DA KAMAR WUYA CHAPTER 3 BY ZULAIHATIDRISMISAU - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DA KAMAR WUYA CHAPTER 3 BY ZULAIHATIDRISMISAU

DA KAMAR WUYA CHAPTER 3 BY ZULAIHATIDRISMISAU

- - Post a Comment

 DA KAMAR WUYA CHAPTER 3 BY ZULAIHATIDRISMISAU                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wani bakin ciki da takaicine ya cikata a lokaci daya. Nan take ta kara tamke fuska, tare da shigewa farfajiyar gidan.+


Bayanta ya bi fuskarsa cike da murmushi Wanda hubby ta dauke shi a rainin hankali.


Sanye yake da black Jens, da shirt mai gajeran hannu, maron colour  mai cubes din adon baki. Kafarsa sanye da covershoe baki, sai agogo silver mai matukar daukar ido, kamar yadda gashin kansa yasha gyara tare da siririn sajen daya hade da gemun da aka sai sayeshi sosai, Wanda ya karama fuskar kyau da kwarjini. Kana ganinshi kaga big guy mai ji da ilmi da hutu, musamman yadda fatarsa ke glowing duk da yake baki.


Ganin tana kokarin shigewa ciki ta barshi yasa shi shan gabanta cikin sauri. Yana mata wani hadadden smiling mai fallasa sakon zuciya ga maabociyar zuciyar.


" me yasa kike hakane? Kin ce nazo yau. nazo tun 4:30pm ina kofar gidan nan, ina faman tunanin ta yadda zan samu mai kiramin ke, tun da kin hanani phone number, Ban samu ba. Allah yaji kaina ya turo min ke. Ta ina kike ganin zan bari ki subuce min?"


Kallon gefenta tayi, " zan fito ai, daga rakiya bai kamata aga na dade ba."


Murmushi yayi yana cikin jin dadi " OK. Ai da sai kiyi bayani." Ya fada yana bata hanya.


Da sauri ta shige cikin gidan. Da kallo ya bita yana murmushi, wani farin ciki ne ya lullube zuciyarsa. Runtse idonsa yayi yana furzar da iskar bakinsa. "Ya Allah" ya fada a hankali tuno kyawawan hannayenta masu dauke da dogayen yatsu, kumbunan dogaye sun sha adon bakin lalle, lukui lukui dasu, haka kafarta gwanin shaawa, kamar ka taba jini ya fito, duk da ba fara bace, amma tanada haske mai daukar ido, don bazaa kirata chocolate ba. Yadda ya lura da juyawar jikinta, ya sa shi shiga wani yanayi,  duk da tana sanye da dogon hijab har kasa, ash mai hannu. don ko kayanta na ciki baka iya hangoshi ta kasa. Sai plat shoe yellow mai adon White stones manya. Wanda ya kara fito da kyan kafafunta.


" ya Allah, suraj aure kazo nema fah!" Ya tunawa kansa tare da shafar sajen kansa. Yana sauke ajiyar zuciya.


"I wander abun da yarunyar nan ke boyewa cikin wannan zunbulelen hijaban, ko zafi bata ji." Wata zuciyarsa ta fada


Kujerun roba ya hango kusa da wani daki, da gani dakin megadi ne, amma bai ga alamar akwai megadin ba. Biyu ya jawo tare da zaro handkerchief a aljihunsa ya goge sannan ya gyara zamansa, kafa daya akan daya yana bin gidan da kallo. "Not too bad"  wata zuciyar ta fada


Gidane dan dai dai, ginin zamani, mai wadataccen fili, da shuke shuke.


Gwaggo ta samu a tsakar gida " har sun tafi." Ta tambayeta " eh!!!"

" To Allah ya saukesu lafiya."


" amen" hubby ta fada tana kallon gwaggo ta rasa yadda zata gaya mata.


Ganin yanayinta yasa gwaggo ta kalleta da kyau " lafiya dai ko?"


Tsaki hubby ta ja dan shiru tayi kafin ta iya lalubo abin cewa. " wannan da nake gaya miki ya takuramin tun a saudiyya, shine mukaci karo dashi, yanzu haka yana get."


Baki gwaggo ta washe " masha Allah. Maza jeki  kin barshi a tsaye, ai haka ba kyau."


Harararta hubby ta yi ganin yadda gwaggo take faraa kamar wadda akawa albishir da gidan aljanna. ". Ke maza wuce mana, kika tsayamin akai."


Har hubby ta juya zata fita gwaggo ta kirata. " a haka zaki fita? Ba dan ko gyara fuska, balle aje da bashi ruwan sha? Ke kuma kalan naki kenan?"


Juyawa hubby tayi ta fice tana mai jin haushin gwaggo dashi kansa suraj din

Bai kai matsayin da zata tsaya tana wani kwalliya saboda shi ba. Mutun daya ne, kuma yanzu babu shi. Ita yanzu neman hanyar da zata rabu da wannan karfen kafar takeyi.


Murmushi ya sakar mata, tare da nuna mata kujerar dake kusa dashi. " bismillah gimbiyata"

Harararsa tayi tare da janye kujerar can gefe ta zauna tana kallon gefenshi. Shi abun ma dariya ya bashi, ganin tazarar data bayar a tsakaninsu.

Matsowa yayi kadan, still akwai space a tsakinsau. Shirune ya biyo baya, na wasu minute.

Kallonta yake yana godiya ga Allah, tare da fatan ta zamo rabonsa. Don shi kansa baisan iya adadin son da yake mata ba.

" kiyi hakuri, nasan na matukar takura miki, I'm sorry."

Shiru tayi masa, ganin bata da niyyar tanka masa yasa ya gyara zamansa. Cikin muryarsa mai dadin sauraro ya fara da " labarin zuciya, masu iya magana suka ce a tambayi fuska. Nasan kin dade da gane manufata a kanki, but yana da kyau kiji daga bakina. Da farko sunana......" Nan ya bata takaitaccen tarihinsa da matakin da yake a yanzu na aiki, ya kara da tun ranar da idona ya sauka a kanki, zuciyata ta kamu da so da kaunarki, Wanda ni kaina ban san adadin son da nake miki ba. Tun daga lokacin na rasa walwala, da natsuwa, har sai idona yayi tozali da naki, koda bazan ji ko kalma daya daga bakin kiba. Ina fatan ki bani dama na shigo cikin rayuwarki, na tabbata ba zakiyi dana saniba, aure nake fatan ya kasance a tsakaninmu nan da dan lokaci kadan, in sha Allah. "

Shiru yayi yana kallonta da kokarin gano yqnayin da take ciki.

Wasa take da yatsunta, a hankali ta dago ta kalli gefensa, tare da sauke ajiyar zuciya. Wani murmushi ne ya subuce mata, saboda idea daya fado mata a rai. Ta dan kalleshi kadan yanda ya kafeta da tsayayyun idonsa yasa tai saurin dauke nata idon.

Dadine ya cika suraj ganin Murmushinta Wanda ya bayyanar da jerarrun kyawawan hakoranta, masu dauke da wushirya. Yana ganin Wanda murmushi ke musu kyau, amma bai taba ganin wadda mirmushi ya mata kyau irin hubby ba.

Cikin muryarta mai dadin sauraro, kamar ana busa sarewa ta ce. " na gode da kaunarka gareni. But ina baka hakuri, don abinda kake so bazaka samu ba."

Kallonta yake cike da so da kauna. Ko kadan kalmarta nata girgizashi ba, don ya dade da sanin hakan, ko yadda ta ki saurarensa yasan zai sha fama da ita. " ko zaki iya gayamin dalili?"

Sai da taja numfashi sannan ta amsa shi " ba wannan a tsarin rayuwata. Sannan kai kanka kasan abinda kazo dashi ba mai yiwuwa bane, so kayi hakuri."

Shafa kansa yayi yana Kallonta. Murmushi yayi " ko zan san dalili.?

Kallon gefen ido ta masa, cike da jin haushi don duk ta kosa ta shiga gida, jinta take kamar akan kaya. Amma ta lura wannan mutumin ya wuce inda ta ke zato a naci. So bari ta masa gwari gwari. " na taba aure, Allah yama mijina rasuwa."

Wani kishi ne ya mamaye zuciyarsa, amma yanzu ba lokacin nuna kishi bane, duk da ya dade da sanin hakan.

" I known. "Ya fada a hankali tare da karawa da " Allah yaji kansa yasa aljanna ta zama makomarsa."

" amen ya Allah. Na gode."

Ta fada, tare da jin zuciyarta na karyewa. " shine mutun na farko da zuciyata ta aminta dashi, ina fatan ya zama na karshe, so na yanke maganar sake aure a rayuwata, har zuwa nawa lokacin. Ina fatan yadda muka rayu a nan duniya, mu rayu a aljannatul firdaus in sha Allah. "

Kallonta yake yi, ya tabbatar iya gaskiyarta ta fada, don idanunta har sun kada sun canza launi. Ajiyar zuciya ya yi.

" ita rayuwa da kika ganta ba mu muke tsarawa kanmu yadda muke son ta tafi ba, huwacewa ce ta ubangiji. Ni nayi imani Allah ya kawoni rayuwarki ne don in maye miki gurbin abinda kika rasa. Don in nayi laakari da tawa rayuwar, wata uku baya duk Wanda zai gayamin zan tsinci kaina a matsananciyar soyaytar wata, tabbas zan ce karyane. Amma ta shi daya Allah ya sanya sonki da kaunarki a raina. Wanda har nake ganin in baki  rayuwata bazata yiyuba. Ina rokonki da ki bani dama, ko ban zama 100% at least  kya samu 80%. "

Shirune ya biyo baya, kowa da abinda yake sakawa.


" 1 baka taba aure ba, ni nayi for 4 good year's. 2 your billionaire only son, I'm no bodys daughter. You're educated, I'm just ordinary secondary school woman. I'm barrier women also."


Ta fada tana kallonsa " so please live me along. Kaje ka nemi dai dai kai."


Murmushi yayi " duk abubuwan da kika lissafo ba Wanda ban Sani ba. I known everything daya kamata na Sani a kanki, so please give me a chance, that all I asks for. "


" sorry. Kamar yadda na gaya maka ne, ba aure a rayuwata. So please ka gyaleni kawai."


Shiru yayi for sometime yana nazarinta da kalamanta.  " OK zan baki lokaci kiyi shawara, sannan kiyi tunani."


Kallon sa tayi kafin ta galla masa harara. " ni kam me yasa baka da ganewa ne? Bana bukatar wani lokaci, ko tunani. This is my decision."


Murmushi yayi " Allah ya huci zuciyarki, I understand  know. Ki bani phone number dinki to, ko gaisawa mu dinga yi."


Karamin tsaki taja ciki ciki. " bani da phone. "

Dariya ce ta kufce masa, yadda take wani shan magani.

Phones din dake hannunsa I phone 10, ya zare sim din ya mika mata. Kallonsa tayi, ta kalli phone din, ba tare da ta nuna ko alamar karba ba. Ta dan tabe baki " bana bukatar ta ne, Shiyasa ban rike ba, bawai don bazan iya mallakanta bane."


Murmushi yayi " na sani, nima ai bance bazaki iya mallanta bane. Amma bazan iya barin nan ba, ba tare da na Samar da wata hanyar da zan dinga jin ko muryarki ba ne. So please ki karba, yanzu zan dauko miki sim card a mota."


" kabar kayanka, don bani da ingress akan rike waya."


" kin yadda in dawo next week?" Kallon data masa ne ya sa shi sakin dariya. " I'm sorry na cika naci ko?"


Ta shi tayi ta nufi cikin gida " don't come hare again. " ta shige ciki


Murya yadan daga yadda zata jiyosa " sai nazo next week. Thanks for the time u give me. " ya juya yana murmushi ya fice.


" yarinya naki wasane yanzu muka fara." Ya fada yana tada motar.


