HAMADA BOOK 1 CHAPTER 2 BY ZAINAB KABIR BIROMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 2 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 2 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

- - Post a Comment

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 2 BY ZAINAB KABIR BIROMAN                     Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA 

Zaliha ta dan tabe baki, gajiya kam ta gaji matuka gaya. ~° — 


"Kamar zafin nema baya kawo samu, ‘yan ' kudaden da muka samu a kwanakin nan basu ishemu rayuwa na wani lokaci mai tsayi ba? Ehem Yagana.:." ’ Ta Katseta. 


"Yan kawowa wani sa‘in, ehem zafin nama ba, irin dai yau din nan ai lallai Kwazo da KoKarin mu ne ya kaimu ga samun abin da aka samu, da mun zauna nan kwance da bamu kai ga samu ba". 


Zaliha taja ta tsaya daga tsotsar Madarar tana dubanta. 


"Wai in tambayeki ma Zaliha? Uhum in _ tambaye ki?" ‘Ta Kara zakudowa. ° . 


. "Ke din ba ki da wani tanadi ne? Ba ki da -wani tanadi da ki ke fatan tsinanawa kanki abun kirki balle ki hango dangi na gaba da suke cikin — tsananin bukata


. Me ye ne a Kasashenmu face fatara da yunwa da ya yiwa mutanen mu katutu". Haka ki ke so ki Kare shahadarki a banza ba tare da kin amfanawa kanki da komai ba balle na gida ya saka ran tsattsaga da zarar Kaddarar komawar gida ta afko mana (Kame)”. Zaliha ta miKe ranta a bace. 

ZAMU TASHI 


* “Ban taba tunanin na iso Kasar nan domin _ tattara dukiya ba, ban taba tunanin na zo ne domin in azurta ‘ba, ban taba tunani.....ban taba tunani....."
Haka ta shiga jerowa cikin wani irin - yanayi mai tsoratarwa, ka yi tsammani ta fice ; daga hankalin tane haka nan ta kan kasance a lokutan da motsin wani abin da ya shafi gida ya ratsa zuciyarta.

Bebi mutuniyar Yola daya daga cikin mutanen da suke daki guda tayi Kwafa taja tsaki. - Www.bankinhausanovels.com.ng

"Da -gan-gan ma Yaganar ta ke KoKarin shiriritar da kanta akan yarinyar da alama yunwar abin da za ta kai baka ne ya kawota Saudi ba neman dukiya ba".

Ita kam Mai gado fadi take, "Dama dai duk kun tsai da hankalinku guri guda, ga wata samuwar nan a Al Hijrayi". (Kauye ne a cikin yankin Jidda). -
Mutanen Chadi sun nutsa sosai suna - samun alheri mai zai hana muma mu gwada tamu sa'ar",

Haka zaman ya ke ba a yiwa juna kyashi akwai matuKar hadin kai).

Cima ita daya data fito daga Kasar ta Niger, da take a cikinsu baki daya ta dubesu.

"Ku ma wasu wawaye ne duka ma kamar

.. Iskance take yawo da mai kayan Kara'‘..kamar yadda ku ‘yan Kasar Hausa ku ke fada, ban ga dalilin da zai sa in wahalar da gangar jikina a .banza ba alhalin ga jari guda a tattare dani". Ta yi nuni da gangar jikinta.

Washe gari’ma an ci kasuwar sosai a’ Haraj, kamar yadda. Yagana ta so, suka wuce Pizza Restaurant, wannan karon Chicken Burger aka yi nufin ci. .

Da farar riga da bakin wando da bakin

Takalmi. Www.bankinhausanovels.com.ng

Tsaf! Shar! Tas! Ya Karaso riKe da Katon Trey a hannunsa kamar rashin sa'ane kusan

kowace rana (saifa dai-daiku) al'amuransu sukan fado hannunsa duk da kasancewar ba shi ne kadai mai hidimar raba abinci a Mut'am din ba. ; Baki ne kamar mu, sai dai yana da kyau irin na Sa'udan garin nan. ; "Shi yasa yake mana shan Kamshin nan". Yagana ta fada cikin saitin Kunnen Zaliha. Ko da yake ba rada ba ce muryarta a bude take maganar.  Zaliha ta kau da kai, ta rasa dalilin da zai sa ka damu da al'amuran wanda ma bai san kana yi ba. Bai dubeta ba balle ya dubi Yaganar da ko da ido yana iya fahimtar saKonnin da take aika. mishi, ya wuce abinsa. Kai ya ma bar sassansu ya nutsa cikin  yiwa wasu Abokanan huldar nasu hidima. Mut'am (Gidan Abinci) ne mai girmaa a mutanen Kasar Italiya ya sami karbuwa — da farin jini a kafatanin Kasar ta Saudi.

