HAMADA BOOK 1 CHAPTER 1 BY ZAINAB KABIR BIROMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 1 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 1 BY ZAINAB KABIR BIROMAN

- - Post a Comment

HAMADA BOOK 1 CHAPTER 1 BY ZAINAB KABIR BIROMAN


                Www.bankinhausanovels.com.ng HARAJ! HARAJ!! HARAJ!!!" Abu hamza ya fada a lokacin da ya ke 


‘nuni da yatsun hannunsa jikin Motarsa _ Kirar Akori-Kura, TOYOTA HILUX da ta yi_ - - matukar nuna gazawa. -


A dai-dai lokacin Yagana tare da Kawarta 


Zakiha - suka keto karshen Unguwar 


HINDAWIYYA, suka Karaso yankin GANY ARI 


wurin da BAKIN HAURE suka mai da shi tashar 


Motar zuwa kasuwar HARAJ ala tilas! 


' Ta daga Kafafunta yunkuri guda ta diraa bayan Motar Abu Hamza, wurin da a bisa al'ada_, aka tanada domin zuba Kaya. : 


Ta yunkura ta janyo hannunta, cikin nuna Kwafa ta ce, "Na ga ranar da za ki wartsake ki saki jikinki, ki san cewa nan din inda ki ke wuri


ne da ya ke buKatar jarumta da jajurcewa ba lalaci ba". Yagana ta ce da Kawarta Zaliha. 


Abu Hamza ya ci gaba da fadin; 


"HADIT! Hadit!! — Hadit!!! HARAJ! Haraj!! Haraj!!!" 


Yana sake maimaitawa har ma ya lura Motar ta cika fal! da Passenger Gaba Mutum biyu, Gidan Tsakiya wanda ya ke shima a rufe Mutum hudu. 


. Sai kuma Gidan Baya da ke dauke da Mutane har takwas. Kowanne bari na cin Mutum hudu. . 


Tsakiyar wurin kuma shake yake da kayan , matafiya, wadanda galibi Gumama ne (tsofaffin Kayan Larabawa).da za a ci Kasuwar su anan 


Kasuwar Haraj. _ . Abu hamza ya miqi hanya ‘ba tare-da wani fargaba ba, don kuwa yana da tabbacin hanya lafiya, tafiya ce da ba ta wuce ta tsayin kilo mita biyuba. .

A haka har suka iso Kasuwar Haraj, Abu Hamza ya karbi hakKinsa Riyal biyu-biyu, — _ sannan kuma ya yi nufin kama gabansa. Da Kyar! ta ke iya jan fagon kayan bugu guda, ga dai nauyi ga kuma tarin yawa. Yagana ta dubeta a hasale. . “Da zafi-zafi akan bugi Karfe!" . . Ko ba ki ji karin maganar da ku Hausawa ku ke fadi ba?"A bari ya wuce kuma shi ke kawo ’ RABON WANI!" Ta finciketa hade da nata kana ta sabesu: a * Kafadunta, Zulaiha na binta kamar Rakumi da. Akala, suka kutsa cikin kasuwar Haraj har suka . dangana da Karshen kasuwar gefen hanya wurin _ da Takari suke baje kolin Hajarsu, daga nan aka shiga cin kasuwa ka'in-da na ‘inda. Galibi baki daga Kasashen (Africa) Afirka _ _ daban-daban ke cin kasuwar, wannan rukuni na kasuwar Haraj dama bakin haure mazauna Kasar da suka fito daga Nahiyar ta (Afnca) Afirka 


. idan kuwa ta fannin masu tallata Hajar ne 'yan Kasar (Chad) Chadi sun yiwa kowa zarrah, kusan ma su suka fi cin gajiyar sana'ar_—


Sun nutsa saKo da lungunan Kauyukan Jiddah domin yin Barah, sukam baranto Kaya _ masu kyau su zo su Kwalar da su a kasuwar ta Haraj. Wani nau'i kuma na Kasuwar Gumama da ke cikin Haraj, akan same su ne ana cikin Haraj. 


. Cikin wata katafariyar Bola da hukumar tattara shara take yasar da ita anan, wani sa'in . Sharar Gidajen Sa'udan ce, wani sa‘in na Kantuna, Gidajen Abinci da kuma Kam fanunuwansu da dai sauransu. .. . 


