Connect with us

Hausa Novels

HALLITAR ALLAH CE COMPLETE BY UMMU INTEESAR

Published

on

Advertisements

 HALLITAR ALLAH CE COMPLETE BY UMMU INTEESAR

Www.bankinhausanovels.com.ng 

*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

*GODIYA* Ina ƙara miƙa godiya ta ga Allah madaukakin sarki wanda ya bani da ma da ikon sake zo maku da wannan ƙayataccen labarin, cikin hikimarsa da iyawarsa ya aramn damar dasa alkamina domin na yi nuni tare da ishara ga wani abun da ba dai-dai ba.

Tsira da aminci su ƙara tabbata ga Annabi Muhammadu (s.a.w) haka ga sahabbansa da iyalan gidansa.

*GARGAƊI* Wannan labarin gaba ɗayansa ƙirƙira ne, na kuma samar dashi ne don yin nuni tare da faɗakarwa akan wasu mutane masu irin halayyar da zata zo a labarin, idan hakan ya yi dai-dai da rayuwarka/rayuwarki, to hasashe ne kawai.
+
DEDICATED TO: ALL MEMBERS OF AREWA WRITERS ASSOCIATION
Ina fatan Allah ya ƙara haɗe kanmu, much love🥰🥰
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

*Page 1-2*

Da misalin karfe 7 na safiyar ranar talata wata daleliyar mota ce ke sharara gudu akan titi, yayin da wata motar ‘yan daba ke binsu a baya da alama hari suka kawo masu.

Tuƙi yake hankalinsa a tashe yayin da yake hangensu ta jikin madubin gefen motar, sai gudu yake shararawa kamar ba gobe, fatarsa shine ya isa makarantarsu yaron ya sauke shi lafiya, idan ya so ko miye shi ya faru akansa, amma ya na so ya kare rayuwar ɗan talikin yaron nan.

Gudun kawai yake yayin da hankalin ƙaramin yaron da ke zaune bayan motar [wanda ba zai wuce 11 – 12 years ba ] yay matukar tashi.
Abdul ya ja nakasasshiyar ƙafarsa tare da juyawa baya ya na hangensu ta cikin glass da idonsa wanda ya kasance kwaya ɗaya jal.
Ganin baƙar motar na cigaba da biyo su ya sanya ya juyo cike da firgici; ya buɗi bakinsa da ya kasance rabi, ya ce ‘’Dan Allah baba direba ka ƙara sauri, in sunka kama mu kashe mu za su yi.’’
Ya faɗa cikin muryarsa da bata fita dai-dai, saboda tawayar dake ga halittar bakinsa.
Idonsa kuwa sai tsiyayar da hawaye yake.
Nan fa hankalin baba direba ya kai ƙololuwa gun tashi.


A dai-dai lokacin ne kuma suka iso Abuja Road,titin da ya kasance tsit,saboda rashin hayaniyarsa.
Anan suka yi yunƙurin shiga gabansa da motarsu, har ma motarsu tana zozar tasa.

Cikin zafin nama Baba Direba ya ture motarsu tare da shammatarsu ya zubawa motarsa speed, kafin su ankara ya kai ƙarshen titin.
Ganin hakan yasa suka karo gudu, ba  su kuma haɗuwa ba sai a round ɗin da zai sadaka da (Government house) gidan gwamnati na jihar Sokoto.

Saboda haka sai suka daina  gudun, suna dai bin shi baya a hankali, kasancewar gun babbar hanya ce suna gudun jama’a su ankara da nufinsu.

Shi kuwa Baba Direba ya na ganin ya samu dama, sai ya miƙe hanya samɓal ta kan babban titi, su kuwa sai suka kewaya ta ɗaya hanyar, da zimmar su haɗu da shi ta hanyar da bata da hayaniya sosai don su samu damar sace yaron cikin sauƙi.

Da wannan damar Baba Direba ya yi amfani ya ci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali har ya isa *Abdulrashid Adisa Raji special school sokoto* ya sauke yaron.

STORY CONTINUES BELOW
¥¥¥¥¥¥¥¥
‘yan daban kuwa, da suka tabbatar sun rasa shi, sai suka nemi guri suka faka motarsu.

Ogansu ne ya fito ya na neman wani layi a wayarsa, ringing biyu ana uku aka ɗaga kiran.

A can bangaren Kulu mai adashen sharri ce ta ɗaga wayar ta na masa kirari da cewa “An gaida Gumush, sannu sikelatu mai magana ƙahwahu masu tahiya da kansu, ka ga hitilar sheri, koy-yada ka ya yadama kai nai hitina, ga ka ranke-ranke amma sherinka ya hika yawa, yaya aiki ya yi kyau dai koh.” Ta ƙarashe zancen da tambaya.

Shi kuwa Gumush tunda ta fara masa kirari, yake hura hanci, sai da ta dasa aya, sannan ya ce “Hajjiya an samu matsala, wallahi Direban nan shegen gudu ga rai, amma kat ki damu na rantse da takobina *Zarta* nan gaba bai isa ya hana mu ɗaukar yaron nan ba.”
Wani uban tsaki mai adashen sharri ta ja, sannan ta ce “Amma wallahi ka ba ni kunya Gumush, ganin ƙwarewarka da can-cantarka yassa nit baka wanga aiki, amma shina kaka hwaɗamin wai an samu matsala?”

Cikin rangaji irin na ‘yan maye ya ce “Ya isheki hwa to, ni dai yanzu ki hwaɗamin inda zan cimmiki in kai miki motakki, ki bamu ‘yan canjinmu mu ware.”

Wata uwar ashar ta lailayo ta ce “Kutuma! Kama raina ma kanka hankali wallahi, har ma wasu kuɗɗi kaka magana bayan ka ɓata muna plan?”

“Haba dai Hajjiya! Ke san dai dole ki bada na chaji, saboda wagga wahala da mun ka sha ni da yarana bai yiwuwa ta tashi ga banza.”
Ya faɗa cikin Muryar ‘yan ƙwaya da alama ya yi mankas ne, duk suma sauran yaransa a make suke.

Akan haushi bata samu damar sake cewa komai ba, kwatance kawai ta musu ta kashe wayarta ta na tunanin yanzu me zata gayawa Hajiya?

Cikin motar suka koma ɗaya daga cikin yaran ya ja motar suka nufi gun da ta kwatanta masu.

Ƙarfe ɗaya da rabi na rana aka tashi yara daga makaranta dama can Baba direba tun ƙarfe ɗaya ya nufi makarantar, don haka koda yara suka turo Abdul akan keken guragunsa sun tarar da Baba Direba a gate ya na jira, buɗe motar yayi ya sunkuci yaron ya saka shi a ciki, sannan ya juya ya ɗauke keken ya saka a Boot ɗin motar, ya kewaya ya shiga ya ja sai Sama-road unguwarsu Abdul ɗin kenan.

%%¥¥¥¥¥¥

Wata mata ce wacce ba za ta haura shekaru talatin da bakwai zuwa da takwas ba, zaune take akan kujerar falo ta miƙe ƙafarta akan table dake gabanta, sai kallon makekiyar screen tvn dake manne a bangon ɗakin take, gefe ɗaya kuma ga juice a gabanta tana kurɓa, hankalinta kwance, kallo ɗaya zaka mata ka fahimci tana cikin nishaɗi, don kuwa murmushi ne kwance akan fuskarta.

Turo ƙofar falon da aka yi ne ya dawo da ita daga duniyar nishaɗin da ta afka.

Zumɓur ta miƙe ganin Baba Direba ne ya turowa Abdul kekensa suka shigo falon, nan da nan fuskarta ta bayyanar da mamaki ƙarara ga kuma tsabar ɓacin rai kwance akan fuskarta, me hakan ke nufi? Ya ta ga Abdul anan ita dake zaman jiran gawarsa?

Baba direba ne ya tsinke mata tunani da cewa “Hajiya Barka da rana, ya gida?”

A hargitse ta juyo cikin murmushin yaƙe ta ce “Alhamdulillah! hak-kun dawo?”

“Eh, Hajiya.” Ya bata amsa.

Murmushin yaƙe ta yi a karo na biyu ta ce “Sannunku da zuwa kun sha hanya, in ce dai babu wani abu da yas-same ku a hanyar tafiyarku da dawowarku?”
Ta ƙarashe zancen a lokacin da ta isa gaban Abdul ta tura kekensa zuwa tsakiyar falon.

Baba Direba ya ce “Babu komi Hajjiya, ƙila wani mummunan abu ya tashi hwaruwa, amma da yake Allah ya na kare salihan bayinsa waɗanda basu da haƙƙi a kansu, sai gashi mun dawo lahiya.”

A firgice ta juyo ta kalle shi domin a zatonta ko ya gano shirinta ne, kun san an ce mara gaskiya ko cikin ruwa ya yi jiɓi.

Murmushi kawai Baba direba ya yi ya juya ya koma bakin aikinsa, zuciyarsa na masa saƙe-saƙe akan uwar ɗakinsa Hajiya Haseena.

Ita kuwa tura keken da yaron ke kai ta yi zuwa ɗakinsa, ta na buɗe ƙofa ta wawwaiga ta ga ba kowa, kawai sai ta ta tura keken da ƙarfi, ta juya abinta cike da jin zafi da raɗaɗin abinda ƙawarta Kulu ta mata.

Keken kuwa sai da ta haɗu da jikin gadonsa sannan ta tsaya sakamakon to kare tan da gadon ya yi, bawan Allah Abdul kuwa tuni ya faɗo ƙasa ji kake tim! Kansa ya ƙumu a ƙasa.

Ba ya da wani ƙarfi ko kuzarin da zai iya miƙewa da kansa, kasancewarsa gurgu wanda ƙafarsa take a lanƙwashe, gashi tun asali shi ba lafiyayye ba ne, hakan ta saka ya kasa tashi daga gun, ya na nan kwance sai kuka yake shi kaɗai, gashi kuma Mamma ta rufe ƙofar ɗakin bare wani ya hango shi ya zo ya taimake shi.

Ko da yake ba mai shigowa cikin falon nasu kai tsaye sai Abbunsa kuma yanzu ya tabbatar ya na kasuwa, saboda haka ya ci gaba da kukansa tare da yunƙurin taimakon kansa da kansa.

¥¥¥¥¥¥¥
Hajiya Haseena kuwa ta na shiga ɗakinta kai tsaye gun da wayarta take ta nufa, cikin fushi ta kira layin ƙawarta Kulu mai adashen sharri, sai dai har kiran ya tsinke bata ɗaga ba, kira biyar ta jera mata amma ba’a ɗaga ko ɗaya bs, a zuciye ta ajiye wayar ta koma kan gadonta ta kwanta ta na famar jijjiga ƙafa tare da ƙissima irin rashin mutuncin da za ta yiwa ƙawar tata, a ranta ta ce “Lallai Kulu ke raina ni, ni zaki yiwa haka?”

A bangaren mai adashen sharri kuwa, ba komai ne ya hana ta ɗaga wayar ba, sai tsoro da fargaba da suka gama mamaye ta, tasan yanda Hajiya ta ɗau zafi a maganar nan, ga shi ta yiwa hajiyar alƙawarin yau za’a gama da wannan matsalar, amma sai ga shi wancan banzan ya rosa masu plan, tun bayan da ya kawo mata motar ya juya take son ta kira Hajiya Haseena a waya amma ta kasa, sai ga shi yanzu ta kira, tabbas kuwa yaron ya koma gida shiyasa take nemanta, ta na ɗaga wayar kuwa tasan kan zancen shiyasa ta ƙi ɗagawa a nufinta bari zata yi sai hajiyar ta huce sannan ta kira ta ta lallashe ta…..
Tofah! Readers ku dagajin wannan labarin kunsan akwai sarƙaƙiya acikinsa.

Shin ya matsayin Hajiya Haseena ya ke agun Abdul?

Ina mahaifinsa?

Wace rayuwa yake fuskanta a cikin gidansu?

Shin wace iriyar halitta ce wannan ga Abdul?

Don cin cigaban wannan labarin ku biyo alƙalamin Ruky don jin ya za’a ƙare.

Adadin Comment naku shi zai bani damar ci gaba ko akasin haka.

Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal

Vote share Comment

RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹

*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Page 2-3

Hakan aka yi sai da yamma liƙis, sannan Kulu ta kira hajiya ta rarrashe ta sosai tare da bata haƙuri, ta kuma yi mata alkawarin za ta sake sabon shiri, kuma Insha’allah a shirinta na gaba sai sun yi nasarar sace Abdul, su nisanta shi daga gidan babansa har abada.

Ba laifi ta yi nasarar shawo kan hajiyar, amma sai hajiyar ta ce mata ‘’na ji batunki kulu, amma kin sanni sarai ban son wasa ga lamarina, ba gidan ubanai ɗai ba, so ni kai a nisanta shi da duniya gaba ɗai, na tsani ganin yaron nan tsoron huskatai ma ni kai, baƙin nakasasshe, ya shiga tsakanina da burina da yasshigo da ni gidan Alhaji, don haka dole a kau da shi.’’
Tana dire zancenta Kulu ta ja dogon numfashi ta ce ‘’Hajjiya in har za ki ɗoki shawarata kak-ki sa a kashe Abdul, don ko in har an ka gaya mutu haka kwatsam, dole Alhaji ko danginai su zarge ki, amma ke ga in har ɓacewa ya yi basu san duniyar da ya shiga ba, dole zuwa wani lokaci su hanƙura  da shi, kuma kahin Alhaji ya mutu sai kisa a biɗo miki Abdul a kashe shi, daccan, sai a kawo gawatai a ce wani gari aka tsinto gawar.’’

Ta na dasa aya hajiya Haseena ta ƙyalƙyace da dariyar mugunta ta ce ‘’Kai amma shiyassa ni ka sonki abokkiyata ke san kan tsiya da sheri, shiyasa sunan mai adashen sheri ya dace dake.’’
Dukansu dariya suka saka a tare, a ran kulu ta ce ‘’Har akwai wata muguwa, ‘yar sheri bayanki haseena?, ke da kike neman ran karamin yaro bawan Allah nakasasshe ma baki bari ba,ina gani in na sabawa umurninki?.

Sai da Haseena ta yi dariya mai isar ta, har ta buɗi baki za ta kuma cewa wani abu, ta jiyo sallamar Alhaji ya na shigowa ɗakin, da sauri ta katse kiran ba tare da ta tsaya yiwa Kulu sallama ba.

Da fara’arta ta nufi Alhajin tana Faɗar ‘’Sannu da dawowa alhajina.’’
Yawwa sannu da gida hajjiya, ya yaron na ki fatan yana lafiya?.

Ai ji ta yi kamar ya caka mata wuka a ƙahon zuci, can cikin ranta ta ce’’ Yaronka dai, amma ni wannan nakasasshen ba ɗana ba ne, Allah ma ya sawwake na haifi nakasasshe.’’ Amma a fili sai ta ce ‘’Yana nan lahiya, tun ɗazu ma ya dawo makaranta.’’
‘’Madallah.” Alhajin ya faɗa ya na nufar hanyar ɗakin Abdul ɗin.
Saurin shan gabansa ta yi tana fadar ‘’Alhaji ina ka yi ko hutawa baka yi ba?.’’+

Da murmushi a fuskarsa ya bata amsa da cewa ‘’Zuwa zan yi inga amanata, ke san shi ɗai gare ni duniya yanzu, kuma kafin mutuwar mahaihiyartai sai da ta bammin amana tai,shine kuma wasiyyarta ta ƙarshe da tabammin, ta roke ni na zaɓa mai uwa ta gari bayan ranta, shiyassa nid-daɗe banyi aure ba, sai da nissame ki, na tabbatat kina da amana kuma za ki iya.’’

Murmushin yaƙe ta yi ta ce ‘’Hakane alhajins ai ɗa na kowana,don ba’a san mai cin unhwaninai ba, yanzu dai zauna ka huta bari na kira maka ɗan Baban, dannan sai in kawo ma abinci.”

Ta yi haka ne don ta hana Alhajin sanin abinda take aikata ma ɗan nasa bayan idonsa, domin muddin ya je ɗakin nan yanzu, asirinta zai iya tonuwa.

STORY CONTINUES BELOW
Zama yayi kan kujera ya na murmushi, ya na jin dadin yadda Haseena ke kula masa da yaron da yafi so akan komai a rayuwarsa.

Ita kuwa wucewa ta yi,zuciyarta na soya, wannan na ɗaya daga cikin abinda yasa ta ƙara tsanar Abdul, saboda Alhaji ya fi muhimmanta shi akan komai na rayuwarsa, da alama sanda uwarsa na raye ta na da babban matsayi a zuciyar Alhajin shiyasa.

Ko da ta shiga ɗakin Abdul na zaune kan kekensa har ya yi barcin wuya, don tun lokacin da ta fita ɗakin bata kuma waiwayo shi ba sai yanzu, bare yasa ran za’a kawo masa abinci, da yake ya saba da horon yunwa, shiyasa da ya samu daƙyar ya miƙe ya hau kekensa, ya je ma’ajiyarsa, ya ɗauko biscuit da nutri-milk ya sha, shine har ya samu damar yin wannan barcin.

Hakika da hajiyar tasan da wannan ma’ajiyar ta Abdul, da tuni ta yashe shi, amma da yake yaron mai wayo ne bai bari ta sani ba, tunda yasan bata son shi.

Fuskarsa ta kalla, cikin hanzari ta kawar da kanta ta na runtse ido da ƙarfi, hakika siffar wannan yaron ita ce siffar ɗan Adam mafi muni da ta taɓa gani a rayuwarta. Rabin fuskarsa a shafe take sumul bako alamar yankan ido ɗaya ko hanci da baki a gefen fuskar na hagu, a bangren dama ne kawai yake da ido ɗaya,rabin hanci, rabin baki.

Saurin kauda tunanin halittarsa ta yi daga ranta, domin ya na gaf da ɗarsa mata tausayinsa a ranta ga shi bata fatan haka, acewarta ɗan kishiya ba ɗa ba ne, ɗan kunama ne, ka sake ka goyasa to tabbas zai harbe ka a baya.

Rangwashi ta zuba masa a tsakiyar kai, firgigit ya farka daga barcin, har ya buɗi baki zai zunduma ihu, ta yi saurin rufe masa baki ta na Faɗar ‘’Karka muri inji shegiyar muryan nan taka, Babanka na falo karka yarda ya gano baka ci abinci ba ko na maka wani abu, in ba haka ba wallahi sai na kusan yanke ka, cikin gidan ga in yat hita.’’

Ta na gama faɗa ta tura keken Abdul zuwa falon ta na murmushi.

Ko da suka fito Alhaji ya na zaune ya na jiransu dama.

Kallon Abdul ta yi yayin da suka kusa ƙarasowa gun babansa, ta ce ‘’Abdul ɗana ga Babanka ya dawo, ko ka na yammin abinda ya kawo maka.’’ Ta ƙarashe zancen ta na masa murmushi.

Shi dai Abdul bai ce komai ba, tsoro ne fal aransa, domin ya na tsoron Mamma bada wasa ba, saboda shi kaɗai yasan irin uƙubar da ya ke sha hannunta, Abbunsa bai san cewa kura ce da fatar damisa ba, shiyasa kullum yake yabon ta.
Alhajin ne ya ce ‘’Iso gare ni ɗana.’’

Dai-dai lokacin ne kuma suka iso daf da Alhajin, ya jan yo shi a jikinsa ya rungume shi.

Har ya buɗi baki zai yiwa ɗansa Magana, suka jiyo sallama a ƙofar falon.

‘’shigo shine kaɗai abinda Alhajin ya ce, kasancewar ya riga ya ɗau muryar mai sallamar.

Yayansa sunusi ne ya shigo falon tare da neman guri kan ɗaya daga cikin kujerun falon, ya zauna.

Gaisawa suka yi da hajiyar, sannan ta juya ciki don kawo musa abinci.

Sosai suka gaisa da ƙanin nasa, sannan ya kalli Abdul ya ce ‘’Ɗana taho nan, taho ka gani ga alewa na kawo ma.’’

Ya faɗa ya na ciro wata bakar leda daga aljihun rigarsa.

Ba musu yaron ya zo cikin hanzari ya karɓi ledar daga hannun Alhaji Sunusi, sai dai bai sha ba, ya riƙe ta dai a hannunsa ya na dariyar murna.

‘’Ka sha alewarka ɗana.’’ Alhaji Sunusin ya faɗa.

Yaron ya ce ‘’Sha zan yi ai Baba.’’

Har ya buɗe ledar ya dauko alawar zai buɗe ya sha kenan, ya jiyo muryar Abbunsa na Faɗar ‘’Ɗan Baba ajiye alewar nan sai mun ci abinci sannan ka sha ka ji.’

Ba musu ya mayar da alawar cikin ledar da ta fito.

Shi kuwa alhaji sanusi tun lokacin da Abdul ya ciro alawar daga leda yake zuba murmushin mugunta, jira kawai yake ya ga yaron ya sha alawar har ya hango kabarin Abdul ɗin, kwatsam sai gashi Alhaji ya hana masa sha, ba ƙaramin haushin ƙanen nasa ya ji a ransa ba.

Kallon ƙanin nasa ya yi ya ce “Da ma maganat kasuwancinmu ta tak-kawo ni, muna so za’a yi sabuwar oda, ya ya za’a yi kenan? don kuɗin hannunmu ya yi ƙaranci.”

Murmushi Alhaji Munir ya yi ya kalli yayansa ya ce “Karka damu yaya, an jima  zan shigo gida sai mu haɗu can mu yi manat.”

To kawai ya ce, ya miƙewa ya na Faɗar “Ni zan tahi, Abdul yaron kirki ka tabbatar ka sha alewarka bayan gama cin abincin ka ji.”
Daga haka ya juya, juyin duniyar nan Alhaji Munir ya yi yayansa ya tsaya ya ci abinci, amma ya ƙi, acewarsa ya na sauri ne.

Ficewa ya yi aransa ya na Faɗar “Ga abinda nake so nan ka hanani ci, sai wani abincin banza zaka ba ni?, ka ga shege mai ɗan banzan wayon tsiya duk lokacin da muka yi yunƙurin kashe ɗan neman yaronga sai ka ga kamar ana hwaɗa mai.”

Daga haka ya bar gidan gaba ɗaya, sai da ya yi nisa da gidan ya fita layin gaba ɗaya sannan ya faka motarsa gefe, tare da janyo wayarsa ya kira yayansa Sani ya shaida masa abinda ya faru.

Buɗar bakin Sani sai cewa ya yi “…….

RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹

*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

Page 5-6
Buɗar bakin Sani sai cewa ya yi ‘’Ka ga shegen  mutum koh?, to ko ya ƙi ko ya so sai mun ga bayansa shi da wannan mummunan ɗan nasa.’’
Huci ya yi, sannan ya rufe zancensa da cewa ‘’Mu haɗu gida anjima da dare, sai mu tattauna maganar tare dasu yaya Bily don ko bata taɓa saɓuwa bindiga a ruwa.’’ Ya na gama faɗa ya kashe wayarsa a hasale, da alama shi yafi sunusi saurin zuciya da ɗaukar abinda ya faru da zafi.

Alhaji sunusi na ganin ɗan uwansa ya sauka a layi, kawai sai ya juya cike da baƙin ciki ya hau motarsa ya wuce, amma ya ɗau alwashin sai ya ga bayan ɗan uwansa Munir da ɗansa kwaya daya jal a duniya, domin kuwa su suka fi dacewa da cin gadon wannan dukiyar ba wannan nakasasshen ba.

A can gidan Alhaji Munir kuwa, bayan sun gama cin abinci shi da ɗansa, sai  ya tashi ya shiga ɗakinsa don hutawa, bayan ya kai Abdul ɗakinsa ya ba shi tsarabar da ya zo masa da ita.

Bayan fitarsa ne Abdul ya fiddo alawarsa da wan mahaifinsa ya kawo masa da zimmar zai sha, kawai sai ya ji kamar an fisge alawar daga hannunsa an yi jifa da ita ƙasa.
Akan dole ya haƙura, domin  ka’idarsa ne da abu ya faɗi ƙasa haƙura yake da sha ko cinsa, ba don komai ba, sai don baya iya durƙusawa ya ɗauko shi.

Faruwar hakan ke da wuya Abdul ya gyaɗa kansa alamar rashin damuwa, ya buɗe ledar da Abbunsa ya kawo masa ya ciro ice-cream ɗinsa ya na sha.

Da dare Alhaji Munir ya shirya ya hau motarsa ya nufi unguwar miyatti Allah, da yake a can gidan iyayensa yake.

Ko da ya je gidan ya tarad da sauran yayyensa su biyar a gidan, kasancewar kusan wannan lokacin shine lokacin zuwan kowannensu gida domin su gaida mahaifiyarsu.

Bayan sun gaisa da hajiya Inna ne, ya fito tsakar gidan ya samu yayyensa suka ƙara gaisawa cikin mutunta juna da nuna ƙaunar junansu.

A nan ya kalli Alhaji Sunusi ya ce ‘’Yawwa yaya Sunusi, ɗazu ka je da magana na ce ka bari sai mun haɗu gida koh?.”
Ya fada da sakin fuska.

Sunusi ya kalle shi fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce ‘’Hakane, mu je waje mu yi maganar.’’
Alhaji Munir ya shiga gaba, Alhaji Sunusi na binsa a baya, ya na masa wani kallo mai cike da tsana, a ransa ya ce ‘’Na tsane ka Munir, me yasa duk wani buri nawa da duk abinda nake so kai Allah ya tattara ya bawa?, dole sai mun ga bayanka, bari dai mu gama da wannan ƙaramin ƙwaron.’’
Haka ya ci gaba da sake-sake da zancen zucinsa, har suka isa wajen suka nemi guri suka zauna don tattauna maganar.

Bayan ya gama shiryawa Alhaji Munir zance, suka ajiye Magana akan gobe ya je ya same sa a inda yake siyar da motoci, don karɓar wasu daga cikin kuɗaɗen.
Daga nan suka miƙe, Sunusi ya je ya tarar da sauran yayyensa kuma abokanan makircinsa suka ci gaba da ƙulle-ƙullensu na yanda za su yi nasarar hallaka ƙanin nasu tare da ɗansa domin su mallaki dukiyarsa, yayinda Alhaji Munir ya je ya tarar da yaya Mizbahu suka ci gaba da hirar zumuncinsu, da yake shi Mizbahun kwata-kwata ba halinsu ɗaya da sauran ‘yan uwansa ba, shi kam ya’na son ƙaninsa Munir da zuciya ɗaya, sabanin yayyensa da suke zaune da Munir ɗin da biyu.

Da misalin ƙarfe tara da rabi na dare suka watse, ko wannensu ya nufi gidansa, amma shi Alhaji Sunusi ya tafi da tunanin ko Abdul ya sha alawar? Shin ya mutu ko yana raye?

A haka ya ƙarasa gidansa cike da jiran tsammanin ganin wayar ɗan uwansa domin ya shaida masa labarin mutuwar ɗan nasa.

¥¥¥¥¥¥¥¥

Bayan kwana biyu, Hajiya Haseena ce zaune a falo ta na ta famar tunani, to me Kulu ke nufi, kar dai ta manta da zancensu?, ta ji shiru har yanzu, hakurinta ya kusa ƙarewa, ita fa ta tsani wannan yaron kamar yanda ta tsani mutuwarta, shi yasa take jin daɗin rashin haihuwarta a gidan nan har yanzu, domin bata so ta haifi ɗan da zai kalli wannan nakasasshen ya ce masa yaya, ta fi son sai ta ɓatar da shi sa’annan ta zuba tata zuri’ar, yanda za su mori dukiyar da kyau.

Ganin wannan ba zai fitar da ita ba, ya saka ta ɗaga waya ta kira Kulu mai adashen sharri.

Bayan sun gaisa ta ke cewa ‘’Wai Abbukiyata mi kika nuhi halam?, kwana biyu na ji shiru bayan kesan na riga na biya kuɗɗin wanga aikin, to in baki iyawa na, ki dawo min da kudɗaɗena, in biɗi wanda ka iyawa.’’

Ta na gama faɗa ta kashe wayarta, ba tare da ta jira cewar Kulun ba.

Har za ta shige ɗakinta ta jiyo sallama a ƙofar falon, juyowa ta yi ta na faɗar “Wa’alaikumus salam, shigo.”

Yayarta Safiya ce ta shigo da sauri ta ƙarasa gun ta, ta na faɗar “Oyoyo oyoyo!! Sannu da zuwa yaya.”

Jan ta ta yi suka shige cikin ɗakinta domin su tattauna a sirrance.

Ba su jima da shigewa ba, Baba direba ya shigo da Abdul falon ya na sallama, dawowarsu kenan daga makaranta, jin shirun ya yi yawa yasa ya dubi yaron ya ce “Abdul yaron kirki mamakka bata kusa ƙoƙarta ka ida shiga ciki.”

Da to yaron ya amsa, sannan ya yunƙura ya tattara dukkan ƙarfinsa ya isa gaban 2sitter dake falon, ganin ba kowa gashi tun a makaranta cikinsa ke murɗa masa, kawai sai ya yi dabara ya haye kujerar ya kwanta ya na sauraren cikinsa dake masa ciwo sosai, sai hawaye ke fita a idonsa.

Lafewa ya yi luf, ya na tunanin da ya saba, domin tun ba yanzu ba tunani ya auri ƙwaƙwalwarsa, Ga shi dai yaro ne mai ƙarancin shekaru, amma matsalar da yake fuskanta koda yaushe ta haddasa masa yawan tunane-tunane.

A ransa yake tunanin Mammansa bata sonsa ko kaɗan, domin bata kula da shi, ko don ya na gurgu ko makaho ne take masa haka?, Ko da yake ba ita kaɗai ce ba ta sonsa ba, ya lura har makaranta yara tsokanarsa suke, wasu ma tsaronsa suke, ba mai son zuwa kusa da shi idan ba nakasasshi ‘yan uwansa ba, sauran duk ƙyamarsa suke, Abbunsa ne kaɗai ke sonsa, shi kaɗai ne yake rungumarsa har ma ya lallashe shi idan ya na kuka.

Tuna wannan da ya yi ya saka ya ce a ransa “In Abbuna ya dawo zance ya cire ni daga makarantar ban son karatun na gaji.”

Haka ya cigaba da rirriƙe ciki ya na kuka har bayan shuɗewar wasu mintuna masu yawa, sai ga Hajiya Haseena ta fito yayarta Safiya na biye da ita a baya sai dariya suke ƙyalƙyalawa da gani kasan ta mugunta ce, wannan na nuna kenan wata munakisar suka ƙulla a cikin ɗakin.

Dai-dai lokacin da suka zo tsakiyar falon, idon Safiya ya sauka akan Abdul da sauri ta runtse idonta ta na faɗar “Innahu min sulaimanu wa Innahu bismillahir-rahmanir rahiim, ku ka ganinmu ba mu mu ka ganinku ba.”

Shi dai Abdul bai ce uffan ba, sai ƙuri da ya yi mata da idonsa ɗaya.

Hajiya Haseena ce ta ƙaraso gabansa ta saka hannu ta murɗe masa kunne ɗaya ta na faɗar “To baƙin maye, kallon ya isa haka, kurwar yayata kur, ka ci kanka ka sha baƙin ruwa.”

Ta na gama faɗa ta sake masa kunne suka nufi hanyar fita falon Safiyar na faɗar “Tab! Lallai Haseena kina ƙoƙari, haka kika zama da wanga yaro? Ke bai ma baki tsoro da dare?”

Dariya Haseena ta ƙyalƙyale da ita ta ce “Yayata ke cika tsoro, ni ai ban ma yadda mu haɗu da shi da dare sai bisa dole, ke san ko in Babanai na nan har ga jikina nake ja nai ina mai wasa?”

“Uhmm! Lallai iyawa kikai, ni dai sai an jima bari In tahi, kafin nakasasshen ɗan ga naku ya samin hawan jini.”

Ta na gama faɗa ta yi gaba abinta.

Shi kuwa bawan Allah Abdul ya na nan inda suka bar shi, sai matsar ƙwalla yake, zafin ya haɗe masa biyu, ga ciwon ciki ga wannan zaluncin da matar babansa ta masa…….

Follow me on Wattpad @ ummu inteesar

RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹

*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

PAGE 7-8
Ko da ta dawo ma wucewa ta yi abinta, ko kallon inda yaron yake bata yi ba, bare ta ji dalilin kukansa.

Sai can wuraren ƙarfe huɗu da rabi na yamma sannan ta fito jiki na rawa, ta turawa Abdul kekensa zuwa ciki ta kira Lami ‘yar aikinsu ta ce “Lami ki yima yaronga wanka, ke ga Babanai ya kusa dawowa.”+

Ta na gama faɗa ta juyowa ta koma inda ta fito.

Lami ce ta masa wankansa tsaf a bathroom ɗin dake ɗakinsa, bayan ta kammala ta shirya shi cikin ƙananun kaya.

Ganin yanayin yaron ya sauya daga yanda ta saba ganinsa, ya sa ta dube shi ta ce “Abdul mika damunka?”

“Yunwa nika ji anty, kuma cikina ka ciwo.” Ya bata amsa.

Cikin alamun tausayawa da mamaki ta juya ta nufi kitchen don nemo masa abinci, mamaki take ya aka yi Hajiya ta bar yaronta da yunwa haka? Kuma baya da lafiya amma da alama bata ma sani ba.

A haka har ta ƙarasa kitchen, ta samu su Ladi masu aiki a kitchen sun gama girki ta ce Su zubowa yaro Abdul zai ci.

Jiki na ɓari Ladi ta ɗauki lafiyayyen filet  ɗan madai-daici ta shaƙe masa shi da cous-cous da miya haɗe da naman rago akai, ta miƙawa Lami.

Ƙarba ta yi ta juyo ta nufi ɗakin Abdul, an yi Sa’a Hajiya bata falo don haka ba a samu wata matsala ba.

Sauke shi ta yi ƙasa kan carfet, sannan ta miƙa masa kwanon, sai ta ga har hannunsa na kyarma gun amsawa, hakan ya nuna tsananin buƙatarsa ga abincin, nan take ya fara ci hannu baka hannu ƙwarya.

Jinjina kai ta yi cikin tausayawa, ta juya zuwa boys quaters da yake can ne mazaunin ‘yan aikin gidan, ta ɗauko masa maganin ciwon ciki ta kawo masa.

Bayan ya gama cin abincin ta ba shi ya sha sannan ta kwantar da shi, nan da nan barci ɓarawo ya yi awon gaba da shi.

A haka Abdul ya ci gaba da rayuwa cikin tsana da tsangwamar matar uba da ƙiyayyar yayyen uba.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
Waye Alhaji Munir?

Sunansa na asali shine  Munir Abbas.
Mahaifinsa Alhaji Abbas tsohon ɗan kasuwa ne, yana da yara Goma sha uku.

Matansa biyu, Saratu da Sa’adatu, Saratu ce uwar gida tana da yara Goma, maza biyar mata biyar.

Bilya shine babba sai Sani, Sunusi, Bello sai Mizbahu.

Acikin ƴaƴanta mata kuwa uku sun mutu saura biyu Hajara da Halima suke nan suka rage mata.

Yayinda Sa’adatu take da ƴaƴa Uku, namiji ɗaya mata biyu, Munir shine babban ɗanta sai Hadiza da Fatima.

Alhaji Abbas ya aurar da duka ƴaƴansa mata, yayin da ya aurar da wasu daga cikin mazan, ya na zaune da iyalinsa a unguwar ƙofar kaɗe can cikin gari.

STORY CONTINUES BELOW
Yaransa sun taso cikin haɗin kai da ƙaunar junansu, da kuma kyakkyawar tarbiya da suka samu daga iyayensu.

Lokacin da Alhaji Abbas ya fuskanci tsufa ya taso masa, sai ya ɗauki ƴaƴansa maza ya saka su a harkar kasuwancinsa, manyan su ke kula masa da shagunansa, ƙananan kuwa ya rarraba su a shagunan abokansa suna masu jiran shago, daga cikin waɗanda ke shagunan abokansa akwai Munir, mai gidansa ya na sonsa sosai saboda gaskiya da riƙon amanarsa, bayan wani dogon lokaci Munir ya bunƙasa har ya tsayu da ƙafafunsa ya buɗe shaguna guda biyu inda yake siyar da yaduka da atamfofin mata, a dai-dai lokacin ne kuma ya samu aikin gwamnati, bayan kammala digirinsa.

Lokacin yana da shekaru ashirin da bakwai a rayuwarsa.

Ya samu aiki a asibitin amanawa na jihar Sokoto, inda yake bangaren gwaje-gwajen jini.

Ya ji daɗi sosai, duk da albashinsa a lokacin ba wani mai yawa ba ne, a haka ya daure, domin da babu gwara ba daɗi, wannan aikin da yake bai hana masa yin kasuwancinsa ba, da ya dawo daga gun aiki yake wucewa kasuwa.

A lokacin ne kuma ya haɗu da wata budurwa mai suna Zulaiha ta waya, sai dai Zulaiha ba mazauniyar jihar Sokoto ba ce ‘yar jihar Taraba ce, da farko bai san ko ita wacece ba, daga ta yi kuskuren number ta Kira shi, shikenan ya kamu da ƙaunarta, su na gaisawa a waya matsayin abokai lokaci zuwa lokaci, sai daga baya ya bayyanar mata da soyayyarsa, ba musu ta karɓa da yake ita ma tun ranar farko da suka fara waya ta ji ya kwanta mata a rai.

Shi a tunaninsa duk ‘yar gari ce sai da tafiya ta yi nisa, sannan ya tambaye ta wace unguwa take anan Sokoto ya na so zai zo su haɗu.

A lokacin ne take shaida masa ita ba ‘yar nan ba ce, ta na zaune a jalingo ne ta jihar Taraba.

Lokacin da ya ji wannan labarin sai jikinsa ya yi sanyi laƙwas, har ya fara sarewa da soyayyarta, sanin a yanzu ba zai iya tafiya har can ba, idan ma ya je ba lallai iyayensa su amince masa auren wacce ba ‘yar gari ba.

Amma saboda tsananin ƙaunarta da yake haka suka cigaba da soyayyarsu, tare da alƙawarin cewa watarana zai zo jihar Taraba su yi zancen aure.

Watarana Munir ya shirya ya je Taraba ya gano Zulaiharsa bayan kwana biyu ya dawo gida cike da murna.

Bayan shekara biyu iyayensa suka shirya zuwa Jalingo don nema masa auren Zulaiha, duk da sai da aka kai ruwa rana, kafin iyayensa su amince masa da batun auren.

Sun isa jalingo lafiya, sannan sun samu tarba iya tarba, da karammawa daga fulanin Jalingo, kasancewar garin da nisa dole sai da suka kwana biyu a ranar na uku suka juyo cike da murna, su na ji a ransu haƙiƙa ɗan su ya yi mata, ya samu natsattsiya mai tarbiyya, daga can aka sako ranar aure nan da shekara ɗaya.

Murna ce fal ran Munir da Zulaiha, ganin suna daf da cika burinsu na zama ma’aurata.

Bayan shekara ɗaya aka sha shagalin bikin auren Munir da Zulaiha.

‘Yan uwan Zulaiha suka yo tattaki har jihar Sokoto, don rako amaryarsu ɗakinta.

Bayan amarya ta tare a gidanta dake unguwar Nakasari bayan school of nursing, suka ci gaba da shimfiɗa ƙauna da soyayyarsu, zaman lafiya suke sosai ba hayaniya bare tashin hankali kasancewarsu masu haƙuri da juna.

Kwanci tashi asarar mai rai, su na nan a haka, har aka share shekaru biyar ko ɓatan wata Zulaiha bata taɓa yi ba, nan fa abin duniya ya dame ta, Munir ɗin ne ma mai lallashinta da lallaɓa ta, yana kwantar mata hankali da cewa ai haihuwa nufin Allah ce, wata rana za su samu.

Da ire-iren waɗannan maganganu yake samu ya na ciwo kanta a duk lokacin da ta tashi hankalinta akan wannan maganar.

A dai-dai lokacin ne kuma arziƙin Munir ya bunƙasa, domin yanzu ya na da babban shago a tsohuwar kasuwa inda yake bada sarin atamfofi, da wasu shaguna guda huɗu a sabuwar kasuwa ya zuba yara a ciki, inda suke sayar da kayan kitchen saura kuwa, suke siyar da yadukan maza.

Haka rayuwa ta cigaba da gudanar masu, suna cikin sukuni sosai, a shekara ta bakwai ne Munir ya canza gida daga Nakasari suka koma sama road commissioner quarters, domin zuwa lokacin Allah ya tarfawa garinsa nono, ya zama hamshaƙin ɗan kasuwa har ya fara siyar da motoci ga kuma aikinsa da yake, an ƙara masa matsayi a shekarar da ta gabata.

A lokacin ne kuma ‘yan uwansa suka ƙullace shi a ransu, suka fara yi mi shi hassada da baƙin ciki, domin duk ya fi su nasibi a harkar kasuwanci saboda riƙe, gaskiya su ko da suka saka zamba sai abin nasu ya lalace, har aka kore su daga shagunan, sai shine ya ɗora su akan dukiyarsa su na kular masa da ita.

Da yake ba masu amana ba ne, sai suke yin yanda suka ga dama da dukiyar, har ta kai wata rana suka haɗa kansu akan cewa kawai za su kashe ɗan uwan ne ta hanyar da ba wanda zai gane, domin su ci dukiyarsa tun kafin matarsa ta haihu.

Akan wannan tsarin suka ci gaba da tafiya, kullum su na cikin ƙulla masa gadar zare, da ya ƙetare wannan sai su shirya wata, yayin da shi kuma yake zaune da su da zuciya ɗaya.

Duk a cikin yayyensa Mizbahu ne kaɗai ba shi da burin cutar da ɗan uwansa, ganin haka ya saka su huɗu suka haɗe kansu tare da ware mizbahun daga cikinsu kullum ce masa suke “Kai dai wallahi ka yadda zucciyarka kare ya ɗauka, ɗan uba ai ba abin so na ba.”

Shi ko sai ya ba su amsa da cewa “Na ji dai, ni ina da imani, sannan ban taɓa yarda a haɗa kai da ni a zalunci ɗan uwana ba, ku dai da kuka ga kuna iyawa sai ku yi, amma ina mai maku nasiha da ku ji tsoron Allah.”

Cikin wannan lokacin ne kuma wataranar Alhamis Alhaji Abbas ya tashi da wata zazzafar rashin lafiya, akan haka ya saka aka tattaro masa kan ƴaƴansa ya masu nasiha tare da gargaɗi akan riƙe amanar junansu da haɗin kai ko bayan ransa.

Bayan ya sallame su kowa ya watse washe gari ya cika, sai saƙon mutuwarsa suka ji, Munir da Mizbahu da ƙannensu mata sun sha kukan wannan rashin da suka yi, yayin da su kuwa su yaya Bilya ko a kwalar rigarsu, a ransu ma cewa suke tafi nono fari, ai gwanda ya mutu tunda dama ba sonsu yake ba ya fi son Munir, shiyasa ya ɗauke shi ya kai shi inda zai yi arziƙi.

Bayan an yi bakwan mutuwar Alhaji Abbas, iyayensu mata suka tattaro su tare da ƙara jadadda masu wasiyar mahaifinsu da ya bari.

Amma su kam su Sani, inda suka ji maganar anan suka bar ta, ba ɗaya da ta shiga kunnensu, sai ma wutar hassadar da ta ruru a ransu, sai dai sun danne hakan a can ƙasan ransu.

Bayan kamar wata uku da mutuwar uban, suka takura akan a raba gado a bawa kowa nasa, ba don iyayensu mata sun so ba, haka aka kira malamai suka raba musu gadon saboda sun takura.

Da aka zo rabon gadon Munir ya kawo shawarar me zai hana a bar wannan gidan da iyayensu suke ciki don su ci gaba da zama, ko ba komai bai kamata don Babansu ya mutu a siyar da gidan ba, amma fafur su Sani su ka ƙi suka ce sai dai a siyar.

Ganin hakan ya saka Munir ya siyawa iyayensa gida a unguwar Miyatti Allah domin su koma can da zama, bayan siyar da wannan, haka kuwa aka yi.
Bayan rasuwar mahaifiyarsu da kamar shekara ɗaya Mamansa ta rasu ita ma, ya shiga damuwa da alhinin mutuwarta ba kaɗan ba, shikenan fa shi yanzu ba shi da kowa sai matarsa Zulaiha, ya yi kuka har ya gaji, da ya ga ba mafita dole ya ɗauki na annabawa wato haƙuri.

Bangaren matarsa kuwa har yanzu bata sake zani ba, domin har zuwa lokacin bata samu haihuwa ba, don haka suka duƙufa da addu’a ba dare ba rana, ya kuma rarrabawa malamai abin sadaka domin su taya su da addu’a har saukar Alqur’ani aka yi.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
Allah maji roƙon bawansa.

Bayan shekara ɗaya da mutuwar Mamansa ciki ya bayyana a jikin Zulaiha, farin cikinsu ya kasa ɓoyuwa.

Bayan wata tara Zulaiha ta haifi ɗanta namiji, ya kama shekara goma cif kenan kafin su samu haihuwar.

Wannan haihuwar ta zo masu da yanayi biyu, farin ciki da kuma damuwa, domin yaron ya zo duniya a cikin wata irin siffa mai ban al’ajabi da sanya imani da tsoron Allah a cikin zuciyar duk wanda ya gansa.

Yaron ya kasance baƙi ne a kalar fata, rabin fuskarsa a shafe yake sumul ba alamar yankan halitta a gun, komai nasa rabi ne, kunne ɗaya, ido ɗaya, rabin hanci da rabin baki.

Duk da wannan irin siffar da yaron ya zo da ita, hakan bai saka Alhaji Munir ko Hajiya Zulaiha sun ƙyamaci ɗan su ba suna matuƙar sonsa, kuma sun yi godiya da wannan kyautar da Allah ya masu……….

Follow me on wattpad @ummu inteesar

ÜMMÜ INTEESAR CE🌹🌹🌹🌹🌹

*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 9-10

A lokacin da ‘yan uwansa suka ji labarin haihuwar tuni sun yi nisa a shirin su na kashe shi da suke, domin a gobe ne ma suke so a kaddamar da shirin, sai ga labarin haihuwar ya zo masu.

Sun yi matuƙar baƙin ciki da haihuwar, amma ba yanda suka iya bisa ga dole suka dakatar da shirinsu, sanin cewa zasu yi ‘aikin banza yiwa kare wanka’ domin ko da ya mutu basu da gado saboda wannan ɗan da aka haifa masa shi zai gaje komai, kenan ya zama dole su yi sabon shiri domin ba’a fafe gora ranar tafiya.+

A ranar ba a kwana ba sai da yayyen Alhaji Munir suka shirya su dukansu da dare suka je ganin jinjirin da aka haifa masa.

Haƙiƙanin gaskiya ba sun tafi ne don taya shi murna ba, sai don su ga wanda ya ɓata masu shiri domin su san irin matakin da zasu ɗauka a kansa.

Bayan shigarsu gidan a babban falo suka yi masauki suka zauna, suka yi zuru-zuru sai rarraba ido suke, kallo ɗaya zaka masu ka gano cewa suna cikin tashin hankali, Mizbahu ne kaɗai ya ke cikin farin ciki.

Bayan Alhaji Munir ya zo sun gaisa ne, suka nemi da a fito masu da Jariri su gani, saboda har zuwa lokacin ba wanda Hajiya Zulaiha ta bari ya ga ɗan, domin tsoron gulmar mutane.

Shiga ɗakin Zulaiha ya yi ya tarad da ita rungume da ɗan nata tana sharar ƙwalla, abu biyu ne ya haɗe mata ga zafin ciwon da take fama da shi tun bayan haihuwar, ga kuma damuwar wannan halittar ta ɗan nata.

Ƙarasawa ya yi, ya zauna bakin gado ya na faɗar “Zulaiha me ka damunki?”

Share hawayenta ta yi tace “Bakomai Alhaji.”

Gyara zamansa ya yi ya dube ta cike da tausayawa da alhini, domin yasan yanda take ji, don kuwa shi ma yana jin irin wannan yanayin, amma ba yanda zasu yi, kyautar Allah ce, haka ya ga dama ya basu wannan kyautar cikin iyawarsa da hikimarsa, domin ya zame musu wa’azi su da sauran al’umma.

Daƙyar ya buɗi bakinsa yace “Ki yi haƙuri Zulaiha, ki jure mu samu mu cinye ƙaddararmu, ki tuna shekara goma muka share ba haihuwa, yau kuma Allah ya dube mu da idon rahama ya mana wannan babbar kyautar bai kamata mu butulce masa ba.”

Nisawa ya yi sannan ya ci gaba da cewa “Allah maɗaukakin sarki yace Inna khalaqnal insana min nuɗufatin amshajin nabtalihi, faja’alnahu sami’an basiraà.” Ma’ana

“Lallai mu muka halicci ɗan adam, daga ɗigon maniyyi garwayayye, muna jarabta shi, muka sanya shi mai ji, kuma mai gani.”

A cikin wata ayar kuwa cewa ya yi
“Inna hadainahus-sabila imma shakiran, wa imma kafuraà.”
Ma’ana

“Lallai mu muka shiryar da shi (Ɗan Adam) hanya guda biyu, ko dai ya zama mai godewa Allah, ko kuma ya zamo mai butulcewa Ubangiji.”

“Duba da wadannan ayoyin guda biyu, ya kamata mu ɗauki haƙuri mu rungumi kaddara domin kada mu kasance cikin masu butulcewa ni’imar Allah.”

STORY CONTINUES BELOW
Ya na gama faɗa ya saka hannu ya ɗauki yaron dake kwance a gabanta, cikin sanyi jiki ya nufi hanyar fita yana faɗar “Su yaya Bilya ne suka zo ganinsa.”

Bai jira amsarta ba ya fice abinsa.

Tafiya yake kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki har ya ƙaraso gabansu, ya miƙawa yaya Bilya yaron yana cewa “Ga yaron.”

Karɓarsa ya yi ba tare da ya lura ba, sai bayan ya saka yaron a cinyarsa ya kai dubansa a kan fuskar yaron, a razane ya kauda kai gefe yana faɗar “Subhanallah! Miye wannan Munir? Ina ka samo wannan dodon?”

Wannan zancen da ya yi ne ya karkato da hankalin sauran, suka kalli fuskar yaron da kyau, nan take suka razana jikinsu ya dinga kyarma, domin ko a mafarki ba su taɓa ganin mummunar halitta irin wannan ba.”

Cikin dakiya Mizbahu ya matso kusa ya saka hannu ya ɗauke yaron daga kan cinyar yaya Bilya yana faɗar “Kai masha’allah! Allah abun godiya, Allah mun gode maka da wannan kyautar da ka mana.”

Sauran suka tada kai suka kalli Alhaji Munir sai suka ga kamar bai ji daɗi ba, ganin hakan ya saka Sani ya yi saurin cewa “Masha’allah! Allah ya raya mana, mu zamu tafi.”

Kamar masu jira, yana rufe bakinsa duk suka miƙe suna faɗar “Allah ya raya.” suka yi gaba, Mizbahu ne kaɗai ya ɗan tsaya, har zuwa lokacin da Alhaji Munir ya harhaɗo kalmomi daƙyar ya ce “Yaya sun tafi fa, kada su barka a nan, mun gode sosai.”

Da gama faɗa ya karɓi ɗansa tare da juyawa ya shige ciki rai a jagule, domin wannan ƙyamar da ‘yan uwansa suka nunawa ɗansa bai ji daɗinta ba ko kaɗan, ko ba komai wannan yaron jininsu ne bai cancanci haka daga gare su ba.

Bayan kwana uku dangin Zulaiha suka zo daga Jalingo, su da suka zo taya murna sai abin ya rikiɗe zuwa taya juna alhini, sun matuƙar razana da ganin halittar wannan yaron.

‘Yan Barka kuwa duk wanda ya zo ba a bari ya ga yaron, sai ‘yan uwan Hajiya su kawo uzurin cewa ana yiwa yaron wanka ne, wani zubin su ce yana gun Babansa ne, domin sun lura da biyu mutane ke zuwa barkar ma’ana dai gulma ce kawai ke kawo su.

Ranar suna yaro ya ci sunan Abdulrazzaƙ(Bawan mai azurtawa) wanda mahaifinsa ya raɗa masa, ba don komai ya raɗa masa wannan sunan ba, sai don tuna shekarun da suka shafe kafin samunsa.

Je ka ga yanda gidan Alhaji Munir ya cika a ranar suna, ‘yan shan miya da magulmata duk sun zo, a cewarsu dole ai a fitar da yaron ran suna kowa ya gani, amma sai suka ga saɓanin haka, domin sun ta bulala ido amma ba su ga jinjirin ba, da alama a ranar ma ɓoye yaron a ka yi.

Wuni cur, aka yi ana shagalin ciye-ciye da shaye-shaye, duk da ba shagalin suna ne irin wanda aka saba gani ba.

®®®®®®®

Bayan watse taron suna dangin Zulaiha suka koma gida, dama sun ƙagu a yi sunan su tafi, saboda tsakani da Allah basa iya jure kallon wannan halittar kowa ƙyamar zuwa kusa da shi yake.

Zulaiha ta yi kuka mai yawa har hawayenta suka ƙafe, ganin yanda ‘yan uwan nata ke ta zumuɗi da murnar tafiya gida, ta gane nufinsu sarai, nan take ta tuno da Margayiyar mahaifiyarta da kuma mahaifinta, ta san da suna raye, ba za’a mata irin wannan cin kashin ba ko don albarkar idonsu.

Ga baki ɗayansu suka watse, ba wacce ta tsaya har zuwa lokacin da za’a fita jego.

Bayan komawarsu Jalingo da kamar kwana uku sai ciwon Hajiya Zulaiha ya motsa, ta dinga fisge-fisge kumfa na fita a bakinta, cikin kiɗima ‘yan aikinta suka kira Alhaji suka shaida masa.

Ko cikakken minti talatin ba a yi ba, sai gashi ya shigo a kiɗime hankali tashe ya kinkime ta zuwa asibitin koyarwa ta Usmanu danfodiyo dake jihar Sokoto.

Bayan yin gwaje-gwaje aka tabbatar masa ta kamu da cutar convortion ne, galibi masu ɗanyar haihuwa sukan haɗu da shi, mafi yawa daga cikin matan da lalura ta sama mutuwa suke, sai mai nisan kwana ce zata rayu, wasu ma haukacewa suke.

Gado aka bata a asibitin, sai da ta shafe kwanaki masu yawa tana jinya ƙarƙashin kulawar likitoci da ‘yan aikinta, sai shi kansa mijin nata.

Bayan doguwar jinya aka dawo da ita gida, ta cigaba da kula da ɗanta cikin nuna soyayya da kulawa, domin ta sa hannu biyu ta rungumi ƙaddararta.

A ranar da ta cika kwana arba’in da haihuwar Abdul, bayan fitar Alhaji Munir daga gida zuwa wurin aikinsa, tana kwance a ɗaki ita kaɗai sai yaronta da yake manne da ita ko-da-yaushe, kawai sai ciwon nata ya motsa ba tare da sanin kowa ba, ta dinga fisge-fisge gumfa na fita a bakinta, ta kwashi kusan awa a haka, kafin shigowar Ladi ɗakin, domin ta tambaye ta kalar abincin da za’a dafa.

Ganin yanayin da hajiyar ke ciki ya saka ta ratsa ihu, ta nufi boys quaters da sauri, ta lalubo wayarta har hannunta na kyarma, ta kira Alhaji ta sanar masa.

A gigice ya ƙara so ya sure ta sai Asibiti, ko tsayawa ɗaukar Abdul bai yi ba, sai Ladi ce ta yi ƙarfin halin ɗauke yaron zuwa sashen su domin ta kula da shi kafin dawowar iyayensa, domin kuwa tana matuƙar son Hajiya Zulaiha saboda yawan alkhairan da take mata.

Da isarsu asibitin, kai tsaye Emergency ya nufa da ita, cikin hanzari a ka karɓe ta zuwa ciki don bata agajin gaggawa, bayan likitoci sun yi iya ƙoƙarin su aka samu ta dawo hayyacinta, sai dai a matuƙar galabai ce ta ke, anan ta roƙi nurses ɗin dake kula da ita da su kira mata mijinta don su yi bankwana.

Bayan ya shiga ɗakin ya nufi gaban gadonta, cikin murya mai sarƙewa haɗe da kakari ta ke cewa “Alhaji ina so ka sani, ni tawa ta riga ta zo ƙarshe, mutuwa zan yi, ga yarona Abdul nan na baka amanar shi, nasan duk duniya ba wanda zai so shi kuma ya iya ba shi kulawa sama da kai,  na roƙe ka da ka kula da shi, sannan ka sama masa uwa ta gari mai jinƙai da imani wacce zata kalli tawayarsa ta tausaya masa, ko bayan raina ka da ka bari Abdul ya wulaƙanta wannan ita ce wasiyata, na so na rayu da yarona don bashi cikakkiyar kulawa amma ina! Kaddara ta riga fata, ina sonka Munir.”

Ta na gama faɗa numfashinta ya sarƙe shaiɗarta ta yi sama, cikin sarkaƙƙiyar murya da karyayyen harshe ta karanto kalmar shahada, sannan numfashinta ya yi fit ya fita.

A gigice Alhaji Munir ya miƙe ya je kusa da gawar matarsa, ya na jijjiga ta faɗar yake “Ki buɗe idonki Zulaihat ba zaki mutu yanzu ba, mun yi alƙawarin zamu rayu tare kuma mu mutu tare, ki tashi mu raini ɗanmu a tare, mu zame masa gata, mu ba shi kulawa irin ta kowanne ɗa mai gata domin shima ai *HALITTAR ALLAH CE*”

Ganin ko motsa wa bata yi ba, ya saka ya fice daga ɗakin a kiɗime domin kirawo likita……

Follow me on wattpad @ummu inteesar

*RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹*

*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 11-12

A tare suka koma ɗakin da likita, bayan likitan ya dudduba ya tabbatar da ta cika, kawai sai ya ja mayafin dake rufe da jikinta ya rufe mata fuska ya juya zai fita, a diririce Alhaji Munir ke kallonsa bakinsa sai rawa yake amma ya kasa furta ko kalma ɗaya.+

“Ka yi haƙuri Alhaji, Hajiya kuma an cimma sa’i.” Ya na gama faɗa ya fice cike da tausayawa ga Alhajin.

Alhaji Munir ya yi kuka mai yawa irin wanda bai taɓa yi ba ko a lokacin rasuwar mahaifansa, wannan mutuwa ta girgiza shi matuƙa, ga baki ɗaya ya fita daga hayyacinsa.

Bayan ya tabbatar da mutuwar abar ƙaunarsa, sai ya koma gida domin duba yaronsu da ya bari a ɗakin lokacin da ya fice da ita zuwa asibiti, ganin ba yaron ya kuma shiga táshin hankali, baki na rawa ya kira ma’aikatan cikin gidan yana tambayar su ina yaronsa da ya bari a ɗaki?

