HAMADA BOOK 1 CHAPTER 4 BY ZAINAB KABIR BIROMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 4 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 4 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

- - Post a Comment

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 4 BY ZAINAB KABIR BIROMAN


                   Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA 

Zaliha ta dubeta cike da damuwa, don kuwa tana sane da cewa ‘yan kudaden da za su biya na hayar gida na wata mai kamawa babu shi, Kiris! ya rage a shigeshi, babu lamuni ko. KanKani a tsakaninsu da. Kafilin gidan (wakili)

balle akai ga Saudin da yake da mallakin gidan _ da yake da mayatar son kudi da nuna rashin ragaya. . . , "Mu wuce Kusha". * Takara nanatawa. Kusha!" ae _ ' “Mene ne kuma Kusha?" Zaliha ta tambaya cike da'yar damuwa Www.bankinhausanovels.com.ng 

" _ “Wani gari ne ko kuwa na ce miki wani . dan yanki ne da ke bayan garin Jeddah da mutanen mu suka kafashi suke kuma gudanar da sana'arsu. .

_ Akwai.samu, ga kuma kwanciyar hankali da nutsuwa, babu wani razani  a tattare da wajen". me

Zaliha ta gyada kai cike da gamsuwa.. : Yagana ta Kara da yi ma ta bayani. _ "Mutane da yawa sun nutsa can...Ke wasu ma a can suke tun kafin rikicewar gari. Sun ce can din ma yafi sauKin rayuwa, gashi kuma ana fita ayyuka ana kuma matuKar samu. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Idan ma mun so da zarar al'amura sun dai-_ . daita sai mu dawo cikin Jeddah City, unguwar ' Hindawiyya makofciyar Babal Shariff." - Anan Zaliha ta yi murmushi.

* * *

Zaliha tayi KoKari ta isa Haraj a bisa al'amarin da sukan kirashi da shahada. Nufinta kawai ta gode masa.  Sama da Kasa ba ta ganshi ba, duk wani
lalube da ta yi babu ko motsinsa. A Karshe wani jami'in _gudanarwar - Kamfanin ya ja kunnenta, baya son ganin burbushin ire-irensu a gidan Abincinsa, suje ya gode da cinikinsu, a banza suna son jazawa Kamfaninsu masiba, in kuwa ba haka ba zai - hadata da Askarawan Saudi.  Cikin nuna Kyara da ban-bami yake furta ‘ hakan cikin harshen larabci na Saudi.

ZAMU TASHI 


. KUSHA
RASHIN KYAWUN hanyar ya wuce misali Suka keta suka keto ta tsakankanin tsaunika da kwazazzabae fetal! Filin Subahana, Sahara mai fadin gaske mai cike da tarin yashi mai Kuna. . .

Haka suka ratsa suka kutsa ta bayan Birnin Jeddah da bangaren Kuryar Kasuwar Haraj.

Suka mike hanya dodar zuwa Kauye, Gari, . ko kuwa mu ce tsakiyar HAMADA, garin na Kusha

Filin Allah ne fetal! iyakar dubanka ' Sahara ce gaba da baya babu ko dogon Ganye balle Tsirrai face iska mai Karfi da ke kadawa a wajen,Www.bankinhausanovels.com.ng 

Akwai rukunin gidaje da aka yi su da Tanti (Shema), wasu kuma na Sandaka ne (Wato

ginin da aka yi shi da Katako)shi din ne ma ya fi yawa. .

, Akan buga Katako ayi gida sosai a rufe saman dakin da bangon dakin da Leda, a fitar da Taga da Kofa, Makewayin girki da Makewayin Bahaya da Wanka, a haKa Rami mai zurfi a saka Katuwar Garwa ko Robar Fenti. ‘

Anan ake tsugunnawa har zuwa lokacin da_ -

zai cika, mazauna Gidan su cire Garwar ko

. Robar su je can nesa da Kusha tsakiyar Sahara su yasar, sai kuma a Kara saka wata Garwar.. .

