GOBE NA CHAPTER 3 BY KHADIJACANDY - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GOBE NA CHAPTER 3 BY KHADIJACANDY

GOBE NA CHAPTER 3 BY KHADIJACANDY

- - Post a Comment

 GOBE NA CHAPTER 3 BY KHADIJACANDY                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Milk shadda ce a jikinsa sai farar hula, fuskarsa na ta sheki kamar shi ne angon ga wani kamshin tutare da yake mai sanarda zuwansa tun kamin ya iso. Abu biyu ne babu a tare da shi walwala da sai kuma yar ramar da yai kadan. Da sallama ya shigo falon Hajiyarsa sannan ya zauna da bismillah, kamin ya mika mata gaisuwa daga inda yake zaune. Sai ta amsa masa tana ta kallon yanayinsa yanayin da ya sauya masa tun sati biyu da suka gabata.+

“Hajiya ta sai yanzu ake karyawa?”


Ya fada yana kallon kofin tea da ke hannunta.

“Aa yau da dumamen tuwo na karya sai yanzu na ke shan tea”


Be sake cewa komai ba ya maida hankalinsa a gurin tv da ke kunne.


“Ba kaje aiki ba yau ko kuma ba a aikin ne yau?”


“Zan je yanzu, Suwaiba na kai gidan Abdulhamid, daman ta matsa min tun kwanaki baya tana son zuwa na hana ta sai yau dai na kai ta”


Har lokacin da yake maganar be kalli gefenta ba. Yana shirin mikewa tsaye ta ce.

“Jiya Mal Dalhatu ya zo nan”


Da sauri Abdallah ya juyo ya kalleta jin ta ambaci mahaifin Halimatu.

“Mi ya kawo shi?”


“Yace yana ta son ya zo yai mana godiya be samu dama sai yau saboda yanayin jikinsa”


Dan murmushi yai ya kawardar fuskarsa.


“Baba Karami akwai karfin hali, miye abun godiya a ciki ai yi wa kai ne”


“Yi wa kai ko kashe kai? Akan me za ka dauki nauyin irin wannan dawainiyar haka? Ya fada ko ruwan da aka sha a gurin wunin nan kai ka kawo su”


Cikin muryar da ke bayyana rashin jindadinta tai masa maganar hakan kuma ba karamin mamaki ya ba Abdallah ba, domin be taba ji ko ganin ta hana su yin wani aikin alheri ba musamman abunda ya shafi yan'uwa.

“Akan me mace zata nuna maka kiyayya kuma ka dauki nauyin hidimarta? Har da wani daukar yara ka saka su makarantar kudi ina ruwanka ba su da uba ne?”


A karon farko ta yi masa maganar a tsawace tana dire kofin tea da ke hannunta da karfi.

“Ban yi dan wani abun ba Hajiya, a gaban ki Alhaji ya bar mana wasiyar taimakon yan'uwa da mabukata, kuma tun ba yau ba idan za ayi biki a gidan Baba Karami mu na yi masa abu mai nauyi saboda mun tashi mun ga Alhaji na yin haka kuma ya mana wannan wasiyar, ba hidimar aure kawai ba har abincin da za su yi ke da kanki kin sha daukar abu daga nan ki aika musu balle kuma mu da muke jininsa”


“Ba alheri na ke hana ka yi ba, wannan karon ka yi alherin ne a gurbin da be kamata ka yi shi ba, akan me mace zata nuna maka kiyayya kuma ka nuna mata kula har da duniyarka”


“Hajiya idan Halimatu ta auri Abdulhamid kamar ni ta aura, ni da Abdulhamid duka daya ne kuma.... ”


Hannu ta daga masa.

“Na fika sanin wannan kai da shi duka ni na haife ku, ina magana ne kawai akan abunda yake bayyane ni na san Abdulhamid ba son Halimatu yake ba, ita ta janyo ra'ayinsa ba kuma saboda kowa ba sai dan kai”


“Haka ya fada miki?”


“Ba sai ya fada min ba, ni na san waye ďana, be taba zo min da maganar wata mace ko son yin aure a wannan yanayin da yake ciki ba sai a wannan lokacin, mutumen ma da neman lafiyarsa ya saka a gabansa? Rana tsaka ya zo min da zancen auren nan idan ba ita ta nuna masa ba taya za ayi ya kawo wannan tunanin a ransa? Kuma ya rasa mace aure sai Halimatu bazawara? Mai yaya hudu yana saurayinsa bayan kuma ba iya komai yake ba Allah yasa dai tsakani da Allah zata zauna da shi”


STORY CONTINUES BELOW

Murmushi Abdallah yai ganin yadda Hajiyarsa take ta bude wuta.

“Ban da abinki Hajiya Abdulhamid ai ba yaro ba ne da zata nuna masa hakan ya yarda idan har ya san baya son ta ko kuma zai cutu”


“Ko dai minene Husaini be dace Halimatu ta auri Hassan ba bayan ta san kana sonta ban goyi bayan Abdulhamid ya auri Bazawara ba a aurinsa na fari na kyale shi ne kawai saboda na lura da ra'ayinsa na son yin haka kuma bana son na karya masa guiwa saboda ya dade yana mafarkin aure be samu ba, kuma na tabbatar shi kansa be san kana son ta ba Wallahi ba zai aure ta ba, amman ita ai ba yarinya ba ce ya kamata tai tunani indan har ba zata aure ka ba to be kamata ta auri dan'uwanka ba, ko da kuwa shi ya nuna mata son da gaske sai da ta fasa aurenku duka, Hassan ya ji da wanne yayanta guda hudu ko kuma lalurar da take gabansa? Da gangan tai wannan saboda ta bata zumunci kuma ya batu”


Abdallah ya shafa kansa tare da hade yawu sannan ya kalli Hajiya a raunana ya fara magana muryarsa kasa kasa.

“Jikina yana yawan ba ni haka, ina yawan jin cewar kamar Halimatu ta jayo soyayyar Abdulhamid ne ba shi ya kai kansa ba, sai dai zuciyata ta kasa yardar da hakan, tun daga lokacin da kika fada min Abdulhamid ya zo miki da maganar auren, ko wane dare sai na lalubo na ga ko zan hango wani abu da zai saka na zargi Halimatu amman Wallahi Hajiya na kasa ganin laifinta, a maimakon haka sai tausayinta ya kara kamani saboda na san Abdulhamid ba kamar ni ba ne baya son yara a rayuwarsa, ko da ma yana son yara ba zai kaunace su a lokacin da yake saurayinsa ba ita kuma take a bazawara ta zo masa da yara, ga mahaifinsu be kula da su ba, and yan gidansu gaba daya mata ne mazan uku duka kanane da ba su yi wani wayo da za su iya kula da tattalin kanensu ba, balle ma yayan yayyu, abu ne mai wahala ta samu mai kula mata da yaranta yadda ya dace”


“Can ta matse mata ina ruwan wani? Ita yarinya ce da ba zata yi tunani ba kamin ta aikata abu? Ni Wallahi da tausayi take ba ni amman yanzu na natse ko ganinta bana son yi, ba dan kuma komai ba sai dan wannan wawanci da ta aikata, ni Wallahi bana son Abdulhamid ya auri bazawara kuma bazawarar ma wacce dan uwansa yake so kuma ita ta san hakan amman ta yarda”


Wannan karon wani dogon numfashi yaja ya sauke.

“Hajiya akwai wani kuskure da na aikata a can baya, wanda na ke tunanin wata kila saboda shi Halimatu take son hukunta ni kuma na cancanci haka”


“Haba Husaini wani irin laifine da zai saka ta auri dan'uwanka saboda kai? Ni ban ga cancanta aurenta da Abdulhamid ba Wallahi na san waye ďana”

“Hajiya na yi kuskuren furtawa Halimtu cewar ina sonta a lokacin da take da aure, tun da na dawo kasar nan na ganta sai ta ga ta canja min kamar ba ita ba sai Allah ya dauki son ta ya saka min a rai, a lokacin na yi ta kokarin ganin na haka zuciyata abunda take son cusa min amman na gagara, Wallahi Hajiya har ta kai idan zan kwanta ko ina wani abun sai tunaninta ya fado min a rai, musamman da na samu labarin yadda mijinta yake da kuma irin yadda take hakurin zama da shi, a lokacin shaidan ya yaudare ni kuma yayi galaba a kaina zuciyata tai ta nuna min cewar Halimatu bata dace da auren Aminu ba, ni ta dace ta aura a lokacin akwai good understanding tsakanina da ita, hakan yasa na fara nuna mata irin halayen mijinta da abubuwan da yake marar kyau, daga lokacin muka fara samun matsala da ita, a lokacin ne na fada mata kai tsaye cewar ina son ta.... ”


Shiru yai for few seconds ya shafa fuskarsa sannan ya sake sauke numfashin a karo na biyu.

“Na fada mata zan iya aurenta idan har zata iya kashe aurenta ta fito, kuma na yi ta aikata abubuwan da nake sa ran za su iya zama silar mutuwar aurenta, Astagafurullah ....Abubuwa da yawa Hajiya har ta fara fada min bakar magana tana min kallon wani shaidani yes ni kaina a ynzu ina jin na aikata ba daidai ba, amman a wacan lokacin sai na kasa gane hakan duk da na san bata dace da auren Aminu ba amman ai he dace na yi sanadin mutuwar aure ba ko?”


STORY CONTINUES BELOW

Hajiya ta gyada masa kai. Sai ya maida kansa kasa yana taba agogon hannunsa


“Yes i know... Kuma na san shi ya janyo min wannan matsalar a yanzu, so ko da ma ita ta janyo soyayyar Abdulhamid batai laifi ba inda dai ta hukunta ni tai i deserve it, and Abdulhamid ya fi ni bukatar aure a yanzu saboda yana a situation din ba ko wace mace zata iya aurensa a yadda yake ba sai mai hakuri da jajircewa kamar Halimatu”


“Babu wanda ya san da wannan matsalar sai mu, sai kuma ita a yanzu waya sani ko ta gagara zaman ta fita ta tona mana asiri kuma ta bayyana ma duniya halin da Hassan yake ciki bayan a da yana cikin rufin asirin Allah? Na fi tausayin Hassan fiye da kai na dade ina jiran zuwan ranar da zan ga Hassana yayi auri yana rayuwa ta farinciki kamar kai kamar kowa, amman na bana farinciki da auren nan, saboda yayi auren a lokacin da be dace ba kuma da wacce ba ta dace ba”

Mikewa tsaye Abdallah yai yana jin wani abu na rashin jindadi yana kawo masa ziyara.

“Haka Allah ya kaddara”


“Haka Allah ya kaddara kuma da son ranta ba, idan ma wannan hukunci ne take tunanin ta yi to kuskure ne babba”


“Zan je gurin aikin Hajiyarmu ba wani abun ko?”


“Babu”


Sai da ya kalli yanayinta sannan ya sa kai ya fice ransa ya susuwa zuciyarta na konuwa.


HALIMATU POV.

Al-hamdulillah shine abunda na ke yawan maimaitawa tun daga lokacin da na saka kafata a gidan Abdulhamid, duk wani abun na jindadi rayuwa da mace zata nema a gidan miji Abdulhamid ya tanadar min shi, tun daga na ci har na sakawa a jikin har na kallo, kamar wata kwai haka yake tarairaiya ta a yadda yake nuna min kulawa da soyayya ban tsamanci samunta a gurinsa kamar haka ba. Yana yawan nanata min cewar ina da wani irin girma da daraja a idonsa saboda aurensa da nai alokacin da yake dauke da lulurar da ba ko wace mace ce za ta yarda ta aure shi a haka ba, wannan dalilin yasa yake da kara gwarjini a idonsa. Ya kara maida hankalinsa gurin neman magani fiye da da, ni ma kuma ina kokarin yi masa abubuwan da zasu taimaka duk dai bana ganin wani alamu na warkewar sai ban taba gajiyawa ba ko na fitar da rai domin na san babu cutar da bata da magani. Ina samun kwanciyar hankali a aurena da Abdulhamid fiye da wanda nai a baya da Aminu, ko ba komai zai nuna min kulawa zan kwanta a kirjinsa na farka a gefensa mu ci abinci tare mu yi fira mu yi hara mu yi nishadi, ba kamar a gidan Aminu ba da ba shi da lokaci na.