Ladi ce ta matso gaba ta na faɗin “Ranka ya dade ni nit ɗauke shi dan na ga babu kowa a sashen, ya jikin Hajiya?.”

Wannan tambayar da ta masa ce ta famo masa da ciwo da zogin dake ransa har bai san lokacin da hawaye suka kece masa ba a gaban ‘yan aikin nasa, cikin hanzari ya juya ya shiga ciki.

Hakan ya tsora ta su sosai, aransu suke cewa duk yanda aka yi jikin hajiyar ne ya yi tsanani, cikin mutuwar jiki Ladi ta juya ta je ta ɗauko masa yaronsa tare da yin sallama a ƙofar ɗakinsa.

Yana fitowa ta miƙa masa yaron ta juya.

Rungume yaron ya yi sosai yana kuka, haƙiƙa an masu mutuwa mai tsayawa a rai, yana matuƙar tausayawa yaronsa don haka ya ƙuduri anniyar tsayawa kai da fata akan al’amuran da suka shafi rayuwar yaronsa ma’ana ya ɗora ɗamarar rainon yaronsa da kansa, domin ya sani cewa a yanda ake ƙyamatar halittar nan tasa ba kowa ba ne zai iya kula da shi.

Sai bayan an yiwa gawar sutura an kawo ta gida ne ‘yan aikin suka fahimci dalilin kukan Alhaji, suma sun sha kuka kam, kuma ba su ga laifin Alhaji ba da ya ke kuka don kuwa ya yi babban rashi, ga kuma ɗan talikin yaron nan da ta bari.

A lokacin da labarin mutuwarta ya riski su yaya Bilya sun yi farin ciki sosai, yanzu mutum biyu ya rage masu su kauda don handame dukiyar Munir, matansu ne kaɗai suka yi baƙin cikin mutuwar, domin su ba su san komai da mazajen nasu ke ƙullawa ba.

A lokacin da labarin mutuwar Zulaiha ya riski mutanen Jalingo sun yi baƙin ciki sosai, musamman ƙanin mahaifinta da dangin mahaifiyarta, anan aka fara shirin tafiya Sokoto don yiwa mijinta da danginsa gaisuwa, sai dai me? Duka mata zame jikinsu suka yi, sai uzuri suke kawo wa, ba don komai ba sai don suna tsoron su je a haɗo su da wannan mummunar halittar, sun sani kuma ba su isa su ce ba za su  karɓa ba saboda jinin Zulaiha ne.

Maza ne kawai suka haɗu suka yo mota ɗaya suka zo, bayan sun yiwa Alhaji Munir gaisuwa suka juya tare da masa fatar Allah Ya ba shi ikon riƙe wannan yaron.

Bayan kamar kwana arba’in da mutuwar Hajiya Zulaiha, su yaya Bilya suka zo gidan don ganin ko lafiya domin a ranar ake saka ran ya koma bakin aikinsa, sai dai da alama ba shi da niyyar komawa aikin bare a yi zancen kasuwanci.

Anan yake gaya masu “Ni fa babu wani aiki da zan komawa, tuni na gama shirya takardar aje aikina turawa ɗai ya rage, ba ma aikina ba ɗai, na dakatar da hita kasuwancina da duk wata harƙalla da ni kai domin in kula da rayuwar yarona wanda ya kasance abin tausayi ga duk wani mai imani.”

Jikinsu ya yi sanyi da jin wannan zancen, Sunusi ya kada baki ya ce “Yanzu kenan haka zaka bari kasuwancinka ya rushe saboda wannan yaron ko ya ya? Ni dai ga nau gani kawai ka biɗammai Nanies masu kula da shi, sai ka ci gaba da harkokinka don in kaz-zauna haka kawai zaka canye abinda kat-tara ne ba tare da kowa ya mora ba.”

Murmushin yaƙe ya yi ya ce “Yaya ba zaku gane ba ne, ba kowa ne zai iya kular min da Abdul tsaka ni da Allah ba, don haka niz-zaɓi na yi aikinga da kaina, yanzu dai kuna iya tahiya zan biɗe ku daga baya akan maganar kasuwancina da ku ka kula da shi, kowa ya ci gaba da kula da ɓangarenai kahin insan abin yi.”

Daga haka ya miƙe ya yi ciki, ya bar su nan zaune suna nazari, wato Munir dai ya zame masu alaƙaƙai ƙadangaren bakin tulu.

Da suka ga zama ba ya yi, domin kuwa zugunne bata ƙare ba wai an sai da akuya an sayi kura, sai suka miƙe tare da ficewa daga gidan baki ɗaya.

Tun daga ranar Alhaji Munir ya dakatar da duk wasu harkokinsa ya zauna a gida domin bawa Abdul kyakkyawar kulawa.

A lokacin ne kuma ya tara ‘yan uwansa ya kuma ɗora su a kan kasuwancinsa domin su cike guraben da ya bari, cikin Sa’a ya bawa Mizbahu kula da gun siyar da motocinsa, su kuwa sauran ya bar su a kasuwa.

Alhaji Munir bai san cewa ya bawa kura fiɗa ba ne.

Hakan ya baƙanta masu rai ba kaɗan ba, duk da cewa Mizbahu jininsu ne uwa ɗaya uba ɗaya, amma ba haka suka so ba, sun so ace ɗaya daga cikinsu ne ke kula da wurin ta yadda zasu yi barnarsu da kyau, amma a yanzu suna da tabbacin Mizbahu ba zai basu damar da za su yi handama ba.

A haka Alhaji Munir ya ci gaba da kula da tilon ɗansa, shi ke masa wanka, wanki, ba shi madara da duk wata ɗawainiya da ya kamata uwa ta yi, yayin da ‘yan aiki ke hidimar gyara gidan tare da dafawa Alhajin abinci.

A takaice dai sai da ya shafe tsayin shekaru biyar ba ya fita ko’ina kuma baya aikin komai sai na kula da yaronsa, zuwa lokacin bakin jama’a ya yi yawa a kansa, sai takura masa ake da zancen aure, musamman Hajiya inna ta sako shi gaba da maganar aure, acewarta bai kamata ya zauna haka ba mata ba, ko don wannan yaron ya kamata ya yi aure a samu mai kula da shi.

Daƙyar da siɗin goshi ta ciyo kan Munir ya yarda zai yi aure, amma ba don soyayya ba, sai don wannan yaron nasa da yake buƙatar tasowa acikin kulawar mace, don kuwa yasan ba zai taɓa maye gurbin uwa ba, sai dai ya yi iya abinda zai iya.

Tuna hakan da ya yi ya saka ya bawa Hajiya inna dama ta nemo masa bazawara mai hankali da imani ya aura.

A cikin shekarar ne ta haɗa shi da Hasina ‘yar ƙawarta, domin a’iya abinda ya bayyana a gare ta yarinyar tana da kirki matuƙa, ga haƙuri, ladabi da biyayya da tausayi, shiyasa ta zaɓa masa ita a matsayin wacce zata riƙe masa amanar ɗansa, bata sani ba ashe kura ce lulluɓe da fatar akuya….

More comment more typing..

Idan na ji shiru kuma zaku ji shiru🤷🏻‍♀️
Follow me on wattpad @ummu inteesar

RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹

*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*
*DEDICATED TO: HAUWA’U S ZARIA (ANTY HAUWA)

SHUGABA TA GARI MUNA ALFAHARI DA KE.

*JINJINA:*Jinjina ta ban girma ga yaya Yusuf gumel, haƙiƙa ba Ni da wani abun faɗa face godiya a gareka da addu’a, Allah ya baku zaman lafiya da kai da amaryrka tare da zuri’a ta gari.

Godiya marar adadi.
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 13-14

Ba a wani ɓata lokaci ba aka ɗaura masu aure, kasancewar dukkaninsu ba yara ba ne, bayan sati biyu da ɗaurin auren amarya Hasina ta tare a ɗakinta.

Washe garin ranar tariya, Alhaji Munir ya zaunar da Hasina ya na mata nasiha da riƙon amana, ya kalle ta sosai ya ce “Da farko dai ina miki Barka da shigowa wanga gida mai albarka, da fatan Allah ya ba mu zaman lahiya mai ɗorewa, bayan haka, ke riga  ke san komi akaina, ke san ina da yaro Abdul ke san kuma na gaya miki ba shi da lafiya, amanata ne shi ɗin, yanzu kuma zan damƙa wannan amana tawa a gare ki, a matsayinki na uwa, da fatar za ki tarbiyyantar da shi, ki kuma riƙe shi amana tare da nuna mai soyayya tamkar ɗan cikinki.”+

Hasina da kanta yake sunkuye, sai lokacin ta ɗago da murmushi a fuskarta ta ce “Insha’allah Alhaji na maka alƙawarin zan riƙe shi amana ai shi ɗa na kowa ne, da ƴaƴa da dukiya ba asan mai morarsu ba.”

Dan tsagaitawa ta yi a lokacin da Alhaji Munir ke saka mata albarka, can ta ce “Alhaji wai ina yaron nawa ne? Bangan shi ba tun jiya.”

Miƙewa ya yi ya je boys quaters da kansa ya karɓo Abdul da ya bari hannun Ladi kwana biyu, ya shigo falon yana janye da hannunsa.

Miƙewa ta yi cikin hanzari ta nufo su tana cewa “oyoyo! ga ɗana.”
Ita a zatonta ko yaron bashi da lafiya ne kawai, kamar yanda mahaifinsa ya gaya mata.

Sai dai me ta na matsawa kusa aka yi rashin Sa’a idonta suka sauka akan mummunar halittar fuskarsa.

Yam! Ta ji tsikar jikinta ta tashi, rintse idonta ta yi da ƙarfi a ranta ta na faɗar “Subhanallah! Innalillahi wa inna ilaihir raji’un!”

Can kuma kamar wacce aka mintsina ta yi saurin buɗe idonta, ta na wanyancewa da faɗar “Bari in buɗe idona in ga kyakkyawan yarona, kasan in za’a wa mutum suprise dole ya ruhe idonai.”

Nan da nan Alhaji ya sake fuska saɓanin ɗazu da ya tamke ta saboda ganin Hasina ta rufe ido, ya ce “To ai ga shi nan yanzu, amana ne shi a hannunki, ina sonai matuƙa, dan haka ina ƙara roƙonki da ki riƙe min shi amana don Allah, ke ga sai ki jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, ga lada ga la’ada.”

Matsawa ya yi kusa da Abdul da tun shigowarsu ɗakin ya yiwa Hasina ƙuri da idonsa ɗaya, ya sunkuya ya ce “Abdul yaron kirki, ga mamakka, nasan baka santa ba koh?”

Yaron ya ɗaga kansa saba alamar eh.

Baban ya ce masa “To ita at mamakka ka ji, ka yi mata biyayya, ita za ta rinƙa maka wanka da wanki da duk abinda ni ka maka da.”

STORY CONTINUES BELOW
Ita kuwa da ta ga Alhaji ya tsinke yana hira da ɗansa kawai sai ta sulale zuwa ɗakinta, sai haƙi take kamar wacce ta shiga gasar tsere.

Ita kam a tsayin rayuwarta bata taɓa cin karo da mummunar halitta irin wannan ba, wai kuma a haka Alhaji Munir ke yaudarar kansa da cewa za ta kular masa da wannan dodon? Inah! Ai sam ba za ta saɓu ba, bindiga a ruwa.

Ita fa ta zo nan gidan ne don ta huta ba don ta yi bauta ba, amma idan yasan wata ai bai san wata ba, za ta ɓullo masa ta bayan gida ne.

Da wannan tunanin ya shigo ya same ta a ɗakin.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
A haka rayuwar ta ci gaba da gangarawa, Alhaji Munir ya ɗauki yarda gaba ɗaya ya bawa matarsa Hasina, don haka yanzu ya koma a bakin kasuwancinsa ba tare da fargabar komai ba, wai shi a dole ya samu mata mai amana, don ganin  irin tarairayar da take yiwa Abdul a gabansa, ya manta cewa ba a yabon ɗan kuturu sai ya shekara goma da yatsa.

‘Yan uwansa ba su ji daɗin wannan komawar tasa kasuwa ba, domin ya dawo ya maye gurbinsa da suka cike.

Sun masa ɓarna mai yawa a dukiya, sun saci ta sata sun ci ta ci, ba tare da yasan me suke aikatawa ba, sai bayan komawarsa ya tarar da wannan ɓarnar, ganin shagunan sun rame sosai, ya saka ya tara su don yin bincike.

Ganin ya titsiye su sai suka yi masa karyar cewa ɓarayi ne suka shiga shagunan da dare suka yi sata, a lokacin sun so su gaya masa, amma gudun kada su tashi hankalinsa a yi haihuwar guzuma ɗa kwance uwa kwance, ya saka suka tsuke bakinsu, kuma wai sun yi iya ƙoƙarin su ganin komai ya dawo dai-dai amma hakan ya ci tura.

Ba dan ya yarda da waɗannan tatsuniyoyin na su ba ya sallame su suka tafi, a ransa yake cewa “Da ba don ku ‘yan uwansa ba ne, da ba abinda zai hanani yin ƙararku, amma idan na yi hakan kamar na daɓawa cikina wuƙa ne.”

A bangaren da ya bar yaya Mizbahu kuwa, ya ji daɗi sosai yanda ya tarar da komai na tafiya yanda ya kamata, ga kuma uwar riba mai yawa da aka samu, don haka ya kasa janye yaya Mizbahu a gun.

Wannan abun ya baƙantawa sauran ‘yan uwansa rai ba kaɗan ba, don haka suka fara tunanin ko zasu haɗa da mizbahun ne a cikin list ɗin maƙiyansu.

©¥¥¥¥¥¥¥

Bayan shekara shida Abubuwa da yawa sun faru tsakanin farin ciki da saɓaninsa, acikin abubuwan da suka faru kuwa har da shiga bokaye da ‘yan tsibbu da ‘yan uwan nasa suka yi domin su ga bayansa.
Akwai wata rana ma da suka saka ma Abdul magani a abinci ya ci, ya sha ciwo sosai kamar zai mutu, amma da yake yana da sauran shan ruwa a gaba sai ya rayu, tun wannan lokacin ne kuma bai kuma lafiya, don kuwa baya cikakken wata bai yi ciwon da zai danganta shi da asibiti ba, maganin ya masa illa sosai a jiki.

A cikin wannan jinyar ce aka samu akasi, watarana da aka masa allura sai ƙafarsa ɗaya ta shanye, anyi maganin an har an gaji amma ƙafar bata miƙe ba.

Wannan ita ce mummunar ƙaddara ta biyu da ta afku a rayuwar yaron, hankalin mahaifinsa ya kai kololuwar tashi, da ya ga an shafe shekaru biyu a haka sai ya siyawa yaron keken guragu don sauƙaƙa masa.

¥¥¥¥¥¥¥¥
Hasina kuwa ta ci gaba da yiwa Alhajin zagon ƙasa ba tare da saninsa ba, ita fatanta bai wuce ta mallaki dukiyarsa gaba ɗaya ba, don haka ta shiga sahun maƙiyansa na ɓoye masu san hallaka shi shi da yaronsa.

Ta ko’ina farautar rayuwar ɗan talikin yaron nan ake, amma da yake Allah shi ke bawa bayinsa na gari kariya, sai gashi har yau sun kasa samun nasarar hallaka shi.

*Dawowa da ga labari.*

Ranar wata Laraba da misalin ƙarfe 10:05 na safe Abdul ne zaune kan kekensa a ƙofar ajinsu, wasu ‘yan yara sa’aninsa ne suka zo wucewa, cikin rashin Sa’a keken ta taɗe ɗaya daga cikinsu ya faɗi bakinsa ya fashe, sauran suka nufe shi don su tada shi.

Abdul ya kalli wanda ya faɗin ya ce “Don Allah ka yi hanƙuri ba da gangan na ba.”

Ɗai daga cikin yaran ya ce “Babu wani nan baƙin mugu, mummunan banza, da gangan kat aje kekenka bisa hanya tun da ka na son ka maida kowa gurmu irinka.”

Sadik abokin Abdul ya yi saurin matsowa ya ce “Kai Shamsu, mi at haka? Halam ku baku da tausai, ai dai ba shi yat maida kai nai haka ba, kuma baku wuce zama haka nan ba, kuma tunda ka ce da gangan na, to an ture, ka yi abinda zaka yi.”

Daga jin haka Shamsu ya matso kusa dama rigimammen yaro ne, nan fa faɗa ya kacame dambe suke sosai.

Su na cikin haka sai ga wani malami ya zo wucewa, tsayawa ya yi, ya raba su tare da neman ba’asi.

Abdul sai kuka yake ganin ana rigima saboda shi.

Sadik ya kwashe komai ya gayawa malamin, nan take malamin ya bawa Shamsu rashin gaskiya kuma ya masa bulala biyar, kasancewar a makarantar ba a raga maka idan a ka kama ka da laifin takurawa ko ciwa nakasasshe zarafi, acewar malaman makarantar, makarantar ta nakasasshi ce, masu lafiyan sakaya su kawai aka yi ba don komai ba, sai don kada nakasasshin su ga an ware su ko an nuna bambanci tsakaninsu da masu lafiya…

Wannan abun da ya faru yau a makaranta ya saka Abdul ya ƙara jin tsanar karatun, ga shi yaro ne mai hazaƙa har yafi masu lafiyar saurin fahimta.

A ransa ya ce “Yau kam, dole in faɗawa Abbuna ya cire ni makarantar na gaji, tunda kowa baya sona gwanda na zauna gida.”

Da aka tashi daga makaranta Baba direba ya zo ya ɗauki Abdul zuwa gida kamar kullum.

Da da dare bayan Alhaji Munir ya dawo, suna cin abincin dare shi da iyalinsa, Abdul ya kalle shi ya ce “Abbu ni don Allah ka cire ni dam-makarantar nan ban son karatun na gaji.” Ya faɗa ya na shirin yin kuka.

Baban ya dube shi cikin kulawa ya ce “Haba ɗana! Mi anka maka kaka son barin makaranta bayan Kana da ƙoƙarinka?”

Murya na rawa yaron ya ce “Ni dai na gaji tun da kowa bai sona an tsane ni, gara in baz-zuwa cikin mutane, ɗazun ga Shamsu yacce min mummuna baƙin gurmu.”
Ya faɗa ya na fashewa da kuka.

Cikin tsananin tausayi Baban nasa ya kalle shi ya ce “…….

Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal
More comment more typing….

RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*
*DEDICATED TO: All members of HALLITTAR ALLAH CE FANS GROUP
Ngd da adduoinku a gare ni, Allah ya bar zumunci, much love🥰🥰
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 15-16

Cikin tsananin tausayi Baban nasa ya kalle shi ya ce “Ka ƙara hanƙuri yarona, kakka damu da maganar Shamsu, insha’allahu za ka ji dama ƙahwakka zata miƙe, yanzu dai ka cigaba da zuwa makaranta, ka ga saura kaɗan ku ƙare primary, kuna ƙarewa shikenan sai ka bar zuwa ka ji.”

Da wannan zantuka ya samu ya yiwa Abdul wayo, har ya yarda zai cigaba da zuwa makaranta.

Bayan kamar sati ɗaya da yin haka Abdul ya kwanta rashin lafiya wacce ta sada shi da asibiti, wani irin zazzafan ciwo ciki ne ke damunsa, a haka ya share sati Uku a asibiti ya na jinya, inda Hajiya Hasina ke kula da shi a asibiti bayan Alhajin ya ɗaga zuwa kasuwa ko wani guri cikin asibitin.+

A zahiri idan ka ga yanda Hasina take yi, za ka rantse da Allah ta na kula da shi tamkar ɗan cikinta, sai dai wannan fuska ce da take ara tana nunawa mutane, idan ya rage ɗakin daga ita sai shi, to fa a nan za ta fitar da fuskarta ta ainahi, ta dinga zubawa yaron ranƙwashi a kai kenan, ita ko tausaya masa ma bata yi, saboda zuciyar kafirai ke gare ta.

Bayan ya warke a ka sallame su zuwa gida.

Washegarin ranar da misalin sha biyu na rana, Abdul ne kan kekensa ya na ta yawo a harabar makeken gidansu shi kaɗai, sai wasarsa yake abinsa, domin tuni ya saba da kaɗaici.

Hasina ce ta zo za ta wuce zuwa ɗakinta, cikin rashin Sa’a Abdul ya taka mata ƙafa da kekensa ba tare da sani ba.

Wata shegiyar ƙara ta saki tare da juyowa a kufule, ta saka hannu biyu ta hantsilar da keken cike da rashin imani.

Jikake Gwaraf! Abdul ya faɗi ƙasa, hancinsa ya ƙumu da ƙasa take hancin ya fara feshin jini.

Yaron ya zabga ihu a wahalce don jin wata irin azaba da ya yi.

Takowa ta yi cike da mugunta ta zo inda yake kwance a kife kan gefen kuncinsa na dama, ta so ta kama kunnensa ta mirɗe, sai dai bangaren hagun dake sama ba shi da kunne nan ma a shafe ne, ganin haka ya saka ta birkito da shi zuwa bangaren dake da halittar kunnen, ta kama kunnen ta mirɗe sosai ta na faɗar “Wato kai dan ubanka ni za ka take ma ƙahwa? Ka ga shegen yaro, dama irinku na aka cema gurmu kahi mai ƙahwa iya shege, ɗan nema mai shafaffar huska, in kak-ƙara takina sai na cire maka sauran kunne gudan da yarrage ma, in ga ta iskanci.”

Shi dai bawan Allah Abdul bai ce komai ba, zafin ya haɗe masa biyu ga zafin gumuwar da ya yi gana mirɗe masa kunne da ta yi, wanda har zuwa yanzu bata saki kunnen ba.

Jin shiru yasa ta ci gaba da cewa “Shina ina magana kak-ƙyale ni? wato ga mahaukacciya koh? To wallahi bari ka jiya duk ranar da kat kuskura kat hwaɗama babanka ko wani ina maka mugunta, wallahi sai na kashe ka….”

Ta na cikin wannan sababin da jiyo sallama a ƙofar shigowa tsakar gidan, a hanzarce ta saki kunnensa tare da  tallabo shi ta na faɗar “Sannu! Sannu ɗan ga, ba ka dai ji ciwo ba koh?”

STORY CONTINUES BELOW
Dai-dai lokacin ne kuma Salamatu ta iso tsakar gidan, kai tsaye gun su ta nufa ta na faɗar “Subhanallah! Mi ka hwaruwa nan?”

Ido cike taf da ƙwalla Hasina ta ɗora Abdul kan kekensa ta na faɗar “Allah sarki bawan Allah!, sannu ka ji!.” Ta faɗa, sannan ta juyo ga Salamatu ta ce “Wallahi hwaɗuwa yay-yi shina hancinai yat hwashe.”

Ta na maganar ta na ƙoƙarin shanye ƙwallarta, idan ka ga yanda take yi ba za ka taɓa tunanin cewa ita ta kayar da shi ba.

“Allah sarki! Sannu Abdul, Allah tsare gaba.” Salamatu ta faɗa.

Tura keken Hajiya Hasina ta yi Salamatu na miye da ita har suka shige falon, inda ta bar Salamatun a falo ta je don kai Abdul ɗakinsa.

Bayan ta shigar da shi ɗakin sai da ta falle shi da kyakkyawan mari a ɓangaren da yake a shafen, daman bata da gurin da take duka a jikinsa sama da nan, acewarta ya fi daɗin mari nan da yake a shafe sumul kamar siminti.

Sai da ta gama zazzare masa ido tare da ƙara tsorata shi a kan idan ya faɗa kashinsa ya bushe, sannan ta fito daga ɗakin ta na shimfiɗa yanayin damuwa a fuskarta.

Anan inda ta bar Salamatun a nan ta same ta, zama ta yi don su gaisa.

“Sannu Hajiya, ya gida, ya ƙoƙarin kula muna da wanga yaron.” Salamatu ta faɗa.

“Alhamdulillah! Ƙoƙari kam, anan nan ana yi, ya anka iya? Ai rayuwa ce.” Ta mayar mata da amsa.

Salamatu ta dube ta ta ce “Hajiya haƙiƙa yaron nan Abdul yana matuƙar ba Ni tausayi, idan na tuna tun haihuwarsa har zuwa yanzu bai san daɗin lafiya ba, gashi ya rasa mahaihiyarshi tun yana jariri, daga baya kuma lalurar gurmunta ta same shi, har kuka nake masa idan na tuna wallahi.”

Hasina ta marai-raice fuska kamar da gaske ta ce “To ya anka iya, dama bawa bai isa ya guje ma ƙaddara tai ba, shi kuma haka tashi ƙaddarar take, ana ta neman magani amma ciwo sai gaba ya kai.”

“Kuna zuwa asibiti ko Hajjiya?” Ta tambaya.

Ta ce “Haba Yaya Salamatu! sanin kanki na yadda Alhaji ka son Abdul bai zuba mai ido haka kurum, bayan yana da kuɗɗin da zai biɗar mai magani, ke gamu kullum yawon asibiti, ɗa kamat ɗan roƙo? Yanzu dai wani sati ma zamu komawa asibiti can Kano, don a mai aikin ƙafar a gani ko Allah na sa a dace, dama tuni munka gama magana da likitoci, rashin lahiyar ga tashi nat tsaishe mu da an daɗe da mai aiki.”

Dogon numfashi Salamatu ta ja ta sauke sannan ta ce “Hmmm! To Allah ya sawwaƙa!, Allah yasa ayi a Sa’a, ko wagga lalurar ya samu ya rabu da ita ai an rage tunda waccen matsalar Halittarsa ce a haka.”

Daga haka suka rufe wannan hirar aka zaro wata, har bayan wani dogon lokaci sannan Salamatu ta yiwa Hajiya sallama ta tafi.

Bata wani tsaida ta ba, dama abu ga mai jira, don tun ɗazu take jin ringing ɗin wayarta harma ta duba ta ga Kulu mai adashen sharri ce, amma ba halin ɗagawa, domin ko giyar wake ta sha ba za ta karɓa kiran Kulu a gaban yaya Salamatu ba.

Bayan ficewartan ne ta ƙule cikin ɗakinta sannan ta kira Kulu a waya, anan Kulun ta shaida mata ga ta nan zuwa gidanta yanzu domin ta samo masu wata hanya da take ganin za ta sada su da cikar burinsu ba tare da kowa ya zargi komai a kai ba.

Hajiyar ta ji daɗin wannan albishirin ba kaɗan ba don haka ta ce “Sai ke taho Abbukiyata ta kaina!.”

Ta na gama faɗa ta kashe wayar, ta gyara zamanta a gefen gadon ta na jin wani nishaɗi, ta zaƙu Kulu ta zo ta ji wace kitimurmurar ta ƙullo, don ta san ƙawar tata ba dai iya makirci ba.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥€€

A bangaren su yaya Bilya kuwa, zuwa lokacin fa abin ya dame su sosai ta yanda wannan matsalar ta ƙi ci ta ƙi cinye wa, don haka suka yi shawarar komawa gidan bokansu don neman mafita.

Su uku ne zaune a gaban bokansu wanda suke kira da malam ilu, kowanne su ya tanƙwashe ƙafafuwa su na sauraren bayaninsa.

Malam ilu ya kalle su ya ce “Wan ga yaron da kuke gani sai ku bar shi kawai, ga dukkan alamu asiri bai tasiri ga jikinai sosai, don na hanga na hango ban ga alamat nasara ba, kullum sai tahiyar hawainiya ake, ana tahiya ana dawowa baya, na rasa dalili, amma ku bar maganar yaron hannuna ni nissan wadda zan yi da shi, yanzu ku maida hankali ga uban ko kuna nasara.”

Yaya Bilya ya gyara zama ya ce “To Allah ya taimaki malam, yanzu….”

Bai gama maganar ba Boka Ilu ya katse shi cikin tsawa “Sau nawa zan ce maka wanga ba aikin Allah na ba? To ka kiyayi gaba, in dai ana gabana ba a kiran sunan Allah balle a nemi taimako daga gare shi, sai dai ka kira rauhanai.”

“Ayi hanƙuri Allah ya huci zucciyar Malam bai sakewa, yanzu ma mantuwa ce.” Sani ya faɗa murya na rawa, domin ko da suke mazaje amma sun razana da furucinsa.

Shiru suka yi ba wanda ya kuma gigin magana can, Ilu ya kalle su ya bushe da wata mahaukaciyar dariya, sai da  ya yi mai isar sa sannan ya dubi Bilya ya ce “ina jinka ci gaba da maganakka.”

Cikin sanyin jiki Bilya ya ce “Yanzu abinda muka so, a mallake muna Alhaji Munir sai yadda muka yi da shi, ina ganin iya haka ɗai ya ishe mu.”

Wata dariyar Ilu ya ƙara kecewa da ita sai da ya kwashi ‘yan mintuna kafin ya tsagaita ya ce “Ka ga la’ananne, maƙi hukuncin Allah! Wato so kake ya zama kuka juya akalarshi da dukiyarsa koh?”

Sunusi ya yi karaf ya ce “Hakan ko Malam.”

“Ta kwana gidan sauƙi.” Boka Ilu ya faɗa, tare da cewa yanzu ku tashi ku tahi, bayan kwana biyu gudanku ya dawo ya amsammuku magani, abinda yassa ban baku yanzu ba, ina son sai na yi dogon bincike akainai shiyasa.”

Miƙewa suka yi su na faɗi to mu muntahi sai mun dawo mai baƙar aniya.”

Dariyar jin daɗi ya yi sannan ya ce “Ku ɓace min daga gani mutanen banza la’ananni.”

Ba musu suka fice daga turakarsa suka nufi motarsu.

A hanyarsu ta komawa gida yaya Bilya ke ta mita wai don me Malam Ilu zai dinga ce masa la’ananne? Shi fa ba la’ananne ba ne.

Da alama dai maganar ta masa ciwo sosai.

Dariya sosai ‘yan uwansa ke masa, can Sunusi ya ce “Haba yaya Bilya! To dama kai minana in ba la’ananne ba? Ka tuna hwa wagga ba hanyar Allah ta munka biyo ba, sannan in ba la’ananne ba, wa ka son hallaka ɗan’uwa nai saboda dukiya?”

Sauran suka amshe zancen da cewa “Eh wallahi ko gaskiyarka Sunusi dukanmu la’ananni ne.”
A haka suka ta zancensu su na dariyar jin daɗi har suka isa gida.

¥¥¥¥¥¥¥¥

Da yamma Kulu mai adashen sharri ta zo, suka kitse magana ita da Hajiya Hasina sannan ta bar gidan da alƙawarin idan ranar aiwatar da aikin ta zo za ta dawo.

Dama bata yawan zuwa gidan domin basa so a ankare da manufarsu, shiyasa suka fi yin waya, idan dai ka ga Kulu a gidan to Babban abu ne ya kawo ta.

Bayan sati ɗaya suka shirya zuwa Kano don kai Abdul gun aikin ƙafar da za’a masa a National othapedic hospital Dala Kano.

Bayan isar su garin ba a wani jima ba a ka kammala komai na shirye-shiryen aikin nasa.

A wata ranar Lahadi aka samu nasarar yi masa aikin ƙafar, sai dai fatar Allah yasa an yi a Sa’a……

More comment more typing…….

Karku manta, idan na ji shiru kuma zaku ji shiru😹🤷🏻‍♀️

Follow me on wattpad @Ruky_I_lawal

RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹

*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*
________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

PAGE 17-18

Masha’allah! An yiwa Abdul aikin ƙafa kuma aiki ya yi kyau sai dai fatan Allah ya tashi kafaɗunsa.

Tare da Hajiya Hasina da kuma Ladi mai aiki a ka tafi, su ne masu kula da shi a asibitin, a kullum kwana duniya sai Ladi ta je masaukinsu a nan Kano ta dafo masu abinci ta kawo masu asibiti.

An sarƙafe ƙafar Abdul ne a cikin wasu ƙarafuna, shi dai ga shi nan kwance ne kawai shi kaɗai ya san irin zogi da raɗaɗin da ƙafarsa ke masa.+

A haka suka ci gaba da jinyarsa har bayan watanni huɗu zuwa biyar sa’annan aka sallame su bayan ya ji dama.

Alhamdulillah! Aiki ya yi kyau domin ko da aka sallame su Abdul ya fara taka ƙafarsa, amma bisa ga jagorancin sanduna guda biyu.

Sai da suka kwana biyu a masaukinsu na Kano suka huta, bayan sun kammala dukkan shirye-shiryen su suka hau mota zuwa Sokoto, da yake tun shekaranjiya Alhajin ya kira direbansa ya zo don maida su gida.

Sai da suka shafe a wanni shida suna tafiya kafin suka iso Birnin Shehu daular Usmaniyya, direban bai zame ko’ina ba sai sama road, a ƙofar gidan Alhaji ya tsayar da motar tare da danna horn, da gudu mai gadi ya zo don buɗe ƙofar, amma sai da ya fara leƙowa ya ga ko suwaye tukunna, sannan ya je ya wangale masu ƙofar gate ɗin suka shige.

Sai da direban ya dai-daita tsayuwar motar, sannan suka fara fitowa, ma’aikatan gidan ne suka yi caa! don kawo gaisuwa a ciki harda mai gadi.

Faɗar suke “Sannu da zuwa Alhaji, kun sha hanya.”

“Yawwa sannu, da hwatar mun same ku lafiya.” Alhajin ya faɗa.

“Ya jikin Abdul? Da hwatar an yi nasarar aikin?” Suka tambaya.

A dai-dai lokacin ne kuma Hasina ta taimakawa Abdul ya fito daga motar tare da tsayuwa kan sandunansa.

Kafin Alhajin ya ce wani abu, Abdul ya bayyana tsaye a gabansu, don haka gaba ɗayan su suka haɗa baki cike da mamaki suka ce “Masha’allah lahiya ta samu, Allah sa lafiyar ta ɗore.”

Alhajin ya amsa da Amin, Hajiya ta dubi Abdul ta ce “Ɗana mu shiga ciki ko?”

Gyaɗa mata kai kawai ya yi, ta shiga gaba ya na biye da ita a baya, ya na takawa a hankali, Ladi na take masa baya har zuwa Babban falon gidan, sai da Hajiya da Alhaji suka shige ɗakinsu, sannan ta ja Abdul zuwa ɗakinsa ta cire masa kaya tare da nuna masa yanda zai yi wanka sannan ta fice daga banɗakin.

A gaban walldrop ɗinsa ta tsaya, ta shiga duba masa kayan shan iska wanda za su dace da yanayin, domin a na tsaka da yanayin zafi.

Wata ƙaramar t-shirt da wando tree-quater ta zaɓar masa ta ajiye masa su a gefen gadonsa inda zai iya ganinsu, ka na ta wuce zuwa kitchen don ganin ko sauran abokanan aikinta sun gama girki?

STORY CONTINUES BELOW
Ai kuwa ta je a sa’a domin har sun kammala komai tuni, sanin cewa masu gidan na hanya, don haka ta samo ɗan madai-daicin plate ta shaƙewa Abdul shi da abincin sannan ta fice zuwa ɗakinsa.

Ko da ta ƙaraso ɗakin ya fito daga wanka ya na kiciniyar saka wandonsa ya kasa, yana jin an buɗe ƙofar ya yi saurin komawa gefen gado ya zauna tare da saka hannayensa yana kare jikinsa, wai shi kada a gane masa jikinsa.

Hakan ya bawa Ladi dariya ba kaɗan ba, sai da ta ɗan dara sannan ta isa gabansa tare da ajiye plate ɗin abincin ta na cewa “Ɗana Abdul kawo wandon in gyara maka shi.”

Ba musu ya miƙa mata ya na sussunne kai ƙasa alamun dai ya na jin kunya, damar abinda dai akwai pant a jikinsa.

Ƙarba ta yi ta gyara masa kana ta ce “Abdul ɗinmu an girma, ka hwara jin kunyata koh?, Uhmm! Maza ka taho ga abinci na kawo maka, ka tabbatar ka canye shi duka.”

Tana gama faɗa ta juya ta bar ɗakin.

Zama ya yi ya ci abincinsa a tsanake.

¥¥¥¥¥¥¥

Bayan kwana uku da dawowarsa daga jinya suka fara jarabawar ƙarshe a makaranta, wato dai da sun kammala ya ƙare primary kenan.

Cike da tsananin murna Abdul ke zuwa makaranta don rubuta jarabawarsa ta ƙarshe, daɗi yake ji sosai ganin zai ƙare ya huta da shiga cikin mutane dama Abbunsa ya masa alƙawarin da ya gama primary shi kenan ya gama boko, hakan ne silar farincikinsa.

Bayan wani ɗan dogon lokaci suka kammala jarabawar za’a je hutu, bayan kammala bikin ƙare makarantar.

A ranar da za’a masu bikin ƙare makarantar Alhaji Munir da kansa ya je tare da Abdul har makarantar don karɓo sakamakon jarabawarsa, tare da Hajiya Hasina suka je, Baba direba ne ke tuƙa su har makarantar.

Tun kusan ƙarfe goma na safe aka fara gudanar da shagalin bikin, ko’ina ka duba ‘yan makaranta ne birjik sanye cikin uniform ɗinsu, wando kalar blue black sai riga ligh blue kowa a tsaftace sai murna yara suke ga iyayensu a gefensu.

Bayan malaman makarantar sun kammala jawabansu, aka fara kiran ɗalibai masu hazaƙa don gabatar da shiraruwan da aka shirya, duk da cewa Abdul baya gari lokacin da ake ta rehazal, amma a kwana ukun da ya dawo sai da aka saka shi a shirin muhawara.
Don haka aka kira Abdul tare da sauran ‘yan team ɗinsa da team ɗin da za su gabza don gabatar da Muhawarar tasu.

An shirya Muhawarar ne a kan maudu’in shin da Manomi da likita wanne ya fi muhimmanci a rayuwar ɗan adam?

Abdul ya na team B team ɗin da za su kawo hujjoji a kan cewa Likita ya fi Manomi muhimmanci a rayuwar ɗan Adam.

A tsanake Abdul ya fita zuwa tsakiyar filin ya na gyara tsayuwa akan sandunansa, har zuwa lokacin da saura suka gama kawo hujjojinsu, dama shi ne last speaker na team ɗinsu, sai da aka zo kansa sannan ya fara zazzago hujjoji dake cike da hikima kamar wanda aka tsarawa a takarda, alhali shi ya tattaro hujjojinsa da kansa, kuma cikin kwana uku ya gama bitarsa.

Ya na zuwa a kan hujjarsa ta ƙarshe ya miƙa abin maganar tare da komawa gefe cikin sauran ‘yan uwansa ɗalibai, nan fa hall ɗin ya kaure da tafi, ji kake raf! raf!! raf!!!

Mutane sai mamakin baiwar yaron suke Gashi dai gurgu amma hikimarsa ta zarta shekarunsa.

Alhaji Munir da Hajiya Hasina suna zaune kusa da juna a ɗan gaba kaɗan, a bayansu suka jiyo wani mutum na magana da ɗan uwansa yana cewa “Gaskiya yaron ga ya cika mai hikima, Gashi dai gurmu na ga Halittatai mai muni da ban tsoro amma kuma hikima tai ta hi shi yawa, ko wane uba zai so ɗanai ya samu irin wagga baiwa ta ilimi.”

Duk da cewa Alhaji ya ji zafin aibanta masa halittar ɗa da aka yi, amma hakan bai hana shi murmusawa ba, domin ko ba komai sun gano irin baiwarsa da hikimarsa, sannan sun yaba da hakan, Allah shine abun godiya.

Bayan dawowar Abdul mazauninsa bada jimawa ba aka fara kiran ɗaliban da za’a karrama tare da basu kyautuka.

Kyauta uku Abdul ya karɓa a jere, ta farko da ya karɓa ita ce kyautar ɗalibin da yafi kowanne ƙwazo a makarantar, ta biyu kyautar ta ɗaya da yi a cikin ajinsu, ta uku kuma kyautar ɗalibin da yafi ko wanne ladabi a makarantar, ga shi ya ciwo wa team ɗinsu kyautar Muhawarar da aka yi.

Zuciyar Alhaji Munir cike da farin ciki suka dawo gida, haƙiƙanin gaskiya ya na alfahari da ɗansa.

Ita kuwa Hasina idan ranta ya yi dubu to ya ɓaci, zuciyarta cike da baƙin cikin wannan nasarar da yaron nan ya samu, sai dai ba ta isa ta nuna ba, saboda gurin wasa ake wasa gurin bindiga waye ƙyastu?.

Abdul ma ya yi farin ciki sosai, sai dai sun yi kukan rabuwa shi da Sadik, da wannan damuwar ya dawo gida.

Bayan dawowarsu gida, Hajiya Hasina cike da ƙuncin zuciya ta dannawa Kulu mai adashen sharri kira, ta ce “Kulu ki hwara shirin aikin nan namu kwanakkin ga  nika son a ƙaddamar da shi.”

Bata saurari Kulu ba saboda yanayin da take ciki kawai sai ta kashe wayarta.

Lokacin da Alhaji Munir na Kano gun jinyar ɗansa, su Bilya suka koma don  karɓo magani gun boka, bayan dawowarsa, suka yi nasarar barbaɗa masa a waina, suka je da ita kasuwa ya ci.

Tun daga ranar Alhaji Munir ya susuce a kan harkar kula da dukiyarsa, sake masu ita yake yanda suke so, komai su yaya Bilya suka ce baya musawa, saboda asirin dake tasiri a jikinsa.

Ganin wannan nasarar da suka fara samu, sai suka afkawa dukiyarsa da ɓarna suna masa shigo-shigo ba zurfi.

¥¥¥¥¥¥^¥¥¥¥

Bayan kwana uku da faruwar hakan Alhaji ya yi tafiya zuwa kwatano don saro wasu atamfofi.

Baƙar Rana….

Wataranar Talata da misalin ƙarfe uku na dare, sahu ya ɗauke duniyar ta yi tsit, baka jin komai sai kukan tsuntsaye.

Hajiya Hasina ta sulale cikin sanɗa ta je gun gate bayan ta gama karɓa waya, dama ta sakawa ma’aikatan gidan maganin barci a abinci sun ci, ko wannensu ya ɓingire, ta je ta buɗe masu ƙofa suka shigo ciki …..

Wasu matasa ne guda uku fuskarsu rufe take ruf da face mask baƙa.

Cikin sanɗa suka tsallake mai gadi da ya baje a gun ya na barci kamar matacce suka wuce zuwa cikin babban falon.

Ɗakin da Abdul yake kwance ciki ta nuna masu tare da komawa ɗakinta ba tare da ta yi magana ba, da yake tun safe sun kitse maganar, kuma bata son wani ya ji muryarta.

Abdul ya na tsakiyar barcinsa mai daɗi, kawai sai ji ya yi an rufe masa hanci da wani ƙyalle, tun daga nan bai kuma sanin yadda aka yi ba………..

More comment more typing……

Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal

Vote share & comment..

*RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹*

*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 19-20

Bayan sun shaƙa masa maganin kawar da hankali, suka tabbatar ya yi barcin sai ɗaya daga cikinsu ya duƙa ya saɓi yaron a kafaɗar ya yi gaba, yayin da ɗaya daga cikinsu ya shiga dudduba ko’ina don nemarwa yaron sandunansa, bai wani sha wahala ba, ya hango su a kusurwar gado inda Abdul ɗin ke ajiye su duk lokacin da zai kwanta barci.+

Cikin hanzari ya ɗauko su sannan suka bi bayan ɗan’uwansa cikin sanɗa har suka fice daga gidan.

A mota suka sami ɗayan har ya shimfiɗe Abdul a bayan mota.

But suka buɗe suka sanya sandunansa a ciki, sannan suka zagaya, ko wannensu ya buɗe gefe ɗaya suka shiga suka saka yaron a tsakiya.

Shigar su ke da wuya Gumush ya ja motar da ƙarfi ya hau titi, sai sharara uban gudu ya ke kamar zai bar duniya.

Kasancewar dare ya raba lokacin shiyasa garin ya yi tsit kamar ba wani mahaluƙi a ciki, wannan ne ya basu damar tiƙar gudu da mota son ransu domin ba kowa a kan kowanne titi, har suka fice daga cikin garin ba su haɗu da wani mahaluƙi ba.

Haka suka wantsu suna sharara gudu a tituna har zuwa lokacin da suka fice daga jahar gaba ɗaya.

A 200 yake tafiya hakan ya saka tafiyar da za’ayi a awa biyar suka yi ta a cikin awa uku kacal.

Zuwa lokacin sun fice daga Sokoto da Zamfara sun kama hanya ɗoɗar, ƙarfe shida na safe suka isa ƙanƙara, gangarawa suka fara yi zuwa cikin surƙuƙin daji, sai da suka yi nisa sosai, ganin haske ya fara hudo sararin samaniya ya sa suka faka motar, sannan suka fito ɗauke da yaron da har zuwa lokacin barci yake bai farka ba, ɗayan ya ɗauko sandunan Abdul suka shiga cikin wata duhuwar bishiyoyi, inda zai yi wuya a ankara da shi, sannan suka jefar da shi a gun, sandunansa suka watsa masa kusa da shi, sannan suka juya da gudu suka bar gun, suna nufar motarsu.

Bayan sun isa bakin motar sai da suka dudduba suka tabbatar ba kowa a gun sannan suka shiga motarsu tare da bata wuta, suka fice daga jejin gaba ɗaya suka hau titi ɗoɗar dan juyowa cikin gari.

Da suka yi ɗan nisa a tafiyarsu, Gumush ya kira Mai adashen sharri ya sanar mata aiki ya yi kyau.

Kirari ta hau yi masa tana faɗar “An gaida ranke-ranke hitilar sheri, duk kihin da yasshiga komakka ya zama nama, ka ga mugu ɗan miyagu, aikinka na kyau Gumush, sai kun taho ansar kuɗɗin aikinku, na san dole Hajjiya ta muku kyauta me tsoka.”

Gumush kuwa daɗi ya gama kashe shi, shi ma kirarin ya mata sannan suka kashe waya, ya ci gaba da murza sitiyarin motar cikin nishaɗi.

Bayan sun kashe wayar, cikin zumuɗi Kulu ta kira Hajiya Hasina ta shaida mata cewa an cika aiki.

A lokacin Hasina tana barci ko farkawa bata yi ba, ba wani zancen sallar asuba a gare ta, cikin magagin barci ta jiyo ƙarar wayarta, miƙa hannu ta yi ta ɗauka ba tare da ta buɗe idonta ba.

Jin albishirin da Kulu ta mata ya saka ta buɗe idonta da ƙarfi tare da hantsilowa daga gadon cikin tsananin murna, baki na ɓari ta ce “Kai! Amma na ji daɗin wanga labari ƙwarai, Kulu ki jira kirana dan ko kina da kaso mai tsoka ke da yaranki, bari in tahi in gama da matsalar mutanen gidan ga.”

Da gama faɗa ta kashe wayarta, ta miƙe cike da tsananin murna ta nufi ɗakin Abdul, shigar ta ke da wuya ta fito kai tsaye tsakar gidansu ta je ta tsaya tare da ware murya ta ƙwalla ƙara cikin wani firgitaccen yanayi, idan ka ganta ka rantse da Allah cewa da gaske ta na cikin tashin hankali.

Ihunta ne ya tayar da ‘yan aikin gidan daga barci mai nauyin da suke.

Mai gadi da Baba direba ne suka fara shigowa tsakar gidan a gigice suna faɗar “Lahiya dai hajjiya meh-hwaru?”

Ko kafin su rufe bakinsu sai ga ma’aikatan kitchen sun iso sashen su ma a firgice suna faɗar “Hajjiya meh-hwaru?.”

Nan take idonta ya fara zubar da ƙwallar makirci, kuka take sosai, daƙyar da siɗin goshi aka samu ta dakatar da kukan, bayan kowa ya gama firgita ta ce “Abdul na yat ɓace, ban ganai ba, Abdul ya tsere daga gidan ga.”

Cikin matuƙar tashin hankali kowa ya zaro ido waje, dukkansu suka runtuma zuwa ɗakin Abdul ba tare da sun jira umurnin Hajiyar ba.

Bayan sun dudduba ko’ina da ko’ina na cikin ɗakin sun tabbatar ba ya nan, suka fito tare da bazuwa kowanne lungu da saƙo na gidan suna nemansa, matan suka ba zama zuwa cikin sauran ɗakunan dake sashen.

Abu kamar wasa sai da suka shafe awanni suna nemansa, har boys quaters suka dudduba amma ko mai kama da shi ba su gani ba.

Hankalinsu ya kai ƙoluluwar tashi, ba ma kamar Hasina wacce ta kasa zaune ta kasa tsaye tsabar kiɗimewa.

A sanyaye suka watse domin sun gaji da jiran gawon shanu, sun cire tsammanin za su gan shi a gidan, sai dai ko wannensu da abinda yake saƙawa a ransa, kamar ba su yarda da maganar Hasina ba ta cewa wai Abdul guduwa ya yi ba, musanman Baba mai gadi da ya digawa hajiyar ayar tambaya, ya na tantama a ransa cewar wai yaron guduwa ya yi, to wanne dalili ne zai sa Abdul ya gudu daga cikin wannan daular bayan Mahaifinsa na matuƙar sonsa? Gaskiya da lauje a cikin naɗi, amma ba komai akwai ranar ƙindillanci ta na zuwa, ranar da za ta girbi abinda ta shuka, domin ya tabbatar in tana da hannu a cikin wannan lamarin watarana asirinta zai tonu, don kuwa ‘yan magana sun ce rana dubu ta ɓarawo   ɗaya ta mai kaya.

Da wannan tunanin Baba Direba ya koma bakin aikinsa cike da alhini.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Har zuwa ɓullowar rana bawan Allah Abdul ya na nan kwance inda suka yada shi bai farka daga sumammen barcinsa ba, sai zuwa lokacin da rana ta ƙwalle ta yi zafi sosai, zafin ranar da kuma zafin gasassun duwatsun dake gefe da gefensa ya saka Abdul ya fara buɗe idonsa a hankali tare da yin juyi don jin baƙon yanayi a tare da shi.

Gama buɗe idonsa ke da wuya ya ci gaba da waige-waige zuciyarsa cike da tsoro, tun kafin ya gama tantance inda yake zuciyarsa ta cika da ruɗani da tashin hankali.

Bayan ya tabbatar da a jeji ya ke kuma bai ga wani mahaluƙi a kusa ba, bar ta mutane ko tsuntsu bai gani ba, kawai sai ya taƙarƙare ya buɗe rabin bakinsa ya tsunduma ihu tun ƙarfinsa…..

More comment more typing……
Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal

RUKY I LAWAL CE

*HALLITAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

16 Safar/4 October.
1442hjr/2020.
DEDICATED TO: Jinin jikina🤭🙈

Allah ya ƙara maka lafiya mai amfani, ya azurtaka arziƙi na halal.

Readers asaka mun Jinin jiki a addu’a🙈🤭🏃🏻‍♀️
Special gift to: Fatima Sunusi Rabi’u(Ummu Affan)

Ƙawar amana..

Allah ya ƙara haɗe kanmu ya saka ki santalo mana ‘yan biyu sau biyu, mu je Kaduna shagalin suna…🤭😹

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

PAGE 21-22

Ihu yake kamar ba gobe, sai dai wannan ihun da yake yi shi ake kira da ihu bayan hari, don kuwa ya na tsakiyar jeji ne ihunka banza, ba wani mahaluƙi a kusa bare ya ji har ya kawo masa ɗauki.+

Ganin wannan ihun ba zai fitar da shi ba, ya saka ya yunƙura cike da ƙarfin hali ya tashi zaune, ya fara waige-waige wai koya ga sandunansa.

Ai kuwa Allah ya masa gyaɗar dogo, don kuwa ya hango su nesa da shi kaɗan, hannu ya miƙa don janyo ɗayar sandarsa da ta ɗan masa nisa, kawai sai hannunsa ya sauka a kan wani gasasshen dutsen dake kusa da shi, ba shiri ya tsandara ihu tare da janye hannun nasa.

Cikin matuƙar ƙarfin hali ya samu ya ɗauko ta tare da miƙewa ya fara dogara sandunan, domin ya ƙara gaba ko ya samu wanda zai taimake shi, don zuwa lokacin yunwa ta fara addabarsa ga kishir ruwa da yake ji sosai.

A haka ya ci gaba da tafiya, ya na tuntuɓe da duwatsu da itace dake gun, sai faɗuwa yake ya na tashi, wasu sassan jikinsa duk sun kukkuje, amma da yake yana da jarumta sai ka ga ya miƙe ya ci gaba da tafiya.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
A can gida kuwa, hankalin mazauna gidan Alhaji Munir ya kasa kwanciya gaba ɗaya, ga shi Hajiya ta hana kowa ya sanar da Alhaji ko wani dake waje ɓatar Abdul, a cewar ta bata so a ɗaga masa hankali alhali ya na gun kasuwancinsa, hakan ya saka kowa ya ja bakinsa ya tsuke suka zubawa sarautar Allah ido.

Can zuwa sha biyu na rana Hajiya Hasina ta fito da shirin fita unguwa, sai dai ba ta yi wata kwalliya ba, duk da cewa mayafi ta saka, amma kallo ɗaya zaka mata ka gane bata cikin walwala.

Da fitowar ta kai tsaye gun motarta ta nufa, Direbanta ne ya zo da sauri don karɓar makulli, domin a zatonsa shi zai fitar da ita, ga mamakinsa sai ya ji ta ce “A’ah! Hamisu komawakka ka huta, yau da kaina zan hita, dan yawo zan yi da yawa a garin.”

Da mamaki ya kalle ta ya ce “Amma hajiyya baki cikin yanayi mai daɗi, kuma kahin Alhaji ya tahi sai da yammin umurnin cewa in tabbatar duk inda za ki na na kai ki, kat in bari ki hita da kanki.”

Ɗago kanta ta yi da alama zancensa ya ɓata mata rai, cikin alamun fushi ta ce “Yau kuma sai nicce ma ban buƙatat tuƙinka, ka banni in ji da damuwata, so ni kai in kai rahoton ɓacewar ɗana wurin ‘yan sanda da kahwahen yaɗa labarai kahin Alhaji ya dawo.”

STORY CONTINUES BELOW
Har ya buɗi baki zai kuma cewa wani abu, ta ɗaga masa hannu ta na cewa “Ban son jin komi dagga gareka, in kakƙara yi min gardama wallahi a bakin aikinka.”

Ta na gama faɗa ta shige motar tare da mata key ta juyo hancin motar da ƙarfi, har ta na yunƙurin bige Hamisu direba, da ba don ya janye da sauri ba, da ɓarna ta auku.

Jiki a sanyaye Hamisu ya isa teburin da Baba direba ke zaune yana kallon duk abinda ke faruwa a gun, ya zauna kawai bai ce komai ba.

Haka ma Baba Direba bai ce komai ba, amma yana ji aransa cewa Uwar ɗakinsu tana da sa hannu a ɓatan yaron nan, yanzu ma wata munaƙisar za ta je ƙullowa wata ƙila, duk kuwa da an ce zato zunubi ko ya kasance gaskiya.

¥¥¥¥¥¥¥

Hajiya Hasina na barin gidan ta miƙi hanya sosai, maimakon ta nufi station ko gidan rediyo sai ta durfafi cikin gari, gidan ƙawarta Kulu mai adashen sharri, da yake awa biyu baya kenan da suka yi waya da ita, ta shaida mata cewa sha biyu na rana su Gumush za su zo karɓar kuɗin aikinsu, don kuwa sun dawo daga aikin da ta saka su.

Mintuna ashirin ne suka kai ta cikin ƙofar Atiku, da yake a unguwar gidan Kulun yake, sai da ta shiga da motarta har cikin lungunsu, sannan ta faka nesa kaɗan da gidan.

Ta fito cike da nishaɗi hannunta riƙe da ƙatuwar jakarta, ta ƙarasa gidan a ƙafa.

“Assalamu alaikum!”

Ta yi sallama a ƙofar gidan, ba tare da ta jira an amsa ba ta faɗa ciki kai tsaye ta na faɗar “Ina kike mai adashen sheri?”

Da murna Kulu ta fito daga ɗakin tana cewa “Gani nan Hajjiyata! Aiki ga mai ƙare ka, mu shiga ciki.”

Murmushi ne kwance a fuskar hajiyar ta nufin ɗakin tana yiwa Kulu mita.

“Gaskiya Kulu ki canza wanga baƙin gida, haba! Dan Allah duk kuɗɗin da kika samu a ce kina zaune cikin wagga baƙar shiya? Wai don bala’i ko mota bata shigowa lungun ga sai dai a aje ta garkat wani? habah!”

Mitarta take har suka isa cikin ɗakin Kulu bata ce komai ba sai dariya da ta yi.

Maimakon ta tamka Hasina a waccan maganar sai cewa ta yi “Hajjiya ga sunan ga ki.”
Ta nuna su Gumush da suka bararraje akan ya galgalallun kujerin falon.

Daƙyar Hasina ta iya zama a kan kujerar, sai da Kulu ta ɗauko mata filo ta ɗora sannan ta zauna a kai, ta na kallon su Gumush da murmushi a fuskarta.

Gumush ne ya ce “An gaida Hajjiya mai yawo da kuɗɗi, nerori basu wuya ga hannunki ga mu mun taho an ce kina biɗar mu.”

“Ƙwarai da gaske, kun yi min aikin da nijji daɗi nai sosai, tun shiga ta gidan Alhaji ba a taɓa ranar da niyyi hwarinciki ƙwarai ba irin na yau, don ko kun kawas min da dodon da nit tsani gani a duniya, yanzu ku hwaɗamin nawa at ladar aikinku?”

Wata uwar Shewa Gumush da yaransa uku suka buga, sannan ogan na su ya ce “Ai Hajjiya ki ɗai kwatanta, mun san zaki yi muna adalci.”

Murmushi kawai Hasina ta yi, ta buɗe jakarta ta ciro bandir ɗin ‘yan dubu guda huɗu ta ajiye masu a gabansu.

Ihu suka hau yi suna godiya, Gumush ya yi saurin kwashe kuɗin ya miƙe ya na faɗar “Ku taso mu tahi, sai mu shaggun madatsa, yau duk sai mun addabi kowane ƙaramin ɗan iska da at madatsa.”

Su na gama faɗa suka yi gaba har sauran sun fice, Gumush ya dawo daga baya ya ce “Hajjiya mun gode, ko gobe an ka samu wani aiki irin wanga ko ma wanda yat hishi karki ji komi ki kira mu, zamu miki shi sussettifully.” Ya faɗa wai shi a dole ya ji turanci.

Da gama faɗa ya juya ya bar ɗakin.

Kulu kuwa har jikinta ke ɓari ta ga an ajiye mata nata kuɗin, gajin haƙuri ta yi, ta ce “Hajjiya nihwa? Ina nawwa?”