               ********************


Tun isowar suraj a idon Hashim, har tafiyarsa. Yana daga benen gidansu yana hango wurin da suraj yayi parking, yaga lokacin da yabi hubby ciki. Zuciyarsa ta fara zafi, ya rasa sukuni, don haka ya fito ya nufo gidan. Amma abinda ya kara rikitashi ganin shi zaune da hubby a farfajiyar gidan. Da sauri ya juya.Wani nauyi ya ji kirjinsa ya masa. Sam idonsa ya rufe har baya iya ganin gabansa. Karo sukaci da abokinsa muh'd shima mazaunin unguwarne.


"Aa doctor daga ina haka? I hope lafiya, na ganka a hargitse.

Ajiyar zuciya yayi, yana Jan numfashi. "I'm in trouble friend"


Kallonsa muh'd ya yi na dan lokaci, yana nazarinsa fuskarsa dauke da murmushi. " ko dai zargin da nake ya tabbata. "


" na me fah" Hashim ya tambaya

" you're in love with habiba, right?. "


Kallon muh'd Hashim yayi, kafin yayi murmushin " yes friend. How do u known? "


" tun da naga kana sintiri a garin nan, nasan akwai bayani ai." Ya fada yana dariya.


Fitowar siraj, yasa duk hankalinsu ya koma kansa. Kasan cewar suna kusa da inda yayi parking ya sa shi yi musu sallama tare da mika musu hannu. Cikin mutunci muh'd ya mika masa, kafin ya juya ga hashim da ke dan basarwa, haka dai ya daure ya mika masa hannu. Zuciyarsa na zafi, kamar ya mangareshi.


" suraj  kangiwa right.?" Muh'd ya fada still da murmushi akan fuskarsa. shima murmushin ya masa " right " kara mika masa hannu Muhd yayi. " nice to meet u, I'm Muhammad mustafa, that my friend doctor Hashim Adam. " 

" nice to meet u too." Ya fada yana murmushi tare da musu sallama, don ya kagu ya bar wurin, ganin irin kallon da Wanda aka kira da doctor Hashim yake binsa dashi.


Bayan bacewarsa ne, muh'd ya kalli Hashim " lallai kam kana cikin matsala abokina. Suraj kangiwa da kansa?."


Cike da jin haushi, Hashim ya ce " saboda iskanci kuma ka zauna kana washe masa baki. Naso in mangare ka, daga kai har shi din."


Dariya muh'd yayi. " I'm sorry, so nake na tabbatar da cewa shidin ne."


"To yanzu da ka tabbatar sai me?"


" let go and find the place to discuss the issue."


              *******************


Gwaggo sai faman washe baki take " har ya tafi?"


Haushine ya cika hubby, so ko kulata bata yi ba ta fara cire hijab dinta.


" ke kam anyi sokuwa, kayi bako ko ruwa baki bashiba har ya tafi? Wannan ai ba hali mai kyau bane, rowa."


" ke meya hana ki dauki ruwan ki kai masa tunda kin damu da yasha?." Ta fada cikin jin haushi


" ai sai in kai masa, ina laifin mai son naka?" Gwaggo ta fada cikin son tura haushi

" sai ki sa himma ai."


" a cikinta nake kin sani, bako bai taba sa kafarsa a gidan nan ba, sai ya sha yaci na tabbatar bashi da damuwa in dai ta cikin sane."


Shiru hubby ta mata, don tasan in har ta tanka to sun dinga kenan, ita kuwa bata da lokacin wannab. She have so many things in her plates.


" ki kira mommynki, ta kira tana maganar zuwa co gurandin din su junaid ko me? Ban gane zancen ba."


" graduation, aka ce." Hubby ta fada tana murmushi.


" koma dai menene. Nayi kokari ai, tunda ba yaren qurani bane."


" kin yi kam Hajiya gwaggo. "


Murmushi su kayi gaba daya.

" bikin gama karatunsu junaid ne, za ayi next week. Tun jiya jafar ya fara min maganar. Mommy ta ce zanbi daddy da jabir muje,."


Washe baki gwaggo tayi " masha Allah, yanzu har su junaid an kammala karatu? Rayuwa kenan."


" abin ba wuya ai." Hubby ta fada


" haka ne kam, kamar yau sukazo min sallama shida balarabena. Kinga har an gama?"


Kiran sallar magriba ne, ya katse musu zancen. Kowacce ta yi alwala suka nufi daki don gabatar da sallah.


              ********************

Zaune suke gaba daya a farfajiyar gidan, dadduma ce mai kyau da laushi shimfide. Sai kayan abinci, gaba dayansu a trey daya suke cin abincin gwanin shaawa. Wannan yana daya daga cikin abinda ke sa hubby son kasan cewa da kakan nin nata. Don in kaga yadda suke gudanar da rayuwarsu abin shaawa, baka taba cewa sun kwashe irin Wannan shekaru a tare, kullun a cikin tarai rayar juna da nuna kulawa suke ga junansu.


Bayan sun kammala, hubby ta tattara wurin, kafin ta dawo kusa da Alhaji Kawu ta zauna. Cike da shagwabar data saba masa " jibi zan tafi Kaduna, zamuje graduation din junaid." Murmushi Alhaji Kawu yayi. " babanki ya min bayani dazu. Allah ya kaimu, ya dawo daku lafiya.


" amen" suka fada a tare.


Alhaji Kawu ne ya gyara zamansa. " dama ina son muyi magana, dazu su Hashim sun sameni da magana a kanki. Sai dai na shaida musu Wannan tsakanin ke da shine, don haka an jima zai zo. In kin aminta dashi mu namu addua ne kawai. Don yanzu ke kike da yancin zabawa kanki miji ba muba."


Baki hubby ta tura " gaskiya ni ban sonshi, da kawai ka bashi hakuri, ban son damuwa, yazo ya ishi mutun da surutan banza."


" aa Habiba ai baa haka. In ma bakya son sa ki bishi a hankali, a rabu lafiya, kin dai san tsakaninmu?"


Haba gwaggo ta rike" oh ni haihuwar Fulani. Hashimun ne mai surutan banza? Ko dai da na dazu zaa yi ne?"


Da sauri hubby ta kalleta " Allah ya kiyaye. Ya takurawa rayuwata ne, shi yasa kawai na saurareshi don ya fita hanyata."


Nan ta kwashe labari Kaf ta basu. " kangiwa, kangiwan da na sani?" Alhaji Kawu ya tambaya cikin mamaki


" shi " ta bashi amsa a takaice

Kada kai yayi. Gwaggo ta amshe da " mai jirgin saman da muka tafi hajji shekarar data wuce?"


Kai Alhaji Kawu ya kada mata " shifa "

Haba gwaggo ta rike, tana kallon hubby " iko sai Allah. Banda abinshi ai kwarya tabi kwarya KO, ina mai sunana ina dan kangiwa?


Murmushi Alhaji Kawu yayi " shi aure ai nufin Allah ne, in Allah yayi matarsa ce ba abun da yake gagararre a wurin Allah. Fatana Allah ya zaba mata miji na gari. "


"Amin dai" gwaggo ta fada


Sallamar da akayi ne, ya sa su maida hankali ga mai shigowar.


Saif ne, kanin Hashim. Bayan ya gaishesu ya shaida musu Hashim ne ke son ganin Habiba.


" kamar wani bako, kace ya shigo." Gwaggo ta fada fita saif yayi don ya Isar da sakon da aka aike shi.


" tashi ki sa muku kujera daga can." Gwaggo ta fada tana nuna mata gaban part din Alhaji Kawu, Wanda daga inda suke suna iya hango su, sai dai bazakaji mai ake fada ba, in ba daga murya nutun yayi ba, saboda yar tazarar dake tsakani.


Ruwa da juice gwaggo ta daura a wani karamin trey da cups. " oya dauka ki kai masa." Bata rai hubby tayi, dama a cike take tam.


Tabe baki gwaggo tayi " in mun ajiyeki gidan me zaki mana? Jikaki ki ke son muyi, musha? Ki shiga hankalinki dani wallahi." Gwaggo ta fada tana aikawa da hubby harara


Zun bura baki tayi, tare da figar trey din tayi gaba.


" kyaji dashi kuma" Alhaji Kawu murmushi kawai yake yana kallonsu.


Sai da ya karasa ya gaishe dasu gwaggo, sannan ya dawo ya zauna, kujerarshi nesa kadan data hubby. Murmushi ya sake mata. Dauke kanta tayi tana kallon gefe.


Gyara zama yayi, tare da gyaran murya. " ba sai na gabatar da kai na ba, already kin san ko ni wanene, daga ina na fito. Abu daya ne baki sani ba, ko in ce kin runtse idonki, shine irin sonki, da kaunarki da nake yi. Hakika zuciyata ta kamu da kaunarki. Fatana ki bani dama, don wallahi ba wasa ya dawo ni ba, in kin amince wata daya yayi yawa, don ni a shirye nake."


Shiru sukayi na wani lokaci, ganin bata da alamar tanka masa yasa ya kara karkace murya. " shirunki na min nuni da amin cewarki." Ai bai karasa ba hubby ta tareshi " aa. Maganar gaskiya, kayi hakuri, ba aure a rayuwata."


Murmushi yayi " ta ya zaki fadi haka? Bayan dukan mu nan aure ya samar damu?"


Numfashi taja tare da dan Kallonsa, yanda ya kafeta da ido, yasa ta daukar da nata kasa. " na san da haka. Ni dai rokonka nake da kayi hakuri, in Karin auren kakeso ga yanmata nan birgik a gari. Na tabbata ko nan cikin unguwar bazaka rasa wadda zaku dai daita ba."


Dariya yayi mai sauti " Habiba kenan,!! Na san dasu din, amma na tsallake zuwa gareki. Don ke kadai zuciyata ta zaba cikin dunbin matan nan, da ke kuma take son kulla alaka ta har abadan. In kuma nine ban miki ba ki fito kai tsaye ki gaya min. Maganar aure ta wuce wasa, duk kanmu nan ba yara bane, mun mallaki hankalin kanmu."


Duk yadda take jin haushinsa, bazata iya bude baki ta ce bata son shi ba. Duk da ko kadan har yau din nan bata kallon ko wanne da namiji da wani kallo na daban. Ta riga ta sawa zuciyarta bata ba wata alaka ta soyayya ko makamancinta tsakaninta da ko wanne da namiji, no matter how Hansom's there are.


Ganin tayi shiru, ya tabbata bazai samu wani gamsashshen amsa daga gareta ba. Duk da yana matukar son jin raayinta a kansa. " shi kenan, tunda kin ki cewa komai, zan baki time kiyi shawara,. "

Ledar dake gefenshi ya mika mata. Kallonsa tayi, ta kalli ledar. Ganin bata da alamar karba " kyauta ce, tsakanin Yaya da kanwansa. So please don't say no." Ya fada cikin muryar lallashi.


Karba tayi, tare da masa godiya. Mikewa yayi ya mata sallama. Ya tafi cike da Karin sonta da kaunarta.


Ta hada kujerun ta maida su mazauninsu, ta juya da nufin komawa wurin su Alhaji Kawu da har lokacin suna wurin suna hira.


Sunanta da taji an kirane yasa ta juyo. Ganin mai kiran yasa ta fadada faraarta. " babana daga ina haka?"


Murmushi ya sake mata, tare da jin Gina da katangar dake kusa dashi, yana kada car keys din dake hannunsa. " tunda baa nemana ai dole ki ce daga ina." Dariya tayi " ni na isa, jiya muke maganarka da dija, Ashe kana tafe."


Dadine ya kamashi, ya kara fadada murmushinsa. " really?"


" of course. Ta ina zamu manta da hero."


Dariya yayi " kun kyauta ai."


Lú" yaushe a gari?"


" jiya na iso, after ishaa. Mun sameku lafiya?.


" lafiya kalau, ya aiki? "

"Alhamdulillah." Ya fada yana gyara tsayuwarsa.


" mu karasa man, ka tsaya daga nan."


" ba matsala zan karasa ai mu gaisa dasu gwaggo. But kafin nan akwai maganar data kawoni."

Kallonshi tayi tana murmushi ba tare data kawo komai a ranta ba. " I'm all Eyer's "

" me ya kawo doctor wurinki?"


" wane irin tambaya ke nan?"


" just want to known. "


" ba abunda ya shafeka bane." Ta fada tana tsareshi da ido


" ni ko ya shafa."