Bana da wani fargaba ko tunani a gidan aurena bayan ta mutum biyu yayana da kuma Hajiya wato mahaifiyarsa domin na lura a duk zuwan da muke gaishewa kamar bata na'am da ni, bayan a baya kuma ba haka na santa ba, duk dai ba wani zuwa muke sosai ba amman a duk lokacin da muka je gaisheta ko kuma muka fito daga wani gurin muka biya sai ta yi min tarba ba a baya da kai ba, ko kuma ta bar a nan a falon ba ita kadai ba har yayanta mata biyu na lura haka suke min basa son fira da ni balle kuma irin wasar nan ta matar yaya, namijin ne kawai babu ruwansa shi kan idan muka tarar da shi a gida mu yi ta fira abun kamar ba kanen mijina ba, amman bayan wannan bana da wata matsala da Abdulhamid idan ka cire na kyamar yayana da yake yi, domin na lura ko zancensu baya son ina yi idan aka kira waya da sunan za mu gaisa da su a lokacin da yake kusa da ni da a take yanayinsa zai canja, be taba siye ko da biscuit din maira goma ya mika min ko ya bawa wani yace a kai musu balle kuma har ya tambayi lafiyarsu ko karatunsu, sai dai ina masa uzuri da wannan ganin cewar shi din be taba aure ba sai yanzu kuma daman can ba mutum ne mai son yara ba, ballanta na san yadda wasu mazan suke basa son yayan wasu a kusa da su, musamman Abdulhamid da na lura da alamar yana ďan da kishi ba kamar wasu ba, tun daga lokacin da yai kokarin hana ni aikina na lura da hakan ga kuma ya hana yin ko. Wane irin social media saboda kar na hadu da maza, yana yawan fada min cewar na rike masa kaina na tsare masa kaina kar na bar shaidan ya rinjaye ni, wani lokacin na kan amsa masa da to ko nai masa alkawarin haka ba wani lokacin kuma sai dai na yi dariya, domin a tunani babu abunda zai kai ni na aikata wani alfama ko da bana da aure balle ina da shi, ba wai na fi karfin shaidan ba ne, kawai dai ina tuna baya ne a lokacin da Aminu zai iya shafe wata da watannani ba neme ni ba kuma babu kulawa da magana mai dadi ga shi ina zuwa aikin ina ganin mazan amman ban aikata ba, balle yanzu da nake auren mutumen da ya san darajar aure kuma bana ganin mazan ma, to mi kam Allah na tuba wace tsiyar ce zata saka ni aikata hakan.

  A zaman aure da Abdulhamid wani abun da zai baka mamaki shine rashin iya girki, wanda ni kaina yake bani mamaki kuma ya ba ni tsoro, tun da na zo gida ban taba dora girki ko da ruwan zafi ne ya tafasa ba, idan na dora miya yadda na hada ta haka zan zo na tararda ita haka tuwo ma, shiyasa ban taba yin jalof ba lalle shimkafa da wake, indai har za mu sha tea sai dai Abdulhamid ya dora mana, indai har ni na dora ba zai tafasa ba ko da kuwa a gas ne ko electric kettle. Sai dai be taba sakawa Abdulhamid ya min fada ko nuna bacin ransa a hakan hakan ba, kullum safe shi zai dora mana ruwan da za mu amfani da su da rana kuma yai mana take away haka ma da dare, na kuma rasa gane dalilin haka bayan a can baya na iya girki na kamar ko wace mace, amman tun da na tsinci kaina a gidan Abdulhamid sai komai ya lalace.

  

Ranar wata labara da misalin sha daya da yan mintuna na ji an buga kofar falona, na yi tsamammi ko daya daga cikin yan matan gidan mu ne hakan yasa na tashi da kuzari na bude, abun mamaki sai nai arba da Suwaiba matar Abdallah kuma uwar yayansa mata guda biyu, na yi mamakin maganinta domin ta dade tana min waken zuwa amman bata zo ba sai yau, mun sha fira a ranar daman can Suwaiba mace ce mai son fira da far'a da haba haba da jama'a, ban yi zaton Abdallah ya kawo ta ba har da ta labarta min cewar shi ya kawo ta amman ya aje ta gurin gate wai yana sauri jaye gurin aiki.

Ta labarta min abubuwa da yawa a ciki har da na rashin son yara da Abdulhamid yake da shi, sannan ta dora min da cewar yawanci maza basa son yayan da ba na su ba, balle kuma Abdulhamid da yake saurayi, tana ta nanata min cewar sai na yi hakurin haka kamar ta san abunda ya fi damu na kenan, duk kuwa da kasancewar ban taba fadawa kowa ba.

  Ganin na dauki waya na kira Abdulhamid na ce yai mana takeaway sai abun yai ta bata mamaki.

STORY CONTINUES BELOW

“Kar dai ace har yanzu baki fara girkin ba, ko kuwa amarcin ne ya motsa kike jin ba za ki iya dafawa ba?”


Dariya nai kamin na bata masa.

“Wallahi ba haka ba ne, idan na dora girkin baya dahuwa yadda na saka shi haka zan tararda shi kuma ga wuta ga komai amman ba ya yi”


“Too kar dai ace Abdulhamid ma yana da kohi kamar Abban Suhaima, ni ma idan nai masa wani laifin ko kuma na bata masa rai haka zan dafa abinci a ranar ba zai dafu ba sai na bashi hakuri”


Ta fada tana dariya... Ni ma dariyar nai sai dai ba irin ta ta domin ni wani tunanin ne ya zo min, kar dai ace Abdallah ne yai min kohi nake ta samun wannan matsalar?


“Ko da yake shi ma a tawaye ne dole za a samu dukansu suna yi, wata kila wani abun kika masa sai kin ba shi hakuri sannan za ki daidaita, amman fa ni kin san da na dauka ko Abdulhamid ba shi da kohi”


Zancenta ne ya dawo da ni daga duniyar tunani sai na sake yin murmushi a karo na biyu.


“Haka ne ai wani ba a iya ganewa sai idan wani abun ya faru”


“Haka ne”


Sai guraren karfi biyu ya kirata a waya yace ta fito bakin gate yana jiranta, a lokacin Abdulhamid be dawo ba, sai na saka Hijabina na rakata har gurin motarsa bayan na deba mata wasu abubuwan daga turaruka na da kayan kwaliya, gilashin motarsa a sauke yake amman ko da wasa Abdallah be dago ya kalleni ba da na gaishe ma sai ya amsa min a gajarce kamar be san ni ba, bayan sun wuce na dawo ciki gidan ina ta nazarin kalamanta. Daga karshe na yanke shawarar kiran Abdallah nai masa magana, haka kuwa akai bayan Abdulhamid ya dawo mun ci abinci mun yi fira ya fita sallah la'asar ni kuma na nemo number Abdallah ya aika masa kira, ringing tai kamar zata katse sannan ya daga, ban tsaya yi masa sallama ba balle gaisuwa kai tsaye na ce.

“Abdallah magana na ke son mu yi”


Sai na yi shiru bayan na fada masa hakan ina jiran na ji amsar da zai ba ni kamin na dora amman be ce min komai ba har sai da nai zaton ko wayar ta katse ne.

“Idan ka kullace ni da wani abun dan Allah ka kwance, tun da na zo gidan nan kullum nai girki ba ya yi”


“Babu hannuna a ciki”


Ya amsa da muryar da na jita kamar ba ta shi ba.

“Wata kila kana jin haushina ne, ko kuma kana jin bacin rai a kaina ne”


“Ban taba jin haushinki ba, kuma ba ki bata min rai ba, abunda kika aikata ne kawai idan na tuna ina jin babu dadi ne”


“To ka daina jin babu dadin, shiyasa bana iya girkin idan na yi ba yayi, dan Allah ka kwance Kohin da kai min”


Ina iya jiyo saukar numfashinsa kamin ya ce.


“Ban kullace ki da komai ba Halimatu, ke yanzu yar'uwata ce kawai kuma matar dan'uwana, yan'uwanta ta fi gaban wasa ko babu Abdulhamid babu abunda zai shiga tsakanin mu”


Yana fada min hakan ya kashe wayar, a take wani abun marar dadi ya kawo ma zuciyata ziyara. Har na gabatar da sallah la'asar ban daina jinsa ba, bayan sallah isha'i ina kwance saman kujera falo Abdulhamid ya fito daga bedroom ya nufo inda nake kwance, sumbatar kaina yai kamin ya daga ni na tashi zaune sai ya zauna sannan ya kwantar da kaina saman kijinsa yana shafa fuskata.

“Gobe fa ina tunanin zanje Abuja”


Dagowa nai na kalleshi sai na ga murmushi a fuskarsa.


“I know za ki yi mamaki ai, ni ma zuwan dole ya zame min kuma i think idan na samu yadda na ke so zan dawo ranar da na tafi”


A take na marairaice fuska kamar zan masa kuka.

“Mi zaka je yi Abuja?”


“Wallahi wasu takardu ne na ma'aikatar mu da ake son su jibi kuma dole sai an kai su Abuja an saka hannu shiyasa zan je, idan an saka hannu za a ba mu kudi masu dan dama sai mu juya su”


“Tare za mu je?”


“Na so haka amman be samu ba dole mi kadai zan je, amman a promise you idan ban dawo ranar ba washe gari zan dawo”


Har cikin raina na ji babu dadi sai na ji kamar tafiyar shekara zai yi, a ranar na kwanta a jikinsa sosai yadda kasan wata jaririya haka na zama.

Washe gari daga ni har shi mun tashi da wuri, shi ya hada mana abun karyawa ni kuma na shirya masa komai na tafiya, a tare muka karya ina ta narke masa a jiki tun yana daujar abun wasa har shi ma ya so ma jin babu dadi.

Na masa complaining din rashin mai gadin mu sai ya ba ni hakuri ya ce za a samu idan ya dawo bayan yayi min izinin zuwa gida na gaishesu ganin duk na bata rai ya san idan naje zan dan sake sosai, har gurin mota na rako shi nai masa addu'a sosai ta neman tsari da kuma alherin hanya, saboda na san yanayin kasar ana cikin halin fargaba balle tafiyar a mota zai je ba a jirgi ba.

  Bayan tafiyarsa da awa daya na shirya na nufi gidanmu, yan gidan mu sun yi murnar ganina sai zolayata suke wai ina ta shining. A yanayin dana tararda Amal be min dadi ba, wai zawo take da amai yau kwana uku amman basu fada min ba ganin ba su gaza mata a komai ba, na san suna bata kulawa sosai ammn dai ai ya kamata ace sun sanar da ni a matsayinta na yata kuma karama, ko da yake na lura sukansu yanzu yaran idan suka gan ni sai su yi kamar ba su gan ni b babu ruwansu da nuna son zuwa ganina in banda Amal da ta kasa sabawa da kowa har yanzu. Wata kila Mama ta ki ta fada min ne ganin kamar zan iya daga hankalina ga shi kuma Abdulhamid ba son yara yake ba kamar yadda kowa ya lura da hakan.

A ranar Amal a jikina ta wuni lokaci zuwa lokaci sai ta kalleni ta sauke ajiyar zuciya abun har ya soma ba ni tsoro, na so na kaita asibiti duk kuwa da Mama ta fada min sun kai ta ga kuma da aka rubuto mata na gani amman hankalina zai fi kwanciya idan na kaita da kaina. A ranar nai deciding na dauko ta na dawo da ita gidan aurena tare da ni ba in yado washe gari sai na kira Abdulhamid na fada masa cewar na zo da ita saboda bata da jindadi kuma na nemi izininsa na kaita asibiti.

  Bayan magariba na baron gidan da ita na debo wasu daga cikin tufafinta, har na iso gida babu komai a zuciyata sai tausayinsa, wata kila har da kewata ta sakata wannan ciwon saboda yadda ta saba da ni sosai. A gaskiya ranar na ji babu dadi marar misaltuwa, wani abun mamaki da muka dawo gida tare sai ta dan sake Allah ya kawo mata sauki har ta labari take ba ni wai Adnan ya dake ta ya zageta, sai dai idan an taba jikinta ina jin zafi a can gidan bata cin komai amman a nan da na bata abaya sai ta ci ta kwanta a jikinta ta tafe sosai kamar wata kyanwa.

  Misalin tara da rabi na shiga kitchen na gwada dora indomie, wani abun Allah sai gashi ta dahu kamar yadda na saba dafata, ban san lokacin da na daka tsalle na dibe ba dan murna. Ta window kitchen na hango dorowar mutum ta gate, ta hanyar hasken fitulun da ke cikin gidan ne na iya gane wanda ya diron yana sanye da bakaken kaya fuskarsa ma a rufe da bakin fuska. A furgice n rugo da gudu na yo falo sai an samu Amal har ta yi  bachi da sauri n rufi kofar falon na rufe zuciyata na bugawa kamar zata fado, abunda ban sani ba ashe na rufe falon da daya daga cikinsu ba, ban lura da hakan ba sai bayan an rufe kofar na yi baya sai na hango mutum ya fito bayan labule rufe da fuska kamar wacan yana nuna ni da bindigar da ke hannunsa.Khadija Abubakar AlkaliInnalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u.+

Shine abunda nake ta maimaita a raina ina kallon bindigar da ake nuna ni da ita, zuciyata na wani irin zillo kamar zata tuma ta fado kasa. Ban ankaro da a filin na ke neman ceton Ubangijina ba har sai da mamalakin bindigar ya dora hannunsa a bakin da bana iya tantance saboda mask din da tai wa fuskarsa kawaya.

“Shiiiiiiiiiiiii, kwanta”


Kamar umarni nake jira a take na kwanta a guri kamar gawa, ina iya jiyo karar bude gate din gidan da akai kamin daga bisani a bude kofar falon sai shigowar mutane na ji ina kyautata zaton wanda ya diro ta gate ne ya bude musu suka shigo shi kuma na falon ya bude musu kofar.

“Ina mai gidan?”


Sautin muryarsa ba jina kadai ya razana ba har da ilahirin jikina da kwakwalwata, ban tana sanin haka tashin hankalin haduwa da mai makami yake ba sai yau, kamar wacce aka cewa ga mutuwa ta nan a gaba na haka na ke ji.

“Ina mai gidan yake...!”


Ya sake daka min tsawar da na ji ta kamar a mafarki, bana jin zan iya amsa musu domin numfashina ma rawa yake balle kuma muryar da na ke jin kamar ta kare a lokacin.

“Ke tashi zaune”


Ya sake daka min tsawa a karo na uku, sai na tashi ta sauri cikina har wani kuka yake saboda tsoro. Da dai-daya na bisu da kallo kamar zan ga wanda na sani ko ya san ni amman ban ga fuskar kowa ba a cikinsu sakamakon mask din da suka saka. Wanda ke kusa da ni ya saita bakin bingarsa a gafen kaina.

