DA KAMAR WUYA CHAPTER 6 BY ZULAIHAT IDRIS MISAU - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DA KAMAR WUYA CHAPTER 6 BY ZULAIHAT IDRIS MISAU

DA KAMAR WUYA CHAPTER 6 BY ZULAIHAT IDRIS MISAU

- - Post a Comment

 DA KAMAR WUYA CHAPTER 6 BY ZULAIHAT IDRIS MISAU


              Www.bankinhausanovels.com.ng 

Murmushi hayder yayi. "  dukiya!!!Mufi yawan mutane suna halaka ne don son duniya da kuma son hutu da jin dadi a duniya.

Shuwagabannin masu rayuwa cikin hutu da jin dadi suke jawa alummarsu halaka don irin fasadin da suke aikatawa a bayan kasa.da yawan mutane na ganin jin dadin duniya shine ka samu kudi. Sun manta da ko kanada kudin, sai Allah yaso kaji dadi dasu. Sannan dukiya kan zama fitina ga maabocinta, don dayawan mutane ita ke halakar dasu, kota wurin nemanta, ko kuma ta wurin gudanar da ita. Dukiya kan kawo shagala da lamuran duniya, ga Wanda ba Allah a zuciyarsa. Mutun zai iya yin komai, don kawai ya tara abin duniya, I mean everything kisan kai, cinamana, zalunci, yaudara duk don yaji dadi a duniya. Kasan abinda yafi daure min kai?" Kallonsa Yusuf yayi, tare da kada kansa.


Ajiyar zuciya harder yayi, " ka gama tara dukiyar, amma baka tanadi lokaci, da kwanakin da zaka zauna ka moreta ba."


Murmushi Yusuf yayi. " rigima ke nan.  Duniya ke nan, yanzu kananan lokaci kadan ka gushe. Shin wane ayyukane na lada da bayan mutun ya gushe zai kawo masa lada?"


Still idon hayder a sama, murmushi yayi. " bayan mutun ya mutu, ayyukansa sun yanke, abunda zai ci gaba da wanzuwa na lada kona kankare zunubi ga bawa, shine da na gari, dazai ci gaba da yi masa addua. Sai sadakatul jariyyah. Kamar gina masallatai, Gina rijiyoyi, tallafawa marayu. Da sauran ayyuka masu gudana."


Ajiyar zuciya Yusuf yayi, tare da gyara zamansa. " ga mutumin da kejin kamar rayuwarsa baza tayi tsayi ba, kuma bai mallaki Dan da zai masa addua ba? Mai zai yi, bayan sadakatul jariyyah.?"


Kallonsa hayder yayi, cike da alamomin tambaya, saboda yanayin da Yusuf yayi tambayar.

Hannun Yusuf ya kamo cikin nashi "1. Ayyukan mutum anan duniya suna tare da shi a duniya da lahira. Makomarsa na tattare da ayyukans a nan duniya.

2. Duk abin da mutum ya fada ko ya aikata anan rayuwa za'a rubuta shi a nuna masashi ranar kiyama kamar yadda ya fada ko ya aikata su.

3. Kotun ranar kiyama kotu ne wanda ayyukan mutum basa boyewa. Hatta da kansa zai iya yiwa kansa hisabi don kasancewar ayyukansa a fili suke. Baya bukatar wani shaida wanda zai tabbatar da ayyukan da ya yi.

4. Bautar Allah shi ne abinda ake gabatarwa kafin a sami kaiwa ga kusanci ga Allah da kuma sanin girmansa. 5. Dare shi lokaci mafi muhimmanci wajen samun kusanci ga Allah. 3. Massalaci shi mahallin da aka fi samun kusanci da Allah. Kuma sallah ce mafi girma daga cikin abidu. Don haka ne ma ake kiranta mirajin mumini. Rashin da baya rage komai ga bawa, sau da yawa ma yakan zama alkhairi ga bawa."


Hannunsa Yusuf ya kara kankamewa tare da dan bubbuga hannun da daya hannunsa, Kallonsa hayder keyi, yana nazarinsa. " tun da kazo na lura da canji sosai a tattare da kai, don Allah ahee!! Meke faruwa.?"

Murmushi Yusuf yayi, tare da Jan numfashi. " yanayin rayuwane kawai. I wish ni kaina nasan abunda ke damuna, I want to ask u a fervour. "

" ask everything u want, in sha Allah zan maka." Hayder ya fada still idonsa a kan Yusuf


Murmushi Yusuf yayi " na gode sosai da soyayyarka gareni, duk a yan'uwana kai ka zama mafi soyuwa a gareni. Ina sonka saboda Allah, fiye da yadda nake son kaina. Ina rokonka ko bayan bana raye ka kasance mai yawan yi min addua, Don kai kadai nake ganin kani kuma da a gareni."

Idon hayder ne suka cicciko da kwalla, saboda yanayin da Yusuf yayi maganar, cike da rauni. Rungumeshi hayder yayi gaba dayansu hawaye suke fitarwa a idonsu. Sun kai lokaci mai tsawo rungume da juna, kafin suka saki juna. " na maka alkawari, matukar ina numfashi, in sha Allah zan kasance mai yawan maka addua. Kamar yadda ban taba ma kaina addua ba tare da na sakaka da sauran yan uwanmu ba."


Murmushi Yusuf yayi still yana rike da hannun hayder. " na gode, hakika kai dan uwane na gari, ina alfahari da kai. A another fervour!!! Ina son ka kulamin da Habiba. Don bayan son Allah da manzonsa, da baa hadashi da komai. Iyayena da kai, sai kuwa Habiba. Habiba tamkar wani bangarene na jikina, bana son rashina yasata shiga wani hali, zan so ka maye mata gurbina, don nayi imanin zaka kulamin da ita, fiye da yadda zan kula da ita."


Kallonsa hayder keyi idonsa na zubar da hawaye, wnnan wasu irin kalamai ne ahehh dinsa keyi, tamkar mai barin wasiyya. Mu samman yanayinsa dake sanya tsoro a zuciyarsa. " aheeh!! Wannan wane irin magana ce mai kama da wasiyya?" Hayder ya fada cikin raunin murya.


Murmushi Yusuf yayi tare da jingina sosai a jikin kujerar. " ka dauketa a matsayin wasiyya hayder.  Ina son bayan bana raye ka auri Habiba,  Habiba mace ce ta gari, abin alfaharin kowanne miji daya dace da samunta, duk yadda zan maka bayani bazaka gane me nake nufi ba, sai zuwa gaba. "


Mikewa hayder yayi zuwa kusa da Yusuf, tsugun nawa yayi, hannunsa duka biyu yasa ya dafa gwuiwowinsa dasu. " don Allah karka karya min zuciya, zan iya daukar komai, amma banda irin wannan kalaman naka. In sha Allah zaka ci gaba da rayuwa damu har tsufanmu, kaga aurena kaga yayana, kamar yadda in sha Allah kaima very soon Habiba zata Haifa maka naka. In wani ciwo ke damunka please don't hide it. Ba cutar da bata da magani."


Kanshi Yusuf ya safa, yana kokarin maida hawayensa. " bawa baya wuce kaddararsa hayder. Allah yasa ina da rabon ganin aurenka in ga yaranka. In har hakan alkhairine gareni. Ina maka fatan samun maratus saliha, kamar yadda na dace. Shi yasa nake tsoron haduwata da Allah, don duk wani jin dadi, da kwanciyar hankali na duniya alhamdulillah na samu,. Kudi, mata ta gari, lafiya, kwanciyar hankali. Lahira kuwa, kaga baka da tabbas din karbar ayyukanka na alkhairi."


" ka Sani mutane kashi uku ne, a duniya: 1. Daga ni'ima zuwa ni'ima, 2 daga ni'ima zuwa azaba,( Allah ya tsaremu) 3 daga wahalar duniya, zuwa azabar lahira, (Allah ya tsaremu). Ina maka fatan jin dadi, duniya da kiyama." Hada hannunsa hayder yayi " don Allah kabar wannan maganar haka, ka fara tsoratani da gaske."


Karamar dariya Yusuf yayi. " shi kenan, Allah yasa mu cika da kyau da imani. Gobe ni zan wuce, Oregon. "


" amen, na dauka zamu kwana biyu a nan." Hayder ya fada yana mikewa tsaye.


Tashi Yusuf yayi, yana murmushi. " no!!! Zan je ziyara Oregon one day, in koma gida,."


" please ahehh! Ka kara ko kwana daya ne." Hayder ya fada cikin fuskar shagwaba.


" no way, I miss my wife already, I have to go." Yusuf ya fada yana tafiya zuwa apartment din


" u love her too much ahehh!!" Hayder ya fada cike da kishin hubby, gani yake Yusuf yafi sonta a kanshi.


" I love u more." Yusuf ya fada yana dariya

" if u say so." Hayder ya fada cikin muryar tausayi.


Juyowa Yusuf yayi, ya kalleshi yana dariya. " ina adduar Allah ya kawo karshen yar tsamarka da my wife. "


" ta cika son girma da yawa." Hayder ya fada yana kwallo da wani karamin dutse.


Kallonsa Yusuf yayi yana murmushi " kai kuma ka cika raini ba? Bansan me yasa ka rainata haka da yawa ba."


" bata jin magana, ba kokari a school, ga dan banzan shagwabar tsiya. Ni Tun dawowarta daga kauye, yadda take behaving take ban haushi, shiyasa bana shiga harkarta, amma duk ban tsira ba, ta tasani a gaba da mugunta. Tayaya zan wani girmamata."


" kafa rama koma me ta maka, kaga kunyi 50-50 don haka sai kayi hakuri. In don kifinka da ta cinye ne, zan biya, a zauna lafiya. Ko ba komai ai ta girmeka, gashi kuma tana matsaya yin matata, bana jin dadin yadda kake treating dinta." Yusuf ya fada


Kunne hayder ya kama " sorry, yanzu kam ai ina gaisheta in mun hadu." Dariya Yusuf yayi " good for u." Ya fada yana shigewa ciki, a baya hayder ya biyoshi, a kofar dakin hayder sukayiwa juna sai da safe, hayder ya shige dakinsa, shi kuma ya wuce nashi masaukin dake gaba da dakin Hafiz...


             *********************

Ajiyar zuciya harder ya sauke. Jin numfashin hubby na sauka a hankali, tare da ajiyar zuciya ya bashi tabbacin tayi bacci. A hankali ya gyara mata kwanciyarta, ya mike ya nufi toilet.


