HAMADA BOOK 1 CHAPTER 3 BY ZAINAB KABIR BIROMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 3 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 3 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

- - Post a Comment

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 3 BY ZAINAB KABIR BIROMAN
                   Www.bankinhausanovels.com.ng 
MUN TSAYA 

wannan sumame da aka kawo kasuwar Hadit da ke gefen Birnin Jedda. . Ya ci gaba da gudanar da dukkanin al'amuransa yana kuma lura da dukkanin al'amuran da ke faruwa, al'amura sun soma daidaita, sai dai har lokacin akwai kai komon jami'an tsaro. A tsorace, a firgice, a kuma razane ta. yunKura miKewa, ya gyada ma ta kai alamar hani. Ya yi amfani da sassauKan Larabci salon na Saudi wato: "Gargaliyya". Akwai matuKar hatsari gilmawarki a wannan lokaci, al'amura basu gama komawa yadda suke ba". Shi ke nan abin da ya ce ma ta, ya dai ci gaba da gudanar da al'amuransa. "Babu dalilin da zai sa dan Adam da Allah Ya girmamashi ya zo yana tozartar da kansa. Rayuwar nan ba mai kyau bace musamman ga 'yamace. . Www.bankinhausanovels.com.ng

Fuskarshi a daure ya fada kamar ma baya son dubanta, ya ma kau da kai daga barin da take. _. Ya dai sake yin amfani da sassauKan Larabcin ya ci gaba da fadin. "Kina iya wucewa. Sai dai akwai buKatar ki tattara nutsuwarki wun guda, hakan zai zamo mai afani a gareki". Har lokacin tana cikin firgici, hasalima a kidime take. _ Tana son ta gode masa, sai dai tuni ya * kauce. , Ko babu komai yai ma ta abin da ba kowane zai iya yi ma ta ba. Kuma ta mayar masa da martanin su din ba su zamo masu wulaKanta kansu ba face : wadanda suke lalube domin nemo halaliyarsu. Har kullum cike take da jin zafin irin haka.


ZAMU TASHI 
Hindawiyya hawa na uku, daki mai lamba ta hudu ta KwanKwasa Kofa kana ta murda mabudin Kofar, ta yi sa'a a bude yake. Tayi rashe-rashe a saman Katifa sai mai da numfarfashi take. Ta taso tana tangal-tangal kai ka ce wata bugaggiyace. — Ba buguwa ba ce, tarin wahala da dimaucewa ce kawai ta yi kab da ita a lokacin data gama saddakarwa. Kawai sai ta saka kuka,. dariya-dariya, murna-murna.  "Na gama saddakarwa kamen Askarawan nan ya fada kanki 'yar uwa. Ya aka yi ne? Ya ya. ne aka yi ku ka kubuta? Ke din daman nufinki ne kullum a kamaki, kin kasa ki goge ki guje, ki jajirce da artabun jami‘an tsaronnan, gashi ni ban ga wata tsiyar da ki ka taka ba*balle in yi tunanin lallai Kaddarar kamen ki ke so ta afka kanki."Www.bankinhausanovels.com.ng 

Lokaci guda yanayinta ya sauya, zuciyarta ta shiga harbawa ba ji ba gani. _

Duk wani hasken nan da ke zuciyarta ya gushe. Kowa din yana iya komawa gida da tunanin wani haske da yake tsammani,. da . tunanin wani farinciki da yake nufin tunkara, da

- tunanin shi din wani abin bege ne da ake maran har ma ya zamo abin so ga kowa. Ta iya yiwuwama shi din wani mai girman daraja da kima da

’ mutunci ne da ake duba.

Duka ba ta yi kuskure ba idan ta ce ta — hade ta tattare ta rasa duka wannan farinciki babu shakka za ta kasance mafi hasara daga

' cikin kamammun nan da aka yi nufin isar da su

_ gida. Dama dai rayuwarta ta Kare, ta gushe a

‘ haka...cikin wahala da Kunci, KasKanci da tozarci

matuKa, za ta cika da imani, shi ke nan abin da take marari. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yagana ba ta lura da yanayin da take ciki ba ta ci gaba da surfa masifa musamman mummunar hasarar da aka jaza musu,; duk cikinsu na ranar da ma ‘yan kudaden da ke

Kugunta wadanda suka fice da su sun watse, sun tarwatse basu tsira da ko Riyal guda ba face tarin wahala. Lokaci guda ta dora alhakin afkuwar lamarin akan Jabir. . _ Babu shakka ya munafurceta, domin kuwa ya nuna ma ta hanya ta yi kyau. (Jabir din daya ne daga cikin Askarawan Saudi, saurayinta ne sun jima ana harkar banza, shi ne ma bangon da ya tsaida Yagana a Birnin Jedda daram! Ya kan sanar da ita a lokutan da za a yi kame, don haka sai sukauce). - _ . Wasu ‘yan kudade da Yagana takewa masifa duk ma basu dameta ba, duk da cewa kudade ne masu girma, basu dameta ba, ba ta - ma iso Kasar domin tarasu ba, ba ta ma zo domin - afkuwar al'amuran da ke afkuwa a gareta ba; Al'amuran bawa sukan kasance cikin sauyi ba da sani ba a lokutan da Ilahi ya so. - §harr! Sai ruwa ya shiga fitowa daga ‘ idanunta, duk dai al'amari ne da ya ratsa zuciyarta.

