GOBE NA CHAPTER 2 BY KHADIJACANDY - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GOBE NA CHAPTER 2 BY KHADIJACANDY

GOBE NA CHAPTER 2 BY KHADIJACANDY

- - Post a Comment

 GOBE NA CHAPTER 2 BY KHADIJACANDY


                   Www.bankinhausanovels.com.ng "Ko yar iska ce ni na fi karfin iskanci da Kabir, mutumen da ke daukar the same salary da na ke dauka, mi ya samu mi ya bani na fi karfin abunda kike tunani na fi karfin aikata alfasha da aurena da yayana"


Na fada mata cikin zafin nama bayan na wanke mata fuska da mari, wata matar da ce da ban wayance wacece ita ba ta zo da sauri ta rike matar Kabir din tana kiranta da sunanta.+

"Haba Maryam wannan abun da kike ba mutunci ba ne, ai ko da gaske mijinki yana aikata alfahari be kamata ki tsare mace a hanya kina mata wannan maganar ba, ballanta baki da tabbaci akan hakan kamata yai ki fara damuwa da damuwar mijinki a yanzu Kabir yana a halin tausayin a yanzu abunda likito suke fada jinin ya kai har cikin kansa zai rayu ba zai rayu ba haukacewa zai yi ko ya manta komai duk be dame ki ba sai wani abun da ba zaki iya canjawa ba! Haba Maryam"


"Wallahi Anty karuwarsa ce kuma saboda ita hakan "

“Wallahi Anty karuwarsa ce kuma saboda ita wannan hadrin ya same shi, yanzu kuma dan rashin kunya har ta sako kafarta ta zo ganinsa? Haba Anty da wanne zan ji da ciwonsa ko da ganinta”


Ta fada cikin kuka ni kan tuni jikina yai sanyi jin abunda ya same Kabir jinin ya taba kwakwalwarsa, abun ya tsorani sosai kuma ya jefani a cikin wata duniyar tunanin da fargabar yadda gobensa zata kasance. Takawa na fara yi ina tafiya na nufo gate din fita daga asibitin gaba daya ba tare da na sake cewa komai ba, kallo daya za ka min ka fahimci akwai damuwa a tare da kamar yadda tunani ya kawo min ziyara a yanzu. Kar dai ace saboda ya rabe ni hakan ya same shi? Kaddararta ta fara wuce iya ni kawai har ta fara taba yayana da mutanen da suke kusa da ni? Tambayar da na yi ma kaina kenan tambayar da ban san wanda zai amsa min ita ba. Guri na samu kusa da gate din na zauna a saman wani guntun dakali idona cike da kwalla, ban samu kaina a cikin tausayin wani mutum wanda ba jinina kamar yadda tausayin Kabir ya dirar min a zuciya yai min kawaya a ruhi, ya nemi jijiyoyin jinina da jiki ya rike.+

“Halimatu”


Muryar Abdallah ce ta hankalto ni har na dago kaina na kalleshi hawaye na min zuba.

“Zama kikai a guri kamar wannan har kina kuka a public? Mutane fa suna ta kallonki”


Cikin wani irin sanyin muryar da natsuwa yai min maganar da sautin da ni kadai zan iya ji da kuma fahimtar kalmomin da yake furta min. Sauke kaina nai daga kallonsa zuwa kallon titi ina ta yawo da ido.

“Abdallah ina tunanin Gobena ne, ya zata kasance? Miyasa abubuwan nan za su faru ta dalilina? Na farko yata? Na biyu kuma abokin aikina? Abunda ya faru da Namra kamar jiya ne, ban sammaci wani abun da zai taba zuciyata kamar haka zai sake faruwa ba, idan wani abun nai nauyi ya sake faruwa da ni ina jin kamar ba zan iya jure ba”


Risinowa yai gabana yana kallon fuskata.

“Share hawayenki zo muje a mota ki min bayani maybe zan sama miki mafita”


Sai na sake dago kai na kalleshi a karo na biyu, a yau Abdallah yai magana ta hankali da nuna kulawarsa a kaina, ko da yake a can baya ma ai yana nunawa sai dai wacan karon ina ganin rashin dacewar hakan saboda akwai igiyar aure a kaina, kuma a baya duk wata magana da zai min ta Aminu ce da abunda ya shafe shi.


“Abdallah zan iya rikon ka kamar dan'uwan? Abokin shawara? Wanda zan labartawa damuwata ya nema min mafita? Dan Allah?”


Sai ya kasa ce min komai, ba dan komai ba dan sai dan ya san inda manufata ta dosa, daga lokacin da zai rike ni a matsayin yar'uwa to babu zancen soyayya ko aure a tsakaninmu, ni kuwa abunda na fi so kenan, domin ban tana yi ma Abdallah kallon so ko kauna ba balle har ta ga kai ga aure! Mikewa yai tsaye ya nufi inda motarsa take, sai a lokacin na lura da inda ya faka ta, tashi nai na bi bayansa ba tare da na share hawayena ba. Na bude front seat ma shiga shi kuma ya tashi motar ya koma da ni cikin asibitin, a daya daga cikin guraren da aka tanada domin likitoci su faka motocinsu ya faka motarsa sannan ya juyo ya kalleni.

“Idan har hakan zai faranta miki rai Halima zan yi, amman ki sani zan cutu domin ba abunda nake so kenan ba, sai dai zan jira har lokacin da zaki fahimci da gaske na ke, fada min minene damuwarki?”


“Abokin aikina yayi hadari saboda ni, kuma yanzu na ji cewar akwai yiyuwar jimin ya tana kansa wata kila ya haukace ko ya manta komai ko ya mutu”


Na fada kai tsaye ina share hawayena. Sosai ya nuna min damuwarsa.

“Subhanallahi miya same shi haka?”


A take na labarta masa komai har zuwa fadan da mukai da matarsa. Na yi zaton ko zai tausaya masa ne sai na ga murmushi a fuskarsa.


“Kin kasa yarda cewar kina da kyau da kan iya jan hankali wasu mazan izuwa gareki saboda Aminu yana yawan fada miki cewar baki da kyau ko? Kina da kyau Halima seriously kina da jikin da ko wane namiji zai so ki kasance a tare da shi, ina tunanin abunda ya ja hankali abokin aikinki kenan har ya kai ga mallakar hotunanki da sakawa sunanki spacial saboda ke din ta musamman ce”


STORY CONTINUES BELOW

Na yi kasa da kaina ina tuna lokacin da Aminu yake fada min cewar kibar jikina ta masa yawa shi yar siririyar mace yake so wacce ke kamar zata kare, mace da zai nuna mata soyayya ta nuna masa yai zaman jindadi da ita ba zaman tara masa yaya ba.

“Bana son ki saboda kawai wadannan abubuwan da na lissafa miki, no ina fada miki hakan ne saboda ki yarda cewar ke din kyakkyawa ce kuma Allah be rage ki da komai ba”


Maganar da yai ce ta dawo da ni daga duniyar tunanin da na fara zuwa, hakan yasa nai kokarin kawarta maganar.

“Taya zan fahimtar da matarsa cewar ni ba karuwarsa ba ce”


Sai da ya danna horn din motarsa kamar wani ne a gaban mu alhalin babu komai a gabanmu sai fulawoyi.


“Ki sakawa ranki sallama for now Halimatu, ki cire zancen cewar saboda ke wannan abun ya samu abokin aikinki, kuma ki manta da zancen fahimtar da matarsa, ki daga musu kafa na wani lokacin idan ya samu lafiya kamin lokacin sai ki je ki ganshi kuma ki fada masa ya fahimtar matarsa sannan kuma ki gargade shi daya cire kansa akan duk wani abun daya shafe ki, Halima kin san abunda nake so da ke?”


Na girgiza masa kai alamar ban sani ba.


“So na ke ki manta da komai da kowa a gabanki ki maida hankalinki gurin aikinki kuma ki kula da yaranki sai kuma zancen Namra shi ma ki jajirce wajen ganin kin kwato mata hakkinta barin wannan maganar zai bawa kanen mahaifinta damar yi ma wata yar ne”


“Amman Mama tace na bar maganar saboda kar na jawa Namra abun kunya idan ta girma”


“Halima ya kamata ki gane wani abu, ke fa uwa ce idan ba ki yi abunda zai kwantar miki da hankali akan yayanki ba to be kamata ki bar damuwa a ranki ba, duk wanda zai nuna miki yadda za ki kula da yaranki a bayanki yake, duk wanda zai damu da abunda ya damu danki ko yarki a bayanki yake, ke fa mutunce ya kamata ki san da wannan, ki yi wani abun da zai zame miki kwanciyar hankali kuma ya zamo abun koyi a gurin wasu matan, bari kashi a ciki baya maganin yunwa hankalinki ba zai taba kwanciya ba har sai kin hukunta wannan mutumen right?”


Na gyada masa kai gaskiya ya fada, ni kaina ina son yin hakan sai dai yadda Mama ta nuna bata so yasa na fara cire rai daga yin abun.

“Zan tsaya miki Halimatu, zan goya miki baya zan miki duk wani abu da kike bukata kuma zan baki kariya i promise you this”


“Zan tattauna da Mama har sai na ji ta bakinta yardar Allah na tare da yardar iyaye, bana son na yi wani abun da zai zamewa mahaifiyata ciwo”


“Yes hakan na kyau, sai dai wani lokacin iyayena suna nuna mana abunda suke gani a kamar zai cutar da mu alhalin ba cutarwa ba ne Allah ya taimake mu”


“Amin ya Rabb na gode Abdallah”


Na fada ina dubansa sai shi ma ya dubuni ido cikin ido wani tsan na ji na rashin jindadi for the first time yau na ji nauyi da kunyar Abdallah ya dira saman kaina.

“Ya jikinki?”


Ya tambaya still idonsa a kaina.

“Al-hamdulillah”


“Ina fatar kin ji sauki sosai”


“Na ji sauki”


“Mashallah. mama tace min kin tafi tafi aiki ashe ganin wani kika zo”


“Na fada mata da ga ganin Kabir zan wuce gurin aiki ne maybe ta dauka na wuce ne, ka biyo da gida ne?”


“Yes na zo na duba jikinki ne kuma ina son nai maganar karatun su Adnan da ke as her mother”


Kallonsa nai ba tare na ce komai ba sai ya cigaba da maganar still idonsa na kaina.

“Ina son canja musu makaranta ne zuwa wacce su Suhaima suke yi idan kin ba ni dama amman kuma kin aminta”


STORY CONTINUES BELOW

“Aa Abdallah na gode da kulawa ka dawo da su gida, ni zan duba musu wata makarantar dabam”


Ina kokarin kai hannu na bude ganbun motar na fita sai ya danna lock motar ta rufe hakan yasa na juyo ya kalleshi shi ma ni yake kallo da kyau.

“Na fadi wani abun ne daya bata miki rai? Ko na yi wani abun ne marar dadi?”


“Ba ko daya, yayana ne babu ruwanka da su”


“Amman yanzu kika gama fadar cewar zan zama miki dam'uwa? To miye laifi dan na saka su Namra a scul”


“Bana so,  yarana ne dan Allah ka kyale su, zan iya kula da abuna zan iya musu komai”


“Ba zan cutar da su Halima kamar ba ki san ni ba”


“Ka kyale ni dan Allah Abdallah bana bukata”


Na fada ina hade hannayena tare da fashewa da kuka.

“Miye abun kuka daga wannan maganar?”


Ya karasa yana unlock din motar, ni kaina ban ga wani abun kuka a cikin lamarin ba, sai dai ina jin a yanzu kamar bana da wata garkuwar shiyasa kukan ya fi kusa da ni. Bude motar nai na fita ina share hawayena.