Addu'o'i sosai ya jerowa dan uwan nasa, kamar yadda ya saba, tare da masa fatan samun rahamar Allah, ya roka masu zama lafiya shifa hubby da zuria masu albarka.


Yana wurin har aka kira sallah. Sai da ya tashi hubby sannan ya wuce masallaci.


Rashinsa a dakin ya bata damar tashi a natse, duk jikinta yayi tsami, a hankali ta taka zuwa cikin toilet dinsa. Ruwa mai zafi ta sa, ta gasa jikinta tare da yin wankan tsarki, Dana sabulu.  Kokari take ta maida hawayen dake kokarin fitowa.

Duk yadda taso manta abinda ya faru dakika kadan da suka wuce, abun yaki fita a ranta.


Gani take kamar a mafarki, lokaci kadan zata farka. Amma wasa wasa mafarkin yaki karewa.


Taso tafiya dakinta, amma still tana tsoron fita. Rigar daya bata jiya, ita ta dauka tasa tayi sallah.

A wurin ta kwanta, minti kadan bacci ya yi gaba da ita..


Sai to 7 hayder ya shigo gidan. Dagata yayi ya mayar kan gadon, bayan ya gyarashi tsaf. Bai saba baccin safe ba, don haka computer dinsa ya dauko ya fara aikinsa kamar yadda ya saba. Har 9:39 kafin ya kashe, ya nufi kitchen don sama musu abinda zasuci.


Karar rufe kofar ne, ya farkar da hubby. Dakin tabi da kallo, kafin ta mike. Sakkowa tayi, ta nufi dakinta, zuciyarta cike da tsoron kar su hadu da mage.


A bakin Kofa ta tsaya, tana lellekawa, sai da ta tabbatar ba komai, tukun ta shiga dakin. Key take kokarin sawa amma sai taga wurin wayam, ba key a jikin door din.


Wanka tayi, ta shirya cikin atamfa Holland mai kyau, dinkin Riga da skirt sunyi mata cip, komai masha Allah. Kwalli kawai ta shafa, ta gyara packing din gashinta. Feshe jikinta tayi, da turarenta mai kamshi, dan da nan dakin ya dauka, dama ga kamshin humra data sa a jikinta. Higab dinta ta zunbula ta nufi kasa, don yunwa takeji, har tana ganin jiri- jiri.


Mamaki sosai tayi, ganin Mariya harta gama gyara komai, ta sa mata turaren wuta, gidan gaba daya ya dauki kamshi. A kitchen suka hadu da Mariya. Da faraa ta ce " Anty ina kwana?" Murmushi ta mata "lafiya kalau, ya mamanki?"


" ta ce in gaisheki." Mariya ta fada

" ina amsawa, sannu da kokari'" hubby ta fada tana kokarin jona kettle.


Murmushi Mariya tayi. " Anty akwai abinda zan kama mikine? Ko inje in gyara falon sama?"


Kallonta hubby tayi, tana murmushi. " ki bari muci abinci, sai in tayaki"


" na gama cin abinci kenan, na wanke plate din kika shigo." Mariya ta fada


Kallonta hubby tayi, ganin iya gaskiyarta ta fada, yasa ta ce taje ta share falon.


Cup ta dauko, ta zuba madara, sugar  da Millo. Tana jiran ruwan ya tafasa.


Kamshin turarensa ne, ya fara mata sallama. Bata juyoba don bata da courage din fuskantarsa after what happen.

Rungumota yayi ta baya, tare da daura kansa a kafadarta. " good morning. " ya fada in husky voice dinsa. Jikinta ne, ya dau rawa. She can believed what hayder do to her, Ta kara yadda mazan yanzu kunyarsu rageggene.

Hijab din ya cire, a kan dogon kujerar da aka tanada a kitchen din ya wurga. Tare da juyo da ita, Kanta a kasa. Hannunsa yasa ya cire ribbon din kanta, gashin ya baje a bayanta. Ya zubo da kadan ta gaba gefe daya, Wanda ya sauka har kirjinta. " u look good, karki kara samin wannan abun, in har ba baki bane a gidan.

Hubby kam tsabar takaici ne, ya hanata koda kwakwaran motsi. Mamakin karfin halin hayder take yi.

Batayi aune ba, sai bakinsa taji a cikin nata. Kokarin tureshi ta fara, amma ina ya mata kyakyakyawan rukon da bazata iya kubu cewa ba.


Sai da ya gaji, don kansa ganin tsayuwar na Neman gagararsu, yasa ya saurara mata. Hannunta ya kamo, suka jero zuwa main falo, A kasa ya shirya musu kayan break fast. Sai da ya tabbatar ta zauna, sannan yaje ya sallami mariya, don yau bayi da bukatarta a gidan.


Cike da karfin, hali, da tusawa zuciya dangana hubby ta ke cin abinci a hankali. Gaba daya idon hayder na kanta, tausayinta yake ji, ganin yadda gaba daya tayi sanyi, kamar ba hubby ba. Shi kansa yasan bai kyauta mata ba. Amma ba yadda ya iya, dole su rungumi kaddararsu.

Gefensa ta dan kallah. " kai ka kawo mage gidan nan?" Ta fada da muryarta cike da rauni.


" nop." Ya fada yana Kallonta


Shiru tayi, ba tare data yadda da abinda ya fada ba. Don ta tuno da kalaminsa na cewa ita da kanta zata kawo masa kanta, yana shararren wurinsa. In ba shi ya shigo da magen ba ta ina ta samu ta shigo?


Ganin alamar bata yadda ba yasa ya gyara zamansa. " look habibi, da gaske bani na shigo da ita ba, magen gidan barrister ce, dawowana masallaci naji suna tambayar malan idi koya ganta.  jiya  aka kawota, sun tashi da safe, basu ganta ba. Shi kanshi malan idi bai San ta shigo ba.  Ina shigowa mukayi karo da ita a kofar falo, shine na dauketa na mika musu ita."


Ajiyar zuciya hubby tayi, tare da Jan Allah ya isanta ga mamallaka magen.


" magen is so cute!! Kinga picture din da na mana tare." Ya fada yana murmushi tare da bude wayarsa don ya nuna mata picture din.


1

Haushine ya kama hubby, bata San lokacin data balla mai harara ba. Murmushi yayi yana nuna mata picture din.


Tashi tayi ta nufi, sama da gudunta. Da ido ya bita yana murmushi, tare da shafa sajensa. Kiss yama magen tare da furta " your the best. ".........Ya Tattare kayan da sukayi break fast, ya gyara wurin.+

Kwanciya tayi, hawaye wani na bin wani. Kuka sosai ta sha, kafin bacci yayi gaba da ita.


               *****************


Alhaji Jamal ya kalli hayder " munyi waya da jamil, Ku aika masa da CV dinku." Dariya hayder yayi " daddy mu kam mun yafe, waye zai tsaya wani bata lokaci aikin government. "


Ido Alhaji Jamal ya dan zaro " kana nufin baza kuyi ba kenan? To su sauran da suka karanta medicine haka zasu bari ya tafi a banza,? ina dama anyi karatun ne don taimakon alumma?"


"A kwai hanyoyi da yawa na taimako, yanzu dai karatu zamu koma, tukunna" Hayder ya fada yana murmushi


Kai Alhaji Jamal ya kada kai, Allah ya taimaka."


" amen Daddy. Gobe in sha Allah zan zo muje kaga store din." Hayder ya fada yana kai kofin shayi bakinsa.


" haka ne, na manta ne ai da yau na dawo da wuri, da munje, amma ba damuwa Allah ya kaimu goben."

" amen. " hayder ya fada


" ya yarinyata? Ba wani matsala ko?" Alhaji Jamal ya tambaya yana kallon hayder.


" lafiya kalau." Ya fada cike da jin nauyin Daddy


Murmushi yayi " Allah ya muku albarka, a ci gaba da hakuri, kasan mata zama dasu sai da hakuri, da kuma juriya."

Murmushi hayder yayi kanshi a kasa.


" ko akwai abunda kake bukata?" Alhaji Jamal ya tambayeshi


" ba komai," hayder ya fada yana murmushi


Murmushi Alhaji Jamal yayi. " na manta Ashe da dan kasuwa nake magana."

Dariya hayder yayi. " karamin dan kasuwa dai."


Ahmad ne yayi sallama ya shigo, daddy ya gaisar, sannan suka gaisa da hayder.


" kun tashi daga kanana yan kasuwa, kun fara zama manya. " Ahmad ya fada yana murmushi


Murmushi Alhaji Jamal keyi cike dajin dadi, " haka ne ko Ahmad? " Alhaji Jamal ya tambaya

" Daddy sai kaje kaga manyan stores din da suka shake da kaya, sannan zaka yadda da maganata." Ahmad ya fada yana hada shayin,.


" shi yasa nayi maganar aikin government aka ce min aa. Allah yasa albarka." Alhaji Jamal ya fada


"Amen" suka amsa gaba daya.


Hira suka ci gaba da mahaifin nasu, gwanin sha'awa, har wani lokaci kafin suka fito kowa yayi hanyarsa.


                  ****************

Hubby sai 1:30 ta farka, da sauri ta daura alwala don yin sallar azahar.  Tun kafin ta idar takejin nocking, tana idarwa ta sakko don ganin ko waye.


Tasha mamakin ganin Abida. Fuska ta sake sosai tana mata sannu da zuwa.

Falo ta kaita, tare da cikata da kayan ciye -ciye, tunda bata samu tayi girki ba.


" Anty hubby ina wuni." Abida ta fada tana mai sakin fuska


Mamaki sosai ya kama hubby, don tunda take da Abida, bata taba ce mata Anty ba. Sau da yawa in sun hadu, ita take jira ta fara gaisheta. In ma ta gaishetan a wulakance zata amsa. " lafiya kalau, ya mai gidan da Abdul?" Hubby ta tambaya


" lafiya kalau, Abdul yana main house." Ta fada tana murmushi


" ayyah! Shine baki zomin dashi ba?" Hubby ta fada cikin rashin jin dadin ta.


" ya samu su jeniour a gidan, shiyasa yaki yadda ya biyoni." Ta fada cikin jindadi.


" yasu mommy? " hubby ta tambaya jin daga main house take.


" lafiya kalau. " ta fada a takaice.


Shirune ya biyo baya, don hubby bawai ta saba da ita bane, asalima tana daya daga cikin wanda suka takurawa rayuwarta a zamanta da Yusuf. Tana mai mamakin ganin yadda ta sakko lokaci daya.