“Ina mijinki?”


“Baya nan....”


Na amsa idanuwa a rufe gam ina jimke hannayena, tashin hankalin da ke cikin kaina yana ta kara hauhauwa.

“Karya kike... Idan ba ki fada mana inda yake ba za mu kashe ki”


Wannan karon na tabbatar ba jikina kawai yake rawa ba har da kayan cikin da ke cikin cikina da kuma kaina.

“Wallahi baya nan ya tafi Abuja”


“Ina kudin da ya shigo da su jiya?”


“Be shigo da kudi ba takardar ce ya je ya kai Abuja a saka masa hannu”


“Idan baki ba mu kudi ba za mu kashe yarki”


Sai a lokacin na bude ido a take na nemi tsoro da gudun kar su kashe ni da na ke na rasa.

“Wallahi Wallahi babu kudi a cikin gidan nan, idan ba ku yarda ba ku duba ko'ina”


“Idan muka duba muka ga kudi za mu kashe ki”


Na gyada kai duk kuwa da kasancewar bana iya tantance mai maganar a cikinsu. A take ya bada umarnin a shiga a duba masa ko'ina na gidan, ba dakina kadai ba har falo sai da suka hankade komai sannan suka yarda da babu kudi a cikin gidan.

“To dauko mana zinari”


“Ba ni da zinari ba ni da komai”


Ina rufe baki na ji saukar mari gafen fuskata.


“Ki dauko mana zinari na ce”


“Ko kashe ni za ku yi, ku sake min wani rai ku sake kashe ni ba ni da abunda zan ba ku bana da azurfa ma balle zinari Wallahi bana da komai”


“Okay Anas dauko mana yarinyar can idan ubanta ya dawo ya ba mu kudi sai ya karbo ta”


Ban san lokacin da na girgiza musu kai ba.

“Aa Wallahi ba yarsa ba ce, ba babanta ba ne kuma bata da lafiya dan Allah ku rufa min asiri karku dauke ta”


Ina ganin ya nufi gurin da Amal take na nufi gurin da rarrafe ina kuka majina na min zuba, fisgota yai da hannu daya ta mikar da ita tsaye sai ta lauye kafafuwanta ta fara kuka irin kukan na yaran da aka tayar daga bachin da be ishe su ba ballantana ita da lafiya bata ishe ta, kafafuwanta na rike na fashe da wani irin kuka marar sauti.

STORY CONTINUES BELOW

“Anas sake ta”


Kamar umarni mutumen da aka kira da Anas yake jira sai ya sake Amal da sauri ni kuma na rumgumeta, ita kuka ni kuka.

“Kin ce ba ki da abunda za ki ba mu ko? To ni ina da abunda zan ba ki ta so nan zan bar ma mijinki sako, idan ya dawo ki fada masa ya aje mana kudi kamin mu sake dawowa...”


Yana fadar hakan ya mikr tsaye ya nufo inda na ke, da wani irin karfi na rashin imani ya fisge Amal daga jikina ya wulgarda ita kasa ya ja bayan rigar atamfar da ke jikina kamar wata baiwa ya nufi bayan kujerar da sauran suke zaune da ni.

A gurin ya yaga mutuncina, a gurin ya karya martabata, a gurin yai min bakin digon da ban taba mafarkin yi ma kaina ba, a gurin ya tarwatsa rayuwata, a gurin ya gussar da ragegen farincikina, a gurin ya saka min tsoro da fargaba da bakincikin GOBENA. a gurin ya biya bukatarsa ina kuka da  gurnani kamar wance bata taba sanin da'namiji ba a rayuwarta.

Ba badurwa wa ce ni ba balle nai kukan karbar budurcina da yai dai dai nai kukan karbe martabata da farincikina.

Har ya daga daga jikina ya gyara wandonsa ban daina kallon fuskarsa ba, so nake ko yayana na ga wanda ya keta min haddi, ji nake kamar ace ina da ikon cire a lokaci na raba shi da rayuwarsa, hawayen da suke sauko min a lokacin ne suka tabbatar min da kukana be kare ba, bakincikina be gushe ba. Risinowa yai kamar zai sumbanci bakina ya dauki zobensa da ya fadi mai alphabet din A ya saka a saman hannunsa sannan ya bar jikin kujerar ya koma gurin da sauran yan'uwansa suke.1

Ina jin lokacin da suka fita daga falon da kuma tashin motarsa, wasu hawaye masu zafi suka sauko min daga inda nake zaune, ban taba jin wulakanci da kaskanci kamar na wannan ranar ba, ban tana jin na tsani rayuwata kamar yau, ban tana jin kyamar kaina kamar yau ba, na dade ina kare mutunci da martaba da aurena ko babu amman a yau wani wulakantacce marar daraja ya kawar da duk wannan.

  Komawa nai a gurin na kwanta kamar gawa, numfashin da ke fita daga hancina ne yake tabbatar da rayuwata,  zuciyata na zafi da ciwo kamar an saka takobi mai kaifi an yanka ta gida biyu. Sannu a hankali na fara jin numfashin kamar baya wadatar da hancina hakan yasa na bude bakina ina fitar da numfashina a hankali.

Ina jin kukan Amal amman na kasa dagawa na je gurin da take, jikina ya mutu kamar wacce akai wa allura, wayata ma dake kitchen ringing take sai dai yau ba ta Amal na ke  ba balle wayar. Kukan Amal da ringing din wayata suka ba ni wani yanayi na dabam, yanayin da ya saka ni tausayawa kaina da kuma yata Namra, ina ta auna irin halin da ta tsinci kanta ko kuma wanda zata tsinci kanta a ciki nan gaba...

  Ina kwance a gurin har dare ya raba, a lokacin Amal ta ci kukanta ta gaji ta tayi bachin wahala, sai a lokacin Allah ya kawo min kuzari har na iya rarrafawa na shiga dakina da rarrafe na iss bandaki, ba karfin jiki na kawai abunda na rasa ba har da na zuciya wanda shine silar rasa na jikin gaba daya. Duk yadda nai unkurin mikewa tsaye sai na kasa kamar wacce bata da fafuwa haka na zama, ba ciwo ko nauyinsu na ke ji ba, jin su nake kamar babu su a jikina raunin da ke zuciyata yana sauka har cikin jikina, ba jimin yai ba, amman a yau ina jina kamar cikkakkiyar budurwar da aka fasawa budurcinta.

Allah nai ta ambata a zuciyata, bakina kuma yana da rawa alamar kuka be kara min ba ko ma nace ban fara shi ba, jin jikina nake kamar ba nawa, daker na iya mikewa tsaye ban san abunda ya same ni ba sai zamewa nai na fadi kasa, ban sake unkurin tashi ba, a gurin na kwanta ruf da ciki hawaye na ce min sallamu alaikum har aka fara kiran farko na sallah asuba. A lokacin ne na samu kuzari har na gwada tashi tsaye bayan an zauna na yan mintuna.

Allah kuma ya amincin min na iya kunna hitar da ke bandakin na zauna a cikin tub din na rafka wani uban tagumi, ina ta neman inda hawaye za su fito min na rasa. Sai da na hada ruwan nai wanka na tsaftace kaina sannan na fito na dawo bakin madubin gadon ana zauna ina ta kallon kaina. A zahiri kaina na ke kallo amman a badini GOBENA na ke hangowa ya zata kasance? Miyasa abubuwa mabanbanta suke ta faruwa da ni? Idan na fita daga wannan sai na fadawa wannan? Mijina ne ya fado min a rai! Idan Abdulhamid ya ji zai zauna da ni? Zai cigaba da so kamar yadda yake? Zai kaunace mi mu cigaba da zama kamar mata da miji? Wata kila kuma ya juya min baya waye zai so wani namijin ya kusanci matarsa balle irin wannan da kika fashi? Ban san lokacin da na dauki Vaseline din dake gaban madubi ba na jefi gaban madubi da shi a take ruwan madubi ya tarwatse wani irin kuka mai taba zuciya ya ziyarce ni, sai ga ni a kasa ina kuka da hargagi kamar mahaukaciya, kamar wacce aka tsakala sai na yi saurin tashi zaune ina girgiza.


STORY CONTINUES BELOW

“A a ba zan fada masa ba, wannan sirina ne ni kadai ni kadai ya dace na rufe abuna babu wanda zai sani, ba zan taba fada masa ba, ba zan iya rusa farincikin aurena da kaina ba, ban shirya fuskantar wani kalubalen na rayuwar aure ba a yanzu, ba zan fadi abunda zai saka Abdulhamid ya tsane ni ba, ba zan fada masa abunda zai saka ya kyamace ni ba, ko wannan bakincikin zai kashe ni ba zan fadasa kowa ba, wannan kaddarar Halimatu ce ita kadai”1


Wannan karon a fili nai maganar ina ta karfafawa kaina guiwa, duk kuwa da ina jin wani bangaren na jiki da zuciyar ya son sauya min tunani daga boyewar zuwa fadawa Abdulhamid gaskiya. Wani irin kuzari da karfin hali ya zo min a take nemi rashin karfin na rasa, tawul din jikina na cire na saka doguwar riga na fito falo da zimmar duba Amal sai na samu kaina da duba bayan kujerar na kasa dauke idona daga barin kallon gurin ina ta aina abunda ya faru hawaye na min zuba. Ba tare da tsoro ko fargabar komai ba na fito harabar gidan ina ta kalle-kalle kamar bakuwa, dubun asuba be hanani ganin ko'ina a gidan ba, ba su fasa mana komai ba bayan gate din da suka bar mana bude. Ba tare da tsoron komai ba na nufi gate din na da kaina  na rufe, ba tsoro ba, a yanzu ina jin ko mutuwa na shirya mata balle kuma tsoro. Falo na dawo na zauna na zubawa Amal ido kamar ance min ita ce maganin damuwata, wayar da ke kitchen din ce ta fara ringing cikin sauri na tashi na shiga kitchen din sai na tararda wayar kife a kasa hannu na kai na dauko wayar sai screen din wayar na gani a tsage sai dai hakan be hana ni ganin kiran Abdulhamid ba da sunan da nai saving din numbersa ✨🔐Final choice❤😍 tare da aljanun da nai yi ma sunan kwaliya da su. Samun kaina nai da kasa daukar kiran har ya katse wani ya sake shigowa ya katse sannan sako ya biyo baya.

“Baby na kira tun jiya ba ki daga ba ina son jin muryarki na isa lafiya. Pls ki kula min da kanki”


Ina gama karanta sakon na narke cikin wani sabon kuka na rumgume wayar a kirjina, ina ta jin kamar ba zan iya boyewa Abdulhamid, idan na boye masa ban masa adalci ba.

“Amman kuma idan na fada masa zai yarda? Zai gasgata ni bayan ba su dauki komi ba? Ba su fasa mana gate ba balle kofa, ba su harba bindiga ba balle na ce makota su ne shaida ta?”


A fili na ke ta aiko tambayoyin ina mai jin kamar akwai wani a kusa da ni ya amsa min su. Waya turo su? Da gaske kudin suka zo karba ko kuma daman can mutunci suka zo yagawa? Turo su aka ko su suka turo kansu? Ina suka ji ko suka san cewa Abdulhamid ya samu kudi ko zai samu kudi? Ban ankara ba na ji an tayarda ssallah Asuba hakan yasa nai hanzarin baro kitchen din na dawo dakina, alwala na fara yi sannan na gabatar da sallah asuba, na sani sarai ba kyau kukan da ba na tsoron Allah ba a sallah amman na kasa tsayarda da hawayena har nai sallah na gama, babu komai a addu'a ta sai tarin Allah ya isa da neman tsarin Allah daga shiga wata damuwar.


Misalin bakwai na fito falo jikina na min nauyi kamar ba nawa, gurin Amal na nufa na dubata har lokacin bachi take sai dai jikinta da zafi kamar jiya, hannu na saka na dauke ta na nufo daki da ita kamin na shiga dakin ta farka da kuka tana kiran sunana, amman na kasa amsa mata sai kokarin rabata da tufafin jikinta nake. Wayata ce ta sake ringing haka yasa na aje Amal na nufi inda wayar take, Final choice ne rubuce akan wayar har na yi kamar kar na dauka sai kuma wata zuciyar ta hanani hakan yasa na danna picking na kara wayar a kunne ina hawaye.

“A ka'ida idan kika daga wayata sallama kike fara min cikin nishadi da walwala, sannan gaisuwa ta biyo baya amman yau babu ko daya”


Ya fada bayan ya dauki lokaci yana sauraren numfashina, lumshe ido nai na bude hawaye na sauko min har lokacin ban samu kwarin guiwar fada masa damuwata, idan na fada masa ban san iya halin da zai shiga ba ban san ya zamantakewar aure zata kasance ba! Ban san ya zamu rika kallon juna ni da shi ba.

“Tabbas akwai damuwa a tare da ke matata, sai dai bana da tabbacin damuwar ta rashina ne a kusa da ke ko kuwa wani abun ne dabam, na ji ba dadi gaskiya domin har ga Allah bana son abunda zai bata miki rai a yanzu Haima, bana son wani abu ta zai taba zuciyarki saboda ina matukar kaunarki.....”


Wasu zafafan hawaye ne suka sauko min ban san lokacin da naja dogon numfashi na sauke ba.

“Fada min waya taba ki?”


Ya sake tambaya, sai na girgiza masa kai kamar yana gabana, sannan nai saurin share hawayena.