  Na isa gurin aikina cikin wani irin yanayi marar misaltuwa, yanayin da ba zan iya fadarsa ba, hakika inacikin damuwa bayan ta yarana da tawa yanzu kuma ta Kabir ta hau kaina. Wunin ranar ban iya tabuka komai ba saboda yawan kallon mazaunin Kabir da neka sai na rika ganin kamar yana nan ko kamar zai shigo irin yadda ya saba. Sai dai idan na tuna cewar yana can kwance asibiti sai na ji babu dadi. Ko dan saboda sabo idan abokin aikinka baya kusa da kai kanki babu dadi balle irin wannan mai dalili. Tun da na fara aikin shekara hudu ban tana jin aiki ya gundure ni ba, ban taba jin na tsani aikina kamar yau ba, idan na kalli inda Kabir yake zaune sai na ji babu dadi ba ni kadai ba har Emanuel ya damu da hakan saboda yanayinsa da na gani, ban tana jin damuwa da lamarin Kabir kamar wannan karon ba, tausayinsa ya hanani sukuni kamin lokacin tashi aikina yai har na tsalwala.

  Biyu da mintuna na tashi daga aiki daman wani lokacin nakan tashi haka wani lokacin har uku saura ko uku da wani abun. Tafiya nakecikin kamfanin ina tunanin abunda zai sake samu na, domin ina jin a jikina kamar kullum wani abun zai yi ta samuna ko wani na kusa da ni marar dadi...


Page din jiya ya kire ban sani ba sai yanzu. Ga shi nan a saman 12 na dora muku 👆


***       ***      ***    ***     ***    ***  ***

Page 12 👇


“Hajiya barka da tashi ya kafafuwan?”


A natse yake mata magana kamar yadda ya saba, ita kuma ta dago ta kalleshi da kyau tana tauna ragowar goron da ke bakinta.


“Hassan kwana nawa rabon ka da gidan nan?”


Shiru be amsa mata ba. Hakan ya bata damar cigaba da yi masa fadan a zuciyarta kuma tausayinsa ne fal a ciki.

“Ana rayuwa haka? Ko wane bawa ai da kalar kaddararsa, amman sai ka rika saka kanka a damuwa ba kai ka dorawa kanka abun nan ba”


Kunya ce ta lullube shi, duk kuwa da ya san gaskiya Hajiya take fada masa and he know rashin lafiyarsa na daga cikin abunda ya fi ko wane daga masa hankali, tun abun baya damunsa yanzu har ya kai matsayin da idan aka auna jininsa za a iya cewa ya hau, babu inda be nemi magani ba a duniyar nan amman babu alamun sauki balle ma saukin, babu abunda be yi ba tun daga na hausa har zuwa na gargajiya amman shiru kamar an shuka dusa. Shi yanzu abun tsoro ma yake ba shi domin yana ayyana a ransa kuma yana jin kamar ba zai taba warkewa ba, burin da ko wane mai rai yake da shi na son yai aure shi kan na shi yana nesa da shi, tun ana kiran yaushe zai yi aure a family da friends har ta kai yanzu dai su tsarge shi suna kiransa da tazuru wasu kuma su ce masa mijin aljana wanda hakan ba karamin ciwo yake masa ba.

STORY CONTINUES BELOW

“Karka yanke kauna daga rahamar Hassan, daman ita rayuwar duniya tana cike da jarrabawa, kuma kowa da irin tasa, karka fasa neman magani kar kuma na ce ba zaka nemi aurenba, ka kwada neman auren kamar yadda kake a da, wata kila a dace wata kila kuma kamin lokacin auren yai sai Allah ya baka mafita”


Ya gyada mata.


“Zan cigaba Hajiya, duk dai ina jin kamar ni haka Allah yai ni”


“Babu wata cuta da bata da magani a duniyar, idan ka cire tsufa da mutuwa shine kawai basa da magani, a kullum ina cikin yi maka addu'a kuma In-Sha-Allah za a karba mana ko ma an karba, kowa da irin jarabarwarsa Hassan ga yar'uwarku nan aure ya mutu ai duk cikin jarabawa ne bayan ta fito kuma ciki ya zube wata kila ma kuma ta zubar da cikin ne ta huta da wahalar duniyar”


Kallon rashin fahimta yai Hajiya, idan tace yar'uwasa zai fara kawo sisters dinsa da suke daki daya kamin ya hango na wani gurin, a cikin familynsu ma sisters dinsa ma ai suna da yawa abunka da mai yawan yan'uwa.

“Wace Hajiya?”


“Halimatu...... ”


Haka ya ji sautin sunan sahibarsa kamar daga wata duniyar, Halimatuu... Ya maimaita cikin mamaki da bakinciki jin abunda ya faru.


“Taya? Garin ya?”


“Ai kasan abunda ya faru da Namra ko to shine sanadi yau kusan kwana uku ma da faruwar abun ko hudu kuma cikin da ta fito da shi ya zube har sai da akai mata wankin mara anjima na ke son zuwa na ganta”


“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, ai kamar saki daya ne ya rage ko?”


“Saki daya ne kuma ya karasa kai wannan mutumen ba shi da imani sam ”


Wani irin na rashin jindadi ne ya ziuarci Abdulhamid, sai yaji kamar kanwarsa da suka fito ciki daya aka saka, a take ya fara ayyana irin yadda Halimatu zata ji halin da zata kasance duk kuwa da ya san dama can ya san ba dadin zaman auren take ji ba. Wanda yake yawan alakanta hakan da kansa domin yana ji a ransa da ace yadda yai soyayyarsa da Halimatu a boye da ya samu cikar burinsa da yanzu shi take aure da yanzu duka yaran na shi ne,ya dade yana fargabar zuwan wannan ranar yau ga ranar ta zo da ba zai iya yi mata komai ba.


_Bana da tabbacin wanda zan aura zai rike ni amana Abdulhamid, amman ina da tabbacin kai idan ka aure ba zaka wulakanta ni ba, bana jin idan ka aureni zaka iya rabuwa da ni har sai idan mutuwa ce ta dauke daya daga cikin mu_


Cikin kuka take masa maganar muryarta har rawa take.

_Ki yi hakuri Haima, ba zan iya cutar da ke ba, ba zan iya aurenki na zaunar da ke a gidana ba bayan na san bana iya yin komai da mace, idan nai hakan na cutar da ke kuma duk abunda zai biyo baya laifina ne ba na ki ba_


_Wallahi zan jira ka zan zauna da kai har zuwa lokacin da zaka samu lafiya, ko wane masoyi yana da burin yin wani abun na faranta rai na sadaukarwar ga masoyinsa, Abdulhamid ka ba ni dama dan Allah zan aureka a haka kuma zan jira har zuwa lokacin da zaka samu lafiya_


_No ba zaki gane abunda na ke nufi ba, ban tsammaci cewar zai kan wannan lokacin ban samu lafiya ba_


_Ka hanani bayyana soyayyarka, daman saboda ka san ba zaka aure ni ba ko? Yanzu kuma ka hanani aurenka_


_na hana ki bayyana soyayyata saboda na san wannan ranar zata so wata kila na samu sauko ko akasin haka, kin ga yanzu da ban samu sauki ba babu wanda ya san mun yi soyayya da ke, da ace na samu sauki kuma da yanzu ne zan bayyana soyayyata, ki fahimce ni mana Haima Wallahi ina kaunar ki amman ba zan iya hana ki auren lafiyayyen miji ni na aureki, ba kuma zan hana ki auren kowa ki jira ni ba domin ban san lokacin samun lafiyata ba, kuma iyayenki a yanzu ma sun damu su aurar da ke, Allah ya riga ya rubuto ba zan aureki ba...._


STORY CONTINUES BELOW

Duk wani magana da Hajiya ke yi be ji ko daya ba saboda ya lula a duniyar tunanin abunda ya faru tsakaninsa da tsohuwar soyayyiyarsa yana murza zoben da ta saka saka mata da kansa a wani lokaci can baya.

“Hassan....”


Da sauri ya dago ya kalli Hajiya domin ya ji kiran kamar daga wata duniyar.


“Na'am Hajiya?”


“Ba ka ji abunda na ce ba ne?”


“Na ji.... Na ji.. Na ce eh ba ki ji ba ne?”


“Saboda me?”


“Haka nan kawai”


“Haka nan kawai sai ka ki zuwa aiki? Abun ya fara taba har da aikinka ne?”


Sai a lokacin ya fahimci abunda Hajiya take magana akai domin a dazun amsa mata kawai yake ba tare da yaji abunda take fada ba. Mikewa yai tsaye yana murmushi.

“Zan je aiki mana Hajiya, ban fahimta ba ne sai yanzu”


“To Allah ya tsare yai muku albarka”


“Amin Hajiya sai na dawo”


Ya fito yana jin cewar a yanzu ne ya dace ya nemi magani ko dan Halimatu, idan ma bar warke ba zai aureta a hakan matukar a yanzun zata aminta domin yana jin cewar shi kadai mutumen da zai iya yarda ya aureta da yaya a yanzu kuma ya mantar da ita komai.

HALIMATU POV.

Wani abunda ya bani mamaki rashin samun abun hawa tun daga kan babura har napep duk wanda na tara ba ya tsayawa. Abun har mamaki ya bani na rika shafa kaina ina lalabawa wai ko basa ganin nane amman sai na jini a mutum kuma ai ina ganin mutane an kallona sai dai tsayawa su dauke ni ne basa yi. Tun ina tsaye ina taro har ta kai ga na fara takawa ina bin gefen titi, da na gaji da tafiyar sai na samu guri na hutu, na sake cigaba da tafiya sai yamma lis na isa gida ban taba jin gajiya irin ta yau ba damin ban taba shan wahalar tafiya kamar yau ba. Na tararda kowa da kowa na tsakar gida kamar yadda aka saba yin shimfida a harabar gidan a zauna ana ta fira da dare dare. Suna ta min sannu da zuwa ni dai ban bi ta kansu ba na wuce zuwa falon Mama sai na samu Abdallah a zaune yana game da wayarsa Namra na gefensa tare da Aiman da Adnan sun zagaye shi Amal kuma na saman cinyarsa tana kallon wayar, tsayawa nai ina kallonsa shi ma ya dago ya kalleni fuskarsa ba yabo ba fallasa.


“Sannu da tafiya”


Sannan ya mike tsaye yana gyara rigar shaddar da ke jikinsa.

“Kin ce na dawo miki da yaranki ko? To ga su nan sai ki saka su makarantar ai”


Yana fadar hakan ya raba gefena ya wuce ni kuma na bishi da kallon takaici da mamakin karfi hali irin nasa, yara dai nawa ne kuma na zabi na saka su da kaina to ina ruwansa, tun ba yau ba Abdallah na da son shiga rayuwata tun igiyoyin aure suna kaina ina yawan nuna masa bana so amman baya fasawa. Ba wai bana son ya saka su karantar ba ne canja musu makaranta abu ne mai kyau wanda ni ma nai tunanin hakan sai dai bana son yadda yake son shige min ne da yawa, har ga Allah bana jin zan iya karbar wani tayi daga gurin Abdallah na so, taya zan so mutunen da na kaunace dan'uwansa kamar na mutu, mutumen da be san darajar aure ba kuma mutumen da be taba martaba ni saboda ina da igiyar aure ba, mutumen da a kullum fatar mutuwar aure yake min.

  Adnan na aika a shago ya siyo min suga da madara da biredi na hada tea mai sanyi na sha, domin yau ban saka komai a cikina ba sai ruwa, a lokacin da zan fita ban ci komai ba ga shi na ci tafiya a kafa kamar marar galihu. Na yi sa'a bana sallah hakan kuma ba karamin dadi yai min ba, domin yau ko ta kan Amal ban bi na hau kafita na fara sheka bachi kamar wacce ta shekara batai bachi ba.

Ban farka ba sai 11pm a lokacin wasu sisters nawa sun yi bachi su kan yara ba a maganarsu daman can abu ne mai wahala su wuce 10 ba su yu bachi ba ko lokacin da muke gida suna ganin game balle nan da babu. Wani irin ciwon kafafuwa ne ya taso min kamar wata tsohuwa da kaina na zauna ina matsa abu saboda azaba. Na yi minti talatin a haka sannan na tashi na shiga bandaki na tsaftace kaina na canja pad na fito na nufi dakin Mama.

   Na same ta tana hamma kamar dai ni da bachin be wadatar da ni ba, kusa da ita na zauna ina amsa mata cewar lafiya kalau gajiya ce kawai ta saka ni bachi.


STORY CONTINUES BELOW

“Ya jikin abokin aikin na ki?”