" as in how?"


" because he want to take what is actually my."


Kallonsa tayi cikin son Karin bayani.

Murmushi yayi " nasan bai wuce zuwa yayi ya shaida miki yana sonki ba. Sai dai baku da ce ba. Daya ma bai iya controlling dinta ba balle ya kara. Koda yake is not my place to say so. But shine your eyes. Ni nafi da cewa dake, ni nasan zafinki, nasan kuma na fishi sonki da bukatarki. So please give me a chance, to show u how much I love u."


"Dakata babana, me kake nufi ne. I don't understand u?"


" please Habiba married me, I'm so much in love with u."


Kallonsa ta tsaya yi, kafin ta kwashe da dariya. " u are joking right? "


Serious face yayi. " I'm serious, Habiba, ba wasa cikin abinda nake fada. Tun ba yau ba nake son gaya miki. Ban samu chance ba.but amma believe me."


Rike baki tayi, tana kallonsa. " lallai ma, to kai koda auren zanyi ai baka ciki. In aureka in ce na auri wah?" Karka manta tare mukayi wasan kuruciya, Duka duka 3 months ka bani a haife. Ta ya ma zuciyarka zata baka irin Wannan lamari?"


Marai raice fuska yayi, yana hada hannunsa guri guda. " Wannan duk ba hujja ba CE, koda kin girmeni ai ba aibu bane don na aureki, kin ga nayi koyi da manzo S.A.W, balle ma na baki har wata uku. Don't say no please. "


" dallal manta da wannan maganar, in aure kake so ni da kaina zan zabo maka, in kai ka kasa. Ni yanzu ba aure bane a gabana. So muje Ku gaisa dasu gwaggo. Tayi gaba tana masa dariya


Binta yayi cikin sanyin jiki, dama abinda yake gudu kenan. Don ya dade da sanin hubby da son girma. Da wuya ta amsheshi cikin sauki, but zai ci gaba da trying don gaskiya yana sonta sosai, ba zai iya hakura ba, sai inda karfinsa ya kare.


Sun dan taba hira dasu Alhaji Kawu, kafin ya masu sallama, har get hubby ta rakosa. Sannan ta juya cikin gida.


              ********************


Munir mustafa da ga Alhaji mustafa, kani ne ga muh'd, Makota ga Alhaji Kawu.

  Munir yaro ne dan shekara 25, ya kammala karatunsa na degree a alkalam, yanzu haka a can yake koyarwa, sannan yana karatun degree dinsa na biyu. Yarone mai kokari sosai, ajinsu daya da hubby a primary shi ke zuwa musu na daya a class.


Da farko basa shiri da hubby, kullun suka hadu sai tasan abin da tayi ta sashi kuka. Saboda Alhaji Kawu na yawan mata fada, da misali da Munir Ta wurin kokari da maida hankali a karatu.

Shirunsu ya faro ne, lokacin still tana aji biyu, shi kuma aji biyar, saboda repeating da ake mata. Su kayi wani danbe ta kusa cire masa yatsa da cizo.

Alhaji Kawu ya musu sulhu ya nuna mata ko don sunan mahaifinta da munir keda shi, ya kamata ta raga masa.  Fada sosai ya mata. Wannan shine musabbabin da take kiransa babana. Daga nan kuma suka fara shiri sosai, koda ya tafi secondary school dake bording ne, in yayi hutu bini bini yana gidansu. Har barinta kankiya.


Ta fannin halitta kam Sam bashi da makusa, yana da dan kyansa dai dai kwargwado, da cikar halitta, bashi da tsawo sosai, average person.


                ****************

Alwala tayi kamar yadda ta saba kafin ta kwanta. Tayi azkar din kwanciya bacci kafin ta janyo ledar da Hashim ya bata.


Waya ce, kirar Samsung galaxy x 10 silver da mtn sim card. Tsaki tayi ta maida wayar cikin gwalinta ta ajiye a gefe. " ko an ce masa ina fatarar waya ne oho? Na rasa me yasa mutane basu da ganewa." Ta kara Jan tsaki. Tunani ne ya rufeta mu samma yadda zata rabu da wa'annan sarakan nacin. Don ta lura baza su barta ta dadin rai ba.  Tunanin King dinta ne ya dawo mata, da moment dinsu a tare, hawaye ne ya fara zarya a kumatunta. Tunawa tayi da alkawarin data dauka. Suratul ikhlas ta karanta 7× ta roka masa gafara da rahamar Allah. A haka barci yayi gaba da ita.


                 ***************


Thursday jirginsu ya daga, Daga Abuja zuwa Cyprus............


Tofa!!!!Suraj, Hashim ko babanmu Munir?Junaid da ashir ne suka je tarbarsu a airport.+


Direct masaukin baki suka wuce, na Don Harris, Wanda ke kusa da apartment din su hayder.


Hubby, umma sulaim, Asiya, dakinsu daya. Sai Hajiya da Hajiya zuwaira, mahaifiyar Hafiz omer. Suma daki daya. Alhaji Munir nashi special suite. Abdul fattah da jabir kam apartment dinsu hayder suka sauka.


Wanka kowacce ta fara gabatarwa, kafin suka fito tafkeken falon da ke tsakiyar dakunan don ba ciki hakkinsa.


Nan suka samu duk kan samarin sun hadu. Nan fa aka fara gaisawa, da tambayar su hubby gajiyar hanya.


Congratulation suka musu na kammala karatu.


Ummu sulaim ta nufi dinning table din da aka Jere shi da dishes na abinci masu matukar kyau, da daukar ido. Bubbudewa ta fara, tana kallon abinda ke ciki. " wowhh!!!! Gaakiya kun burge, irin wannan delicious haka?" Ta fada tana Jan pleat signal tama hubby dake zaune a kusa da junaid suna hirar zuminci.


Tashi tayi ta nufi in da sulaim ta ke.


" na dauka zamu jira su Hajiya su fito, tukunna. Kin San cin abinci a tare nada dadi." Hubby ta fada tana kallon pleat din

Harararta ummu sulaim tayi " tab har yaushe ina ganin abinci a gabana, zan wani tsaya jira? Kin ko San kalan yunwar da nakeji?"


" maida wukar na manta, bakya juriyar yunwa."


Ummu sulaim ta kalli Asiya dake zaune. " Uhtee ."


Ajiyar zuciya Asiya taja tare da mikewa. Cikin sanyin jiki ta nufi wurin su hubby.


Murmushi hubby ta mata, tare da dafa kafadarta " take it easy sis," ita ma murmushin tayi cikin jin kunya. Ummu sulaim ta tabe baki " aiki ya ganki,"

Fitowar su Hajiya ya sa falon kara armashi, kowa ya dibi abinda zaici, suna ci, suna hira sama sama. Cike da farin ciki. Kowa ka kalla fuskar nan a sake.


Hayder na zaune kusa da Hajiya, kamar zai koma ciki, sai shagwaba yake kamar wani karamin yaro. Abincin ma pleat daya suke ci.


Bayan sun ci, sun sha, ko wanne ya koma dakinsu don su  kwanta  huta gajiya. Suka bar samarin a falon, suna shan hirar yaushe gamo.


" take this one." Ummu sulaim ta fada, tana mikawa hubby wani hadadden Dinki, atamfa mai combination din boil. Atamfar baki da touch din lemon green, voil din lemon green dinkin free half bubu da stret skirt. " wow amma kayan nan sunyi kyau sosai. Thanks " murmushi ummu sulaim tayi. " meye na wani godiya, yiwa kai Ne. Kin manta har yau bikici alayina na nysc ba." " gashi naci ai yanzu."


Shiryawa sukayi don tafiya wurin convocations. Ummu sulaim ma da asiya same kaya sukasa sai dai colours din is different. Lemon green Vail mai touch din white da stone masu haske hubby ta sa. Sai black shoe and bag. Na kamfanin cucchi new design.


" kuda ya kamata kuyi shigar larabawa, kuka je kuka zunbulo kaya haka kamar masu zuwa didan biki." Hajiya zuwaira ta fada tana murmushi tare da gyara zaman after dress dinta mai matukar kyau da tsada.


" mommy kowa yabar gida, gida ya barshi, na tabbata yawanci arebian dress zasu sa. Kinga mu munyi namu different don bama son mu saje dasu. We want something different than others, shiyasa." Rike baki Hajiya tayi da itama take sanye da nata alkabbar mai matukar kyau. " lallai fa!! Kishin kasa Abu ne mai kyau, ana ganinka aga alamar in da ka fito. Nigerian lady's kunyi kyau kam ba karya. Kowa ya ganku yaga cikakkun yan arewacin Nigeria. Masha Allah."


" a takaice dai Hajiya yaran nan na nufin mu bamu da kishin kasa fa kenan?"


Dariya sukayi gaba daya, ganin yadda take bin dressing dinta da kallo.


" Allah ba abunda muke nufi ba kenan. " Asiya ta fada tana rungume mahaifiyar tata tana dariya. Ta kara da cewa " don baki ga yadda kukayi kyau bane, wannan su daddy's suka ganku, kasa ganeku, zasuyi." Ummu sulaim tayi dariya " kina ga su Hajiya harda alkyabba kamar mai kai ziyara emir's place. "

Duka hubby ta kaiwa ummu sulaim. " Ku barsu su wala, don shigarsu tafi tamu daukar ido, anya baza mu canza ba?"


" yauwa yata, gaya musu dai. Ba maganar canzawa Nigerian lady's kumu tafi kawai kar kusa mu makara." Hajiya ta fada tana daukar hand bag dinta.

                       ******************************************

A farfajiyan school din sukayi parking din land cruiser da suka zo da ita. Already wurin ya fara cika, a wurin da aka kayata shi da decoration. Suka nufa,. Gefen perent. sun samu har Alhaji Munir da Alhaji Jamil sun iso, sai mahaifin Hafiz Alhaji ayuba da yayansa Ahmad da suma suka samu isowa. Sai yayan alim da suke tare da jabir. Amir ma yasamu zuwa taya abokan nasa murnan gamawa.

Zamansu ba dadewa, bayan sun gama gaishe gaishe. Aka fara gudanar da programs din.

Bayan jawabin director na school din, da masu fada aji na kasar da suka samu halatta, aka Dan gudanar da entertainment, sannan aka fara rabon aword da gifts.  Cikin su shidan nan ba Wanda bai karbi aword ba. Don hayder aword uku ya samu, da gifts 2. Sai Hafiz omer daya samu aword 2, sauran 1. Abun yama iyayensu dadi, musamman kyakyawan yabon da yaran suka samu, daga bakin malaman har da students.


Bayan an gama raba aword da gifts, sai entertainment, sannan aka nufi hall din da aka kawatashi don cin abinci. Tablets Ne da kowanne aka zagayeshi da kujeru sunsha decoration na cotton White da satin Amy green sai flowers da vases masu matukar kyau da daukar ido. Su Kansu plets da spoons din abin kallo Ne. Nan take aka  fara serving din jamaa, bayan kowa ya samu wuri ya zauna, ga kida mai taushi da sanyaya rai na tashi, cikin low voice.  already drinks kam waiters nata zagayawa dashi, ga maiso ya karba duk irin Wanda kake so. Ban dawanda ke kan tables din. Ga fresh fruit kala kala.


Anyi hotuna videos kowa, da iyayensa da friends dinsa. Sai teacher's da baa barsu a baya ba suma.


Asiya ta kalli ummu sulaim dake gefenta ta rada mata a kunne " waccan da take faman shishshigewa Yaya hayder wacece?" Kallonsu ummu sulaim tayi don itama tun dazu take son tambaya, bata samu damar da zata tambaya ba.


Rada mata tayi " I don't known, ina ga school mate din su ce."


" ki kalli fa irin kallon da take masa? Allah ba wani class mate. There is something "


" jealousy beby. I don't thing so. Amma koma menene we go figure it out, ammafa ta hadu."


Harara Asiya ta zuba mata. "Ina haduwa a nan? Abu a bushe." Dariya ummu sulaim tayi. Dan da nan Asiya ta toshe mata baki, tana kallon table din. Ganin duk hankalinsu baya Kansu, ta saki ajiyar zuciya.

