HAMADA BOOK 1 CHAPTER 6 BY ZAINAB KABIR BIROMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 6 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 6 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

- - Post a Comment

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 6 BY ZAINAB KABIR BIROMAN


                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Kafin ‘sallar Magariba kusan duk wani da yake zaune a Kusha ya iso daga duk inda yake sabi da duhu da rashin kyawun hanya, akan yi_

KoKari a iso Kusha kafin faduwar rana, kamar daga Karfe biyar zuwa shida na yammaci.Yagana ta iso cike da kaya fal cikin Ledoji - har sai da Hauwa ta taimaka musu.

‘Galibi kayan Abinci ne da kuma kayan : *amfanin YAU DA GOBE, don ko kwalliya baa . cika damuwa daita ba a wannan gari. a Wannan kam sai wadanda suke zaune cikin maraya ka ga ado har da Zinariya.-. - Ta cire baKar Abayar jikinta ta cire NiKab_ daga fuskarta, al'amarin da ya zama wajibi ga Matan Saudi, da ma wadanda ke cikinta ta ‘kowacce siga matuKar za su fita. Ta zube saman Katifarta mai cin mutum guda da galibi bakin haure suka fi amfani daita kafasarta Saudi.

Cike take da gajiya, ta yi shawagi cikin gari. ita ce har cikin Jeddah International Shopping Centre ta hada da Al-Mahmal Centre

- da Al-Sayiomar Kaseem Market, ga kuma rashin kyawun hanya wanda ya kan haddasar musu da gwabzuwar da take tsamar musu da jiki.

"Garin da ba naka ba bashi da wani dadin zama ga dan karen rashin ‘yanci." Yagana ta fada cikin nuna gajiyawa. Hauwa ta dauka. WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

- “Mu kuma mun nace zama daram daKau! _ Sai mun kai ga sa'ar tattare hatiman na Saudi ba?

Ko da tsiya ko da arziki, ko ana ha mazaha mata, ana KoKarin kai ruwa rana tsakaninmu da jami'an Saudi."

‘ Hauwa ta saka Huwaila dariya sosai, Ba ta cika shiga sabgar kowa ba, independer ce mai zaman kanta. - .

Zaliha kam ta yi shiru, ta yi tsit! kamar ma yanayin ya mortsa ma ta wasu al'amura.

Al'amarin’ da ya sa ta cikin wani irin yanayi, kusan duka ma da abin da ya tsugunnar

ZAMU TASHI 

da ita a Kasar ta Saudi ke nan da ya zamo mafi - sauki a gareta.  Shi ke nan ta nutsa tafkin kogin funanin al'amuran nan da suka faru daki-daki. Yagana tana ta santi Zaliha bata ma san mai take ba, tana ta sauri su wuce, ba shaka sun so su yi latti da Jarkokin Ruwa a hannunta sabo ‘da buKatarsa a lokutan da aka dawo, tana ta laluben mai shiga cikin gari kawai saiga Mansur ' agabanta. - Ya dubeta yana dan murmushi, a lokaci guda ya mika hannu ya karbi jerkokin hannunta. — - "Ka bar shi fa Mansur wahalar ta isa haka,  baka taba karbar ko Riyal guda ba, ga wahala da nisan da ke tsakankanin Www.bankinhausanovels.com.ng hanya. Jigilar ruwan nan abu ne mai matuKar wuya daga Birni zuwa surKukin nan. = Kai din ma sai ka cire ka bayar kafin a dauko maka, bayan wahalar da ke cikin debowa". _ _ "Kima da matsayinki a raina ya wuce duka wadannan abubuwan da kike lissafawa, idan dani mai shi ne zan yi miki abin da ya wuce haka ma Zaliha". Yagana na ta zungureta akan mene ne za ta dinga KoKarin yi musu manaKisa, ta zo kawai su wuce Allah ne ya kashe Ya basu. Kuma dai ita Yagana tafi Karfin ta dauki. yar uwarta ta baiwa mai dakon ruwa.  Kai tafi Karfin ta bawa dukkanin wani dan * kuci ku bamu dake cikin Kusha. Abin da kullum take fada ke nan. Da yawa sun nuna_ ra'ayisu. akan ‘abokiyarta, Yaganar ta ce a‘a ba tsarar su ba ce, idan ma har da tsarar ta su ce al'amarin da - Zalihar take ganin muddin rai ba mai yiwuwa - bane, don haka ba ta cika damuwa da ire-iren tarin shigegen da Yagana ke sakawa a tsakaninsu . Kafin wani lokaci sun nutsa tsakiyar rairarayi mai matuKar Kuna, Kunar da har ta kan so ta tayar da fatar tafikan Kafafunsu duk kuwa da matuKar gautsinta. ‘