STORY CONTINUES BELOW
Dariya Hasina ta yi ta ce “Matsalata dake kenan Abbukiyata gajin haƙuri, to ga na ki.”

Ta faɗa a lokacin da ta zura hannu jaka ta ɗauko dubu ɗari biyu ta bata.

A raine ta kalli kuɗin ta ce “Haba dai Hasinata! Waɗanga ai ke san sun min kaɗan, ko su sun hini samu hwa?”

“To ai sun hiki shan wahalar aikin.” Ta mayar mata da zance.

Ita kuwa ta ce “A’ah hwa Hajjiya! Ni ke san hat inda nissamo su? Sai da hwa nittahi har tsakiyar madatsa, nit lalubo tataccin ‘yan daba sannan ni sasu aikinki.”

Gyaɗa Kai Hasina ta yi da murmushi a labbanta ta ce “Ina motata sun kawo miki?”

Maƙullan ta miƙo mata ba tare da ta yi magana ba.

“Riƙe su can hannunki, ki ɗauki motar ki ƙara na baki ita halak malak, sai dai in aikina ya tashi zaki bashe ta amin.”

Ihun murna Kulu ta saka, sai da ta gama murnarta da godiya, sannan ta ce “Ni kam Hajjiya Alhaji Munir hwa? Ya san shegen ɗan nan ya ɓace?”

Wata Shewa Hasina ta yi ta ce “Ina hwa yassani? Ai na hana kowa ya hwaɗa mai, kuma nima  ban hwaɗa mai ba, don ban son ya taho ya ɓata min ranar hwarincikina, ke san yau dole in yi kwanan hwarin ciki.”

Ta ƙarashe zancen cike da fara’a.

Kulu ta ce “Kai! Gaskiya sai yanzu nika ganin ba mu kyauta ba, don yadda Alhaji ka son ɗan nan ya na iya haukacewa dan rashi nai.”

Miƙewa Hasina ta yi ta na jan wani uban tsaki tare da faɗar “Ke shi at matsalakki wallahi, to ni ke ga tahiyata, in kina jin tausai nai ki tai ki dawo da shi.”

Ta na gama faɗa ta yi fuu! Ta wuce, Kulu na lallashinta bata ko saurare ta ba, ta faɗa motarta ta wuce station ta kai report don kare kanta daga zargi, daga nan ta je gidan rediyon vision fm sokoto da garkuwa FM da sauran kafafen yaɗa labarai ta kai rahoto, sannan ta wuce gida.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Bawan Allah Abdul kuwa, a haka ya wanzu ya na tafiya a cikin jeji har shuɗewar wasu sa’o’i ba tare da ya haɗu da kowa ba.

Zuwa lokacin yunwa ta gama cinsa ya rasa abinda zai ci, don haka ya shiga zince-zince a ƙasa, duk wani abun da ya gani a ƙasa mai kama da abinci ɗauka yake ya kai baki, haka ma daƙyar ya samu wasu ruwan kududdufi ya ɗiba ya sha.

Tafe yake a hanya tun ya na kuka har hawayensa suka ƙafe, ya rasa wanene ya masa wannan ɗanyen aikin, duk da cewa shi ƙaramin yaro ne amma ba wanda ya fara zargi a ransa inba Mamansa ba, ya na ji a ransa da saka hannunta a jefar da shi da aka yi.

In ba ita ba, waya isa ya shiga ɗakinsa har kan gadonsa ya dauƙo shi ya fito da shi daga gidansu?

Haka ya ci gaba har dare ya riske shi, ya yasu a nan cikin tsakuwoyi ya kwanta ya na tunani kala-kala.

A ransa yake cewa “Allah sarki ni! Yau ina haɗaɗɗen gadona? Ga ni kwance babu ko shimfiɗa.”

Abbunsa ne ya faɗo masa a rai, a take ya shiga tuno ran da suka rabu na ƙarshe a daren ranar da zai yi tafiya zuwa kwatano, ya zaunar da shi su na hira, a cikin hirarsu yake cewa “Abdul ɗina gobe tun da sahe zan yin tahiya, ka kula da kanka, ga mamakka nan na san zata kula da kai sosai, ka mata biyayya, ka maida hankali ga karatu, in zan dawowa ina kawo maka kayan daɗi, sannan bayan na dawo muna komawa asibiti a duba ma ƙahwakka ka ji? Yanzu dai mi kaka son in kawo ma?.”

Gyaɗa Kai ya yi ya ce “Abu dai mai daɗi da kyau.”

Abdul na zuwa nan a zancen zucinsa ya share hawayen da ya gangaro masa, ya rufe idonsa, nan take barcin wahala ya yi gaba da shi…

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Bayan kwana biyu da ɓatar Abdul Alhaji Munir ya dawo gida cike da farin ciki da sa ran zai ɗora idonsa a kan tilon ɗansa, don ko ya jibgo masa tsaraba mai yawa, sai dai me? Ya dawo gida ya tarar da mummunan labari wanda ya tarwatsa tunaninsa da farincikinsa gaba ɗaya.

Ya shiga tsananin tashin hankali da damuwa da ruɗewar ƙwaƙwalwa, a ranar bai samu runtsawa ba, zuciyarsa cike da zargi.

Washegari ya tara dukkan mazauna gidansa ya shiga tuhumar su a kan ya a ka yi ɗansa ya ɓata?, sannan me suka yi bayan ɓatarsa? me yasa ba’a gaya masa ba?”

Baba Direba ne ya yi karaf ya ce “Tun shekaranjiya da yat ɓace munka so hwaɗa maka, amma Hajjiya ta hana mu sanar maka ta ce za ta biɗo shi kahin ka dawo.”

Juyawa ya yi zuwa ga Hasina ya na tambayar ta cike da tuhuma.?

“Missa kin ka min haka Hajjiya?”

Nan take idonta suka kawo ruwa, ta yi rau-rau da ido, cike da damuwa ta ce “Da ma ni ban son a ɗaga maka hankali, shiyasa nicce kat a hwaɗa ma, amma ai na kai rahoto a….”

Bata samu damar ƙarasawa ba saboda saukar wani gigitaccen mari da ta ji a kuncinta, cike da mamaki ta ɗago idonta da take gani disishi ta sauke su a fuskar Alhaji, da yake tsaye cikin ficewar hayyaci.

Mamaki ne ya rufe ta, yayinda Alhajin ke tsaye cikin ficewar hayyaci, shi kan shi bai san ya aka yi ya mare ta ba….

Sai dai bai damu da hakan ba ya hau ta da masifa a gaban ‘yan aikinta, faɗar ya ke “Ke san abinda kinka aikata min kuwa? Ina hankalinki da wayonki sun ka tahi? Ta a’a tilon ɗana kuma amanata ka ɓacewa baki hwaɗamin ba? Ya ma anka yi har kuka bari masu garkuwa da mutane suka shigo har cikin gida sun ka ɗauke min gudan jinina?”

Ganin Alhaji ya rufe ido ya na ta surfawa matarsa masifa, cikin wani irin yanayi da ba su taɓa ganinsa a ciki ba, ya saka duka ma’aikatan suka sulale daga wajen kafin ya juyo kansu, don ko da ɗai basu taɓa gani ko jin ya yiwa matarsa ko da tsawa ba sai ga shi yau har da mari, dole abin ya bawa mutum tsoro.

¥¥¥¥¥¥¥¥

Lokacin da labarin ɓatar Abdul ya riski ‘yan’uwan Alhaji da Mamansu kuwa, Mizbahu da Hajiya Inna sun shiga damuwa matuƙa yayin da su yaya Bilya,Sani da Sunusi suka ji tamkar su zuba ruwa a ƙasa su sha, labarin ya musu daɗi sosai don ko abin nema ne ya samu matar falke ta haifi jaki.

Sai dai sun ɓoye wannan murna a ƙasan ransu, don ko duk ƙwanƙwantonka baka isa ka gano wannan ɓoyayyiyar murnar tasu ba, inka gan su zaka rantse da Allah sun fi Alhaji Munir ɗin shiga damuwa.

Har gida suka je masa jaje, sannan su kansu mutane kan zo har gidajensu don masu jajen ɓatan yaron ɗan’uwansu……..
More comment
More typing………
Follow me on wattpad @ Ruky_i_lawal.

RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹

*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*
*DEDICATED TO: YAYA MUKTAR MUSA ƘARAMI (ABU HISHAM)*

MILIYOYIN GODIYA ZUWA GAREKA, RABBI YA BAR ZUMUNCI, ALLAH YA RAYA MANA YARANMU;

HISHAM MUKTAR MUSA ƘARAMI
AISHA MUKTAR MUSA ƘARAMI (MIMIE).

ALLAH YA RAYA SU CIKIN AMINCI, SU TA SO DA ƘAUNAR JUNANSU, SU ZAMA MASU AMFANAR DA AL’UMMA, AMEEN YA RABBI🥰🥰

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 23-24

Mutane basu sani ba cewa murna ya kamata a taya su ba jaje ba, don kuwa murna ce fal ransu, yanzu abu ɗaya ya rage masu shi ne; su kawar da ƙaninsu don su mallake dukiyarsu, sai dai fa har yanzu da sauran rina a kaba, kuma har yanzu tsugunne bata ƙare ba wai an sai da akuya an sayi kura, domin ko da sun kashe shi za’a raba gado kuma dole za’a ajiyewa yaron dukiyarsa har a gansa, tunda ba a da tabbacin ya mutu ko yana raye.+

Suna cikin wannan damuwar ne suka hau teburin shawara bayan sun haɗu a gidan Hajiya inna….

Yaya Bilya duk yafi su ɗaukar zafi, don haka ya kada baki ya ce “Ba abinda yafi kyau sai mu maida hankali mu nemo yaronga mu kashe shi tun kahin wankin hulla ya kai mu dare, don ko wanga aikin namu, shi aka kira da tufkar makaho ta gaba ta baya na warware wa.”

Sani ya saki ajiyar zuciya ya ce “Gaskiyakka yaya, dole sai mun yi da gaske, tunda aikin namu a sirrance  muka yinai, yanzu dai a ganina mu hanƙura mu ci gaba da biɗat yaron, tun da yanzu Munir ɗin a hannunmu yake sai yadda muka so mu yi da shi.”

Sunusi ya gyaɗa kai yana faɗar “Hakane, sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba.”

Da haka suka ci gaba da tattaunawarsu har zuwa wani tsawon lokaci, Mizbahu na daga gefe yana kallonsu, duk da ba ya jin me suke tattaunawa, ya san ba alkhairi suke ƙullawa ba.
Bai ce da su komai ba, sai fatan shiriya da ya bisu da ita.

¥¥¥¥¥^¥^¥^^¥¥¥

A can gidan Alhaji Munir kuwa bayan saɓanin da suka samu shi da matarsa, ta bi shi har ɗakinsa ta lallaɓa shi tare da ba shi haƙuri, kuma ta nuna masa bata damu da marin da ya mata ba, da haka ta shawo kansa ya yarda da ita, sannan ta sanar mishi ta kai report ɗin ɓatan Abdul a Marna police station ne.

Ya bata haƙurin marin da ya mata, ta kuma yafe masa cike da sakin Fuska ta ce “Bakomai mijina, na sani ka mare ni ne a cikin zafin zuciya da kuma kiɗima, ɓatan ɗa ai ba wasa ba ne, musamman mai lalura irinta Abdul.”

“Nagode sosai Hasina matar albarka!.” Ya faɗa cike da sakin Fuska, duk da cewa ba walwala ƙwata-ƙwata a tattare da shi tun lokacin ɓatan yaronsa.

Abinda bai sani ba shine; Hasina fa bata yafe masa da zuciya ɗaya ba, ta ƙudurce a ranta sai ta ɗau fansar wannan marin da ya mata, ko da za ta yi yawo tsirara.

STORY CONTINUES BELOW
¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Abdul kuwa tun a ranar da ya tabbatar ba shi da wani mai ceto ko majiɓinci al’amarinsa, duniya ta masa ƙunci, ya rasa inda zai fake ya ji daɗi, shi kaɗai a dokar daji ba ruwa ba abinci, sai dai ya yi ‘yan tsince-tsincensa a ƙasa yana ci, ko kuwa ya kakkabo kunnuwan fure ya ci, ruwa kuwa sai Sa’a yake haɗuwa da ruwan kududdufi ya sha, ga shi lokacin ƙarshen bazara ne, ba a fara ruwan sama ba, don haka ne ba wata inuwa mai daɗi ko wani damshin laima da zai zauna ya fake ya ji daɗi, a haka ya ci gaba da tafiya in ya gaji ya zauna ya huta, tunani kala-kala yake har tunanin da ya girmi ƙwaƙwalwarsa a wannan yanayin sai da ya yi shi, bai haɗu da kowa ba bare a samu mai taimaka masa ya maida shi gida gun Abbunsa…

Wani lokacin haka zai zauna yana kuka yana kiran “Abbuna! ka taho ka taimake ni, yunwa zata kashe ni, ga shi bansan hanyar komawa gida ba.”

¥¥¥¥¥¥^^

Ranar wuni na uku, Hasina ta nemi izinin mijinta, a kan cewa zata je duba wani ƙanin mahaifiyarta dake kwance a asibiti.

Kai tsaye ya amince mata don ba ya zaton ƙarya daga gare ta.

Tana fita bata zarce ko’ina ba sai gidan abokiyar cin mushenta, da yake a ranar ma ta ƙi yarda Direba ya kai ta.

Ɗaukar Kulu ta yi suka wuce can wani ƙauye dake gaban bafarawa estate domin a can gidan bokan Kulu ya ke.

Isar su ƙauyen Dundume ke da wuya, suka kutsa can ƙarshen garin inda gidan bokan yake, daga nesa da gidan suka yi fakin motar sannan suka ƙarasa ciki da ƙafa.

Layi suka tarar mata ne birjik waɗanda suka kauce hanya, kowacce jira take layi ya zo kanta.

Nan suka hau layi, har bayan shuɗewar awa layi bai zo kansu ba.

Hasina ta kalli Kulu da damuwa a fuskarta ta ce “Ni hwa na hwara gajiya, ke san hwa ƙarya niwwa Alhaji cewa zan je duba Kawu Basiru a asibiti, yanzu dana daɗe an samu matsala, yana iya kiran inna, ita ko ke san kwafsamin zata yi, bata iya ruhin asiri ba.”

Kallonta Kulu ta yi da ɗan murmushi a fuskarta ta ce “Abukkiyata ki kwantat da hankalinki, saura kaɗan ai mu kai ga layi, ke san dama shi aski in yattaho gaban goshi ya hi zahi.”

Tsagaitawa ta yi tana kallon Hasina don ta ga yanda ta karɓi zancen, jin ba ta ce komai ba kuma har yanzu da alamun damuwa a fuskarta, yasa ta ci gaba da cewa “Habah Hajjiyata! Ki ƙara hanƙuri, yanzu so kikai mu koma ya ci gaba da tuhumarki ɗanai har ya gano ke kinka ɓatar da shi? Ko so kikai Abdul ya samu mai maisai gida?”

Jin tambayoyin da Kulu ta watso mata yasa hankalinta ya yi mugun tashi, haƙiƙa ta yi ragon azanci da bata saka an kashe mata shi ba; ga shi yana son zame mata alaƙaƙai ƙadangaren bakin tulu.

Don haka dole ta haƙura har zuwa lokacin da layi zai zo kanta.

Bayan shuɗewar mintuna sha biyar, layi ya zo kansu, suka faɗa bukkar bokan..

“Salamu alaikum.”
Hasina ta faɗa cikin ɓarin baki, domin ta tsorata da yanayin gurin.

“Ke la’ananna!” Boka ya daka mata tsawa ya na faɗar “Ba a min sallama a nan, don ko ba aminci kinka zo nema ba..”

Jikin Hasina ne ya fara rawa da ta yi arba da mummunan mutumin dake zaune a gabanta, kasa yin magana ta yi, sai Kulu ce ta yi magana cikin ƙarfin hali ta ce “A yi hanƙuri boka bata sani ba ne.”

“A kiyaye gaba, in ba haka ba, in maida mutum kiyashi…”

Cikin ɓarin jiki Kulu ta ja hannun Hasina ta danƙwafar da ita suka zauna tare a gabansa..

“Meke tafe daku.”
Ya faɗa cikin sauti mara daɗin sauraro.

“Dama Abukkiyata ce na rako don ta kawo kukanta gare ka, tana so a mallake mata mijinta, kuma a……”

STORY CONTINUES BELOW
(Wa’iyazu billahi! mata mu ji tsoron Allah, idan kina da wata damuwa a zuci, ki miƙa ƙoƙon bararki zuwa ga mahaliccin wannan zuciyar, haƙiƙa ya fi ki sanin damuwarki, kuma shine kaɗai zai magance miki, zuwa gun boka ba zai amfanar dake komai ba, face ya saka ki a halaka da taɓewa, ya maidaki mushrika.)

Hannu bokan ya ɗaga mata alamun ta dakata, sannan ya tada kansa sama kamar mai nazarin wani abu, can ya dawo da fuskarsa ya zubawa Hasina jajayen idanunsa ya ce “Na sani, ki na son a mallake miki mijinki ne, ya bar damunki game da ɓacewar ɗa nai, shi ko ɗan a nisanta shi daga gida kuma a shahe mai tunanin gida da kowa da ya sani a ƙwaƙwalwarsa koh?”

Cikin alamun mamaki ta gyaɗa kanta sama alamar tabbatarwa.

Bayansa ya juya, ya ɗauko sauran tarkacensa sannan ya kuma juyowa kamar yanda yake da.

Bukkar ce ta yi shiru baka jin komai, sai ‘yan surutan da bokan ke yi ƙasa-ƙasa, yana yiwa kansa kirari.

Wasu ƙullukan gyallaye ya ciro guda biyu, ya miƙa mata ya ce “Wannan na jan ƙyalen ki saka masa a ruwan wanka, ki tabbatar ya yi wanka da su, sannan garin maganin ya bushe a jikinsa, na shuɗin ƙyallen kuwa ki tabbatar kin saka masa a abinci ya ci, yana ci magana ta ƙare.”

Cike da murna ta karɓi ƙullukan ta saka a jaka tana godiya, a ranta ta ce “Alhaji ƙaryarka ta ƙare, sai na nuna maka ba a taɓa Hasina a zauna lafiya, don ko kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha. Ja da ni tamkar ka yi kashi gonar fara ne, ka san kuwa zata rama.”

Mintsinar da Kulu ta mata, ita ta dawo da ita hayyacinta.

Kallon bokan ta yi ta ce “To boka yaron fa?”

Dariya sosai ya bushe da ita, can kuma ya gimtse kamar bai taɓa dariya ba, ya ce; “Maganar yaron nan ki bar ta, asiri baya tasiri a kansa sosai, sai dai yanzun nan zan miki aikin da zai mantar da shi kowa nasa, kuma zamu saka tsanar gida a ransa, ta yanda ba zai waiwayo ba, ke ko labarin jihar nan ba zai kuma son ji ba bale ya dawo.”

Murna ce ta gama kashe Hasina.

Wani ɗan kasko ya janyo mai kama da tukunya na ƙasa, wanda ya kusan cika da wasu ruwan asiri, ya ajiye shi a gabansa.

Wasu surkulle ya karanta sannan ya shafi saman ruwan da hannunsa, sai ga hoton taswirar Abdul ta bayyana a saman ruwan.

“Ku matso ku ga ni.”

Ba musu suka matsa ya nuna masu ruwan ya ce “Ko ba wannan ba ne yaron?”

Gyaɗa kai ta yi bata ma samu damar yin magana ba, ganin Abdul zaune cikin rana ƙwayam, yana sharar ƙwalla duk ya lalace a cikin kwana biyun nan.

“Madallah!” Ya faɗa sannan ya ciro wata tsabga dake kusa da shi, ya kuma karanta wasu surkulle sannan ya shauɗa tsabgar a kan hoton Abdul ɗin.

Take yaron ya yi wata uwar zabura daga zaunen da yake ya miƙe kamar zarararre…

Kallonsa su Kulu suka yi da alamun rashin fahimta.

Shi ko gogan ya taƙarƙare ya kwarara wata uwar dariya dake barazanar tsaga masu kunne.

Sai da ya yi mai isar sa sannan ya gimtse ya ce “Aiki ya kammala, wannan zaburar da kika ga ya yi ta tabbatar da cewa aikin ya tafi yanda ake so.”

Cike da tsananin murna Hasina ta zaro kuɗi daga jakarta masu ɗan dama ta ajiye masa, sannan suka miƙe suka bar cikin bukkar zuwa waje; inda har yanzu akwai layi na wasu ɓatattu daga cikin mutane dake jiran fitowar su.
Takawa suka yi har gun da Hasina ta faka mota suka shiga.

Sai kuma a lokacin ne ta duba agogon hannunta, zazzaro ido ta yi ganin agogon ya buga ƙarfe biyu da rabi na rana, ita da ta baro gida sha biyu da rabi, ga shi yanzu awar ta biyu a waje bata ma je asibitin ba.

Cikin hanzari ta ja motar ta nufi cikin gari, a nan ƙofar asibitin specialist sokoto ta sauke Kulu, tare da bata kuɗin napep ta ce ta ƙarasa gida, ita tana sauri ne, zata shiga asibitin a gurguje ta dubo shi ta juya, gudun kada asirinta ya tonu.

Ba musu Kulu ta sauka ta hau napep zuwa gida; da yake ita tana girmama duk wani aiki na mugunta da kuma kare kai daga zargi.

A gurguje Hasina ta dubo kawo Basiru, sannan ta juya zuwa gidanta, domin ta san Alhaji na nan bai fita ba.

Ko da ta isa gidan ta tarar da ‘yan sanda suna bincike, don haka cikinta ya ɗuri ruwa, fargaba ta kamata, kamar ta juya ta bar gidan ta ji, amma bata da mafita face ta tsaya ayi duk ya ce za’a yi; ta sani dai kushewar baɗi sai baɗi, mai rabon ganin baɗi kuwa sai ya kai, don haka ta shige cikin gidan kai tsaye.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

A ranar wuni na uku Abdul ne tafe a galabaice, ɗan idonsa ɗayan ma ya fara gani disishi, saboda yunwa da ta masa mugun illa, ga shi tun jiya yake cikin tsanani, ya yi-ya yi ƙwaƙwalwarsa ta tuna masa wani abu game da shi amma ta kasa.

Jin ƙafarsa ta yi tsami, yasa ya nemi guri ya kwanta, da yake yamma ta riga ta yi.

Ko banza ma ƙafar ba wani warkewa ta yi ba, kasancewar ba a jima da yin aikin ba wannan ƙaddarar ta farmasa, ga shi ya daina shan magani, wannan yasa ƙafar ta ruruce masa, ɗan taka ta da yake yi a da ma yanzu ya kasa..

Yana nan kwance yana sauraron ƙafarsa har barci ɓarawo ya ɗauke shi….

Wani bafatake ne ke gangarowa cikin jejin, yayin da ya baro ƙauyensu ya nufi birni mafi kusa don kasuwancinsa.

Ya ɗan yi nisa acikin tafiyarsa, ba abinda yake sai tunanin da kuma fatan ya isa kan babban titi da wuri yanda zai samu mota zuwa cikin garin da za shi.

Bai yi aune ba sai ji ya yi ya yi tuntuɓe da abu mai ɗan nauyi.

Dubawar da zai yi haka ya ga yaro kwance kamar yana barci.

Ɗan ja da baya ya yi yana faɗar “Auzubillahi minas-shaiɗanir-rajim!”

Lura da ya yi kamar yaron na neman taimako, ya sa ya matsa yana dudduba shi, a lokacin kuwa Abdul na kwance ne a ɓarin fuskarsa dake a shafe don haka mutumin bai gano komai ba.

Sai da ya birkito shi, da niyyar ya taɓa ya ji ko yana a raye? Sa’annan ya lura da halittar fuskarsa, duk da gun ya kwaso ƙasa sosai, hakan bai hana mutumin gane mummunar halittar yaron mai ban al’ajabi ba.

Ja da baya ya yi da ƙarfi ya na faɗar “Innahu min sulaimanu wa Innahu bismillahir-rahmanir rahiim!”

A dai-dai lokacin ne Abdul ya buɗe idonsa ƙwaya ɗaya ya kafe mutumin da ido, sai ƙifƙiftawa yake……

More comment more typing…..

In har bansamu comment mai yawa ba tabbas zaku ji hiru, sati ɗaya ba typing😒🤷🏻‍♀️

Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal.

Vote share and comment…

RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹

*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

22safar/10 October.
1442hjr/2020.

DEDICATED TO: YARAN ALBARKA;
AFFAN, ABDUL DA IKRAM BABYNA.

ALLAH YA RAYA KU CIKIN AMINCI KU TASO DA ƘAUNAR JUNA, YA SANYA KU CIKIN SHIRYAYYI MASU SHIRYARSUWA, MUCH LOVE YARAN ALBARKA🥰🥰 Mommynku na ɗago maku hannu🙋🏻‍♀️

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com+

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 25-26

Daƙyar mutumin ya tattaro duk jarumtarsa ya ce “Mutum ko aljan?”

Abdul na jin wannan tambayar da sauri ya ce “Mutum ne hwa.”
Don baya son mutumin ya tafi ya bar shi; don ko yau ce ranar farko da ya saka ran zai samu taimako daga wani, haka ita ce ranar farko da ya yi arba da wani mahaluƙi bayan ya riski kansa a jeji.

Cike da ƙarfin hali mutumin nan ya matso ga Abdul yana tambayarsa Wanene kai? Daga ina ka ke? Ina iyayenka ko ‘yan’uwanka? Me kake kwance a cikin wannan jejin kai kaɗai?”

A jere ya jerowa yaron tambayoyin.

Maimakon ya ba shi amsa, sai ya yunƙura ya miƙe zaune ya na faɗar “Dan Allah taimakamin da ruwa da abinci, yunwa nika ji ƙwarai.”

Mamakin mutumin ne ya ƙaru fiye da farko, ba tare da ya yi magana ba ya janyo salkar ruwan dake cikin kayansa, ya miƙa wa yaron.

Karɓa Abdul ɗin ya yi ya tada ita, bai ajiye ba sai da ya shinye ruwan tas, ka na ganin yanayin yanda yake shan ruwan zaka san an daɗe ba a haɗu ba.

Tausayinsa ne ya shiga ran bawan Allan nan, a take ya ji a ransa cewa zai taimaki wannan yaro, don ko da gani ka san ya na neman taimako.

Salkar Abdul ya ba shi ya na cewa “Na gode Baba, saura abinci.”

“Yaro yanzu bani da abinci a tare da ni, don ina cikin halin tafiya ne, amma ta shi mu je gidana ka ci.”

Jikin Abdul har mazari yake ya ɗauki sandunansa tare da miƙewa ya ce “Baba mu tahi.”

Girgiza kai kawai mutumin ya yi, ya shiga gaba Abdul na biye da shi a baya.

Ganin cewa in ya biyewa tafiyar yaron Lallai sai sun yi dare a hanya; kasancewar ƙauyen nasu da ɗan nisa, ya saka ya duƙa ya cewa Abdul “Hau bayana na goya ka.”

Ba musu yaron ya haye dama ya gaji, sanin ba shi da wanda zai kokawa damuwarsa ne ya saka ya dangana.

Tafiya mai nisa suka yi sannan suka isa ƙauyen, lokacin har an kira sallar magriba, don haka mutumin ya ja Abdul suka je masallaci…

Bayan idar da sallar ne suka ƙarasa gidansa.

“Assalamu alaikum.” Mutumin ya yi sallama a ƙofar gida.

Daga ciki wata mace ta amsa “Wa’alaikumus salam, Muryar waye na ke ji kamar mai gida?”

“Ni ne kande.” Ya bada amsa a lokacin da yake shiga cikin gidan Abdul kuwa na biye da shi a baya kamar jela.

STORY CONTINUES BELOW
Ita ma Kande lokacin ta matso tana cewa “Mai gida lafiya kuwa ka dawo, kai da ka fita fatauci.”

“Wani muhimmin al’amari ne ya dawo da ni, yanzu dai kawo mana abinci.”

Ba musu ta juya, ta nufi madafa ta ɗebo  tuwon dawa da miyar kuɓewa a samira ta kawo ta ajiye masa, a lokacin har ya shimfiɗa tabarmar kaba a ƙasa, a ƙofar ɗakinsa ya zaunar da Abdul.

Ruwa ta je ta ɗebo sannan ta dawo ta zauna ta na faɗar “Mai gida wannan yaron fa daga ina?”

Domin ita sai a lokacin ta lura da yaron da ke zaune tare da shi; kuma duk da cewa duhu ya sauka ba ta gani sosai, amma ta san ba ɗaya daga cikin yaranta ba ne.

Zama ta yi gefen tabarmar cikin alamun mamaki ta ce “Mai gida wannan yaron daga ina?”

Murmushi ya yi ya ce “Wani bawan Allah ne a hanya na tsinto shi, shi ne dalilin dawowa ta gida don na ajiye shi a nan na juya.”

Kallonsa ta yi a ɗage, bata ce komai ba, Allah ya sa ma a duhu ne bai lura ba.

Abdul da ya wanke hannunsa zai fara loma ya ce “Mama ina yini?”

Ba dan ta so ba, ta karɓa da ƙalau don ta na shakkar mai gidan nata.

Abdul kuwa ya shiga zuba loma, hannu baka hannu ƙwarya haka yake cin abincin, da ka gani ka san yunwa ta masa kamun kazar kuku.

Sai a lokacin Kande ta haska fitila ta na faɗar “Bari na haska na ga yaron.”

Torch light ɗin da ke hannunta ta haska tare da saita fuskar Abdul ta dalla masa ita da gayyah.

Abin da ta gani ne ya saka ta zabura ta yi zumɓur ta miƙe tsaye tare da ja da baya, ta na faɗar “Na shiga uku, yau na ga abin da ya fi ƙarfina, mai gida ina ka samo wannan dodon?”

Inda sabo Abdul ya saba da wannan sunan da mutane ke masa, don haka ko kallon ta bai yi ba ya ci gaba da zuba loma; don ko ya daɗe bai haɗu da lafiyayyen abinci irin wannan ba.

Ɗaki ta shige jikinta na kakkarwa don ta tsorata ainun, jikinta sai ɓari yake.

Bukar ya miƙe tare da kallon Abdul ya ce “Yarona ci gaba da cin abincinka ina zuwa ka ji?”

Bai jira amsar yaron ba ya bi matarsa Kande zuwa ɗakin don ya fahimtar da ita.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Isarta falon ke da wuya ta zauna kan kujera kusa da Alhaji tana faɗar “Alhaji ka gane ni sai yanzu ko? wallahi…..” Domin yi ta yi kamar bata san da wanzuwar ‘yan sandan a falo ba.

Kallonta Alhaji ya yi, maimakon ya tamka ta a waccan maganar sai ya ce “Hasina ga jami’ai sun zo bincike kan ɓacewar yaronmu.”

“Yaronka dai.” Ta faɗa a ranta.
A fili kuwa yaƙe ta yi haɗe da kallon ‘yan sandan ta ce “Sannunku da zuwa.”

Babba daga cikinsu ne ya kalle ta ya ce “Yawwa Hajjiya, zamu miki wasu ‘yan tambayoyi idan babu damuwa.”

Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi; wanda da Alhaji ya ajiye hankalinsa tabbas zai jiyo ƙarar bugawarsa.

“Ina jin ku.” Ta faɗa a ɗan sanyaye, alamun damuwa sun bayyana ƙarara a fuskarta.

Ɗan sandan ya ce “Yawwa! Tambayar farko da zan miki ita ce “Me ya hwaru yinin  ranar da anka sace Abdul?”

“Iya kat sani na dai babu abinda ya hwaru da shi a ranar; don lahiya lau mun ka ci abinci dare, kuma da kaina nit rakke shi har ɗakinai, sai da nig-ga ya kwanta nit hito.” Hasina ta faɗa.

“Ok.” Ya faɗa, ɗayan ɗan sandan dake gefen shi ya rubuta.

Sannan ogan ya ci gaba “Ma’aikatan gidanga sun shaida muna cewar; a daren ranar kowanensu kwana mai nauyi yat kama shi, kamar waɗanda suka sha ƙwayar barci. Haka kuma sun shaida muna a washegarin ranar ke ce mutum ta farko da kinka lura yaron bai gidan, kuma ke kinka shelanta cewa ya tsere ne daga gidan, shin ya anka yi kissan yaron tserewa yay-yi ba sace shi anka yi ba?”

Wata mummunar faɗuwar gaba ce ta ziyarce ta, har sai da ‘yan hanjinta suka murɗa tsabar tsoro.

Ita sai a lokacin ma ta lura ashe falon cike yake da duk ilahirin mazauna gidan tun daga kan mai gadi har mai shara kowa na nan, hakan yasa ta ƙara burkicewa.

Nan fa zufa ya fara tattartsowa a kowace kafar ga shi dake jikinta, dama ance mara gaskiya ko cikin ruwa ya yi jiɓi.

Inda-inda ta fara yi “Am dama…. Dama na ta shi ne na je ɗakin yaron don Duba lahiya tai, sai nigga wayam bai nan, nan fa nit ruɗe nit shiga kiran ma’aikatan gidan don su tanyan biɗa tai….”

Ta na kaiwa nan ta dakata, ɗan sandan ya ce “Uhmm! Ina jin ki, ya an ka yi kissan tserewa yayyi ba sace shi anka yi ba? Kuma mi anka yi mi shi da har zai sa ya tsere daggidan Ubanai da yaka mugun so? Yaron da adda tawaya ga ƙafa, taya ya iya tserewa ba wanda yajji ko sautin sandunanai yayin da yaka tserewar?”

Waɗannan tambayoyi ya kuma watso mata.

Hasina fa ta ruɗe iya ruɗewa, don kuwa ko da wasa bata yi tunanin za’a iya zuwa wannan matakin ba, da ta tanadi kalamai don wannan ranar ; ga shi ita ba gwanar tsara abu kai tsaye ba ce sai ta ga wuya.

Ganin asirinta ya na gaf da tonuwa ga kuma Alhaji da ya kafe ta da ido tun lokacin da ta fara amsa tambayoyin, ya saka ta miƙe ta na faɗar “Don Allah ku min uzuri in shiga ciki in hito, kun ga yanzu niddawo ina da ɗan uzuri.”

Ogan ya ga rashin gaskiya ƙarara a idonta, don haka ya dakatar da ita da cewa “Hajjiya da ke taimaka ke ba mu amsa sai ki shigewakki, mu ma ta shi za mu yi.”

Bata saurari ɗan sandan ba, ta wuce da sauri zuwa cikin ɗakinta, ƙirjinta na lugude.

Ta sani muddin ta bari Alhaji ya gano tana da sa hannu a wannan al’amari tabbas kashinta ya bushe; don ko a kan Abdul zai iya komai ciki kuwa har da sakinta; ga shi ita ko bata gama cika burinta ba a zaman gidan.
Ganin ta shige ya saka jami’an suka miƙe su na faɗar “To Alhaji mu zamu tahi, sai mun dawo.”

Ogan ya juya ga ma’aikatan dake zaune gun shiru kamar ruwa ya ci su, ya ce “Kuna iya tahiya, amma ku sani kowane lokaci mu na iya dawowa, don ko ba za mu taɓa barin case ɗinga ba, har sai mun gano mai laifin,  an hukunta shi.”

Alhaji Munir dake zaune gun ya yi tsit, kamar ba ya nan tun shigowar Hasina sai a lokacin ya miƙe ya na cewa ” To officer Nagode sosai, sai kun zagayo.”

Su ma godiyar haɗin kan da aka ba su suka yi, sannan suka fice daga gidan cike da zargin Hasina don ganin yanda ta rikice, tabbas ruwa baya tsami banza.

Bayan ficewar su ma’aikatan suka watse kowa ya koma bakin aikinsa, Baba Direba ya koma kan bencinsu ya zauna, sai fara’a yake, tabbas addu’arsa ta fara karɓuwa, don ga shi alamun rashin gaskiya sun fara bayyana ga Uwargidan ta su, Lallai ko ba ita ce da laifin duka ba, to ta na da masaniya ko sa hannu a cikin wannan aika-aikar.

Dama tun lokacin da aka sace Abdul ya duƙufa da addu’ar Allah ya tonawa koma waye asiri, sannan ya kare Abdul a duk inda yake idan ya na raye; don ko ya shaƙu matuƙa da yaron, shiyasa ya fi duk ma’aikatan gidan damuwa da ɓatan yaron.

Alhaji kuwa bayan ficewar su komawa ya yi ya zauna, ya na mamakin yanda ya ga matarsa ta rikice,  haƙiƙa idan ba kuskuren fahimta ya yi ba, ya ga kamar hankalinta ya tashi matuƙa, duk wata alamar rashin gaskiya ta tabbata a gare ta.

“To me hakan ke nufi? Ta na da saka hannu a ɓacewar yaronsa?”

Zuciyarsa ta bijiro masa da tambayoyin, nan take hankalinsa ya tashi, sai kuma ya shiga girgiza kai yana ƙaryata zuciyarsa.

A bayyane ya ke faɗar “Ina ba zai yiwu ba! Matata ta na da amana, ba za ta taɓa iya cin amanata ba.”

Ganin wannan ba mafita ba ne ya yanke shawarar bin ta cikin ɗakin, don tabbatar da zarginsa ba gaskiya ba ne…..

More comment more typing……..
Na ji shiru zaku ji shiru…

Idan na ga guntun sharhi zaku ga guntun page next😹😹

Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal

RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹

*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

26safar/14 October.
1442hjr/2020.

DEDICATED TO: ALZAZ GROUP🥰🥰

Mutanena wannan page naku ne, ku ji daɗin ku dashi🥰🥰

So da ƙauna mara iyaka, ina ƙaunar ku fisabilillahi🥰🥰

Da fatan Allah ya ƙara haɗe kanku.

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
+
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 27-28

A cikin ɗakin ya same ta ya shiga watsa mata tambayoyi cike da tuhuma.

Sosai antar cikinta ta kaɗa, daƙyar ta samu dabarar fitar da kanta, a ranta ta ce “Cab! Lallai ya zama dole a gare ni na yi gaggawar amfani da maganin nan da boka ya ban tun kan tusa ta ƙurewa bodari.”

Ta yi iya bakin ƙoƙarinta a wurin ranar domin ta samu Alhaji ya yi wanka da ruwan maganin, amma abin ya ci tura, don kuwa cewa ya yi shi ba wani wanka da zai sake yi yanzu, a kan dole ta haƙura domin ba ta so ta takura shi har ya ɗago jirginta.

Sai dai ta saka mi shi ɗayan maganin a abincin dare ya ci, hakan ya saka ta tsananin murna, tare da fatar ta samu irin wannan nasarar a gobe.

¥¥¥¥¥¥

A can gidan Bukar kowa bayan ya bi matarsa ɗaki ya shiga lallaɓata a kan ta daure ta riƙe masa yaron nan, faɗar yake “Kande ki yi haƙuri ki riƙe yaron nan amana, shi ɗa na kowa ne idan kika taimaki wannan watarana Allah zai kawo wanda zai taimaki ƴaƴanki a lokacin da suka yi nisa dake.”

“Habah! Mai gida ka gane mana ni bance bana son riƙe shi ba, halittarsa nake tsoro, da ace gurgu ne kawai ko kuma wani lafiyayyen yaro ka tsinto da zan fika farinciki ma, amma ni dai gaskiya tsoron wannan dodon nake.” Ta mayar masa da amsa.

“Haƙuri zaki yi Kande Allah ya kan jarabci bayinsa ta ko wacce fuska don ya gwada imaninsu, shima wannan ai *HALITTAR ALLAH NE* haka Allah ya tsara halittarsa, ba shi ya yi kansa ba, meye laifinsa don ya zama nakasasshe? Hallau ma bamu san meya rabo shi da gidan iyayensa ba, barinsa cikin jeji shi kaɗai hatsari ne sosai shiyasa na kawo maki shi, kin san ‘yan magana sun ce ka taimaki na ƙasa gare ka sai Allah ya taimake ka.”

Ɗagowa ta yi ta kalle shi a ɗage ta ce “Mai gida gaskiya ni ba zan iya riƙon wannan dodon ba, haka kurum ya tsorata ni cikin da…..”

Kafin ta ƙara sa ya tari numfashinta da tsawa “Dakata Kande! Bar ganin ina lallaɓaki ki ce zaki zo min da raini, yanzu sai inci mutuncinki, yaro kuma dolenki ki riƙe shi umurni ne ba shawara ba, gobe-goben nan zan juya idan ya zo in na tafi ki yanka shi.”

Ya na gama faɗa ya fice a kufule ya koma gun Abdul.

Ita ko Kande tun lokacin da ya daka mata tsawa jikinta ya hau rawa tamkar mazari, ta tsorata ainun, don ta san halin mai gidan nata da fushi, idan abin ya motsa masa  kowa sai ya ji ajikinsa.

STORY CONTINUES BELOW
Cikin hanzari ta bi shi waje tana ba shi haƙuri.

Lokacin kuwa tuni ya iso gun Abdul da ya gama cin abincin ya sha ruwa, sai dai da alama bai ƙoshi ba, don kuwa sai rarraba ido yake, ko bai faɗa ba ka san ƙari yake so.

Bukar ya kalle shi ya ce “Abdul baka ƙoshi ba koh?”
Da yake tun a hanya yaron ya gaya mai sunansa.

Gyaɗa kai sama ya yi alamar “Eh.”

Bukar ya ɗauki kwanon tare da miƙewa zai je madafa don ƙarowa yaron abinci.

A dai-dai lokacin Kande ta fito, cikin ɓarin baki ta ce “Mai gida kawo na ɗebo masa.”

Ko kallonta Bukar bai yi ba ya wuce abinsa, don kuwa ta mugun ɓata masa rai.

Sai da ya kuma cikowa yaron kwano da abinci ya kawo masa.

Miƙawa Abdul kwanon da yake ya yi dai-dai da shigowar yara maza guda biyu a gidan.

Ɗayan ba zai wuce sa’ar Abdul ba, ɗayan kuma zai kai shekara sha huɗu.

Kai tsaye suka nufo gun Babansu suna faɗar “Sannu da dawowa Baba, ashe baka tafi fa?.”

Wani mummunan kallo ya aika masu, sai dai abinda ya yi shi ake kira aikin banza harara a duhu, don kuwa ba su ma lura da yanayin fuskar tasa ba saboda duhu, sai ji suka yi ya ce “Eh, da kun ɗauka na tafi, shiyasa kuka fita yawon shashanci a gari? Ashe haka kuke idan bana nan koh?”

Sanin halin Baban  nasu yasa suka shiga inda-inda daga ƙarshe Basiru ya yi wuf, ya ce ashe baƙo muka yi?”

Domin sai a lokacin ya lura da yaron dake cin abinci, saurin waigawa Badaru ya yi don ya ga baƙon da ya ji ƙaninsa ya faɗa.

Cikin sake fuska Baban ya ce “Na samo maka aboki ne Basiru.”

Daɗi sosai yaron ya ji ya tafi da gudu gun Abdul ya rungume shi ya na jin daɗi, har ya na faɗar “Yau shimfiɗa ɗaya zamu kwana.”

Baya da sanannen ciki a kan yanda halittar Abdul ɗin take.

Bayan Abdul ya gama cin abincin, Bukar ya tasa shi gaba da tambayar garinsu, ‘yan’uwansa da dalilin zaman shi a jeji.

Nan fa Abdul ya saka masu kuka, don kuwa ya yi-ya yi
Ƙwaƙwalwarsa ta tuna masa wani abu game da shi ya kasa, shi dai ya san yana da iyaye amma ya manta komai game da su, sunansa ne kawai bai manta ba, don haka ya ce “Baba na mance komi, ni ban ma san kowa anni ba.”

Shiru ya yi alamar tunani, can ya ce “Na san dai ina da Uwaye, amma dai na mance komi.”

Haka Bukar ya yi iya ƙoƙarinsa ya sa Abdul ya tuna wani abu ya gaya masa, amma abin ya ci tura, a kan dole ya bar zancen, don ba ya son tursasawa yaron, ya ƙudurce a ransa idan ya dawo daga fatauci zai sake tambayarsa, ya san zuwa lokacin yaron ya sake sosai.

Daƙyar Kande ta shawo kan mijin nata, ta nuna masa ta amince ta kuwa gane kuskurenta, amma a ranta faɗar ta ke “Ba dai gobe zaka tafi ba? Kana tafiya zan kora ɗan banzan dodon nan, waya sani ma ko aljani ka kwaso mana, garin kwashe-kwashenka? Haka kawai ka ɗebo mana ƙamaya-maya? Ai ba zai yiwu ba.”
Tun da asuba kowa na gidan ya tashi, Bukar ya ja yaransa maza zuwa masallaci, da yake shi mutum ne mai riƙon addini dai-dai gwargwado.

Har zuwa lokacin su Badaru ba su ankara da fuskar Abdul ba, kasancewar har lokacin da duhu.

Sai bayan sun dawo ne da haske ya fito suka gan shi, nan fa hankalin Badaru ya tashi, Kande ma ta ƙara ruɗewa, ashe munin halittar yaron nan yafi yanda take tunani, duhu ne ya saka bata gani sosai ba.

Shi kam Basiru bai wani damu ba duk da cewa a farko ya ɗan tsorata kaɗan, amma da yake shi yaro ne ƙarami, sai bai damu da hakan ba, shi murna ma yake ya samu aboki, ga shi daga daren jiya zuwa yau har ya ɗan saba da Abdul ɗin.

Da hantsi Bukar ya tara iyalan gidansa ya basu amanar yaro Abdul, tare da jaddadawa Kande ta yi haƙuri ta riƙe masa amanar yaron Kafin ya dawo ya maida shi gidansu, sannan ya tafi.

¥¥¥¥¥

A ɓangaren su Alhaji Bilya kuwa, sun baza koma sai neman yaro Abdul suke ta ko ina, sun baza yaransu don su nemo masu shi.

Ga kuma dukiyar ƙanin nasu da suka shiga ragarza-gaza don kawai sun san sun asirce shi baya iya masu magana.

¥¥¥¥¥¥¥

Da misalin ƙarfe tara na safe Hajiya Hasina ce a banɗaki ta na haɗawa Alhaji ruwan wanka; Abunda bata saba yi ba.

Amma da yake ta san abinda take son ƙullawa ne jikinta ke ɓari gun aikin.

Haɗa mi shi ruwan ta yi, sannan ta ɗauko maganin ta barbaɗa kaɗan yanda ba zai sauyawa ruwan kala ba, sannan ta fito ta na kwarkwasa kamar wata kilaki.

Gefe gado ta same shi zaune, ta matso ta na cewa “Alhajina ruwanka sun zama ready, wanka ɗai yarrage ma.”

Miƙewa ya yi jiki ba kuzari ya ce “Na gode matar albarka, bari na fito.”

Ya nufi ban ɗakin ya na takawa a hankali kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki, da ganin yanayinsa ka san ya na cikin matsananciyar damuwa, don ko duk ya rame ya yi baƙi, ɓatan tilon ɗansa ya taɓa shi matuƙa, ta yanda da har abinci baya iya ci sosai, baya da wata sauran nutsuwa, farinciki ya ƙaura daga gare shi.

Bayan shigewarsa, Hasina ta zauna gefen gadon tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, a ranta take faɗar “Munir ƙaryarka ta ƙare! ka na gama wannan wankan ka zama ƙarƙashin ikona sai yanda na yi da kai, ni ko na maka alƙawarin zan juya ka kamar waina a tanda, yanzu lokaci ne da zan ɗau fansar marina da ka yi a kan dodon ɗanka.”

More comment more typing…….
Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal

RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

28safar/16 October.
1442hjr/2020

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
+
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 29-30
Tana nan zaune ta kafe, ƙofar da ido sai zuba wani shu’umin murmushi take har zuwa lokacin da ta ji ya turo ƙofar banɗakin, Alamun ya gama zai fito.

Ƙara gyara zamanta tayi tare da faɗaɗa murmushinta ta ce “yawwa! Abu ya yi daɗi an bawa mayya jiran gawa.”

A hankali ta furta maganar.

“Mi kika cewa ne matar albarka?” Ya faɗa yayin da yake takowa zuwa gunta.

“Ah! Babu komi Alhajina, hat ka gama wankan?”

“Eh.” ya ce a taƙaice.

Daɗi ne ya lulluɓeta, sai kuma wata zuciyar ta ce mata “Idan zubar da ruwan ya yi fa?”

Dam! Ta ji ƙirjinta ya buga.

Kallonsa ta yi ta ce “Am! Alhaji nit ce da ruwan da nit zuba ma kayyi wanka ko?” Ta tambaya cike da zullumi.

“A’a tusshesu niyyi…”

Da ƙarfi ta miƙe tsaye tana zazzaro ido waje “Tussuwa hwa Alhaji? Kamar wani ƙaramin yaro?” Ta faɗa.

Yanda yanayinta ya canza kai tsaye ya matuƙar ba shi mamaki da dariya, duk da baya jin zai iya dariya yanzu, sai dai ya ɗan murmusa; kasancewar tun da ya fara wankan yake jin wani sabon yanayi ga ƙai-ƙaiyi da yake ji ajikinsa, hakan yasa bayan ya gama wanka da ruwan, ya ɗebi wasu tsabtataccin ruwa ya ɗauraye jikinsa, ko ya daina jin ƙaiƙayin.

Sai da ya wuce gaban madubi ya tsaya sannan ya ce “Wasa ni kai miki, ina ni ina tussa ruwan da yau aka fara haɗa min?”

Wata uwar ajiyar zuciya ta saki har sai da ya juyo ya kalle ta, kamar zai tambaye ta kuma ya share.

Murmushin mugunta ta yi ta ce “Ina zuwa Alhaji.”

Da Gama faɗa ta fice daga ɗakin zuwa na Abdul da ba kowa a ciki yanzu, ta rufe ta hau ɓaɓɓaka dariya tana cewa “Na kama babban kihi, Munir ka dawo ƙarƙashin ikona yanzu muddin ruwan maganin sun bushe ga jikinka.”

Wata mahaukaciyar dariya ta kuma bushewa da ita, wacce da akwai mutane a kusa da falon tabbas da sun jiyo ta.

Kulu ta kira ta shaida mata ta gama aiki sannan ta ɗora da cewa “Gobe ki taho gidana da sahe kahin ya hita, ki ga ikon Allah.”

Sun yi nisa a wayar ta tuna da Alhaji yana shiryawa a ɗaki.

A hanzarce ta kashe wayar ta fito zuwa ɗakin.
STORY CONTINUES BELOW
¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

A can gidan Bukar kuwa, bayan tafiyarsa rayuwar Abdul na tsakanin yanayi biyu, farinciki da damuwa.

Don kuwa tun bayan tafiyar tasa, Kande ta saka Abdul a gaba da hantara, muzguna wa kala-kala ba wacce bata masa.

Basiru ko idan ya ga Abdul na kuka sai ya zauna ya taya shi, yana matuƙar son Abdul, shi kaɗai ne ke nawa Abdul farinciki a gidan sai Zaliha babbar yar Kande (mai shekaru 16) da take tsananin tausayin yaron tun bayan da ta dawo gidan ta same shi.

Kande ta sha ƙudurin ta kori Abdul daga gidan, sai dai tana tsoron kada mai gidan ya shammace ta ya juyo da wuri, shiyasa ta ɗaga ƙafa zuwa wani lokacin.

Yau ma kamar kullum, tun da asuba Kande ta tashi, ta nufi tulunta da ya yi sanyi raɗau, ta tsiyayo ruwa cike da babban kofin silver ta nufo ɗakin da yaran ke kwana.

Haska fitila ta yi, ta tashi yaranta “Badaru! Basiru! ku tashi zuwa Sallah, ko ɗan kun ga Babanku baya nan ne? Wai ba zaku tashi ba?”

Haka ta yi ta faɗa ta na daddaɓarsu har zuwa lokacin da suka tashi suna mitsittsika ido, kowannensu ya fita waje don yin Alwala ba tare da sun tamkata ba.

Da ta tabbatar sun fita ta juya zuwa inda Abdul ke kwance, cike da ƙeta ta kwarara masa ruwan sanyi nan a jiki.

Firgigit ya farka da ƙarfi ya zabura kamar zai miƙe sai kuma ya dawo zaune ba shiri, don jin yanda ƙafarsa ke raɗaɗi.

A take ya hau rarraba idonsa yana ƙyafƙyaftawa, don neman wanda ya masa wannan aikin.

A gabansa ya ganta tsaye ta na ƙyalƙyala dariya, can kuma ta tsuƙe fuska kamar bata taɓa dariya ba ta ce “Kai kuma ɗan iska nakasasshe me kake jira, duk sauran yara sun tashi zuwa Sallah amma kai kana kwance?”

Hannu ya kai ya janyo sandunansa, sai sake ajiyar zuciya yake, don kwata-kwata jikinsa baya son sanyi sosai, ga shi an yi ruwa a daren jiya don ko damana ta fara.

Miƙewa ya yi ya nufi ƙofar fita, dai-dai lokacin Basiru ya shigo ɗakin don canza kayan jikinsa.

Haska fitila ya yi ya ga Abdul a jiƙe, ga kuma Mamarsu riƙe da kofin ruwa.

Ya fashe da kuka tare da rungume Abdul yana cewa “Ka yi haƙuri Abdul, muje ka canza kaya.”

“Ba wasu kayan da zai sauya a haka zai je masallaci, ko Kanada wasu kaya a gidan nan ne?” Ta ƙarashe zancen da tambayar Abdul.

Gyaɗa kai alamar a’a.

Ta ce “To ɓace mun da gani Dodon banza.”

Basiru ya ja hannunsa zuwa gun bakon kayansa, ya ciro wasu yana faɗar “Yi maza ka saka mu je, ka ji an kira sallah.”

Har hannunsa na ɓari gun karɓa domin tuni ya fara makyarkyata.

“Kai Basiru! dan ubanka baka ji me nace ba?”
Kande ta faɗa cikin ƙaraji.

“Habah Inna! Don Allah ki bar shi ya canza baki ga yana jin sanyi ba?”

Harara ta wurgawa ɗan nata ta ce “Ya mutu mana, ina ruwanka?”

Matsawa ta yi ta ƙwace kayan a hannun Abdul tare da zuba mishi ranƙwashi a kai.

Ai ko Basiru ya fashe da kuka, cikin kukan yake cewa “Wallahi Mama ko ki ba shi kayan nan ya saka, ko Baba na dawowa gidan nan in gaya mai duk abinda kikewa Abdul.”

Ganin ta yi shiru kuma bata bayar ba ya ce “Kin dai san halin Baba da masifa, har dukanki zai iya yi a kan haka.”

Jikinta ne ya yi laƙwas da jin zancen yaron, ba shiri ta watsawa Abdul kayan ta fice daga ɗakin tana zancen zuci.

Ɗaukowa Basiru ya yi, ya miƙawa Abdul ya saka suka fice zuwa masallaci don ko tuni Badaru ɗan baƙin hali ya bar gidan.

¥¥¥¥¥¥¥
Da hantsi Badaru da Basiru suka je gona don taya manoma aikin gyaran gona, kamar kullum.

Abdul shi kaɗai zaune a tsakar gidan abun duniya duk ya dame shi, ga yunwa ta fara kama shi, amma ya san ko giyar wake ya sha ba zai cewa Mama Kande ta sammasa abinci ba.

Hannu biyu ya saka ƙarƙashin haɓarsa ya zuba tagumi sai tunani ya ke, haƙiƙa gidan ya kasance masa tamkar inuwar bagaruwa ga sanyi ga ƙaya.

“Assalamu alaikum.” Ya jiyo sallama a ƙofar gidan.

Amsawa ya yi daƙyar.
Zaliha ce ta shigo gidan hannunta rungume da ƙwarya, da alama ta dawo daga niƙa ne.

Ganin yanayin shi ya saka ta ajiye ƙwaryar ta nufe shi, a gabansa ta durƙusa, ta ɗora hannunta a kafaɗarsa “Abdul meke damunka?”

“Yunwa nika ji yaya Zaliha.” Ya faɗa idonsa na kawo ƙwalla.

Girgiza kai ta yi cikin tausayawa ta ce “Share hawayenka bari na kawo maka abinci.”

Da hanzari ta je madafa ta sako masa ɗumamen tuwon masara da miyar kuka ta zo ta miƙa masa tana faɗar “Ga shi daina kukan, ai nan gidanku ne ba zamu….”

Bata ƙarasa ba don jiyo Muryar Kande daga nesa tana faɗar “Sannu mai gida!”

Zaliha bata ce komai ba sai miƙewa tsaye da ta yi, don ta na shakkar Maman tasu.

“Uban wa ya ce ki bawa wannan dodon Abincina?”

“Yi haƙuri Mama, na ga yana jin yunwa ne, kuma shi amana ne a gurinmu idan muka….”

“Rufe mun baki ja’ira!”  Kande ta daka mata tsawa.

Ta ci gaba da cewa “Lallai wuyanki ya isa yanka Zaliha! ni kike gayawa wai shi amana ne a gurinmu? To sai dai a gunki amma ba ni ba, kuma ki sani abincinki kika ba shi, don Wallahi ba za ki ɗibi wani ba.”

Tana gama faɗa ta juya ta koma cikin ɗakin rai a ɓace; dama ta na tsaye ne a ƙofar ɗakin….

More comment more typing…….
Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal
Vote, share & comment.

RUKY I LAWAL🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*+

3Rabi’ul awwal/20 October.
1442hjr/2020.

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

PAGE 31-32
Zaliha kasa motsi ta yi tsabar mamaki, “wai meyasa Mama bata son yaron nan ne? Ko ta manta cewa shi ma iyaye ne suka haife shi? Har yanzu fa bata san ko ɗan waye ba amma take wulaƙanta shi, mai yiwuwa ma ɗan wani hamshaƙin mai kuɗi ne.”

“Yaya Zaliha!” Abdul  ya katse mata zancen zucin da take.

Juyowa ta yi tana faɗar “Na’am ƙanina Abdul, ya aka yi ne?”

“Ga abincin ni na ƙoshi ki canye sauran.” Ya faɗa.

Murmushi sosai ta yi, a ranta ta ce “Ka ga yaro mai hankali, Allah ne kaɗai ya san irin baiwar da ya yiwa wannan bawa nasa.”

A zahiri kuwa cewa ta yi “A’a ƙanina ka ƙara ci dai, karka damu da ni, a ƙoshe nake.”

Ta faɗa mishi haka ne don ta kwantar masa da hankali ya ci abincin sosai, amma zahirin gaskiya tana jin yunwa sosai, sai dai ta sani zata fi shi samun abinci cikin sauƙi duk sanda ta buƙata.

Bai musa ba ya saka abincin a gaba ya cinye, da yake dama bai ƙoshi ba, sanin halin Mama ne ya sashi faɗar haka.

Sai da ya cinye shi tas, sannan Zaliha ta ɗebo masa ruwa ya sha.

