GIDAN NAGOGGO COMPLETE BY FATEEZAH - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GIDAN NAGOGGO COMPLETE BY FATEEZAH

GIDAN NAGOGGO COMPLETE BY FATEEZAH

- - Post a Comment

 GIDAN NAGOGGO COMPLETE BY FATEEZAH

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Tsawar da naji shi ya dakatar dani da bude dakin Ammy na.

"wallahi Bahijja in kika shiga dakin nan sai na bata miki rai,Uban mai kika zo yi mini a gida,ki tashi ki koma inda kika fito,tunda baki daukeni a bakina komai ba "cewar Alhaji kenan.

Take naji wata wata fargaba ta ziyarceni,wai yaushe zan fara samun kwanciyar hankali da maslaha tsakanina da Mahaifina,maganar Ammy tace ta tsinke min dan gajeran tunanin da na shiga wacce take tambaya abunda ke faruwa.

Alhaji ne ya fara magana cikin fushi "Amina ki juya ki koma ciki, in ba  so kike   fushin wannan mara kunyar ya shafeki ba,in kuma ba haka ba wallahi zanyi mummunar saba miki".

Da sauri na juya domin fita daga gidan don ganin Ammy na ta juya tana hawaye,ji nayi na tsani kaina,don tun ina Yarinya har girmana ta dalilina Ammyna ke zubar da hawaye.

Daga gefen gidan na tsaya ina kokarin tsaida  hawayena da tunanin mafita.

Yanke hukunci nayi kawai akan na tunkari gidan Yaya Baffa wanda shine Babba a mazan gidan,don ina tunanin duk da 'Yan Uba nake dashi zai iya taimakona ya rokan mun Alhaji duk da wannan karan bansan laifin da nayiba.


Achaba na tare na hau tare da fada mai Anguwan dazai kaini,cikin 10minutes muka isa gidan saboda bamu da nisa,kasancewa Alhaji yana Banzazzau shikuma Yaya Baffa yana filin Mallawa,sallamar dan Achaba nayi na karasa nayI knocking din gidan,after some seconds Gateman yazo ya budemin tare da mun sannu da zuwa na kutsa kai harabar gidan.

Gida ne wanda ya amsa sunansa wanda kallo daya kayi ma gidan kasan mai gidan ya jiku da naira,hanyar da zata sa dani da main door din gidan na nufa,zuciyata na bugawa kamar zata tsago ta fito saboda shima bansan irin karban da zaya min ba.

Knocking din main door din nayi ,sai da nayi some seconds tukunna aka bude min kofar,Murmushi tamin tare da cewa "Bahijjah ce,sannu da zuwa,yaushe a Garin" dukka ta min wannan tambayar a lokaci daya.
Nima na maida mata da martanin murmushi tare da cewa"Nice  Aunty Hanna,yau nazo".
"Karaso ciki mana"cewar Aunty Hanna.
Shiga cikin parlour nayi tare da kulle kofar,nan danan ta cika mini gaba da Snack da Drinks,tukunna ta zauna muka kuma gaisawa tare da tambayarta ina Yara.
Tace "Sun tafi school.
sannan tace "kici Snacks din mana"
Nace "Aunty Hanna bazan iya cin komai ba,don Allah Yaya nanan"?
Ta amsa min da"Yana nan bari inyi masa magana amma don Allah Bahijjah ki daure ki danci Snack din ko kadan ne".
Na amsa da "to Aunty"
Tashi tayi ta nufi ciki,ni kuma nasa Hannu na dauki Samosa daya na fara ci,ji nayi kamar ina cin magani.

Sun dau lokaci Basu fito ba,don har na fara gundura da zaman,sai gashi Sun fito dukkansu fuska ba yabo ba fallasa,nan da nan nasha jinin jikina,na zamo daga one sitter da nake zaune na gaisheshi,Ya amsa fuska a hade kamar hadari,sannan na koma na zauna,suma suka zauna a 2sitter dake facing din inda nake zaune.
Gyaran murya Yayi tare da tambaya ta"me ke tafe dake"?
Muryata a sanyaye nace "Yaya nazo ne don Allah ka taimake ka rokan min afuwa a gurin Alhaji Don naje ya koreni,kuma ni bansan mai nayi mai ba wannan lokacin "na kara she tare da kokarin maida kwallar dake barazanar saukomin.
Ya tambayeni "Bahijjah kikace baki son mai kikayi ma Alhaji ba"?
Na amsa da gyada kana sama.
Yace" alhaji Yace tunda kika koma Sokoto baki taba kiranshi kin gaishe shiba har maganar auren nan naki da ya taso,baki kira kin sanar dashi ba sai da  Yaya Arsala ya kira shi ya fada mai,kuma Tace yana ji kuna waya da Ammy,amma shi kin maida shi Makiyinki,yanxu watan ki nawa da komawar ki Sokoto amma ko so daya baki taba kiranshi ba,yanxu tsakaninki da 
Allah Bahijjah kin 
kyauta?,yanda fa Ammy keda hakki a kanki haka Alhaji shima yana da hakki a kanki".

Kaina a duke nace"Yaya nasan nayi laifi amma wallahi Yaya ko na kirashi baya dauka,so uku ina kiranshi bai daukaba,shi yasa ni kuma ban kuma kiransa 
ba,saboda na dauka bai bukatar gaisuwar tawa".

Kara gyaran murya yayi tare da cewa"look Bahijja ni kwata kwata ban ganin laifinku,na Ammy nake gani,amma zan sami Alhaji muyi magana,yanxu dai mai ya kawo ki garinnan,ina zaton yau saura 3weeks bikinki?"ya karashe da tambayata.
Nace"Kaduna zan wuce,in gyara kayan bed dina"
Yace"to da kike maganar gyaran kayan bed 
kina da kudi ne?"
"eh,angon ya ban 10k saboda in gyaran kayan"
Anan Aunty Hanna ta saka baki tare da cewa«Honey,ni a ganina da Bahijja tabar maganar gyaran gadonnan kawai ka canza mata sababbin gado,tunda wancan auren nata shekara 10,kaga sun tsufa da yawa"
Yace"A,ah Sweety kibarta taje ta gyara kayanta,tunda tazo da niyyar gyarawa"sannan ya juyo gareni tare da cewa"Bahijja kije ki gyara kayanki,zan sami sauran 'yan uwa muyi maganar gudunmawar da za a hada miki ".ya karashe tare da mikewa yana kallon Aunty Hanna sannan yace Sweety ni na dita,in zata tafi ki duba drawerta ki bata 2k tayi transport"
Bai jira cewarmu ba yasa kai ya fita,sai da mukaji fitar motor dinshi sannan Aunty Hanna ta juyo tare da cewa"Bahijjah kiyi hakuri da rayuwa wata rana sai labari".

Post a Comment for "GIDAN NAGOGGO COMPLETE BY FATEEZAH"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...