HAMADA BOOK 1 CHAPTER 5 BY ZAINAB KABIR BIROMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 5 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 5 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

- - Post a Comment

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 5 BY ZAINAB KABIR BIROMAN                WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG MUN TSAYA 

Sai dai ba su cika tasiri anan ba kasancewar akwai tsarin shugabanci mai kyau a garin na Kusha da ya hada da hukumomin tsaro, hukumar zartarwa da ladabtarwa, duk dai daga cikin al'ummatan da ke cikin Kusha akan duba_ . dacewa da nagartarka kafin samun wannan matsayi daga kowacce Kabilar ka fito.

Kai idan wani laifi ma aka tafka a garuruwan Jidda, Makka da sauran garuruwan da Ajnabai suka yi kaka-gida sukan sami mafaki a Kusha kafin al'anmura su lafa.

Don haka muna iya cewa garin na KUSHA ya hada kowa da komai daga cikin

mutanen kirki da na banza.

Haka al'amura ‘suka dinga faruwa a idanunsu, kafin wani lokaci garin na Kusha ya dade sai ‘yan tsirarin da aka ambata a baya.

‘ A wannan lokaci Zaliha da Kawarta Yagana da su Jimi ‘yar Chadi sun nutsa tsakiyar Www.bankinhausanovels.com.ng 

HAMADA ba ji ba gani, ga zafin rana ga Kunar rairayin Sahara. , ‘ A haka har suka nutsa Kauyen ALBASATEEN. Garin yana hegen sananniyar Makarantar nan ta kasar, Birkniya, wato BRITISH INTERNATIONAL SCHOOL OF JEDDAH ~ Daga nan ne fa aka rarrabu, aka warwatsu loko da saKon Kauyen Al-Basateen. Ko kuwa mu ce kasancewar akwai ababen more rayuwa. - Jimi ta karya hannu ta kandareshi. ta sakeshi kamar wani shanyaye. Fadi ta ke; "Fisabilillahi! Fisabilillahi!! _ Karama fisabilillahi!!!" Wanda ya basu sai su amisa da . “Shukuran", Take Yagana ta bi sahu, hasalima har ta so ta fi Jimi nuna kasawarta (nakasa). . Haka ta ke, tana da matuKar basira da kwanya, ga jarumta da nuna jajircewa, duk wani - abu da ta saka a gaba. ,

ZAMU TASHI 

. . Zaliha ta saka kuka a lokacin da Yagana take ma ta ishara (nuni) ga fa yadda ake, tun tana Karamarta ba ta kasance mai kasasshiyar zuciya ba, haka nan duk wasu al'amura da suka kasance ta kan nuna kana'a ba dai tace bani ba balle ta aikatawa kanta wannan tozarcin.

Bara? Barar ma bisa KarKashin inuwar Zamba cikin aminci? -Kawai sai ta dada saka kuka. "Me ya sa ne Yagana ta kawota wannan . wuri?" ' Don haka ma a wannan fita Zaliha ba ta . sami wani abin kirki ba, Yagana tana dada yi ma _ ta nasiha. , ; . "Nan wuri ne fa da dole sai ka tashi ka nemi na kanka.Neman na kanka kuwa ga tunanina irin wannan zai fiye miki alfanu".  Wuri neda babu uwa babu uba, babu - gauran dangi balle wani ya agajeka, a'a kowa ki ka gani anan tasa ce zata fissheshi www.bankinhausanovels.com.ng 

A lokaci guda zuciyarta ta harba, ta shiga kai da komo ba KaKKautawa. Al'amura da yawa

_suka shiga bijiro ma ta.”

Sanadi....Kaddara.....kaddarorinta ba za su Kidayu ba. Babu: ko shakka ita din’ wata ' MARAINIYA ce da tafi kowa kasancewa cikin MARAICI. . . . . Haka rayuwar za ta Kare ta tuke? Haka al'amura za su ci gaba da faruwa muddin rai? -

: Ba ta da wani fatan samun farinciki a rayuwarta, TUN RANAR GINI....TUN RAN ZANE....:.!