Kallonta take a kai -kaice, kamar ba abida ba, duk yanga da gayun nan babu, tayi wani iri kamar wadda ta taso daga ciwo.


Abida kuwa kallon hubby take, cike da shaawarta, a yadda tai tunanin ko tarbar arziki bazata samu ba, saboda abubuwan da ta mata a baya, amma sai taga sabanin hakan. Yanzu ne take nadamar abubuwanda ta ma hubby, gashi baa je ko ina ba, gashi tana ganin saka mako. Don yanzu wulakancin da kannen mijinta suke mata karema bazai ci ba, gashi  baya ganin laifin kannen nasa ko kadan, in Abu ya hadata dasu  A gabansu zai ci mutuncinta. Gashi bata da ikon kai kararsa gida. Saboda ita tace taji ta gani. Ba yadda ba ayi ta auri dan uwanta Khalil ba taki, karshe sai Ai'ra aka aura masa, an bata zabin ranta da sharadin komai ya faru ba ruwan kowa a ciki. Takuma ji ta gani. Wanda sai yanzu take gane kuskuren data tafka ma kanta.

Ajiyar zuciya ta sauke, da har tasa hubby juyowa ta kalleta. " hayder fah?"


Gaban hubby ne ya fadi, cikin yaken karfin hali ta kalli Abida " ya fita."

Kai Abida ta kada tana kokarin maida hawayen da suke kokarin zubowa a idonta.

Jikin hubby ne yayi, sanyi, tashi tayi taje ta daura musu abinci.


" gidanku yayi kyau sosai." Abida ta fada tana murmushi


Murmushi hubby tayi " na gode. Kiyi hakuri na sha'afa, bakizo ganin daki ba, muje ki gani." Hubby ta mike tayi gaba Abida na biye da ita.


Murmushi Abida tayi mai ciwo " kuyi hakuri duk kanku ba wanda naje dakinsa, sai ke da nazo yau. Bikin ma da yaya ya bari naje! Shi yasa duka programs din baku ganni a wurin ba."


Kallonta hubby take cike da mamaki, don har ga Allah bata lura da rashin zuwan Abidan ba, saboda dama can in sun hadun ma ranta sai ya baci, da bakar magana, da kallon banza. Tama manta da ita.  " amma dai baki kyauta ba, bikin kannenki guda amma baki raka kowacce cikinsu ba? Ko bakije na kowa ba ai kyaje na Aisha. "


Bakinta tadan ciza tana kada kai. " ni kaina nasan ban kyauta ba, amma ya na iya tunda bani nake iko da kaina ba? A hakan ma yayi kokari da ya banni nazo har 3 days a Jere, duk da ba dadewa nakeyi ba. Ni kaina kullen sa na damuna, na rasa yadda zanyi, gashi ba wanda zan kai kararsa ko na samu sassauci. Iyayensa kuma da na musu maganar budan bakin hajiyansa sai cewa tayi " wai so nake ya barni in ta yawo a gari kamar wata akuya? Ta inda take shiga ba tanan take fita ba, nayi nadamar kai kararsa wurinsu. Duk da ba wannan bane karo na farko da hakan ke faruwa ba."


Ajiyar zuciya hubby tayi cike da yausayin Abida.

Abida ta ci gaba da cewa " haka lokacin dana kai kararshi, daya hanani fita aiki, baban ya min tatas ba kunya ba tsoron Allah ya goyi bayan dansa. Daga karshe yace in har na matsu lallai dole sai nayi aiki, to inzo zai bani a company dinsa. Ba yadda na iya, haka na ajiye aikina, na koma ina aiki a company din, sai da na share wata biyar ko sisi baa taba biyana ba, danayi complain bakiji bakar magana da daddyn Abdul ya gaya minba. Hakan yasa na ajiye musu aikinsu. Tun daga nan muke takun saka dashi, har yau dinnan da nake miki magana."


" Allah ya kyauta, ki ci gaba da addua, sai kiga komai ya dai daita, da yardar Allah. " hubby ta fada cikin muryar tausayawa

Murmushi Abida tayi, tana zama a daya daga kujerun kitchen din. " duk abunda ya faru dani, ni na siya da kudina. Da nabi maganar Daddy da duk haka bata faruba, Daddy yasan Alhaji sammani farin sani, don haka ya nuna baya son in auri danshi, don wani lokaci, yaro kan dauko halayyar uba, kwabo da kwabo, koda bazan auri zabin Mmn Yusuf ba, to in kawo wani, amma ba jinin Alhaji sammani ba. Lokacin so ya rufemin ido, babban kuskuren dana tafka shine, duk abinda ke faruwa a gidanmu, ba wanda bana kwashewa in gaya masa. Yasan masu adawa da aurena dashi, yasan yan ba ruwana, Shiyasa yanzu sai abu ya faru a yan' uwa, amma yayi mursisi, ya hanani zuwa, in nai magana yace mai zanje inyi a wurin wanda baya kaunarsa. Kiri- kiri yana son rabani da yan 'uwana, rabon da wani nawa ya kai min ziyara ya kai 4month, sai dawowar hayder. Saboda wulakancin da yake musu, haka kannensa sun sha fada da Aisha, ita ce dama mai kokarin zuwa min akai akai. Daga baya ita din ma ta dauke kafarta, don bazata juri wulakanci ba. Nasan banda hakkin iyayena, har da hakkinki, na musguna miki da nayi, yake bibiyata. Kannanen mijina zagi, wulakancin da cin mutunci ba wanda basa min, jiyama karamarsu harda yun kurin dukana." Ta fada idonta na zubar da hawaye


Cike da tausayawa hubby ta fara bata, baki har ta samu tayi shiru. " ba abunda yafi karfin Allah, ki dage sosai da tashi da daddare kina kai kukanki ga Allah, in sha Allah komai zai wuce."


" na gode sosai Anty hubby, har naji zuciyata tayi min sanyi, da na samu na fitar da abinda ke damuna ."

Hira suka ci gaba, cikin kwanciyar hankali, hubby na bata shawarwarin yadda zata bullowa lamuranta. Abida taji dadi, don duk yan uwanta ba wanda zata iya budewa cikinta. Saboda gudun abinda zai je ya dawo.


Sai 5 Abida ta tafi, bayan hubby ta cikata da kayan kwalliya, turaruka, da materials har guda 4. Godiya tayi sosai, cikin sanyin jiki tabar gidan hubby.


Duniya kenan? Kaji tsoron Allah kaji tsoron mutun. Tunowa da yadda soyayyar Abida da mijinta yake, kafin auren. Kamar zasu cinye juna, don so da kaunar juna da sukeyi, ko yaushe suna tare, ko unguwa taje, yana biye da ita. amma duka duka auren da baifi 2²/¹ years ba, amma rigingimun dake  cikinsa yafi farin cikin yawa.

               *******************


Tana tsaye a gaban mirror. Sanye da kayan bacci Riga da wando dogo, pitch color, sunyi mata kyau sosai,   gashinta ta kama tare da saka hula mai raga -raga. Ta kara feshe jikinta da turare.


Kwanciya tayi, tare da jero Addu'o'i kwanciya bacci.


Duk da zuciyarta ta kasa natsuwa, don tun a wurin break fast da suka rabu da hayder, bai dawo gidan ba, gashi har fast 9. Damuwarta rashin key din dakinta, ta tabbatar shiya kwashe keys din, har da na daya dakin duka.


Sai 9:30 ya shigo gidan. Direct dakinsa ya nufa sai da ya gama shirin baccinshi sannan ya nufi dakin hubby.


Sanyin AC tare da kamshin turaren wuta suka fara masa sallama, lumshe idonsa yayi, yana jin dadin kamshin nan, yana son turare a rayuwarsa, ya lura itama maabociyar turare ce, sosai.


Hangota yayi, cikin duvet ta dukun kune. Murmushi yayi yana shafa sagensa ya nufi gadon.


A hankali ya rab'a gefenta ya kwanta cikin lallabawa kar ta farka ya jawota jikinshi ya rungume ta tsam a faffad'an k'irjinshi sai sauk'e ajiyar zuciya yake yana shafa bayan ta da gashin kanta, a hankali,Kamar a mafarki hubby ta ji ana shashsha fata. Ido hudu sukayi da hayder da already idonsa ya fara sauya kala. Da sauri ta runtse nata, jikinta ya dauki rawa zuciyarta na bugawa, don bata manta wuyar data sha a hannunsa ba. Ganin ta farka ya kara mishi kwarin gwuiwar ci gaba da aika mata da sakwanninsa, masu matukar rikitata.

Ganin yana Neman wuce gona da iri, tai saurin janye jikinta, tana zaro ido  cike da tsoro ganin abin da yake da niyar aikata mata ta k'amk'ame jikinta, baki na rawa tace.

"a,a Please hayder ka barni wallahi ban da lafiya, har yanzu jikina ciwo yakeyi."


dariya ya d'anyi ganin duk ta rud'e sai karkarwa take bakinshi ya kai kan nata ya fara bata hot kiss. Gaba daya jinkin hubby ya sake,  Bata da sauran karfin da zata kwaci kanta. Kansa ya dago yana kallonta. Muryarshi can kasa  " yaushe na tashi daga agric chicken na koma hayder? " ya tambaya yana sake mata wani killer smile.


Kasa cewa komai hubby tayi, don gaba daya ya kashe mata jiki, da salonsa.


Murmushi yayi ganin sai karkarwa take, bakinshi ya kai kan k'irjinta ya rink'a juyata,

ita kuwa a hankali ta rink'a mik'a tare da ruggume shi, hakan ya kara masa kaimi wurin ci gaba da abunda ya fara. Sai da ya tabbatar ta samu gamsuwa yadda ya dace, haka shima, tukun ya tsahirta mata jawota jikinshi yayi sannan ya ruggume ta yana maida numfashi da lumshe ido yana mai sa mata albarka.


Ganin tana kokarin yin bacci, hayder ya dago kanta, dake kwance a kan kirjinsa. " tashi muje muyi wanka, ba kyau mutun ya kwanta yayi bacci ba tare da ya gusar da najasar jikinsa ba, ana son ko alwala mutun yayi kafin yayi bacci. "Hannunta ya daura a kansa. Hannunta tai niyyar cirewa a cikin gashin nashi, ko tunanin me tayi, kuma sai ta fasa. Massage ta fara masa a kan, cikin natsuwa, lumshe idonsa yayi, saboda jin dadin abunda take masa.+

Cikin husky voice dinsa " meye planning dinki, a kan rayuwar aurenmu?"