" Don haka suke da rassa daban-daban a kafatanin yankin Kasar, musamman ma manyan biranensu da ya hada da wannan reshe'nasu da . ke cikin garin na Jiddah.
Yana da tarin Ma'aikata masu Kwazo a sassa daban-daban, a gidan akwai_ sassan gudanarwa da sassan da ke kula da girka abinci da sassan da ke kula da amsar kudi da bada_ Tikitin Abinci da ma sassan da ya ke karbar

- Tikitin. ., .

Haka zalika da sassan da ke kula da tsaftar kayan Abincin da sassan da ke kula da tsaftar Kwanonin girkawa da Kwanonin zubawa da sassan da ke kula da tsaftar shi kansa Mut'am din -baki daya. ;

* * *

Kwana biyu hanya ba kyau ana yawan -  tsare hanya, anan ne ake kamen bakin haure da suke zaune ba bisa

Ka'ida ba, don haka kwanaki kamar biyu zuwa uku Haraj ta yi wuyar shiga, sai dai aci a sha cikin abin da yake hannu. Www.bankinhausanovels.com.ng

Irin hakan.a wasu lokutan daman tana faruwa musamman idan aka sami bullar wasu  laifuffukan da suke kai komo a yankunan da bakin hauren ke da zama da sauran wuraren.

Da ya ke a wannan lokaci an soma lalata musu gari da yawaitar sace-sace a manyan Kantunansu, akan datse hanya da nufin bincike a_

- kuma cafke bakin hauren da ke zaune ba bisa Ka'ida ba madamar tsautsayi ya gifta maka, domin kuwa kullum cike suke da dabarun kaucewa kaman Askarawan Saudi Arebiya.
Tuni al'amura sun soma kan-kama a lokacin da suka iso Ganyari domin shiga Motar Haraj, kasancewar al'amura sun soma komawa - yadda yakamata, sai dai ba har can ba.

- Yana "Hadit, Haraj". Ya dubeta yana dan murmushi da farar Jallabiya Kal! A jikinsa,

saman kanshi jan Rawani mai ratsin fari da akai, irin na shigar mutanen Saudi. "Babu shakka yau na kasance cikin samun tsananin sa‘a". Abdallah ya fada yana dan murmushi. Ya - dade yana Kaunar Yagana, gashi kuma ita din kamar ta raina Kurarshi. . . Ta den harareshi. “Bani wuri in shiga". .  Ya dan bude -gidan gaba, ta ko Kara hararar tashi. _ “Mugu! Muguntar ku ta mutanen Chadi za ka gwada min? Askarawan Saudi su datse hanya ka arce ka guje ka barni su tunkuda Keyata zuwa Kasata Nijeriya. Bana tunanin ko a tunani za ka Kara tunano ni"... — ~ Yagana ta fada cikin kakkausan harshe. = . A'a ke dai kawai ki ce ina ke ina wani dan kuci ku bamu Abdullahi, irin amasan yanzu sai manya, mu din ba komai bane. Hajiya Zaliha ya al'amuranki? Kina jin mu da mutuniyar taki ko?" Www.bankinhausanovels.com.ng

Zaliha ta yi murmushi.

"Bani wuri in shige Abdallah Garin da sauki-sauki ai ka sani, mu zauna a bayan ya wadatar duk dai wuri guda zamuisa". - —

Tuni ta tattare doguwar Jallabiyarta har Kasa ta yunKura ba tare da wasa ba ta dare bayan_ . Akori-Kurar Abdallah. Kafin wani loakci Motar ta cika.

