GOBE NA CHAPTER 4 BY KHADIJACANDY - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GOBE NA CHAPTER 4 BY KHADIJACANDY

GOBE NA CHAPTER 4 BY KHADIJACANDY

- - Post a Comment

 GOBE NA CHAPTER 4 BY KHADIJACANDY               Www.bankinhausanovels.com.ng ABDALLAH POV.

Yayi parking daidai da lokacin da yake sauke wayarsa daga kunne. A natse ya bude motar ya fita ya nufi kofar shiga falon. Da sallama ya shiga falon kamar yadda ya saba, Suwaiba ta amsa masa murya kasa kasa ba tare da ta kalle inda yake ba sai aikin latsa waya take. Kusa da ita ya zauna yana sauke gajiya idonsa na kan matarsa.+

“Kawo min ruwa”


Ya fada bayan ya kai hannu ya fisge wayar daga hannunta, facebook take kan wani page na Real Life Diaries, sannen shafi ne da yake wallafa matsalolin mata da mazan ma aurata domin samun mafita ta addu'a ko shawara ko taimako idan ta kama.

  Sama sama ya duba labarin page din wani gurin yai dariya wani abun kuma yai tsaki musamman idan ya leka comment section.

“Gashi”


Ta mika masa ruwan fuakarta ba yabo ba fallasa bayan ta bata yan mintuna kamin ta kawo masa.

“Ni na manta when last na leka page din nan, wani lokacin post din mutane bata min rai yake wallahi”


“Wani lokacin kuma ana samun mafita ai, shiyasa ake yin posting din”


Ta fada tana kokarin zama kusa da shi wato a inda ta tashi dazun. Kallonta yai kamin ya kai ruwan a bakinsa ya shaye gaba daya sannan ya aje kofin ya kai hannunsa ya janyota ta kwanto jikinsa.


“Ya akai Subee? Fada min matsalar ki”


“Babu komai”


Ya fada still fuskarta na nuna akwai damuwa.

“Ba mu saba boyewa juna damuwa ba, fada min matsalarki”


“Ba komai”


Ta sake maimaitawa. Wayarta ya mika mata yana fadin.

“Ba ki tambaya ko anga Namra ba?”


“Ai na san an ganta, da ba a ganta ba da ba zaka dawo gidan nan ba”


Kallonta yai for few seconds sai kuma yai murmushi as usual.

“Shine abunda ya bata miki rai?”


“Tun safe ka fita gidanan baka dawo ba sai yanzu, ko rantsuwa nai ba zan yi kaffara ba wata kila ko aiki baka je ba, ka tashi hankalinka gurin neman yarinyar nan wanda na san ko Inteesar ta bata ba zaka tashi hankalinka kamar haka ba”


Wannan karon raba jikinsa yai da nata ya juyo da kyau ya kalleta yana karantar yanayinta.

“Yar yar'uwata ce ta bata fa, ita ma din kamar yata ce”


“Ta ma fi yarka ai, gatan da kake musu baka ma yayanka wannan gatan, makarantar da ka saka su Inteesar 60,000 ake biya duk bayan wata uku amman Namra makarantar da aka saka su dubu 130,000 ake biya duk term”


“And...?”


“And ba su da wanda zai dauki dawainiyarsu ne sai kai Abdallah? Why kai why?”


“Amman ai kin san mahaifinsu ya rabu da Halimatu ko? Kuma yaran nan a yanzu abun tausayi ne suna bukatar tallafi a rayuwarsu, kuma Halimatu yar'uwata ce kin fi kowa sanin haka”


“Dan ya rabu da ita sai dawainiyarsu ta dawo kanka? Miyasa Abdulhamid b dauki dawainiyarsu ba? Be fika kusanci da mahaifiyarsu ba?”


“Abdulhamid babu ruwansa da yara kin sani, ba sai an fada miki ba”


“Amman ita kadai ce mai yaya a familynku? Miyasa ba kai wa wasu ba sai ita? Komai daga ita sai familynta? Lokacin da Hafiza ta zo nan ta fada maka Namra ta bata kuka fita tare ko magana ba ka min ba”


“What are you try say?”


“Dawaniyar ta maka yawa Abdallah, kai mata kai wa iyayenta kai wai yayanta kai wa yan'uwanta why?”


STORY CONTINUES BELOW

“Pls just stop.....”


Ya fada yana daga mata hannu fuskarsa na nuna tsananin bacin ransa.

“Dukan abunda zan yi ma wani a familyna ki kawarda idonki, babu nairar ki a ciki, kuma familyna ne ba naki ba so babu ruwanki da abunda ya shafi family na, dukiyata ce yan'uwana ne”


Yana kaiwa nan ya mike tsaye ya nufi hanyar dakinsa cikin bacin rai. A take ranta ya kara baci, iyakar abunda zuciyarta take raya Abdallah yana son daya daga cikin kannenta Especially Hafiza ganin kamar jininsu ya fi haduwa a cikin kanenta, daman can tana raya ma zuciyarta haka sai dai bata dauki abun da gaske ba kamar yau ganin yadda hankalin mijinta ya tashi akan bata Namra.


Yana shiga dakin ya cire kayan jikinsa ya daura tawul, yana kokarin shiga wanka wayarsa tai ringing, dawowa yai ya dauki wayar Doc Auwal ne rubuce a wayarsa.


“Hello Doc Auwal”


“Doc Abdallah ya kake?”


“Lafiya kalau”


“baka shigo ba yau gashi Abdulhamid ya ce na baka sakonsa”


“Sakon me?”


“Ban san na minene ba daga kano dai jiya Doc Faruk ya kawo min yace na baka kai kuma ka bada Abdulhamid”


“Ba zan shigo yau ba sai gobe, wallahi wata yata ta bata ba mu ganta ba sai yanzu”


“Okay bari na biya na kai masa kawai”


“Okay”


Wulga wayar yai a saman bed dinsa yama fadin.

“Abdulhamid kana ta wahalar da kanka, tun asirinka na rufe har kowa ya ji sirrinka, after you already know za ka samu lafiya ne kawai only if na haifi da namiji....”


Bathroom ya shiga ya sakarwa kansa ruwa, har yai wankan ya fito ransa a bace yake da maganar da matarsa tai masa.

HALIMATU POV.

sai da hankali ya kwanta sannan na kira Abdulhamid na fada masa cewar an ga Namra tana tare da ni ma, godiya yai ma Allah ta cikin wayar nake ina jiyo shaukin muryarsa kamin mu yi sallama.

A lokacin ne Husna take min zancen wai ta kira Abdulhamid tace yaje gidan radio saboda an yi sanarwa wata yarinyar kamar yadda suka ji daga bakin jama'a.


“Ayya ma zai je ai ba wani son motsa jiki yake ba ni har mamaki nake idan yai nasa yayan ko ya zai yi”


Kallonta nai ina murmushi yayinda na ke gyarawa Namra zama a cinyata.

“Kin san kowa da rayuwarsa, na fi kyautata zaton Abdulhamid yana kishin rika yaran wasu ne, kuma kin ga daman can Abdulhamid babu ruwansa da yara”


“Ai ba yara kadai ba har manya ba wani so yake ba, shiyasa be taba burgeni ba ni Wallahi da ma Abdallah kika aura tun farko  ya.....”


Hafiza bata karasa ba Mama ta tari numfashinta, wanda hakan yai min daidai.


“Wannan wace irin magana ce Hafiza? Mace ta taba auren wanda ba mijinta ba? Kuma wanda mace take so ai shi zata aura, kar na sake jin irin wannan maganar a bakinki”


Bata sake cewa komai ba ta dauki wayarta da dan guntun gyalenta ta da saba yafawa ta fice daga falon na Mama zuwa dakin Inna wato dakin Mahaifiyarta. A gidan an wuni sai bayan sallah isha'i Abdulhamid ya zo daukata ya shiga cikin gida ya gaisa da su Mama sannan ya fito muka kama hanyar gida.

   Ba mu yi wata fira a motar ba saboda ciwon marar da ya kasa sakina, pad ma sau hudu ina canjawa, shi kuma na lura kamar baya cikin walwala. A haka muka kwana ko wanne da abunda take sakawa a zuciyarsa, nawa tunanin dabam shi ma nashi dabam duk kuwa da kasancewar ban san damuwarsa ba.

  A rungume da juna muka kwana kamar yadda muka saba, sai dai na riga shi tashi saboda na gyara kaina, sannan na shiga dora mana abun karyawa cikin kankane lokacin na gama komai saboda ina son zuwa asibiti.

  Sai da nai wanka na shirya sannan na shiga na tashe shi ya fito muka soma karyawan.

STORY CONTINUES BELOW

“Ban maka magana tun jiya ba, ina son naje asibiti marata tana min ciwo tun jiya na yi zaton ko zan ji sauki kamin yau amman ban ji alamun haka ba”


Na masa maganar a yayinda muke cikin karyawa. Dagowa yai ya kalleni sai kuma ya kai fork dinsa ya dauki dankali ya ci.

“Kina Menstruation ne?”


“Yes”


Mikewa yai tsaye kamar ya nufi dakinsa ya dauko wayarsa kamin ya karaso kusa da ni ya kira Abdallah.

“Kana asibiti ko gida?”


Ban san mi yace masa ba na ji dai ya sake cewa.

“Okay ga mu nan zuwa, Halima ce bata jindadi zan kawo ta yanzu”


A take na ji gabana ya yanke ya fadi, gashi bana son ya zargi wani abun balle na ce masa bana son Abdallah ya duba ni.

“Bari nai wanka sai n kai ki gidan Abdallah ya dubaki”


Kai kawai na iya gyada masa ya juya ya koma ciki, har yai wankan ya shirya ya fito ban samawa kaina mafita akan abunda zan yi ko na ce da zai hana zuwan gurin dan'uwansa ba.

A dole tasa na saka hijab dina na na dauki jakata da wayata na fice ina gaba yana baya har muka fito daga falon, a gaban motarsa naje na tsaya ina jiran ya karaso ya cire key din na bude sai ji nai an rumgumeni ta bayana.

“I love you so much”


A hankali ya fada min haka sannan ya sake ni ya danna keys din hannunsa motar ta fita daga lock. Front seat na zauna shi kuma ya shiga driver seat a usual, sai dai har muka isa gidan Abdallah be kalli inda nake ba be ce min uffan ba kuma ban ga wata walwala a fuskarsa ba, hakan yasa na fi kyautata zaton wata kila rashin lafiyarsa ce ya saka a rai ta hana ni sukuni a take tausayinsa ya rufe har idanuwa suka soma cika da kwalla. Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na bude motar na fita, wannan karon shi ne a gaba ni ina baya. Mun dan jima tsaye a gurin kofar kamin Suwaiba ta bude mana. Na yi kokarin kirkirar far'a na yaɓa a fuskata duk kuwa da irin halin da nake ciki, sai dai yau na same ta akasin yadda na saba samunta ko kuma na ce nake ganinta, domin tun da na auri Abdulhamid ban taba zuwa gidan da sunan kawo mata wuni ba sai yau shi ma kuma wannan da daliline.

Cikin falon muka shiga na zauna a saman cushion Abdulhamid kuma ya zauna kusa da ni yana ta kallona kamar ba shi ba. Bayan kamar minti biyar Abdallah ya fito a daya daga cikin bedroom din da suke falon. Shi ma dai fuskarsa babu walwala kamar ta matarsa, sai da ya mikawa Abdulhamid hannu suka gaisa sannan ya zauna ba tare da ya kalli inda nake zaune ba.

“Ina kwana?”


Na mika masa gaisuwa ina ta kallon zoben hannunsa, zoben da ba kasa samun natsuwa da shi har yanzu.

“Ina kwana”


Sai ya dawo min da gaisuwar still be kalleni ba sai Abdulhamid yake tambaya abunda yake damuna.

“Mararta ke ciwo”


“Tun yaushe?”


“Tun jiya, magani nake son ka rubuta mata”


“Ya kike jin abun?”


Wannan karon ya kalleni a yayinda yake tambayar tawa.

“Ina dan jin tana min ciwo ne”


“Sosai ko kadan and tun yaushe?”


“Jiya”


Tashi yai ya shiga daki, be dade ba ya fito rike da takardar magani ya mikawa Abdulhamid.

“Dan Allah daga yau idan matarka bata da lafiya ka kai ta asibiti direct ba sai sai nan ba, ko ba komai zata fi sakewa idan tana ganin mace yar'uwarta”


STORY CONTINUES BELOW

Ba Abdulhamid kadai ba, ni kaina da nake matar Abdulhamid na yi mamakin jin furuncinsa, wanda na tabbatar hakan be yi ma Abdulhamid min dadi ba ko kadan. Uffan be ce masa ba bayan kallonsa da yai ya karbi takardar tare da ce min na tashi mu tafi. Daga gidan Abdallah kai tsaye gidan Hajiya ya wuce da ni, ban so haka ba amman ban isa na nuna masa ba kasancewar mahaifiyarsa ce. Ita kanta ta lura da yanayinsa na rashin jindadi daman can yana fama da shi balle kuma yanzu da Abdallah ya kara masa da wata maganar.

A gaban idona take tambayarsa abunda yake damunsa sai ya amsa mata da cewar babu komai, daga bisani ya kalleni ya ce.

“Ki zauna a nan idan an dawo aiki zan biyo miki da maganin sai mu wuce gida, Hajiya ba ta jindadi shiyasa na kawo ta nan ta huta kamin na tashi aiki”


Ya karasa yana fadawa Hajiyar.


“Allah ya saukewa”


Ta fada tana dauke kai irin abun be dame ta ba. Shi kuma yai mana sallama ya tashi ya fice. Da kallo Hajiya ta bishi har ya fice sannan ta kalleni.


“Ke me ke damun mijinki?”


“Kwana biyu nan haka yake, kuma yanzu muka fito gidan Abdullahi ya kai ni ya dubani shine ya ce karya sake kawo ni to ban san ko shi ya bata masa rai ba”


“Husaini ne ya ce masa haka?”


A take ta daga wayarta a gurin ta jira Abdallah ta fada masa tana son ganinsa, abun ka da mai jiran kiran uwa a ko da yaushe, sai gashi ya zo cikin kankanen lokaci dama can babu tazara sosai tsakanin unguwarsu Hajiya da ta Abdallah.

  Fuska a sake ya shigo kamar ba shi ne na tarar a can ya hade rai ba, ko dan wannan mahaifiyarsa ce oho. Bayan ya zauka Hajiya ta sallame ni ta hanyar cewa na tashi na ba su guri.

Ba musu n tashi na fita daga falon sai an samu guri kusa da kofar falon na zauna ina ta sake sake a raina, ta wani bangare raina fes yake da zubar jinin da nake domin na san indai ciki na zube a yanzu, ta dayan bangaren kuma ina jin tausayin mijina. Ban san abunda Hajiya tace masa ba sai dai na ga ya fito ransa a bace har ya wuce ni sai kuma ya juya ya nuna ni da yatsa kamar ba Abdallah ba.


“Ina ta kokarin ganin na fita daga hanyarki, ya kamata ke gane ke matar dan'uwana na ce a yanzu, duk wani abu daya shafe ni ko kika san zai saka dan'uwana kusantar da ke a gareni ki yi kokarin kauce masa, idan ba haka ba ran mijinki zai yi ta baci fiye da yadda kike zato kuma za ki jawa mijinki shiga damuwa fiye da wacce yake ciki...”


Idanuwa ne suka fara yawo a fuskarsa.


“Baka da tausayi Abdallah ba ka da kirki, ba ka san damuwar kowa ba sai ta ka, kai baka tausayin dan'uwanka ma? Bayan halin da yake ciki na damuwa kake neman kara saka shi wani? Kamar ba uwa daya ta haife ku ba? Abun da ya kamata ace ka taya shi tausayin kansa da neman lafiyarsa amman sai neman kara jefa shi a damuwa kake?”


“Babu ruwana da matsalar mijinki, ba tausaya min ba, dan haka babu tausayi a tsakaninmu samun lafiyarsa ko zamansa haka har a bada be dame ni ba saboda shi ma be bar ni na samu farinciki na ba”


Kallon mamaki nai masa.

“Ya kake kokarin aron wadansu dabi'u da halaye marar kyau ka yafawa kanka Abdallah, kana abu kamar ba kai ba? Dan'uwanka jininka? Wallahi Abdulhamid ba zai taba yi maka abunda zai hana ka samun farinciki ba, ba ka da kirki da halin kwarai shiyasa baka taba burge ni ba, kana da son kanka da yawa shiyasa ban tana jin son ka a zuciyata ba....!”


Fadada fuskarsa yai da murmushi kamar ba shi ba.


“Wani lokacin Wallahi mata ba ku da hankali”


Yana fadar hakan ya juya ya nufi gurin motarsa.

AHMAD POV.

Tura kofar falon yai ya shiga da sallama, Momy ta amsa masa tana rike da wayarta.

“Dan halak, yanzu nake kokarin kiranka fa, tun da ka fita baka dawo ba”


“Ban dade da fita ba ai”


Ya fada yana kokarin zama.

“Eh na sani, bana son kana yawon nan idan ba aiki ba ko wani uzurin”


“Haba Momy sai kace wani karamin yaro”


“Ba zaka gane ba ne ai, yan mata yanzu shegen wayo ne da su a take za su ci maka kudi su gudu, kuma na sna indai ka bar gidan nan ba iya kula kake da kanka ba”


“Yanzu ni kamata yan mata za su yi wa wayo?”


Ya nuna kansa.

“Hmmm Baka san mace ba, har yanzu kai yaro ne, ka ci abinci?”


“Eh na ci abinci”


“Ka koshi?”


Murmushi yai yana ta mamakin yadda Momy take ta maida shi karamin yaro, sam ta ki yarda shi din namiji ne kamar kowa, sometimes har mamaki yake shi dai yasan ba girma ne be da shi ba balle ace tana ganinsa da karamin jiki, shiyasa wani lokacin ko yana bukatar baya nunawa saboda kar ta samu damar yi masa haka. Baby Namra ce ta fito daga bedroom dinta tana masa oyoyo.

“Daddy sannu da zuwa”


Ya mika hannunsa ya rikota.


“Yauwa darling y scul?”


“Fine Daddy wannan Name sake din tawa ta tafi”


“Yeah Momy ta zo ta dauketa did you miss her”


“Yes Daddy”


“Ke da kika ce ba ki sonta?”


“Yanzu kuma na ji ina sonta, daddy za ka kai ni gidansu?”


“Ban san gidansu ba”


“Pls daddy”


“I'm serious”


Ya fada yana kara gyara mata zama a jikinsa, har cikin ransa yake jin son yarsa fiye da komai a rayuwarsa, musamman idan ya tuna cewar bata da mahaifiya a raye.

“Idan kin je makaranta ki tambaye unguwarsu sai a kai ki”


Wannan karon Momy ce take maganar.

“Wane class take Momy?”


“4 tace min kamar 4 kamar 3 na manta dai ki bincika”


Da sauri ta gyada kai tana murmushi.Gaba daya littafin nan Sadaukarwar ne ga Zainab A Baba💖


AHMAD POV.2

Wayarsa ce tai ringing, da gangan ya ki duba wayar ya ga mai kiran balle yai deciding idan zai dauka ko ba zai yi picking ba. Babu kira mai muhimman a gurinsa kamar na Hajiyarsa sai kuma na kanwarsa da yarsa su ne kadai mutanen da suke da muhimmanci fiye da komai a rayuwarsa, yana girmama kiransu yana mutunta bukatunsu, kamar yadda yake martaba su. As long as yana tare da Hajiya ko yana cikin gida, duk wanda ya kira shi sai idan yaga dama zai daga kiransa kowa shi a duniyar nan kuwa.+

“Ba wayarka ce ke ringing ba?”


Cewar Hajiya ganin be daga ba duk kuwa da ta san halinsa na kin son call, ya fi son sako fiye da kira.


“Ita ce wata kila wane ni bana son amsawa yanzu”


“Ko dai yan matan ne ke kira?”


Kallonta yai da murmushi a fuskarsa.

“Kowa da bukin zuciyarsa, Allah na tuba wace mace ce zata wahalar da kanta yanzu na son dan Hajiya?”


“Hmmm ai yan matan yanzu shegen wayo ne da su, yanzu sai su tatse ka tass baka sani ba”


“Hajiyata, kin kasa gane cewar ni ba yaro ba ne, ka ci abinci? Me ka ci? Yaushe zaka dawo, karka wuce minti talatin a waje, da sauransu na yara ne, Hajiya ni babban mutum ne a yanzu tun da har Daddy ya kirani nai min wasiyar kula da ku, kuma cikin ikon Allah da iyawarsa na iya rike gidan nan da kula da ku da tafiyar da komai na kamfani yadda ya dace ya kamata ace kin fahimci cewar dan ki ba yaro ba ne a yanzu”


Murmushi tai Murmushi mai sautin irin na su na manya.

“Har gobe kai yaro ne Gwarzo, maza ai ba wayo ne da ku ba, ba komai kuke ganewa ba sai na nuna muku”


Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya kalli Baby Namra.

“My Love je ki dakinki bari mu yi magana da Hajiyarki ko?”


“Okay Daddy”


Sai da ta sumbanci kumatunsa sannan ta haye sama, shi kuma ya bita kallo kamin ya ciro wayar tasa da ke ringing yai picking.

“Yusuf ya akai?”


“Lafiya kalau, oga ya gida ya family?”

   

“Fine go straight to the point”


“Oga maganar vip ne”


“No ya dai kusa ka san kace baka son sai abu yai gab a fada maka, shiyasa na tuna maka”


“I think kudin shekara ya kamata mu fara biya na wata wata nan yana confusing dina, ka lissafa na shekara nawa ya kama zan turawa abokina number ka sai ku yi magana”


Be jira Yusuf din da ya kira wayar ya kashe ba, balle har ya saurare abunda zai fada ya kashe wayar, yana kallon Hajiyarsa zai yi magana ta tari numfashinsa.


“Har yanzu ba a daina biya Vip din nan ba? Shekara nawa Gwarzo? A yanzu ka gama maganar cewar ka girma, ni nasan abunda na ke ai na san waye kai”


“Ba haka ba ne Hajiya, abunda kika kasa ganewa freedom din danki,  Hajiya kin kasa bari na yi komai kamar ko wane namiji, kin ki aminta na zauna a gidan kaina, kin hana auren duk yarinyar na kawo, ko fita nai idan na wuce ka'idar da kika ba ni sai kin nuna bacin ranki ko kuma ki nuna min hankalinki ya tashi ba ki san inda na ke ba, duk yadda nake son na fita na fira a waje na wuce 9 ko na kai 10pm sai ki ce min ba haka ba.


Exclusive City, a nan na hadu da Halima, a kujerar da nake biya a yanzu a gurin na same ta zauna, kin sani Hajiya every week muna zuwa gurin mu sha iska, and ta taba fada min ita take biyan gurin ko da bata zo ba, and after mun yi aure ita ta cigaba da biyan gurin, duk yadda na so na cigaba da biya sai ta hana ni, she once told me na bari sai idan bata da rayuwa sannan na cigaba da biya, and nai mata alkawari daga lokacin da na auri wata macen ba zan sake biya ba, alkawarinta nake kokarin cikawa Hajiya gurin nan yana da muhimmanci a gareni saboda mahaifiyar Namra, ko rai aka bata mata a gurin take zuwa tai kuka, idan kika mata wani abun a gurin take zuwa ta zauna tai bacin ranta ta gama sannan ta kira tace idan na taso daga office na biyo ta nan na dauke ta, wani lokacin kuma da kaina nake zuwa nemanta a gurin, ni kaina a yanzu ko anjima ko wani lokaci na kan je can na zauna kuma na samu natsuwa kamar tana raye... ”


STORY CONTINUES BELOW

Ya yi shiru idonsa tab da kwalla, uffan Hajiya ba ta ce ba har ya mike tsaye ya saka wayar aljihun shaddarsa da ya zuba hannayensa aljihu ya nufi upstairs. Wani irin abun na rashin jindadi ke masa yawo a zuciya, haka yake samun kansa a duk lokacin da ya tuna da matarsa Halima, wacce yake yawan fada mata cewar daga ita ya gama so, mace da yake ganin babu mai hakurinta da kirkinta a duniyar nan.

Ajiyar zuciya ya sauke sau uku zuwa hudu sannan yaja wani dogon numfashi ya busar a bakinsa. Ya kai hannunsa ya murda kofar dakin Baby Namra ya tura ya shiga ciki. Agaban plasma take zaune rike da drawing book da pencil a hannunta tana drawing wani bird da ake nuna a kids channel. Daga bakin kofar ya tsaya yana kallonta zuciyarsa fal da kaunar yarsa, sannan ya karaso kusa da ita yana ayyana abubuwa da dama akan rayuwarsa da nata.

‘Ko da na ayi aure zan yi ne kawai saboda ke, saboda ni da ke mu samu kulawa amman ba dan zan taba son ko wace mace a duniyar nan ba’


Kanta ya shafa yana murmushi kamar yadda ita ma ta dago ta kalleshi tana murmushin.


“Daddy what”


“Ba komai”


Ya fada yana cigaba da kallonta, ita kuma ta maida hankalinta gurin tv ta cigaba da abunda yake. Wayarsa ya ciro ya nemo number Rayyan.


“Rayyan”


“Ranka ya dade”


“Yusuf ya kira ni wai kudin wata sun kare, na ce masa za ku yi magana akan na year sai ka bashi zai fi”


“Okay amman ban gane Yusuf din ba”


“Wanda yake Exclusive City, kudin Vip nake nufi”


“Okay ina da number shi ai bari na kira shi yanzu”


“Okay ya fada maka ko nawa ne na shekara sai na bashi”


“Consider it done”


Daga haka ya yanke wayar ya cigaba da kallon abunda yarsa take zanawa.


HALIMATU POV.


daga karshe na yanke shawarar fadawa Abdulhamid gaskiya, na san duk yadda zai ji zafi da tashin hankali ba zai kai kamar lokacin da abun ya faru ba, kwana biyun nan na lura yana cikin damuwa wata kila saboda abunda Abdallah yai masa ne a kwana baya duk da be fada min ba amman ni kaina na lura da hakan, abunda zuciyata take yawan fada min idan ban fada masa gaskiya ba, idan ya ji a wani gurin ba zai ji dadi ba ba kuma zai fahimce ni ba. Amman kuma ta ina zai ji? Wa zai fada masa bayan babu wanda ya san wannan sirri daga ni sai Allah sai kuma kawata Hajara?

Doyar da nake ferayewa na aje na rike wukar kamar ita ce zata sama min mafita.


“Zan fada masa gaskiya, ina jin kamar ba zan samu peace of mind ba idan ban fada masa ba, ina jin kamar na ci amanarsa ne”


Ni kadai nake magana da kaina a kitchen kamin na aje wukar na wanke hannuna saboda wayata da na ji tana ringing. Cikin hanzari na nufi inda wayar take, a lokacin da na kai hannu na dauki wayar sai na kasa picking din call din ganin number mai kiran duk kuwa da ba suna, Aminu ne na san ba wata magana mai dadi zai fada min ba, wata kila haukansa zai min ko kuma ya min gargadinsa na iska da ya saba, sai da ya jera min four miss calls sannan na daga, nai masa shiru tare da hade rai kamar yana a gabana.

“Hello Halima”


“Ya akai?”