“Babu komai babu komai I'm fine”


“No you're not pls....”


“Trust me babu abunda ya faru kawai dai ya farka ne jikina babu dadi kuma i miss you so much”


Daga can cikin wayar ina iyo jiyo sautin murmushinsa tare da aje numfashin jindadi a lokaci daya.

“Karki damu yau zan dawo ai ni kaina i miss you alot, fada min me kika ci?”


“Yanzu zan karya ban farka da wuri ba”


“Haima bana son kina zama da yunwa fa, ace har yanzu ba ki karya ba? Pls ki daina haka bana so okay”


“Yes ba zan sake ba”


“Je ki karya zan sake kiranki, i love you”


Kai kawai na iya gyadawa na sauke wayar daga kunne na hawaye na min zuba kamar ba gobe, a hankali na zauna a gurin ina jin wani abun marar dadi yana ratsa zuciyata.

“Wani ya taba ni Abdulhamid wani ta taba maka mata, wani ya keta haddin matarka wani ne ya rusa raguwar farincikina, wani ne ya saka ni a dakin da ake dandana dakin fyade da ke da ke tarbar ko wace mace mai aure ko budurwa wacce namiji ya keta mata haddi, an yi ma yata jiya kuma ni akai yi wa? Right.... ”


“Yes kuma wannan sirrina ne ni kadai babu wanda zai sani be kamata kowa ya sani ba, ko da Mama ce ba zan fadawa kowa ba, ni kadai na sani kuma ni kadai ya kamata na dandana dacin abun daman”


Magana nake da kaina ina ta kokarin karfafawa kaina guiwa. Hawayena na share na mike tsaye sai wasu suka sake zubo min, saurin runtse ido na nai gam  na dantse bakina tareda hannuna na hagu.

“Za ki iya, za ki iya Halima.... ”


Shine abunda na ke ta fadawa kaina kamin na ji muryar Amal tana kwala min kira.Sai da na gyara Amal na gasa mata jikinta sosai da ruwan dumi wanda hakan yasa ta dan kara sakewa har na hada mata tea ta sha ta rike yankan biredin a hannu sannan na shiga gyara ko'ina na gidan.

Duk kuwa da kasancewar barayin ba su mana barna ba ko barin wata alama da zata saka a gane cewar sun shigo cikin gidan ba, ba su balla mana gate ba balle kofa ba su yi harbi ba balle su tafi da wani abun, babu ma wanda zai shigo cikin gidan ya yarda wani ya shigo da sunan sata.+

Sanin cewar Abdulhamid na son sakwara yasa na dafa da miyar agusi, bayan na gama na shiga nai wanka na dawo palo na zauna rumgume da Amal jikinta da dan zafi sai dai ba kamar jiya, ni kuma zuciyata cike da zafi fiye da ko yaushe har bana iya controlling hawayena. Sai daf da magariba Abdulhamid ya dawo sai da na wanke fuskata sannan na fita na bude masa gate, iya kar kokarin da zan iya yi na boye damuwa na yi amman hakan sai ya ci tura saboda damuwar da ke raina a yanzu mai girma ce.

  Tun daga muryata da kin son hada ido da nake da shi ya fara karantar damuwata.

“Kin fada sosai Haima idonki kuma ya kumbura gaba daya ba ki cikin natsuwarki, na fada miki zan taso daga Abuja zuwa nan amman ba ki kira kin tambayi lafiyata ba bayan ba ki saba haka ba”


Cikin rashin natsuwar da kirkirar irin karyar da zan masa na kalleshi ina hade yawu, sai a lokacin na tuna cewar yunin ranar ban saka komai a cikina ba sai ruwa shi ma ba da yawa ba, a rayuwar yau na manta da an taba halittar yunwa a cikin duniyar nan.

“Hankalina ba kwance ba Amal ba lafiya”


“Subhanallahi miya same ta?”


Ya fada yana rufe motarsa ya matsa kusa da ni ya kama hannuna yana murza yatsuna a hankali. Dagowa nai ya kalleshi a maimakon na amsa masa sai hawaye suka sauko min.

“Je ki dauko mayafi na kai ki ki ganta yi sauri”


Ya fada cike da kulawa a zatonsa Amal tana gida ne ba a gidansa ba.

“Tana nan a falo jiya na dauko ta... ”


Saurin sakin hannuna yai ya nufi kofar falo, wanda hakan ya ba ni damar share hawayena na bi bayansa, ina shiga na same shi kusa da Amal zaune yana taba jikinta fuskarsa dauke da murmushi, a hannun kujerar na zauna ina ta kallon bayansa, a zahiri bayansa na ke kallo a badini kuma makomar aurenmu na ke hangowa a tsakanin fada masa gaskiya da kuma boyewa, idan na fada masa zai jure? Zai zauna da ni a haka? Idan ma na boye mi ye amfanin boyewar? Wace iri zan ci?

“Ashe ma da sauki kike ta kuka haka har kin tada min da hankali”


Ya fada yana juyowa ya kalleni ba karamin jihadi nai ba na aron murmushin da ban san da zaman sa a duniyata ba na yafa a fuskata.

“Al-hamdulillah amman dazun jikinta kam akwai zafi sosai, kuma ina ta fargabar rashin fada maka da ban yi ba na dauko ta ka yi hakuri”


“Karki damu ai lalura ce”


Ya ba ni amsar yana maida hankalinsa gurin Amal. Ni kuma na tashi na shiga bedroom cikin rashin kuzari na hada masa ruwan wanka ina mikewa tsaye na ji an rungume ni ta baya.


“I love you so much Haima, kuma na zo miki da albishir In-Sha-Allah ina daf da samu lafiya ko yau kamin na baro Abuja sai da na ga wani likita kuma kwarare ne, ki cigaba da hakuri very soon za ki zama kamar ko wace matar aure”


A hankali na sauke ajiyar zuciya sannan na share hawayena na juyo ina fuskantarsa wasu hawayen na sauko min fuskata kuma da murmushi har na bude baki nai masa magana sai ya rumgume ni a zatonsa hawayen murna ne. Mun dauki lokaci mai tsawo a haka kamin ya sake ni ya shiga wanka ni kuma na fita na hado masa abinci na kawo masa dakinsa.

  Bayan sallah isha'i na fara shirye shiryen mai da Amal gida gurin Mama saboda nasan Amal idan har tana ganina ba zata iya kwana ita kadai ba ko kuma ita da wani ba, kamar yadda nake zaton Abdulhamid ba zai min lamanin kwana shi kadai ba ni na kwana da yata, na yi zaton zai ce na barta ta har na wani lokaci ko kuma gobe amman be ce min komai ba be hanani ba kuma be ce min na kai ta ba.

  Bayan na gama shiryata nai masa magana cewar ya kai ni a motarsa na maida ita gida, ga mamakina sai ya saka hallabiyarsa ya dauko makullinsa ya bude mana mota muka shiga ni da ita, abun ka da yaro sai ta kara lafewa a jikina har da saka hannayenta ta rumgume ni ta bata fuska sosai kamar zata fasa kuka. Ban ce masa komai ba har muka isa gida duk kuwa da kasancewar shi din yana ta min fira sama sama. Wani abun mamaki tun da na shiga gidan Namra ba ta yi na'am da ganina ba, kallo na ma sau daya tai ta dauke kanta bata sake kallon inda na ke ba, Aiman dai na tarar yayi bachi Adnan ne kawai ke kwance tsakar gida rike da karamar wayar Haulat yana kallo. A lokacin da na aje Amal sai ta fara kuka alamar bata son rabuwa da ni da sauri Namra ta zo ta dauke ta ta nufi dakin Inna da ita ba tare da tace min komai ba. Raina ya sosu ba kadan ba, kar dai ace yayana sun fara tunani ko na zabi wani ne na bar su? Babu ubansu a kusa da su kuma ni na na tafi na bar su. Har muka dawo gidan ban sake na yi walwala yadda ya kamata ba, sai dai ko kadan hakan be damu Abdulhamid ba saboda a tunaninsa ina son saka damuwar yara a raina ne.


STORY CONTINUES BELOW

A haka muka kwashe wata uku na saka sakewa da shi kamar yadda muke a da, har ya fara zargi yana tambayar ko dai na fara kosawa da zama da shi ne haka  ne saboda baya iya komai, na fada masa ba haka ba ne amman be yarda ba har ta kai ya fara kokarin gamsar da ni da hannunsa, hakan kuma be kara min komai ba sai damuwa na fada masa bana jindadin yadda nake zaune dabam da yayana ne.


“Ai aure ya gaji haka, yaran ba daya ba ne Halimatu balle a ce a dauko su mu zauna da su, kuma tsakani da Allah ba zan biye miki ba idan har aka dauko yaranta zan takura kuma zan cutu ba dan bana son su ba sai dan irin tsarina kuma na ra'ayina bana son yanayi kin san ni, kuma any how ina iya rumgumarki ko nai kissing dinki idan akwai yara ba zan iya ba”


Ban ce masa komai ba, iya kar kokarin da nai na fahimtarsa ne da kuma yi masa uzuri sai na danna nawa damuwar da kyautata masa zato tun da shi be taba yin yayan ba kuma be saba da su ba na sani shi ba kamar Abdallah ne ba.

“Na san kina hakuri Halimatu na zama da namiji irina mai kamar fanko, shiyasa matsayinki yake da girma azuciya saboda kin yi jihadin da ba ko wace mace ce zata iya ba, ko da kuma kin bukaci rabuwa da ni a yanzu ba zan ga laifinki ba....”


“Na aureka ne saboda ina son ka Abdulhamid, ba aureka dan saboda nai sadaukarwar kawai ba, sai dai son ka ne ya fara gina zuciyata tun farkon fari da soyayyarka ka fara sanin miye so”


Na fada ina kallon cikin idonsa da dukan gaskiyata, murmushi yai ya kai hannu ya shafa fuskata.


“Ina ta saurare ina ta jira.... ina ta tsammani yaushe zan samu lafiya na nuna miki irin son da nake miki? Wata kila nan kusa ne wata kila kuma nesa ne, ban sani ba, ba a sanar min ba, fata kawai na ke yi, sai dai ba zan gushe ina neman taimakonki na addu'a ba da kuma rokon ki kara hakuri da ni har zuwa lokacin da zan samu lafiya, idan kuma lafiyar ta gagara samuwa zan sawwake miki kije ki auri mai lafiya saboda kar na tauye miki hakki, ba burina ne nai ta kallonki a haka ba Halima”


Tausayinsa ne ya nemi gurbi a zuciyata yai kwance, kalamansa suka rasa ni kaunarsa ta kara samu muhallin a zuciyata, murmushin na sakar masa sai ya kama hannuna ya kai saitin zuciyarsa.

“Ina jinki sosai a zuciyata, ina jin kaunarki fiye da yadda kike tunani, dan Allah ki tsare min mutunci, kuma ki rika kula min da kanki ba fata na ke ba amman ina fargabar ranar da wani abu zai faru ace za ki bar ni”


“Ba zan taba barinka ba ban aureka dan na rabu da kai ba”


“Thank you”


Ya fada yana kissing din hannuna. Ni kaina na san Abdulhamid na so na, na san mijina yana kaunarta kuma ina kaunarsa amman na rasa dalilin rashin sakewa da samun farinciki da bana yi a yanzu wanda hakan ke saka shi cikin damuwa.

“Gobe zamu je mu gaishe da Hajiya,ya kamata muje cikin daren nan mu siya abunda za mu rika mata domin da safe zan aje ki can idan zan wuce gurin aiki kuma ba lallai ace lokacin masu super market sun bude ba”


Tashi nai na shiga dakina na canja tufafi jikina a tsakanin shiryawa da na shi be wuce minti ashiri ba ya yan kai sannan mu ka fito, da kansa ya bude min motar na shiga sannan ya shiga mazauninsa ya tashi motar, da mu kai bakin gate sai ya fita ya bude mana gate din ya fita da motar sai kuma ya rufe ta muka kama hanyar jifatu.

Har muka isa zuciyata raya min take na fada masa gaskiya, ko ba komai ai shi mijina ne be kamata na boye masa ba, abunda ban sani ba ashe shi fira yake ta min ban lura ba sai da ya kira sunana.

“Na'am”


Na amsa da sauri a daidai lokacin da kiransa ya dawo da ni hayyacina.


“Me kike tunani?”


“Komai bana na tunanin komai”


Da hannu ya nuna min alamar na bude motar na fita yana ta kallon yanayi kamar mai tuhumar wani abu, a hankali na bude motar na fito kamar wata marar lafiya, a tare muka jera muna tafiya daf da za mu shiga cikin gurin wani mutume mai kama da mahaukaci ya miko mana hannu alamar mu ba shi, da na kalleshi da kyau sai na nemi damuwata ta da tunani na rasa, hankalina ya tashi har na kusan rikicewa. Kabir ne Kabir abokin aikina Kabir din da ya kamu da lalurar saboda ni ashe da gaske abun ya taba kwakwalwarsa, da gaske ya haukace. Ni yake mikowa hannuna yana ta kallona sai kuma ya juya yana kallon Abdulhamid ya mika masa hannu, Abdulhamid ya saka hannunsa aljihu ya ciro dari biyu ya mika masa, sai ya juya ya fara tafiya yana dingishi alamar kafar tasa akwai ciwo ko rauni a gurin.

STORY CONTINUES BELOW

“Haima kuka kike yi?”


A rikice na kalli Abdulhamid ba dan na san abunda ya fada ba sai dan sunana da na ji ya ambata.