Shiru tayi kamar bazata tanka masa ba. Sai can ta sauke ajiyar zuciya " ka riga ka gama rusa min duk wani plans dina. Sai dai ka sani gangar jikin Habiba kawai zaka mallaka, banda zuciyarta. Shiyasa na maka kwadayin ka auri zabin ranka, in da zaka samu kyakyawar kulawa da soyayya."


Murmushi yayi ba tare daya bude idonsa ba. Sun dau lokaci shiru ba wanda ya kuma cewa komai, kafin ya ce " ban rusa miki plans don wani abuba, illa don in taimakeki. Nasan bazaki iya cika sharuddan ba."


Harararsa tayi " waya gaya maka hakan.?"


Idonsa ya bude, kallonta yayi yana smacking tare da daga mata gira daya. " I'm not a kid!!!  Allah ya halicci ko wanne mutun da filling, matukar baligi ko baliga, lafiyayyu, zasu ci, mai kyau, su sha mai kyau, the next thing shine bukatuwa ga dayansu, Baki isa ki kare kanki daga wannan ba, no matter how u try. Koda na amince da sharuddanki, nasan zuwa gaba kadan bazaki jure ba. Hakan ma kinyi kokari."


" is not true!!!" Ta fada tana harararsa


Dariya yayi. " karki zo kina reaping dina a banza. Kinga ai gara a wuce wurin. Ban damu ki bani zuciyarki ba, kamar yadda kema ban son kisa rai da tawa zuciyar. Amma duk wani hakki naki, in sha Allah zanyi iya abunda zan iya."


Rankwashi ta zuba mishi a kai, da sauri ya mike, " ouch!!!!" Ya fada yana shafa sumar wurin. " what? " ya fada yana daga mata gira.


" for saying I'm going to rep u." Ta fada tana gyara kwanciyarta.


" ba kyau mugunta, kin san dai yanzu ina da hanyoyin ramawa da yawa? So be care full. " 

Banza tayi dashi, kwanciya yayi, ya jawota jikinshi. " na tambayeki dazu baki bani amsa ba. Meya faru aka daina kirana da agric chicken? Na dawo hayder? " ya fada yana murmushi


Tureshi tayi, tare da juya mai baya. Juyo da ita, yayi tare da dago fuskarta. Murmushi ne a kan fuskarsa, gira ya daga mata daya. Duka ta kai masa a kirji, yayi saurin tike hannun, yakai bakinsa  kiss ya mata tare da bin hannun yana kissing. Cikin rawar murya ta ce " please agric chicken let me sleep. " tana kokarin kwace hannun.


Dagowa yayi ya kalleta, fuskarsa dauke da murmushin mugunta. " agric chicken never sleep at night. They spend the night eating and play, so let us play. "


Bata fuska tayi, don har ga Allah ta gaji, bacci kawai take bukata a lokacin already past 12am.


" agric chicken ka ce, I'm not a agric chicken, U are. So go to your room and play alone. "


" u are agric chicken wife, u also a agric chicken. " ya fada yana kara shigewa jikinta.


" please hayder!! " ta fada cikin muryar tausayi


" I'm in the mood, please let me be. " ko kafin ta kara cewa komai ya zira bakinsa cikin nata.


                *******************


Yau ma hubby da tsamin jiki ta tashi. Bayan ta gasa jikinta tayi sallah, komawa tayi ta kwanta. Tambayoyine fal ranta. Tana mamakin hayder, wanda yasa har take zargin anya bai saba ma'amala da mata ba? Saboda wasu salon nashi, ko ita da ta shekara hudu a gidan miji, bata taba sanin su ba.  Yawan bukatarsa ya fara bata tsoro. Tasan Yusuf ma yana da yawan bukata, amma ko kadan bai kai hayder ba.


Baccine mai dadi yayi gaba da ita. Hayder daga masallaci ya wuce main house. Saboda nemansa da daddy keyi.


                *******************

Da sauri sauri take hada break fast din, Mariya na gyaran gida. Sai 10 ta samu ta kammala. A dinning table din main falo ta jera nasu, bayan ta zubama, Mariya da malan idi nasu.


Sama ta haura don ta samu tayi wanka.


Shiryawa tayi cikin wata pitted grown na less ash and pink, mai kyau da asalin tsada. Tayi kyau sosai, ba wani makeup tayi ba, just powder, kwalli, sai wet lips. Fuskarnan sai daukar ido take, bata tsaya daura dan kwali ba, karamin gyale ta yafa pink, tare da kara feshe jikinta da turaruka.

Kujerar dinning din ta janyo, tama kanta mazauni. Plate dinta ta gama hadawa da abinda take da muradi. Irish with liver source, sai pray eggs. Ta hada tea.  Ta fara ci kenan taji takun hayder tare da kamshin turarensa daya cika hancinta.

Sanye yake da farar shadda,  dinkin zamani ya zauna a jikinsa sosai, sharddar sai daukar ido take, ta kara fito da hasken fatarshi sosai, Very handsome.


Kujerar dake kallonta ya ja ya zauna. Idonsa na kanta, ta masa kyau ba kadan ba. Ko don bai saba ganinta da karamin gyale bane? Wayarshi dake faman ringing ya daga, tare da gyara zamansa sosai a cikin kujerar, idonsa a kan hubby da tun shigowarsa bata dago idonta ba, illah abincinta data ci gaba daci,.


Tana jin yadda idonsa ke yawo a jikinta. Hakan yasa ta kasa dago idonta ta kalleshi, ta riga tawa kanta alkawarin biyayyar aure, dai dai iyawarta. Zata tursasa zuciyarta wurin kokarin kyautata masa komai kan kantar hakan. Sai dai har lokacin tana jin jina, yadda zata sakko da kanta kasa gareshi,. Gaishe shi take son yi, amma ta kasa yin  hakan.

" antashi lafiya? " ya fada still idonsa na kanta.


Sai da ta hadiye abincin bakinta kafin ta amsa masa " lafiya kalau. " ba tare data dago ta kalleshi ba. Tana mamakin irin wannan kallo na hayder, kamar ta tsole idon nasa ta huta, haka take ji.


" kinyi kyau. " ya fad in husky voice dinsa yana bubbude wormers din dake table din. " wow!! all this for agric chicken.?" Ya fada yana smacking.


Harararsa hubby tayi, karaf idonsu ya hadu, gabanta ne ya fadi, lokaci daya, Karin kamarsu sosai ta gani da Yusuf.


Murmushi gefen baki hayder yayi, ya rungume hannunsa tare da jin gina da kujerar. " a zuba min in har ana son inci!" Ya fada da wata irin sansanyar muryar da hubby bata taba jin yayi magana a irin sigar ba.

Kallonsa tayi, ta kalli wormers din. Abincinta ta ci gaba da ci, wayarsa ya fito da ita yana latsawa. Har hubby ta kammala break fast dinta, mikewa tayi, tare da daukar plate da cup din da tayi, anfani dasu, ta nufi Kofa. " Habiba " taji ya kirata. Tsayawa tayi, ta juyo a hankali tana kallonsa.


" I'm serious." Ya fada yana kai kallonsa ga  wormers din.


Juyawa tayi ta tafi, abunta, "saban salo! Ka da Allah yasa kaci mana, da wake serving din naka?" Hubby ta fada a ranta tana Jan tsaki. Tare da ganin laifinta in the first place data dafa abincin ma dashi. Tsaki ta kara ja ta nufi kitchen. Wanke plate da cup din tayi, ganin Mariya bata kitchen din tayi tunanin ko tana gyaran falon sama. Freezer ta bude ta fitar da nama, don yasha iska kafin lokacin daura abincin rana yayi.


Mariya ce ta shigo da womers a hannunta, ta ajiye tare da komawa ta tattaro sauran. Budewa hubby tayi, ga mamakinta komai bai diba ba. Tabe baki tayi. Ta rufe wormers din.


Mariya ta dawo da sauran plate's din. Har hubby ta ce ta samu robe ta juye ragowar sai kuma taga kamar bata kyauta ba. Tashi tayi, ta dau plate ta diba masa abincin, dai dai yadda take tunanin zai iya cinyewa. Ta jera a wani kyakyawan trey, ta dauka ta nufi falonsa.


A zaune ta sameshi ya daura kafa daya kan daya, yana daddanna waya. Da sallama ta shiga, Dagowa yayi ya kalleta, tare da amsa sallamar. Ya ci gaba da abinda yakeyi.


Haushi ne ya kama hubby, ganin yadda ya shareta, ji take kamar ta juya ta koma. Karamin tsaki taja tare da dan harararsa kasa kasa. " in ajiye a dinning din ko in kawo maka nan?"


Ba tare daya dago ba yace mata " kawo nan." A hankali ta taka zuwa in da yake, a gabansa ta ajiye trey din. Tare da mikewa ta tafi. Hannunta ya kamo ya dawo da ita.


" saurin me kikeyi?" Ya tambaya yana ajiye wayar a gefen, Side table.

A kan carpet din ya zauna, tare da mata nunin ta zauna. Ba tare data so ba ta zauna. Idanunsa dake kashe mata jiki, ya zuba mata " kamata yayi in  mace ta kawowa miji abinci, ba  ta dungura masa ta tafi ba, tsayawa zatayi ta tabbatar yaci, tana mai masa hira mai dadi. Kinga koda gishiri, ko barkono yayi yawa, duk bazai jiba, saboda zamowarta a tare dashi."


Dauke kanta tayi. " in da so da kauna a baki ma sai a bashi." Ta fada tana tabe baki kadan


" wow!!! Kice  randa nasrin ta shigo gidana zanga tarai raya?" Ya fada yana smacking


" sosai ma kuwa, mu samman in tana sonka." Ta fada tana kallonsa


Sagensa ya shafa da Zara zaran yatsunsa, Fuskarsa dauke da murmushi. " amma dai bazakiji haushi ba ko, don kinsan ina son mace data iya soyayya sosai, don ba kunyarki zamuji ba."


"Allah ya kiyaye!! Haushin me zanji?" Ta fada tana tabe baki.


Gira ya daga, yare da tabe baki. " haka ne fah! Thanks for the food." Ya fada yana janyo trey din


" za muje kankiya anjima, in kina da sako?" Ya fada yana kai chips bakinsa.


Murmushi ne ya kufcewa hubby " da gaske?" Ta tambaya.