“Jiki ba dadi Mama ance ma wai jini zai iya taba kansa ni abun ya bani tsoro sosai, amman matarsa sai ci min mutunci take”


“Akan me? Miye hadinki da matarsa?”


Na jera mata komai kamar a gabanta ya faru, sosa abun ya bata mata rai har take yabon matar da rashin kunya da kuma tunani, mun dan dauki lokaci muna tattaunawa maganar kamin na soma mata shimfida da zancen Sadi.


“Wai Halimatu ba zaki share maganar nan ba? Yanzu fa aurenki ne ya mutu kin dawo cikin kenanki kin zauna su ma muna fatar rabuwa da su ke kin dawo maimakon ki fara tunanin yadda Goben ki zata kasance ki samu mijin aure shine kike neman batawa yarki da kanki suna? Ke yanzu kina ganin wani ma idan ya ji kina da yara hudu zai aure ki ne? Ai ba kowa ke son mace mai yaya ba ma, sannan wani ko ya so ki ba zai yarda ke je masa da yaya ba”


Kallo mamaki nai mata.

“Mama yaushe aurena ya mutu ma balle har ace wani ya zo nemana? Kuma ni yanzu ai ban shirya ma aure ba”


“Baki shirya ma aure ba? Kika magana kamar ba yar musulmi ba? Ke yanzu ko dan ki bawa Aminu haushi ai kyayi aure da wuri, sannan ga kanenki nan suma neman rabuwa na ke su ke kuma kin dawo har ki fara tunanin zama? Halimatu kina da tunani kuwa?”


Babu juyin duniyar nan da ban yi ba dan na fahimtar da ita irin matsalar da na fuskanta a gidan Aminu wanda ya saka aure ya fita a raina amman ta kasa fahimta, idan na dauko zancen kotu kuma sai ta tare ta nuna min ba haka har na gaji na taso na baro mata dakin. As usual na farka raina babu dadi babu walwalah daman na saba tashi a haka tun ina gida Aminu balle kuma yanzu da abubuwan suka kara min yawa.

  Kudina na saka na siyo ma yarana koko da kosai na basu suka sha suka koshi, na san ba za su iya jiran na gida ba domin sun saba da cin abinci da wuri, balle kuma abincin gida na taru ba ba lallai ayi musu yadda zai wadatar da su ba. Bayan na gama da su na aika aka siyo min madara da biredi na hada tea ina sha. Wayata da ke gefena ce tai kara alamar sako tun daga saman screen din wayar na karanta da sakon tare da sunan mallakin sakin.


“Good Morning.”


Dauke kai nai ganin Abdallah na dauka ma ko zai yi zuciya ya kyaleni ashe ba shi da zuciyar ma, ina jin lokacin da wayar ta koma ringing na ki kulawa saboda bana bukatar kallon mai kiran ba, abunda ban sani ba ashe kawata ce Hajara take kirana ba Abdallah ba, ankarowa da hakan yasa nai saurin picking.

“Hello Hajara”


“Na'am Halimatu ya gida ya aiki? Ko baki kusa da wayar ne?”


“Eh ina breakfast ne ya yaran?”


“Lafiya kalau ga ni kofar gidanku ki fito mu gaisa”


Mamaki ne ya kamani.


“Kofar gida kuma? Miyasa ba za ki shigo ba?”


“Ke dai ki fito kawai”


Mamaki ne ya kamani ba dan kankane ba, taya Hajara zata so har gidanmu bata shigo ba tace wai na fito mu gaisa?

Wata kila wata maganar ce mai muhimmanci ita ce amsar da zuciyata ta bani a take na bar cin abincin da na ke na dauka hijabina na saka Amal ta biyo bayan muka fita tare. A bakin kofar gidan mu na yi arba da motar Isma'il sai dai ban kawo komai a raina ba a zatona ko tana cikin motar ne, haka ne yasa na karasa ya buga kofar gilashin motarta. Saukar gilashin motar sai yai min almara mijin Hajara ne kadai a motar ba tare da ita ba, mamaki ya hanani cewa komai sai sakar masa ido yai, shi kuma yana ta faman zuba min murmushi kamar auduga, bude motar yai ya fito yana ta kara min murmushi da haurensa na makka fari.

“Hajara tace min na fito tana kofar gida”


“Eh haka ne, amman dai ya kamata mu kamin a dora da bayani ko”


STORY CONTINUES BELOW

“Ba da kai ba da ita”


Na maimaita masa saboda ya fahimta amman sai ya kara dilmiyar da ni.

“Da ni zaki gaisa ba da ita ba”


Ya fada Yan mikawa Amal hannu ta zo sai tai bayana ta boya kamar wacce bata san shi ba.

“Ina fatar kina lafiya”


Nauyi baki na yi na kasa ce masa komai har ya sake jefo min wata tambayar.

“Ya gida ya yaran?”


“Lafiya Kalau”


Na juya da sauri sai ya kira ni.

“Halimatu... ”


Har na yi kamar ba zan juyo ba sai kuma na juyo na kalleshi. Bude motarsa yai ya dauko wata ledar ya miko min.

“Ga wannan inji kawarki tace a gaishe ki”


“Ka maida maita ka fada mata bana son gaisuwarta kuma ka fada mata karta sake aiko ka a kofar gidanmu da sunan gaisuwa”


Dariya yai yana gyara tsayuwar agogon hannunsa.

“Halimatu kenan, ba zuwa Hajara ne kawai ba, ni kana na ga akwai bukatar na kawo gaisuwa kuma na jajanta miki akan abunda ya faru”


“Da alama baka fahimci da wane yare nake maka magana ba, amman idan ita idan ka isar mata zata fassara maka”


Ina fada masa hakan ta juya na koma cikin cike da mamakin karfin hali irin na Hajara, shi ma kansa Isma'il din mamaki ya bani domin na lura ba shi da kunya irin yadda na ke da Hajara ai ko ni na tallata masa kaina a tunani be kamata ya amsa min ba.

  Bayan na koma cikin gidan na shirya, na fito da zimmar zuwa gurin aikina ba, abun mamaki sai na kasa samun abun hawa kamar dai wacan karon, ganin haka yasa na canja shawara daga zuwa gurin aiki na nufi Hauwa International School, wato makarantar su Namra kamar da wasa na tari wani mai napep ya tsaya hakan ba karamin dadi yai min ba ban ko tsaya fada masa inda zanje ba na shiga ciki da murna yadda kasa wance bata saba shiga Napep ba, ina cikin fada masa inda zai kai ni wayata tai ringing, sai da Hajara ta jera min kira hudu sannan na daga rai a bace.

“Minene?”


“Haba Halimatu ai ko dan ya kamata ki mutunta Mijina”


“Naga alamar ke da mijin na ki kamar ba ku da hankali Hajara, na gargade shi ke ma kuma na gargade ki karki sake yi min wannan wasa”


“Ni dai van kora dan wani gargadin ki ba, na kira ne kawai na fada miki ban fada masa abunda ya fito dake daga gidan mijinki ba, kuma ban fada masa abunda ya samu Namra ba, kuma ni mijina ba zuwa yai ya fada miki cewar yana son ki ba, cewa ina son ki abu ne mai tsada a gurin mijina ya fara gadaki ne ya ga ruwanki...”


Ta karasa tana dariya sannan ta kashe wayar ba tare da jiran irin amsar da zan bata ba. Kadan ya rage mamaki ya kashe ni anya Hajara na cikin hankalinta kuwa kuma ta san abunda take kokarin aikatawa? Wai daman da gaske take da take zancen mijinta ya aureni? Ko kuwa dai gwadani take? Idan gaskoya ne ko karya ni ba zan iya auren mijin kawata ba, yar'uwata ma zance domin Hajara ta fi karfin kawa a gurina. Har na isa makarantar nai abunda zan yi na gama na kama hanyar aikina ban daina mamaki ba da kuma jinjina karfi hali irin yana anya irin matan nan suna nan kuwa? Ni sam na kasa yarda da gaske take ma.

*BAYAN WATA DAYA.*


Babu makarantar da ban leka ba nai yawo da takardun transfer su Adnan ba amman aka ki karbarsu a ko'ina, daga private school har na gobnati abun har tsoro ya soma ba ni, a duk makarantar da na kai su sai su kamar za su karba sai kuma su bullo da wani abun, wata makaranta ma ko kallona ba sa yi yadda kasan wacce akai wa wani magani haka nai ta shimlalo a gari neman makarantar da zata dauki su Adnan da Namra amman ina!

Hakan yasa n watsar da zancen karatunsu na maida hankalina gurin aikina duk kuwa da kasancewar bana jindadin aiki a yanzu saboda rashin Kabir ba kuma dan na shaku da shi ba sai dan tuna abunda ya same ni yana ni walwala a cikin office din, musamman da aka kawo wani da zai maye gurbinsa, ko da wasa ban sake gwada zuwa duba shi asibiti ba, sai dai na kan gwada kiran wayarsa kuma bana samu, ta hanyar wani abokinsa da ke aiki a inda nake na samu labarin cewar an kai shi kano a asibitin kwakwalwa saboda abun ya taba hankalinsa, na tauyasa masa ba kadan ba na kuma tausayawa matarsa da duka danginsa musamman da na samu labarin cewar iyayensa duka biyu basa raye, ta wani bangaren kuma ina tausayin kaina domin ban san me gobena ta tanadar min ba ban san abunda zan tarar nan gaba ba.


   *Lahadi*


Kasancewar yau ranar hutu ce kamar dai jiya sa ta kasance asabar, dukan mu muna zaune gida har kanena ana ta zancen duniya, yawancin firar da muke ta rashin tsaro da ke addabar al'ummar mu ne da kuma tsadar rayuwa da muke ciki, ina zaune Abdallah ya shigo ya gaishe da Mama da Inna kanena kuma suka gaishe shi ya amsa musu amman bakina be hadu da na shi ba, ba baki kadai ba idona ma ban daga na kalleshi ba balle har na mika masa gaisuwa. Tashi nai ya nufi daki yana rike da hannu Namra waccena lura tana sakewa da shi sosai a duk lokacin da ya leko mu, Mama ta tashi ta bi bayansa suka shiga falon tare, ina nan waje zaune amman hankalina yana can inda suke duk na bi na tsargu sai kace wacce tai wani abun gulma.

Bayan yan mintuna Namra ta fito hannunta rike da chocolate.


“Momy wai ki zo inji Mama”


Na tashi cikin kuzari na bi bayanta, ina shigowa idonsa na kaina kamar daman can rayuwarsa ta takaita akan kallona ne kawai.

“Miya hanaki saka su makaranta”


“Na kai su ba a karba ne”


Na fada ina dan turo baki a shagwabe abunda ban saba ba, kuma ban san dalilin zuwansa a yanzu ba.

“Daman ai ba za akarbe su ba tunda kika bata min rai”


Ya fada yaa ta kallona da idonsa kamar maye, sai a yanzu na fahimci inda zance ya dosa, kar dai kwahi yai min aka ki karbar su a makaranta saboda shi twins ne shi da Abdulhamid.

“Kwahi kai min kenan? Ai ni kwahin ka ba zai kama ni ba”


“Kwarai shiyasa ranar ai kika samu Napep ta kawo ki har gida”

Har yanzu kallona yake yi irin kallon nan kamar ni din tv sa ce.

“To wani abun kika masa kenan?”


Cewar Mama tana murmushi, ni kuma na maida hankali gurin kiran wayata da ke shigowa.

Abdulhamid ne rubuce a screen din wayar, hakan ya saka gabana faduwa ba dan komai na sai dan Abdallah na zaune a falon, kusan tun lokacin da na fito nai bari Abdulhamid be taba kirana da sunan yi min jaye ko sannu ba, ba zan ce dan be ji ba, domin ko last time da Hajiya ta zo ta fada min cewar Abdulhamid ya kawo ta amman be shigo cikin gida ba.

“Hello....”


“Haima”

Gabana ne ya yanke ya fadi jin ya kira ni da sunan da na manta when last ya kirani da sunan.


“Na'am... ”


Na amsa kamar mai koyon magana.


“Kina lafiya?”