Hubby kam gaba daya hankalinta baya Kansu. Tunanin yusuf da kewarsa ne taji nan take ya rufeta. Musamman  yadda yaci burin akan graduation din nan. Amma Allah ya kaddara badashi zaa yi ba.

A hankali take diban chocolate cake din zuwa bakinta. Dariyar da taji ummu sulaim tayi yasa ta dago ta kallesu tare da kada kanta ta ci gaba da cin cake dinta. Don tasan maganar bata wuce ta hayder har tausayin asiya ta ke, ganin yadda ta kwallafa rai ga yaron da bai ma San tanayiba.


" da alama sis kinyi babban catch, " ummu sulaim ta fada tana kallon hubby tana dariya.


Tsaki hubby tayi, ta ci gaba da cin cake dinta.


Asiya ta kalli hubby tana murmushi " gaskiya kam, tunda muka zauna a wurin nan idon bawan Allah nan a kanki."


Hubby dai tana jinsu tayi musu banza. Don gaba daya haushi ma suka bata. Tun da suka shigo school din ta ankare da yadda ya sa mata ido,.

Daya daga cikin yanmatan da suke zaune table daya dasu hubby ce, ta kalli yar uwarta. " I can believed what my aye's so." Kallonta yar uwar tayi. Tare da bin inda yar uwar ke kallo tana nuna mata.


" suraj kangiwa." Dayar ta fada under her breath


Gaban hubby ne ya buga dam. Su ummu sulaim kam jin sunan suma suka bi wurin da kallo. Yana zaune a daya daga cikin kujerun table dinsu Alhaji Munir, suna magana.


Ummu sulaim ce ta tambaya " dama shine, kangiwan da naji ana magana?"


Dayar cikin farin ciki, da tun zamansu  wurin, ba Wanda zai dauka tana faraa haka. " Ally son of M. Saad kangiwa, CEO of kangiwa group of companies. " ta fada tana kada ido.


" what bring him here." Dayar ta tambaya still idonta a kansa.


" me be yazo wurin daddy ne."


" I don't thing so, Sis."


Hamida da Sadiya (sady) yayan abokin Alhaji Jamil ne, Alhaji salis,. Shima yazo graduation din yaron sa , Imran tare dasu sady Wanda suke yayye ga Imran, da mahaifiyarsu Hajiya fatee.


Hamida da sady yan Hutu ne na karshe, don a England ma sukayi nasu degree din. Akwai jin kai da yanga ga son nuna su yayan wani ne. Shi yasa Sam tasu bata zo daya da hubby ba, don ta dade da saninsu, age mates ne, kuma duk shaanin da ake na family din Oregon suna zuwa, in dai suna kasar.


" is he your boyfriend? " Asiya ta tambayi sady

Rike baki sady tayi tana yamutsa baki. " no."


" fadi gaskiya sady? Don naga tun tuni kin kasa dauke idonki a kansa."

Kallon ummu sulaim sady tayi. Tare da yin murmushi. " he is my crush, amma yafi karfina."


" haba babbar yarinya irinki har akwai wani da namiji da zaifi karfinki? Kin ganki kuwa?" Dadine ya kama sady don tana son a yabata ko a kodata. Ta kalli ummu sulaim " thanks for compliment. Amma da gaske yafi karfina. In kinga manyan bebs dake dying a kan guy din nan zakiyi mamaki."


" ya hadu kam ba karya." Asiya ta fada tana kara kallonsa.


Hamida ta ce " ko kema kin kyasa ne?"


Ido Asiya ta zaro " ni ? Aa ko daya, nima ina da nawa crush din."


Duka dariya suka sa. Banda hubby dake zaune kamar bata wurin.


Hafiz omer da amir ne suka iso wurin. " hello sisters? How fah?" Hafiz ya fada yana murmushi, tare da Jan empty sit din daya rage ya zauna. " Anty hubby ba matsala ko?" Murmushi ta masa tare da kada kai.


Amir ya ce " muje mu dan kashe pictures da zaman da kuke a nan."


Asiya ce tai saurin mikewa " gaskiya kam, na gaji da zama wuri daya. Ina son in ga yanayin school din, don gaskiya ta burgeni ba kadan ba. Dana Sani nima nan nayi applying."


Tashi sukayi, hubby ce ta gayawa su Hajiya zasu Dan zaga cikin school din. Sannan suka fito.


A garden dake cike da dalibai da yanuwa anata kashe hoto, da videos. Masu hira nayi. A nan suka samu su hayder.


Kallon ummu sulaim Asiya tayi, tana nuna mata hayder da wannan yarinyar zaune suna magana kasa kasa. Sai annuri ke fita daga fuskar yarinyar da gani tana jin dadin yanayin.


" wa cece waccan yarinyar? Tun  dazu nake ganinsu a tare." Ummu sulaim ta tambayi Hafiz omer


Murmushi yayi " Nasrin  Nada Khan ke nan, da alama da ita zaayi." Kirjin Asiya ne yayi wani irin dokawa, cikin tashin hankali take kallon su amir " kamar Yaya?" Da kallo suka bita. Murmushi ta kakalo  tana kokarin saita natsuwarta. Hannunta ummu sulaim ta kamo cikin nata.


" ita ce fist yarinyar da hayder ya saurara, har ya bata lokacinsa a kanta. Kinga ko ai ta ciri tuta. Na tabbata tana da matsayi ko Yaya ne a ransa. Yarinyar bata da laifi, tana kuma balain son shi." Amir ya fada yana murmushi


" he is lucky guy." Hafiz omer ya fada

Da ido ummu sulaim ta ma Asiya alamar tayi cooling down.

Hubby kam ta dade da isa wurinsu junaid. Cikin girma mawa suka kara gaisheta. Nan alim ya fara daukarsu pictures.


A hankali hayder da nasrin suka karaso in da su hubby suke. Sallama ya musu.

Cikin murmushinsa na miskilanci ya kalli ummu sulaim., sannan ya kalli nasrin dake binsu hubby da kallo. Jikinta yayi sanyi, ganin irin kallon fire da Asiya ke aiko mata, tun da suka nufo wurin.


" meet my sisters. Ummu sulaim, hamida, Sadiya sady and Asiya. " hannu ta mika musu suka gaisa tare da rungume juna. Duk da zuciyar Asiya na zafi haka ta daure.


Kallonsa ya kai kan hubby yana murmushin gefen baki " meet our Anty hubby. " hannu ta mika mata tare da rungume ta. Gaisuwa ta mata cike da nuna tausayawa.


" thanks. " hubby ta fada don ji tayi kamar mutuwar ta dawo mata sabo a lokacin.


" she is nasrin Nada khan. My friend " hayder ya fada yana kallonsu. Still da murmushi a fuskarsa.


Murmushi sukayi. " friend manya, kuji wani sabon salo." Hafiz ya fada yana murmushi


Harararsa hayder yayi. Nan suka ci gaba da daukar pictures dinsu.


" can I joined u." Gaba daya suka juyo ganin mai maganar


Sanye yake da blue Jean's, sai T-shirt White da lines din blue mai dogon hannu. Kafar sa sanye da White canvas mai kyau, sai agogon silver mai matukar daukar ido. Kanshi yasha gyara, ga farin glass a idonsa, Wanda ya karawa fuskarsa kyau da kwarjini. Ga wani kamshi mai dadi dake tashi a jikinsa.


Suraj m saad kangiwa.


Murmushi su Hafiz omer suka mayar masa " why not." Alim ya fada yana mika masa hannu.


Kirjin hubby banda bugawa ba abun da yake yi. Ita kam taga ta kanta.

Kin yadda su hada ido tayi, tana ji sunata gaishe shi. Shima cike da sakin fuska yake amsa musu, tare da musu congratulations.


" very sorry, I came un invited. It's you're sister fault she didn't Tell me. But I can Miss our brothers gradations." Suraj ya fada yana murmushi idonsa kafe a kan hubby da ta sunkuyar da kanta, ta gagara dagowa. Don haushi da nauyin kannen nata.


Gaba daya kallonsu ya koma kan hubby cike da mamaki.............Jin yadda gaba daya ido a kanta, ba tare da ta kalli kowa ba ta juya ta nufi hall din dasu Hajiya suke.+


Murmushi suraj yayi " 2min" ya fada tare da bin bayanta.


Hafiz ne ya kalli alim, da jikinsa ya gama sanyi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da zama a kujerar dake kusa dashi. Ummu sulaim da su hamida sai kallon kallo ake tsakaninsu.


"Habiba" jin ya kira sunanta, ta tabbatar biyota yayi kenan. Cikin fushi ta juyo tana jifanshi da wani riki taccen kallo. " don Allah wai maina tsare maka ne a rayuwa, kake son takuramin? Na Riga na gayama iya gaskiyata why can't u understand?"


Murmushi ya sake mata, tare da kashe mata ido daya. " I never understand you're language Habiba. The ally think I known is that I'm  crazy about u. So duk yadda kike tunanin I will live u. Is not gonna happen. Ta Yaya zaki tafi da zuciyata sannan kiyi tsammanin zan iya barmiki ita?"


Kallon sa tayi for the fist time ta tsaya ta kalleshi da kyau, for some second. Ta kauda kanta gefe tana jin jina naci irin na wannan bawan Allah.


Maganar shi ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi.


" nasan kin San so? kin kuma San yadda bawa yakeji a duk lokacin da ya tsinci kansa a cikinsa. Ina rokonki don Allah ki bani dama mu fahimci juna. Wallahi ba yaudara tsakanina dake, face alkhairi. Har ga Allah ina sonki tsakani da Allah. Son da nake jin tamkar in baki ba zan iya ci gaba da rayuwa mai dadi ba, ke ce farin cikina. "


For the fist time taji ya Dan bata tausayi. Tabbas da baya sonta bazai ajiye dunbin ayyukansa ya tako tun daga Nigeria zuwa Cyprus kawai don ya ganta ba. Duk da bata da tabbas din ita ya biyo ko tashi ce ta kawoshi. Ajiyar zuciya ta yi kafin ta dago ta kalleshi, still idonsa na kanta yana sake mata murmushi mai kayatarwa.


Ganin Dan sassauci a kan fuskarta yasa shi jin wani kwarin gwuiwa da farin ciki, ya lullube zuciyarsa.

" baki tambayeni ya akayi nazo nan ba."


Tabe baki tayi, tana kallon gefe. Murmushi yayi, don hakan ba karamin burgeshi yayi ba." naje kankiya on Thursday, kamar yadda na miki alkawarin dawowa a satin. a ka cemin  ranar kika tafi Kaduna, sorry nayi magana da Alhaji kawu ba tare da izininki ba. I'm happy yadda suka karbeni shida takwararki."


Da sauri ta dago tana kallon sa. Murmushi yayi tare da daga mata gira daya.


Ajiyar zuciya ta yi, don ta yadda da gaske yake nashi abun.


" tun jiya naso in taho, ayyuka sun sha karfina, amma fa still kina raina. Yau gari na wayewa ko mai ban jiraba. Burina in ga rabin raina, duk da nasan bazaayi farin ciki da ganin nawa ba."


Ganin bata da niyyar tankashi, shikuma zuwa lokacin muryarta kawai yake son ji, mai dadin sauraro da tsumashi. Kallonta yayi yaga yadda take wasa da yatsunta da sukasha bakin lalle. Tabbas akwai sassauci a tare da ita, alamar ta fara sakkowa, hakan yafi komai yi masa dadi.


Hubby kam yaki take da zuciyarta data kasu kashi uku. Daya na bata shawarar ta bashi dama ta gani, daya na mata shawarar ta tatamai rashin mutunci kawai yadda gobe ko mai sunanta ya gani bazai tsaya a kusa ba. Dayar na gargadinta data watsar da komai ta koma makaranta. Kamar zabin da Mommy hauwa ta bata, zuwantan nan.


Muryarsa taji ta daki dodon kunnenta

" yawan tunani bashi da kyau ga lafiya, ya kamata ki rage."


Ajiyar zuciya ta yi ta kalleshi " naji zan baka chance, amma banyi maka alkawarin komai ba."