Na tambaya ina kara hade fuska kamar ance yana ganina.

“Sai an yi wani abun zan kira? Alaka fa har yanzu bata yanke a tsakaninmu ba saboda yara”


“Babu wata alaka a tsakanina da kai Aminu, kuma bana fatar wata alakar ta sake kulluwa a tsakaninmu, wacan da mu kai a baya ma ka dauka cewar labari ne”


STORY CONTINUES BELOW

“Ta wuce labari Halimatu tun da har kika haifa min yara hudu, maza biyu mata biyu Al-hamdulillah, yanzu ma kira nai na tambaye lafiyarsu, kuma na ji idan akwai abunda suke bukata idan zan taho musu da kaya sai na siyo musu”


Duba wayar nai dan tabbatarwa idan har number Aminu ce da gaske ko kuma a a. Kamin na maida wayar a kunne na ya kira sunana ya kai sau uku cikin tausasshiyar murya kamar ba shi ba.

“Lokacin da nake gidanka ma baka damu da tambayar lafiyar yayanka ba, sai yau? Ko kunya baka ji ba? Yarana ba sa bukatar komai daga uba irinka Aminu, mahaifiyarsu ta ishesu kuma zata iya yi musu komai, karka sake kirana domin ni matar wani ce a yanzu”


Ban jira abunda zai ce ba na yanke wayar, mamaki fal a zuciyata wanda ya kasa boyuwa har ya bayyana a fuskata, sake duba wayar nai a karo na biyu, neman dalilin kiran Aminu na ke a wannan lokacin na rasa? Me yake so? Ko kuma na ce mi yake kokarin aikatawa? Me zai saka ya tambayi yaransa? Gaba kaina sai ya kulle har na girkin na gama ban raba dayan biyu ba, ko dai Aminu yana da wata manufar akan yaransa ko kuma yana shirin lalata min aure ne.


Abdulhamid be shigo ba sai bayan sallah magariba, na masa sannu da zuwa kamar yadda na saba na raka shi har daki na hada masa ruwan wanka domin na san wanka ne abunda mijina yafi bukata a duk lokacin da ya dawo daga gurin aiki. Kamin ya fito na jera masa abinci da ruwa mai sanyi sannan na fiddo masa da jallabiyarsa, da kaina na karbi karamin tawul din na natse masa jiki sannan na shafa masa mai sannan ya saka gajeren wando ya dora Jallabiyar sama. Zaunawa yai ni kuma na soma zuba masa abincin  ina ta kallon yanayinsa kamar yadda na lura da kwana biyun nan ya fiye kallona.

A tare muka soma cin abincin kamar yadda muka saba sai da na tabbatar ya kusa koshi sannan na fara bijiro masa da maganar.

“Hubby Akwai wata magana da nake son mu yi mai muhimmanci....”


Tarar numfashina yai.

“Ya jikinki....? Na manta dazun da muka tashi ban tambaye ki ciwon marar ba”


Wani dif na ji numfashina yai dogon zango, kamar wacce zata suma sannan ya dawo min kamar an jefo shi.

“Na ji sauki, akan hakan ne nake son mu yi magana”


“Uhm ina jinki”


Yadda yai maganar da yadda ya fuskance ni sai ya saka ni tsoro da fargaba kwarjinisa duk sai ya cika ni, har na kasa furta komai.

“Ina jinki”


Spoon din hannuna na aje na kama hannunsa na rike na saka idona cikin nasa.


“Ban san yadda zaka dauki abunda zan fada maka ba, ban san ya za ka ji a zuciyarka ba, ban san wani irin kallo za kamin ba, za ka iya cigaba da zama da ni akan kaddarar da ta same ni ko a'a, ban sani ba iyakar abunda na sani shine bana da kwanciyar hankali idan ban fada maka.....”


Idona ne ya cika da hawaye sai nai saurin kawar da fuskata daga barin kallonsa.

“Me kika aikata?”


Yawun bakina na hade na sake kallonsa a karo na biyu sannan na ce


“Ban aikata komai ba, darajata aka taba....!”


“Ban gane ba”


Shiru nai na kasa cewa komai sai hawaye na ke shar kamar ba gobe, shi kuma bayan kallona babu abunda yake.

“Zaka iya tuna lokacin da ka tafi Abuja karbar wasu takardu? Ka bar ni ni kadai?.....”


Cikin natsuwa irin ta masu gaskiya na zayyana masa komai, ba natsuwa irinta ta masu kwanciyar hankali ba, kallon kallo muka ko yi ma junanmu akuya kallom kura, idona na hawaye ina kallonsa, yayinda shi ma yake min kallon da ban san na minene ba, yarda ko akasin hakan ko kuma tausayi? Sosai nake Kallona na kasa dauke idona daga kansa, so nake ya fada min cewar ya aminta da ni tausayi da kulawa da kauna nake son gani a fuskata, so nake na ga idonsa sun cika da hawaye saboda mu yi kukan a tare mu yi jumamin a tare.

Be ce min komai ba, be kuma daina kallona ba, be nuna min wata alama ta yarda ko akasin hakan ba, ban tsinka jimami a idonsa ba balle har na iya hararo tausayi a zuciyarsa.

STORY CONTINUES BELOW

Ni din ce da kaina na tsargu na mike tsaye na bar masa gurin, ina jin zuciyata na min wani irin zafi kamar zata fashe, idonuwana kuma suna ta min yaji saboda hawaye daya hana ni gani daidai. Dakina na dawo na kwanta saman gadona na mika hannuna na janyo fillo ya dora kaina dayan hannun kuma na rika shafa gadon da shi kamar ban san abunda nake ba, kwancin ya gagareni sai na sauko na zauna a kasa na dora kaina a saman gadon.

Uwa ce ni, amman a yau ji nake kamar ace akwai wata uwar a kusa da ni ta rarrashen ta fada min komai zai wuce, ina son naji wata kalma mai dadi ina son na ji an fada min cewar wata rana zan yi dariya wata rana zan yi farinciki, ina ma a ce Mama ta san da maganar nan da ita kadai zata iya ba ni hakuri ita ce kadai zata taya ni mu yi kuka tare kamar yadda nai da Namra.1

“Kaicon ki Halimatu? Wace ƴa ce za a yi mata fyade kuma ayi ma uwarta? Nai kukan yata kuma nai nawa? Yau kenan ya gobena zata kasance?”


Mikewa nai tsaye ina kara magana da kaina kamar wata tabbabiya.


“Ya isa shikenan komai ya wuce, abunda ya faru ya riga ya faru ba zan iya canja shi ba, ba kuma zan iya goge shi ba, shikenan ai kaddarata ce wannan”


Ina kaina nan na fadi kasa zaune na fashe da wani irin kuka da ban san ta ina hawayen ke fito min ba. Na kan yi kuka har na samuwa natsuwa ko kuma na samu sukuni amman a yau sai na nemi natsuwa da sukunin na rasa, kukan ya ko ya tsaya min kamar yadda hawayen ma ce min sallamu alaikum. Wani kalar sara na ji kaina na yi idonawa har rufewa suke saboda ciwo, har kuma lokacin hawayen ba su daina min zuba ba. Karfin hali nai na tashi na shiga kitchen na dauko flask din na hadawa kaina tea da cup nai ta feta har ya sha iska sannan na kurba kadan, wani abun mamaki sai na kas hadewa kamar wacce tasha wani abun mutuwa, kuka ya subuce min.


‘Ke fa uwace Halimatu, idan Namra ko Amal ko Adnan ko Amir suka shiga damuwa gurinki za su zo, ke za ki sama musu mafita, so be a strong woman....’


Shine abunda zuciyata yake fada min, kai na gyada ina karfafawa kaina kuiwa sannan na shiga bandaki nai wanka har kan nawa da ke ciwo sai da wanke dan kaiwa na samu salama. Daure da tawul na fito na nufi gaban madubi na zauna ina ta kallon kaina, hawayen idona be daina zuba ba kamar yadda ruwan kaina suke zuba. Ina jin motsin shigowar Abdulhamid gabana ya yanke ya fadi, daga jikin kofar dakin ya tsaya yana kallona.


“Amman Halima ba su bar wata alama da za a gane cewar yan fashi sun shigo gidan nan ba? Ba su fasa komai ba? Ba su dauki komai ba? Ba su harbi kowa ba? Kuma duk a unguwar nan ba su shiga ko'ina ba sai nan? Kuma ba su zo ba sai ranar da bana nan?”


Ta cikin madubin na aika masa da kallo sai murmushi ya bayyana a fuskata, still hawaye na sauko min.

“Wacce zan fara amsawa a cikin tambayoyinka?”


“Halima babu yadda za ayi 6arawo mai makami ya shigo gidan nan be bar wata alama da zata nuna cewar ya shigo ba, and if gaskiya ne miyasa ba ki fada min tun farko ba sai yanzu, and miyasa kika yi kokarin zubar da cikin? Ba ki fada min ba sai da kika fara gano cewar na gane halin da ake ciki shiyasa kika kirkiri wannan? Na kasa yarda cewar ke ce Halima!”


Wannan karon juyowa nai na fuskance shi.

“Ni din ce dai Abdulhamid, ka yi tunani iya yadda zuciyarka ta kawo maka, Halimatu ce! Karka damu wannan din ma yana cikin kaddararta, na yarda wani sabwar kaddarar ce ta fuskance ni kuma ta bude min sabon shafi, na shirya karbar ta da hannu biyu, na sani bakinciki baya taba dawwama, kamar yadda jindadi ba ya dawwama, ko dai bakincikin ya tafi ya bar ni, ko kuma ni na mutu na bar shi, kuma gaskiya a duk inda take gaskiya ce zata bayyana ko da bayan raina...”


Takowa yai ya karaso kusa da ni ya dafa ni ya tayarda ni tsaye ya kalle ni da idonsa da ke zubar da kwalla.


“Saboda ina kaunarki na aureki, har ga Allah na yarda da ke..... amman zuciyata ta kasa natsuwa da wannan, duk wani kuduri da nake da shi akanki ne, duk wani buri da nake da shi akan ki ne, na san kin yi jihadin aurena bayan kin san bana iya komai, wannan kadai ya isa ya nuna cewar kina kaunata, amman be isa ya wadatar da cewar za ki iya tsare kanki ba, wannan abun da ya faru laifina ne na cutar da ke, taya son rai yasa na cilasta miki aurena bayan na san ba zan iya sauke hakokinki ba, komai kika aikata ba ki yi laifi ba Halima saboda ni ne ba mutum ba, da ace ni din namiji ne kamar kowa da duk hakan be faru ba da baki rasa komai ba”


Hannayensa ya kai ya riko fuskata ya matso da tasa fuskar daf da tawa yana hawaye kamar yadda ni ma nake.

“Wannan sirrinmu ne, babu wanda zai ji? Karki fadawa kowa mu bar wannan a tsakaninmu, na miki alkawari ba zan ta a fadawa kowa ba, babu wanda zai ji wannan abun daga gareni, kuma zan cigaba da zama da ke kamar yadda muka saba, na sani ni ma wannan jarabawata ce, and i think this is the only way da zan iya repay na aurena da kika a yadda na ke marar lafiya, saboda Allah ya kaddaro min haka a rayuwata, na yafe miki har Allah na yafe miki kuma ina fatar Allah ya yafe miki....!”


Yana kaiwa nan ya hade yawun bakinsa ya dauke hannayensa daga fuskata ya juya yana cigaba da hawaye ya fice. Ban yi zaton akwai wani sauran karfi a jikina ba, a take kafafuwana suka fara rawa sai gani a kasa zaune jikina na ta rawa kamar wacce ta fito daga cikin kankara.!


ABDALLAH POV.


Cikin wani irin bachin rai ya shigo gidan, tun daga yanayin parking dinsa ma ya isa a gane hakan balle kuma idan a kai arba da fuskarsa, zuciyarsa har wani bugawa take da karfi kamar zata fito.

Dukan yaransa suna falo kasancewar yau Thursday babu islamiya school, suna masa sannu da zuwa amman be amsa musu ba kai tsaye ya nufi dakin Mahaifiyarsu. Tana zaune saman gado tana waya ganinsa da kuma yanayinsa yasa ta katse wayar tana kallonsa.

“Me yake damunki Suwaiba?”


Da karfi ya aika mata da tambaya sai da hantar cikinta ta kada.

“Me na aikata?”


“Ba ki san abunda kika aikata ba? Ba a nan muka gama maganar Halimatu ba? Akan me za ki dauki wannan maganar ki kaita social media a page irin wannan?”


“Ba ni bace ni ban kai komai a page ba.. ”


“Ba ke bace wacece? Taya za asan da labarin idan ba ki fada ba? Har da sunan Namra? Da maganar School fees? Haka kawai ki dauki maganar da an riga an yi ta ki saka a media? Wace irin shawara kike nema? Kin san mutane sai zagina suke, a ina za su sama miki mafitar? Kina tunanin idan Halima ko Abdulhamid suka ga wannan ya za su ji? And look at the way da kika fadi labarin is like zargina kike ma? Kin ja ana ta tsina mana alrbaka ni da ita”


“Maganar kenan Halima Halima....”


Ya kara matsowa kusa da ita yana nuna mata wayarsa da ke hannunsa.

“Yes Halima Halima, Halima yar uwata ce, kuma ni ba mazina ce ba ne, ban nemai matan waje ba ma babu yadda za ayi na nemi yar'uwata yar'uwar ma matar dan'uwana, ko a lokacin da Halima take gidan Aminu ban neme ta ba balle yanzu da take auren dan'uwana, ni ba mahaukaci ba ne kuma na jahili ba ne ba zan taba neman aikata Zina da Halima ba har abada! no matter how much I love her, ki shiga hankalinki karna sake jin sirrin gidan nan a media”


Yana fadar hakan ya juyawa ya fice daga dakin cikin bacin rai. Second to last sentence na sa ya fi komai rudata ya yanke mata hanzari kuma ya jefata a duniyar tunani.

‘No matter how much I love her....’


Those that means Abdallah yana son Halimatu? Zargin da yan comments suke ya zama gaskiya kenan? Cewar da suke yana son ta ne wasu kuma na fadar cewar yana tarayya da ita ne ya zama gaskiya kenan? Ada kam sam ita bata kawo ma kanta wannan tunanin ba, ta fi zargin ko Abdallah yana son kanenta ne, amman yanzu kam gaskiyarta fito. Da sauri ta kunna data ta shiga page din da ta tura neman shawara ta shiga kara duba Comments din followers.

Al-hamdulillah, mun dawo fatar dai Yan Team Halimatu da Abdullah da Abdulhamid da Ahmad har ma da Aminu ba su yi fushi ba 😊2Na kan dora komai a mizanin kaddara, na yarda dukan abunda ya same ni ko zai same ni rubuttacen al'amari ne daga gurin mahaliccina, wani be isa ya goge min ba kamat yadda ban iya na yayewa kaina ba.+


Wannan ma yana cikin kaddararki Halimatu, haka zuciyata take yawan fada min kuma ina samun natsuwa sosai idan na tuna cewa ko wane abu da izinin Ubangijina yake samu na. Iyakar kokarin da nai na danne zuciyata ne daga kokarin aikata wani abu marar kyau wanda wani bangare nata yake hararo na ke ganin kamar mafita a gareni. Tun daga lokacin ba mu sake hada shimfida da Abdulhamid zai ba, ma'ana dai be sake leko dakina ba kamar yadda ni ma ban sake taka kafata dakinsa ba matukar yana a cikin gidan, ban fasa masa girki ba be fasa ci ba, ban kasa mika masa ko wace  irin gaisuwa ba, sannu da dawowa, Allah ya tsare daman halina ne. Sai dai ban sake ganin walwalar fuskarsa ba kamar yadda walwalarsa ta hana tawa walwalar.

Idan ina zaune a falo baya zama, idan kuma yana zaune na zauna sai yai kamar ya tsargu a take zai tashi ya shige dakinsa.

Ban taba ganin laifin Abdulhamid min akan wannan ba, idan na saka kaina a matsayinsa ni kaina na san kwatankwacin abunda zan yi kenan, ba lallai ne ya gasgata ni ba, kamar yadda ba kowa zan fada haka ya yarda ba, sai dai abunda yafi min ciwo kallon da yake min na cewar na ci amanarsa.

  Ina ji ina gani zaman gidan yaki yai min dadi, na kasa sakewa, kwanciyar hankali yai min kwara walwala ta yi min bankwana, kuka da damuwa suka kwankwaso min kofa.

Har ta kai bana iya bachi idan lokacin bachin yai, sai dai na raya dare da sallah ko kuma na zauna nai ta kallon sillin ko da kuwa bana tunanin komai bachin ba zai dauke ni, da rana kuma sai na tsargu ina ganin kamar ni ce kadai nake cikin matsala. Da kaina na fita chemist din dake unguwar na siyo maganin mura na ruwa a duk lokacin da na ji ina bukatar bachi sai na sha, wani abun mamaki a take bachi zai dauke ni kuma sai na manta da duk wata damuwa dake tare da ni.

Da dare kawai ba, da rana ma idan na ji damuwar ta matsa min na dan kan sha sai kuma na samu salama da natsuwa, na sani akwai illa abunda nakr sha, kuma na san ba abu ne mai kyau ba, mace kamar ni mai yaya hudu ace na buge da shan kayan maye domin na samu bachi, wannan ma yana saka ni damuwa sai dai babu yadda na iya idan ban yi hakan ba ban san abunda rashin bachin zai janyo min ba. Gaba daya yanayi na ya canja ni kaina na sani, bana sakewa kamar da ga ciwon ido ya saka ni a gaba har ta kai bana iya daga idon sosai.

  Tun lokacin da abun ya faru ban sake fita da sunan zuwa unguwa ba ko wani gurin, Hajara ma ban sake labarta mata komai ba, a ganina duk wanda zan fadawa ba zai sama min mafita ba dan haka babu amfanin fallasa sirrin nawa.

Yau ma kamar jiya ta kama weekend sai dai yau Sunday ba Saturday ba, Abdulhamid tun safe ya fita kamar yadda ya sabawar kansa yanzu da fita ranar weekend ya wuni a wani gurin sai dare zai dawo, bayan da can ba haka ya saba ba. Lamarinsa na ya bani tausayi ta wani bangaren kuma sai ya bani tsoro na kan yi tunani anya ko wace mace zata iya sadaukarwar da nai? Auren mutum kamar Abdulhamid a lokacin da tawa kaddarar ta same ni sai ya juya min baya? No be kamata nai wannan tunanin ba, shi ai ba shi da lafiya rashin lafiyarsa babbar damuwarsa ce sai kuma ni na kara masa wata, ya fa kamata na gane wani abu a duk lokacin da wani ya rabe ni sai wani abu marar kyau ko kuma na bakinciki ya same shi, misali kamar Kabir ko yana ina ma yanzu?

Ni kadai nake zaune a falona ina ta sake sake da tunani kala kala wasu masu amfani wasu kuma marar amfanin. A tsorace na kalli kofar falon saboda knocked din da akai, haka nake yawan tsorata ko iska ya kada sai gabana ya yanke ya fadi. Sai da na sake jin an kwankwasa kuma na ji kamar hayani a waje sannan na tashi na nufi kofar na bude. Kanwata ce Hafiza tare da Namra da Aiman da Adnan da Amal da kuma wata yarinyar da ban waye ta sosai ba. Da gudu suka rumgume ni su dukansu wani kalar farinciki na ji wanda na dade ban ji irinsa ba, lallai ya'ya rahama ne, a take idona ya cika da kwalla ni kaina na san na yi kewar ya'yana, dukawa nai na dauki Amal muka shigo falon tare da su.

  Bayan sun huta na dauko musu abincinmu, sannan na shiga dora wani domin ban san da zuwansu ba kuma nasan wanda za su cin ma ba isarsu zai yi ba, ina cikin kitchen din Hafiza ta same ni da zancen siyayyar da Aminu yake ta musu Namra a kwanakin nan, daman kuma Mama ta fada min a waya a duk lokacin da ya zo sai ta fada min domin ita ma mamaki abun yake bata kamar ni. Daga ni har sun mun rasa dalilinsa na nunawa yarana kulawa a yanzu, bayan siyayya ma duk bayan kwana biyu sai ya zo ya fita da su ko kuma ya duba lafiyarsu.


STORY CONTINUES BELOW

“Ni kaina Hafiza na rasa ganene dalilin Aminu na yin haka, mutumen da can ma be kula da yaran ba, har cewa yake na tara masa yara har hudu da kurciyarsa, yanzu kuma shine yake nuna musu kulawa abun yana bani tsoro”


“Ko ma minene nufinsa ba zai samu nasara ba, matukar dan ya cutar ke ko su zai yi”


“In-Sha-Allah, ba zai samu wata dama ta yin wani abu ba”


“Amman Anty miyasa kika daina zuwa gida? Baba ma kwana biyu ciwon kafafuwansa sai tashi suke?”


A take gabana ya fadi hankali kuma ya tashi abunka y'a da uba.

“Subhanallahi amman shine ba a fada min ko a waya ba?”


“Ba ke kadai ba ko su Anty Murja da suke nesa ya hana a fada musu wai za a daga musu hankali kawai, kin san ciwon nasa idan ya tashi yau ciwo gobe lafiya haka yake masa shiyasa”


“Allah ya bashi lafiya”


“Amin, Mama da Inna sai zancen ki suke su suka ce na zo da su Namra ma mu duba ki lafiya kike? Kuma gaskiya na ga alamar ba lafiya ba”


“Kamar ya?”


Na tambaya ina kokarin kirkiro murmushi.

“Haba Anty kalle ki fa, duk kin rame kin koma kamar ba ke ba, ke da kika da jikinki mulmul ma sha Allah amman yanzu ko ki na fi ki ki ba, duk kin yi baki kin lalace Gaskiya akwai abunda yake damunki”


“Babu abunda yake damuna Hafiza”


Ina fadar hakan na juyo na fito daga kitchen din domin bana son ta cika ni da tambayoyi. Ina fitowa Namra ta fara bani labarin Daddynsu yana zuwa gurinsu yanzu har ma siyayyar da yai musu, tana cikin lissafa abubuwan da ya siyo musu sai Adnan ya karbe daga nan sai Aiman har da Amal ma labarta min take abubuwan da Daddy yake musu, wani irin farinciki da annushuwa nake ganin a fuskar yayana, da alama hakan da yake musu a yanzu yana musu dadi, ko ni da nake babban na so mahaifina a kusa da ni balle su da suke kanana kuma babu ni a kusa da su. A nan Namra take nuna min new friend dinta mai irin sunanta.

“Momi kin tuna lokacin dana bata a gidansu aka kai ni, kin suna ita ce yarinyar gidan”


Sai a lokacin na tuna har na wayi fuskarka.


“Momi Daddynta yana sonta sosai komai siya mata yake, kuma har shi yake zuwa daukarta idan zata koma gida”


“A ina kika hadu da ita?”


“A school din mu take ita ce tana so na friend tace ita bata da friends kuma Momi ita ma sunan Mominta Halima, amman ta rasu.... ”


Hannu na mika mata alamar ta zo, sai ta taso daga inda take zaune a kan Center tebur ta nufo inda nake sanye da English Wears dinta kanta babu dankwali balle ayi maganar hijabi.

“Kin ganeni?”


Na tambaya bayan na rike hannunta, sai ta gyada min kai tana murmushi irin murmushin nan na yara masu kiriniya.

“Momi na fada mata yau za mu zo gidanki shine tace tana son ta ganki, tace daddynta ya kawota kuma ya kawo ta”


Namra ta fada da mamaki a fuskarta, domin ita bata tashi cikin irin wannan gatan ba, da mahaifinta zai mata abu ko kuma ya nuna mata kula balle har ya dauketa ya fita da ita.

“Daddynta yana sonta sosai Momi har da waya ya siya mata, yana bata chocolate komai siya mata yake, kuma gidansu har da motar wasan yara ya siya mata da lilo irin an scul dinmu”


Ta sake fada, ni kuma sai nai murmushi na shafa kanta domin na san abunda yata take ji, kwatankwacin abunda nake ji idan na ga wata mace ta yi dacen mijin aure.

STORY CONTINUES BELOW

“Kin yi dacen uba, Allah yai miki albarka ya jikan mahaifiyarki”


Da kanta ta amsa min da Ameen kamin ta saki hannuna ta nufi gurin su Adnan, da alama dai ta sake sosai da su kamar wasu yan'uwanta.

A gidan suka wuni tare da Hafiza sai dare suka tafi, duk yadda ta so na labarta mata damuwa ban yarda na bude mata cikina ba. Tafiyarsu da minti ashirin Abdulhamid ya dawo a lokacin ina zaune falo, bai yi knocked ba daman yanzu ya gane sai dai ya saka key ya bude kofar falon ya shigo. Na masa sannu da zuwa ya amsa min irin amsawar nan kamar an masa dole, a yadda na lura Abdulhamid yana zaune da ni ne irin zaman nan kamar na dole domin ba zaka ga zamantakewar aurenmu ka ce zaman ne na masoya ba. Na so na gabatar masa da zancen zuwa gida duba Abbah a wannan lokacin sai kuma wata zuciyar ta hana ni, na yanke shawarar da safe zan fada masa idan ya gama karyawa.

   Ashe abunda ban sani ba Abdulhamid tafiya zai yi a garin da ban san ina ba ne, sai da safiyar ta waye bayan na gama hada masa abun karyawar na yi ta jiran ya fito shiru be fito ba, har tara da rabi ganin be saba kai wa hakan ba yasa na shiga dakinsa sai na samu dakin wayam babu kowa a ciki sai wata farar takardar a saman gadonsa, karasa nai na dauki takardar wacce ke saman kudin da ban san na minene ba har sai dana karanta takardar.

“Tafiya ta kamani zuwa Kaduna, zan dawo on Tuesday ko Wednesday ga kudi nan ki yi amfani da su.....”


Ina gama karanta takardar hawaye ya wanke min fuska, a yanzu bana da martabar da Abdulhamid zai kalli ya fada min cewar zai yi tafiya? Zauna nai bakin gadon ina tuna irin rayuwar da nai a gidan Aminu, a da na yi tunanin komai ya wuce, ashe abubuwan da zan fuskatanta suna da yawa, ko wace mace da irin jarrabawar da take tsintar kanta a cikin a gidan mijinta, wata mijinta neman mata yake, wata ya hana ta ci da sha, wata ya hana ta lokacinsa, wata ya hana ta kudin kashewa. ni kuma irin tawa kaddarar kenan.


“Al-hamdulillah”


Na furta sannan na share hawayena na taso na fito daga dakin, dakina na dawo na bude drawer ta na dauko maganin bachi na kurba kadan na kwanta, da niyar nai bachin kadan sai ga shi na zarce da dogon bachi ban farka ba sai la'asar. Azahar ma sai da na ramata sannan na dora da la'asar din, haka kuma be min dadi ba domin ban saba ramuwar sallah ba, idan ba da wani dalili mai karfi ba. Ganin ni kadai ce a gidan yasa ban wahalar da kaina wajen girka komai ba, daman can ba ci nake ba saboda shi nake girkawa kuma yanzu baya ma garin.

  Wayarta na dauko na kira layin Baba, ringing biyu ya dauka na gaishe shi cikin girmama da kauna ya amsa min da kuzarinsa.

“Baba ya jikin?”