Al'amuran sun gama tabbata, ta shiga ja da

fitar dawani numfashi ba ., KakKautawa. ,Al'amarin da ya firgitar da Yagana fiye da  dukkan al'amuran dake faruwa abaya. —  YAU DA GOBE..,.Yau da goben da tilas taki wasa.

. ' Yagana ba za ta iya da hidimar ta ba, balle kuma Hauwa.

Tilas ta zage ta kau da duk wani Bacin rai da ke cinta ta himmantu wajen kwaikwayon su _ Yagana wajen neman Ta-annabi (Bara). Abu guda da ta sani ba ta taba tanKware ko lanKwashe wani sassanta balle ta kai ga . KoKarin sauya halittar da Sarki Allah ya bata da ba ta isa - ta biyashi da wannan ni'ima da Ya yi ma taba. . Cikakkiyar mutum mai hankali da nutsuwa da bata da tawaya a cikin gangar jikinta. Kafin wani lokaci sun nutsa Kauyukan da ba ta taba tsammani ba, a kuma tafukan Kafafunsu, kamar Kauyukan Makareem Annakeel da ke arewacin Jeddah, Kauyen ebsar ’ da kuma Kauyen Shakar. : so * Wani lokacin a basu kudi, wani lokacin sutura da Abinci. Wani lokacin har komatsan daki, kayan . lantarki da shimfidu (Darduma). Haka dai ba irin abin da ba sa samowa. _ .

Yau in sun je wancan Kauye, gobe suna wancan, jibi ma ka iske su wani bigiren. Sukan jima kafin su yi maimaici.

Larabawan Kauyukan mutane ne masu tausayi da jin Kai. Sai dai gaskiya ba su wani waye da ilimin zamani ba, da zarar ka ce; "Karama Fisabilillaht! Fisabiftllafi!!" Duk abin

. da yake hannunsu sa rarumo su baka. ~ Sai dai hakan bai hana a sami cikakken * ilimin addini da na zamani ba, kwanyarsu a bude . take don haka za ka ji suna fadi, babu kasawa cikin addinin Islama, don haka addinin ~ . Musulunci ba addinin kasawa bane. .WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Annabinmu Muhammad (S.A.W) ba kasasshe bane da ake nema dominsa bai yi ‘wafati ba har sai da ya nunar mana halaccin neman nakai.

Sai ka ji suna kawo maka Kissar mutumin nan da ya zo gurin Manzon Allah (S.A.W) da neman taimako alhali yana cikin Koshin lafiya. - Manzo ya umarceshi da ya samo gatari,

‘Da ya dawo ya umarceshi da ya je daji ya saro Ice, ya Kara dawowa da Icen. Annabi ya sake umartarsa da ya je Kasuwa ya siyar.

Da wannan Manzo (SAW) ya hori zuciyar wannan bawan Allah har ya zama mai neman na kai Haka nan ake fatan dukkan wani mutum. yakasance. ce

. .A irin wannan wurare ba su cika samu ba, don haka sukan kauce masa. ._ A wasu garuruwan kuwa suna da ‘yar . Kyamar baki. Nan din ma babu wata samuwa. Za ka ji suna fadin, "Hayya! Hayya....!! Ku tafi! Ku tafil!!" . .

A wasu garuruwan kuwa, kacokam Yara - har ma da wadanda suka dan tasa kacokam tsoronsu ake ji. _Ka ga Yaro yana Buya a bayan Babansu ". . ko Ummanshi kasancewar ya ga wata halittarda

'‘ bai taba duba ba. . . .

Irin wadannan mutane za ka iske su basu

da wata mu'amala da mutan ‘Birni balle su ' shigeta su ilmantu da abubuwan da ke cikinta.