Www.bankinhausanovels.com.ng

Tafiya ce mai nisa tsakanin Kusha da galibin Kauyukan da Mabaratan ke ziyarta. Akwai tafin Kafafu (‘yar tazara) a tsakanin Kusha da SIERRA, Kauyen da suka ziyarta a wannan - lokaci, Ta gajiya, ta fita hayyacinta Kwarai da gaske sai wani mugun Kishi take ji, Allah Ya taimaketa karon farko suka ratsa gefen wani kanti. . . ;
Kanti ne babba na sai da kayan masarnfi._—Fadi suke, "Fisabilillaht Karama ‘'MOYA' (wato ruwa)"
-Mai Kantin Balaraben Sa'udi ya miko musu robar ruwan kwalba. na “AFNAN DRINKING WATER‘ har guda hudu, sai dai yana dan guna-gunin su wuce su barshi haka, su bari ya isa shima fitowarsa ke nan. :

Haka aka warwatsu aka rarrabu saKo da lungunan Kauyen Sierra gida-gida, bakin shago da kantuna har ma da bakin Masallatai, fadi suke, "Karama! Karama — Fisabilillahi!! Fisabthtlahr kerama....Ana miskin....ana MISKIn.Kullum dai da salon Karyar da suke kwantsamawa, wasunsu’ subayar_ cikin tausayawa;-wasun su ko su bayar sabi da kawai an haiyaci kunnuwansu, a Kalla ko sa kauce su sami afuwa. Wasun su kuwa Kyara da hantara suke musu, wasu kuwa Kyan-Kyami har da tsoro suke basu. . A haka dai al'amuran suka cigaba da gudana, kusan kowanne lokaci sai dai ba ka yi  fita ba, amma ba za ka yi fitar banza ba, idan ka fita za ka iso gida tare da damman gumamai da ababan amfani  ga kuma ‘yan Riyalai da suke samu masu dan dama.  Dalili ke nan da al'ummatai da dama mazauna Kusha mafi rinjayensu matan sun mai da barar KakKarfar sana'ar da suke matuKar cin gajiyarta har ma tuni zukatansu sun mace da dan yunKuribn neman na kai. Wani lokaci ta zubar da hawaye, wani lokaci ta yi kukan zuciya. Ko can baya ba ta kasanee mai kasassiyar zuciya ba, don haka al'amarin ya ke ma ta Kuna har ma ta shiga lalube-a garin na Kusha ko ta dace da sana‘ar dogaro da kai.

Babu shakka ta gaji, ta gajida tozartar da kai, nemawa kai KasKanci da wulaKantar , tuni zuciyarla ta gama gajiyawa da hakan. Sai dai kuma kash! ta kasance kifin Rijiya! ° Ga al'ummar Kusha suna da al'adar fitowa . waje a lokacin da rana ta yi sanyi, sukan yi Www.bankinhausanovels.com.ng

‘shimfida a bakin Sandakokin su, musamman a lokutan zafi da shi ya fi rinjaye a kafatanin Kasar ta Saudi ma baki daya balle ga yanayi na zama a tsakiyar Sahara,
A kan yi shimfida aci abinci, a ma gabatar da sallah har ma yawancin lokuta wasun su su kwana anan sai fa in yanayi ne na hunturi akan yi sanyi sosai fiye da tsammani har ma ka yi tsammanin ba a tsakiyar Sahara ka ke ba, duk da . kasancewar wasu ‘yan watanni ne da ba su da yawa. Ita daya tana cikin Shemar a Kunshe, Yagana kam tuni an baje a filin Kusha musamman saboda sababbin abokan da ta yi Samahir ‘yan Kasar Itofiya.