“Al-hamdulillah jiki da sauki sosai sai da suka fada miki ko?”


“Hafiza ta zo jiya ta fada min, Baba ciwo ba abun boyu ba ne, musamman irin naka da idan kafafuwan suka tashi baka iya takasu, ya kamata aje asibiti a sake dubawa”


“Kafafuwan da sauki fa, yanzu nan ma Abdullahi ya dawo da ni gurin gashi, shi ke kaini aka gasa kafafuwan kullum, da sauki sosai ki kwantar da hankalinki”


“To Baba na so na shigo sai Abdulhamid yai tafiya, amman idan ya dawo ko kuma na yi waya da shi na nemi izininsa zan zo na dubaka”


“Allah ya miki albarka Halimatu, karki zoba da izininsa ba, ayi ta hakuri”


“To Baba Allah ya kara maka lafiya”


Da amin ya amsa na sauke wayar ina hawaye, duk yadda na so na daga waya na kira Abdulhamid na tambayi izininsa na zuwa gida sai na kasa, daga karshe na yanke shawarar tura masa sako. Ko minti biyu ba ayi ba ya dawo min da reply har da kalmar da nake zaton zolayace kawai ko kuma ya rubutu min ne saboda ya saba rubuto haka a karshen ko wane irin text da zai min.

“Subhanallahi Allah ba shi lafiya, ki je gobe, kuma idan na dawo zamu je mu duba shi, zan kira shi na masa ya jiki.

Ki kula da kanki i love you.....”


Daker na iya hadeye yawun bakina tare da wani abu da na ji ya tsaya min a makoshi. Sannan na tashi na shiga gyara gidan domin yau ban yi gyaran safe ba tunda wuni nai ina bachi.

Sai na kimtsa ko'ina na gyara komai sannan na shiga nai wanka, sai kuma na dawo gaban madubi na zauna ina ta kallon kaina, ni kaina ban lura da na yi rama sosai haka ba sai yau, ban ɗaga daga gurin ba sai da na ji wayata na ringing, number mama ce cikin sauri na dauka tare da sallama, bayan mun gaisa na sake mata ya jikin Baba ta amsa min da sauki tare da kara fada min Abdallah yana ta hidima da shi.

“Allah ya saka masa da alheri ya biyaki”


“Amin. Halimatu me ke damunki?”


“Me ya faru mama?”


“Kin daina zuwa gida, kuma Hafiza ta fada min kina cikin damuwa amman kin ki ki fada mata”


“Babu komai Mama kawai dai bana jindadi ne kwana biyu”


“Halimatu, ni fa mahaifiyarki ce, ko ms ke damunki ni ya kamata na fara sani kamin kowa, kuma idan ba ki fada min damuwarki ba wa kike da shi da za ki fada masa?”


Hawayen na ji ya cika min ido, tabbas ina bukatar mahaifiyata a kusa da ni kamar ko wace ƴa.


“Mama idan na zo gobe zan fada miki komai, maganar ba zata yiyu ta waya ba”


“To Allah ya kawo ki lafiya”


“Amin”


Na sauke wayar sannan na tashi na nufi wardrobe na dauko kayan bachina wando da riga na saka. Da kaina na tafi na rufe gate din gidan saboda yau ni ce kadai a gidan daman Abdulhamid ya saba rufewa yau kuma ba ya nan, bayan na rufe gate a dawo na rufe kofar falo na kashe kayan kallo da wutar falon sannan na shiga dakina na kwanta ba dan bachi ba domin na san bachi ba zai dauke ni haka nan kawai ba sai idan wani abun na sha.

Data ta na kunna na shiga media rabon da na yi chat ma har na manta, na samu sakkwanin da yawa musamman ta whatsapp, na groups da na private har na gaji da bibiyar grps din na kashe datar.


Misalin daya da yan mintuna da na ji kamar ana taba kofar falonmu, da farko tsoro ya kamani a tunanina ko aljanuna, sai da na jai motsin yayi yawa har da saka abu aka dukan kofar ana kokarin ballanta sannan na taso na fito daga dakin cikin karfin hali. Isowa falon tai daidai da balla kofar da akai domin kadan ya rage ba su cireta ba har ginin gurin sai da suka taba gurin balle kofar. Wadancan mutanen ne dai wadanda suka zo wacan karon, masu sanye da mask da kuma bingogi. A take a nemi tsoron da ke cikina na rasa, ashe akwai ranar da ko mutuwa za kai arba da ita baka tsoronta.

“Waye ku? Me kuke nema agurina? Waya turo k? Shi wanda ya turo ku me na tare masa?, miyasa ba ku zuwa sai a lokacin da mijina baya nan? Fyade kuka sake zuwa min? Ku sake sakawa mijina ya ki yarda da ni kamar wancen karon? Ku saka bindiga ku harbe ni zai fi min jindadi da kwanciyar hankali sama da ku same min wani cikin, ko waye kai ka san ni kuma ka san cewa mijin ba shi da lafiyar da zai iya kusantata shiyasa kake min haka saboda ka tarwatsa rayuwata, to Allah ba zai barku ba sai ya saka min.... ”


Ina rufe bakina daya daga cikinsu ya karaso kusa da ni ya buga min kan karamar bindigar da ke hannunsa abaki, wani azababben zafi na ji kamar babu bakin ma, ko kuma wacce aka cirewa hakora, a take jini ya samu hanya. Uku suka zauna a kujera yayinda sauran suke a tsaye.

Ban iya sake cewa komai ba, dan ban yi zaton bakina yana ajikina ba har lokacin, faduwa nai zaune na tara hannuna jinin dake zuba daga bakina yana ta tsiyayomin.

“Yau ba gurin mijinki muka zo ba, kuma ba mu san cewar mijinki baya gari ba, ba turo mu akai ba zuwan kanmu ne, kuma baki san daya daga cikinmu ba, sai dai na lura zuciyarki tana da tauri a yanzu”


Wanda ya buga min bindigar ne ya fada min haka yana tsaye akaina, muryarsa gargada take kamar wani boss kuma kamar yana taunar wani abu a baki, da alama ya boye ainahim muryarsa ne dan kar na gane shi, domin zuciyata bata yarda cewar wani ne dabam wanda ban sani ba. Risinowa yai ya kai hannunsa da cikin bakar safar hannu ya taba cikina.


“Amman da gaske kin yi ciki? Da gaske a akwai ciki a jikinki?”


Ya tambaya yana matsa cikin nawa da karfi kamin ya daga bindigarsa sama har sau uku, ban tana sani haka bindiga take da kara da kuma firgirtawarta ba sai yau, wani abu na ji cikin kaina daga nan ban sake sanin inda nake ba.!A yanzun ma ina bukatar wani ya tsaya min? Har a yanzun ma akwai wata hujja da nakr bukata kamin na gamsar da Abdulhamid ko wani da yake kusa da ni cewar an shigo gidanmu? Bayan fasa min baki da sukai ga kuma halbi da balle kofar falo, ashe har da gate din gidan suka fasa mana, sai dai maganin bachin da na sha bachin da na sha be bar ni na ji bude gate din ba sai na kofar falo.

  Sama sama nake jin maganar da su Mama da sauran kanena mata na yi, ban bude idona ba balle na iya tantance dare ne ko safiya ko kuma rana, sai dai a haniyar da nake ji kusa da ni har da Abdallah da wata macen da nake jin suna ta kira da Doc Safiyya.

 

“Halimatu....”+


Macen ta kira sunana, sai dai ban iya amsawa ba saboda ban yi zaton akwai sauran magana a bakin da nake jin kamar babu shi a sauran halittar jikina, saboda zugin da na ke ji. Kamar a mafarki na ji ta taba bakin ba shi na bude ido na zabura na tashi zaune da sauri.

“Sannu...”


Shine abunda ya fito daga bakin Abdallah yana kallona da mugun tausayi. Ban san yadda bakin nawa yai ba amman ina jinsa kamar ya min nauyi ga wani uban zugin da yake min kamar an cireshi. Fita yai ya bar mana dakin likitar ce ta gyara min bakinta ta saka min bandeji sannan suka canja min daki zuwa wani.

  A lokacin da aka shiga da ni a na kiran sallah asuba, tun da na lumshe idona ban bude ba har Abdallah ya shigo yana miki min waya.

“Mijinki yana son waya da ke”


Ban bude idona ba ban kuma yi wata alama ta zan bude din ba, har ya gaji ya maida wayar a kunnesa ina jin yana fada masa cewar bachi na ke. Yana fita Mama ta shigo da shesshekar kukanta ta zauna a kujerar da ke kusa da gadona, a lokacin ne na bude idona na kalleta idonta sun yi ja sosai alamar kuka tai da yawa.

“Sannu Halimatu...”


Daker na gyada mata kai sannan na sake maida idon n lumshe, ban sake budewa ba sai da rana ta soma haskowa cikin dakin. A wannan karon ba Mama na gani ba Inna ce zaune a mazaunin Mama.

“Sannu”


Nan ma kan na gyada mata ina jin ya min nauyi kamar ba nawa ba. Da kanta ta je ta kira wani likita namiji ya zo ya duba ni ban samu matsala ta ko'ina ba sai ta bakina shi ma kuma gindin bindigar da suka buga min ne, kamar wata karamar yarinya haka na zama duk yadda aka so na ci abu sai na kasa saboda zafin da bakin ke min. Ruwa kawai na sha shi ma kadan, sannan na tashi na shiga bandakin da ke cikin asibitin nai alwala na gabatar da sallah asuba. Ina sallame sallar abunda ya faru ya dawo min, a wannan karon ban samu wata shaida kmar wacan karon da na samu zoben mutumen ba wanda na ganshi a hannun Abdallah, a yanzu abunda nake ta kokarin shine siffanta surar mutumen ko zan iya gano waye ne yake min haka, idan an siffanta shi da Abdallah sai idanuwa su nuna min kamar Abdallah ya fi shi jiki, wata kila kuma dimaucewa ce ta sa ba zan iya tantancewa yadda ya kamata ba.

Idan ba Abdallah ba waye? Wana tarewa wani abu? Amman miyasa zan yi ta zargin Abdallah? Saboda shi ya saka ki a gaba ya hana ki rawar gaban hantsi, ita ce amsar da zuciyata ta ba ni.

  “Ba mu san cewar mijinki baya nan ba, wannan karon ba gurin mijinki muka zo ba, da gaske akwai ciki a jikinki?”


Su ne kalmomin da ke ta maimaita kanta a cikin kwalkwalwata, dalilinsu na ke bukata, da gaske ba su san cewar mijina baya gari ba? And idan ba a gurin Abdulhamid suka zo ba, me za su zo su yi gurina? Fyaden suka sake zuwa su min ko kuma wani abun dabam? Ban raba dayan biyu ba Hajiya tai sallama ta shigo tare da yar autarta wato kanwar su Abdallah, Inna ce ta amsa mata, ni kuma na juyo daga saman carpet din da nake zaune na kalleta. Ba shakka na ga tausayi a fuskarta tana ta min sannu ina gyada mata kai domin har lokacin ban yarda wata kalmar ta fito daga bakina.

“Ta ci abincin?”


“A a ruwa kawai ta sha shi ma kadan”


Inna ta bata sai ta sake cewa.

STORY CONTINUES BELOW

“Allah dai yasa ba su mata komai ba”


“Aa bakinta dai ne suka fasa, ina jin ko sun buga mata abu ne”


“Ayyah, Allah dai yasa ba su taba ta”


Wannan karon sarai na fahimci gun da tambayar Hajiya da dosa, ba lafiyata take nufin an taba ba, martaba take magana, da farko na ji ba dadi wata zuciyar na fada min cewar danta take tayawa kishi ko kuma take yi ma fargaba, ta wani gurin kuma tana da gaskiya domin mai kaunar ka ne kawai zai iya kulawa da wannan. Ba ita kadai ba na san mutane da yawa ma za su kawo wannan tunanin a zuciyarsu wata kila har da Abdulhamid din.


“Aa ba su mata komai ba, bakin ne dai suka taba”


Inna ta bata amsa sai Hajiya ta dora da bayanin yadda aka kawo ni asibiti.

“Ni ai ina kwance sai ga kiran Hassan, tsoro duk ya kama ni domin be saba kirana irin wannan lokacin ba, gashi kuma yace min zai yi tafiya har ya kira ni ya ce min su isa, cikin tsoro na dauka sai na ji shi ma hankalinsa a tashe muryarsa har rawa take wai na kira Husaini na fada masa yaje asibiti,na ce wace asibitin lafiya, a nan ya fada min wai makocinsa ya fada masa yan fashi sun shiga gidansa har sun yi harbe harbe”


A nan Inna ta tari numfashinta da cewar.

“To ya akai ya san sun shiga?”


“Ai makoncin nasa ma sun shiga gidansa suka karbe zinari, kuma suka shiga gidan da ke kallon na su Halimatu shi mai gidan ma sun kashe shi, to shi wannan wanda ya kira Hassan din shi ya kira yan sanda kin san shi ma dpo ne, ko da suka zo har sun gudu sai ganin gate din gidan Hassan akai a bude, shi ma na makocinsu a bude iyalai sai kuka suke”


“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, to wai turo su akai ko me?”


Inna ta tambaya sai Hajiya ta tabe baki

“To waya sani, shi dai wannan Alhaji ance ba su karbi komai ba kashe shi kawai sukai wai sun ce ransa kawai suke so, shi kuma na wannan Alhaji Munir din sun karbi gulagulai da kudi, shi ma Alhaji Munir din sun fasa masa kai ai, ko da suka kawo Halimatu Asibitin nan kansa na jini shi ma an bashi gado aka ce”


“Subhanallahi, ko shine na ji Anty na cewa na leka na ganshi? Allah sarki Allah ya tona asirin ko su waye”


A zuciyata na amsa da amin, ina ta tsarguwa da kallon da Hajiya ke min.


“Amman ke ba su dauki komai a gidan ba ai ko?”


Na girgiwa Hajiya kai alamar a'a


“Ikon Allah sai suka fasa miki baki kawai dan zalumci, kai mutum.....”


Ta karasa da fuskar tausayi, ni kam tuni hawaye sun cika min ido har sun fara wanke min fuska. Ban sake maida hankali akan duk wata fira da suke da Inna ba, domin tunani ya rabu biyu, makomata na ke hangowa da kuma kokarin wanke Abdallah da zuciyata ke yi. Anya zai iya aikata kisa? Taya mutum mai aikin kamarsa ma zai iya shiga fashi da makami? Me zai kai shi shiga? Yes wata kila ba shiga yai ba gaba daya ba, what if labawa yai a cikinsu saboda ya samu biyan bukatarsa? Can kuma wani bangare na zuciyata ya jefo min wata tambayar? Miyasa sai Abdallah na ke zargi? Mi zai saka dan'uwa yai ma matar dan'uwansa haka? Miyasa be min a lokacin da nake gidan Aminu ba sai a nan? Saboda a can yana ganin zan iya fitowa wata rana kamar haka na aureshi amman a yanzu babu wannan damar? Na riga na auri dan'uwansa dan uwan ma twins brother dinsa....

   Na kasa yarda cewar shi kadai din ne, zuciyata kuma ta kasa natsuwa cewar ba shi din ne ba, na kasa zargin kowa sai shi.

  Sai da Hajiya ta fice sannan na samu natsuwa da sukunin mikewa tsaye na nufi gurin windows domin ba Hajiya kadai ba, Inna bata cikin dakin a wannan lokacin, tsakanin kalaman Hajiya da zargin Abdallah da kuma tambayayin da mutumen yai min da kalaman Hajiya sai na rasa wanne zan fara tunani? Wasu abubuwa na ji suna min yawo a cikin kai ga wani uban nauyi da zuciyata tai. Kaina na jingina jikin window ya lumshe ido ina jin kamar zan samu mafita a nan. Ajiyar zuciya na sauke ya fi a kirga sannan bude idon da ke cike da hawaye ina ta kallon mutane da ke kai kawo harabar asibitin, duk wanda na hango burge ni yake domin na san damuwarsa ba ta kai kamar tawa ba, murmushi nake hangowa a fuskar wasu wasu kuma dariya na ke gani a fuskarsu abunda ni na gagara samu.

Wani na soma hangowa kamar Kabir kamar ba shi ba, sai da na kara maida hankalina sosai gurin kallonsa da yanayinsa na hauka da yake ciki ya tabbatar min da Kabir din ne, har yanzu tsingiltar take yana tafiya ya nufo cikin asibitin, sai ga securities din da sauri su ka zo suka rika shi suka fitar da shi daga asibitin.

STORY CONTINUES BELOW

Neman natsuwata da damuwata nai na rasa, gaba daya sai hankalina na koma gurin Kabir din. Ban san kuka nake mai sauti ba, har dai da yarana suka shogo na ji muryar Adnan yana min magana.


“Momy kuke kike yi?”


Juyowa nai na kallesu na gyada masa kai alamar eh kukan nake, domin a bayyana hake kuma ba zan iya boye shi ba a wannan lokacin, gaba dayansu suka fashe da kuka har Amal da take karama ganin nima ina kuka, risinawa nai a gurin na zauna a kasa sai suka zo kusa da ni suka zauna. Ni da su aka mai rarrashin wani, wani bangare na rayuwata ta baya ya fara fado min a rai, a lokacin da na samu cikina na farko cikin Adnan, ina farinciki ina jindadi saboda ina son ya'ya, amman Aminu ya nuna min ba haka ba sai dai a zubar shi be shirya haihuwa yanzu ba, rana za su tsufar da shi, za su hana shi shakatawa yadda ya kamata, daga lokacin komai ya sauya min na fara fuskantar kalubalen na rayuwa kala kala har na haifi Amal. Babu sunan da be kira ni da shi ba, yace min ina ta haihuwa kamar kaza, ina ta tara masa yaya saboda idan ya mutu na co gadonsa. Daga lokacin da na baro gidansa na yi zaton damuwar ta wuce na yi tsammani dadi zanji a gidan Abdulhamid ashe ba haka ne ba, wahalar bata kare ba damuwar ba ta wuce ba.

“Haba Halimatu ya za ki saka yaya a gaba kina kuka suna kuka? Miye haka?”


Maganar Inna ce ta saka na dawo hayyacina har na goge hawayena na mike tsaye na hau saman gadon na kwanta.

ABDALLAH POV.

Yana fitowa daga dakin theater ya nufi wani dakin dan tsabbace jikinsa da kuma cire tufafin da ya fito da su daga tiyatar, sai da ya cire komai ya wanke hannunsa sannan ya nufo office dinsa.

Zaunawa a saman kujerarsa sai ya ji kamar be zauna ba, sai da ya gyara zamansa sai yaji ba zaman ne abunda yake bukata ba. Tsaye yai dafe da kansa yana motsawa a hankali sai hawaye suka sauko masa.

“Why....?”


Jinginawa yai da ginar office din yana hawaye, he can't remember when last yai hawaye ko ya shiga damuwa irin haka, ko a lokacin da Halimatu ta auri dan'uwansa be samu kansa cikin damuwa kamar haka ba.

“I'm such a stupid.... Me yake damuna wai? What is wrong with me?”


Ya daga kansa sama hana hawaye tare da kuka marar sauti.

“Miyasa jabawata za ta zo a nan? Mi nai? Oh my God Allah kai kadai kasan dalilin da ya saka ka dora min son Halimatu....”


Juyawa yai yana kallon wayarsa da ke ringing.


“Kuskure ne abunda na ke yi, be kamata na bar Abdulhamid ya gano komai ba”


Ya busar da iskar bakinsa sannan ya nufi gaban teburin ya dauki tissue paper ya goge fuskarsa. Kiran na sake shigowa yai picking.

“Hello Hajiya”


“Na'am ya aikin?”


“Al-hamdulillah”


“Husaini na ce ka saka a yi ma Halimatu gwajin ciki da na hiv”


Mamaki ne ya cika fuskarsa.

“Why?”


“Why? Kamar ba ka san abunda ya faru ba?”


“Amman Hajiya kin ce ita da kanta ta ce ba su mata komai ba”


“Ai to fada za tai? Ai ba zata fada ba”


“Hajiya be kamata ki yi wannan maganar a yanzu ba, za ki kara sakata cikin damuwa ne, kar ma ki kawo ma Abdulhamid wannan tunanin dan Allah, ki aje wannan maganar na gafe”


“Wallahi ba zan aje ba, dan ba zan yarda ta cutar min da ɗa ba”


Tana fada hakan ta kashe wayar. Zaunawa yai a kujerar ya dafe kansa.

STORY CONTINUES BELOW

HALIMATU POV.

Da yamma Abdulhamid ya shigo asibitin, shi ma na ga damuwa da tausayi a fuskarsa da kuma kulawa a mu'amalarsa. Ni kuma na kasa sakewa da shi ko da na minti daya, irin kallon da nake ma Aminu na ke masa a yanzu. Bayan magariba polices suka zo suka suna min bincike sai a lokacin na yi dauriyar da na bude bakina na rika amsa musu tambayoyinsu, sun tambaya ko zan iya gane mutane na amsa musu da a a domin fuskokinsu a rufe suke kuma muryarsu ma a boye take, sun dauki duk bayanin da ya kamata su dauka sannan suka tafi.

  Kwana na biyu a asibiti suka sallame ni ganin na samun sauki, sai dai a cikin magunguna da suka ba ni har da na hawan jini kamar yadda suka fada min cewar ina da shi, a ranar da zan koma gidan mijina sai na ji kamar zan koma a cikin wata duniyar ta dabam, domin a asibitin ina ganin mutane familyna abokaina da kuma yayana suna cire min kewa ba kamar a yanzu ba da zan koma ni kadai.

  An gyara komai a gidan kamar babu wanda ya shigo, kofar ma an canja ta kamar yadda aka canja gate din, har na shiga dakina Abdulhamid be ce min komai ba, ni ma kuma ban ce masa ba, daman kuma ni me zan fada masa? Ce masa zan yi ka yarda da ni? Ko na tausaya min? Ko kuma ya zo mu yi kuka tare? A daren ranar ji nai kamar ba zan iya bachi ba dan haka na tashi nemam maganina da ke saka ni bachi amman ban samu ba. Na tsorota sosai rashin ganin maganin da nai domin na san akwai wanda ya ga maganin har ya saka hannu ya dauka. Wanin kuma ba zai wuce Abdulhamid ba domin shi kadai nake da tabbacin zai iya bincika duk abunda yake so a gidan nan.

A haka na kwana bachi ba bachi ba, minti daya biyu uku na farka, kamin ya sake daukata kuma sai an dade, da safe shi ya shirya mana abun karyawa da kansa ya shigo ya tashe ni na fito falo, amman sai na kasa cin komai, shi kan ya ci biredi ya sha tea sannan ya tambaye ni akwai wata matsala? Ko abunda na ke bukata na girgiza masa kai.

“Okay zan aiko miki da takeway da rana, da dare ma idan za a dawo zan siyo mana wani abu, me kika so ki ci?”


“Bana bukatar komai”


Kallo kawai yai ya dauke kai ya shiga dakinsa ya shirya ya fita. Daga lokacin sai zanantakewar mu ta sake sauya sabon salo baya bari nai girki sai dai ya siyo mana abinci, na sa yana min hakan ne domin ya nuna min ya damu da ni bayan kuma ya kasa kwanta a gadon da nake kwana kamar da, ya kasa sakewa da ni kamar da, sai yawan kallona da yake kamar mai tunani, zuciyata na raya min be natsu da ni ba,  wani lokacin ina jin kamar barin gidan shine mafita a agare ni da kuma shi, Har nai sati da sallamowa Hajiyarsa bata sake daga waya ta kira da sunan ta tambaya ya jikina ba balle har ta zo ko ta aiko a dubani, Abdallah ma tun a lokacin da ya miko min waya a asibiti ban sake jin duriyarsa ba, ba ma wacce ta fi ba ni mamaki kamar Suwaiba matarsa wacce bata zo ba kuma bata kirani ta tambayi lafiyata ba balle tai min jaje, abun har ya daure min kai wata kila kuma ita ta fara bin bayan Hajiya ne wajen tsanata duk da ban san na musu komai ba, ni kam bana dacewa da iyyen miji, haka uwar Aminu da kanensa suka tsane ni, ko da yake bana da sa'a da dacen rayuwa shiyasa saka hakan yake faruwa da ni.

Bayan mun gama cin abincin dare ya fada min cewar na shirya gobe za mu je asibiti, be fada min dalilin zuwan ba ni kuma ban cire tsammanin wani ko wata za mu je gani ba, ashe abunda ban sani ba gurin gwaji zai kai ni gwaji zai kai ni, mamaki ya cika ni, har na kasa boye damuwata da kuka a lokacin, sai dai ban ce masa komai ba duk kuwa da kasancewar a yanzu na kara katsewa da lamarinsa. Mijina be yarda da ni ba kenan.


“Zanje office na dawo kamin a gama, saboda akwai layi sosai”


Kai kawai na iya gyada masa na bishi da kallo har na daina hangoshi. Miyasa ba zai fada min naje nai gwajin ba? Mi yasa ba zai fada inda za mu je ba tun jiya? Idan ma aka samu ina dauke da hiv ko wata cutar Abdulhamid rabuwa zai yi da mi kenan? Lallai na sake sarewa da lamarin maza!

  Ina zaune a gurin ina bin layi hawaye na min zuba har aka kawo kaina, duk wanda ya gan ni a cikin wannan yanayin zai yi tunanin ko ina tsoron kar ace ina dauke da cutar ne. Bayan an dibi jinin nawa na fito na baro asibitin ba tare da tsayawa sauraren komai ba, ba fargaba nake kar ace ina dauke da cutar ba, na kasa raba dayan biyu a tsakanin neman Abdulhamid ya sake ni ko kuma na cigaba da hakurin zama da shi? Da kafa nake tafiya ina ta kallon ababen hawa da mutanen da ke kai kawo ba dan bana da kudin napep ba sai dan ina jin kamar tafiyar kasa zata sama min sassauci, ban san inda zanje ba tafiyar kawai nake duniyata na juya min. Wayata na ji tana ringing alamar kira ban tsaya komai ba na saka hannuna a jaka na fiddo wayar ba tare da na duba sunan mai kiran ba nai picking.1


“Kin fito daga asibitin ne?”


Muryar mai kiran ta karantar da ni ko waye ne.

“Na fito ina bakin titi”


“Bakin titi gurin me?”


“Ban sani ba....”


Na amsa ina jin kuka kamar zai kubuce min.

“Daidai ina kike tsaye?”


Waigawa nai na duba hagu da damana sannan na soma masa kwantanci.

“Ina kusa da Exclusive City”


“Okay shiga ciki ki zauna ga ni nan zuwa”


Kai na gyada masa kamar ance yana kallona sannan sauke wayar na share hawayen da suk zubo min na nufi Exclusive City din, babba guri ne na manyan mutane yan kasaita, gurina da masoya suka fi zuwa saboda tsarinsa da kuma abubuwan kawa da aka tanadar a gurin ga abinci kala kala, haka na ke jin ana yawa fada duk da ban taba zuwa ba sai yau.

Duk sai na ji dabam abun ka da wanda be saba ba, duk kuwa da kasancewar gurin kowa be kula da kowa ba, akwai guraren zama da yawa amman sai na ji na tsawwala kamar ba zan iya zama a gurin ba.

“Akwai wanda kike jira ne?”


