarrabawa, yaran biyu da shekarunsu ba zai gaza goma ba, daya aka wuce da shi Makkah, daya kuma ta ga wata Hajiya ta wuce da shi wani gari wai Jabib. Cikin su guda uku matasan kuwa daya daga ciki wata Haule da ta fito daga Garin Gabas itama an wuce da ita Makka gidan Hajiya Laure mai dafe-dafen Abinci.
An jiyo tana cigiyar matasan yara domin tayata girkawa da wanke-wanken kwanonin abinci, illa iyaka za a yanka ma ta albashin da za ta dinga biya a duk Karshen wata.Hajiya Sarai ce ta shawarci Www.bankinhausanovels.com.ng aminiyarta, tana fadin akwai Kauye a kanta babu wani abin kirki da za ta aiwatarwa Ya rage daga ita sai Karima, Hajiya Saran ita ce irin wadanda ake da buKata ke nan aka shiga tattali da tarairayarsu har zuwa lokacin da Hajiya Sabuwa ta yi nufin wucewa domin kuwa ciniki ya yi riba. . "Hajiya za ki wuce ki barni ba mu je Makkan ba kuma ya haka? Madina garin Manzo shima din ba ki cika min wannan alKawarin ba, ki Karasa ladanki Hajiya ko Ilahu Ya biyaki, kinsan matsalata na iso ne domin in roki Ubangijina yayewar al'amuran da nake ciki". Idanunta raurau kamar za ta yi kuka. Kiris! ta kece da dariya, ta dai nuna juriya tare da bata tabbacin wasu al'amura ne suka taso ma ta na al'amuran saye da sayarwa. "Ba wai wani nisan zango zan yi ba, da zarar na iso zamu wuce Birnin Makka har ma da Madina, har ma da Darus-Salama, duk inda na gaya miki zamu je, ki kwantar da hankalinki  kin ji Kawalliya, ga Hajiya Sarai nan, aminiyata ce za ta yi miki duk abin da ki ke so, na bar amanarki a hannunta.  Ke dai abin da na ke so da ke, duk abin da ta ce miki kada ki saba. Tana da karamci, mace ce da ake Karuwa da ita har ma a sami alkhairi matuKar an nuna ma ta biyayya. Kai ta gyada."Na gode Hajiya, Allah Ya dawo da ke lafiya”.Www.bankinhausanovels.com.ng
Ita ko daman mai girmamawace ga kowa da kowa, balle ma ga wanda ya darata. Ta dinga ji kamar al'amuranta sun yaye da zarar ta ishe ga babban daki na mai girma da daukaka (Kaaba) wannan yana dada sanyayar da ranta da share dukkan wata matsala da ta yi ma ta katutu. Haka al'amura suka ci gaba da wakana, kullum zuciyarta ta kasance cikin tsammani, suka kuma kasance cikin alfarmar Haj-Sarai, komai da komai a bisa KarKashin kulawarta ne, ci da sha da kuma kyakkyawar suturar da basu taba zato ba, kafin wani lokaci dukkan wata  sun murje sun yi mul-mul, sai dai suci su sha su gaisa cikin kyakkyawar shimfidar alfarma da. sassanyar inuwar rabar nan data gauraye dakin (Air Condition). Haka al'amuran suka ci gaba da kasancewa mutane da yawa na kawo cafka akan Zaliha, Hajiyan ta kan ce, "Wane mutum,wannan ta manya ce ba ta fakiran Ajnaban da ba za su iya ko cika mini lalita ta ko da haka guda ta Sa‘udi ba. ;
-Gidan Hajiyar mahada ce ta mutanen kirki da na banza mata da mazansu a yadda ta fahimta, wannan ya sa ta dinga Allahu-Allahu Hajiya Sabuwa ta iso su wuce musamman a wannan lokaci da yanayin da ke tattare da ita ya soma nuna alamu. Cikin rawar banjo ta Karaso tana faman taunar Chewingum, Kiris ta take Kafafunta. Tana da kazar-kazar da rashin damuwa da al'amuran da basu shafeta ba. Sai dai kuma kyawunta kadai ya "isa jan hankalinka ala tilas. . Ta dauko kyawun Mahaifiyarta ‘yar > Kabilar Shuwa mai alaka da mutan Chadi. Mahaifinta Bakanure ne sai dai ya dauko kyawun Mahaifiyarsa Bafulatanar Yola, don . haka fara ce tas! Doguwa sabal! Haske irin na - mutanen garin. Manyan idanu da dogon hanci da ya dada Kayatar da fuskarta, gashin nan nata baki sidik, ya so ya yi kamanceceniya da na mutanan garin, sai dai bai kai aukin nasu ba. - Www.bankinhausanovels.com.ng
A shekaru da kadan za ta zarta Zaliha, sai dai fa yanayinta sam bai nuna hakan ba. Ta tsaya Kyam! a gabanta, ba ta damu da ko KoKarin ta ke Kafafunta da ta ke shirin yi ba. Tana dan duban Hajiyan tamkar a raine. Ta ban ‘dan Zaki ya girma! "Yagana mene ne haka? Ai ina jin matsayina ya zarta ki yi min Kerere haka?" Ta watso dami (Wrafer) guda na kudin Sa'udi sababbi fil! ‘yan Riyal goma-goma a Kafafun Hajiya.
"Inji Faisal! Akwai idanu a zagayen don haka ya ce ba zai Karaso ba!" Ta wuce.tana dan rawar banjonta zuwa Kasurgumin dakin mai cike da kayan alatun nata guda.
Ta bar Hajiya cike da sambatun farinciki, ga sa'a ga dan karen Shaidanci. Yarinya dai mai sa'a kamar Yagana ba ta taba samun ta ba. Idanunta fal da hawaye ta dubeta. "Haytya ban zo da nufin wannan sana'a ba... ban zo domin in sabawa Ubangijina ba...ban zo sabo da wannan mummunar dabi'ar ba..." "Idan ma ba ki zova kin zo din!" - Hajiya Sarai ta katseta cikin tsabar hasala. , - Ta jima tana tarairayarta da lallamin yarinyar ta Kiya. A wasu lokutan akan sami irin hakan a idanun yaran da ba su gama wayewa ba, sai dai bai cika ja da nisa ba, don haka ta tashi haikan, domin kuwa yarinyar na shirin haddasar ma ta da 'SAMU DA RASHI".Ba Karamin samu bane zai sa mutane irin su. Farisu ..su waiwayeta da bukatarsu, buKatar da ke KarKashin ikonta, take kuma shirin gagararta...Akwai matukar Karuwa.Farisu babban dan wankiya ne (419). Mutumin Kasar Cameroon (Kamaru) ne, sai dai ya kan yawaita alaKa da mutan Najertya. Yana da matukar daurin Kafafu da tarin nera. Sai dai duk inda ta ke tsammani ba haka bane, yarinyar ta nuna ma ta gagara! . Ta yi lallami, ta yi lallashi, tana tsammanin bakunta ce. Ta yi amfani da samfurin muzayin dinta da ake amfani da shi wajen yaudarar da zukatan yaran al'umma ta hanyar kwadaitar da su da tarin dukiyar da za su tara ta wannan hanyar, amma duka a banza. Yarinyar ta yi kunnuwan Kashi da ita har _ma Farisu yayi.fishi ya Kyale su Saran ma balle - wasu 'yan iska dake KarKashinta Www.bankinhausanovels.com.ng