Kai ya daga mata, tare da lumshe idonsa. " in shirya mu tafi tare?" Ta fada cike da zumudi.


Kada kansa yayi. Bata rai tayi " please! "


" nop" ya fada a takaice


Kwabe fuska tayi, kamar zatayi kuka. " don Allah fah? Just one week." Ido ya fito dashi " one week. " ya maimaita.


Kada kai tayi.

" u are not serious. " ya fada in low voice


" don Allah?"  Ta fada tana hada hannayenta biyu.


" ni kuma ki barni da wa?" Ya fada yana tsareta da ido


Baki ta dan tura kadan. " kai kadai mana! Me zai kama ka?" Ta fada cikin muryar lallashi.


" mage zata kamani, ina tsoro gaskiya." Ya fada yana smacking.


Takaicine ya kama hubby, bata San lokacin da ta rarumo pillow din kujerar kusa da ita ba, ta jefeshi da shi.


Tashi tayi, cikin fushi zata fita. Da sauri ya tareta, tare da janyota jikinsa.


" sorry. " ya fada yana dariya


Duka ta kai masa a kirji. " please kuje dani, nayi missing gwaggo sosai." Ta fada


" I'm sorry, not today." Ya fada yana dago da kanta, Kwace kanta tayi, tana kokarin barin jikinsa, Idonta ya ciko da kwalla.

Wai yau ita hubby ke rokon hayder yana mata yanga? Duniya kenan juyi juyi, abun da kake ganin da wuya sai kasha mamakin saukinsa da yuwuwarsa in Allah yaso hakan.


" look Habiba, bani kadai zan tafi ba, muna da yawa, kuma bazan so tafiya dake a cikinsu ba, ki bari zuwa next week sai in kai ki."  Kallonsa tayi, tare da kauda kanta tana sauke ajiyar zuciya. Kai ta kada masa, alamar amincewa.


" good!! Amma a ranar zamu dawo." Ya fada

" aa!! Sati zanyi." Ta fada kai ya kada a hankali

" shi kenan an fasa zuwan."

Haushine ya kama hubby, ganin yadda ya hade rai a dole oga" wai meyasa kake min haka ne? Don kaga ina rokonka shine kake min wulakancin."

"Da week din daya wuce kika tambayeni zan iya barinki, but not now." Ya fada yana tashi a wurin, tare da daukar wayarsa dake ajiye a side table ya zura a aljihu, bayan ya duba time.


" meye ban banci?" Ta tambaya idonta a kansa.


Murmushi yayi mai sauti " tambayata ma kikeyi? Ke kanki kin san difference din."


Harararshi tayi ta mike, ta bar masa dakin don ta lura abun nashi harda rainin wayo.


Rungumota yayi, jikinsa. Kiss ya fara manna mata a wuyanta. Tana ko karin zamewa.


Sukaji sallamar su junaid. Gaba daya suka shigo falon, saboda ganin kofar a bude, Ganin hayder rungume da hubby, suka juya da sauri suka fita.


Tsaki hayder yayi, ya juya yana kallon hubby dake kokarin kwace jikinta daga nashi, cike da jin kunyarsu junaid da takaicin yadda suka samesu.


Kiss ya mata a samman labbanta, da goshinta, ya saketa, Da sauri tabar falon. Murmushi yayi yadau wayarsa ya fita.


"Lafiya kuka juyo haka da sauri,"  amir dake daga bayansu  ya tambaya. Kai Hafiz ya shafa yana kallon junaid dake masa warning da ido, Murmushi yayi. Gamo mu kayi Hafiz ya fada yana komawa jikin mota ya tsaya. Cikin rashin fahimta amir yake mai maita gamo- gamo. " gamo wane iri?" Ya tambaya yana kallon junaid.


" kyale dan iska mu jirashi a nan." Ya fada yana hararar Hafiz dake dariya kasa- kasa

Hayder ne ya fito, hannu ya mika musu suka gaisa. Hafiz na ci gaba da dariyarsa. Harara hayder ya aika masa. " daga yau in zaa shigomin gida a tabbatar na bada izinin shigowa, ba daga sallama a fado min gida ba!"

" masu gida manya!! ayi hakuri. " Hafiz ya fada yana bushewa da dariya.


Murmushi amir yayi " ka mayi kokari, in nine a bakin get zamu dinga haduwa. ba abinda yafi aure dadi, kalli yadda hayder ya canza, in just one month!."

Mortar hayder ya shiga, gaba kusa da junaid dake sit din driver. " kan ku akeji, let go" Ya fada

" kullun nazo gidan nan da kwadayin aure nake komawa gida. I have to get married soon."  Amir ya fada lokacin da suke barin gidan.


Dariya suka yi. " ka samu Abba kawai  da maganar, nan da yan watanni ka shiga daga ciki kai ma." Hafiz ya fada yana dariya


Tsaki amir ya ja " na masa magana, yestaday sai kunga yanda ya taso min kamar zai hadiyeni, Wai su saifullah basu yi maganar aure ba sai ni, Shiyasa gaba daya kartin banzan nan sun fara ban haushi." Dariya su Hafiz suke harda kyakyatawa.


Hayder kam murmushi ne kwance a kan fuskarsa.


" har na tausaya maka, gashi banga alamar su nada niyyar yin aure nan kusa ba." Junaid ya fada


"Barsu hajiyan gano, zan je in samu, dolensu suyi,."

" ka daure kayi masters din da Abba ke son kayi mana, kana dawowa kayi aurenka." Hafiz ya fada


Kada kai amir yayi " ina!!! Da Sana'a ta ni ba komai zan nema wurin wani ba, auren nan shi nake so yanzu. Bayan nayi, na ci gaba da karatun tunda dama akwai niyyah."


" kaida ko budurwar baka da ita, kake maganar aure.?" Hayder ya fada yana kallon amir ta mirror


" hajiyata zata zabo min nima. " ya fada yana murmushi


Dariya sukayi. " to in ta zabo maka wadda bata maka ba kuma fa?" Junaid ya fada yana dariya


" take your time guy, kar kyallin fuskar hayder ya rudeka kayi gaggawar da zakayi dana sani." Hafiz ya fada


"Say something mana." Junaid ya kalli hayder


Tabe baki hayder yayi "what can I say."


" irin jinger da kake sha wurin antynmu, ko ya shiga hankalinsa." Hafiz ya fada


Tabe baki yayi " Ku barshi yayi aurensa in yana raayi."


" thank u broth." Amir ya fada yana murmushi...........Wata uku kenan cif da bikin hubby da hayder,  suna zaune lafiya, kowanne na kokarin sauke hakkin dan uwansa dake kansa, dai dai iyawarsa.+


Har zuwa lokacin ba wani maganar soyayya a tsakaninsu, sai dai akwai shakuwa mai ban mamaki.

Hubby ta kwantar da hankalinta, duk da dayawan lokaci, tana shiga damuwa. Tunowa da zamanta da Yusuf wanda gaba daya sunyi hannun riga da zamanta da hayder. Sai dai dama bata da higher expectation a kansa.


Yau su hayder suka tafi kasar India, shida Hafiz omer. Kayanta take hadawa, zuwa gidan Hajiya kafin ya dawo. Taso zuwa gidansu, amma yaki yadda. Har yanzu a tsorace take da gidan, gani take magen gidan barrister zata kara kawo mata ziyara.


Mariya ce ta dauka mata akwatin, ita kuma ta dauki Jakarta, Suka fita. A gida ta sauke Mariya ta wuce gidan Hajiya.


Cike da farin ciki Hajiya ta tarbeta. " yanzu nake kokarin kiran wayarki,"

Hajiya ta fada tana kallon hubby da faraa a fuskarta.


Cikin shagwabe fuska hubby ta zauna a kusa da Hajiya, tare da daura kanta a cinyar Hajiya. " tun dazu na keson in fito, na jira sai da Mariya tazo, yau ta makara bata zo da wuri ba."


" ya gidan? Ba dai matsala ko?" Hajiya ta tambaya.


Kai hubby ta daga mata.


Sun dade suna hira hubby na kwance a cinyar Hajiya. Shiru Hajiya taji, tana magana hubby bata amsa taba. Kanta ta sunkiyo tana kallon fuskar hubby da tayi wani gaske, sai glowing take, kamar ka taba jini ya fito. Murmushi tayi ganin hubby tayi bacci. Tashi Hajiya tayi ta gyara mata kwanciyarta, da yake 3 sitter ce, kujerar.


Ko ba komai yanzu, hankalinta ya fara kwanciya da zamansu hubby. Kara kallon hubby tayi, tayi kiba kadan, ta murje, kirarta ya kara fitowa sosai, kamar yadda kirjinta, yadan kara habaka. Tayi haske gwanin sha'awa. Masha Allah ta fada cikin jin dadi.


                 ******************


Zaune suke a reception na hotel din da suka sauka.  Ya kara cika, yayi kyau na ban mamaki. Yana sanye da black Jens da light green shirt mai dogon hannu. Kafarsa sanye cikin cover shoe black sai daukan ido yake. Jingina yayi jikin kujerar tare da runtse idonsa. Gaba daya kewar hubby ta lullube shi, bai taba tunanin zaiji kewarta haka ba. Moment dinsu yake tunowa. Bai san lokacin da murmushi ya subuce a kan fuskarsa ba.


Kallonsa Hafiz omer yake, yana kallon yadda hayder ke faman shafa sage, ido a rufe yana murmushi. Duka ya dada masa a cinya. Da sauri ya bude idonsa, da suka fara canza color. Gira ya dagama Hafiz omer " lafiya. "


Kallonsa Hafiz omer keyi, " kai zan tambaya? Nasrin ko antynmu ake tunani haka? Irin wannan smiling "


Harararsa hayder yayi " ban son sa ido."


Ido Hafiz omer ya fito dashi tare da nuna kanshi " nine dan sa idon."

Da ido hayder ya amsa shi, tare da mikewa, let live that place. "


Gyara zama Hafiz omer yayi " u can go, I'm enjoying my self hare."


"Allah ya shiryeka Hafiz, a dai dinga tsoron Allah." Hayder ya fada yana hararar Hafiz


" amen, jeka." Hafiz omer Ya fada yana murmushi


Kada kai hayder yayi, ya nufi lifter da zata kaishi room dinsa.


Gaba daya Allah Allah yake yabar wurin. yan mata ne gasunan sun sha matsatstsun kaya, wasun ma bai sake da tsirara ba, sai kai kowo suke a kansu.


