GOBE NA CHAPTER 1 BY KHADIJACANDY - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GOBE NA CHAPTER 1 BY KHADIJACANDY

GOBE NA CHAPTER 1 BY KHADIJACANDY

- - Post a Comment

 GOBE NA CHAPTER 1 BY KHADIJACANDY


                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

⚠️ Ban yarda a canja min ko da harafi daya na littafin nan ba, balle kuma har a saffara shi a dora a Youtube ba tare da izinina ba, yin haka kan iya janyo wa mamallakin Channel din babbar matsala dan haka a kiyaye!*


_Hasbunallahu Wa Nimal Wakeel_


                     ***       ***     ***


FREE PAGE


*GUSAU ZAMFARA STATE NIGERIA.*

*Gusau Rd/Sokoto Rd*


Jifatu Shopping Mall

 


3:16pm


Madara ta fi komai yawa a cikin abubuwan da na siya, ba dan komai ba sai dan sanin cewa mahaifina ya fi bukatar tea fiye da komai a yanzu. Gwando daya na cika da siyayyar kayan ciye-ciye da tande tande sannan na dauki wani kwando na cika shi da da wasu abubuwa na bukatun yau da kullum kamar sabulun wanka da wanki da turare sai kuma omo.

Bakar abaya ce a jikina sai dan karamin mayafinta wanda hakan ya bani damar rika duka kwandunan na nufi gurin biya Amal na bayana rike da biscuit dinta. A saman dan teburin da suka tana dan lissafa kaya na dora kwandunan sannan na saka hannuna a jaka na ciro atm dina na rike a hannu ina jiran ya gama da wadanda suka gabana ya fara da ni sai na biya da pos din da yake gurin, domin na saba indai ban ciro albashi gaba daya idan na siye abu ina biya ne da atm.

Sai da ya gama da mutum biyu sannan ya fara da nawa, sai da ya gama lissafa komai kamin na mika masa kudin ya fara dauko leda yana sakawa, ni kuma a iya sanina idan kai siyayya a jifatu sai ka biya suke saka maka a leda su sallameka.+

“Nawa ne?”


“Hajiya an biya”


Ya fada min yana ga aikin harhada min kayan a leda. A take gabana ya yanke ya fadi har sai da na dauki yan awanin sannan na sake tambayarsa.3

“Waya biya?”


“Gashi can a waje”


Juyawa nai na kallin wajen sai n hango Abdallah tsaye jikin motarsa idonsa akan wayar da yake dannawa. Dauke kai nai na cigaba da kallonsa har ya gama saka kayan a leda sannan na mika hannu na karba.

“Thank you”


“No mune da godiya Hajiya”


Da duka hannayena na riko ledodin na nufo kofar fita Amal na rike da gefen rigata muka fito, ko da wasa ban kalli inda Abdallah yake tsaye ba balle har ya ga fuskata duk kuwa da na san hakan ba zai hana shi yi min magana ba idanya tashi.

Bakin titin na nufo ina ta tafiya ina sai jin maganarsa nai bayana.

“Ban biya kudin dan ki min godiya ba, kuma na san ba zaki min godiyar ba, amman ai ko kallona kya yi na dan ji sanyi ko?”


Tsayawa nai cak na juyo na watsa masa wata banzar harara fuskata a hade kamar bakin hadari. Sai dai da alama harar tawa dadi take masa domin murmushi ne ya cika masa fuska har ya cire farin gilashin idonsa yana kallona. Dauke kai nai na cigaba da tafiya sai jin nai ya riko hannun Amal wanda hakan yasa na juyo da sauri sai ganinsa nai yana danka mata kudi a hannu.

“Ku hau napep da wannan kin ji Amal nasan ko na ce na kai stubborn mother dinki a mota ba zata je ba”


Amal bata ce masa komai ba ta karbi kudin daman haka take indai kudi ne da biscuit bata kin karba ko a hannun waye, jan hannunta nai muka cigaba da tafiya.

“Yanzu na baro mijinki a can gurin damba area tare da abokansa da wasu mata”


Sake juyowa nai karo na biyu na dubeshi da duba na bakincikin jin kalaminsa da kuma na tsanar ganin fuskarsa.

STORY CONTINUES BELOW

“Miye ribar da zaka samu idan ka labarta min wannan? Kana tunanin zan yarda da kai? Mi zai saka mijina neman wasu matan banza a waje?”


“To ni ma dai shi na gani, namijin da zai aje mace kamarki mi zai saka ya nemi wasu a waje?”


“Baka tsoron Allah Abdallah saboda baka gudun taka dokarsa, kana isgili da ganganci ga dokokin aure da kumana Allah, shin zaka jidadi idan wani namijin ya kula matarka? Wani namijin ya iya furta wata mummunar kalma akanka gurin matarka? Kai baka kishin kanka? Daga yau karka sake yi min wata magana da ta shafi mijina ni mijina ba mazinaci ba ne, na lura kai baka san darajar aure ba kuma baka san kimar kanka ba balle har ka iya tsare mutuncin iyalanka”


“Na san darajar Aure Halimatu, na san martabar aure, kuma ina mutunta aure da duk wani mai aure, kawai dai ina son ki ne, ina son ki san kamanni da hallita suna canjawa amman zuciya bata taba canjawa, alakar da ke tsakanina da ke ba zata taba yankewa ba, ko bayan so ai ni dan'uwanki ne ko?”


“Ajinabi ba, kuma ina fatar ka san da hakan”


Ya gyada min kai yana murmushi. Ni kuma na juya na cigaba da tafiyata.


“Da ni nake da mace kamar ke ba zan bari ko tawaye na ya kalleta ba, balle kuma har wani namijin ya tsaya magana da ita, zan yi duk abunda zan yi na kare mutuncinta da martabarta”


Ban sake kulashi ba balle har na tsaya sake ce masa wani abun, na yi sa'a ina kaiwa titin na samu napep a take na daga mata hannu ta tsaya na shiga.

“Yan mangurora zaka kai ni”


“Dari biyu”


“Zan dai baka dari da hansi”


“To muje”


Sai da na fara saka ledodin hannuna na shigar da yana ta hudu wato Amal sannan shiga na zauna.


“Momy ga kudin”


Amal ta fada tana miko min kudin da Abdallah ya bata, karba nai na saka a jakata ina hade yawu, kamar hadin baki ina saka kudin karamar wayata tai ringing sai na fiddo hannuna tare da wayar ganin number surukata yasa ni saurin dauka.

“Assalamu Alaikum Hajiya”


“Na'am Halimatu kina lafiya?”


“Lafiya kalau Hajiya ya jikin?”


“Al-hamdulillah, na ce kin fadawa Aminu maganar kudin nan kuwa?”


“Eh Hajiya na fada masa”


“Idan ma baki fada masa ba ya kamata dai ki fada masa, har yanzu na ji shiru be ce komai ba ban sani ba ko baki fada masa ba, idan ma baki fada masa ba ya kamata dai ki fada masa yanzu, kuma izuwa yanzu ya kamata ace kina fahimtar cewar uwar miji ma kamar uwa ce, duk abunda ya shafe ni ya kamata ace kina daukarsa da muhimmanci”


“Wallahi na fada masa Hajiya, amman zan sake masa magana”


Bata ko bari mun yi sallama ba ta katse wayar, hakan kuma alamune da ke nuna cewar yau a fusace ta kirani. Haka na ke da yan'uwansa idan suna bukatar abu sai dai su kira su ce nai masa magana bayan ni kuma ba magana ta hake ji ba, mahaifiyarsa ma ta fi kusa da shi amman ita ma kanta sai dai tace na fada masa tana bukatar abu kaza da kaza, saboda gani suke komai na kame na mallake shi sai abunda na ce yake yi. Ko da yake shi ya nuna musu hakan domin a duk lokacin da suka bukaci abu ko da naira biyar ne sai yace balle nai magana da Halima, ganin hakan yasa suka dauki ido da baki suka dora min wai na mallake shi, ni kuwa nasan da zan samu mallakar kamar yadda suke zato da ba haka ba.

  Har kofar gida mai napep din ya kai mu na fita na ciro kudinsa na mika masa sannan Amal ta fito tana bata fuska wai rana sai kace a kafa muka zo. Ganin motar Abdulhamit wato tawayen Abdallah fake gefen icen da ke kofar gidanmu ya tabbatar min da zuwansa, daman can ya kan zo jifa jifa ya gaishe da su Mama.

Ina gaba Amal na bayana tana kukan rana, gidanmu gidane mai yan mata da samari ina shiga yan matan gidanmu wato kanne waenda muke uwa daya uba daya da kuma waenda muke uba daya suka hau ihu da murna ganina.

STORY CONTINUES BELOW

“Oyoyo Anty Halima”


Da sauri kananna suka zo suka rika ledar hannuna, dayar kuma ta dauke Amal tai sama da ita tana dariya, daman haka gidan mu yake yana da wahala ka iya banbance yan dakin mu da waenda muke uba daya domin mu ba musan wani abu wai ubanci ba ko kuma yayan kishiya. Sai da na fara shiga dakin Inna na gaisheta sannan na nufi dakin mahaifiyata


“Maraba da Sadiya”


Cewar Mama da murmushi a fuskarta, ni kuma na zauna saman kujera ina mika mata gaisuwa tare da gaisawa da Abdulhamid.

“Yau kuma nan aka zo?”


“Eh Wallahi ya gida ya yaran?”


“Lafiya kalau”


“Yanzu ko na ke tambayarki aka ce kin kwana biyu ba ki zo ba”


“Wallahi yanzu na rage fitar nan sosai saboda abubuwan sun yi yawa ga hidimar yara ga zuwa gurin aiki idan na dawo kuma nai aikin gida, ba ni da hutu ne Wallahi”


“To Allah ya taimaka ni zan wuce”


“Tun yanzu”


“Tun dazu na zo fa, nan na ci abincin rana ma”


“To a gaishe da su Hajiya”


“Za su ji”


Ya mike tsaye yana ciro makullinsa a aljihu, banbancinsa da Abdallah kadan ne ta wajen hakoransa na gaba dayan ya dan kare kadan sai kuma yanayinsa da ba na Abdallah ba, amman kama iri daya ni kaina ba dan banbanci tufafi ba da motar da na gani a waje idan har na shigo be bude baki ya min magana ba zan iya cewa Abdallah ne.

Sai da Mama ta raka shi har gurin motarsa ta dawo, sannan take labarta min shinkafa ce ya kawo musu yar gobnati, daman haka familyn Baba suke suna da son zumuncin da son yi ma wanda ba shi da karfi a cikinsu, musamman ma Baba da suke ganin baya aikin komai kuma ga ciwon kafar da yake fama da shi, ga kuma iyali rututu mashallah, domin yan matan dakinmu kadai su hudu ne, idan aka cire ni da nake ta biyu da kuma yayana Maimunatu wace ke aure Kano da yaranta, ga kuma yayan Inna su ma su bakwai duka mata sa dai ita ta aurarda matanta hudu saura uku.

“Kai shinkafar nan mai tsada, Allah ya saka musu da alheri”


“Amin”


Ta amsa tana tambayar ina na baro su Namra da Salim.


“Suna gidan kanen babansu kin san yau weekend ne wai yace zai kaisu yawo tare da yaransa shine suka tafi Amal ce kawai ta ki zuwa”


“Ita sarkin lakuwa daman kullum tana nan manne da ke, idan kika haifo wani sai na ga yadda za tai”


Cewar kanwata Amina, ni kuma nai dariya na ce.

“Aa yar auta ce ai”


Kausar ta ce

“Ba wani auta wata zaki haihu mu ga karshen lakuwa”


Ban bi ta kansu ba na kalli Mama ina dariya na ce


“Ga sabulu nan na kawo muku, sauran siyayyar ssai wani watan”


“Babu komai Allah ya miki albarka”


Daman haka nake wata siyayar da ban yi ba a wani watan na ke musu ita saboda ni ma kaina ina yi ma kaina wata lalurar domin ba komai namiji yake dauke ma ba, balle miji irin nawa, daman kuma can maza ba sa son ba ni ba ni wannan yasa na tsaya kai da fata akan aikina, a duk lokacin da an karbi albashina sai nai ma kaina da iyayena lalurar da bata gagareni ba.

Bayan sallah la'asar na shiga dakin Baba na gaishe shi na bashi dubu biyar a cikin albashina kamar yadda na saba masa ko wane wata bayan siyayyar da na ke, yayi murna kuma ya min addu'a sannan na taso na fito harabar gidan inda kanenna suke zaune na zauna muna ta fira, a gurin Maryam na ga wani slim tea da kawarta ke saidawa na siye daya, ba dan ina da tabbacin yana yi ba sai dan neman rabuwa da kibar da na ke ko dan na huta da ci mun fuska da Abbah Adnan ke yi.

“Wai Anty Halima kin gama karanta Littafin Zaki kuwa?”


Jawahir ta tambaye ni. Ni ko na tabe baki ina murmushi.


“Hmmm na karanta gaskiya ba laifi littafin yayi dadi, wannan iya gata da soyayya da Aliyu ke nuna ma Ataa”


“Wallahi nima soyayyarsu ta tafi da ni, idan nai aure haka zan yi da mijina”


Ta karasa tana rage murna dan kar Inna ko Mama su jiyota. Sai muka kwashe da dariya.


“Ai auren yanzu ba wani soyayya a ciki Jawahir sai dai kawai hakuri da neman aljanna, amman duk wata soyayya ta littafi karki saka ran samunta a gaske, ban ce ba a samu ba ana samu amman kadan ba da yawa ba”


Na fada ina tuna irin tsarin rayuwar da na shirya ma kaina da mijin da na aura kamin aure, sai dai ina yin aure sai na tarar da ba haka ba daga lokacin da na fara haihuwa kuma sai na ga canji a gurin mijina, har ta kai yanzu bana burge shi saboda na yi kiba na yi fadi litattana ta canja daga budurwa zuwa mai aure da yara hudu.

Haka dai muka cigaba da firarmu gurin dariya mu yi har akai magariba, bayan na yi sallah na shiga dakin Mama na bata dubu biyar na bawa Inna budu biyu sannan na dauko Amal muka fito kannena biyu suka rakoni. Na samu napep nai min jinga daga unguwar zuwa igala quarters zai kawo ni dari biyu, a take na shiga su kuma suka kama hanya.


Ko da muka isa na tarar Abban Adnan ya dawo domin na ga motarsa a harabar gidan tun kamin na shiga, da sallama na tura kofar falon na shiga, sai dai be amsa min ba kuma be dago ya kalli inda na ke ba, yana zaune saman cushion idonsa akan tv yana kallon hausa bakwai suna haska wani hausa film da ban tantance shi ba, jin muryar yara a upstairs ya tabbatar min da sun dawo kenan suna dakinsu domin shi kadai ne a falon.

“Sannu da zuwa yanzu ka dawo?”


Be amsa ni ba sai wani cin magani da yai ya kalleni.

“Karki sake tura min yara gurin yawo, kin tura su kuma kema kin fita yawon ki”


“Ba yawo naje ba gida naje kuma na fada maka kamin na tafi”


“Na dai fada miki, bana son yarana suna zuwa gidan kowa, kuma na fada miki ki aje aikin nan bana so saboda aure na auro ki ba dan ki rika fita zuwa aiki ba”


Bance masa uffan ba, idan sabo na saba da jin maganarsa ta na aje aiki, ni kuma na gagara ajewar kamar yadda yake bukata saboda be dauke min duka lalurorina ba, kuma ga iyayena suna da bukatar taimakona a yanzu, aikin ma da be fi shekara uku da farawa ba. Amal ta tafi kusa da shi ta zauna shi ko hankalinsa na kan tv sai yabon kyau Fati washe yake, na san yana yin hakan ne saboda na ji haushi kuma na ji, domin har yanzu na kasa sabawa da halinsa na yabon kyawun wasu matan a gabana. Ina jin ba dadi idan ya yabi wace bata da jiki ko ya nuna yana son mace marar jiki saboda na san ni din ba siririya ce ba, duk kuwa da kasancewar ba wata shahararriyar kiba ce da ni ta kaico ba, kuma na san matukar mutun be ce min kyakkyawa ba to ko ba zai kira ni da mummuna ba, domin ni ma ina da kyau na iya yadda Allah ya ga zai dace da ni, ina da haske sai dai ba can sosai ba.

Upstairs na nufa dakin yarana na fara shiga na sai na samu Adnan da Aiman suna buga game a system dina, Namra kuma tana kwance saman gado ta rufe ido sai juyi take, cike da damuwa na zauna kusa da ita na kai hannu ina shafa bayanta.


“Namra lafiya?”


“Momy cikina ke ciwo sosai”


“Me kika ci?”


“Banci komai ba”


Ta fada cikin kuka ba tare da ta bude idon ba.

“Adnan me Namra ta ci? Ta ci yaji ko?”


Sai a lokacin ya dago har ya lura da ba dawo, ya zo inda nake da murnarsa shi da Aiman suka dafa ni.

“Momy kin dawo?”


“Eh me Namra ta ci?”


Adnan ya ce


“Wallahi ban sani ba, Baba Sadi ya kai mu gurin wasa yara ita kuma ya fita da ita yace zata raka shi wani guri kila can ta taci wani abun, domin da suka dawo ta rika cewa cikina na ciwo”


“Namra kin ci wani abu a can?”


“Ya siya min nama na ci kuma da yaji a ciki amman kadan ne yajin na ci saboda kin ce na daina cin yaji”


“To yajin ne ya saki ciwon ciki, bari na jika miki kanwa”


Ya fada ina mikewa tsaye na nufi kofar fita, Aiman ta biyo ni a bayana yana fadin shi ma zai sha, daman haka yake duk abunda ya ga yar'uwarsa Namra ta sha shi ma sai ya sha komai dacin abun saboda tsabar rigima.

Sai da na jika mata kanwar ta sha na shiga dakina nai sallah isha'i, ina sallamewa nai saurin mikewa tsaye na nufi inda wayata take tana ringing na duba na yi zaton ko Abban Namra ne da farko sai dai ganin bakuwar number yasa ni aje wayar har sai na koma saman carpet har sai da na gama tasbihina nai addu'a ma mijina nai ma kaina da iyayena sannan na nemawa yara na shiriya. Daga bisani na mike tsaye na nufi inda wayar take aje na dauka na sake kiran layin da aka kirani da shi.+
“Assalamu Alaikum”

Ni na fara mika sallamar kamin wanda na kiran ya fara min sallamar.
“Wa'alaikissalam Halimatu”

“Na'am Ranka ya dade”

Na gane cewar ogana ne na gurin aiki wato oga Dahiru.
“Ki yi kokarin hada document dinka kamin gobe ina da bukatarsu”

“To ranka ya dade”

“Kuma ki yi saving din wannan number ita ma number ta ce”

“To ranka ya dade”

Daga haka ya kashe wayar be sake ce min komai ba, ni ma kuma ban ce ba, daman kuma me zan ce masa, bayan kiran da yake min ma yana damuna balle kuma har nai wata magana da shi, zauna nai bakin gadon ina ta mamakin dalilin kiran da oga Dahiru yake yawan min a duk lokacin da yake bukatar wani abun, shin yana manta cewar ni ma ina da aure da iyali kamar shi, ban san miyasa yake son kira akan abunda be kai ya kawo ba, ba kira kadai ba har wasu abubuwna da yake min bana jindadinsu, domin duk abunda na ke ina kokarin kare mutuncin aure da kuma na yayana da mijina.
“Momy ni dai gobe idan mun dawo daga scul gidan zan dawo ba zan je gidan Baba Sadi ba”

Namra ce ta shigo tana wannan maganar tana wani bata fuska kamar zata fashe da kuka.
“Saboda me?”

“Bana son zawa can Momy dan Allah”

“Ki yi hakuri Mamana, idan kun dawo nan gidan ba wani abun za ku yi ba, kuma kin ga ba girki balle ku ci, amman can Momy Hassana tana girkawa, za ku samu ku ci”

“Momy to ki daina zuwa aikin nan pls ko kuma mu rika zama a gida a haka muna jiranki ki dawo”

“Mamana akwai abunda ake miki a gidan ne da baki so?”

Ta girgiza kai alamar aa sannan ta kwantar da kanta jikina.

“Cikin ya daina ciwo?”

“Eh amman yana min kadan-kadan ba sosai ba”

“Zai daina In-Sha-Allah, na zubo miki abinci za ki ci?”

“Za mu ci tare Momy zan wanke hannuna ba zan saka miki datti ba”

Murmushi nai mata sannan na mike tsaye na fito daga dakin na sauko downstairs. Ban samun Abban Namra a falon ba, daman kuma ban saka rai ba domin ba kasafai yake dawowa da wuri ba, idan kuma har ya dawo to sai idan wani abun zai yi ko zai dauka amman dai ba haka nan kawai zai dawo gida da wuri ba ko kuma ya wuni ba. Tuwon da na girka dazun kamin na fita na zubo miyar kuka sannan na fito bakin kofar kitchen rike da abincin ina kiran Adnan domin bana son sai na zauna ya zo yace min zai ci abincin.

“Adnan Aiman za ku ci abinci yanzu?”

Babu wanda ya amsa ni a cikinsu balle kuma har su sauko kasan da sunan cin abincin, sai Amal da ban kora ba.
“Ommy Ommy zan ci abinci”

“To zo ki ci yar autana”

Na fada ina karasa fitowa falon sannan na zauna kasan carpet din na zaunar da ita saman kafafuwana na soma bata.
STORY CONTINUES BELOW
“Namra zo ga abincin”

Da sauri ta sauko ta shiga kitchen ta wanke hannunta sannan ta saka min a plate, loma uku zuwa hudu kawai tai ta cire hannunta wai ta koshi.

“Cikin ne har yanzu Namra?”