- Takari kan tone Bolar iyakar Karfinsu da nufin samun rabo, ko mu ce dubi da kanka, domin kuwa sai dai ka tone ka duba iyakar iyawarka, ba domin ka rasa abin tsinta ba, kayane masu inganci da suka hada da Suttura, kayan Lantarki, Katakon Daki (Furnutures), Shimfidun daki (Carpet) Kai! wani sa'in abincin gwangwani, Nama, Kifi, sandararriyar Kaza 


tamkar daga freezer aka zarota, kayan lambu da . __ dai makamantansu, duk ana tsinta a bolar da ke cikin kasuwar Harajin. . Idan ko Allah Ya tarfawa garinka nono har ‘yan Kudade da Zinariya kana iya tsinta, Agoguna masu kyau da Takalma na isa masu matuKar Kudi irin na Sa'udan na usul da ba ka isa rabar Kantinan da ake siyar da su ka ce za ka siya ba sabo da tsananin tsadarsu. Haka za ka yi ‘ta tsintar. kaya kala-kala,. balle ma kuma ranar da Kamfanunuwa suke fito_.. da Shararsu, anan kam ana matuKar Karuwa. Don haka kayan da ake lalube a Bolar Haraj, Kaya ne masu inganci da tsada da aka .. * saka domin Sa'udan. Wasun su ma ba a sakawa, idan kuma an sakan ba su wani sha jiki ba, idan kuwa sun sha din ma kai din baka isa ka sayi sababbinsu ba sabi da tarin kudi. : Don haka kasuwar Takarin ta Haraj take ‘mutuKar ja musamman ga baki da suka fito daga yankunan (Africa) Afirka daban-dabam. . 


Wasunsu kuwa sun fi mai da hankaline da - tsintar Karafa da (Alminiyom) Alminiyom, (gwana-gwanen Lemo sukafi yawa), inda zasu 


’ kai wurin masu siya da suma suka fito daga yankin Afirka a auna kilo-kilo a baka Kudin . adadin kilonka. . 


Kilon baya wuce Riyal daya zuwa biyu. Da ya ke irin wadannan mutanen suna da igama (Takardar izinin zama a Kasar) sukan kai Kamfanunuwa su siya su basukudin. —


Tana da tarin sa'a duk wani al'amari da ta saka a gaba ta kan yi KoKarin ta gano bayansa, bata da kasala bare nuna gajiyawa. * 


_ Yarinya ce mai karsashi a wani lokaci ka ce ta hada jinsi da mutanen Boye sabi da saurin motsi, kafin wani lokaci duk wani abu da suka zo da shi Haraj da ma wadanda suka yi Asubancin tsinta a bolar Haraj sun Kare sai ‘yan tsirari da amfaninsu ba shi da wani yawa suka yasar, duk dai cikin Kwazo da juriyar Yagana. 


Kasuwa TA YI KYAU, saura dame? Mu wuce italian Vera’ Pizza Restaurant mu yi guzurin Pizza Vera 


(Nadadden Burodi mai nama da kayan lambu a ciki) sannan mu ci Abinci mu wuce gida Hindawiyya ko ma kai haKarKarin mu Kasa mu sami afuwa (Kasancewar tunda Asubahi ake = sammakon fitowa)." . : 


Yagana ta fada a lokacin da take duban Zaliha. . 


Ta kuma ja hannunta, taki kaďabn ya sanar da su Vera Pizza Restaurant anan dai cikin kasuwar ta Haraj


Gidan abinci ne da yake da matuKar farin jini a idanun Bakaken Fata ga saukin farashi ga kuma_ galibi nau'in abinci ne da_yake kamanceceniya da nasu. 


Kusan koda yaushe kusan kowacce rana matukar sun tako Haraj anan suke cin abinci su kuma yi guzurin tafiya da shi. 


- Da farar riga, bakin mashaKin wuya (neck tail) da baKin wando, baKin takalmin sau ciki da baKar Safar Kafa ya Karaso hannunsa riKe da Katon tire mai launin zinariya shake da kwanonin masu tarin sheKi a ciki. 


Dukkansu suna da tarin tsafta, sai ‘dai kamar wannan din ya daresu, kawai dai yana wani ji-ji da kai ne kamar ya mance shi din boyiboyi ne mai wanke kwanonin da muka ci Abinci, 


, yaushe ne likkafar ta ci gaba har ya sami muKamin rarraba mana abinci? (Service). 


Yagana ta fada muryarta sake. Haka take ba ta iya munafurci ba, balle ma da wannan da suka sha bam-ban ta fannin harshe. 