Ɗakin Mama ta je ta ƙara bata haƙuri sannan ta gaya mata zata je gidan su ƙawarta Rabiba.

Da Zaliha ta san me fitar ta zata janyo, tabbas da ta gwammace ta kwana da yunwa a kan ta fitan.
Fitar ta ke da wuya Kande ta fito ƙofar ɗakinta ta tsaya ta na ƙare wa Abdul kallo, ta ma rasa me zata masa ta fashe ƙurjinsa da take da, kwatsam sai dabara ta faɗo mata.

“Tabbas wannan kyakkyawar dama ce a gare ni tunda gidan ba kowa.” Ta faɗa a ɗan bayyane.

Bata tsaya wani dogon nazari ba, ta hau waige-waige da ta tabbatarwa kanta ba kowa kawai sai ta nufi Abdul gadan-gadan.

Finciko hannunsa ta yi da ƙarfi tana faɗar “Hatsabibin yaro kawai, maza ka ɗauki wannan ƙarafan naka yanzun nan za ka bar gidan nan.”

Abdul na kuka wiwi yana rokonta ta bari Basiru ya dawo su yi sallama, amma da yake an ce wanda ya yi nisa baya jin kira, sai bata sauraresa ba.

Haka ta tasa ƙeyarsa gaba tabi ta ƙofar baya suka fice daga gidan tana ingizar ƙeyarsa.

Ganin baya sauri ya saka ta duƙa ta goya shi don ko bata son ɗaya daga cikin yaranta ya dawo gida ya samu bata nan, gudun kada su zarge ta.

Tafiya take tana zabga sauri, duk wanda suka haɗu a hanya ya tambaye ta lafiya a’ina ta samu yaro, ina za su? Sai ta ce abokin Basiru ne gurgu ne ya kawo masa ziyara shi ne zata mai dashi ƙauyensu.

STORY CONTINUES BELOW
Sai da ta yi nisa da ƙauyensu sosai, don har ta fara fita karkarar(da yake ƙauyen nasu ƙaramin ƙauye ne sosai) sannan ta ajiye shi, tare da masa gargaɗi sosai.

Kunnensa ta kama ta murɗe ta ce “Ka na jina ai ko?”

Gyaɗa kai ya yi alamar Eh.

“Ko da wasa kada ka sake na ga nakasasshin ƙafafun nan naka a gidana, idan ka sake ka dawo aradu sai na ƙona ka da wuta, na tsani ganin wannan mummunar halittar taka.”

Shi dai Abdul banda kuka ba abinda yake, abubuwa sun taru sun caɓe masa.
Duk wannan masifar da ta masa bata ishe ta ba, tsabar mugunta ta saka hannu biyu ta tura shi ya faɗi baya da ƙarfi a kan wani dutse mai tsini, har sai da bayansa ya fitar da jini.

Wata mahaukaciyar dariya Kande ta bushe da ita ta juya cike da annashuwa ta fara tafiya.

“Don Allah Mama ki temake ni kamat yadda Allah ya temake ki! dan Allah ki koma da ni gidanki na miki alƙawarin ba ni sake cin abincin gidanki zan tahi in yi bara a maƙwafta, ni dai ki banni in zauna tare da abokina Basiru, Wallahi in yaddawo bannan zai shiga damuwa.”

Duk wannan uwar magiyar da yake zubawa bai saka Kande ta ji tausayinsa ba, sai ma haushinsa da ya ƙaru a ranta, a haka ta wuce abinta ta bar sa nan yashe yana faman magiya.

¥¥¥¥¥¥¥

A can Sokoto kuwa, sai yamma liƙis Alhaji Munir ya dawo gidansa.

Ya dawo a gajiye sosai, don haka bai ko zauna falo ba kamar yanda ya al’adanta, kawai sai ya wuce uwar ɗakansa ya watsa ruwa sannan ya kwanta.

Hasina ta na ɗakinta don haka ba ta san ma ya dawo ba, sai wuraren ƙarfe shidda na yamma ta fito daga ɗakin.

Kai tsaye ta nufi ɗakin Alhajin sanin har yanzu bai dawo ba da ta gan shi a falo ko kuma a ɗakinta.
Ta na shiga bata zame ko’ina ba sai gurin walldrop ɗinsa, sannu a hankali ta buɗe ta ba tare da fargabar komai ba ta janyo akwatin sirrinsa (inda yake ɓoye duk wasu takardu ko wani abu nasa mai muhimmanci) ta ajiye shi a ƙasa sannan ta fara kiciniyar buɗewa.

Alhajin dake lafe a kan gado ya rufa da blanket tsabar gajiya, tun shigowarta ɗakin yake binta da kallo, da fari har zai mata magana sai ya ga ta nufi walldrop, wata zuciyar ta ce masa “Bari ka ga me zata yi?”

Don haka ya ƙara lafewa tare da daina motsi, ikon Allah sai kallo kawai sai ya ga ta ɗauko akwatin sirrinsa, nan fa ya cika da mamaki matuƙa, shi dai a iya saninsa ba wanda ya san da wannan ajiyar tasa, bai taɓa tunanin hankalin Hasina zai kai kan wannan akwatin ba.

“Tafɗijam! Dole na canza gurin ɓoyo.”

Ya faɗa a ransa.

Ita ko Madam Hasina shagalin gabanta take bata ma san da wanzuwar mutum a ɗakin ba.

Daƙyar ta samu ta buɗe akwatin, wani shu’umin murmushi ta yi ta ce “Alhamdulillah!”

Nan fa ta shiga fitar da takardun kadarorinsa ɗaya bayan ɗaya tana dubawa har ta je kan takardar wata makekiyar Gona da ya mallaka a ƙauyen Tangaza.

Faɗaɗa murmushinta ta yi ta ware takardar gefe sannan ta tattare saura ta mayar kamar yanda suke ta rufe akwatin tare da maida shi muhallinsa kamar dai ba wanda ya taɓa gun.

Shi dai Alhaji sai kallon ikon Allah ya ke, zuciyarsa na masa saƙe-saƙe a kan matar tasa, hakan na nufin sata take masa kenan? Ita ce mai satar masa kuɗaɗe idan ya ajiye dama?”

Bai taɓa tsammanin haka daga gare ta ba.

Kallonta kawai yake har ta duƙa ta ɗauki takardar ta saka a bayanta, ta nufi hanyar fita tana faɗar “Yanzu komai ya yi dai-dai….”

“Hasina!” Ta jiyo muryarsa daga bayanta kamar saukar Aradu.

A kiɗime ta juyo don tabbatar da abinda kunnuwanta suka jiyo mata.

Ƙafafunta ne suka kasa ɗaukar ta tsabar kiɗimewa, ganin shi zaune kan gado a bayanta ba ƙaramin razana ta ya yi ba,hakan ya saka ta zauna daɓas a gun.

Ƙoƙari take ta tuna lokacin da ya shigo ɗakin, sai dai a iya hangenta da tunaninta bata tuna lokacin da ta ga shigowarsa ba, hasalima ƙofar a rufe take tun shigowarta har yanzu.
¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
Tashin hankali!

A can ƙauye bayan komawar Kande gida bata tarar da kowa ba, hakan ba ƙaramin daɗi ya mata, don haka ta shige cikin ɗakinta tana faɗar “Kai har na ji sakayau wallahi! Yau dai na rabu da wannan dodon.”

Muryar Abdul ɗin ta jiyo daga waje yana faɗar “Mama ai ba mu rabu ba gani nan na biyo ki.”

A kufule ta yo waje tana ƙunduma ashar “Kutuma! Amma yaron nan ka raina ni, bance karka sake ka biyo ni b……”

Sauran maganar ce ta maƙale a maƙogwaronta lokacin da ta fito wajen bukkar.

Ba komai ne ya hana ta ƙarasawa ba, face ganin yara da yawa masu siffar Abdul ɗin sun cika gidan taf, ko’ina ka waiga sune tufafin jikinsu iri ɗaya dana Abdul ɗin, ba dai bambanci sak shi ɗin.

Cike da tsananin tashin hankali Kande ta faɗa ɗakin  haɗe da faɗawa kan gadon ƙarfenta tana ɓoye fuskarta, jikinta sai kakkarwa yake.

Ba shakka yaron nan aljani ne, yau ta jangwalowa kanta abinda yafi ƙarfinta.

Daga waje ta ji Abdul ɗin yana nufo ɗakin bai kuma daina kiran sunanta ba ya na kuka.

“Mama Kande ki taimaka min na zauna tare da ke a gidanki.” Muryar na fita bibbiyu cikin sautin kuka.

Ƙara ɗungulewa ta yi guri ɗaya kamar an cura ta a gun sai kakkarwa take, ta ma kasa yin addu’a…

Can ta ɗan ji shiru ba sautin yaro Abdul hakan ya saka ta ɗago kanta a hankali.

Ba shiri ta kuma sunne kanta ƙasa saboda ganin Abdul ɗin zaune kan ɗaya gadonta ya na baɓɓaka dariya, ga kuma sautin waɗancan yaran na farko daga waje suna kiranta da neman ta taimaka masu…..

Hmmmm!🤔🤔🤔

To fah readers! Me Kande ta jangwalowa kanta? Da alama fa ta faɗa trkon jinnu.

Miye alaƙar waɗannan aljanun da Abdul da suka zo a siffarsa?

Shin ya Hasina zata ƙare a gaban Alhaji?

Wohoho! Ku dai ku tara da ni a page na gaba don jin ya zata kaya.

Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal

RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

6Rabiul awwal/23 October.
1442hjr/2020.

DEDICATED TO: Nana, mom Islam,mom Khalil, da sauran masoyan wannan book.+

Ina miƙo gaisu ga members na HALITTAR ALLAH CE FANS GROUP

Haƙika ina jin daɗin ƙaunar da kuke nunawa book ɗin nan ina yinku over.

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

PAGE 33-34

Kande ta shiga ruɗani da rikicewar ƙwaƙwalwa, ba abinda take sai wasi-wasi.

Ita dai tas an ta baro Abdul a jejin farkon gari, kuma yaron gurgu ne saboda haka ko da ace biyo ta yayi tabbas bai isa zuwa nan ba, ajiye wannan maganar a gefe, idan ma shi ne ya akayi ya kasu kashi-kashi? Wannan sai dai aikin aljannu.

Ƙwaƙwalwarta ce ta tsaya cak daga tunanin da take, a firgice ta ɗago.

Ihu ta zunduma don ganin yaro Abdul ya zama zabgege, ya cika ɗakin gaba ɗaya, bata ma iya hango kansa, saboda tsawonsa har kan ya fita ta saman rufin ɗakin, iya cinyoyinsa da sandunansa kawai kake iya gani a cikin ɗakin, sauran gangar jikin tana saman rufin.

Nan take nadamar jefar da yaron nan ta shige ta, tabbas da ta samu hanyar ficewa daga ɗakin ba abinda zai hana ta koma ta ɗauko Abdul ta dawo da shi.

Wohoho! Firgici idan ya amsa sunansa firgici ya kansa ma’abocinsa ya ƙeƙashi ido ya zama jarumin dole.

Irin wannan yanayin ne ya faru da Kande, har bata san lokacin da ta buɗi baki cikin tsawa ba ta ce “Wai wannan wane irin iskanci ne! Me kuke so da ni ne? Idan kashe ni zaka yi ka kashe ni Kawai na huta, ina dalilin wannan…..”

Kau! Kau!! Kau!!! Ta ji saukar kyawawan maruka guda uku a jejjere, wanda ko wane mari ɗaya yake a matsayin marin sadaukin jarumi guda uku.

Saukar marukan a kuncinta ke da wuya, haƙoranta biyu na gaba suka yi fitar burgu ɗaga bakinta, sai jini ke fesowa daga bakin.

Take ganinta ya ɗauke har na tsawon daƙiƙu goma, tama kasa tantance a wace duniyar take.

Wata buɗaɗɗiyar murya ce ta karaɗe ilahirin gidan inda ake faɗar “Ke Azzaluma! Ki sani yau ƙaryarki ta ƙare,  me wancan ɗan talikin ya yi miki kika tsane shi? Shin laifinsa ne don ya zo duniya a cikin irin wannan siffar? Ubangijin dake sarrafa kowa da komai shi ya halicce shi a haka, me yasa ke baki da imani ne?”

Kande dai ba baki sai kunne, don ko iya muryar kawai take ji, kan dake maganar yana wajen rufin.

Duk da cewa mutanen karkara basu cika tsoron aljanu ba, amma dai a yau Kande ta tsure iya tsurewa, saura kaɗan ta saki fitsari don tsoro.

Wata kakkausar murya ce ta ci gaba da cewa “Ba kowane mutum ba ne ake wulaƙantawa don an gan shi kamar a banza, da kin san ko wanene yaron nan da irin arziƙin mahaifinsa, tabbas da ba ki yi gigin ɗora ƙazamin hannunki a kan shi ba, bare har ki dinga dukansa.”

Cikin dakiya Kande ta ɗago kai ta ce “To don Allah wanene kai? Meye alaƙarka da Abdul? A Iya tsawon mako biyun da muka yi tare da shi a nan bansan shi da matsalar jinnu ba…”

Wata iriyar dariya aljanin ya bushe da ita, mara daɗi sauraro, sannan ya ɓace ɓat, amma bata daina jin dariyar ba.

Ai da gani ya ɓace ta runtuma da gudu zuwa wace ta na ihu duk ta fice daga hayyacinta.

Kamar daga sama ta ji wata Muryar ƙananun yara na faɗar “Ba ki kai matsayin da zaki yi min wannan tambayar ba mutuniyar banza! Amma zan baki amsa a haɗuwarmu ta gaba.”

Daga haka ta ji ɗif, dama gudu take, ta na zuwa ƙofar fita daga gidan, suka yi kaura da Zaliha da ke shigowa a hanzarce, har sai da Zalihan ta baje a ƙasa, saboda ƙarfin bankar da Mamanta ta mata.

“Wai Mama lafiyarki? Tun daga maƙota nake jiyo ihunki.” Zaliha ta faɗa ta na ƙoƙarin miƙewa tsaye.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Abdul kuwa, da ya tabbatar Kande ba zata taimake shi ba, hasalima ta tafi ta bar shi, kawai sai ya miƙe ya juya yana kuka, ya nausa cikin jejin dake mararraba da karkarar.

A haka ya ci gaba da tafiya kamar yanda ya yi a baya, ba abinci ba ruwa ba wani mataimaki.

Ga shi Damana ta kawo kai, tunda har an fara ruwa haka Abdul ya ci gaba, duk iska da ruwan da ake a kansa suke ƙarewa saboda rashin mafaka, wani lokacin idan ana sheƙa ruwan sama sai ya samu guri ya takure tare da haɗa kai da gwuiwa ya na kukan maraici.

Idan an gama ruwan ya miƙe ya ci gaba da tafiya, wasu lokutan talalaɓiya ta ja shi ya faɗi ƙasa, duk jikinsa ya kukkuje.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
A can Sokoto Kuwa, Hajiya Hasina ce  zane a ƙasa duk ta daburce, ta kasa furta ko da harafin A ne.

Alhajin ya sauko daga kan gadon ya zo gabanta ya tsaya yana cewa “Hajjiya mi zaki yi da takardun gonata?”

“Am dama…dama, na ce dama.” Sai kuma ta yi shiru tare da duƙar da kanta ƙasa.

“Dama me?” Ya jefo mata tambaya.

Gabanta ya yanke ya faɗi, can kuma ta tuna cewa ai ta magance shi, don haka ta ɗago kai cike da gadara da yaƙinin aikinta ya yi ta ce “Dama ina so ne in duba in akwai yiwuwar a saishe ta sai a sesuwa.”

Shiru ya yi tsabar mamaki, baki a sake yake kallonta.

Ita kuwa ganin bai ce komai ba ta sakankance a ranta maganin ya ci, don haka, ta miƙe haɗe da  juyawa cike da tsiwa ta na rausaya ta wuce ɗakinta cikin nishaɗi……

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Lamarinsu Alhaji Bilya kuwa, abin ya ta’azzara don kuwa tuni sun baza yaransu a ƙauyukkan garin da kewaye, kusan sati Uku kenan amma har yanzu shiru kamar an shuka dusa.

Wannan lamarin ya fusata yayyen alhajin sosai, don haka suka sauke fushinsu a kan dukiyarsa.

Ganin abinda suke aikatawa ya yi yawa ya saka Mizbahu ya same su watarana da dare, suna tsaka da shawararsu ya shigo masu, yana cewa “Yan uwana ina mai muku wasiyya da ku ji tsoron Allah mahaliccinku, ku sani makirci, tuggu ko hassada ba za su kai ku ko’ina ba, face su jefa ku a tafkin nadama da danasani mara amfani, haƙiƙa duk wanda ya hau motar kwaɗayi ba inda za ta sauke shi sai tashar wulaƙanci.”

A fusace yaya Sunusi ya wanke shi da mari, kamar ya samu ƙaramin yaro.

Bilya kuwa ya miƙe yana faɗar “Da kyau! Ka burge ni Sunusi, na lura yaron ga yanzu ganin ya kai dai-dai yake damu, saboda ya yi aure kamar yadda munka yi, haka yahi mu kuɗɗi yaka ji shiyasa ya ga damar hwaɗa muna magana.”

Mizbahu dai murmushi kawai ya yi ya juya ya na faɗar “Ita gaskiya guda ta daga ƙin ta kuma sai ɓata, haka kuma ɗan hakkin da ka raina, shike tsokale maka ido, Allah ya shirye ku.”
Yana gama faɗa ya sa kai ya wuce zuwa gidansa, saboda ba a taɓa ci masa zarafi irin na yau ba, haƙiƙa da ba yayansa ba ne, ko wanene ya mare shi a yau sai ya gani.

*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*+

9Rabiul awwal/26 October.
1442hjr/2020.

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 35-36

Alhaji Munir kuwa tsabar mamaki ko zama ya kasa yi, a gun da ta bar shi tsaye a nan yake har  zuwa wani lokaci mai tsawo.

Ranar dai bai kuma tamka mata a kan maganar ba, jira yake ya ga iya gudun ruwanta, yana so ya tabbatar da zarginsa, shin ta haukace ne ko kuwa raini ne ya cika mata ciki?

Isar ta ɗakinta ke da wuya, ta zauna kan gado tana mai da numfashi, haƙiƙa daga farko ta tsorata ainun, shiyasa har yanzu ƙirjinta ya ke harbawa kaɗan-kaɗan.

Bayan ta gama sai ta nutsuwarta ta kira Kulu a karo na biyu, ta labarta mata abun da ya faru.

Buɗar bakin Kulu sai cewa ta yi “Ai bokan nau aikinai kamar yankan yuƙa na, dama tun da yacce miki haka, indai ke yi aiki da maganin yadda ya kamata ina tabbatar miki da cewa sai ke yi duk yadda kika so da Alhaji, ke ko cewa kiyyi ya kwanta ki taka shi da ƙahwa, wallahi sai ya kwanta.”

“Ke habah! Da gaske mutuniyata?.” Hasina ta faɗa
“Kina wasa da boka Bakuza, ni na san aikinai kuma ina jin daɗin aikinai sosai, ke dai Allah ya kashe ya baki.”

Dukkansu suka bushe da dariyar keta sai ƙyaƙyatawa suke, haka dai suka ci gaba da hirarsu kafin daga bisani suka sauka a layi, da alƙawarin cewa gobe tun safe Kulu zata zo.

Haka kuwa a ka yi, washegari Tun ƙarfe takwas na safe, Napep ta sauke Kulu a ƙofar gidan.

Mai gadi ya sha mamakin ganin ta tun da sassafe haka, amma sanin cewa ƙawar hajiya ce yasa bai yi yunƙurin hana ta shiga gidan ba, buɗe mata ƙofar ya yi, kai tsaye ta shige zuwa ciki.

Tun a harabar gidan ta kira Hasina a waya ta shaida mata.

Hasinar da kanta ta zo ta shigar da ita ciki.

A falo suka zauna, Hajiya ta ƙwalawa Ladi kira “Ladi! Ladi!! Ke Ladi!!!”

Kafin ta gama rufe bakinta sai ga Ladi ta shigo da sauri tana faɗar “Gani Hajjiya.”

“Yawwa Ladi kawo ma Abbukiyata abincin kari ke ji.” Hasina ta faɗa.

Cikin girmamawa ta miƙe ta juya zuwa ɗakin girkin don cika umarnin uwar gida.

Ba jimawa ta dawo da tiren abinci ta dire a gaban baƙuwar, ta juya tana mamakin wannan ziyarar haka.

Bayan Kulu ta ci ta yi nak, Hasina ta ce “To ina ga yanzu ke yi ƙwarinda zaki iya kallon dramar da kyau, bari in kira shi.”

Miƙewa ta yi zuwa ciki, jimawa kaɗan sai ga su sun fito a tare tana gaba yana biye.

Dinning Area ya nufa kai tsaye, don ko bai ma san da zaman wata baƙuwa a gun ba, ko da Hasina ta shiga ciki bata gaya masa ba,cewa kawai ta yi ya fito su karya.

STORY CONTINUES BELOW
Sai bayan ya zauna ya fara cin abincin sannan ya lura da wanzuwar Kulu a kan kujerar da yake fuskanta.

“Alhaji ina kwana.” Kulu ta faɗa tana sunne kai saboda kwarjinin da ya mata.

“Lahiya lau.” Ya amsa, sannan ya maida kallonsa ga Hasina da alamar mamaki a fuskarsa.

“Abukkiyata ta Kulu ai kasanta.” Hasina ta faɗa.

Shi dai bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da cin abincinsa har zuwa lokacin da ya kammala.

Miƙewa ya yi da zimmar shiga ɗaki, dama tuni Hasina ta gama cin abincin ta dawo kan kujera kusa da ƙawarta ta zauna.

“Alhaji taho nan ka zauna.” Ta faɗa cikin bada umurni.

Juyowa ya yi ya kalle ta, sosai ya ke mamakin sauyawar hajiyar daga jiya zuwa yau, amma bai musa mata ba ya je ya zauna kusa da ita, a tunaninsa ko akwai abinda take son gaya masa ne.

Murmushi ta jefe shi da shi tana kallon Kulu ta wutsiyar ido.

“Gani Hajjiya mi halam?” Ya tambaya.

“babu komi kiranka ɗai niyyi.”
“Ko da yake danna min ƙahwahuna, yau na tashi suna min ciwo.” Cike da izza take maganar, wai ita a dole ta asirce shi.

Wani shegen kallo ya watsa mata, wanda ya saka ta shiga ruɗani gami da al’ajabi.

Amma duk da haka bata karaya ba, ta kalle shi a ɗage ta ce “Ka danna min ƙahwahuna nicce, mi kat tsaya kallo?”

Kulu dai na daga gefe tana kallon show sai ƙunshe dariya take, ba abinda take jira sai ta ga yanda alhaji sai durƙusa yana matsar ƙafa.

Shi ko Alhajin ɗaga mata hannu yayi cikin tsawa ya ce “Ya ishe ki haka Hasina! Wai mi ka damunki ne? tsakanin jiya da yau na kasa gane miki, sai hauka kikai iri-iri, in ke samu taɓin ƙwaƙwalwa na ki hwaɗamin in kai ki asibiti ya hi ki tsaya kina karanta min shirme.”

Har ya juya zai tafi kuma ya ci birki yana cewa “Kuma daga yau sai yau, kakki ƙara yimin maganar banza irin wagga ko da gani sai ke, balle gaban wata ƙazamar mata, sannan ki tabbatar ke maisammin takardar gona ta kahin dare, in ba haka ba…..”
Bai samu damar ƙarasawa ba tsabar taƙaici da ya turniƙe shi kawai sai ya wuce fuu! Zuwa cikin ɗaki.

Dukkansu suka saki baki sototo! Kamar garkar wawa, suka bi shi da kallo.

Kulu ta ci haushin kiranta Ƙazama da ya yi, don ko kalmar nan ta caki zuciyarta sosai.

Hasina ta sha kunya, ji ta yi tamkar ƙasa ta tsage ta shige ciki, wai ita zai ciwa zarafi a gaban macen dake ƙasa da ita? Ko da yaushe Kulu na girmamata da jin shakkarta amma yau Alhaji Munir ya zubar mata da mutunci da darajar ta, tabbas ba zata taɓa barin shi ya ci bulus ba, dole ta ɗauki mummunan mataki a kansa.

Hasina ta manta cewa shi ta so ta wulaƙanta sai reshe ya juye da mujiya.

Kulu ce ta katse mata tunanin da take ta hanyar faɗar “Hmm! Tofah! Meka  hwaruwa nan wurin ga? Ko dai ke yi kure wurin anhwani da maganin?”

Dogon numfashi ta ja ta sauke sannan ta ce “Tabbas akwai matsala, ni dai na san na bi komi bisa tsari, amma yanzu ki tahi gida zan binciki inda matsalat take.”

Kulu ta ɗauki jakarta ta fice daga gidan tana yiwa Hasina dariya a ranta ta ce “Yau fa rana ta ɓaci ga mata, su Hasina an shiga hannun kwalawa, ai na so ace ya zabga mata mari wallahi da na ci dariya, amma bakomai randa rana ta kuma ɓaci inda rabo na gani.”

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Ina labarin yaro Abdul?

Yaro Abdul dai ya nausa a cikin jeji sai tafiya yake, tun yana ƙirgen kwanaki idan ya ga dare ya yi gari ya waye ya ce ɗaya, gobe ya ce biyu, har a ka kai lokacin da lissafi ya ƙwace masa.

Zuwa lokacin shanyayyiyar ƙafarsa ta ɗage sosai, da ba don Albarkacin sandunan da yake tare da su ba, tabbas da ba zai iya matsawa ko daga nan zuwa can ba.

Tun yana damuwa tare da licin ciwukan dake jikinsa har ya daina damuwa dasu, ya yanke ƙauna, hawayensa ko tuni sun ƙafe, ya kuma fitar da rai ga samun mataimaka.

Ba abinda yake sai roƙon Allah a zuci da sarari domin ya kawo masa ɗauki.

Allah ma ji roƙon bawa.

A wata rana daga cikin ranaku a ka kwana a na tsala ruwan sama kama da bakin ƙwarya, Abdul bai samu mafaka ba, don haka a kansa ruwan suka ƙare.

Da safe ruwan ya tsaya cak kamar ba a yi ba, can zuwa rana tsaka rana ta ƙwalle sosai, tamkar ba jiyan nan aka tsala ruwa ba, ikon Allah kenan.

A daren ranar Abdul ya kwana da wani irin zazzaɓi mai zafi,  don haka ya kasa tashi ya ci gaba da tafiya yana nan kwance a’inda ya kwana, zuwa can da ya ji rana ta yi zafi sosai ya yunƙura daƙyar ya kwashi sandunansa ya ci gaba da gangarawa cikin jejin jikinsa sai kyarma yake.

Tun daga nesa yake jiyo busa mai daɗin gaske ta na kawowa kunnensa ziyara.

Cike da tsananin murna ya ci gaba da bin sautin busar ya na jin nishaɗi.

Ba komai ne ya saka shi farinciki ba, sai don tunanin cewa zai samu mataimaki, ko ba komai dai ya san zai samu abinda zai sakawa bakinsa idan mutumin dake tafe mai jinƙai ne.

Can bayan wasu daƙiƙu ya iso gun wata bishiya mai girma da inuwa sassanya, a ƙasan bishiyar ya hango mabushin zaune, sai dai bayan mutumin kawai yake iya gani, domin daga bayansa Abdul ɗin ya ɓullo.

Nan ya ci gaba da nufar mutumin da zimmar ya kewaya ta gabansa su haɗu.
Shi ko wannan mutumin jin motsi a bayansa ya saka shi miƙewa cikin hanzari tare da saita bindonsa da wani mulmullen dutsi mai ɗan girma, ya juyo a fusace ya na jiran ƙarasowar mai kawo harin…….
Hmmmm! Tofah! Shin mutuminan wanene shi? Me yake a jeji? Zai harbi Abdul kuwa?

Ba wannan ba, anyah zai taimaki yaro Abdul idan ya yi arba da halittarsa?🤔🤔🤔

Don jin ya zata kaya sai ku biyo NI a pages na gaba.
More comment more typing…..

Follow me on Wattpad @Ruky_I_Lawal.

Vote share and comment.

RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹
Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal.

RUKY I LAWAL🌹🌹🌹🌹🌹

*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

15Rabiul awwal/1 November.
1442hjr/2020.

Wannan page SADAUKARWA ne ga masoya wannan book ɗin, iya wuya ana jone🥰🥰

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*

PAGE 37-38

Ganin haka yasa antar Abdul kaɗawa, a take ya tsaya cak a gun, tare da runtse idonsa da ƙarfi, domin a tunaninsa ba abinda zai hana mutumin nan ya same shi a dai irin wannan saitin da ya yi.

Shi kuwa mutumin har yanzu bai sauke bindonsa ba, sannan bai yi yunƙurin matsowa kusa ba, domin halittar yaron ta saka shi al’ajabi, sai dai bai ji ko ɗigon tsoro ba, kasancewarsa maharfi da ya saba yawo a dazuka, ba irin abinda baya cin karo da shi a yayin da ya shiga jeji, don haka ganin wannan ma bai saka shi tsorata ba.

Jin shiru ya saka Abdul ya buɗe idonsa, ganin mutumin bai yi ko gezau ba, ya saka shi fara takawa don zuwa gun shi.

“Dakata yaro!.”

Maharbin ya faɗa cikin ɗaga murya.

Tsayawa ya yi cak a inda yake, kamar yanda aka umurce shi.

“Mutum ko aljan?”
Ya jefo masa tambaya.

“Mutum na.” Ya bada amsa.

“Yaro meke tafe da kai?”

Cikin raunanniyar murya ya ce “Taimako nika biɗa, ka temake ni, ba ni da lahiya kuma ina jin kishirwa da yunwa.”

Da ganin yanayinsa ka san yana jin jiki.

Sai a lokacin Maharbin ya mayar da bindonsa, sannan ya matso kusa da Abdul ɗin.

Hannunsa ya saka a jakar bayansa ya fito da shantalin ruwansa ya miƙa wa yaron ya sha, sa’annan ya ja shi zuwa gindin bishiyar da yake zaune, ya ɗauko ragowar gasasshiyar tsuntsuwar da ya ci ɗazu ya miƙa masa.

Da sauri ya ƙarba ya cinye, duk da naman ba yawa kuma bai masa maganin yunwa ba, amma ya toshe masa wata kafa, don kuwa ya ji damar yunwar da ta addabe shi.

Bayan ya yiwa yaron duk taimakon da ya kamata sai ya miƙe ya cigaba da zagayawa a jejin ko ya samu wani naman da zai kai gida.

Abdul ya bi bayan shi, har ya fara nisa a tafiyarsa ya ji motsin mutum a bayansa, juyowar da zai yi haka sai ya ga wannan yaron ne da ya taimaka ‘yan mintinan da suka wuce.

“Yaro lafiya dai?” Ya tambaya cike da mamaki.

“Babu komi, dama cewa niyyi zan bika mutahi.” Abdul ya faɗa cikin rawar murya.

“Ni fa ba na gane wannan Hausar taka, wai ina zaka bi ni?” Ya kuma tambayarsa.

“Ni ko ma ina na mu tahi ɗai.” Ya faɗa.

Zuwa lokacin Maharbin ya fara ƙuluwa, ga haushin rashin samun abun farauta tun safe da ya fito, ga shi baya gane Hausar yaron, saboda haka ya ce “Kai yaro saurare ni da kyau, na riga na maka taimakon da zan iya, ko kai aljani ne ya kamata ka bar ni haka.”

STORY CONTINUES BELOW
Ya na gama faɗa ya yi gaba abinsa, Abdul ya fashe da kuka ya kuma binsa a baya tamkar jela.

Da Maharbin nan ya ga abun ba na ƙare ba ne, sai ya tsaya ya yiwa Abdul gargaɗi da babbar murya tare da tsoratar da shi, a kan idan ya yarda ya biyo shi sai ya yanka shi ya kai namansa gida a madadin naman tsuntsaye.

Bisa ga tilas Abdul ya haƙura, ya yasu a gun ya na kuka, Maharbin kuma ya ci gaba da nausawa jeji ran shi wasai, yana neman abun farauta.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

A can gidan Alhaji Munir kuwa, hankalin Hajiya Hasina ya kai ƙoluluwar tashi da ta fahimci cewa maganinta bai ci ba, sai zarya take a falon ta na ƙoƙarin tuna inda ta yi kuskure a cikin aikin.

Ta yi iya yinta amma ta kasa gano inda matsalar take, haka ta ci gaba da zarya, ranta sai tuƙuƙi yake mata, ko ta halin ƙaƙa tana so ta nunawa Alhaji Munir cewa ruwa fa ba sa’an kwando ba ne.

Ta na cikin wannan halin Alhajin ya fito da shirin zuwa kasuwa, ya zo zai gifta ta gabanta ya wuce ta kira sunansa.
“Alhaji!”
Ko kallonta bai yi ba ya ci gaba da tafiya.

Har ya je ƙofa ya tsinto muryarta tana faɗar “A dawo lafiya mai gida.”

Wani uban tsaki ya ja ya fita, cike da ƙunar zuciya.

Haƙiƙa yana daf da kamuwa da ciwon zuciya, ga damuwar ɓatan tilon ɗansa, ga wannan matar da take so ta ƙara mishi damuwa a kan wadda yake ciki.

Haka ya bar gidan da kuntaccen kai.

Tafe yake a mota shi kaɗai ya na tunanin rayuwa, damuwa ce cunkushe a ƙasan ransa, har ya zama na cewa tuƙin kawai yake amma hankalinsa baya kan titin.

Ikon Allah ne kaɗai ya kai shi Marna police station, ya je don ganawa da officern da ke riƙe da case ɗin ɓatan Abdul.

Bayan sun gaisa officern yake tambayarsa, “Alhaji hay-yanzu dai shiru a ɓangarenku babu labarin komi? Ba wani wanda kaka zargi da aikata wanga laihin?”

Shiru ya yi kamar mai nazarin wani abu, can ya ɗago kai ya ce “A’a officer ba na zargin kowa, yanzu dai abinda nika so gare ku, don Allah ku ƙara tsaurara bincike wallahi ina cikin damuwa, ku yi ƙoƙari ku gano min maƙiyina da ya raba ni da tilon ɗana, ya sani cikin zullumi da tunanin halin da rayuwar ɗana za ta kasance a lokacin da ya nisanta da gida.”

Shiru ya yi na ɗan lokaci, yayin da ɗan sandan ke faɗar “Insha’allah! Alhaji zamu ƙara ƙoƙari akan wanda mu kai, da yardar Allah sai mun kama mai wannan laifin mun tabbatar da an yanke mai hukuncin da yaddace da shi.”

Nisawa Alhajin ya yi sannan ya ce “Ina ji a jikina cewa Abdul ya na cikin matsala, ko barcin kirki ba na iya yi, ina yawan mafarki da shi ya zo yana kiran ‘Abbu ka temake ni, ina cikin matsananciyar matsala’ shiyassa ka ga hankali yana kasa kwanciya Officer.”

“Dole hankalinka ya tashi Alhaji, ɓacewar ɗan mutum ba wasa ba na, yanzu dai ka koma insha’allah za mu zo nan gida domin akwai wadda muka zargi a cikin ahalin gidan.” Cewar ɗan sandan.

Zaro ido Alhaji ya yi ya ce “Wa kuke zargi?”
“Matarka Hajiya Hasina.” Ya ba shi amsa.

Ya so ya musa, amma shi kansa yanzu ya fara zargin ta don haka bai ce komai ba ya yiwa officern sallama ya ƙara gaba.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Hasina kuwa bayan fitar Alhaji ta kuma faɗawa dogon nazari, can ta yanke hukuncin cewa za ta ƙara amfani da maganin wankan, domin a nan kokontonta yake, don kuwa ba ko  shakka a gabanta ya ci abincin da ta sakawa maganin, wankan ne dai bai yi da kyau ba.

Da yamma bayan dawowar Alhaji gida Hasina ta same shi a ɗaki ta durƙusa a gabansa.
“Don Allah Alhaji ka yi hanƙuri ka yafe min, na tuba ban ƙarawa, kuma ma na mai samma takardun gonakka ka yi hanƙuri mijina.”

Banza ya mata kamar ta na yi da bangon ɗakin.

Ganin hakan yasa ta fashe da kukan makirci ta na ƙara roƙarsa.

“Don girman Allah Alhaji ka yi hanƙuri na tuba, ni kaina ban san mi ya hau kaina ba nit aikata abubuwan da niyyi, ka yahe min.”

Kuka take kashirɓan kamar gaske, a zahiri za ka rantse ta yi nadama, amma a cikin ranta ba haka ba ne, zuciyarta cike da son ganin ta mallake shi.

Sai a lokacin ya ɗago zuciyarsa cike da tausayinta, ya lallashe ta ka na ya yafe mata, tare da tabbatar mata da cewa komai ya wuce a gunsa.

Take a gun suka shirya suka dawo kamar da.

Ganin ta samu wannan nasarar ya saka ta shiga shirya yanda za ta yaudare shi ya yi wankan ruwan maganin.

Kashegari kamar waccan ranar, ta kuma zuba magani a ruwan wankansa, sa’annan ta tsaya a ƙofar banɗakin ta yanda za ta iya jiyo duk motsinsa.

Bai kawo komai a ransa ba ya shiga wankan, sai dai kamar waccen ranar, ƙaiƙayi ya ta so masa, da kamar zai ɗibi wasu ruwan ya wanke sai kuma ya tuna ya na sauri ne, da yake ba sosai yake jin ƙaiƙayin ba, kawai sai ya ɗora towel ɗinsa ya fito.

¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥

Wasa-wasa sai da Maharbin nan ya share sama da sa’o’i biyar amma ko tsuntsu ɗaya bai haɗu da shi ba, har ya sare ya cire rai ga samun wani naman.

Gwuiwoyi a sanyaye ya juya don komawa gida, sai dai ya na cike da zullumi da tunanin yanda zai tunkari iyalinsa hannu rabbana.

Har ya ci rabin tafiya, kamar daga sama ya ji an ce “Ka manta da yaron da ka wulaƙanta ɗazun nan, da dai ka koma gare shi wataƙil da ka dace.”

Nan fa ya hau waige-waige ya na neman mai maganar, amma bai ga kowa ba.

Sai a lokacin ya tuna da wancan yaron da suka haɗu, har ga Allah shi ya ma manta da rayuwar yaron shaf, sai yanzu da aka tuna masa….

RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹

*HALITTAR ALLAH CE*
👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*+

          *AND NOW*
*HALLITAR ALLAH CE*

21 Rabiul awwal/7 November, 2020.
1442hjr/2020.

DEDICATED TO: ANTY HAUWA (MAMAN USWAN)

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
PAGE 39-40

Cikin hanzari ya juya ya nufi inda suka haɗu da yaron ɗazu.

Sai da ya iso bakin bishiyar da suka zauna ɗazu, nan fa ya hau dube-dube ko’ina ya na neman yaron, amma bai gan shi ba sam, nan fa hankalinsa ya dugunzuma, ya bazama a cikin jejin yana neman yaron, sai da ya shafe tsawon lokaci ya na nemansa, amma ba amo ba labari.

Zuwa lokacin gajiya ta gama riskar dukkan gaɓɓan jikinsa, gun bishiyar ya dawo ya zauna don ya huta, sa’annan ya nufi gida.

¥¥¥™™™

Yaro Abdul kuwa, tun lokacin da ya fahimci cewa Maharbin nan ba zai  taimaka masa ba, kawai sai ya miƙe daga inda ya yasu, ya ci gaba da tafiya yana sharar ƙwalla, zuwa lokacin zazzaɓin dake jikinsa ya tsananta, amma saboda kafiya da ƙarfin hali irin na shi ya ci gaba da tafiya, cikinsa tamkar ba na shi ba saboda yunwa….

Komai rashin imanin mutum idan ya haɗu da Abdul a cikin wannan yanayin, tilas ya tausaya masa, saboda yanda ya ƙwarjame ya yi duhu sosai, dauɗa ta gama samun muhalli a jikinsa, tufafinsa kuwa har sun canza launi saboda datti.

Da yake lokacin da zai baro gidan Kande tufafin da ya baro gida dasu ne ajikinsa, tun barinsa gida sau ɗaya aka wanke su, lokacin da Basiru zai yi wanki ya haɗa dasu, nan ma ba don sun fita ba, tunda yaron bawai ya iya wankin ba ne sosai…

Wandon jins kalar blue black ne a jikinsa da riga light blue, amma wandon har ya fara dafewa saboda datti, rigar kuma ta fara zama brown.

Yau kusan kwana goma kenan rabonsa da gidan Kande.

Haka ya ci gaba da gangarawa, yana cikin tafiya kawai sai ya yi tuntuɓe da wata baƙar leda.

Cikin rawar jiki ya durƙusa tare da ajiye sandarsa, ya zauna.

Janyo ledar ya yi ya buɗe ta, sai ga lafiyayyar shinkafa da wake a ciki, dama ledar kusan a cike take.

Cikin tsananin murna mara misaltuwa Abdul ya ɗaga hannu sama ya ce, “Allah na gode ma.”

Nan da nan ya fara afa shinkafar nan, tamkar mayunwacin zakin da ya jima bai yi kalaci ba.

Duk da cewa baya da lafiya sai da ya cinye shinkafar tas sa’annan ya miƙe don neman ruwa.

Abun mamaki, sai ya ji rabin ciwon ya tafi, har wani irin ƙarfi ya ji ya zo masa.

A bayyane ya ce “Kai! Dama ashe yunwa ta nika ji, ita at rabin ciyon.” Hahaha, ya bushe da dariya shi kaɗai cike da nishaɗi ya matsa gaba.

Can zuwa rabin sa’a yana tafiya, idonsa ya sauka kan wata kwalba cike da ruwa, murmushi ya bayyana a fuskarsa, ya je ya ɗauko ta, ya buɗe ya kwankwaɗa sai da ya sha fiye da rabi sannan ya wanke hannunsa ya tafi da sauran.

Abinda Abdul bai sani ba shine, duk abin nan da ke faruwa aljani Barkuza ya na tare da shi, kuma shine asalin aljanin da ke tare da shi ya na gadinsa tun yana gida, shine ya ƙwace alewar hannun Abdul ya yar, lokacin da yaya Sunusi ya kawo masa alewa mai guba.

Haka a lokacin da su Gumush suka sace Abdul ya ɗan ɗaga zuwa wani guri, da ya dawo ya tarar ba yaron shi ne ya ba zama nemansa, har ya taddo inda yake.

Tun lokacin ya na tare da shi, har zamansa a gidan Kande, ya bar yaron ne ya ɗanɗana wahalar rayuwa, domin ya san zafi da ɗacin rashin iyaye da kuma wahalar nema saboda rayuwarsa ta gaba ta inganta.

Shi ne ya ajiyewa Abdul wannan shinkafar da ruwa da siyo a kasuwar wani ƙauye dake kusa da su, ya ajiye masa a fakaice yanda ba zai tsorata ba.

Shi kuwa Aljani Mazkud shi ne ya shiga jikin Abdul a kwanaki uku na farkon zamansa a jeji, haka zalika shi ne wanda ya je gidan Kande ya tsorata ta, shine kuma wanda ya bi Maharbi a baya ya tuna masa da yaro Abdul.

¥¥¥¥¥¥™™™™™™

A Sokoto kuwa, labari ya sha bam-bam da na baya, domin ko a cikin satin nan biyu abubuwa da dama sun faru marasa daɗi, domin kuwa Hasina ta yi nasarar mallake Alhaji Munir, yanzu fa sai abinda take so yake yi, bayan kwana uku da zuwansa station ‘yan sandan suka zo gida domin sake gudanar da bincike, buɗar bakin Alhaji sai cewa ya yi “Ku tahi ɗai ofisa ni ba ni da wani ɗa da ya ɓace don kuwa ban ma taɓa haihuwa ba, ga matata nan ku tanbaye ta.”

Ƙwalalo ido waje suka yi su duka, suka cika da tsananin mamaki, to miya ke damunsa? Shekaranjiyan nan fa ya je da buƙatar a tsananta bincike a kan ɗansa yanzu kuma ya ce baya da wani ɗa.

Ofisan ya shanye mamakinsa ya ce “Alhaji ko dai ka sha’afa ne? Nina hwa Asp Bello Yahaya, wanda case ɗin ɓacewar ɗanka Abdul yake hannuna.”

Alhaji Munir ya kalle shi a ɗage cikin wata irin murya ya ce “Na ce maka ni ban taɓa haihuwa ba… Hajjiya ko na taɓa haihuwa?” Ya ƙarashe zancen ya na kallon Hasina.

Cike da izza da isa ta ce “Har sai ka tambaya Munir? Ni ce dai matarka kuma ban haihu ba.”

Maida dubanta ta yi ga tawagar ‘yan sandan ta ce “Ofisa kuna iya tahiya mu ba mu da wani yaro da yat ɓace.”

Har ogansu zai buɗi baki ya yi magana, Hasina ta ɗaga mishi hannu cikin tsawa ta ce “Kuna hita ko sena jissat muku kwandon rashin mutunci?”

Kallon inda Alhaji ke tsaye suka yi, ya na nan a gun baya da niyyar motsawa bare ya yi yunƙurin dakatar da ita, tsaye kawai yake kamar wani soko.

Ganin hakan ya saka ta ce a ranta “Bari na nuna muku ƙarfin ikona.”

Kallon Alhaji ta yi cikin isa da bada umurni ta ce “Munir shiga cikin gida.”

Ba musu ya juya zuwa ciki, tamkar yaron da uwarsa ta masa umurni.

Nan take idon ogansu ya fara tara ƙwallar tausayi, “Tabbas ta na ƙasa tana dabo.” Ya faɗa a ransa tare da juyawa bai ce komai ba ya yi gaba, sauran tawagarsa suka bi sa a baya, yayinda Hasina ta raka su da harara…

RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹

*HALITTAR ALLAH CE*

👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

          *AND NOW*
   *HALITTAR ALLAH CE*

PAGE 41-42

Abdul kuwa ya cigaba da nausawa cikin jeji ba tare da gajiyawa ba, duk da cewa ita kanta sandar hannunsa ta ɗanɗana kuɗarta, don zuwa wannan ranar har rufin sandar na ƙasa ya guntule, duk ta moƙaɗe a wasu gurare, tsabar faɗi tashin da yake a cikin duwarwatsu.+

Ƙafarsa kuwa, tun yana damuwa da zogin da take masa, har ya zo ya daina damuwa, tuni ma ƙafar ta ɗage sama, saboda rashin kulawa.

A haka ya cigaba har bayan shuɗewar wasu kwanaki.
Watarana yana cikin tafiya ya hango alamar wani gari a gabansa.

Farinciki ne ya cika zuciyar Abdul, sai sauri yake zubawa cike da zumuɗin ganin ya isa garin.

Tafiya kawai yake bai yi aune ba sai ji ya yi ya yi tuntuɓe da wani murgujejen dutse, kansa ya bugu da dutsen, wata uwar hantsilawa ya yi, har sai da ya tsallake dutsen, ba shiri ya baje a ƙasa magashiyan, jini kuwa sai tsartuwa yake daga goshinsa.

Daga nan bai kuma sanin inda kansa yake ba.

**************

Wata tsaleliyar mota ce ke tafe, sai sharara gudu take tana nufo gun, da dukkan alama matuƙin motar yana sauri ne.

Saura kaɗan ya taka yaron,ba shiri ya taka burki yana sakin ajiyar zuciya da alama ya firgita.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un!” Shi ne kaɗai abinda mutumin ke maimaitawa.

Buɗe motar ya yi tare da fitowa ya yo kan yaron.

Hannu ya saka ya birkito shi da nufin ya taimaka masa.

Ba shiri ya janye hannunsa, don yin arba, da mummunar halittar yaron, ja da baya kaɗan ya yi, haƙiƙa ya kaɗu matuƙa da ganin wannan yaron.

A ransa ya ce “Ko dai aljani ne?” Ras! Ƙirjinsa ya buga, tsayawa ya yi jim, kafin ya maida dubansa ga yaron, ganin goshin yaron nata zubar da jini ya saka ya kai hannu ya ɗauki yaron bakinsa na furta duk addu’ar da ta zo mashi.

Ya yanke a ransa zai tafi da wannan yaron zuwa cikin gari don kai shi asibiti, ko da kuwa aljani ne, yasan Allah zai kare shi daga sharrinsa, don shi ya yi ne saboda Allah.

Motarsa ya nufa ya saka yaron a gidan baya, ba tare da ya lura da ƙafar yaron ba, bare har ya fahimci cewa gurgu ne ya nemo masa sandunansa.
Zagayawa ya yi ya shiga mazaunin direba, sannan ya ja motar da gudu ya ci gaba da tafiya cikin sauri, dama can a hanzarce yake, yanzu kuma ga yaron nan da yake ƙoƙarin ceto ransa.

A haka yata zuba gudu a hanya, har Allah yasa ya isa cikin garin Kano, kai tsaye asibiti ya nufa da yaron, dama can kafin ya ƙarasa asibitin ya kira wani abokinsa likita sanar mashi buƙatarsa, don haka bai sha wata wahala ba, yana zuwa aka karɓi yaron.

STORY CONTINUES BELOW
******™™™™™™™™™

Su kuwa su yaya Bilya yanzu duniya ta masu daɗi, sai cin karensu suke ba babbaka.

Mizbahu da a kullum yake cikin takaicin wannan hali na ‘yan uwansa, da kuma mamakin abinda ya sami Munir ya susuce haka, ya zubawa su yaya Bilya ido suna ɓarnatar masa da dukiya haka.

Da dai ya ga abun bana ƙare ba ne, ya shirya watarana bayan Magriba ya tarar da Alhaji Munir a gida, tunda yanzu gidan iyayensu da yake zuwa kullum ma ya daina, sai can ba a rasa ba zaka gan shi.

A harabar gidan ya tarar da Munir ɗin kan kujerar roba, ya yi shiru ya zuba tagumi kamar mai son tuna wani abu.

“Assalamu alaikum.” Ya faɗa.

Munir bai ko ɗago ba, da alama bai ma ji sallamar ba.

“Assalamu alaikum.” Mizbahu ya kuma faɗa, a lokacin da ya ƙarasa daf da Munir ɗin.

Nan ma bai ɗago ba, sai da ya dafa kafaɗarsa, sannan ya yi firgigit, kamar wanda ya dawo daga duniyar mummunan mafarki.

“Tunanin mina kaka yi  haka Munir?” Mizbahu ya faɗa.
Murmushi ya yi ya ce: “Sannu da zuwa yaya ashe har ka ƙaraso.”

Girgiza kai ya yi alamun tausayawa ƙanin nasa, sannan ya ɗauko ɗayar kujerar dake nesa kaɗan dasu, ya ajiye kusa da Munir ya zauna.

Kallon Ƙanin nasa ya yi ya ce; “Alhaji, nasan kana sane da irin ɓarnat da su yaya Bilya sukai da dukiyakka, shin mi yassa har yanzu baka ɗauki mataki ba?.”

“To ni kam yaya mi zan musu? Ai ‘yan uwana na, miye a ciki don sun ci dukiyata, tunda ba nida Magaji, ko na mutu suna dai at magadan.” Cewar Munir.

Da mamaki Mizbahu ke kallonsa, “Ba kada Magaji hwa nij-ji ka ce.” Ya faɗa.

Ɗaga mashi kai ya yi alamar tabbatarwa.

Nan fa mamakinsa ya ƙaru, tabbas ɗan uwansa na cikin wani hali, ko dai ɓatar ɗansa ce ta zautar dashi har haka?.

Shanye mamakinsa ya yi ya ce “In har baka da ɗa, shi kuma Abdul ɗin hwa, wa at Babanai?”

Da kallon mamaki Munir ya bi yayan nasa, sannan ya ce “Wa at Abdul kuma yaya? Ni hwa ban taɓa haihuwa ba ko ka mance?.”

Zuwa yanzu mamakin Mizbahu ya rikiɗe zuwa tsoron lamarin ƙanin nasa, tabbas akwai lauje a cikin naɗi, don kuwa ruwa baya tsami banza, amma ko miye ya yi alƙawarin bankaɗo shi, don kuwa shi ba waɗanda yake zargi sama da su yaya Sunusi, don haka bai ko tsaya sun ƙarasa maganar data kawo shi gidan ba, sanin hakan bai da amfani a yanzu, yasa ya miƙe tare da yiwa Ƙanin nasa sallama ya tafi.

*®®®©©©©©©©*
Bayan an shigar da Abdul ɗakin majinyata Mahmud ya wuce office ɗin likita Yasir abokinsa don tattauna matsalar.

Dr Yasir na zaune kan kujerarsa Mahmud ya shigo, su ka kuma gaisawa, sannan ya zauna kan kujerar dake fuskantar ta Yasir.

“Likita bokan Turai, ya aikin kuma?” Cewar Mahmud.

“Aiki gashi nan muna fama, Mutanen Kd yaushe a gari? Da alama ba don matsala ta kawo ka ba, ba zansan ka shigo garin bahar ka tafi.”

Dariya Mahmud ya yi ya ce “Ba haka bane, tafiyar ce ta gaggawa, nima wani Meeting ɗin gaggawa ne ya kawo ni nan garin, ƙarfe biyu za’a fara, ina son magriba ta riske ni a garin Kaduna, don kuwa a can ma ina da wata fita ta musamman bayan isha’i, kasan bana son saɓa alƙawari.”

Yasir ya yi ɗan murmushi da cewa “Hakane.”

“Amma wannan yaron fa, a’ina ka samo shi?”

Fuskarsa ta canza zuwa yanayin damuwa ya ce “Wallahi akan hanyata ta zuwa nan na tarar da shi kwance a tsakiyar wani titi mara hayaniya, saura kaɗan na taka shi, Allah ne ya kiyaye, da na ga yana neman agajin gaggawa yasa na kawo shi nan.”
“Da fatar dai ba wata babbar matsala.”

Yasir ya ce “Ba wata  babbar matsala bace, ya samu babban rauni a goshinsa, muna kan bincike dai ko zamu gano wata matsalar dabam.”

“Ohk, Ni bari na shiga gari na shirya don zuwa Meeting ɗin, kaga yanzu har ƙarfe ɗaya ta yi.” Mahmud ya faɗa tare da miƙewa, ya miƙa wa Yasir hannu suka kuma yin musabiha, sannan ya juya.

Har ya kai ƙofa, kamar wanda ya tuna wani abu ya waigo ya ce “Don Allah Abokina ka samarwa yaron nurses da zasu kula dashi ko da zai farka kafin na dawo.”
“Insha’allah, baka da matsala akan wannan.” Yasir ya faɗa.
Shiko ya juya ya fice daga office ɗin.
A cikin ɗakin majinyatan Abdul ne kwance kan gadon Asibiti, annaɗe mishi kai da bandage bayan an ɗinke gun.

A hankali ya buɗe idonsa dake kallon sama, sai ya ganshi kwance a guri mai rufi, nan fa ya fara tunani “To yanzu kuma me ya same ni?, Ina ne nan?”
Da sauri ya tashi zaune yana kuka.

Sister aysher ta yo kansa tana lallashinsa, har aka samu ya ɗan yi shiru.

®®®®®®®®

Shi kuwa Mahmud bashi ya dawo ba, sai wuraren ƙarfe biyar na yamma.

Koda ya dawo ya tarar Abdul ya tashi, don haka ya matsa kusa da yaron yana masa sannu.

“Sannu yaro, ya jikin?”
Nan fa Abdul ya shiga rarraba ido, sai a lokacin ya ji kansa ya masa nauyi, ko da ya shafa sai ya ji bandeji, nan fa ya saka sabon kuka…

Daƙyar da siɗin goshi Mahmud ya samu ya ciwo kan Abdul ya daina kukan.

Anan yake tambayarsa “Yaro ya sunanka?”
Ya ce “Sunana Abdul.”
“Ina ne garinku, sannan ina iyayenka? Ya kuma tambayarsa.

Nan fa ya yi shiru kamar mai son tuna wani abu, can kuma ya ce “Bansani ba, Ni dai nasan cikin daji nika rayuwata ni ɗai, tunda Mama Kande takkore ni daga gidanta.”

Zaro ido Mahmud ya yi, jin yaron ya ce a jeji yake rayuwarsa shi kaɗai, har ya buɗi baki zai ce wani abu, Yasir ya turo ƙofa ya shigo bakinsa ɗauke da sallama.

“Wa’alaikumus salam.” Sister aysher ta faɗa.

Shi kuma Abdul a dai-dai lokacin fitsari yake ji sosai, nan ya shiga dube-dube  ko ya ga sandunansa amma wayam, nan ya shiga damuwa, sai ƙara raba ido yake.

Sister Aysher ce ta lura da damuwar da yaron ya shiga, ta matso tana faɗar “Abdul me kake nema ne?”

Idanunsa suka cicciko da ƙwalla ya ce “Sandunana nika biɗa ban ga su ba.”

“Sanduna kuma?” Cewar Mahmud da mamaki a fuskarsa.

Abdul ya ce “Eh, hitsari nika ji, ina son in tai in yi amma ban ga sandunana da nika tahiya dasu ba.”

Duk da basa fahimtar Hausar yaron sosai, amma sun fahimci cewa da sandunan yake tafiya.

“Hakan na nufin yaron gurgu ne?” Mahmud ya faɗa a ransa.

Advertisements

Dr Yasir ya matsa kusa yana duba ƙafafun yaron, nan fa ya shiga damuwa, ya juyo kan Mahmud ya ce “Yaron nan fa gurgu ne, da dukkan alamu ƙafar tasa bata samun kyakkyawar kulawa, saboda yanda ta fara lalacewa, yana da buƙatar kyakkyawar kulawa cikin gaggawa.”

“Hmmm!” Mahmud ya sauke ajiyar zuciya tare da faɗar “Gashi ina sauri yanzu nake so na wuce Kaduna ya za’ayi kenan?”

Suna cikin maganar sister aysher ta goya Abdul a bayanta, ta kai shi banɗaki ya yi fitsari.

****

Yasir ya ce “Idan ba damuwa kabar shi anan, ni zan san yanda za’a yi, zan kuma sama masa sabbin sanduna, in yaso daga baya ka dawo ayi maganar….

RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹🌹🌹

*HALITTAR ALLAH CE*

👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

          *AND NOW*
   *HALITTAR ALLAH CE*

*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
PAGE 43-44

Ajiyar zuciya Mahmud ya sauke, sannan ya janyo ledar hannunsa ya miƙa wa sister aysher abincin da ya siyowa yaron ya ce “Mun manta anata zance,ki bashi abincin nan ya ci yanzu.”

Juyawa ya yi ga Dr Yasir ya ce “Mu je office ɗinka sai mu ƙarasa tattaunawa a can.”+

A tare suka fice daga ɗakin, suka bar sister aysher tana bawa Abdul abinci.