. Sai kacacar-kacacar ka ke ji, kasancewar titi an saki sayiyiyar hanyar yanke ne ko ko mu ce ratsen gefen gari hanyar da ko Kwalba babu

' duk domin kaucewa Askarawan Saudi Arebiya.

Yadda mutanen cikinta suke zaune ba bisa Ka'ida ba hakan nan Motar da mai ita da ke jigilar Jeddah zuwa Haraj duk ba bisa Ka'idar ake ba, don haka suke kaucewa dukkanin wata .

’ hanyar da hukuma ta san da shi.

Fasinjojin kuma suke tsoron shiga gidan gaba ko na tsakiya sabo da, tsoron haduwa da Askarawa, don haka sun gwammacewa zama a bayan Motar inda da zarar ka ji wani motsi za ka dira ka arce ba tare da wani bata lokaci ba. .

Lokaci zuwa lokaci ta kan yi ajiyar zuciya , sabi da tsabar rashin kyawun hanyar duka jiki sai ya sami motsuwa, al'amari ne da ya riga ya zamewa bawa dole. . Www.bankinhausanovels.com.ng

Ita kam Yagana sai 'yan guna-guni take, ga hanya babbar Kwalta daga Jedda zuwa Hajar a sauKake sai dai babu halin ratsawa, Ga dai tsadar abin hawa Riyal dai-dai har goma, (AsArar Riyal) motoci ne na isa na alfarma (Limozine) musamman ma a Kasashen Afrika, ko da yake ba tsadar abin hawan aka fi dubawa ba, a'a hatsarin

. da ke tattare cikin bin sahihiyar hanya kasancewar za ka iya kicibus da jami'an tsaro.

Don haka suka gwammacewa shiga rubabbun motcin da akan bi a hadasu ta barauniyar hanya a kudi da bai gaza fam arba'in zuwa hamsin ba.

Cikin wannan yanayi suka Karaso Haraj ko .kuma Hadit da Larabawan Saudi suka fi fada,. . .

Abdallah ya karbi hakKokinsa daga wurin Passenger tuni Yagana ta yi gaba, Zaliha kam ita

ta tsaya tana yi masa godiya, duk dai albarkacin Yagana kusan tun saninta da Abdallah bai taba amsar kudin Motarta ba, gashi kuma Yaganar ba ta duban Abdallah a matsayin wani mutum mai daraja. . Kasuwa ta yi kyau fiye da tsammani musamman da ya ke kwanaki masu dan dama ba a sami damar isowa Haraj ba, don haka bolar ' tsintsir take da ababen alfanu musamman wannan ~ rana da Arab Supply Treading Company - (Kamfanin da ke harkar amfanin Gona) suka iso da bolar Kamfaninsu. Abn tsinci na tsinta, an sai da na sayarwa, ‘yan wadanda suka yi saura an yi nufin komawa da su gida. Anan din ma akan ci kasuwar su musamman ga mutanen da ba su da ra'ayin shiga Haraj da kuma baki da ba su ma wanye da Haraj ba. A dai-dai bakin Vera Pizza Restaurant, Kiris su Karasa ciki, Zaliha na daga gaba Yagana na bayanta tana cikin tarin nishadi, an jima ba a yi samuwa irin ta yau ba. '

A lokaci guda al'amuran suka yi KoKarin sauyawa mutane da dama galibi da suka fito daga yankin A firika suka shiga gudun in baka yi

. bani waje. Ba a duban gaba bare duban baya, - KoKari na tsira da kai.

Baka wani buKatar bayani balle dogon’ nazari. A lokacin Askarawan Kiris ya rage. su Karaso. . .

Yagana ta yi wani tsalle ta dire, ta yi  kwana ta lakwasa barinta na hagu ta miki layin Kantunan Shagunan Haraj.

Kafin wani lokaci ta bace cikin jama'a. Tana da saurin motsi. Wani lokacin kana iya ...

‘ dubanta matsayin hatsabibiya. .

” Ta rude ta kidime ta ma diririce baki daya. Akwai rashin tabbas sai dai duk da hakan tayi amfani da laKaninsu ta dora Kafa bakin Kofar Vera Pizza Restaurant. Www.bankinhausanovels.com.ng

Bisa SHAHADA aikuwa idanu ya dawo kanta, cikin rufaffen dakin da aka tanada domin abokan_.