Daya daga cikin ma'aikatan gurin ne yai min tambayar yana sanye da rigar aikinsa.


“Aa ina son na zauna a gurin da babu mutane sosai”


“Okay ga vip 1 can ga kuma vip 2 can, za ki iya zama a daya daga ciki”


Ya fada yana nuna min vip 1 da ke kasa da kuma 2 din da ke sama, zuciyata ta fi natsuwa da 2 din ganin shi a sama yake kuma bana iya hango komai daga inda tsaye hakan na nufi na cikin ne zai iya hango na waje, tsabanin na waje da ba zai iya hango wainar da ake toya a cikin ba. Kai tsaye na nufi hanyar da zata kai ni VIP 2 din, ina shiga na samu gurin fiye da yadda nake tsammaninsa domin tsakanin wani teburin da wani a akwa doguwar tazara ga kamshi da iska mai dadi na kadawa, komai na gurin ja ne gwanin sha'awa sai wani dan sauti da ke tashi mai dadi ta taba zuciya mai kuma daidai da kowane irin yanayi.

   Ko wane tebur kujera uku ce zagaye da shi amman ban da tebur daya mai kujera biyu masu fuskantar juna. Zuciyata ta fi natsuwa da shi fiye da sauran hakan yasa na nufi gurin na ja kujera daya na zauna. Wata irin natsuwa ta sauko min ba natsuwa irin ta masu kwanciyar hankali ba, natsuwa da samun damar yin kuka issasshe ta samu damar tausayawa, ta samu damar yin tunani da kuma nemawa kai mafita....!“Abun nan fa ya wuce iya abunda kike tunani, Wallahi mutanen nan ba za du yi karya ba, kuma ga zahiri kina gani, abubuwa sai kara kwabewa suke”+


Aminu ne yake wannan maganar yana shafa kansa cikin tsananin damuwa, hannunsa na dama rike da takardar transfer.

“Iko sai Allah, ni wani abun yana bani mamaki Wallahi, taya za ka biye maganar bokaye? Tun farkon fari ma mi ya kai ka gurin ya saka tsinbo? Da har za su fada maka karya da gaskiya ka yarda”


“Hajiya ai dubiya yanzu babu wanda yake zaune, ba maza ba mata ba kowa kuma yadda lamurran nan suka fara lalacewa ai dole na saka a bincika min, ba ni kadai ba ko Alfa da ya kai ni sai da abun ya daure mata kai”


“Allah kadai ya san gaskiyar wannan lamarin wata kila ma gurin malaminta ka fada, ko kuma shi alfan yana goyon bayanta ne, shiyasa suka hada kai ai maka haka”


“Babu wani zancen goyon baya Hajiya fa a zahiri kike ganin komai sai lalacewa yake”


“Kai fa baka iya tashin hankali ba, kai yanzu dan Allah Aminu har ka kawo maganar dawowa da Halimatu a gidanka? Mace da bata kaunar uwarka bata son yan'uwanka? Ka duba ja ga har kazafi tai wa Sadi fa? Wallahi har a bada ba zan taba son Halimatu ba”


“Hajiya abunda ba ki sani ba, ko wane dan'adam yana da good side of him kuma bad side, Wallahi Hajiya ba dan ina son dawowo da Halimatu ba, acire zancen arziki, Hajiya Halimatu ta fi Murja hakurin zama da ni, Halima ko bata son abu bata nuna, sannan ko fada nai mata ko na ci zarafinta sai dai tai kuka ta ba ni hakuri, and tana kokarin ganin ta gujewa bachin raina, zan iya tafiya inda nake so nai iya adadin kwanakin da nake so na dawo bata ce min komai, amman ban isa nai ma Murja haka ba Wallahi Hajiya, idan na dawo tara na dare Wallahi sai Murja ta yi min fada, amman a lokacin da Halima take nan zai iya kai wa 1 na dare a waje kuma ba zata ce min komai ba, Murja ta bi ta saka min ido akan komai nawa, ba ni d sukunin daukar waya na latsa a cikin gidana idonta na kai”


Hajiya ta saki baki.

“Ban gane idan kai dare tai maka fada ba? Uwarka ce ita? Ita ta aje ka ko kai ka aje ta da zata maka fada? Ita ba mata ba ce da ba zaka mata magana ba”


“Hajiya ba za ki gane ba ne, idan ranta ya bace, jikina har rawa yake Wallahi”


“To acan gurin malaman da kaje ba su fada maka komai akanta ba?”


“Me za su fada min? Ni yanzu ba ta nata nake ba, ta Halimatu na ke domin sun fada min matukar ban mayar da ita ba, ba zan taba ganin komai daidai ba, kuma ga alama nan kina ganin bayan rage min mukami da akai yanzu an min transfer zuwa enugu, duka duka yaushe ne rabuwar mu? Idan aka kara dadewa kila ma bara zan koma, tun da sun ce ita ke da kashin arzikin duk abunda na samu saboda ina tare da ita ne, ni da farko ma na dauka ko sammu ne kai mi shiyasa ma har na biye ta Alfa ya kai ni gurin ashe ba asiri ba ne rabuwar da mu kai ce, Hajiya ki duba fa ki ga abun hawa ma neman gagara ta yake, motata na mata gyara uku abunda ban taba ba, yanzu na siye sabuwa ita ma engine dinta ya tsaya, sabuwar mota fa Hajiya Motar miliyan biyar ace engine dinta ya tsaya”


“Wai kana nufin ba da motar ka zo ba?”


“Wallahi Alfa ne ya sauke ni bakin gate, tun jiya motar ta tsaya tana can gurin ma su gyara”


“To abun nan fa d daure kai ni na fi zargin sammu gaskiya, asiri ne akai maka, ko ita ai zata iya maka asirin na ka lalace tun da ta ga ka sake ta, ko kuma abokan aiki ko makota”


“Hajiya Malami hudu msgana daya suke, babu wanda yace asiri ne, ni dai ki taimaka min ta dawo dan Allah”


“To ai ban ga ta inda zan iya taimaka maka ba, matar nan fa ma aure tai gidan wani take”


STORY CONTINUES BELOW

Dafe kansa yai.


“Kai Hajiya, ko wane da idan yana cikin matsala gurin uwarsa yake zuwa ta sama masa mafita, amman ke sai kokarin kin yarda kike da ni”


“Ba yarda ne ban yi da kai ba, nawa binciken zan yi akai”


“To ki kara bincika mu ji idan za a samu results daya, ni yanzu yarana nake son na fara dawowa da su hannuna, na san ina dauko yaran nan hankali zai dawo kaina dan bata hada su da kowa ba”


“Tana son su za tai aure ta bar su?”


Cewar Hajiya tana tabe baki.

“Wannan ai na dabam ne, idan naja yaran a jikina na nuna musu su janyo uwarsu ai dole hankalinta ya dawo nan, Wallahi shegen son ya'ya ne da ita Allah kadai ya san yadda akai ma tai aure ta bar su”


“Kudi ta bi, shi wanda ta auran ba ance dan uwanta ba ne kuma mahaifinsu ya bar musu dukiya, ai kudi babu abunda basa sakawa, ni ganin na ke komai kai ba zata bar wacan mijin ta dawo maka ba”


“Zata dawo ai kin dan yadda take so na, kuma daman first love shine so ai, kuma ni na san Halima na so sosai Wallahi, zata dawo da gudu ma”


“Uhm... ”


Mikewa yai tsaye.

“Motarki na nan Hajiya?”


“Wallahi na aiki Musa direba da ita Mafara sako zai karbo min, ka kira Sadi ya kawo maka motarsa daya mana ai mota biyu ne da shi”


Ba musu ya koma ya zauna ya ciro wayarsa ya kira kanensa Sadi. Ringing biyu zuwa na uku ya daga.

“Sadi kana ina?”


“Gani kusa da gidan Hajiya”


“To ina gidan karaso ka sauke ni gida”


“Okay”


Bayan na sauke wayar, Hajiya ta cigaba da yi masa maganar so take ta karkarto hankalinsa da barin zancen maido Halimatu domin ita a ganinta ba mafita ba ce, zuciyarta ta fi natsuwa da sammu akai masa ko dai Halimatun tai masa ko kuma wani dabam, ba a wuce minti ashirin ba Sadi ya shigo gidan cikin sabuwar shadda light yellow da hula kubu sai kamshin turare yake. S tsaye ya gaisa da Hajiya domin shi ma a hanya yake akwai inda yake son zuwa.

“Gida zaka sauke shi”


“Ina motarka ne?”


Sadi ya tambaya yana barin kallon Hajiya wacce tai masa maganar.

“Wallahi ta samu matsala wai engine dinta ta buga”


Aminu ya fada cike da damuwa a fuskarsa.

“What, motar da ka siyo satin nan ko dai wacan tsohuwar”


“Tsohuwar ai siyar da ita nai, wannan dai sabuwar”


“Garin ya?”


“To ni ina ma zan iya cewa ga dalili, abubuwan ne dai sai hamdala”


“Allah ya kyauta, tashi muje”


Sai da Aminu da Hajiya suka amsa da Amin sannan ya mike tsaye suka fice tare. Har gida Sadi ya kawo Aminu, bayan ya bude motar ya fita Sadi ma ya bude ya fito wai bari ya gaisa da Madam. Aminu na shiga cikin falon Murja da taso da sauri ta rumgume shi tana masa oyoyo sai shagwaba take zubawa kamar wata karamar yarinya.


“Ina tare da shi fa Hajiya”

“Dan kana tare da shi sai ya hanani nunawa mijina soyayya?”


Murmushi Sadi yai ya dauke idonsa ya nufi kitchen.

“Bari na sha ruwa”


Kitchen din ya shiga da kansa ya dauko cup ya bude freezer ya dauko robar ruwa ya bude ya soma bulbulawa. Kamar daga sama ya ji am rumgume shi ba shiri ya dire ruwan da yake sha ya juyo da sauri yana kallon kofar kitchen din.

STORY CONTINUES BELOW

“Kai dan Allah sarkin tsiro, ya shiga dakinsa”


“Amman ai zai iya saukowa yanzu kuma ya shigo nan”


Ya fada da rada hankalinsa a tashe yana kallon kofar kitchen din dan ya san the worst thing da zai aikata shine ya bar dan'uwansa ya san alakar da ke tsakaninsu.


“Ka daina zuwa kwana biyu, i miss you”


Ta fada tana dora hannunta a saman lips dinsa sai lumshe ido take da fake eyelashes dinta.

“Murja alakar mu ta da ba kamar ta yanzu ba ce fa, saboda dan'uwana kike aure dole nai tsaka tsantsan”


“Auren dan'uwanka ya hana alakar mu cigaba ne? Tun farko ba kai kaja ba, da aka aurena zan auri yayanka ne, sai wani kwana kwana kake min jikina kawai kake so”


Saurin turarenta yai daga jikinss ya fito daga cikin kitchen din jin kamar motsin fitowar Aminu a falo, kai tsaye ya nufi kofa ya fice daga falon gaba daya. Dariya murja tai ta nufi dakin mijinta, da taimakonta yai wanka ya shirya cikin farin yadi marar nauyi sannan ta gabatar masa da abincin rana. Cin abincin suke yana ta sake2 yadda zai bullo mata, so yake ya fada mata cewar yana son ya dawo da yaransa a gidansa amman yana jin tsoronta, baya son bacin ranta idan ranta ya bace ji yake kamar zai mutu, ko motsi dai sai ya rasa natsuwarsa saboda tsoron abunda zai fito daga bakinta, haka Allah ya saka masa tsoronta kamar mutuwarsa, idan ranta ya bace har kuka yake mata gurin bata hakuri abunda be taba yi ma wata mace ba, ko Hajiyarsa baya tsoro yadda yake tsoron Murja.

AHMAD POV.

“Na dauko Baby Namra daga gidan Hajiya, ka dawo gida da wuri karka wuce 8”


Sai da ya hade yawun bakinsa sannan ya amsa mata ta okay.

“Yayi Mommy's Boy”


Rahim ya fada yana dariya.


“Ba fa abun dariya ba ne seriously bana jindadin abunda kake min”


“Okay sorry but abun nan yana ba ni dariya”


“Ba abun dariya ba ne, abun nan gaba yake kara yi ba baya ba, na rasa yadda zan bullowa lamarin nan, yanzu fa ta kai har wayata Hajiya ta ke karba ta duba, irin ita bata yarda da ni ba,kullum ganin take kamar yan mata wayo za su min”


Rahim ya kara matsowa kusa da shi ya da fashi.


“Magani kawai kai aure Gwarzo, matukar ba aure kai ba zai Hajiya ba zata daina ganinki a yaro ba”


“Auren ba mafita ba ne, yaure uku nai kamin na auri Halima amman ko wace ta kasa zama da ni sai Halima ita ma kuma saboda ta yi hakuri ne, bayan rasuwarta mace biyu na aura Hajiya bata barin na zauna da mata, tun da idan bata ga dama ba sai ta hana ni cin abincin mace ta ce bata yarda da shi ba, kuma ko yarinyar na nemo idan bata gamsu da ita ba ba zata bar ni na aureta ba”


“Wata mace zaka aura ba yarinya ba, mace mai hakuri da sanin ya kamata, kuma kamin ka aureta ka fara gabatar mata da Hajiya ka fada mata komai na ka karka boye mata, kai idan ta kama ma kai auren a boye kai yi dan samawa kanka mafita, dan Hajiya har yanzu bata daina ganinka a yaro ba, bata yarda ka girma ba”


“Wallahi abunda take min ko Baby Namra albarka, dan yau idan Baby Namra ta ga dama zata iya zuwa wani guri a cikin familymu tace can zata kwana kuma Hajiya ta barta amman ni ban isa ba, abun da Hajiya take min har dauren min kai yake wani lokacin har daure min kai yake”


“Ka samu wata ka aura, irin macen nan da ta saba shan wahalar gidan aure, ka aureta kuma ka fada mata komai karka bi soyayya ka auri yarinya ta zo tai ma Hajiyarka hauka ko ta kasa hakuri da kai, iirin dai mace mai yaya biyu uku aha”


“Kai ba zan iya auren macen da wani ya aura ba, you know ina da kishi sosai, ba zan iya zama macen da wani ya aura ba balle ma wacce tai aure har fiye da daya”


“To ai kaji matsalar ka fi son ka auro yan matan nan na zamani kansu na hayaki dole su ce ba za su zauna da Hajiya ba, ba wai dan kana sonta zata aureta ba, kai ko auren kwangila ne kai kawai da zarar ka samu yancinka gurin Hajiya sai ka rabu da ita ta auro wacce kake so, ya kamata ka amsa sunanka na Gwarzo fa, na san baka daukar rainin kowa a kamfani, idan ka bawa mutum umarni jikinsa har rawa yake ya cika maka aikinka, to ko a gida ya kamata kana motsawa”


“Da Halima na nan da yanzu na amsa, Ba zan taba son wata ba Rahim, ni mijin matacciya ne, na riga na auri Halima kuma na auru, duk mace da zan aura zan aureta ne kawai dan samun mafita amman ba dan kauna ba”


Yayi maganar cikin sanyayyiyar murya, yana sotsa lips din, zuciyarsa na sosuwa da kauna Halimatunsa Uwar Baby Namra.

“Halima ta yi min abunda wata macen bata taba min ba, ta haifa min Baby Namra, ta yi hakurin zama da Hajiya har na tsawon shekara biyu...”


Rahim ya soma lura da yanayin abokinsa, daman ya saba shiga a irin wannan yanayin a duk lokacin da aoa dauko maganar Halimatu, a kokarinsa na kawar da maganar ya dauko masa maganar kamfani.

“Yauwa na manta ban fada maka ba, sun fa turo takardun nan ta mail din kamfani amman sai mun yi printing out....”


Mikewa Ahmad yai tsaye cikin damuwa.

“Dan Allah ka daina maganar wani kamfani a yanzu, lemme go and rest...”


Fita yai daga gurin ya nufi motarsa, yana shiga ya dauki hanyar Exclusive City.

HALIMATU POV.

Na yi kuka iya wanda zan iya, na yi na gaji na rarrashi kaina domin ba ni da mai rarrashina a wannan lokacin. Daya daga cikin waitress din dake gurin ne ya zo yana tambaya idan ina bukatar wani abu?

“Bana bukatar komai, akwai wanda na ke jira ne”


Juyawa yai ya koma gurin da yake tsaye, ya cigaba da danna wayarsa, binsa nai da kallo kamin na ji wata murya mai cike da bacin rai tana min magana.

“Waya aje wannan matar a nan?”


Juyowa nai na kalleshi da kumburarrin idanuwana, mutunen nan ne daya taba ture ni a keke, kuma shi ne wanda na gani a lokacin da naje kai Namra School, kuma shi ne mutumen da ya tsinci Namra. Da saurin waiter din dazun ya zo yana tambayar ba'asi.

“Taya za a bar wata ta zauna a seat din nan? Me ke damunku? Da alama kai bako ne, kuma laifin ba na ku ba ne laifin shugabanku ne, for more than ten years ina biyan kudin gurin nan saboda tsabar rainin hankali yau za ku bar wani ya zauna? Oh haka kuke idan bana nan daman you're very stupid”


Sauran waitress din suka zo suns bashi hakuri, wanda ni ban ga dalilin hakan ba, ko da yake na ji ya ambaci sama da shekara goma yana biyan seat din da alama baya son kowa ya zauna ne.

“Ke dalla malama tashi ki rasa kujerar da za ki zauna sai wannan”


Ko kadan maganarsa bata 6ata min rai ba, da alama macen da yake biyawa kudin kujerar tana da muhimmanci a gareshi, ba kamar ni ba. Mikewa nai tsaye na kalli kujerar sannan na kalleshi na ce.

“Ka yi hakuri ban san cewa kujerar ta ka bace, ban san alakarka da mai seat din ba, mata, yar'uwa, uwa, ko ya ko kanwa, amman ka bata hakuri a madadina, domin ko wacece duniyarta kyakkyawa ce, kuma mai fadi ce shiyasa tai dace da mai kare martabar gurin zamanta ba ma ita din ba”


Hannu na kai na dauki jakata na yi gaba abuna ina jin zuciyata kamar zata fito, na taki sa'a ina kawowa bakin gate din gurin Motar Abdulhamid na kunno kai a harabar gurin, sai da ya faka motar yana kokarin fita na nufi gurin motar na bude na shiga. Ba tare da yace da ni komai ba yai ma motar key muka kama hanyar gida.

__________________


Wai ni kadai na ke hango wani abu?🤔

Bari mu ga masu brain me kuke hangowa? 🤔

Tafdijam 😲 fatar dai kun shirya tafiyar domin yanzu aka fara..... 😊3Na yi mamakin ganin kawata Sa'adatu tana jirana a farkon shiga falona, ko wa nuna mata gidana ma oho ni har na manta da ita a cikin duniyar nan. Tun kam Abdulhamid ya faka motarsa ta mike tsaye tana ta kallon motarmu. Har ya faka motar ya bude ya fita be ce mim komai ba kamar yadda nima ban ce masa ba tun bayan shigowa a motar.

  Irin kallon nan da ta saba na yan bariki ta fara yi min kamin ta mikawa Abdulhamid shi tare da gaisuwa. Shi kuma ya amsa mata da fuskarsa ta rashin sakewa da mutane, ma'ana ba yabo ba fallasa ba kamar Aminu ba da idan ya ganta bakinsa har rawa yake wajen amsa mata gaisuwa.+


“Wa nake ganin kamar Sa'adatu?”


“Ba kamar ba ce ni dince, tun da kin yadani ni ai na nemo ki”


Na yi dariya kamar yadda ita ma tai tana bin Abdulhamid da kallo har ya shige falon sannan ta kalleni.

“Shine angon na mu?”


“Eh shine”


Sai ta tabe baki har da wani lumshe ido ta bude.


“No wonder ake mana rowarsa, ashe kyakkyawa ne mai naira, gaskiya Halima kina dacen auren maza masu kyau da kudi, ko da yake kina da kyau ne shiyasa, da ni ke da kyaunki da yanzu na ci kudi”


‘Yes ina dacen aure a gidan hutun amman ba dan na hutu ba, sai dan na fuskanci wani kabulen’


Na fada a raina a fili kuma sai nai dariya na ce.

“A takaice dai mijina ya burge ki, gashi kuma shi ba kamar Aminu ba ne balle ku kulla”1


Kallon rashin fahimta tai min tana yar dariya kamar ta ji kunya.

“Ban gane ba?”


“To ya za'ayi ki gane kuwa? Ke dai zo muje ciki”


Ina gaba tana biye da ni a baya har muka shiga falo. A kujerar da ke kusada kofar ta zauna ta zubawa Abdulhamid ido ni kuma na nufi two seater da yake zaune yana lasa waya na zauna a kusa shi, kamar wanda wani abun ki ya zauna kusa da shi haka yai saurin tashi ya nufi dakinsa, iyakar kokarin da nai na danne damuwar da na ji ne dan kar Sa'adatu ta zargi wani abu. Na tashi na shiga kitchen na dauko mata ruwa da lemun mu na hausa na kawo mata. Sai gashi ya sauko ko inda nake be kalla ba ya nufi kofa ya fice a uzurce.

“Halimatu wane irin zama kike da mijinki?”


Kamar daga sama na ji tambayar Sa'adatu tana mire baki.

“Kamar ya?”


“Ato kin san ni bakina baya shiru, na ga kamar akwai yar matsala a tsakaninku ko kuma shi haka rayuwarsa take?”


“Wai Sa'adatu sakin fuska yasa raini ya shiga tsakaninmu har ta kai kike iya fada min duk abunda ya zo bakin kina mu'amulantata yadda kika ga dama”


Sakin baki tai ganin kamar na taso mata da fada.


“Haba Hajiya ta, makano ne kawai zai shigo gidan nan yace be fahimci akwai rashin jituwa tsakaninki da mijinki ba, kuma wanda ya damu da kai ne ya damu da matsalar ne kawai yake nuna maka damuwarsa, kalle ki Halima Wallahi har kin fi auki a gidan Aminu dama da nan”


“Zuciyarki bata raya miki ko bana da lafiya ba? Babu abunda ya zo kanki sai rashin Jituwa?”


“Hmm yanzu dai Allah ya baki hakuri, mu bar wannan maganar, ya yaranmu ya su Amal?”


“Suna lafiya”


Na amsa mata ina kara hade fuska tare da dauke kai. Shiru ya shiga tsakaninmu kamin ta sake dauko wata maganar.

“Amman wai Halimatu ba kya kewar yayanki? Na ga Aminu ma da ke damu da yaya ba, yanzu yana ta shiga damuwar rashinku balle ke da kike tare da su kullum”


STORY CONTINUES BELOW

“Ke da kike iya barin Salim da Yusura kina zuwa wani gurin, ba tare da sanin irin kulawar da za a basu ba kika tafi hankalinki kwance har wani gari, balle ni da a gari daya ne kuma bautar Allah zan yi?”


“Ba ki gane ba ne, ni ai tafiyar kwana biyu ce ko uku, idan na dade na yi sati ke kuma aure ne fa, kin san wani lokacin baka sanin darajar abu sai idan baya kusa da kai kamar yadda Aminu yake a yanzu karki so ganin yadda ya koma abun tausayi duk inda ya zauna sai zancenki yake da na yaransa”


“Idan abu yana da muhimmanci a gurinka baka taba yarda ka rasa shi, tattalinsa kake, kana Ala ala kar ya subuce maka, domin duk ranar da ka rasa abun nan ka rasa shi kenan har abada, be kamata ki kawo min zancen wani namijin ba a gidan mijina, na dade da mantawa da Aminu ko wani abun daya shafe shi, ko da wasa karki sake min maganar Aminu”


“Ai na san Aminu ya kuntata miki amman Wallahi Halimatu yana cikin damuwar rashinki a yanzu, matar da ya aura ma ta rasa gane kansa”


“Wai Aminun ne ya turo ki yace ki zo ki fada min yana cikin matsala?”


Ta dan wara ido.

“Ahhh ni ina na ga Aminu da har zai ce min haka”


“Za ki gansa mana ke ai falkalsa ce, za ki iya sanin halin da yake ciki ko ma ya fada miki da kansa”


“Subhanallahi Haba Halimatu wannan bawa irin magana ce, na san dai ina raba wasu mazan, amman taya za ayi na raba mijinki Fisabilillahi, ni ba zan iya wannan cin amanar ba”


“Shiyasa a kike biyarsa kuna zuwa har wani garin kuna kwana, ke fa san komai da ke tsakaninki da Aminu, na samu ido ne kawai saboda na bar ku da Allah, shiyasa na tattara lamarinku na aje gefe, ba Aminu ba ko mai sunansa bana son ji yanzu balle shi din da kansa daga ke har shi na tsaneku tashi ki bar min gida”


Da sauri ta mike tsaye jikinta har bari yake.


“Kamar ba Halimar da na sani ba, da alama dai wani ya shiga tsakaninmu”


“Za ki fita ko sai na wulakanta ki”


Daukar jakarta tai ta juya da sauri ta fice tana waigena. Har bakin kofar gate na bita na tsaya sai da na tabbatar ta fice daga gidan sannan na rufe gate din na dawo cike da bacin rai.

  A lokacin dana zauna falo sai bacin ran abunda Abdulhamid yai min a gaban Sa'adatu ya tsaya min a rai, yanzu har ta kai Abdulhamid na kyamar zama a kusa da ni kuma ba zai iya boyewa a gaban mutane ba sai ya nuna? To ko dai ina dauke da cutar ne?ko kuma kiyayyar ce tai zurfi har haka a zuciyarsa. Ba yau kadai ba tun daga lokacin da abun nan ya faru na fahimci irin zaman da nake da Abdulhamid sai dai na yau yafi na ko yaushe.

Ba zan iya wannan zaman ba, sai kace an masa dole da ni ko kuma auren kiyayya mu ka yi? Idan har ya zai iya rabu da ni kai tsaye ba to ni zan iya neman rabuwa da shi domin rabuwar ce mafi a'ala a yanzu, zai fi samun natsuwa idan bana kusa da shi kamar yadda ni ma zan fi samun natsuwa idan na san bana tare da shi.

Ba Abdulhamid kadai ba ni inajin idan ma na rabu da shi ba zan sake auren wani namijin ba, domin na fahimcin gaba daya maza basa da kirki kansu kawai suka sani, ina ji a raina da ace ni ce ba zan iya yi ma Abdulhamid haka ba bazan iya rabuwa da shi ko nuna masa damuwa ba.

“Gaba daya mazan duniyar nan ba su da karki, gaba daya kansu kawai suka sani, su auri mace suna wulakantata suna yi mata yadda suka ga dama”


Na furta da karfi ina fashewa da kuka tare da dafe kai.


“Zan nemi saki, dole ne Abdulhamid ya sakeni, kuma ba zan sake aure ba, zan samu wani aikin zan rike yayana na cigaba da kula da su, ba zan sake yarda ciwon da namiji ya kashe ni ba, na gahi hakan nan wahalar ta isa haka...... ”


Wani abu na ji ya taso min ya tsaya min a kahon zuciya ya danne min numfashi, a guje naje na bude freezer na dauko ruwa mai sanyi na sha sannan na samu relief. Ji nai bana bukatar komai sai shan maganina shi kadai na ke sha ya lulani wata duniyar da nake mantawa da komai, gashi kwana biyun da nai ba sha ba har wani abu nake ji a cikin kaina kamar hayaki. Falon na dawo na bude jakata na dauko 2k na saka Hijab din da n cire na shiga bedroom na dauko keys na rufe gidan na nufi chemist din unguwar inda na saba siyen maganin.STORY CONTINUES BELOW

AHMAD POV.