“Eh ciwo yake min”

Ya fada tana yamutsa fuska sannan ta kwanta a gurin ba tare da ta wanke hannunta ba, ni kuma ban matsa ba ganin gata jindadi har sai da na gama sannan na dauke plate din na kai kitchen na wanke hannuna da na Amal a can sannan na dawo na dauki Namra na shigar da ita dakinsu na cire mata tufafin jikinta na nai mata wankan dare kamar yadda na saba musu na saka mata kayan bachi sannan na kwantar da ita, Adnan nan kam sai da nai kamar ina yi sannan ya bar gabar system din ya tafi yai wanka nai ma Aiman suka kwanta, ni kuma na dauke system dina na fito na baro musu dakin.
Dakina na dawo na kwanta gefen gadon Amal ta haye min kafafuwa tana kokarin fara kukanta na banza. Wayata na dauka na kunna data dama bana samun hawa online sai da dare idan yara sun yi bachi kuma na gama komai, grps din muna na Nothen Women's Advice na fara budewa na duba chat din sannan na shiga na Salma pre-order na duba abubuwan da ta turo cikin har da injimin wanki wanda na fi kowa bukatarsa a cikin gidan nan saboda wanki da nake na yaran nan gashi kwana biyu sun lalata.  Ban bar online din ba sai kusan sha daya da rabi na dare, sannan na tashi Amal wacce a lokacin ta dade da fara bachi a take ta saka min kuka daman ta saba ko ba ai mata komai ba tana kuka balle kuma an yi da dalili. A haka nai mata wanka na saka mata tufafin bachinta na goyata saboda na samu ta daina min kukan.
Dakin yaran na koma na ciro musu dayan set din uniform dinsu na dora musu a inda na saba aje musu sannan fito na shiga kitchen din n dauko abincin Abbah Namra na kai masa dakinsa duk kuwa da na san ba lallai ne ya ci ba domin ba ko da yaushe yake cin abinci a gida ba. A falo na fito da laptop dina na duba document din da oga Dahiru yace na shigo da su na fida su dabam a cikin wata folder sannan na rufe laptop din na koma dakin yara na kwantar da Amal. Na shiga nawa dakin nai wanka na saka kayan bachi na dawo dakin Abbah su na kwanta a take bachi yai gaba da ni abun ka da wanda ya gaji. Can cikin bachin nawa ina jin lokacin da Abbansu ya shigo duk yadda na so na dago nai masa sannu da dawowa sai na kasa saboda bachin da ya ci idona.
Washe gari tun da asuba na tashi, sallah ce farkon abunda na fara yi sannan gabatar da addu'o'ina suma ba duka ba daman idan ba weekend ba bana samun tsayawa nai yi su gaba daya, ina saukowa kasa na shiga kitchen na shiga shirya musu abincin makaranta da kuma na karyawarmu, bayan na firaye dan na fasa kwai sannan na shiga dora ruwan zafin, Amal ce farkon tashi daman haka take tafi kowa rigima ko a dare idan ta motsa bata ji ba, indai yan rigimar suna nan sai ta saka kuka ta dawo dakinmu ta kwana.
“Ommy Ommy”

Ta fada tana murja ido cikin kuka.
“Minene Amal?”

“Bachi”

“Je ki dauko zane”

Sai kawai ta fashe da kuka, haka yasa dole na cire dankwalina na goyata da shi na cigaba da aikina. Ban tashi su Adnan ba sai da na tabbatar na shirya musu komai na makaranta sannan na tashe su nai musu wanka suka sauko kasa na hada musu tea kawai suka sha suka hau sama suka shirya cikin uniform dinsu kasancewar yau monday. Ni kuma na shiga cikin dakina na dauko kudin napep na saka hijab dina na fito na saka yarana a gaba muka fito har Amal muka nufi titi ina kokarin taron napep sai ga makocinmu kuma mijin kawata Hajara ya faka gefenmu tare da yaransa a cikin motar ya sauke gilashin motar yana miko min gaisuwa, sai da muka gaisa sannan ya ce da su Adnan su shigo motarsa suka shiga da saurin ganin yaransa daman can makarantarsu daya kuma yana yawan wucewa da su idan zai kai nasa yaran, wani lokacin ma har gida yake aikowa yace su fito zai kaisu makaranta. Sai da suka shiga motarsa sannan na juyo na dawo ni da Amal ina yanje da hannunta muka shigo cikin gida. Tea ta na dazun da bata karasa shanyewa ba na mika mata sannan na nufi dakin Abbansu, tufafin daya cire na jiya na fara dauka dan hade su da waendan kayan daudan nashi, al'adata ce duba aljihun rigarsa da wando kamin na saka su a kayan dauda saboda cire masa duk wani abu nasa da yake cikin aljihu. Rigar na fara dubawa sannan na saka hannuna a aljihun wandonsa, sai na ji abu kamar kwalin wani abu ina cirowa na ga kwalin kwandon sai dai ba cikakke ba da alama an yi amfani da shi. Ni a
Kadai na san abunda na ji a wannan lokacin a take jikina na dauki rawa kamar dai yadda zuciyata ma take ta bugawa da karfi idanuwa na cika da hawaye. Juyawa nai ina rike da kwandon din a hannuna na kalli Abbah Namra da yake kwance saman gado yana ta sharar bachinsa hankalinsa kwance ni kuma nawa hankalin a tashe da kwandon a hannu. Dayan hannuna na saka na share hawayena da suka zubo na dauke kayan na fita da su, sai dai har nai aikin da nake na shirya Amal nai wanka nai shirin aikina hawayen ba su daina min zuba ba, ni kuma ban fasa sharewa da hannuna ba. Kamar yadda na saba yau ma na hada masa komai nasa na karyawa na shigar masa da shi dakinsa na kai masa, sai dai ban same shi a kwance ba sai na samu ya shiga bandaki da alama yana wanke baki ne, a can na baro Amal na fito na sauko kasa na nufi dinning na hadawa kaina tea amman sai na kasa sha saboda bacin rai da ke cikin raina, i decided na aje tea din na dawo saman cushion na zauna na dafe kaina. Wannan karon ba hawaye na ke ba wani abun ya ke jin ya tsaya min a zuciya marar misaltuwa daker na ke iya hadeye yawu da numfashi. Na kai minti talatin a haka sannan na tashi na koma dakina na dauko kwalin condom din na nufi dakinsa, kamin na kai hannu na tura kofar dakin na jiyo sautin dariyarsa hakan ya tabbatar min ko dai yana magana da Amal da take dakin ko kuma waya yake, ban yake dayan biyu ba na ji yana fadin.
“Na samu hutu satin nan ina kike son muje?”

Hakan yasa ni dauke hannuna daga jikin kofar daman can rikawa kawai nai ban tura ba.
“Kaduna? To yayi ba matsala zan shirya mana komai, amman kamin na turo account dinki zan saka miki wani abu sai ki yi siyayyar da kanki kin san ni ba zan iya zuwa siyayya yanzu ba, kuma kin san idan ina fita da ke yau da gobe za a iya fara cewa wani abu”

Kadan kadan yake maganar amman hakan be hana ni ji ba, domin mutun ne mai daga murya idan yana magana da wani ko da kuwa kadan-kadan yake yi. Ji nai kamar ba zan iya sauraren firarsu suka ba hakan yasa na murda kofar dakin na shiga ina kokarin maida hawayen da suka cika min ido.
“Oh Okay Faruk sai na shigo”

Shine abunda ya fada sannan yai hanzarin kashe wayar, ya gyara zamansa yana kokarin fara cin abinci, ko da wasa ban bar wata alama da zata nuna cewar na fahimci da mace yake waya ba, duk kuwa da kasancewar bana iya sauya yanayi na rashin jindadi da walwala dake tare da ni a yanzu. Zaunawa nai gabansa.

“Ina kwana”

Na fada ba tare da na kalleshi ba. Shi ma bana tsammani ya kalleni kamin ya amsa min sai Amal kawai yake wasa da ita yana bata abincin shi ma yana ci.
“Jiya Hajiya ta sake min maganar kudin ac”

“Ai sai ki ce mata kin fada min magana, ni Wallahi na manta amman yau zanje na fada kudin In-Sha-Allah”

“To Allah ya bada iko”

Be amsa min da amin ba sai ya dago ya kalleni.
“Ya akai kin san bana son ana tsare ni idan ina cin abinci akwai wani abun ne?”

Har zan mishi maganar condom din sai kuma na hade yawu na gabatar masa da abunda na san ba lallai ne yai min ba.
“Jiya ne naga wani injimin wanki da ake order daga waje shine na ce ko zaka saka min wani sai na hada da abunda yake hannuna sai na siya na huta da kai wanki”

“Ba ni da kudi yanzu, ina albashinki? Ko aikin kawai kike ba a biyanki?”

“Ana biyana mana kai ma ai ka sani domin da su na ke rage wasu abubuwan nawa”

“To ki siya da shi ni ba ni da kudi yanzu, da kin ga mutun ya zauna kin fara masa maganar kudi kenan shiyasa ko zama gidan nan bana son yi kuma baki da lokacin magana sai lokacin da nake cin abinci”

“Irin wannan lokacin kawai nake samun damar magana da kai Abban Namra, baka dawowa da rana sai idan wani abun zaka yi da dare kuma sai 12 ko 1 kake dawowa”

“To ni dai ba ni da kudi yanzu”

Ya fada yana wani kara hade fuska. Sai na aje masa condom din da ke hannuna murya a sanyaye na ce.
“Ga wannan na gani a cikin kayan da ka cire jiya”

“Oh jiya Bala ya bani ajiyarshi na manta na bashi abarsa”

Ya fada kai tsaye kamar gaske ba tare da ya kalleni ba. Idanuwana cike da kwalla na ce

“Ko dai na wanene Allah ya sani kuma yana jiran kowa a madakata”

Ina fadar hakan na mike tsaye sai dai kamin na kai tsayen ya rigani yana daka min tsawa.
“To me kike nufi? Zagin kike ko kuma Allah ya isa za ki min? Wai mi yake damunki ne Halima? Daman munanan mata kun fi komai bakin hali ku ba kyau ba sai sakawa mutum damuwa da bakin zargin tsiya”

“Ba ni n hallici kaina ba Abban Namra, kuma saboda bana da siffar da kake so a jikin mace ba shi yake nufi ka bi wasu matan ba, kai kanka kasan ba haka ka aureni ba, auren shekara goma sha biyu bana kwana biyu ba ne, dole wani abu a jikina ya canja, na haihu har hudu dole jikina ya bude, ka dinga jin tsoron Allah Abban Namra....”

Kamar jira yake na kare a take ya wanka min wani mahaukacin mare mai zafi kamar garwasun wuta, kamin nai ihu Amal ta fara fashewa da kuka ta rike masa kafa damn ta saba masa haka ida da su Namra da Adnan idan yana dukana, ni kuma ban tsaya komai ba ya juya da sauri na fice daga dakin ina kuka.
“Dacan bana tsoron Allah aka ce miki? Wawuya kawai”

Shine kadai abunda na ke iya jiyo yana fada bayan na baro dakin, da gudu na dawo dakina na zauna kasa na fashe da wani irin kuka mai ban tausayi da taba zuciya.

Kuka nai mai isata sannan na tashi na shiga bandakin na wanke fuskarta na fito na nufi gaban madubin na dan shafa mai kadan da hoda sai dai hakan be boye kumburin da fuskata da kuma idanuwana sukai ba.

  Hijab din da yai yanayi da farar atamfar da nake saye na dauka na saka sannan na dauki wayata na saka a jakata na dauki laptop din na saka takalmi na fito daga dakina. Yau ban tsaya bin ta kan Amal ba balle har na kaita da kaina gidan kanensa daman wani lokacin shi yake kaita idan na fita na barta a gunsa wani lokacin kuma ni nake kai ta sai dai idan ni na kaita ta fi min kuka saboda takuwa irin nata. Na saba daman a duk lokacin da zanje aiki sai dai naje a napep ba dai ya kai ni ba, kusan tun da na fara aiki sau biyu ya taba rage min hanya ya kai ni da motarsa, babu kuma yadda ban yi ba da shi akan ya siya min mota amman ya ki ba dan bashi da hali ba, sai dan ya fi son nai ta wahalar zuwa aiki a napep ga kuma kai yara scul da nake duka a napep, ya bar ni da dawainiya kala kala kamin a dan bashi da halin dauka ba sai dan keta irin na shi.

  Har na shiga napep ban daina tunanin wayar da naji yanayi da wata ba, ciki har da zancen kudin da zai bata bayan ni na roki alfarmar ya cika min na samu na siye injimin wanki yace min ba shi da su, ga kuma zancen hutun daya samu har yana fadin wane gari take son suje, ada can kam na kasa yarda cewar Aminu yana neman matan banza duk kuwa da kasancewar ina ganin chat dinsa da wasu matan wani lokaci ko kuma na ji yana fira da su, sai dai a nawa tunanin irin chatting din nan ne na budurwa da saurayi da maza suke yi, wanda ba zaka iya raba maza da shi ba, sai dai ganin condom a aljihun wandonsa ya tabbatar min da abunda Abdallah yake yawan fada min, sukar auren da yake min na uban diyata yau na tabbatar da shi, no matter what Aminu zai fada min ba zan taba yarda ba, taya abokinsa zai bashi ajiyar condom miyasa shi ba zai aje da kansa ba sai ya bashi ajiya? Ban san lokacin da kuka ya kubuce min ba, ashe tun da na soma tunanin nake hawaye ban sani ba.+

“Hajiya Lafiya dai?”


“Lafiya kalau dan Allah juya da ni inda ka dauko ni”


Na fada ina jan majinar hancina,tare da saka hannuna na share hawayena. Kamar yadda na umarce shi haka ya juya ya koma, sai dai ban bari ya karasa ba na tsayar da shi na sauka na bashi kudin shi, daman ba gidan zan koma ba, gidan su kawata Hajara zan je na saba zuwa can a duk lokacin da abun duniya ya taru yai min yawa ita kanta da zarra ta ganni ta san akwai wata matsalar. Sallamar da nai cikin muryar kuka ce ta karantar da ita ina cikin wani hali.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”


Shi ta furta amaimakon ta amsa min sallamar, ta aje Affan da ke hannunta saman kujera ta taso ta nufo inda nake ta dafa ni ganin kamar ba zan iya karasowa saboda kukan da ya koma min sabo.

“Halimatu”


“Na'am”


Na amsa daker, sannan na zauna a kujerar da ke kusa da ni ita ta zauna kusa da ni tana ta kallon kukan da nake cikin damuwa, har sai da nai wanda zan iya sannan na labarta mata abunda ya saka ni kuka a yau.

“Wata kila da gaske ajiya aka bashi, ki rika kyautata masa zato dan Allah”


Kaina na daga na kalleta.

“Idan wacan ajiya aka bashi wayar da na ji yana yi fa?”


Sai tai shiru domin a nan bata da amsar ba ni, ina da tabbacin babu wani abun da zata fada da zai kare shi a nan.

“Ba zan ce kunne ki be ji daidai ba, amnan ina son ki sani yawancin mazan nan haka suke, suna nan kashewa matan waje kudi ko da kuwa ba su yi ma na gida ba, ki yi hakuri Halima”


“Ko da yaushe idan na fada miki damuwa nai shiru kike cewa, ba ki tunanin hakurin nan zai iya zame min illa? Wallahi na gaji Haraja na gaji”


“Karki gaji da bautar Allah, ki dauki aure a matsayin idaba kuma ibadar da ta fi ko wace wahala, dan'adam be tana yin hakuri ya kasa cin ribar hakurin ba, idan rashin kyautawa Aminu baya kyauta miki amman ki yi hakuri wata rana za ki ji dadi”


STORY CONTINUES BELOW

“Yaushe zan jidadin? Tun da na haifi Adnan nake fuskantar wulakanci daga gurin Aminu har yau, haihuwa ta hudu kawai yake min wannan abun ime kike tunani a gaba? Ya GOBE NA zata kasance? Ina jin kamar babu wata matar auren da zata iya hakurin zaman auren da na ke da Aminu, shi ya min yan'uwansa su min ya zan ji?”


Dafani tai tana min magana a hankali


“Suna nan da yawa wadanda suka fi ki hakuri Halimatu, wasu ko abincin basa samu amman haka suke hakuri su zauna, ke ko har yana aje miki abinci ko da bashi da dadi ya dai baki lokacinsa ne kawai baya bashi da wasu hakokin, shin idan ba ki yi hakuri ba Halima so kike na ce ki kashe aurenki ki koma gidanku da zama cikin kannenki? Ya matan gidan ku a yanzu taskwas ne so kike a fara kirgawa da ke a zaurawan unguwarku? Ki tashi hankalin iyayenki da na yayanki? Kina da tabbacin shi wani mijin da zaki aura baya nema mata ko kuma zai baki lokacinsa? Ki bar yayanki su tashi a hannun wata wacce ba uwarsu ba? Adnan shekararsa goma sha daya kuma shine babba shi din ma kina da tabbacin zai iya yi ma kansa wata lalurar balle kuma sauran?”


“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u.

Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u.

Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u.”


Shine abunda nake ta furtawa na dafe kaina.

“Ki yi taka tsantsan da aurenki Halima saki daya ya rage a tsakaninku, wani abun ko dan yaranki ai kya yi hakuri ki zauna da mijinki a haka, kuma ki gode Allah da har mijinki yana amfani da Condom din, wasu mazan kamar tumaki suke babu ruwansu da kariyar kai, kuma wani lokacin mu kan mu mata muna da matsala, Halima ko yan gyare gyaren nan ba ki yi su kuma maza basa son haka, mace sai da gyra ko da ko baki haihuwa ba balle kin yi haihuwa har hudu”


“Namijin da ba ya maka kallon sha'awa Hajara wani gyara zan tsaya yi akansa? Idan ma nace zan yi gyara zan bata kudina da lokaci na ne a banza”


Na fada ina share hawayena.

“Ba haka ba ne, ba jira za ki yi har sai shi ya kawo kansa gareki ba, ke ma zaki iya yin wasu abubuwan na wayewa da janyo hankalin mijinki izuwa gareki, su ma matan waje ai ai janyo hankalin mazanjenmu suke har su kao garesu”


Kallonta nai ina sauke ajiyar zuciya.

“Hajara yace na daina burge shi wai shi baya son mata masu kiba, kuma shi yanzu farar mace yake so ni kuma ba fara ce fes ba, kuma ina da ji ba siririya ba ce ni, bana ganin ina da wani sauran digon kyau da zan iya jan hankalin Aminu da shi a yanzu”


“Bayan jan hankali, zamantakewar aure tana bukatar tattauna da fahimtar juna, kin rigani aure Halima amman kamar na riga ki karanta halin maza, ki zauna da mijin ki bashi hakurin abunda ya faru dazun ki nuna masa ke ce mai laifi ko da kuwa shi ne da laifi kuma ki fada masa zaki kiyaye, abu na biyu ki lura da abunda zaki iya canjawa sai ki yi kokarin yi, yar kwaliyar nan t tarbon miji ki rikayi mana haba Halima sai kace ba wayayya ba?”


“Namijin da baya dawowa sai 12 ko 1 na dare shi zan yi ma kwaliya? Kuma ya riga ya furta cewar bana burgeshi a yanzu duk wani abun da zan yi aikin banza ne Hajara”


“Ki gwada dai, akwai wasu kayan mata masu kyau anjima za a kawo min zan aika miki ki gwada amfani da su, ki maida komai ba komai ba Halima dan Allah ki yi hakuri ki zauna ko dan yayanki”


“Da ma kin bar kayanki, rabon da Abban Namra yai mu'amala da ni tun daga lokacin daya fahimci ina da ciki, daman can ba bukatana yake ba balle kuma yanzu”


“Ba daga nan take ba, ke dai ki yarda da ni ki gwada dan Allah, wanna kam ba mota ba ko jirgi kika ce kina so sai ya siya miki”


Kai na gyada mata ina tabe baki gare da sake share hawayen da suke min zuba, jin motar mijinta yasa na mikewa tsaye, kamin mijinta ya shigo falon nai mata sallama na fita da sauri domin ba kasafai na ke son yana ganina a gidan ba, ba dan komai ba sai dan tsaron mutuncin aurena.

  Daga gidansu Hajara kai tsaye gurin aikinmu na nufi, sai dai ban shiga Office ba sai da na biya ta gurin masu printing na cikin company nai printing documents din sannan na shiga cikin office din.

  Na shiga a lokacin da wasu sun dade da shigowa ma'aikatar wasu kuma yanzu suke shigowa a yayinda wasu kuma sai anjima za su shigo kowa da yanayin aikinsa da kuma lokacin shigowarsa. A inda muke zaune mu uku ne a Office din daga ni sai wasu abokan aikina biyu duka maza, daga ni sai Kabeer sai kuma Emmanuel wanda yake ba bahaushe ba. As usual idan na shiga ina gaishe da duk wanda na tarar a office din, idan kuma su suka tarar da ni suna miko min gaisuwa cikin mutunci da girmamawa.

Yau kam Kabeer kawai na tarar na office din hakan na nufi ya riga Emmanuel shigowa kenan.

STORY CONTINUES BELOW

“Good morning Kabeer”


“Morning Halimatu”


Na mika masa gaisuwar a lokacin da nake kokarin zaunawa, shi kuma ya amsa min yana baro bangarensa zuwa inda nake zaune.

“Kamar kina cikin damuwa yau kin karya kuwa?”


Haka yake min a lokacin dana shigo office din yana kokarin kula da ni kamar matarsa duk kuwa da na san kular bata Allah da Annabi ce ba, na san yana da wata manufar akaina

Hannu ya kai zai taba jikina sai nai saurin buge masa hannun na mike tsaye cikin bacin rai na ce.

“Miye haka Kabeer taba ni za kai? Ka manta da ina da aure ko me? Wai miyasa kake min wasu abubuwan kamar baka cikin hayyacinka ne?”


“Halima kenan, ni da ke mun zama daya a nan fa? Miye laifin dan na na taba jikinki?”


“Idan a gurinka ba laifi ba ne ni a gurina laifi ne, ina da aure har da yara hudu abunda ban aijata shi da budurcina ba ba zan aikata shi da aurena ba”


Ina fadar hakan na dauki documents din na wuce zuwa office din ogan mu, na yi zaton yana cikin musamman da na ga ya kirani jiya yace na shigo da takardun nan a zaton ko da saffafe zai duba su amman sai gashi ban same shi a office din ba. Hakan yasa na dawo nawa office din na zauna na soma aikina, gaba dayan ranar Oga Dahiru be shigo ba, haka ma wunin ranar Kabeer be ga wata sakewa a tare da ni kamar yadda ya saba gani ba. Har muka tashi daga aikin ban sake ce masa komai ba shi ma kuma be yi kokarin yi min magana ba.