A irin wadannan garuruwan da ke cikinta, a irin wadannan garuruwan samunsu Kalilan ne.

Ba za ta mance da wannan gari ba, wani Kauye da ke kusa-:da Kauyen Bahara da ke kan hanyar zuwa garin Makkah.
Haka al'amarin ya kasance da su babu Kaharu. 

A haka dai har suka sami tsayin, Watanni -. Uku Garin Kusha cikin wannan yanayi. Sun yi Baki, sun soma sajewa da mutan Kauyen, illa iyaka sun yi kumari domin kuwa suna cin mai kyau da ko a Birnin sai haka. Yagana ta tattare 'yan kudaden da suka samu, zahirin gaskiya’ sun wuce ‘yan kudade, masu dama ne.  Ta yi nufin isa Birnin Jidda gurin wata amintacciyarta da za ta. bawa ajiya.

Haka al'amarin ke faruwa ga duk wani mazaunin Kusha, babu aminci, barin dukiyarka a cikin Gidan da ba shi da wani tabbas (tsaro) ba kuma zai yiwu ka yi ta yawo a da su a Kugunka ba, sabi da gudun Bacin rana, ko ma su sunce su zube ba tare da ka sani ba a lokacin da ka ke haKilon samun wasu. ,

. A duk bayan wata guda biyu ko uku, da wuya ma akai ukun, ka kan shiga cikin Gari WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

‘ wurin wani amintaccen na ka ka bashi ajiya, ka kuma Kara nutsawa wajen roro wasu, idan sun taru ka sayi kayan da kasuwa take ja ga tubi wurgaran bangalai (‘yan kasar Bangaladash) da Pakistan,. (‘yan Kasar Fakistan) sai ko Turkawa da Yamalanai, a gurin su ne dai Ajnabai suka fi siyayyar kayan kasuwar da suke ja a can Gida Najeriya. .

- Idan an siyar a turo maka da kudin ka hada da wanda ka Kara rora ka danno wasu -kayan. .

Mutane da yawa sun azurta da wannan ‘layin ya zamo silar arziKi mai girma a garesu

kamar yadda ya zamo silar durkushewar wasu da mummunar hasara ka kasa amfanawa kai wani abu har ka Kare SHAHIADARKA (wato wanda ya zauna a Kasar Saudi ba bisa Ka'ida ba).

Zaliha ta yiwa Yagana fatan alkhairi ta kuma bata sautin ababen da take da buKata, kana ta taho musu da ruwan amfani domin kuwa ruwansu ya Kare. , Sannu a haakali zaman Kusha ya soma — ratsata da kuma uwa uban shakkun (tsaro) da ta ke da shi na ratsawa Birnin Jeddah, duk da kasancewar al'amura sun dai-daita, wadanda ma suke gudanar da sana‘a a cikin Haraj tuni sun koma bakin aiki.

A duk ranar Allah sukan shiga kuma su fito lafiya.

-Ta leKa Shemar su Ramlatu mutuniyar Kasar Somaliya da nufin samun ruwa kafin Yagana ta iso da shi.

Garin na Kusha babu ruwa ko da digo kasancewar wurin Sahara ne balle a tona a samu
Ruwa, da kuma cewa wuri ne da aka kafa shi ba bisa Ka'ida ba balle a sami tagomashin hukuma. Don haka duk wani ruwa da ake amfani da shi a garin Kusha
akan shiga cikin gari ne a lokutan "Hamsa Salawat" a debo a cikin _ Masallatai. (Abin nufi a lokacin ne suke a bude) cikin _ manyan Jarkoki, a kuma yi safarar su zuwa garin _ Kusha ta cikin rubabbun Akori-Kurar nan Kirar Toyota a kudin da ba su gaza Riyal daya duk . Jarka guda.ba  Idan kuwa duka Motar ka kama Riyal _ biyar za ka biya komai yawan adadin Jarkokin. . Ta yi mamaki Kwarai irin yadda garin ya ke da matukar hadakar jama'a yake kamawa a lokutan rana da yini. a Kai tun daga safiyar Allah garin yaiwasayau, sai dai-daikun jama'a wadanda suke da - sana'a ta din-din-din anan, sai ko ‘yan tsirari da wasu ‘yan uzurori suka hanasu zuwa, ciki har da Zaliha da take cikin hutu a wannan rana

kasancewar Yagana ta je adana musu kudi a Birni. _

Yagana ce idanunta kusan a kafatannin zamanta cikin Kasar Saudi.