“Lafiya Kalau”


“Ina fatar kina gida, gani nan zuwa amman ba zan shigo cikin gida ba magana kawai zan yi da ke na koma”


“To... ”


Ina amsawa ya kashe wayar, idon Abdallah na kaina tana ta min kallon tuhuma, ni kuma na gagara tsayuwa na gagara zama sai yawo na ke da ido kamar marar gaskiya, ba dan komai ba sai dan bana son Abdulhamid ya zo ya tarar da Abdallah, duk kuwa da ban san abunda zai kawo shi ba na san dole daya daga cikinsu ya zargi wani abu. Musamman Abdallah da ya fiye shiga hanci da saka min ido.#TeamAbdulhamind

#TeamAbdallah

#TeamAminu 😜

#TeamHalimatu

“Kamar baki da gaskiya Halimatu...”


Sai da na kalli Mama sannan na kalleshi.

“Bana da gaskiya kamar ya? Wannan wace irin magana ce Abdallah?”


Ya dan tabe baki yana ta wasa da hannun Amal kamar ba shi yai maganar ba. Kamar an daki hannuna sai na yi yai min majiyar, ban san lokacin da na saki wayar hannuna ta subuce ta fadi kasa, a take ta watse a saman tedar da ke falon kamar abar da aka taka da mota ko aka sakawa dutse aka daddaka. Subhanallahi Mama ta furta ni kuma na risina a gurin ina kallon wayar ina jin kamar na fasa kuka tuni idona suka cika da kwalla, har ga Allah na tsani na rasa wani abun da na ke matukar so ko yake da muhimmancin sosai a rayuwata, na san phone ce amman ina jin babu dadi domin samun irinta a yanzu ba abu mai sauki a gareni a lokacin da na ke gidanmu dawainiya ta zata min yawa yanzu fiye da, ga kuma zuwan da Abdulhamid zai yi ban san abunda zai kawo shi ba wata kila ma baya son kowa ya san da zuwansa.+

“Ya akai wayar ta fadi?”


Mama ta tambaya sai an amsa mata muryata na gargada alamar ina daf da fashe da kuka.


“Ban sani ba Mama a hannu ta zame ta fadi”


“Laa shikenan wayar Momy ta fashe bamu da wayar game”


Namra ta fada tana wani bude baki, Abdallah kam ko dago kai be yi ya kalleni ba sai wasa yake da yatsun Amal kamar be san abunda ya faru ba.

“Momy yanzu da wace wayar za mu rika game...?”


Wani bakin haushi na ji ban san lokacin da na dakawa Namra wacce tai maganar tsawa ba.


“Da wayar ubanki... ”


Sai a lokaci Abdallah ya dago ya kalleni sai kuma ya kalli inda wayar take ba ce min komai ba sai dai fuskarsa ta nuna alamar bachin rai, mikewa yai tsaye yana saa dayan hannunsa a aljihu.


“Mama ni zan tafi, kuma yaran nan a yi kokarin saka su makaranta domin barin su hakan nan ba zai yiyu ba ya kamata a san abun yi lokaci na ta tafiya”

Wata uwar harara na watsa masa saboda haushinsa da na ke ji, wacce be san ma ina yi ba domin be kalli inda na ke ba da Mama yake ta maganarsa, ita kuma tana nanata masa cewar za a saka su makarantar, hannu ya saka aljihu ya ciro kudin da ban san ko nawa ne ba ya aje mata a hannun kujerar da take zaune sannan ya karaso inda na ke duke ina ta kallin wayar da na gagara tattarawa na kwashe ya ce.

“Halimatuuu mu kwana lafiya”


Har na yi kamar na bude baki na aika masa da bakar magana sai kuma wata zuciyar ta hanani ganin a gaban Mama ne da kuma yara. Tare ya fita da Amal da Namra Aiman ma ya bi bayansa.

“Halimatu kina jin yana miki sai da safe amman kika gagara karba mishi miye haka?”


Mama ta fada cikin yanayin damuwa da rashin amsa masa da ban yi ba.

“Mama ba ki kohi yai min wayar ta fadi ta fashe ba”


“Kohin zai saka waya ta fadi har ta fashe? Ai naga ko kallon ki be yi ba kuma ba wata maganar ta bacin rai kika masa ba balle ace, abu ne dai da Allah ya kawo”


Ban sake cewa komai ba na tattara wayar na mike tsaye na nufi dakin Mama na zauna bakin gadonta kamar wacce aka kwashewa tunani a kwakwalwa, babu komai a raina sai bacin ran faduwar wayata, ina zaune a gurin yara suka shigo da yan dari biyar biyar a hannu wai Uncle Abdallah ya basu, ni dai ko kallonsu ban yi ba balle har na karbi kudin na adana musu saboda bakin haushin Abdallah da na ke ji.

Ban yi dabarar na karbi wayar daya daga cikin yan matan gidanmu na kira Abdulhamid ba sai da aka sallame sallar isha'i, a lokacin kuma yan zaman majalisar kofar gida sun soma shimfida tabarsu su zauna. Idan ma nace zan yi magana da shi sai dai na koma ta kofar gidan makotan mu wanda hakan ba zai min dadi ba domin a hanya ne.

Ban yi kasa a guiwa ba na karbi wayar Hafiza na lalabo number Abdulhamid a wayarta na aika masa da kira, kamar jira yake a take tai picking din call din yana rangadamin sallama, bayan na amsa na koro masa da bayanin wayata ta fadi har ta fashe.


STORY CONTINUES BELOW

“Oh ni na dauka ko kashe wayar ki kai, domin nata kira ban samu ba”


“Wallahi faduwa tai ta fashe screen din ma ya watse gaba daya”


“Subhanallahi garin ya?”


“Ba zan iya fada ba, ni dai kawai tana hannuna ta subuce ta fadi kasa, ka zo ne?”


“Na zo, sai dai ban karaso kofar gida ba saboda bana son kowa ya san da zuwana, dan ki kawai na zo”


“Ka tafi ko kana nan?”


“Na tafi amman na fi karfin one hour a gurin kamin na tafi”


“Ayyah ban jidadi ba”


“Karki damu zan shigo gobe In-Sha-Allah”


“To Allah ya kai mu”


“Amin mu kwana lafiya”


Ba bari na sake cewa komai ba ya katse kiran, ni kuma na sauke wayar ina ta tunanin abunda zai kawo shi gurina ni kadai, wata kila kum zai yi min jajen abunda ya faru ne ko kuma ya bani wata shawarar, ban raba dayan biyu ba Hafiza ta shigo dakin na mika mata wayarta bayan n goge call din domin Bana son ta san da wanda nai wayar. Sai kuma na nufi inda jakata take na bude na dauko dubu biyu saboda ina son siyo man goge baki da Vaseline din mu daya kare. Hijabina na saka ina Kwalawa Namra kira ta zo ta raka domin ta fi sauran natsuwa da abun hankali, sai dai duk yadda nai ta noke noken na fita ni kadai ban samu sa'a ba har sai da Amal ta gan ni ta biyo da gudu tana kuka, a dole na tsaya na rika hannunta sannan na nufi dakin Mama na shaida mata cewar zan je shagon titi na siyo man shafawa da kuma na wanke baki.

“Ba zaki aika kanenki si siyo miki ba?”


“Ina son fitar ne Mama”


“To Allah ya tsare”


Na amsa da amin sannan na kama hanya ina rike da hannu Amal Namra kuma na gefena na hagu dukansu suna sanye da riga da wando ne yan kanti. Cikin tsananin kunya na ratsa kofar gidanmu na wuce saboda taron da maza yan zaman majalis sukai yi. Wanda na san a nan ma ba zan rasa wanda zai yi gulma ta ba, koma na ce gulmarmu yan gidan gaba daya domin mun tara yan mata Masha-Allah, wanenda aka dade ana zancen wai mai kudi suke jira wasu kuma tuni suka fara yi kanena zargin masu nemansu duk na neman auren suke zuwa ba iskanci ne kawai ke kawo su, ni kuma na dade da yin zurfi wajen sanin cewar aure da haihuwa da mutuwa da rayuwa duka na Ubangijin Annabi Adamuna, wato Allah S W T wanda ke rubutowa bawa abunda zai same shi tun gaban bawa ya zo duniya.

Lokuta da dama kan jarabi bawa da abu ba dan Allah baya son bawan ba sai dan gwada karfin imaninsa da kuma aikinsa. Idan na tuna mahaifina da mahaifiyata ina samun kaina a cikin wani kogo mai cike da tausayinsu musamman ubana wanda na san shi mutane za su zaga, kuma shi zai fi kowa shiga damuwa, domin bayan yan dakin Mama akwai na dakin Inna waenda sukansu yan mata ne da suka kasance a karkashin inuwarsa. Gashi lafiyar kafafuwa ma bata wadace shi ba.

“Momy a nan za mu yi ta zama? Daddyn ba zai zo ba?”


Maganar da Namra tai ka katse min zancen zuci da na dade da yin zurfi a cikinsa, gabana ya fadi ba faduwa ta tsoro ko fargaba ba, ba faduwa ta irin amsar da zan bata ba, ko kuma abunda zan mata ta fahimta ba, faduwa dai irin ta ko wace uwa mai yayana yana daya daga cikin dalilin daya hana ni fitowa a gidan Aminu gudun irin rayuwar da yayana za su yi idan bana gidan, sai dai kuma yanzu da suke hanuna kuma ya rufe idonsa daga kallonsu balle waiwayarsu ya rayuwarsu zata kasance?  Mama tana yawan fada min ba ko wane namiji ne zai auri da yayana ba, idan ma ya aure ni ba zai yarda na zauna da su ba, anya idan na bar su a gida za su samu kulawar da nake musu fatan samu? Ya makomarsu zata kasance lallai juma'ar da za tai kyau tun daga laraba ake gane ta, indai har yau ba tai musu kyau ba ya gobensu kenan?

STORY CONTINUES BELOW

“Momy ga fa shagon can, ko ba shagon Takur ba?”


Namra ta fada tana girgiza hijab dina, wani irin numfashi naja na sauke hawayen kam tuni suke wanke min fuska sai dai ban fahimci hakan ba sai da Namra tai min magana ganin ina kokarin wuce shagon da ban san mun kawo ba sai yanzu.

“Eh shi”


Na fada ina share hawayena sannan na karasa gurin shago, sai da ya sallami duka mutanen da suke gabana sannan na mika nawa kudin na fada masa abunda za a bani ya mikon na siya ma Amal da Namra biscuit na rike biyu domin na san indai Adnan da Aiman sun gani sai sun tambaya ina na su? Bayan na karbi canji na juyo tare da yarana muka kamo hanyar dawowa gida. Tunanin dai na dazun ya sake fado min a rai, har na kasa fahimtar shi Aminu ya yafe min su ne gaba daya hakan ya saka ya kwashe har wata daya ba kira ba aike ko kuwa yana jira sai su kara girma ne ya karbe su?

Karar qaraurawar keke na ji kamin na yi kokarin kauchewa tuni keken ta bugeni ni kuma na gibi Namra ni da wadanda suke kan keken muna fadi kasa, saurin tashi nai cike da kunya Allah ma ya tsare ba mutane sosai a gurin da na ji kunya kam. Mutumen da ke rike da keken yayi saurin karaso inda na ke ya daga Namra yana kabe mata jikinta tare da rika fuskarta.

“Cutest ba ki ji ciwo ba?”


Ta gyada masa kai, Amal kam da gudu taje ta dauke chocolate din da ya fadi a gurin dawo inda nake da gudu ta boya.


“Daddy wacan yar yarinyar ta dauke min chocolate dina wanda ban fasa ba”

Wata yar karamar yarinya ce maganar wacce bata wuce sa'ar Adnan ba, kananan kayana a jikina sai dan kwalin atamfa da aka daura mata, a kusa da ita wata matashiyar mace ce tana sanye da abaya wacce na ke kyautata zaton budurwa ce ganin jikinta babu mayafi sai hula mai kyau sai kyalli take kamar an watsa mata kananan taurari a jiki.

“Sannu....”


Ta fada tana dan kawarda fuska kamar tana jin kunya ta.