Baki ne masu izinin zama a Kasa da ma tsirarun Larabawan na saudi sai ko wasu daga cikin ma'‘aikatan da ke kulawa da walwalar

‘ abokan ciniki. Ke nan babu wani idon sani, sai ' shi daya tal! da ya duKa gaban Katon Teburin da yake harhadawa abokan hulda abinci.

Ya dubeta ta dubeshi, ta kuma Kara - dubansa_ cikin wani irin karayar zuciya, yanayinta kadai zai nunar maka da tsagwaron firgici da tashin hankalin da take ciki.: -

Zuciyarsa ta shiga wani irin Kunci na.

_banzatar da kai da al'amarinsu na Kasashen Afirika ke yi, abin da kan janyo musu raini. A lokaci guda Askari guda ya sako _ Kafafunsa cikin rufaffen ‘gurin Vera Pizza Restaurant.

Ba ta sani ba ko ta sani? Ta dai cusa kai a takure, ta kanannade ta kuma cure wuri guda a Karkashin Teburin d ya kau da kai ya kuma ci gaba da ayyukansa duk ' da kasancewar hakan matuKar hatsari ne a

gareshi, kusan kowa din ya _ ga_ shigarta KarKashin teburin sai fa wadanda suke haramar - shigowa a lokacin da ba za su iya sanin abin da ke KarKashi ba, kasancewar teburin rabe yake da bango a .jikin bangon wajen ma aka likashi, zaunannen Teburi ne da ake hidimar shiyawa abukanan hulda abinci. Ya Karaso cikin kwarjini da isa na jami'in~ - tsaron Saudi, ya dan yi waige-waige, daman baya tunanin akwai bara gurbi a ciki, domin kuwa ko a ruwa mara gaskiya aka ce gumi yake Ya dan yi shawagi a cikin rufaffen ginin kana ya yi JAN KUNNE ga Ma’aikatan da ke bisa bakin aiki, shi ke nan ya fice Kwas! Kwas!! Kwas!!! - : Ko da yake, Motar Askarawan na nan kafe a bakin gidan abincin na mutanen Kasar Italiya. Duriya (Motar kamen bakin haure da masu laifi) ma ta iso da mutane makil da aka yi

nasarar cafkewa a wannan sumame da aka kawo kasuwar Hadit da ke gefen Birnin Jedda. . Ya ci gaba da gudanar da dukkanin al'amuransa yana kuma lura da dukkanin al'amuran da ke faruwa, al'amura sun soma daidaita, sai dai har lokacin akwai kai komon jami'an tsaro. A tsorace, a firgice, a kuma razane ta. yunKura miKewa, ya gyada ma ta kai alamar hani. Ya yi amfani da sassauKan Larabci salon na Saudi wato: "Gargaliyya". Akwai matuKar hatsari gilmawarki a wannan lokaci, al'amura basu gama komawa yadda suke ba". Shi ke nan abin da ya ce ma ta, ya dai ci gaba da gudanar da al'amuransa. "Babu dalilin da zai sa dan Adam da Allah Ya girmamashi ya zo yana tozartar da kansa. Rayuwar nan ba mai kyau bace musamman ga 'yamace. . Www.bankinhausanovels.com.ng

Fuskarshi a daure ya fada kamar ma baya son dubanta, ya ma kau da kai daga barin da take. _. Ya dai sake yin amfani da sassauKan Larabcin ya ci gaba da fadin. "Kina iya wucewa. Sai dai akwai buKatar ki tattara nutsuwarki wun guda, hakan zai zamo mai afani a gareki". Har lokacin tana cikin firgici, hasalima a kidime take. _ Tana son ta gode masa, sai dai tuni ya * kauce. , Ko babu komai yai ma ta abin da ba kowane zai iya yi ma ta ba. Kuma ta mayar masa da martanin su din ba su zamo masu wulaKanta kansu ba face : wadanda suke lalube domin nemo halaliyarsu. Har kullum cike take da jin zafin irin haka.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG


Post a Comment for "HAMADA BOOK 1 CHAPTER 2 BY ZAINAB KABIR BIROMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...