Kallonta yayi for some time yana nazarinta. Murmushi yayi.


" ban gane baki min alkawarin komai ba?"


" just friends. " ta fada tana kallonsa.

Dariya yayi wadda ta kara masa kyau

" na yadda friends, but ki Sani  zata iya riki dewa."


Kallon sa tayi " kamar Yaya riki dewa?


Shafa kansa yayi yana murmushin gefen baki " forget it. Yanzu dai ni dake are friends right? "


Kai ta daga masa.


" good." ya fada yana murmushi


"Muje nima a kashe pictures din dani ko?"


Harararsa ta yi.


Marai raice fiska yayi " don't forget  I'm you're friend, Kinga ba laifi ki dauki photo da friend dinki."


" karka manta akwai ban banci da friend mace, da friend namiji. So stay in your limit. "


" ban Sani ba, amma ya kamata mu zauna ki jeromin differences din don in kiyaye."


Ganin tayi gaba, yasa shi binta. A tare suka jero zuwa wurinsu ummu sulaim da lokacin sun babbaje a kan grass carpet dake malale a garden din suna kwasar hira.


Gefen ummu sulaim ta nema ta zauna. Shikuma jabir ne ya tashi ya mishi alamar ya zauna. Sannan suka gaisa, don dazu basa wurin shida Abdul Karim, Ahmad.


Gaba daya hubby a tsarge take ganin irin kallon da kowa ke binta tashi. Ummu sulaim ce ta rada mata " kin kyauta" dagowa tayi ta kalleta da ido ta mata alamar " sorry I have no idea. " su sady kam haushin hubby ne ya kara cikata. Sai Kallonta take tana son ganin abinda tafi sauran mata da tayi mata zarra a rayuwa. Duk iya Kallonta ta kasa gano makusarta. Illa kawai ta ce, bata da wayewa a nata fassarar. Don da wuya kaga hubby cikin kaya masu nuna siffar mutun. Dressing dinta is decent.

Shikam ya saki jikinsa da samarin sai hirarsu suke kwasa. Duk wani movement na hubby a kan idonsa.


Sai 2oclock sannan taro ya watse kowa ya fara kama hanyar masaukinsa, masu tafiya a ranar sun kama hanyarsu. Su hubby sun so dawowa ranar but ba dama saboda walima da sheikh dawood al- maisani ya shiryawa su hayder na haddar alqurani da yayi a wurin sa, shida wasu matasa su biyar sai mata 2.


Suraj ne ya kalli samarin da suka rakoshi har mota, bayan su hubby sun wuce masauki. " Ku mai ya hanaku joining din hayder?"


Murmushi sukayi junaid na shafa kai. " nida shine dama mukayi joining banfi sati ba na gudu."


Dariya su Hafiz suka sa tunowa da drama din.


" as how" suraj ya tambaya still da murmushi a kan fuskarsa. Don yaran sun matukar burgeshi.


" kana ji ko? Fist day da mukaje tun a fatiha an min gyaran tajweed yafi goma, a fatiha kawai, duk iya dagewata ranar ban samu wuce fatiha ba. Shima hayder yasha gyara. Duk kanmu a fatiha ranar muka kare. The next 3day hayder ya wuce ikhlas da kyar ni kuma ina nan a fatiha. In takaita maka 5 days nayi a fatiha, sannan na tafi ikhlas, lokacin hayder yana suratul nas. 1days ina ikhlas ranar na dauka zan shiga sabuwar sura amma Dan malaminka haka yayita dawo dani. In takaita ma gani nayi bazan iya ba kwana 7 a fatiha da ikhlas ina kuma mun fara shiga manyan sura. Malamin Dan gani kashenin tajweed ne, ko ja daya ka manta sai ka faro daga farko. Ai tun daga nan ban sake komawa ba." Dariya sosai suke masa. Hayder na daga gefe yana danna waya.


" daka daure ai, da komai ya wuce." Suraj ya fada yana dariya


" ina wane mutun. Sauka biyu fa mukayi kafin mu taho nan. Waye besan karatu irin na ibn kayyim memorial college ba.? Munje gasa yafi a kirga, muna winning.Amma dan malaminka kamar ya samu fresh meat."


" don't insults my sheikh. " hayder ya fada yana hararar junaid.


Murmushi junaid yayi, " sorry na manta kana wurin ai.?"


Card hayder ya mikawa suraj 5oclck tare da masa sallama ya shige mota, don a gajiye yake, Allah Allah yake su je ya huta kafin su wuce gidan sheikh.


Sallama sukawa suraj tare da godiya. Don wasu manyan gifts ne da akayi rapping dinsu, guda six ya basu, kowa da sunanshi a jiki.


                 *******************


"Yanzu kiyi irin wannan catch din amma ki kasa sanarmin gaskiya banji dadi ba ko kadan"  ummu sulaim ta fada tana shafa lotion,.

Tsaki hubby tayi " me kike son in gaya miki."


" sorry na manta, na Yaya Yusuf ma saida magana tayi karfi mukaji. Amma dai kin San mu ba haka muke miki ba. Its un fair. Yanzu da wani mugun halinshi su sady suke fada da ya zakiji."


Kafada ta makale tare da tabe baki " so what. Ke baki San kalan nacin mutumin nan bane, ba wai son shi nake ba, balle in damu don an fadi mugun halinsa." Nan ta kwashe labari Kaf ta fada musu. Baki suka rike suna mamaki.


" kun masifar dacewa, sai kin ganku lokacin da kuka jero tare, don har picture na kashe muku baku Sani ba." Asiya ta fada yana murmushi tare da nunawa ummu sulaim pic din.


" its true. Gaskiya yana sonki sosai, kar ki bari ya kufce miki hubby, zamanin yanzu ka samu Wanda zai soka haka yana da wuya. You're very luky, ji yadda Yaya Yusuf ya soki, yanzu kuma ga suraj. Ki gode Allah don ba kowa ke sanun hakan ba."


Asiya ce ta kara da " gaskiya kam."


Banza dasu hubby tayi ta ci gaba da shiryawarta. Don har lokacin bata jin natsuwa da lamarin ta da suraj.


Hajiya ce ta shigo. Wuri ta samu ta zauna tana kallon hubby. " Ummi wane labari nake ji ne?" Kallon Hajiya hubby tayi cikin rashin fahimta. ummu sulaim tayi murmushi tana kallon hubby " na biki da muka kusa sha mana"


Tsaki hubby tayi ta harareta. Asiya ce ta korowa Hajiya bayani dalla dalla kamar yadda hubby ta gaya musu.


Ajiyar zuciya Hajiya tayi " ai ni hankalina bai kwanta bane, amma ba komai zamu ci gaba da addua. Allah ya zaba miki mafi alkhairi. Ki ci gaba da addua."


" in sha Allah." Ta fada kanta a kasa.


Ajiyar zuciya tayi bayan Hajiya ta fita.


Dariya su Asiya suka sa baki daya suna tsokanarta.


                ****"**************


1

Hayder

"


Agric chiken" hubby ta fada tana murmushi.


Kallon ta ummu sulaim dake kusa da ita tayi, ta kalli su junaid da suka sha jallabiyyoyi da nadi irin na larabawa.


Murmushi tayi " Allah girma ba wuya, ni kaina bana gajiya da kallon yaran nan ina mamakin girmansu. Musamman hayder da junaid. Har gara junaid shi bashi da jiki, amma dubi hayder wa ze ce 19 going to 20 years.

             ********************


Walima ta kayatar sosai. Hajiya tasha kukan farin ciki, hatta su Alhaji Jamil dasu hubby sai da sukai hawayen dadi. Jin yadda haidar ke kwararo karatun alkurani cikin kiraar kalun. Haka su Hafiz


Bakajin komai sai kabbara, duk inda aka ja masa in ya amshe, sai yakai inda zaa ja wata, haka tambayoyi kan tajweed da tafsir, Abin masha Allah. Ya samu kyaututtuka da dama, bayan an kammala akaci aka sha sannan kowa ya kama gabansa.


Rungume shi Hajiya tayi tana kuka, shima hawayen yake fitarwa na dadi.

Burin hajiyarsa ke nan, ya samu yalwataccen ilmin addini. Kullun taga yara a wurin gasar alkurani takance ina ma wata ran inga hayder dina haka. Yana secondary school ansha zabansa ya wakilci school dinsu, hakan ya kara sashi son zurfafa ilmin addini,  alkawari ne ya daukarwa kansa duk wuya duk runtsi, yadda ya dage neman ilmin zamani, haka zai dage a kan ilmin addini koma, fiye. Shiyasa duk tsaurin sheikh ya daure ya cige batare da kosawaba don ya cimma burinsa. Kuma alhamdulillah ya samu ya taka mataki na farko da yake fata a rayuwarsa.


Albarka kam yau hayder ya sha a wurin su Alhaji Jamil. Nan take ya tura ma yan uwansa da mahaifinsu.


Alhaji Jamal na masallaci sallar magrib yaji shigowar sako wayarsa. Bayan ya kammala tasbihi da azkhar ya fito da wayar don ya duba.

Gaba daya kiraar hayder ta fara tashi a cikin wayar, Wanda ya jawo hankalin liman, da sauran mamu da suka rage a masallacin. Hawayen dadi Alhaji Jamal ya fara ya dago yana kallon liman da ya masa zuru da ido. Wayar ya fara nuna masa, cikin rawar murya " Aliyu, Aliyu hayder. " liman da mamu suka zagaye Alhaji Jamal suna kallon hayder dake zubo kiraa cikin kwarewa da dadin murya. " Allahu Akbar suka fara fada. Har bidion ya kare. Alhaji Jamal na ta sharar kwalla. Murna suka dinga tayashi tare da fatan Allah yasa albarka a karatun, yasa ya zama mai anfani ga alummar musulmi. Nan liman ya fara kwararo falalar mahaddacin qurani da darajarsa a wurin Allah. Gaba daya imani ya kara cika zukatansu.


Hakika a cikin zuriarka a samu mahaddacin qurani ko da guda daya ne, ba karamin falala bace ga wannan zuri'a.

Haka ta faru da Alhaji babba da Hajiya Aisha. Suna tare a babban falo dasu Ahmad da iyalansa sun kawo musu ziyara. Kamar Alhaji babba bazai daga wayarba ganin sunan Jamil yasa ya duba.


Duk Kansu sunyi farin ciki matuka. Hajiya Aisha kam har da kukanta ita ma.


                 ****************

Zaune suke a babban falon masaukinsu. Gifts din su hayder ne baje a falon, sai manyan jakun kuna da su hubby ke arranging din gift's din a ciki, bayan sun ciresu a kwalayensu. Saboda in sunce zasu tafi dasu haka zasuyi accupying  space da yawa.

Wani hadadden box hubby ta daga, ya matukar burgeta yadda akayi rapping dinsa. Da ita kanta rapping sheet din. " wow!!!" Asiya ta fada tana karba daga hannun hubby.


Sunan da Asiya ta gani an rubuta yasa jikinta daukar rawa, cike da son ganin abinda ke cikin rapper ta fara yagawa cikin sauri, da kaguwa ido ta zaro...  Gaba daya su hubby dake Kallonta cike da mamakin abunda ya fusata ta lokaci daya sukabi box din da kallo.


Zaro wani hadadden box din turare da aka rubuta SHUMUKH ( The sprite of Dubai )da manyan baki sa a Kansan an rubuta ( Deserving The Highest)

Budewa tayi ta zaro kwalbar yar madai dai ciya mai kyau. Ga wani kamshin dadi dake tashi tun bata fesa ba


1

Tsaki hubby tayi, tana juya turaren a hannunta. " yanzu duk girman abun nan, abunda ke ciki kenan?"


" wannan mayyar yarinyar ce ta bashi, nasrin take ko wace?" Asiya ta fada cikin jin haushi, tana tabe baki.


Dariya suka mata " nama dauka wani Abu ne, yadda naga kin haukace lokaci daya, kina son ganin abunda ke ciki." Ummu sulaim ta fada still tana dariya.


Hafiz ne ya ankare da abunda suke yi.