“Muna ta miki horn amman baki ji ba, har Daddy ya kade ki”


Yarinyar ta fada ita tana kallona.


“Ko kuma ku baku lura ba? A hanyar nan ba dan keke kawai akai ta, at least tun da kun gan ni agefen hanya ai sai ku koma tsakiyar hanyar ku wuce”


Na fada da dan fusata domin har ga Allah na ji haushi kuma ba da yarinyar na ke ba da mahaifinta nake.

“Hey cutest hold this for your Mom”


Da murmushi ya mikawa Namra ledar da ta subuce daga hannuna ta fadi bayan ya kwashe kayan ciki ya saka a ledar. Ni kan ko kallona be yi ba ya nufi inda kekensa take irin kenan nan ce mai tsada sosai ya tashi keken, dogon jeans ne a jikinsa sai yar vest fara ya daure jacket dinsa a kunkurunsa, kana ganinsa ka san irin mazan nan ne marasa kunya domin namiji mai kunya ba zai biyo hanya da vest ba duk dai ban san inda suka fito ba, sai da ya hau keken sannan na daga yarinyar da ke kiransa da Daddy ya dora ta daga gaban keken.


“Kin ga yarinyar ta dauke min chocolate kuma mug dina ya fadi? Sai ya kenan?”


Yarinyar ta fada yana nuna inda Mug din yake sai a lokacin na lura da mug din, da alama yarinyar irin yaran nan masu shegen kodin tsiya da tsiwa, domin har wani juya ido take tana motsa baki kamar wata babba. Babbar kuma wacce ta fi tsananin kama da shi ta hau baya tana dago min hannu.

“Bye..... ”


Ikon Allah su kuma haka suke? Sun buge ni ko sannu babu? Ko ma miya tsayar da ni kallonsu oho, daman can da ganinsu ai ba gidan mutunci suka fito ba. Ni kadai nake ta mita ta a cikin raina har muka iso gida, sannan na karbe chocolate din da Amal ta dauka na yarinyar na jefar, babu irin kukan da ba tai ba na ki na kulata har ta gaji tai bachi.

STORY CONTINUES BELOW

Washe gari bayan mun gama karyawa na fara shirin zuwa aikina, kanwata Husna ta shigo wai na zo falon Mama ana kirana, ta gwarin guiwata na nufi falon Mama ance karka ji tsoron kira ka ji tsoron laifin da ka aikata, na shiga falon da rabon ido dan ganin mai kirana sai naga Mama ce kadai a falon hannunta rike da farar leda mai rubutu da zanen wayoyi a jiki.

“Mama ke kike kirana?”


“Aa Abdulhamid ne yana waje saka hijabinki ki masa godiya waya ya kawo yace a baki”


Ta amsa min cikin rashin jindadi da walwala. Dakinta na shiga na dauko hijabi na nufi kofar gidan. Sai na same shi cikin farar motarsa zaune yana danna wayarsa, farin gilashin motar na kwankwasa da zimmar ya bude min na gaishe shi kuma nai masa godiya sai na ga ya miko hannunsa daga can cikin motar ya bude min motar da alama so yake na shiga ciki na zauna. Haka kuwa akai na shiga uncomfortable na zauna sannan na mika masa gaisuwa be amsa min ba kuma be kalleshi ba har lokacin taba wayarsa yake.

“Yau ba zaki je aiki ba ne?”


“Zanje ina cikin ne aka ce kana kirana”


Sai a lokacin ya dago ya kalleshi a natse. To je ki karasa shirinki sai na kai ki. Kallonsa nai har na bude baki na ce masa a a sai kuma na tuna da abunda ya faru da ni a lokacin da nai gardama da Abdallah ban sani ba shi ma ko yana da kohin kar ya min na kasa samun abun hawa.

“To by the way na ga waya na gode sosai”


“No no no never mind je ki shirya kawai”


Ya fada yana dauke idonsa daga barin kallona, ni kuma na fita daga motar na shiga cikin gidan na karasa shirina sannan na shiga falon Mama dan mata sallama kuma n karbi wayar da har yanzu bana jin murnar siya min ita da yai. Wani kallo tuhuma Mama tai min sai duk na ji babu dadi a take shikan shikan rashin natsuwa suka bayyana a jikina da kuma fuskata.

“Ina kyautata zaton Abdulhamid be san Abdallah na zuwa gidan nan ba, kamar yadda yau din ma nake kyautata zaton Abdallah be san Abdulhamid ya zo ba, sai dai ke kin sani kuma ina tunanin kin san daidai da rashinsa, na dade da fahimtar cewar Abdallah yana son ki ko dan saboda kulawar da yake nunawa yaran nan, sai dai abunda ban sani ba kuma nake son sani a yanzu shi ma Abdulhamid son ki yake yi?”


I find it so difficult na amsa mata, ni kaina a yanzu ban sani ba iyakar abunda na sani Abdallah na so ko be fada min ba ya nuna min balle kuma ya fada min tun a lokacin da igiyar auren Aminu take kaina, ba zan iya shaidar abunda ya kawo Abdulhamid a yau ba, domin bana da tabbaci yana so na har yanzu kamar yadda zuciyata ya kasa goge shi a raina, ko kuwa dai tausayine kawai a tsakaninmu.

“Dukansu yan'uwna junane Halimatu kin sani, bayan yan'uwanta ta jini ma su tagwaye ni a ciki daya suka fito a rana daya kuma a mahaifa daya, mace daya ta raine su uba daya ya haife su, karki aikata abunda zai zame mana matsala ni da mahaifinki domin uwar data haifi mahaifinki ita ce ta haifi mahaifin Abdallah, mahaifin Abdallah da mahaifinki uwa daya uba daya suke karki lalata alaka Halimatu”


“Ban kira Abdallah na ce ya zo nan, zuwan Abdulhamid a yau ma bana da masaniya sai da na ganshi”


“Ba shi nake kokarin fahimtar da ke ba, ki sallami daya daga cikinsu saboda gudun abunda zai iya faruwa a gobenki, idan kuma dukansu ba ki ra'ayinsu to ki sallame su duka shi ya fi alheri Allah ya tsare a dawo lafiya”


Ya miko min ledar sannan ta mike tsaye ta fice ta bar a falon tsaye, ji nai kamar a san saka gatari an sare duk wata gaba ta kuzari da ke jikina. Kamar wata marar lakka haka na fito daga cikin gidan na nufi inda motarsa take na bude na shiga shi kuma ya tashi motar muka hau hanya.

“Ban jajanta miki kan abunda ya faru ba, na yi hakan ne saboda na baki lokaci ki huce bacin ranki, kuma bana son wata magana ta shiga tsakanina da ke a lokacin da kike idda, ko da ko gaisuwa ce, amman yanzu ina jin I'm free to name what ever i want daga gareki saboda kina da yanci”


Ban ce masa komai ba ina ta kokarin maida hankalina gurin titi amman na kasa, magaganun Mama sun tsaya min a kai.

“Ban jidadin abunda ya faru ba, Aminu kuma be yi miki hallaci ba amman mai hakuri yana tare da nasara, kuma kansa yai ma na san wata rana zai yi nadama ya gane cewar yayi kuskure a lokacin da ke din kin masa nisa”


Still ban ce masa kuma ba, hakan kuma be hana shi cigaba da magana ba.

“Jarabawa ce ta rayuwa, you know wani lokacin Allah yana jarraba bayinsa da abubuwa daban dabam, kamar yadda ya jarrabe ki da miji kamar Aminu ni kuma ya jarabe ni da cutar da na kasa samun maganinta har yanzu, wanda hakan yasa har bana son kawo tunanin aure a rayuwata....”


Juyowa nai na kalleshi a take zuciyata ta cika da tausayinsa.


“A da na sadakar na cire rai daga samun lafiya, kuma na aje duk wani abu na neman magani, amman daga lokacin da na ji cewar Aminu ya sake ki sai na nemi duk wannan abun na rasa, na ji cewar a yanzu ya dace na nemi magani kuma na nemi aurenki ko da ba za ki so ni ba, ba dan komai ba sai dan na faranta miki kuma na cika burina a kanki, ban sani ba ko akwai soyayyar Abdulhamid a zuciyar Halimatu ko a a, idan ma babu zan yi kokarin samawa idan kuma akwai sai na kafafata na ingantata”


Ya karasa daidai lokacin da ya faka motarsa a ma'aikatarmu sai ya zauna daidai yana dubana da fuskarsa ta tausayi.

“Na san za ki mamaki jin irin wannan maganar daga bakina kai tsaye kuma a karon farko da na ziyarce ki, daman abunda na ke son mu tattauna kenan a jiya, saboda ina son nai mata sha daya ne idan ma hadiye zuciya zan yi na mutu na san makomata idan kuma dama za ki ba ni nan ma na san makomata, ni dai har gobe ina son ki Halimatu kuma ina alakanta abunda Aminu yai miki da rashin aurenki da nai ta hanyar kin yarda da shawararki ta cewar na aureki na cigaba da neman magani za ki yi hakuri da ni a haka, ko kuma ki jira ni na nemi magani amman duka na ki yarda, na san da cewar Allah ta rubuto hakan zai faru amman komai yana da sila....”


Jimmm nai na dan wasu mintuna sannan na ya cigaba.


“Wata kila zuciyarki ta raya miki cewar na cika son kai a yanzu ko? Kina da gaskiya ba ko wace mace ce zata auri namiji irina ba, shiyasa ban gwada neman kowa ba sai ke ban taba saka son wata mace a raina ba sai ke kuma har gobe ke ce a raina Halimatu, zan iya baki damar yin shawara matukar kika ji za ki iya aurena a haka, ko kuma ki jira har na samu lafiya zan fi kowa farinciki, idan kuma kika ji ba za ki iya ba nan ma ba zan zarge ki ba.... ”


“Zan shiga office na gode”


Shine kawai abunda na fada na share hawayen da suka fara min zuba tun a lokacin daya fara maganar.......

Anya Halimatu zata iya zabe tsakanin dan'uwa da dan'uwa?

Anya zata iya zaba tsakanin mutuwa da rayuwa? Domin auren namiji irin Abdulhamid mutuwa da rayuwa ne.

A ganinku waya dace ta zaba?

Ina labarin Aminu ne?

Ko ya Kabir yake?

Shi kuma Abdallah haka yake da an bata masa rai sai kohi 🤣🤔

#TeamAminu

#TeamAbdulhamid

#TeamAbdallah

#TeamHalimatu

#ZawarcinHalimatu

#Gobena

A bakin gate din gidan ya tsaya da kekan Namra da ke gaban keken ta sauka, sannan Barra ta sauka suka nufi yar karamar kofar gate din sukai knocked mai gadin ya bude musu suka shiga sannan ya budewa Ahmad gate din gaba daya ya shiga da keken ciki. Katon gida ne plate mai dauke da shuke shuke gaban gidan kamar bayansa yake domin za kai tai kallon fuskar gidan amman ka gagara gane kofar shiga har sai idan an nuna kama ka, daga fentin kofar har fentin gidan har mayan motocin da ke harabar gidan duka farare ne tasss, irin farincikin nan mai burgewa da dare da rana kuma ya kawata maka ido idan kuma ya hadu da hasken rana sai ka dauka ba a Nigeria kake ba.

   Bangaren da aka faka motocin ya nufa ya sauka daga kan keken ya kai hannunsa ya bude gareji ya saka keken ciki sannan ya maida garejin ya rufe, sannan ya soma tafiya cikin wani irin taku da ba na sarauta ba kuma bana kasaita ko ci da kai ba, sai dai duk wanda zai kalli yadda yake dora kafarsa a kasa zai yi tsammanin tausayin kasar yake ko kyamarta, wata kila ma a iya fassarashi da mai nuna isa da dagawa.