“Maganar gaskiya ba ka kyauta ba Gwarzo....”


Yayi saurin taron numfashinsa yana shafa kansa.


“Na sani.... Ni kaina bayan na mata fadan na ji cewar ban yi daidai ba, musamman da bata min tsawa ba kamar yadda nai mata, you know i hate mutum yai min tsawa”


“Ita ai ba laifinta ba ne laifin ma'aikantan gurin ne kuma.... ”


“Kuma What Rahim...? Sai son nanata maganar nan kake yi, i feel like na yi abunda be dace ba hakan be wadatar ba?”


Da mamaki Rahim yake kallon abokin na sa, daman can haka yake wani irin murdaden mutum ne mai wuyar sha'ani, shi ya kawo maganar abunda yai ma Halima, kuma ya fadawa masa be ji dadin yadda yai mata ba and now yana kokarin bleme Rahim akan ya bashi laifinsa.

“Muna magana ka ce you need to rest ka bar nan baka ce min ga gun da zaka je ba, ashe Exclusive City ka nufa, yanzu kuma ina zaune ne ka dawo ka bani labarin abunda ya faru, and now kana son ganin laifina, shiyasa kake samun rashin jituwa da mutanen ka, mutum ko naman jikinsa zai yanka ya baka sai ka ce da biyu yai, Hajiya ce kawai maganinka Wallahi, ba Hajiya ce kadai take saka matanka na guduwa ba Gwarzo Kai kanka matsala ne”


Tsaki yaja ya dauki hularsa ya saka ya fice daga falon yana ciro keys din motarsa a aljihu.

@360 isa gidan Hajiyarsa, as usual sai da ya fara shiga falonsa kamin ya wuce dakinsa, sai dai wannan karon be shiga da yanayin da ya saba ba, idan har bw shiga da sallama ba to zai shiga da far'a fuskarsa a sake sai dai yau babu ko daya. Be ma ankaro da ba kuwar da ke falon ba har sai da ta gaishe shi.

“Ina wuni”


“Lafiya kalau”


Ya amsa mata sannan ya zarce dakin Hajiya kasancewar be same ta a falon ba. A daki ya same ta tana aikin fesa ma jikinta turare da alama wanka tai ko kuma ta saka sabon kaya kamar yadda ya ga kwaliya a fuskarta.

“Gwarzo yanzu nake kokarin kiranka fa?”


Ta fada far'a fal tana aje turaren da ke hannunta.

“Amman dai a lokacin dawowa ta bwyi ba ko?”


“Ba wannan ba ne, ba ka ga bakuwa a falo ba?”


“Na ganta”


“Je ku gaisa”


“Mun gaisa ai”


“Je ku gaisa dai, ai ba irin wacan gaisuwar ba ka kalleta da kyau”


“Eh sai in ji me?”


“Ka ji kana sonta mana”


Kwantawa yai a kan kujerar da ke dakin yana girgiza kai.


“No no no no Hajiya, yanzu kuma ai bata mata na ke ba, ina ni ina mace yanzu”


Wani kallo Hajiya take masa shi kan be ma kula ba sai zuba zance yake.


“Da ma namiji ne sai naje na zauna mu sha fira amman mace a yanzu ni... No lalalalala, na dai namiji ne”


“Mace ta daina baka sha'awa a yanzu”


“Eh mana da ma namiji ne”


“Mazan ke burge ka kenan?”


Dagowa yai ya kalleta ganin ta zuba masa ido yasa ya tashi zaune.

“A'uzubillahi bafa can nake nufi ba, i mean da namiji ne dan'uwan sai mu yi fira”


Ya mike tsaye tare da zuba hannayensa aljihu ya fice daga dakin, dan yasan halin Hajiyarsa yanzu sai ta sauya ma zancensa ma'ana shi ko ba dagon zance yake so ba. Part dinsa ya nufo har lokacin hannayensa a aljihu yana takawa a hankali kamar mai jin wuyar cira kafar. Be yi  mamakin ganin kofar falonsa a bude ba tun da ya san mai masa haka a duk lokacin da aljanun nata suka tashi. Yana shiga ta zo da gudu ta rumgume shi tana dariya.

STORY CONTINUES BELOW

“Yes Daddy Oyoyo, Daddy na gyara maka dakinka na goge komai na sa turare”


Kanta ya shafa cike da kaunarta, yana murmushi.

“Good girl Allah yai miki albarka”


“Ameen Daddy za ka kai ni gidansu kawata Namra ko?”


Iskar bakinsa ya busar ya rika hannunta suka nufi kujera ya zauna, ya zaunar da ita saman cinyarsa sannan ya soma mata magana a hankali.

“Baby ke kullum kina zuwa gidansu kawarki nan amman ita ba kasafai take zuwa nan ba”


“Daddy ai su gidansu ba su da mota, shiyasa bata yawan zuwa, ni dai ina son zuwa gidan Daddy pls... ”


“And Baby na yi m maman kawarki fada”


Ya fada yana shafa kanta har yanzu jin yake be kyauta ba. Ta zaro ido tana rufe baki.

“No Daddy how?”


“Laifin tai min nai mata fada, so ko kinje gidansu ba zata miki yar fuska”


“Daddy tana aiki a karkashinka ne?”


“No”


“Then why kai mata fada?”


“Wani abun tai min wanda ya bani haushi”


Baby Namra ta yi masa wani kallo.

“Daddy waye be da gaskiya tsakanin kai da ita?”


“Ni ne”


Ya amsa kai tsaye sai ta sauka daga saman kafafuwansa.

“You should apologize to her”


Sakin baki yai be ce mata komai ba.

“For the sake of me Daddy bana son na bata da kawata Namra ina sonta, idan muje gidan ina jindadi akwai mutane da yawa a gidan kuma duka suna suna kuma Daddy scul din mu daya, Mommynta ta shafa kaina tace Allah ya min albarka Daddy why za ka yi fada da ita?”


Kokarin fashewa da kuka take, domin har cikin zuciyarta take son zuwa gidan su kawarta Namra and tana jindadin yadda yan gidan suke mu'amalantarta.


Hannayenta ya kama


“Zan kaiki gidan amman ba zan bata hakuri ba, ni nake da gaskiya ai”


“Amman yanzu ka ce kai ne da laifi fa”


“I mean na yi fadan da yawa amman dai ni ne mai gaskiya”


“Daddy.... ”


“Baby.... ”


Shi ma ya marairaice fuska kamar yadda tai yana kokarin rarrashinta Hajiya ta shigo falon.

“Gwarzo”


“Na'am Hajiya”


“Taso ka kaita gida”


“Bata wuce ba?”


“Eh kai zaka kaita gida, kuma ka tsaya ka kalleta da kyau”


“Tooo....”


Ya fada da dan mamaki, sannan ya saki hannun Baby Namra.

“Baby zan je na dawo sai na kaiki gidan ki bata hakuri a madadina kinji?”


Ta gyada masa kai tana share kwalla, Hajiya na gani hankalinta ya tashi.

“Baby ya akai? Me kike yi ma kuka?”


“Daddy ne ya tsokani momyn kawata Namra”


“Garin ya? Shi ne kika kuka kuma?”


STORY CONTINUES BELOW

Ta gyadawa Hajiya kai, shi kuma ya fice yana ta sake sake a ransa.  Falon Hajiya ya shigo sai ya samu yarinyar a zaune ta natsu sosai guri daya tana wasa da yatsun hannunta.

“Hajiya ta ce zan kai ki gida”


“Okay tau”


Ta mike tsaye tana daukar katuwar ledar da Hajiya ta bata tana unkurin tafiya sai ga Hajiyar ta shigo rike da hannun Baby Namra tana fadin.

“Ka biya da ita asibiti kanta ke ciwo, na bata magani ta sha tace min be daina ba”


Da okay ya amsa can kasan zuciyarsa kuma ya raya cewar lallai da gani hajiya na ji da bakuwar nan. Har gurin mota ta rakosu sai da ta shiga sannan tace..

“Ikilima ki ce ina gaishe da Hajiya na gode sosai sai na zo”


“In-Sha-Allah zan fada mata na gode Hajiya Allah ya saka da alheri”


“Ba komai Wallahi a sauka lafiya”


Sai da ya tashi motar aka bude musu gate sannan ta koma ciki. Tafiya kadan sukai Ahmad ya rage gudun da yake ba tare da ya kalleta ba ya ce.

“Ke ni ban san asibitin da zan kaiki ba, duk asibitin da zamu je yanzu sai mun bata lokaci kuma company mu yau basa aiki balle na kai ki chemist din dake ce, ku ba ku da likita ne da yake duba ku ko kika saba zuwa gurinsa?”


“Akwai wani likita da ke dubani, amman yanzu na sa ya tashi asibiti yana chemist dinsa”


“Ina chemist din take?”


“Tana can gurin tudun wada locos”


“Za ki gane gurin?”


“Eh na san gurin”


Be sake ce mata komai ya canja hanyar tafiyarsa zuwa gurin da ta fada masa, ita tai ta fada masa gurin har suka iso.

“Ki shiga ki ganshi zan jiraki a mota, duk yadda akai sai ki fada min zan ji da komai”


Ba musu ta bude motar ta fita shi kuma ya ciro wayarsa ya soma latsawa tare da kwantar da kujerar motar. Kamar hadin baki sai ga sakon karta kwana ta line Hajiya ya shigo.

_Ka samu wani abu ka bata, ko ka siya mata wani abun_


“To duk dai”


Ya furta yana murmushi, kamar wanda aka cewa dago, yana dago kansa yana hago Halima ta fito daga chemist din rike da leda baka. Bude motar yai ya fito, sai ya fito sai ya fara tambayar kansa me zai ce mata sorry? No ai ya girmi wannan yana jin idan yace mata haka ya kayardar girmansa. Amman ai ya kamata ya bata hakuri ko dan Namra, kuma tabbasa ya san be kyauta mata ba. zagaya yai ta inda take tafiyar dayan hannunsa a aljihu dayan kuma rike da waya ya sunkuyar da kansa kamar da gaske hankalinsa yana kan wayar ne.

“Ya akai lafiya? ”


Ta tambaya ganin kamar zai tare mata hanya. Dagowa yai ya kalleta sai kuma yaji nauyi bude baki yai mata magana.

“Ko nan din ma hanyarta ne? Ko kuma tsabar rainon wayo ne kawai da wulakanci irin na ka, ko na maka kama da yar tasha ne, domin yanzu na fahimci babu komai a tare da kai sai wulakanci kawai, a duk lokacin da na hadu da kai sai ka wulankanta ni ko kasa a wulakanta ni, kai na fahimci sam ba mutumen kirki ba ne, sai wani jijji da kai, kana jin kai wani ne kuma kai ba kowan kowa ba, abun kai min dazun na kyale ka ne kawai saboda ina ganin kamar ni ce bana da gaskiya but then i realized na fi ka gaskiya, kai sam baka da kirki sai wani son nuna isa kamar mai garin Gusau, to bari na fada maka karka sake cewa zaka min wani rainon wayo Wallahi zan mugun wulakantaka, dan na gane ku mazan nan ba ku da mutumci, by the way ina da miji ina da aure ina da yaya karka sake ka ce zaka min magana Mtscheeeessss.....”


tun da ta fara maganar yake kallonta har ta gama taja masa tsaki ta kara gaba ta bar shi a gurin da mamaki.

“I just....”


Ya fada yana daga hannunsa tare da bin bayanta da kallo, sai kuma ya ksa cewa komai ya jimke hannun.

“Am... Baya nan wai be shigo ba yau”


Ikilima ta fada shi kam har ya manta tare da wata suka zo, sai a lokacin ya soma lura da ba su kadai ba ne a gurin. Kasa kasa yake satar kallon mutane be taba jin tozarci irin wannan ba. Matsawa yai kusa da Ikilima.

“Mutane suna ganinmu lokacin da take min fada?”


“Yes da karfi fa take yi dole kowa ya kalleku ai”


Wani abu na ji kamar ya netse a kasa, saboda ya san people would think ko ya mata wani maganar banza ne. And she's right be kamata yai magana da matar aure ba, dan idan shi ne wani nai magana da matarsa zai iya masa komai ma, but shi ya manta da maganar aurenta ma.

Oh does she think sonta yake yi? Ko kuma ta maida shi wani banza ne take fada masa haka, har ya shiga motar be daina sake sake ba.


“She got lucky bana fada da mata, amman wallahi da namiji ne yai min haka sai an dauki gawarsa a nan i hate nonsense”


Ya fada yana fisgar motar kamar zai tashi sama, after few minutes ya bugu sitiyarin motar da karfi.

“Matar nan ba tai ba, i hate her so much, da ganinta mahaukaciya ce”


Ikilima dai bata ce masa komai ba bayan kallonsa da tai, tsoro dai ya gama kamata dan ta lura ransa ya bace sosai.

“Ai duk laifinki ne da kika kawo ni gurin nan, da ta isa tai min kallon banza ma, amman ji irin maganar da ta fada min son ranta, sai yanzu ai na gane bakar magana ta fada min”


Nan da nan jikin Ikilima ya fara rawa domin ta lura har fuskarsa ta canja sa gumi yake kamar marar gaskiya duk kuwa da irin ac da ke cikin motar.

“Har da wani wai kana jin kai wani ne, ai ni wani din ne ke ba kowa ba.... Mtchhhh”


Yaja tsaki yana jin kamar a gabanta ne ya rama, domin a duniyar nan yafi tsanar tsaki fiye da komai, da ka yi masa tsaki ko ka tofar masa da yawu kara ka mare shi ko ka zage shi.....Na isa gida cikin bacin rai, ban taba jin na tsane wata halitta kamar yadda na tsani wannan mutumen ba, a yadda na fahimci rayuwata ina ta faduwa da mazaje marasa mutunci, maso sun su taka ni yadda ransu yake so, wanda ni kuma nake ganin ba zan dauki hakan a yanzu ba, na gama indai kuka ne akan wani namiji ko shiga damuwa akan wani namijin ba zan sake bari wani ya saka ni damuwa ba.

I can live without aure indai har zan iya tsare kaina da mutumcin na tarbiyantar da yayana, zan iya shiga aljanna, haka zuciyata ke raya min i feel like idan har Abdulhamid ya sake ni ba zan sake wani auren ba, zan cigaba da aikina ina kula da yayana, zan nemi ya sake ni bana bukatar sake zama da shi ji nai na tsani duk wani namiji a duniyar har na rika jin na matsu ya dawo gidan, kamar ance min da ya dawo zai rubuta takardarta ya ba ni.

  Maganin da na siyo dan na sha na samu bachi ne ammn sai bachin rai ya hana ni sha. Wani irin kuzari da karfin hali nake jin yana ratsa ni, i feel like ko da duniyar nan za su taru su tsane ni i can live, even for the sake of my children right? Yes this is right time da zan nunawa duniya wacece ni, wannan lokacin ne ya kamata na amsa suna, i don't know what the future bring ban ce ba zan sake facing wani challenge ba, but zan iya jurewa zan iya daurewa daga lokacin na fara rayawa kaina cewar gobena mai kyau ce. Na yi kuka a lokacin da na ke fuskantar wulakanci a gidan Aminu, na yi kuka a lokacin da akai ma Namra fyade, na yi kuka a lokacin da Aminu ya sake ni, na yi kuka a lokacin da akai min fyade, amman hakan yana nufi sai na zauna nai ta kuka akan komai akai min na bar damuwa a raina? No be kamata na karaya ba, be kamata na lauyewa kaina hakkina dan ina mace ba! I have to say it out loud, i have to fight for my right.+

Kamin dare yai Abdulhamid ya shigo duk na matsu sosai, saboda irin abunda na kudirewa zuciyata, ban girka komai ba har dare, can bayan sallah isha'i sai gashi ya shigo gida kamar yadda ya saba, da ada ne ko be yi sallama ba ya shigo zan masa sannu da zuwa amman a yau sai na ji ba zan iya yi masa hakan ba. Ga duka alamu yau da yunwa ya dawo, domin yana dawowa ko dankinsa be shiga ba ya nufi dinning rike da wasu takardu a hannunsa. Ganin babu abincin a dinning din yasa ya juyo ya kalleni.

“Ina abinci?”


“Ban girka ba”


Daga inda nake zaune saman kujerana bashi amsa kai tsaye. Be sake cewa komai ba ya tashi ya nufi hanyar dakinsa yana shiga na rufe masa baya, sai na same shi yana kokarin cire rigar shaddar da ke jikinsa, hango shigowata ta madubi da yai ne yasa ya tsayar da cire rigar ya juyo ya kalleni


“Kina son wani abu ne?”


“Ina son sanin result din gwajin da nai nake son sani”

Juyowa yai da kyau yana kallona for like ten seconds sai kuma ha dauke idonsa daga kallon da yake min ya kalli wani gurin dabam.


“Positive....”


“Al-hamdulillah.... Abu na biyu kuma ina son ka san cewar komai yana da lokaci kuma yana da iyaka, a lokacin da na aureka babu wanda ya cilasta ni ra'ayin kaina ne, and now mun gaji we need some space”


Sake kallona yai a karo na biyu kamar wanda be fahimci yarena ba, wata kila kuma yana mamakin furucina ne.

“Saki na ke bukata...!”


I say it..


“Are you sure? Ba ki bukatar sake shawara ko tunani”


Shine abunda ya fito daga bakinsa, sai kuma ya matsa kusa da ni ya kai hannunsa biyu zai dafa kafadata, ni kuma nai saurin matsawa.

“Bana bukatar ko daya”


Sai da ya hade yawun bakinsa sannan ya furta.

“Shikenan zan ga abunda zan iya yi akai”


Yana fadar hakan ya juya ya cigaba da cire rigarsa ni kuma na fice na bar masa dakin. Ko kadan ban ji kuka a tare da ni ba kamar yadda na saba yin kukan a duk lokacin da wani abun bacin rai ya same ni, but i feel bad ina jin na yi abunda be dace ba, miyasa ba zan jira har zuwa lokacin da shi din zai bukaci sakina ba? Why? Bana da wata hanyar ne sai wannan idan har zan jira to zan cigaba da kashe kaina ne da rai na. Can bayan na yi sallah isha'i ina kokarin kwanciya ya shigo dakina ya aje min takeway ya fice.


STORY CONTINUES BELOW

AHMAD POV.

Hajiya na kallonsa ta san danta yana cikin bacin rai, sai dai ta yi shiru ne saboda ta saba masa haka a duk lokacin da yake cikin damuwa idan har taji bata ji yace mata komai ba sai ta tambaya.

“Hajiya yau ko?... No first of all ita wannan yarinyar da kika saka na kai gida wacece ita?”


“Sai ka fara fada min damuwar”


“Wallahi wata bad luck na hadu da ita yau, ban taba jin na tsani mace kamar yadda na tsani matar nan ba, i hate her... ”


“Me tai?”


Kadan ya gutsurawa Hajiya labarinta yana ta tsaki.

“Kai ma ai be kamata kai haka ba, ko dan yarta na abota da yarka, sannan matar aure ce akan me zaka tare ta a hanya da sunan ba ta hakuri? Kai yanzu yadda kake da kishin tsiyar nan wani ya isa ko kallon matar ka yai?”


Kallon Hajiya yake da mamaki he thought zata bashi gaskiya ta bawa wacan rashin gaskiya ne.

“Okay....”


Sai yai shiru, kamin ya sake tambayarta.


“Ita wannan yarinyar fa?”


“Yarinyar nan da ka gani bazawara ce”


“What....?”


Ya tambaya da mugun mamaki domin a tunaninsa budurwa ce, a yadda ya ganta yarinya karama.

“Yes ta yi aure bata dace ba mijinta har dukanta yake kuma ta hakura ta zauna har sai da yan uwanta suka kashe aure, sannan gidansu mahaifiyarta ita ce ta hudu, so ta san  halin rayuwa tun da ta taso a gidan yawa kuma duk mace da zata yi hakurin zama da miji mai duka zata iya hakurin zaman aure a ko'ina, shiyasa na ke son idan ta maka ka aureta”


“Aure yanzu Hajiya? Hajiya ba tai min ba, abu kamar ta tsinke ni bana son mace ramanmiya irin wannan, and kin san abunda ba zai taba yiyuwa ba ne na auri matar wani Allah ya sauwake, ba zan taba auren bazawara ba, ba zan iya auren matar da wani namijin ya aureta ya sake ta ba, ko kuma mijinta ya mutu har a bada, Hajiya ke ma kin san wannan”


“To wai miye a zaurawan nan ne? Haba Gwarzo, na aje wannan akidar dan Allah ni fa yan matan nan na yanzu ba yarda zan yi da su ba, kara wacce tai aure ta dandana dacin auren zata fi iya zaman aure a gidan nan”


“Ba dai bazawara ba Hajiya”


Ya sake nanatawa sannan ya tashi ya fice daga falon, part dinsa ya nufo har yanzu zuciyarsa cike da take da bacin rai abunda ya faru.

“Imagine wai ni matar nan ta tsaya ta fada wa maganar banza wai... Wani ni Ahmad hmmm”


Yayi kwafa sannan ya tura kofar falonsa ya shiga gumi na karyo masa, daman can haka yake da ransa ya bace sai ya fara gumi jikinsa yai zafi sosai kamar marar lafiya, idonsa ma a take suke canja, zuciyarsa kuma tai ta wani zillo kamar ta fito, shi kansa idan ransa ya bace baya iya controlling kansa, that's why yake taka tsantsan yana gujewa duk wani abu da zai kawo masa bacin rai.

AMINU POV.

Hajiya ba ta yarda ba har sai da ta saka aka yi mata na ta bincike, a gurin malamanta da kuma malaman kawayenta, sai dai duk inda take abu daya ake fada mata cewar arzikin danta hana tare da matar da ya rabu da ita, wasu ma har kara rura wutar abun suke ana fada mata cewar da ace be sake ta ba da yana daf da samun wani abun. Sai dai hakan be gamsar da ita ba har sai da ta sake saka kawarta Hajiya Mairo a gaba suka tafi gurin wani malamin. Ba su tsaya bin layi ba abun ka da masu kudi, sai aka bi da su ta wata hanyar suka shiga cikin dakin malamin. After sun gaisa ya dauko kasa ya fara bincike domin shi haka yake ba ya bari mutum ya fada masa dalilin zuwansa, sai dai shi ya fada maka abunda ya kawo ka. Yayi kusan minti ashirin yana duba kasar sannan ya dago ya kalli Hajiya Mairo.

STORY CONTINUES BELOW

“Waye Aminu? Gashi nan yau sun nuna min da Maganarsa kuka zo”


“Tabbas hakika maganar Aminu ta kawo mu, yaron abokiyata ne kuma aminiyata”


Ya gyada kai sannan ya kalli Hajiyar Zuwaira wato mahaifiyar Aminu ya ce.

“Sun fada min komai, dan ki na fama da gurguncewar cigaban rayuwa haka ne?”


Tai saurin gyada kai.


“Haka ne”


“To ai danki ya baro kyau tun ranar haihuwa, ga shi dauke da kwaryar alheri sai kuma ya bari ta fadi ta fashe”


Hajiya Zuwaira ta yi masa kallon rashin fahimta. Sai yai yar dariya ya gyara zamansa.

“Na san baki fahimta ba, wato tauraruwar danki sakaina'u ce, irin wannan tauraruwar bata iya haske har sai ta hadu da yar'uwarta mai iya daukar nauyinta, ma'ana mai taimaka mata ta haskaka, da danki zai hadu da taurari dubu idan be hadu da wannan tauraruwar ba gasri to abu ne mai wahala ya iya haskaka ya daukaka yadda yake so, daman ko wane dan'adam yana da tauraruwarsa to ita ta danki haka take”


“To amman Malam.... ”


Sai ya daga mata hannu.

“Wacece Halima?”


“Matar da ya saki ce ita ce uwargidansa”


“To ita ce mai wannan tauraruwar gasri, tauraruwa ce mai tsananin haske da kaifi gaske, tana haska ko wane irin tauraruwa, ban ce dan ki ba zai arziki ba, amman da ace yana tare da ita ina mai tabbatar miki ko matar gobna bata ita ta nuna miki yatsa ba”


“Amman Malam ai can baya tare da ita kuma yana al'amuranshi”


“Amman ya kai kamar haka?”


Ta girgiza kai alamar a'a.


“To kin gani, zai iya samun mai irin tauraruwar amman abun ne mai wahalar gaske”


Hajiya Mairo ta ce.

“To amman Malam dole sai Aminu ne kawai idan ya aureta zai yi arziki ko kuwa idan wani ya aureta shi ma zai iya yin arzikin?”


“Sosai kuwa ai kowa ta raba zai yi arziki, ita daman haka tauraruwar take”


Cikin damuwa Hajiya Zuwaira ta ce


“Yanzu babu yadda za'ayi tauraruwar tasa tai haske? Kenan dole sai da ita?”


“Akwai mana, amman aiki ne mai wahalar gaske kuma za a ci kudi”


“Karka damu indai har za a samu biyan bukata ba matsala”


“Za ki siye sa daya, da fararen balbelu uku sai fafaren kaji bakwai, sannan za a biya masu aiki 30k”


Murmushi Hajiya tai.

“Wannan ai ba wata matsala ba ce, sai dai ba zan iya siyowa ba zan dai bada kudin sai ka siyo komai da kanka, sai dai ba ka fada mana nawa za a biya ka”


“Ni sai bukata ta biya sannan za a biyani”


A take a gurin ya lissafa mata kusan dubu dari biyu da za a bada na kayan aiki, sai ta karbi account dinsa da zimmar idan ta koma gida zata turo masa, bata bar gurin ba sai da ta aje masa 10k na shan ruwa. Har suka dawo ita da Hajiya Mairo ba su daina mamaki da jinjina lamarin ba.

Ba ma kamar Hajiya Mairo domin ita nata tunanin dabam.

ABDALLAH POV.

Tun daga lokacin da suka samu matsala da Suwaiba ta canja masa, ya lura da hakan a dabi'unta da halayyarta da kuma yadda take mu'amalantarsa a yanzu.

  Shi kau iya kokarin da yake na ya fahimtar da ita ne ta daina ganin laifinsa ko kishin Halimatu, a iya ganinsa shi be ga dalilin wannan kishin da take ba, be san abunda zai saka ta ji haushi dan yayi ma yar'uwarsa alheri ba, tun da ita ma babu abunda ya rageta duk wani abu da take bukata yana yi ma kuma yai ma yan'uwanta, sai dai duk bata ga na kowa ba sai na Halimatu. Duk yadda take kokarin avoiding dinsa shi kuma kara shige mata yake yana nuna kamar wani abu na bacin rai be taba shiga tsakaninsu, daman can haka yake idan yai fada da ita kokarin mantawa yake saboda kullum auna tunaninta yake yana ganin be kai na shi ba, a ganinsa mace mai rauni ce kuma ba komai suke iya tsayawa su yi tunani ba, duk yadda abu ya zo musu haka suke karbarsa shiyasa shaidan yake yin galaba akansu. Idan har ya ce zai rike ta a ransa zata iya shiga matsala, matukar ya rike bacin ran mutun a zuciyarsa sai wani abun ya faru da mutun domin yana da kofi, idan har ka bata masa rai za ka ga daidai ba, shi kansa har mamakin kansa yake wani lokacin abu yake kamar wani maye.


