HAMADA BOOK 1 CHAPTER 7 BY ZAINAB KABIR BIROMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 7 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 7 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

- - Post a Comment

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 7 BY ZAINAB KABIR BIROMAN                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

 

MUN TSAYA 

Kaico! da wannan rayuwa mara dadi. Al'amura da yawa suka hadu suka zamo sanadi...mujaza...silar kabbatuwar komai...Sai kawai ta saka kuka ta durkushe cikin tsakiyar Sahara tana fitar da wani irin sauti mai ban tausayi. Jimy na ta lallashinta tana fadin ta daure su Karasa, kadan ya rage su isa Kauyen Sufrati. Ana matuKar samu, galibi al‘'ummar da ke zaune a garin sun fito ne daga kudancin Asiya.

Ta yi hakuri ta daure tana tsammanibn tsabar wahala da gajiya ce, su Tasalluwa da su Kyauta suka shiga guna-guni da jan dogon tsaki.

"Kowa din ba dauriya bace, waye din bai gajiya da wannan dan karen wahalar ? Tilas ne a wawuri duk wacce ta zo hannu, ya ki halak, ya ki haram!" "Ya ki koma mene ne...." Kyauta ta Karasa fadin hakan cikin tsananin fusata. Haka suka Karasa Kauyen Sufrati cikin Kishi da tarin gajiya, cikin kumatarin KasKanci. -

ZAMU TASHI 

Wani lokacin har ‘yan Kudade na binsu duk da tarin kiwon lafiya na Kasar ta Saudi da ya game Birni da Kauye. Hakan ce ma ta sa wasu ke jin Kyankyaminsu. Kai wasu ma firgici suke da su, aka shiga "Yallah!"

Suna tsananin firgicin kada su haddasar musu da wata gagarumar Kwayar Cutar, domin kuwa zahirin gaskiya cikin Asaben Jimeta, wata daga cikin 'yan tawagar su ya saki sakamakon handamar gasasshen naman rago da suka sami sadakarsa fal cikin takarda a Kauyen Essama'a. Www.bankinhausanovels.com.ng

Tun akan hanya kafin su iso Asaben Jimeta ke ta kwasa, tun akan hanyar cikinta ya murda, ko kafin su iso Sufrati tuni Zawayi ya tsinke ma ta, ta kuma mursiye abinta. . Bangajejiyar rigar da ke jikinta baKar Abaya na iya sakaye komai. Zaman Kusha ya mai da da yawa daga cikinsu Kazaman dole sabi da rashin yalwar ruwa. Don haka yau babu wani abin kirki da aka Samu a wannan tafiya, don ma dai sun dan yi raise wasu Kauyukan da ke kan hanyar zuwa Kushan. Gab da faduwar rana suka iso Kusha, a lokacin Mallam Abdul Rahaman na jagorancin Salatul Janazati (Sallar Gawa) na wani mutumin Kasar Senegal da ya rasu da yammacin ranar. Al'aumma da yawa daga kowanne jinsi sun sami halarta. Dama dai akwai wannan hadin kai. Daga Karshe aka bizne_ shi cikin makabartar Kusha, wato can nesa da inda mutane suke zaune tsakiyar Sahara, filin Allah fetal. : Nan ne al'ummar Kusha suka kewaye da duwatsu suka mai da shi

