DR TAHEER CHAPTER 1 BY UMMU ASHRAF - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DR TAHEER CHAPTER 1 BY UMMU ASHRAF

DR TAHEER CHAPTER 1 BY UMMU ASHRAF

- - Post a Comment

 DR TAHEER CHAPTER 1 BY UMMU ASHRAF              Www.bankinhausanovels.com.ng 


Budurwa ce da bazata wuce 17 years ba a kitchen da katon bowl me daukeda kayan miya a gabanta sai jujjuyasu kawai take da sunan gyarawa,wata dattijuwa dake kokarin sauke tukunya a kan gas ta juyo tana kallon kayan miyan tace "oh ni hauwa!yanxu Layla gyaran kayan miyan ne har yanxu sai kace wadda bata da lfy?Wanda ta Kira da Layla ta turo baki tace "to ba na kusa gamawaba mama hauwa wanki na uku fa kenan nake musu"hauwa bata sake cewa komai ba ta juya tacigaba da aikinta,,ko minti biyu batai da juyawan ba Layla ta fasa wani uban ihu tana tsalle tana yarfe hannu "tace wayyo na shiga uku Mama hauwa ya shigan min idona wlh wayyo Allah daddynaaa"...da sauri wani matashi ya shigo

kitchen a guje dagashi sai singlet da three quatre ya kamo Layla da sauri yace "menene"?Mama hauwa na kokarin yi masa bayani kawai taga ya dauketa cak yayi part dinshi da ita sai tsala ihu take,tai murmushi kawai ta dauki kayan miyan zata karasa da gyarawa wata dattijuwan Mata ta shigo kitchen din tanasanyeda hijab a gigice tace" hauwa meke faruwane Ina sallah naji ihun Layla,lafiya kuwa"?hauwa tai murmushi "tace wlh lafiya qalou hajiya,gyaran kayan miyan da aka sata nefa tun dazu takeyi sai kawai ihunta naji wai yaji ya shigan mata ido"matar ta dafa goshi tai salati snn "tace yanzu duk wnn uban ihun da naji na yaji ne kawai?mama ta sake murmusawa tace "wlh shine hajiya",to ynxu tana Ina?ta tambaya tana waigawa ko zata ganta a kitchen din,Mama hauwa "tace babanta ya dauketa yayi bangarensa da ita"matar da jijjiga Kai kawai ta fita tana mita"dama shi yake lalata ta wlh,inba don iskanci ba meye yaji a ido Allah na tuba da zata dagama mutane hankali haka zataci ubanta sai nayi maganinsu daga ita har uban nata wlh"itadai hauwa dariya kawai tayi tacigaba da aikinta.+


Suna shiga part dinshi direct bathroom ya wuce da ita ya ajiyeta gaban sink snn ya kunna tap ya shiga wanke mata fuskan da hanunshi,har yanxu bata bar kuka ba ta rike hanunshi tace "daddy da zafi kayimin a hankali pls",ba musu ya dinga shafa fuskan a hankali kmr yana wanke kwai,seda ya gama snn yace "oya open up mu gani ko ya fita",ta bude idon a hankali sai Kuma ta sake buga wani ihun tana rukunkumeshi tace "wlh har yanxu akwai zafi daddy bai fitaba wlh",ya janyeta a jikinshi ya sake wanke mata fuskan snn yace "bude muga",ta shiga bude idon a hankali har ta budeshi fess tana kallonshi tace "ya fita",baice komai ba ya kama hanunta zuwa bedroom dinshi,gefen gado ya zaunar da ita shima ya zauna snn yace "tell me garin ya kikasa yaji a idon?ta wani marairaice tace "daddy ummi ce tace wai saina taya Mama hauwa aiki a kitchen wai ban iya komaiba sai shagwaba,shine Mama hauwa tace in gyara Mata kayn miya shine Ina cikin yi kawai yaji ya shigan min ido,kallonta kawai yake yanda take mgn kana ganinta dama zakasan shagwababbiya ce ta bugawa a jarida,ya kamo hanunta yace "yanxu baby sbd yajin shine zaki cika mana gida da ihu haka?,kinji yanda hankalina ya tashi kuwa?I was thinking ko konewa kikayi ko wani abu"ta kwanta a kirjinshi tace "to kayi hakuri bazan karaba Amma Allah yajin da akwai zafi,ya lumshe ido Yana  shafa kanta can kasan makoshi yace "it's okay ya wuce but next time ki ringa kula sosae idan an saki gyara kayan miyan kinji,ta daga mishi Kai a hankali tace "toh daddy"Good yanxu tashi muje in tayaki ki gyara kayan miy...bai karasaba ta Mike tana kallonshi a marairaice tace "don Allah daddy kayi hakuri ni baccima nakeji kuma har yanxu idon be dena yin zafi ba,,murmushi kawai yai yace alright ki kwanta abinki bari inje in samu ummin,ta rungumeshi tace "yawwa daddyna I love u,,I love u too ya fada yana pecking dinta a forehead snn ya fita,ita Kuma ta dauko iPad dinta data bari nan dakinshi daxu ta koma kan gadon tana dariya tace haka kawai inje yanxu nasan mukayi ido hudu da ummi to me rabata Dani sai Allah.


Yana shiga bai samu ummi a parlor ba don haka ya wuce bedroom dinta,tana zaune gefen gado waya kare a kunnenta fuska ba walwala take mgn,a hankali ya karaso ya zauna kusada ita sai yaji tana fadin"saboda Allah Aisha wnn ba iskanchi bane,ace wai kamar Layla me shekara 17 common gyaran kayan miya bazata iyaba,kinji yanda ta kurma ihu wlh ni da farko ma na dauka karyewa tayi,shi Kuma uban ya dauketa xuwa sashensa sbd shima  hankali be ishesa ba,to gsky kija masa kunne ya dena sangartamin jika ya barta ta koyi abinda ya kamata don ba zama zatai Babu aure kamar yanda shima yake zaune Babu auren ba,,a daya bangaren matar tayi dariya tace "inshaAllah zanyi masa mgn yaya,kiyi hakuri"tace to shknn sai anjima,ta ajiye wayarta gefe ta daure fuska kmr bata ganshi ba,yai murmushi ya matsa jikinta sosae bai kaiga yin mgn ba wayarshi dake hanunshi ya fara ringing"Ummata"shine sunan dake kan screen din still Yana murmushi ya daga wayan yakai kunne yace "barka da rana Ummata"wadda ya kirada umman ta amsa mai da "barka dai son ya aiki,yace "alhamdulillah ya kano,tace "kano gata muna cinkinta son yanxu umminku ta kawomin kararka"ya Dan saci kallon ummin da har ynxu bata kalli inda yakeba yace "to me Kuma nayi umma?tace wai kana sangarta 'yarka baka bari a koya mata aikin gida"yai Dan murmushi yace to zaa gyara umma InshaAllah,umma tace "yawwa ayi kokari don Allah Kuma har gori tayimin wai ba zama zatayi ba aure kmr yanda kake zaune ba,don Allah son ka daure kayi auren nan ko bakason hankulan mu su kwanta ne?yace "inaso umma"then why bazakayi auren nn ba tunda shine abinda mukeso muga kayi?ya sake kwantar da murya yace "zaayi umma InshaAllah lokacine beyiba"umma tace "to shknn Allah ya nuna mana lokacin ya amsa da ameen snn sukai hanging wayar,,ya ajiye wayar tashi a gefe ya kamo hanun ummi daketa kauda Kai ya kwantar da murya kmr wani karamin yaro yace "ummi am so sorry plss"ta sake dauke Kai batace komai ba,ya saki hanun nata ya durkusa gabanta ya hada hannaye yace "plss ummi kiyi hakuri,nida baby bamu kyauta ba Amma bazamu karaba plss"ta sauke ajiyar zuciya ta kamo hannayen nashi cikeda kulawa tace bakajin mgn Taheer gashi Layla itama ka fara koya mata irin wnn halin naka,yace "we're sorry ummi"ta jijjiga tace shknn ya wuce Amma gsky ya kamata ka ringa bari ana koya mata aiyukan gida mace cefa ita Kuma nan gaba kadan aure zatayi,yace "toh ummi"ta mikar dashi ya zauna gefenta tana fuskantarshi tace "Taheer",ya amsha da naam ummi snn tacigaba"sbd kaga na damu kayi aure shine kakemin haka?ya girgiza Kai da sauri yace wlh ba haka bane umm...ta katseshi da fadin inba don haka bane to meye dalili,kana da kudi kanada ilmi kanada lfy snn Kuma kanada kirar da ba kowacce mace ce zata kalleji bataji ka kwanta mata a rai ba then why bazakayi auren ba?ya shafa Kai yace ummi lokacin...bai gamaba ta sake katseshi da fadin dont tell me lokacine beyiba Kaine dai bakaga daman yiba Taheer Ina sane da matan dake binka kana wulakantasu kodai bakada lfy ne?ya girgiza Kai a hankali yace aah,

To meyasa bazakayi ba sai ka fadamin dalili Ina sauraronka,yai shiru kawai don bashida amsa,