A wannan rana ta kasance cike da samun afuwa, don haka ta yi nufin shirya musu abinci _ mai armashi.

Suka gaisa da Mallam Abdul-Rahaman, babban limamin Kusha, yana shirye-shiryen isa Masallaci da nufin Limancin Sallah.

Yana da nagarta don haka take matuKar

‘ girmamashi, har ma ya shiga tambayar, "Lafiya dai ko?" domin kuwa ya ga fitar ‘yar uwarta.

Kafin Yagana ta iso ta shirya musu abin motsa Baki mai armashi, babu laifi kamar dai ba _ girki na Zaliha ba, girki ne da aka kwaikwayeshi daga gidan abincin mutan Turkiya wato “Hugeke bab". .WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

- Dama can sun shahara wajen sarrafa , nama, a wurin Hauwa abokiyar zamansu ta koyeshi.

Gwana ce ta wurin sarrafa girki. Ta ma. lura akwai mutanen da kullum take girkawa abinci a garin na Kusha. ,

- Kafin ‘sallar Magariba kusan duk wani da yake zaune a Kusha ya iso daga duk inda yake sabi da duhu da rashin kyawun hanya, akan yi_

KoKari a iso Kusha kafin faduwar rana, kamar daga Karfe biyar zuwa shida na yammaci.Yagana ta iso cike da kaya fal cikin Ledoji - har sai da Hauwa ta taimaka musu.

‘Galibi kayan Abinci ne da kuma kayan : *amfanin YAU DA GOBE, don ko kwalliya baa . cika damuwa daita ba a wannan gari. a Wannan kam sai wadanda suke zaune cikin maraya ka ga ado har da Zinariya.-. - Ta cire baKar Abayar jikinta ta cire NiKab_ daga fuskarta, al'amarin da ya zama wajibi ga Matan Saudi, da ma wadanda ke cikinta ta ‘kowacce siga matuKar za su fita. Ta zube saman Katifarta mai cin mutum guda da galibi bakin haure suka fi amfani daita kafasarta Saudi.

Cike take da gajiya, ta yi shawagi cikin gari. ita ce har cikin Jeddah International Shopping Centre ta hada da Al-Mahmal Centre

- da Al-Sayiomar Kaseem Market, ga kuma rashin kyawun hanya wanda ya kan haddasar musu da gwabzuwar da take tsamar musu da jiki.

"Garin da ba naka ba bashi da wani dadin zama ga dan karen rashin ‘yanci." Yagana ta fada cikin nuna gajiyawa. Hauwa ta dauka. WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

- “Mu kuma mun nace zama daram daKau! _ Sai mun kai ga sa'ar tattare hatiman na Saudi ba?

Ko da tsiya ko da arziki, ko ana ha mazaha mata, ana KoKarin kai ruwa rana tsakaninmu da jami'an Saudi."

‘ Hauwa ta saka Huwaila dariya sosai, Ba ta cika shiga sabgar kowa ba, independer ce mai zaman kanta. - .

Zaliha kam ta yi shiru, ta yi tsit! kamar ma yanayin ya mortsa ma ta wasu al'amura.

Al'amarin’ da ya sa ta cikin wani irin yanayi, kusan duka ma da abin da ya tsugunnar


HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Post a Comment for "HAMADA BOOK 1 CHAPTER 5 BY ZAINAB KABIR BIROMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...