Makabartarsu. Inda ake aure, ake haihuwa, ake bikin suna, har yara sun tasa su shiga Islamiyyar da ke cikin jama'ar Kusha.
Haka nan ake rashi, ake kuma binnewa a Kushewar Www.bankinhausanovels.com.ng Kusha. Cikin sanda da dabara aka hure fitilar Acibal-bal din da ta haskake dakin, a lokaci guda ya tunkarota. Cikin tsananin firgici ta farka, ta dinga salati tana ambatar sunan Ubangiji, a lokacin da wani abu ya rabi jikinta, ake kuma KoKarin danne ma ta baki. Ta dinga yunKuri tana fadin,"Huwaila! Ki taimakeni! "Yar uwa ki ceceni!!!!" Ta yunkura kamar a dan razane ta zauna sosai kan shimfidarta, a lokaci guda ta fahimci al'amaran, kawai sai ta kau da kai ta yi mika abinta ta koma ta kwanta tana mai dogon tsaki.  rainin hankalin da yarinyar nan take - musu ya isa haka. Ya saki iyakar Karfinsa a Kalla a rana guda ko ya cimma burinsa.. . ‘ Bai damu da bugu da mangarin da take kawo mishi ba.ta ci gaba da ambaton Ubangiji tana neman dauki kai ka ce babu wani mai numfashi a garin na Kusha a lokacin. A dai-dai lokacin da ya ke Kokarin cin galabarta aka bankado yan dakin da ya zamo tamkar Kofar shiga.
Ba shi da wani suffar Karfi sai dai yana da Karfin zuciyar da ta kyautatu da tsoron Allah, hakan ce ma ta sa ya uya hankade Iliyasu dan Agullan Saudi daga jikin Zalihar Yagana. Ya tafi taga-taga ya hade da kafaffen Karfen da ya tsaida Tantin (Shema) ya ko bugu Kwarai har cikin kwanyarsa. Sai kawai ya tsaya yai sandar-dar bai yi gaba ba, shi kuma bai yi baya ba. Ta cakure, ta nannade ta kuma cure guri _ guda cikin wani irin razani da firgici mai tarin yawa. Ya fisge Mayafin da ya sarfe Kafafunsa ba .
' tare da ya waigo ba ya watse a cikin jikinta, ta ko kasance cikin suturta domin kuwa suturar jikinta yai ma ta kaca-kaca.Dai-dai lokacin ya waigo, hasken farin watan da ke ratsowa ta jikin tagar tantin ta dalle fuskarsa, babu alamun annuri a tare da shi. Ta ko dubeshi da wani irin razani. Ba ta mance da kamanninsa ba balle ya Gace ma ta, yana nan a yadda ta sanshi. Dai-dai_ lokacin dai-daikun al'umma wadanda barci bai riga ya gama dannesu ba  suka fara kunno kai ciki har da Liman Abdul Rahaman.
Fadi ya ke, "Assha-assha! Mutane irin haka a cikin garin nan? Irin ayyukan ta'addancin da za a shiga yi mana ke nan? Fice! Fice!! Fice.....!!! Kada na Kara ganin irin haka". Yace da Iliya dan Agullan Saudi. Ya mai da hankalinsa akan Jabir. , Allah ne kadai Zai biyaka da wannan JAHADI da ka yi. Kada ka damu da hukuncin da na zartar maka", Kamar bai so ba ya gyada kai a lokacinda yake KoKarin ficewa, ta yi kamar ta zabura ta tari - gabansa kada ya Kara Bace mata ba tare da ta gode masa ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Amma ina! Fit! ya fice ya bace cikin . rurumar jama'ar da suka dan fara taruwa, ga kuma tasirin rashin yalwar haske a wajen, bat! ya bace ya kuma Kara subuce ma tan. Ko wayewar garni zancen da ake dan kunjikunjinsa ke nan a garin Kusha, wasu na ganin kawai shafcin gizo ne, rainin hankali, yunKurin mai da mutane sokaye ne. Manyan matan garin Kusha sun zarta tunanin ayi musu fyade. Wasu ko da suka wanye da dabi'arta suna da tabbacin ba aKi nemanta ba. Yagana ba ta kwana a gida ba (shemarsu), _itama kuwa Hauwa ba sabon ta bane, daga Zaliha sai Huwaila akaa bari a ciki, Zaliha na aikin kuka a rana guda ta yi dakacen zuwanta Birnin Kusha, ta yi dakacen al'amura daki-daki da suka yi mujazar komai. Ina ma dai da hakan ba ta faru ba. Hauwa ta dinga tsaki tana dan ciccijewa, har ma da alamun dan rashin gaskiya. Yagana ko ta dinga masifa, ta dinga bala’i. "Sabo da babu idanunta za a yi ma ta wannan cin amanar? Allah Ka rabata da dan Agullan, hakika za ta nuna mishi shi din KanKanin dan banza ne tun da har ya shigo hurumin 'yar uwarta. Hakika za ta nuna mishi kuskurenta”". Ta dinga bambami da bala'i, ta hada ta ci zarafin kowa, domin kuwa ta lura da Www.bankinhausanovels.com.ng hadin bakin su Hauwa. Hauwa ba ta tanka ba, domin kuwa ta tsorata da hatsabibancin Yagana. Sai dai tana jiye mata tsoro, Yagana ta zame ma ta fitila mai haskakawa, ta kai inda ba ta tsammani a fage na rakashewa, albarkacin ~ Yagana. Har dai Maryam da ba ta cika shiga hurumin kowa ba ta yi furucin, ta dai yi hankali da ‘yan Agullan Saudi, idan ma har tana tunanin tabasu ta wanye lafiya sabo da taKamar tarin Askar (Yan sanda) da suke hannunta, to fa ban da Ilyas dan Agullan da ya burunkasa ya buwaya da muyagun ayyuka, ki ka gani a garin nan cikin shakkunsa yake, sun buwaya, sun gagari duk wani da ba kya tsammani. Allah dai Ya taimaka basu hadu ba, akwai alamun ya fice daga Kushan, kamar hakan ya fiyewa Yagana alheri, daga dai karon batta da ‘yan Agullan Saudi (wato 'yan daba ko kuma ‘yan iskan gar1). Galibi Ajnabai ne (bakake) masu rike da takardun kasancewa dan Kasa na din-din-din (Tab'iyya) babbar dagawar tasu ke nan. Da yawa daga ciki anan «aka haifi iyayensu aka kuma haifesu, akan kuma sami Larabawan Saudi jefi-jefi a cikinsu. .Yagana na Kaunar Zaliha da gaske irin shirin da ta yi akan dan Agullan har abin ya soma ba ta tsoro. Ta zamo ita ce mai lallashi da ba ta baki. Sannu a hankali al'amura suka shiga bijiro ma ta, ba yau ne ta fara irin haka a kanta ba, ba. yau ne ta fara daga hankalin kowa akanta ba, ba yau ne ta fara damuwa da damuwarta ba, ba yau ne ta fara yi ma ta wannan taimakon ba, a'a tun farkon haduwarsu. _ Tiryan-tiryan al'amuran suka __ shiga warwarewa a kwanyarta tamkar faifan Majigi a Silima. Www.bankinhausanovels.com.ng