Zagayawa yai can baya inda ya sama kamar dabam da gidan kofarsa ma a can baya take, tun kan ya karasa ya saka hannunsa ya kwance daurin jacket din dake kugunsa, sannan ya kai hannunsa ya tura kofar ya shiga. Sanyin ac ne da hasken garin gulub tare da dadadden kamshi suka fara masa lale marhabun, katuwar plasma kuma na ta aikinta, remote ne farkon abunda ya fara dauka ya canja channel din daga Al Jazeera zuwa Tvc news. Sannan ya nufi hanyar dakinsayana shiga ya rana jikinsa da tufafin da ke jikin nasa ya daura tawul, a take farin fatar jikinsa da siffarsa ta zati ta bayyana, cikin wani irin ya na saka su a washing machine sannan ya shiga ya bawa jikinsa hakkinsa sai da ya tabbatar komai na jikinsaya wanku sannan ya fito ya shirya cikin wata farar shadda mai kyau da haske zanen jikin shaddar ma abun kallo ne balle kuma aikin da ke jikinta.

Wani tsadden turare ya dauko ya saka bayan ya saka wani a cikin jikinsa da vest din da zai saka. Murmushi yai yana kallon kansa a madubi, shi kansa ya san yayi kyau balle kuma da ya dora hular da ta dace da shaddar. Sajen fuskarsa ya kwanta gwanin sha'awa har wani shining yake.

  Wallet dinsa ta fara ziyartar aljihunsa kamin makulin mota da sababin kudade su biyo baya, sannan ya dauki agogon hannunsa ya saka, for the second time ya sake duba kansa agaban katon madubin da ke dakin madubi da mutun zai iya ganin har kasansa da takalminsa. Cike da annshuwa ya fito daga dakin zuwa falonsa sai ya duba agogon hannunsa sannan ya zauna a saman manyan cushion din ya kalli labarai na yan mutuna kamar mai jiran ciron lokaci domin tsadadden agogon hannunsa na nuna 9pm ya mike tsaye ba tare da ya kashe tv ba ya fice daga falon.

Bangaren mahaifiyarsa ya nufa wacce ta zame masa dole a duk lokacin da zai fita ko da zuwa nan da kofar gida ne sai ya sanar mata, hakan ya saka cousins dinsa da yan'uwansa and friends suke kiransa da Mommy's Boy domin har time take ba shi na fita da dawowa matukar ba aiki zaije ba ko wani lalurar na dabam wanda ita ma kanta ta san mai muhimmanci ne, duk da kasancewarsa ya girma har ya haifi ya mace yar shekara tara bata daina masa haka ba, shi kansa ya saba abun ya bi masa jiki idan ya fita be sanar da ita ba sai ya ji kamar ya aikata wani babban zunubi, ita ce abokiyar shawararsa kuma abokiyarsa domin komai zai yi sai ya sanar mata ko da ko abun be taka kara ya karya ba, hakan yasa take sanin ko wane sirrin na zamantakewar aurensu, domin a cikin dabi'un daya sabunta da su a gurinta ko dankwali ya siyawa matarsa sai ya siya mata kuma sai ya fada mata tun kamin ya siya din, idan kuma ya siyo zai kawo mata ta fara gani ta zaba ko ta canja masa tukuna ya kaiwa matarsa.+

Ya shiga falon da fuskarsa da annuri kamar sabon ango, daman can yana da irin fuskar nan ta samarin aljanna wadanda zaka gansu kullum fuskarsu kamar suna murmushi ko da kuwa ba murmushin sukai ba ga haske fuska da haiba, ga natsuwa da kwarji kamar wani Zaki.

  Hakimce take saman kujera sanye da wata holland yar ubansu wuyanta ya ji zinari kamar yadda hannunta ke amsa amo a ko wane motsi da tai, kallo daya za kai mata ka karanci sifofin da ke fuskar mahaifiyar sune a fuskar dan, kamanni na hanci baki da kuma ido a siffa da sura da hallita irin ta da'namiji kuma Ahmad Gwarzo kamar yadda mahaifiyarsa take kiransa.

“Momy barka da dare.... ”


Ta juyo cike da isa tana kallonsa, irin kallon nan na farinciki da kaunar uwa ta ga danta.

STORY CONTINUES BELOW

“Barka da Gwarzo irin wannan shiri haka ina zuwa?”


“Zance zanje mana Mom”


A yayinda kalmar zancen ta dira a dodon kunnenta sai ta za me mata kamar wata mummunar kalamar marar dadin jin, annushuwa da ke fuskarta ta sai ta gushe murmushin kamar na dole. Dauke kai tai kamar ba ita ya bawa amsar ba ta maida dubanta gurin plasma.


“Bari na je kai na saba alkawari tace na zo 9”


Ya fada yana shirin juya daman can tun da ya shigo be zauna ba.

“Karka wuce 10pm”


Ta fada bayan ta kalli agogon zinarin da ke jikinta fuskarta babu alamun wasa. Juyowa yai kamar zai ce wani abu sai kuma yai murmushi ya juya ya fice. Ita kuma ta bishi da kallo tana jin kamar ta hana shi tafiya zancen, Hajiya Uwani irin iyayen nan ne da ke kishin matan yayansu musamman Gwarzo da bata hada shi da kowa ba a duniya, ba tun ba ta saba kashe masa aure ta kan saka shi ya saki matarsa idan zamanta a gidan be mata ba ko ma ta sake ta da kanta wani lokaci, wasu matan ma da kansu suke neman fita idan suka ga matsuwar ta musu yawa, ba dan kuma babu arzikin ki akwai shi har na zubarwa amman haka take bi ta takurwa matan da Ahmad Garba Gwarzo yake aurowa har sai ta fitar da su a gidan, Hajiya Uwani na da wani irin hali da ba san mutanen Kano da shi ko ma na ce mutanen Gwarzo domin daga ida har mijinta yan asalin karamar hukumar Gwarzo ne, wannan dalilin ya saka daga abokan Ahmad har ita kanta Momy da duka familynsu suke kiran dan nata da Gwarzo.

  Juwuriyya ce mace ta tara da Ahmad ya aura kuma ita ce mace da ta jajirce a wajen zama da shi har tai nasarar haifa masa ya mace wato Namra, duk kuwa da irin kin son haihuwar da Hajiya Uwani take yi, ta jure duk wani cin zarafi da muguwa daga uwar mijinta saboda kawai ta zauna da Ahmad, kuma ta zauna da shi ra rayu da shi na tsawon shekara biyar kamin tai hadarin mota ta rasu. Hajiya uwa bata yarda danta ya cire kudi mai yawa da sunan yi ma mace hidima idan ma yayi ta kan rage tace ta yi yawa, haka ta ke juya duk matan da Ahmad take aure kamar waina tana kishin matan Ahmad sosai.

   Latest Benz ya shiga White color daman duk motocin da suke gidan farare ne, sai dai kawai sunanyensu da kudinsu su banbanta, tun kan ya kai gate mai gadin ya bude masa gate ya fisge motar kamar domin shi kawai akai titin GRA ring road.

in time ya isa kofar gidan Alhaji Yunusa Dan-Gaske, kamin ya danna horn ya ka kai hannunsa ya dauki iPhone dinsa da ke cikin motar ya kira Zainab.

“Hello Ina kofar gidan”


Ya fada kamar wani dan sarki sannan ya danna horn aka bude masa gate din ya kunna kai a harabar gidan..
HALIMATU POV.

*Bayan sati biyu...*


Sati daya nai ina raya ko wane dare da sallah da salatin Annabi, na mikawa Allah zabina a tsakanin zama a gida nan ba tare da aure ba da kuma yin auren, domin ni ba dan Abdulhamid ba da ban kawo maganar aure a kusa ba, a da na yi planning akan na cigaba da aikina na rike yayana har zuwa wani lokacin domin ban shirya fuskantar wani kalulen zaman aure ba a yanzu saboda wahalar da na sha a gidan Aminu, sai dai yadda Mama da Inna suka tsaya kai ta fata wajen ganin na cire wannan burin a raina yasa na sassautawa kaina, ga kuma rokon Allah da nai sai ya saka min son auren a raina fiye da lokacin da nakr budurwa ma. Na roki Allah ya zaba min a tsakanin yin auren a yanzu da kuma hakura da auren har na wani lokaci, amman ban roki Allah ya zaba min a tsakanin yan uwa guda biyu ba wato Abdallah da Abdulhamid, a iya ganina da fahimta Abdulhamid ya fi Abdallah cancantar aure a yanzu domin shi be taba auren ba gaba daya a rayuwarsa, kuma ni ya so tun a lokacin da nake budurwa yanzu kuma da auren ya mutu ya dawo min. Ko ba komai ya hade kwadayinsa na furta min kalmar so ko cancantar zama da Aminu be taba fadin wata mummanar kalma akan Aminu ba, duk kuwa da irin sanin da yai na irin zamantakewar auren da muke da halayensa, be taba daga waya ya kira ya fada min wani abun marar dadin ji ba, idan har ya kirani sai idan wani babbab dalilin ne ko kuma idan mun gadu da shi a gida. Tsabanin Abdallah da yake yawan fada min abubuwan da Aminu yake aikatawa a waje bayan yabon surata da yake da nuna yana sona tun daga lokacin da ya dawo daga kasarsa ya saka ni a idonsa. Wani lokacin har mamakin yadda Abdallah yake min wasu abubuwan na ke domin an tabbatar da ace shi ne a matsayin Abdulhamid da ya so ni tun ina budurwa da Allah kadai ya san irin chabar da za ayi.

   Na fi jin natsuwa da Abdulhamid fiye da Abdallah, wata kila saboda zuciyata ta taba son sa ne, ko kuwa dan ina tausayinsa ne oho, ga shi ya dage sai kai kawo yake, domin idan be zo yau ba, to zai zo gobe tun ina fargabar kar wata rana Abdallah ya tarar da shi har na daina, ko da yake Abdallah ma tun daga wacan ranar da ya min koho wayata ta fashe be sake dawowa gidan ba, kuma be sake gwada kiran sabuwar wayar da Abdulhamid ya siya min ba, hakan kuma ba karamin dadi yai min ba, domin ya bani damar sakewa da kula Abdulhamid a duk lokacin da yai min sallama.

   Ta wani bangaren kuma ina yabon Abdallah sama da Abdulhamid, domin shi mutum ne mai son yara ko na ce mutum ne mai son yayana tsabanin Abdulhamid da ko fuska baya sake musu daman can kowa ya sani Abdulhamid ba a mutum ne mai son yara ba, sai dai ban dauka har da nawa ba ganin kamar ni din ta dabam ce a gurinsa. Yes yana nuna min so da kulawa irin wadanda na rasa a gidan Aminu, shi tun a yanzu ya fara nuna min su sai dai a duk lokacin da muke waya be taba cewa ya yarana ko ya gaishesu balle kuma har ya riko musu wani abun taba. Ba kamar Abdallah ba da har saman jikinsa suke hawa su karbi wayarsa su yi game, rashin sakewa da yarana yana daya daga cikin abunda yake daga min hankalin bayan maganar daina aikina da yai min idan har na amince zan aurenshi. Ya nuna min cewar shi yana da kishin da ba zai iya barina nai aiki ba, kuma yana da halin da zai iya dauke min komai, daga lokacin da yai maganar daina aikina zuwa yau na kasa yanke hukunci kuma na kasa zaba na kasa shawara da kowa, ba dan komai ba sai dan na san duk wanda zai shawarce ni zai ce na daina aikin na yi zaman aure. Na san dole ne Abdulhamid ya ji tsoron naje nai aiki saboda kar na hadu da wani namijin ya burge shi bayan shi baya iya komai, wai da gasken ne baya iya komai din ko kuwa dai gwadani yake ya ga idan zan iya zama da shi? Ko kuma karfin soyayyar da nake masa? Ni dai na san ba dan soyayya kawai zan aure shi ba har da tausayin halin da ya samu kansa wanda na so yin wannan jihadin tun a baya.

Yana yawa fada min sai na ji na ki ji, saboda za ayi ta kananna maganganun akan mu, ganin ni bazarawa ce har da yaya hudu shi kuma saurayi, ko da yake ba irin yaran samarin nan ba ne irin tazuran nan ne da suka dade ba su yi aure ba, amman duk da hakan na san sai yi magana, ban kawo zancen rashin lafiyarsa ba saboda na san ba kowa da ya san da matsalar ba.