“Kabirr...... ”


Na ambaci sunansa ina maida numfashi.


“Kin san shi ne?”


Wannan karo na ji abunda ya fada hakan yasa nai saurin gyada masa kai na juya da sauri fuskanci kofar shiga Jifatu din.

“Kuka fa kike”


Da na taba fuskata sai na ji hawaye masu zafi suna sauko min, da sauri na share hawayena na karasa ciki sai ya biyo bayana, har na yi zaben abunda za mu siyawa Hajiya ban daina hawaye ba, babu yadda ban yi ba dan na tsaida hawayena amman abu ya ci tura. Na riga shi dawowa cikin motar na zauna kamin ya biya kudin siyayyar, a front na zauna ina ta kallon Kabir da ke mikawa masu zuwa gurin hannu idan aka ba shi sai ya koma ya zauna, idan ya hango wani ya sake tasowa, kallonsa be haifa min da komai ba sai bakinciki da kuka mai tsanani? Rayuwarsa da baya ta dawo min, ina ta ganin murmushinsa da kulawarsa a kaina. Mutumen da ke da son kwaliya ga tsafta yau shine a wannan halin? Ina matarsa? Ina mahaifiyarsa? Ina danginsa? Miyasa suka bar shi haka babu kulawa?

Hango Abdulhamid tafe yasa na share hawayena na yi saurin gyara fuskata, gidan baya ya bude ya saka ledar sannan ya dawo mazauninsa ya tashi motar, har muka isa gida be ce min komai ba yana farkin na bude motar na fita ina shiga falo wani sabon kuka yai min lale marhabun hakan yasa na nufi kitchen da sauri na wanke fuskata.


“Ba zan hana zuciyarki tausayin wani ba, amman yana da kyau idan za ki ji tausayinsa ki yi a bayan idona ba gaban idona ba, na ji zafi sosai Halima ace hawayen nan saboda wani namijin kike zubar da su ba ni ba, abunda ba ki taba sani ba shine ina da tsananin kishi, ina kishin ace matata ta kula wani ba ni ba, I'm sorry to say yaran nan ma idan na tuna ba da ni kika haife su ba ina jin babu dadi, saboda ina tsananin sonki kuma ina kishinki, na san idan nai shiru zan cutu ne kuma na kwari kaina ke kuma kin kasa gane haka....”


Magana yake min a yayinda yake tsaye a kofar kitchen din yana kallon bayana ni kuma ina kallon windows din kitchen wasu sabbin hawayena na sauko min. Ban yarda na jiyo ba har sai da na ji motsi ficewarsa daga kitchen din, sannan na dawo dakina na shiga bandaki nai kuka mai isa har sai da na ji amai ya taso min sannan na sassautawa kaina, sai dai ban samu salama ba har sai da nai aman sannan na hada ruwan nai wanka na shirya cikin kayan bachi na hau gadona na kwanta, a yanayin yadda ya nuna min bacin ransa ban yi zaton zai zo dakina ba, domin haka Aminu yake min a duk lokacin da muka samu tsabani, sai dai a mamakina sai ga Abdulhamid ya shigo dakina ya kwanta bayana yana sumbatata ya saka ni a kirjinsa ya rumgume ni sosai.


“I Love you”


Shine abunda na san ya rada min a kunne kamin bachi yai gaba da shi, ni kan har kusan biyu saura na dare ban yi bachi ba, babu komai a duniyata sai tunani da damuwa. Kiran sallah farko muka farka shi ya tafi masallaci ni kuma na nai sallah a gida, Misalin takwas muka karya sannan na shiga nai wanka shi ma ya shirya muka fito da zimmar zai aje ni gidan Hajiya ya wuce gurin aiki, ya lura da yadda na saka sakewa tun jiya damuwa karara a fuskata sai dai be min magana ba har muka isa. Tare muka shiga cikin falon sai muka same Hajiya zaune a kujera daya ita da Abdallah, tun da na kalleshi sau daya ban sake kallon inda yake ba har na zauna sai dai jikina yana ta ba ni cewar idonsa na kaina, ni kam na manta when last na saka Abdallah a idona ma dan ni har na manta da shi a duniyata.

“Hajiya ina kwana”


Ya mika mata gaisuwa ina dan risinawa, sai tai kamar bata ji ba ta maida hankalinta gurin Abdulhamid da ke magana da Abdallah.

“Lafiya kake karyawa a nan”


“As you know ko Madam tana nan ina karyawa a nan ai balle yanzu da tai tafiya”


STORY CONTINUES BELOW

Yadda Abdallah ya amsawa dan'uwansa sai da abun ya ban mamaki domin babu alamar shauki ko wani far'a a tare da shi.


“Matarsa bata nan taje Kaduna gurin biki”


Hajiya ta amsawa Abdulhamid, sannan ta kalli inda nake ta dauke kai kamar ta ga wata makiyiyarta.

“Hajiya ina kwana”


Na sake miki mata gaisuwa,wannan karon ta amsa amman sai da ta dauki lokaci, ban damu ba daman tun da na auri Abdulhamid na lura da Hajiya kamar bata na'am da ni, ledar siyayyar da muka mata na tura mata gabanta sai kawai ta kalli ledar ta mike tsaye ta nufi dakinta tana fadin.

“Kai ma ka karya ko na kawo maka abun kari”


“A a ni kam sai da muka ci abinci muka fito gida”


Ya fada yana kallona da murmushi a fuskarsa, ni ma murmushi nai masa kamin na maida dubana gurin roben da ke saman glass table din da Abdallah ya aje mug din hannunsa. Farin zobe ne mai kamar na silver da alphabet din A a ciki, alphabet din baka kamar na wacan zoben da na gani a daren bakinciki.

“Kin ji sai na dawo zan zo na dauke ki”


Abdulhamid ya fada min haka bayan ya mike tsaye, kai na gyada masa sai ya shiga dakin Hajiya yai mata sallama ya fice, kamar fitarsa na ke jira nai saurin kai hannu na dauki zoben da ke aje, da sauri Abdallah ya miko hannunsa fuska a hade ya rike hannuna.

“Ba ni zobena”


“A ina ka same shi?”


Nima na tambaya rai a hade cike da tsananin mamaki, a maimakon ya amsa min sai kawai ya watsa min wani kallo da ban san ma'anarsa ba, tunani be tunatar da ni cewar a falon Hajiya muke ba, ban kawo a raina cewar Abdulhamid zai iya dawowa ba, ban damuwa da rikon hannu da karfi da Abdallah yai ba saboda hankalina ya dauku akan zoben da son sanin dalilinsa, daman ya san za mu zo da har yasa ya cire zoben ya aje a inda zan gani ko dai na yi gamda da katar din ganin ne? Motsi muka ji daga bakin kofar shigowa falon alamar za a shigo hakan yasa yai saurin sakin hannuna ya sake miko min dayan hannunsa.

“Ba ni na ce”


Ya fada a tsawace wanda hakan yai daidai da shigowar Abdulhamid a falon.


“Minene?”


Ya fada yana kallon yanayi da nasa. Da sauri na saki zoben ya fadi kasa shi kuma ya mike tsaye ya kai hannu ya dauka ya fice zuwa dakin Hajiya, a sannan Abdulhamid ya karasa kusa da ni ya miko min wayata yana kallon fuskata.


“Ga wayarki”


Ya miko min yana aje mumfashi a hankali sannan ya juya ba tare da ya sake ce min komai ba ya fice, dafe kaina nai gabana na mugun faduwa, faduwar da ba ban san ta Minenen ta fargabar kar ya zargi wani abu ko kuwa ta fargabar ganinmu ko kuma ta fargabar zoben da na gani a hannun Abdallah?
AHMAD POV.

Kansa a kasa yake sauraren Momy, idonsa sun rikide gaba daya saboda bacin rai, ta ya yanzu Momy za ta zo masa da wannan maganar? Wani irin magana ce wannan wacce hankali ba zai dauka ba, taya zata hana shi auren wannan saboda kawai ita Shuwa ce?

“Wallahi ance mallake miji suke ni sam ban yarda ka aureta ba ka nemo mata”


Dagowa yai ya kalleta cikin tsananin bacin rai da damuwa.


“Amman tun farko da na fada miki family yarinyar na fada miki wacece ita ya kamata ki hana ni ba sai yanzu da yar mutane ya kamu da so na ba, har na gaisa da mahaifita sun yi magana sun ce na turo magabata sannan ki kawo wannan maganar haba Momy wannan na reason ba ne.... ”


Zare masa ido tai ta wurgarda remote din tv a kujera.


“Idan a gurinka ba komai ba ne, ni a gurina komai ne, ba zan bari ka auri yarinyar da zata mallake min Kai ba, ka juya min baya ni da Baby Namra ba zai yiyu ba”


STORY CONTINUES BELOW

Tana kai wa nan ta mike tsaye ta nufi upstairs tana fadin.


“Ai dole ne idan za ayi aure ayi bincike ba zan yarda ka auro min yarinyar da zata canja ka ba, ko wacce zata zo ta kashe ka ta kwashe dukiyarka ba, mata ba abun yarda ba ne musamman na yanzu.... ”


Tana shigewa dakinta, kanwarsa ta taso ta dawo kusa da shi ta zauna tana masa rada.

“Wallahi ka kai je ka kaita gurin wani boka ayi mata asiri ta yarda ka auri wannan yarinyar... ”


Duk yadda yake cikin bacin rai sai da ta saka shi murmushin dole saboda wautarta, sannan ya mike tsaye yasa hannuns aljihu ya fice daga falon harabar gidan ya fito ya jingina da motar yana cikawa bakinss iska ya san halin mahaifiyarsa idan ta ce bata yarda da abu ba, babu yadda za ayi ta yarda da shi har abada, idan kuma bata son abu babu mai cilasta ta so shi, shi yanzu ya zai yi da matsalarsa a duk lokacin da ya taso da maganar aure sai ta nuna bata so, ya kasa fahimta wace irin uwa ce ita? Miyasa ko da yaushe take kishin ganin yayi aure? Ko take kishin duk matar da ya aura? Forget about the past shi yanzu ya zai yi da yar mutane idan ya barta za a ce ya yaudareta daman can ba auren yai niya ba, after that idan ya nemo wata ita ba Momy zata iya cewa tana da wata matsalar. Kansa ya daga yana kallon katon gidan mai cike da kayan alatu, mi mahaifiyarsa ta nema ta rasa? Then miyasa shi ba zata bar shi ya samu nasa farincikin ba? Miyasa ba zata bar shi ya gina rayuwarsa ba? Kara wayar da ke hannunsa tai alamar sako number Momy ce.


_Ka dawo karfe 8pm_


Yana karanta sakon ya shafa kansa yana busar da iskar bakinsa.

“Ohhh Momy ni fa ba yaro ba ne why all these rules?”


Bude motarsa yai shiga ransa babu dadi yai ma motar key ya danna horn aka bude masa gate ya hau titi ba tare da sani inda zai je ba, gari yake ta zagawa a titi, maganganun Hajiya ne suke ta masa yawo a kai shi ya rasa gane abunda yake damun mahaifiyarsa. Har ya daga wayarsa ya kira abokinsa wanda ya saba labarta masa damuwarsa sai kuma wata zuciyar ta hana shi, he decided ya faka motarsa gefen titi yai relaxing cikin motar for a while sannan ya koma gida, after ya faka motarsa gefen titi ya sauke gilashin motar ya kwantar da kujerar motar tare da cire hular kansa.

  Wata yarinya ya hango gefen titi tana kuka, sai da ya kalli ko'ina yaga babu kowa a tare da ita sannan ya bude motar ya fita ya nufi inda take.

“Ke lafiya? Me kike yi ma kuka?”


“Bacewa nai”


Ta amsa masa cikin kuka.


“Garin ya?”


“Muna tare da Mama Hafiza mun zo biki shine kuma yanzu ban ganta ba, tace na zo bakin titi na same ta mu wuce na zo ban ganta ba kuma na koma ban gane gidan da na fito ba”


“Ina Mamanki?”


“Tana can gidanta”


“Babanki fa”


“Ban san inda yake ba”


“Rasuwa yai?”


“Aa tunda ya saki Momy mu ban sake ganinsa ba, ita kuma Momy mu ta auri wani...”


The way da tai masa maganar sai ta bashi tausayi, ya san da ace tare take da mahaifiyarta ko mahaifinta ba zai su tafi su barta ba ko kuma su yi saken da zata bata, risinawa yai yana kallon fuskarsa.


“Miye sunanki”


“Namra”


“Wow cute you sunan yata, yanzu za ki iya gane gidan ku?”


Ta girgiza kai alamar no.


“Wace unguwa kike zaune?”


“Yan magurora”


“Gurin wa?”


“Karkar mu”


“Ita ke rikonku?”


Ta gyada masa kai.

“To yanzu kin san yadda za mu yi? Zan saka ki a motata na kai ki gidanmu da safe sai na kai cigiyarki, ko kuma naje unguwarku na nemi nai unguwar na damka masa ke kin yarda”


A take ta gyada kai sai ya rika hannuta ya nufo motarsa da ita ya saka ta shi ma ya zagaya ya shiga.

“Ita Mamanki wane unguwa take?”


“Ban san sunan unguwar ba”


“Ba ki taba zuwa ba?”


“Na taba zuwa sau daya”


“Sau daya?”


Ya tambaya yana kallonta da mamaki sai ta gyada masa kai.

“Miyasa sau daya kawai?”


“Kaka tace mana wanda ta aura baya son yara shiyasa bata tafi da mu ba”


Tabe baki yai yana yi ma motar key.