Bayan isar su office ɗin, Dr Yasir ya zauna kan kujerarsa, shi kuwa Mahmud tsabar damuwa ko zama bai samu yi ba ya ce “Ina jinka Dr yanzu me kake ganin za’a yi akan matsalar yaron nan.”

“Kamar dai yanda na faɗa maka daga farko, a ganina kabar shi anan mu zamu cigaba da kulawa da shi har zuwa lokaci da zai fara samun sauƙi, in ya so idan ka kammala uzurorinka sai ka zo ka tafi da shi.” Cewar Dr Yasir.

Huci ya yi kaɗan tare da furzar da iska cikin damuwa ya ce “Shikenan zan tafi na bar amanar yaron a hannunka, amma don Allah ka kula sosai, ina matuƙar jin tausayin yaron nan saboda yanada special needs, zan tafi na barshi anan ne kawai saboda na yarda da kai sosai, kuma akwai buƙatar yaron ya samu kulawar likitoci a yanzu, da nake ganin idan na ce zan tafi dashi zai jiggata a hanya ne, da ba don haka ba ai….

Shikenan dai, don Allah ka kula da shi sosai.”

“Ka kwantar da hankalinka insha’allah zan yi abinda ya dace.” Cewar Dr Yasir.

Nan Mahmud ya masa Sallama ya fita jiki a saɓule, da har zai kuma leƙawa ɗakin don ya ga yaron, sai ya ji ba zai iya kuma kallarsa sannan ya tafi ba shi ba, don haka ya juya tare da ɗaukar motarsa ya fice daga asibitin gaba ɗaya.

@@@@@@@@@

Hajiya Hasina kuwa rayuwa ta mata daɗi yanzu, sai nishaɗi take abunta.

Kusan rabin kadarorin Alhajin yanzu duk sun zama nata, don kuwa ta saka shi yasa hannu a takardun wasu filayensa da gonakinsa cewar ya mallaka mata su…

Sai bushasharta take, a yanzu ko kasuwa Alhaji baya fita sai da izinin ta.

Ganin ta samu wannan damar ya saka ta fara tara ƙawayenta a gidan.
Kulu da ada take tsoron zuwa gidan, yanzu kanta tsaye take zuwa duk lokacin da ta ga dama, wani zubin ma sai ta yi sati a gidan, sannan ta tafi.
Ɗakin Abdul ada shi ne ya zama na ƙawayen hajiyar duk sanda suka zo gidan.

Yau ma kamar ko yaushe, zaune suke a falo suna hirarsu ta duniya da ƙyaƙyata dariya, a gabansu abinci ne kala-kala sai ci suke suna nishaɗi.

Binta Angulu (ɗaya daga cikin ƙawayen Hajiya Hasina) ta ce “Gaskiya Hajiya kina burge ni, dubi yanda kika juya alhajinki son ranki, nima gaskiya ato a kai ni wurin bokan ga in samu a mallake min Alhaji Tanimu, ke san duk cikin zawarawana babu wanda ya kai shi kuɗi duk da dai mummuna na..”

Gabaki ɗaya suka saka dariya, Hajiya Hasina ta ce “Ai gaki ga
Kulu nima ita takkaini, don ma ban tashi komawa ba, da tare muka tahiya a koma yimin wani aiki.”

Fiddo ido waje Jummai Jaɓa ta yi tare da cewa “Wani aiki kuma! Wai kuna nufin Duk mallakar Alhaji da kinka yi bai ishe ki ba, sai kin haɗa da wani aiki?.”

Dariya Hasina ta yi ta ce “Ba ki ganewa, akwai wani aiki guda da yar-rage gabana.”

“Wane aiki kenan?” Cewar Kulu.

“Ke dai a yi sha’ani kawai, in lokaci yayyi ji kikai.” ta mayar mata da amsa.

Tana gama faɗa ta miƙe ta yi cikin uwar ɗakanta, su kuma suka ci gaba da kallon Tv.

@@@@@@##

Tafiya yake a mota amma hankalinsa yaƙi kwanciya, sai tunanin halin da yaron zai iya shiga bayan baya nan yake.

Har ya durfafi hanyar fita garin, ganin ya kasa samun nutsuwa yasa ya juyo zuwa Asibitin.

A dai-dai lokacin da Yasir ya ɗaga Allura zai masa, shi kuma ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo.

Da sauri Yasir ya juyo, ganin mai shigowar ya saka ya zazzaro ido alamun mamaki.

“Mahmud kai ne?”

“Ni ne Dr, hankalina ya kasa kwanciya shi ne na zo na tafi da shi.” Ya bashi amsa.

Nan fa Yasir ya shiga bashi baki da nuna masa illar tafiya da shi a cikin wannan halin da yake, amma Fur Mahmud ya ƙi ji ya kafe sai ya tafi da shi.

“To idan ka tafi da shi ina zaka ajiye shi? Kai dai Gwauro ne bare kace zaka kaiwa matarka shi, kuma ba zaka iya kula da shi ba saboda aikinka, yaya kenan?”
“Hajiyata zan kaiwa amanarsa….”

Tun bai ƙarasa ba Yasir ya katse shi da cewa “Ka dai san halin Hajiya sarai, kafi ni sanin yanda ta tsani talaka da Musakai amma….”

Hannu ya ɗaga masa alamun ya isa ya ce “Koma dai menene ita ce Mahaifiyata na san za ta fahimce ni, Malam cire masa wannan drip ɗin zamu tafi……

RUKY I LAWAL❤️❤️❤️❤️

*HALITTAR ALLAH CE*

👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*+

          *AND NOW*
   *HALITTAR ALLAH CE*

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

PAGE 45-46
Jiki a sanyaye Dr Yasir ya cirewa Abdul drip ɗin, bai kuma cewa komai ba, saboda lura da ya yi ran abokinsa ya ɓaci da maganarsa.

Shima Mahmud ɗin bai kuma cewa kanzil ba, ya ɗauki Abdul zuwa motarsa.

Abdul ya kalle shi ya ce “Yaya ina zamu na?”

Murmushi ya sakar masa ya ce “Abdul gidanmu zan kai ka, ai nasan zaka so zuwa Kaduna koh?”

“Lah! Kaduna ta cikin state and Capital da anka koya muna a NURSERY?”
Abdul ya faɗa cike da fara’a.

Sosai ya bawa Mahmud dariya, sai da ya ɗan dara sannan ya ce “Ita fa, da alama baka taɓa zuwa ba koh?”

Ya tambayi yaron dai-dai lokacin da ya gama dai-daita zamansa a gaban motar tare da kunna ta.

“Eh yaya ban taɓa zuwa ba ba……” Sai kuma ya yi ɗif kamar wanda wuta ta ɗaukewa.

“Ba me ba Abdul?” Mahmud ya tambaya.

“Na mance abinda nika son cewa.”

Murmushi Mahmud ya yi a ransa ya ce “ƙuruciya kenan.”

Ji yayi yaron ya ƙara shiga ransa, duk da shima zancen gaskiya daurewa kawai yake yana kallon yaron, tun yana tsoronsa har ya ji ya fara sabawa da ganin halittarsa.

A haka ya ci gaba da jan Abdul da hirar da ta shafi danginsa yana tuƙi,  amma bai yi nasarar samun wani labari da zai haska masa waye Abdul ɗin ba, domin kuwa an riga an shafewa yaron tunanin ahalinsa gaba ɗaya.

Sai gab da Magriba Mahmud ya fara shiga garin Kaduna, ko da ya isa unguwarsu an idar da Sallah don haka kafin ya ƙarasa ya tsaya massalacin farkon layinsu ya yi Sallah sannan suka ƙarasa gida.
Ko da ya shiga falonsu Hajiyarsa bata nan, da alama tana sama.

Anan ya ɗaga waya ya kirata.
“Hello Hajiyata Barka da dare.”

Shiru ya yi alamun ana magana a ɗaya ɓangaren, zuwa can ya ce “uhmm! Hajiya ai na ƙaraso gida.”

Ya kuma yin shiru, ba jimawa ya yi murmushi ya ƙara cewa “Allah da gaske Hajiyata yanzu haka ina falon ƙasa, sauko ki gani.”

Daga haka ya kashe waya tare da yin ‘yar dariya ya ce “Hajiyata kenan! To banda abin Hajiya miye abun mamaki ma a cikin dawowata yanzu?.”

Bayan kamar mintuna biyar sai ga Hajiya ta fito cikin shigarta ta alfarma tana washe baki.

Shi kuwa Mahmud yana zaune kan kujera ya bawa ƙofar ɗakin hajiyar baya, don haka bayansu kawai take iya gani.

“Welcome My Son, kai da wanne yaro ne zaune?” Ta faɗa a lokacin da take takowa zuwa inda suke.

Da sauri ya juyo yana washe haƙora ya ƙarasa gare ta tare da durƙusawa ya gaishe ta.

Cike da fara’a ta amsa shi tana nufar kujerar da yaron ke zaune, burinta shine ta isa gaban kujerar don ganin wane yaro ne wannan ya zo ya zauna mata kan kujera haka.

Ko kusa bata kawo tunanin cewa Mahmud ya zo da yaron ba, ta zata irin yaran nan ne masu tsaurin ido.

Ganin ta nufi gun gadan-gadan yasa cikin Mahmud ya ɗuri ruwa, sai yanzu ne yake ganin girman wautarsa ta zuwa da yaron gidan…

Tun bai ƙarƙare tunaninsa ba ya ji Hajiyarsa ta tsunduma ihu tare da runtse idonta da ƙarfi, a lokacin da Abdul ɗin ke faɗar “Mama ina yini?”

Ido a rufe ta ce “Son fitar mun da wannan yaron daga nan pls.”

Kasaƙe ya yi kamar bai ji ba, jin shirun ya fara yawa ya saka ta yi tunanin ko Mahmud ɗin ya je fitar da yaron, kawai sai ta buɗe idonta.

Wani ɓacin rai ne ya ziyarci zuciyarta a lokacin da ta sauke idonta kan Abdul, shiko sai rarraba ido yake kamar an koro shege daga lahira.

Tsawa ta dakawa Mahmud wanda ba iya Abdul kaɗai ba, har shi Mahmud ɗin sai da ‘yan hanjinsa suka kaɗa ta ce “Ban ce ka fitar mun da wannan nakasasshen yaron ba? Su ma masu gadin nan bansan amfaninsu ba, da suka bar wannan yaron ya shigo mun har falo, amma zan gamu dasu ne.” Ta yi ƙwafa.

Daƙyar ya tattaro nutsuwarsa ya ce “Ki yi haƙuri Hajiyata ni ne fa na shigo dashi nan.”

Wani irin kukan kura hajiyar ta yi ta yi cikin Mahmud gadan-gadan tare da balbale shi da Masifa.

Faɗar take “Wannan wane irin iskanci ne? Sarai ka sani cewa na tsani ganin nakasasshi bare kuma wannan da dukkan Alama ba iya nakasa kaɗai yake da ba, harda talauci.”

Jiki a sanyaye Mahmud ya ce “Don Allah Hajiya ki saurare ni, wannan yaron yana matuƙar buƙatar taimakon mu, yanzu idan kika kore shi fa ko tafiya ba zai iya yi ba, saboda gurgu ne, na ɗauko shi ba tare da sanin hakan ba, sandunansa kuma suna can yashe a inda na ɗauko shi…”

Zama ta yi tana huci ta baza kunnuwa tana jin tatsuniyar da ɗan nata yake gayamata.

Ganin ta zauna ya saka masa ƙwarin gwuiwar ci gaba da magana.

“Yanzu dai Hajiyata don Allah ki taimaka ki barshi ya zauna anan….”

Tun bai gama rufe bakinsa ba ta daka masa tsawa “Wai baka da hankali ne son? Ni ce zan zauna da wannan abun anan gidan? To kasani ko kwana ba zan barshi ya yi anan ba, yanzun nan zaka mayar dashi duk inda ka ɗauko shi, waya sani ma ko aljani ne.”

Durƙusawa ya yi a gabanta yana mata magiya, “Don Allah Hajiya ko sati ɗaya ne ki barshi ya yi, zan nema masa sanduna daga nan sai na mayar dashi.”

Duk wannan magiyar da yake bai saka Hajiyarsa jin tausayinsu ba, daga ƙarshe ma miƙewa ta yi, ta ce “Bari ma ka gani, in kai ka kasa.”

“Hanne! Hanne!!”

Ta ƙwalawa mai aikinta kira.
Da gudu hanne ta fito tare da faɗar “Ranki yadaɗe gani.”

Cike da tsanar yaron ta nunawa Hanne shi da hannu ta ce “Fitar mun da wannan abun daga nan.”

Cike da mugunta ta nufi Abdul da tun ɗazu ya ke kuka, ta kinkime shi kamar kayan wanki ta watsar a wajen sashen Hajiyar.

Mahmud na ganin hakan ya tashi rai a ɓace ya nufi kofar fita, Hajiya na kiransa amma ko waiwayowa bai yi ba.

A ƙofa suka haɗu da Hanne ya aika mata wata muguwar harara, tare da yin ƙwafa mai nuni da zaki gane kurenki.

A ɗarare Hanne ta yi ciki, don tana Masifar tsoron wannan fitinannen boss ɗin nasu.

A zuciye ya fice yana neman inda aka jefar da yaron.

A dai-dai lokacin ne kuma wayarsa ta hau ƙugin neman agaji, ya zaro ta daga gaban aljihu ya duba, wani uban tsaki ya ja cike da jin haushin mai kiran.

Shi sam ma ya manta da abinda ya maido shi garin cikin gaggawa, ya manta da alƙawarin da ya yiwa masoyiyar tasa saboda tsabar tashin hankalin da ya shiga yanzu.

Wayar ya kashe gaba ɗaya tare da mayar da ita aljihu ya ci gaba da neman yaro Abdul….

RUKY I LAWAL CE❤️🌹🌹

*HALITTAR ALLAH CE*

👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼👨🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*+

          *AND NOW*
   *HALITTAR ALLAH CE*

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

PAGE 45-46

Jiki a sanyaye Dr Yasir ya cirewa Abdul drip ɗin, bai kuma cewa komai ba, saboda lura da ya yi ran abokinsa ya ɓaci da maganarsa.

Shima Mahmud ɗin bai kuma cewa kanzil ba, ya ɗauki Abdul zuwa motarsa.

Abdul ya kalle shi ya ce “Yaya ina zamu na?”

Murmushi ya sakar masa ya ce “Abdul gidanmu zan kai ka, ai nasan zaka so zuwa Kaduna koh?”

“Lah! Kaduna ta cikin state and Capital da anka koya muna a NURSERY?”
Abdul ya faɗa cike da fara’a.

Sosai ya bawa Mahmud dariya, sai da ya ɗan dara sannan ya ce “Ita fa, da alama baka taɓa zuwa ba koh?”

Ya tambayi yaron dai-dai lokacin da ya gama dai-daita zamansa a gaban motar tare da kunna ta.

“Eh yaya ban taɓa zuwa ba ba……” Sai kuma ya yi ɗif kamar wanda wuta ta ɗaukewa.

“Ba me ba Abdul?” Mahmud ya tambaya.

“Na mance abinda nika son cewa.”

Murmushi Mahmud ya yi a ransa ya ce “ƙuruciya kenan.”

Ji yayi yaron ya ƙara shiga ransa, duk da shima zancen gaskiya daurewa kawai yake yana kallon yaron, tun yana tsoronsa har ya ji ya fara sabawa da ganin halittarsa.

A haka ya ci gaba da jan Abdul da hirar da ta shafi danginsa yana tuƙi,  amma bai yi nasarar samun wani labari da zai haska masa waye Abdul ɗin ba, domin kuwa an riga an shafewa yaron tunanin ahalinsa gaba ɗaya.

Sai gab da Magriba Mahmud ya fara shiga garin Kaduna, ko da ya isa unguwarsu an idar da Sallah don haka kafin ya ƙarasa ya tsaya massalacin farkon layinsu ya yi Sallah sannan suka ƙarasa gida.

Ko da ya shiga falonsu Hajiyarsa bata nan, da alama tana sama.

Anan ya ɗaga waya ya kirata.
“Hello Hajiyata Barka da dare.”

Shiru ya yi alamun ana magana a ɗaya ɓangaren, zuwa can ya ce “uhmm! Hajiya ai na ƙaraso gida.”

Ya kuma yin shiru, ba jimawa ya yi murmushi ya ƙara cewa “Allah da gaske Hajiyata yanzu haka ina falon ƙasa, sauko ki gani.”

Daga haka ya kashe waya tare da yin ‘yar dariya ya ce “Hajiyata kenan! To banda abin Hajiya miye abun mamaki ma a cikin dawowata yanzu?.”

Bayan kamar mintuna biyar sai ga Hajiya ta fito cikin shigarta ta alfarma tana washe baki.

Shi kuwa Mahmud yana zaune kan kujera ya bawa ƙofar ɗakin hajiyar baya, don haka bayansu kawai take iya gani.

“Welcome My Son, kai da wanne yaro ne zaune?” Ta faɗa a lokacin da take takowa zuwa inda suke.

Da sauri ya juyo yana washe haƙora ya ƙarasa gare ta tare da durƙusawa ya gaishe ta.

Cike da fara’a ta amsa shi tana nufar kujerar da yaron ke zaune, burinta shine ta isa gaban kujerar don ganin wane yaro ne wannan ya zo ya zauna mata kan kujera haka.

Ko kusa bata kawo tunanin cewa Mahmud ya zo da yaron ba, ta zata irin yaran nan ne masu tsaurin ido.

Ganin ta nufi gun gadan-gadan yasa cikin Mahmud ya ɗuri ruwa, sai yanzu ne yake ganin girman wautarsa ta zuwa da yaron gidan…

Tun bai ƙarƙare tunaninsa ba ya ji Hajiyarsa ta tsunduma ihu tare da runtse idonta da ƙarfi, a lokacin da Abdul ɗin ke faɗar “Mama ina yini?”

Ido a rufe ta ce “Son fitar mun da wannan yaron daga nan pls.”

Kasaƙe ya yi kamar bai ji ba, jin shirun ya fara yawa ya saka ta yi tunanin ko Mahmud ɗin ya je fitar da yaron, kawai sai ta buɗe idonta.

Wani ɓacin rai ne ya ziyarci zuciyarta a lokacin da ta sauke idonta kan Abdul, shiko sai rarraba ido yake kamar an koro shege daga lahira.

Tsawa ta dakawa Mahmud wanda ba iya Abdul kaɗai ba, har shi Mahmud ɗin sai da ‘yan hanjinsa suka kaɗa ta ce “Ban ce ka fitar mun da wannan nakasasshen yaron ba? Su ma masu gadin nan bansan amfaninsu ba, da suka bar wannan yaron ya shigo mun har falo, amma zan gamu dasu ne.” Ta yi ƙwafa.

Daƙyar ya tattaro nutsuwarsa ya ce “Ki yi haƙuri Hajiyata ni ne fa na shigo dashi nan.”

Wani irin kukan kura hajiyar ta yi ta yi cikin Mahmud gadan-gadan tare da balbale shi da Masifa.

Faɗar take “Wannan wane irin iskanci ne? Sarai ka sani cewa na tsani ganin nakasasshi bare kuma wannan da dukkan Alama ba iya nakasa kaɗai yake da ba, harda talauci.”

Jiki a sanyaye Mahmud ya ce “Don Allah Hajiya ki saurare ni, wannan yaron yana matuƙar buƙatar taimakon mu, yanzu idan kika kore shi fa ko tafiya ba zai iya yi ba, saboda gurgu ne, na ɗauko shi ba tare da sanin hakan ba, sandunansa kuma suna can yashe a inda na ɗauko shi…”

Zama ta yi tana huci ta baza kunnuwa tana jin tatsuniyar da ɗan nata yake gayamata.

Ganin ta zauna ya saka masa ƙwarin gwuiwar ci gaba da magana.

“Yanzu dai Hajiyata don Allah ki taimaka ki barshi ya zauna anan….”

Tun bai gama rufe bakinsa ba ta daka masa tsawa “Wai baka da hankali ne son? Ni ce zan zauna da wannan abun anan gidan? To kasani ko kwana ba zan barshi ya yi anan ba, yanzun nan zaka mayar dashi duk inda ka ɗauko shi, waya sani ma ko aljani ne.”

Durƙusawa ya yi a gabanta yana mata magiya, “Don Allah Hajiya ko sati ɗaya ne ki barshi ya yi, zan nema masa sanduna daga nan sai na mayar dashi.”

Duk wannan magiyar da yake bai saka Hajiyarsa jin tausayinsu ba, daga ƙarshe ma miƙewa ta yi, ta ce “Bari ma ka gani, in kai ka kasa.”

“Hanne! Hanne!!”

Ta ƙwalawa mai aikinta kira.
Da gudu hanne ta fito tare da faɗar “Ranki yadaɗe gani.”

Cike da tsanar yaron ta nunawa Hanne shi da hannu ta ce “Fitar mun da wannan abun daga nan.”

Cike da mugunta ta nufi Abdul da tun ɗazu ya ke kuka, ta kinkime shi kamar kayan wanki ta watsar a wajen sashen Hajiyar.

Mahmud na ganin hakan ya tashi rai a ɓace ya nufi kofar fita, Hajiya na kiransa amma ko waiwayowa bai yi ba.

A ƙofa suka haɗu da Hanne ya aika mata wata muguwar harara, tare da yin ƙwafa mai nuni da zaki gane kurenki.

A ɗarare Hanne ta yi ciki, don tana Masifar tsoron wannan fitinannen boss ɗin nasu.

A zuciye ya fice yana neman inda aka jefar da yaron.

A dai-dai lokacin ne kuma wayarsa ta hau ƙugin neman agaji, ya zaro ta daga gaban aljihu ya dub

*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYGAR MEERAH*

*Y’AR GANTALI*

*RIKICIN MASOYA*

*A SANADIN KAMA*

*RASHIN GATA*

*WATA ƘAWA*

        *AND NOW*

   *HALITTAR ALLAH CE*

*AREWA WRITERS ASSOCIATION*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

PAGE 47-48

Sai da ya ɗan yi tafiya kaɗan sannan ya hango shi yashe a gefe yana kuka.+

Cike da tausayin yaron ya ƙarasa gurinsa, durƙusawa ya yi ya juya masa bayansa ya ce “Abdul hau na goyaka.”

Ba musu Abdul ya haye bayansa yana cigaba da kukansa mai taɓa zuciya.

Miƙewa ya yi ransa a jagule yana cin takaicin irin wannan halin na Mahaifiyarsa a ransa.

A haka ya nufi motarsa ya sanya Abdul ɗin cike tare da janta ya bar gidan.

Tunda ya fita bai zame ko’ina ba sai ƙofar wani katafaren restaurant, fitowa yayi daga motar, da har zai shiga da Abdul ɗin cikin gidan abincin, sai ya tuna cewa ashe fa ba zai iya tafiya ba, sannan akwai al’umma da yawa a cikin gidan abincin, zasu iya tsorata da halittarsa.

Tuna hakan da ya yi yasa ya kalli Abdul ya ce “Abdul ka jira ni anan zan siyo ma abinci, ai kana jin yunwa koh?”

Da sauri ya ɗaga kansa yana faɗar “Eh.”

“Yawwa to ka jirani a nan, me kake so na siyo maka?”

Ya faɗa yana masa murmushi.

Cike da fara’a Abdul ya ce “Ni komai ma ina ci yaya.”

Murmushi ya kuma yi ya ce “Shikenan bari na shiga na fito yaron kirki.”

Motar ya sakawa lock sannan ya shige cikin restaurant ɗin yana saka muƙullan motarsa a aljihu.

Shi ko Abdul yana ganin shigewar Mahmud ciki ya shiga rarraba ido a gaban motar, nan ya ƙyalla ido ya ga wayar Mahmud ɗin da ya manta a motar ya ɗauka.

Cikin sa’a kuwa bai sakawa wayar lock ba, don haka Abdul ya ɗauka ya shiga buga Games kamar yanda yake yi a wayar Abbunsa lokacin da yana gida.

Can bayan kamar mintuna goma sai ga Mahmud ya dawo, buɗe motar yayi ya shiga a nan ya tarar da abinda Abdul ɗin ke yi da wayarsa, sai a lokacin ma yasan yabar wayar a mota.

Murmushi kawai ya yi ya ce “Abdul ashe ka iya Game haka?”

“Eh,” Abdul ya ce yana dariya.

“A’ina ka koya har ka iya?.” Ya faɗa a ƙoƙarinsa na sake bugun cikin yaron a karo na biyu.

“Na iya, ai ina yi a wayar Ba….” Sai kuma ya yi shiru.

Nan fa yayi iya ƙoƙarinsa domin ya ji wani abu daga bakin yaron wanda zai haska masa rayuwarsa ta baya, ko ya gano danginsa ya maida shi gida, amma Abdul ya kasa tuna komai bare ya faɗa, bisa tilas Mahmud ya haƙura.

A haka suka koma gida, ko kallon part ɗin Hajiya bai yi ba, ya wuce zuwa ɓangarensa ɗauke da Abdul a bayansa, hannuwansa kuma suna ɗauke da ledojin abincin da ya siyo masu.

Yana shiga ya kullo ƙofar part ɗinsa da makulli suka shige ciki.

®®®®®®®©©

A ɓangaren Hajiya Hasina kuwa faka

Motarta ta yi a ƙofar gidan bokansu, fuskarta ɗauke da alamun damuwa ta kalli Kulu dake zaune a gefenta ta ce “Ni fa ke ga abinda yassa ban son zuwa wurin bokan ga, kullum sai ka isko layi kamat bone.”

Murmushi Kulu ta yi ta ce “Hajiya ki yi hanƙuri, suma nan duk buƙatassu takkawo su kamar dai ke…”

Sosai Hasina ta kara cika kamar ta fashe, yaushe Kulu ta rainata har haka?….

RUKY I LAWAL CE❤️❤️❤️❤

*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYGAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

        *AND NOW*
   *HALITTAR ALLAH CE*
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

PAGE 49-50

Banda raini kamar ita Kulu zata gayawa wannan maganar “wai duk buƙatarsu ta kawo su?”
Ɗaga kai ta yi ta kalli matan da suka yi tururuwa a gurin tana kallonsu a rene,  waɗannan kucakan matan ne Kulu ke haɗawa da ita?”

Siririn tsaki ta ja tare da maida hankalinta ga Kulu tace “Waɗanga mata in banda ɓidat a sani kiran sallah da Usur mikkawo su nan, banda ɓacewa? Ni banga abinda zuwa wurin boka yat ctinana musu ba, tunda duk suturarsu a koɗe take…”
“Mtsw!” Ta koma jan tsaki a karo na biyu.
“Ku ji matag-ga wai mai bunu ga gindi ka kai gudumuwat gobara ai duk taron zani-zaka na, duk waku-waku na ɓatattu, ke ma banda bala’i mi zuwa wurin bokan zai ctsinana miki….” Kulu ce ke wannan zancen a ranta kafin ta ɗago ta kalli Hasina dake tsumayen amsarta ta ce “Ke dai bari Hajjiya wanda ya yi nisa ai bai jin kira, kuma shi ɓatacce bai gane kan ɓata yake sai ya hwaɗa cikin kwatamin nadama.”
Dariya sosai Hasina ta dinga yi na tare da ta lura cewa yaɓa mata magana ne Kulu ta yi ba.+

Sai can ta tsagaita da dariyar ta ce “Wallahi ko Kulu da gaskiyakki, basu ganewa da sun bar wahalar da kansu.”

Kulu ta mata wani irin kallo mai nuni da shashantar da mutum ta ce “To ke gani ba?, don haka mance da su hito mu bi layi kahin wasu su muna rigaye.”

Da wannan maganar suka rufe babin hirar tasu tare da fitowa daga motar, Hasina ta rufe motar suka nufi  gun layin, sai wani takun ƙasaita Hasina ke yi tana shan ƙamshi Kulu na take mata baya.

Kulu ta ce a ranta ” ki gama iskancinki Akwai ranar ƙindillacin tana zuwa, ranar da haƙƙin ɗan talikin yaron nan Abdul ya tashi kama ki zaki yabawa aya zaƙinta.”

Sun jima a layin sai bayan shuɗewar awanni biyu sa’annan suka samu ganin bokan, a nan Hasina ta bayyana masa buƙatar ta son ganin ta samu haihuwa da alhajin.
Boka Barkuza ya ƙyalkyace da wata mahaukaciyar dariya data firgita su sannan ya gimtse fuska, ya karanto wasu surƙulle tare da shauɗa gezar hannunsa a ƙasa sannan ya ɗago da gwala-gwalan idanunsa ya kalli Hasina ya ce “Aiki ja, ki aje maganar haihuwa yanzu don akwai wani tarnaƙi da ke tunkaro ki a yanzu, mu mai da hankali kan binciko matsalar dake tunkaro ki tana son shiga tsakaninki da burinki kahin ayi maganar haihu, don ko zaki haihu da Alhaji ba yanzu ba…”

Jin wannan batun ya saka hankalin Hasina ya yi mummunan tashi.
A haka suka yi bankwana da boka bisa alƙawarin zai binciko mata tarnaƙin dake fuskanto burin rayuwarta.

@@@@@@@@@@

Bayan Mahmud ya rufo part ɗinsa ya ɗauko plate ya zubawa Abdul abinci yana ci, kamar wanda ya tuna wani abu sai ya miƙe ya nufi uwar ɗakansa ya ɗauki wayarsa ya kira Likitansu don ya zo ya duba Abdul yagaya masa matsalar yaron da kuma halin da yake ciki.

Jiyo ihun Abdul ɗin daga falo ya saka shi katse wayar ba shiri ya yo waje don ganin meke faruwa.

Tarar dashi ya yi ya yada cokalin ƙasa sai faman ihu yake yana riƙe baki.
Dasauri ya yi kansa yana duddubawa jikin yaron don har cikin ransa yake jin kukan yaron.
A ɗan firgice yace “Abdul Menene?”

“Halshena, na taune halshena.” Ya faɗa cikin ƙarfin hali.
Tallabo shi ya yi ya duba har gun ya fashe kaɗan, haka ya cigaba da rarrashinsa.

Bayan mintuna sha biyar sai ga Likita ya iso, nan take ya shiga yiwa Abdul gwaje-gwaje.
Bayan ya kammala Mahmud ya kwaso magungunan da Yasir ya bawa Abdul a Kano ya nuna masa.

Nan ya ware waɗanda za’a yi amfani dasu ya nunawa Mahmud tare da rubuta mashi ƙarin waɗanda ake buƙata.

A nan ya mishi bayanin lalurar yaron ya nemi da a sama masa sanduna.
Dr Amir ya kalli Mahmud yace “Kasan ni ba ɓangaren ƙashi nake ba, amma zan bincika maka gun aminina dake ɓangaren, duk yanda muka yi zaka ji insha’allah.”

“To madallah Nagode sosai, sai na ji ka.” Cewar Mahmud.
Daga haka suka yi sallama, Dr Amir ya fito takawa ya yi zuwa inda ya ajiye motarsa.
Yana zuwa dai-dai part ɗin Hajiya suka haɗu da Hajiyar lokacin ta fito don Sallamar bakonta lokacin kusan ƙarfe tara na dare.

“Barka da dare Hajiya.” Cewar Dr.
Cike da sakin fuska ta kalle shi, “A’ah! Dr kai ne a gidan? Yaushe ka zo?” Ta tambaya da mamaki a fuskarta.

Da murmushi a fuskarsa yace “Ban jima da zuwa ba, bros Mahmud ya kira ni, ina cikin uzuri ne shiyasa ban leƙo mun gaisa ba.”

Cikin alamun kaɗuwa ta zaro ido “Meke damunsa ne?”
“Kwantar da hankalinki Hajiya bashi ne mara lafiyan ba yaron dake tare dashi ne.” Ya faɗa.
Wani irin ɓacin rai ne ya taso mata, amma don bata son Mahmud ya gane ta saki fuska ta ce “Ok yana part ɗinsa ko?”
“Eh.” kawai yace mata ya mata sallama ya ƙarasa bakin motarsa a hanzarce, ya shige yabar gidan.

Cike da ɓacin rai mara misaltuwa ta juya ba tare da tayi abunda ya fito da ita daga sashenta ba, ta nufi sacen Mahmud tana zancen zuci.
Lallai Son ya raina ni, da nace yaron nan ba zai kwana a gidan nan ba shine zai nuna mun ban isa ba koh?”

Ƙwanƙwasar ƙofar sashen take tun ƙarfinta, tsabar ɓacin rai ta manta da bell ɗin ƙofar bare ta matsa.

Jin irin wannan bugun ƙofar da ake cikin rikitaccen yanayi, ya saka shi tsurewa, bako shakka ya san wannan aikin Hajiya ne, wataƙil ta samu labarin yaron yana tare da shi, to waya gaya mata?………

RUKY I LAWAL CE❤️❤️❤️❤️❤️❤️

*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

        *AND NOW*
    *HALITTAR ALLAH CE*
DEDICATED TO: ALL MEMBERS OF AREWA WRITERS ASSOCIATION, SON SO FISABILLAHI NAKE MUKU❤️🥰❤️
________________________________
+
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

PAGE 51-52

Cike da ruɗewa ya ja hannun Abdul ya nufi uwar ɗakansa ya saka yaron a banɗaki ya rufe tare da masa umurnin duk abinda za’ayi ko kyakkyawan motsi kada ya yi har sai in shi ya bashi dama.

Rufo ƙofar banɗakin ya yi da makulli tare da jefa makulin saman walldrob ɗinsa.

A gigice ya fito jin ƙarar bugun ƙofar na daɗuwa har yana  ƙoƙarin fasa masa dodon kunne.

Cikin dakiya da nuna kamar bai san komai ba, ya zo ƙofar ɗakin aro Muryar masu barci ya ce “Waye ne?”

Jin muryarsa yasa ta daga murya tace “Ni ce buɗe.”

Ba musu ya buɗe tare da janye wa ya bata hanya.

Bata yi wata-wata ba, ta shiga dube-dube a falon, kamar wacce aka bawa ajiyar rai ya ɓata.

Bin bayanta Mahmud ya yi yana cewa “Hajiyata me kike nema ne da dare haka?”

Harara ta aika masa wacce ta saka shi ƙara kiɗimewa ta ce “Ba dai ka raina ni ba ko Son? Ince bana buƙatar zaman yaron nan a gidan nan shine zaka nuna mun ban isa da kai ba koh?”

Tana maganar ne cikin masifa da ɗaga murya.

“Wane yaron kuma Hajiya? Ina ce ke da kanki kika saka a fitar da shi, taya zan gan shi, har ki yi tunanin ko na ɓoye shi?”

Kallonsa ta yi taga ba alamun tsoro a tare da shi, hakan yasa wani sashe na zuciyarta ya bijiro mata da tambaya, “Idan har yana nan to ina ya ɓoye shi? kamar ma daga barci ya tashi fa.”

Kamar yasan me take tunani ya hau mitsitsika ido yana hamma……

Duk da hakan bai saka ta haƙura ba, sai da ta shiga har uwar ɗakansa ta duba ba Abdul ba dalilinsa.

Ganin haka ya saka ta tsaya ta ce “Yanzun nan fa na haɗu da Dr yace ya zo duba wani yaro anan sashenka, amma yanzu kace baya nan?”

“Hajiya da yana nan ai da kin ganshi, kawai na tausaya masa ne, ganin baya da lafiya na kira likita ya duba shi, yana gama aikinsa na haɗa masa maganin a leda na fitar da shi ta ƙofar baya, ki yarda da ni.”

Da wannan kalaman ya yaudare   ta ta yarda da zancensa. Kawai sai ta juya tana faɗar “Shikenan Allah ya maka albarka je ka ƙarasa barcinka, amma da farko hankalina ya tashi ganin zaka bijire mun, sai na yi tunanin kodan yana gidan gadonka ne kake ganin ka isa ka yi abunda ka ga dama…”

Tana gama faɗa ta juya ba tare da ta jira cewarsa ba, ta fice daga sashen zuwa nata.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke ganin ya sha daƙyar, ya bi bayanta tare da rufo kofar sashensa, ya bar makullin jikin ƙofa, gudun kada ta shammace shi ta dawo ta buɗe ƙofar da spare key dake hannunta.

@@@@@#

Haka ya ci gaba da ɓoye Abdul a sashensa har na tsawon mako ɗaya, ba tare da wani daga cikin mutanen dake rayuwa a gidan sun sani ba.

Domin in zai fita sai ya kulle yaron a daki, ya bashi ɗaya makulin ya ja masa kunne da kada ya sake ya koda leƙo waje ne, idan ya dawo shi zai buɗe ƙofar da makullin hannunsa.
A wata ranar Litinin Bayan fitar Mahmud gun aiki, da misalin ƙarfe 11:30 na safe Abdul na kwance kan gadon Mahmud yana shaƙar barcinsa cikin kwanciyar hankali, juyawar da zai yi haka, ya ji ya rungume wani abu mai gashi ga santsi, kafin ya gama tattance miye magen dake kwance daf da shi ta zabura tana neman guduwa, cikin rashin Sa’a tabi takan fuskarsa.

Saukar daginta akan fuskarsa ke da wuya ya buɗe ido tare da kwarara wani uban ihu mai firgitarwa, gashi shi ba ƙafafu ba bare ya gudu don haka ya silmiyo ƙasa cikin kiɗima.

Ita kuwa mager ta fara zagaye ɗakin tana neman fita..
Ko da Abdul ya gama gane mage ce a gabansa, abinda yake tsananin tsoro a duniyarsa, kawai sai ya hau rarrafe ya nufi ƙofar falon yana kwarara ihu.

Har ya kusa fita, ya tuna da makullin kofar dake ajiye a bedsite durowa, a kiɗime ya juyo da rarrafe ya ɗauka ya fice da sauri itama mager ta biyo bayansa kowa na gudun wani, wannan fa shi ake kira banza ta kori wofi.

Ashe daidai lokacin da Abdul ya ratsa ihu a karon farko, Hanne mai’aiki ta zo wucewa ta kusa da part ɗin Mahmud.

Jiyo ihun yaro kuma ga part ɗin a rufe, ya sakata ƙara sauri don kai gulma da zafinta, don bata raba ɗayan biyu, kodai shegen yaron nan ne Boss ya ɓoye a ɗakinsa ko wani abun dabam ke faruwa.

Cikin mintuna da basu wuce uku ba sai ga Hajiya ta fito cikin sauri, kallo ɗaya zaka mata kasan cike take fal da Masifa.

Hanne ta biyo ta abaya don bawa idonta abinci.

Isowarsu ƙofar part ɗin ya yi dai-dai da lokacin da Abdul ya buɗe ɗakin da makulli yafito da rarrafe cikin sauri, da alama iya ƙarfin gudun gwuiwoyinsa kenan.

Ganinsa ya ɓatawa Hajiya rai ba kaɗan ba, domin da za’a bata aron rai a ranar da har shi sai ya ɓaci saboda wannan abun da ɗan cikinta ya mata.

“Chabɗijam! Lallai Mahmud ka gama raina ni, amma bakomai Allah ya dawo da kai lafiya zamu gamu ne…”

Ta yi ƙwafa cikr da haushi ta ci-gaba da bambaminta kamar Mahmud ɗin na tsaye gabanta, ta ce “Bari na ɓatar da kai kafin ya dawo sai mu ga abinda zai iya yi.”

Tana kai nan ta kira ma’aikatan gidan maza ta masu umurni su fitar mata da wannan mummunar halittar…

Ba musu suka yi kan Abdul don cika umurnin uwar gidan tasu.

Abdul yana kuka shaɓe-shaɓe ya fara magana kamar haka “Don Allah Mama ki yi hanƙuri, ki taimake ni wallahi in kit kore ni bansan inda zanna ba…”

Katse shi ta yi da faɗar “Yi mun shiru, Ni na tsani Musakai ba zan zauna da kai ba wallahi.”

Cikin kuka Abdul ya ce “Meyasa Mama? Me yasa Mutane suka tsane mu mu Musakai? shin laifin waye ya sa muka zama musakai?. Malaminmu na islamiyya ya ce ba kyau wulaƙanta ɗan adam, sa’annan ba wanda yafi wani a wurin Allah sai wanda ya fi jin tsoronsa…”

Ranta ne ya yi ƙololuwar ɓaci wai ita ɗan wannan talikin yaron zai ma wa’azi?

Cikin ɓacin rai ta nufe shi gadan-gadan har ta daga hannu zata……

Hmmm! Kome Hajiya zata ma Abdul?
Mahmud zai dawo gida ya tarar da Abdul kuwa?

Miye makomar rayuwar Abdul in har hajiya ta kore shi?
Don jin wadannan amsoshin ku biyo NI a pages na gaba.

Kada ku manta More comment more typing, in na ji tsit kunsan sauran masoya🥰

Alƙamin:✍🏻✍🏻✍🏻UMMU INTEESAR NE❤️❤️🥰

*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

         *AND NOW*
    *HALITTAR ALLAH CE*

DEDICATED TO ALL MEMBERS OF HALITTAR ALLAH CE FANS GROUP.

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR_RAHMANIR_RAHIM*
PAGE 53-54

Cikin ɓacin rai ta nufe shi gadan-gadan, har ta daga hannu zata mare shi, suka jiyo sautin shigowar mota cikin hanzari.

Waigayawa suka yi gabaki ɗayansu don ganin waye.
Mahmud ne ya fito daga motar a sukwane ya nufi inda Abdul ke sunkuye yana kuka.

Dama shi tun lokacin da agogon hannunsa ya buga ƙarfe sha ɗaya na safe yake jin matsananciyar faɗuwar gaba, da yaga abun bana ƙare ba ne shine ya ɗebo mota ya dawo gida domin tunawa da ya yi da ajiyar sirrin dake ɗakinsa. Shigowarsa gate ɗin gidan ke da wuya ya hango tashin hankalin dake faruwa.
“Shi ke nan yau kashina ya bushe, tabbas yau nasan daƙyar nasha a hannun Hajiya.”
Ya faɗa a ransa.

Sai dai wannan fargabar bata hana shi tunkarar matsalarsa don magance ta ba.

Yana isa gun ya tsaya a gaban Abdul tare da kare shi, ya haɗa hannayensa biyu guri ɗaya tare da zubewa akan gwuiwoyinsa yana magiya.

Ganin hakan ya saka su Hanne da sauran ma’aikatan ‘yan ganin ƙwaf suka watse, don sun san waye Boss sarai, baya ɗaukar raini, idan suka yi wasa wannan kallon da zasu tsaya zai zame masu silar kubcewar ayyukan da suka dogara da su.

Ita ko Hajiya tana nan tsaye sai huci take, har yanzu bata sauke hannayenta ƙasa ba, sai cika da batsewa take.

Magiya ya fara mata kamar haka:
“Don girman Allah Hajiya ki yi haƙuri, ki tausayawa yaron nan, ki dubi maraicinsa da halin da yake ciki na ƙunci da kuma larurar dake tare da shi, ina tsoron abinda zai biyo baya bayan kin kore shi daga gidan nan, ba mamaki zai koma faɗawa rayuwar jeji cikin tsuntsaye Da dabbobi, sa’annan ina tsoron Allah ya kama mu da laifin ƙin taimakawa wannan rayuwar dake buƙatar taimakon gaggawa..”1

Yana maganar yana marairaicewa kamar zai saka kuka.
Sai a lokacin Hajiya ta sauke hannunta, da alama zuciyarta ta fara sanyaya.
Ba tace masa komai ba kuma bata bar wajen ba.

Ganin wannan nasarar da ya fara samu ya saka shi cigaba da cewa “Hajiya a ganina da kin haƙura mu taimaki rayuwar wannan talikin yaron, wataƙila hakan ya zama silar rabautarmu duniya da Lahira, sannan na maki alƙawarin zan nemo iyayensa a duk inda suke a faɗin duniya don maida shi ga tsatsonsa kuma mahaifarsa.”

Yana kai nan a zancensa ya ga Hajiyarsa ta juya fuu ta yi gaba abinta ba tare da ta sake tamka shi ba.

Zahiri Hanne mai’aiki da Ƙasimu mai gadi basu ji daɗin wannan al’amari ba, don kuwa akan idonsu komai ya faru. Saboda bayan watsewar ma’aikatan ashe su basu tafi gaba ɗaya ba, wata kusurwa suka samu suka maƙe don ganin ya zata kaya, duk da basa jiyo sautinsu Mahmud ɗin.

Ganin juyowar Hajiya a sanyaye ya sagar masu da gwuiwa don da alama ta haƙura, cikin hanzari suka gudu daga malaɓarsu.

Shi kuwa Abdul har zuwa lokacin kuka yake ba ƙaƙƙautawa.

Miƙewa kawai Mahmud ya yi ya ja hannunsa ba tare da ya ce ƙala ba, ya shige da shi ɗakinsa ya rufo ƙofa.

Zama ya yi gefen gado yana dafe kansa da ya fara sara masa, zahiri baya son hayaniya, ga kukan Abdul da yake ji har cikin ƙoƙon zuciyarsa.

Don haka ya shiga rarrashin Abdul har sai da ya yi shiru sannan ya ce “Ka kwantar da hankalinka Abdul insha’allah ba inda zaka kana nan gidan tare damu.”

“Don Allah yaya ka taimake ni, wallahi in tak-kore ni bansan inda zanina ba, sai dai in koma daji.”
Abdul ya faɗa cikin dasasshiyar murya.
Sosai yake jin tausayin yaron a ransa, ya rasa inda zai saka ransa ya ji sanyi. Nan take ya tuna da zancen abokinsa Dr Yasir inda ya ke masa tuni da yanda Hajiya ta tsani nakasasshi da talakawa kuma ya nuna masa kada ya je gidan da yaron ya bar masa shi, amma fafur yaƙi.

Nan take yaji nadamar bijirewa shawarar amininsa.

Nan ya fara tunanin ko dai zai kira Dr Yasir ne ya nemi shawara? Sai kuma ya ji kunyar abinda ya masa. “Kai ina! Ba zan iya ba, ai abin da kunya.” Ya faɗa a ɗan bayyane.

Da yamma Mahmud ya shiga sashen Hajiya don gaidata anan ya tada maganar zaman Abdul a gidan, yana ƙara bata haƙuri ya ce “Ki ƙara haƙuri Hajiya na bawa Dr cigiyar sanduna, kafin nan zan nemo masa iyayensa na maida shi gida, bana son ya kuma shiga garari tausayi yake ban matuƙa.”

Hajiya ta nisa ta ce “Shi ke nan na fahimta kuma na amince, amma ka ci gaba da ajiye shi a sashenka, bana son ganin wulgawarsa ta gaban idona, tsoron fuskarsa nake.”

Murna ce ta bayyana a saman fuskarsa ya ce “Na gode sosai Hajiyata Allah ya ƙara girma.”
Tashi ya yi ya fice da murna.  Raka shi ta yi da ido a ranta ta yi wani zance wanda ita kaɗai tasan me ta ƙissima, ta yi murmushi itama ta tashi ta haye sama.

Bayan kamar kwana huɗu Maganar komawa ƙaro karatun da Mahmud zai yi ƙasar Spain ta tashi.

Dama tuni ya yi applying lokaci kawai yake jira, tsintar Abdul da ya yi shi ya mantar masa da tafiyar, sai gashi ƙwatsam abokinsa ya yo masa waya yana tunatar da shi wajibinsu ne su yiwa ƙasar zobe a wannan satin.

Sosai ya yi murna dama ya jima yana jiran lokacin amma tunawa da Abdul da ya yi ya ji kamar ya fasa tafiyar.

Sai kuma ya tuna ai Hajiya ta amince da zaman yaron a gidan don haka ya ci gaba da shirye-shiryensa a gaggauce ba tare da ya sanar da yaron tafiyar ba gudun kada ya tayar masa da hankali.

A daren ranar da zai wuce ya samu Hajiya a sashenta ya ƙara tuna mata da Abdul tare da damƙa amanar yaron a hannunta ya ce “Na yi waya da Dr ya ce ana kan bincike da zaran an samu sanduna zai zo ya sanar miki, sai ki bada kuɗin kawai ki karɓa masa pls Hajiyata ki mun wannan taimakon.”

Da farko ta so ta nuna masa rashin amincewarta amma sanin halin tilon ɗan nata ya saka ta bar abun a zuciyarta.
“Shi ke nan insha’allah! Allah ya bashi lfy.”

Sosai ya ji daɗin amincewarta da haka suka ci gaba da hirar bankwana domin ya sani gobe iwar haka baya ƙasar…
Hmmm! Yaya zata kaya bayan tafiyar Mahmud?

Anyah kuna ganin Hajiya zata bar Abdul ya zauna a gidan kuwa?🤔

To mu je zuwa dai don jin yanda zata kaya.
More comment more typing🥰

Ummu inteesar ce❤️❤️❤️❤

️*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

         *AND NOW*
    *HALITTAR ALLAH CE*

DEDICATED TO: Yar malam member ta halittar Allah ce fans group ina jin daɗin comment ɗinki sosai Allah bar ƙauna
________________________________
+
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

PAGE 55-56

Bayan ya koma sashensa ya tarar da Abdul zaune ya buga tagumi da duka hannayensa guda biyu ga hawaye dake bin kuncinsa.

Tsayawa ya yi ya kafe shi da ido, sai dai da alama Abdul ɗin ya yi zurfi a kogin tunani.

Girgiza kai Mahmud ya yi alamun tausayawa, ƙarasawa ya yi gunshi ya zauna daf dashi amma duk yaron bai ɗago ba, alamun ma bai san da zamansa a gun ba.

Sai da Mahmud ɗin ya dafa kafaɗarsa sannan ya yi firgigit kamar wanda aka tayar daga barci.

“Me ya faru Abdul?” Mahmud ya tambaya da damuwa a fuskarsa.
Don har a zuciyarsa baya son ganin damuwar yaron, jinsa yake tamkar ɗansa ko wani jininsa.

“Yaya missa kowa yat-tsani ganin huskata na? Missa  kowa bai son in zauna kusa garai?
Saboda banda lahiyar ƙahwa ko don ina da rabin huska? Abin na damuna…..”

Yana kai nan a zancensa ya fashe da kuka kamar an kunna shi.

Duk da bakomai Mahmud yake fahimta a Hausar yaron ba, amma ya fara jin wani abu saboda zama da Abdul ɗin.

Nan fa ya shiga rarrashin yaron yana bashi baki “Ka yi haƙuri Abdul, shi komai da ka gani muƙaddari ne daga Allah shi ke jarabtar bayinsa don ya gwada ƙarfin imaninsu. Insha’allah zaka warke watarana kamar ma baka taɓa yin ciwon ƙafa ba…”

“To ita huskata hwa tana gyaruwa?” Abdul ya jefo masa tambaya yana nuna bangaren dake shafe a fuskarsa da yatsa.

Sosai ya ƙara bawa Mahmud tausayi.

A ransa ya ce “Sai dai ka yi haƙuri Abdul wannan halitta ce ba zata taɓa sauyawa ba, haka Allah ya so ya nufe ka da zama, ba wanda zai iya canza maka halitta sai….”

Yana tsaka da zancen zucin Muryar Abdul ta daki dodon kunnensa in da yake cewa “Yaya huskata hwa? Bata gyaruwa koh?” Ya fada kamar zai yi kuka.

“A’a Abdul zata iya gyaruwa watarana kai dai ka ci gaba da addu’a kawai ka ji.”

Girgiza kai Abdu ya yi alamun “Eh”

Har Mahmud ya miƙe zai wuce ciki ya tuna abinda ya shigo da ƙudurin yi.

Nan ya ji damuwa ta lulluɓe shi. Amma bashi da wata mafita da ya wuce ya sanar da yaron tafiyarsa don ta yiwu ko da zai wuce da safe yaron na barci ba kuma zai iya tashinsa ba.

Dawowa ya yi ya zauna.
“Abdul!” Ya kira sunan yaron.

Yaron ya ɗago ya kalle shi.

Sai da ya yi jim, sannan ya ce “Gobe zan yi tafiya, zan je ƙasar Spain Amma ba jimawa zan dawo…”

Ai tun bai gama rufe bakinsa ba, Abdul ya rungume shi ƙam-ƙam yana faɗar “Don Allah yaya kat ka tahi ka banni Mama bata sona kora ta zata yi.”

“Ba zata kore ka ba mun yi magana da ita ka kwantar da hankalinka.” Da haka ya ci gaba da lalaɓa shi har ya samu ya masa wayo ya yarda.

A haka suka kwanta rungume da juna, sosai Abdul ya ƙanƙame shi don ganin yake kamar guduwar zai yi ya bar shi.

A wannan daren Abdul kasa barci ya yi sai wuraren uku na dare barci ɓarawo ya yi awon gaba da shi.

Wannan dalilin ne ya saka da safe ya kasa tashi da wuri sai ƙarfe 9 na safe ya farka.

A hankali ya buɗe idon shi ya sauke su kan katifar sai dai me? Wayam ba Mahmud ba dalilinsa.

Nan ya shiga ƙwalawa Mahmud ɗin kira “Yaya! Yaya!!” Jin shiru ya yi tunanin ko yana banɗaki ne, can kuma ya tuna da maganar tafiyarsa ta jiya kenan bai haƙura ba?

Hankalin Abdul ya yi ƙololuwar tashi. Dabara ya yi ya sako daga kan gadon yana rarrafe tare da duba ko wane lungu da saƙo a part ɗin ba Mahmud ba dalilinsa sai kayan break fast da ya ajiye masa, hakan ya tabbatar masa da Mahmud ya yi nisa da shi ya tafi ya bar shi.

Don haka ya fashe da kuka tare da zama guri ɗaya yana raira waƙa cikin kuka “Yayana ka tahi ka banni, nii Abdul ya zan yi da raina…. Hajiya bata hwa sona ya zata zauna da ni kuma… Don Allah yaya ka dawo ni Abdul na ga ta kaina, kai kaɗai ke sona a duniyata yanzu.”

Haka ya cigaba da rera kukansa tare da waƙa har ya gaji amma ko mai kama da Mahmud bai koma gani ba.

Zuwa lokacin tuni jirginsu Mahmud ya lula cikin gajimare sai dai fatan Allah ya sauke su lafiya.

Tun bayan dawowar Hajiya daga rakiyar yaronta a airport take zaune a falonta tana shaƙatawa tuni ta manta da wata amana da ya bar mata har wajajen azahar sannan ta tashi ta shiga ciki domin ta shirya ta fita.

Sai bayan ta shirya ta fito zata fita ne da ta ga sashen Mahmud ta tuna ajiyarsa.

Ya mutsa fuska ta yi tana faɗar “Na manta da ajiyarka son.”

Hanne ta ƙwalawa kira da gudu ta ƙaraso ta ce “Gani rankiya daɗe.”

Cikin ya mutsa fuska ta ce “Ki ɗebo abinci ki kaiwa waccan halittar dake rayuwa a can sashen.” Ta faɗa tana nuna sashen Mahmud da hannu.

“To ranki ya dade.” Hanne ta faɗa tare da juyawa ciki don cika umurnin uwargijiyarta.

Ita kuwa Hajiya ɗauke kai ta yi tare da wuce parking space ba tare da ta kuma kallon sashen ba ma bare ta je duba halin da amanarta ke ciki.

Ko da Hanne ta je kicin sai da ta tsaya ta ciji yatsa sannan ta fara zuba masa abincin, irin ƙanzon nan na ƙasa ta karkaro ta zuba masa sannan ta ɗebo gishiri mai ɗan dama ta ƙara masa ta yanda ba zai iya ci ba, ta ɗauka ta fito. Ko da Baba Ladi ta haɗu da ita a kofar fitowa daga kitchen din ta ce mata “Hanne wa zaki kaiwa wannan ƙanzon? Ba dai bil adama zaki bawa wannan abincin ba?”
Sai ta ya mutsa fuska ta ce “Almajirai zan bawa ai su suna so ya fi a zubar.”

Girgiza kai Baba Ladi ta yi ta shige kicin ɗin abunta tana yiwa Hanne fatan shiriya don yanzu ta sani tana ƙara magana zata iya zaginta.

Ita kuwa Hanne tsaki ta ja tana faɗar “Gulmammiyar tsohuwa kawai ‘yar sa’ido. Wallahi kowa ya shiga gonata a gidan nan sai na aske shi tas, bari dai na gama da wannan mummunar halittar na dawo kanki daga baya.” Ta faɗa ƙasa-kasa tare da wucewa zuwa sashen Mahmud don kaiwa Abdul abunda take kira da abincinsa.
To fah readers? Me Hanne ke shirin aikatawa..
Wannan fa shi ake kira da rijiya ta bada ruwa guga ta hana.
Mu je zuwa dai don ganin ya za’a garƙe.

More comment more typing

Follow me on Wattpad @Ruky_i_lawal

Instagram: Rukayyarh_ibraheem

*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

         *AND NOW*
    *HALITTAR ALLAH CE*+

DEDICATED TO ALL MEMBERS OF HALITTAR ALLAH CE FANS GROUP.

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
PAGE 57-58
Ƙofar Sashen a buɗe take don haka ta shige kai tsaye.

Lokacin Abdul na kwance kan doguwar kujera fuskarsa har ta kumbura ɗayan idonsa ya yi ja, da alamu ya ci kuka har ya ƙoshi.

Jin an banko kofar da ƙarfi ya saka shi zabura, ya tsorata sosai.

Hanne ta ƙaraso gabansa tana tamke fuska, sannan ta miƙa masa abincin.

“Kai Dabba tashi ga abincinka.” Ta faɗa.

Baki na rawa ya ce “to.” Tare da amsar kwanon don tun ranar farkon zuwansa gidan yake tsoronta.

Fara ci ya yi hannu baka hannu ƙwarya saboda matsananciyar yunwa da ya jima bai ji irinta ba.

Lomar farko da ya yi ya fito da idonsa waje, kamar zai dawo da abincin waje. Sai kuma ya tuna ai ya saba da irin wannan, tunda ya ci wanda bai ma kai wannan tsafta da daɗi ba.

Tsawa ta daga mishi “Ubanwa kake fiddowa ido? Nakasasshen banza maza ka cinye shi tas. Kuma wallahi idan ka sake ka gayawa wani a cikin gidan nan kalar abincin dana baka sai na ƙwaƙule ma ɗayan idon da kake da kowa ya huta. Dama miye amfanin ka?”

Ɗaga mata kai ya yi alamar to. Ya ci gaba da tura abincin yayin da ta yi ƙwafa ta juya ta fice daga ɗakin.

Hawaye ne suka ci gaba da bin kuncin yaro Abdul. Kukan zuciya yake tare da kuka na sarari. Maganganu Hanne sun tsaya masa a rai, haka sun zauna a kwanyarsa daram.

“Dama ashe bani da amfani shiyasa mutane basa sona?” Ya faɗa a ransa.
Nan fa zuciyarsa ta yi ta masa saƙe-saƙe akan rayuwarsa.

“Tabbas banda amhwani ga kowa, don ga shi sauran yara dut suna makaranta wanga lokaci amma ni gani nan kulle cikin ɗaki saboda kowa tsoro na ya kai.”