Ay dama nasan bazakace komai ba Taheer Amma inaso ka sani ko mahaifinka da yanada rai bazaiji dadin wnn zaman da kakeyi ba aure ba Taheer lokaci Kara tafiya yakeyi yanxu shekara arba'in zakayi wnn watan meyasa bazakayi auren nan ba ko don hankalinmu ya kwanta,,ya kama hanunta cikin sigan lallashi yace InshaAllah zanyi ummi nan bada dadewa ba don Allah ki dena damun kanki akan mgnr nn pls,,,idan kanaso in dena damuwa then kayi aure,sa'anninka da kannenka duk sunyi aurensu with kids Kai Kuma kana nan ko auren ma bakayi ba,yanxu kalli nafeesa,kawarka ce Taheer shekara biyu ka bata Amma gata nan da yara hudu Kai har ynxu kana nan a matsayin saurayi u better wake up wlh wnn zaman ba inda zai kaika,yai Dan murmushi jin mgnrta na karshe yace InshaAllah kwanan nn ummi zakiji good news I promise u this,tace better in Kuma baso kake diyartaka ta rigaka yin auren ba,shidai baice komai ba sai dariyar yake da yayi,,ya mike a hankali yace ummi zan wuce clinic yanxu akwai patients din dake jirana,tace to saika dawo Allah ya kiyaye hanya ya amsada ameen Yana gab da fita dakin tace ita Kuma waccan data makale a sashenka saika turomin Ina nemanta,ya amsa da toh snn ya fita,,koda ya shiga bedroom dinshi bacci ya samu Layla nayi,ya karasa gadon a hankali a tsaya yana kallonta,fara ce sosae irin farin nn mai sirkin ja,hancinta dogo dan siriri dashi idanunta so Masha Allah dake daukeda yalwataccen gashin gira me sansti,ya sauke idonshi kan bakinta dake nan dan tsut dashi kmr an sammata,a hankali ya haura kan gadon yana shafa dogon gashinta daya hargitse sbd kwanciyan da tayi,ta dan turo baki ta sake rungume pillow tana Shirin juya mai baya ya mikar da ita zaune,ta wani narke tana kallonshi da sexy eyes dinta tace dady plss bacci nakeji wlh,yaja hancinta yace to ki tashi ummi ce tace a kiraki,,ta zaro ido da sauri hadda rufe baki da hannayenta tace la'ilaillallahu dady bakace zaka bata hakuri ba,Yana murmushi yace don't worry na bata hakurin ai kuma tace ta hakura kawai cewa tai in turoki maybe wani abun Zaki mata,ta kamo hanunshi tace are you sure dady?ya gyada Mata kai yace am pretty sure baby,tashi kije ba abinda zata miki Nima ynxu xan shirya in tafi clinic,,da sauri tace dady Dan girman Allah zan rakaka clinic din ay dama na dade banje ba,yace to je kiji me ummin zata saki idan kin gama kafin in fito sai mu tafi tare ta Mike da sauri tai hanyar fita tace toh daddy Allah yasa dai ummi ba fada zatamin ba,yabita da kallo yana murmushi saida ta fita ya sauke ajiyar zuciya snn ya nufi toilet don yin wanka.


STORY CONTINUES BELOW

Washe gari Wednesday cikin shirinshi na tafiya aiki ya shiga parlor bai samu kowaba sai tv dake aiki sai Kuma Mama hauwa dake shirya abinci a dinning ya gaisheta da Respect kmr yanda ya saba snn ya shiga dakin ummi,zaune ya samesu su biyu a gefen gado Layla nama ummin mgn kasa kasa yana shigowa tayi shiru,ya karasa kusada su yana kallonsu da alamar tambaya yace ummi me kuke cewa ne haka naji Ina shigowa kunyi shiru,tace meko muke cewa Taheer hira ne kawai takeyimin na yan skul dinsu,ya kalleta kmr dai bai yadda da abinda tace ba snn ya kalli Layla daketa faman murmushi yace ohk!ni zan wuce aiki yanxu,,da sauri Layla ta mike tace daddy ni zan bika clinic din don Allah,yace baby idan naje ma ba zama zanyiba theatre zamu shiga,,tace eh nidai zan bika daddy sai in zauna aboffice ko kuma inje wurin anty Sara daddy zaman gidan boring wlh idan baka nan nidai kar kace aah plsss,yai murmushi kawai yace to je dauko hijab dinki Ina jiranki,ta Mike da gudu ta fita a dakin tana fadin thank u dady,,yai dariya kawai ya kalli ummi yace to ummi zamu tafi,ummi ta tabe baki tace a dawo lfy ita Kuma zataci ubanta tunda cewa take gidan ba dadi idan baka nan,yace ummi bafa haka take nufi ba kawai dai tana nufin tafi jin dadi idan Ina nn,,koma dai menene sai naci ubanta wlh,yace ummi kawai wayon zagina ne wnn ni banga laifi a mgnrta ba,ummi tai dariya kawai tace wayon zagin nakne kaima don ubanka,ya kyalkyale da dariya kawai ya fice daga dakin.A bakin mota ya sameta har ta dauko mayafi tana jiranshi,ya kalleta from head to toe pencil trouser ne jikinta blue sai shirt dinta red ta dora kimono mai red n black kan kayan snn ta yafa veil dinta red duk rabin gashinta a waje,ya karasa still idonshi a kanta yace baby bana hanaki yin irin wnn dressing din kice zaki fita dashi ba ne?ta marairaice tace dady ai naga fa mota zamu fita Kuma muna zuwa clinic a office zan zauna ai ba cikin mutane zan shigaba,,ya daure fuska yace su mutanen dake clinic din ba mutane bane knn,ko Kuma su muharraman kine da Zaki shiga cikinsu a haka,,zatai mgn yace common go back and wear hijab before i knock u,,ta Dan turo baki tace to dady nidai kar ka tafi ka barni pls,sai ta juya ciki da sauri ta sako hijab dark blue me hannu ya dan wuce guiwanta kadan,ta dawo ta tarar har ya shiga mota itamata bude front seat ta shiga,yaima motan key mai gadi ya bude mai gate suka fita,sunyi nisa da tafiya wayanshi dake hanunta tanayin game ya fara ringing,ta Mika mai wayan tace daddy ana Kira,ya Dan kalli wayan ganin unknown number ne ya danja tsaki yace barshi ya gama ringing ki cigaba da game dinki,tai shiru tana kallonshi kmr zatace wani abu sai Kuma ta fasa,yana gama ringing ta cigaba da game dinta wani Kiran ya sake shigowa ta sake mikomai hankalinshi na kan titi yace reject it"a hankali tace why dady?yai mata shiru yacigaba da tukinshi,cikin sanyin murya tace daddy aunty Sameera ce koh,ya daga mata Kai kawai ita Kuma taci gaba,daddy meyasa kake Mata haka don Allah wlh tana sonka,she loves u sosae shiyasa Nima nake sonta daddy,,meyasa baka sonta pls?murmushin gefen baki ya saki ya juyo ya kalleta snn yace"wato ke ynxu baby har kin wani San so koh"ta Dan turo baki tace na sani mana dady Allah tana sonka,Nima Kuma tanasona kuma duk wulakancin da kake Mata tana hakura sbd tana sonka nidai Dan Allah kaima ka sota daddy,Allah inaso inga kayi aure Nima a haifamin kanne,,dariya sosae yayi daidai lokacin suka isa clinic din,ya gama parking suka fito,ya kalli hijab dinta da bai karasa kasa ba yace baki da wani hijab din daya Kai maki har kass ne?tace inadashi,guda nawa?two"yace kafin mu koma gida zamuje a siyo wasu naga wadan nn duk sun maki kadan,itadai batace komai ba,tunda suka shigo dama mutane  keta gaisheshi Yana amsa musu da faraa kmr yadda ya saba,itama tana gaishesu don kusan duk clinic din ba Wanda bai santa ba sbd Yana zuwa da ita time to time haka,,suka shiga personal elevator dinshi da zai kaisu 3rd floor inda office dinshi yake,suna shiga office kmr jira take tace daddy nidai am serious kan mgnr da mukeyi fa, seriously inason inga kayi aure ka samu mai kwantar ma da hankali kaim...tai shiru da mgnr ganin irin kallon da yake Mata,ta rufe bakinta da hannu tana dariya,ya dawo kusada ita ya zauna yana kallonta face dinshi da murmushi yace so babyna har tasan wani kwanciyan hankalin aure koh?ta boye fuskanta a kirjinshi tace Noo daddy niba abinda nake nufi kenan bafa,ya dagota Yana kallon fuskanta yace to fadamin me kike nufi,tasa hannayenta biyu ta boye fuskarta snn tace nidai kawai daddy inaso kayi aure Nima Kuma in samu siblings,,yana shafa gemunshi still face dinshi da murmushi yace alright zanyi auren nn dai tinda ynxu har babyna ma mgnr auren takemin,ya mike ya koma seat dinshi akai knocking kofa,come in"ya fada yana duba time wata nurse ce ta shigo ta risina ta gaisheshi ya amsa snn tace mgnr theatre din nan me doctor everything is ready Kai kadai ake jira,yace ok kice musu su shiga da ita theatre gani nn zuwa ta amsa da yes sir snn ta kalli Layla tace 'yar gidan daddy yau an tuna damu knn?Layla tai dariya tace Ina kwana anty Sara,,lfy Lou babyn daddy ya sch?ta Dan wara ido tace aunty Sara nayi graduation ai,shiyasa ma kikaga bana zuwa sbd Ina exams ne,,to Masha Allah Ashe babyn daddy an fara girma to Allah ya Sanya alkhairi ta amsada ameen snn ta fita,ya mike tareda daukan lab coat dinshi yace baby zamu shiga theatre ynxu ki zauna nan sai ki kunna kallo,ta makale kafada tace dady nidai zanje wurin aunty Sara,yace ohk ki kullemin office din tohta amsa mai snn ya fita don ana jiranshi.