“Ji wani irin selfishness dan Allah mutum be son yara kuma ka yi aure ka tafi ya bar su, yanzu nan idan ni bana kwarai ba ne shikenan kin fada mugun hannu mtsszzzzzzzzzzzzzzzzz”


Yaja wani dogon tsaki yana jin kamar ace shine uban yarinyar ya ci mutunci uwar, ko da yake shi miyasa uban ma ya bar su hannunta.

“Imagine ayi ta haihuwa bana iya kula da yara ko ba a son dawainiya da su, shi uban baya so ita ma bata so”


Ya fada yana mai jin haushi iyayen duka biyu.

‘Ba ma gidan uban da zan kai ki cigiya, idan suna son ki su nemi ki da kansu’


Wannan karon a zuciyarsa yai maganar. Sannan ya cigaba da tuka motar, abun da yaro ta man ta sha kuka ta koshi kamin ya isa gida har ta yi bachi. After yayi farkin ya zagayo ya bude motar yana kokarin daukarta ya dora a kafadarsa ta farka, sai dai hakan be hana shi daukarta ba ya nufi cikin gidan da ita, kamin ya karasa Baby Namra ta fito daga falon tana masa oyoyo.

“Daddy sannu da zuwa”


“Yauwa Baby”


Ya fada yana shafa kansa da dayan hannunsa tare da murmushi.

“Daddy wacece wannan?”


Ta tambaya tana kallonsa be amsa mata ba sai da ya shiga falon Hajiya ya sauke Namra saman kujera.

“Je ki kawo mata ruwa ta sha, kawa na samo miki”


Sai ta bata fuska.


“Ni Allah ya tsare ni ba kawata ce ba”


Ta fada tana nufar hanyar kitchen, shi kuma yai murmushi yana kallon Namra wacce ta takure guri daya kamar mai jin tsoro, shi sai yanzu yake ganin kamar ma ya taba ganinta.

“Ina ka samo ya?”


Hajiya da ke tsaye upstairs tana latsa waya ta tambaya daga can inda take tsaye tana kallonsa.


“Wasu mahaukatan iyaye ne da ba su san darajar yaya ba suka jefar da ita”


“Jefarwa kuma?”


Hajiya ta tambaya tana saukowa daga stairs din.

“Yes”


Ya amsa mata yana maida dubansa gurin Baby Namra wacce ta fito kitchen rike da kofin ruwan.

Labarin GOBE NA ba labari irin wanda na saba yi ba, shiyasa tun kamin na fara sakinsa na fada muku cewar rayuwar aure ce mai cike da kalubale, idan ba ku manta ba inkiyar labarin ZAWARCIN HALIMATU, labari ne na rayuwar kala kala ta gidan aure da zawarci, da kuma rikon yara da kula da tarbiyarsu, zancen dan Allah Candy kar ayi kaza ko ki canja kaza be taso ba, matukar ana son labarin ya tafi a yadda aka tsara kuma a isar da sakon da ake son isarwa.+


GOBE NA ba labarine na zallar soyayya ba, yana tafe ne da kalubalen na rayuwa, duk irin halin da Halimatu take ciki ko zata kasance a ciki akwai mata da yawa da suka dade da shiga cikin wannan halin, ko suka fita shiga matsala ma. Wallahi a three weeks ago akwai wacce ta kirani tana kuka tana fada min abunda akai wa Namra a labarin haka akai wa yarta kuma har yau babu wanda ya sani mijinta ya hanata magana, secondly mijinta kamar Aminu yake, a lokacin da ta ba ni labarin mijinta sai da kaina ya daure Wallahi. So akwai mata da yawa da suke fuskantar rayuwar gida aure kala kala, ko da ba mu tabo duka ba ya kamata ace muna taba wani bangaren na rayuwarmu ta yau da kullum ai.


Labarin zai tafi a yadda na tsara shi ga wanda yaji zai iya bi fine.

                   ***       ***      ***


“Aa Gwarzo wace uwar ce zata jefar da yarta haka nan kawai? Ka taba ganin bolar yaya?”


Momy ta fada bayan ta zauna tana kallon Namra.

“Oh Momy ba ki ji inda na samo ta ba, uwarta na son ta zata jefar da ita”


“Idan ma haka ne ai ba laifi uwar ba ne, na uban ne akan me zaka bar yarinya na tsawon lokaci ba ka neme su ba? Taya ma zaka bar ma mace dawainiyar yara bayan ba da su ta zo ba?”


“Ita na fa uwar da laifinta”


“Baka san abunda ya fito da ita daga gidan mijin ba, ba duk  mace ce bata son yaranta ba ni ban yarda akwai mace da bata son yaranta ba, wata kila ma hankalinta yana can tashe”


“Ko dai zan maida ita sai gobe sai jikinsu ya fada musu, ko goben ma sai da maraice”


Ya fada yana shafa kan Namra.


“Yarinya kyakkyawa suna son wufintar da ita”


Momy ta yi murmushi.

“Ya sunanki?”


“Namra”


Ta amsa hankalinta kwance kamar ta san su.

“Allah sarki Baby Namra kin samu takwara”


Baby Namra dai bata komai ba sai wani shigewa take jikin Momy.

“Sai gobe zan bada cigiyarta a radio idan sun ga dama su zo nan su dauke ta”


Ya fada yana mikewa tsaye. Sai ita Namra ta mike tsaye zata bi shi.

“Zauna nan Momy zata kula da ke”


Momy ta mika mata hannu tana murmushi.

“Zo nan jikata yar albarka”


Ba musu taje ta zauna saman kujerar sai Momy ta dorata a kafafuwanta.

“Ajikin nawa?”


“Uku”


“Wace makaranta kike?”


“Gwarzo International school”


Momy ta yi dariya, Ahmad ma da ke kokarin fita juyowa yai ya kalleta.

“Wow i feel it tun farko na ji kamar ina da alaka da ita, ashe yarinya yar makarantar mu ce shiyasa take da natsuwa”


Ya fada yana wani miskilin murmushi. Momy dai ta girgiza kai tana kwantar da Namra a ciyarta.

STORY CONTINUES BELOW

“Idan kuma iyayenki sun ba mu ke sai mu rike abar mu mun kara samun wata daman ina son yara”


“Da gaske?”


Namra ta tambaya Momy ta gyada mata kai.


HALIMATU POV.

Ban samu wani sakewa da ya kamata ko wace matar da ta yi a gidan uwar mijinta ba, saboda ban ga fuskar Hajiya ba, kamar wata bakuwa haka na zama a cikin gidan.

Har aka kira azahar babu komai a zuciyata sai tunanin dalilin tsanar da Hajiya tai min daga auren dan ta zuwa yanzu amman ban samu dalili ba, a iya tunani wanda ya ce yana son naka ya gama da kai ko da kuwa Abdulhamid yana da lafiya kamar kowa ballanta ta san yadda lalurar danta take amman na amince a haka na ce zan zauna da shi a kalla na cancanci girmamawa da ganin mutuncin da kauna daga gareta. Amman ban samu haka ba sai wulakanci da tsana da suka boyo baya bayan a baya kuma ba haka take min ba.

Wata kila kuma jinina ne a haka domin Hajiya ma mahaifiyar Aminu da kanensa basa kaunata saboda gani suke na tare komai na mallake musu dan'uwa wata kila ita ma tana min wannan kallon ne.

   Bayan na shiga bandakin tsakar gidan nai alwala na yi sallah a saman dankwalina, ban jira ta ce min na shigo ciki ba,kamar na san ba zata ce na shigo din ba domin ko ruwa bata ba ni ba, abincin rana ma da aka gama kanen Abdulhamid ne suka kawo min.

Ina zaune ina lazimi da hannuna Abdulhamid ya kira cikin sauri na daga  kiran domin duk na tsawwala da zaman gidan na yi zaton zai fada min na fito mu tafi ne kamar yadda yace zai dawo ya dauke ni.1


“Aiki ya min yawa Haima, sai da la'asar zan zo daukarki”


Bana son na kara zama gidan ko da na minti talati ne a yanzu hakan yasa nai saurin yi masa requesting.


“Ko na tafi gidan su Hajara kamin ka zo? Ba nisa sosai daga nan zuwa can daman tana ta min complain wai ban je gidanta tun da nai aure”


“Bana son ki hau achaba”


“Napep zan hau”


“Okay sai kin dawo”


“Na gode”


Har dakin Hajiya na shiga nai mata sallama ta amsa min ciki ciki, na fito raina babu dadi na nufi gidansu aminiyata Hajara, har ga Allah ban jidadin yadda mahaifiyar mijina take min ba, domin ni mace ce mai son dace da uwar miji yadda yake ganin wasu iyayen mijin suna nunawa surukansu kulawa abun har burgeni yake amman ni na kasa samu a aurena na farin a wannan ma ban dace ba.

    Na isa gidan a Napep kamar yadda na fadawa Abdulhamid, sai dai ban jidadin samun mijinta a gidan ba, domin kunyarsa na ke ji tun daga lokacin da ya nuna yana son ya aure. Da sallama na shiga shi ya fara mika min gaisuwa sannan na zauna saman cushion dinta shi kuma ya tashi ya fita.

“Amarya ba kya laifi yau an tuna da mu”


“Kullum ai kina cikin raina”


“Ni ai fushi na ke da ke ni da nai miki kyautar miji sukutun kika gujemu kika kama dan'uwanki”


Ta fada bayan ta dire min kofin ruwa, murmushi nai sai na maida kaina kasa ina kallon carpet dinta.

“Kawata kamar kina cikin damuwa”


Dagowa nai na kalleta ina ta tunani ta ina za ki fara dora mata bayani.


“Ina ciki ba daya ba ma, amman naga kamar Abban Afrah na nan....”


Rufe bakina ke da wuya muka ji tashin motarsa, sai ta tashi ta sakawa kofar key sannan ta dawo kusa da ni ta zauna tana kallona cike da damuwa.

“Ban san wane zan fara fada miki ba, tsanar da mahaifiyar Abdulhamid tai min ko kuma ganin Kabir da nai a titi yana yawo a haukace? Ko fyaden da akai min, ko kuma son yayana da Abdulhamid ba yayi?”


STORY CONTINUES BELOW

Ina maganar hawaye na sauko min, rikicewa tasa ka ta kasa ce min komai, har na wadansu dakiku.


“Halimatu akai miki fyade ko kuma wanda akai wa Namra kike magana?”


“Ni dai akaiwa”


“How, when? Waya miki fyade?”


“Ban sani ba Hajara shi nake kokarin sani yanzu, kaina gaba daya ya kulle”


“Fada min yaushe abun ya faru?”


Ban boye mata komai ba tun daga a to z ganin ita din ta zama kamar yar'uwata, kuma daman can ina bukatar abokin tattaunawa.

“Amman miyasa kika boye masa Halima? Miye ribar boyewar? Mijinki ne kuma shi aka zo nema da ba a tararda shi ba akai miki haka ai ya kamata ya sani”


“Hajara kina ganin idan na fada masa zai zauna da ni? Ba zai iya zama da ni ba, na ji kuma na gani da yawa akwai matan da suke fansar ran mazajensu a yi mu su fyade saboda kar a kashe mazanjensu daga karshe mazanjen su rabu da su su kasa zama da su, babu namijin da zai ji anyi ma mace fyade tana a gidansa kuma ya cigaba da zama da ita, ballanta Abdulhamid da baya iya komai da mace”


A firgice ta kalleni.

“Kamar ya baya iya komai?”


Tun daga farko nai mata shimfidar labarin har zuwa auren mu.

“Amman Halimatu kin yi wauta, akan mi za ki auri miji kamar wannan? Ba ki san za ki iya jefa rayuwarki cikin hatsari ba?”


“Na riga na raba tun a gidan Aminu yana da lafiya amman sai mu kwashe wata hudu uku har biyar be neme ni ba, shi ma da yake da lafiya na daure balle wannan?”


“Ba daga nan take ba, a can baki da kwanciyar hankali, a nan kuma hankali a kwance yake za ki ci ki koshi dole wata rana ki ji kina bukatar mijinki a kusa da ke, bayan rashin lafiyar na Halimatu mutumen baya son yara kuma kika aureshi a haka, and kin san dan'uwansa yana son ki kuma kika take hakan kika aure shi? Fada min taya mahaifiyarsa zata so ki wata kila ita din ta san dan'uwansa yana son ki amman kika zabi ki auri daya ki bar daya, wanda be dace ki yi haka ba tun daga farko”


Hannu na saka na rufe fuskata ina kuka a hankali.

“Ki fada masa gaskiya na san ba zai gujeki ba, duk namijin da za ayi ma wannan Sadaukarwar ba zai taba gudunki saboda wannan ba, musamman idan yaji cewar shi aka zo nema”


“Idan kuma ba shi aka zo nema ba fa Halima? Idan wanda yai min fyade ya zo ne saboda kawai yai min fyade fa?”


“Akwai wanda kike zargi?”1


“Dan'uwansa?”


Ta yi saurin rufe baki tana kallona.

“Ya taba miki maganar banza ne?”


“Be taba ba, amman zoben da na gani a hannun mutumen da ya min fyade yau na ganshi a gurin Abdullah har na kai hannu na dauka ya ce na bashi”


“Amman daman can yana da dabi'ar neman mata ne? Kuma jiya kawai kika gan shi da zobe?”