Wayarsa ya dauko, zai kira hubby sai kuma ya fasa, to in ya kira ya ce mata mene? Tun da yazo da su kayi waya da Hajiya taba hubby suka gaisa, ya shaida musu ya isa lafiya, bai sake kiranta ba, haka itama batayi tunani kiranshi  ko sau daya ba. Iyaka ya kira Hajiya. Hajiya kuma, a tunaninta suna waya da juna.


Nasrin ya dannawa kira, ringing biyu ta daga, cike da jindadi.


              ********************

Yau gaba daya main house a cike yake, da yayan gidan mata. Saboda sa ranar bikin Abdul Karim da Abdul fatta da akayi, nan da 3month.


Hubby dasu Aisha, ummu sulaim, Ummul khair. Sun lume a dakin Hajiya. Don tun bikinsu, wannan ne zuwansu gida na farko.


Baka jin komai sai dararrakunsu da shewa. Ummu aiman ta shigo cike da faraa " wai yaran nan me kuke ci a dakin ne, kowa na waje, Ku kun kunshe kanku a daki, kun ishi mutane da ife -ife.'"


Dariya suka sa " an dade baa haduba, so hirar zumunci muke yi." Aisha ta fada


Zama ummu aiman tayi " in zumuncin ne, Ku fito ayi shi gaba daya mana? Ba Ku ware kanku ba."


" wannan hirar tamuce, bama son saura suji." Ummul khair ta fada. Harararta ummu aiman tayi " ai dama nasan ke kam sai addua. A dai dinga son jamaa, don jamaa rahama ne."


Kallon ummu sulaim, aiman tayi, "ke kuma Anty samira na nemanki."

Baki ummu sulaim ta tabe " banni ina nan ina kallon Matar hayder. Don Allah ko ni kadai nake ganin abinda nake gani?" Ta tambaya tana kallon su


" me kike kallo." Ummul khair ta fada tana kwantowa kusa da ummu sulaim


Hubby ta nuna da yatsanta. Dariya Ummul khair ta bushe dashi. " tun tuni nake son inji wani ya fara maganar, kar inyi nawa yayi zafi, kunsan nafi kowa daukar laifi a gidan nan." Ta fada tana dariya.


Harara hubby ta aika mata, ganin duk sun zuba mata ido, sai taji tadan muzanta. " kallon na lafiya ne?" Ta fada

Gaba daya suka sa dariya " Kinga yadda ki kai wani kyau, ki kayi jiki. Gaskiya gaba daya auren yafi karbarki." Aisha ta fada

Tsaki hubby tayi " saboda ni ce marainiyar wayonku ko? Kowacce bata kalli kanta ba sai ni?" Hubby ta fada tana huhhura hanci


Ummu aiman ta dawo kusa da hubby " Anty hubby dan gaya min anya, ba ajiyarmu a nan?" Ta fada tana daura hannunta a kan plat Tommy din hubby. Hannunta hubby ta buge.

" Allah ya kiyaye!!! Ki dai tambayesu, banda ni.?" Ta fada tana harararta


Dariya sukayi " Allah ban yadda da ke ba. Tun da na kawo miki favorite chocolate dinki naga kin ajiye baki shaba, na sa miki ayar tambaya?" Ummul khair ta fada tana kallon hubby


" don ban sha chocolate ba, bashi zai nuna komai ba, just bana jin sha a lokacin ne kawai." Ta fada tana harararsu


P - test, Ummul khair ta fito dashi a Jakarta, "gashi a gwada, in har Anty hubby bata da komai, in zama agwagwa."1


Dariya suka yi, hubby da haushinsu ya isheta, ga faduwa da gabanta keyi. " zako ki zama abun da yafi  agwagwa kuwa. "


Ummu sulaim dake kallon hubby tana dariya. " ke Ummul khair meye naki na sauri? In ma shine, ai baya boyuwa."


" kunfa samin besty a gaba!!!" Aisha ta fada


" Ummul khair naga alama sai na miki wankin babban bargo kafin kibar gidan nan. In har baki fita daga idona ba." Hubby ta fada ganin yadda Ummul khair ke binta da kallo tana dariya


" Allah ya huci zuciyar Amarya a gidan Aliyu hayder. "  mikewa hubby tayi ta nufeta gadan gadan. Waje Ummul khair tayi da gudu tana dariya. Binta hubby tayi sai da ta tabbatar ta fita a dakin ta dawo, tana huci.


" karku ja mana asara, da kananan cik' kunanku kuke wannan guje -gujen." Ummu aiman ta fada tana kallon hubby


Harara hubby ta aika mata, ta zauna a bakin gadon kusa da Aisha

" da yake a ruwa ake sha ba." Hubby ta fada tana duba wayarta


Da kallo dukan su suka bita, baki sake. Ummu aiman ta zaro ido " kar dai duk kayan aikin nan, komai masha Allah, rowarsu akewa kanina."  Banza hubby ta mata, don duk haushinsu take ji.


Tabe baki ummu sulaim tayi, tana mikewa, " meye naki na damuwa Anty sulaim? Komai wayon Amarya sai ansha romonta, balle na yadda da kanina." Ta fada tana barin dakin


Ummu aiman ma baya ta rufa mata, tana hararar hubby, Don har ga Allah ta yadda da abinda hubby ta fada.

Aisha data tsare hubby da kallo, kallonta hubby tayi, ta harareta tare da Jan tsaki. " kallonfa? Me kike jira baki bisu ba?"


Murmushi Aisha tayi, hannun hubby ta kamo ta kurawa hannun ido, idon hubby ta gwale tana kallo, buge hannunta hubby tayi, " ban son iskanci, likitancin naki a kaina zai fara?" Murmushi Aisha ta sake yi. " alhamdulillah ki yadda ko karki yadda tabbas kina da ciki." Ido hubby ta zaro tana kallon Aisha, kirjinta na bugawa da sauri da sauri. A take wani tashin hankali ya shigeta. Amma tai saurin saita kanta.


Dariya tayi. " wasa kikeyi." Daure fuska Aisha tayi " bamu taba wannan dake ba, abin farin ciki ne, amma naga kina kokarin denied, bayan abunda kike nema ne, shekara da shekaru. I'm very happy for u." Ta rungumeta cike da farin ciki.


Tureta hubby tayi " u are joking right? "


" I'm not joking, in baki yadda ba, kije any   hospital a gwada." Aisha ta fada tana mikewa.


Har takai kofa hubby ta kira sunanta, juyowa tayi, tana kallonta. " please don't tell anybody." Murmushi Aisha tayi ta fice a dakin.


" innalillahi wa inna ilaihir rajiun. I'm finish." Hubby ta fada tana shafa flat Tommy dinta. Gaba daya jikinta da zuciyarta sun dau rawa. Tunani ta fara don ta gano amsar ta da kanta.


Zata iya tuna tun bayan haduwarta da hayder batayi mensuration ba. A tunaninta juyin da yake mata ne, don wani lokacin sai tayi 2 months bata yiba. A yan kwanakin kam tafi son Abu mai ruwa -ruwa, yawanci yanzu bata cika cin Abu mai nauyi ba, amma ta danganta hakan da son kartayi gaining weight. Chocolate da sauran kayan zaki ma a kwanakin bata ko sha'awasu. In banda wannan bata jin wani canji a tare da ita.

It can be possible, 4 good years tayi da Yusuf, ko batan wata bata taba yi ba, duk irin magun gunan da tasha don tayi  conceiving, amma shiru. Amma a ce yanzu wai she is pregnant, "pregnant with hayder." Ta fada kasan ranta, tana dafe kanta " no it can be." Ta fada hawaye na bin kuncinta. " ina zan kai wannan abin kunyar ni Habiba." Kwanciya tayi ta ci gaba da kukanta. Jin kamar an tunkaro dakin, tai saurin share hawayenta tare da rufe idonta kamar mai bacci.


Murmushi Hajiya tayi, ganin hubby na bacci. Ta dauki abinda zata dauka ta fita.


               ********************


" don Allah Anty hubby da gaske, maganar da kika fada dazu?" Ummu aiman ta tambaya bayan ta rutsa hubby a daki ita kadai, don abun na cin zuciyarta.


Kallonta hubby tayi cikin rashin fahimtar kan zancen " wace magana kenan?"


" ina nufin da gaske ba abunda ya shiga tsakaninki da hayder har yanzu?" Ta fada tana tsare hubby da ido.


" ba kyau bin kwakwafi Anty aiman.? Hubby ta fada tana murmushi


Harararta ummu aiman tayi " kiji tsoron Allah, kar ki cutar min da kani, kin san girman hakkin miji a kan matansa? Me yasa kike son halakar da kanki, kan wani dalili naki mara tushe? Ko kina tunanin kinfi iyayenmu sanin abinda ya dace ne? Da suka hada ki da hayder?"


Baki sake hubby take kallon ummu aiman, kai ta kada tana jin jina, son kai irin na Anty aiman. " sannu mai dan' uwa." Hubby ta fada tana tashi don tabar dakin.


Da sauri ummu aiman ta rikota " ba haka nake nufiba, kinfi kowa sanin, akwai mutane da yawa da suke zuba muku ido, suga yanayin zaman naku, ba nason a samu kofar da wani zai samu abin fade, amma kiyi hakuri, tabbas bai dace in muku shishshigi cikin lamarin aurenku ba, I'm sorry. " ta fada cikin sanyin murya.


" its OK." Hubby ta fada tare da fita ta nufi falon yara inda su Aisha suke.


Da kallo ummu aiman tabi hubby.  Hajiya ce ta shigo dakin, ganin ummu aiman a zaune ta kalleta" ke kuma lafiya kike zaune ke kadai a nan? Ina sauran yan' uwan naki?"


Ajiyar zuciya Ummu aiman tayi " nida Anty hubby ne, yanzu ta fita."  Kai Hajiya ta kada tare da bude woodruff dinta, don ta dauki kayan da zata sa, fito warta kenan daga wanka.


" amma Hajiya kina ganin zaman Anty hubby da hayder ba wani matsala?" Ummu aiman ta fada cikin sanyin jiki


Barin abinda take yi tayi tana kallon ummu aiman " me yasa kike wannan tambayar?"


" dazu muke tsokanarta a kan tana da ciki, shine take cewa wai  in ba a ruwa zata shaba ba."


Shiru Hajiya tayi, tana nazarin maganar. Juyawa tayi ta ci gaba da shirinta, ba tare da tace komai ba.


Ganin haka, yasa Ummu aiman barin dakin.