Yan fita ta dauki phone dinshi da har ynxu ke hanunta ta fita tai locking office din kmr yanda yace dnn ta tafi Nurses Station,,tana gab da shiga wurin taji an kirata,ta juya a hankali tana neman me Kiran nata,lokaci daya ta saki murmushi tace laa uncle Salees(Salees student doctor ne yake house man ship dinshi a asibitin)ya karaso kusada ita Yana murmushi shima yace umh 'yar gidan daddy dama ana ganinku?tace ana ganinmu mana uncle ay sbd Ina exams ne daddy ya dena xuwa Dani Amma ynxu na gama,yadan wara ido yace wow!congratulation sweetheart Allah yasa albarka,tace Ameen,,kallonta kawai Salees keyi don ba karamin burgeshi yarinyar keyi ba,ba karamin missing dinta yai ba da bata zuwa,,ganin kallonta kawai yake tace umh uncle bari inje wurin aunty Sara har ta juya yai saurin tsayar da ita yace wait mana,,inason muyi wata mgn fa dake dama,ta wara ido kadan sai Kuma tace mgn Kuma uncle?wace irin mgn kenan?yace let's go to my office,,tayi shiru kmr bazata jeba tace ai daddyna fada zaiyimin,yace daddynki ya shiga theatre madam and I assure u bazai fitoba sai nan 2 hours beside Saida na fara tambayanshi ma kafin inxo wurinki,are u sure?ta fada tana kallonshi yace am very very sure,,tace alright muje,nan suka tafi office din nashi.

Da kanshi yaja Mata kujera yace bismillah ba musu ta zauna shima ya zauna opposite to her yace baby I missed u sosae,,dayi Dan murmushi tace sunana Layla yace to Layla nayi missing dinki da yawa da yawa hope dai ynxu kullum zaki ringa biyo dad dinki kuna tahowa tunda exams ya kare,ta daga mai kai alamar eh,ya wani sauke ajiyan zuciya hadda Dora hanu a saitin heart dinshi yace thank God,,ya cikata da surutu tun bata saki jikiba har daga karshe ta ware yanata bata labarai ita Kuma tana dariya sai admiring kyanta yake.


Taheer...


Kusan 2 hours sukai spending kan matar kafin su gama,Yana fitowa direct office dinshi ya nufa gaba daya hankalinshi na kanta,,koda yaji office din a rufe gashi duk wayoyinshi na ciki,wata nurse ya samu yace ta Kira mai sister Sara ba bata lokaci saiga Sara tazo,yace kicema baby na dawo ta kawomin key"cikeda girmamawa tace ai batazo wurina ba sir Amma bari in duba office din Dr Salees,,har ta fara tafiya ya dakatar da ita yace u mean tun dazu tana tare dashi knn?..No sir am not sure kawai dai nasan tinda batazo wurina maybe sun hadune shine taje office dinshi ya firzar da iska snn yace it's okay u can go bari in duba da kaina ta amsa mai snn ta juya ta tafi shi Kuma ya nufi office din Dr Salees din,,,tun daga bakin office din yakejiyo dariyarta snn ga mgn nn kasa kasa yana jiyowa,wani irin bugawa zuciyarshi tayi yai saurin dafe kirjinshi tareda jingina a jikin bango,,ya Kai kusan minti 3 a haka kafin ya bude kofan ko knocking beyiba,,tana zaune kan 2 seater dake office din shi Kuma Yana zaune dirshan a kasa yana facing dinta ya wani sunkuyo Yana mata mgn a hankali ita Kuma tana murmushi,,wani irin jiri yaji ya daukeshi yai saurin dafa bango still daya hanunshi dafeda kirjinshi,,jin motsin mutum yasa gaba dayansu suka juyo Layla da sauri ta karaso inda yake tace daddy what's wrong are u okay?yai kokarin daidaita kanshi fuska ba walwala yace bani key"ta koma inda key din yake da sauri ta dauko kafin ta juyo har ya fita a office din tabi bayanshi da sauri ba tareda ta dauki wayanshi data bari nan ciki ba,,,a kofar office dinshi ta sameshi ta karasa ta bude office din tana kallonshi kafin tayi mgn ya shige ciki ya barta nan tsaye,jiki a sanyaye ta shiga itama,Yana kwance kan 3 seater sai yanxu ya cire hanunshi dake dafeda chest dinshi idanunshi na kallon sama,,tana kokarin zama kusa dashi yace"Don't u dare"ba da karfi yai mgnr ba Amma a yanayin daya fada tasan ba karamin bacin rai yake cikiba,,tai saurin matsawa baya jikinta na rawa sai kawai ta durkusa a wurin tafashe da kuka,,ya runtse ido baya son jin kukan nn Sam,,har ynxu zuciyarshi bata dawo normal ba,,ya mike zaune Yana kallonta da idonshi daya sauya kala yace where is my phone?ta share hawayen idonta ta mike zata fita yace Ina zakike Kuma?ta juyo tana kallonshi tace zanje in dauko wayan ne,na barshi a can,,,ya mike zuwa table dinshi ya Kira messenger yace ya dauko mai wayan snn ya koma ya zauna,,bayan 2 minutes messenger ya kawo mai wayan ya dau keys dinshi Yana kallonta yace muje"ba musu ta shiga gaba Yana bayanta suka fita daga office din,yai locking snn suka shiga elevator,,sai share hawaye take tana sheshsheka a hankali.