STORY CONTINUES BELOW

***   ***    ***


Yau dai na yanke shawara ba zan je aiki ba sai na sake gwada nemawa yarana wata makarantar ko Allah zai saka a dace idan kohin Abdallah ya janye daga jikinsu ko kuma jikina zance tun da ni ce mahaifiyarsu kuma ni ce sila.

  A Napep na saka su muka kama hanyar Gwarzo International School, babbar makaranta ce da babu irinta a garin Gusau makaranta ce da ta amsa sunan makaranta kamar yadda na ke jin ana fada babu kamar dalibansu, sai dai makaranta ce mai tsada sosai ba kowa ke iya saka yaransa a makaranta ba saboda kudin da ake kashewa.

   Ni kaina na san ba lallai na iya jurar biya musu kudin ba, zan dai gwada ne kawai idan an karbe su sun fara karatun sai na canja musu ni dai burina kohin da Abdallah yai mana ya karye kawai. A lokacin da mai napep din ya faka bakin gate din makarantar na ji wani iri ganin irin manyan motocin da ke kawo yaran makarantar. Sai dai ban yi kasa a guiwa na biya mai Napep din kudinsa na kama hannun yarana muka nufi cikin makarantar, wani abun da zai kara burgeka da makarantar yadda aka tsaurara tsaro domin sai da aka gama bincikamu sannan aka bar mu muka wuce a nan na soma ganin malaman makarantar har da turawa.

  Da tambaya na isa office din principal din dake can hawa na biyu, office ne da aka kawata shi da kayan alatu kamar ba a cikin scul ba, guri na samu na zauna daman tun kan na shigo office din sun fada min cewar yana gurin Assembly.

Su Namra suka zauna a a doguwar kujerar da ke kusa da kofa ni kuma na zauna a kujerar da ke kallon teburin principal din. Bayan kamar minti goma zuwa shabiyar aka turo kofar office din aka shigo. Mutumen nan ne da ya kade ni da kekensa yana rike da hannun yarinyar da wacce ta sha kitso mai kyau kuma take tsananin kama da shi, shadda ce a jikinsa ita kuma tana sanye da uniform din makaranta dan guntun skirt ne blue da farar riga sai takalmin makaranta da Scul bag a bayanta mahaifinta, sai wani babbata fuska take da alama wani abun akai mata shi kuma yana ta sham kamshi sai kace wani hege😏

Ni dai kallo daya nai musu daga shi yar sagartacciyar yar tasa na dauke kai shi ko kallon inda muke ma be yi ba.

“Ke tashi ta zauna...”


Fuskata na gabas na jiyo munafukar muryarsa yana yi ma Namra magana wai ta sauka ta bawa yarsa guri ta zauna, juyo nai ina masa kallo uku saura kwata na dakartar da Namra da ke kokarin tashi ta bar yar tasa guri...

“Ke karki tashi, ai da be fi da ba yadda ka kawo yarka a makaranta haka na kawo tawa, dan haka ba zata sauka daga kujera ba tun da kujerar makaranta ce ba da gidan kowa ba”


Yadda kasan ina fada da mutum mutume haka yai min, yana ta lasa wayarsa kamar ba da shi na ke magana ba, ni ma haushi na ji na bawa banza ajiyarsa ina gyara gyalen abayata dake kaina. Muna haka principal din ya shigo, wani abun da zai baka haushi yana ganin mutumen ya fara rawar jiki da shi har da janyo masa kujerarsa ya zauna.

“Ai na san abunda ya kawo ka ranka ya dade daman na san sai Karamar Hajiya ta tsokano mana kai”


Principal din ya fada yana ta washe hauro, da alama dai wannan mutumen yana dan ba shi lashi ne shiyasa ya ke ta masa far'a yana yin kamar be gam mu ba.

“Karamar Hajiya tace kun dake ta”


“Wallahi ranka ya dade bulala biyu ne kawai akai mata ita da yarinyar da sukai fadan”


“Amman kasab ka'idar makarantar nan ba a duka? Then why za ku dake su daga ita har wacan yarinyar?”


“A yi hakuri ranka ya dade dan horo ne kawai ba wai wani abun ba”


“To wannan dai ya zama na karshe”


“In-Sha-Allah ranka ya dade In-Sha-Allah”


“Hajiyata wuce class kinji”


Yarinyar ta dan bata fuska.

“Daddy baka ba ni komai ba”


“Kin san ai bana baki kudi”


“Daddy pls”


Sai kawai ta saka kuka, tsawa ya daka da alama kuma tana tsoron fushinsa ba shiri ta ranta a cikin na kare ta fice daga office din. Sai ta fice sannan principal din ya kalleni.

“Hajiya lafiya dai?”


“Yarana na kawo ina son na saka su a makarantar nan”


“Su duka? Ina mahaifinsu yake?”


Na dan yi shiru na dakiku kamin na amsa masa.

“Baya kusa shi ya ce na kawo su”

“A ka'idar makarantar nan maza suke kawo yara ba mata ba, sannan ba ma karbar yara a irin wannan lokacin saboda an yi nisa da karatu ko wane aji akwai adadin dalibin da ake bukata”


“Dan Allah ku taimaka min zan biya kudin makarantar ko nawa ne In-Sha-Allah”


“Zancen biyan kudin makaranta ai wajibi ne, taimakon ne dai ba zai yi yu ba yanzu”


Rasa nai abunda zan sake ce masa sai na bata fuska kamar mai shirin yin kuka.

“Miya hana su karatu da wuri?”


Mutumen ya tsomo min baki a magana yana kallon yarana.

“Canja musu za ayi”


Na bashi amsa kamar an min dole.

“Saboda mi za a canja musu scul din? Kuma kika kawo su a wannan makarantar”


“Ra'ayi”


Na fada ina mikewa tsaye cike da fusata sai a lokacin ya kalleni domin duk maganar da yake su yake kallo ba ni ba.

“Ya ana magana za ki tashi kuma kika sani ko a taimaka miki... ”


“Bayan ka ce babu a taimakon da zaka iya yi mana? Sai ka ce mu ba kudin za mu biya ba ai kyauta na roka ba, kuma ba wannan ce kawai makaranta ba”


Principal din ya fada, ni kuma na bashi amsa a fusace domin har ga Allah na ji haushi wato saboda ya ga alamar mu ba masu arziki ne kamar wannan ba shine zai wani ce a tainaka mana tun da ya saka ba ki bayan farko ya fada mana ba wani taimako, irin wannan makarantar ma ko yaran ka sun yi karatu aciki wulakanta ka za ayi da yaran. Har principal din ya bude baki yai magana sai mutumen ya daga masa hannu yana lasa wayar da ta zame masa dole. Ni kuma na sako yarana a gaba muka baro makarantar cike da dana sanin zuwan da nai.

Sai da na sauke su gida sannan na wuce gurin aikina cikin damuwa, damuwar rashin karatunsu da kuma na abunda ya faru a makarantar yau.

Na yi mamakin ganin wani a kujerarta mamakin ba dan kankane ba sai kuma tsoro ya biyo na soma rayawa a zuciyata ko sun kore ni ne kuma? Ko kuma wani abun ne? Ban cewa Emanuel komai ba balle kuma bakon mutumen kai tsaye na nufi office din oga Dahiru.

Sai na fara knocked bayan ya ba ni izinin shiga na tura na shiga. Gaisuwa na fara mika masa a maimakon ya amsa min sai ya kai hannu ya dauki wayarsa ya shiga waya da wanda na ke zaton abokinsa ne domin yanayin firar da yake ya nuna haka, ina tsaye a gurin har yai wayar ya gama sannan ya kalleni da murmushi a fuskarsa kamar zai ce wani abu sai kuma ya mike tsaye ya zago inda na ke ua miko min hannu.+

“Congratulations kin hau matsayin Kabeer a yanzu kin samu karin mukami....”


A tsakanin miko min hannunsa da yai da kuma sanarwar karin girman sai na rasa wanne yafi ba ni mamaki, miyasa za a kara min girma kai tsaye bayan akwai waenda suka fini cancantar hawa kujerar Kabir? Da wata manufa yai ko kuwa dai rabo ne ya koka kamar yadda na kowa yake kokawa? Ban ankaro ba na ji na rika hannun nawa yana shaking.


“Congrats Dear”


“Kabir fa?”


Na tambaya bayan na yi saurin cire hannuna daga na shi, ina ta fargabar kar ace min ya mutu. Sai ya juya ya koma kujerarsa ya zauna ni kuma na bi shi da kallo.

“Kabir ya samu tabin hankali, abun nan ya taba shi har cikin kwakwalwarsa, a yadda suka rubuto mana ma an tafi tashi lagos yanzu haka, bayan an bar Kaduna da shi”


Tausayinsa ya kamani ni a lokacin da yake can yana rashin lafiya yana fama da kanshi a lokacin aka dauki position dinsa na aiki a aka ba ni, da ace ba ni ba ce da murna zan hau shi yayinda shi yake can hana fama da kansa.

“Ku kuka cire shi daga aikin?”


“Dole ne wannan ai Halimatu saboda kamfani ne ba aikin gobnati ba, ba za mu iya jiransa har ranar da ya warke ba, ko da ma ya warke ba za mu iya sake daukarsa aiki ba”


Babu tantana idan na sake bude bakina kuka ne zai fito, hakan yasa ban sake ce masa komai ba na juyo kamar kazar da kwai ya fashewa na fito daga office din.

“Halimatu....”


Na ji kiransa bayan an fito daga office din, juyawa nai na koma cikin office din ba tare da na amsa ba, sai ya miko miko min wata takardar da ke tabbatar da zamana a position din, karasa nai cikin rashin kwarin guiwa na karba na fito. Na sake dawowa office din mu cike da damuwa ina zaunawa a kujerar da Kabir yake sai hawaye suka ce min sallamu alaikum, babu wani dan 'adam da za ayi ma bushara da karin girma a duniyar ya ji babu dadi sai ni da tawa kaddarar ta zo a haka, ba san abunda ya hanani sukuni da farinciki ba, na kasa samun jindadi da annashuwa, tun ina hawaye kadai har na koma yin kuka mai sauti, Emanuel ne yai ta ba ni hakuri amman sai na ji kamar yana horara min wutar kukan a zuciyata, bayan ko wace dakika biyar fuskar Kabir ce take min gizo, rayuwar da mukai a baya idan zai miko min wata takardar ko ya karba ko ya min wata maganar a cikin har da yawan murmushin da yake min, ina ta jin sautin muryarsa.

Bar bar gurin aikin ba sai da na rubuta takardar resigned ba tare da neman shawarar kowa ba, a lokacin da na aje takadar a office din oga Dahiru baya ciki hakan ya bani damar ficewa ba tare da shan kai ba. Na isa gida da kumburarrin idanuwa saboda kukan da na yi a office, duk wanda ya kalleni ya san bana cikin walwala da nishadi, daga Babana har Mama ba su farinciki da aje aikin da nai ba, ba su fada min ba amman na gani a fuskarsu da kuma yanayin maganarsu. Allah yasa hakan shi ya fi alheri shine abunda suka fada min, ni kuma na amsa da min kamin na taso na baro musu dakin na dawo dakin da nake kwana cikin damuwa.

Kwana biyu da faruwar hakan Abdulhamid ya turo magabatansa aka tsayar da magana, Baba be yi komai ba sai da amincewata kamar yadda shari'a ta shar'anta. An saka lokacin auren saba ga watan Rajab wato watan azumin tsofi. A daren ranar na kasa ganin walwala a fuskar Namra, tun kan nai maganar kanenna suka fara cewa kishi take ni kuwa na san ba kishi ba ne domin har yau Namra bata san cewa mahaifinta ya sake ni ba ita dai tana ta ga ya daina zuwa kuma ba mu koma gidansa ba, tun daga wacan lokacin da ta min maganarsa bata sake min ba, Namra ma ina ta san wani saki   balle ta kawo wani abu a ranta ko da yake yaran yanzu wayo ne da su ba kamar mu ba.

  Ina daki ina fidda musu kayan bachi ta shigo ta kwanta saman katifar tana ta kallona kamar wata bakuwarta, ni kai na sai da kallon nata ya saka na tsargu duk kuwa da kasancewar karamar yarinya ce.

STORY CONTINUES BELOW

“Namra minene?”