Yagana ta kasance cikin mamaki a lokacin da ta ankara da yadda Zalihar ta kubuta, ta dinga mamakinta tana nanantawa.

."Na yi mamaki fa! Dan bakin mutumin mai duban kowa Kasa-Kana? - Yana wani dubanka kamar kashi? Yana - dubanka da KasKanci? Ban yi tsammanin haka - daga gareshi ba". , Zaliha ba ta ce komai ba, tunanowa take wace hanyar za ta bi ta koma Haraj ta yiwa wannan mutumin godiya, yai ‘mata ceton da ba -za ta taba mancewa da shi ba. . ~ A wannan kame da jami'an tsaron Saudin  suka gudanar sanadiyyar laifuffukan barace-barace, mayar musu da hanya wuraren saye da sayarwa, kazalika tare da haddasa musu tarin _ Kazanta a yankunan kasuwar Hadit da Haraj, don = - ‘haka suka’barzama kewaye da zagaycn kasuwar ta Haraj aka shiga kamen kan mai uwa da wabi, da mai laifin da ma wanda bai ji ba kuma bai '. gani ba.
Yagana ta sambatu tana kewar abokanan zuamanta, musamman Cima. kamen ya rutsata da ita a bisa shammaci domin kuwa ba harkar saye da sayarwa ta cika ba, kat ba ma ta yi, . kasancewar Cima Kwankwareriyar Kilaki ce da samunta kacokam ya dogara ne a bisa wannan . mummunar dabi'a da take dubanta matsayin babbar haja, har ma a wasu lokutan take yiwa  ire-iren su Yagana jagora,Www.bankinhausanovels.com.ng 

Zaliha kam na ta rayawa a ranta idan dai ire-iren -su’ Cima jami'an tsaron Saudi suke damKewa su kuma aike da su gida, to babu shakka da an ce sun yi dai-dai matuKar ba su ba da suke yunKurin neman halaliyarsu, su gurgura su Karashe rayuwar da tai musu saura kafin zuwan sa’i.

Da aka dan kwana biyu aka nutsu kuwa Bebin Yola ta nutsa Makka.

A cewarta can din yafi dama-dama sakamakon kwazazzabar Askarawan da sukewa bakin hauren a kafatanin Birnin na Jedda, sai fa in tsautsayin bai rutsa da kai ba. To ta ina za ka sami zarafin fita balle ka nemi na kanka? .

Ita kuwa Mai Gado ta makale a can

_ Ashafbatly, wani gari (Kauye) da ke cikin yankin Jedda.

Ana matuKar samu fiye da kasuwar Hajraj, don haka ta sauya sheKa daga Hajraj din zuwa Sharbatly, a.cewarta akwai samu hankali cikin ~

_ nutsuwa ba kamar zaman dari da ake cikin garin Jedda ba, suna bara suna samun ‘yan kudade da abinci da tarin gumama mafi kyau.

Da zarar gari yai kyau za su iso  haraj su ci kasuwarsu.

Wasun su ma sun fara yunKurin aikewa . da su gida da basu iya haKurin kasuwar Haraj ta daidaita ba. .

- Ko da yake sun ce idan aka aike da su gida (Najeriya) ai an samu sai dai kawai‘tarin- 'yan kudaden da ake kashewa kafin isar su ta -Karkashin (CARGo) Jirgin saman daukar kaya mallakin Kasa, wato Nigerian Air Ways (CARGO).

Rayuwar ta yi matuKar yi musu tsauri, wasu Kabila ne:da suka fito daga Kudancin Najeriya ke KoKarin bata musu gari da sacc-sace, ‘zamba cikin aminci (419), wasu da suka fito Www.bankinhausanovels.com.ng 

, daga cikin Kasashen da suka fito daga cikin yammacin Afirika suka fi shuhura wajen shaye-shayen “ mugayen Kwayoyi, ana iya cewa daga kowanne bari na Kasashen duniya. . - A sana'ar Karuwanci kuwa ‘yan Kasar ' Chadi sun zamo Zakaran gwajin dafi!

Fataucin Kananan Yara da harkar Bara

‘yan Najeriya sun zamanto ja gaba a wannan _ fanni, bayan wasu ‘yan tsirarun laifuffukan da " suke aikatawa.