Kwalbar ya amsa daga hannun ummu sulaim yana kallo. Kallon su junaid yayi " guys look hare." Gaba daya suka juyo suna kallonsa


" oh my world. " junaid ya taso da sauri ya amshi turaren yana juyashi a hannunsa cike da mamaki. Rapper din da box suka dauka suka nufi wurin sauran guys din.


" amma gaskiya yarinyar nan tana ji dakai. Kasan nawa kudin turaren nan?"


Hafiz omer ya fada yana kallon hayder da duk abinda suke ko a jikinsa. Laptop dinsa ma yake daddannawa. Tabe baki yayi ya kalli amir da turaren ke hannunsa yana fesawa ya ci gaba da aikinsa.


" nawa? Don gaskiya akwai kamshi ba karya ko nawa ne yaci kudinsa. Jabir ya karba yana kallo


" 3,571 USD."

" What?" Suka fada a tare.

Dariya Hafiz omer yayi " da gaske nake yi. Ranar ba na baku labarin turaren da huzaifa ya siyo a Dubai ba? Har nake cewa zan yi oder don yamin dadi sosai. To shine wannan. Last month akayi launch dinsa. It's take them 3 years to create it. That why there called it deserving the highest. "


" gaskiya yaci sunansa. Amma ban iya cire makudan kudi haka in sai just one perfume!!" Amir ya fada yana karewa turaren kallo


Junaid yayi murmushi " tasan mutumin nata kan son kamshi, turaren komai tsadarsa zai saya in har ya masa. Hakan na nuna ta gama karantar mutumin nata. Don in kanason burge haider bashi turare ammafa designer mai dan banzan kamshi."


Harararsa hayder yayi " what do you mean?"


" nasan kaji dadin wannan kyautar. Kuma dama burinta kenan kaji dadi. Right? "


" of course. " hayder ya fada yana kallon junaid dake masa murmushi


Hafiz ne ya dan Sosa kai " da har ina cewa na samu turare?"


" in kana ciki, mu buga oder kawai. Tunda bamu da wadda zata bamu." Hafiz omer ya fada


Asiya dake gefe ta cika tayi fam, ganin yadda suketa koda turaren. Ta kallesu tana tabe baki " banda abinku meye abun burgewa a wannan turaren da har za a shekara uku wurin kirkirarsa? Ni wannan ko kyauta ban so balle insa kudina in siya."


Gaba daya kallonta suke cike da mamakin maganarta. Alim ne yayi dariya don sun dade da harbo jirginta. " haba kanwarmu kema kinsan kin fada ne kawai, amma ba Wanda zai ji kamshin turaren nan ko ya ganshi, ya ce bai burge shiba."


Junaid shima murmushi yayi " anya kanwarmu? Kodai kishi kike?"


Baki ta tura " Allah ya kiyaye in tsaya kishi da wannan slender din." Gaba daya dariya suka kwashe dashi


Hafiz omer ne ya harareta, kauda kanta tayi. Ido hudu sukayi da hayder dake aika mata da wani irin kallo mai kamada gargadi gargadi, harara harara. Zuciyarta ne ta fara rawa, don tunda suka zo banda gaisuwa ba abun da ya hadasu, ko kallon arziki bata samu ba. Da sauri ta dauke idonta don bazata jure kallon fire da yake aiko mata ba. Kwafa yayi kadan ya ci gaba da abinda yake yi.


Jabir ne ya canza akalar hirar. Nanfa aka koma musun kwallo, su hubby suka ci gaba da parking din gift din. Asiya kam jikinta yayi sanyi, don haka tashi tayi ta nufi room din su Hajiya.


Abdul fatta ne ya shigo, kusa da hayder yama kansa mazauni. " wash!!!! " sannu suka fara masa, tare da gaisuwa. Hubby ya kalla " suraj na jiranki a waje, nayi nayi ya shigo yaki,." " OK" ta fada tana ci gaba da abin da takeyi.


" na manta munada uwa a bakin murhu, kuka Samu wahala. Allah yasa muna shiga airport muka hadu da suraj. Yanzu haka tare da maaikatan company dinsu muke, zasuyi packaging din sauran kayan."


Hafiz omer ne ya cabe da " haka nefa!!."


Junaid ne ya fita ya shigo dasu. " amma dai kin San kin ajiye mutun a waje ko?"


Harararta hubby tayi " na ajiyeshi ko ya ajiye kansa? Ko gayyatoshi nayi?"


" ba kyau wulakanci, ki tashi kije, kar ya gaji da jira."


" so what? " hubby ta fada


Tashi ummu sulaim tayi, " muje in rakaki to."


Ganin hankulan samarin ya fara kaiwa Kansu, duk da a hankali suke maganar yadda baza suji ba, yasa hubby mikewa.

" bari in tambayi Hajiya tukunna.?"


Baki ummu sulaim ta rike " to fah!!!"


Ido hubby ta zaro mata tare da daga gira daya. " what? Ko kina tunanin zan iya fita ne ba tare da sanin taba."


" no wai gani nayi nan ne, ba wani dadewa zakiyi ba. Its almost late." Ummu sulaim ta fada tana duba agogo.


" dozen matter."

Bayan ta gayawa Hajiya ta basu izni tare da jaddada mata karta Dade.


Zaman gyalenta ta gyara, Suka fito. Suna zuwa dai dai corridor din wurin ummu sulaim ta juya abinta. Ko kafin hubby ta bude baki, har ta shige ciki da dan gudunta. Baki hubby ta sake tana kallonta, kafin tayi kwafa. " zamu hadu ne."


Juyawa tayi tana scanning din wurin. Motar Kangiwa air ways. Ta fara hangowa, daga gefe ta hangoshi tsaye jikin wata farar mota kirar Mitsubishi


A hankali cikin takunta mai daukar ido, da natsuwa ta nufi inda yake. Tun fitowarta idonsa a kanta, ya kasa dauke idonsa.

Sai yau ya kara kare mata kallo sosai. A cikin hasken fitulun da suka kawata wurin, ga kamshin furanni.


Sanye take da material purple, yellow, blue, brawn. Sai mayafi purple Wanda har kana iya hango kitsonta back and front, daya kara fito da kyan fuskarta sosai. This is the first time da ya ganta ba zunbulelen hijab. Duk da yanzu dinma rigar bubu ce, wadatacciya har kasa, don ko takalminta bai iya gani, Sai dan tsininsa da yake hangowa.

Dressing din ya matukar burgeshi, don ya bashi damar ganin daya daga cikin abunda yake fatan matarsa ta sunna ta kasance tana dashi. Gashinta da yake iya hango tudunsa ta bayan gyalen yayi kamar a cuci.


Kanta a kasa, amma tana jin yadda idonsa yake a kanta. Gyara gyaleta tayi, ta kara jawoshi da kyau, yadda zai rufe gashinta.


Sallama ta masa, cike da nutsuwa.


Murmushi ya sake mata " waalaikumus salam, barka da fitowa gimbiyar mata."

" ya gajiyarka." Ta fada a hankali, kamar bata so.


" alhamdulillah, mu kam ai mun saba, so ba wata gajiya, wannan Sai Ku mata."


Shiru tayi tana wasa da yatsunta. She is uncomfortable, don ko yan matancinta bata yi wani tsayawa da samari ba. Zata iya cewa Yusuf ne kawai. Shidin ma ba ko yaushe ba. Don zata iya kirga zancen da suka yi alone, after all she known him. Wannan kuwa is total stranger.


Tsayuwarsa ya gyara fuskarsa cike da annuri " nazo miki sallama ne, zan wuce tomorrow morning. Yaushe zaki wuce kankiya in kin koma?"


Shiru tayi tana dan nazari " one week my be."


" OK. In that case ina ga zanzo kafin ki koma, don nima yanzu haka Italy zan wuce. Ina sa ran dawowa nan da 3days."


Kallonshi tayi kafin ta kauda idonta gefe.


" OK. Allah ya kiyaye hanya."


Yaji dadi sosai, daya kasa boyuwa a kan fuskarsa. "Amen na gode,."


Shiru sukayi na dan lokaci. Ita ta kauda shirun. " zan shiga ciki."


" OK. Sai nazo din."


Harta juya tadan dawo " mun gode sosai da hidima." Ta juya ba tare da taji mai zai ce ba.


Yana tsaye har ta shige ciki,. Murmushi yayi yana shafa sumar kansa. Allah yayi halitta a nan. Komai nata mai kyau. Ya fada a ransa.


Lokacin ne maaikatan nasu ke kokarin saka manyan jakun kunan a bayan van din. Su hayder ne suka karasa wurinshi don su kara masa godiya.


********************


Hajiya da ummu sulaim jirgin Lebanon suka hau zuwa Oregon. Don dubo ummu kulsum dake fama da laulayin ciki, shiya hanata zuwa graduation duk da suna kusa. So time din flight din su da safe 7:30. Su Hajiya Balkisu, Asiya, Hafiz omer, kuma jirgin Lego's. 1:15. Alhaji munir, jabir, junaid, haider, alim, da amir. Direct jirgin Kaduna 4:00. Alhaji Jamil da ashir sunbi jirgin abuja tun last night.


Wuraren tarihi su junaid suka kai hubby don tunda su ummu sulaim suka tafi, taji garin ya fita a ranta gaba daya.

Golden lake sukayi branching. In da kowa yasai abinda yake so na ciye ciye suka nemi wuri suka zauna suna ci suna hira, duk labarin school ne, da friends dinsu.


Hayder kam gefe daya ya samu ya zauna yana kallon jamaar dake shige da fice. Yau shigar ash and black yayi yayi kyau sosai.


Hubby ta kalleshi tana tabe baki. " a karatun harda miskilanci ake kara koyar daku ko?"


Kallon hayder suke yi da ke waya hankali kwance.


Junaid yayi murmushi " ina kika taba jin an koyawa mutun miskilanci? Dama dai miskilin ne."


" naga abin ya kara shaharane, na Sani ko harda shi ya koya."


Dariya sukayi


Amir yace "gaskiyarki Anty miskilanci ya karu, ni kaina shaida ne."


Murya hubby ta dan daga yadda zai jiyota " agric chicken. " ya jita sarai ya mata banza, bai ma nuna ko alamar yasan dashi take ba. " agric chicken " ta kara daga murya.


Haushine ya kama hayder musamman jin dariyarsu amir. Don ya tsani sunan.


" arage dai a sami ta gobe, kowa na hira da dan uwansa, don mugun hali ka koma gefe."


Ko kallon ta bai yi ba. Ya ci gaba da danna wayarsa.


" Allah ya shiryi mai bakin hali."


" amin" su junaid suka fada suna dariya.


" Matar hayder ta banu, wallahi har tausayinta nake." Alim ya fada


Tabe baki hubby ta yi " ita taga zata iya ai."


" haka ne kam, tunda yanzu ma yan matan duk da sanin halin nasa suke kara manne masa." Alim ya fada


Dariya junaid yayi " kasan mata da yawa na son muskilayen maza."


" in ji wah?" Hubby ta fada tana tsareshi da ido.


" kema fa kina ciki, naga Yaya Yusuf ma ai miskilin ne,." Junaid ya fada


Harararsa tayi " in kana maganarka karka kuskira ka tsomani ciki."


" afuwan."


" in kun gama shirmen Ku tashi mu tafi." Hayder ya fada yana yin gaba


Agogo junaid ya duba past 3. Da sauri suka mike suka nufi mota. Don isa airport don sunyi dama da Alhaji Munir da jabir zasu hadu a can.


" waye yake shirmen? Allah ka shiga hankalinka, don kaga kayi tsawon kafa, bashi zai baka lasisin yimin rashin kunya ba."


Juyowa yayi ya kalleta, ya juya ya ci gaba da tafiyarsa. " mai hali bai fasa halinsa." Ya fada a ransa


Haushine ya kara kama hubby. Ta yi tsaki

*******************

Kallon sit din tayi, ta kalleshi. " dawo nan! Ban son sit din kusa da window" kallonta yayi ya kalli sit din, Ya kauda kanshi.


" agric chicken!! Da kaifa nake magana, ka koma can sit din."