  Kamar yadda na saba bayan na taso daga aiki na wuce gidansu Baban Sadi wato kenen mahaifinsu domin dauko yarana daman yana daukarsu tare da yaransa ya kai su gidansa idan an tashi scul har sai idan na taso aiki na biya na dauko su a Napep mu dawo. A bakin kofar falon muka gaisa da matarsa sannan na kirasu suka fito banda Namra.


“Ina Namra?”


“Tana can part dinsa ai kin san indai yana nan to tana can part dinsa, ko fita zai yi da ita yake fita Allah ya hada jininsu”


Cewar Safiya matarsa. Ni kuma nai murmushi ba tare da tunanin komai ba na kalli Aiman na ce yaje ya kirata na saka Amal da Adnan a gaba muka nufi gate da zimmar Namra da Aiman su cin mana. Kamin mu fice daga gate din gidan sai gasu sun ci mana Namra na ta sharar kwalla idonta ya yi ja sosai.

“Ke lafiya?”


“Cikina ke ciwo”


“Oh wannan ciwon cikin ya matsa miki, bari yanzu idan muka muka je gida su Adnan suka wuce Islamiya sai na kai ki asibiti”


“To Momy”


Ta amsa min cikin kuka har sai da ta bani tausayi. Napep na tara na saka yarana sannan na shiga muka nufo gida. Indomie na fara dafa musu suka ci sukai shirin islamiya sannan na dora tuwo na shiga nai wanka nai ma Namra na shirya ta, sannan na fita na kira Kausar wata kanwar makociyata wacce budurwa ce daman na kan kirata ta rika min wasu abubuwa. Ita na barwa girkin sannan na ja Namra muka nufi Asibitin Yarima ganin likitan yara na maraice.

  Ba mu tararda jira kamar safe ba, daman da maraici ba a cika taruwa ba, a lokacin da muka shiga dakin likita ya tambaye ta komai ta fada masa yadda take jin cikin nata yana mata ciwo, sannan na rubuta mana hoto da awon fitsari sannan na rubuta mata magani. Sai da na kaita akai mata hoton fitsarin kuma suka ce a kawo na safe wanda zata fara yi kamin ta ci komai. Maganin ne kawai ban siya mata ba muka dawo. A saman kujera ta kwanta ni kuma na shiga kitchen na dora miya domin ko da muka dawo Kausar ta toke mana tuwon.

Daf da magariba Adnan suka dawo daga makarantar islamiya, daker na tattara su sukai sallah sannan na kwashe miyar na zuba musu nasu na sako nawa ni da Amal muka ci Namra kan ko ruwa kasa sha tai, hakan yasa na dauki wayata na kira shi. Sai da ta dade tana ringing sannan na daga.


“Ya akai?”


Shine abunda ya far tambaya, ni kuma na mika masa gaisuwa


“Ina wuni?”


“Lafiya Kalau”


“Namra ce bata da lafiya tun jiya cikina na ciwo shine na kaita asibiti dazun suka bamu awon fitsari da hoto kuma suka rubuto mata magani”


“Wa kika tambaya kamin ki fita? Da izinin wa kika fita?”


Sai na kasa amsa masa domin na san bana da gaskiya a nan, be kamata na fita ba tare da na tambaye shi ba, sai dai na san idan na tsaya tambayarsa ba lallai ne yace na tafi ba domin duk wani abu daya fito daga bangarena baya daukar sa da muhimmancin wata kila ma zai ce kashin kudin ne zan ja masa.

“Ka yi hakuri dan Allah”


Be amsa min ba yaja tsaki ya kashe wayar. Ji kuma na sauke ina jin raina ba dadi a take abincin ya fita raina daman da safe ban iya karyawa ba.

“Adnan je ka kira min Kausar ta siyo ma Namra magani a chemist”


Da sauri ya tashi daman dan son yawo ne shi da Amal a take ta rufa masa baya har da gudunta. I decided na aiki Kausar din na bata kudin da ke hannu ta siyo mata maganin kamin shi ya gama fushinsa ya siyo mata. Adnan na fita sai ga Afrah ta shigo wato yar Hajara da bakar leda a hannuna.

“Wai ga shi Momy tace a kawo miki”


Karba kawai nai na aje ba dan ina tunanin amfani da shi ba, domin na saba amfani da irin abubuwan nan ban taba ganin ribarsu ba, sai dai na ji wasu matan suna labarin abu kaza yana da kyau ko yana yi, ni dai nawa mijin bayan nuna min idan ma na sh wata kila kuma ni tawa hallintar bara karbar irin waennan abubuwan.  Afrah na fita sai aka sake turo kofar falon aka shigo wannan karon Sa'adatu ce kawata.

“A a maraba da manya”


Na fada ina dariya.

“Ah ai kune manya kuna cikin irin wannan gida haka ga uwar daula ai kukan ku kukai dacen auren mu mata kawai muka rako duniya”


“Uhmm”


Kawai na iya fada domin yawancin mutanen da suke zuwa gidana suka ganin kyakkyawan falona da gidan sai su tai min kallon kamar na fi kowa dacen aure.


“Bari dai na kawo miki ruwa”


Na fada ina nufar kitchen, ita kuma ta hau tambayar ina Amal da sauran yaran.


__________________


Anya da gaske akwai mata irin Halimatu kuwa? 🤔“Sa'adatu kenan, kwana biyu ma kin daina dan lekowa, ko ya fara hana yawo ne?”


Na fada bayan na mika mata ruwan sai ta wara ido.

“Tab ya isa? Ai a hannuna yake sai yadda na ga dama na juya shi”+


“Too kaji manya a bamu sirrin”


“Sirrin mai wuya ne Halima,amman Wallahi da ni nake da kyau ki da irin wannna jikin na ki sai na more”


Kallon rashin fahimta nai mata.

“Kamar ya ba?”


“Ka more rayuwa mana, kai ta sha'aninka kana zuwa duk inda kake so”


Ta fada tana janye mayafinta daga jikinta a take kirjinta ya bayyana, daman irin dinkin nan mai bayyana maman mace daga gaba.


“Ai kin san halin wani namjin ba daya ne da wani ba, kin ga ke idan mijin ki mai sauki kai ne baban naki ba shi da dama”


Na fada tare da kiran Aminu da babanta kamar yadda take kiransa kasancewar sunan mahaifinta ne.

“Babu namijin da yake da dama Halima, ni kin ga mijina Wallahi zan iya tafiya wani garin na kwana iya kwanakin da naji sun min na dawo be isa ya ce min komai ba”


“Too ku manya ne Sa'adatu”


Na fada cike da sha'awa da kuma jinjina abunda ta fada, ko bata fada min da bakinta ba na san zata iya domin ta saba zuwa wani gari da sunan biki ko ganin yan'uwa ta bar masa yaransa sai ranar data ga dama ta dawo kuma ba zai yi komai ba. Abun har burgeni yake ni da wani lokacin ko makota sai Abban Namra ya hana ni zuwa.

“Wai ya kika ba ni ruwa zalla a tsirara ba masu kala ne?”


“Baban na ki ne be siyo masu kala ba”


“Aa Babana fa komai kawowa yake karki cutar da shi, daman kin saba bakin sherinki ni bari ma na tashi daman bankwana na zo nai miki zanje Kaduna gobe In-Sha-Allah”


“Kaduna kuma? Gurin me?”


“Wallahi wani abun bikin ne ya taso mana zanje na kwana hudu ko sati ma a can”


“Da yaran zaki je kenan”


“Aa ni kadai zanje na shakatawata abuna yara su zauna gurin Babansu”


“To indai baki yi hankali ba sai ya dauko miki wata”


“Ai be isa ba Wallahi wa? Ni? Hmmmm ai na bashi wannan ya shanye”


Ta fada tana wani turo dankwali tare da nuna min kasan kafarta.

“Haka fa, na ji ance ana yi ko?”


“Au tsayawa ji kikai? Ba ki ma aikata ba”


“Ina ganin kamar akwai rashin dacewa a haka”


“To yar sarkin Malamai”


Dariya nai zan sake magana sai jin tsayawar motar Abban Namra mu ka ji, a take gabana ya fadi domin na san zai tambaye shi yaransa gashi tun da na aikasu basu dawo ba, kamin ya shigo falon hankalina ya tashi sosai saboda aiken da nai musu ga kuma fita kai Namra asibiti da nai ba tare da izininsa ba na san zai iya yi min fada a gaban kowa, ni kuwa abunda na tsana kenan ayi min fada a gaban wani musamman kawayena.

Fuska a hade ya shigo falon ni kuma nai saurin mikewa tsaye na nufi inda yake ina masa sannu da zuwa tare da kai hannu na karbi jakarsa.

Da kamar ba zai amsa min sannun da nai masa ba, sai dai yana gada ido da Sa'adatu sai ya sake fuskarsa.

“Yauwa, a a diyata ce da kanta a gidan?”


“Nice Babana ya garin ya gararin garin?”


Ta amsa tana wani karkada ido, na yi zaton ko zata ja mayafinta ta rufe kirjinta ne kuma ta gyara ture kaga tsiyar da tai na dankwalinta amman ba ko daya, zama yai a kujerar da ke facing din tata yana murmushi.

STORY CONTINUES BELOW

“Fatar kin zo lafiya?”


“Lafiya kalau matarka ta bani ruwa masu sanyi amman ba masu kala na yi magana tace Babana be siyo ba”


Sai juyo yai ya kalleni ina kokarin zama kusa da shi.

“Ah ah drinks ya kare ne daman? Ai baki fada min ba”


Kasa ce masa komai nai bayan kallon mamaki da nake masa rabon da ya siyo mana wani abu mai sunan lemu mu sha a gidan har na manta, amman yau saboda ya nuna yana siya har yake tambayar yaushe ya kare? Haka yake min idan ya ga mutane ni kuma bana iya karyata shi.


“Jiya ya kare”


Na fada ina hade yawun bakina.

“Okay bari sai gobe a siyo ai ban sani ba, ina fatar kin ci abinci?”


Ya karasa yana naida dubansa gurin Sa'adatu.


“Aa ban ci ba”


Sai ya juyo kaina.

“Miyasa ba a bata abinci ba? Ko ba a gama ba? A kawo mata abincin mana”


“Aa ni tafiya ma zanyi”


Ta fada tana janyo mayafinta ta rufe jikinta tare da gyara dankwalinta. Sai shi ma ya mike tsaye da sauri yana ta kallonta.

“Bari na rage miki hanya, ina takardar maganin take?”


“Tana daki”


“Je ki dauko sai na siyo daga can”


Har na bude baki nai magana ganin da gaske yake zai wuce da ita sai kuma wata zuciyar tace nai kawaici na kyale shi. Dakina na shiga na dauko takardar maganin na kawo masa sai ya karba yana duba sannan ya kalleta ya ce.

“Muje”


“Matar Baba sai wani gamon kuma”


“To Allah ya kiyaye hanya”


Na fada ina binsu da kallon zuciyata na mugun tsoyuwa. Sai da suka fice daga falon na koma gurin windows din ina hangensu har suk shiga motar yaja sukai gaba, ajiyar zuciya na saki tare da sakin labulen falon sannan na dawo saman kujera ya zauna, na san Sa'adatu zata dauki hankalin Aminu saboda bata da jiki kamar ni kuma ita fara ce sosai kamar dai yadda yake yawan fada min yana son mace fara marar jiki ba irina ba. Tunanin yadda zan yi na rage kibar ne ya fara zuwa min a rai shi farin na san mai sauki ne zan iya siyen mayukan fari na shafa nai fari amman rage kibar ne zai ba ni wahala domin na gwada abubuwa da dama na rage kibar har yau ban dace ba, sai a yanzu na tuno da wani maganin rage kibar da na siye, tashi nai na nufi upstairs, ina shiga dakin na nufi gurin dana rataye jaka na dauka bude n dauko maganin na sauko kasa na shiga kitchen na zuba ruwan zafin da suke a filas na zuba maganin na kasa sugar kadan na fita shi, sannan na zauna ina sha a hankali, zuciyata cike da fatar ya karbe ni ni dai duk abunda zai shiryani da mijina mu yi zaman auren na jindadi da kaunar juna ina son shi, ina ji a raina inda har idan na kawarda kibar nan da ke jikina nai fari fes Aminu zai so ni to na shirya yi ko da kuwa zan kashe kudi da yawa.

Ina cikin sha na jiyo Namra tana amai da sauri na aje kofin na fito da sauri na rikata, amai take babu kakkautawa, a take hankalina ya tashi daman abu kadan ya saka ni faduwar gaba ko kuka. A cikin falon tai aman har ta gama sannan na rika ta na kaita bandakinsu na wanke mata jikinta na saka mata wasu tufafin.


“Momy sanyi na ke ji kum cikina ciwo yake”


Ta fada cikin kuka jikinta na ta kyarma. Rigar sanyi na dauko na saka mata na kwantar da ita saman gadonsu na lullube ta sannan na fito na gyara falon. Sai da na gama gyaran sannan Adnan da Aiman suka dawo daga aiken da nai musu tare da Kausar din.

“Ina kuke je kuka tsaya tun dazun?”


Na fada cikin tsawa a take tsoro ya rufe Adnan.

“Momy ko da muka je bata cikin gidan sai muka jira har ta dawo muka fada mata, ki yi hakuri dan Allah”


STORY CONTINUES BELOW

Abunda sukai min be kai ya saka raina baci ba balle har na dake su, amman sai zuciyata ta rufe a take a gurin na mari Adnan kamar wani babba na ciro wayar caja na saka na zanesu tas suna da kuka da ihu Aiman na ni yake ta kira amman nai kunne uwar shegu da ihun na su kuma na tirsasu su yi shiru.


“Kausar ki bar shi kawai daman magani za ki yo ma Namra kuma Babansu ya karbi takardar maganin”

Da to ta amsa min ta fice da sauri ganin kamar raina a bace yake. Ni kuma na koma kitchen din na hada wa Namra tea wai ko zata iya sha amman ta kasa sha, sai kuka take hakan yasa hankalina ya tashi na sake gwada kiran Abbansu wayar tai ringing har ta gama be dauka ba. Be kuma shigo gidan ba sai sha biyu da mintuna kamar yadda ya saba, ni kuma har lokacin ban yi bachi ba ina rumgume da Namra ga Amal a bayana wacce ta cilasta ni goyonta saboda bakar rigima irin nata.

“Sannu da zuwa”


“yauwa”


Ya amsa min fuskarsa ba yabo ba fallasa sannan na wulgo min ledar maganin ya nufi hanyar dakinsa, kwantar da Namra nai daga saman jikina zuwa jikin kujera na tashi na nufi inda ledar maganin take na dauka zuciyata nata soyuwa, na rasa gane wane irin zama na ke da Aminu, kamar waenda akai auren dole ko kuma basa kaunar junansu haka yake mu'amala da ni, ko za a yanka ni ba zan iya fadar abunda nai masa ba wanda ya saka yake min wannan wulakancin. Ta jikin kwalin maganin na duba yadda ake badawa na zuba na bata ta sha sannan na dauketa daga falon na sake maida ita dakinsu tare da yan'uwanta na kwantar da ita, kana na nufi gadon Amal na kwantar da ita ita ma nai mata addu'a na tofa mata sannan na janyo kofar dakin na fito. Dakina na koma na sauya tufafin jikina daga atamfa zuwa wani yadi mai kyau da kyalli na fesa turare na gyara fuska na shafa janbaki da dan man baki kadan dan yai kyali sannan na fito na nufi dakinsa. Da sallama na shiga ya amsa min yana cin abinci ba tare da ya kalleni ba. Sai na zauna gabansa ina ta kallon yanayinsa shi kuma hankalinsa na kan wayarsa.

“Ya akai?”


“Ba ni da hali na zauna da kai da sunan hira ko kallonka sai ka tambaye ni minene? Ban san abunda nai maka ba Abban Namra amman gaba daya ka canja min kamar ba kai ba, ni dai na san ba auren kiyayya mu kai ba amman irin zaman da muke da kai kamar na kiyayya”


“Da bakamar yanzu ba ce Halima, auren soyayya mukai kuma ai zaman soyayya muke ko? Ko na kiyayya ne? Ke kanki kin san da bana son ki ba zan zauna da ke ba, kuma rayuwa tana sauyasa ke kanki ai ba kamar yadda kike ada kike a yanzu ba kin canja”


Hawaye ne ya fara min zuba.

“Canjin jikina kadai be isa ya saka ka wulakanta ni ba, ban sani ba ko na aikata maka wani laifi mai girma da ban sani ba, ko kuma a sani ni ina ganin kamar ba laifi ba ne, dan Allah ka yafe min Abban Namra, na kasa sabawa da zamankewar auren da muke, na kasa fahimtar juya min baya da kai ka yafe min idan wani abun nai maka dan girman Allah”


Be ce min uffan ba har ya gama cin abincin ya sha ruwa sannan ya dago kansa ya kalleni ya ce.

“Indai kina son mu shirya da ke, to ki aje aikin nan babu yadda za ayi kina aiki kina mu'amala da wasu maza a waje ni kuma kina zaune a gidana kawai a matsayin mata, gashi nan har idonki ya fara zarewa kina fita ba tare da kin tambaye ni ba abunda baki saba ba, Allah kadai yasan kalolin mazan da kike gamuwa da su”


“Ka rika kyautata min zato, ko da yaushe kana yawan cewa ina mu'amala da wasu mazan a waje, kana yawan ganin kamar ina aikata fasikanci ne da aurena, ba zan iya aikata zina ba ba zan iya da hakki hudu ba, naka na iyeyena na yayana da kuma na Ubangijina, ina aikin nan ne saboda daukewa kaina wasu lalurorin kai ma ka sani, muna da hidima da yawa a gidanmu iyayena ma suna bukatar taimakona”


“Dauke ma kanki wasu lalurorin? Miye bana miki ci ko sha?”


“Ba ci da sha ne kadai abunda mace take bukata a gurin mijinta ba Abban Namra, akwai kulawa da wasu bukatun na yau da kullum da kuma ta yan'uwa da iyaye, amman indai har aje aikin nan zai saka ka shirya da ni mu koma muna zama da juna cikin amince da kauna, zan aje sai na kama sana'a”


“Aa idan kin san idan kika aje aikin wata sana'ar zaki kama kar na ki aje aikinki daman ai ban isa da ke ba”


Kasa cewa komai nai har kuma lokacin hawaye nake, Aminu wani irin murdadden mutum ne wanda baya fahimtar abu idan baya so ba. Taya zai hanani aiki kuma yace ba zan yi sana'a ba, kuma ba zai dauke min duka lalurorina ba?

“Ga cikin nan na ce miki a zubar kin ki yarda, haba wane irin abu ne haihuwa hudu a shekara goma sha biyu, ai gashi nan duk kin bude kin wani tsufa, kuma yanxu ana ta abinci ai ba ta haihuwa ake ba ina zan iya da lalurar yara biyar a yanzu, idan kin yaye ki sake daukar wani kuma? Haba abu ai yayi yawa”


Ya fada min kai tsaye, sai a yanzu na gane dalilin kauracewa shimfidata da Aminu yai. Mikewa nai tsaye na juyo da zimmar fitowa na baro masa dakin, sai na ji ya ce.

“Zanje Kaduna gobe gurin wani aiki, wata kila nai kwana hudu ko sati”


Ban juyo ba ban kuma ce masa komai ba, na baro masa dakin na dawo falo na zauna na rungume hannayena ina wani abun a zuciyata, idan nace zan kashe aurena hakika ban san wane hali yarana zasu fada ba, ban kuma san wane kalar mijin zan aura ba, idan kuma na cigaba da zama da shi zan saka kaina cikin damuwa ne kawai marar misaltuwa, domin ko a yanzu idan aka auna na san ba za a sara samuna da hawan jini ba, shekara goma sha daya ba yau ko jiya ba ne.

“Idan kika cigaba da zama da mutumen nan, hawan jini ne zai kama ki, zaki kai wani mataki da baki iya komai daga lokacin kin tashi aiki, ba zaki iya tsinanawa kanki komai ba, ban ga dalilin da zai saka ki yi hakurin zama da mutunen nan ba wai wani zaman yayanki shi be san da yayan ba ne yake musguna miki? Ko ke kadai aka dorawa hakkin kula da su”


Dafe kaina nai tunawa da maganar da Abdallah yai min akan Aminu, wani bangaren yana da gaskiya idan na ce nai hakurin zama ni ce zan cutu idan kuma na bar gidan still zan cutu da rashin yayana a kusa da ni.

“Ko wane aure yana da kalubale Halimatu, ki yi hakuri ki ta addu'a ki karbi kaddararki da hannu biyu, idan kin bar Aminu kina da tabbacin shi mijin da za ki aura ba kamar Aminu ba ne? Idan ba ki hakurin zama da uban diyanki ba ba zaki iya hakurin zama da kowa ba, kuma daga haka za a fara kirga miki aure”


Haka Mama take yawan fada min idan ina mata complain din Cewar na gaji da zaman auren nan. Yanzu kumaga sharadin Aminu na aje aiki idan har ina son ya shirya da ni, ba ni da tabbacin idan na aje aiki zai kula ni domin tun kamin aiki ya fara min wannan wulakancin, idan kuma na bar aikin wasu abubuwan da nake iya yi ma iyayena ba zan iya daukar dawainiyar ba, wasu abubuwan da nake iya yi ma kaina dole za su gagareni. Haka dai nai ta tunanina kala kala har kusan biyu na dare sannan na tashi na nufi dakina, wutar dakin na kashe sannan na hau saman gadon na kwanta na lumtse idona ba dan ina jin bachi zai dauke ni ba. Dilllll wayata tai kara alamar shigowar sako bude idona nai na ka hannuna saman aljihun gadon na dauki wayar ina dubawa.