STORY CONTINUES BELOW

sai da yai shirin office saf sannan ya nufi dakin matarsa yana kamshi turare mai dadi. Yana shigowa ta wani dauke kai be damu ba ya karasa kusa da ita ya kama hannunta ya sumbata.

“Zan tafi office sai na dawo”


Bata ce masa koma ba, shi ma kuma be jira ya ji wani abu daga gurinta ba, daman be yi tsammanin ta fada masa wani abun ba ko da Allah ya tsare ne ba tun da fushi take da shi, ba kamar da ba da har bakin mota take rakoshi. Daga gidanshi gidan Hajiya ya nufa as usual daman sai ya biya ya gaisheta yake wucewa office, ko a dawowa ma idam time be kure masa ba sai yayi mata sallama yake dawowa gida. Ya dauki Hajiya kamar wata abokiyasa yana jindadin fira da ita sosai duk wano sirri na shi ko shawara ita ce, kamar yadda ita ma ta fi shakuwa da shi fiye da Abdulhamid.

  Ba kasafai Abdulhamid yake zuwa da safe gaishe da Hajiya ba, wani lokacin sai da rana ko dare, wani lokacin ma sai ya wuni be shigo ba sai dai yai mata waya. A kujerar da mahaifiyarsa take zaune ya zauna yana mika mata gaisuwa.

“Lafiya Kalau ya aka tashi ya yaran”


Ta amsa masa fuskarta da alamun magana.

“Abdulhamid”


Daman haka yake masa he can't say Abdulhamid ina kwana saboda yana jin age mate dinsa ne, tun da yake a rayuwarsa be taba bude baki yace wa Abdulhamid ina kwana ko ina wuni ba, sai dai ya kira sunansa.

“Likita ykk”


“Lafiya kalau”


Ya amsa yana kallon yanayin Hajiya da kuma shi kansa Abdulhamid din.

“Lafiya wai?”


“Lafiya kalau wai Halimatu ce tace ta gaji da zama da shi saki take so.... ”


Ji yai kamar an zuba masa ruwan sayi a kai a take tsigar jikinsa ta tashi.

“Saki?”


“Eh”


Hajiya ta amsa masa.

“Why?”


Abdulhamid ya daga kafadunsa alamar be san dalili ba.

“No dole akwai wani abu, akwa abunda kai wa yarinyar nan Abdulhamid haka nan kawai Halimatu ba zata ce ka sake ta ba, i know who's her”


Hajiya ta tabe baki tana fadin.

“Ni nace dai ko ta gaji da zama da kai haka nan ne ba”


“No bana tunanin haka duk dai na san matsalar ce tai haifar da komai, amman wata kila tana jin kunyar kan ta ne akan abunda ya faru”


Cewar Abdulhamid, a take Abdallah ya gyara zamansa yana girgiza masa kai.

“idan har akan matsalar ne be kamata ta saka kanta cikin damuwa ba, matar da zata bar yayanta ta bar aikinta ta yarda ta aureka bayan kuma ta san irin lalurar da kake tare da ita, be kamata dan wani abun ya same ta ka barta ta shiga damuwa ba, and she told you ba su yi raped dinta ba, miyasa ba za ku yarda da ita ba?, Abdulhamid Halimatu kamar amanace a gurinka kuma matarka ce ka zaunar da ita ta nuna mata baka da matsala da hakan kuma ta kwantar da hankalinta, Abdulhamid yarinyar nan.... ”


Be karasa ba Abdulhamid ya tari numfashinsa.

“Halima ba yarinya ba ce, yaranta hudu ta san me take yi. She told me babu wanda yai forcing dinta ta aure ni and now she want divorce”


“Ai sakin ma shi ya fi alheri”


Abdallah ya juyo ya kalleta cike da damuwa.

“No Hajiya ke kika haifar da wannan matsalar kika saka Abdulhamid ya rika ji a ransa kamar an yi raped matarsa, and now kina kokarin ki karfafa nasa guiwa ya sake ta haba Hajiya be.... ”


STORY CONTINUES BELOW

“No tun kamin ayi wannan abun i suspect something, and yes na kai ta an mata hiv test and the result din positive, maybe dai tana jin kunyar kanta ne.... ”


Da mugun mamaki Abdallah yake kallon dan'uwansa.

“Don't tell me you don't trust your wife...? Why all the insult bro? Taya za kai ta ayi mata hiv test? Kasan halin da za ta shiga?”


“Ba zaka fahimta ba ne Abdallah, ni na san abunda yake nan, and matar nan yanzu har shaye-shaye take fa, na ga kwalaben maye a dakinta, and wani lokacin zan tarar tana ta bachi kamar wacce ta mutu, idan ta farka idonta har canjawa yake”


Kamar an saka scissors an yanke jiyojin jikinsa haka ya ji, be taba jin tausayinta irin yanzu ba, yana jin da ace shi ne Halimatu ta fada masa cewar ba'ayi mata fyade ba babu abunda zai hana shi yarda da ita, even if an yi mata fyaden ma zai iya zama da ita a haka.

“Akwai abunda yake faruwa a tsakaninku Abdulhamid, wanda ba ka son mu ji kuma ba lallai ne sai mun ji ba, amman ka dubi girman Allah ka ji tausayin yarinyar nan, ace har ta fara shaye-shaye amman kake maganar sakinta? Abunda ya same ta kaddara ne miyasa ba zaka nuna mata hakan ba? Rashin lafiyarka ma ka nuna mata zaka nemo magani, i promise you zaka samu sauki soon...”


shiru Abdulhamid yai for a while kamin ya sake bude bakinsa ya ce.


“I think rabuwar shi ya fi alheri a tsakaninmu dukan mu za mu samu kwanciyar hankali”


Wani irin kallon Abdallah yai masa.

“Ta auri mutunen da be cancanta ya zama mijinta ba, Abdulhamid ban yi tsammani haka daga gareka ba... ”


“Ba ka fahimta ba ne Abdallah tun kamin wannan abun ya faru Halima tai ciki, kuma ta zubar da shi ba tare da na sani ba....”


“Ciki? pregnant.... Ciki?”


Ya maimaita har sau uku, sai kuma yai saurin mikewa tsaye ya nufi window falon ya tsaya a gurin yana shafa kansa, gaba daya zuciyarsa ta gama narkewa da tausayin Halimatu yanzu kam. A hankali ya busar da iskar bakinsa yana sauraren yadda Abdulhamid yake labarta abunda ta fada masa da kuma kin yardar da yai da ita. Lumshe ido yai ya bude, so yake yacewa dan'uwansa Halimatu tana da gaskiya amman taya? Shi kansa ba shi da hujja, iyakar abunda yai imani da shi, shi kam ya yarda da Halimatu ko da bata kafa hujja da komai ba, and ya san idan har Halimatu za ta aikata zina to zata aikata ne tun a lokacin da take gidan Aminu. Juyowa yai ya kalli dan'uwansa.

“Amman ka yi magana da ita? Abdulhamid ko da da gaske Halima ta aikata haka ta cancanci ka zauna da ita, macen da zata bar yayanta, ya bar duk wani abu mai muhimmancin a gareta ta yarda ta aureka da matsalarka ta gama maka komai, kama yai ka tambaye ta ka bincike ta wata kila ta iya gane wanda yai mata wannan abun sai a bincike shi amman duka ba ka yi wannan ba sai kawai ka juya mata baya? And now kana maganar ka sake ta? Ka yi convince dinta ka nuna mata sakin ba mafita ba ne a gareta, ta shiga damuwa da yawa, Abdulhamid, Halima deserve a happiness”


“Ya isa haka Husaini wuce ka je gurin aikinka”


Hajiya ta fada a tsawace tana daga masa hannu. Ya gyada mata kai yana hade wani irin abu daya tsaya masa a kahon zuciya. Ko minti biyu be kara cikin falon ba ya fito ya shiga motarsa, Halimatun dai ce ta tsaya masa a rai ya kasa rika ko da sitiyarin motar har na tsawon lokaci ba yi wata halitta da yake tausayi a duniya kamar Halimatu ba. How he wish shi ne a step din Abdulhamid da ya nuna mata soyayya da kauna ya rumgumeta har sai ta manta da duk wani bacin rai a duniyar nan. Ya dade a gurin kamin ya tashi motarsa ya danna horn a bude nasa gate ya fita da motar, titi ya hau yana tunanin inda zai je direct asibiti gurin aikinsa ko kuma gurin Halimatu? He need to talk to her, sai kuma wata zuciyar ta ce nasa no, kuskure ne yai magana da ita a yanzu, ba zata fahimta ba, son da yake mata ma yana jin a ransa cewar ya aikata baban zunubi kuma yana jin kamar ya ci amanar dan'uwa, wannan kadai ya saka shi a damuwa. And maybe idan yai magana da ita ta fahimta ta daina zancen sakin, he can talk to her as her brother wata kila ta fahimta.

STORY CONTINUES BELOW

Haka yake ta sake sake a ransa, daga karshe ya yanke shawarar kiranta a waya, sai dai kuma idan ya kirata a waya dan'uwansa ya ji he may think something else... But yes he can talk to her as Abdulhamid brother as his best friend, as her husband best friend. Har cikin ransa baya son ta rabu da Abdulhamid saboda ba mafita ba ne a gareta, and idan ta rabu da shi yanzu zuciyarsa kan iya bijiro masa abunda ba mai yiyuwa ba ne akanta. Wayarsa ya ciro ya aikawa Abdulhamid sms.

“Can i talk to her? As your brother”


Immediately yai masa reply.

“Yes i trust you”


The truth word break his heart sai yaji ina ma be tambaya ba. But yes mace ta bukaci saki a gurin miji ai ya kamata yan'uwansa su ji daga gareta su ji dalilinta. Sai da ya saita natsuwarsa sannan ya dauki hanyar gidan Abdulhamid yana ta tunanin a irin halin da zai samu Halimatu. Zuciyarsa sai raya masa take kar yaje, ya faka motarsa a bakin gate sannan ya fito ya tura kofar gate din ya shiga cikin gidan.    Ya dade tsaye a kofar falon sannan yai knocked. For like five minutes ta bude kofar suna hada ido, idonsa ya cika da kwalla wani irin tausayinta yake ji yake kamar ya dauke ta ya hade ta manta da komai.

“Abdulhamid ba ya nan”


“Gurinki na zo”


Sai ta saki kofar falon shi kuma ya turo ya shigo cikin falon ya zauna a kujerar da ke kusa da kofar falon. Daga inda take tsaye fuska babu annuri ta ce


“Ina jinka”


Sai ya nuna mata kujera alamar ta zauna, ba musu ta zauna a kujerar da ke nesa da shi sosai, after ta zauna ya soma magana a natse.

“zan yi magana da ke as Abdulhamid brother, Abdulhamid ya zo mana da magana marar dadin ji daga gareki, b zan iya nanata maganar ba amman ina fatar ba haka zan ji daga bakinki ba.... ”


Bata ko jira ya karasa ba ta dora da nata.

“Haka yake ko ba zancen saki ba?”


“Amman Halimatu wannan ba mafita ba ce a gareki and... ”


“And what? Idan ya sake ni mutuwa zan yi?”


Kasa ce masa komai yai, gaba daya ta canja a tsaye take kamar ba ita ba.

“Be kamata ki canja rayuwarki ba akan abunda ya same ki, kowa ya san kaddara ce, ki tattara komai ki aje a gafe ki barwa Allah labarinsa, dabi'un da kika dauka yanzu ba za su kai ki ko'ina ba and mijinki yana son ki yana cikin damuwar abunda ya same ki....”


“Babu abunda zaka fada min da zai saka na canja kudirina Abdallah, bana son jin wata magana daga gareka ko wace iri ce, let it go can't hold me back anymore, duk abunda ya faru ai kai ka janyo you try to act innocent, da ba ka aikata min abunda ka aikata ba, da yanzu komai be faru ba, na rasa gane wane irin mutum ne kai Abdallah na kwarai mai son taimakona da yarana, ko kuma mai son ruguza rayuwata?”


Still now be iya ce mata komai ba, gaba daya jikinsa ya gama sanyi, be fahimci inda zancen ta ya dosa ba. Ita kuma bata fasa fayyace masa komai ba.

“Mutumen da yai min fyade be rage komai a zoben hannunka ba, na danna na cige ina ta boye abu saboda na samu natsuwa a zaman aurena, amman Abdulhamid ya masa yarda da ni, ba zubar da cikin nai ba zubewa yai saboda tashin hankalin batan Namra, amman yana ganin kamar na aikata alfasha da wani ne na zubar da cikin, shin idan na fada masa dan'uwansa ne ya aikata ya kake tunanin zai ji?”


Rumtse idonsa yai da mugun karfi ya fisgi kansa kamar ba shi ba. Be taba jin magana daci ba irin wannan, ba a taba munana masa zato ba irin wannan, amman a maimakon ya ga laifinta sai tausayinta ya kara rufe shi, tausayin da be san daga ina yake ba, gani yake yanzu kanta a chushe yake, bata fahimtar komai da kyau kuma tana da raunin tunani.

A lokacin da ya bude ido sai ya ji kamar ba a duniyar nan yake ba, maganganunta na ta maimaita kansu a cikin kunnuwansa. Zoben hannunsa ya kurawa ido, kokarin tuna inda ya tsiya zoben yake a office right! Wani mai kawo musu kaya ya kawo rings even though shi ba masoyin zobe ba ne ya tsiya daya ya saka saboda zoben ya masa kyau. Yes he remembers at first ma mai alphabet H ya dauka sai kuma ya ga rashin dacewar hakan then ya canja to A mai sunansa. Magana ya fara yi tana rabe masa hawaye na sauko masa.

“Na san kin san ina son ki... Na fada miki... Kuma... Kin san haka.... Amman soyayyarki.... Bata taba saka min sha'awarki ba.... Ban tana jin sha'awar na rika hannunki ba daidai da minti daya Halimatu..... Indai har dan jikinki ne.... Zan bukace ko a lokacin da kike gidan.... Aminu.... Ko a lokacin da kike zawarci.... Ba yanzu da kika auren dan'uwana ba.... Wallahi ban tana aikata zina ba.... Zuciyata bata taba raya min akanki ba..... Kullum burina da fata na aurenki ne.... Saboda ki huta ki samu kwanciyar hankali.... Tausayi kike ba ni Halimatu... Yana daya daga cikin dalilin da ya saka nake daukar dawainiyar yaranki..... Da ke kanki... Na ke damuwa da damuwarki..... Yes i love you.... I do love you..... I love more i did before... Amman yanzu duk wannan ya wuce saboda kin riga kin auri dan'uwana twins brother na..... And yes na so na aure ki saboda na samu da namiji ko ba komai hakan zai kara min kaunarki.... Amman yanzu duk wannan ya wuce.... ”


Lumshe ido yai ya bude har lokacin yana hawaye.

“Idan har zan miki fyade, ba zan bar wata alama da za a gane ni ba, bazan shigavgidan makotanku har a kashe wani da ni ba saboda kawai na biya bukatar da zan tashi a gaban Allah ina tsoron amsata ba, a lokacin da akai wa Namra fyade ji nai kamar yar cikina aka taba, da acce Mama bata saka baki ta hana abun ba, da sai inda karfin ya kare, then mi zai saka ke nai miki? Robe kadai ya isa ya bada hujja Halimatu? Ni kadai ne sunana yake tashi da A ko kuwa ni na fi kowa arzikin da za a kero min irin wannan zoben? Ni da na ke fargabar ki shiga tashin hankali kuma ni zan saka ki ciki? Siffar mutumen da muryarsa irin tawa ce? Komai na sa irin nawa ne? Miyasa za ki nunana min zato? Saboda na ce ina son ki....! Wallahi ko ke kadai kika rage a cikin mata Halimatu na zan bi dare nai ma matar dan'uwana fyade ba.... ”


Mikewa yai tsaye ya cire zoben hannunsa ya nufi center table din da ke tsakiyar falon ya dora zoben sannan ya tada kai ya kalli Halimatu.


“Karki kashe aurenki saboda ni, karki fadawa Abdulhamid wannan maganar, domin na san dan'uwana ya fi so na akanki, kuma karki fadawa Hajiya wannan maganar, itama na san ta fi so na akanki, ki yi tunani Halimatu karki jefa kanki cikin matsala lastly ki daina shaye-shayen da kike for the sake of your children...”


Yana kaiwa nan ya juya ya fice yana share hawayensa da handkerchief. Amman hawaye suka ki tsaya masa har ya shiga motarsa, key yai mata sai da yai nisa da unguwar sannan ya faka motarsa gefe ya jingina kansa jikin kujerar motar ya Lumashe ido.


“Allah kai kadai kasan dalilin da ya sa saka min kaunar Halimatu, Wallahi na kasa ganin laifinta.....”8


A fili ya furta zuciyarsa cike da tausayinsa, gani yake kanta ba daidai yake ba damuwar da take ciki bata iya barinta tai tunani da kyau, tabbas ta jefeshi da mummunan zato kuma ya ji zafin hakan yai bakinciki sai dai ya kasa ganin laifinta uzuri yake ta mata!


5K WORDS 😲ABDALLAH POV.

Be iya zuwa gurin aikin ba kamar yadda ya tsara zuwa tun farko, gaba daya ji yake kamar ba shi da lafiya, ji yai baya bukatar ko'ina sai gidansa. A take ya dauki hanyar gidan, a ka'idan zai shiga gidansa yana shiga da sallama kuma fuska a sake ko da kau yana cikin damuwa yana kokarin yin hakan saboda yaransa, duk damuwarsa ko wata matsala nasa baya son tana shafar iyalinsa musamman yaransa Abdallah mutum ne mai tsananin son yara ko da ba na shi ba balle kuma na shi, wannan yasa duk irin matsalar da suka samu da Suwaiba matarsa baya taba bari yaransa su gane.

  Babu kowa falon at that time, daman yara suna scul Suwaiba kuma tana dakinta, kai tsaye dakinsa ya wuce yana jin wani irin zazzabi na rufe shi, kwantawa yai saman gadonsa yai ruf da ciki ya rumtse idonsa sosai. Yana jin wayarsa na ringing ya ki ya duba mai kira ma balle yai deciding zai dauko ko a'a, ya kusan awa daya a haka sannan ya bude idonsa ya tashi zaune yana duba wayar, Abdulhamid ne ke kiransa. Sai da ya busar da iskar bakinsa sannan ya danna picking.+

“Abdallah”


“Na'am”


Ya amsa yana gyaran muryar.

“Ya kuka yi da ita?”


Shiru yai for few seconds sannan ya ce.

“Tace ta fi bukatar sakin ko dan cutar da take dauke da ita”


Daga dayan bangaren Abdulhamid yai shiru kamar mai nazari har Abdallah ya dauka ko ya kashe wayar sannan yai magana.

“Idan kuma na ce bata dauke da cutar fa? Zata zauna?”


“Amman miye gaskiyar lamarin ne?”


“Maganar gaskiya bata dauke da cutar”


“Then miyasa ka ce tana dauke da ita?”


“Ina son na gane wani abu ne, kuma ina tunanin idan na ce mata haka zan ji wani abu daga gareta, amman na ga hankalinta sam be tashi ba, even i thought zata yarda ta zauna saboda tunanin idan ta fita za a kyamace ta, but then i realized idan har na cigaba da zama da ita, zan iya cutar da ita kuma ni ma zan cutu, domin har ga Allah zuciyata ta kasa natsuwa da ita, ta wani bangaren ina ganin kamar rabuwar shi ya fi alheri”


“Amman Abdulhamid miyasa za ka ce tana dauke da cutar, na kasa yarda da kai, wani lokacin sai kai ta abu kamar marar tunani”


“Idan taje wani gurin ta yi gwajin ai za a tabbatar mata idan tana dauke da cutar ko akasin haka”


“Ina fatar rabuwar ta zame muku alheri kai da ita”


Shine kawai abunda Abdallah ya fada ya kashe wayar ya kaita a goshinsa, babu abunda ke ransa sai irin halin da Halimatu zata shiga.

“What if Abdulhamid yana da lafiya? Da duk wannan zai faru? Da ko kin yi cikin ba zai gane cewar ba na shi ba ne, ni na jefaki a wannan matsalar, saboda ni ne silar wannan matsalar....”


Ya furta yana kara rumtse idonsa, kokarin da yake na kawarda damuwar abunda Halimatu ta fada masa ne, gudun kar wani abun ya same ta, and the most of all zai wanke Abdulhamid daga rikon da yai masa a zuciyarsa. Bude idonsa ya sake yi ya lalubo number Halimatu ya aika mata sako.

“Na zurfafa a son ki na sani, na nuna miki son kaina na sani, na kaurara da yawa na sani, kina da gaskiyar ki yi yarda da duk wani abu da zuciyarki ta fada miki, amman ina dada jadadda miki karki kuskura fadawa Abdulhamid wannan maganar”


After the sms ya kwanta saman gadon yana jin kamar ba shi da wani kuzari. Abubuwan da ta fada masa is painful suna ta kona masa zuciya, after like two hours ya kira wani a asibitin ya fada masa cewar ba zai sami damar zuwa ba a yau. Tun da ya kwanta babu fuskar da yake ganin sai ta Halimatu old memories yake tunawa daga lokacin da take yan mata ba tai aure ba, a lokacin duk be fara son ta ba har tai aure shi kuma ya bar kasar duk be fara son ta har ya dawo yai aure ya haifi yarsa ta fari be fara sonta ba, sai da suka hadu a family meeting a lokacin tana da aurenta har ta haifi yara uku, tun daga ranar Allah ya dora masa sonta, yanayin jikinta mu'amalarta kyauta da komai nata sai ya rike burge shi, musamman da ya samu labarin waye mijinta da irin kalubalen da take fuskanta a gidan aure sai ya fara tausayinta yana ganin kamar shi ya dace ta aura ta samu jindadi, kamar yadda yake jin cewar idan ya aureta zai iya haifar ɗa namiji tunda ita duk tana haihuwar maza da mata, and bugu da gari ga sonta da yake.

But why he fell in love with her? Sai yanzu yake ta ganin laifin kansa, he know maybe da be so duniyarta da tunaninta be bata haka ba ta bata munana masa zato ba. Har scul bus ta kawo yaransa daga makaranta yana a dakinsa kwance, yana jin hayaniyarsu amman damuwar da ke ransa ta hana shi tashi ko da zaune balle har ya fito falo.

  After yayi sallah azahar a cikin dakin Suwaiba ta shigo ta zauna kusa da sallayar tana karantar damuwar mijinta.


STORY CONTINUES BELOW

“Lafiya dai? Na ji ka dawo tun dazun kuma baka fito ba”


Kallonta yai yana kirkirar murmushin da yaki ya fito a kumatunsa balle har ya tsaga bakinsa, a kokarinsa na boye mata damuwarsa ya kirkiro mata wasa.

“Ba fushi kike da ni ba”


“Wannan dabam, kana cikin damuwa ga idonka nan ya nuna”


“Bana jindadi ne, dazun da na fita sai da nai amai shiyasa na dawo”


“Ka sha magani?”


Hannunta ya kama.


“Ina likita har ake tambayar na sha magani?”


“Na kawo maka abinci?”


“No ba yanzu ba”


Kamin ta sake cewa wani abun su Inteesar suka shigo dakin ita da kanwat suka fado jikinsa. Sai Suwaiba ta rika kokarin daga su.

“Kyale su tafiyarki”


Ya fada yana shafa kansu, tashi tai ta fice tana musu fada wai kar su dami Daddynsu ba shi da lafiya duk kuwa rashin gamsuwar da tai na cewa ba shi da lafiya din da gaske.

   Sama sama ya tambaye scul sannan ya ciro wayarsa ya cire mata key ya mika musu su game so that su kyale shi ya samu natsuwa, a gurin ya kwanta su kuma suka tashi suka bar dakin suna murya Daddy ya ba su iPhone dinsa su yi game.

  Har yanzu jikinsa ya kasa sakewa yana ta jin kansa kamar marar lafiya irin wanda ya dade kwance yana jinya, tsakanin fitar su Inteesar da kwantarwarsa be wuce 40 minutes ba Suwaiba shigo dakin rike da wayarsa fuskarta a jagule.

“Abdallah miye haka?”


Saurin bude ido yai jin muryarta kamar mai shirin yin kuka, sakon da ya aikawa Halimatu ne dazun take nuna masa, tuni kwalla sun cika idonta. Tashi yai zaune yana kallon fuskarta, gaba daya sai abun ya kara jagule masa shi ya manta ba be goge ba, and ko da ma be goge ba why zata karbi wayarsa a hannun yara ta masa bincike?

“A lokacin da nai zargi cewa kai ban yi daidai ba, yanzu miye haka? Yar'uwarka kuma matar dan'uwanka Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un....”


Hannu ya kai ya rikota ya zaunar da ita bakin gadon sannan shi ma ya tashi daga kan tile din da yake ya zauna bakin gado ya rike hannayenta.

“Babu alakar komai a tsakaninmu”


“To wannan wane irin sako ne? Miye ma'anarsa? Na kasa gane wace irin alaka ce a tsakaninku? Idan nai zargi ka ce min ba haka ba, Abdallah da me na rage ka?”


“Ba ki rage ni da komai ba, idan ina wani abun da be kamata ba zaki fi kowa sani”


Fashewa tai da kuka ta runtse ido, kamar yadda shi ma ya rufe idon ya hada kansa da nata yana hawayen da be yi zaton za su sake zubo masa ba.

“Ashe ba za ki iya shaidun mijinki ba? Ba kisan abunda mijinki zai iya yi da wanda ba zai iya ba? Wani ba zai zo yace miki ga mijinki can a dakin wata karuwa ba ki karyata shi? Har yanzu ba ki san waye Abdallah ba Suwaiba?”


Bude idonsa yai yana kallon idanuwanta da ke rufe suna zubar da hawaye still goshinsa da nata suna hade guri daya.

“Me kika son nai miki ki yarda da ni? Rantsuwa kike son nai miki? Ko qur'ane kike son na dafa miki? Ko kuma Halimatun kike son na dauko miki da kanta ta fada miki?”


Kai ta girgiza ta jimke hannunsa sosai a cikin nata alamar ta yarda da shi, sai dai har yanzu kukan take mai sauti. Kansa ya daga ya janta jikinsa ya rumgume yana hade yawun bakinsa tare da saka dayan hannunsa ya share hawayensa.

“Wani lokacin wani abun yana faruwa da mu saboda yana daga cikin kaddararmu, wani na dan lokaci ne kawai na jarabawa, wani kuma har a abada zai zauna da kai”


STORY CONTINUES BELOW

A fili yai furucin yana sauke ajiyar zuciya, kamin ya koma zancen zuci.

‘Da ace na san zan hadu da ke Halima da ban dawo kasar nan ba, ko da na dawo da ban zauna garin nan, hakika duk wanda aka jarrabe shi da son wani an fi kowa yi masa babbar jarabawa, Allah kadai yasan abunda yake nufi da ni’


Ya kara rumgume matarsa yai ya kai bakinsa saitin kunnenta.