Ya faɗa yana daɗa fashewa da kuka.

Bayan kwana biyu gidan ya gama yiwa Abdul zafi don nan ɗin ma dai kamar gidan Kande, ya zame masa inuwar bagaruwa ga sanyi ga ƙaya.

Don haka ya fara tunanin guduwa sai dai ba hali tunda ƙafafunsa basa tare dashi (sanduna). Dole ta saka ya haƙura don ba zai iya guduwa da rarrafe ba.

Haka ya cigaba da addu’ar neman mafita, dama yaron akwai son ibada ko wacce sallah bata wuce shi. Ko lokacin da yake jeji da ya kwatanci lokacin sallah ya yi koda bai samu ruwan alwala ba a haka yake sallarsa don bai ma san da zama taimama ba bare ya iya ta.

STORY CONTINUES BELOW
Allah maji roƙon bawa, a kwana na uku da tafiyar Mahmud Likitansu ya samo sandunan bayan shafe tsawon makwanni yana nema. Don haka ya kawowa su Hajiya har gida kamar yanda ya alƙawartawa Mahmud.

Haka ma ya nemi akai shi ga Abdul don ya gwada sandunan ya ga ko zasu ma yaron.

Hajiya ce ta masa jagora har sashen a karo na farko da ta leƙa sashen tun bayan tafiyar ɗan nata. Wannan ma don bata son likita ya zargi wani abu har ya faɗawa Mahmud ne.

A bedroom suka same shi zaune akan tiles ya buga tagumi sai sana’arsa yake ta hawaye.

Da sauri Hajiya ta dube shi “Subhanallah! Abdul me ya same ka kake kuka? Ya ma aka yi ka rame ko baka cin abincin da ake kawo maka ne?”

Kallon zargi likitan ya mata, sannan ya dubi yaron ya ga alamun tsoron hajiyar tattare da shi.
Girgiza kai kawai ya yi alamun tausayawa da mamaki ya ce “Yaro karɓi waɗannan mu gani ko za su maka.” Ya miƙa masa.

Karɓa ya yi ya miƙe, sai dai sun masa tsayi kaɗan. Cikin Sa’a kuwa aka yi dace da irin sandunan nan ne masu maɓallai da ake iya ƙara tsawonsu ko ragewa.

Don haka likitan ya rage masa su ta yanda zasu masa dai-dai.

Daga nan ya yi Sallama da Hajiya ya fice daga gidan yana tausayawa wannan yaron da masa addu’ar samun lafiya.

Amma ya ƙudurce a ransa zai faɗawa Mahmud gaskiyar halin da yaron ke ciki, don ga dukkan alamu bai sani ba.

Hajiya kuwa tana ganin tafiyar likitan ta fara tsara yanda zata kori yaron daga gidan ba tare da kowa ya sani ba bare a samu mai bawa ɗanta labari idan ya dawo.

Washegarin ranar tun sassafe ta tashi da shirye-shiryen taron baƙuwarta (Anty Habi) yayarta da zata zo daga Taraba state. Don haka ta yi amfani da damar ta aiki duka ma’aikatanta nesa, yanda zata kori yaron cikin sauƙi.

Hanne kawai ta rage don haka ta ce “Yawwa Hanne zamu yi wani sirri kada ki sake kowa ya ji ko ya ganki a lokacin da kike aiwatar da shirinmu, don ko tun za’a tafi ake shiri ba sai an dawo ba.”

Hanne ta ɗaga kai tare da faɗar”Na fahimta aikin sirri ne za’a yi ko?

Eh, yanzu ki je Sashen Son ki tattare duk abinda yake mallakin wannan halittar sannan ki fito da shi a sirrance ki je ki hau abun hawa ku yi nesa sosai da unguwar nan, ta yadda ba zai taɓa gane ta ba bare ya dawo. Kin ji ni koh? Bana son a samu kuskure, ki tabbatar angama da wannan matsalar kafin yaya Habi ta ƙaraso, dama sanduna nake jiran ya samu.”

“Haka ne ranki ya daɗe kin ga sai mu gayawa Boss cewar guduwa ya yi ba da sanin kowa ba.” cewar Hanne.

Hajiya ta yi murmushi tace “Maza ki je lokaci na tafiya, ki kula bana son a samu kuskure.”

Kuɗin abun hawa Hajiya ta miƙa mata sannan ta tsaya don ganin fitowar su.

Cikin zumuɗi Hanne ta nufi sashen tana murnar burinta ya cika.

Duk yanda Hajiya ta faɗa mata haka ta aikata.
Janyo shi ta yi har gaban Hajiya.
Abdul na kuka yana roƙon Hajiya faɗar yake “Don Allah Mama ki temake ni ki banni in rinƙa kwana nan, in yasso da rana in tahi inyo Bara cikin gari in samu abinci amma kat ki kore ni ina son ƙara ganin yayana ina son shi matuƙa.”

Hajiya takai ƙololuwar ƙuluwa ta daka mashi tsawa tana faɗar “Yi mun shiru, wato dai so kake ka tona mun asiri a nan unguwar ma kake tunanin yin Bara?
Mai da dubanta ta yi ga Hanne “Zaki fice mun da shi ko sai sun dawo tukunna?”

Ganin yanda ran Hajiya ya ɓaci yasa ta tungume shi ta fita ta ƙofar baya ta tare abun hawa.

Sai da suka yi tafiyar awa ɗaya da kusan rabi a abun hawan, har sai da mai abun hawan ya gaji ya ja ya tsaya tare da faɗar “Malama na gaji da yawo ina zan sauke ki ne wai?”

“Nan ma ya yi ai.’ Ta faɗa tana fitowa daga abin hawan fito da Abdul ta yi ta ɗauko masa kayansa ta ajiye masa.

Ta sallami mai abun hawan.
Abdul sai faman kuka yake, dariya ta yi tace “To dodon gidanmu ni na tafi Allah ya kawo wani mai rabon wahalar kamar Boss.”

sannan ta taka da ƙafa ta nufi titi don neman wani abun hawan. Ta yi hakan ne don kada a samu wata matsala.

Da dai Abdul ya ga tabbas ta tafi, ga shi gurin shiru-shiru ba kowa, irin bayan garin nan ne ba kowa sai wanda hanya ta biyo da shi.

Ɗaukar kayansa ya yi cikin ƙarfin hali ya matsa gaba, nan ya samu ɗan wani ɗakin langa-langa da gani irin na masu gadi ne ko ‘yan ci rani da basu da muhalli.

Don haka ya shige ciki tare da ajiye kayansa ya bazama cikin gari don yin Bara ko ya samu abinci don yunwa yake ji sosai.

@@@@@@@@

Bayan barinsu gidan da kamar awa Uku Anty Habi ta ƙaraso.

Da murna Hajiya ta tare ta tuni ta manta da wani Abdul kowa ya dawo sai shagali ake.

Anty Habi na tsaka da cin abincin taron baƙin da aka mata.
A hankali suka fara jiyo-hayaniya da iface-iface abun sai ƙara daɗuwa yake da kaɗan-kaɗan.

Nan fa hankalin Hajiya ya fara tashi dama gata da ɗan banzan tsoro kuma tana da hawan jini.

Zuwa can aka callara wata ƙara mai Masifar ƙarfi da take barazanar fasa masu dodon kunne……
Hmmm! Tofah readers meke shirin faruwa a gidan Hajiya ne?🤔🤔

Ina Abdul ya nufa, rayuwar Bara zata riƙe shi kuwa?

Waima shin ina labarin Hajiya Hasina da yan uwan Alhaji Munir?

Shi kanshi Alhaji Munir ɗin meke faruwa da shi?🤔🤔

Don samun wadannan amsoshin ku juri bibiyar alƙamin Ummu inteesar don jin ya zata kaya.

Kada ku manta more comment more typing.

UMMU INTEESAR CE😍🥰❤️❤️

*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

         *AND NOW*
    *HALITTAR ALLAH CE*
Ga masu buƙatar na tallata masu hajojinsu a shafukan littafina dama shafukana na sada zumunta kamar instagram, whatsapp, telegram, facebook da sauransu sai su tuntuɓe ni ta wannan number __08109634202__+

Kowacce irin haja je gareka zamu tallata ma cikin rahusa insha’allah.

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
PAGE 59-60

Nan fa mutanen dake gidan suka birkice, yaya Habi ta ajiye cokali tana neman guduwa amma ina! Kafin ta gudun abun ya ƙaraso.

A kiɗime Hajiya ta ɗaga kanta don ganin menene ke wannan Masifar ƙarar. Wani curin dunƙulallen abu ne a hankali yake ƙara girma har faɗinsa ya mamaye ilahirin inda yake. Zuwa can kuma ya rabu gida goma.

Hanne da tashin hankali ya korota daga kitchen ta nufo falon, a nan ta tarad da sabon tashin hankali. Amma duk da haka bata yi kuskuren komawa kitchen ba, domin kuwa duk abinda ya koro ɓera har ya faɗa wuta ba ƙaramin abu ba ne.

A hankali waɗannan curin suke mulmulowa sai hayaƙi suke fitarwa ga wasu sautukan Muryar yara iri-iri dake fitowa daga curin. Suka nufo inda yaya Habi, Hajiya da Hanne suka manne waje ɗaya don tsoro..
Wani tsalle yaya Habi ta daka, tana yin sa’ar ƙetare abun ta yi wuf ta faɗa ɗaya daga cikin ɗakunan dake falon ta rufo da makulli tana mayar da ajiyar zuciya.

Hajiya kuwa ganin curin na nufo ta, tun bai ƙaraso gare ta ba hankalinta ya gushe ta fadi a gun kafin ta kai ga suma ta ji wata mummunar murya na faɗar “Kin tsani ganin Musakai a rayuwa koh? To kishirya don kina dab da tsanar kanki.” Daga haka aka bushe da matsananciyar dariya mai ƙara birkita birkitacce.

Kafin idonta su ƙarasa rufewa ta hango bayyana wata mummunar halitta a gabanta mai ido ɗaya saman hanci da wani wagegen baki. tsaya faɗa maku munin halittar bata lokaci ne don tafi Abdul muni nesa.

Haka halittar ta ƙarasa ga hajiyar ta rungume ta. A take idon hajiyar ya rufe ruf alamun ta suma.

Hanne kuwa yau taga tashin hankali da bata taɓa ganin irinsa ba. To wai duk me wannan abun ke nufi? Me ya janyo musu wannan masifar? Tana tsaka da wannan tunanin ta ji an sure ta anyi sama da ita.
Waige-waige ta hau yi tana ƙwala ihu amma bata ga abinda ke riƙe da ita ba. Kawai ta ganta a sama.

Can kuma aka makata ga ƙauren ƙofar falo ta faɗo a galabaice.

Zahirin siffar Abdul ce ta bayyana a gabanta, amma wannan ba Abdul bane don ya ninka tsawo da kaurinsa sau biyar.

A haka ya nufota ya shiga yin Ball da ita tun daga ƙofar falon har zuwa harabar gidan.

Sai ihu take amma a banza banda Ƙasimu mai gadi ba mai jinta. Sauran ma’aikatan gidan duk barci suke.
Shima Ƙasimun ashe rabon ya girbi abinda ya shuka ne.

STORY CONTINUES BELOW
Don haka aljani Mazkud da ya zo a siffar Abdul ya haɗe su gu ɗaya shida Hanne ya ci gaba da wahalar da su har zuwa lokacin da ya tabbatar sun karɓi saƙo sannan ya ɓace yayin da suke jiyo kakkausar muryarsa na faɗar “Sai ku kiyaye gaba, ko wane mai kama da Abdul kuka kuma wulakantawa zamu gamu ne.” Daga haks suka ji tsit kamar Muryar bata taɓa wanzuwa a gidan ba..

Ai da gudu suka watse kowa ya nufi maɓoyarsa.

@@@@@@@@@@@@

A bangaren Abdul kuwa haka ya cigaba da yawo cikin gari yana Bara, ko kwano baya da daƙyar aka samu wata mata ta taimaka ta ba shi kwanon. Haka ya yi ta yi, wani lokacin idan mutane suka gan shi su gudu musamman yara. Masu ƙarfin halin cikin mutanen ne ke tsayawa su ba shi haƙuri, masu abin ba shi su bashi.
Idan yamma ta yi ya dawo malaɓarsa ya zauna.

Haka ya ci-gaba da aikatawa tsawon shekara biyu zuwa uku, har wasu daga cikin mutanen yankin suka fara sabawa da shi suna saka shi aiki kamar wanki,wanke-wanke suna biyan shi. Don a lokacin ya kai shekaru 16 a rayuwa.
Ɓangaren Mahmud kuwa har zuwa lokacin yana waccan ƙasar bai san halin da ake ciki ba. Don kuwa tun bayan fitar Likitansu daga gidan ya samu kiran gaggawa zuwa ƙasar Turkiyya, wannan dalilin ne ya mantar da shi kudurinsa na sanar da Mahmud halin da ya samu Abdul ciki.
Shiko Mahmud duk sanda zai kira Hajiya sai ya nemi ta haɗa shi da Abdul su gaisa amma sai ta samu karyar data masa. Daga ƙarshe ma tace masa ta maida yaron boarding school ne. Sosai ya ji daɗin ganin Hajiyarsa ta karɓi yaron. Bai san cewa ta ɗinke shi a bai-bai ba ne.

@@@@@####

A gidan Hajiya bayan ƙura ta lafa yaya Habi ta buɗe ɗakin ta fito. Nan ta samu Hajiya a some, kinkimarta suka yi zuwa asibiti. Sai da likitoci suka kwashe tsayin wasu awanni a kanta kafin ta dawo hayyacinta, amma jininta ya hau sosai.
Kuma tun tashinta take jin ƙafarta ɗaya wani iri. Sosai ƙafar ke ciwo, likitoci sun yi iya ƙoƙarinsu ba su gano komai ba. Daga ƙarshe suka yi tunanin ko hawan jinin ne ya taɓa ƙafar don haka suka ɗora ta akan magani.

Tun a lokacin Hajiya ke fama da matsanancin ciwon ƙafa, anyi maganin har an gaji.

Bayan dawowar su gida yaya Habi ke tambayar musabbabin wannan tashin hankalin.
Cikin damuwa Hajiya ta dube ta tace “Wani nakasasshen yaro ne Son ya zo da shi nan gidan, da zai tafi ya ban amanarsa, shine na saka aka jefar da shi. Dalilin haka aljanu suka zo mana a siffarsa suka tsorata mu don ɗaukar masa fansa. Wannan shine tunani na.”

Girgiza kai yaya Habi ta yi tace “Meyasa kika kore shi?”

“Halittarsa nake tsoro, don wannan bai yi kama da mutane ba,rabin fuskarsa fa a shafe take.”

Zaro ido ta yi tare da nisawa ta ce “Tab! Wannan yaron sai kace yaron da Zulaihar Baba ta haifa? Kinsan lokacin da ni aka je Sokoto suna, amma a ƙagare na yi sati ɗayan ni da na je da zimmar zaman jego.”
Ita ma Hajiyar fiddo ido ta yi tace “Yaya dama ƙanwata da nafi so kalar abinda ta haifa kenan shine baku sanar mun ba? Kin san fa lokacin Alhaji yana ciwon ajali shiyasa ban je ba. Amma kuka ce mana yaron kyakkyawa ne kuma yana ƙalau?”

Shiru yaya Habi ta yi kamar ba ita aka tambaya ba.

Nisawa ta yi ta ce “Allah sarki ƙanwata mai yawan sona, kin mun rana, kin zame mun lema a lokacin da rayuwata ta shiga wani yanayin ƙunci. Ina ma ace a lokacin da kika mutu na san wannan, da duk tsanata da Musakai sai na riƙi wannan yaron naki hannu biyu na masa gata, da ban wulaƙanta ko da mai irin siffarsa ba…”

Ta faɗa tana hawaye.

“Allah ya jikanki da Rahama ƙanwata. Na miki alƙawarin zan je har Sokoto don karɓo yaronki daga hannun dangin ubansa, ba wanda zan bari ya wulakanta jinina. Ko waye kuwa ya yi kuskuren aikatawa sai na yi Shari’a da shi.”

Haka ta yi ta sambatu har sai da yaya Habi ta dakatar da ita da faɗar “Ya isa haka, haƙuri zaki yi, ki ci gaba da masu addu’a.”

@@@@@@@@@@@@@@

Bayan kamar watanni bakwai da wannan maganar Hajiya ta shirya zuwa Sokoto don karɓo yaronta.

A da taso ta bari har ta ji damar ƙafa, amma da taga ba alamun haka, ta ce “Ina amfanin baɗi ba rai?” Gwanda ta je tun lokacin da take da abun yi.

A ranar wata Assabar Hajiya tare da wani kawunsu (dake zaune a nan Kaduna) suka yiwa Birnin shehu dirar mikiya…..
To fah! Readers Hajiya na neman yaronta, wanda ta wulakanta fa waye?

Ya zasu kwashe tsakaninta da a halin Alh Munir dama Hajiya Hasina?

Ya rayuwa Abdul zata ci gaba da wakana?.

Ku biyo alƙalamin Ummu inteesar don ji ya zata kaya.

More comment more typing

Ummu inteesar ce.❤️😍

*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

         *AND NOW*
    *HALITTAR ALLAH CE*

Ga masu buƙatar na tallata masu hajojinsu a shafukan littafina dama shafukana na sada zumunta kamar instagram, whatsapp, telegram, facebook da sauransu sai su tuntuɓe ni ta wannan number __08109634202__

Kowacce irin haja je gareka zamu tallata ma cikin rahusa insha’allah.

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com+

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
PAGE 61-62

Daga shigarsu garin basu zame ko’ina ba, sai tsohon gidan  Alhaji Abbas dake ƙofar kaɗe.

Sai dai me? Tana shiga gidan taga sauye-sauye. A ciki kuwa harda sauyawar mutanen dake rayuwa a cikin gidan. Duk da sau ɗaya ta taɓa zuwa garin kafin ma Zulaiha ta haihu.

Anan mutanen gidan suka shaida masu sun sayi wannan gidan ne daga magada shekaru da yawa da suka shuɗe.

Duk dai anan suka samu labarin mutuwar Alhaji Abbas ɗin.

“Allahu akbar! Allah ya masa Rahama. Yanzu don Allah a cikinku ba wanda yasan inda iyalansa suka koma da zama?”

Iya (tsohuwar gidan) ta ce “Gaskiya dai bamu sani ba. Amma dai makwacciyagga tamu ta sani, don ta bani labarin da ita anka rakke su lokacin da sunka koma sabon gida. Bari insa a kira ta.”

Nan ta tashi ɗaya daga cikin jikokinta ya kirawo Asabe. Asaber ce ma ta raka su Hajiya har gidan innarsu Munir dake Miyatti Allah.

Tashin hankali nan ma suka tarar da labarin mutuwar Hajiya saudatu (Mahaifiyar Munir).

Suka mata fatan samun Rahama.

Bayan sun huta sosai sun ci abinci Hajiya ta nemi da a kira mata Munir don tana son yin magana da shi. A nan kuma ta bayyanar da ƙudurinta na son a bata ɗan yar’uwarta zata tafi da shi gidanta.

Jin wannan zancen ya ɗagawa inna hankali sosai don ta san dai ya zama dole su faɗawa hajiyar gaskiya. Kuma ɗanta za’a zarga da sakaci. Hakan yasa jikinta ya yi laƙwas.

Bata yi gaggawar faɗa masu gaskiya ba. Ta aika aka kira mata Munir.

Da sallamarsa ya shigo falon da suke Zazzaune suna jiran ƙarasowar sa.

“Wa’alaikumus salam! Hjy inna ta amsa masa.”

A hankali ya ƙaraso cikin falon, ya ji mamaki sosai da yaga baƙin fuskoki a dai-dai lokacin.

Gaida su ya yi sannan ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun falon.

“Sannu da zuwa Alhaji Munir.” Hajiya ta faɗa.

Da mamaki ya kalle ta yana so ya gano inda ya san wannan fuskar amma ya kasa tunawa. (Da yake Hajiya Fatima tana kama sosai da Zulaiha ƙanwarta Maman Abdul).

STORY CONTINUES BELOW
Ganin irin kallon kurillar da yakewa hajiyar ya saka Hajiya inna ta ce “Na san baka gane su ba koh?”

Ɗaga kai ya yi alamun eh.

Hjy inna ta cigaba da cewa “To Waɗanga da kaggani ‘yan’uwan matakka na Zulaiha, waɗanda ak-kaduna. Wagga sunanta Hajiya Fatima yayar Zulaiha ta uwarsu guda. Shiko wanga…
Ta nuna namijin da suke tare.
“Suna nai Alhaji shu’aibu shi kuma kawon Zulaiha na.”

Tun da ta fara magana Alhaji Munir ke bin su da ido yana son ya tuna mai irin wannan sunan da aka ambata. Amma sam ƙwaƙwalwarsa ta ƙi ba shi damar hakan.

Hajiya ce ta karɓe zancen da cewa “To Alhaji Munir yanda hajiyarka ta maka bayani haka zancen yake. Ina ƙara baku haƙuri lokacin da Zulaiha ta rasu mijina ne ya rasu a daidai lokacin shiyasa ban samu zuwa ba. Allah ya mata Rahama.”

Ya amsa da ameen ba don ya san wanda akewa addu’ar ba.

Hajiya ta cigaba “Abunda yake tafe damu shine, na zo karɓar yaron da ‘yar’uwata ta mutu ta bari domin ya koma hannuna da zama.”

Wani kallon uku saura kwata alhj Munir ɗin ya mata, jin maganganunta yake kamar tatsuniya “wane ɗan kuma wannan take magana, sannan wace ‘yar’uwarta ta bar mun ajiyar ɗa? Ji wani rainin hankali.” Ya faɗa a ransa.

Ganin bai ce komai ba ta cigaba. “Tunda na samu labarin yaron na da buƙatar kulawa ta musamman na ji ya kamata in karɓo shi don ba zan yarda ɗana ya fuskanci  wulaƙancin matar uba ba.”

Miƙewa tsaye Alhaji Munir ya yi yana faɗar “Ki yi hanƙuri Hajiya da alama ke yi batan kai, baki zo gidan dai-dai ba. Don ni da kika gani ban taɓa haihuwa ba, mata guda gare ni Hajiya Hasina kuma har yanzu bata taɓa ko bari ba tsawon shekara 9 kenan.”

Daga haka yiwa hjy inna Sallama ya juya zai bar falon.

Hajiya ta miƙe da nufin dakatar da shi amma hjy inna ta mata alamar ta dakata da hannu.

Haka ya bar gidan rai a ɓace.

Bayan fitarsa Alhaji Shu’aibu ya kalli Hajiya inna. “To me hakan ke nufi kenan? Bamu gane kan wannan ɗan naki ba.”

Doguwar ajiyar zuciya ta sauke ta ɗan yi tari irin nasu na tsoffi sannan tace “Sai hanƙuri muma nan hanƙuri mukai da shi tun bayan mutuwat Zulaiha yak-kasa dawowa dai-dai. Daƙyar aka shawo kainai ma yay-yi aure, lokacin ya hwara samun natsuwa amma yanzu da yar- rasa……”

Sai kuma ta yi shiru.
Taya zata iya gaya masu Abdul ya ɓace.

“Muna jinki inna me ya rasa? Ina kuma ɗan namu ko sunansa baki kama ba duk a labarin naki.”

Wata ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce “Hajiya,Alhaji sai dai ku yi haƙuri Abdulrazaƙ ya ɓata wanda tun bayan ɓatan nasa ne Munir ya zama tamkar zautacce….”

Ai tun bata ƙarasa ba Hajiya ta miƙe tsaye duk da ciwon ƙafar da take fama da shi. Ta dafe kirji Wane Abdulrazaƙ? Ba dai ɗan namu ba?”

“Sai dai hanƙuri amma shi yat-ɓace.” Faɗar hjy inna.
Ba shiri Hajiya ta koma ta zauna.
Kawu Alhaji ne ya yi ƙarfin halin tambayar mafarin ɓatarsa da kuma yanda aka soma.

A gajarce hjy inna ta labarta masu abinda ta sani.

Daga ƙarshe dai suka nemi akai su gidan Alhaji Munir don ganawa da matar ubansa da kuma sauran waɗanda abun ya faru akan kunnensu.

Daƙyar suka yarda suka bari har safiya ta waye a kai su gidan. Kasancewar lokacin dare ya fara yi.

@@@@@@@@@@

Tun ƙarfe 12 na washegarin ranar Su Hajiya suka yiwa gidan Alhaji Munir tsinke.

Haka Hajiya Hasina ta tarbe su ba yabo ba fallasa tun ma bata san ko su su waye ba.

Bayan sun gaisa sama-sama Hajiya ta masu bayanin ko su suwaye da kuma abinda ke tafe dasu.

Nan take hajiya Hasina ta zama cikakkiyar yar wasar kwaikwayo don kuwa kuka ta saka tana faɗar “Allah sarki ɗana Abdul ina ma ace kana nan ka ga dangin Mamanka, ga shi yau sun zo nemanka amma ka masu nisan da ba zasu taɓa iya cimma ka ba.”

Ta kuma fashewa da kukan munafurci.

Su dai duk abun nan da take da ido kawai suke rakata, ba don sun yarda da ita ba.

Barin ma kawu Alhaji da yake tsohon lauya. Lafuzanta kaɗai sun isa tabbatar masa da zargin da yake a kanta.

Hakanan suka tambaye ta abubuwan da suka faru. Sannan suka saka aka tara masu ma’aikatan gidan suma suka faɗi iya abinda suka san ya faru a ranar dama lokacin da ake ta fafutukar nemansa.

Bayan tattara waɗannan bayanai suka bar gidan lokacin duk Alhaji Munir yana kasuwa.

Kafin su tafi Kawu Alhaji ya karɓi number Baba direba don ya gan shi dattijo mai kamala sannan da alama akwai sauran zance a bakinsa.

Hmm! To fah! Wannan zazzafar chakwakiya dake shirin faruwa ta saka alƙamina ya kubuce mun.

Kome zai faru idan suka gano an batar masu da yaro ne?

Yaya hjy zata yi idan ta gano ɗan data wulaƙanta shine yaron da ta fito nema ruwa a jallo harda shan alwashi akan wanda ya wulakanta mata shi?🤔🤔

Abdul fa yana ina yanzu?🤔

Mu je zuwa dai wai mahaukaci ya hau kura.

More comment more typing…..

UMMU INTEESAR CE🥰🥰❤️🥰

*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

         *AND NOW*
    *HALITTAR ALLAH CE*
Ga masu buƙatar na tallata masu hajojinsu a shafukan littafina dama shafukana na sada zumunta kamar instagram, whatsapp, telegram, facebook da sauransu sai su tuntuɓe ni ta wannan number __08109634202__+

Kowacce irin haja je gareka zamu tallata ma cikin rahusa insha’allah.

*WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GA: 11STARS INDEED*

1:Haupha
2: Zayyeshatul humaira
3:Jannat m Nasir
4:Maryam Nasir (manab)
5:Sweery
6:Real Nana A’isha
7:Maryam Ibrahim (Doctor maryam)

Da sauran cikinmu waɗanda ban ƙarƙare kirgawa ba.

Allah ya ƙara mana haɗin kai.🥰🥰

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

PAGE 63-64

Bayan komawar su masauki da dare Kawu Alhaji ya kira Baba direba suka gaisa.

A lokacin Baba direba ya koma gidansa don haka ya samu nutsuwar yiwa Kawu Alhaji bayanin abinda ya sani tiryan-tiryan. Sannan ya ƙara da cewa “Ni tuntuni na ɗiga ma Hajiya ayar tambaya, Don ko da walakin goro a miya. Ban nutsu da ita ba nafi tunanin ko akwai maƙarƙarshiyar data ƙulla duk da a zahirance baka ce haka ba. Kuma ba hujja ɗaya ƙwaƙƙwara da za’a kamata da ita.”

Godiya Kawu Alhaji ya masa ya kashe wayar. Koda ya shiga ya kira Hajiya Fatima a keɓe ya gaya mata yanda suka yi da Baba Direba.

Jin haka ya saka ranta ya ɓaci matuƙa, don haka tasha alwashin sai ta yi Shari’a da Hajiya Hasina in har suka tabbatar da zarginsu a kanta.

Wannan dalilin yasa  ta ƙi komawa Kaduna, sai Kawu Alhaji ne ya koma saboda iyali da aikinsa, ita kuma ta zauna a nan tana saka ido a al’amurran rayuwar gidan Alhaji Munir.

Tana so ta gano dalilin ɓacewar hankalinsa da har ya saka ya manta da ɗan lelen ɗansa kuma amanarsa.

@@@@###@@@
Abdul kuwa ya ci-gaba da rayuwa a cikin mutanen dake tsoronsa kuma suka tsane shi.

Ganin idan ya durfafo guri jama’a na watsewa ya saka ya ɗaure kayansa ya ƙara matsawa gaba a lokacin.

A haka ya cigaba da rayuwa idan yaga an tsane shi a guri sai ya matsa gaba. Kwanci ta shi har Allah ya sada shi da mutanen wannan unguwar da ya rayu tsawon shekara biyu a cikinsu yana masu wanki, wanke-wanke da ƙananan ayyuka, a cikin omon da sabulun da yake ragawa yakewa kansa wanka da wanki.

Wata rana ya fito Bara daga gidan wani Alhaji mai hannu da shuni, ya samo lafiyayyen abinci harda nama. Ya zauna yana ci a ƙofar gidan sai ga wani Almajiri ya zo ya zauna daf da shi.

STORY CONTINUES BELOW
Ko magana bai masa ba kawai ya kaɗa hannunsa a kwanon yana ci hannu baka hannu ƙwarya.

Abdul bai dakatar dashi ba, kallonsa kawai ya yi ya girgiza kai yana tausayin rayuwa irin tasu ta mabarata. Da gani wannan yaron yunwa ta addabe shi ne.

Bayan sun gama cin abincin sun sha ruwa almajirin ya kalli Abdul ya ce “Abokina bagode maka. Wace makaranta kake?”

Murmushin yaƙe Abdul ya yi ya ce “Ni banda makaranta, kawai ina rayuwata a layi ne. Bara kuma ina yi don banda sana’ar data fishi.”

Jin haka yasa yaron ya tausayawa Abdul ya ce “In ba damuwa Abokina ka zo na kaika gun mai gidanmu, shi zai sama maka abun yi.  Ko da yake a wurinsa ma Bara ita ce babbar sana’ar da yake koya mana, sai ƙananun sana’o’in hannu.”

Abdul ya yi farinciki da hakan don haka ba musu yabi Abu sabon abokinsa zuwa gun ogansu.

Ogan ya yi murna sosai don har kyauta ya yiwa Abu saboda janyo masa yara da yake musamman nakasasshi wanda ya san ba ƙaramin samu zai yi ba in ya horar dasu.

A nan Abdul ya zauna tsawon Sati biyu ba Arabi bare boko. Amma shi Abu ya kan je makarantarshi dama malaminsu ne ya kawo su koyon sana’ar gyaran rediyo gurin Oga Master. Wanda shiko ogan yake amfani da yaran wurin samun kuɗaɗensa.

Tun a satin Farko Master ya fahimci cewa za’a je da yaro Abdul saboda yana kawo kuɗi sosai. Gashi daga kallon farko wasu mutanen ke jin tausayinsa suna ba shi sadaka.

Sannan yaron akwai hazaƙa da sa kai bai rufe satin da ya zo ba sai da ya iya abubuwa da yawa cikin harkar gyaran rediyo da fitila.

Wannan dalilin ya saka Oga master ya yanke hukuncin idan lokacin zuwansa Legos ya yi tare da Abdul zai je tunda ba wanda ya isa ya hana, yaron zaman kansa yake.

Bayan Sati biyu da kwana huɗu lokacin cirawar Oga Master zuwa Legos ya yi. Dama ya saba zuwa can ya zauna na tsawon lokaci yana sana’arsa kafin ya dawo.

Don haka a wata Ranar Laraba motarsu ta daga daga Kaduna zuwa Legos.

Abdul ya yi murna sosai ganin ya samu shiga har za’a yi tafiya da shi.

Amma ya tafi cike da kewar mutanen da ya saba dasu a ɗan zamansa a garin. Cikin waɗanda yake alhinin barin su harda Abokinsa Abu almajiri.

Ko a mota lafewa ya yi Luf kamar mai tunani. Ɗayan yaron da oga ya zo da shi sai hira suke shida ogan amma Abdul shiru kawai ya yi yana kallon gefen hanya.

Bayan shuɗewar wasu awanni masu tsayi suka isa birnin Legos.

Tun farkon shigowarsu garin Abdul ya hangame baki yana kallon baƙon garin da ganin yanda ya ƙawatu.

A haka aka sauke su a tasha kowa ya kama gabansa.
Oga master ya ja yaransa suka shiga abun hawan da zai sada su da masaukinsa.

Wani gidan Maza ne irin na hayar nan wanda yan ci rani masu zaman Legos ke kamawa, a nan suka yada zango.

Da gari ya waye suka fita nema, yayinda Oga Master yake zaune a kasuwa ya kasa hajarsa gefe ɗaya kuma ga sana’arsa ta gyare-gyaren abubuwa.

Su kuwa Abdul da Ali tun daga gida yayo masu shiri tare da ƙara koya masu hanyoyin da zasu bi wurin Bara idan sun je Kasuwar.

Don haka suna isa ba jira kowa ya kama hanyarsa, Abdul ya nufi tasa hanya shima ɗayan haka.

Da yake shima Alin ido ɗaya ke gare shi kuma gurgu ne Kamar Abdul.

@@@@@@@@#

Bayan zaman sati Uku da Hajiya ta yi a garin Sokoto tana bincike-binciken son gano mai hannu a ɓatan ɗanta, ta tabbatar da cewa Hajiya Hasina nada hannu dumu-dumu a ciki.

Don haka ta yiwa Kawu Alhaji waya ya dawo tare da ƙwaƙƙwaran shiri na maka Hasina kotu.

A safiyar wata Litinin takardar sammaci ta samu Hajiya Hasina har falonta. Hankalinta ya dugunzuma sosai, sai zufa ke tartsowa ta kowace kafar ga shi da ke jikinta.

Ta sani sarai waɗannan mutanen sun fita arziƙi ba zata iya kayar dasu a kotu ba, koda a ce kuɗi za’a zuba don yin nasara a shari’ar.

Kasa zama ta yi, sai kai komo take a tsakar falon, a bayyane ta ce “Na shiga Uku ni Hasina! Yau ga shi tusa na neman ƙurewa budari. Yanzu ya zan yi kenan?”

Haka ta shafe tsawon mintuna 15 tana tunanin mafita.

Kanta ya ɗau caji sosai, ganin ta kasa samawar kanta takamammiyar mafita ya saka ta shiga banɗaki don watso ruwa ko ta samu salama.

Bayan fitowarta ne dabarar kiran Mai adashen sharri ya faɗo mata. Wayarta ta ɗaga ta kira Kulu domin neman mafita…
Tirƙashi🤔 lallai gaskiyar yan magana da suka ce karen bana shike maganin zomon bana, gashi Hasina ta haɗu da waɗanda suka fi ƙarfinta ya kenan?

Ya Abdul zai ƙare a birnin ikko?🤔

Muje zuwa dai.

UMMU INTEESAR CE🥰🥰❤️

*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

         *AND NOW*
    *HALITTAR ALLAH CE*
Ga masu buƙatar na tallata masu hajojinsu a shafukan littafina dama shafukana na sada zumunta kamar instagram, whatsapp, telegram, facebook da sauransu sai su tuntuɓe ni ta wannan number __08109634202__+

Kowacce irin haja je gareka zamu tallata ma cikin rahusa insha’allah.

SAI KUN MUN AFUWA YAU BA EDITING DA FATAR ZA’A MUN UZURI😢
________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
PAGE 65-66
Bayan doguwar tattaunawar da suka yi da Kulu a waya ta katse kiran.

Dama sun yake cewa da yamma Kulu zata zo su je neman mafita.

Haka kuwa aka yi, Kulu na zuwa suka fice daga gidan kai tsaye gurin Bokansu suka nufa.

Dama da matsala irin wannan ta taso shi suke nufa da bukatunsu maimakon su koma ga Allah. (Wa’iyazubillah)

Ba su suka dawo ba sai bayan isha’i. Cike da ƙarfin gwuiwa Hasina ta shige ɗakinta tana murna.
Sai dai fa murnarta na neman komawa ciki da ta tuna da Abu ɗaya. A ƙa’idar maganin da boka ya basu dole sai ɗaya daga cikin mutanen nan biyu ya ci maganin sannan burinta zai cika.
Tana cikin wannan tunanin ƙirjinta ya yi mummunan faɗuwa da alama ta tuno wani sabon abun ne.
Muryar Bokan ke mata amsa kuwa inda yake cewa “Ki kula kisa lura sosai, idan kika sake anka samu mishkila wurin aiwatar da aikin to reshe ne zai juye da mujiya. A maimakon kici galaba akansu sai su zuci a kanki.”

Dogon numfashi ta ja ta yi shiru tana ƙara tuna wani abun “Akwai tsari sosai a jikin Matar, da wuya muci galaba akanta shiyasa a baya na faɗa miki wani tarnaƙi na fuskanto rayuwarki, wannan shine tarnaƙin.”

Sosai hankalinta ya dugunzuma ta rasa mema zata yi, maimakon ta samu nutsuwa bayan dawowarta daga gunsa saima ta ƙara shiga tashin hankali fiye dana ɗazu.

A bayyane ta ce “Wannan yaron ka zame mun alaƙaƙai ƙadangaren bakin tulu. Gashi dai na kashe macijin amma na kasa sare kan da yake neman zama barazana a rayuwata. Anyah kuwa Abdul kai Mutum ne? Meyasa na yi nasarar gamawa da kowa ciki harda Abbanka amma kai na kasa har yanz…….
“Meke damunki kike ta Surutu ke kaɗai Hajiya?” Ta ji an faɗa a bayanta.

Jin Muryar Alhaji Munir ya saka ta juyo a kiɗime “ba fa komai Alhaji me ka ji ina cewa ne?”

Ta yi masa wannan tambayar ne don ta gano ko yaji maganganunta.

Girgiza kai kawai ya yi alamun A’a ya shige ɗakinsa.

A zahiri kuwa ya jita sarai tun sanda ta fara maganganun. Kansa ya ɗaure, so yake ya tuna wani abu amma ya kasa.

To wane yaro take magana, wane Uban yaron da take iƙirarin cin galaba a kansa?

Duk yanda ya so ƙwaƙwalwarsa ta bashi amsar hakan ya ci turo, nan take kansa ya fara juyawa tunaninsa na neman……

STORY CONTINUES BELOW
@@

Daƙyar da siɗin Goshi Hajiya Hasina ta ga ta samu ke tare rijiya da baya. Kuma hakarta ta cimma ruwa bayan shafe sati Uku ana Shari’a alƙali ya yi watsi da ƙarar saboda rashin gamsassun hujjoji na zahiri akan wacca ake zargi.

Cike da baƙin cikin wannan al’amarin Hajiya Fatima ta shirya ta koma Kaduna bayan ta shafe tsawon lokaci a Sokoton.

A zahiri zaka ɗauka Hajiya Fatima ta haƙura da wannan shari’ar bayan tasha ƙasa a kotu. Amma a cikin ranta tana nan da ƙudurin ɗaukaka ƙara ko ɗaukar tsattsauran mataki akan Hasina don ba zata taɓa yarda ta ci bulus ba.

@@@
Isar ta Kaduna ke da wuya ciwon ƙafarta ya tashi ga kuma yawan jini, don haka aka garzaya da ita asibiti ta jima sosai tana jinya kafin a salamo ta ta dawo gida.

A lokacin ne kuma ta fara tunanin hanyar da zata bi don gano ɗan ‘yar uwarta da ya ɓata.

@@@######

Abdul kuwa bayan da suka rabu da abokin tafiyarsa yabi tasa hanya yana bara. Ba laifi ya samu sadaka gwargwado, sai yamma lis ya juyo da Zimmar komawa gun sana’ar megidan nasu da yake zaune a kasuwar obalenden.

Sai dai me? Abdul ya rikice ya kasa gane hanyar da zai bi ta sada shi da inda ya nufa.

Abinci ya siya da kuɗin bararsa ya nemi guri ya zauna ya ci sai da ya ƙoshi sannan ya miƙe ya ci gaba da kewayar kasuwar har Allah ya sada shi da Ali.

Da yake shi Alin an saba zuwa dashi garin hakan yasaka bai sha wahalar gane hanya ba. Sai gasu gaban oga master.

Karɓar kuɗin ya yi ya ƙirga su can ya ɗago ya kalli Abdul da alamar tuhuma a fuskarsa “Amma Abdul ba waɗannan ne iya kuɗin da ka samu a yau ba koh?”

Murmushin yaron ya yi yace “Iya sune Oga abinci kaɗai na siya na ci.”

Nan fa Oga master ya tubure yanata zabgawa Abdul faɗa akan cewa da dalilin me yasa zai siyi abinci da kuɗin? Shima abincin ai bararsa ya kamata ya yi.

Abdul ya cika da tsananin mamaki a ransa ya ce “Ji wannan bawan Allah ko tausayinmu baya, gani musha wahalar nema ya ƙwace, banda kaddara ma Ni me zan yi da Bara bare har na mai dashi sana’ata?”

Haka suka ci gaba da gudanar da rayuwarsu, kullum basu da sana’ar da tafi Bara dai gyaran rediyon da oga ke saka su da dare bayan sun dawo gida.

Har yau wa jiya dai Abdul bai samu hutu ba.

Bayan sati biyu da zuwansu Legos wataranar Lahadi bayan sun dawo daga kasuwa da misalin ƙarfe shida na yamma, Oga master ya ce “Abdul ɗauko waccan baƙar ledar ai nasan zaka iya ko?” Bai jira amsar Abdul ba yace kaima Ali ɗauko waccan mu tafi.”

Kafin su aiwatar da ayyukan da ya saka su yaga ana siyar da yalo a tsallaken titin dake gabansu.

Nan take ya yanke shawarar ya tsallaka ya siyo dama yana matuƙar sonta.

Tsautsayi ba’a saka maka rana, haka kuma in ajali ya yi kira ko ba ciwo aje.

Yana hawan titin baisan ya aka fara ba kawai ya ji gif! Wata babbar mota ta yi sama dashi kuma tabi takansa a take jikinsa ya rabe gida biyu ko shurawa bai yi ba ya mutu.

Su kuwa su Abdul sun ɗauko ledojin kenan suka ji kar’ar wani abu mai ƙarfi, ɗagowar da zasu yi haka suka ga anyi sama da mutum.

Anan suka yadda ledojin suka ruga da yan sandunansudon ganin ko waye.

Da ƙarfi suka ja da baya bayan sun yi arba da wanda motar ta kaɗe da yanda gangar jikinsa ta zama. Nan gurin suka faɗi suna kuka.

Bayan an janye gawar daga kan titin aka shiga neman wanda ya santa babu. Abdul ne ya yi ƙarfin halin matsawa yana goge hawayensa yace na sanshi oganmu ne tare muke.

Masu sauran imani a cikin hausawa da yarbawan dake gurin sun tausayawa yasa. A haka aka samu daƙyar aka kawar da gawar.

Daga haka aka rufe shafin rayuwar Oga master ya mutu a tafarkin neman kuɗi harda na haram, danne haƙƙi da yin ruf da ciki da dukiyar wasu, yau gashi ya mutu ya bar dukiyar, kuɗin da ya tara basu amfane shi ba ya mutu a wulaƙance.

Abun tausayi Abdul ya faɗa maraici karo na biyu a garin da baida kowa sai Allah da abokin sana’arsa Ali.

Sun ci kuka har sun gode Allah. Komawa suka yi gidan da suke kwana jiki a sanyaye.
Mutanen gidan sai tambayar yaran suke ina oga Master? Cikin matuƙar ƙarfin hali Abdul yace “Mota ta kaɗe shi ya mutu.” Yana gama faɗa ya saka sabon kuka.

Bayan sun kwana biyu a gidan suka bar gidan don basu da abinda zasu ci gaba da biyan haya, gashi basu san inda oga ke ɓoye kuɗinsa ba, ɗan bashin da yake biyar mutan gidan aka tattara masu suka tafi.

Daga gidan suka miƙa sai kasuwar Bandir layin da mabarata suke zama anan suka tare, suna ci gaba da sana’ar bararsu.

MORE COMMENT MORE TYPING

Follow me on wattpad @Ruky-i-lawal

UMMU INTEESAR CE.

*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

              *AND NOW*
         *HALITTAR ALLAH CE*

Ga masu buƙatar na tallata masu hajojinsu a shafukan littafina dama shafukana na sada zumunta kamar instagram whatsapp, telegram, Facebook da sauransu sai su tuntuɓe ni ta wannan number _08109634202_+

Kowacce irin haja ce gareka/ki zamu tallata maka/ki cikin rahusa insha’allah.

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

PAGE 67-68
Haka rayuwa ta cigaba da gangarawa Abdul har zuwa yanzu dai ba wani sauyi da aka samu na game da halin ƙuncin rayuwa da yake ciki.

Sai da suka shafe rabin shekara suna rayuwa a cikin mabarata, basu da muhalli sai dai in dare ya yi su kwanta gaban rumfunan ‘yan kasuwa da safe kuma su shiga sana’arsu ta Bara, wacca da ita ne suka dogara.

Watarana bayan sun tashi daga barci kowa ya kama gabansa, Abdul ya bi nasa bangaren Ali ma ya bi tasa hanyar.

Ali na cikin tafiya kwatsam ya ji an kira sunansa da ƙarfi.
“Ali!”
Tsayawa ya yi cak, tare da juyawa bayansa don ganin waye mai kiran.

Cikin hanzari ya ja sandunansa ya ƙarasa gare shi cike da tsananin farin ciki.
“Oga Sunusi oyoyo!” Yaron ya faɗa da murnarsa.

“Sannu Ali, ina mutumin nawa?” Ya tambaya.

Ali na jin wannan tambayar ya fashe da kuka.
Daƙyar Oga Sunusi ya shawo kansa ya yi shiru.
Anan Ali ke basa labarin rasuwar Oga master watannin baya.

Sosai ya tausayawa yaron, haka ya shiga alhinin mutuwar abokin nasa. Ya yi fatan su sake haɗuwa ko sau ɗaya ne, Amma ba yanda ya iya ƙaddara ta riga fata.

Ali ya kalle shi ya ce “Don Allah Oga ka taimaka ka mayar da ni garinmu.”

Gyaɗa masa kai ya yi ya ce “Kada ka damu dama daga nan tasha zan wuce kai tsaye, mu je kawai.”

Cike da murna Ali ya bi bayansa suka tafi. Shi kwata-kwata ma ya manta da abokin tafiyarsa Abdul sai da mota ta tashi tukunna ya tuna.

Gayawa Ogan ya yi, shi kuwa ya ce “Sai haƙuri Ali, lokaci ya ƙure, Allah ya jefa shi hannu na gari.”
“Ameen.” Ali yace ba walwala tattare da shi, ya san Abdul zai shiga damuwa inya neme sa ya rasa.

@@@@@@@@@@

Al’amarin Hajiya Hasina kuwa sai daɗa gaba yake. Domin tun da ta tabbatar komai ya dawo ƙarƙashin ikonta ta shiga sace kadarorin Alhaji tana ba shi yana saka hannu a kai, yanzu kusan duk kadororinsa sun zama nata sai wanda bata san da zamansu ba.

Su kuwa su yaya Bilya duk wani al’amarin kasuwancin ƙanin nasu sun lalata masa, sun sace kusan duka kuɗaɗen jarinsa dama ribar.

Yanzu Shago biyu ya rage mallakinsa, wanda yaya Mizbahu ke kula dashi, sai wanda shi alhajin ke kula da abinsa.

STORY CONTINUES BELOW
Ko da Hajiya Hasina ta waiwayo kan kasuwancin Alhaji ta tarar da wannan ɓarnar ta shiga tsananin ɓacin rai.

“Taya hakan ya faru? Tabbas da zagon ƙasa a cikin lamarin, taya dukiyar zata lalace haka?” Waɗannan tambayoyin ne ke ta yawo a ƙwaƙwalwarta kuma ta kasa samun Amsa don haka ta sha alwashin, sai ta gano gaskiyar lamarin, kuma ko su waye keda hannu a ciki tabbas zata yi maganinsu.

Sai dai ba wannan ne Babbar damuwarta ba, hakan ya sa ta tarkata zancen ta ajiye gefe, domin a yanzu haihuwa take nema ido buɗe.

Abokiyar cin mushenta ta kira suka kuma rankayawa gurin boka a karo na barkatai.

Zaune suke a gaban bokan nasu, yayinda yake ‘yan asirce-asircensa da karatun wasu surkulle, bayan ya gama yiwa kansa kirari.

“Tabbas wannan karo za’a miki aiki kuma za’a yi nasara matuƙar kin amince da sharaɗin da zan faɗa miki yanzu.”

Gyara zama Hasina ta yi tare da gyara mayafinta, murna fal ranta tace koma miye na amince amun aiki kawai.”

“Hahahahaha! Ya ƙyalƙyale da wata mahaukaciyar dariya yana yamutsa haukataccen gashin kansa da hannunsa ɗaya. Can kuma ya gimtse kamar bai taɓa dariya ba ya kalle ta ya ce “wannan aikin mai tsada ne, idan kin amince amma dole sai mun haɗa da aikin jinnu, shi kaɗai ne zai sa hakan ya yiwu.”

Da fari taso ta ji tsoro amma saboda bushewar zuciya da son cika mummunan ƙudurinta a kan Alhajin ta amince kai tsaye.

“Tashi ki tafi la’ananniya angama wannan aikin.”

Kuɗi ta ciro a jakarta wanda ita kanta bata tantance ko nawa bane ta ajiye a gabansa, sannan suka miƙe cikin hanzari suka fita, ranta fari ƙal tamkar takarda.

@@@@@@@@@

Al’amarin Hajiya Fatima kuwa bayan tashinta daga jinya ta kira Baba Direba, bayan sun gaisa ta sanar masa buƙatarta ta neman hoton Abdul ko ta halin yaya.

“Kada ki damu Hajiya, duk da cewa neman hoton Abdul tamkar neman jaki mai ƙaho ne, amma…. Ya yi jim, yana tunani can ya ce
“Yawwa na tuna watarana wani makwafcinmu ya taɓa ɗaukarmu hoto nida Abdul a wayarsa lokacin zan kai yaron makaranta, bari na neme shi na ji ko za’a samu, don gaskiya anjima sosai.”

“Kai! Amma Na gode sosai, don Allah ka yi ƙoƙarin samo shi sai na jika.”

Daga haka suka yi sallama.

Bayan kwana Uku sai ga kiran Baba Direba yana shaida mata an samu hoton amma baisan ya za’ayi ya zo gare ta ba, (da yake shi ba  mutumin zamani bane bai san komai game da waya ba.)

Anan ta gaya masa yanda za’ayi. Suna gama waya
Ya je ya bawa Hashim (makwafcin nasu) number Hajiyar ya tura mata hoton through WhatsApp.

Lokacin da saƙon ya shigo tana kishingiɗe akan gadonta, kafafunta na damunta da zogi yayin da Hanne ke gefe tana ɓallo mata magani.

Duba wayarta ya yi dai-dai da lokacin da take karɓar magani hannun Hanne, kafin ta kai ga shan maganin ta yi tozali da abunda ya gigita tunaninta.

Watsar da ƙwayoyin maganin ta yi tare da zazzaro ido waje, ta miƙe zaune da ƙarfi. Kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin tsananin tashin hankali da kiɗima.

“Subhanallah! Hajiya me ya faru?”
Hanne ta tambaya.

Bata iya bata amsa ba sai nuna mata hoton ta yi, yayin da idonta ke zubar da ƙwalla.

“Ai Hajiya wannan kamar shine yaron da kika saka na fitar da shi daga gidan nan ko?.”
Gyaɗa mata kai ta yi tare da miƙewa tsaye tana faɗar “Innalillahi wa innailaihir raji’un! Me na aikata? Da kaina na cutar da kai ɗana akan rashin sani, ki yafe mun Zulaiha, na san baki cancancin wannan sakamakon daga gare ni ba yar uwata.”

STORY CONTINUES BELOW
Numfashi ta ja tana ci gaba da tsiyayar da ƙwalla a idonta.

Hanne dai kanta ya ƙulle ta rasa gane kan wannan al’amari, cikin ƙarfin hali ta ce “Don Allah Hajiya ki gaya mun Waye ɗan naki? Ba dai wannan dodon ba…..”

Kafin ta gama rufe bakinta ta ji saukar gigitaccen mari ba zato ba tsammani.

Ɗagowar da zata yi haka ta ga Hajiya na huci, ta ce “Ya ishe ki Hanne! A baya ni da ke mun aikata wannan Babban kuskure, amma yanzu ko da wasa kika ƙara ambatar ɗana da wannan sunan sai……”

Ƙasa ƙarasawa ta yi ta sulale ta zauna kan gadon tana jin yanda zuciyarta ke ƙuna yayin da take tunowa da yanda ta wulaƙanta Abdul, da kuma tarin alkhairan mahaifiyarsa a gare ta.

A haka ta shafe tsawon lokaci a gurin tana nadama mara amfani, ganin wannan ba zai fidda ta ba ta miƙe tare da ɗaukar wayarta ta kira Kawu Alhaji akan batun.

Cikin kwanaki ƙalilan hoto da kuma sanarwar neman yaro Abdul ta bazu a faɗin jihar Kaduna da kewaye.

Bayan mako biyu Hajiya ta shiga tashin hankali fiye da baya, ganin tsawon lokacin da aka shafe ana nemansa amma ba amo ba labari. Ƙarin tashin hankalinta shine Mahmud da ya shaida mata yana nan dawowa Kwanan nan, ta sani in Mahmud ya dawo ba su samo Abdul ba abun sai yafi haka muni, sai addu’a take ba dare ba rana akan Allah ya bayyanar mata da shi kafin lokacin.

@@@@@###@@@

BIRNIN IKKO

Da misalin ƙarfe tara na dare, Abdul ne zaune kan suminti gaban rumfar wani shago inda suka saba kwanciya, barci yake ji sosai har idonsa sun fara zafi, amma saboda rashin ganin abokinsa Ali ya kasa barci, yana ta tunanin iri-iri akan Alin. Har wuraren 11 pm, ganin abun ya ƙi ci ya cinyewa ya saka ya kwanta agun, bako shimfiɗa bare abun rufa, duk da tsananin sanyin garin da kuma yanayin gun da suke.

A haka ya takure jikinsa yana jin sanyi na ratsa kasusuwansa, amma saboda sabo da yayi da irin wannan yanayin ko damuwa bai yi ba. A haka barci ɓarawo ya sace shi.

Da safe ma a haka ya tashi ba walwala ya shiga sana’arsa. can zuwa rana tsaka yana cikin tafiya sandarsa ta yi karo da wani dutse, sai ji kake rikija! Ya faɗi gasa kansa ya bugu da wani dutsen, a take gefen goshinsa kusa da idonsa ɗayan ya fashe sai jini, sai lafiyayyar ƙafarsa ɗaya da ta samu rauni itama.

Sai dai ba wanda ya kula da Abdul ɗin bare ya tausaya masa, a irin wannan garin na ka zo na zo, kuma ga shi a cikin kasuwa kowa harkar gabansa yake.

Yunƙurawa ya yi ya tashi cikin ƙarfin hali, ya miƙe kan sandunansa ya fara tafiya don neman chemist mafi kusa.

Dukda cewa a zamansa na rabin shekara a kasuwar ya san ciki da bai na kasuwar amma bai san inda zai samu chemist ba, hakan ya saka ya tambaya, aka kwatanta masa.

Yan kuɗin da ya tara da zimmar fara sana’ar gyaran rediyo don dogaro da kai, su ya fitar ya bada aka wanke masa raunin ƙafarsa dana goshinsa, sannan aka bashi magunguna ya juyo zuwa matsugunninsa.
A hanyarsa ta dawowa ne ya ji ana ƙwala masa kira ta bayansa.

“kai yaro tsaya mana….”
Ci gaba da tafiyarsa ya yi don koda wasa bai kawo da shi ake ba, sai da mutumin ya matso kusa yana faɗar “Yaro mai sanda da kai nake fa.”

Sai a lokacin ya tsaya tare da juyowa cikin murmushi ya kalli mutumin da zai kai shekaru 50 zuwa da biyar a rayuwa, ya ce “Ah! Baba Alhaji da ni kake?” “Da kai nake ɗana. Ya sunanka?”

Faɗaɗa murmushinsa ya yi ya ce “Abdulrazaƙ sunana, amma an fi kirana da Abdul.”
Murmushi Alhajin ya yi ya ce “Mu je mota ina son ka bani labarinka.”

Shiru Abdul ya yi tsoro ne ya kama zuciyarsa, duniya yanzu ba gaskiya kaga mutum rumui-rumui kamar na Allah amma mugun nufi fal cikinsa.

Lura da yanayin yaron ya saka ya ce “Ɗana kada ka ji tsorona ba zan taɓa cutar da kai ba sai dai akan rashin sani ka yarda da ni.”

Jin hakan yasa Abdul ya yi ta maza ya bi bayansa zuwa motarsa, Abdul na shiga mutumin ya tada mota ba tare da ya yiwa yaron cikakken bayani ba, ya bar kasuwar cikin hanzari….
“Tofah! Meke shirin faruwa da Abdul ne?
Wannan mutumin na gari ne ko mugu?🤔

Hajiya Fatima zata samo Abdul kuwa?

Hajiya Hasina zata haihu da Alhaji Munir kuwa?

Sojoji!

Ku tara da Ni a shafi na gaba don jin ya za’a kaya.
Follo me on wattpad @Ruky_i_lawal

Instagram @Rukayyarh_ibraheem.
Vote, share & comment.

UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️

*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*

*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

              *AND NOW*
         *HALITTAR ALLAH CE*

Ga masu buƙatar na tallata masu hajojinsu a shafukan littafina dama shafukana na sada zumunta kamar instagram whatsapp, telegram, Facebook da sauransu sai su tuntuɓe ni ta wannan number _08109634202_+

Kowacce irin haja ce gareka/ki zamu tallata maka/ki cikin rahusa insha’allah.

DEDICATED TO ALL MY REAL FANS🥰 son so fisabillillah nake maku, ku kuke kara mun ƙarin gwuiwa.

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

PAGE 69-70

Tunda ya tada motar bai cewa Abdul ƙala ba, sai tsala gudu yake akan titin.

Abdul dai wuƙi-wuƙi ya yi da ido ya kasa cewa komai sai addu’a da yake a can ƙasan ransa.

Dattijon nan bai zame ko ina ba sai wani katafaren asibiti, a harabar asibitin ya yi parking, sai a lokacin ya dubi Abdul da murmushi a fuskarsa ya ce “Mu shiga a duba ma raunukanka.”