’ Galibi gine-ginen Sandakar.da Shemar akan yi su ne a tsakankanin Duwarwatsun da suke warwatse a wurin jefi-jefi, domin kaucewa

Karfin iskar da ke kadawa a ~ wurin. Wasu gidajen ‘haya ake, akwai masu shi. wadanda suka ginata daga cikin al'ummatan da ke zaune awajen. .

' Sai dai Hayar tana da matuKar rahusa, wata guda Riyar din da za ka biya bai.taka kara ° ya karya ba idan ka hada da wanda ake biyaa -.Www.bankinhausanovels.com.ng 

cikin Birnin Jedda, sai ka ga ma kamar wannan kyauta ne.

_ Wasu Gidajen kuma bana Haya bane, wuri ne filin Allah fetal! debi da kanka, ka yanka ka diba iyakar son ranka ka kafa Shema ko kuwa ma ka gina Sandaka (Ginin Katako) matukar nufin zama ka yi sosai a wajen, idan kana da halin gina SandaKar.

Idan ko ta bangaren al'ummar da ke wajen ne, ma iya cewa ta hade galibin dukkan wani jinsi da ya fito daga Afirika dama wasu daga cikin Kasashen Larabawan da tattalin arziKin Kasashensu yake da matuKar rauni kamar irin KASAR YEMAN. '

Ta barin al'ummatan da ke cékon Kasashen Afirika kuwa da sukafi tasiri a wajen, akwai mutanen Somali, Mali, Sudan, Itofiya (Ehtopta) da Iritiyiya (Habasha), Chadi, Nijer da makofciyarta Najeriya, da dai sauran Kasashe da dama daga cikin yankin Afirika da Musulmi ke da tasiri a ciki.

Zaliha da Yagana suka kasance cikin alfarmar Hauwa ‘yar mutan Chadi.

A bisa alfarmar tata ne ma suka iso garin na Kusha. A can baya sun san juna, sun ma taba zama wuri guda kafin Hauwa ta zabi zaman Kusha a bisa zama cikin Birnin Jeddah. ,

A cikin Shemar su Hauwa, domin kuwa sun yi sa'a Hauwa da Kawarta Nana ne kadai ke da mallakin Shemar. -
Take ta kunna na'urar girki mai aiki da iskar Gas, take ta tasar musu da ruwan gahawa Www.bankinhausanovels.com.ng 
Dakakken Kwallon Dabino da 'ya'yan Gahawa da Sukari mai dama) mai Karfi domin wattsake gajiya.

Kana tayi amfani da kayan Abincin gwangwani, take ta tasar musu girki mai dadi. Fried Chicken da kuma Shrimps. - girki ne da ta kwaikwayeshi daga babban Kamfanin nan na Sa'udi da suke matuKar ji da.
shi ta fannin Kaza da Abinci, wato AL-BAIK RESTAURANTA.

Yagana ta ci abincinta sosai. Zaliha kam ko tsakwari ta kasa yi, tsoro da firgici ne fal cikinta.

Wace irin rayuwa ce haka-cikin dokar

‘ daji? Ba daji bane. Kai gwanda dajin ko digon tsirrai ka duba . ka ji sanyi.. . Kawai sai ta dinga jin hawaye na zubar — mata a kumatu.

Babu shakka amincin da ke tsakaninsu-da~ Yagana ba ta zaci haka ba.

Sai dai hakan ba yana nufin ta kasa  dimbin alherin da tai ma ta bane, wata aba cebaza ta taba mancewa da ita ba a kafatanin zamanta a Kasar Saudi.

Ko ita Yaganar ta dan razana a lokacin da aka nuna filin Allah fetal tsakiyar HAMADA aka ce sun iso Kusha. .

Babu dogayen gine-ginen nan na Birnin Jeddah face tarin ginin Katako da Tanti.

Ko da ta san Kusha ba a cikin Kwaryar _ Birni-bane sai dai bata zaci irin haka sosai ba, amma dai ta dake ta matse, ko ba komai suna iya

. fita wuraren sana'arsu hankali kwance.