Shiryawa take amma tana nazarin maganar ummu aiman. Ita tana nan tana murna, ganin kamar hubby nada ciki, a she shirmen banza take? Kada kai tayi, yaran yanzu sai Allah ya shirya. Hubby son girma, hayder son girma, watan an rasa mai sauke nashi? In sun san wata ai basu san wata ba.

Ta wani gefen kuma tana kwakwkwanton maganar ganin, daga hayder din har hubby, sunyi kyau, sun murje abinsu, alamar kwanciyar hankali, Koma menene she will find it out.


Washe gari su Ummul khair, kowacce ta koma dakinta.


Gaba daya hubby ta shiga damuwa, gashi ta rasa hanyar da zata bi ta fita, at lest ta je ko hospital ne, amma ta rasa dabarar da zatawa Hajiya. Gashi nauyi da kunya, ya hanata ta amshi P -Test din Ummul khair.


                 ****************

Kwanan su hayder goma, a kasar India, kafin suka nufo gida Nigeria.


Hajiya tasa hubby da mai aikinta, suka gyara dakin hayder, don tun da yabar gidan ba kowa a ciki. Tare da turara, turaren wuta,  Hajiya na sane da dawowar hayder a ranar. Abunda ya kara sa jikinta sanyi, bata ga hubby na wani shirin tarbar mijin nata ba. Ya kamata tayi mata maganar zuwa share gidansu, da goge- goge, tunda sun dade basa gidan, gashi an fara sanyi. Amma hubby bata yi mata maganarba, itama share wa tayi.


Hubby kam bata da masaniyar dawowar hayder. Mantawa ma wani lokaci take dashi, sai in ta tuna da damuwarta tukun take tuno da musabbabin.

Girki na musamman Hajiya tasa hubby ta mata, aka zuba a wormars masu kyau da daukar ido.


Suna zaune a falon Hajiya, wurin 8:9 na dare. Hubby na sanye da cotton material, dinkin bubu, mai shape. Yayi mata kyau sosai ya zauna a jikinta, material din irin mai sharking din nan ne, saboda full stones. Shima Kamar yadda jikinta ke rawa, in ta motsa, haka yake sharking, tare da daukar ido. Sai gyalensa da ta rufe  kanta dashi. Simple makeup ne a fuskarta.


Tana kwance a cinyar Hajiya kamar yadda ta mayarma Hajiya cinya filo. Suna kallon news. Tare da hira jefi jefi.

" ni kam Ummi, kin shanye abinda na baki, ko yauma ajiye min shi ki kayi?"

Baki hubby ta turo, cike da shagwaba, don ji take in tana tare da Hajiya, kamar tana tare da gwaggonta ne. " zan sha anjima."

Bata rai Hajiya tayi " tashi ki dauko min, haka jiya kikayi, karshenta sai zubarwa akayi." Tashi hubby tayi taje ta dauko kofin mai cike tugudi, wanda yaji kayan kamshi. Zama tayi tana sha tana bata rai. Don harga Allah yanzu bata son Abu mai zaki, ji take har tsakiyar kanta.

Mikawa Hajiya tayi " na koshi." Karba Hajiya tayi ta duba cup din, ganin tasha ba laifi ta ajiye shi a kan side table.


Sallamar da suka ji, yasa su maida kallon su bakin kofar, Hajiya dauke da fara'a, yayin da hubby zuciyarta ke faman dukan uku- uku...........Rungume juna sukayi da Hajiya, tana "oyo-oyo auta, bakin India."+


Hubby kam daskarewa tayi a wurin tana kallonsu, tasan girman soyayyar dake tsakanin Hajiya da autan nata, bata hada son sa da kowa, cikin yayanta.


Har lokacin zuciyarta rawa take, ganin yadda hayder ya kara haske, da ciki. Sanye yake da kananan kaya. Trouser army green da White shirt, mai layi- layin army grean color. Hannunsa daure da black  I phone watch. Ga wani kamshi, mai dadi da sanyi daya cika dakin.


Zama yayi kusa da Hajiya, suka fara gaisawa, da tambayarsa hanya. " "alhamdulillah tafiya tayi riba." Ya fada yana kallon Hajiya yana murmushi.


Lallausan gashin Kansas, da yasha gyara, sai daukar ido yake, ta shafa " Masha Allah, Allah yasa albarka a abunda ake nema."

" amen." Ya fada yana kai kallonsa kan hubby, da gaba daya take kokarin jawo jaruntarta. Ido hudu sukayi. Cikin rawar murya " ka dawo lafiya."


Smacking yayi, " na sameku lafiya." Ya fada still idonsa na kanta. Don wani kyau yaga ta kara masa, daga zaunen da take, yana iya hango komai mu samman kirjinta daya kara cikowa. Shigar tata ta burgeshi sosai. Maganar Hajiya ya dawo dashi hankalinsa.

Murmushi yayi, yana shafa sajensa. Harararshi hubby tayi, kasa- kasa. Don ta lura bashi da kunyar kallo, gashi ta kasa tambayarsa abun da yake kallon, kullun ya tsareta da mayun idonsa.


Hajiya ta kalli hubby " ki shiryawa auta table. "


Tashi tayi, don ta nufi dinning. " no barshi tukun, kisa a warmer in munje gida naci, yanzu ban jin yunwa." Ya fada yana kwanciya tare da daura kansa a cinyar Hajiya. " I miss this very much. " ya fada yana lumshe ido.


" daga kai har matarka in kun karsa min cinya kun huta, kun mayarmin da cinya kamar filo."  Kara gyara kwanciya yayi, cikin shagwabar da yasa hubby sake baki tana kallon ikon Allah, duk da ba yau ta fara ganiba, amma a tunaninta ya girma yanxu. " ki daina barinta tana kwanciyamin a cinya. It's ally for me. "


Dariya Hajiya tayi. " kai ma yaranka na xuwa, ban sake yadda ka kwanta min a cinya."


" kai Hajiya, autanki ne fah? Su ma  suna da cinyar mama ai."

" tawan dai zaku bar musu, suma su Mora." Ta fada tana murmushi


Hubby kam kunya ne ya kamata, musamman irin kallon da Hayder ke mata a kai- kaice, yasa ta kasa sakewa. Mikewa tayi, zata koma dakin Hajiya.


" ki dauko akwatinki, mu tafi." Ya fada

" aa hayder! Ku kwana a nan, gobe in sha Allah ido na ganin ido, sai Ku tafi, tunda baa gyara gidan ba, gashi yanzu an fara sanyi, akwai kura. Nasa an gyara maka dakinka."


Ba haka yaso ba, " OK, bari in je inyi wanka, sai in ci abincin."


" Ummi debo masa ruwan zafi, a toilet dina. Na manta baa gyara water hitter din dakin ba."


Tashi hubby tayi, ta nufi dakin Hajiya.

Shi kuma, ya dau wayarsa ya shaidawa driver ya shigo masa da kayansa."


                ********************

Ta gama hada ruwan tana kokarin fitowa falon, shi kuma yana sawo kai dakin.


Matsawa tayi, ta bashi hanya. Kallon kallo, a ka tsaya yi, tsakanin hubby da hayder. Ganin bashi da niyyar bata hanya " Hajiya na falo, bari in wuce."


" and so." Ya fada yana daga mata gira

Kokarin bi ta gefenshi tayi ta wuce. Jefa jakar hannunsa yayi kan bed din, ya jawota zuwa jikinsa. A tare suka sauke ajiyar zuciya. Kara rungumeta yayi a jikinsa. Yayi missing everything about her,. Ga wani filling dake fusgarsa, Allah -Allah yake ya dawo gida, gashi Hajiya ta rusa masa plans, sai yanzu yayi regretting turota, da tana gidansu, ba abinda zai hanashi nemar ma kanshi natsuwa a yanzu.


Da kyar hubby ta kwace jikinta, tayi falo da saurinta.  Dafe kirjinta tayi " thanks to Allah. " Hajiya bata falon.


Jingina yayi da bangon dakin, yana maida numfashi. Ya dade a haka, kafin ya lallaba ya shige toilet. Yana jin jina, yadda yau zai iya bacci ba tare da ya sauke damuwarsa ba. Don ganinta gaba daya ya kara rikitashi.


Hajiya tasha mamakin ganin hubby kwance a falo. Kai ta kada ta nemi wuri ta zauna.


Sanye ya fito da kayan bacci farare. Yayi kyau, sai kamshi ke tashi. Direct dinning table ya wuce.


Kallo daya hubby ta masa, ta dauke kanta. Ido suka hada da Hajiya, kunya ce ta kamata. Da sauri ta mike ta nufi dinning table din, don tayi serving dinsa. Ko don ta cire zargi a zuciyar Hajiya


Hannayenta yake bi da kallo, yadda sukayi kyau, sukayi wani haske, kamar ka taba jini ya fito. Kallonsa ya kai kan fiskarta, ta kara haske sai glowing take. Bakin nan yasha pink wet lips.


Harararsa tayi kasa- kasa. Jin ya kamo hannunta, yana murzawa a nashi. Wani shock ne gaba daya ya xiyarcesu, Hajiya ta kalla, ganin hankalinta gaba daya yana kan nta news. Yasa tasa daya hannun da nufin banbare hannunta.


Duka hannun biyu, ya rike yana murzawa a hankali. Kiss ya mata a hannun, sannan ya saketa, ganin yadda take a tsorace.


Abincin ya masa dadi, amma darene, don haka kadan yaci, ya hada green tea. Ya koma kusa da Hajiya yana sha suna hira sama - sama.


Mikewa hubby tayi ta shige dakin Hajiya, wanka tayi, ta sa kayan baccinta, tare da feshe jikinta da turare masu sanyin kamshi. Tayi kwanciyarta.


Tsayawa Hajiya tayi, tana bin hubby dake sharar baccinta hankali kwance da kallo.


" Ummi, Ummi." Hajiya ta fada tana dukan kafar hubby kadan.


Bude ido hubby tayi mai cike da bacci, tana kallon Hajiya.


Daure fuska Hajiya tayi. " oya tashi ki wuce wurin mijinki, bazaki kwana min a nan ba."


Ido hubby ta zaro, tare da shagwabe fuska tana turo baki. Zatayi magana Hajiya ta katseta. " tashi kafin ranki ya baci, bada ni zaayi wannan rashin hankalin ba." Mikewa hubby tayi, tana tura baki. Zani ta daura akan kayan baccin, tare da zunbula hijab dinta. Hajiya na kallonta, bata ce komai ba. Sai da tazo zata fita, ta kirata. Dawowa tayi, Flack's Hajiya ta mika mata, irin 5 liter electric Flack's, wanda zaka jona shi da wuta, kamar kettle.