Ko staff dinshi dake mai Allah ya kiyaye hanya yau bai amsa su kmr yanda ya saba ba ya shiga mota kawai itama ta shiga suka fita daga clinic din,ko a cikin mota sai Satan kallonshi take tana share hawaye duk yana lurada ita amma baiyi mgn ba,yasan indai zata cigaba da kukan nn to raunana mai zuciya zatai shi Kuma yafison yanuna Mata abinda ta aikata na daidai bane,da wnn tunanin ya isa gida ko ciki bai shigaba yai parking idonshi a kan hanya yace "shiga gida"ta juyo tana kallonshi idanunta duk sunyi ja tace daddy pl...bata karasa ba ya katseta ta hanyar daga Mata hanu tayi shiru tana sauke ajiyan zuciya ya sake cewa ki shiga gida mana u're wasting my time,,a hankali ta bude motan ta fita ko kullewa batai ba ta shiga gida da gudu,,ya kwantar da kanshi kan starring motan yana jan numfashi,yafi minti 4 a haka kafin yaja motan ya koma clinic.Koda ya koma clinic din gaba daya kasa aikata komai yayi duk zuciyarshi ba dadi,dama shi haka yake indai ranshi ya baci to gaba daya al'amuranshi tsayawa suke,ya mike kawai ya dau car key dinshi ya fita,ya shiga mota ya bar clinic din,Saida ya hau titi snn yai dialing number da yayi saving da"Friend"a wayarsa ya sa a speaker ya ajiye wayan kan laps dinshi yana cigaba da tuki,a daya bangaren akai picking da sallama,bayan sun gaisa yace Yusuf wai har yanxu baka dawo bane?Wanda ya kirada Yusuf din ya amsa da"na dawo jiya da dare wlh"banyi niyyan kiranka ba kawai da yamma zanje in gaida ummi sai in biyo ta office dinka"ya sauke ajiyan heart snn yace "ynxu kana Ina?"at home,anything for me?yace ok gani nn xuwa bai jira abunda zaice ba ya kashe wayan snn ya dauki hanyan dazai kaishi gwarinpa inda gidan abokin nashi yake,,tafiyan mintina kalilan ya kaishi gidan ya har ciki ya shiga da mota yai parking Amma bai fitoba ya shiga dialing number Yusuf din,shima baiyi picking call dinba ya fito Yana sanyeda ash jallabiya,ya karaso wurinshi da murmushi a fuska yace "welcome bismillah muje ciki,Taheer yace no ba sai na shigaba kawai kace ina gaida madam da yara,Yusuf ya wani zare ido yace are u for real?kazo har cikin gidan nawa ka wanice bazaka shigaba ai kaima kasan wasa kakeyi wlh,bai sake cewa komai ba ya bishi suka shiga ciki,,nabila matar Yusuf ta cika masu gaba da kayn ciye ciye snn ta zauna suka gaisa da Taheer tace yasu ummi da Layla?yace suna nn lfy wlh,, madallah ace muna gaishesu pls muna nn shigowa InshaAllah,yace ba damuwa Allah ya kaimu,nan ta mike ta bar musu parlon,,Yusuf ya kalleshi da kyau yace to Ina jinka meke faruwa?ya Dan kalli Yusuf din da mamaki kafin yai mgn ya sake cewa tunda na ganka a haka nasan for sure akwai abinda ke damunka,,ya sauke numfashi kafin yadanja siririn tsaki yace baby ce wlh"wace babyn?ya juyo yadan harareshi kafin yace wace mace nake kirada baby idan ba Layla ba,ohk what about her?wani tsakin ya Kara ja yace could u imagine wai yarinyar nn na gani da wani student doc a clinic daxu ya wani sata gaba a office dinshi yana Mata surutu ita Kuma sai dariya take mai,har office dinshi fa ya kaita sbd bashida hankali,wlh badon nakai zuciyata nesa ba da korashi zanyi daga clinic dina don bazan dauki iskanchi ba wlh,,Yusuf Saida ya bari ya gama mgn snn ya gyara zama yace"so har ynxu kana nn a yanda na sanka knn,fisabilillahi Taheer kanama kanka adalci knn?duk kabi ka dorama kanka abinda kaima kasan ba me yiwuwa bane...a fusace Taheer dake kallonshi yace "mene rashin yiwuwan nashi wai,meyasa kakemin haka ne for God sake,idan bazaka tayani son abinda nakeso ba bai kamata ka ringa kokarin discouraging dinaba gsky,,Yusuf yai shiru ganin yanda yake mgn rai a bace,sai kuma yai Dan kasa da murya yace"ba haka nake nufiba Friend,ya kamata ka fahumceni,Ina guje maka abunda zai jefa rayuwanka cikin wahala ne,kaga dai na farko yarinyar nn kallon uba take maka mahaifi ya kake tunanin zakazo Mata da mgnr SO ta yadda bayan ita ba wnn kallon take maka ba,na biyu Kuma iyayen yarinyar nn,kaga sunyi maka Kara iya Kara a kanta suka dauketa tun tana karama suka baka kuma basu taba nuna maka wai sunfika iko da itaba,hatta 'yan uwan mahaifinta ba Wanda yake nuna mka Kai din ba ubanta bane to ta yaya kke tunanin zakazo musu da mgnr kana son aurenta su yadda,dukda addini bai hanaba Amma gsky wnn abune mai kmr wuya, beside yarinyar nn qarama ce Taheer mgnr gsky yarinyan nn tayima qanqanta,ga babes nan Wanda suka amsa sunan babes suna binka kmr zasu ma sujada, matured,amma ka tsaya zaka bata lokaci akan 'yar cikinka, ya kamata ka tsaya kayi tunani Taheer kasan abinda kake ciki,yanxu ka gwammace kayita zaman jiran abinda bakada tabbas din samunshi kan Wanda kake da tabbas?look at me mana,age mate dinka ne ni amma shekarana 10 da aure da yara 4,ita kanta uwar yarinyar nn qanwarka cefa ka bata good 2 years dukda dai ita mace ce amma yaranta nawa ynxu,kafiso kayita zama a haka kana batama umminka rai knn,,ynxu ko bakason auren nn kodan farin cikin ummi bai kamata ka ajiye wnn batu ka samu mace ka auraba,meka nema ka rasane a rayuwa?"Babu,komai Allah ya baka,kanada kyau kanada kudi kanada ilimi snn ga Mata nn dake sonka duk kaki basu dama kan yarinyar da ka raineta a hannunka Taheer wane irin sone wnn don Allah da yake neman zautan min da abokina,I want my old friend back,u have to think about this Taheer pls,"tunda ya fara mgn idanun Taheer a lumshe Amma jin duk wata mgn daya yake tamkar saukan guduma kan kirjinshi,yasan duk abinda abokinshi ya fada gsky ne Amma abinda Yusuf ya kasa fahimta shine da ace zai iya rabuwa da wnn tunanin da tuni ya yakiceshi a zuciyarshi kodan shima ya samu sukuni Amma hakan ba mai yiwuwa bane,it's not that easy ace ka rabu da abunda ka kwashi tsahon shekaru kana kauna,shi kanshi at times yakan ce zuciyarshi bata mai adalciba ta rasa wa zataso duk fadin duniya sai yarinyarda ya raina a hannunsa,yarinyarda ta daukeshi matsayin mahaifi,so kuma mai tsanani irin wnn"Taheer"Yusuf ya katse mai tunani ta hanyar Kiran sunanshi,yq bude idanunshi da sukai ja yana kallon Yusuf din mgn yakesonyi Amma ya kasa,sai kawai ya komar da iadanunshi ya rufe tareda jingina da bayan kujera for some minutes snn yai gyaran murya a hankali yace"naji duk abinda ka fada friend and nasan gsky kke fadamin Kuma InshaAllah zanyi kokari inyi kmr yanda kace but please ka tayani da addu'a kaji,Ni kadai nasan me nakeji wlh InshaAllah Allahn daya doramin shi zai yayemin,,maganganunshi ba karamin tausayi sukaba Yusuf yai Dan murmushi yace InshaAllah zan tayaka and kayi kokari ka rage damuwan nn cox it will affect ur health,ya gyada mai Kai alamar zaiyi,ya jima a gidan don jiyayi bayason komawa gidan gaba daya,sai wurin 6 snn ya nufi gida,shima bai shigaba sbd anyi magrib yana hanya sai kawai ya wuce masjid bai shigo gidan ba Saida akayi isha'i,,a hankali yake tafiya tamkar mara lfy har ya iso parlor,ummi ce zaune da system kan laps dinta tana video call Banda murmushi ba abinda takeyi,ya karaso ya zauna yana leka system din don ganin da wa take mgn,,wasu kyawawan yarane suka bayyana babban cikinsu baifi 15 yrs ba sai dayan da bazai wuce 12 sai Kuma 'yar karamarsu da bazatafi 7 ba,yaran na ganinshi suka fara rige rigen Kiran daddy kowa na gaishesi,dukda bacin ran da yake tare dashi Saida ya saki murmushi yana kallonsu suka gaisa Yana tambayansu skul,babban cikinsu ne yace daddy next week zamuzo Abuja muma idan anyi holiday,still Yana murmushi yace to Allah ya kaimu Al'ameen ina maminku?tana kitchen,yaron ya fada,yana Shirin mikewa zai kirata sai gata ta fito ta zauna gefen yaran ta matso da system din gabanta yanda zata gansu da kyau tana kallon ummi da fara'a tace "ummina barka da dare,,barka dai nafisa ya gida ya yara?wlh alhamdulillah ummi muna nn zuwa next week da zaran yara sunyi hutu,ummi tace to Allah ya kawoku lfy ta amsa da ameen ummina snn ta kalli Taheer dake kallonta shima ta daga mai gira tana fadin ba gaisuwa?ya zare ido sasai ya kalleta snn ya kalli ummi yace ummi kinji yarinyar nn wai Ni zan gaisheta niba yayanki bane?ummi ta tabe baki tace to mene ne idan ka gaishetan Taheer,,ya sake zare idon yace ummi qanwa tace fa,,to da take qanwarka ai tafika daraja ko a wurin Allah ynxu,kalleta fa da aurenta harda 'ya'ya nta mene laifi idan ka gaisheta,ai ta karbe girman ynxu,,nafisa dake dariya tace yawwa fada masa ummina,itadai bata sake cewa komai ba ta mike ta barshi a wurin,ya janyo system din ya dora gab dashi yace wato rainin da kikaimin har yakai haka koh?tana dariya tace wasa nefa bro yanxu fadamin ya kke ya aiki,,aiki alhamdulillah ya kids dina,tace suna nn lfy Ina babyn taka yau ban ganta kusa dakai ba,ya Dan shafa Kai yace laifi tayi nake fushi da ita nasan tana daki a kwance,,nafisa tace haba koda naji,Ashe ana fushi da 'yar lelen dama,dariya kawai yayi yace kinga je kiji da yaranki nima ynxu xanje in kaimata abinci nasan duk yau bazataci komai ba indai bani na bata ba,,tace to ay shknn sai ka dawo ni yarana ba shagwababbu bane irin taka sai anjima,sukai sallama snn ya ajiye system din ya mike zuwa dinnig,abinci ya xuba a plate yasan for sure bataci komaiba yau ya nufi dakinta dashi,tana zaune ta hada Kai da gwuiwa sai kuka take,zuciyarshi ba karamin karyewa tasoyi ba ganinta a haka Amma ya daure ya karasa ciki,Saida ya ajiye abincin kan stool snn yace"zo kici abinci"ta dago da sauri don bataji shigowarshi ba,ta matso a hankali ta sauke legs dinta kasa tana share hawaye tana kokarin mgn yace I don't want to hear anything,just eat,ta sunkuyar da kanta tana shesheka kafin a hankali ta faracin abincin kmr tanacin magani Kuma bata bar hawayen da takeba,,duk yana jinta yai pretending sai Danna waya yake yanata yaki da tausayinta dayakeji,,kadan taci tace ta koshi yace saita Kara haka nan da kyar yaci rabi tace ya isa,bai Mata musuba ya bata ruwa Tasha snn yace shiga kiyi brush ki fito Ina jiranki,,jiki ba kwari ta nufi toilet tayo brush din kafin ta fito ya dauko Mata sleeping dress ta karba tana Shirin cire kayan a gabanshi yace shiga bayi ki cire,,nn ma ba musu ta shiga tasa kayan ta fito"kwanta"ya fada yana nuna Mata godon,a hankali ta hau ta kwanta ya janyo duvet ya rufeta dashi yai addu'a ya tofa Mata kmr dai yanda ya saba snn ya kashe wutan dakin ya fita,aiko Yana fitata sake rushewa da kuka,,shima dakin ummi ya shiga yi Mata Saida safe tace Layla fa takicin abinci babu yanda banyi da itaba wlh takici wai batada lfy,nadai bata paracetamol nace ta kwanta idan ka dawo saika dubata,yace eh na bata drugs ynxu,,to taci abincin ne?shima taci nasan ynxu bacci zai dauketa,,to Allah ya sawake kaima ka kwantar da hankalinka don Allah zata samu sauki ai naga duk ka zama kmr mara lafiyan kaima,yace InshaAllah ummi Saida safe,Allah ya tashemu lfy,har ya fita ummi na binshi da kallo tasan for sure wani abun na damunshi.+