Dama me? dama bukatar Maje-Hajji ya yi Sallah!

Sai dai ta su buKatar ta kan tattara ne ga tara damman na Sa'udi, nufinta ke nan ta zama Hajiyar sosai ta Birnin Shehu Www.bankinhausanovels.com.ng 

. Wane al'amari ne ma ya fito da ita bayan wannan? , _ Zaliha ba ta dada kasancewa _ cikin damuwa ba sai bayan duhun dare, babu ko . Burbushin wutar Lantarki ko KanKani, garin yai dumdim babu dadin duba, illaka iyaka kusan duka Shemomin sukan yi amfani da Fitilar Acibal-bal mai amfani da Kalanzir, don haka wajen ya kan dan haskaka kadaran-kadahan. Sai ga Zaliha na kuka Hauwa na dubanta tana dariya. "Muma din haka muka yi kewar, zaki ware ne yarinya. Za ki ji cewa nan gaba zaman

garin Kusha ya fiye miki zama koda a cikin Birnin Riyal ne fadar mulkin Saudi Arabiya.

Ko ita Yaganar sai yaKe da Karfin hali ne, ba ta mancewa ko Kauyensu da ke can Birnin Shehu ya zarta.wannan wurin ababan more rayuwa nesa ba kusa ba.

Haka Hauwa ta dinga hidima da su har na tsawon kwanaki uku.

To ko a Musulunce haka ne Ka'idar, don haka Hauwa ta nunar musu cewar kowa din sai fa ya jajirce ya nemi na kansa, akwai nau'in . Sana'a nau'i-nau'l, sai fa wacce ran mutum yake so. .

Ai lallai sun gane Hauwa gaskiya take fada ba za ta iya hidima da su a haka siddan babu sidi babu sadada. . Ba

Da yake sun gane wurine na kowa tasa ta fissheshi, ga dai ba halin shiga Haraj har lokacin. Akwai Liman da yake jagorantar Sallolin nan wajibabbu ga duk wani Musulmi (hamsa salawal).

Har ma da Limancin sallar Juma'a a Garin na Kusha.

Jim kadan da idar da sallar Asubahi _ al'amura suka shiga sauyawa. Akwai yawaitar zirga-zirga da hada-hada ga ilahirin mazauna Kusha mata da mazansu. ;

Mafi yawa daga cikin mazaje sun nutsa tsakiyar Hamada domin isa ga kamfanonin da suke samun aiki, idan har an yi katari ke nan, kasancewar Ma'aikata ne na wucin gadi da suke fita neman aikin Kwadago a kowacce ranar Www.bankinhausanovels.com.ng 
Wasun su kuwa sako da _ lungunan Kauyukan Jeddah da ke maKoftaka da garin Kusha suke isa, anan ba mata ba maza.

Mata su yi barance (Aikin gida) su-yi_ bara, maza kuma su yi aikin Kwadago; kamar . kiwon dabbobi, saukar ‘ya'yan Dabino da  makamantansu.
A wurin Kauyawa mazauna garuruwan idan ka kammala sai su biyaka hakKinka, sai kuma wayewar gari idan kana da rabo Ajnabai basu riga sun cika garin ba.

, Wasunsu kuwa Haraj suke shiga su yi tsince-tsince a Bola su ci Kasuwa, kana a juyo - Kusha.

Babbar hikimar anan hanya _tsakanin Kusha da Haraj ba matsala, barauniyar hanya ce da ake bi ta bayan garin cikin rairayi mai Kubna, rairayin da jami'an tsaro ba sa iya tunkara sai fa idan ta yi matuKar baci. —

Wani ginshiki ma da ya dada tabbatar da garin Kusha shi ne wuri ne da yake a bayan gari, ya kuma hada galibin hanyoyin da kamfanunuwa da masana'antun Jedda ke ciki. — Kazalika ya yi kusa da kasuwar Haraj da Ajnabai (bakake) ke matuKar cin gajiyarta.