_Ki yafe min dan Allah, na kasa bachi saboda na san yau na bata miki rai, amman ban yi zimmar daba ki da wata manufa ba, ina ganin kamar ni da ke mun zama daya ne, kuma ni na dauke shi a matsayin wayewa ba wai dan wani abun ba, sai dai naga kamar ranki ya bace ki yi hakuri dan Allah ki shafa min kan yaran nan ki gaishe su_


_Kabeer_


Ina gama karant sakon hawaye ya wanke min fuska, wani wanda ba mijina ba shi yake damuwa da fushi da bacin raina har ya gaishe da yarana. Rumgume wayar nai a kirjina ina jin wani irin kyautata da ganin kimar Kabeer.__________________


Anya Halimtu zata aje aikin kuwa? Ko kuwa dai zata zabi zama da Aminu a haka? Wai mi yake damun Namra ne? 🤔2Iyayena na gari abun alfahari idan kai dace da iyaye hakika ka yi babban dace, bayan su kuma sai miji shi ma idan kai dace da miji na gari ka samu ingantacciyar rayuwa idan Allah yai maka falala ka sake dace da yayana nagari ko kai an gama maka komai a rayuwarka. Al-hamdulillah ban san yanda tarbiyar yarana zata kasance ba bayan girmansu amman ina fatar su tashi akan tafarkin da na dora su akai, idan na samu haka ko da shi kadai zan iya gode Allah, duk kuwa da na san babbar jarabawar duniya ita ce ta rashin dacen miji.

Ban taba jin kewar budurci ba irin yau, ji nake kamar ace yau ni din budurwa ce da na sake zaben wani mijin ba Aminu ba, na kwana rungume da sakon wani a kirjina saboda rashin kulawar mijina, da ace na san rayuwa zata sauya min haka bayan aure da na zabi zama a budurcin har na bar duniyar nan, bachi be dauke ni da wuri ba, haka kuma ban dade ina bachin ba na farka, kaina har wani nauyi nake jin yana min ga wani uban ciwon zuciya da nake jinsa har cikin kashin bayana.+

After sallah nai addu'o'in da na saba sannan na nufi kitchen domin hada ma yarana abincin zuwa makaranta, misalin bakwai saura na safe ya shigo kitchen din rike da jakarsa sai ya tsaya a jikin kofa, ni kuma nai kamar ba san da mutum a gurin ba har sai da yai gyaran murya sannan na juyo na kalleshi

“Ina kwana?”


“Lafiya kalau, ga wannan ki rike da wuri zan tafi saboda bana son rana yai min”


Ya fada yana miko min dubu uku, kallon kudin nai na girgiza masa kai.


“Ka kara akwai kudin da za su ishemu har ka dawo”1


Be ce min komai ba, ya aje kudin saman kitchen cabinet ya juya, a karon farko yau zai tafi wani gari amman na kasa ce masa Allah ya tsare sai binsa da nai da kallo. Juyowa yai ya kalleni.1

“Da ki min addu'a da karki min duka uwarsu daya ubansu daya, sai abunda Allah ya rubuto zai same ni, mugun nufinki ya koma kanki”1


Yana fadar hakan ya juya ya fice, ni kuma nai murmushi ina jin bakar maganar da ya fada min har cikin raina. Kaina na daga ina kallon kitchen din yadda tsarin gidanmu yake da siffar masu arziki ko kyautar rabin miliyan nai ba za ayi mamaki ba saboda ana ganin mai arzikin nake aure, amman yau zai yi tafiya saboda bakar keta irin nasa ya dauki dubu uku ya bani.

Dauke kai nai domin na san idan na ce zan cigaba da tunani zan iya faduwa a gurin ko kuma wani abun ya same ni.

Bakwai da rabi na shiga na tashi yarana nai musu wanka sukai alwala sukai sallah sannan na shirya su cikin uniform dinsu na makarantar boko ban da Namra da har yanzu bachi take jikinta kuma da dan zafi. Kasa suka sauko suka karya tare da Amal sannan na shiga dakina na saka hijab na fito na saka su gaba muka nufi gate. Sai dai mun yi sa'ar haduwa da mijin Hajara kamar jiya.


“Ina Namra yau?”


“Bata jindadi”


“Subhanallahi Allah ya sauwake”


“Amin”


Sai ya saka yaran a motarsa har da Amal suka tafi, daman ta saba idan yan kwarai suna kanta tana yarda ta bisu su tafi idan ya dawo sai ya kaita gurin Hajara.

Juyowa nai na dawo cikin gidan, sai na shiga dakina nai wanka ina cikin shiryawa wayarta tai ringing, dauka nai na duba sai ga number Abdulhamid hakan yasa ni picking na kara a kunne.


“Hello”


“Good morning Halima ya gida ya yaran?”


“Lafiya kalau”


“Na miki sako ta whatsapp wai baki hau ba so i decided na kira ki”


“Lafiya dai?”


“Account number dinki na k so dan Allah zan dan saka miki wani a ciki”


Dauke wayar nai daga kunnena na duba dan kara tabbatarwa idab Abdulhamid din ne, ganin shi ne yasa na maida wayar a kunne na ce.

“Abdallah yace ka saka min?”


STORY CONTINUES BELOW

“Abdallah kuma?”


Shiru nai na kasa cewa komai, na san tawayensa Abdallah shine mai yi min irin wannan dabi'un yana yawan fada min ba dadi Akan Aminu da aure daga daga cikin dalilin daya saka nai blocking dinsa ta ko'ina.

“Halima Abdallah yace zai baki kudi ne?”


“A a, eh yace amman an dade”


“Rokonsa kikai?”


“Eh”


“Miyasa baki tambaye ni ba? Ba na fada miki ki rika fada min idan kina bukatar wani abun ba?”


Na yi shiru ban ce komai ba.


“Ki turo min account number dinki yanzu”


“To na gode”


Na sauke wayar daga kunnena ina tunanin dayan biyu, mi zai saka haka nan kawai Abdulhamid zai ce na turo account ya saka min kudi abunda be ta a ba, ko dai Abdallah ya saka shi yace yai kamar shi ne saboda na karba? Ban yanke dayan biyu ba na tura masa account din. Sannan na aje wayar na tashi na nufi dakin yara ina tuna rayuwar da mukai a baya, wata kila da shi na aura kamar yadda na tsarawa kaina da yanzu na yi dacen aure, sai dai lalurra da ke tare da shi ta sauya kaddararmu shi ya a zauna a haka har yanzu babu aure ni kuma nai auren na kasa dacewa da mijin.

_Zan jira har zuwa lokacin da zaka samu lafiya Abdulhamid_


_Aa mace ce ke Halima be kamata ki zauna a haka na tsawon lokaci ba ba, idan na hana ki aure a yanzu zai zama na cutar da ke ne kawai_


_To zan aureka na zauna a gidanka har ka samu lafiya_


_Shi ma cutarwa ne Halima ba zan iya aurenki na danne miki hakki ba, ban san iya yaushe zan dauka kamin na samu lafiya ba, ke kuma wannan ce kadai damar da kike da ita ta zabar mijin aure, kuma iyayenki suna son ganin aurenki a yanzu kin kai matakin da ya kamata ace kina dakin mijinki_


_Yanzu rabuwa za mu yi kenan Abdulhamid?_


_Rabuwa ta zame mana dole shiyasa ban taba fadawa kowa ina kaunarki ba, kuma ban taba nunawa ba, ke ma kuma na nuna miki ne a zaton kamin ki gama karatunki wata kila na samu lafiya, ashe abun ba nan kusa ba ne wata kila ma ba zan warke ba_


Tunawa da wannan ya saka ni zubar hawaye, sai dai ina shiga dakin yara sai nai saurin sharewa na nufi inda Namra take kwance ya yaye blanket din na kai hannu na taba ta, sai ta bude ido.

“Sannu Namra”


“To Momy yau ba zan je scul ba”


“Eh yau asbitin zan koma da ke ai su sake dubaki saboda ciwon cikinan”


Jin na goya mata baya ba zata je scul ba sai ya saka ta sauko da kafafuwanta, na rika ta muka nufi bathroom. Mai na soma saka mata a brush ita kuma ta fara yin fitsari sai ta saka kuka.


“Momy zafi”


“Minene zafi?”


“Fitsarin zafi sosai”


Brush din n aje na zo na daga ta na saka ta a cikin tub din na ware kafafuwanta ina dubawa. Gurin ya mata ja sosai kamar an watsa mata yaji a ciki gashi har ya mata rame a ciki.

“Namra me ya same ki a nan?”


Sai kawai ta kara bare baki tana lekawa ta kasa ce min komai.

“Ba komai”


Na fada tana kuka, tsawa na daka mata har sai da ta zabura.


“Fada min mi ya same mi a gurin”


STORY CONTINUES BELOW

“Wayyo Allah na ba ni, Momy dan Allah ki yi hakuri”


Ta fada cikin kuka tana yarfar da hannu. Mikewa nai tsaye fuska a hade na ce mata.

“Kin san idan kika min laifi dukanki na ke ko? To yau yankaki zan yi kamar rago na soya namanki na zubar a bola”


Ina fadar hakan na juya ya fice daga bandakin na sauko kasa gabana sai dukan shida-shida yake tsabanin uku-uku da na kowa ke yi. Kitchen na nufa na dauko wuka na hawo saman na shiga dakin sai an samu ta fito daga bandakin ta labe gefen gado tana ta rusa ihu.


“Momy dan Allah ki yi hakuri karki kashe ni bana son na mutu dan Allah ki yi hakuri”


“To fada min mi ya same ni a nan”


“Idan na fada shi ma Baba Sadi yanka ni zai yi, wayyo na shiga uku Abbah..... ”


Kasa magana nai jin abunda ta fada gaba daya sai jikina ya kara yin sanyi, ga wani uban kuka da take kamar zata shude. Aje wukar nai na mika mata hannuna.

“Taso zo nan”


Sai ta girgiza min kai.

“Aa yanka ni za ki yi Momy ba zan zo ba”


“Ba zan yanka ki ba ni mahaifiyarki ce ba zan iya yankaki ba, idan kin fada min abunda Baba Sadi yake miki ba zan miki komai ba”


“Idan kuma na fada shi ma yanka ni zai yi wayyo Allah na”


“Ba zan bari na yanka ki ba, kuma ba zan fada masa cewar kin fada min ba, wannan sirrin mu ne ai ba zan fadawa kowa ba”


Na fada ina karasawa kusa da ita a hankali, sannan na kai hannu na rika ya dawo da ita saman jikina na rumgume har lokacin kuka take jikinta na ta rawa sosai. Kyale ta nai sai da ta ci kukan ta a jikina sannan na dago ta na share mata hawayenta ina mata murmushi ta yadda hankalinta zai kwanta ta yarda da ni.

“Yata Namra fada min mi Baba Sadi yake miki?”


“Ba zaki min komai ba?”


“Eh kuma ba za su fada masa ba ai wannan sirrin mu ne mu kadai ko Abbah ba zan fadawa ba”


“Yace idan na fada sai ya yanka ni kuma na kone gawata kuma yace idan an mutu can zan samu wuta tai ta kona ni ciki kasa”


“Karya ne kawai yakr baki tsoro ne, fada min zan siya miki duk abunda kike so”


Shiru tai na wani lokaci sannan ta sake daga kanta ta kalleni.


“Momy ni bana son na mutu”


“Ba zaki mutu ba idan kika fada min”


“A nan yake saka min abu”


Ta nuna gabanta tana kallon fuskata, sai nai mata murmushi ina nuna gurin.

“A nan?”


“Eh da kuma abaki yake saka min wannan abun”


“Shine wani abun tsoro? Ai ba wani abun ba ne, da har zaki ji tsoro”


“Amman shi yace karna fada”


“Shikenan abunda yake miki?”


Na tambaya ina jin kamar kuka sai kubuce min, su kan hawaye tuni na fara yinsu.

“Eh da hannu yake saka min sai jiya da wacan monday ya sska min abun fitsarinsa a nan, kuma da zafi sosai idan nai kuka sai ya ce ba zai ba ni chocolate ba, kuma idan na fada zai ya ka ni?”


“Da yaushe da yaushe yake miki haka?”


“Idan muna part dinsa sai na kore su Adnan da su Safwan yace su tafi ni kadai na tsaya wai suna masa yahaniya ni ce kawai bana masa ihu sai su tafi idan suka tafi sai ya saka min hannu a nan ko kuma ya bani yace na sha, kuma ya ce idan ban hade wannan majinar ba sai doke ni, ko kuma ya saka bakinsa a nan ya yi min yadda nake masa, wata rana kuma idan mun tafi wani gurin sai ya fita da ni ya siya min abun dadi yai min haka nan ko yace nai masa, ko ranar da muka tafi yawo sai ya aje su Safwan da Aiman a gurin wasan yara ni ya tafi da ni a mota ya saka ni na sha masa tsanar sa, tsana haka yake cewa”


Ban iya komai ba a lokacin bayan fashewa da kuka mai tsanani. Babu mace da zata labarta yadda wata macen take ji har sai ta taba kasancewa a cikin halin da wacan macen da ta taba kasancewa. Daga ni sai ire-irena mu ke iya bayyana yadda mace ta ke ji idan aka keta haddin yarta ko kuma ita kanta! Ina ma ace yau haddina ni Halimatu aka keta ba na yata ba?

“Namra miyasa baki fada min ba tuntuni?”


“Ai yace idan na fada zai yanka ni kuma na fada miki bana son zuwa can ke kuma sai ki ce sai mun tafi kamin ki dawo daga aiki”


Rasa nai abunda zan yi ko na ce mata sai kawai na sauke ta daga jikina na aje ta saman gadon na taso na baro mata dakin na dawo falo na zauna na safe kaina ina jin zuciyata kamar zata fashe. Kuka nai sosai ba na wasa ba ji nake kamar na hade zuciya na mutu na hutu gaba daya. Kamar wacce aka tsikara na tashi da sauri na koma sama na dauki Hijab dina na saka na dauki jakata da wayata na nufo dakinsu na dauke ta da kayan bachinta muka fito ko rufe gidan ban tsaya yi ba na nufi titi ina samun napep muka nufi asibiti. Har cikin asibitin hawaye nake ina sharewa gashi na yi rashin sa'a na tarar har an gama daukar suna, a karon na farko bayan na yi blocking din number Abdallah yau da kaina ba daga waya na kira shi. Bugu biyu ya dauka.

“Ko dai kin kira ki min bakar magana ko kuma ki zage ni, domin na san ina da farinjinin da ba zaki kirani ki min magana kamar yar'uwa ba”


Fashewa nai da kuka.

“Dan Allah Abdallah ka taimaka min na zo an gama daukar suna na kawo Namra ne”


“Kina ina?”


“Ina bangaren yara bakin kofar shiga”


“To zan zo na same ki a nan”


Tsakanin kashe wayarsa da zuwansa be wuce minti biyar ba, da alama yana kusa da gurin kuma ya karasa inda na ke da sauri har yana hadawa da gudu. Ganin yadda hawaye ke min zuba yasa shi tsayawa yana kallona.


“Halima lafiya?”


Kasa magana nai sai yaja hannun Namra yana dubata.

“Mi ya same ta wai? Lafiya kike?”


Hankalinsa ya tashi sosai ganin ina kuka.

“Lafiyarta nake son a abinci ka min”


Na fada ina hawaye kamar ba gobe bakina na rawa.

“Lafiyarta kuma?”


Kasa amsa masa nai sai na juya da zimmar tafiya.


“Halima?”


Na juyo.

“Lafiyar ki kuwa?”


“Ban sani ba, ina jin kamar bana da damuwa kuma ina jin kamar akwai abunda yake damuna, gida nake son naje”


“Wane gida?”


“Gida gurin Mama da Baba na fada musu”


Magana nake ni kaina ina jin kamar a mafarki nake maganar ba a zahiri ba. Tallabar Namra yai ya dorata a kafadarsa ni kuma ya rika hannuna.


“Zo muje”


Ya nufi hanyar da ya fito da ni, ni kuma ina ta binsa ba tare da nasan inda zai kai ni ba, mutumen da na ke ciwa mutunci ina zaginsa yau yana jaye da hannuna na kyaleshi.

_______________________


Tsakanin Namra da Halima wa yafi zama abun tausayi? Namra da aka lalatawa rayuwa ko kuma Halima da take mahaifiyarta kuma take rayuwa da mugun miji? 😭5


Allah kasa mu dace 🙏😪Office dinsa ya shiga da ni, sai ya saki hannuna ya sauke Namra daga saman kafadarsa ya zaunar da ita a saman kujerarsa sannan ya rufe kofar office din ya sake rika hannuna ya zaunar da ni a dayar kujerar dake kusa da kofar, sai ya zauna shi ma yana ta kallona ya kasa cewa komai, ni ma shi nake kallo amman ba kallo na ainahin kyausa ko wani abun daya shafi jikinsa ko fuskarsa ba, kallonsa nake a zahiri amman a badini zuciyata tana can gurin tunanin yau da kuma GOBENA, har yanzu na kasa yarda ba mafarki na ke ba, har yanzu hawayen ba su daina sauko min ba, har yanzu ban daina jin sautin muryar Namra na maimaita kanta a kwakwalwata ba, ji nake kamar yanzu take ba ni labarin nan, rumtse ido nai na kulle gam ina jin kamar idan na bude zan ga komai be faru ba, ji na ke kamar ace idan na bude idon zan farka daga mummunan mafarkin da nai yi ne.1

“Halima”


Can cikin kaina na ji kiran Abdallah da sauri na bude idon ina kallonsa har nunfashina na rawa kamar wacce ta farka daga bachi, da gaske ji nake kamar ace mafarki ne ba gaske ba.

“Miya samu Namra?”


Ya tambaya fuskarsa na nuna tsantsar damuwa da ganin hawayen. Nuna masa Namra din nai na kasa cewa komai, bakina nai nauyi sosai kamar an saka min dutse a ciki, wata kila kalaman da zan furta a duniya sun kare ne, domin ina jin idan har bakina zai bude da sunan magana a yanzu to kuka ne kawai zai fito amman ba magana irin wacce ko wane lafiyayen mutum yake ba. Kai nake ta daga masa alamar ita din ce ita dince kamar wanda ya sake tambaya, shi kuma ya tattara hankalinsa ya maida akaina sai yawo yake da idonsa a fuskata.

“Bana son zubar hawayen nan na ki Halima, ki bude baki yi min magana maybe i can help”


Ya fada yana dauke kansa daga barin kallona ya dafe da hannunsa yana sauke numfashin da karfi, can kuma ya mike tsaye ya nufi gurin windows din ya tsaya yana kallon waje kamin ya buga hannunsa da karfi jikin ginin gurin.

“Matsalarki duk ba zata wuce ta shegen mijin nan na ki ba, can you pls talk”


Ya fada yana juyowa ya kalleni, yunkurin bude baki nai da zimmar magana da gaske sai na kasa maganar har kuma lokacin ban daina hawaye ba kamar an rubuto min ranar kawai domin kuka. Teburinsa ya nufa ya dauko takardarda biro ya aje min a gabana.

“Rubuta idan ba zaki iya min magana ba”


_So na ke a duba min Namra fyade akai mata_

Haka na rubuta a takardar na mika masa, yana karantawa ya zaro ido ya kalli Namra da sauri sannan ya kalle ni.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, garin ya?”


Nan ma kasa magana nai sai dai na bude bakina ba kamar dazun ba da dantse har da hakorana. Barin gurin da nake yai ya nufi gurin Namra.

“Namra wa yai miki haka? Fada min ya akai hakan ya faru?”


Tana kallonsa sai ta fashe da kuka daman tun da muka shigo take alamar kukan ganin nima kukan na ke yi. Sauko tai daga kan kujera ta rugo a guje inda nake zaune ta rumgume ni tana wani irin kuka mai taba zuba zuciya, ni ma fashewa nai da kukan mai sauti na rumgume yata kankan a jikina ita kuka ni kuma, sai a lokacin na fara tambayar kaina ina tunanin abunda nai wa Sadi da zai yi ma yata haka? A kullum burina da mafarkina na tsare mutuncin kaina da na mijina da na yayana, amman yau wani a cikin familyn mijina ya keta yadda yata, ya rusa min komai.


“Miyasa zai min haka? Mi masa a duniyar nan? Me zai ji a jikin karamar yarinya kamar Namra? Kuma yar dan'uwansa? Mi yasa zai saka mu a wannan halin ni da ita?”


Magana na ke ina kallon Abdallah kamar shi zai ba ni amsar duka tambayoyina. Mikewa nai tsaye rumgume da Namra na fara zagaye dakin.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”


STORY CONTINUES BELOW

Haka nai ta maimaita ina jin zuciyata kamar zata rabe gida biyu, numfashina kuma yana ta kokuwa da jikina, sai na yi da gaske yake fita ya shiga. Abdallah ne ya miko hannu ya karbe ta.

“Zan kula da ita zan yi mata duk abunda ya dace ke ki zauna a nan”


Daga haka ya juya ya fice, ni kuma na nufi kujerar da sauri na zauna saboda kafafuwana da na ke jin kamar ba za su dauke ni ba, ga wani sanyi da nake jin na taso min har hakorana na son haduwa da juna. Babu wanda ya fado min a rai yanzu sai Abban Namra shi ya kamata ace yana tsaye a tare da ni muna wannan jimamin a tare ya kamata ace ya san halin da yarsa take ciki, da sauri na bude jakata na fiddo wayata na kira numbersa haka tai ringing har ta katse be daga ba, na sake gwadawa nan ma be daga ba, sai da na jira masa miss calls har hudu a na biyar ya daga a fusace.