“Ban san shi da wannan dabi'ar ba, ko a lokacin da yake ta son na kashe aure be taba min maganar banza ba, ni ban taba lura da hannubsa ba balle har na tantace kalar zobensa, amman ba a shaidun mutum kuma yanzu yana ganin na auri dan'uwansa babu yadda zai yi”


Hannu ta kai ta dafa kafadata.

“Ki kyautata masa zato Halimatu ganin zobe kawai ba zai tabbatar da cewar shi din ne ba, ba ayi ma mutum daya zobe kuma idan har shi din ne mi zai saka ya aje zobe a inda za ki gani? Mi ma zai saka ya nemi yi ma matar dan'uwansa fyade? Dan'uwan ma twin brother? Haba Halimatu”


STORY CONTINUES BELOW

“Zai iya mana ko kin manta abunda Sadi yai ma Namra?”


“Saboda Sadi ya lalata diyar yayansa ba shi yake nufin Abdallah yai ma matar yayansa fyade ba, duk yadda duniya ta lalace akwai na gari, duk kuma yadda duniya take ciki da mutane kirki dole akwai bata gari, karki saka ranki a rudu ki sake janyo wata matsalar a tsakanin yan'uwa, ni yanzu abunda na ke so da ke ki shirya gobe zan zo na rakaki kije asibiti a duba lafiyarki domin irin waennan mutane wani lokacin baka san ko suna dauke da ciwo ba, kuma baki sani ba ko ciki ya shige ki tun da abun ya faru ya kamata kije ayi miki wankin mara”

A take hankalina ya tashi da Hajara ta kawo min maganar ciki, dacan ban kawo hakan a raina ba hankalina ya karkata ne a gurin fyaden kawai ba dan kuma na san bana iya daukar cikin ba, lallai na zama doluwa wani lokacin haka nake abu kamar marar kwakwalwa kuma marar ilmi, tabbas idan nai ciki na shiga uku kuwa.

“Yaushe rabon da ki ga al'adarki? Idan ma akwai cikin ai za ki gane”


“Bana iya ganewa saboda ina wata shida ban yi al'ada ba wani lokacin biyar, idan ina al'ada akai akai sai idan ina shayarwa, shiyasa na ke saurin daukar ciki idan ina shayarwa, amman bana jin wata alama da ke nuna ina da ciki bana jin komai a yanzu”


“Duk da haka muna bukatar zuwa asibiti saboda cire kwankwanta, ai wani cikin sai ya fara girma yake wahalarwa kin manta cikin Adnan? Shi da ma yake cikin farin amman ba ki sha wahala kamar sauran ba?”


“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”


Shine abunda nai ta maimaitawa na dafe kaina ina kuka.

“Ki kwantar da hankalinki Halimatu, akwai mata da yawa da aka ketawa haddi ba ke kadai ba, wasu ta dalilin wani abu kalilan, ba ke kadai ce a cikin wannan halin ba, amman shawarar da zan baki ki fadawa mijinki gaskiya idan ma ya zabi rayuwa da ke ai ba akanki farau ba”1


“idan na bar wannan gidan auren Hajara ban san ina zan sake shiga ba, ban san wa zan fadawa ba, a can mi zan tarar, idan kuma na zauna zaman gaban iyaye ba dadi da shi ba ko ga budurwa balle a gurin mai yara kamar ni, bana son a fara kirga min aure Aminu ma idab ya samu labari ai zai ce gashi nan har aurena ya mutu tun ba a je ko'ina ba, zaman zawarci ba shi da dadi Hajara dan zaman da nai na iya sakin da Aminu yai min zuwa auren Abdulhamid ban jidadin ba ga natsatsin iyaye, ga lalurar yara tun da mahaifinsu babu ruwansa da su, bana son na fadawa Abdulhamid wannan abun ya sake ni saboda haka, idan ma har na samu cikin zubarwa zan yi a sirrance na cigaba da zama da mijina, ina jindadin Abdulhamid kuma ina son sa bana son shiga wata matsalar a yanzu, idan na fada masa ba lallai ne ya yarda ba, saboda ba ni da wata shaidar, wata kila ma ya zargi cewar na kasa tsare kaina ne na kasa hakuri shiyasa na aikata hakan yanzu kuma nai masa wannan karyar, tun da Allah ya rufe min asiri kara na rufewa kaina ko na samu salama”


Kai ta gyada min tana share hawayenta.

“Hakan yayi idan ma kin samu cikin ki zubar kawai mu rufe wannan sirrin, Allah ya dafa miki ya rufe mana asiri”1


Jinginawa nai da kujerarta ina jin zuciyata na wani irin kona marar misaltuwa.

Hajara ta yi ta saka min maganganun na kwantar da hankali da karfafa guiwa a gareni har zuwa lokacin da Abdulhamid ya zo daukarta, ba ni kadai ba shi kansa na lura kamar baya cikin walwala sosai, ni da shi mukai shiru cikin motar kamar wasu kurame ni da abunda nake ta sakawa a zuciyata shi kuma yana ta tukinsa yana kallon titi.

Daf da za mu isa kiran Mama ya shigo wayata, ba tare da tunanin komai ba na danna picking na soma magana cikin muryar da ke karantar damuwarta ga mai saurarenta.


“Hello Mama”


“Halimatu Namra na gurin?”


“Aa tace aka kawo ta ne?”


“Aa mun dauka ko taba nan ne, Teema taje gidanki bata tararda kowa ba”


“Eh mun fita ne tun safe lafiya”


“Namra ce ba a gani ba tun jiya”


Kamar saukar aradu haka na ji maganar ban san lokacin da na ambaci sunan Ubangijina da karfi ba, wanda hakan yasa Abdulhamid kallona da sauri.

“Kamar ya ba a ganta ba? Ina ta shiga? Waya fita da ita?”


“Tare da Hafiza suka je biki wai Hafiza tace ta same ta bakin titi bata zo ba, kuma taje gidan bikin ta duba bata can sun jiya muke ta nemanta har makarantar anje bata can”


“Amman tun jiya Mama ba a fada min ba?”


Na tambaya idanuwa na kawo ruwa.


“Wallahi saboda tsoron kar hankalinki ya tashi ne yasa ba a fada ba”


Sauke wayar nai ina kuka ina jin wani irin tashin hankali na ratsa ni marar misaltuwa har gumi karyo min yake.

“Lafiya?”


“Namra ta bata”


“Subhanallahi garin ya?”


Ban iya ba shi amsa ba saboda kukan da ya ci karfina.

“Yi hakuri za a ganta In-Sha-Allah bari na sauke ki gida yanzu”


Ya fada yana miko min tissue.DEDICATED THIS PAGE TO Mai Dambu, Allah kara miki lafiya Gwanata❤ son so Fisabilillahi💞😍

                  ***        ***      ***


Kamin mu isa gidan har wani jiri nake jin yana dibana, zuciyata kam kamar ta fashe ga wani uban zafi da kirjina ke yi, kaina sai sarawa yake.

   Ko parking din kirki be yi ba na bude motar na fita na shiga cikin gidan cikin tashin hankali kamar yadda su ma na tararda su cikin tashin hankali, gaba daya ban tarardar yan mata gidan mu ba da samarin biyun duk sun fita neman Namra Baba na tsakar gida rike da sandar damuwa kara a fuskarsa. A bakin balcony na zauna na dafe kaina. Inna na min bayanin yadda abun ya faru da guraren da aka je nemanta bata can. Mahaifinta ne ya fado min a rai.+


“Ko Aminu ya dauke ta ba a sani ba?”


Na fada ina kallon Mama, a yayinda Abdulhamid ya shigo yana gaisawa da su.

“Mi zai saka Aminu ya dauke ta, mutumen da tun da ya bata baya be sake dawo ko tambayar lafiyarsu ba”


Cewar Inna sai Mama ta karba mata.

“Nima dai shi na gani, kuma a ina ma zai ganta?”


“Ko tana gidan Abdallah?”


Na fada ciki ina hawaye.

“A a bata can tun dazun da shi ake ta nemanta, shi ma yace kar a fada miki saboda kar hankalinki ya tashi, yanzu yanzu ma suka fita da Samira har.... ”


Baba ne ya tari numfashin Inna da ke maganar yana fadin.

“Ku ba Allah cigiya In-Sha-Allah za a ganta, idan ba dan sake irin na Hafiza ba taya zaka fita da yaro ka ce ya same ka titi bayan yaron be san gurin ba”


Komawa nai na zauna a gurin na fara rare musu kuka, idan ba kukan ba ban san abunda zan yi a yanzu ba.


“Bari naje na duba makarantarsu...”


Cewar Abdulhamid yana kokarin juyawa sai Inna tai karaf tace.

“Ai har can Abdallah ya tafi....”


Baba ya sake saurin tarar numfashinta.

“A a be je can ba, islamiyarsu dai yaje, zaka iya zuwa can ka duba”


Sai da Abdulhamid ya fice sannan Baba ya hau yi ma Inna fada wai ta cika tsoma baki a maganar da babu ruwanta. Ni kam sam ban ga illar maganarta ba kamar yadda ita ma kanta da Mama ba su ga haka ba, wata kila kuma akwai abunda Baba ya hango.

“Mama zan je gidansu Aminu na duba ko tana can”


“To da Abdulhamid din be wuce ba ai sai ya karaki”


“A a shi yaje can din ni zan duba gidansu Aminu”


Na bawa Mama amsar ina mikewa tsaye.


“Mi zai kaita can ma”


“Nema ne ai Mama”


Ban tsaya na jira su kara kashe min jiki ba na zari jakata na fito cikin gidan kamar wata mahaukaciya. Kamin mai napep din na kai ni gidan su iyayen Aminu har na matsu abunka da wanda je cikin tashin hankali. A bakin gate ya tsaya ni kuma na shiga cikin gidan da sallama. Kana gani na kasan hankalina ba a kwance yake, ba Hajiyar Aminu ba ko kanensa sun yi mamakin ganina a cikin gidan, ban musu magana ba kamar yadda suma suka saki ido suna kallona kamar wata bakuwarsu. Har cikin falon na shiga na gaishe ta ita ta amsa min da dan mamaki sannan na tambaya ko Namra tana nan.

“Namra da kuka kekashe kasa ke da yan'uwanki kuka ce ba za ku bayar ba, bayan kun gama ikirarin an bata ta mi za mu dauko ta tai mana? Ai mun yafe miki ita ki dafa ki ci ko ki saida babu abunda za mu da ita”


STORY CONTINUES BELOW

Mikewa nai tsaye cikin bacin rai na ce.

“Ke kika fi kowa abun yi da ita saboda jininki ce, kuma tambaya kawai na zo saboda idan tana nan na tafi da ita saboda kula da tarbiyar”


Mikewa tai tsaye ta nuna ni da yatsa.

“Ke Halima ki shiga hankalinki karki ce za ki so har cikin gidan nan ki min rashin kunya, ki bar ganin an kyale ki Wallahi kika min iskanci sai an karbe yaran nan daga hannunki”


“Da kuwa kin bude abunda yake rufe, da kin tona asirin danki dan sai duniya ta ji abunda ya aikatawa yar dan'uwansa”


Na bata amsa a fusace sannan na juya na fice na barta tana ta surutanta, inda na bar mai Napep din a nan na same shi.

“Kai ni igala quarters”


Na fada bayan an shiga Napep din, yana tafiya ina nuna masa inda za abi har ya sauke ni a kofar gidan Aminu, bayan Hajiya ban san ko tana gidan ba neman be ba a cire tsammani wata kila ma ya ganta a wani gurin ko kuma ita ta fadi can a kai ta ba tare da mun sani ba.

  Mai gadin yai na'am da ganina yana ta washe min hakora da tambayar yaushe gamo.


“Dan Allah Malam Garba tambaya nake ko kaga Namra a gidan nan?”


“Namra dai ta wajenki?”


“Ita, ta bata tun jiya”


“Subhanallahi Wallahi ban ganta ba, amman ki tambayi Alhaji ai yana ciki, Hajiyar ma tana ciki”


Fadar Hajiya ma tana nan ciki ya tabbatar da cewar Aminu yayi sabon aure kenan.

“Aa bana bukata na gode”


“Allah ya tsananta rabo”


“Amin”


Na amsa ina hawaye, ina shiga cikin napep din kuka ya kwace min.


“Hajiya Lafiya?”


“Yata ta bata tun jiya kuma ba a ganta ba... ”


“Subhanallahi a ina?”


“A gurin biki taje ita da kanwata”


“Aiko na ji ana cigiyar wata yarinya a fm dazun, amman ban sani ba ko ita ce”


Da sauri na kalleshi.

“Yaushe? A ina? Ya sunanta?”


“Wallahi ban rike sunanta ba amman dai dazun ina sauraren fm a napep na ji ana cigiyarta”


Ya karasa yana kunna fm din.

“Dan Allah ka taimaka ka kai ni can mu binka kasan inda fm din take?”


“Eh na sani Allah yasa ita ce”


Kamar nai tsuntsuwa na tashi na isa fm din haka naji, abun ka da guri mai nisa daga igala quarters zuwa Damba sai tafiyar ta zame min kamar ta wani gari, muna isa na fita na shiga ciki na fara tambayar mutane hankalina a tashe, sai wani ya shiga ciki ya duba takardun cigiyar ya rubuto mana number wayar da aka bada sannan ya fada min sunanta. Ina jin ya ambaci Namra wani dadi marar misaltuwa ya lullube ni.