* ****

RANAR laraba da take tsammanin ta

ZAme mata Tabarawa ranar samu, har ma ta zamo mai sa'a a cikinta suka dira filin tashi da saukar Jiragen sama na Kasa da Kasa na Sarki Abdulaziz Al-Saudi da ke gefen Birnin Jiddah! Jirgin ya yi parking gaf da Kofar da aka tanadarwa Matafiyan gate 6 Ba wata tazara ba ce a tsakani, amma sai da mota Kirar ‘Saptco’ ta kwashesu zuwa_ bakin Kofar get na shida din. Tun a nan ta soma duban tarin bam-banci da cigaban zamani da Sa'udin take da shi. Sun shiga cikin dakin tantancewa (Severing room) da ya Kawatu da kayan alatu na > zamani, ga fadi da girman gaske, ga tarin fitilu da suka haskake wajen.
Dadin-dadawa ko ina Jawazen (imagration) na Saudi ne cikin shigar kayan aiki, al'amarin saiya hadu ya zame mata wani ban-barakwai, daga nan suka zauna akan kuyjera. Cikin layi ma'aikata na bi na duba katunan kiwon lafiyar mutum (yellow card) da wasu
muhimman takardu. Kana aka shiga mikewa daya bayan daya - zuwa Ofishin jami'an shige da fice na Kasa * Jawazen. Ofishin yana kamanceceniya da _ ofishoshin * Kananun Ma’aikatan Banki mai kama da Akurki. A bayan nan ne suka shiga dan Karamin ofishi mai Kofa biyu,mata ne zuryan sanye da bakar Abaya da Nikab da ko Kwayar idanunsu ba a gani.
Anan ne aka caje jikinsu da kayan hannunsu aka kuma saka na'urar ,zamani mai kama da makunnin sarrafa na'ura daga nesa (Remote control). Nan ma din duk babu wata matsala suka wuce ta Kofar wacce ta isar da su wani faffadan daki mai yalwa da alatun zamani. Anan ne na'urar da take iso da kayan da aka sakosu cikin ma'‘aunin kaya (skell) mai amfani da lantarki, tana ta tafiya tana sake juyowa da Jakunkunan Matafiya mutane suna tsaitsaye bakin na'urar cikin tsari kowa na daukar nasa. Jagorar tafiyar Zaliha, wato Hajiya Sabuwa ta zari wata zungureriyar jaka kana ta danKawa Zaliha ta Kuma WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG dada jan kunnenta da ta kula da kyau taje ta bi layin cajin kaya itama tana nan. tafe da zarar ta dauko ragowar kayansu. Ta ko yi kamar yadda ta ce, wani wuri ne dogo da aka ginashi da Siminti kamar dandamali a tsakiyar faffadan dakin, jami‘an bincike na tsaitsaye suna caje kayan Matafiya.
A haka har layi ya zo kan Zaliha aka caje ba wata matsala sai faman hamami da doyin daddawa ma Jakar take, don haka da hanzari jami'in binciken ya liKa mata wata ‘yar takarda mai danko cikin Kyama da nuna Kyara ya sallameta. Zuciyarta ta buga ta yi wani dum! tun anan ta soma gano bambancin. Sai bayan ta zo bakin Kofa ne ta fahimci muhimmancin takardar nanda_aka manna mata.
Akwai wani jami'i mai kula da Kofar fita Sai ya saka hannu (wato ya yi rubutu) a jikin mannanniyar Takardar nan sannan za ka wuce, tabbacin kayanka halastattu ne, wato an cajesu  ba tare da samun kayan laifi ba. Ta dan yi duru-duru bayan ta fita daga Screening room din zuwa farfajiyar da aka _ " tanadarwa Matafiya mai girma da fadi da tarin kayan alatu da isarta ta wuce misali. Tana dai iya halkanta da wasu korayen Kujeru kamar na Karau kamar na Roba, an bi an Kawace kafatannin farfajiyar da ita. Rufin ginin wajen shi ya fi komai jan hankalinta, an bi an kifeshi kamar Laima.
Ko da yake ba siffar Laima ba ce, kwaikwayo ne daga Gizo-gizonda ya yiwa


HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Post a Comment for "HAMADA BOOK 1 CHAPTER 7 BY ZAINAB KABIR BIROMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...