Daren nan dai dagashi har ita ba Wanda ya samu baccin kirki,shi ya kwana tunanin maganganun da sukai da Yusuf tareda neman mafita ita Kuma ta kwana tana kukan fushin da yakeyi da ita dama duk ranar daya dauke mata wuta haka take rasa sukuni har sai sun shirya.


Wurin karfe sha daya yana tsaye gaban mirror yana combing gashinshi yayi kyau sosae cikin faran shirt daya Dan kama jikinshi long sleeve,sai trouser dinshi black,dogo ne sosae irin mazan da ake cema masu zatin jiki,kalan fatanshi ba me haske ba Kuma ba fari tass ba,yanada manyan idanu farare qal dasu sai dogon hanci dayai daidai da fuskarshi,bakinshi madaidaici sai qasimba me daukeda gemu da suka sake qawata fuskan nashi,ya gama ya feshe jikinshi da designer perfumes dinshi ya dau phone dinshi snn ya fita zuwa part din ummi,tana zaune parlor suna kallo itada Mama hauwa,ya gaishesu Yana kokarin zama ummi tace Layla fa batayi bacci ba jiya,bayan ka tafi naje dakin zazzabi ya rufeta sosae dashi ma ta kwana wlh,sai safiyar nn baccin ya dauketa,,da sauri ya mike yana dafa goshi yace ya Salam!meyasa baki kirani ba ummi,,ita ta hana in kiraka wlh wai kar in tasheka a bacci gaba dayama ta hanani tashi in dauko wayan wai bazan barta ita kadai ba,ya nufi dakin da saurinshi ya shiga,tana kwance tsakiyar gado tana rungume da teddy dinta,,lokaci daya murmushi ya kubce mai,ganinta kawai can flush his sadness,a hankali ya zauna gefen gadon yana kallon duvet din data tattareshi gefe,murmushi ya qara saki ya rasa me yasa batason lulluba ba ko kadan,haka take tun tana karama,lokacin tana kwana tare dashi yana lullubeta dama zata yaye,ya shafa kanshi yama nemi bacin ran da yake ciki yarasa,dama yasan fushin nashi ba wani tsayi zaiyi ba yamayi kokari daya iya jurewa har haka,yakai hanu yana feeling temperature dinta yaji normal ya sauke ajiyan zuciya me karfi ta farka firgigit don kmr a mafarki taji ajiyan zuciyan nashi.Fuska daukeda murmushi yake kallonta sai kawai ta fada jikinshi ta fashe da kuka...ya rungumeta gam yana shafa gashin kanta yace" it's ok kukan ya isa haka nn...ba tareda ta dagoba tace "am so sorry dady kayi hakuri don Allah"ya sake cewa "it's ok ynxu fadamin akwai inda ke maki ciwo?ta girgiza Kai alaman aa,ya dagota Yana kallonta yace" baby are u sure ba inda ke maki ciwo ynxu,ummi tacemin kin kwana da zazzabi jiya"ta langabar da kai "tace ai kaine kaketa fushi dani daddy Kuma na baka hakuri kaki hakura"yaja hancinta yana murmushi yace"to ynxu na dena fushin baby,shima zazzabin ya tafi?ta daga Kai tana murmushi "alright"ya fada snn ya mike zuwa toilet dinta,ruwan wanka ya hada mata yasa Mata maclean a brush snn ya fito yace oya shiga kiyo wanka I'll wait for u here,ta sauka daga gadon tana kokarin cire dan rigan baccin jikinta yace"baby wai bana hanaki cire kaya gaban mutane ba?ta Dan turo baki tace daddy ai ba kowa a dakin naga,it's only me and u"ya gyara zama yana kallonta fuska a daure yace "ko keda wane ban yadda ki cire kaya gaban wani ba ko gaban ummi ne"toh daddy"ta fada snn ta nufi toilet,,bayan kaman 6 mins ta fito daure da dan towel dinta iya cinya,ya taso ya kamo hanunta ya zaunar gaban mirror snn ya janyo mata lotion dinta na shafawa ya miko mata karamin towel na goge jiki yana smiling yace "yi sauri ki shirya toh"ba musu ta tsane jikinta snn ta fara shafa lotion din kafin ta gama ya fiddo mata kaya har inners,,ta sa snn ta koma gaban mirror ta shafa powder ta goga eye pencil a idonta sai dan chapette a lips dinta,kallonta kawai yake riga da skirt ne na atampa dinkin ya zauna daidai a jikinta...ta Mika mai dankwali tana murmushi tace "daura min daddy"...baice komaiba ya karba ya zaunar da ita gaban mirror ya shiga daura Mata....dama ya saba daura Mata dankwali... hakanan yana zaune part dinshi ma wataran zatazo tace ya daura mata tun bai iyaba har ya fara koya....ta juyo tana kallonshi da faraa bayan ya gama daurin  tace"daurin yayi kyau daddy,thank u"ya kama hanunta suka fita parlor....saida ta gaisa da ummi da Mama hauwa snn yace suje dinning taci abinci....ummi ta kama haba tana kallon hauwa tace"kinga yarinya kmr ba itace ta kusa sume min ba jiya Amma ki ganta ynxu kmr warce zataje gasar kyau sbd uban ya shiga ya lallabota....mama hauwa tayi dariya kawai.

Shi yaja Mata kujera ta zauna snn yayi serving dinta yace "oya yi sauri kici unguwa nakeso muje"tana kallonshi tace "daddy Kai kayi break fast din ne?....shi sai ynxu ma ya tuna rabonshi da abinci tun break fast din jiya....yaja kujera ya zauna itama tayi serving dinshi snn suka faraci.

Parlor suka dawo bayan sun kammala yace baby je dauko hijab dinki zamu fita....da murnarta ta tafi daki ummi na kallonshi tace in Kuma zakuje? shopping zamuje ummi ko zakije kema?ta girgiza Kai tace ni bazan iya wnn gantalin nakuba Taheer...gadai sako zan bada sai ku biya gidan Ramla ku Kai Mata.... zan kirata sai in Mata bayani.....yace "ba damuwa ummi sai ki bama baby ta taho dashi"....to shknn sai Kun dawo"snn ta mike xuwa dakinta...ta dauko saqon tabama Layla kmr yanda yace......a cikin mota ta sameshi ta bude front seat ta shiga itama....gidan Ramla suka fara zuwa bayan yayi parking yace"baby yi sauri ki Kai mata sakon ki fito"tace

Daddy bazaka shiga ciki ba"....ya Dan shafa Kai yace kice ina gaisheta kawai....ba saina shigaba...kafin ma tayi mgn ya bude mata mota yace "oya jeki fito Ina jira....ta sauka ta shiga gidan bayan some mins suka fito tareda Ramlan da katon cikinta don da gani ta kusa haihuwa.... ta karaso side dinshi tana smiling tace yaya Ina wuni"....ya amsada lfy Lou Ramla ya jikinki?...ta danyi murmushi tace "Alhamdulillah ya aiki"....aiki alhamdulillah muna sauri shiyasa ban shigoba...tayi murmushi kawai don tasan dama koba sauri yakeba bai zama lallai ya shigaba....gidan Yaya nafisa data girmeta ma bai shiga balle ita da yake ganinta yar karama....ya zaro kudi daga aljihu ya Mika Mata... tayi godia snn yaja motar suka bar layin....Saida suka hau titi Layla tace"dady Ina zamuje?....ya juya ya kalleta sai yadanyi murmushi yace" zance Zaki rakani".....ta wara ido hadda gyara zama tace "are u for real dady?don Allah da gske?....kawai taga ya kwashe da dariya sai ta koma gefe tana turo baki....daidai wani boutique na kayan mata taga yayi parking.....ta juyo da sauri tana kallonshi ya daga Mata gira yace"ba nace zamuzo a siya hijabs ba"... dan murmushi kawai tayi...yaa bude mota ya fita itama ta fito suka shiga ciki.+