Na tambaya ina dan murmushi da ban san ma ta ina ya samu hanyar fito min ba.

“Momy aure za ki yi?”


Na gyada mata kai ina karfafa ma kaina guiwa.

“Daddy fa?”


Na dan yi jimm kamin na amsa mata.

“Namra mun rabu da Daddynki shiyasa na dawo nan gidan na zauna, shiyasa Daddynku ya zo ranar yana fada yana cewa sai an ba shi ku”


“Ba za ki sake komawa gidan ba?”


Na gyada mata kai.

“Shi ma ba zai zo nan ba?”


Nan ma na gyada mata kai, sai ta ɓata fuska kan ka ce kwabo hawaye sun fara mata zuba, janyota nai a jikina na rumgumeta ina rarrashinta.

“Namra ai ba daina ganin Daddy za ku yi ba, za ku ganshi lokaci zuwa lokaci, ni kuma kuna nan tare da ni babu wata damuwa”


Kuka tai sosai kamar wacce akai wa bushara da mutuwar ubanta ko tawa mutuwar har wani shidewa take numfashinta na yin sama, ni kaina ban san lokacin da na fara hawayen ba. Daga ni har ita muka kwana kamar marasa lafiya, na kasa farinciki da auren Abdulhamid da zan yi kuma na rasa na rasa dalilin hakan.

   Washe garin ranar Abdallah ya sallamo gidanmu, a yawance ya shigo falon ya gaisa da Mama ya shiga ya gaishe da Baba sannan ya shigo dakin da na ke ya tsaya a bakin kofa yana kallona fuskarsa ba yabo ba fallasa. Ni kuma na kasa kallon inda yake ma balle har na bude baki nai masa magana.

“Am... Yaran nan ya maganar karatunsu?”


Sai a lokacin na dago na kalleshi kwarjininsa ya cika idona sai dai hakan be saka ni dauke kai ko janye idanuwa daga nasa ba.

“Na je Gwarzo ba su karbe su ba, wai sai da ubansu”


“To miyasa ba ki fada min ba? Yanzu idan ban yi magana ba haka za ki zuba musu ido karatunsu ya lalace?”


Sai na ji wani iri kamar ba ni ba, magana yake da ni kamar wanda be taba furta kalma so a gareni ba.

“Kin amince a akai su?”


Na dan kawar da idona daga kallonsa ina girgiza kai alamar ban amince ba.

“Haba Halimatu idan ba ki amince ba ya za ki yi? Ko Aminu za ki maidawa su ki ce ya saka su? Ya kamata ace idan za ki yi abu kina tunani gaskiya, ko da yake har yanzu akwai kurciya a take tare ke yaran ma ai mabiyi da mabiyi ne ba wani dogon tazara”


Sai na ji kamar magana ya fada min a cikin magana, ban yi aune ba na ji yana wata maganar da dariya a sautin muryarsa.

“Idan baki amince ba zan kai karar ki gurin Baba na ce kin hana asaka yara a makaranta”1


“Abdallah zan saka su”


Na yi maganar a cikin muryar da ke karantar da mai saurarenta damuwata, sai yai min wani kallon tausayi yai min magana a hankali.

“Zan saka su Halimatu karki damu, karki min musu pls”


Ya roka kuma ya samu domin ban iya masa musun ba sai gyada masa kai da nai alamar na amince.

“Thank you”


Ya furta sannan ya fice daga dakin ni kuma na hade wani abu marar dadi da ban san ko minene ba na rumtse ido.

***     ***   ***


A satin suka fara zuwa makaranta, daga uniform har Littafai da school bus da ke zuwa daukarsu da komai Abdallah yai, aikina kawai wanke musu uniform shi ma ba kullum ba domi kanena ne suke wankewa su goge musu, bangaren abinci na samu sauki sosai domin a makarantar ake ba su na safe da kuma na karfe sha biyu daya da rabi kuma a kawo su gida. Tun daga lokacin ban sake saka Abdallah a ido ba da na kira wayarsa nai masa godiya ma kin dauka yai.

Wata rana muna cikin fira da Abdulhamid na ke masa zancen yarana akan tafiyar da zan yi na bar su a gidan.

STORY CONTINUES BELOW

“Amman za su rika zuwa suna ganina a gidanka”


Na fada ina karantar yanayinsa.

“Haka ne”


Ya fada yana hade yawu, ni kuma na ji wani iri, be karfafa min guiwa ba kuma ba ce zai hana su zuwa ba, a ranar har muka karkare ba mu tattauna wani abun arziki ba. Misalin goma na dare na shigo gida, dakinmu na wuce kai tsaye sai na samu dukansu sun kwanta a saman katifa sun yi bachi har Amal da bata bachi da wuri. Ido na kura musu ina ta kallonsu kamin na zauna na kai hannuna na safa su, ina ta jin su kamar wasu marayu zan auri wanda baya farinciki da zuwansu a gidansa ga mahaifinsu har yau be leko ko ya turo a duba lafiyarsu ba, gaba daya ma sai na ji kamar na fasa auren kuma babu dama. Shinfida nai musu na kwantar da su a inda nasaba kwantar da su Amal kuma na rumgumeta mu kai bachi rumgume da juna. Tun daga lokacin wata irin shakuwa da kauna ta kara shiga tsakanina da yayana ba ma kamar Amal da take karama, har ta kai ko laifinsu bana son a gani dana ji kukan daya daga cikinsu sai na ji babu dadi. Ban sanarda kowa zancen auren ba sai ana sauran sati biyu ciki kuwa har da aminiyata Hajara, a ranar da ta sallamo gidanmu ta nuna min bachin ranta sosai har take labarta min wai mijinta ya fara gina gida mai part biyu saboda ni da ita.

“Hajara ba ki da hankali”


“Babu wani rashin hankali Halimatu, abokiyar zama tana da dadi ko da dan yau da gobe, kuma ko Abban Afra be aure ki ba zai karo aure saboda akwai son karin auren a ransa, ba ki san kudirinmu ba, ba ki san iya abunda muka shirya akanki ba”


“Wai ba ki ma kishin mijinki?”


“Wallahi ban taba jin kishi akan ki auren mijina ba, na san waye mijina za sama miki rayuwa mai kyau irin wacce kika rasa a gidan Aminu, kuma zai rike yaran nan da muhimmanci ko ba komai ai hakan zai bawa Aminu haushi tunda abokinsa ne”


“Wallahi ni ba zan iya ba Hajara, taya zan yi kishi da yar'uwata?”


“Ba zaman kishi za mu yi ba, zaman yan'uwa za mu yi”


Duk yadda tai ta kokarin convince dina na yarda da ita sai na kasa, ni kallon marar tunani ma na koma yi mata, a ranar dai mun sha fira sai da yamma ta tafi. Washe gari sai ga kawata Sa'adatu na yi mamakin ganinta ba ni kadai ba har da kanwata Hafiza domin ni dai na san ban fada mata cewar zan yi aure ba, rabona da ita ma tun a lokacin da ta fada min cewar za tai tafiya tafiyar da Hafiza ke labarta min cewar da Aminu tai yi ta. A al'adar ko ma na kira shi da dabi'a bana iya cin fuskarka mutum a kusa da shi kamar yadda na ke saurin yarda da mutane, komai mutum yai min zan shanye na mai da komai ba komai ba. Haka muka zauna muka sha fira da ita daman a gidan babu wanda ya san akwai wata alaka tsakaninta da Aminu daga ni sai Hafiza, hakan yasa Inna da Mama suka sakar mata fuska kamar yadda suka basa tun ina budurwa.

Sosai ta nuna min rashin jindadin mutuwar aurena da Aminu da kuma tambayar wai da su Namra zanje gidan sabon mijin nawa ko a'a.

“Ya ce na je da su, ni kuma na ga kara dai na bar su a gida tun da sun fara sabawa da nan din”


“Eh kuma kin yi tunani, tun da na ji ance saurayi ne wanda za ki aura”


Na kalleta da mamaki.

“A ina kika ji?”


“Hmmm Halimatu kenan, ai abun duniya baya boyuwa ballantana ma kin san wannan babban sakamako ne Allah yai miki Allah yasa dai kyakkyawa ne kamar yadda kike kyakkyawa kin san ke fa matar manya ce”


Murmushi nai tare da canja mata fuska, hakan yasa ta hade duk wani zancen da ke kunce a bakinta tai min sallama ta wuce har da mikawa su Amal 2k ni dai ko rakiya ban mata ba.

Duk yadda kawaye da yan'uwa suke ba ni kayan gyara da tsima jiki kin sha nai sanin mijin da zan aura, dan haka ba zan sha abun da zai zo ya dame ni ba ko ya zame min matsala. Sai dai bana nunawa kowa sanin cewar babu wanda yasan da matsalar Abdulhamid sai ni. Daga ni har shi ba mu tsara yin wani event ba, dama ni ba budurwa ce shi ne dai ya kamata yai hakn kuma be yi ba, wata kila saboda shi ma din kansa ya san be cika cikakakken ango ba ko kuma dan baya da son hayaniya ne oho.

  Ranar da aka daura aurena da Abdulhamid sai na kasa farinciki kamar wacce akai ma auren dole, wata kila saboda na san irin mijin da na aura ko saboda zan tafi na bar yayana ko kuwa saboda dan'uwan Abdallah na aura wanda ya saka ce min komai akan hakan har yanzu. Duk wata murna ta iya fuska ce da hakora amman bata kai zuci ba, gaba daya ma neman son Abdulhamid nai da ke zuciyata na rasa, da na tuna cewar baya son yarana sai ji kamar bana bukatar zama shi, duk kuwa da kasancewar be fito kai tsaye ya fada min ba amman alamu ya nuna haka. A wunin ranar da akai wunin biki Amal na biye da ni duk inda zanje, ba Amal kadai ba har da Namra Aiman da Adnan ne kawai ke ta sha'aninsu su kan fito basu kula ba, Amal har wani sabon kuka ta tsira ba tare da am mata komai ba. Tun da magariba kanena Zayyanu ya karbe ta ya fita da ita da Namra saboda ya dauke musu hankali kar su ga tafiyata.

Inna da Mama sun min huduba kamar yadda su kai min a farkon daren da za a kai ni gidan Aminu, sai abun ya dawo min sabo ina ta hawaye kamar bakuwar aure. Baba ma ya min tasa bayan wacce yake ywan min tun daga lokacin da aka saka ranar auren. Ban san abunda ya hana jin bana son tarewa a ranar ba sai naji kamar ace sai nan da kwana biyu zan tare. Motoci da Abdulhamid ya turo na daukar amarya motoci ne amsu kyau da tsada, ba mota daya ko biyu aka kawo ba, motoci da yawa aka kawo na daukar amarya da kawayenta ni kaina abun har mamaki ya ba ni sai ka ce wata budurwa, ko da yake a gurinsa auren fari ne dole abokai da yan'uwa su yi masa kara.

“Hafiza ga yayanki dan Allah ki kula min da su, na san kowa yana kula da su yadda ya dace amman zan kara tunatar da ke ne saboda na san halin yara da cin rai, ta bangaren makarantar su a kula min da su dan Allah”


Haka na fadawa Hafiza kanwata wacce muka fi shakuwa, ina jin wani abu ba dadi kamar ina bar mata wasiya. Dafa ni tai tana karfafa min kuiwa.

“Karki damu Yaya Halimatu za'a kula da su In-Sha-Allah, Allah dai ya baku zama lafiya da hakuri, idan kika cire komai a ranki sai ki ga kin saba kamar can baya”


“Na gode Hafiza”


Misalin tara da yan mintuna aka kai ni gidan Abdulhamid da ke can bayan science, har muka isa kafata ta taka cikin katon gidan mai kyau ban daina jin kewar yayana a raina ba, ba ma kamar Amal sarkin takuwa yau ko a jikin wa zata kwana oho...


AMINU POV.........✍️


___________________________


To fa Halimatu za a fara sabuwar rayuwa, Allah bada zaman lafiya.

Anya dai ta kyautawa Abdallah kuwa? 🙄😏2

Post a Comment for "GOBE NA CHAPTER 2 BY KHADIJACANDY"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...