“Wai ya akai? Ina aiki kina ta damuna da kira”


Kasa ce masa komai nai sai sauke numfashi nake, har ya gaji ya kashe wayar, wani irin abu marar misaltuwa na ji ya ratsa zuciyata ya tsaya min a makoshi, mutumen da ya fita be tambaya lafiyar yarsa ba bayan ya sa bata da lafiya yanzu kuma na kira shi yace min aiki yake ina damunsa, wane irin aiki ne wanda ya fi iyalinsa muhimmanci, wane aiki ma mutumen da yace min tafiya zai yi? A yanzu shi na ya kamata ace yana tsaye a bayana yana jimamin wannan lamarin tare da ni, shi ne ya kamata ace ya tsare min komai da ban nemi yin aiki ba da yanzu ina tare da yayana ba sai na kai su gidan wani ba, wata kila da be yi da yar wani ba da yanzu ba ayi da tasa ba. Jikina ne ya fara rawa har wayar da ke hannuna ta fadi ina ta jin wani abu na juya min a ciki kai kamar kwaro, ban san lokacin da Abdallah ya shigo ba sai muryarsa na ji.

“Halima karki jawa kan ki depression”


Kallonsa nai.

“Kwanta”


Ya fada sai na kwanta kamar daman can umarninsa nake jira. Sai ya cire rigar likitoci dake jikinsa ya rufa min.

“Abunda na ke jiye miki kenan, shiyasa tun kamin ki haifi yaran nan nai ta nuna miki cewar ki rabu da mijinki, ki kashe aurenki amman kika ji, daman namijin da be iya komai ba sai neman mata ai dole shi ma a dana yarsa, yanzu ai sai yaji idan da dadi, wani abun bakinciki ma wai kanensa ne zai masa haka? Hakan na nufin familynsu gaba daya lalatacci ne kenan! Wai ya ma san abunda ya faru kuwa? Ko kuma yana can gurin bakin neme nemen matansa?”


Haka yai ta magangunsa cikin bacin rai har yai ya gama ya fita bance masa uffan ba, daman can ba son aurena da Aminu yake ba, babu ranar da zan hadu da shi ba zai labarta min cewar ya ga Aminu tare da wata ba, kullum cikin bibiyar rayuwar Aminu yake saboda kawai ya ga aibunsa ya fada min, hakan yasa nai blocking dinsa a fb whatsapp da ma kiransa, shi kadai ne mutummen da bana jituwa da shi a cikin familynmu saboda sukar Aminu da yake min, a duk lokacin da ya fadi min cewar Aminu yana neman mata nakan karyata kuma na hana zuciyata aminta da hakan saboda kar na sakawa kaina rudani kar na saka shakku a zaman aurena da mijina. Na sha jin Aminu yana waya da mata ko na ga chat dinsu amman ina kokarin ganin ban zarge shi ba sai na dora abun akan ruwan dare da zamanin nan da wasu mazan aure suke na chat da mata a waje, duk kuwa da irin dadewar da yake a waje, sai dai kamashi da condom da jin zai yi tafiya wani garin da mace yafi komai karya min guiwa, ga kuma fyaden da akai wa Namra a yanzu, na san akwai kaddara wacce ki giftawa bawa, amman ina jin a jikina wata kila da Aminu be yi ba da ayi ma yarsa ba, domin ni dai na san ko zinar ido ban taba aikatawa ba, amman yau an yi ma yata.

Tashi nai zaune na share hawayen idona, ina jin ba Baba Sadi ba, ko Aminu ne ya keta ma Namra haddi a yau ba zan kyale shi ba, rigar Abdallah da ke jikina na aje na mike tsaye na dauki jakata da wayata da ke kasa na nufi kofa kamin na kai hannu na bude sai Abdallah ya turo kofa ya shigo tsayawa yai kallona.

“Ina zaki je?”


“Gida, ina Namra?”


“Zaki iya tafiya, idan na gama zan kawo ta”


STORY CONTINUES BELOW

Tsayawa nai a gurin kamar an dasa ni, sai na ji kamar ba zan iya tafiya na bar shi da yata ba.

“You can trust me, tana gurin blood test ma yanzu”


“Thank you”


Na fada sannan na ratsa ta gefensa zan wuce.

“Ke kanki rayuwarki tana cikin hadari Halima, abunda zai fi miki kwanciyar hankali is ki raba kanki da wannan mutum, gashi yanzu dan'uwansa ya maida miki Namra babbar mace!”


Wani banza kallo na watsa masa.

“Kana tunanin akwai hikima abunda kake fada min a yanzu? Kana ji a ranka ya dace kai min wannan maganar a yanzu? Na kashe aurena na fito na bar yarana a can? Shine kwanciyar hankali da kake fada min? Ko kuma na zuba masa magani ya mutu shine zai nisanta ni da shi? Kullum burinka ka fada min wata bakar magana akan Aminu, kana tunanin dadi na ke ji? Ko kuma kana tunanin hakan zai saka na so ka ne? Hakan be kara min komai ba sai tsanarka Abdallah, ba yau na nake yiwa tanadi ba GOBENA, duk abunda nake ina yi ne saboda yayana da kuma GOBENA....”


Cikin fushi na fada mishi hakan sannan na fice ba tare da sake ce min komai ba. Tun daga yanayin tafiyata za ka gane cewa ina cikin fusata, wannan karon ba kuka ne a zuciyata ba, kuzari ne irin na neman hakki ga wanda aka dannewa shi, ina jin a raina zan iya kwatarwa yata hakkinta, ko da hakan zai zama silar mutuwar aurena. Mai napep na tara na shiga be tsaya da ni ko ina ba sai kofar gida, dari biyu na ciro na bashi ban ko tsaya karbar canji ba na shiga cikin gidan.

  Yan matan gidan mu basa nan kasancewar ranar akwai scul masu zuwa aiki sun tafi masu makaranta ma sun tafi kuma a isa dawowo ba, Mama ta kawai na tarar tsakar gidan Inna na can dakinta tana bachi, tana ganin yanayi na ta san ba lafiya ba.

“Halimatu?”


Kusa da ita na zauna,sai na ji wani irin natsuwa da kauna ya shiga zuciyata irin na uwa da ƴa, ban shiga da kuka ba, kuma ban shiga dan nai musu kuka ba amman ganin mahaifiyata sai naji kamar ni ma din karamar yarinya ce a jikin uwarta a take na fara hawaye.

“Lafiya? Lafiya? Miya same ki Halimatu”


Wannan tambayar ce ta fito da Inna daga dakinta tana hamma.

“Lafiya dai?”


Wani irin abu na ji taya zan fada cewar kanen mahaifinta ya lalata? Sai da na ji na samu natsuwar ruhi da ta zuciya sannan na labarta musu komai.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”


Shine abunda dukansu suka fada, Inna ta dafe kai, Mama kuma ta daka kirjinta ido a waje tana ta maimaita Hasbiyallahu.

“Wallahi Mama ba zan kyale wannan maganar ba, sai na kai shi kotu sai an kwatar mata hakkinta”


Na fada cikin kuka, sai Mama ta nuna ni da yatsa.

“Kul....! Karki so ma, ki kai kotu? Ki tonawa kanki asiri? So kike a yada ki a redio da tv ke da yarki a buga ku a jaridu? So kike idan yarki tai wayo ta koma ganin laifinki? So kike yarki ta rasa mijin aure? Halima karki yi wannan kuskuren Halima, karki alata rayuwar yarki da taki rayuwar”


Inna ta karba mata.

“Lallai kam duk yadda za a kwato mata hakkinta, zai zubar da mutuncinta ne kawai, wanda be san ayi ma ba yanzu ya sani, suma waenda ake yi ma wa kika taba jin an yankewa wani dogon hukunci? Balle wannan da zai iya tsayawa ya kwaci hakkinsa ya barki nan ke da yarki a cikin mummunar rayuwa, kuma ki jawa kanki da yayanki tsana a gurin dangin mahaifinsu, sannan ki kashe aurenki domin akan wannan abun kin san Aminu zai iya rabuwa da ke daman igiya daya ta rage”


Mama ta gyada kai

“Ko ma be sake ta ba, ai Mahaifiyarsa zata iya saka ya saketa tunda daman can ba sonta take ba”


STORY CONTINUES BELOW

Hawaye ne suke min zuba irin zubar da bazan iya misaltawa ba, gaba daya kaina na kulle duk wani kuzari na kwatarwa yata hakkinta da nake da shi sai na neme shi na rasa, lankwafar da kai nai ina kallon Mama da abokiyar zamanta Inna hawaye na min zuba na ce


“Mutuwar aurena kuke ji ba abunda akai wa yata ba?”


Inna ce ta dawo gefena ta zauna ta juyo da ni.

“Halimatu, duk wanda zai ce miki be ji zafin abunda akai wa Namra ba to makiyinki ne, sannan kuma duk wanda zai baki shawarar zama a gidan mijinki ki rike yayanki hakika masoyinki ne, Halimatu kanenki mata nawa ne a gidan nan suma neman rabuwa muke da su kai kuma sai ki ce zaki kashe aurenki ki dawo? Kuma kisan auren ma ya zama akan fyaden da akai wa yarki? Ki tonawa kanki asiri? Irin wannan maganar sasantawa ake sai a dauki matakin dan gaba, sirrinki ne wannan ki rike abunki ko yan'uwanki karki ba ri su ji, ki haka rame ki saka shi ciki ki rufe, ko a familyn mijinki karki ba ri kowa ya ji, ki yi hakuri karki ce za ki kai wannan maganar a waje, shi ma Abdallah da yaji ki yi magana da shi ki roke shi ki ce kar ya fadawa kowa kinji?”1


Na gyada mata kai ina share hawayena.

“Na ji”


“Na ji”


Na sake maimaitawa ina gyada mata kai ido kuma suna ta yawo a tsakar gidan.

“Na gane”


Na fada ina cizon lisp dina, ni kadai na san abunda nake ji, ni kadai nake jin abunda yake min yawo a zuciya.

“Aminu ya san da maganar?”


“A a be sani ba”


Na amsawa Inna kamar ba ni ba.

“To a tsakaninku za ki yi wannan maganar karki nuna masa ma mun ji, kuma karki nuna masa kin kaita asibiti”


“To”


Na fada ina mikewa tsaye.

“Ina za ki je?”


Inna tace.

“Ai da kin zauna har a jima tunda yace zai kawo miki ita”


“Aa kara dai na je gida”


Na fada ina tafiya. Mama ta mike tsaye ta biyo bayana tana fadin


“Ki rike Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, kinji? Dan Allah karki fitarta da maganar nan Halimatu”


“To Mama”


Na amsa mata ba tare da na jiyo ba, tafiya na fara yi a unguwarmu hawaye na sauko min ina saurin saka hannu na share, har na isa titi na tari napep mai mutum biyu na shiga nice ta uku, mai napep na tafiya ina hawaye har muka hau babban titi, ni aka fara saukewa sai na fito na saka hannu a jaka na dauko kudin mai Napep na mika masa sannan na tura kofar gidana zan shiga sai na jita a kunne, da alama mai gadin ya rufe daga can ciki har sai da na buga sannan ya bude min na shiga yana min sannu da zuwa. Yadda na bar gidan haka na same shi daman da zan fita ban rufe ba domin na fita hankalina baya jikina. Lokacin da n shigo falon sai na zauna a saman kujera kamar wata bakuwa na saka hannuna na dama cikin na hagu na fashe da wani irin kuka, zuciyata na ayyana min na sha wani abun na mutu kawai na huta.

  Hakika na ci kuma kuma kuka ya ci ni domin ya san da zamana a duniya a wannan yau, ina zaune a gurin ina aikin kuka har aka kira sallah azahar idona ya kumbura sosai har bana iya gani da shi sosai, tun ina kukan a zaune saman cushion har ta kai na fado kasa har na kwanta a gurin na mulmula na buga hannayena a kasa. Sai da na ji tsayawar mota sannan na tashi da sauri na leka ta window bata bakar motace da ban wayeta ba, sai dai hango mai kama da Abdallah ya fito cikin motar da shadda nai ruwan kwai yasa ni koma na dauki hijabina an saka na bude kofar falon na fita, ko da na fito ya doso kofar rumgume da Namra a kafadarsa.

A bakin kofa na tsaya shi kuma ya karaso kusa da ni, tun daga yanayin tafiyar da kallon na fahimci ba Abdallah ne ba, domin mutun daya yake min irin wanna kallon wato Abdulhamid domin shi komai nashi a natse yake, saboda kara tantancewa na ce.

“Abdallah....”


“Abdulhamid”


Da sunansa da ya fada yasa na kara tantance shi din ne ta hanyar kallon da nai wa bakinsa a lokacin da yake furta sunansa, domin shi haurensa na gaba ya dan kaure kadan.

“Ya fada maka?”


Ya gyada min kai.

“Naje yin wani abun ne sai yace na biyo da ita zai shiga theater”


Ya mika hannu na karbeta ina hade yawu.

“Ki yi hakuri Halimatu, ko wane bawa da irin kaddararsa, kuma ko wane gidan aure da kalar nasa kalubale, duk wanda ya fada miki aurena da dadi 100% karya yake, akwai kalubale a cikin aure da rayuwa kala kala, dan haka ki yi hakuri, an rubuto haka zai samu Namra so no matter what you did ba zaki iya tare jaddararta ba, rayuwa ko da yaushe tana cike da kalubale  so dukan abunda za ki yi karki yi shi dan yau ki yi dan Goben ki, ina rokon Allah ya zama a tare da ke kuma ya baki juriyar daukar wannan kaddarar”


“Amin na gode”


Na juya ina hawaye kamar ba wacce aka tsamo daga kogin kuka na shigo ciki jikina na bani kallona yake har na shigo. A saman kujera na aje ta tana ta bachinta da alama allurar bachi yai mata domin ko motsi bata yi. Wani sabon kuka ne ya zo min tausayinta da nawa ya rufe ni.


“Al-hamdulillah Allah duk abunda kai dai-daine, idan ka ga dama sai ka akashe mu mu duka kuma daidai ne, da baka so ba, da komai be faru ba, kai ka kaddara min auren Aminu, kuma kai ka kaddarar abunda zai faru a yau, komai a cikin ikonsa da yardar ka ne Allah, ya ka zama gatana ka zama tare da ni Allah ya min mafita ka isar ka isar ma yata, Allah ka zaba min tsakanin kwato hakkin yata da igiyar aurena ya Rahamanin Rahim....”


Na karasa cikin wani irin kuka da ban san da zamansa a cikina na sai yau....

________________


Wane Halimatu zata zaba? Aurenta da Aminu wanda shine rufin asirinta da na yarta kamar yadda Mahaifiyarta ta fada?

Ko kuwa kwato hakkin yarta wacce aka lalatawa rayuwa aka maida babban mace?


#Abdallah

#Abdulhamid

#Aminu

#Halimatu

#ZawarcinHalimatu

#Gobena

#Freepage

#TwinbrothersHawayena na share na tashi na shiga dakina nai alwala na soma gabatar da sallah azahar, ina Sallah shiedan na ta kawo min wasu abubuwan da be kamata nai tunaninsu a lokacin da nake a gaban Ubangijina ba, sai dai na yi nasarar fadawa Allah bukatata kuma na kai masa kuka. A lokacin da na sallame sai addu'a ta subuce bakina saboda tunanin da ya taru yai min yawa. Ida har na hakura na bar rayuwar Namra ta tafi a haka ni tawa rayuwar zata inganta kuwa? Taya zata inganta bayan yata zata kasance cikin kunci? Kyale Baba Sadi zai canja mishi hali ne daga abun yake? No sai dai ya kara masa kwarin guiwar yin hakan saboda an kyaleshi, hakan kuma ba zai saka Aminu sauya halinsa ba, miye ma amfanin zama da mutumen da ke mu'alama da wasu matan a waje, wanda har ya zama silar lalacewar ta wa yar? Shin yin shiru zai amfanin wani abu ne? Jin bugun kofar falo ne ya dawo a ni daga duniyar tunanin da na tafi. Tashi nai sanye da hijab da nai sallah na nufi kofar falon, ina budewa na ga Abdallah tsaye rike da hannun Adnan dayan hannunsa kuma rike da leda fara irin babbar nan ta pharmacy, Aiman kuma na gefensa, sam na manta da zancen dauko su daga makaranta sai yanzu.+


“Be kamata ace har yanzu kina barin kanen mijinki yana zuwa dauko yaranki daga makaranta ba, domin idan be samu mace ba mazan zai iya lalata su tun da duniyar ta canja ba maza ba mata”


Shine abunda ya fada min kai tsaye, ni kuma na kwara bude kofar falon.


“Adnan ku shigo ciki”


Da sauri suka shiga falon ni kuma na fito na tsaya bakin kofar falon na janyo kofar na rufe.

“Kin yi kuka da yawa Halima ga fuskarki nan ya nuna, kina tunanin kuka zan canja komai ne? Kina tunanin kukam zai saka Kanen mijinki nadamar abunda yai? Ko kuma mijinki zai fasa neman matan da yake ne yana gallaza miki? Haka zaki saka ranki a kunci kina ta damuwa?”


Kasa nai da kaina ina jin wasu hawayen suna kokarin cika min ido.

“Na je gida na kai miki yaran na yi tsammani kina gida, sai suka ce kin zo kin tafi, tun da na ji haka na san cewar sun karya miki kuiwa ko? Su baki shawarar rufe sirrin saboda kar wani yaji, Kanen mijinki ya ci bulus kenan? Bayan ya ci amanar dan'uwansa, rayuwar aure ba rayuwar kunci ce ba Halima, saboda kina neman lahirarki ko kuma kina son kyautata rayuwarki be kamata kullum ki yi zama da kunci kina tauye kanki ba, musulunci ma be yarda da irin wannan auren ba, yaushe rabon da ko kusantarki mijinki yai?”


Hawaye ya fara sauko min, tabbas Abdallah yana da gaskiya akan dauki wata daya biyu wani lokacin har uku kamin Aminu ya zo min da bukatarsa.


“Ba sai kin fada min ba na sani, namiji mai neman matar sosai kamar yadda Aminu yake baya iya kula matar gida, duk abunda zaki yi ba zaki burgeshi ba saboda idonsa sun bude akan wasu matan na waje kuma ya yarda sun fi ki komai, so baki da wata daraja da kima a idonsa, yana yawan fadar baya son mace mai irin siffarki halittarki bata burge shi, kuma kin tara masa yayana yana da kananan shekarunsa a lokacin da yake bukatar hutu ke kuma kika son hana shi jindadin rayuwa, shiyasa yake gallaza miki”


Dagowa nai na kalleshia fusace na ce


“Kana ta fadin karya da gaskiya akan mijinki, tsayawa a ina saurarenka ba shi yake nufin na yarda da kai ba, baka san komai akan mijina ba babu ruwanka da rayuwarsa”


“Kwarai na san komai akansa, da yawa daga abokansa ina hulda da su kuma kin sani mazinata basa da sirri, har jinjirin cikin da kike dauke da shi na sani Halima, babu wanda be san irin zaman da Aminu yake da ke ba a cikin abokansa, saboda mijinki ba shi da sirri, ban san taya akai ma kika auri Aminu ba Halima sam ba mijin daya dace ki aura ba ne”


“Baka isa ka shigo har cikin gidana ka ce zaka fada min wata maganar banza akan mijina ba, ka fice”


Cikin wani irin tsawa na nuna masa gate raina na bace, daman ya saba a duk lokacin da muka hadu da shi sai ya fada min wata maganar marar dadi akan Aminu. Murmushi yai ya tabe baki ya miko min ledar hannunsa.

STORY CONTINUES BELOW

“Maganin Namra ne, karki sake mata abunda zai tsoratata saboda kwakwalwarta a tsorace take a yanzu ya riga ya gama tsoratata so tsoron yana tare da ita har sai ta samu sakewa na wani lokacin kamin ta koma Normal, ki rika gasa mata da ruwan zafi. And idan kin ga dama ki dauketa ki kai ta riko gidan Kenan mijinki sai na yarda kin fi ganin kimar mijinki fiye da yarki, duk abunda kike idan saboda goben ki kike to goben ta fara lalacewa a yanzu tun da har zaki iya barin hakkin yarki akan aurenki......!”


Yana fada min haka ya juya a fusace ya sauka daga dan gudun stairs din dake gurin ya nufi motarsa ya shiga yai ribas da karfi alamun da ke nuna ransa ya bace sosai kenan. Bude kofar falon nai na shigo ya maida kofar na rufe na jingina jikin kofar ina fashewa da kuka mai karfi. Na rasa abunda zan yi maganar mahaifiyata zan bi ko kuwa abunda nake ganin yafi?

“Momy mi kike kuka?”


Adnan ya tambaya daga shi har Aiman kallona suke.

“Ba kuka na ke ba”


“Gashi nan hawaye yana miki zuba”


“Kaina ke ciwo”


Na fada ina kirkiro murmushi tare da share hawayen. Hannu na mika musu sai duka suka zo na zaunar da su kusa da ni na shafa kansu sannan na daga kaina na kalli Namra da ke bachi saman cushion. Yayana na daya daga cikin babban kyautar da Allah kan yi ma bawa, wasu nema suke yi saboda Allah be basu ba, da ana siya da kudi da sun siya ko nawa ne, wasu kuma Allah ya basu mazan be basu matan ba, suna ta son mata ba su samu ba, wasu kuma matan Allah ya basu be basu maza ba, amman ni Allah ya hada min duka biyu ya bani maza biyu mata biyu a cikin shekara 11, sai dai ya bani su a inda ni kadai nake masa godiya da kyautar da ya ba ni, ni kadai na ke kallonsu na jidadi, mahaifinsu kan ganin yake na tara masa tsufa, har yana guduna saboda su saboda haihuwarsu ta canja min halitta na tashi daga buduwar zuwa mace mai yaya hudu da ciki na biyar, cikin da yake cewar na zubar baya bukatarsa.

“Allah ya raya ku ya sakawa rayuwarka albarka ya tsare min ku”


Na fada ina kara shafa kansu, sannan na mike tsaye na nufi kitchen na kunna gas na hada musu tea na gama musu da sauran biredin safe da yai saura na mika musu, ni kuma na shiga dora girkin rana duk kuwa da ina jin cewar ba zan iya ci ba amman dole na dora saboda yarana. Komai saboda su ne, zaman da nake da Aminu saboda su ne, idan na fita na barsu ban san wace irin rayuwa za su shiga ba, ban san wace macen ce zata raine su ba, fatar shiriyar da nake masa ko bana aurensa ina masa ita saboda na riga na haihu da shi. Ina cikin wanki shimkafa na ji yara suna murna.