Air piece ya sa a kinnensa tare da kunna kiraa ya kyara belt dinsa da zamansa da kyau.


Haushi ya kuma hubby, ji take kamar ta kifa masa mari, ta rasa yadda akayi number din sit din su yazo a hargitse. su junaid ma kowa sit dinsa da ban dana juna, ita da hayder ne kawai sit dinsu ya zo daya.


Tsaki tayi, ta gyara yadda zata wuce ciki, bata son window sit. Koda za su mata burking ta gayawa jabir amma see how she end of. Kafarsa ta take da karfinta kafin ta wuce.


Ya jita sarai, don yaji zafi sosai, amma ko motsi be yi ba, balle tasa ran zai tankata.


Wayarsa ce tayi kara, a yan gace ya duba, tare da answering din call din. Hatta hubby dake kusa bata iya jin me yake fada, saboda yadda yake maganar, cikin Jan aji da natsuwa. Sake baki hubby tayi tana kallon ikon Allah.

Kallon ta yayi, tare da mika mata wayar. Wayar tabi da kallo, kafin ta amsa. Nasrin ce ke son mata sallama, don basu hadu ba a wurin walima, saboda tana jin kunyar Hajiya so bata xoba.


Jininsu ya hadu, da hubby duk da ba wani dadewa sukayi suna magana ba. She respect her, don tasan matsayin Yusuf a wurin hayder. Haka tana jin labarin hubby sosai a bakin su Hafiz. Gani daya ta mata taji ta kwanta mata a rai.


Hira sosai suka yi, har sai da akayi annausing cewa jirgi zai tashi, kowa ya kashe wayarsa. Sannan sukayi sallama ta mika masa phone din.


" she is nice girl. In baka shawara?" Ta fada tana kafeshi da ido.


Kallonta yayi cikin muryarsa mai kama da anmasa dole " ina jinki?"


Tabe baki ta yi tana dan rainin sense a gasan ranta.


" mai zai hana ka nemi Asiya. She is the perfect choice for u. Kun matukar dacewa."


Kallonta yake, girarshi ya dan Sosa ganin takai karshe.


" thanks for the advice, keep it to your self, I don't need it."

Harararsa tayi " wai kai me yasa baa abin arziki da kai ne?" Tsaki ta yi ta gyara zamanta. Tunawa tayi da assignment dinta na islamiyy da ta taho dashi don tayi, amma bata samu time ba. So yanzu da zaman banza bari ta dauko tayi, ko ta rage takaicin hayder. Tausayin Asiya take. Yarinyar na matukar sonshi..........Tattaunawa akan daya daga cikin wannan mau'du'in. Muhimmancin ilmin da namiji, da ya'mace, sai muhimmancin auratayya tsakanin maban banta kabilu. Da harshen larabci+


Tsaki hubby ta yi ta jerowa daya bayan daya. Ba wai larabcin bane bata iya ba, yanda zata jera point din. Sannan tana da matsala har yanzu wurin jera wasula.

"Alhamdulillah" ta fada lokacin da aka fara raba abinci, don tana bukatar sake nazari, duk point din data dade da tanada sun watse.

Hankalinta kwance ta dibi girki yadda ya kamata, ta kora da coca cola mai sanyi. Hayder ta kalla da ke shan tea. Ta tabe baki

Book dinta ta dauko ta ci gaba. Takaici ne ya ishi hayder, yadda hubby ta cika masa kunne da tsakinta

Littafin ya kalla don ganin me take rubutawa. Dariya ce ta kusa kamashi. " zero head, aikin yan kananan yara, amma ta kasa ta ishi mutane da tsaki." Ya fada a ransa


Kallonta yayi yadda ta takar kare kamar gaske.


Biron ya fige a hannunta, da sauri ta bishi da kallo, book din ya janyo ba tare daya ce mata komai ba, ya daura kan abin cin abinci, da zaka janyo mai kama da table ya fara rubutu.


" ban son rashin mutunci, taya zaka wani fige Abu a hannuna, kana shigamin hanci da kudun dune fah."

Ko kulata bai yiba, kallon rubutun take mai matukar kyau, a tsare. Kamar ingin ke rubutawa. " komai sai an masa yanga, rubutun ma ji yadda yake, kamar baya son yi."


Sai da ya gama, ya ajiyemata a gabanta da biron. " please leat me sleep in peace. " ya fada yana tsareta da ido.


" da yake na rike maka ido ba?" Kai ya kada tare da lumshe idanuwansa.

Taji dadi sosai, yanda ya tsara mata bayanan dalla dallah. In gan taccen Arabic. A Jakarta ta tura book din " shishshigi kawai, ko an gaya maka na kasa ne?"

Ya jita sarai, ya shareta. Don yasan albarkacin Yusuf take ci. Da ba dan haka ba da ko kusa bazata kara wargin shiga harkarsa ba. Yana respecting dinta ne saboda sanin matsayinta a zuciyar yayan nasa, da irin kyakykyawan zaman da sukayi, da duk lokacin da zaka zauna da Yusuf Ku dan dade sai kasan yadda ya damu da ita, haka ita ma. ta wani gefen kuma yana tausaya mata saboda rashin da tayi, Wanda maye gurbinsa zai mata wuya a rayuwa. Shi duk da jinin da suka hada da ita, kwata kwata baya jinta a ransa. Har mantawa ma yake da ita.

*******************


Dawowarsu da one week aka shirya wasu hayder hadaden get together and babaque. A harabar gidan Alhaji Jamal.


Abun ya kayatar sosai, yan uwa da abokan arziki duk sun hallara. Sir omer, da iyalansa, Jamil ma da nasa iyalan, Alhaji babba, shima da friends dinsa. Gidan ba masaka tsinke, kamar ana wani gagarumin biki.


Mommy Hauwa da friend dinta Hajiya salwa suna zaune a falon mommy Hauwa, yan aikinta na faman hada gifts din da already anyi packaging dinsu a manyan buhu, suna fita dasu mota.

Hubby ce ta shigo kamar an korota. Kallo daya mommy Hauwa ta mata taji gabanta ya fadi.


Batayi tsammanin samun mommy a gida ba. So ganinsu a zaune yasa tayi kokarin saita kanta, tare da share hawayen da suka wanke mata fuska.


" sannunku da gida." Ta fada tana wucewa dakinta da sauri, gudu gudu.

Dukkansu da kallo suka bita. Mommy Hauwa ta ja ajiyar zuciya ganin ta shige.


Hajiya salwa ta kalli mommy Hauwa dake kokarin yafa mayafinta. Bayan sammani ya fita da buhun karshe. " kina nufin tafiya zakiyi ba tare da kin je kinga halin da yarinyar nan take cikiba? Wai ke me yasa kike haka ne? Kina ganin ta shigo da irin wannan damuwar, ai kya je kiji abinda ya fusatata haka? In baki jata a jikinki ba kin san matsalarta,wa kike son ya miki wannan aikin. Bayan keda kike uwarta kina nuna ko in kula kan lamurranta. Shiyasa ta zabi zama da gwaggo sama da ke da kika haifeta."


Murmushi mommy Hauwa tayi, mai kama da yake " bazaki gane lamarin Ummi ba ne."


" ta ya zaki gane kuwa? Tunda baki jata a jikinki ba." Hajiya salwa ta fada tana nufan dakin hubby cikin jin haushin kawartata.

Tana jikin Woodruff kayanta take fito dasu, ga akwatunana har biyu manya ta bude tana jefa kayan a ciki. Hawayene wani na bin wani a fuskarta. Sai Jan hanci take. Tausayinta ne ya kama Hajiya salwa. Hannunta ta kamo suka nufi bakin gadon hubby. Kuka mai karfi hubby ta fashe dashi ta daura kanta a cinyar Hajiya salwa. Hajiya salwa bata ce mata komai ba, sai shafa kanta da takeyi alamar lallashi. Ta bata damar tayi kukan ko taji saukin damuwarta.


Mommy Hauwa ce ta leko, don taji shirun yayi yawa, gashi ana can ana jiranta. Kallonta Hajiya salwa ta yi " ki tafi kawai, zan isoki" juyawa mommy Hauwa tayi ba tare data ce komai ba. Amma ita kadai tasan damuwar da zuciyarta ke ciki. Mawuyacin Abu ne kaga kukan hubby, don ita sha yanzu ne, maganin yanzu. Kana gaya mata cuta ta gayama mutuwa, shike nan ya wuce a wurinta. Amma muddin kaga tana ma Abu kuka to ba karamin Abu aka mata ba.


Sai da tayi kukanta mai isarta. Sannan tayi shiru, tana Jan ajiyar zuciya. " komai yayi zafi maganinsa Allah. Ki daina sama kanki damuwa irin haka, duk da bansan dalilin kukan ba na tabbata ba karamin Abu bane zai saki kukaba." Hajiya salwa ta fada tana mai mata kallon tausayawa. Kanta ta sunkuyar tana wasa da yatsunta. Don duk a kawayen mommy Hauwa tafi jin nauyin ta da ganin girmanta. Don Matar tanada mutunci sosai. Ga sanin ya kamata.


" ki gaya min waye ya taba min ke?"

Shiru tayi ta kara sunkuyar da kanta. Duk yadda Hajiya salwa ta so hubby ta gaya mata damuwarta amma ta kasa. Saboda nauyinta da takeji. " shi ke nan, ni zan tafi tunda ban kai matsayin da zaki gayamin damuwarki ba."


Hannunta hubby ta riko " kiyi hakuri wallahi ba haka bane."


" I understand. But waannan kayan fa da kika fara hadawa?"


Kallon kayan hubby ta yi sannan ta sunkuyar da kanta " gobe zan koma kankiya."


Kada kai tayi, tana jin jina sakaci irin mommy Hauwa.


" ita matsala in ta samu ba guje mata ya kamata a yiba, fuskantarta za ayi don a maganceta, saboda guje mata kamar barin baya da kura ne." Ta fada tana mikewa.


" na gode sosai, ki gaishe min dasu Faisal." Hubby ta fada cikin girmamawa


" zasuji." Ta fada Tate da ficewa a dakin. A harabar gidan sukayi karo da Ummul khair da ummu sulaim suna shigowa. Gaisheta sukayi cikin girmamawa, sannan suka wuce ciki.


A gogo hubby ta kalla 9:43 na dare. Tsaki tayi ta tashi ta ci gaba da hada kayanta.


Kai tsaye dakin hubby suka nufa. Da sallama suka shigo. Dagowa tayi daga jera kayan da take cikin akwatin ta bisu da kallo. Tare da amsa sallamar." Me zan gani haka?" Ummul khair ta fada tana zama a bakin gadon. Ummu sulaim kam kujerar madubi taja ta zauna tana bin kayan dake wargaje da kallo.


" abinda idonki ya gane miki." Hubby ta bata amsa


" kar dai maganar waannan sakarkarun ne? yasaki kike son tafiya?"


Tabe baki hubby tayi tana ci gaba da ninke kayanta. " ko kadan, lokacin tafiyar tawa ne yayi."


" be kamata ki damu kanki ba, kan wannan maganganun shirmen, tun da kin San ba gaskiya bane. Ba komai yake damun munaya ba illah kishi da zugan su Anty samira." Ummu sulaim ta fada cikin takaici


Hawaye ne suka fara bin kuncin hubby " ta Yaya bazan damu ba? Kina jin irin sunayen data dinga kirana dasu a cikin jamaa. Tun da nake baa taba min tozarcin da ya bakanta min rai ba irin na yau. In kece ya zakiji?"


Kada kai ummu sulaim ta yi, cikin jin zafin abinda akawa yar uwarta. " a kwai ciwo kam, shi yasa na tsaya na basu nawa piece of mind din."

" na rasa abin da ya kawo wannan maganar. Naga da safe har gaisawa kukayi da ita lafiyar Allah." Ummul khair ta fada


" ki kyale abu, in har aka ce da munafurci a ciki. Anty samira yar uwata ce, amma Sam halayyarta basu min ba. Ta cika kananun magana da son hada wuri. Ina wurin munaya ke bamu labarin Ahmad ya kaiwa hubby su Arafat sun mata wuni. Da irin yadda yaran suketa labarin yadda ta kula dasu har basu so komawa ba. Munaya na ba su Anty samira labarin yadda take jin dadi, da yadda take son hubby saboda tana son yaranta. So na barsu suna ta hirar kin San munaya in kanason ka gama da ita to ki nuna kina son yaranta. Yanzu zaki ga mutunci. So ina ganin bayan na bar wurin ne suka zugeta."