Ba dai irin shegantakar da ba a yi a wannan fili, don haka ma bata taba marmarin fita shan

‘ iskar da al'ummar Kusha ke yi ba. . Ta leKo tana dan murmushi. "Ke daya Kwal a daki a cikin tsakiyar , Kusha, ki fito kawai ki wataya kamar kowa ko kya shaKi sassanyar iskar da ake kadawa a _ kewaye da zagayen Kusha". ,

Sassanyar iskar ta zame ma ta zazzafar iskamai wuta sakamakon ‘yar barazanar da take fuskanta, ai sai ta girgiza kai alamar um-um.

"Nan din ma ya wadatar Jamila". Ta fadi ainahin sunanta. , Makofciyarta ce da Allah Ya hada jininsu, Sandaka kamar uku ce ta raba matsugunninsu.

Ta dada kunno kai sosai tana mai yi ma ta kallon Kurullah a lokacin da hasken farin wata ya haskake fuskarta ta barin tagar Shemar. Akwai wani sirri da ke tattare da ke mutuniyar Yagana. Akwai wani sirri da mutane da yawa ke duba a idanunki suke ganin lallai Kusha ba bigire ne na mutane irin ku ba. Www.bankinhausanovels.com.ng

Kina da kamun kai, nutsuwarki na burgeni Zaliha. Sai dai ina mamakin yadda ku ke tare da su Hauwa da Yagana". Zaliha ta yi shiru ba ta ce komai ba. .
Yagana ta sauya hanya sosai fiye da — zamansu a Bimin Jidda, wani lokaci ba sosai take kwana a gidan su ba (Shema) balle kuma Hauwan Chadi. Duk wani iya hatsabibanci na Yagana kamar ma ba ta san komai ba idan aka kwatanta ta da Hauwa. . Sai dai hakan zai zamo tamkar cin naman dan uwanka ne. Shi ke nan",
Ta rintse idunu. Allah Ya tashemu da alheri Jimy".
Sam ba ta jin dadin irin yadda suke fita, ga dai rashin Yagana a wannan lokaci ta fi yawaita alaka da su Samahir, barar ma ba sosai take fita ba, daga bisani ma ta janye Kafafunta baki daya. Sai dai ta damKa amanarta a hannunsu Jimy, suna kuma kulawa da ita sosai, in bayan 'yan kunji-kun jin da ke faruwa, ‘yan kunjikunjin ko bai wuce dabi'ar dogon hannu (sata) da
wasu daga cikin 'yan tawagar Kauyawan da suke zuwa bara ba. Kai wani sa'in har cikin gida sai fa idan idanu bai dauke ba, don haka ana bara ana kuma sane, al'amarin ya soma damunta,

A hakikanin gaskiya abokin barawo, barawo ne, kuma zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai, ba wani abin mamaki bane nan gaba ta budi idanu dumu-dumu cikin wannan sana’‘a, idan ma ance ba hakan ba ina ta taba tunanin za ta miKa hannu da nufin neman ta Annabi (bara)? Yanayin ne ya samar, yanayin ne kuma zai samar da hakan. '