“Sai kinje Samaru ki tambaya gidan Alhaji Muhamad Gwarzo”


“Na gode”


Tun kan ya gama magana na juya da sauri na fito na shiga napep din na fada masa unguwar da zai kai ni, a hanyar mu ta tafiya kiran Aminu ya shigo wayata, na gane ne numbersa ne saboda na haddace ba dan number tana da suna ba. Har na yi kamar ba zan dauka ba sai kuma wata zuciyar ta hana ni na danna picking na kara a kunne na.

“An ga Namra?”


“Ashe kana iya damuwa da ganinta ai na dauka ka manta da kana da yaya”


“Halima bari kiji na fada miki wallahi duk yata ta bata ko wani abun ya sameta sai na wulakanta ki, sai na sa kin yi nadamar haihuwarki da akai a duniyar nan Wallahi Wallahi dan haka ki nemo min yata tun wuri”


STORY CONTINUES BELOW

Be jira abunda zance ba ya katse kiran, wani uban haushi ne ya cika ni har na ji ina ma dai ace ban dauki wayar ba.

  Da tambaya muka gane gidan, domin number da aka bamu mun yi ta kira ba a dauka ba, daga baya ma sai aka kashe wayar. Wani irin katon gidane mai katon gate irin na manyan mutanen nan da suka ci arziki har sukai kashinsa, kai idam ma baka sani ba za kai zaton gidan fillar kai ne saboda girmansa da tsaruwarsa, ko ina na gidan an kawatashi da fulawoyi da kuma irin dagayen itacen nan masu haska gida.

“Sannu Malam dan Allah yata na ke nema kuma ance tana nan”


Na fadawa mai gadin bayan nai kwankwasa kofar gidan ya bude min na shiga ciki.

“Ina aka ce miki?”


“Ce min akai gidan Alhaji Muhammad Gwarzo”


“Eh nan ne shiga ciki”


Kai tsaye na doshi cikin gidan, a maimakon na shiga part din farko sai na nufi dayan part din da shi nake hango kofarsa tsabanin babban part din da na kasa ganin kofar shigarsa, wata kila kuma ta karamin ake shiga.

  Kofar falon na hango a bude tun ka na karasa, na yi iya yadda shari'a tace wato yin sallama da na ji ba amsa min ba na kunna kai cikin katon falon mai cike da sanyin ac da daddadan kamshi sai dai ban fasa sallamar duk kuwa da ban ga kowa ba.

Ina kokarin juyawa na fita wani mutun ya fito daga wani bangare na falon yana rike da plate da ke dauke da soyayyen kwai sai kofin tea. Wani shegen short ne a jikinsa kirjinsa kuma a tsirara dan babu riga a jikinsa. Da gila ya tambayi abunda ya kawo ni falon.


“Yata ta bata aka ce tana nan gidan Alhaji Muhammad Gwarzo... ”


Wani kallo na watsa min daga sama zuwa kasa sannan ya zauna ya aje plate din hannunsa a saman center table din dake kusa da shi yana cigaba da kallo, zuwa can kuma ya dauke kai ba tare da ya ce da ni komai ba.

“Yata nake nema na fada maka”


Banza yai min kamar ba zai amsani ba, sannan ya ce.

“Idan kin ganta ai sai ki dauka”


“Idan bata nan ka fada min bata nan ba sai ka wulakanta ni ba domin ba bara na zo yi ba”


Na fada a fusace, ina tuna inda na taba ganinsa. Uffan be ce min ba ya dauki tea gabansa yana sha tare da maida hankalinsa gurin katuwar plasma dake manne a wallpaper falon. Juyowa nai a hasale na fito daga falon marasa na murdawa, kamin na isa dayan part din sai da na rike cikina kusan sau uku. Ina isa na zauna a gurin na runtse ido ina sauraren radadin da take min. Daker na iya tsada hankalina har na lura da kofar falon, cike da karfin hali na unkura na mike tsaye na isa bakin kofar ina kokarin kai hannu na nai knocked aka bude kofar daga can ciki. Fuskar Mutumen dazun din nan ne da ke wacan part din da na baro, sai dai wannan karon akwai jallabiya a jikinsa, mamaki ya kama ni shi din ko kuwa su ma twins ne kamar Abdallah da Abdulhamid? Ko kuma wata hanyar ya biyo ta can ciki ya isa wannan part din? Sai da nai kamar ba zan masa magana ba, sai kuma wata zuciyar ta hana ni abunka da nama.

“Dan Allah yata nake nema aka ce min tana nan”


Be ce min komai ba ya fito daga falon ya sauko stairs din ya nufi gurin wata mota dake fake kusa da inda nake zaune.


“Tana nan ciki”


Ya fada bayan ya bude motar. Unkurawa nai na tashi na nufi kofar falon na shiga ina takawa a hankali saboda abu nake jin kamar zai zubo min. Na yi mamakin karamci da sakin fuskar da na tarar a fuskar Hajiyar gidan ina yin sallama ta amsa min tana min sannu da zuwa kamar ta san ni, Namra na ganina ta taso da sauri ta nufo inda nake tana dariya.

“Momy”


Rumgumeta nai na lumshe ido.

AHMAD POV.

STORY CONTINUES BELOW

Da gangan yake son ya shiga motarsa ya yi tafiyarsa saboda kar ma mahaifiyar yarinyar ta ga fuskar yi masa godiya ko yi masa wata maganar. Ji yake kamar ya fada mata bakar magana son ransa aka my wufintar da yar da tai amman ba shi da damar wannan tun da shi ba uban yar ba ne kuma ba shi da alaka da ita. Ko ba komai dai ya san hankalinta ya tashi tun da ga shi har tana zubar jini.

  Tun kamin ya karasa gate aka bude masa gate din, ganin wani tsaye da mota a bakin gate din gidan yasa ya tsaya ya sauke gilashin motar yana kallon Abdulhamid da na shi gilashin yake sauke.

“Malam lafiya?”


“Wata yarinya muke nema aka ce tana nan gidan mun kira number da aka ba da a sanarwa muka jita a kashe shiyasa na zo”


“Kai ne mahaifinta?”


“No ni ne dai nake auren mahaifiyarta”


Abdulhamid ya amsa kai tsaye, sai Ahmad ya kalleshi da kyau sannan ya dauke kai.

“To ka tsaya nan za a fito maka da matarka”


Ya karasa yana kallon wayarsa. Number sis dinsa ya lalubo ya aika mata kira, in few seconds tai picking.


“Sis ki fadawa matarta mijinta yana jiranta a waje”


“Okay Ammn bro bleeding ta ke, ya dan jira ta shiga bandaki”


“Ki fada mata na ce”


Yana fadar haka ya kashe wayar ya karawa motarsa wuta ya hau titi, Abdulhamid na zaune cikin wata mai kama da Ahmad din ta budo karamar kofar gate din ta leko shi daga can cikin motar da yake zaune tace.

“Kai ne mijinta?”


Abdulhamid ya gyada mata kai.

“To ka dan jira ta fito tana bleeding amman ta dan shiga toilet ne”


“Ta ji ciwo ne?”


“No i think ta samu miscarriage ne... ”


Ta fada tana dan zare.

“Miscarriage...?”


Ya maimaita.

“Yes ban dai tabbatar ba, amman kasan idan am samu tashin hankali yana iya causing wannan matsalar, amman ba lallai ne ya zube duka ba, amman dai shawara ka kaita asibiti yanzu dan tabbatarwa”


Tun da ta fara yake kallon yadda take ta zuba masa zance har ta gama, daman daga ganinta irin yan matan nan ne masu surutun fadi baa tambaye ka ba.


“Okay”


Ya amsa mata zuciyarsa cike da mamaki, kai ta gyada masa sannan ta juya ta koma ciki, kamin ta isa falon wayar da ke hannunta tai ringing alamar kira. Soul mate ne rubuce a saman screen din, murmushi ne ya bayyana a fuskarta jikinta har rawa yake ta kara wayar a kunnenta sannan ta nufi wani bangare na gida cike da shauki tana amsa wayar.

HALIMATU POV.

Ban lura da jini dake zubo min ba har sai da na zauna a saman manyan cushion din dake falo, shi ma saboda Hajiyar ta yi magana ne.

“Subhanallahi kin ji ciwo ne?”


A lokacin da na duba sai na lura da jinin ya bata duk sawun kafata yake jini ya bata gurin. A iya sanina dai ban ji ciwo ba ban fadi ba balle na ce na ji ciwo ne, jini ba ta kafa yake min zuba ba ta cikina ne duk da kuwa da bana da tabbacin hakan domin ban ji zubowar komai ba sai jin alamar zubowar da na ji dazun ashe har ya zubo ban sani ba.

“A a ban ji ciwo ba”


Na amsa mata gabana na faduwa wani sabon tashin hankali na kusantata.

“Allah ya tsare idan ba miscarriage kika samu ba”


Hajiyar na rufe baki wata budurwar da ke zaune a dinning ta ta amsa da.

“Shi ne ma, kin san tashin hankali yana saka haka ko da ciki ya yi kwari ba re kuma ace yana sabo kuma.... ”


Bata karasa Hajiyar ta daka mata tsawa.

“Haba idan kin fara zubawa ba ki san ki tsaya ba? Shiyasa kike samu matsala da Yayanki kina da yawan magana”


Da hannu tai zip up din bakinta.


“Taso muje ciki ki gyara jikinki”


Naga karamci sosai a gurin matar nan babu kyama ta shiga da ni har cikin dakinta ta kai ni bandakin ta bani duk wani abu da nake bukata tun daga pad da pant da doguwar rigar da zan canja. Kamar kazar da kwai ya fashewa haka na fito daga bandaki jikina babu kwari na dawo falon a maimakon na zauna sai na yi tsaye kamar an dasa ni wasu sabbin hawayen na cika min ido.

“Baiwar Allah ki zauna mana yau masu aikin na mu basa nan balle akwai miki ruwa”


“Aa na gode sosai Hajiya, gida zan tafi yan uwana suna can suna ta neman Namra, na gode sosai da karamci na ji dadi da yata ta fada hannun mace mai karamci da son mutane kamar ki Allah ya saka da alheri”


“Babu komai Gwarzo za ki m godiya ai, muna zaune ya zo da ita sai fada yake wai kun wofintar da ita, dan Allah a rika kula”


“In-Sha-Allah”


Bayan na amsa mata, ta dauki wayarta dake gefen cushion din ta kira number da na ke zaton ta wacan mutumen ce.

“Za ta tafi da yarinyar nan”


Shine abunda na ji ta fada ban ji abunda ya fada mata ba, murmushi kawai na ga ta yi sannan ta aje wayar tana kallona.

“A kula dan Allah ina zuwa”


Tsakanin shigarta dakinta da fitowarta be wuce minti biyar ba ta mikowa Namra dake rike da hannuna abu a leda sannan ta shafa kanta.

“To bye bye jikata”


Murmushi Namra tai ta yi mata bye bye sannan nai mata godiya muka fito, har mu ka bar gidan ban saje ganin yarinyar nan mai shegen surutu kaar suda ba. Na yi mamakin ganin mai napep din a gafen gidan fake da napep dinsa, ni har na manta da shi lallai ba karamin hakurin yai ba na tsayawa jirana har na fito. Ya nuna min jindadin ganin yata kamar ya san ni har yake tsokar Namra wai ta tashu hankalin Mamanta. Ni dai na san na fada masa unguwar da zai kai ni wato family house dinmu sai dai tafiyar da isa cikin unguwar ban san an yi ba har sai da Namra ta girgiza ne, ashe hawaye na ke ban sani ba tashin hankalin da ke cikin kaina ya mantar da ni duniyata na dan kankanen lokaci, tsoro nake idan ba cikin ba ne kamar yadda Hajara tai min hasashe, sai dai taya bayan ban tana jin wata alama ta cikin ba? Hasalima ni sai na gama al'ada na ke saurin daukar ciki? Wata jarrabar ce ta sake hawa kaina? Ko kuma dai wani ciwon ne dabam ba ciki ba? No ciki ne! Ita ce amsar da nabawa kaina saboda azabar ciwon mararda neke ji ba irin wanda na saba ji ba ne,hakan ya tabbatar min da cewar cikin ne yake zubewa ko ma ya zube duk da ban tana yin bari ba ban san yadda abun yake ba. Muna fita daga Napep din yan gidan mu suka fito waje da sauri ganin Namra suka saka ihu, sai a lokacin na lura da motar Abdallah da ke fake kofar gidan. Jakata na bude na dauko dubu biyu na mikawa mai napep din ya amsa da murna yana min godiya, sannan na shiga cikin gidan kamar bana cikin hayyacina.1

“Al-hamdulillah”


Shine abunda Abdallah ya fada ganin an shigo da Namra, sai dai ko da wasa be kalli inda na ke ba. A lokacin ne na ji suna fadar su ma sun ji sanarwa a gidan radio kanen maza biyu ma sun nufi can tare da Hafiza. Ko minti biyar Abdallah be kara cikin gidan ba ya ce zai tafi Mama da Inna da Baba suna ta masa addu'ar Allah ya raya mana zuri'a ya saka masa da alheri.

“Kuma Allah ya ba ni da namiji Mama ina son namiji sosai”


Ya fada yana saka hannayensa aljihu.


“To Allah ya baka namijin mai albarka, ko ya baka tagwaye maza irinku”


Cewar Inna tana dariya shi kuma ya amsa da amin shi da Baba da Mama. Daf da zai fice na yi juyo ina kallon bayansa zuciyarta na raya min abubuwa da dama, sai wani zafi take min kamar a dora tasa a saman garwasu a yanka zuciyata an saka ciki ana soyawa...

Post a Comment for "GOBE NA CHAPTER 3 BY KHADIJACANDY"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...