Don haka jami'an tsaron na Saudi suka tashi haikam wajen yaki da mugayen mutancn da suke neman gurbata musu Kasa.__

Ayyukan yi suka Karanta sai zaman dari da firgicin kame. . ,

Kusan dan abin da aka tara na neman Karewa a biyan kudaden Haya, ci da kuma sha da

_ sauran buKatun dan Adam na yau da gobe, balle  ma wata irin rayuwa ce da aka fadadata da fadin gaske, ala tilas sai an yi zaman kece raini da jin - dadi, don haka komai yawan kudaden da aka samu sukan nutse cikin wadannan buKatu, musamman ta fannin mata mazauna Shahadar.

“Yagana na matuKar yi musu KoKarin musamman ta fannin biyan kudin hayar gidan, shi ne ma babban tashin hankalin bakin hauren musamman a wannan lokaci da suka kasance su ~ biyu kudaden sun yi musu nauyi, fama-famai na Saudi har fam goma sha takwas, adadin Riyal dari da tamanin a wata guda daya tal
Babbar hikimar da ta sa akan yi zaman hadakar ke nan; za ka iske kamar mutum hudu zuwa takwas a cikin dan Karamin daki guda a Kalla ka sami saukin ‘yan kudaden hayar Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ga dai rashin abin yi sabi da rashin tabbacin hanya. Hanyoyin duka sun lalace da jami'an tsaro.

Takamar dai ta Haraj ce, Askarawan tsaro kuma na yawan datse hanya a shiga kamen mai uwa da wabi. .

. Idan ma ba a Haraj din ka ke cin kasuwa . ba, kana dai da abin yi, abin yin da ka riKe shine ~ sana'a, ka ke kuma samu, abin yin da tilas sai ka fita ka nema, a kuma jajurce wajen yinsa, koda kuwa sana‘ace ta rashin gaskiya.

To kusan duk hanyoyin sun bi sun datse, don haka mutane da yawa suka shiga yin Kaura zuwa garuruwan da ke KarKashin yankin Jeddah, can ma ana samu ga kuma sauKin fita neman na

. kai babu idanun jami‘an tsaro a kai

++++++
Zamman ya zame mana dole, nikam haka ‘ne a gurina ban sani ba ko haka ne a idanunki?" Yagana ta ce da Zaliha. . Lokaci guda ta ci gaba tana mai dan jan tsaki.  "Ban taba nufin zama a wani Kauye ba Birni ba, ko a ina ne Yagana ta saka Kafafu..." Ta Kara yin dogon tsaki. - . "Tilas ne mu bar Birnin Jeddah matukar — ba fatan aikewa da mu gida muke fata ba. Dan Askarawan nan sun matsa, idan ma mun nace mun zauna din ayyukan yi babu tunda babu halin shiga Hadit a halin yanzu, 'yar walwalar - ma da ake duk dai hakan ta gaza samuwa, mafita kawai mu wuce KUSHA", > . Zaliha ta dubeta cike da damuwa, don kuwa tana sane da cewa ‘yan kudaden da za su biya na hayar gida na wata mai kamawa babu shi, Kiris! ya rage a shigeshi, babu lamuni ko. KanKani a tsakaninsu da. Kafilin gidan (wakili)

balle akai ga Saudin da yake da mallakin gidan _ da yake da mayatar son kudi da nuna rashin ragaya. . . , "Mu wuce Kusha". * Takara nanatawa. Kusha!" ae _ ' “Mene ne kuma Kusha?" Zaliha ta tambaya cike da'yar damuwa Www.bankinhausanovels.com.ng 

" _ “Wani gari ne ko kuwa na ce miki wani . dan yanki ne da ke bayan garin Jeddah da mutanen mu suka kafashi suke kuma gudanar da sana'arsu. .

_ Akwai.samu, ga kuma kwanciyar hankali da nutsuwa, babu wani razani  a tattare da wajen". me

Zaliha ta gyada kai cike da gamsuwa.. : Yagana ta Kara da yi ma ta bayani. _ "Mutane da yawa sun nutsa can...Ke wasu ma a can suke tun kafin rikicewar gari. Sun ce can din ma yafi sauKin rayuwa, gashi kuma ana fita ayyuka ana kuma matuKar samu. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Idan ma mun so da zarar al'amura sun dai-_ . daita sai mu dawo cikin Jeddah City, unguwar ' Hindawiyya makofciyar Babal Shariff." - Anan Zaliha ta yi murmushi.

* * *

Zaliha tayi KoKari ta isa Haraj a bisa al'amarin da sukan kirashi da shahada. Nufinta kawai ta gode masa.  Sama da Kasa ba ta ganshi ba, duk wani
lalube da ta yi babu ko motsinsa. A Karshe wani jami'in _gudanarwar - Kamfanin ya ja kunnenta, baya son ganin burbushin ire-irensu a gidan Abincinsa, suje ya gode da cinikinsu, a banza suna son jazawa Kamfaninsu masiba, in kuwa ba haka ba zai - hadata da Askarawan Saudi.  Cikin nuna Kyara da ban-bami yake furta ‘ hakan cikin harshen larabci na Saudi.HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "HAMADA BOOK 1 CHAPTER 3 BY ZAINAB KABIR BIROMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...