’ Wani lokacin ta yi kuka, wani lokaci kam sai dai zuciyarta ta yi Kuna musamman ‘yar tsangwamar da ta soma fuskanta a hannun aboka nan tafiyarta, su kam arziki suka zo bida, ya ki halak, ya ki haram
“A banza muka sarayar da duk wata kadara _ tamu muka hawo tikitin jirgi? Wanda duk ba arziKi ya zo bida ba ai sai ya kauce ya basu wuri."Irin martanin da abokanan tafiyarta ke ° mayar ma ta ke nan, domin kawai ta nusar. Har sai da Jimy ta nuna jan wuya sannan aka dan tsahirta ma ta. "Kowa din ki ka gani anan uwa ce babu kwaba balle harara, zama ne na cin gashin kai, babu mai daukan dawainiyar wani balle ya yi tutiyar shi ya kawoshi wajen. Ki bari kowa ya yi abin da ya ke so, me yiwuwa ne hakan yake ganin ya fiye mishi, shi ke nan sai ki zauna lafiya salamun-salamun da kowa da kowa". Jimy take shawartarta da kuma ba ta wasu ‘yan shawarwari da ta ke ganin za su amfaneta. Www.bankinhausanovels.com.ng

Su Magajiya da su Maiga da manyamanyan matan Kusha duka haushinta suke ji sabo da kasa samun hadin kanta da suka yi. Ala tilas ta yi musu bakin ciki damman kudaden da za su samu daga hannun mazajen da suka dinga kawo ma ta cafka. Akwai wadanda suka nuna za su dauke - dukkan wata dawainiyarta matuKar ta amincewa buKatarsu, buKatar ko.ba ta wuce a zauna ayi zaman banza tamkar Miji da Mata ba tare da daura Sunnar Mai‘aiki ba (aure).
Ko da yake wasu domin kawai a shaKi iska na wani lokaci ne, a kuma wasu lokutan da aka yi ra'ayi. Duk ta KarKashin su Mai gadon aka nemi wannan alfarma, idan dai da babbar sana'ar wadannan manyan matan biyu bai wuce wannan ba, wato kawalci. Waiyazubillah!   wahala da wahalhalun da suke fuskanta kafin isa Kauyukan da suke zuwa bara ta isa ta wuce misali, cikin tsakiyar rairayi mai Kuna, haka suke wannan sakaraftu, wani lokacin a girmamasu, a tausaya musu, wani lokacin ko kishiyar hakan, a Karshe su tattare komatsansu su fice cikin tarin KasKanci.
Ta yi kukan zuci ta yi na Kwayar ido. Alal hakiKa Yagana ba ta fayyace ma ta zahirin rayuwa a garin Kusha ba, ta rufeta ta ma so ta yaudareta. Me ya sa Yagana ta yi ma ta haka? Rayuwa a Birnin Kusha ba abu ne mai sauki ba, rayuwa ce mai cike da sarKakiya da tarin wahala. . Ko dai ka bi hanya dodar ka kwashi azaba (wahala) ko dai ka saki, ka yi walwala a can kuma makoma ka je ka tarar da mummunan guzurinka. WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
Kaico! da wannan rayuwa mara dadi. Al'amura da yawa suka hadu suka zamo sanadi...mujaza...silar kabbatuwar komai...Sai kawai ta saka kuka ta durkushe cikin tsakiyar Sahara tana fitar da wani irin sauti mai ban tausayi. Jimy na ta lallashinta tana fadin ta daure su Karasa, kadan ya rage su isa Kauyen Sufrati. Ana matuKar samu, galibi al‘'ummar da ke zaune a garin sun fito ne daga kudancin Asiya.

Ta yi hakuri ta daure tana tsammanibn tsabar wahala da gajiya ce, su Tasalluwa da su Kyauta suka shiga guna-guni da jan dogon tsaki.

"Kowa din ba dauriya bace, waye din bai gajiya da wannan dan karen wahalar ? Tilas ne a wawuri duk wacce ta zo hannu, ya ki halak, ya ki haram!" "Ya ki koma mene ne...." Kyauta ta Karasa fadin hakan cikin tsananin fusata. Haka suka Karasa Kauyen Sufrati cikin Kishi da tarin gajiya, cikin kumatarin KasKanci. -


ASHA RUWA A KOMA AIKI HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "HAMADA BOOK 1 CHAPTER 6 BY ZAINAB KABIR BIROMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...