*************

fito in gaya miki gaskiya, kowa kika gani anan ba wani abin kirki yake alwatarwa ba, manufar dai guda ce,  KoKarin tattare damman na Sa'udi (Riyal). ne, don haka babu haufi idan ka rufe idanu ka lalubesu ta kowacce siga. Ke bari ma na fito Karara in gaya miki, wane mutumin kirki ne zai baro iyayensa,'dangi da kowa nasa yaZO ya zauna a wata duniyar? Ai ko ban ce ba kin san kowa ya sayi Rariya yana da tabbacin za ta zubar da ruwa ne!" Das! Das!! Takun Yagana. Ta game Hajiya har da Zalihar ta watsar ta wuce abinta lokacin da Abbati shi kuma dan Kasar Ghana ya zo daukanta. Akwai Riyalai dammai a hannunsa, ga shi da tarin sakin masu gidan ranar. Suna samun kudi tamkar yayi a Bola. Madugu ne na masu Safarar Miyagun Kwayoyl. . Yagana sam ba ta ra‘ayinsa, yana da wata dabi'a da take Kyamarta, gashi kuma dan gaban goshin Hajiya ne, tana matuKar Karuwa da shi, don haka Yagana ta ke ra'ayinsa ko da taki.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Hajiya bata dada tsinkewa da al'amarin yarinyar ba sai bayan da Hanifa dan Sa'udin asali ya yi matukar yi ma ta barazana. Jami’ tsaro ne. . Hajiya ta dade tana hadashi da kyawawan matan Najeriya, shi kuma yana saka ma ta da tabbacin kasancewarta a Saudi. . _ Kowa dai ya san bisa daurin Kafafun da Sarai take samu ne take cin karenta babu babbaka. Sai fa a wannan lokaci da take shirin kwabewa, a lokacin da ta shirya dabarar isar da Zaliha gidan shaKatawarsa kamar yadda aka saba, yarinyar ta yi KoKarin yi mishi tijara da fallasar da shi ta hanyar kururuwa, in ban da Allah Ya so shi da sirrin Boyen ya fasu.
Dalili ke nan da ya yiwa Hajiyar barazana. Tana nufin ja mishi masifa, to ko zai maganin su baki daya. da Kyar da sidin goshi ya iya fahimtarta. Ta ko sauke kwandon tsiyarta akan Zaliha. Duk wani aikin gida akanta ya Kare, babu kuma ciyarwar kirki, ta bar Kara hasarar dukiyarta a banza, kafin sabuwa ta juyo su yi wacce Za su yi ta ba ta fansar kudinta.
Sabuwan ta san komai ta hadota da wannan jidali har ma ake shirin janyo ma ta asara, ko don kawai sunanta Sarai? Www.bankinhausanovels.com.ng
To kuwa babu shakka bata zamo mai daukan hasara ba. .
Haka al'amura suka ci gaba da faruwa, babu tausayi bare nuna tausayawa, aka barta da ayyukan da komai cikakken Karfi sai yai namijin koKari kafin ya iya cimma rabinsa, balle ita da take dauke da lalura, larurar da babu wani da ya sani Sai ita sai ko Allah da Ya halicceta. A dai wannan Kasa da ta ke cikin Www.bankinhausanovels.com.ng

Ta kode, ta rame, ta fita hayyacinta. A lokacin da Karima tuni duniyar ta gama saisaita a gurinta, tana da ra'ayin Sarai, dama da ra'ayin ne ta iso Kasar ta Saudi, don haka ma sam ba a ma sha wahala akanta ba sai damman take bubbugowa Sarai cikin jin dadi.
Sai ita daya Kwal ce data zame mata Jangwam-gwam! Zako su hadu da Sabuwa

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "HAMADA BOOK 1 CHAPTER 8 BY ZAINAB KABIR BIROMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...