STORY CONTINUES BELOW

Bangaren Hijabai suka fara nufa.....ya shiga deban mata maka makan Hijabai Yana zubawa cikin basket..... itadai kallonshi kawai take da mamaki ganin uban hijaban da yake diba da alama ko irgawa bayayi....yana gamawa da nan suka nufi wurin dogayen riguna.....nanma ya ringa daukan duk Wanda tai masa kyau Yana tarawa.... itako murmushi kawai take tana kallonshi....dama sun saba indai zasuje shopping to shi zai dauka mata komai Kuma luckily duk abinda ya dauka yanayi Mata kyau and daidai size dinta yake dauka.....daidai da panties da bras nata duk shi yake siya....yasan perfect size nata na koma da komai....bayan ya gama da nn sai shoes da bags....nanma ya Debi son ranshi snn yace" muje wurin cosmetics"....ta riko hanunshi tace" dady ya isa haka please,wancan ma daka siyo ko half dinsu banyi amfani dashiba"....ya zare hanun nashi yace muje dai ko perfumes sai a dauka.....bata sake mgn ba tabi bayanshi..... tasan kota ce aah ma ba yadda zaiyi ba......a ranta sai ayyana irin son da daddyn nata yake mata take....... ita badon an fada Mata bashi ya haifeta ba da bazata taba ganewa ba cox son da yake Mata is beyond expectation shiyasa itama duk duniya babu Wanda takeso kmr shi.....ko iyayenta batajin tana musu son da take mai ko don tafi sabawa dashi ne oho?......haka tasa mai ido ya debi perfumes dinma son ranshi snn suka tafi counter......ya biya kudin through pos snn aka Kai musu kayan mota suka tafi.....basuyi nisaba ya kalleta yace"what do u want to eat?....hadda wani gyara zama tace "dady ice cream nakeso da chocolate"....ya girgiza Kai yace"No Banda wnn fadi wani abun dae".....ta marairaice dady Allah nidai su nakeso ko kadan ne ka siyamin plss.....ta karashe mgnr da sigar lallashi.....ya kalleta ganin yanda ta wani narke yace"in siya maki ice cream da chocolate salon in period dinki yazo kisani a gaba kinamin kuka kina cewa zaki mutu koh....i won't".....ya karasa yana makale mata kafada kmr yanda takeyi.....tayi murmushi tace dady don Allah ko kadan ka siyamin plss".....naji zan siya amma ba dayawa ba".....tace thank u my dady.....daga nn bai sake cewa komaiba har suka isa wani eatry me kyau....bayn an kawo musu abinda sukai order sun faraci kenan ya daga kanshi.....kmr ance ya waiga gefenshi yaga wani saurayi zaune Dan nesa dasu......banda kallon Layla ba abinda yake....ko abincin dake gabanshi bai taba ba yayi concentrating kawai a kanta yana kallo kmr ya samu tv....wani irin bacin rai yaji ya tasomai......ya maida kallonshi ga Layla dake cin abincinta hankali kwance.....duk sai yaji abincinma ya fita a ranshi.....batai aune ba sai gani tayi ya mike ya kama hanunta Yana kokarin janta subar wurin... tace dady what's wrong.....bakaci abincin bafa.....ko kallonta baiyiba ya cigaba da janta har suka fita a wurin....ya bude mota ya sata ciki snn ya zagaya shima ya shiga yaima motan key suka fita a eatry din....har suka hau titi Layla kallon mamaki take mai....bata San meya bata ranshi ba all of a sudden....cikeda damuwa tace dady don Allah me ya faru?...ya juyo ya kalleta sai yayi Dan murmushi yace"it's nothing kawai naji banson wurin ne....don't worry zanyi mana takeaway a wani wurin saimu wuce gida"....batace komaiba har suka isa wani eatry din wnn karon shi kadai ya shiga sai gashi ya fito da ledoji ya zubasu back seat snn ya shiga suka dauki hanyar gida.


The journey was silent har suka isa gidan duk suka fito bayan yayi parking..... ya shiga daukan kayan yana shiga dasu itama ta dauki Wanda zata iya ta shiga ciki.

Ummi da mamaki fal fsukanta take kallonshi bayan ya gama shigo da kayan....ta shiga binsu da kallo daya bayan daya sai Kuma ta kai dubanta gareshi tace "wnn kayan na meye ni Maryama!!....lefe zaka fara hadawa ban saniba?...dagashi har Layla dariya mgnr ummi ya basu...da kanshi ya shiga bude mata ledojin Yana nuna Mata kayan ciki.... ita Kuma Layla ta samu ta dauki ice cream da chocolate dinta ta sulale dakinta....still da mamaki a fuskan ummi tace" ynxu Taheer Ina Layla zatakai wnn uban Hijabai haka sai kace kayan sawa....idan aka hada da wanda take dasu wlh zasu iya yin talatin" yace...."ummi ai basa yawa....nafiso duk inda zataje ta ringa sasu.... ummi kinsan Mata masu kyau sunada hadari sosae....Kuma duniya ynxu ta lalace.... yara qanana ma ana raping dinsu balle baby data fara girma..... duk inda ta shiga fa kar kiso kiga yanda maza ke kallonta..... ni wlh abin ma har tsoro yake bani.....wai kowa dai ynxu burinshi ya auri mace me kyau mtsssww"....ummi ta danyi shiru tana kallonshi kmr me nazari sai Kuma tace" hakane kanada gsky Kuma....Allah ya tayamu kiyayewa" ya amsa da ameen "yana kokarin mikewa ummi tace "koma ka zauna zamuyi mgn...ba musu ya koma gabanshi har faduwa yake don yasan dai tatsuniyar gizo baya wuce koki"...ya mgnr da mukayi dakai Taheer"...ya dan sosa keya snn yace "tana nn ummi...an kusa InshaAllah"....ka tabbatar ba wasa da hankalina kke ba?...yace na tabbata ummi"...shknn Allah ya zaba mafi alkhairi.


Kwanakin da suka biyo baya Sam baya samun hutu sosae sbd aiyuka da suka mai yawa kullum yini yake a clinic.....yau ma bai samu barin clinic dinba sai around six....Yana zuwa gida part dinshi ya wuce direct yayi wanka yayi changing xuwa farar riga armless da trouser dinshi three quatre shima white ya kwashi phones dinshi ya nufi part din ummi....bai samu kowa a parlor ba ya wuce bedroom din ummi nan ma bata ciki ya dan zauna for about 5 mins ko toilet ta shiga nn ma bai ganta ba sai ya mike kawai ya nufi dakin Layla wondering ina ummi ta shiga at this time of the night.....tun kafin ya shiga dakin ya fara jiyo kukan Layla.... ya karasa ciki da sauri....tana kwance jikin ummi hannunta biyu dafe da mararta sai kuka take tana fadin zata mutu....yai saurin xuwa ya zauna yana kallon ummi cikeda tashin hankali yace ummi what happened?....wlh maranta ne ke ciwo Taheer"....ya janyota jikinshi har idanunshi sun Dan canxa kala....ta kankameshi hawaye na fita a idonta tace "wayyo daddy marata...mutuwa zanyi dady"....rungumeta shima yayi sai Kuma da sauri ya ajiyeta yace "ummi Bari in dauko allura in dawo....ta rike hanunshi still tana kuka tace dady nidai kar ka tafi pls...dn Allah ka zauna"Bai sake cewa komai ba kawai ya dauketa yai part dinshi da ita ummi na mara musu baya....ya ajiyeta kan bed dinshi snn ya nufi fridge din da yake ajiye drugs da injections ya lalabo alluran da zai Mata... ya dauko syringe a first aid box duk ya diririce da kyar ya gama withdrawing injection din ya dawo kan gadon yace "ummi riketa"...ba musu ummi ta kwantar da ita rub da ciki ta rike hannayenta.... a hankali yayi Mata alluran sai kuka take....bayan ya gama ya zauna gefen ummi tareda dafe kai da hannayenshi biyu....har ya fara developing fever....ummi tagyarama Layla kwamciya ta rufeta da duvet snn ta dafa kafadanshi cikin sigan lallashi tace"don Allah ka dena wnn damuwan Taheer....ya kamata ace by now ka saba da ciwon maran nn nata tunda haka takeyi every month... Kuma kai da kanka kasan it's normal da zaran tayi aure zata dena....ko kana suspecting wani abun ne?.....da sauri ya girgiza mata kai yace "ba abinda nake suspecting ummi.... am just worried about her... tanashan wahala sosae"....ummi tayi murmushi ta shiga patting dinshi har ya dan sakko snn tace Bari ta tafi tunda Layla ta samu bacci.....ya dade zaune a wurin yanata kallonta tana bacci sai can dayaga dare yayi ya mike jiki a sanyaye ya shiga bathroom yayi wanka yasa pyjamas dinsa snn ya kwanta can karshen gadon....ya jima sosae Yana kallonta kafin bacci ya daukeshi.+


Can cikin dare ta farka tasa mai kuka wai bayanta na ciwo Kuma....ya bata drugs Tasha snn ya samu ya lallabata ta koma baccin.... shi kuwa kasawa yayi daga karshe sai kawai ya mike zuwa bathroom ya dauro alwala yazo ya fara sallah bai komaba saida yayi sallahn subhi.