“Oyoyo Anty Hafiza”


Kanwata ce wacce muke uba daya da ita, sai dai Allah ya hada jininmu kamar yan daki daya, bata boye min komai ni ma bana boye mata damuwata.

“Yar aljanna... Da aka fada miki kuma sai kika ji kika dawo gida har kina girki, Allah mai ikon, da ya tashi sai yai mu uba daya amman hali kowa da na shi”


Juyowa nai na kalleta da idona da suke kumbure, sai na ga hawaye na mata zuba mayafinta ma a hannu yake tare da jakarta.

“Da ace ko wace mace zatai irin zaman auren da kike da mijinki, da maza sun huta da korafin matansu, kuma da ko wane yaro mai uwa da uba a raye be girma ya ga uwayensa a rabe ba, kina da hakuri Halima fiye da kima, sai dai hakurin idan yai yawa yana cutarwa, abun ya wuce kanki a yanzu rayuwar yaranki ake neman lalatawa, be kamata ki yi hakuri a nan gurin ba”


Sai da na hade yawun bakina sannan na ce.

“Inna ta fada miki abunda ya faru?”


Sai ta matso kusa da ni tana kallon irin kallon nan na tsantsar tausayi.

“Mama ce ta fada min, na rasa gane dalilin shirun da za ki yi, ban san mi yake damun iyayenmu ba, dukansu tsoron mutuwar aurenki suke ji, mu kuma da muke gida suna matsa mana akan lallai sai mun yi auren, suna matsa mana akan auren ko wane irin miji saboda mu bar gabansu mu kaucewa maganar mutane, ku kuma da kuke da aure suna son ku yi da zama auren ko da babu dadi saboda gudun magana, sun kasa gane aure rai ne da shi, idan lokacin mutuwarsa yai dole sai ya mutu, idan kuma lokacin yinsa yai sai anyi ammn sai su dauki damuwar duniya su sakawa kansu, yanzu so suke ki zauna da mutumen da be san darajarki ba kuma ki kyale kanensa ya ci bulus kenan? Idan ma bakinciki kashe ki zai yi sai dai ya kashe ki? No ban zan goyi bayan wannan abun ba, ba za ki kyale mutumen nan ba, ba ki fada min ba amman nasan Aminu yace miki yayi tafiya zuwa Kaduna to Wallahi ya tafi   tare da kawarki Sa'adatu, Sa'adatu kin san ai kanwar Basira kawata ce ita Basira kawar Sa'adatu ce ita ta fada mata ita kuma Rahila ta fada min, yanzu irin wannan mijin har abun so ne? Irin wannan mijin ABOKIN RAYUWA ne?”


STORY CONTINUES BELOW

Tsame hannu na yi daga cikin shimkafar da na ke wankewa na sake kallonta na ce.

“Rayuwar da Aminu yake a yanzu bata dame ni ba, shawara nake da zuciyata na rasa abun dauka, maganar su Mama ko kuma kyato hakkin yata, ta wani bangaren gaskiya suke fada, idan na fita rayuwar yayana zata zama abar tausayi, idan kuma na cigaba da zama zan cutarta da kaina, dalili na farko da ya saka Aminu ya fara sakina saboda na yi fada da kanwarsa, na biyun kuma saboda aikina ne yace kar nai na ce sai na yi saboda be dauke min duka hakokina ba, akan hakan ya sake ni daga baya yace ya yarda na dawo na yi aikin, yanzu kuma saki daya ya rage idan ya sake ni babu zancen komawa saboda shika uku ne babu gyara, kuma bana jin zan tana iya auren wani mutun na fito saboda yayana na tsabawa mahallincina, idan har Aminu yai kuskuren rabuwa da ni a yanzu mun rabu kenan har abada ko da kuwa zan rasa duka yayana ne, amman a yanzu da nake cikin igiyar aurena ina kokarin zaba tsakanin auren, rayuwar yayana da kuma Gobena, duk idan auren da zanje duk more jindadi da soyayyar wani mutum da zan yi a gidan wani auren zuciyata tana gurin yayana, idan na bar gidan nan kamin Aminu ya auri wata matar gidan iyayensa zai sai su kuma idan har ya zama saboda fyaden da akai ma Namra na fita tabbas ba za su taba son yayana ba, idan kuma yai aure wace uwar zai auro musu?”


“Amman kina da tabbacin wata rana Aminu zai iya sakinki ko baki masa komai ba? Saboda ya gaji da zama da ke? A lokacin ne sakin zai fi miki zafi fiye da yanzu, zancen ki zabi aurenki akan abunda akai wa namra be ko taso ba, Halima ya kamata ki sani ba Aminu ne kadai mikin aure ba, kuma akwa yara da yawa da suke tashi ba uwa ba uba balle ke da har kina da rai, kar maganar Mama da Inna ta karya miki guiwa”


Kallona ta nake maganganunta na shiga jikina ta ko wace shiga, sai dai har yanzu idan na tuna maganar Mama sai na ji kamar ba zan iya komai ba. Ita ce ta karasa min girkin ni kuma na cigaba da gyaran gidan kaina a kulle, misalin biyar da yan mituna ta tafi gida ni kuma na dauki wayata na kira Hajara. Bugu daya ta dauka sai hayaniyar mutane nake ji sauti na tashi.


“Halima muna gurin biki, ga yarki Amal ta dame ni da kuka wai ita Momy Momy”


Na yi dariya kadan ba dan ina jin dariyar ba.


“To ai ya kamata dai ta dawi gida haka nan tun safe ba bata gan ni ba”


“Da na gama bikin za mu dawo ai In-Sha-Allah ya jikin Namra? Abban su Baby yace kin ce masa bata jindadi na so na shigo kuma dai sai na wuce sai idan na dawo dan nasan kina gurin aiki”


“Eh to sai kun dawo a kula min da yata”


Daga haka na kashe wayar, kamin na aje ta kiran Kabeer ya shigo wayata har na yi kamar ba zan daga ba sai kuma na daga a tunani wata maganar ce.

“Allah yasa ba abunda ya faru tsakaninmu ne ya saka kika ki zuwa aiki ba”


“Bana jindadi ne”


“Subhanallahi kin sha magani?”


“Allah ya sauwake ya baki lafiya, oga Dahiru ma ya tambaye ki dazun sai na ce masa kin ce za ki je ganin wata yau ba za ki samu shigowa ba, ita fatar ban yi laifi ba”


“Ba kai ba na gode”


Kamin ya sake cewa wani abu na kashe wayar, na bar jikin dinning din ina ta tunanin yadda zan fadawa Aminu abunda ya faru, na kyale shi har zuwa lokacin da Mama tace idan ya dawo, anya zan iya haka? Ba zan bar Sadi ya sake daukar min yara daga makaranta ya kai su gidansa, ba ma shi kadai ba ko mijin Hajara ba zan sake yarda ya kai yarana makaranta na ni zan kai su ni zan dauko su, Amal ma ba zata sake zuwa gidan ita kadai ba sai idan tare da ni ne, ba zan sake yarda da kowa akan yarana ba ko da kuwa mahaifinsu ne.

  Dole na fara fada masa a matsayinsa na ubansu kamin na dauki wani matakin, ko kuma yin gargadin kar Sadi ya sake dauko min yara daga makaranta, aikin nawa ma ina jin ajewa zan yi na tsaya na kula da yarana. Komawa nai dinning din na zauna na danna Number Abban Namra na aika masa kira, na yi sa'a bugu daya ya daga da far'arsa, ko da ma be daga ba na yanke shawarar aika masa sako.


“Hello ya kai?”


“Komai an yi Aminu, hankalinka kwance kana can tare da wasu matan ka tsare musu hakokinsu mu ka kasa tsare mana namu, mu da Allah ya dora maka, mu da idan ka mana zaka samu lada, tirrr da wannan kazamar rayuwar da kake zina har da matan aure? Duk karuwan garin nan ba su isheka sai ka nemi mai aure! Abunda kake aikatawa yau kaja an aikatawa yarta, ka yi da yar wani an yi da taka ka lalata rayuwar yar wani na lalata taka, ban tana zina ba kullum burina na kare mutuncin kaina da na yayana da na aurena da na iyayena da naka amman kai kullum burinka ka zubar mana da kima, yau saboda abunda ka ke Aminu wani ya yi ma yarka fyade”


Tun da na fara jera masa zancen be ce uffan ba har na kai aya.

“What! Me kike fada? Wa akai wa fyade, uban wa ya taba min ya? Kin je gurin bakin aikinki kin barta hannun wani an lalata ko? Waya sani ma ko can gun aikin kika tafi da ita kika sake ta? Saboda ba ki san zafin haihuwa ba sai son haihuwar kike baki iya zama ki kula da su, to Wallahi idan kin san wani ya taba min ya kamin na dawo ma gidan nan ma ki tattara kayanki ki koma gidanku”


Duk fadan da yake a daukarsa Amal ce aka lalata ganin itace karamar su kuma ita ce marar wayo sosai.

“Wanda ya lalata Namra a jininka yake, wanda kuka fito daki daya da shu uwa daya uba daya, Sadi Aminu Sadi dan'uwanka kanenka shi yai ma Namra fyade...!”


Shiru yai na wasu yan dakiku kamin ya sake yin wata maganar kamar a rikice.

“Kin san abunda kike fadawa kuwa? Sadi fa kika ce? Taya Sadi zai wa Namra fyade? Kuma idan ma an mata uban waye yaja mata? Da kin zauna kin kula da su wani abun zai same su ne? Karya ma kike Sadi ba zai yi ma Namra haka ba akwai dai abunda kike nufi me Sadi zai ji a jikin karamar yarinya? Kuma yata? Wallahi ki yi hankali da igiyar aurenki Halima.... Mace kamar riga take a wuyana”


“Abunda kake ji a jikin wasu matan shi yake ji a jikin yarka, zaka gene ba ni da hankali idan kotu ta kwatar mata yancinta, tirrr da uba irin ka Aminu na yi nadamar aurenka a yau na tsare ka bana kaunarka Aminu, kuma idan ka haihu ga Zainab da Ibrahim ka sake ki a cikin wayar nan Aminu, abunda akai ma yarka be dame ka ba sai wasu maganganun banza! Tirrrr na yi nadamar haihuwar da nai da kai a yau, na gaji da auren yau ka baro garin Kaduna ka zo gusau ka sake saki dari ba daya ba....!”1


Na karasa fadar hakan ina buga hannuna da karfi a dinning table din, yarana gaba daya kallona suke har Namra da ke bachi sai da ta farka ta sakar min ido..Ina kallonta sai tausayinta da nawa ya rufe ni, ban san lokacin da na fashe da kuka ba na dafe kaina.


“Kai Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”


Na fada cikin kuka, sai Adnan ya nufo ni yana fadin.+

“Yi hakuri Momy sannu”


A zatonsa ciwon da nake masa ina na na dazun da ma fada masa ban sda lafiya ne yake damuna. A dole na share hawayena na kirkiro murmushi na mike tsaye na nufi inda Namra take.

“Kin tashi?”


“Ya jikin?”


“Bana jin ciwon komai”


Ta fada tana ta kallona da idonta da sukai ja saboda bachi, sai kuma ta kwanto da jikinta jikina.

“Bari na kawo miki wani abun ki ci kinji yar kirki”


Ta gyada min kai sai dai ina sauka mikewa tsaye daga kan kujerar sai ita ma ta sauko ta matsa kusa da ni kamar zata shige cikina.

“Zauna bari na kawo miki”


“A'a Uncle Abdallah yace ya daina bari kina yin nisa da ni duk inda kika je na biki ko da gurin aiki ne idan ba haka ba Baba Sadi zai iya zuwa ya yanke ni saboda na fada”


Kamin nai wata magana Adnan ya nufo inda mike da sauri yan zaro ido.

“Baba Sadi ne zai yanke ki? Mi kika fada”


“Ba komai, zo muje”


Hannunta naja ban bari ta sake cewa komai ba. Na nufi kitchen din da ita.


“A cikin gidan nan wani be isa ya zo ya taba ki ba, ke ba a nan ba ko a wani wajen ne wani be isa ya taba ki ba, ki kwantar da hankalinki kinji yar kirki”


Na fada mata ina kokarin zuba mata abincin, sai ta fara motsa ido.

“Mama ina jin tsoro”


“Ai Baba Sadi be san kin fadi wannan maganar ba, kuma ba fada masa zan yi ba dan haka ki kwantar da hankalinki kinji?”


Ta gyada min kai, a plate na zuba mata abincin sannan na janyo hannunta muka fito falo, zaunar ita nai ina kokarin bata abincin sai ta ce.

“Momy ban wanke baki ba”


“To je ki wanke”


Bata min musu ba ta tashi zuwa cikin dakinsu, daman can Namra ba yarinya ce mai kiriniya da jan magana ba, ko abu yake cinta yana da wahala ta iya fada ga ladabi da hankali kamar ita ce yayar Adnan, duk abunda na saka ta sai ta yi ba musu idan nace daina zata daina, ga jinkai duk abunda ta samu ita dai Momy dai Momy dai. Rashin ji da kiriniya sai Adnan shi da yake babba da Aiman dakr binta sai kuma wannan yar berar nan Amal ita kam fitinar ta tafi ta kowa ga barna komai ta dauka sai ta lalata.

  Wayata ce dake kan dinning tai kara, sai na aje plate din a kasa na tashi na nufi inda wayar take, number Abdallah ce har na yi kamar ba zan dauka ba idan sai kuma wata zuciya tace min na dauka wata kila wata maganar ce aka Namra.

“Assalamu Alaikum”


Na masa sallama da sanyayyiyar muryar da ke fassara irin damuwar dake tare da ni, domin bana da wani sauran kuzari a yanzu. Sai da yai shiru for few seconds sannan na amsa min.


“Wa'alaikissalam Halima ya jikin Namra na san ta farka yanzu ko?”


Na gyada kain kamar yana gabana, shi kuma kamar ya san abunda nai sai ya ce.

“Good ki yi hakuri na fada miki magana marar dadi dazun, rai na ne ya bace shiyasa, kuma dan Allah Halima karki saka damuwa a ranki, karki kamar ba zaki iya ba, kina da yan'uwan da zasu iya goya miki baya ki yi komai, karki bar Baba Sadi ya ci bulus”


STORY CONTINUES BELOW

“Zan aje wayar”


“Okay ki kula da kanki”


Sauke wayar nai ina ta tunanin ranar da Abdallah zai canja, wannan wa'azin ma yana min shi ne saboda ya san idan har na ce zan kwace hakkin yata dole aurena zai mutu, shi kuma abunda ya dade yana jira kenan tun kamin na haifi Namra, ya kwallafa min rai kullum burinsa da addu'arsa aurena dai ya mutu shiyasa yake yawan fada min maganganu marasa dadin ji akan Aminu, ko da yaushe yana fada min be kamata na zauna da shi ba.

Ni kuma ina daukar hakan da son zuciya da kuma son kai irin na bahaushen mutum, taya zaka kwallafawa ranka son matar aure matar wani? Saboda kawai kana da alaka da yan'uwantaka, wani lokacin har haukarsa nake gani domin mutun mai hankali da tunani ba zai yi abunda yake ba.

  Ina cikin wannan tunanin na ji an buga kofar falon.

“Shigo”


Na fada domin na san kofar a bude take ban saka mata key ba. Hajara ce ta turo kofar falon ta shigo tana dauke da Amal sai dariya take bakina har kunne, rayuwarta na burni ne ita kan ta yi dacen aure ba kamar ni ba, abu mai wahala ka ganta a cikin damuwa duk wani abun da take bukata a take mijinta yake mata shi sai idan ba shi da hali.

“Ga yarki nan ta ishe ni da kuka daga kawai na taimaka na je da ita biki, sai ka ce na sato ta”


Na mika hannu na karbe ta sai ta ki zuwa sai ita fushi take tana turo baki.


“Yi hakuri Amal kyale Mama Hajara mun bata da ita har da tufafin Afrah aka saka miki iyeee yarinyata ta yi gayu”


Daker ta zo gareni shi ma da kuka, sai na rungume ta ina dariya. Sai dariyar da nake bata hana kawata kuma aminiyata fahimtar ina cikin damuwa ba.

“Halima kamar akwai damuwa ko?”


Dagowa nai na kalleta kamin na ce wani abun Namra ta fito daga dakinsu ta nufo inda nake.


“Momy ina abinci Maman su Salma ina wuni”


Hajara ta amsa mata ni kuma na fada mata inda tuwon yake.

“Ina cikin damuwa Hajara, damuwar da ta fi ta ko da yaushe kuma damuwar da zata dauwama a zuciyata har abada, ko da kuwa yan hukunta Sadi, ban taba jin na tsani Aminu ba sa yanzu, ban taba dana sanin auren Aminu ba sai yanzu, ban taba jin natsani rayuwa ba sai yanzu, ban taba mafarkin ko jin ina son mutuwa a kusa da ni ba kamar yau, Wallahi Hajara ji nake kamar na sha wani abu na mutu na huta, ina ma Allah be hallice ni ba da duk wannan rayuwar ban ganta ba, ita ba bata gan ni ba, da Aminu be aureni ba”


Da hawaye na ke maganar hawayen da ban yi zaton akwai sauransu ba. Cike da tashin hankali take kallona.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Halima me ya same ki haka?”


Ban boye mata komai ba, tun daga zubin farko na fada mata komai ina kuka, ita ma fashewa tai ya kuka ta saka hannunta biyu ta dafe kanta.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Allah ka tsayar mana wannan abun a nan”


Sannan ta dago ta kalleni.


“Ban taba ji uba kamar Aminu ba, taya za ayi ma yarka fyade kuma ka tsaya karyatawa, ai ko ubanka aka ce yayi ma yarka fyade ba zaka karyata ba saboda duniyar yanzu ta lalace, ammn ke yake dorawa laifin? Da ya tsaya ya kula da iyalinsa yadda ya kamata kuma ya tsare mutuncin kansa hakan zai faru ne? Ban taba goyon bayan ki yi ma Aminu komai ba ban taba goyon bayan ki kashe aurenki ba, a kullum ina cikin addu'ar Allah ya karkato miki da mijinki gareki, amman yau kam ba zan goyi bayan ki bar wannan maganar ba, gobe zan je nai magana da Mama zan fahimtar da su abunda kika kasa fahimta, kuma zan tsayawa Namra sai inda karfina ya kare saki ne dai ko? Aminu ya sake ki Abban Afrah zai aureki In-Sha-Allah, ko kin yi lalacewar da kika rasa mijin aure ba zaki rasa nawa ba”


STORY CONTINUES BELOW

Kallon yar'uwa nake mata ba kawa ko aminiya ba, na san a yadda Hajara ta dauke ni da kuma yadda yake jina zata iya min komai, ko da bana raye balle yanzu da take ganin idona. Sai dai na san abunda ta fada ta fada ne kawai a yanzu saboda ranta a bace yanke, domin ba wata macen da zata yarda mijinta ya auro mata kawarta da amincewarta. Hannuna na kai ya rika hannunta.

“Na gode Hajara kin karfafa min guiwa sosai”


“Wannan abun yayi yawa Halima Aminu yai miki yan'uwansa su rika ganin laifinki kina ganin kin maye komai na dan'uwansu sun dauki kiyayya sun dora miki, yanzu kuma abun ya wuce kanki ya koma har akan yaranki? Ace Kanen mijinki ya kai yana lalata da yaranki? Miyasa be yi da nasa ba sai na ki? Ko naki ne kawai yayan dan'uwansa, kai wannan tashin hankali da me nai kama? Kina cikin jarabawar aure kuma wani ya karo fado miki? Allah ya miki mafita Halima”


“Ameen”


Mun dade muna ta fira da ita tana ta kwantar min da hankali sannan ta tashi na rak har gurin gate ta wuce gidanta ni kuma na dawo cikin. Ina shigowa na shiga kitchen na debowa su Adnan na su tuwon na kawo musu sannan na dauko maganin Namra da ruwa na soma bata. Ina jin lokacin da mota ta tsaya da karfi har na daga labulen windows na leka waje sai na hango Hajiya tare da yayata mata uku wato mahaifiyar Aminu ce da kenensa. Ban ji komai a raina ba domin a yanzu zuciyata a dake kuma na san zuwan nata baya rasa nasaba da fadan da mukai da Aminu a waya dazun wata kila ya fada mata ne. Ashe kuwa na canka a dai dai domin ta shigo falon babu ko sallama tana shigowa cikin falon ta hau fadin.

“Halima mi kika fadawa Aminu a waya?”


Juyowa nai na kalleta na saba sauka na risina har masa na gaisheta idan ta zo gidan ko ni aje ko muka hadu da juna, sai dai yau bana jin zan iya yin haka.

“Hajiya sannu da zuwa”


“Ba sannu da zuwanki na ke so ba, wata magana na ji nake son ki sake maimaita min da bakinki”


“Indai har Aminu ya fada miki, to ba bukatar na sake maimaita miki, iya kar abunda ya kamata ki gane shine ba zan yi ma Sadi kazafi ba haka nan kawai”


“Kazafi ne mana, ai kin dade kina son raba kan gidan nan, kin rasa abunda za ki yi shine kika fake da wannan waya sani ko can gurin aikin naki kika kai yarinya aka lalata sai kuma ki zo ki fake da Sadi, wai ko baki san cewar ni na haifi Sadi ba? Kuma ni din mahaifiyar Aminu ce uba daya ya haife su nono daya suka sha”


“Ko tagwaye ne su Hajiya be dame ni ba, yayanki kike tsaye a nan kina karewa ni kuma na san zafin haihuwa kuma na san zafin keta haddi saboda ni ma mace ce”


Zakiya ta matso kusa da ni tana min tsawa.

“Halima karki ce zaki ma Hajiya rashin kunya Wallahi na ci mutuncin ki”


Ni kuma na mike tsaye ina nuna ga da yatsa a fusace.