Kallon Flack's din tayi, ta kalli Hajiya cikin rashin fahimta. " kije dashi, ko zakusha tea."  Dauka hubby tayi ta wuce, cikin sanyin jiki. Ajiyar zuciya Hajiya taja tare da shirin baccinta ta kwanta.


A hankali ta tura kofar ta shiga. Kwance yake yana juyi, gaba daya hankalinsa a tashe yake, tunanin yadda zai fito da hubby daga dakin Hajiya yake yi, don gaskiya bazai iya hakuri ba. Yaji an bude Kofa an shigo. Ajiyar zuciya yayi, tare da fesar da iskar bakinsa. Wani dadi ne ya ziyarci zuciyarsa tare da furta " alhamdulillah" a saman labbansa.

A kan table ta ajiye Flack's din. Dakin tabi da kallo, a tunaninta yayi bacci, ganin wuta a kashe, sai hasken fitilar waje dake hasko dakin. " wannan Flack's din kuma fah?" Ya tambaya yana tashi zaune.


Gabanta ya fadi, jin maganar kamar daga sama. " Hajiya ta ce in taho dashi, ko zaka sha tea." Murmushi yayi yana shafa kansa. Tare da godewa Hajiya a ransa.

" ta kyauta kam, kamar tasan ina da bukatarsa sosai."

Kofar fita hubby tayi, da sauri ya tsayar da ita. " ina kuma zaki?" Ya tambaya yana kallonta


" wai zan kawo maka kayan tea din ne." Ta fada


Smacking yayi, Tare da mika mata hannunsa. " I have them already, let me show u." Dawowa tayi ta tsaya, ba tare data mika masa hannunba.


" ban son Jan aji, I know you Miss me." Ya fada yana jawota ta fada saman jikinsa, in da ya mata kyakyakyawar runguma. " please hayder, Hajiya nanan, she can hear us."  Hayder kam bama ya jinta, hijab din da zanin ya zame ya watsasu gefe.


Gaba daya jikinsu, rawa yake, hubby kam harda na tsoron kar Hajiya ta jiyosu. Don dakunan a Jere suke da juna. Hayder kam tsabar bukatuwa, yasa yama manta da Hajiya can hear them.


Hajiya kam ranar kwanan dakinta, bai samu ba, sai dakinsu ummu sulaim ta kwana. Hankalinta kam yanzu ya kwanta, dama abinda take da bukatar tabbatarwa kenan.


Tunaninta da wane idon zata kalli Hajiya, don ta tabbatar ba abinda zai hanata jiyosu, kasan cewarta mutun mara nauyin bacci. A gogon gefen gadon ta kalla 4am dai dai lokacin da hayder ya fito daga toilet din. Jallabiyya ya zura, tare da shinfida dadduma ya kabbara sallah.


Tashi tayi, duk jikinta yayi tsami.  Tsaki tayi a hankali, taga alama ciwon bacci sai ya kamata in batayi da gaske ba, a ce mutun baya gajiya, a dare sai tayi wanka ya kai  hudu- biyar. Duk don karta kwanta da najasa, amma sai ya San yadda yayi, ya bata mata wankanta.


A hankali ta bude dakin ta fita, dakinsu Ummul khair ta wuce, ga mamakinta, mutun ta gani kwance a kan gadon ummu sulaim. Da sanda ta nufi dakin Hajiya. Ganin bata dakin ta sauke ajiyar zuciya. Toilet ta wuce, ta tsarkake jikinta, tare da dauro alwala.


Hand rayed tasa ta busar da kanta. Ta maida kayan baccinta. Sai da tayi sallar asuba, sannan ta dale gadon Hajiya, taja bargo nan da nan bacci yayi gaba da ita.


Hajiya na kallon hubby, murmushi tayi tana binta da kallo, yadda take sanda abin ma har yaso yaba Hajiya dariya. Wai nan ita a dole mai wayau. In dauka kamar a dakinsu ummu sulaim ta kwana. Hubby na fita, ta tashi ta dauro alwala ta kabbara nafila.


Sai to 9, ya shigo gidan tun daga fita sallar asubah. Ba kowa a falon, kai tsaye yayi dakin Hajiya. A gadonta ya hango hubby lullube da bargo, tanata bacci, hankalinta kwance.

Karasawa yayi dai -dai fuskarta, lallausan hannunsa yasa yana shafa fuskarta a hankali, gyara kwanciyarta tayi " lazy bone." Ya fada yana sumbatar goshinta.


She look beautiful, sai yanzu ya kara karewa fuskarta kallo,ta kara kyau, tayi haske kamar ka taba jini ya fito, bakinta ya kai idonsa da zagayen bakin ya kara bifowa sosai,. Bakinsa ya kai ya sumbaci labbanta, sannan ya fita. A falo suka ci karo da Hajiya tana shigowa.


Rungumeta yayi, tare da gaisheta. Cike da faraa Hajiya ke amsawa, tare da tambayar gajiyar hanya.


" alhamdulillah. " ya fada yana nufan dinning table.


Yana fita, ta mike, tare da kai kallonta kan agogon dake makale a bangon dakin yana kallonta, After 9. Da sauri ta sakko daga gadon, cikin sauri sauri ta gyara gadon, tare da gyara dakin. Wanka ta shiga, bayan ta fito ta shirya cikin wani red Chinese dress, mai matukar kyau da santsi.  Riga da wando. Simple makeup tayi, cikin sauri take shiryawa don ko Hajiya bata gaisar ba.  Red Vail ta yafa, Wanda ya dace da kayan, ta feshe jikinta da turaruka bayan deodorant da humra, ta tasa a jikinta.


Cike da jin nauyi ta gaishe da Hajiya. Cike da faraa take bin hubby da kallo. " masha Allah, wannan kwalliya tayi kyau. Kamar mai zuwa gasar sarauniyar kyau?" Hajiya ta fada dariya hubby tayi " tsarabar China da junaid ya kawo min."


" ya kauta, sunyi kyau, suka kuma tarar da kyan."  Hajiya ta fada tana mikewa " maza kije kici abinci, gashi can har ya huce." Ta fita a falon


Gaba daya idonsa na kanta, tunda ta fito, kamshin turarenta ya fara masa sallama, gaba daya shigar tata ta matukar burgeshi, kayan sun mata matukar kyau, kamar don ita aka halittasu. Kasa dauke idonsa yayi a kanta.


Takunta da yadda jikinta ke juyawa, gwanin sha'awa ya zuba ma ido, yana tasbihi a ransa.


" ban son kallo." Ta fada a hankali tana Jan kujerar dinning din daya, ta zauna.


Smacking yayi " its my property. " ya fada in his husky voice


Gug din kunu ta jawo ta zuba a cup. Ta kai bakinta, Still idonsa a kanta. Harararsa tayi, ji take kamar ta makeshi, wannan murmushin rainin hankalin da yake binta dashi.


" kayan sunyi kyau, ina imagining dinsu a jikin My Nasrin." Ya fada


Sai da ta hadiye kunun bakinta cikin tabe baki. " in kana so, sai in cire ka kai mata."


Jingina yayi da kujerar sosai, yana shafa sagensa. " ya zama second use."

Tabe baki tayi " good for u."

Waina da soup din kayan cikin, data zuba zata ci, ya janye gabansa.


Kada kai tayi, ta zuba wani.


" ki shirya da wuri." 

Kai kawai ta daga mishi.


Mariya ce ta shigo, ita da mai aikin Hajiya. A nan take shaidawa hubby tun safe Hajiya ta sasu suka je gyaran gidan, dawowarsu ke nan.


Hubby taji dadin hakan.

              *******************

Hajiya da Hajiya Balkisu, suna zaune a falon Hajiya suna hira irin ta aminan juna. Don zuwan Hajiya Balkisu kenan bata dade ba. Hubby ta fito rataye da Jakarta. Ganin Hajiya Balkisu yasa ta rusuna tana gaisheta. Cike da faraa take amsa mata, tare da tambayarta mai gidan.


" yayi, tafiya ne, shine aka zomin kwana biyu, Jiya ya dawo. So zasu tattara suyi gidansu." Hajiya ta fada cike da jin dadi.


" Masha Allah, mun gaisa da hayder din ai yanzu da zan shigo."


Sallama hubby ta musu, cike da kewa Hajiya ta sallameta, part din Mmn samira da Mmn Yusuf taje ta musu sallama, ta fito already hayder na cikin motarta driver sit yana jiranta.


              *******************

" kinga ikon Allah ko? Wannan shine rabo ajali." Kallon  rashin fahimta Hajiya kebin Hajiya Balkisu dashi. " ban gane maganarki ba." Hajiya ta fada


Baki Hajiya Balkisu ta rike " kar dai ace, baki hango abinda na hango ba, duk kwana kin nan da kukayi tare?"


Zama Hajiya ta gyara, tana fuskantar Hajiya Balkisu da kyau. " kin kara Sani a duhu."


Cike da mamaki Hajiya Balkisu ke bin Hajiya da kallo " zaki ce min baki ga alamun ciki a tattare da Habiba ba?"


Kara gyara zama Hajiya tayi " ciki fa kika ce?" Ta tambaya


" sosai ma kuwa ciki." Hajiya Balkisu ta fada With Confidence


" kinsan ni in ba laulayi naga mace nayi ba, bana ganewa, sai kuma in ya fito."  Hajiya ta fada


" lallai kuwa, amma tabbas ciki ne jikin Habiba. "


Da sauri Hajiya ta tashi ta rungumeta Hajiya Balkisu cike da farin ciki. Dariya Hajiya Balkisu tayi. " auta ya girma, mun kusa zama kakan nin asali."

" kai!!! Na so in zargi hakan, amma ganin ba wani laulayi take ba, na dauka kawai cikar daki ne, da kwanciyar hankali. Ashe abin farin ciki ne? Wai!! Allah na gode maka, daka nunamin wannan rana ta farin ciki. Yau ina masu kiran Ummi juya? Yanzu kuma mai zasu fada kenan?"

" barsu tukun, Lokacin maida martani na nan zuwa, very soon." Hajiya Balkisu ta fada tana murmu

Post a Comment for "DA KAMAR WUYA CHAPTER 6 BY ZULAIHAT IDRIS MISAU"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...