Har wurin 10 Layla bata tashi ba shi Kuma ya kasa barin inda take Yana nn zaune sai kallonta yake kmr tv....sai after 11 ta tashi lokacin ummi bata dade da fita ba....ya hada Mata ruwa tayi wanka ta shirya nn dakinshi snn ya kama hanunta zuwa part din ummi ya bata abinci da kanshi taci snn tasha drugs ta sake kwanciya.... dukda dai ciwon bai Kai na jiyaba amma still ya kasa barin inda take don gani yake kmr wani abu zai sameta idan ya matsa...motsi kadan zai fara tambayan"what's wrong baby are u okay?...ba inda ke maki ciwo...do you need something...ummi ma na nn kusa dashi suna jinyan tare...lol😝


Bayan ya dawo daga masjid sallahn zuhr yanata sauri ya koma gida wai don karta bukaci wani abu baya kusa...Yana shiga gidan yaci karo da Yusuf zaune parlor shida ummi...ya karaso ya zauna shima suka gaisa duk hankalinshi na kanta...ummi ta mike zuwa dakin Layla su Kuma suka koma part din Taheer...Duk hiranda suke da Yusuf dai dai da second daya hankalinshi bai bar kanta ba.... har sukaje masjid sukayi sallan asr snn Yusuf  ya wuce shima da sauri ya nufi part dinsu don yaga jikinta.

Saida Layla tayi kwana uku snn period dinta ya dauke ta koma normal activities dinta.


Yau Thursday tun safe suka tashi da shirye shiryen tarban qanwar ummi da zatazo daga kano.... hajia Aisha Wanda suke kirada umma...gobe Kuma nafeesa itama zatazo daga porthacourt itada yaranta...kallo daya zakama ummi ka ga tsantsar farin cikin da take ciki na zuwan sister din nata da Kuma 'yarta ba...tun jiya aketa Shirin tarban baqin har zuwa yau....Karfe 3 daidai jirginsu yayi landing....Taheer ne yayi picking dinta daga airport...farin cikin da 'yan uwan suka shiga na ganin junansu bazai misaltu ba sbd ba karamin kaunar junansu sukeba...ranan raba dare sukayi suna hira gaba dayansu a parlor...bayan sun koma daki ma suka Dora...don ummi cewa tayi kusada 'yar uwarta zata kwana.


Washe gari misalin karfe 11 Taheer ya shigo parlorn ummi cikin shirinshi don 12 ne jirginsu nafeesa zaiyi landing...ya samesu su biyun a parlo ya zauna gefen umma ya Mata side hug yace"Ummata barka da safiya"...tana murmushi tace "barka dai son...hope ka tashi lfy...lfy Lou Ummata"ya dubi inda ummi ke zaune yana murmushi yace" ummi barka da safiya"....ummi ta dan tabe baki tace barka dai....ynxu bazakaje ka dauko min yarinya daga airport ba salon tayita zaman jiranka Taheer"....ya mike Yana fadin "ynxu xan tafi ummi ai akwai sauran time... bari inyima baby mgn ta fito mu taf...tun bai karasa ba ummi tace"don Allah ka rabu da Layla kaje ka daukomin su  ka dawo...idan kace zaka biyema Layla bata lokaci zakuyi wlh...yadan wara ido yana kallon ummi still smiling yace "ynxu ummi sbd zanje dauko 'yarki ni Kuma sai in tafi in bar tawa 'yar"...ummi tayi murmushi kawai tace fitsararre kawai"...shi Kuma ya karasa dakin Layla...tana tsaye ta gama shirinta cikin black Arabian gown daya mugun yi Mata kyau....ta danyi rolling da mayafin rigan qafanta sanye cikin loafas shoe dinta kalan stones din rigan sai wayanta datake jujjuyawa a hanunuta tana tunanin ta inda zata fara fita a haka....tasan da kyar idan baice sai tasa hijab ba...tana cikin tunani tajishi gab da ita...ta dago kanta da sauri tana kallonshi kmr yanda shima kallon nata yake with adoration...shigarta ba karamin tafiya yayi dashi ba...tayi mai kyau fiyeda tunani...ta danyi murmushi ta kamo hanunshi tace"daddy ka shirya ne?...yace"na shirya mana baby...kema kiyi sauri ki gama ynxu xamu tafi"...har ya juya zai fita tayi karfin halin cewa ai Nima na gama daddy...muje kawai...da sauri ya juyo yana kallonta from head to toe thinking ko baiji daidai bane...why on Earth zatace zata fara fita da such dressing....ganin kallonda yake mata ta marairaice tace"dady dn Allah ka barni yau in fita a haka kaga iyakan mu airport....Kuma dagani sai Kai zamu tafi dady kar kace sai nasa hijab plss...yai shiru Yana kallonta Yana tunanin kar Kuma taga kmr Yana matsa Mata....Sam baison taga kmr takurata yakeyi amma seriously bai son ta ringa fita a haka...yasan tanada hadari cox tanada sura mai daukan hankali...dole zai hakura yau dayadai ya barta taje a haka... after all family dinta zasuje dauka...sai ya danyi Mata murmushi yace alright muje"...mamaki sosae ya kamata cox she never thought zai amince haka so easily...ya juya ya fita ta mara mai baya...ko da sukaje parlor umma ta hau tsokanarta wai duk su Al'ameen akama wnn kwalliyan" tayi dariya kawai snn tace umma ko dai kishi kikeyi sbd kinga nafiki kyau...dakuwa umma tayi Mata tace "kinci gidanku...Zaki dawo ki sameni kuma...tana dariya ta fita ta samu har ya shiga mota....ta bude itama ta shiga snn suka bar gidan....Tafiya suke cikin silence duk ranshi a bace baiso ta fito a hakaba...suka tsaya a wani danja shi kawai gani yake kowama kallonta yakeyi sbd tayi kyau...wani bakin cikin yaji ya sake taso mai...how he wish ba da wnn motan ya fitoba cox wnn babu tint...dole haka ya hakura har suka karasa airport...nan cikin mota suka zauna har jirginsu yayi landing passengers din ciki suka fara fitowa....ya bude motan yafita itama ta fito....

A hankali take saukowa daga jirgin tana sanye cikin dogon riga na wani lace peach...ta yafa veil dinta shima peach color hanunta rikeda hand bag dinta...sai phone dinta a wani hanun...tanada dan jiki amma ba sosae ba...snn tanada tsawo...kallo daya zaka Mata kagane ita ta haifi Layla sbd tsananin kmr da sukeyi...Al'ameen na bayanta yana janye da trolleys dinsu...sai ramadhan dake rikeda hanun hibba...da gudu Layla ta nufi wurinsu ta shiga hugging yaran daya bayan daya...bayan sun saketa Kuma suka yi wurin Taheer shima da gudu suna hugging dinshi...shima yai hugging nasu back tareda pecking cheeks dinsu...nafisa ta karaso gefensu tana kallonsu sai kawai taji Layla tayi hugging dinta itama hadda yi mata peck a cheeks dinta....nafisa tadan wara ido da murmushi tana kallon Taheer dayake rikeda hanun yaran hr yanxu snn ta girgiza kai tace"ka lalata 'yarka wlh...jifa hadda wani yimin peck kmr saar wasanta"..Yana murmushin shima ya shiga sa yaran cikin mota yace"yarinya dadi ma ya kamata kiji babyna tayi pecking dinki...and idan ku ba haka kuke ba to mu haka mukeyi ko baby?...Layla ta daga mai Kai tana murmushi yace"yes daddy"..nan dai suka shiga mota zuwa gida.


Bayan isansu gida aka gaisa...ummi tace suje su Dan watsa ruwa kafin a gama lunch... nan kowa ya tafi respective dakinshi.