“Ke Zakiya iskanci ya tsaya a kanki, karki sake saka min baki a magana ke kanwar mijina ce ba yarsa ba, idan baki da tarbiya Wallahi zan gyara miki zama”


Ta nuna kanta

“Ni din? Ai kece marar tarbiya mai son hada yan'uwa bawan Allah yana can yana nema muku abunda za ku ci kina nan kina tada mishi hankali da yan'uwasa, ko da ya kira har kuka yake yace yana gurin aikin Kaduna amman kin daga masa hankali da maganar fyade”


“Karya dan uwanki yake miki, ba aiki  yaje yi ba hutu ya samu ya dauki karuwarsa suka je can gurin hutu, abunda yake ne yaja akai wa Namra kuma aka rasa wanda zai mata sai dan'uwansa”


Hajiya ta nuna ni da yatsanta.


“Ke marar kunya, fitsararki ta tsaya kanki karki ce zaki min iskanci, ni danaba mazina ce bane, daman can baki da aiki sai kawo kararsa kullum cikin kawo kararsa kike baki taba gode abunda yake miki ba, ke da kike aiki ba ace miki mazinaciya ba sai shi? Tirrr Wallahi mugun abun ki ya biki, kuma Wallahi ki hada kayanki ki bar gidanan ko ke kadai ce mace a duniya ya gama aurenki, ki koma can cikin agolayen gidanku,kuma Yaya sai an kaiwa Sadi shi zai rikasu sai dai ki mutu, wannan zumuncin baki isa ki raba shi ba”


STORY CONTINUES BELOW

“Zan bar gidan nan Hajiya, amman idan Aminu ya damka min takardar sakina, ba zanje gidanmu na zauna da igiyar auren danki a kaina ba, kuma Wallahi ko ina za'aje sai na je sai na kwatowa yata hakkinta, ban san yayanki haka suke ba Hajiya da ban auri Aminu ba da Sadi be ganni ya ci zarafin yata ba, hakuri na ya kare indai aurena da Aminu na kare ko da kuwa hakan na nufin karshen rayuwata ne, tirr da ɗa irin na ki dan da za a cewa an yi ma yarsa fyade ya karyata ba tare da bincikar komai ba, ke kuma ki sako kafa ki zo ci mun mutunci ko? Kin zo ki shigarwa yayanki to Namra ma ƴa ce idan Aminu be san darajar ta da kimarta ba ni na sani kuma ba zan bar wannan maganar ba, kotu zata kwatar mana hakkinmu”


Tun da na fara maganar babu wanda ya sake cewa uffan ba kanensa kadai ba har Hajiya tsaye tana kallona, ni kaina na san na yi mata abunda ban taba ba, ko kusanyar magana bana iyawa da ita balle kuma har nai sa'insa da ita. A yadda nakr jin kaina a yau ko marina tai zan iya ramawa, domin ina jin babu wata sauran alaka tsakanina da dangin Aminu yanzu. Har Laweeza ta bude baki zatai magana sai Hajiya ta hana ta ta hanyar daga mata hannu sannan ta saka su gaba suka fice daga falon.

Faduwa nai zaune a gurin ina wani irin fuci kamar zakayan.

“Momy ni ce naja fada ko?”


Namra ta tambaya tana kallona tare da fashewa da kuka. Kallonta kawai nai sai na kasa cewa komai na mike tsaye tare da maganin da nake bata na nufi dakina, ina shiga na fada saman gadon a ruf da ciki, wani irin soya nake jin zuciyata na min bana jin kuma ba kuma za a kawo zancen dariya ko farinciki a tare da ni a yanzu ba, gaba daya bana jindadin komai ciki kuwa har da rayuwata. Ina yi awa daya a gurin sannan na mike tsaye na nufi bandaki amai nai bayan na gama na wanke bakina na fito ina shafa cikin da ke jikina, abunda be isa shigowa duniya ba na ke tausayawa wani abu na hade mai nauyi sannan na fito na nufo falo. Wani abun mamaki sai an samu Namra tana ta kuka har da shisshika kamar ranta zai fita, haka ne na nuna alamar ta ci kuka ta kenan sosai har ta gaji. Adnan da Aiman kuma suna zaune a guri daya kusa da ita sun rakube kasa kamar wasu marayu, Amal ce kawai ke ta sha'aninta da wayata da ke hannunta.

“Adnan kuje ku kwanta kunsan gobe akwai scul”


“To Momy”


Suka tashi a tare suka nufi dakinsu a natse kamar ba su ba, yaran da sai na yi da gaske suke zuwa su kwanta ko kuma su yi bachi a duk inda ransu ya so sai na dauke su na kai dakinsu. Kusa da Namra na zauna ya dago ta idonta har yayi ja tsababen kuka.


“Yar Kirki mi akai miki?”


Bata ce min komai ba sai na kwantar da kanta jikina ina ta shafa kanta a hankali. Amal na gani ta rugo a guje tana kuka, daman haka take bata kaunar wani ya taba min jiki ko ya kwanta a jikina sai dai ita kadai. Dagata nai na ajeta a gefena na rumgume ta sannan na karbi wayata. Ganin sako a saman wayar yasa na shiga messages box sunan Abban Namra ne a saman kamar yadda nai saving number. Wani irin fargaba da tsoron bude sakon ne ya kamani a lokacin. Saurin sauke Namra da Amal dake jikina nai na mike tsaye na nufi gaban windows falon rike da wayar ba tare da na bude sakon ba. Na hade yawu ya fi a kirga numfashi na ma har gargada yake zuciyata na raya min saki na Aminu yai. Cikin karfin hali na kai hannu na bude sakon.

_Ni Aminu Idrees na saki mata ta Halimatu Ibrahim saki daya a yau 4 ga watan 3, ya zama saki uku kenan babu gwara a tsakaninmu_


Ina gama karantawa na ji kamar ba a duniyar nan nake ba, ba dan bana bukatar sakin ba, sai dan saki abu ne mai kirma wanda ko baka kaunar mutum idan aka sake ka dole ne sai ka ji wani abun marar dadi ya ratsaka.

_Karki kara minti daya a cikin gidana! Karki yarda na dawo gobe na same ki a cikin gidana, kuma karki daukar min yara_


Shine sako na biyu bayan na farkon, ban san ta inda hawaye suka taru a idona har suka zubo min ba, sai jika screen din wayata suke.

“Zaki iya wannan Halimatu, wasu uwa da uba suka rasa balle ke da igiyar aure ce kawai kike rasa kuma auren mutumen da be san darajarki ba, akan yaranki ne right? Zaki iya yin komai akan yaranki, wannan be isa ya karya miki guiwa ba, be kamata ma hawaye ya ziyarci idonki ba saboda kin rabu da mugun mutum right?”


Ni kadai nake magana da kaina kamar wata tabbabiya da sauri na share hawayena, na nufi Namra dake kallona.

“Tashi muje gida”


Na fada ina daukar Amal, dakin su Adnan na shiga har sun fara bachi na taso su na saka Hijab dina na dauki jakata domin bana jin iya tsayawa daukar komai a yanzu, waje muka fito gaba daya na rufe kofar falon sannan na saka yarana gaba muka fita gate din.

   Misalin tara da rabi muka isa unguwarmu wato family house dinmu, tun a waje na san Abdallah na cikin gidan sakamakon ganin motarsa da nai a waje, bayan an sallame mai Napep di na ji kamar ba zan iya shiga cikin gidan ba saboda Abdallah. Sai da na sauke ajiyar zuciya sannan na saka kafata a cikin gidan, babu kwalla ko kadan a tare da ni a lokacin da na shiga cikin gidan sai dai ina shiga falon nai arba da Mama da kanena biyu da kuma Abdallah sai na ji kuka ya zo min marar misaltuwa.

“Lafiya dai Halimatu”


Mama ta tambaya tana kallona da yara hankalinta a tashe.


“Mama Aminu ya sake ni.....”


Na fada ina fashewa da kuka, kanwata Salma dake kwance kan kujera ta yi saurin tashi zaune tana zaro ido, Mama kuma ta dafe kai ita da Ummi.

“Wow..... ”


Shine abunda Abdallah ya fada yana mika dukan kallonsa a gareni fuskarsa da murmushi kamar ya manta a inda yake.


________________


Saki mace mai ƴaƴa huɗu saboda son zuciya 💔😪

  Anya akwai imani a zuciyar Aminu kuwa?

A matsayinki na mace ya kike auna abun nan ya kike ji a ranki?😪

 

Abdallah me yake yi ma murmushi? 🙄

Idan tawayensa Abdulhamid yaji ya zai yi 🤔

Anya Aminu zai barwa Halimatu yaranta kuwa?.“Wannan kaddararen aure yau Allah ya kawo karshensa, ni ban ga abun kuka ba ma balle wata damuwa”


Shine abunda ya fito daga bakin Abdallah, Mama kam kasa cewa komai tai har lokacin tana dafe da kanta nima na kasa daina hawaye zuciyata tana min wani mugun zafi.

“Ummi rikata ki shiga da ita daki mana”


Cewar Abdallah yana kallona kamar ya taso da kansa din ya rikani. Salma ta taso ta zo ta rika daga tsayen da nake muka nufin dakin Mama tana rike da ni kamar yadda Abdallah ya bukata, muna shiga dakin na zauna bakin gado sai ta zauna kusa da ni tana kallona idonta taf da hawaye.

“Ki yi hakuri Anty Halima haka Allah ya so, ki dauka wannan ma yana rubuce a cikin abunda Allah ya rubuto zai same ki”


Na gyada mata kai ina ta kokarin taushe kukan da ke cina, Amal ce ta shigo ta zauna saman kafafuwana ya lafe kamar zatai kuka sai kace wacce ta san abunda ke faruwa. Salma kuma ta tashi ta fita ta barni a dakin daga ni sai Amal a nan na samu damar yin kukana iya yadda raina yake son, ina cikin kukan Mama ta shigo ta zauna bakin gado na yi zaton zata fara tambayar abunda ya faru ne ko kum ta tausaya min ko ta karfafa min kuiwa akan abunda ya faru, amman sai na ji wani abu dabam na fitowa daga bakin.


“Ai ga irin ta nan kin kashe aure tun ba a aje ko'ina ba kin fara kuka, ina amfanin wannan abun? Kin saka kanki da yayanki a cikin matsala bayan kuma kin san saki daya ya rage ba wani gyara a tsakaninku? Halima rayuwa zatai yi? Yanzu duk maganar da muka miki muka ce ki rufe abun nan sai da kika tona shi?”


Daga kaina nai na kalleta, ban san abunda take hango min ba na kokarin hanani yin komai akan abunda akaiwa Namra, na san tana gudun zaman gida a gurina kuma tana jin kwatankwacin zafin da nake ji na baro yayana a wani gidan, amman har yanzu na kasa gane dalilin na son boye maganar, indai na janyo ma yayana tsanena ina ganin kamar ba hujja ba ce.


“Ko wace Uwa Mama tana goyon bayan abunda yayanta suke aikatawa ko da kuwa abun nan marar kyau ne, na kasa ganin kuskure abunda nake son aikatawa, na san kina min tunanin mutuwar aurena ne, amman tabbas aurena mutu ko da ta wannan dalilin ba, duk yadda kike jin zafi idan wani abun ya same ni haka nake jin zafi idan ya samu Namra, saboda nima uwa ce, kin taba fada mana cewar saboda mu kika zauna da Abbah a cikin lalurar da yake ciki ta rashin lafiya, mama ya dan Allah ki fahimta nima saboda Namra ne, kuma ba dan bana son aurena ba sai dan ganin kamar mutuwar auren a yanzu zata fi sauki sama da idan yayana suka girma, Mama Aminu ya sake ni akan be yarda da abunda na fada ba, ba wai ma ya roki na boye sirrin ba ko kuma ya roki kar na kai kotu ba, mahaifiyarsa har ikirarin cewa tai sai an kaiwa Sadi Namra ya rikata sai dai na mutu, Mama ina kuke son na saka kaina na ji sanyi? Me kuka son nai a duniyar nan?”


Wannan karon hawayene yake zuba a idon Mahaifiyata, na sani kalamaina sun ratsata matuka kuma ta fahimci inda na dosa.

“Kwatarwa yarki hakki abu ne mai kyau Halimatu, amman kwatar hakki a inda kwatar yafi rashin kwatar alheri to barin shi ya fi, idan kika kai maganar nan kotu kin sani Sadi da yan'uwansa ba yarda za su yi ba, kuma za su yi komai dan su wanke shi ciki har da mijinki tunda kin ce be yarda da abun ba, daga haka maganar zata tashi sama kanki ankaro an fara buga ku a jaridu ana fira da ku, kamin a kwato miki hakkin ki sai kin sha wahala, idab kikai nasa a hukunta na shekara daya ko watanin kadan me akai kenan? Idan kuma ba ki yi sa'a ba sai a kori kararku  bayan na gama fadar kin batawa yarinya suna, irin wannan abun Halimatu rufewa ake saboda rayuwar yar ki a nan gaba wa zata aura? Wa zai aureta? Mi zata je ta tarar? Ina hango miki abunda zai zame miki matsala ne nan da wadansu shekaru masu zuwa wanda ke ba zaki gani ba a yanzu, zaki batawa yarki sunane kawai a cikin kawayenta yan'uwanta da kuma wandanda zata hadu da su nan gaba, ke da Hafiza da Doc Abdallah kun kasa fahimtar abunda nake nufi ne kawai wata kila sai nan gaba, shi ma abunda ya zo yana min magana akai kenan? Wa be kamata a kyale wannan maganar ba, ni kuma na fada masa indai da yawuna za aje kotu da wannan maganar a matsayina na mahaifiyarki ban yarda ba!”


STORY CONTINUES BELOW

Kamar wacce aka saka da mashi haka magana Mama ta ratsa kirjina ta shiga har cikin kaina, tsakanin maganar fyaden da sakin da Aminu yai min da kuma maganar Mama sai na rasa wane yafi yi min zafi a kirji.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”


Na fada ina jin kirjina kamar zai fashe zuciyata ta fito waje, muna haka Baba ya shigo dakin yana turo wheelchair dinsa Inna na bayansa tana hawaye shu kuma fuskarsa na nuna tsantsar damuwar da ke tattare da shi. Ina kallonsu sai ya tuna min da wacan lokacin na baya lokacin da aka dura aurena da Aminu, lokacin da ko wace fuska take dauke da murmushi da annashuwa da jindadi.

“Halimatu ya akai hakan ta faru?”


Ban boye masa komai ba ciki har da ikirarin da Hajiya tai na kaiwa Sadi Namra ya rika.

“Wannan maganar banza ce! Taya zai sake ki ba tare da sauraren gaskiya ba kuma be yi bincike ba sannan ya ce zai dauki yaya ya kai wa kanensa? Babu wanda ya isa ya rabaki da yayanki a nan za su zauna tare da ke idan kuma yayi musu kotu zata rabu mu da shi, domin yanzu babu sauran mutunci a tsakaninmu da shi, duk abunda yake takama da shi sai na gani!”


Baba ya fada cikin fushi da daga murya kana kallonsa kasan ransa ya bace sosai, wanda ban yi zaton haka ba domin yana da wahala ka ji bakinsa maganar zamana da Aminu bayan ki yi hakuri aure sai da hakuri, na ji sanyi sosai kuma ina jin na samu kwarin guiwar rike yayana da kyau domin na samu mai goya min baya.

  Sun dade suna da maganar aurena da Aminu tun daga kan haihuwa ta ta fari har zuwa yau abubuwan da sukai ta faru da kuma abubuwan da suke gani ko ji, ni dai ban ce uffan ba domin har lokacin da kennana suka shigo suka saka baki ana yi da su ban ji ina furta ko da sunan Aminu ba a zance balle kuma har nai wata firar abunda ya shafeshi, sannan suna yi an saboda su nuna min kar na damu akan abunda ya faru.

Sai kuma sha biyu sannan kowa ya nemi gurin kwanciya, a lokacin Amal ta dade da bachi a kirjina, sai da na kwantar da ita a kasa saboda fitsarin da take sannan na fito falon Mama neman su Adnan.

“Ai tun dazun Abdallah ya tafi ta su gidansa, yace can za su kwana”


Mama ta fada.


“Har da Namra?”


“Eh har da ita”


“Akan me zai tafi da ita bana son tana rabar kowa a yanzu bari na kira shi...”


Ina juyawa Hafiza ta kirani.

“Anty Halima dan Allah karki kira shi yanzu, kin san dai indan kowa zai lalata miki yara ban da Yaya Abdallah, kuma saboda yana tausayin yaran yai so karki bashi kunya a yanzu”


“Bana iya yarda da kowa akan yarana yanzu, indai har kannen mahaifinsu zai iya yin wani abu na lalata da Namra, to kowa ma zai iya lalata da ita, rayuwar ya mace a yanzu tafi ko yaushe bukatar tattali, idan na nesa be lalata maka ita ba, na kusa zai iya samu damar hakan, idon kowa ya rufe a yanzu Hafiza, ba zaki taba gane abunda nake nufi ba har sai kin yi aure kin haihu sannan za ki gane tarbiya da tsare yaya abu ne mai wahala, ban son na sake aikata kuskuren da na aikata na barin Sadi da yarana har ya samu damar yi min tabon da ba zai gogu ba har na koma ga mahallincina, da na san cewar zuwa na gurin aiki zai haifar da haka da ban yi aikin ba, da na zauna da yayana a ko wane irin hali, a ko da yaushe ina aina yadda Namra zata ji idan ta girma ta samu irin wannan labarin, ida na kuma na sake bari wani ya sake faruwa? Laifin akan wa zan dora shi?daman tun farko be kamata na yarda da kowa akan yayana ba”


Na karasa tare da saka hannuna na share hawayen idona, sannan na kai dubana gurin mahaifiyata wacce ke kallona fuskarta da murmushi.

“Kinji kwatankwacin abunda nake ji a lokacin da kike budurwa ke da yan'uwanki da kuma yadda nake ji a yanzu da nake tare da kanenki, a kullum ina cikin fargaba da tsoron kar wani abun ya same su kar wani ya lalata musu rayuwa, ko daga nan zuwa gidanki suka fita hankalina a tashe yake har sai sun dawo sannan na ke samun natsuwa, shiyasa a kullum bana da burin da ya wuce ko wacce na ganta a dakinta, Halimatu kina jin abunda na ke ji a matsayina na uwa, ke ma uwa ce”


STORY CONTINUES BELOW

Dan murmushi nai kadan sannan na nufi dakinta na kwanta a kusa da Amal ina ta kallon fuskarta, kamin na sake tashi na nufi inda handbag dina take na dauko na danna number Abdallah sai na jita a rufe wata kila ya rufeta ne saboda ya san zan kira ko kuma ya saba rufe idan zai kwanta ne oho.

  A wani abun mamaki a daren sai na kasa runtsawa har safe, bachi ya kauracewa idona ba dan kuma ina tunanin komai ba, domin ban ji tunanin kowa ya zo min rai ba a wannan daren sai Allah ya saka min saukin abun har na ke jin kamar bana da damuwa a tare da ni.

  Misalin hudu saura na asuba na tashi na shiga bandakin domin yin alwala nai nafila kamin ayi assalatu, ina tsugunawa gurin fitsari sai jini ya fara min zuba a madadin fitsarin, sai da ya zubo min da dan yawa har da sare sannan nai fitsarin na wanke na tashi sai na ji abun be tsaya min ba.

  A dole na nufi dakin kanena na tashi Marwa ta bani pad na saka sannan na dawo na zauna na dauki carbi Mama ina ta ja, marata na dan murda min kadan-kadan.

Haka nai ta dauri har kusan takwas da yan mintuna na safe, ina bawa Amal koko wayar Abdallah ta shigo.


“Hello Assalamu Alaikum”


“Wa'alaikissalam Momy ina kwana?”


“Lafiya kalau Namra an tashi lafiya?”


“Lafiya Kalau”


Ta amsa min da muryarta radau har tana yar dariya.

“Momy ga maman su Nabeela”


Ta mikawa matar Abdallah wayar muka gaisa, sannan ta bawa su Adnan da Aiman, daga bisani ya karba ba tare da ya min magana ba ya kashe wayar. Number Hajara na kira na labarta mata abunda yake faruwa sai ta saka salati da sallami tana fadin sai ta zo. Bayan na gama da matsalar Amal na aika yaro aka siyo min pad da pants a shago na shiga nai wanka na fito na saka tufafin jiya, sannan a shiga dakin Baba na gaishe shi tare yi masa ya jiki.


“Al-hamdulillah, na yi waya da Almu direba, zai zo anjima kadan sai aje kwaso miki kayanki, makulin gidan yana gurin Aminu ne?”


“Eh dayan yana can daya yana gurina”


“To za aje tare da ke saboda kar a hado da na shi, ki kwaso yana yaranki da na ki sai a kawo a nan,kamin na dawo ma ya tarar an kwashe komai na ki”


“To Baba na gode”

“Babu komai Allah ya bamu hakurin zama, kin san shi zaman gida sai da hakuri musamman ma gida nai kanne da yawa haka, sai kin yi hakuri d yan'uwanko kamin Allah ya kawo miki wani na gari”


“In-Sha-Allah Baba”


Na jidadin yadda ya nuna min kulawa sosai, tara da yan mintuna direban ya zo da babbar motarsa irin wannan ta kwasar kaya, tare da ni da kanena uku aka je muka kwaso komai sai da mu kai wa gidan tas da kayan sannan muka dawo, a unguwa kuwa kowa sai kallon yake ganin an kwaso kayan wanda be san da maganar ba ma yanzu ya sani. A dayan dakin da ake zuba kaya aka zuba gado na da kujeru da sauran tarkashe kayan sakawata kuma na kai su dakin su Marwa domin shi ne ke da girma sosai har ma na samu gurin shimfida katifa ta, na raba yan tsoman karana gefe. Tabbas na ji babu dadi a wannan lokacin domin bbu wanda zai so baro wadatacen gidansa ya dawo wani guri ya raba. Bayan mun gama na sanja wasu tufafin na bar Amal a gida na nufi gurin aikina. Kowa yayi mamakin ganina a wannan lokacin dmin ban saba zuwa da aiki a late ba ko ma naje late ba kamar haka ba, domin sha daya saura. Mun gaisa da Kabeer da Emanuel kamar yadda muka saba da halshen turanci kamin Kabir ya koma yana magana da ni da hausa daga can inda yake zaune ni kuma ina zaune a teburina.