Ba musu Abdul ya bi bayansa suka shiga ciki.

Bayan kamar rabin Sa’a suka fito daga Asibitin.
A harabar tangamemen gidansa ya yi parking sannan ya juyo ya kalli Abdul ya ce “Ɗana mu shiga ciki ko?”

Cikin matuƙar ƙarfin hali Abdul ya buɗi baki ya ce “Ina ne nan Baba?.” Tamkar zai yi kuka ya yi maganar, don har zuwa lokacin hankalinsa bai gama kwanciya da mutumin ba.

“Nan gidana ne ka kwantar da hankalinka ba zan cutar da kai ba, mu shiga ciki.”

Jiki ba ƙwari ya sauka daga motar, suka nufi cikin gidan.

Abdul sai ɗaga kai yake yana kallon kyau da tsaruwar gidan, duk da cewa ba a wani ƙyalƙyala gidan da yawa ba, amma kallo ɗaya zaka masa ka gane shewar na masu hannu da shuni ne.

A babban falon gidan suka yi masauki.

Waya Alhaji Salim ya ɗaga ya kira uwargidansa.

“Hello uwar gida mun ƙaraso fa.”

“Wow! Sannunku da zuwa bari na sauko.” Hajja Fahima ta faɗa.

Cikin hanzari ta miƙe daga kan kujerar dressing mirrow da ke zaune a kai, har ta juya zata tafi sai kuma ta ɗan juyo ta kalli kanta jikin madubin.

Ƙayataccen murmushi ta yi, ganin kwalliyar ta yi dai-dai da yanda take buƙatarta, sannan ta juya ta fita.

Tun kan ta ƙaraso cikin falon take faɗar Oyoyo my husband! Sannu da zuwa, ina yaron namu yake?”

STORY CONTINUES BELOW
“Oh! Madam Heema Sarkin zumuɗi, bakya bari ma ki ƙaraso ba kenan?” Ya faɗa yana sakar mata murmushi.

Maida masa martanin murmushi ta yi sannan ta ce “Shekara nawa na share ina jiran wannan ranar? Yau kuma na kai ga ɗa namiji saurayi ma kace ba na yi murna ba?”

‘Yar dariya ya yi ya ce “kuma fa kina da gaskiya.”

A dai-dai lokacin ne kuma ta ƙaraso inda suke zaune kan doguwar kujerar falon, Abdul dai sai bin su yake da ido ƙirjinsa na tsananta faɗuwa, kwata-kwata bai fahimce su ba, to me suke nufi da shi?

Bai samu damar ƙarasa zancen zucinsa ba saboda jin ta dafa kafaɗarsa da ya yi.

A ɗan razane ya ɗago, ganin ta masa murmushi ya saka ya dake ya ce “Mommy Ina wuni?”

Cike da jin daɗin sunan da ya kirata da shi ta ce “Lafiya ƙalau yarona Abdul, ya jikin naka?”

“Na ji sauƙi.” Ya faɗa a taƙaice.

Sake kafaɗarsa ta yi ta juya zuwa ciki ba tare da tace wa kowa komai ba.

Zuwa can ta fara fitowa da kulolin abinci tana shiryawa a dinning table.

Sai da ta kammala ta maida dubanta ga Alhajin tare da masa nuni da hannu ta ce “Yallaɓai bismillah the lunch is ready.”

Cike da so da ƙauna yake dubanta, a haka ya janyo hannun Abdul zuwa dinning, ita ce ta yi serving ɗin su da kanta.

Abdul sai bin amincin ya ke da ido ganin lafiyayyen abincin da aka ajiye a gabansa harda su naman kaza, ƙwai da sauransu a kai.

“Allah mai iko, buwayi gagara misali, yau ni Abdul ne aka kawowa wannan abincin? Allah abun godiya….”
Ya faɗa a ransa.

Bai ko jira ance ya ci ba kawai ya ture cokali gefe ɗaya ya saka hannunsa, ba tare da ya damu da wanke hannun ba.

Fara ci ya yi hannu baka hannu ƙwarya.
Hajja Fahima ta ɗago suka haɗa ido da Alhajin sai kawai suka gyaɗa kai cikin alamun tausayawa.

Abdul bai ma san me suke ba, don tun da yafara saka loma bai ɗago ba sai da ya ji ya yi naƙ, tukunna ya ɗago ya ɗauki robar ruwa ko tsiyayawa a kofi bai tsaya yi ba ya kwankwaɗa sai da ya shanye ƙaramar robar ruwan tukunna ya ajiye ta.

Ga lemukan roba da kayan marmari nan birjik a gabansa amma bai ko bi takan su ba, dama bai saba shan su ba, bare ya san daɗinsu.

Kallon Hajja Fahima ya yi sai murmushi yake ya ce “Mommy Ina ake wanke hannu?”

Abun ya so bata dariya amma sai ta gimtse ta ce “Abincin ya yi daɗi kuwa yarona?”

“Wai daɗi kai! Ai wannan abincin ko a Saudiyya sai haka.”

Wannan karon kam kasa jurewa ta yi ta fashe da dariya Alhajin na taya ta.

Bayan sun gama dare-darensu ta nunawa Abdul inda zai wanke hannunsa, daga bisani kuma ta nuna masa ɗakin da zai zauna a ciki, da banɗaki.

Sai da ta nuna masa yanda zai yi amfani da komai na banɗakin sannan ta fito ta bashi guri don ya yi wanka.

Abdul sai taɓa abubuwa yake yana dariya shi kaɗai, ya kusan awa yana dirzar jikinsa kafin ya samu dattin jikinsa ya tafi gaba ɗaya.

Bayan ya gama wankan ya tarar ta ajiye masa ƙananun kaya sabbi dal ya ɗauka ya saka, sai kuwa suka mishi tsaf kamar an gwada.

Kai tsaye falon ya fito ya tarad da su zaune, a tare suka kalle shi tare da faɗar “masha’allah!”

Ganin yanda ya fito ras abunsa duk da ba ya da wani fasali mai kyau tun daga kan mummunar fuskarsa har zuwa yanƙwanannen jikinsa da yaga wahalar rayuwa. Ko da yake zuwa lokacin ya na cikin shekara ta 17 ne a rayuwarsa, amma idan ka gan shi zaka ɗauka ɗan 13years ne saboda yanayin ciwo da ya tauye shi ya hana masa girma, ga kuma jarabawar rayuwa da yake ciki.

“Zo ka zauna yarona.” Fahima ta faɗa.

Ba musu ya ƙaraso ya zauna kusa da su daga gefe.

Gyaran murya Alhajin ya yi sannan ya ce “Yanzun zan gayama dalilin ɗauko ka da na yi dama ina so ka samu nutsuwa ne kafin mu yi maganar, shiyasa ban faɗa ma a can ba.”

Gyaɗa masa kai kawai yaron ya yi, ya ƙagu ya ji dalilin da yasa aka rabo shi da muhallinsa.

Alhajin ya ci gaba “Da farko sunana Alhaji Salim ni ɗan asalin jihar Kano ne, dalilin kasuwanci ya dawo da ni zama nan Legos tare da iyalina…..”
Ya nuna Hajja Fahima da yatsa ya ce “Wannan ita ce matata Uwar gidana Hajja Fahima yara suna kiranta da Mommy sai kuma…..”

Kafin ya ƙarasa wata kyakkyawar yarinya da ba zata haura shekaru sha biyu ba a duniya ta shigo falon da gudu tana faɗar “Mommyna ki na ina gani nan na dawo.” Rufe bakinta ya yi dai-dai da lokacin da ta iso inda suke zaune ga baki ɗaya, turus ta yi tana ƙare masu kallo ganin baƙuwar fuska a gidan. Can kuma kamar wacca aka tsikara ta buga tsalle ta haye jikin Alhaji tana faɗar Daddyna shi ne ka dowa gida yanzu, baka bari na rigaka ba? To gaskiya ba ruwana ice-cream ɗina dai sai an ba ni.”

Mommy da Abdul murmushi kaɗai suka yi, yayin da Alhajin ya ja mata hanci ya na faɗar “To na ji rigimatu ‘yar Daddy ki shiga ciki ki cire uniform ki yi wanka da Sallah ki ci abinci sai ki zo ki karɓa.”

Da alama ya faɗa mata haka ne don ya kore ta su ƙarasa zancen da suka fara.

Sauka ta yi daga kansa har za ta tafi ta juyo ta kalli ɓangaren da Abdul ke zaune.

Da yatsa ta nuna shi ta ce Daddy wannan fa?

Mommy ce ta kada baki ta ce da ita “Sabon yayanki ne sunansa Abdul.”

“Lah! Mommy yanzu kenan nima na yi yaya su Aysher ba za su sake mun gorin Yaya ba?.”

“Ƙwarai.” Mommyn ta faɗa mata.

Ta faɗa tare da zuwa ta rungume shi ba tare da ta tsorata da Halittar fuskarsa ba ta ce “Sannu da zuwa Yayana! Na ji daɗin ganinka, gobe zan bawa ƙawayena labarinka.” Daga haka ta sake shi ta yi ciki da gudu Abdul dai sai murmushi yake.

Tun tasowarsa banda Mahmud ahalin wannan gidan ne kaɗai ya san sun karɓe shi ba tare da ƙyama ko nuna jin tsoronsa ba, hakan yasa ya ji ya samu nutsuwa da su.

Bayan shigewarta Alhajin ya ci gaba da cewa “Wannan ita ce ‘yata Sabira ita kenan muke da duk da mun shafe sama da shekaru 25 da yin aure.”

Jim ya yi kafin ya ci gaba da cewa “A watannin baya na fara ganinka a kasuwar Obalenden ka na yawon Bara, na ɗauki sadaka na baka na wuce abina, bayan wasu makwanni na koma kasuwar nan ma na ciki karo da kai, a taƙaice kusan sau uku ina cin karo da kai a kasuwar har ma na baka sadaka.  A gani na ukun dana maka bayan tafiyarka na fara tunani a kanka, a lokacin na yi tunanin koma waye kai kana buƙatar taimako, ko don yanayin halittarka da lalurar dake tare da kai. Tun a lokacin kuma ban sake ganinka ba sai a wancan makon da na shiga kasuwar Bandir, na hangon ka sai dai kafin na samu ƙarasowa ka ɓace mun, bisa dole na haƙura.
Daga lokacin ne kuma duk bayan kwana biyu nake zuwa kasuwar ko Allah zai sa na yi katari da samunka. Cikin iyawar Ubangiji ɗazu na shiga kasuwar kenan na yi gam da katar da kai. Wannan dalilin ne ya saka na ɗaukoka zuwa nan don ka zamto babban ɗana kuma ɗa namiji tilo a gidannan. Muna so ka cika mana gurbin abinda muka rasa, insha’allah zamu riƙe ka da amana.”

Tun da ya fara magana Abdul bai ce komai ba, sai ajiyar zuciya da yake saukewa a hankali.

Bayan ya gama ne Abdul ya ɗago ƙwayar idonsa ɗaya  ta fara tara ƙwalla ya kalli Alhajin ya ce “Daddy na gode sosai da karamci Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi.”

Gyaɗa masa kai kawai ya yi ya ce “Uhmm! Babu komai shi ɗa ai na kowa ne, yanzu dai muna son ka bamu taƙaitaccen tarihinka, waye kai? Ina mahaifanka? Wane dalili ya sanya kake Bara da ƙarancin shekarunka?”

“Tabdijam! Ka ji irinta ba.” Abdul ya faɗa a ransa a fili kuwa ya yi narau-narau da ido ya ce “………

Hmmm!🤔 Wace amsa Abdul zai basu?
Ka da ku manta more comment more typing.

Idan na ga ruwan comment Mai yiwuwa zuwa daren yau ku ji Ni.

Follow me on wattpad @Ruky_i_lawal

Instagram @Rukayyarh_ibraheem.

Vote share nd comment

UMMU INTEESAR CE🥰🥰🥰❤️

*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

              *AND NOW*
         *HALITTAR ALLAH CE*

Ga masu buƙatar na tallata masu hajojinsu a shafukan littafina dama shafukana na sada zumunta kamar instagram whatsapp, telegram, Facebook da sauransu sai su tuntuɓe ni ta wannan number _08109634202_

Kowacce irin haja ce gareka/ki zamu tallata maka/ki cikin rahusa insha’allah.

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

PAGE 71-72
Ya ce “Sunana Abdulrazaƙ kamar yanda na faɗa maka, ba zan iya tuna ko ina da iyaye da ‘yan uwa ko babu ba, iya abinda na sani shine na yi rayuwar jeji a shekarun baya, ni kaɗai na ba gida gaba bare baya sai tsuntsaye da ƙwari da sauran halittun dake rayuwa a gun, ba abinci sai dai na yi tsince-tsince ko na tsinki furanni na ci na sha ruwan kududdufi. Sanadin barowa ta jeji wani bawan Allah ne bafatake da ya kai ni gidansa matarsa ta kore ni…….”
Ya ci gaba da basu labarin baƙar wuya da ya sha har kawo yanzu da yake zaune a falonsu.+

Idanun Alhaji suka cicciko da ƙwalla, Madam Heema kuwa harda hawayen tausayi sai da ta zubarwa Abdul don jin yanda rayuwar ƙanƙanin yaro irin wannan ta shiga cikin mayuwancin hali haka.
“Insha’allah daga yau wahalarka ta ƙare, ba zamu bari ka yi kukan maraici ba, har kawo lokacin da zaka tuna da iyayenka mu maida ka gida.” Hajja Fahima ta faɗa.

Daga haka suka watse daga falon Abdul ya ja sandunansa zuwa ɗakinsa ya na ƙwallar farinciki.

@@@@@@@@@

A Kaduna kuwa an yi sanarwar neman Abdul har an gaji ba labari, duk da mutanen da ya yi zama a unguwarsu ya na masu aiki sun samu labari, sai dai a lokacin suma ba su san inda za su same shi ba, don bai gayawa kowa ba lokacin da ya tafi, sai nemansa suka yi suka rasa.

A cikin satin ne kuma Mahmud ya dawo. Da murnarsa ya nufi sashensa don yin tozali da ajiyarsa, tun daga ƙofa ya ke ƙwala masa kira “Abdul! Abdul!! Abdul!!!”

Sai dai shiru ya ji kamar an shuka dusa. A haka ya fito jiki a mace ya nufi sashen Hajiyarsa cikinsa fal da tambayoyi.

Daƙyar ya bari suka gaisa sannan ya fara jefo mata tambayoyin da suka rikitata da jefata a damuwa,fiye da wacce take ciki.

“Ina Abdul ne?”
Murmushin yaƙe ta yi, so take ta masa ƙaryar yana boarding school kamar yanda ta saba faɗa amma yau ta kasa. Ta san halin nacin Mahmud zai iya cewa a faɗa masa makarantar ya je, tuna hakan ya saka ta kasa magana.

Jin shirun ya yi yawa yasa Mahmud ya fahimci akwai damuwa “To ko dai ta kore shi ne?”
Ras! ƙirjinsa ya buga. Nan ya tsare ta da tambayoyi ganin ba ta da tsimi bare dabara ya saka ta faɗa masa gaskiyar duk abinda ya faru tun bayan tafiyarsa har zuwa yanzu da take neman yaron ‘yar uwar tata.

A gurin ya zube idonsa na zubar da ƙwallah ya ce “Ai ga irinta nan Mommy, yanzu me tsanar bayin Allah ta ja maki, kin wulaƙanta jininki ɗan da yakamata ki masa gata fiye da wanda Mahaifiyarsa zata masa.”

Dogon numfashi ya ja sannan ya ci gaba “Allah sarki Mommyna Zulaiha duk irin yanda kika kula da ni da Mommyna a lokacin da muke buƙatar kulawa muka rasa, yau ga sakayyar da ta maki a kan na ki ɗan……”

Rinannun idanunsa ya ɗago ya zubawa Hajiya kana ya ce “Anya kin yiwa Mommy adalci kuwa Hajiya? Bata cancanci wannan sakayyar daga gare ki ba.”

Hajiya Fatima kasa magana ta yi sai kuka da take.
Miƙewa kawai ya yi ya bar ɗakin ciki da ƙuncin rayuwa da tunanin mafita.

Ya sha alwashin nemo ƙanin nasa komai ruwa da iska kuma ya masa gatan da yayar mahaifiyarsa ta kasa masa.

@@@@@@@@

Bayan kamar wata biyu da zuwan Hajiya Hasina gurin boka, wata safiyar Lahadi ta tashi da yanayin kasala a jikinta, wunin ranar a haka ta yi shi ba walwala. Bawan kamar kwana uku ta fahimci cewa duk alamomin ciki sun bayyana a gare ta, tsananin farin ciki ne ya kamata ji take kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha.

Ba tare da bata lokaci ba ta ɗaga waya ta kira Kulu ta ce “Albishirinki ‘yar uwa!.”

“Goro fari ƙal” Kulu ta faɗa tana washe haƙora tamkar gonar auduga.

“Kulu ciki gare ni.” Ta faɗa da murna.

Kulu dake kishingiɗe kan yagalgalallun kujerun falonta ta zabura da ƙarfi ta miƙe tsaye.
Hannunta ta saka a hanci tana rangaɗa guɗa “Ayyiri-yiri, sai uwat gida a gidan Alhaji Munir, Allah ya kawo yan biu kuma dut maza mu sha shagali, gida ya zama namu.”

Hasina ta ce “ameen.” Tana murmushi.

“Sai na shigo mu hwara tsare-tsaren shagalin da za’a yi ranar suna tun yanzu, don akwai ƙaton shagali wallah.”

Dariya kawai Hasina ta yi ta kashe wayar tana faɗar “ji min Kulu da zumuɗi.”

Tun daga ranar ne kuma ta fara tufka da warwarar yanda zata ƙarasa mallake komai na Alhajin bayan ta haifa masa namiji.

@@@@@@@@@@

LEGOS

Bayan shuɗewar watanni Uku Abdul ya murmure fatarsa ta ƙara haske yanzu yana cikin kwanciyar hankali a sabon gidansu.

Tun zuwansa bai taɓa neman wani abu ya rasa ba, ga wata shaƙuwa mai ƙarfi da ta shiga tsakaninsa da Sabira, yanzu komai a tare suke hatta cin abinci ma, barci kaɗai ke raba su. Shi ɗin ma sai ta fara barci a cinyarsa sannan Mommy ta zo ta ɗauke ta zuwa ɗakinta to a lokacin ne fa shi ma zai samu ya kwanta.

Daddy da Mommy sun yanke Shawarar fita da Abdul ƙasar waje domin a gyara masa ƙafarsa lanƙwasasshiya, kafin ya fara karatu. Suna so su mai da shi cikakken mutum kamar kowa, don haka suka shiga binciken ƙasar da za su fitar da shi don wannan aikin…..

Kada ku manta more comment more typing

Haƙiƙa na raina ƙarancin comment naku shi ke sake mun gwuiwa, idan kuna so mu kammala kafin a zumi damar na hannunku in ga ruwan comment ta ko’ina.
Follow me on wattpad@Ruky_i_lawal

Vote, share and comment

UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️

*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

              *AND NOW*
         *HALITTAR ALLAH CE*

Ga masu buƙatar na tallata masu hajojinsu a shafukan littafina dama shafukana na sada zumunta kamar instagram whatsapp, telegram, Facebook da sauransu sai su tuntuɓe ni ta wannan number _08109634202_

Kowacce irin haja ce gareka/ki zamu tallata maka/ki cikin rahusa insha’allah.

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

PAGE 73-74

Bayan wasu kwanaki Daddy da Mommy suka tsayar da magana kan za su kai shi ƙasar Italy domin a binciken da Daddy ya yi akwai ƙwararrin likitoci masana harkar ƙashi a can.

Nan fa suka shiga shiri gadan-gadan cikin kwanaki ƙalilan visa da passport nasu ya kammala, sai aka yi Sa’a Sabira ta kammala jarabawarta ta ƙare primary kawai sai suka ɗunguma zuwa can ƙasar.

Bayan isar su sun yi katari da samun ƙwararrin likitoci kamar yanda suka ji labari, don haka aka saka rana don yiwa Abdul aikin ƙafar da aka cire tsammani daga miƙewarta.

Cikin Sa’a aikin ya yi kyau sai lokacin jinyar da aka ɗibar masu suke jira.

Wata Uku cur suka shafe a ƙasar sai da suka tabbatar ba tawaya ko ɗaya a tare da shi face wannan halittar tasa wacce ba zata taɓa sauyuwa ba har abada, sa’annan suka juyo zuwa gida Nigeria.

Karfe 12 dai-dai na rana jirginsu ya sauka a harabar filin jirgin sama na jihar Legos.

Can sai ga wani saurayi yana saukowa daga jirgin a hankali yake takowa har ya sauko daga tsanin jirgin.

John direban Daddy da mamaki yake kallonsa tun daga nesa, wannan kamar Abdul “Ya faɗa a ransa.”

Kafin ya gama gulmar ya ga saukowar Daddy, Mommy da Sabira a tare suka nufo shi.

“Shi ne ko..” Ya faɗa da a bayyane da hausarsa da bata nuna ba.

Motar suka shiga ya ƙarasa da su gida, kallo ɗaya zaka yiwa fuskokinsu ka tabbatar suna cikin tsananin farinciki. Ba kamar Abdul da yake jinsa tamkar sakakken tsuntsu.

Bayan isarsu gida suka ci abincin da direban ya yo masu odering sannan kowa ya miƙe zuwa ɗakinsa don yin wanka.

Abdul da ya ji shi ya miƙe Samɓal kan duga-dugansa ya na takawa ba wata tawaya, sai abunda ba a rasa ba. Sai ya ɗaga kansa sama tare da hannayensa yana Faɗar “Tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, mai rayarwa da kashewa, wanda ya yi halitta kuma ya tsara ta yanda yake so cikin ikonsa da isarsa, ya Ubangiji ina godiya a gare ka da ka dawo mun da tafiyata a kan duga-dugaina biyu, Alhamdulillah.”

Mommy da Daddy har sun juya za su tafi suka jiyo yaron yana godiya ga Allah cikin hikima, sai suka tsaya kallonsa.

Gamawarsa ke da wuya ya juyo tare da takowa zuwa inda suke ya ce “Mommy, Daddy na gode muku sosai a kan kulawar da kuka ba ni, kun zame mun gata a lokacin da na rasa dukkan gata, a silarku rayuwata ta kyautata, ga shi yau ina iya tafiya da ƙafafuna biyu bayan share tsawon shekaru ina tafiya da sanda, duk da har yanzu ban tuna ko bi waye ba, bare na tuna su waye iyayena, amma dai na san kun fi mun su…. Na gode sosai.”

“Shii!!” Mommy ta ɗora yatsanta manuni a kan labbanta ta na masa inkiya da ya yi shiru sannan ta ce “A’a yarona kada ka faɗi komai a kan iyayenka baka san me ya rabo ka da su ba, sai dai ina ji a raina koma miye silar hakan to ba laifinsu a ciki. Mu ci gaba da addu’a Allah ya tunatar da kai ya kuma bayyanar mana da su.”

Abdul bai ce mata komai ba ya juya zuwa ɗakinsa jiki a saɓule suma suka juya zuwa nasu ɗakin.

Bayan wannan lokacin ne kuma Daddy ya nemowa Abdul makarantar secondry mai kyau, bayan ya saka an masa takardun shaidar kammala junior secondry school.

Bayan ya kai shi makarantar  suka masa gwaji sai suka tabbatar yana da fahimta sosai, hakan ya saka suka ba shi Ss2.
Don haka Abdul ya zama cikakken ɗan makaranta ya fara karatu sai dai a fannin Fasaha yake wato social science/ business class, kasancewar ya sanar da Daddy cewa baya da ra’ayin fannin Kimiyya kwata-kwata.

Daddy ya so ya yi science ɗin amma baya so ya tauye masa rayuwa ne, shi ne dalilin da yasa ya haƙura ya bi ra’ayinsa.

Sabira ma an shiga Jss1, rayuwarsu suke cike da farin ciki da annashuwa.

A cikin ‘yan watannin nan da Abdul da ya yi har ya fara Manta miye damuwa da faɗi-tashin rayuwa. Ya yi ƙiba ya yi kyau abunsa.

@@@@@@@@@

SOKOTO

Samuwar cikin Hajiya Hasina ya tabbata zo ku ga murna a gun Alhaji Munir kamar ya taka kan ɗan jariri yake ji.

Hasina kuwa ubanta take ci sosai da wannan cikin domin tana fama da matsanancin laulayi, komai ta ci sai ya dawo baya zama a cikinta. A cikin wata huɗu ta bi ta ƙarmushe tamkar wacce aka zago daga rame. Ɗakinta ma bata son warinsa, sai ɗakin Abdul na da ta koma da zama.

Shi kuwa Alhaji Munir sai nan-nan yake da ita ko ƙuda baya son ya hau kanta.

Lokacin da wannan labarin ya riski su yaya Bilya sai suka haɗu a majalisar su inda suka saba taruwa in za su yi ƙulle-ƙullen makircinsu.

Yaya Bilya ne ke ta kai komo a harabar gidan, can ya dunƙule hannunsa ɗaya ya buga a jikin ɗayan cikin ƙaraji ya ce “Kaico! Kaico!!”

“Yi hanƙuri yaya ka saurare mu, mu zauna mu ga yadda za’a ɓullo ma lamarin.” Sunusi ya faɗa yana dafa kafaɗarsa.

Hannunsa ya saka ya kwaɓar da hannun Sunusin ya ce “Mi za’a tattaunawa bayan kuna ka ɓidat kassara mu? Babu yadda ban yi da ku ba bayan ɓacewar mummunan halittar ga nicce a kashe shi mu huta amma kunka ƙiya. Yanzu ga irinta nan wagga tsinanniyar mata na shirin mai da mu baya, ga ƙoshi ga kwanan yunwa. Ina tsoron ma mu yi biu babu. Haka na hwaruwa mun tashi a ɓakan-ɓakatantan.”

Ya na gama faɗa ya yi huci bai kuma cewa komai ba, sai cika da batsewa ya ke dama kun san duk ya fi sauran ƙannensa kafirar zuciya.

Sani ya ta so daga Zaune ya ce “Kwantat da hankalinka yaya Abinda bai yiwuwa na dole ma mu san yadda zamu yi mu halaka abinda at cikinta, don yanzu ko mun kashe Munir dukiyar ta ɗan cikinta ta.”

Sunusi ya ce “To ko mu koma wurin boka, ya ba mu maganin dudda cikin mu sa mata ga abinci ya ɓare?.”

A hasale Yaya Bilya ya juyo ya ce “A’a dai mu sa a kashe muna ita Hasinar ka ga sun tahi da ita da ɗan cikin nata kowa ya huta.”

Tirƙashi! Rigiji gabji

Shin Hasina zata tsira daga zaluncin su Yaya Bilya kuwa?

Wannan cikin za’a haife shi kuwa?

🤔

Ku biyo ni don jin ƙarshen Wannan rigimar….

Follow me on waatpad @Ruky_i_lawal

Telegram Rukayya Ibrahim lawal

Instagram @Rukayyarh_ibraheem
Ka da ku manta more comment more typing🥰

Vote, share and comment

UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️

*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

              *AND NOW*
         *HALITTAR ALLAH CE*

Ga masu buƙatar na tallata masu hajojinsu a shafukan littafina dama shafukana na sada zumunta kamar instagram whatsapp, telegram, Facebook da sauransu sai su tuntuɓe ni ta wannan number _08109634202_

Kowacce irin haja ce gareka/ki zamu tallata maka/ki cikin rahusa insha’allah.

DEDICATED TO ALL MEMBERS OF AREWA WRITERS ASSOCIATION
HAPPY SALLAH

Ina taya ɗaukacin jama’ar musulmi murnan Barka da Sallah, Allah ya nuna mana ta badin baɗaɗa.

Fans ɗina na kirki ga wannan don ya taya ku murnar sallah nasan dama kun ƙagu ku ji karshen wannan labari.

Masu ƙorafin ba a ƙarasa masu ba azumi ya zo ku yi hakuri, yanzu an wuce gun.
________________________________
+
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
PAGE 75-76
Haka suka kwashe tsawon lokaci suna tufka da warwara, kafin daga bisani suka watse bayan sun tsayar da magana akan za su je gun boka ya basu magani su barar da cikin.
Bayan wani dogon lokaci suka samo magani, nan suka haɗa kai da direbanta. Watarana ta aike shi sayen gasasshen nama kamar yanda ta saba tunda ta fara laulayi.  Don haka ya yi amfani da damar bayan ya siyo naman ya biya ya kaiwa Alhaji Sunusi ya barbaɗa mata maganin sannan ya zo ya kawo mata…

Hajiya Hasina ta gyara zama ta saka ledar nama a gabanta burinta ta ci naman ko zata samu sassaucin kwaɗayin da take ji kamar zata ci babu.

Har ta ɗebo yanka biyu ta kai bakinta ta tauna sai dai me? tana haɗiye kaɗan sai ga shi ta dawo da shi.

Amai ta shiga kelayawa ba ƙaƙƙautawa. Ɗaya daga cikin ma’aikatan kitchen ce ta shigo ta risketa a wannan halin, har ta fara aman jini.

“Wayyo Allah na jama’a ku kawo mana ɗauki.” Rabin ta faɗa yayin da ta bar ɗakin da gudu ta nufi gate tana ihu.

A haka suka rarumi Hasina zuwa asibiti,  daga can suka kira Alhaji Munir suka sanar masa halin da ake ciki.

Bayan dogon nazari da binciken da likitoci suka yi suka tabbatar da cewa ta ci guba mai zafi ne a abincinta, ta jigata sosai sai dai cikin jikinta bai fita ba sakamakon kaɗan ta haɗiyi gubar, amma fa zai iya shafar ɗan cikinta.

Sai da ta shafe tsawon lokaci tana jinya kafin ta wartsake daga dafin gubar.

Bayan shuɗewar watanni huɗu a ranar wata Lahadi tun safe naƙuda ta kama Hajiya Hasina.

STORY CONTINUES BELOW
Cikin hanzari Alhaji Munir ya kaita asibiti sai da ta shafe wuni ɗaya cur tana shan baƙar azaba kafin da dare ta haifi ɗanta namiji sai dai me? Hasina ta shiga tsananin tashin hankali da ganin kalar abunda ta haifa.

Wannan ne karo na farko a rayuwarta da ta taɓa yin nadama mafi tsanani akan abinda ta aikata.

Sake kallon halittar dake kwance a gabanta matsayin ɗan cikinta ta yi tana tunano abubuwan da ta aikatawa Abdul da irin tsanar Halittarsa da ta yi, ta manta cewa Allah shi ne yake halitta abunda ya so a sanda ya so kuma ya sanya shi daga tsatson wanda ya so. Ga shi yau ta haifi halittar da tafi ta Abdul muni.

Hawaye ne ke sartu akan kumatunta, Alhaji Munir ne ya shigo ɗakin da murnarsa su Yaya Bilya na take masa baya, domin tun da suka samu labarin haihuwar suka kasa zaune bare tsaye tashin hankali ya cika ruhinsu don haka suka garzayo cikin hanzari don bawa idonsu abinci ko za su san kalar matakin da za su ɗauka tunda sun bar baya da ƙura.

Hasina na jin shigowarsu ta rufe idonta tana tsananin jin kunyar Alhaji Munir a zuciyarta. Bata son ya ga abinda ta haifa masa a matsayin ɗa amma bakin alƙalamin ya riga ya bushe anbar kyau tun ranar wanka.

Hannu ya saka ya ɗauki ɗansa cikin ɗoki yana jin ƙaunar yaron na ratsa shi, bai damu da munin halittarsa ba, sai yake ji kamar ya saba da ganin irin wannan halittar a wani gurin amma ya kasa tunawa. Sai faɗar ya ke “Alhamdulillah! Allah na gode maka da kat nuna min magajina kahin in kwanta dama.”

Yaya Bilya ne ya matso kusa yana faɗar “To Munir ai sai ka ba mu yaron namu mu gani ko?”

Ƙirjin Hasina ya fara harbawa da jin wannan zancen.
Ɗora masa yaron Munir ya yi a hannu, shi kuwa Bilya hannu ya saka ya yaye mayafin da ya rufe rabin fuskar yaron.

Sai ya ga kamar yaron yana kallonsa yana masa dariya da murmushi kamar wani shekararren ɗa, har da ɗaya masa gira. Yaron fari ne ba sosai ba, sai wani ƙungurumemen kansa tamkar Tulu, ga shi da tsamurarren jiki, har kan ya rinjayi jikin, sai idanuwansa ƙwala-ƙwala dake fitar da wani haske dake razana mai kallonsu, dukkan ƙafafunsa biyu a juye suke tafin ƙafar yana kallon sama. siffar yaron tsaf irin ta aljanu.

Kallo ɗaya ya yiwa yaron ya zazzaro ido jikinsa ya soma ɓari bai san lokacin da ya jefar da yaron ba ya na faɗar “Wayyo Allah na! Yau na ga abinda ya fi ƙarfina ni Bilya.”

Mizbahu da ya matso kusa da niyyar leƙen fuskar yaron dake hannun yaya Bilya, ganin yayan ya jefar da shi ya saka ya yi saurin tarbe yaron da saura kaɗan ya kai ƙasa.

Shi ma murmushi da dariya ya ga yaron ya masa, sai ya ji tsoro ya ratsa shi, da sauri ya miƙawa yaya Sunusi shi.

Ja da baya Sunusi ya yi ya na faɗar “Baka da hankali ne Mizbahu? Ta ya zan amsat abinda yat razana min  ‘yan’uwa?”

Kallon Munir Mizbahun ya yi sai ya ga kamar Munir ɗin bai ji daɗi ba, hakan ya saka ya miƙa masa ɗan tare da ciro kuɗi a aljihunsa ya ɗora kan yaron yana faɗar “Don Allah ka yi hanƙuri Munir kasan halinsu ai, Allah ya raya akan sunna, ita kuma Hajiya Allah ya bata lafiya, ka gaisheta in tat tashi.”

Gama fadarsa ke da wuya ya juya da zimmar ya bi yan’uwansa su tafi, sai dai ko da ya juyo wayam ba kowa ashe tuni sun fice daga ɗakin, don haka shi ma ya bi bayansu.

Sosai Alhaji Munir ya ji zafin hakan da suka masa a ransa. Hasina kuwa da yake akan kunnenta komai ya faru, nan fa hankalinta ya ƙara tashi fiye da ɗazu.

A ranta ta ce “Yau fa ake yinta, ni Hasina ake wulaƙantawa ɗa? Ko da yake duk abin da ya samu shamuwa ai watan bakwai ne ya ja mata, kuma kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha.”

Alhaji Munir ya ajiye mata ɗan ya fita, ƙwaƙwalwarsa na son ta tuna masa rana makamanciyar wannan da irin wannan ya faru a rayuwarsa, amma ina……

STORY CONTINUES BELOW
Nan da nan kansa ya fara sara masa saboda haka ya hau motarsa ya je gida ya kwanta.

@@@@@@@@@

KADUNA
Bayan wani lokaci mai tsawo Mahmud har ya fara sarewa da neman Abdul ganin kusan shekara biyu ya shafe ya na abu ɗaya ba labari.

Don zuwa yanzu har ya fara daina fita yawon nemansa da yake kusan kullum.
Watarana yana zaune a ɗakinsa shi da abokinsa Kamal hira suke sama-sama yayin da Mahmud ke aiki a laptop ɗinsa, shi kuwa Kamal yana duba hotuna a wayar Mahmud ɗin.

“Wai Kamal me kake mun da waya ne haka har yanzu?” Mahmud ya faɗa.

Kamal bai ko ɗago ba ya ce”Bana son iskanci Mahmud, Lalatawa zan…. Kai! Wa zan gani haka kamar Abdul?” Ya faɗa yana zazzaro ido.

Mahmud da ada yake ci gaba da aikinsa ba tare da damuwa da abinda Kamal ke faɗa ba, jin ya ambaci sunan Abdul ya saka ya miƙe ya yi gunsa yana faɗar “Wane Abdul kake magana Kamal?”

Nuna masa hoton yaron ya yi ya ce “Wannan yaron kamar na san shi a’ina ka samu hotonsa?”

Cikin tsananin murna Mahmud ya ce “Shike nan kayana ya tsinke a gindin kaba, gaya mun a’ina kasan shi, ina kuma kasan zan same shi yanzu?”

“Waye shi a gareka?” Kamal ya tambaya.

“Ƙanina ne shi, Kamal ai na san ba zaka manta Mommy Zulaiha ƙanwar Hajiya dake aure a Sokoto ba.”

“Tabbas na tuna ta, ai ta kan zo nan lokaci zuwa lokaci ita ce matar nan mai fara’a da son jama’a ko? Idan ban manta ba ka ce duk wani abu da ka zama a yau silarta ne.” Kamal ya faɗa yana gyara zamansa akan kujerar.

“Hakane to ita ce mahaifiyar yaro Abdul, Hajiyata ce ta yi silar ɓatarsa daga hannunmu.”

“Hajiyar da kanta?” Kamal ya ce yana fito da ido waje.

“Eh.” Mahmud ya faɗa yana miƙewa tare da cewa “Labari ne mai tsawo yanzu dai mu je ka kai ni inda zan same shi.”

Miƙewa Kamal ya yi suka nufi gun mota yana faɗar “Zan dai kai ka inda zaka iya samun labarinsa.”

Hanyar unguwarsu Kamal suka ɗauka kai tsaye Mahmud ne ke tuƙin yayin da kamal ke sanar mi shi cewa Abdul ya zauna a unguwarsu kimanin shekaru biyu kafin ya masu ɓatan dabo, har ma yana yiwa mutanen gidansu wanki ana biyansa a lokacin.

Bayan sun isa unguwar Kamal ya nunawa Mahmud inda Abdul ya yi zama dama shagon Oga master na da, inda ya kasance nanne sheƙarsu.

Sai dai me? Ya shaida masa shi ma mai shagon lokaci ɗaya aka neme su shi da Abdul da Ali amma ba a san inda suka je ba.

Mahmud na nan tsaye cikin jimami yana tunanin mafita, Kamal ya Hango tahowar Ali yana dogara sandunansa.

Cikin azama ya girgiza Kafaɗar Abokin nasa, firgigit ya dawo daga duniyar tunani. Nuna masa yaron ya yi ya ce “Ga shi can shi ne Ali tare suka ɓata abokinsa ne.”

Ai da sauri Mahmud ya ƙarasa gun yaron ya masa magana. Guri suka nema suka zauna ya kwashe duk labarin abunda ya faru tun daga isarsu Legos har zuwa ranar da ya taho ya manta da shi can.

Mahmud ya kaɗu ya girgiza matuƙa da jin halin da ɗan’uwansa ke ciki ta wani ɓangaren kuma ya ji daɗin samun labarinsa don haka ya kalli Ali ya ce “Ya sunan kasuwar da kuke zaune, inda zan same shi yanzu?”

“Kasuwar Bandir.” Cewar Ali.

Godiya sosai ya ma Ali sannan ya masa kyauta suka juya, ƙofar gidansu Kamal ya sauke shi ya wuce gida domin shirin zuwa Legos.

Haƙiƙa yanzu yana process ɗin neman aiki ne, amma ya ji a ransa cewa ya fasa nema a nan zai je Legos ɗin in har bai samo Abdul ba to ba shakka a can zai nemi aiki domin ba zai daina neman Abdul ma muddin Rai har sai ya gano koda gawarsa ce.

STORY CONTINUES BELOW
Don haka koda ya je gida ma ya shaidawa Hajiyarsa ƙudurinsa bata hana shi ba, itama zata so hakan. Don haka ta masa fatan nasara.

@@@@@@@@

Hasina bata janye ƙudurinta na son mallakar dukiyar Alhaji Munir ba, duk da cewa jikinta ya yi sanyi laƙwas da wannan haihuwar tata, sai dai wanda ya riga ya yi nisa baya jin kira don haka take matuƙar son Mummunan ɗan nan nata kamar rai,domin shine jarinta.

Tarairayarsa take kamar ƙwai bata son ko ƙuda ya hau kansa duk da uwar Azabar da take sha gun shayar da shi, domin tsotonta yake kamar ba gobe, haka ji take kamar yana tsotse jinin jikinta ne domin duk ta zuƙe ta lalace Kamar ba Hasina dirarriyar mace ‘yar ƙwalisa ba.

Kulu kuwa tun ranar da aka haihu ta je asibitin, data yi arba da wannan mummunar halittar bata dawo ba tun ranar, ko Hasina ta kira ta haka zata bata wani uzurin na ƙarya, don har ga Allah tsoron wannan aljanin yaron take.

‘Yan Barka kuwa duk wanda ya zo sau ɗaya baya dawowa, yaron Allah ya zuba masa baƙin jini tamkar ɗan jaɓa. In ka ɗauke mahaifiya da mahaifinsa ba mai sonsa.

‘Yan shan miyar hajiyar kowa ya watse bikin da ta yi fatan ayi babban shagali na gani na faɗa haka aka yi shi ba kowa, abincin da aka dafa ma sai bi aka yi gida-gida ana rabarwa.

Ɓakin ciki kamar ya kashe Hasina.

Yaron da ya ci sunan Kabir kuwa yana nan sai wayo kamar shekararre, haka ta ci gaba da rainon abinta har tsawon wani lokaci.

Tsakanin ‘yan’uwa da ƙawayenta kuwa da yawa sun bata shawarar ta kai yaron bakin gulbi in har zargin mutane ya tabbata cewa ɗan ruwa ne ko aljani to zai faɗa cikin ruwan ne kowa ya huta.

Sai dai jin su kawai take, bata jin zata iya jefar da ɗan cikinta wanda ta sha wahalar haihuwarsa, hakan ya sa duk wanda ya bata shawarar nan suke rabuwa baram-baram.

@@@@@@@@@

Bayan shekara ɗaya.

Har zuwa lokacin su Alhaji Bilya basu daina farautar ran Kabir ba, kuma basu yi nasara ba, abun ya zame musu tamkar tufkar makaho ta gaba ta baya na warware wa.

Hakan ya saka watarana Alhaji Bilya ya sulale shi kaɗai ya nufi gun wani boka da ya samu labarin cewa aikinsa kamar yankan wuƙa.

Bayan shafe doguwar tafiya ya sadu da dajin da bokan yake.
Nan ma ya yi dogon jira kafin a masa izinin shiga.

Bokan ya kalle shi ya bushe da dariya tsawon lokaci kafin ya murtuke fuska ya ce “Sannu da zuwa la’ananne na san meke tafe da kai, wato ka gaji da jiran lalataccin yan’uwanka da jijiyoyinsu suka yi sanyi akan tafiyar shi ne kai ka zo?

Da tun farko nan kuka zo da tuni Alhaji Munir ya tsufa a lahira, amma….”

Sai kuma ya yi shiru can ya kalli Bilya da tulu-tulun idanunsa da suke razanar da mai kallonsu ya ce “Me kake so a yiwa yaron da yan’uwanka?”

“Ina son a kashe min yaron da ubanai su kuma ƙannena a mallake min su su dawo ƙarƙashin ikona sai abinda na ba su, dukiyar Munir ta zama tau gaba ɗai.” Cewar Bilya.

Wata irin mahaukaciyar dariya bokan ya kuma kwashewa da ita sannan ya ce “Lallai ka cika mugu azzalumi la’ananne, irinku muke so marasa imani, yanzu zan haɗa maka magani in har ka yi nasarar amfani da shi shikenan Kakarka ta yanke saƙa.”

Sosai Bilya ya ji daɗi ya shiga washe haƙora.

Bayan wani ɗan lokaci bokan ya haɗa masa komai ya hau motarsa ya kamo hanyar gida.

Tafiya yake a hanya ransa fes har zuciyarsa ta fara hasko masa tsiyar da zai tsulawa yan’uwa da dangi idan ya mallaki kuɗin, sai murmushi yake zabgawa shi kaɗai. Shaf ya manta cewa ramin ƙarya ƙurarre ne, sannan ‘yan magana sunce idan zaka gina ramin mugunta gina shi gajere domin watarana zaka iya afkawa.

STORY CONTINUES BELOW
Yana cikin wannan saƙe-saƙen bai san ya aka fara ba sitiyarin motar ya ƙwace masa motar ta daki wani ice, tun lokacin bai kuma sanin ya aka yi ba, sai farkawa ya yi ya ganshi kwance a wata buka ƙafarsa ɗaya ɗaure tamau da karan ɗori haka kansa ma a ɗaure yake da wani tsumma sai dai ba kowa a kusa da shi.

A can gida kuwa da ‘yan’uwansa suka ga an kwana basu gansa ba, suka kira wayarsa nan ma shiru, sai suka shiga nemansa. Hankalin matansa da ƴaƴansa ya dugunzuma da aka shafe sati ɗaya ba a ji ɗuriyarsa ba.

Sai a sati na uku da batarsa wani makiyayi ya zo har gida ya sanar masu abinda ya faru sannan ya shaida masu majinyacin yana gidansa yanzun haka shi ne ma ya kwatanta masa nan ya zo.

Jin haka ya sassauta tashin hankalin da iyalan nasa ke ciki don haka suka je suka ka taho da shi gida don iyalansa su ci gaba da kula da shi.

Asibiti suka kai shi nan likitoci suka shaida masu sai dai a yanke ƙafar domin ta riga ta lalace saboda rashin samun kyakkyawar kulawa har na tsawon Sati Uku, inda ma aka ɗaure masa a ƙauyen ba nan ne asalin ciwon yake ba.

Jin wannan labarin ya tashi hankalinsa matuƙa, shikenan yanzu zai rasa ƙafarsa ba tare da ya cimma burinsa ba? Nan take ya gano duniya ba a bakin komai take ba, duniya budurwar wawa ce tabbas yanzu ya yarda da haka.

Bayan kamar shekara da faruwar wannan al’amari Bilya yana zaune a gida da yankakkiyar ƙafarsa ɗaya yana tunanin yanda lokaci ɗaya duniya ta masa atishawar jaki tsakar ka. Ga shi yanzu iyalansa da yake son cimma wannan burin saboda su sun juya masa baya, matansa biyu sun gudu a cewarsu sun gaji da zama da nakasasshe gashi yanzu komai nasa ya ƙare dama can shi ba mai tanaji bane da ya samu yake cinyewa, ko banza ma ƙasusuwansa sun raunana don zai kai shekaru 60. Uwar gidansa Hannatu ce kaɗai ta zauna da shi, a faɗarta zata kula dashi ko dan albarkacin yaran dake tsakaninsu da zumuntar dake tsakani.

Ƴaƴansa ma sun fara gajiya wa da hidimarsa, a taƙaice dai komai ya dagulewa Alhaji Bilya.

A na tsaka da haka ƙaddara ta faɗawa Sani watarana ‘yan fashi suka rutsa shi a gidansa, bayan sun saci adadin dukiyar da ta masu, sai suka harbe shi a take ya mutu ko shurawa bai yi ba.

Lokacin da labarin ya riski yan’uwansa sun kiɗime sosai ba shakka sun sani suna girban abunda suka shuka ne, sakayya ce suke gani tun a gidan duniya.

Sunusi kam duk ya fi su kiɗimewa don ya san abinda ya samu sauran yan’uwansa ba zai barsa ba don a tare suka aikata komai, nan take ya ji yana sha’awar rayuwar ƙaninsu Mizbahu, inama ace shine Mizbahun da yafi kowa farinciki a yau.

Mutane sun cika da ta’ajibin wannan abu da ya faru da ‘yan’uwan nan a cikin yan shekarun nan. Sai dai banda Mizbahu da ya san duk abinda suke ƙullawa.

Watarana Mizbahu ya je gida gaida Babarsa ya same ta cikin yanayin damuwa.

Zama ya yi kusa da ita ya ce “Hajiya Inna meka damunki  haka?”

Numfashi ta sauke cikin Muryar tsoffi ta ce “Babu komi kawai ina jinjina abinda yat hwaru da yan’uwanka na a ‘yan shekarun ga,sai ka ce waɗanda sunka aikata wani zunubin, Allah na tuba astaqfurullah.”

Gyara zama ya yi ya nisa sannan ya ce “Tabbas Hajiya Inna, su yaya sun fara girbat abinda sunka shukka ne, dama duk wanda yacce tukunyat wani ba ta tawhasa  to tashi ko zahi ba ta yi. Dama kuma duk tsuntsun da yat jawo ruwa shi ruwa ka bugu.”

“Bangane ba ɗan ga, yimin kwata-hilla, shin wani mummunan abu sunka aikata haka?.”  Ta tambaya.

“Tabbas Hajiya Inna Ɗiyanki sun aikata abu mahi muni ga rayuwa, sun cutar da ɗan’uwansu mai yawan ƙaunarsu, yaron da bai taɓa nuna miki banbanci tsakaninki da Uwatai ba, su da kinka haihwa sun hana miki shigihwar zama amma shi ya se miki gida dungurungum. Basu dubi karamci nai ba hassada tasa suka miƙe tsaye don ganin baya nai har gidan bokaye suka zuwa, sun so sani cikin tsarin su Allah ya kare ni shiyassa kinka ga ba su ga maciji da ni.”

STORY CONTINUES BELOW
Salati kawai ta hau yi sannan ta ce”su su Sanin?”

“Ƙwarai ko, dut wata badaƙala da kinka ga tana hwaruwa gidan Munir har zuwa ɓacewar ɗanai Abdul su nika zargi.” Ya faɗa

Tari ta fara yi yana mata sannu tare da miƙa mata kofin ruwan dake kusa da shi, bayan tasha ta nutsu ta ce “Tabbas Abunda sunka shukka suke girba, saura Sunusi bamu san kalar ta shi kaddarar ba.” Ta faɗa da yanayin damuwa sosai a fuskarta.

Ganin ta shiga damuwa sosai ya saka ya tsaya yana ta kwantar mata da hankali har ta samu ‘yar nutsuwa sannan ya bar gidan.

Wannan labarin da ta ji shi ya haifar mata da damuwa har ta kamu da ciwon zuciya.

Bayan kamar wata biyar Amaryar Sunusi ta haihu(dama tana da ciki)

Mizbahu bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya shirya ya je shi kaɗai, kasancewar yaya Bilya ba zai iya zuwa ba, Sani kuma ta Allah ta kasance da shi, Munir ne kaɗai ya rage wanda zasu iya zuwa tare, sai dai ko da ya kira shi, sai ya ce masa “Yaya ka tahiyakka ɗai, ni na yi alƙawarin ban zuwa barkar kowa cikinsu, shi ma ya ɗanɗana ya ji inda daɗi.”

Hakan ya sa jiki a mace ya hau motarsa ya nufi gidan Sunusi, da yake a gida ta haihu.

Sai dai me? Bayan sun gaisa da Yaya Sunusin ya zauna jiran a bashi yarinyar ya ji shiru. Hakan ya sa ya kada baki ya ce “Yaya a ɗauko min yarinyarmu in gani.”

Nan Sunusi ya shiga yi masa hanya-hanya, har ya gano da matsala. Su na nan zaune sai ga yayar Amaryar ta fito da yarinyar a hannu ta miƙawa Mizbahu tana faɗar “Haba Sunusi! Ya zaka hana mai ganin ɗiya tai? shi ma yana da haƙƙi akanta hwa.”

Kallo ɗaya Mizbahu ya yiwa ‘Yar y kauda kai, haƙiƙa yayunsa suna ganin jarabawa Sakamakon abunda suka aikata. Yarinyar Baƙa ce mummuna ta ƙarshe wani abun ban tsoro da al’ajabi a halittarta shi ne yanda bata da fatar hanci , ga ƙwarmin hancin kana gani amma a buɗe yake ba rufin saman. Sosai imani ya ƙara shiga zuciyar Mizbahu ya ce a ransa.
“Allah gwanin iya halitta, mamallakin sarki mai fitar da rayayye daga cikin matacce, wanda cikin ikonsa da isarsa yake Halitta abinda ya so, ya sanya shi ya fito daga tsatson wanda ya so buwayi gagara misali kenan. Yau ga shi duk irin tsanar da yaya Sunusi ya yiwa Halittar Abdul ga shi ya samu kwatankwacinta.”

‘Yar bata fi minti uku a hannunsa ba ya miƙawa Alhajin ita tare da ɗora kuɗin Barka a jikinta ya ce “To Yaya Allah ya raya ya ɗayyaba, a ci gaba da tsarkake zucciya ana kiyaye halshe don ko Allah shi ne mai yin yadda ya so.”

Daga haka ya wuce abunsa.

Sarai Yayan ya gane magana ƙaninsa ya yaɓa masa ya kuwa ji zafin haka sosai a ransa ya ce “bakomai ai duk abinda ya samu shamuwa watan bakwai ne ya ja mata.”

Wannan ita ce rana ta farko da Sunusi ya ji ya yi nadamar abunda suka aikatawa ƙaninsu, har yake jin kamar ya je ya roƙi gafara, sai dai ina ba zai iya ba, abun da kunya.

Bayan kamar wata Shida ciwon zuciya ya yiwa Hajiya Inna yawa da dare ta ce ga garinku. Sai gawarta aka tarar wanda silar hakan bakomai ba ne face yawan tunawa da take da abunda ƴaƴanta Uku suka aikatawa ɗan uwansu mai yawan son su, da kuma sakayyar da suke gani. (Allah ka bamu zuri’a shiryayya ka azurta mu da yayan da zasu ji ƙanmu ba waɗanda zasu yi silar aikamu lahira ba ameen.)

@@@@@@@@@@@@@@

Abdul kuwa yana Legos yana ci gaba da rayuwa cikin Sabbin iyalansa, maganar ƙauna da shaƙuwa dake tsakaninsa da ƙanwarsa Sabira kuwa sai dai ayı kurum don zuwa yanzu abun nasu ya wuce yan’uwantaka ya rikiɗe zuwa soyayya, domin basa iya yin nesa da junansu, makaranta kaɗai ke raba su saboda shi yana jami’a ne yanzu ita kuwa tana secondry school.

Daddy da Mummy suna jin daɗin wannan soyayyar dake tsakanin ƴaƴansu ko bakomai zasu cika burinsu na aurar da yarsu ƙwalli ɗaya ga abun alfaharin su Abdul.

Don zuwa lokacin ya ciyo kyautuka da dama tun yana secondry har zuwa yanzu sai nasarori suke ƙara samu a rayuwa silar riƙon Abdul, ga shi ya janyo wa gidan ɗaukaka sosai.

Bayan shekaru Bakwai da Haihuwar Hasina wani tashin hankali ya Kunno a rayuwarta, domin zuwa yanzu ita da kanta ta tabbatar wannan yaron aljani ta haifa ba Mutum ba, bayan duk wani burinta ya ruguje silar faɗan da ta yi da bokanta akan turo mata cikin iska da ya yi.

Kwance take tana juyi cike da damuwa Muryar Bokan ke dawo mata a kunne tamkar yanzu yake faɗa “Hahaha Hasina kenan, ba ke kika ce tusa zata hura wuta ba? Yanzu ne zaki shiga tashin hankali irin wanda baki taɓa hasasowa a rayuwarki ba, Ni kika ƙarewa zaki ko? Ki je zaki ga Ni. Zamu ƙwace yaron mu ke da haihuwa kuwa sai a lahira in ana yi, kuma zan ruguza dukkan burukanki a rayuwa.”

Cike da tashin hankali ta ƙara mirgina wa ta na tuno irin amsar da ta Mayar masa “Ai baka isa ba Bakuza, Ni na fi karfinka da izinin Allah da kai da ba kai sai na cimma burina a rayuwa.”

Dogon numfashi ta ja, cike da razana ta miƙe zaune jin ƙarar yaronta Kabir, da gudu ta fita tana jin yanda cikinta ke murɗawa ba don komai ba sai don tuna alƙawarin Bokanta a kanta, yau sati ɗaya kenan da suka yi faɗan.

Ko da ta je ta tarar da ya faɗo ne daga kan kujera don har a lokacin baya iya tafiya, iya zama kawai yake.
A daren ranar ne Alhaji Munir ya farka daga barci a matuƙar razane da alama ya yi wani mafarkin da ya rikita masa ƙwaƙwalwa ne.

“Innalillahi wa innailaihir raji’un!” Ya faɗa yana dafe kansa tare da saukowa daga kan gadon a ransa yana Faɗar “Wannan miskinin yaron da ya addabi duniyar mafarkina ba mamaki ina da alaƙa da shi, kamar yanda aka nuna mun a mafarkin nan nawa.”

Arwallah ya ɗoro ya zo ya tada sallah tare da kwararo addu’a kamar haka “…….
To fa readers mun dawo, karku manta more comment more typing ƙarancin comment kuwa….☹️

Follow me on wattpad@Ruky_i_lawal

Instagram @Rukayyarh_ibraheem
Facebook…..
Telegram……

UMMU INTEESAR CE❤️❤️
@@@@@@@@@@@@@@@

*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

              *AND NOW*
         *HALITTAR ALLAH CE*

Ga masu buƙatar na tallata masu hajojinsu a shafukan littafina dama shafukana na sada zumunta kamar instagram whatsapp, telegram, Facebook da sauransu sai su tuntuɓe ni ta wannan number _08109634202_

Kowacce irin haja ce gareka/ki zamu tallata maka/ki cikin rahusa insha’allah.

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 77-78

“Ya ubangijina kai ne mahallicin ruhukanmu kai kasan sirrin ɓoye dana sarari, Allah ka bayyanar mun da gaskiyar abunda na gani a mafarki. La’ilaha illa antas-subhanaka inni kuntu minaz-zalimin, Allah ka kwance mun wannan ƙullin in har da gaske ina cikin kullin sihiri, sa’annan ka bayyanar mun da maƙiyana na baɗini don na nisance su.”

Yana gama addu’ar ya shafa ya miƙe har ya hau gado zai kwanta ya ji kunnuwansa na tariyo masa zancen da aka gaya masa a mafarki, nan danan idanunsa suka shiga hasko masa yanda ya ga mutumin mai sanye da fararen kaya a tsaye gabansa, duk da bai yi nasarar ganin fuskar mutumin ba saboda tsayinsa, amma kunnuwansa basu manta abunda ya ji ba “Da akwai sihiri a jikinka ya kai bawan Allah, rayuwarka tana zagaye da Mahassada masu son ganin bayanka kai da tilon ɗanka a duniya, ka je ka nemo ɗanka tun lokaci bai yi ba da zaka rasa shi har abada.” A cikin mafarkin yake tambayar mutumin “Yanzu ya zan yi don warware Sihirin daga jikina.”

Juya mutumin ya yi kamar zai tafi sai ya gaya masa wasu ayoyi da addu’o’i na warware sirri ya ce “Ka karanta ka tofa a ruwa ka dinga sha kana shafe jikinka, insha’allah zaka dawo kamar da.”

Tuna hakan ke da wuya ya juya ya ɗauki robar swan dake kusa da shi ya tsiyaya ruwan a kofi ya tofa addu’o’in da suka zauna a kwanyarsa daram ya sha ruwan saura kuma ya shafe a jikinsa.