WAIWAYE...+

Taheer Ibraheem Jakada shine cikakken sunanshi,mahaifinshi haifaffen garin kano ne hakama mahaifiyarshi mai suna Hajia Maryama.Lokacin da sukayi aure sun kwashi tsahon shekaru Allah bai basu haihuwa ba sai daga baya Allah ya kawo aka samu namiji aka Sanya mai suna Taheer bayanshi Kuma Allah bai sake basu wani ba.
Mahaifiyarshi wato maryama tana da qanwa wadda ke aure cikin garin kano itama mai suna Aisha.Su kadai iyayensu suka mutu suka bari hakan yasa suka matukar son junansu.
Taheer nada shekaru biyu a duniya itama Aisha ta haifo 'yarta mace aka sa Mata suna Nafeesa.Kasancewar gidajen su na kusa yasa Nafeesa kusan kullum gidan yayar mahaifiyarta take wuni wanda hakan ya haifar da soyayya mai karfi tsakaninsu da Nafeesan,suna sonta sosae snn suna kulawa da ita.
Nafeesa nada shekara daya Taheer Kuma nada uku a duniya mahaifinshi ya samu sauyin wurin aiki daga nn kano zuwa Abuja,wnn shine dalilin daya Sanya suka koma Abuja da zama saidai suna tsananin kewar nafeesa sbd sabon dake tsakaninsu,hakan yasa lokacinda ta isa yaye Aisha da mijinta suka yanke shawaran baiwa maryama ita hakan Kuma akayi domin da kanta taje har can Abuja ta Kai musu ita tareda alqawarin sun bar musu ita har abada,wannan shine dalilin dawowar nafisa hanun maryama wadda suke kirada ummi,nafisa bata taba neman wani abu ta rasa ba,daga ummi har abie suna sonta matuka hakama Taheer,dukda cewa suna yawan yin fada Amma hakan bai hanasu son junansu ba,tare sukeyin komai hatta boko da islamiyya tare aka sanyasu saidai Taheer yafita aji sbd ya Dan girme Mata.
Wannan kenan..
Bayan haihuwan Nafeesa Aisha ta sake haihuwan yara biyu,Sadiq da Kuma autarta Ramla,haka nn suna cigaba da zumunchi da yar uwarta duk da nisan dake tsakaninsu.

Lokacinda nafeesa ta kammala secondary school wani cousin dinta ta bangaren mahaifinta mai suna Awwal ya fito yana sonta,itama bata qishi ba ta amince,koda labarin soyayyar ya iske iyayensu sunyi farin ciki sosae domin da mahaifita da mahaifin shi Awwal din uwa daya uba daya suke.
Bayan shekara daya akayi aurensu lokacin tanada shekaru 20 cif a duniya Taheer Kuma yanada 22.Aka gama biki snn aka mika amarya nafeesa gidanta dake Lagos kasancewar mijin nata soja ne a can yake aiki.Bayan auren bata samu daman cigaba da karatu kmr yanda aka tsara ba sbd cikinda ta samu.Cikin nata nada 8 months aka tura Awwal wani course na watanni shidda a qasar Ukraine daga wurin aikinsu,wnn dalilin ya Sanya Nafeesa komawa Abuja har zuwa lokacinda zai dawo don bazai yiwu ya tafi da ita da tsohon cikiba.Ummi na kulawa da ita sosae hakama abie,suna bata kulawan da duk mai tsohon ciki take bukata,hakama Taheer,lokacin yana 300 level a university,yanada Kuma shekaru 23 a duniya nafeesa Kuma 21.
Watannin cikinta tara daidai ta haifi yarinyarta kyakywa son kowa kin Wanda ya rasa,tunda Taheer ya Dora idanu kan yarinyar yaji Yana sonta sosae.Bayan an sanar da Awwal haihuwan yayi farin ciki sosae snn yace ya wakilta abie yayi mata huduba da sunan ummi wato Maryam,ummi tayi farin ciki sosae da wnn Kara da aka Mata,hakan kuwa akayi ranar suna aka Sanya Mata suna Maryam ummi tace sai dinga kiranta da Layla.
Layla ta kasance yarinya lafiyayya hakan yasa takeda farin jini da Kuma shiga ran mutane,Taheer bai tabajin soyayya irin Wanda yakema yarinyar nn ba yanajinta tamkar 'yar da ya Haifa a cikinshi,wani lokacin har missing lectures dinshi yakeyi sbd ita,kawai ya zauna gida yayita wasa da ita,hakan yasa Layla ta saba dashi sosae har ta ganeshi don Yana zuwa wuri zata fara dariya tana miko mai hannu wato ya dauketa,,Saida Layla tayi wata biyar a duniya snn mahaifinta ya dawo,ba karamin bacin rai sukayi da komawan nafeesa gidanta ba sbd sunyi missing Layla sosae,ita kanta ummi ynxu kusan duk son da takema nafeesan ne ya dawo kan laylan.

A gurguje plss...

Layla nada shekara daya Allah ya karbi ran abie wato mahaifin Taheer,sunji mutuwanshi sosae,amma kmr yanda Allah ke Sanya mantuwa irin wnn a zukatan mutane haka suka fara rage damuwa har suka warware gaba daya.

Layla nada watanni 20 aka kawota yaye Abuja,daga ummi har Taheer sai aka kasa gane wanda yafi farin cikin zuwan nata,shi kanshi mahaifin Layla ya tabbatarda soyayyan da sukema Layla is real musamman Taheer da yakega ko Dan da ya Haifa iyakan soyayyan da zaiyi mai knn.
Bayan watanni biyu aka sake tura Awwal wani course din a China na tsahon shekaru shidda,,wnn al'amari ba karamin daga hankulansu yayi ba sbd suna ganin kmr bazasu iya rabuwa da Layla har na tsahon 6 years ba Amma ga mamakinsu lokacinda sukazo yi mus sallama sai Awwal yace bazasu tafi da Layla ba sbd sunga irin kaunan da suke Mata,don haka ya bar musu ita halak malak snn har abada bazai taba nuna kanshi matsayin wai shi ya haifi Layla ba,ya bar ma Taheer har abada,sunyi farin ciki sosae musamman Taheer da bai iya cikakken 3 hours ba tareda Layla ba,wnn dalilin ya sake  karfafa zumunchi a tsakaninsu,hatta iyayen Awwal basu nuna rashin amincewansu ga hakan ba,daga nan Abuja suka je kano sukayi sallama dasu umma snn suka je Dutse inda mahaifin shi Awwal din yake suka musu sallama bayan dawowansu da sati daya suka tafi zuwa qasar China.

Layla na samun kulawa sosae,ta sake sabawa da Taheer snn tayi mishi farin sani da ko bacci takeyi tanajin muryanshi zata tashi,wani lokacin in suna wasansu ummi saidai taita kallonsu tana ayyana irin sonda Taheer keyima laylan,sai takega kmr ma yafita sonta,sau tari sai tayi da gske snn zai tafi sch Yana dawowa Kuma zasu Dora inda suka tsaya,tun tana hanshi idan yace Layla zata kwana tareda shi harta hakura,ya zamana tare suke kwana da ita,shike Mata komai,ya Mata wanka ya shiryata ya bata abinci har goyata yakeyi ya sata tayi bacci,duk ta fara rashin lfy kuwa tamkar tare suke jinyan don shima komai nashi tsayawa yake cak har sai yaga ta warke ta koma normal,koda ta fara mgn da sunanshi ta fara,shi ya koya mata ta ringa kiranshi daddy hakn kuma take Kiran nashi.
Shekaranta ukku ya sanyata makaranta kasancewar tanada wayo da Kuma surutu sosae,lokacin shima ya kammala first degree dinshi fannin medicine,ko a makarantan da sunanshi take amfani"Maryam Taheer Jakada"shi ke kaita school kullum snn time din tashi nayi zaije ya daukota wani lokacin ya maidata gida wani lokacin kuma su tafi yawo abunsu.
Bayan shekara uku nafeesa tazo hutu Nigeria,lokacin Kuma tana goyon yaronta kyakyawa mai suna Al'ameen,watanta daya ta koma China sbd ta fara karatu a Chan har ma ta kusa kammalawa.

Soyayya da Kuma shakuwa mai karfin gaske suka shiga tsakanin Taheer da Layla har zuwa ynxu soyayyan da uba zaima 'yarshi haka yake Mata,Yana sonta fiyeda tunanin mai karatu,haka itama tana sonshi fiyeda komai a duniya,tana damuwa duk al'amuranshi tun tana karamarta kmr yanda shima yake damuwa da nata.
Bayan wasu shekaru ukkun Nafeesa suka dawo Nigeria,lokacin ta sake haifan wani yaron bayan Al'ameen,mai suna Ramadhan,wnn karon maimakon Lagos sai suka koma porthacourt sakamakon transfer da akamai.bayan wasu shekaru ta sake haifan mace aka sa mata sunan Maman mahaifinta ake kiranta da Hibba.

Wannan kenan

Bayan shekaru Sha daya,abubuwan da dama sun faru ciki hadda auren Ramla 'yar autan umma tana nn zaune a abuja da Kuma sadiq shi Kuma Yana kano,sai kuma rasuwan mahaifinsu Nafeesa,da kammala secondary school din Layla lokacin she's 17 years old.Sai kammala first and second degree din Taheer duk fannin medicine ynxu haka yanada clinc nashi na kanshi nan cikin Abuja snn akwai different hospitals da yake visiting Har zuwa wnn lokacin kuma baiyi aure ba bai Kuma San lokacinda soyayyan da yakema Layla ya rikide ya koma so irin na aure ba bayan bashida hope at all.

Post a Comment for "DR TAHEER CHAPTER 1 BY UMMU ASHRAF"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...