“Ya jikin na ki?”


Shiru nai wata kila na fada masa bana jindadi ko? Oho na dai manta.


“Al-hamdulillah”


“Kin karya kuwa?”


Nan ma shiru nai kamin na bashi amsa, na manta when last wani ya tambaye ni ko ya damu da na ci abinci.

“Eh na karya”


“Baki karya ba Haima na sani”


Na fada yana dariya sannan ya mike tsaye yana fadin.

“Bari na sauka kasa naje restaurant na siyo miki wani abun”


“Aa Kabir na karya ban bukatar komai...”


Be saurareni ba ya fice yana ciro wayarsa daga aljihu, dafe kaina nai kamin na dauki takadun da na tarar a gurin an shiga da su office din Oga Dahiru, da sallama na shiga na mika nasa gaisuwa sai ya amsa min yana kallona.


“Kwana biyu ba ki zo office ba”


“Bana jindadi”


Na fada ina mika masa files din hannuna.


“Kin ga likita?”


“Eh malaria ce”


Wani kallo yai min kamar be yarda ba, sai kuma ya karbi file din yana murmushi.

“Halimatu kenan, Thank you you can go”


Na juyo na fito daga office din ina ta mamakin kallon da yai min da kuma murmushin da ke fuskarsa. Ina kokarin zama a kujera ta gabana ya fadi na rashin dalili har sai da na kira Allah sannan na samu natsuwa, aikina na cigaba da yi har na tsawon minti talatin sannan Hafsat ya shigo office din mu hankalinta a tashe tana fadin.

“Ku kuna nan zaune ba ku san an kade Kabir ba”


Na riga Emanuel mikewa tsaye domin da hausa tai furucin kamin ta sake fada da turanci, sai naji abu kamar daga sama.


“Taya?”


Na tambaya hankalina a tashe.


“Gashi can waje ban san yadda akai ba amman har kafarshi ta cire gashi can ana saka shi a mota za a kai shi asibiti... ”

Ban san lokacin da na rufe bakina na watsa da gudu zuwa sakan ma'aikatar ba, tsakanin ni da Emanuel sai aka rasa wanda yafi wani saurin saka ya ganshi,  sai dai dukan mu mun yi rashin sa'a domin tuni an saka shi a mota an nufi asibiti da shi, babu komai a tsakan titi sai shimkafa da ya siyo min da kuma jini, ban san lokacin da na fashe da kuka ba har sai da Raliya abokiyar aikina ta rikoni muka dawo cikin ma'aikata, a lokacin kasa yin komai nai kuma ban yi tunanin binsa zuwa asibitin ba a wannan lokacin sai sauraren marata dake murdawa na ke, kamin na dauki jakata na fito na tari napep na koma gida.

  Ina isa na tarar su ma sun gama na su fadan da Familyn Aminu akan yayana, wai sai an basu yara Baba kuma yace idan suna son yara su tafi kotu, sun labarta min abunda ya faru sai dai sun lura nawa hankalin ba a gurin nan yake ba a yanzu, gani sai wani duke duke nake saboda ciwon marar da nake ji.

“Lafiya Halimatu”


“Mama marata ke masifar ciwo”


Ta yi saurin janyo kujera ta ba ni.


“Zauna sannu”


Na zauna ina jin kamar ba zan iya zaman ba, domin ko ciwon nakuda be kai wannan ciwon da nake ji a yanzu zafi ba. Wayata dake cikin jaka tai ringing sai dai ban kula wayar ba saboda ba ta wayar nake a yanzu ba.

“Salma je ki taro Napep muje asibiti”


Mama ta fada cikin tashin hankali ganin yadda nake cizon baki saboda azaba domin ta san ni da juriya. Kamin a taro napep din mu shiga zuwa asibiti sai na ji kamar zan mutu har da kuka hannuna akan marata sai murjawa nake. Mun yi sa'ar ganin likitar nai mata bayanin abunda nake ji a take ta saka a bani gado sannan ya rubuta min magani ta kuma fada min cewar abunda ke cikina ne yake kokarin zubewa za a min wanki mara.

___________


Kwana biyu nan ina busy shiyasa bana post kullum amman da zarar komai ya zama normal zan cigaba kamar yadda aka saba In-Sha-Allah.Ba mu dawo gida ba sai 6pm na yamma, domin bayan mace ta min wankin mara sai da likita ya bani damar hutawa na awa biyu da rabi zuwa uku sannan muka dawo gida.

  Da dare Hajara ta kawo min ziyara ta nuna min damuwarta da kulawa sosai kamin addu'arta ta biyo baya, mun dade muna fira da ita sai goma na dare mijinta ya zo ya dauketa. Bayan tafiyarsu da kamar mintuna talatin Abdallah ya kirani a waya har na yi kamar ba zan daga ba sai dai tunawa da bana da aure a yanzu ya yake min hanzarin kin daukar da nake yi a baya, wata kila ma Namra ce take son magana da ni ko Aiman.

Da nai picking ban ce masa komai ba, ko sallama da hello da ake idan an kira mutum ko kuma shi ya kira wannan karon bance ba, sai kawai nai shiruna ina jiran ya fara min magana. Shi kuma ya gagara cewa komai kamar wanda ya kira domin kawai yaji saukar numfashina, jin hakan yasa na kashe wayar na mike tsaye na nufi dakina ko kuma nace dakinmu ni da kannena. Tufafin jikina na canja na saka marar nauyi saboda yanayin garin da nake gani da kamar akwai hadari saboda zafin da yai yawa. Amal kuma na saka mata nata kayan bachi na kwantar da ita ina lallaba tai bachi sai ta fara min kukanta na banza daya saba yi wani lokacin idan za tai bachi.+


“Ai da an sani a bawa Ya Abdallah ya hada da ke ya tafi mu huta”


Cewar Kanwata Haulat tana hararar Amal daman can basa shan inuwa daya da juna. Ni kuma nai murmushi na mika hannu na dago Amal na rumgumeta ina rarrashinta.


“Ya Abdallah yazo dazun lokacin kina asibiti”


“Ya kawo su Namra ne?”


Na tambaya ina kallonta.

“A a ba da su ya zo ba, shi kadai ya zo yana tambayarki sai Inna ta fada masa kina asibiti za a miki wanki mara”

Tana rufe baki kiran wayarsa na shigowa a wayata, nan ma sai dai nai kamar kar na dauka sai kuma wata zuciyar ta hana ni, picking nai na kara a kunne tare da sallama. Be amsa min ba kuma be ce min komai ba sai dai daga cikin wayar ina iya jiyo yadda yake ja da aje numfashi da karfi. Katse kiran nai na kwantar da Amal sannan nima na kwanta bayanta ina ta tunanin Kabir ko a wane hali yake ciki a yanzu inata auna zafin barin da na da kuma kafarsa da aka ce ta cire da gaske ma ta cire din ko kuwa dan karawa labarin magi dagishiri yasa tace haka? Number wayarsa na gwada kira da fari ta yi ringing har aka daga sai dai ina yin sallama sai aka kashe kiran na sake bugawa na ji wayar a rufe. Damuwa sosai ta shiga raina, ko ba komai ai mun yi zaman mutunci da Kabir idan na tsallake ko kuma na cire son tana jikin ko yi min maganar banza da Kabir yake kokarin yi ban san shi da wani hali na assha ba, tun ba jiya ba yana yawan damuwa na al'amurana, duk wani abun da ya dame ni zai nuna damuwarsa sosai a kaina, idan kuma akan wani laifin ne a gurin aiki to zai yi kokarin tare min ko ya wanke ki ko a gurin waye ne. Ko a kan wannan kadai ya kamata na damu da Kabir balle kuma saboda yaje siyo min abinci wannan abun ya same shi, ko da ciwon kai ne ya same shi ta dalilina dole na damu balle kuma hadari, abun sai ya hade min a guri daya har na rasa wanne zan fara tunani bayan damuwar da ke cina yanzu kuma wani abun ta samu Kabir ta dalilina.

Har garin Allah ya waye Kabir na cikin raina ban jidadin rashin zuwa ganinsa da ban samu yi ba, kusan rabin mafarkin da nai na Kabir ne sai dai ba zan iya fahimtar sakon mafarkin ba, kuma na alakanta hakan da kwanta da nai ina tunaninsa.

Duk da bana sallah haka ba be hana ni tashi da asuba da wuri ba kamar yadda na saba, ko bana sallah na kan yi addu'oina na safe idan ina lokacin period ne.

ABDALLAH POV.

Da gangan yake yai magana ya yi shiru yana ta sauraren yadda numfashinta ke fita fuskarsa na yalwantuwa da murmushin da shi kadai ya san sikarsa, bayan ta kashe wayar ya sake kira sallamar da tai masa ta saukar masa da natsuwa da kwnaciyar hankali daman can muryarta kawai yake son ji, domin ba shi da wani abun da zai ce mata, bayan son yai mata jajen ɓarin da tai ta waya, ɓarin kuma ba karamin dadi yai masa ba, domin ya kusanto masa da nesa kusa zuciyarsa na raya nasa a yanzu yana cikin ko wane mataki da zai iya nunawa Halimatu soyayyah, domin bata da auren a yanzu kuma ta cika idda indai har jinin ya tsaya mata. Kansa ya daga sama yana kallon tauraren da sukai ma sararin samaniya ado. Sannan ya maida wayar aljihunsa tare da zuba duk hanneyensa aljihun wandon, Halimatu ba zata so shi ba, ba zata taba amincewa da shi kai tsaye ba, domin yayi kuskuren nuna mata kauna a lokacin da take da igiya uku ta aure akanta har ta koma biyu har da zama daya, shi yake yawan fada mata mijinta yayi kaza ya yi kaza, yana yawan nuna mata Aminu ba irin mijin daya dace ta aura ba ne, ya dade yana jira zuwan wannan ranar ya dade yana addu'ar Allah ya raba auren Aminu da yar'uwarsa Halimatu saboda kawai shi ya aureta, yana ji a ransa kuma yana yawan rayawa a zuciyarsa cewar shi kadai ya dace ya zama mijin Halimatu, domin shi ne mutumen da zai iya nuna mata kauna zallarta ya kare mutuncinta ta martaba, and he know exactly how to lighten the candle of happiness in her life. Tun daga lokacin da ya dawo kasar nan tare da iyalinsa ya kyalle ido ya ga Halima sai Allah ya dauki sonta mai tsanani ya saka masa, har ya zama bashi da sukuni da walwala idan ban ganta ba ko be ji daga gareta ba, tun yana kokarin cire abun a zuciyarsa ya kawarda komai har ya gagareshi, har yake ji da ace ya san lokacin da take budurwa ko kuma yayi arba da ita tabbas da Halimatu bata da wani mijin bayan shi, domin tana da siffar da yake so a jikin mace komai na rayuwarta burge shi yake, the way she dressed, yadda take tafiyarda rayuwarta ga hakuri da kawaici ga magana ma so calmly, even simple makeup din da take burge shi yake.

Daga lokacin da ya gano kalar mijin da take aure kuma sai tausayinta ya samu muhalli a zuciyarsa, kuma ya samu makamin yaki da igiyar aurenta.

STORY CONTINUES BELOW

Ba abu ne mai sauki Halimatu ta karba tayinsa a yanzu ba, shi kansa ya sani domin haka ba zai yi kuskure nuna mata haka a yanzu ba ko kuma furta mata kalma so ko aure a yanzu ba, duk kuwa da kasancewar ta dade da jin daga gareshi saboda ya fada mata ba daya ba ba biyu ba cewar yana sonta yana kaunarta a lokacij da take da igiyar auren a akanta har take masa kallon mahaukaci ko kuma marar tunani, wannan dalili ya saka Halimatu tsanarsa fiye da kowa a familynsa.

Ba irin wannan lokacin ya kamata ya nuna mata so ba, wata kila ma bata sha'awar auren a yanzu, sai dai ya shirya nuna mata kulawa da kwantar mata da hankali da kuma kaunar yaranta.

“Daddy ba zaka shigo ba?”


Juyowa yai yana kallon yarsa Suhaima fuskarsa dauke da murmushi, ya kai hannunsa ya daga sama.

“Eyyyy ba ki kwanta ba Mamana?”


“Yes mu na ta kallo da Aiman, amman kowa yayi bachi sai ni da kai da Aiman muka rage”


“Okay je ciki ina zuwa”


Ya fada yana sauketa kasa sai ta juya da gudunta ta koma ciki, shi kuma ya sake ciro wayarsa sai dai wannan karon ba Halimatu ya kira ba Hajiyarsa ya kira duk kuwa da bashi da tabbacin cewar zata dauka wata kila ma ta yi bachi. A mamakinsa sai tai picking call din da muryarta radau babu alamun bachi.

“Hajiyata ba ki kwanta ba?”


“Ban kwanta ba Husaini kai me kake a farke?”


Jimmm yai na wani lokacin sannan ya ce.

“To ni ma dai ba zan iya fada ba for now, amman dai na kira na fada miki cewar Halima ta yi miscarriage ya kamata ki dubata gobe inda hali, kin ga ko sakin da akai mata Hajiyata ba ki je kin mata jajaye ba”


Daga dayan bangaren Hajiya tai murmushi mai sauti sannan ta dora da.

“Zanje gobe In-Sha-Allah shikenan? Jikin nata dai da sauki ko?”


“Ban sani ba, amman naje dazun ban tararda ita ba wai tana asibiti ni kuma bana son su fara zargin wani abun ne shiyasa ban je ba, amman ni ma gobe zanje ma dubata”


“To sai ka biyo ka dauke mu mu tafi ai”


“Aa Hajiyata zuwanki dabam na Abdallah dabam”


Ya fada da murmushi a fuskarsa sannan yai mata sallama ya sauke wayar, fira da mahaifiyarsa ko yayansa na daya daga cikin abunda yake saka shi ciki nishadi da farinciki ko da kuwa yana cikin damuwa ne. Juyowa yai ya nufo balcony ya tura kofar falon ya shiga. To His surprise sai ya samu uwargidansa tsaye jikin window dakin tana kallon waje sai dai shigowarsa yasa ta juyo ta da dubanta gurinsa. Ya dan wara ido yana murmushi daya saba yi mata.

“Suhaima ta ce kina bachi”


Ta wani marairaice kamar karamar yarinya marar.

“Taya zan iya bachi Doc be kusa da ni, na yi na dan guntun lokaci sai ya farka bachi ma ba dadi”


Murmushi yai ya katsa kusa da ita yana mai jin son uwargidan har cikin ransa, ya kai hannunsa ya rumgumeta ta baya ya dora kansa saman wuyanta.

“That's right Teema”


Ta yi saurin juyowa ta kalleshi.

“Teema kace fa?”


“Eh ba sunanki ba ne?”


“Amman ai ba haka kake kirana ba sai dai ka ce min Baby ko Madam ko Mom Suhaima”


Dariya yai ya jiyarda ita ya sake rungumeta ta baya.

“To Baby yau yan tsokarna sun motsa ne shiyasa”


“Da wa kake waya?”


“Da Hajiya”


STORY CONTINUES BELOW

“Amman ka dade a waje fa”


Ya sauke hannayensa daga rikon da yai mata ya saka hannayensa aljihu.


“Ina ta tunanin mutuwa ne, mutuwa kawai ake a yanzu any how abun har tsoro yake ba ni, ina ta tunanin makomarmu ne”


Ya fada yana hade yawun bakinsa domin shi ma yasan karya yai. A take Teema ta bata fuska damuwa ta bayyana a fuskarta jin furuncin daya fito daga bakin mijinta, hakika mutuwa abun tunawa a ko wane dare ko dakika sai dai ba kowa ne ke tunawa da ita ba sai masu imani da tunanin ya goben su zata kasance.

“Allah dai ya saka mun cika da imani, nima abun na taba ni Wallahi”


Ta fada bayan ta sauke ajiyar zuciya. Hannunsa ya kai ya riko hannunta ya nufi hanyar dakinsa da ita.

“Ina Aiman? Suhaima tace sune kawai ba su yi bachi ba”


“Na saka su bachin dole ai, kun zauna gaban tv kamar a gurin za su tabbata”


Hannunta ya saki ya nufi dakin yaransa, a bakin kofar dakin ya tsaya yana kallon Suhaima da Lubna sai kuma yayan Halimatu wato Namra da Aiman da Adnan, a ransa ya rika kwatatta yadda abun zai burge idan da ace shi Halimatu ta haifawa yaran nan gaba daya musamman Aiman da Adnan domin shi Allah be ba shi yaya maza ba, yan mata biyu matarsa ta haifa masa. Zuwa tai ta tsaya bayansa tana kallon yaran.

“Minene?”


“Ba komai”


Ya kai hannu ya janyo kofar dakin sannan ya nufi dakinsa Teema na biye da shi a baya.HALIMATU POV.

Karfe takwas na safe kofar shiga dakin da Kabir yake tai min, domin na kwana da shi a raina da na farka kuma sai na ji bana bukatar ganin kowa sai shi hakan yasa ban wani tsaya karyawa ba na nufo asibitin daman can abinci be dame ni balle kuma yanzu da damuwa ta zame min ci da sha, kuma ta zame min abokiyar fira.

  Ba ni kadai aka hana shiga ba, har da sauran masu ganin marasa lafiya da masu kawo abinci balle kuma ni da ban kawo komai ba. Muna tsaye a gurin har kusan tara da wani abu ba bar mu mum shiga ba sai dai an bar masu dauke da abinci sun shiga, ni kan sai na samu guri kusa da inda kofar take na zauna, na bawa kofar baya zaman jiran gawon shanu domin ban san lokacin da za a bada damar shigar ba, sai dai bana jin a yau zan wuni ban saka Kabir a ido ba ba dan komai ba sai dan damuwa da halin da yake ciki a yanzu wanda silata ne komai ya afko. Ji nai a dabani da wani hannu mai sanyi da alama mamallakin hannun ya taba ruwa mai sanyi ne ko kankara, ashe mamallakin hannu mace ce ba namiji ba ban fahimci hakan ba har sai da na juyo na kalleta na kuma tabbatar da macece ta hanyar sautin muryarta.

“Kamar Haima?”


Gabana ya fadi har na kasa amsa mata da eh ni din ce ko kuma a a ba ni ba ce, domin mutun biyu ne suke kirana da wannan sunan a duk fadin duniyar nan. Daga Abdulhamid sai Kabir, ba kuma zan ce a gurin Abdulhamid ta samu sunan ba, domin be taba kirana a gabab kowa da wannan lakanin ba, mutumen da be yarda na bayyana soyayyarsa ba taya zai fadawa wata ya taba kirana da wannan sunan a lokacin da na ke budurwa.

“Har na wuce ki na dawo saboda kin min kama da Haima, kuma wannan shirun da kikai ya tabbatar min da cewar ke ce Haima! matar da Kabir ya cika wayarsa da hotunanta kuma matar da aka ce ita yaje siyo ma abinci wannan hadarin ya same shi, wani abun mamaki kuma jiya da kika kira wayarsa sunanki yai appearing da Spacial Haima”


Wani dimmmm na ji kamar an dora min abu akao na kunya da nauyin kalamanta, hakika ni ma mace ce ba zan zo mijina ya kula wata mace ba kuma ba zan jidadi ba, sai a iya zamana da Kabir ban taba daukar hoto daga ni sai shi ba ko kuma ni kadai na tura masa to a ina ya samu hotona wata kila a media ko kuma a gurin wani wata kila kuma ya dauke ni ne a lokacin da nake aiki.

“Shin baki taba sanin Kabir yana aure da yaya ba?”


Ta jefo min tambayar da ban san ta ina zan tattara amsar da mika mata ba har ta gamsar da ita.

“Ya kamata ace na damu da lafiyar mijina a yanzu ko dan saboda yayan mu, amman saboda ke idan na tuno sai na ce masa Allah ya kara, ke ya kamata ace kin fi ni damuwa da shi, ko ba komai kin fini samun lokacinsa kin fi ni samun soyayarsa da kularwarsa, kin fini muhimmanci a gurinsa”


Tana fadar hakan ta fara takawa zata bar ni a gurin da dafin furucinta, cikin kuzari da hanzari na mika sautin muryarta dan isar da mata da abunda bata sani ba.


“Babu wata alaka tsakanina da mijin, abokin aikina ne kawai kuma ni ma matar aure ce har da yaya be kamata ki zarge ni ba”


Juyowa tai ta tsaya tana kallona kamar mai mamakin abunda ya fito daga bakina, a zatona zata yarda da kalamaina ne ko kuma ta dora su a ma'aunin tunani.

“Matar aure? Kina nufin irin auren nan da be hana mai yinsa aikata komai ko? Kina nufin irin ijiyar auren da wasu kan take su aikata alfasha da wasu mazan ko?”


Wani irin abu na ji ya taso min ina iya jure komai a cikin har da kazafin sata ko maita amman ba zan juri a kira mi karuwaba, domin na san illa da kazantar zina ban aikata ba dan haka ba zan yarda wasu su bata min suna ba.

“Ke malama ban san ki ba bana da wata alaka da ke, ko ki iya halsheki ba zan jure irin wadannan kalaman daga bakin kowa ba...!”


“Baki san ni ba ba ki da alaka da ni amman kina da ita da mijina ko? Banza marar sanin ciwon wawuya wacce igiyar aure bata hana ta aikata komai ba....”


Cikin daga muryar take fada min haka, ban san lokacin da na karasa kusa da ita na wanke mata fuska da mari ba, abunda ya janyo hankalin wasu mutanen izuwa gare mu kenan daman tun da ta fara maganar aka fara tsayawa yana kallon mu...

___________


Tofaaaaaaaaa.


Al-hamdulillah yanzu kan Al-hamdulillah na gama komai hankali ya dawo gurin typing.....✍️1

Post a Comment for "GOBE NA CHAPTER 1 BY KHADIJACANDY"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...