Zaliha ta dubeta ta kuma dubeshi sai kawai ta gyada kai cikin ‘nuna rashin jin dadi. : Ita din ma ba wai gwani ne a idanunta ba, sai dai a Kalla tozarta dan adam ba shi da amfani. ’ Dalilin da ya sa bai zamo gwani a idanunta ba kuwa shi ne, wani lokaci da ya taba gaya ma ta magana wai suna zubar da mutuncin: jinsin su (baKaKe). 


Dama duka Affican su baki daya suna tsince-tsince a bola?": 


Ta tuna ta bashi amsa, "Da ta je ta dauko na wani fa? Ko kuwa ta yi aikin banza?" 


Kusan komai da suke buKata ya ajiye. musu ya kuma Kara koda akwai wani abu da suke da buKata? 


Ya fada ne cikin harshen Larabci kamar — yadda al'adar Mutam (Gidan Abinci) din yake 


_ karrama abokanan huldarsu. 


Yagana ta kashe ido tana murmushi lokaci - guda ta juye harshe.


"Kawai dai muna buKatar sakin fuskar Oga abokanan huldarmu, har lokacin tana kashe idanu. 


Ya yi tsai yana dan nazari yama gano 


’ babu abin da ya hada wannan da daya daga cikin nauye-nauyen da aka dora a wuyan Ma’aikatan .PIZZA VERA RESTAURANT. . Ke nan kaucewa wannan babu abin da zai shafi sana'ar da yake ci da sha a cikinta. 

Sai kawai ya yi gaba ba tare da ya Kara ko daga kai ya dubi Teburin su ba balle ma ya dubeta, hasali ma ya karkata ga _ hidimar abokanan cinikinsu da suke ta kai da kamo. 


* * *  A cikin Hindawiyya gidansu yake, gini ne mai hawa shida ba dai na zamani ne har can ba, ginin sama yana daya daga cikin tsofaffin gine-ginen da ke cikin Jeddah. Sai dai sabo ne dal! Na zamani ne shar! Idan aka kwatantashi da gine-ginen da ke cikin Kasashenmu na Afirika musamman Kasarta 


Nigeria da suka fito daga cikinta. A hawa na uku, daki mai lamba hudu _ suke. ’ 


Gidane na hadaka kamar yadda rukunin dakunan suka zamanto na hadakar mafi Karanta mutane biyar a daki guda ba don sabi da komai ba, ba don kowa din baya so ya sake ba sai don 


tarin dan karen tsadar da haya take yi a Jeddah da ma Kasar ta Saudi take da shi. * * * 


Ta -bude bakin tatacciyar Madarar 


(Halib Sa'udi) ta soka tsinken tsotsa ta 


‘ fara tsotsa cikin dadin rai, domin kuwa 


yau kasuwar ta yi riba, ga hanya wasai yau babu matsala. . . 


“Ana idar da sallah asubahi zamu nutsa Haraj ina da labarin Heraq International Mall za su iso da sharar katafaren kantinsu. Babu ko‘ shakka samun da ke ciki ya wuce misali, ki kwanta da shiri, kada ma in tada ke ki miqe kina mini layin nan naki"


‘Zaliha ta dan tabe baki, gajiya kam ta gaji matuka gaya. ~° — 


"Kamar zafin nema baya kawo samu, ‘yan ' kudaden da muka samu a kwanakin nan basu ishemu rayuwa na wani lokaci mai tsayi ba? Ehem Yagana.:." ’ Ta Katseta. 


"Yan kawowa wani sa‘in, ehem zafin nama ba, irin dai yau din nan ai lallai Kwazo da KoKarin mu ne ya kaimu ga samun abin da aka samu, da mun zauna nan kwance da bamu kai ga samu ba". 


Zaliha taja ta tsaya daga tsotsar Madarar tana dubanta. 


"Wai in tambayeki ma Zaliha? Uhum in _ tambaye ki?" ‘Ta Kara zakudowa. ° . 


. "Ke din ba ki da wani tanadi ne? Ba ki da -wani tanadi da ki ke fatan tsinanawa kanki abun kirki balle ki hango dangi na gaba da suke cikin — tsananin bukata


. Me ye ne a Kasashenmu face fatara da yunwa da ya yiwa mutanen mu katutu". Haka ki ke so ki Kare shahadarki a banza ba tare da kin amfanawa kanki da komai ba balle na gida ya saka ran tsattsaga da zarar Kaddarar komawar gida ta afko mana (Kame)”. Zaliha ta miKe ranta a bace. 
Post a Comment for "HAMADA BOOK 1 CHAPTER 1 BY ZAINAB KABIR BIROMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...