Duk wannan abun da yake Hasina bata sani ba, tana kan gado ita da Mummunan ɗanta,ta ba shi baya sai shaƙar barcinta take har da minshari. Da ta san abunda Munir ke shirin aikata mata da tabbas ta yi yanda duk zata yi don hana faruwar hakan sai dai Rashin sani ya fi dare duhu.
Bayan kamar sati Uku Munir na shan Ruwan addu’ar da ya mayar tamkar abinci, cikin ikon Allah wata ranar Talata da dare ya kwanta ya yi mafarki da Abdul ya zo masa cikin Sutura mai kyau kuma da lafiyayyen ƙafafunsa yana Faɗar “Abbuna duba ka gani na samu sauƙi yanzu ina iya tafiya  dadaɗɗen burinka ya cika, Abbuna ka zo gare ni ina tsananin buƙatarka a kusa da ni.”

Firgigit ya farka yana ambaton sunan Allah a bakinsa.

Hasina da yake bata yi barci ba tana ta tufka da warwara na ƙulle-ƙullen da ta saba, jin motsinsa ta miƙe zaune tana faɗar “Baban Kabir lafiya meya faru?”

STORY CONTINUES BELOW
Tamkar wanda ya tashi daga dogon suma ya zuba mata ido zuru-zuru, jin Sunan ya yi wani banbarakwai wai Namiji da suna Zainabu. Don haka bai ko Kulata ba jin kansa na masifar ciwo, ya koma ya kwanta tare da juya mata baya.

Ai kamar an kunna masa Tv a hankali ya ci gaba da tuno rayuwarsa ta baya tun daga aurensa da Zulaiha har zuwa sanda kansa ya motse.

Miƙewa ya yi Zumbur ya fita yana dafe bango gudun kada ya fadi.

“Ina zaka na Baban Kabir?.”

Falo zan je na sha iska, na ji yanayin nan ya fara sauyawa zuwa mara daɗi.

Bata kula da shi ba kawai ta tabe baki ta mayar da kanta ta kwanta.

Shi kuwa yana fita bai zame ko’ina ba sai tsohon ɗakin Abdul ya zauna bakin gado ya yi shiru yana tunanin halin da rayuwar tilon ɗansa zata iya faɗawa “Yana ina yanzu? Shin ko yana da makwanci? Yana samun wadataccen abinci? Zancen karatunsa fa?”

Wannan tunanin ya zauna yana yi tsawon lokaci kafin ya miƙe ya koma ɗaki, bayan ya yanke hukuncin zai yi bincike cikin ruwan sanyi don ya gano suwa suka aikata masa hakan, ita kanta Hasinar ba zai sanar mata ba har sai ya kammala binciken domin ‘yan magana sun ce ‘in baka iya kama ɓarawo ba, shi sai ya kamaka.’

Don haka ba wanda ya nunawa cewa ya tuna komai.
Sosai ya zurawa Hasina ido Game da al’amurranta.

Wata rana kamar ko yaushe Hasina na zaune Falo da ƙawayenta da yamma wajajen 5, Alhaji Munir ya shigo, bako sannu da zuwa ta dube shi a sheƙe ta ce “Har ka dawo?”

“Eh Hajiya.” Ya amsata kamar yanda ya saba.

Yamutse fuska ta yi ta ce “Ok tahi yiwa Kabir wanka, idan ka gama ka gyaramun Uwar
Ɗakana, ka da ka sake kamun kuskure yau don zan mugu saɓa maka wallahi.”

Dama haka take masa duk ta ga ƙawayenta don ace takai isasshiya, wai don ma yanzu ta yi sanyi.

Har ya buɗi baki zai yi magana zuciyarsa ta kwabe shi can ƙasan ransa ya ce “Wato ke ga kin samu kan miji ko? Ba dan ina son ganin gudun ruwanki ba yau da na nuna miki shayi ruwa ne.” Ya yi ƙwafa a  can ƙasa-ƙasa yanda ba zata ji ba.

Sumi-sumi ya wuce kamar kullum yana Faɗar “To rankiyadade.”

Wani shu’umin murmushi ta yi tare da rausayar da kai ta ci gaba da Hira da ƙawayenta.

Bayan minti Biyu Shatu marar haƙuri ta ce “Gaskiya Abukkiyata kina zuba lokacinki, ji yadda kika ba shi umurni kamar wani ɗanki.”

Wata shu’umar dariya Hasina ta sheƙe da ita tana Faɗar “Sa wasa macce, an gaya miki hakanan kurum nike zaune shirim kamar ku da mazaje ke walaƙantawa a gida, ni Boka na aikinai kamar yankan yuƙa yake in hwaɗa miki, in cewa ma niyyi ya maidammin shi kamar jela ya zama ko gidan buki yana tare da ni yana iyawa.”

Shewa sauran ƙawayen Uku suka saka tare da tafa hannayensu wacca ta yi magana ɗazu ta sake cewa “Gaskiya ina nan tahe ki rakkan gidan Bokan ga, da Mijina yana da arziƙi kamar haka kai tsaye zan sa a kashe min shi mu ci gado, amma ina tsiya ta masa katutu.”

Ras! Kirjin alhaji Munir ya buga da ya ji wannan zancen, dama yana laɓe a bayan labule daga ciki don ya san dama za’a rina tunda aka saci zanin mahaukaciya.

Ci gaba su ka yi da hirarsu yayin da shi kuma yake jiyo su. A nan Hasina take shaida masu ita ma ta so ta saka a kashe mata shi, don zuwa yanzu ta ƙosa da jiran mutuwarsa mutum tsawon rai sai kace aljani?.

Anan kuma ta shaida Musu ta yi faɗa da Bokanta sai dai ta ɓoye musu alƙawarin karɓe yaronsu da ya mata.

Suna dakatawa da zancen Alhaji Munir ya juya cikin sassarfa kamar zai kifa da ƙasa tsabar gigicewa dishi-dishi ma yake gani.
“Kai jama’a wannan rayuwar dame ta yi kama, ace mace zata iya cutar da mijinta kan abun duniya? Ina ma ban tara wannan dukiyar da kuke rububi a kai ba da na huta.” Munir ne ke zancen zuci kan hanyarsa ta shiga ɗaki.

STORY CONTINUES BELOW
A daren ranar Hasina ta farka ta shiga bayi kenan ta jiyo alamun motsi-motsi da surutai can ƙasa-ƙasa. Ƙara kashe kunne ta yi don ta ji ko Munir ne, sai dai ba muryarsa ba ce. A hankali wata murya ta raɗa mata wannan zancen a kunne “Mun zo tafiya da yaronmu ne fa Hajiya kuma baki isa ki hana ba, alfarma ɗaya zamu miki zamu bar miki siffar gangar jikin a nan.” A razane ta ɗago tana neman mai mata magana amma bakowa a bayin sai ita kaɗai. Duk da haka ta dake tace “Don Allah kumin rai ku bammin Kabir wallahi in sonai matuƙa ni kaɗai na san wahalar da na sha tun dagga kan cikinai har renonai.”

Sai dai har ta ƙaraci surutunta bata sake jin motsin komai ba bare ta saka ran za’a amsa mata. Hakan ya saka ta fito a hanzarce har tana haɗawa da gudu ta nufo kan gadon don duba yaronta.
Abunda ta gani ya matuƙar gigita duniyarta, a kiɗime take bin farin hasken dake fita daga jikin yaronta yana yi sama, haka ta cigaba da bin hasken da ido har ya ɓacewa ganinta, hankali a matuƙar tashe ta maida dubanta ga yaron sai ta ga kamar baya motsi, hakan ya saka ta ɗora hannunta kan hancinsa ta ji baya sheda, da alama ruhinsa ne ya bar gangar jikinsa shi ne kuma farin hasken da idonta suka gane mata fitarsa.

Duk wannan abun dake faruwa Alhaji Munir na kwance a gefen gadon bai sani ba (kasancewar har zuwa wannan shekarun Hasina bata yarda ta raba Shimfiɗa da ɗan nata ba, duk da ya shekara bakwai a ta takwas, a cewar ta mabuƙaci ne ko yaushe zai iya neman taimako, tunda ko tafiya baya iya yi.)

Ihun da ta zunduma ne ya tashi Alhaji Munir daga nannauyan barcin da yake yi.
“Lafiya Hajjiya? Ya kike mana ihu da dare haka?”

“Alhaji duba min Kabir ka gani kamat babu shi.” Ta faɗa a lokacin da take girgiza gawar idonta na kanshi sai hawaye take tsiyayarwa daga idonta.”

Matsowa kusa ya yi yana kallon gawar, hannu ya saka ya tattaɓa wasu sassan jikinsa. Kawai sai ya koma ya kwanta ba tare da yace mata Uffan ba. Hakan da ya yi yasa ta gano bakin zaren don haka ta ƙara sautin kukanta tana faɗar “Na shiga Ukku na lalace ni Hasina, tabbas ina cikin ɗemuwa da dana sani. Baka kyauta min ba Bakuza, da ka banni da ɗana da ina iya baka komi da nit mallaka a rayuwa don a yanzu nafi son ɗannan akan komai.”

Munir na jinta amma bai tamkata ba kawai ya rufe idonsa yana neman janyo barci da ƙarfi, domin haƙiƙa yana jin raɗaɗin wannan hali da matarsa ta jefa kanta don kawai kwaɗayin abun duniya yanzu ga shi ta janyo masa ya rasa magajinsa a karo na biyu.
Wasa-wasa ƙaramar magana ta zama babba domin a ranar dai Hasina bata yi barci ba sai wasu Surutai take marasa kan gado.

Washegari aka fara zaman makoki gidan ya cika da jama’a, sai zuwa ake ana jajanta masu, wasu kuma kwaɗayi ne da gulma kawai ya tara su.

Hasina ce zaune a falo ita da ‘yan uwanta mata sai Surutai take kowa ya kasa gane kanta, can ta zabura ta miƙe da sauri ta nufi hanyar waje ana ta kiranta ko waiwayowa bata yi, hakan ya saka yaya Hafsa (yayar Hasina) ta biyo bayanta don ganin kamar ba a hayyacinta take ba, haka su mai adashen sharri duk suka rufa masu baya.

Bata zame ko’ina ba sai cikin dandazon mazan dake zaune a harabar gidan. Kai tsaye gaban Alhaji Munir ta je tare da saka hannu ta janyo hannunsa tana faɗar “Alhaji tashi mu tahi, ka taimaka ka rakke ni eurin Boka na karɓo ɗana.”

Kowa dake gurin ya zubo mata ido cike da al’ajabin zancenta. Hakanan Munir duk da bai yi mamaki ba don ya ji a bakinta tana biyar bokaye.
“Hasina ki koma ciki kawai, baki da imani ne ko baki yarda Allah shine mai rayawa da kashewa ba?.” Ya faɗa a ɗan zafafe.

“Wannan kam ba Allah yat ɗauke shi ba boka na, dama ya hwaɗa min cewa zasu amshe ɗansu da sunka ba ni, kuma wallahi ni ina son ɗan ko aljani ne su bar min. Tashi mu je.” Ta kuma faɗa tana ƙara jan hannunsa a zafafe ya ƙwace hannunsa tare da kwaɗa mata mari yana cewa “Dama ni nit tura ki wurin boka balle in rakke ki ki amso wani ɗa? Ashe ma ɗan Aljanu ne ake yaudara ta da shi.”

STORY CONTINUES BELOW
Marin da ya mata ne ya ƙara birkitata, da har zata faɗi yaya Hafsa ta tare ta, Kulu mai adashen sharri kuwa sai ƙoƙarin janye ta take daga gurin ganin zata fallasa dadden sirrinsu.

Dariya Hasina ta kwashe da ita sannan ta ce “Ni ka mara dai? Gaskiya na yi sakaci lokacin da boka yat bani shawarat a kashe ka niƙƙiya, ko da yake dama burina bai wuce in mallake dut abinda kat tara ba, dalili kenan da yadda nit aureka tun hwarko, kuma shi at dalilin da yassa nicce ma boka ina son haihuwa har aka ban ɗan aljanu don ya zama shi ne mai gadon dukiyarka bayan ranka tunda har na yi nasarat nisantaka da ɗanka Abdul, nisan da har abada ba zai dawo ba don na sa an ɓassarmai da komi game da tunanin dangi balle ya dawo.”

Kulu na jin Hasina ta fara tone-tone sai ta sulale ta bar gidan gudun kada sunanta ya faɗo a jawabin Hasina. Ashe fa ta yi farar dabara don tun bata ƙarasa gate ba ta jiyo Muryar Hasina na faɗar “Bisa ga jagorancin Abukkiyata Kulu mai adashen sheri munka aikata komi.” Da sauri ta ida ficewa daga gidan tana sassarfa, fatanta shi ne ta samu abun hawa kafin a fara nemanta.

A takaice ce dai haka Hasina ta gama tona asirin kanta tas kafin daga bisani ta shiga ɓaɓɓaka dariya tana rawa tana wa kanta kirari “Sai Ni Hasina Matar Munir Uwa ga Kabir ɗan sarki ƙawar Kulu mai adashen sheri burinmu cikakke ne.”

Ganin abun ya zama hauka tubran ya sanya yaya Hafsa dake tsaye gefe jiki a mace ta kamata, sauran matan dake gurin suka kamata da ƙarfin tuwo suka shigar da ita ciki tare da sakata ɗakinta suka rufe. Duk da sun sha naushi gwargwado.

Nan fa Mizbahu da Sunusi suka shiga kallon kallo, Mizbahu na tausayawa rayuwar ƙaninsa da ganin waɗannan jarabawoyin dake bibiyar rayuwarsa.

Alhaji Munir da ya gama kunyata a cikin jama’a ya yi tsamo-tsamo da shi kamar kazar da aka zaro daga ruwan zafi. Har ya miƙe zai shiga ciki da hanzari Sunusi ya ta so daga inda yake ya zo ya kama ƙafarsa yana ba shi haƙuri faɗar yake “Don girman Allah ka gafarta mana ɗan uwana, haƙiƙa mun aikata babban kuskure a rayuwa wanda a yanzu muke girbarsa mu duka, dama zunubi romo ne. A madadin ni da sauran yayyena muna ƙara neman afuwarka.”

A daddafe ya ce “Da kuka yi min me yaya? Don Allah tashi kana sa ina jin kunya.” A nan Sunusi ya kwashe komai da suka aikatawa Munir ɗin tun daga farko har yanzu ya faɗa.

Munir ya firgita matuƙa dalilin da ya saka ya wuce zuwa ɗakinsa ba tare da yace komai ba, daƙyar ya ƙarasa ɗakin ko gani baya yi tsabar damuwa da ta yiwa rayuwarsa ƙawanya a yau. Yau ya tsinci kansa a cikin halin da ko a duniyar mafarkinsa bai taɓa zato ba, ƙwaƙwalwarsa bata taɓa hakaito masa cewa irin waɗannan mutanen na jikinsa sosai za su iya cutar da shi ba, lallai duniya abar tsoro ce.

Jama’ar dake harabar gidan kowa ya shiga tofa albarkacin bakinsa. Masu tsinewa ‘yan’uwan Alhaji da matarsa na yi masu addu’a na yi, kowa yana ta’ajibin wannan al’amari.

Sosai Mizbahu ya ji kunyar wannan abun da ya faru hakan ya saka ya miƙe yana Faɗar “Dama shi alhaki kwuikuyo ne mai shi yake bi, yau ga shi ko wannenku ya girbi dai-dai da abinda yay shukka.” Yana faɗa idonsa na kan yaya Sunusi (dake zaune a gurin jiki ba ƙwari) da alama da shi yake.
Yana gama faɗa ya fice daga gidan ‘yan zaman makokin ma duk suka  tunda sun ji komai basu ga dalilin da zai sa su ci gaba da zaman makokin jinsin da bana su ba.
Anan suka bar yaya Sunusi ya kasa tashi daga gun yana jiran gafarar ɗan uwansa, in ba haka ba yau baya jin zai iya barci
Tun daga ranar Munir ya kwanta ciwo sakamakon saka damuwar ‘yan’uwansa da matarsa da ya yi a ransa.
@@@@@@@@@

Bayan wasu shekaru da Mahmud ya share zaune a Legos tare da iyalansa yana aikinsa tare da cigaba da neman ɗan’uwansa Abdul wanda hakan ya zame masa tamkar shan maganin Bature. A kullum kwanan duniya in ya fita waje sai ya ji a ransa cewa zai ga ɗan uwansa Abdul, kasuwar Bandir kuwa ta zame masa gida. Shida Hajiya sai dai su yi waya ko in yaje Kaduna ganin gida shi da iyalansa. Yaransa guda Uku kuwa har sun saba da Labarin Uncle Abdul domin ba ranar da zata zo ta wuce ba tare da Abbansu ya basu labarin Uncle Abdul ba matuƙar yana gari, har ƙatuwar poster hotonsa suke da a falonsu. Hakan yasa suka taso da ƙaunar uncle ɗin na su duk da cewa ba su taɓa ganinsa ba sai dai a hoto.

STORY CONTINUES BELOW
Wataranar Laraba Mahmud ya ta so daga gurin aiki da misalin ƙarfe biyu na rana ya biya bankin First bank domin ya gyara matsalar account ɗinsa da take ci masa tuwo a ƙwarya kusan sati biyu kenan bai samu damar zuwa ba sai yau ya rutsa ya je.

A bakin bankin ya yi fakin motarsa yana ƙoƙarin ruɗewa idonsa ya hango masa wani abun mamaki, sai dai kafin ya tantance fuskar mutumin mai sanye da bak’ar cot tuni ya shige bankin.

Daga kafaɗarsa ya yi alamar abun bai dame shi ba, shi ma ya shige bankin. Kai tsaye wurin mai kula da bayar da reciti da kuma cike Form ya nufa, anan ya masa bayanin matsalarsa.

“Ok in wannan matsalarce ka bi can… Ya nuna masa wani gurin dake da layi da yawa na jama’a waɗanda matsalolinsu suka kawo su, ga ma’aikata daga cikin ginin da aka killace ƙasan sa ta yanda ba zaka iya shiga ciki ba sai dai ka yi magana dasu ta nan kawai.

Gyaɗa kai Mahmud ya yi alamar ya gane gun.
Ma’aikacin yace “in ka je kace a Nuna maka Abdulrazaƙ S..”

“Ok Nagode bari in je.” Ya faɗa tare da juyawa ya nufi can.
Da yake ya tarar da layi shi ne ya tsaya a baya, amma ya ƙagu ya ɗora idonsa akan wannan bawan Allah mai suna irin na ɗan uwansa.

Kasancewar shi Babban mutum mai cikar zati da kwarjini ya saka wasu matasa su huɗu suka hakura suka bar masa layinsu. Dalilin kenan da ya saka ya yi saurin kai ga layi. A lokacin mai kula da gurin ya juya bayansa yana magana da sauran ma’aikatan dake ciki. Can ya juyo yana fadar “Yes miye matsalar….”
Bai samu damar ƙarasawa ba ganin fuskar da ko a mafarki ya ganta ba zai taɓa mantawa ba.

Shi ma Mahmud turus ya yi kawai yana ƙarewa halittar da ko da a cikin tsananin duhu ya hangota zai shaidata. Halittar da a kullum kwanan duniya hotonta ke shawagi a ƙwaƙwalwarsa da kuma mafarkinsa. Sai dai ƙwaƙwalwarsa na cunkushe da tambayoyi iri-iri game da Abdul ɗin.

Sun fi minti nawa tsaye a haka, cikin tsananin mamaki da farinciki Mahmud ya ce “Abdul da gaske kai nake gani a gabana yau?”

Abdul kam ya ma kasa magana, sai gyaɗa masa kai kawai da ya yi.

Tuni Mahmud ya manta da matsalar data kawo shi nan, kawai ya kalli gabas ya yi sujjadar godiya ga Allah da ya nuna masa wannan rana a rayuwarsa.

In baku manta ba wannan ya zamewa Mahmud tamkar matafiyin dake cikin Sahara ba ruwa gaba bare baya ga tsananin yunwa da ƙishi, kwatsam sai ya yi tsintuwar ruwa a gabansa. Ku kwatanta irin farin cikin da zai shiga.

Abdul kasa jure tsayuwa ya yi da gudunsa ya zagayo ya rungume Mahmud yana hawaye.

Ga baki ɗaya hankalin jama’ar gurin ya dawo kansu.

Abdul ya ce “Yaya Mahmud da gaske kai ne? Ina Hajiya fatan tana ƙalau?”

Hawaye ne ya ke ƙoƙarin ƙwacewa Mahmud ganin duk irin abinda Hajiyarsa ta yiwa Abdul amma bai manta taba yake tambayar lafiyarta tabbas al’amarin jini muhimmancinsa dabam ne.

Wani ma’aikaci daga ciki (mai saurin hasala) ne ya ce “Haba Abdulrazaƙ aiki fa kake jama’a da yawa ne akan layi ka dawo bakin aikinka mana.”

Wannan zancen nasa ne ya dawo dasu daga duniyar shauƙin haɗuwa Mahmud ya ce “Am! Ka ga Abdul koma bakin aikinka, zan jiraka har ka gama mu tafi, ƙarfe nawa ne zaka tashi?”

“Ƙarfe huɗu na yamma, zaka iya jiran awa biyu kuwa yaya ko dai na zo muje kawai?”

“Ah Haba Haba! Ƙanina ka ci gaba da aikinka kawai, ni da na yi yawon nemanka tsayin shekaru goma sha uku, kuma nake zaune a nan garin da ba ni da kowa tsayin shekaru goma don awa biyu kawai sai na kasa jira?”

A haka yaci gaba da lallaɓa Abdul shi ko sai shagwaɓewa yake kamar ɗan shekara 10 alhali ya shekara 30 a duniya.
Daƙyar ya koma bakin aikinsa har sauran ma’aikatan gun sun fara jin haushin hakan, wasu kuwa suna mamakin irin shaƙuwar dake tsakaninsu, da alakar da zata saka har mutumin ya shekara 13 yana neman Abdul kamar yanda ya faɗa.

A daddafe Abdul ya ƙarasa aikin dama dai Mahmud ne akan layi don haka aka masa aikinsa ya koma gefe ya zauna yana jiran Abdul ɗin.

Da ya so ya yiwa iyalansa surprise na bayyanar Uncle Abdul amma ya kasa jurewa sai da ya kira matarsa Mufida ya sanar mata, zo kaga murna da ihu a gunta yana jin Sabır na tambayar miye Mommy ta ce masa Daddynku ne ya ga Uncle Abdul yanzu. Shi ma yaron ihun murna ya saka, da ya ji zasu fasa masa kunne da ihu ya kashe wayarsa yana dariya cike da nishaɗi.

Bayan awa ɗaya da rabi Abdul ya kammala aikinsa suka fito tare zuwa gidan Yaya Mahmud dake nan Legos.

Tun a hanya ya kira Daddynsa ya sanar masa ya haɗu da Yaya Mahmud da yake ba su labari, yanzu ma suna hanyar zuwa gidansa daga nan za su yo nan gida a gayawa Sabira ta shirya za su zo anjima……….

More comment more typing

Follow me on wattpad@Ruky_i_lawal

Instagram Rukayyarh_ibraheem
Facebook ……

Ummu inteesar ce

*HALITTAR ALLAH CE*

🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼🧑🏻‍🦼

*(Labari mai taɓa zuciya, da sanya imani da tsoron Allah a zuciyar mai karatu)*

*ALƘALAMIN: RUƘAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y’AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*A SANADIN KAMA*
*RASHIN GATA*
*WATA ƘAWA*

*AND NOW*
*HALITTAR ALLAH CE*

Ga masu buƙatar na tallata masu hajojinsu a shafukan littafina dama shafukana na sada zumunta kamar instagram whatsapp, telegram, Facebook da sauransu sai su tuntuɓe ni ta wannan number _08109634202_

Kowacce irin haja ce gareka/ki zamu tallata maka/ki cikin rahusa insha’allah.

________________________________
*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*+

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
END! END!! END!!!

PAGE 79-80

Bayan wasu mintuna suka isa gidan Mahmud. Iyalan Mahmud sun yi matuƙar farinciki da wannan ziyarar da Abdul ya kawo masu, sai washe haƙora suke kamar gonar auduga.
Murna a gun yaran kuwa ba a magana, haka suka zagaye Abdul suna ta zuba masa surutu cike da shauƙin haɗuwa da shi.
Bayan sun gama cin daddaɗan girkin da Madam Mufida ta shirya musamman don taron Babban bakonsu, (wanda a dalilinsa ta ga farincikin da bata taɓa gani ba a fuskar maigidanta tun lokacin aurensu kawo yanzu.)
Ya miƙe ya na faɗar “Yaya sai mu tafi ko? Madam na jiranmu a gida.

Da mamaki a fuskar Mahmud ya kalle shi ya ce “Wai dama ka yi aure ne ƙanina?”
Yar dariya ya yi kana ya ce “Eh na yi aure da yar Alhajin da nake zaune a hannunsa shekara ɗaya baya.”
“Ayyah! Ko ita ce Sabirar da na ji ka faɗa?” Kai kawai Abdul ya ɗaga masa alamun tabbatarwa.
“Masha’allah Allah ya baku zaman lafiya mai ɗorewa.” Ya faɗa.

“Ameen.” Ya faɗa yana miƙewa tsaye, duban Mufida ya yi ya ce “Anty Babba ni zan tafi, sai na dawo cin wata garar wacce tafi wannan.” Da sigar zolaya ya yi maganar.
Yar dariya ta yi ta ce “In zaka dawo sai ka zo da cefanenka don banganewa lusarin miji wanda baya bada na cefa ne.”
Dukansu dariya suka yi cikin Raha. Mahmud ya mike tare da faɗar “Ƙyaleta ƙanina shige mu je, haka take in ka daka ta tata sai mu kwana a nan.”

Har sun fara tafiya Sabira(yar Mahmud ta biyu) ta biyo su da ɗan gudunta tana faɗar “Daddy nima zan biku don Allah.” Jin hakan ke da wuya kamar ta tsikaro sauran yaran da allura, su ma suka yi gun da sauri. A tare Sabır da Fadil suka haɗa baki gun faɗar “Uncle Abdul muna zamu bi ku pls.”

Mahmud ne ya ɗan haɗe fuska kaɗan ya kalle su ya ce “Duk ku je ku zauna, wannan ba tafiyar yara ba ce, zan kai ku watarana.”

Sum-sum suka ja jikinsu zuwa gun mamansu don sun san halin Abban na su, baya wasa.

Ganin yanda yaran suka takure ya sa Abdul ya kalle shi ya ce “Habah yaya! Me yasa zaka hana su can ma ɗin na ga ai gidansu ne ko?”
Maida dubansa ya yi ga yaran ya ce “Yaran kirki ku zo mu je.”
Da gudu yaran suka taho suna murna ganin Abbansu shi ma ya sake fuskar yanzu.

Har sun kai kofa Mufida ta ce “Lallai ma mutanen nan, to ai ni ba mai gadinku ba ce don haka ku jira ni.”

STORY CONTINUES BELOW
Dariya kawai suka yi ba wanda ya tamkata.

Daga haka su ka rankaya zuwa gidan Daddy dama ya yi waya da Sabira akan ta tarar da su gidan.

Suna zaune ana gaggaisawa Sabira ta shigo ɗauke da kayan abinci niƙi-niƙi, a bayanta direbansu ne ya shigo mata da sauran kayan.

Nan fa aka baje ana hirar yaushe gamo tsakanin Abdul da Mahmud.

A nan Mahmud ya ba su labarin irin gwagwarmayar da ya sha gun neman Abdul tun daga dawowarsa daga ƙasar waje har zuwa yau da ya yi gam da Katar da da shi.

Nan kuma ya ƙara da bayyanar masu da cewa Abdul ƙaninsa ne na jini.
Abdul ya yi mamakin jin cewa ashe akwai alaƙa ta jini mai ƙarfi tsakaninsa da yaya Mahmud, ba mamaki shi ya sa yake jin ƙaunar yaya Mahmud sosai a ransa kuma ya kasa mantawa da shi tsayin lokaci, mai yiwuwa wannan ne sirrin shaƙuwarsu cikin lokaci kanƙanin lokaci.

Mahmud ya ƙara da cewa “Mahaifiyarka ta taka rawar gani sosai a rayuwata ba na gajiya da faɗar cewa duk abinda na zama a rayuwa silarta ne. Dalili kuwa shi ne a shekarun baya lokacin ina primary aji uku, muka shiga wani mawuyacin yanayi a gidanmu da yake Babana mai ƙaramin ƙarfi ne a lokacin sai kuma ya kwanta rashin lafiya ta yanda ba ya ko iya fita neman abinda zamu ci, Mahaifiyata kuwa bata da jarin da zata yi sana’a komai ya ƙare aka koro ni daga makaranta saboda rashin biyan kuɗin PTA. Mamana ta rasa yanda zata yi ga shi kuwa an rabo ta da mahaifarta bata da kowa a garin Kaduna ga baki ɗaya ahalinta suna jihar Taraba, ta kuma kasa kiran waya ta sanarwa iyayenta halin da take ciki. Momy Zulaiha ce kaɗai ta yi ƙoƙarin fahimtar damuwar Mamana a’iya waya da suke yi, hakan ya saka ta yi ta lallaɓa ta da kalamai masu daɗi har ta gaya mata gaskiyar yanayin da take ciki.
Duk da cewa a lokacin budurwa ce tana gaban iyayenta amma tana da matuƙar hankali da nutsuwa ga tsagwaron tausayi hakan yasa ta lallaɓa mahaifinsu akan cewa zata je gidan yayarta Kaduna ta tayata zama na ɗan wani lokaci daƙyar ya yarda ya bar ta ta je Kaduna.

Ganin yanayin da ta same mu a ciki ta ci kuka har ta gode Allah daga ƙarshe ta fara sana’ar suyar kosai a ƙofar gidanmu da kuɗin jarin da ta yo guzurinsu tun daga gida, ashe Bankinta na ajiya ta fasa lokacin da zata zo ta ɗebo kuɗin ta zo dasu ba wanda ya sani.

Ba yanda Mamana bata yi ta hanata suyar kosan ba a cewar ta “Mommy Zulaiha zata ɓata ƙuruciyarta garin taimakonta.”
Ita kuwa baiwar Allah budar bakinta sai cewa ta yi “Haba yar’uwata kada ki manta mu biyu ne kacal a gurin mahaifiyarmu, idan ban tallafi rayuwarki da yar damar da nake da ita ba, miye amfanin rayuwata?”

Da wannan Sana’ar ta Koko da kosai ta tallafi rayuwar majinyacin Abbana da ni kaina, domin a cikin kuɗin ne ta maida ni makaranta na ci gaba da karatu, haka ita ke ɗauke da dawainiyar ci da sha na gidan har tsayin shekara ɗaya da rabi kafin daga bisani Babansu ya takura ta koma gida. Ko da yake a lokacin alhamdulillah jikin Abbana ya yi sauƙi sosai har ya koma bakin sana’arsa, amma bata tafi ba sai da ta tabbatar Mamana na cikin walwala. Wannan ne Babban taimakon da ta yi mana wanda har gobe Mahaifiyata take tunawa. Ko bayan aurenta da Abbanka takan je mana ziyara akai-akai duk da ita Hajiyata sai tafi shekara biyar bata je mata Sokoto ba.”

Ɗakin an yi tsit kowa ya zubawa Mahmud kunne ba kamar Abdul da ake bawa labarin.
Cike da fara’a Alhaji Salim(Daddy) ya ce “Madallah da wannan labari na ka. Na yi farin cikin samun fitilar da zata haskawa Yarona Abdul hanya zuwa ga Ahalinsa da ya kasa tunawa tsayin lokaci. Yanzu kana so ka ce mana a Sokoto iyayensa suke kenan?”

Gyaɗa kai Mahmud ya yi alamun tabbatarwa.

“Insha’allah kwanan nan zamu je na san iyayensa zasu yi matuƙar farinciki da ganinsa ba ma kamar Mahaifiyarsa.” Faɗar Daddy.

Mahmud ya yi murmushin yaƙe ya ce “Sai dai mahaifin nasa don ita Mahaifiyarsa ta rasu.”

Abdul dake zaune gurin kamar an dasa shi baya motsi tsayin lokaci jin wannan zancen ya zabura “Yaushe…. Mamma ta rasu?” Domin shi a’iya saninsa Hasina ce Mahaifiyarsa domin da ita ya buɗi ido, dukda watarana yana kokonton hakan.

STORY CONTINUES BELOW
(Da yake yanzu asirin ya daina tasiri akansa tun lokacin da Hasina ta tonawa kanta asiri a bainar jama’a, sai dai ya gagara tuna komai sai yanzu da Mahmud ke ba shi labari komai ya shiga dawo masa kamar yanzu abun yake faruwa.)

Yaƙe Mahmud ya yi sannan ya ce “Ba Mamanka wacce ka sani ba, ainihin Mahaifiyarka wacce ta kawo ka duniya ta rasu ne tun bayan da ta yi arba’in ɗinka.”

Miƙewa tsaye Abdul ya yi yana Faɗar “Yanzu na tabbatar da kokonton da nake akan cewa Mamma ba ita ce Mahaifiyata ba duk da Abbuna na ƙoƙarin tabbatar mun da hakan. Iya baƙar wuyar da na ci a hannunta ya isa shaida a kan hakan, bana raba ɗayan biyu ɓata ta daga gida ma duk yanda aka yi da saka hannunta.”

Mahmud ya karɓe da cewar “Tabbas baka faɗi ƙarya ba, binciken da Hajiyata ta yi ya tabbatar da hakan a ƙarshe ma Baba Direba ya kira daga baya yake shaida mata cewar Hajiya Hasina ta fallasa asirin duk wata badaƙala da ta ƙulla a ciki kuwa har da sace ka da ta saka yan daba suka yi da asirin manta gida da ta yi maka bayan da Allah ya jarabceta da abubuwa sakamakon Abinda ta maka, har ma ta haukace daga bisani.”

Nan fa hankalin Abdul ya kai kololuwar tashi zuciyarsa ta cika da muradin komawa ga a halinsa domin yana son sanin halin da Abbunsa ke ciki.

Kallon Mahmud ya yi ya ce “Abbuna fa? Wane hali yake ciki na san rashina zai taɓa shi matuƙa a yanda yake matuƙar sona.”

“Abbunka yana jinya a gida tun lokacin da ya ji irin cin amanar da abokiyar rayuwarsa da yan’uwansa suka masa yake kwance mun samu labarin hawan jini yake damunsa kullum da sunanka a laɓɓansa yake farkawa daga barci komawarka gida tana da matuƙar amfani.”

Jin haka ya ƙara dugunzuma hankalinsa buƙatarsa ta komawa gida ta ninku don haka ya juya ga Alhaji Salim da Madam Fahima dake zaune ya ce “Daddy! Mommy! ku min uzuri a karon farko da na taɓa yanke hukunci ba tare da shawararku ba. Zan bi yaya Mahmud ya kai ni ga Ahalina gobe.”

Ɗan murmushi suka yi cikin alamun tausaya masa Alhaji Salim ya ce “Haba Yarona! Karka damu muma muna matuƙar farinciki da hakan abunda muka jima muna roƙon Allah ya kawo lokacin yinsa kenan.”

Sai a lokacin Mahmud ya tuna cewa ashe bai sanar da Hajiyarsa cewa ya ga yaronta ba. Kallon Matarsa dake zaune kusa da matar Abdul ya yi ya ce “Kin ga na manta ashe fa ban yiwa Hajiyata Albishir na ganin yaronta ba.”

Murmushi ta yi ta ce “Gaskiya ka yi laifi kuma ni ba ruwana, amma dai bari na riga ka kira domin goron albishirin na san mai tsoka ne.”

Dariya dukan mutanen Falon suka yi banda Abdul da notikan kansa suka gama kuncewa Hajiyar da ta tsane shi ce za’a yiwa albishir da dawowarsa a rayuwarsu har ma ta bada tukuici? Ko da yake wancan ma yana ji a rashin sani ne hada ta aikata …..

Kafin ya dawo daga duniyar tunanin da ƙwaƙwalwarsa ke shawagi a ciki ya jiyo Murya yaya Mahmud na fadar “Yes na riga ki kamawa Mufee sai ki ci ji bulo.” Yana yar dariya yayi zancen.

Mufida ta ci ji yatsa tana faɗar “Ban so haka ba, amma ba komai sai mu raba goron.”

Sabira da iyayenta banda dariya ba abinda suke rayuwar auren Mahmud ta burge su lokaci ƙalilan da shigowarsa rayuwarsu.

“Wallahi Hajiyata ba wasa nake ba, ga ma yaron naki a gabana ko na ba shi wayar?”

“Kasan Allah Mahmud karka sake na gano ba dagaske kake ba, ko da yake kira ni vedio call don na ga shaida.” A ka faɗa a can bangaren.

“Allah Hajiya har da matarsa mai tsohon ciki gata nan a gabana,amma barin kira ki ga shaida.” Ya faɗa.

Nan take ya kira vedio call ya bawa Abdul wayar, Hajiya har kusan faɗowa ta yi daga gado tsabar rawar jiki.

STORY CONTINUES BELOW
Cikin Muryar kuka ta gaisa da Abdul tana ƙara ba shi haƙurin abinda ta masa, sannan ta roƙe shi da su fara zuwa gurinta, ta masa alƙawarin ita da kanta zata raka shi har gaban Mahaifinsa duk da cewa yanzu girma ya kama sosai ga ciwon ƙafa. Haka kuma Abdul ya bawa Sabira da iyayenta duk suka gaisa da Hajiya da alƙawarin cewa jibi zasu zo Kaduna.

Bayan gama waya da Hajiyar duk suka miƙe suka je Sallar Magriba, bayan sun idar aka kuma haɗuwa a falon wannan karon har yaran nasu, abincin da Sabira ta dafo masu suka ci, suna gama ci su Mahmud suka miƙe tare da yiwa ahalin gidan sallama zasu tafi.

Sabira ta kalli Mufida tare da shagwaɓe fuska ta ce “Kai Anty har zaku tafi?,baku je gidana ba fa.”

Dariya Mufida ta yi ta ce “Bayan ci zama tsegumi, gidanki kuma zamu je daga baya.”

Daga haka suka ɗebi yaransu suka bar gidan.

@@@@@@@@@

Bayan kwana biyu dukkansu suka ɗunguma zuwa Kaduna kamar yanda suka yiwa Hajiya Alƙawari, kuma sun je ne da shirinsu gaba-daya daga can zasu wuce Sokoto.

Hajiya ta yi matuƙar farincikin sake saduwa da ɗan ƙanwarta abun alfaharinta, ta kuma ci kuka sosai har sai da Abdul ya nuna ɓacin ransa game da wannan koke-koken da take duk suka haɗu ko a waya ne sannan ta daina.

Kwanansu biyu a Kaduna suka ɗunguma zuwa Sokoto bisa jagorancin Hajiya Fatima.

Sanin cewa Hajiya Inna ta rasu ya saka kai tsaye Hajiya ta faɗawa direbanta sunan unguwar da zai kai su, da yake direban ya saba yawon garuruwa yasan unguwanninsu musamman ma nan Sokoto da cibiyarsa kenan ya saka bai sha wahalar gane gurin ba, kai tsaye ya ɗauki hanyar sama-road.

A mota Hajiya ta kira Baba Direba take shaida masa ga su a cikin Sokoto kuma ta taho masa da mutuminsa. Kafin ma su ƙaraso Baba Direba ya riga su zuwa gidan saboda zumuɗin haɗuwa da yaro Abdul.

Abdul kuwa tun da suka shigo welcome to Sokoto yake ƙarewa garin kallo, musamman da aka biyo ta guraren da ya sani kallon yanda aka ƙara gyara garin kawai yake yana tuna lokacin da yake yaro ƙarami, har aka shiga unguwarsu bai cewa kowa Uffan ba, sai da ya ga direba zai kauce hanya sannan ya ce “A’a ɗan’uwa ba wannan kwanar ba ce ta gaba ce.”

Shi ya kwantawa direban har ƙofar gidan, duk da ya ga sauye-sauye a unguwar dama gidan nasu gaba ɗaya hakan bai hana ya gane gidan da aka haifeshi ya taso a ciki ba.

Tun kan su ƙarasa gidan ya hango Baba Direba duk da cewa ya ƙara tsufa hakan bai hana Abdul gane shi ba, don haka ya ce da Direba “ɗan tsaya nan.”

Tun kan Direban ya kashe motar ya buɗe murfin motar ya fita da sauri har yana haɗawa da gudu ya je ya rungume Baba Direba yana hawaye.

Girgiza kai kawai mutanen cikin motar suka yi tare da ƙarasawa daf da gate inda suka tarar da Abdul yana hawaye ya kwantar da kansa kan Kafaɗar tsohon yana faɗar “Nagode Baba Direba ka nuna mun ƙaunar da tun tashina banda mahaifina sai waɗannan bayin Allahn ba wanda ya kwatanta mun ita, rayuwarka ta sha shiga hatsari a dalilina amma hakan bai sa ka manta da ni ba, har zuwa yanzu kana zaune a gidanmu don jiran ranar da zan dawo gare ku.”

Baba Direba ma hawaye kawai yake ya kasa magana daƙyar ya buɗi baki ya ce “Babu komi ɗana, dama ƙarshen alewa ƙasa, hakanan munafunci dodo mai shi yakan ci, yau ga shi an wayi gari ka dawo mahaifarka kuma gaban idon maƙiyanka da suka son ganin bayanka, Allah ya nuna musu shi at Babban sarki mai Shinhiɗa mulki kuma shika yin yadda yasso, mu shiga ciki.”

Daga haka ya buɗe masu ƙofar suka shigar da motarsu ciki.

Alhaji Munir na kwance a falonsa yana shan iska ya ji sautin shigowar mota cikin harabar gidan. Nan da nan ya ji gabansa na tsananta faɗuwa gashi shi ba isasshiyar lafiya ba bare ya ce zai tashi ya dubo ko su waye, bisa dole ya haƙura.

STORY CONTINUES BELOW
Yana nan yana saƙe-saƙe a ransa ya ji sallamar Baba Direba daga ƙofa “Shigo Malam.” Ya furta a hankali.

Shiga ya yi ya gaida shi da jiki sannan ya ce “Alhaji ka yi manyan baƙi daga Kaduna.”

Da mamaki a fuskar Munir ya ce “Ɓaki daga Kaduna su waye?”

Murmushi kawai Baba Direba ya yi fuskarsa cike da fara’a ya ce “in ka bada izini za su shigo da kanka zaka shaida su.”

“Ok je ka ce su shigo.”

Bana Direba ya fice shi kuwa ya yunƙura daƙyar ya tashi zaune.
Alhaji Salim ne ya fara shiga ɗakin matarsa na biye dashi a baya sai Hajiya Fatima sannan sauran…

Hajiya Fatima kaɗai ya shaida a cikinsu cikin barin baki ya ce “Haj-jiya da…ma kina nan, shi ne ko ziyara baki taho muna ba ko dan yar’uwarki bata n…..

Kafin ya gama rufe baki Abdul ya sako kai cikin falon tare da Baba Direba.

Da ƙarfi ya Zabura yana ƙoƙarin miƙewa tsaye, amma sai ya durkushe akan kujerar kasancewar ƙasusuwansa sun yi rauni shekarunsa kusan saba’in da Uku a rayuwa.

“Subhanallah!” Mutanen dake gurin suka haɗa baki gurin faɗa.

Cikin zafin nama Abdul da Mahmud suka ƙarasa gare shi tare da kama shi suka zaunar da shi kan kujera. Mahmud ya ce “Yi a hankali Alhaji, sannu.”

Abdul ya kasa magana ma sai ƙwalla da ta cika masa ido taf.

Alhaji Munir ya sake duban Abdul da kyau ya ce “Abdul yarona da gaske kai nake gani a gabana yau?

Gyaɗa masa kai kawai ya yi kamar wani karamin yaro.
Janyo shi ya yi ya rungume shi a jikinsa yana ƙwallar farinciki a hankali ya furta “Alhamdulillah! Allah ma ji roƙon bawa, yau ɗana ya dawo gare ni bayan shekaru goma sha takwas da ɓatarsa.”

Suna tsaka da haka ne Alhaji Mizbahu ya shigo falon da sallamarsa ganin baƙi ya saka ya tsaya suna gaisawa kwatsam idonsa ya faɗa kan Abdul. Fiddo ido waje ya yi ya ce “Abdul ɗana kai ne?” Da sauri Abdul ya taso ya rungume shi suna ta murnar haɗuwa. Domin bai mantawa Baba Mizbahu duk ya fi jansa a
Jiki da nuna masa ƙauna.

Nan fa falon ya rikice da murnar dawowar Abdul sai hira ake, tuni Alhaji Munir ya wartsake kamar ba shi ke kwance mintuna 30 baya ba.

Sallama suka jiyo daga Kofar Falon ta cikin gida, kowa ya maida hankalinsa don ganin mai shigowa falon.
Wata ƙyamurarrar macece ta Kunno kai cikin ɗakin, da farko idan ka ganta zaka ɗauka lafiyayya ce sai ka ƙare mata kallo zaka ga alamun motsuwa tattare da ita.

Shigowa ɗakin ta yi tana ƙarewa baƙin kallo can ta ce “Ina yininku.” Tana faɗa tana yar dariya tare da jujjuya kai.

“Lafiya qlau.” Suka amsa suna Binta da ido daƙyar Hajiya Fatima ta shaida fuskar ta ce “Hajiya Hasina ce ko?”

Gyaɗa mata kai ta yi tana washe haƙora tare da faɗar “Haka kuwa, Uwar Kabiru ɗan sarki ƙawar Kulu mai adashen sheri.”

Binta kawai suka yi da ido Alhaji Munir ne ya yi yaƙe ya ce “Ku yi haƙuri kun ga tana maku abubuwa haka ta samu motsuwa ne tun lokacin da asirinta ya tonu duk da cewa yanzu an samu da ƙarfin addu’a an ciyo kan matsalar ta daina haukar amma fa kanta ya riga ya motsu. Da yake ni saki baya cikin tsarina kuma na duba albarkacin zumunci dake tsakaninta da Hajiya Inna shi ya sa nake zaune da ita har yanzu.”

Jama’ar dake falon baki ɗayansu sun ga imanin Alhaji Munir da ya iya zama da Hasina har yanzu duk kuwa irin abunda ta aikata masa.

Sai a lokacin Abdul da fargaba ta hana shi juyowa ya kalli Mamma ya juyo ya ƙura mata idonsa ɗaya yana kallonta.

Tana yin arba dashi ta yi wata uwar zabura ta miƙe zata bar ɗakin.

Alhaji Munir ya ce “Dawo ki zauna,” kin ga kainuwa dashen Allah ko?

STORY CONTINUES BELOW
Sosa ƙeya ta din ga yi duk ta gama kunyata nan ta shiga roƙon gafarar Abdul ta na cewa “Abdul ka yahemin sakamakon cutar da kai da na yi yau ga yanda rayuwata ta dawo, don ma Allah ya haɗa ni da miji mai yawan haƙuri da yahiya da yanzu bansan inda zan kasancewa ba ga rayuwa. Abunda ya faru da ni yanzu ya isa ishara ga masu hali irin nau, son zuciya da bin bokaye babu inda yaka kai mutum sai tafkin nadama, dama yan magana sunce kowa ya hau motar kwaɗayi ba inda zata sauke shi sai tashar wulaƙanci.”

Tana gama faɗa kuma abun nata ya motsa ta hau dariya.

Duk mutanen ɗakin sun tausaya mata banda Hajiya Fatima da ta tuna rashin mutuncin da ta musu lokacin da suka zo karɓar yaronsu. Acewarta komai ya same ta ita ta jawa kanta.

Daga nan Hasina ta masu iso zuwa ciki ta saka yan aiki suka kawo masu abinci da abun sha bayan kowa ya wadatu, aka kuma haɗuwa a tsakar gidan ƙatuwar tabarma aka Shimfiɗa masu kowa ya zauna, yaran kuma an barsu a falon Hasina suna barci saboda gajiyar tafiya.

Nan Abdul ya gabatarwa Alhaji Munir da sabbin iyayensa kuma ya basu labarin irin kulawar da suka bashi tun lokacin da ya haɗu da su.

Alhaji Munir ya masu godiya sosai, anan kuma Abdul ya shiga basu labarin uƙubar rayuwa da ya sha tun lokacin da ya buɗe ido ya gansa a jeji har zuwa ranar da ya haɗu da Alhaji Salim.

Masu saurin kuka a cikinsu har da hawaye jaɓe-jaɓe, Bama kamar Hajiya Fatima da take ganin ita ce silar zamansa Mabaraci.

Alhaji Munir da Mizbahu kuwa sun ma kasa kukan, tsananin tausayin yaron da ya cika masu zuciya. Shi kam Abdul ya sha gwagwarmayar rayuwa tun lokacin da aka haife shi bai san daɗin rayuwa ba sai bayan haduwarsa da wadancan mutane

Daga bisani Abdul ya ɗorawa iyayensa da labarin yanda aka yi aurensa da Sabira da zamansu mai daɗi da suke har kawo yanzu da take da ciki wata tara, kuma ya ba su labarin nasarorin da ya samu a rayuwa a nan yake gayawa Abbunsa yanzu haka yana aiki a bankin First bank dake Lagos kuma ya ƙware a harkar gyare-gyaren kayan lantarki duk da a yanzu baya samun damar yi, amma dai ya buɗe shago a kasuwa can Legos inda ya tara yara ya koya masu yanda ake gyaran tun kafin ya gama jami’a. Yanzu haka su ke kula da shagon gyaran bayan kowanne wata uku sukan yi zama a cire riba da uwar kuɗin su kuwa ya cire masu haƙƙinsu, domin yanzu shagon ya zama kamar wani kamfani ba iya rediyo ba har wayoyi suna gyarawa da sauran kayan dake amfani da wuta.

Allah ya azurtashi da fasahar gyare-gyare bangaren ilimin boko da addini kuma ba a cewa komai abun sai hamdallah.

Ranar dai kusan kwana aka yi anata hira tsakanin Alhaji da baƙinsa.

Washe gari yaya Mizbahu ya kwaso iyalinsa suka zo har nan gidan suka gaida baƙi daga bisani suka ɗunguma zuwa gidan yaya Bilya don su duba shi da jiki, wannan karon har Alhaji Munir aka je gidan.

Yaya Bilya ya sha kunya ganin Abdul da Munir har ɓoye fuskarsa yake don kunya.
Abdul ya matuƙar tausayawa Yayan mahaifin nasa ganin mutumin da ya sani hamshaƙi mai cikar zati ya koma wani irin yamutsattsen tsoho, wancan gidan nasa na yan gayu ma yaransa sun siyar suna sai masa magani a cewarsu ba zasu iya ci gaba da kashe dukiyarsu a banza da wofi ba, dama ya mutu da sun huta, saboda haka yanzu yashe yake cikin wani gidan da ko filasta ba yi da, gidan bayada banbanci da kango sai wannan matar tasa kaɗai ta ci gaba da jure zama da shi tana jinyarsa. Ba yanda yaran basu yi ba don ganin sun raba Mahaifiyarsu da wannan wahala ta jinyar nakasasshen Ubansu amma ta ƙi.

Ranar yaya Bilya ya sha kuka ya nemi gafarar Abdul data ƙaninsa Munir. Munir ya ce “Babu komi yaya in ta nina na yahe tunda Allah ya dawo min da ɗana, dama zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai ya yi. Ga shi dukiyar da kuka wawaso kanta yau an wayi gari baku da ko sule cikinta, tawan ma da nit tara duk ta kusan ƙarewa wurin ɓidam ma kaina maganin da ku at silar ciwon, wannan gidan ɗai yat rage min, sai ɗan abinda ba a rasa ba. abunda muka ci ma ruhin asirin Allah na sakamakon zama da mutane lahiya, duk wanda zai tahowa ganina sai ya kawo min abinci shiyassa har yanzu babu wanda yaggane ina cikin matsala.”

STORY CONTINUES BELOW
A ranar yaya Bilya ya kara gane duniya budurwar wawace, ba abinda yafi bashi mamaki irin jin labarin baiwar da Allah ya yiwa Abdul da kuma yanda ya samu kyakkyawar mata kamar wannan duk da munin halittarsa.

@@@@@@@@@@@@

Bayan komawarsu gidan Alhaji Munir da dare labarin Rasuwar Alhaji Bilya ya same su, sun kaɗu matuƙa da wannan mutuwa ta farat ɗaya bayan ɗazun nan suka rabu da shi. Dama yaya Sunusi ya Rasu shekara Biyu baya, yarsa nakasasshiya kuwa tana nan ta zama yar budurwa amma ba hanci.

Lokacin da labarin mutuwar ya riski Alhaji Munir ya girgiza sosai ganin cewa a yau ya wayi gari duk yan’uwansa da ya taso tare dasu sun ƙare sai yaya Mizbahu kaɗai ya rage masa. Ya kuma tuno duk irin badaƙalar da yan’uwansa suka shirya masa akan abun duniya yau gashi an wayi gari bako ɗaya a cikinsu kuma zasu je can su tarar da hukuncin abunda suka aikata, duk da cewa shi ya yafe musu duka amma bai cire ran ko sun cutar da wani ba tare da haƙƙi ba tunda halinsu ne.

Nan take ya tuna da huɗubar mahaifinsu ta ƙarshe a gare su da ya masu wasiyya da haɗin kai da riƙe gaskiya da amana.

Nan take ya shiga yi masu addu’ar samun Rahama dukkansu tare da fatar su da suka rage su samu cikawa da imani.

@@@@@@@
Bayan sati ɗaya da zuwansu Mahmud ya tattare yaransa da matarsa har ma da Hajiyarsa suka koma Kaduna domin hutun da ya ɗauka daga gun aiki ya kare. Amma a nan suka bar Abdul da matarsa dama tuni su Alhaji Salim suka koma Legos.

A ranar da suka tafi ko isa basu yi ba Allah ya sauki Sabira ta haifi yarta mace santaleliya fara sol mai kama da mahaifiyarta sak.
Sai hoton yar Abdul ya tura masu tun suna mota. Murna a gun Alhaji Munir ba a magana ya kai ga jika kuma mace abunda bai da.

Ranar suna aka yi shagali yarinya ta ci Sunan Mahaifiyar Abdul Zulaiha yana kiranta Da Mamaa.

Hajiya Fatima bata dawo suna ba amma ta kira danginsu na Taraba ta gaya musu. Haka suka yi mota-mota suka zo Sokoto suna. Yaron da suka guda a lokacin haihuwarsa da kuruciyarsa yau shine suka zo tayawa murna.
Bayan komai ya natsa ya saka hannayen jari a kasuwancin da mahaifinsa ke yi, duk da yanzu mahaifin nasa ba zai iya yi kamar da ba, sai dai ya nemo masu yi masa kasuwanci.
@@@@@@@@
Bayan shekara biyar Alhaji Abdulrazaƙ ya zama cikakken ɗan kasuwa, dukiyar mahaifinsa ta dawo fiye da da domin shine mai kula da ita, tuni ya bar aikin banki da yake a Legos ya dawo Sokoto domin ya zauna tare da mahaifinsa ko ya mantar da shi damuwar da ya shiga a baya dalilin rashinsa a kusa da shi.

Hasina ita ta ci gaba da kula da Sabira da Maamaa har tsawon wannan lokaci duk da abun nata yana motsawa lokaci zuwa lokaci amma tana matukar son Abdul da yarsa Mamaa, inta tuna abunda ta masa a baya har kuka take.

Dawowar Abdul garin Sokoto ya dawo da farincikin tsohonsa tamkar da, haka ya ci gaba da kula da kasuwancinsa da yake a Legos ta hanyar amintattun yaransa.

A nan garin Sokoto ma ya buɗe wani reshe da ake gyare-gyaren a kasuwa har ya zamana yayi ƙaurin suna a harkar kowa baya son gyara sai na shagunan *Bawan Allah* kamar yanda ya masu take.

Mahaifinsa ya so ya komawa aikin bankin anan amma ya ce “Ka yi haƙuri Abbuna aikin banki yana kawo kuɗi tabbas amma baya bawa mutum cikakken lokacin da zai kula da iyalansa, ga shi kuma dukkanku kuna buƙatar kulawa ta musamman kai.”

Jin haka yasa dole Alhaji Munir ya haƙura. A ranar ne kuma su Aljani Barkuza suka zo yiwa Abdul ban kwana na ƙarshe da alƙawarin zasu fita daga rayuwar shi tunda yanzu ya samu cikakkiyar nutsuwa.

Abdul ya masu godiya sosai, cikin dauriya ba tare da nuna tsoro ba, da yake a siffar mutane suka zo masu.

Alhaji Munir ya ƙara cika da tsananin mamaki kuma ya kara jaddada girman Ubangiji da ya bawa waɗannan bayi nasa damar zama kariya a rayuwar tilon ɗansa.

Bayan wasu makwanni hawan jinin Alhaji Munir ya tashi, ba bata lokaci Abdul ya kai shi asibiti isarsu asibitin ke da wuya ya cika tun ma kan likitoci su zo.

Abdul ya shiga tsananin tashin hankali da faruwar wannan al’amari.

Yafi sati Uku a kiɗime ba nutsuwa Daƙyar aka ciyo kansa ya dawo dai-dai.

Yanzu kowa ya ƙare a dangin mahaifinsa sai Baba Mizbahu kawai, shi ma shekaru sun ja lokaci kawai ake jira.

Shi ne ya mayewa Abdul gurbin Alhaji Munir.

Maganar dukiyar Alhaji Munir kuwa ba a sha wani wahalar rabon gado ba kasancewar Abdul ne kaɗai dansa tilo kuma namiji.

Wata rana alhaji Abdulrazaƙ na zaune shi kaɗai a ɗaki yana tunanin yanda rayuwa ta dawo masa, wai yau shine mai mallakar dukiyar da tafi wacce aka so salwantar da ransa akanta. Dangin Mahaifiyarsa da suka juya masa baya da mutanen da suka ƙyamace shi a baya sune suke neman ƙulla a laƙa dashi a yau. Yau shi ne ya wayi gari da mata har da yaya biyu duk a cikin abubuwan da Allah ya mallaka masa. Nan kuma ya shiga tuno uƙubar da ya sha lokacin da baisan kowa ba a bayyane ya ce
“Alhamdulillah Ubangijina godiya ta tabbata a gareka na gode da ni’imomin da ka mani, kuma ka azurta ni da haƙuri a lokacin da ka jarabce ni ban kauce hanya ba, yau gashi ina ganin ribar haƙurin.”

Tammat bi hamdillah anan na kawo ƙarshen wannan labarin mai suna *HALITTAR ALLAH CE.*

Fatan Allah ya ba mu ladar fadakarwar dake ciki ya kuma yafe kura-kuran da ke ciki. 

Advertisements

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Trending

Copyright © 2022 Hausa Novels