Don haka idan dai har sana'ar Kwadago ka ke garin na Kusha ya zame maslaha a gareka, ga nutsuwa hankali kwance babu hasarin kame, babu kuma tsadar haya, ga kuma sauKin isa ga wuraren Kwadago. .

Sai dai duk da hakan akwai wadanda zaunannu ne a wajen, anan suke ayyukan Kwadagonsu,a sai dai aje cikin gari lokaci-lokaci

ayo siyayya kamar mata masu girka Abincin siyarwa.

Da Liman da Malaman Islamiyya duka . suna karbar (Sail) sadaKa daga wurini mazauna Kusha.

Kazalika baka rasa masu zaman banza da marasa nagarta masu miyagun laifuka nau'l° nau'i, kamar; Karuwai, masu .zaman_ kansu, magajiyar da take tara mazan banza, ‘yan Daudu, ‘yan Agullan ‘yan daban da suka gagari gari,Www.bankinhausanovels.com.ng 

’ sukan sami mafaka a Kusha. Wasunsu ko zama ake tamkar na miji da mata har a jima a haife duk kuma ba tare da an Kulla Sunnar Ma'aiki ba (aure). . ,

_Akwai kuma masu zamba cikin amuinci (419) daga ko ina a cikin Saudin kana iya samunsu a Kusha matuKar Ajnabati ne; wasu ma |na ganin nan ne ma gidansu, mafakar da sukan bace a lokuten da suka aikata laifuka. .

’ Kazalika akwai masu sana'ar dogon hannu (sata) galibi sun fi buwayar al'ummar gari, wani’

sa'in ma na garuruwa daban-daban ne, idan ta yi halima har a cikin Kushaa akan taba sana‘ar.

Sai dai ba su cika tasiri anan ba kasancewar akwai tsarin shugabanci mai kyau a garin na Kusha da ya hada da hukumomin tsaro, hukumar zartarwa da ladabtarwa, duk dai daga cikin al'ummatan da ke cikin Kusha akan duba_ . dacewa da nagartarka kafin samun wannan matsayi daga kowacce Kabilar ka fito.

Kai idan wani laifi ma aka tafka a garuruwan Jidda, Makka da sauran garuruwan da Ajnabai suka yi kaka-gida sukan sami mafaki a Kusha kafin al'anmura su lafa.

Don haka muna iya cewa garin na KUSHA ya hada kowa da komai daga cikin

mutanen kirki da na banza.

Haka al'amura ‘suka dinga faruwa a idanunsu, kafin wani lokaci garin na Kusha ya dade sai ‘yan tsirarin da aka ambata a baya.

‘ A wannan lokaci Zaliha da Kawarta Yagana da su Jimi ‘yar Chadi sun nutsa tsakiyar Www.bankinhausanovels.com.ng 

HAMADA ba ji ba gani, ga zafin rana ga Kunar rairayin Sahara. , ‘ A haka har suka nutsa Kauyen ALBASATEEN. Garin yana hegen sananniyar Makarantar nan ta kasar, Birkniya, wato BRITISH INTERNATIONAL SCHOOL OF JEDDAH ~ Daga nan ne fa aka rarrabu, aka warwatsu loko da saKon Kauyen Al-Basateen. Ko kuwa mu ce kasancewar akwai ababen more rayuwa. - Jimi ta karya hannu ta kandareshi. ta sakeshi kamar wani shanyaye. Fadi ta ke; "Fisabilillahi! Fisabilillahi!! _ Karama fisabilillahi!!!" Wanda ya basu sai su amisa da . “Shukuran", Take Yagana ta bi sahu, hasalima har ta so ta fi Jimi nuna kasawarta (nakasa). . Haka ta ke, tana da matuKar basira da kwanya, ga jarumta da nuna jajircewa, duk wani - abu da ta saka a gaba. ,HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "HAMADA BOOK 1 CHAPTER 4 BY ZAINAB KABIR BIROMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...