“Babu komai a zuciyata yanzu sai tausayin Halimatu, ki kwantar da hankalinki ki daina damuwar kanki da matsalar nan dan Allah”


“Dama kaunarta kake yi Abdallah wata kila da zan fi samu natsuwa fiye da ka fada min cewar tausayinta kake, tausayi ya fi so tsatsa a zuciya Abdallah”


“Ki daina saka kanki a cikin damuwa, Halimatu ta riga ta auri dan'uwana, ba zan taba iya aurenta ba a yanzu ko da ko Abdulhamid ya rabu da ita, duk wani abun da zan mata ko nai ma yayanta zan yi mata ne kawai dan kyautata da kuma tausayinta da na ke, Halimatu yar'uwata ce ko ba komai dole na taimaka mata ballantana akwai yan'uwanta, kuma duka familynsu babu wani mai karfi da Halimatu zata iya jingina da shi yai mata irin abunda na ke mata”


Ta gamsu da bayanansa abunda bata gamsu da shi ba, shine zancen cewa ba zai auri Halimatu ba ko da Abdulhamid ya sake ta, ko da dai hausawa suna cewa ana barin halak dan kunya, amman a yadda Abdallah yake damuwa da lamarin Halimatu abu yana daure mata kai, ta sani abun kunya a gurinsa ace dan'uwansa ya saki mata shi ya aura, dan uwan ma twins brother dinsa, amman ta kasa yarda tausayin Halimatu kawai yake ta san ba tausayi ne kawa ba har da so, wannan abun ya tsaya mata a zuciya, abun da ciwo ace kana tare da mijinka zuciyarsa tana begen wata.

HALIMATU POV.

I thought ba zan sake zubar da kwalla ba, i promise my own self ba zan sake shiga damuwar wani namiji ba, but i feel like ban kyautawa Abdallah ba, i feel like na yi kuskure na fada masa haka, miyasa ba zan bari har sai asiri ya tonu ba? Amman da na bar maganar a cikina da har yanzu zargin Abdallah yana a cikinta. And now da ba Abdallah ba ne wanene? Babu wanda zan iya zargi a iya hangena da tunanina, wata kila yan fashin ne da gaske! Amman miyasa ya shafa cikina har ya tambaya da gaske ina dauke da ciki, miyasa yace wannan karon ba gurin mijina suka zo ba? A gaban madubi nake zaune ina kallon kaina hawaye na sauko min, nazarina ya ki ya kare, tunanina ya ki ya gano komai. Ban matsa daga inda na ke ba har sai da na ji motsin motar Abdulhamid.

Bandaki na shiga na wanke fuskata na fito bakin gado na zauna.

Sai ga shi ya shigo ya zauna kusa da ni, ban kalleshi ba amman jikina ya ba ni cewar kallona yake.

“Abdallah ya fada min kin ce kin fi son sakin, ni kuma ba zan ki yi miki abunda kike so....”


Yana fadar hakan ya saka hannunsa aljihu ya dauko takardu guda biyu ya miko min.

“Ina miki albishir din cewar ba ki dauke da cutar hiv na fada miki haka ne kawai saboda na ga reaction dinki”


Hannu na saka na karba at first na yi zaton ko takardar gwajince sai nai arba da abunda ya kusan raba zuciyata gida biyu.

_Ni Abdulhamid na saki matata Halimatu saki daya a yau_


Bayan rubutun saki sai kuma na kwanan wata a kasa, Wallahi na yi zaton kukan a lokacin amman sai na nemi shi na rasa babu ko alamunsa a tare da ni, a dayar takadar kuma cheque din kudi ne dubu dari biyar.


“Wannan na minene?”


“In case of....”


Ya amsa min muryarsa na rawa. Sai na girgiza masa kai ya dora cheque din a saman gadon.

“Bana da bukata”


Ina furta hakan na nufi wardrobe dina na bude na dauko akwaiti na fara zuba kayana, abubuwan da ya kamata ace na zuba a ciki ba su na zuba sai tarkace jikina na ta rawa kamar wata marar gaskiya. Ina kokarin rufe akwatin ya zo ya rike akwatin sai na daga kai na kalleshi, hawaye fal a fuskarsa a maimakon ni da aka saka na yi kuka ban yi ba, sai shi da yai sakin yake kuka.

STORY CONTINUES BELOW

“Zan kula da komai, idan kina bukata za ki iya yin iddarki a nan”


“Bana da bukata”


Sai ya kada min kai kamar wani yaro da mai bashi umarni, mikewa nai tsaye na dauko hijbina sai ya rike.

“Ba za ki bari sai da dare ba?”


“Gida na ke son zuwa”


Nan ma kan ya gyada min.


“Bari na kai ki, zan saka a kwashe komai na ki a kai miki”


Ya fada yana ficewa daga dakin, ni kuma na bi bayansa rike da jakar hannuna, da kuma takardar sakin, har lokacin ban ji kuka ko wani abu makamancin kukan a tare da ni ba, sai dai zuciyata ta yi wani irin nauyi kamar dutse. Ko da na fito har ya tashi motar ya bude min front seat, ni kuma na bude back seat of a shiga na zauna, sai ya fito ya rufe front seat din ya bude gate ya fita da motar sannan ya koma ya rufe ya dawo cikin motar. Sai da yai nisa da tukun ya faka motarsa gefen titi ya jinginar da kansa jikin sitiriyarin motar ya fashe da kuka kamar karamin yaro. Kamar hadin baki sai nawa idanuwan suka cika da kwalla.

“Why? Why all this?”


Ya furta cikin sautin kuka, sai ya dago kansa ya jingina da kujerar motar, ina iya jiyo lokacin da ya sauke ajiyar zuciya ya kai hannu ya share hawayensa ya cigaba da tukin, sai da muka iso kofar gidan mu sannan ya juyo ya kalleni.

“Zan iya maida auren idan kina so”


Kai kawai na iya girgiza masa alamar a'a ma bude motar na fita, sai da na taka har bakin kofar gidan na saka kafata, sai na ji babu abunda na ke bukata sai kallon Abdulhamid. Juyowa nai na kalleshi, lokacin da ya turo da motoci aka dauke ni aka kai gidansa nake tunawa yau kuma gashi ya dawo da ni da kansa, zancen mahaifiyata na bata son a fara kirga min aure ya fado min a rai, da na san zan haka GOBENA zata kasance a gidan Abdulhamid da ban aureshi ba, ban ji ina tsanarsa ba, sai dai na nemi soyayyarsa da ke zuciya na rasa, hawaye yake kamar yadda ni ma nake yi. Hannu na saka na share hawayena duk kuwa da na san fuskata ba zata iya boye kukana ba, sannan na shiga ciki gidan, iyakar kokari na yi dan na tsayar da hawayena amman abun ya faskara haka na shiga gida ina hawaye.

Inna da Mama da Baba da Hafiza duka suna tsakar gidan zaune ko wane fuskarsa dauke da far'a da alama nishadi suke. Baba na kishingide saman tabarma Inna na tsaye jikin kofar kitchen din dake tsakar gidan, Mama kuma na zauna a saman kujerar mata kusa da Baba Hafiza ce zaune a kofar dakin Mama tana shan rake, suna ganina da yanayi sai duk jikinsu yai sanyi.

Gaban Baba naje na gurfana rike da takardar a hannuna ina hawaye na kasa daga kai na kalleshi.

“Shi aure yana da rayuwa da mutuwa kamar mutum da rayuwa, idan lokacin mutuwarsa yai babu mahani, kuma abu kalilin kan iya sakawa ya afku ko ya mutu, ko da dalili ko babu, dan haka ki sawa rayuwarki sallama ki dauka cewar ajalin aurenki a gidan Abdulhamid ne yai”


Da sauri na dago na kalleshi, jin magana mai dadi da kwantar da zuciya da samar da natsuwa daga bakinsa, tun kan na furta ya fahimci cewar aurena ya mutu. A take na share hawayena ina gyada masa kai alamar na gamsu.

“Saki nawa yai miki?”


“Daya ne Baba daya yai min”


Na furta muryata na rawa, sai Mama tai karaf ta ce.

“Amman me kika masa mi ya hada ku?”


Kamin na ce komai ba Baba ya daga mata hannu.

“Ba yanzu ba, tashi ki je ciki ki huta, Allah yai miki albarka”


Ban san lokacin da murmushi ya kubuce min ba, kaunar mahaifina ta kara cika min zuciya, ya famshe ni daga tambayar da ban san mi zan fada a matsayin amsa ba.


STORY CONTINUES BELOW

“Madallah da kai Baba, ina ma ko wane uba kamar kai yake? Madallah da uba irinka, madalla daka zama jigo ga Halimatu....”


Na fada ina hawaye cike da shaukin sonsa, Hafiza ce ta taso daga bakin kofar da take zaune ta zo da gudu ta rumgume Baba tana kuka tana fadin.

“Ina kaunarka Baba Allah kara maka lafiya”


Dariya yai ya tashi tureta daga jikinsa ya tashi zaune. Ni kuma na dago na shiga dakin Mama. A dare Mama bata iya hakura ba har sai da ta ji dalilin mutuwar auren, ni kuma ban boye mata komai ba cikin har da fyade da kai min da abubuwan da suka faru, sai dai ban yarda na fada mata cewar Abdallah na ke zargi ba.

Na ga rashin jindadin mutuwar auren a fuskarta, daman wace uwa ce zata zo auren yarta ya mutu? Balle Mama da take daukar abu ta saka a rai, su Salma da Hafiza ma da suke yan mata ba su yi aure ba abun ya dame ta balle kuma ji ace aure na biyu ya mutu. Sai dai duk da hakan ta nuna min zama da Abdulhamid din ba mafita ba ne sakin ya fi tunda har yana zargina. Da yamma Su Adnan suka dawo daga islamiya, ganina suka hau murna kamar wacce suka shekara ba su gani ba, ganin na kai har bayan i'shai yasa Namra ta fara tambaya wai nan zan kwana.


“ A nan zan kwana, yanzu na dawo kenan sai illla ma shaa Allahu”


Wani irin tsalle ta daka ta dire tana murna ta kama hannuna ta rike.

“Momy da gaske?”


Na gyada mata sai ta kara rumgume ni tana ta murna.

“Yeee mun huta Momy ta dawo”


Iya murnar da yata take na ganina a kusa da ita ya isa da tabbatar da cewar yarana sun yi marmarina duk kuwa da suna zuwa su ganni ko na gansu idan bukatar hakan ta kama, sai dai ko wane d'a yana bukatar mahaifiyarsa a kusa da shi, amman ni na bar su na auri Abdulhamid, a yau ya saka min da haka! Da tunanin abun na kwana a zuciyata har safe.

   Washe gari Baba ya kira ni a dakinsa ya tambaye ni abunda ya faru, a nan na tsige masa tun daga biri har wutsiya, a ganina shi mahaifina ne be kamata na boye masa komai ba. Shi ya ba ni shawarar zuwa asibiti na sake yin gwajin hiv dan tabbatarwa. Ban yi wata wata ba na shirya na tafi gurin gwajin. Ban dawo ba sai yamma domin daga asibitin na wuce gidansu kawata Hajara, a lokacin da na labarta mata mutuwar auren sai ta fashe da kuka kamar an mata mutuwa.

“Wannan wane irin abu ne yake ta bibiyarki Halimatu? Tun farko sai da na ce ki auri Abban Ikram da yanzu duk wannan abun be faru ba kika ki”


Kai na girgiza mata.

“Wallahi sai ya faru, abunda Allah ya rubuta ya samu bawa babu mahani, na yarda da wannan”


“Allah sarki Halimatu, ga ki da tauhidi ga yarda da kaddara, Allah ya yaye miki wannan abu da yake bibiyarki”


Ta fada cikin kuka ni kuma na amsa da amin. Bayan sallah magariba na koma gida, sai na tararda tsakar gidamu cike da kayana na daki, alamar Abdulhamid ya aiko min da su kenan kamar yadda yai alkawari, mama ce take labarta min cewar a gurin kawo kayan har da mahaifiyarsa wai tai ma baba bayanin komai, wata kila shi ya turo ta dan ta wanke shi kar a ga laifinsa, wata kila kum ita ta saka kanta a tunanin ba zan fada musu gaskiyar lamarin ba, mama ta fada min har da cheque din kudi ta bawa baba ya ki ya karba, hakan kuma ba karamin dadi yai min, domin bana bukatar komai na Abdulhamid a yanzu.

Da kaina na shiga na fadawa Baba result dina cewar ban daukr da shi, yayi murna matuka dai kuma ya sake ba ni shawarar zuwa wata asibitin na sake yin gwaji. Ban watsar da shawararsa ba, na tafi kusa asibiti uku ana min gwaji result na fada cewar bana dauke da cutar, daman can ni hankali na be taba tashi akan hakan ba, ko da Abdulhamid ya fada min ban ji komai a raina kuma ban san dalilin hakan ba. A dakin da na bari cikina na koma da kaya na jera komai kamar wacan karon, a nan kam gaskiya na ji babu dadi sosai domin a takure na ke duk kuwa da kasancewar gidan ubana ne amman gidan yawa ne, ba irin gidan nan ne na masu kudi ba da za a ce kowa da dakinsa.

   Ranar da na cika kwana uku da dawowa sai ga Aminu ya zo kofar gidan ya aiko da siyayya wai a bawa yaransa kuma yana kiransu, an fada min haka yake musu a yanzu duk bayan kwana biyu ko uku, ni kau na rasa dalilinsa na yin hakan bayan dacan ba haka ya saba ba. Be san ina cikin gidan ba na sani tun da ba kowa ya san aurena ya mutu ba, na san yana cikin mutunen da za su yi murna da mutuwar aurena domin ya sha fada min a lokacin da nake gidabsa cewar babu namijin da zai iya zama da ni sai shi saboda bakin halina. Fita yai da da su yai musu waya siyayyar ya hado musu da kudi sannan ya dawo da su suka shigo gida suna ta murna.

A daren mun dade muna tattaunar maganar yadda a yanzu hankalinsa ya dawo gurin yaransa, abunda ya bawa kowa mamaki a gidan mu, Mama ta karkarta min hankali da wata maganar wai ko shine mutumen da yai min fyade.

STORY CONTINUES BELOW

“A a mama ba Aminu ba ne, na san siffar Aminu ciki da waje, yadda yake idan ya saka tufafi kanana kaya ko manya kuma yadda yake mu'amalarsa, da shi ne da tuni zan gane, ko kadan wannan mutumen be yi min yanayi da Aminu ba, idan har shine dole zan gane, kuma me ma zai saka Aminu yai min haka, mutumen da baya kaunata, wanda ya kasa hakuri har ya dawo ya saki ni ta waya ya sake ni fa, mutumen ya wulakanta ni Mama Wallahi ko sunansa bana son ji”


“Ai saboda kiyayyar da yake miki na ke zaton haka, saboda ya jefa ki a matsala ki kasa zaman auren”


“Ko ma wanene ina rokon Allah ya bayyana min shi”


Na furta ina hawaye zuciyata cike da kuna, Mama ta amsa da amin. Mun dade muna fira a dakinta, cikin har da zancen Abdallah tana cewa da ma shi na aura ita tun farko shi ta so na aura amman na ki ni dai ban ce mata komai, saboda ban taba fada mata cewar Abdallah yayi ta neman na kashe aurena na aure shi ba....

AHMAD POV.

Tarin takardu ne a gabansa da laptop yana ta aikin cika wannan cire wannan saka wannan, aikin daya taru masa ne na satin daya shige wanda be be yi ba yake yi yau ganin yau assabar ce babu karatu.

Mug din coffee na gefensa lokaci zuwa lokaci ya ke dauka ya sha. Be tashi daga gurin ba sai da aka kira sallah azahar sannan na fito daga garden din

ya shiga part dinsa yai alwala ya nufi masallacin dake unguwar, after sun yi sallah ya shigo gida, as usual ya nufi part din Hajiya, yar aikinta kawai ya samu a falo hakan yasa ya nufi dakinta tun kan ya karasa ya jiyo muryarta ita da abokiyarta suna fira, har ya juyo da zimmar ya fasa shiga sai kuma ya juya ya shiga da zimmar ya tambaya iya Baby Namra.

  Sai da ya gaishe da abokiyar Hajiyar sannan ya kalli Hajiya ya ce.

“Hajiya ina Baby?”


“Bata nan, wannan mahaifiyar Ikilima ce, Hajiya ga danki nan ko da yake ai kin san shi”


“Na san Gwarzo ai tun ba yau ba”


Cewar matar tana dariya, shi kuma ya saci kallonsa ya sake kallon Hajiya ya ce.


“Ina taje Hajiya?”


“Gidansu kawarta Namra”


Kansa ya daga sama ya saka hannunsa ya dafe.

“Oh Hajiya kin san na ce miki kar a kaita can, matar nan ba mutunci ne da ita ba wata kila ma kallon banza zata mata, shiyasa duk bibiyar da take min ban yarda na kai ta ba”


“To ina ruwan yara da lamarinku, ta sha mun kai tana son zuwa can sai a hana ta? Su fa yarane babu ruwansu da wannan, kuma dazu ta fada min cewar Momyn kawarta ba a gidan take ba”


“Hajiya dan Allah ki aika a dauko ta, ni dai bana son abotar nan, bana son yawan fitar nan da take Wallahi”


“Zan aika amman sai da yamma, abincin ka yana part dinka”


Be sake ce mata komai ba ya juyo ya baro jikin kofar, sai a yanzu yake mamaki no wonder yau weekend kuma bata zo ta dame shi ba, da yanzu tana nan ta saka shi gaba da hana shi aikin nan tace sai su yi game ko ya fita da ita kamar yadda ya saba mata every weekend. A dayan bangaren kuma yana ta ganin karfin halin Hajiya na zon hada shi aure da bazawara dan shi dai kam ya raya a ransa ba zai taba auren bazawara ba.

“Allah kadai ya sani wata kila ma yarta bata da miji, miye na wani zuwa gidan iyayen mai son yarki a yi maganar auren da ke”


Ya fada yana kokarin zama sai jin haushi yake kamar ance masa zancen aurensu ya kawo ta.


HALIMATU POV.

   Washe gari ya kama Saturday babu scul sai islamiya, dan haka na tashi da wuri na gyarawa yarana suka tafi makaranta, har Amal a yanzu tana son zuwa islamiya duk wani kuiya da son jiki yanzu ta daina shi ganin babu ni a kusa da ita. Around 12 suka dawo daga islamiyar suka cire uniform suka saka kayan gida na zuba musu shinkafa da wake da akai a gidan, sai Amal ta murje ido ta kanne kafadarta ita sam ba zata ci wake ba, daman can na san Amal is not fan of wake da shimkafa amman na dauka ta canja ganin bana nan, a dole na tashi na dora mata indomie da kwai. Ina cikin kitchen din ta zo ta same ni ta rike rigata tana tabe baki.

“Momy za ki goyani”


Dariya yai ina mata kallon Mamaki.

“Wato kin ga Momy a banza ko? Amal kin fa girma yanzu ya kamata ki daina wani abun, yanzu ba kamar da kike ba”


Bata fuska tai tana kokarin kuka. Kanwata Salima tai dariya ta ce.

“Kin ganta nan wallahi dole sai an goyata a cikin gidan nan, ko dai Namra ta goyata ko wani a cikin gidan nan idan ba haka ba sai ta shige cikin daki tai ta kuka tana kiranki, yanzu kuma kin dawo dan haka ki yi ta goyon abarki daman can ke kika saba mata”


Dariya nai na kai hannu na dauke na dorata a bayana, ina kokarin kwance dankalin kaina na goyata da shi na ji Sallamar Baby Namra wato kawar Namra yar mutumen nan marar mutunci, da kuzarinta ta shigo da far'a har da yar ledarta a hannu. Gaba daya yan matan gidan mu suka hau yi mata oyoyo suna ta murna da zuwanta da alama dai sun saba da ita ba kamar yadda na ke tunani ba. Ita ma da far'a take ta gaishe su daya bayan daya sannan ta nufi dakin Mama inda ta san su Namra suna can.

  Ni dai ina goye da Amal ina dahuwar indomie sa gata ta shigo tare da Namra, Namra na nuna min ledar hannunta.

“Momy kalla turare da chocolate Hajiyarta ta ce ta kawo mana”


“Eyeee lallai kun gode”


“Laaaa Momy Good afternoon”


Ta fada tana mamakin ganina


“Ykk ya makaranta?”


“Fine”


Sosai yarinyar take kama da mahaifinta, sai dai ita tana da far'a da son mutane ba kamar shi ba. Kana ganin fuskarta ita da Namra ka san suna murna da ganin junansu, daman kwana biyu nan suna da damuna da maganar zuwa gidan ni kuma na banzantar da maganar sai ga ta a yau ta zo. Amal ma sauka tai daga bayana ta bi bayansu.

Ina sallame sallar la'asar Adnan da Namra suka shigo tambaya wai za su je waje su yi wasa, har ta bukaci na bata kudi ta biya kudin lilon da ake kusa da mu su biya su hau, ban musa musu ba na dauko jakata na ciro naira hansin na mika mata suka fita da gudu har suna rigengen. Wani irin faduwar gaba ne ya same ni sai na ji kamar na kira su na ce su dawo, gaba daya na ji babu dadi, ban kuma san dalilin hakan ba, zuciyata tai ta bugawa da karfi kamar zata fito tsabar faduwar gaban da nake, a take na soma ambaton Allah, sai dai ban wani damu ba ganin yamma ce na san shaidanun aljanu ma suna saka haka.  Bayan na gama azkar na dauko wayata na shiga YouTube in duba wasu videos har biyar da rabi tai sannan na fito tsakar gidan kamar yadda muka saba zama na zauna cikin ya'uwana. Sallama akai mana muka amsa sai yaro ya shigo yace wai ana kiran Baby Namra direban ta ne ya zo daukarta. Kamin mu ba shi amsa Adnan ya shigo gidan da gudu har ya faduwa wasu yara na biye da shi jikinsa duk kasa ya fado kaina.

“Momy Namra Namra....ta fada rijiya..... ”


Ban san lokacin da na ture shi ba na mike tsaye na daki kirji idanuwana a waje.


“Wace Namra?”

“Baby Namra....”


Jin maganar tasa nai kamar daga sama, ban san lokacin da na doshi kofar fita da gudu ba, har sai da Inna ta riko ni.1

“Tsaya ki saka hijab dinki”


Sai na koma cikin gidan da gudu na shiga dakin Mama ban tsaya neman hijab na janyo zanen da nai arba da shi a saman gadonta na lufe kaina kamar wata tsohuwa na fito hankali a tashe. Yan mata gidan mu na biye da ni, rijiyar da na sani a unguwar mu na nufa sai Adnan yace min ba ita ba.


“Momy ba ita ba, rijiyar malam ya'u”


Tsayawa nai cak jin ya ambaci rijiyar da na manta when last a dibi ruwa a cikinta, rijiyar da ake cewa har ma sha ruwa akwai a ciki.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, miya kaiku gurin rijiyar malam ya'u”


Sai na maida dubana gurin Salma wacce tai maganar.

“Namra ce ta ce muje can mu yi wasa”


A nan ma kallon Adnan nake, kamar wacce bata da makoma haka na zama, jikina yai sanyi ga uban sara da kaina ya soma yi. Tafiya nake ina jin kamar ana mayarda ni baya ina tafiyar ina jin kamar ba kasa nake takawa, sam ban lura da babu talkami a kafafuwana ba sai da na isa bakin rijiyar kafafuwana suka taka sanyin ruwan da ke gurin. Leka rijiyar da nai ma sai da wani jiri ya kama ni saboda hudunta da kuma dadewarda tai ba a bude ta ba. Wasu mazan unguwar mu ne suka shiga ciki suka daukota a yanayin da na ganta na sam abu ne mai wahala ta rayu, ta ji ciwo a kai a fafafuwanta ma ta samu rauni hannunta har zubar da jini yake.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”


Shine abunda kawai na iya furta na saka hannu biyu na dauke, abun ka da marar karfi ga kuma rashin kuzari na tashin hankali sai na fadi a gurin tare da ita, har sai da kanena suka zo suka dauketa ni kuma na bi bayansu hankali tashe, har na isa gida kuka nake ina jin mutane na tambayar ko mi ya kai su can, garin ya suka fada a wannan tsohuwar rijiyar, sam ni kam ba tambayar ce a gabana yanzu ba ceto ran yar mutane ne a gabana. Muna shiga gida na dauko hijabi da jakar kudina na saka takalmi na muka nufi titi ni da kanena kusan rabin unguwar suna biye da mu wasu na fadi bata da rai wasu na tambayar yadda abun ya afku. Napep muka shiga kai tsaye muka nufi asibitin fmc, mun tararda mutane da yawa a emergency kuma sai mu ka yi rashin sa'a babu likitoci da yawa kasancewar yau Saturday. Sun karbe ta domin duk wanda ya ganta a dole ya tausaya mata, sai dai duk da sun karbe ta din hankalina be kwanta ba na kasa zaune na kasa tsaye, zuciyata ta na ta raya min cewar bata da rai ganin tun da aka cirota daga rijiyar bata motsi bata numfashi ga raunukan da ta ji.

“Anty ki zauna”


Salma ce ta dafa ni tana fadin haka, sai na girgiza mata kai ina kuka domin ba zan iya ba.

“Ko ki kira yaya Abdallah...”


Salma na fadin haka zuciyata ta raya min yes na kira shi maybe he can help, jaka na lalaba ban ji wayata ba sam ban lura da jakar kudi ce kawai a hannuna ba har sai da Salma ta miko min ta ta wayar.

“Gashi ki yi magana”


Da na karbi wayar sai na rike na rasa yadda zan yi da ita.


“Ya dauka fa”


Sai nai saurin karawa a kunne.


“Hello....”


“Wake magana”


Muryar Suwaiba ce da alama wayar tana hannunta ne.

“Ni ce Halima ce Ina Abdallah”


Ta dade bata ce min komai ba har sai da nai zaton wayar ta tsinke.

“Hello”


“Bachi yake”


“Ki taimaka min dan Allah ki tashe shi, ina cikin matsala yarinyar da..... ”


Ban gama fadar abunda zan fada ba ta tari numfashina da masifa.

“Haba Halima ya kamata ki gane Abdallah fa kanen mijinki ne, duk da ya rabu da ke be kamata wata alaka na shiga tsakaninku ba, ki shafa matsa lafiya dan Allah”


“Yanzu ma in cikin matsala ne shiyasa na kira shi...”


Na fada domin kawai ta fahimci akwai dalilin kiran ba hakan nan kawai nake kiransa ba.

“To bachi yake”


Ta tsinke wayar. Kwallar idona ta hanani ganin komai, hayaniyar mutanen da suke emergency sai na ji kamar ina wata duniyar, tabbas ina jin bakina yana motsi amman ban san me nake fada ba, Salma ta karbi wayarta ko na bata ko jefarwa nai duk ban sani ba, sai kuma na ji wani na tambayar ina yayen yarinyar nan, wata kila da mu yake wata kila kuma ba da mu yake ba duk ba zan iya ganewa a yanzu wani hudu ne ya rufe min ido ga idon a bude amman na kasa ganin komai.

“Anty.....”


Can cikin a na ji muryar Salma ta kirani kamar tana wata uwa duniyar. Tassssss na ji saukar wani azababben mari a gefen kumatuna, marin da ba a taba min irinsa ba tun da uwata ta haife ni a duniya, wani zafi na ji ya mamaye min ilahirin fuskata kamar wuta, a take kafafuwana suka kasa daukata.


“Ku rike ta....”


Shine abunda na iya jiyowa shi ma kamar daga can wata uwa duniyar, ji jai na buga hannuna a wani abun mai kamar karfi sai dai ko kadan ban ji zafin ba har numfashin da ke jikina yai gaba abunsa...

AHMAD POV.


Aikin yake ta yi zuciyarsa na gurin yarsa, hakan nan kawai yake jin cewar baby Namra is not safe, yana ta ganin kamar matar nan zata mata kallon banza ko ta fada mata magana marar dadi saboda shi, and he can't take it anymore ko akansa balle akan yarsa da yake ji da ita, zuciyarsa na ta raya masa abubuwa, he feels like ba zai sake barinta taje gidan ba zai dauke mata hankali da wani abun.+

“Daga ganin matar nan bata da mutumci ko na five naira”


Ya furta zuciyarsa na kara raya masa cewar macen auren mai mutumci ba zata iya tsayawa ta fada masa magana marar dadi kamar yadda Halimatu tai ba. Sai yanzu ma yake jin shi be yarda fa tarbiyar gidansu ba kar su lalata masa ya. Mikewa yai tsaye yana kallon agogo hannunsa da ya nuna masa karfe biyar da yan mintuna. Takardunsa ya kwashe ya dauko laptop dinsa ya nufi part dinsa ya aje su a can sannan ya fito harabar gidan ya kira almu direba, Almu ya zo da gudunsa.


“Kaje ka dauko Baby inda ka kaita dazun”


“To Alhaji”


Direct bangaren Hajiya ya nufa, sai ya same ta a falonta mai mata mopping na matsa mata kafafuwanta. A one seater ya zauna yana kallon fuskar Hajiya da ke cike da far'a, wanda yake kyautata zaton nasabar farincikinta da zuwan matar nan ta dazun.


“Ka ci abinci kuwa?”


“No kin san ai idan ina aikin nan bana iya tsayawa cin komai”


“Larai tashi ki dauko kulolin na zuba masa”


“No zan ci after magrib”


Ya fada zuciyarsa na ta yi masa sake sake akan farincikin Hajiya, baya son ya tambaya tai masa maganar Ikilima ko abunda ya shafeta so he decided ya kyaleta kawai idan ma maganar da ya kamata ace ta ji ce yana zaunesa za tai masa maganar. Hannu Hajiya ta kai ta dauko wayarta ta kira direban Baby Namra bugu daya ya dauka.


“Hello Almu kaje ka dauko Baby Namra”


“Ga ni a hanya Hajiya Alhaji ya fada min ai”


“Okay”


Ta aje wayar sannan ta kalli Ahmad tana murmushi.

“Ko dan Baby ai ya kamata ka auri yarinyar nan, dan nasan yadda Baby take da rigima kamar kai ita kadai zata iya zama da ku, Wallahi dazun da mahaifiyarta na ba ni labarin irin hakurin zaman auren da tai sai ta kara burge ni”


Shiru yai kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya kalli Larai ya ce.

“Za ki iya ba mu guri Larai”


Da sauri Larai ta mike tsaye sai Hajiya ta ce.

“Why?”


“We need privacy Hajiya, idan muka maganar Family be kamata wani ya ji ba”


“Aiko dai ina jindadin matsa min kafafuwan nan da take”


Tashi yai ya tare a gaban Hajiya kasan carpet yaja kafarta daya ya soma matsawa.

“Hajiya ki ce matar nan ta zo miki tallar yarta kawai, ai kamata yai ace ta bari wasu su fada, kuma ni babu abunda za ku fada min da zai saka na aureta, na fada miki bana son auren matar wani Hajiya you know it”


“Wallahi wannan yar albarka ce, irin wannan mai hakuri ba har tausa sai ta min ba”


Kansa ya daga ya kalli Hajiya, ya san suna da arzikin da za su iya yin duk yadda suke so, after masu mata girki da shara da wanke wanke da gyara harabar gida da mai bawa fulawa ruwa everyday, now sukukarta take son ta rika matsa mata kafafuwanta, he just don't know why Hajiya take son mulkar sukukanta da hana su yancinsu, be isa ya siyawa matarsa abu ba ba da sanin Hajiya ba ko da ko anko ne, balle kayan sallah komai sai ta zaba ake musu.

STORY CONTINUES BELOW

“Hajiya.....”


Sai kuma yai shiru ya busar da iskar bakinsa, ya san mahaifiyarsa so tana da right ta yi duk yadda take so da shi ko da iyalinsa, but this time around maganin kar ayi kar a fara ba zai yarda yai auren a yanzu ba, idan ma zai yi ba bazawara ba kamar yadda take so, domin shi dai a rayuwarsa yana kyamar ragin wani, ya fi son shi ya rage maka as long as mace ta auri wani ta fito ba zai iya aurenta ba ko wacece ita a duniyar nan and no matter how much he loves her.


“Ka amince kenan?”


Da sauri ya amsa.

“No Hajiya ba zan iya auren yarinyar nan ba, I Wallahi ko hannun macen da wani namijin ya aura bana jin zan iya rikewa balle kuma har na aureta”


“Wai wannan wace irin bakar akida ce?”


Hajiya ta fada a fusace tana janye kafarta.

“Wallahi Haka Allah yai ni Hajiya, ina da masifar kishi ina da kishin bala'i ni kadai na san abunda na ke ji”


“To Allah ya raba mu da bala'i.... ”


Kamin ya amsa da Amin Almu ya shigo jikinsa na rawa cikin falon har yana kokarin faduwa, ko sallama be yi ba abunda be taba tun da yazo gidan ba Hajiya ba ko Ahmad sai da ya firgita da yanayinsa.

“Alhaji....Hajiya... An jefa Baby...Na ji ana fadin Baby ta fada rigiya”


“Na shiga uku ban lalace ba”


Hajiya ta fada Ahmad kuma ya mike tsaye da sauri yana kallon Almu.


“Wace Baby?”


“Baby Namra Wallahi yanzu na ji ana fadar hakan ina tsaye kofar gidan na aika yaro ya kirata sai yaron ya shigo gida da gudu yan..... ”


“Almu Enough...!”


Be gama ba Ahmad ya daka matsa wata mahaukaciyar tsawar da ko Hajiya sai ta ta ji zuciyarta kamar zata fado, balle shi Almu da Ahmad yake kallo kamar idonsa zai ciro. Hannunsa ya saka aljihu ya ji babu keys juyawa yai da wani irin gudu da ya manta when last yai irinsa ya shiga part dinsa ga keys din a inda ya saba aje su amman ya kasa ganinsu sai da ya rumtse idonsa.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”


Ya furta gabansa na kara faduwa, bude idon yai ya kai hannunsa ya dauki keys din ya fito da sauri ya nufi gurin motarsa, a yanayin yadda ya bar gidan da yadda ya hau titi duk wanda ya kalleshi ya san ba tukin hankali yake ba, ko dai ace yayi shaye-shaye ko kuma ba shi da hankali ko so yake ya kashe kansa. Cikin kankanen lokaci ya isa unguwarsu Halimatu, sau biyu kawai ya taba zuwa kawo Namra da kuma daukarta, ya san inda kofar gidan take amman be taba takawa ba sai yau, haka ya fita be ko kashe motar ba ya shiga cikin gidan su Halimatu kamar ba gidan matan aure ba.

“Ina yata take?”


Ita ce sallamarsa, sai aka rasa mai bashi amsa kowa yai cirkocirko.

“Ta fada rigiya Momy taje da ita Asibiti”


Adnan ya amsa masa.


“Wace asibitin?”


“Na ji tace fmc a napep suka je”


A nan ma Adnan ne ya bashi amsa, juyawa yai da sauri ya koma cikin motar, da wani irin karfi ya fizgeta sai da kura ta mamaye gurin. Yana shiga fmc ka tsaye ya wuce emergency ko'ina dubawa yake har ya hango Halimatu tsaye tare da kanenta biyu. Tun ka ya karasa ya rika ganinta kamar wani bakin maciji, yana isa gurin tana juyowa a take ya kifa mata mari, tangal-tangal tai tana kokarin faduwa sai mutane suka fara fadin a riketa Salma ta riko ta amman ina tuni ta kai kasa, hannunta ya daki wheelchair dake gurin.

STORY CONTINUES BELOW

Haba malam, haba bawan Allah Subhanallahi, sune abubuwan da suke fitowa a bakunan mutanen da ke gurin.

“Ina yata”


Ya tambayi likitan.

“Mahaifinta ne kai?”


Runtse ido yai kamar ba zai amsa masa ba, sai kuma ya gyada masa gudun bata lokaci.

“Muna bukatar jini”


“Ina take?”


Ya tambaya numfashinsa na fita kamar wanda yai wani aiki ya gaji. Da hannun likitan ya nuna masa kofar dakin.

“Tana ciki”


Da sauri ya shiga gurin, katon guri ne da ake aje mutane wasu kasa wasu saman gado ana shiga da su wani dakin likita na dubasu. Tsaye yai yana kallon yarsa kama da matacciya take masa domin bata motsi kuma babu alamar rai a tare da ita.

“Baby.... ”


Ya furta cikin tashin hankali.


“Tana da rai jini likitan ya ce a kawo sai a duba ta, sun tafi su dauko gado... ”


Be ko tsaya kallon mai matsa bayanin ba ya nufi yarsa yasa hannu biyu ya dauke ta cike da kuzari jin cewar tana da rai. Kamar wani mahaukaci haka ya fito da ita mutane sai kallonsa suke, ya sakata a mota sannan ya zagayo ya shiga mazauninsa da gudun tsiya ya bar cikin asibitin SJT hospital ya nufa da ita kasancewar ita ce asibitinsu kuma asibitin masu kudi wacce za a baka kulawa a take. Kamin ya karasa ya saka hannunsa aljihu ya lalaba wayarsa sai ya ji wayam babu komai sam ya manta da cewar a gida ya bar wayar sai yanzu da yake bukatar kiran family Doctor su.

Yana isa suka karbata a take suka fara bata kulawa, jini ne abunda suka bukata bayan sun shiga da ita ICU, kamin ya kai gurin da za a dibi jinin nasa jikinsa har rawa yake. A ana cikin dibar jinin sai ga family Doc su ya shigo gurin hankalinsa a tashe.

“Subhanallahi Gwarzo, yanzu ta kira tace na duba mata ko ka zo nan, na shiga emergency Doc Nura ke fada min an shiga da Baby ICU kai kuma kana nan, garin ya hakan ya faru...?”


Kai kawai Ahmad ya daga ya kalleshi, shi da kansa ya karancin irin tashin hankalin da Gwarzo yake ciki ya fi gaban kwatance. After an gama dibar jinin Ahmad ya riko rigar Doc Nura da idanuwansa da suka gama rikedewa ya ce.

“Dan Allah ka yi duk yadda za ka yi ka ceto rayuwar Baby, dan girman Allah”


Ba Doc Nura kadai ba duk mutanen da ke gurin sai da ta ji tausayin Ahmad, gashi dai ba kuka yake ba amman idanuwansa da jikinsa da fuskarsa sun nuna damuwarsa karara, even the way da yake numfashin kasan yana cikin tashin hankali. Doc Nura ya gyada masa kai.


“Karka damu In-Sha-Allah zata tashi”


Sai a lokacin ya sake shi, ya dafe kansa ji yake kamar ace yana da wani abun da zai yi yarsa ta dawo normal. Mikewa yai tsaye ya bi bayansa a bakin kofar dakin da aka shiga da ita ya tsaya ya jingina jikin bangon dakin ya Runtse ido, yana jin muryar Hajiya amman ja kasa daga kansa sai kokuwa yake da numfashinsa.

ABDALLAH POV.


Daure da tawul ya fito daga bathroom dan karamin tawul a kafadarsa yana goge ruwan da ke kansa.

“Waya kara ni”


Ya tambayi Suwaiba da ke zaune bakin gadonsa.


“Babu kowa”


“Amman na ji wayata ta yi ringing kuma na ji kin yi picking sai kuma kika fita”


“Ni ce na gwada kiran ina son na gane idan wayata tana aiki ne”


STORY CONTINUES BELOW

The way da tai masa magana sai ya ji be gamsu da abunda ta fada ba, if gaskiya ne then why da tai picking ya bar dakin? Be sake ce mata komai ba, ya zauna gaban madubi ya soma shafa mai, jin bata zo ta taya shi ba yasa ya juyo ya kalleta.


“Ba za ki taya ni ba?”


Bata bashi amsa ba, sai dai irin kallon kunar zuciya da take masa ya karantar da shi damuwarta.

“It seems like kamar akwai abunda yake damunki”


“Yes alakarka da Halimatun nan ne ya ishe ni”


Juyowa yai gaba daya ya fuskance ta.

“I thought we talk about this issue kuma kin fahimce ni”


“No i didn't,and i won't”


Kai tsaye ta amsa masa da kamar fada, mikewa yai tsaye ya dauki wayarsa ya cire password din ya shiga call list ya duba mai kiran, bakuwar number ya gani a take ya aikawa Number kira, sai da tai ringing har ta katse ba a dauka sannan ya sake kiran layin aka daga cikin muryar kuka Salma take magana.


“Hello.. Ya Abdallah”


“Miya faru?”


Ya tambaya ba dan ya san mai maganar ba, sai dai ita Salma tana da number sa.

“Anty Halima ce sume”


Gabansa ya fadi.

“Ta suma kamar ya?”


“Dazun ba Anty Halima ta kira ka ba? daman muna asibiti wannan Namra ce ta fada rijiya shine babanta yanzu ya mari Anty Halima ta suma”


“Kuna ina?”


“Muna asibitin Fmc”


Be saka cewa komai ba ya katse kiran, zuciyarsa bata bashi kowa ba sai Namra ta ya akai ta fada rijiya ita tambayar da ta fado masa a rai, and why Aminu zai saka hannu ya daki Halimatu bayan ita take dawainiya da yarta, saboda kawai ya mayarda ita wata banza shine yake ta yi mata yadda ya ga dama.

“Miyasa bata kira wani ba a family sai kai? Bata fi kusa da Abdulhamid ba shi da ya aureta ya saketa cikin mutunci? Ji yadda kake zanzana kamar.... ”


Kan ta karasa ya daga mata hannu.


“Please....”


Sai kuma ya juyo daga jikin wardrobe da yake tsaye ya kalleta yana gyara hannun rigarsa.

“Alaka ta da Halimatu ba ta yankewa matukar ina da rai, saboda haka ki sakawa zuciyarki salama, idan za ki iya yarda da mijikin fine, idan kuma aka samu akasin haka za ki wahalar da rayuwarki ne kawai, na fada miki kuma a yanzu zan sake maimaita miki hakan, for now on ba saboda na auri Halimatu nake wannan abun ba i just want to make her happy....”


Yana kawai nan ya nufi gurin da kananan abubuwansa suke ya dauka ya saka aljihu ya fice daga dakin cikin sauri. Kamin ya isa asibitin zuciyarsa ta cika, ransa ya bace sosai from now on zai rika defending Halimatu as her brother, taya wani can wai shi tsohon mijinta zai saka hannu ya daketa saboda kawai yarta ta fada rijiya.

“Ji wani irin zalimci”


Ya furta yana jin wani irin bacin rai an taba masa Halimatu, a take wani bangare na zuciyarsa ya aika masa tambayar da ya rasa amsar ta.

“Miyasa na damu har haka? What if mutane suka zargi wani abu? Miyasa nake ta zurfafa lamarinta a raina har yanzu....?”


Yayi farkin motarsa gurin da kowa yake fakin sannan ya fito ya nufi cikin asibitin yana kokarin sake kiran Salma dan sanin inda suke a cikin asibitin.


HALIMATU POV.

Ashe suma na tana da dadi kamar dai shan maganin bachi, ta kan mantar da kai duniyar da kake ciki da kuma duniyar kuncinka balle kuma wata damuwa da fargaba ko kuka da tsoro. Indai har haka itama mutuwar take to ni kam ina maraba da ita daga yanzu har zuwa lokacin da zata sallamomin.

Sannu sannu Halimatu.

STORY CONTINUES BELOW

Muryoyi biyu na ji wadanda ba zan iya tantancewa ba kamar na Inna da Mama kuma kamar ba na su ba, iyakar unkurin da nai na bude idanuwa ne sai na ji sun min nauyi sosai, a cikin kaina kuma kamar babu komai ina jinsa kamar fanko. Ban ankaro ba na ji numfashina yai nauyi gurin fita daga kirjina haka ma gurin shiga sai na yi da karfi yake wucewa. Da wani irin karfi na umkuro na tashi zaune tare da bude idanuwa har sai da Inna da rike ni. Tabbas Inna ce ga fuskarta nan ina gani kamar a mafarki bakina na motsi amman ban san mi nake cewa ba, kai na daga sama gaba daya komai kamar ba gaske ba nake ganinsa. Kamar a min shokin sai na ji na farko daga mafarkin da nake. A zahirin ma ga Inna nan rike da ni Sai Salma da Aisha da Fati tsaye a kaina, Salma ta rufe bakina tana kuka tana kallona kamar yadda Inna ma take kuka ita da Fati.

“Anty Halima...”


Aisha ta kira sunana tana kallona kamar a firgice.

“Na'am”


Na amsa mata ina kokarin tuna abunda yasa aka kawo ni a nan. Na tuna Namra ta fada rijiya muka kawota ko? Sai aka mare ni? Amman waya mareni? Miyasa aka mareni?

“Ina Namra take?”


“Babanta ya dauke ta”


Salma ta amsa tana share hawayenta. Daga lokacin ban sake sanin inda nake ba, sai na ji kamar wata tsotsa tana min yawo akai. A lokacin da hankalina ya dawo sai na ga Abdallah da wasu likitocin uku tsaye a kaina suna kallona. Wannan karon Salma hannu ta dora saman kai tana hawaye, Aisha ma kuka take.

“Wai miya faru? Namra ta mutu ne?”


“Bata mutu ba... ”


Abdallah ne ya amsa min yana saka hannunsa a aljihu.


“Ina son na ganta”


Ina kokarin sauka daga kan gadon ya ce.

“Akwai drip hannunki ki zauna sai ya kare”


“A a ba zan iya ba ina son na ganta”


“Ba mu san inda ya kaita ba”


Ya amsa min fuskarsa ba yabo ba fallasa. Hakan yasa na koma na kwanta sai kuma na ji yana maganar hoto.

“Idan drip din ya kare Mama za ta kaita ayi mata hoto”


“Ba ni da lafiya ne?”


Na tambaya sai yai saurin ba ni amsa.

“Lafiyarki kalau”


Bayan ya amsa min ya cigaba da kallona kamar mai tunani.


“Ina son ganin yarinyar nan ina son ganinta ta mutu bata mutu ba ban sani ba i need to see her!”


Na fada a tsawace kamar ba a hayyacina ba.


“Idan ka san inda take a kaita ta ganta”


“Ban sani ba amman zan bincika”


Yana fadar hakan ya juya ya fice daga dakin sai sauran likotocin suka bi bayansa. Ni kuma na lumshe idona ban bude ba har sai da na ji motsin shigowar mutum, Hafiza ce ta shigo hankalinta a tashe tana sharar kwalla.

“Sannu Halimatu”

Haka take kirana yana da wahala ta ce min Anty indai ba mutane sai arzikin ke saman kanta ba.


“Yauwa, yarinyar ta rayu”


“Ance tana da rai, mahaifinta ya kaita wata asibitin aka ce”


Ban sake ce mata komai ba, har sai da Abdallah ya shigo da kansa ya karaso ya cire min drip sannan ya ciro wayarsa ya kira wani likita da ban san wanene ba ya ce.

STORY CONTINUES BELOW

“Zan dauketa na kaita ta ga yarinyar yanzu idan mun dawo i will call you”


Daga haka ya maida wayar aljihu ni kuma na sauko daga saman gadon na biyo bayansa, a harabar kofar shiga Ward din inda mutane suke shinfida tabarma suna zaunawa na hango Inna sai ta taso ta tare ni.


“Halimatu kin taso”


“eh zan kaita ta dubo Namra ne idan mun dawo sai a je da ita gurin hoton”


Abdallah ne ya bata amsa a madadina sannan tai mana Allah ya tsare ta bimu da kallo, yana gaba ina biye har gurin motarsa, da kaina na saka hannu na bude motar na shiga na zauna daga lokacin kuma ban sake sanin inda nake ba. Sai can na farka na ga yana kallona.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”


Shine abunda ya furta, kallonsa nai kamin na kalli titin sai a lokacin na lura da motarsa fake take a gefen titi kuma ba a cikin asibitin muke ba, Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tashi motar muka hau titi, SJT hospital muka shiga, babbar asibiti mai zaman kanta a zamfara, asibitin masu kudi domin ko katin ganin likita kawai ya isa siyen wani maganin a yadda nake jin ana fada domin ban taba zuwa ba.


Agurin da aka tanada domin faka motoci ya faka motarsa sannan ya bude ya fita, ni ma na bude na fita sai wani irin sanyi baibaye ni sanyi ba na wasa ba, a take hakorana suka fara haduwa da juna. 

“Koma cikin motar ki zauna”


Ya fada min sannan ya ciro wayarsa ya kira Hafiza yai mata kwatancen inda muke, tun da ya soma wayar na ke kallonsa har ya gama ya cigaba da latsa wayarsa, sak Abdulhamid nake gani a sura da hallitarsu sai dai shi ya dan fi Abdulhamid kwauri kadan, a hallaya kuma sun banbanta, tunawa da Abdulhamid sai ya haifar min da wata kalar damuwa a cikin raina.

“Abdallah”


Ni dai na san na kira sunansa har ya dago ya kalleni ban kuma san dalilin kiran nasa da nai ba, bayan ga wannan ban sake sani ko jin abunda ya fito daga bakina ba, kamar an min shocking dai na ji na dawo normal, amman a kasa nake zaune fuskarta har da hawaye da ban san yadda akai suka zubo ba, saurin tashi nai zaune na saka hannu na share hawayena a lokacin da na kalli Abdallah sai na ga idonsa cike da kwalla yana ta min kallon tausayi.

“Miyasa nai hawaye? Mi yake faruwa da ni...?”


Na tambaya ina kokarin fashewa da kuka, sai ya busar da iskar bakinsa


“Ba komai”


Da kansa ya kai hannunsa ya bude min motar.

“Shiga ciki ki zauna na ce”


“Ina son ganin yarinyar”


“Idan Hafiza ta zo zamu shiga ciki ki ganta”


Zaunawa nai cikin motar sai a lokacin na tuna da yata.

“Ko ina Namra take? Ko har da ita ta fada rijiyar? Kamar bata fada ba ko?”


Na tambayi kamar ya san amsar.

“Tana nan lafiya kalau”


Ban sake cewa komai ba, har Hafiza ta isa sannan na fito daga motar daman kafafuwa na waje suke, shi kuma ya rufe motar yai gaba muka bishi, mun yar tafiya mai dan ni sa sai dai ba sosai ba har muka isa bakin wasu dakuna, daki na hudu ya tura kofar ta bude sai ya tsaya be shiga ba yai min alama da na wuce. Ni na fara shiga sannan Hafiza sai kuma shi.

Baby Namra ce kwance saman gado tana bachi jini na ta shiga a jikinta. An saka mata wani abu a wuya an daure kafarta da hannu a gefen idonta ma bandeji ne.

Mutum hudu muka tarar a dakin ciki har da mahaifinta, kamar wanda ya ga bakin maciji haka yake kallona fuskarsa babu annuri, ban taba hada ido da wani naji firgita kamar yadda na ji a lokacin da na kalli Abban Baby Namra ba, a take na nemi natsuwata da karfin halina na rasa, na rasa sai fargaba da razana suka lullube ni, kamar wata karamar yarinya haka na zama na rasa sukuni har sai da na koma bayan Abdallah na tsaya.

“Kina da wani irin karfin hali, how dare you”


Babu wanda yace uffan daga mutane da suke dakin har Abdallah da Hafiza.

“And let me tell you Wallahi idan yata ta mutu i will make your life miserable, you will die in jail kina ji kina gani zan tarwatsa rayuwarki, you will pay for this, ba kin zabi kashe min ya ba?”


The word jail ta saka ni jin wani iri, is like kamar ban taba jin kalmar ba, kuma kamar ance min gunduwa gunduwa za ayi da ni. Ba tsoron gidan yari nake ko police ba amman ban san abunda ya saka ni tsoro ba har jikina ya fara rawa kamar wata bakuwar kalma haka na rika jinta a kaina, a take garin ya fara sauya min zuwa wani yanayin dabam, can na tsinkayo Abdallah nayi masa magana.

“Taya mace da ta haifa ta san zafin haihuwa zata dauki yar wani ta jefa rijiya? Ya kake magana kamar ba namiji ba”


Wani banzan kallon yai masa irin na sai a yanzu na lura da kai din nan.

“And who are you? Her husband?”


“No I'm her brother”


“Just?”


Ya tambaya da irin sigar rainin wayo.

“Just ne?”


Abdallah ya tambaya a fusace.

“Who do you fucking think you're? After all the slap da maganar da ka fada mata yanzu and you want to deal with me? Daga ganinka ba ka yarda da kaddara ba”


Sai ya daga wa Abdallah gira.

“Yes ban santa ba, saboda ban hada hanya da ita ba, akan yata?..... Hummmm”


Wata budurwa ce ta taso ma Abdallah budurwar da na tana gani a gidansu lokacin da naje.

“Excuse me man, yar mu aka taba kasan darajar ranta?”


“Hey young lady control yourself, and ban sani ba kuma ba na son na sani”


Juyowa yai ya kalleni.

“Muje Hafiza riko hannu”


Yana fadar hakan ya fice, a maimakon ya ta kama hannun nawa kamar yadda ya fada sai ta tsaya yi musu bayani.


“Ku fahimce mu, Halima ba zata kama yar wani ta jefa a rijiya ba, ko da kau bata santa ba balle ta santa, yanzu haka ba a hayyacinta take ba amman ta damu sai an kawo ta ta ganta, tun daga lokacin da ka mareta bata sake zama mutum kamar kowa ba, daga ni har ita ba mu san yadda akai yarka ta fada rijiya ba.... ”


“Aljanune da ita kenan? Shiyasa ta dauki Baby ta jefa rijiya, daman ai ba tai kama da masu hankali ba, ita aljannu take takama da su ni a kaina rauhanai ne, na fita hauka”


“Ba haka nake nufi ba...”


“Idan baki min shiru ab har da ke zan daure fita ki ba ni guri”


Ita yake ma masifar ni ce da jin tsoro sai hawaye nake kamar domin hawayen kawai aka hallaci ni. Hannu ta rika muka fice daga dakin ita hawaye ni hawaye har muka isa gurin motar Abdallah. Gidan baya muka zauna ni da ita, kamar uwa da ya haka kanwata ta rumgume ni a jikinta sai na fashe da kuka mai tsanani.

“Gida nake so dan Allah ka kai ji gida... ”


Na furta cikin kuka, shi dai be ce min uffan ba har muka bar asibitin.

Post a Comment for "GOBE NA CHAPTER 4 BY KHADIJACANDY"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...