" in banda dabbanci tayaya zatayi tunanin ni hubby in rasa Wanda zan so sai Ahmad? Tsakanina da Ahmad mutunci ne, da ganin darajar juna. Duk cikin yan uwan Yusuf ba Wanda yake bibiyar rayuwata sama da shi. Su suna ganin kaman zuwan da yake yi kankiya wani abun ke kaishi. Wanda kuma wallahi ba haka bane. Ko da wasa ban taba ganin wani alama ko kadan sabanin zumunci da mutuncin dake tsakaninmu ba. Shi yasa nima nake mutuntashi nake ganin girmansa."


" that's it. Wannan shine yasa suke ganin soyayya kukeyi. Don ni Anty samira ta so ta bugi ruwan cikina don taji wani Abu a bakina. Amma na nuna mata ban taba ji bama, har nake ce mata wannan ai tatsuniyar yara ce, ina hubby ina Yaya Ahmad. " Ummul khair ta fada cike da takaici.


" amma dai kin San baki mana adalci ba in har kika ce tafiya zakiyi, bayan kin San biki nan ba wani lokaci aka sa da yawa ba, just 3weeks." Ummu sulaim ta fada tana kallon hubby


" kiyi hakuri, gaba daya garin ya fita a raina. Kin San jiya salis har gidan nan yazo, ni na dauka abin arziki ya kawoshi,ba kunya ba tsoron Allah wai sona yake yi.

Ido suka zaro a tare " wane salis din? Yaya salis?" Ummul khair ta tambaya harda sassarfar magana.


" shifa!!!! Bama shi yafi ban haushi ba irin Engr Sahabi, harda wani shi ya dace ya maye gurbin marigayi. Mu rufawa juna asiri." Dariya su ummu sulaim suka sa. Haushi da takaici ya kara cika hubby.


Cikin dariya Ummul khair ta ce " sai kika ce masa me to?"


" bar dan iska, an gaya masa kwantai nayi? Ko kwantan nayi nafi karfinsa wallahi. In ba rashin kunya da rashin tunani ba tayaya yana abokin mijina, kawai don ya rasu ya wani zagayo. Sai ma kunji yadda yake wani kashe murya kamar in sanu muciya in ta dukan banza don haushi."


Har lokacin su ummu sulaim dariya suke ma hubby. " kin San dama an ce da budurwa da bazawara, kamar kasuwa ce, da mai brush da Mara brush kowa ya gani ya gyasa sai ya lallabo, sai in yaga no go no go sai ya kara mai. So kadan ma kika gani. Shiyasa gara mutun yayi aurensa ya huta. " Ummul khair ta fada


Harararta hubby ta yi " dama ke kam gara da aka hada dake, don naga kin fiye son aure da yawa. Ni kam ban shirya ba, ba kuma rana."


" ai kuwa yanzu kika fara ganin irinsu Engr masu son rufa miki asiri." Ummu sulaim ta fada tana dariya.


" zan kara ganin kafarsa a nan gidan, sai na tata masa rashin mutunci. Yanda gobe ko mai kama dani bazai kuma marmarin tunkara ba."


" kar kiyi haka, tunda bakya son sa just find a way da zaku rabu a mutunce, yaci albarkacin Yaya Yusuf kodan mutunci da zumuncin dake tsakaninsu." Ummu sulaim ta fada


" ya labarin hot guy?" Kallonta hubby tayi. " waye kuma hot guy? "


Harararta Ummul khair ta yi " karki raina min hankali man. Bayan naji labarin komai."


Tsaki hubby ta yi "sai ki je ki tambayi Wanda ya baki labarin. Kinfa fara raina ni, kar kiga ansa miki ranar aure ki shiga hankalinki dani."


" Allah baki hakuri. Don Allah dan ban labarinsa mana? Yaushe ze zo, na kosa in ganshi"


" ban Sani ba." Hubby ta fada


Sun dade suna hira, har 11 na dare, sannan sukayi sallama da hubby ta rakosu har jikin mota. Sannan ta koma. Already lokacin an tashi daga get together da babaque din su hayder.


Hubby na shirin kwanciya su mommy Hauwa dasu jabir duka dawo. Tana jin hayaniyarsu a falo taki fitowa, adduar bacci tayi ta gyara kwanciyarta.

Sai da kowa ya kwanta, sannan mommy Hauwa ta nufi dakin hubby.


Da akwatunan hubby ta fara karo. Kafin ta nufi gadon da hubby ke kwance. Bubbuga kafarta tayi, Wanda yasa hubby bude idonta, ganin mommy Hauwa yasa ta tashi ta zauna. Itama zama tayi a bakin gadon tare da kamo hannun hubby cikin nata. Cikin murya mai taushi " me ya faru kika dawo, dazu ba tare da an kammala abin da ya kai ki ba? Rai a bace? Ke da wa?" Ta jero mata tambayoyin a tare.


Cikin damuwa ta fara zayyanowa mommy Hauwa yadda sukayi da munaya. Dasu Anty samira. Ajiyar zuciya mommy Hauwa tayi ranta ya baci sosai amma bata nuna ba.


" wannan kayan fa?" Ta tambaya tana kallon kayan


" gobe zan koma."


Kada kai mommy Hauwa tayi " ki cire maganar komawa kankiya a ranki, don babu. Lokaci yayi da zaki tsaya ki zaba ma kanki mafita. Tunda kin nuna baki son karatu, to ki fito da miji mu aurad dake, don bazai yiwu ba karatu ba aure ba. Wannan yaron in har da gaske yake, to ki shaida masa ya fito."


" bafa soyayya muke ba, just friend dina ne." Hubby ta fada da saurinta.


Kallon ta mommy Hauwa tayi na dan lokaci kafin ta ce " shi kenan dama Hajiya salwa ta dade damun maganar tana son hada ki da Husain, ni na dakatar da ita, saboda sanin halinki, but zan gaya mata ta turoshi Ku dai dai ta. Hankalina dama bai kwanta da wan can yaron ba."


Da sauri hubby ta diro daga gadon, " mommy wane Hussain din?"


Harararta mommy Hauwa tayi " daya da kika Sani. Ki zama a cikin shiri daga gobe zuwa jibi zaki iya ganinsa a gidan nan. Ki natsu banda rashin hankali, kin dai San yadda muke da Hajiya salwa." Ta fada tana kokarin barin dakin.


" don Allah mommy kiyi hakuri, wallahi ni dai bai min ba."


Kallonta mommy Hauwa ta tsaya yi kafin ta kada kai ta fita.


" innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Meke faruwa da rayuwata ne? Daga wannan sai wannan. Ina ita ina Hussain miskilin mutun number daya hatta ita hanta Hajiya salwa kullun cikin korafin miskilancinsa take, gashi da murdadden hali ya hadu da zamowarsa soja. Tun da suke haduwa dai dai da rana daya bata taba ganin dariyarsa ba, magana ma wannan ko gaishe shi sukayi sai dai ya daga maka kannu kawai. Bata manta hutun data taba zuwa gidansu lokacin tana SS 1 irin dukan da sukaci ita da kanwarsa salma kafin ta rasu. Saboda surutunsu,.


Akwai ranar da har tsallen kwado ya sasu. Kwanansu biyu suna jinyar kafafu. Ita kanta Hajiya salwa shakkarsa take yi.

Ta kasa barci, saboda damuwa da nema ma kanta mafita. At last ta gama tunanin abinyi. Ajiyar zuciya tayi. Tana Allah Allah gari ya waye taje ta samu daddynta..........Sunday, tun da sassafe hubby ta tashi. Ta gama saka kayanta a mota. Sannan ta kira malan iro. Don ta shaida masa ya zama cikin shiri by 11 zasu wuce zuwa kankiya. Saboda daddy dinta baya yadda tayi driving zuwa wani gari.+

Sai 10 sannan mommy ta fito daga side din daddy. Dama hubby ta dade da shiryawa tana jiran tashin daddyn nata. Don tasan weekdays baya tashi da wuri.


With full confidence ta nufi part din daddy tare da sallama. A falo ta sameshi yana kallon tashar CNN. Cike da faraa da jin dadi yake kallon tilon yar tasa. " ummina an har tashi?" Murmushi tayi tare da gaisheshi tana zama kasan carpet cike da ladabi. Kallonta yayi yana murmushi " sai inah? Da safen nan?" Murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta. " ina son komawa kankiya yau. Kayi hakuri da ban sanar maka da wuriba." Kallonta yake yi yana karantar yanayinta.


"  mun riga mun gama magana da Alhaji. Zaki ci gaba da zama damu a nan. Har Allah ya fito miki da miji kiyi aure. So ba maganar komawarki kankiya, u stay with us."


Lokaci daya hawaye suka fara bin kuncin hubby. " please daddy kayi hakuri ka barni in tafi, nafi son zama a can don Allah. "


Ajiyar zuciya Alhaji Munir yayi. " me muke miki da kike gudun zama damu Ummi?" Kar ta kada cikin muryar kuka ta ce "ba komai, bakumin komai ba."


" so kamar yadda na fada ne, ba komawa kankiya. Sannan ki fito da miji cikin masu sonki Wanda hankalinki ya kwanta dashi.  Don so nake a hada dana jafar tunda Allah yasa ya fito da yarinyar da yake so.

Kuka ta fashe dashi tana ba daddy hakuri, ita wallahi ba Wanda take so.

" shi kenan dama mommynki tamin bayanin dan wurin Hajiya salwa. So in yazo naji yanda kukayi."


" wallahi ni ban sonshi, don Allah daddy ka taimakeni ka gayawa mommy karta ce musu yazo."


Tausayi hubby ta bashi, ganin yadda take ta risgar kuka, amma ba yadda ya iya dole a matsayinsa na uba ya sauke nauyin da Allah ya dora masa. Ya tuno da maganganun da sukayi da Alhaji kawu.


Gyara murya yayi. " shi kenan zan gaya mata, amma bisa sharadi daya."


Da sauri hubby ta rarrafo hannunta ta daura kan gwuiwowin Daddy tare da kwantar da kanta. " na yadda da koma wane sharadi ne. Matukar mommy baza ta turo min wannan monster din ba." Ta fada tana Jan hanci saboda kuka.


" na baki nan da 2weeks ki fito  da miji, don gaskiya na gaji da ganinki ke ba aure ba, ke ba karatu ba. Sai gararanbar association"


Da sauri ta dago cike da firgici da tsoron kalaman daddy. " kaji tausayina daddy don Allah. " ta fada cikin marairaice murya, baki na rawa ga hawaye nabin fuskarta.


Tausayi sosai ya kara kama Alhaji Munir. Gyara zama yayi. " Ummi hakan shine soyayyar, kowanne uba yayin da yarsa takai munzali fatansa ya aurad da ita. Don shine mutuncinsa kuma mutuncinta, ballan tana ke da kin taba yin auren, kin San dadinsa da rashin dadinsa. Don wata kaddara ta gitta, baya yuwuwa ki yankewa kanki kin sake wani auren. Hakan na nuni da kina fushi kenan da hukuncin Allah. Bayan sanin kanki ne duk abun da ya samu bawa to kaddararsa kenan, ya kamata ya rungumeta hannu bibbiyu, yayi fatan ta zamo masa alkhairi duniya da kiyama. Wannan shine daya daga cikin alamomin musulmi na kwarai. Yadda da kaddara mai kyau ko akasinta. A yan kananan shekarunki bai yiyuwa mu ajiyeki muna kallo, ba muyi miki adalci ba, bamuyi wa kanmu ba. Don haka ki kwantar da hankalinki, ki natsu cikin masu sonki in akwai Wanda ya kwanta miki, ki shaida masa ya fito, kiyi aurenki, shine cikar kamalarki, in kinyi haka muma kin tsare mana namu mutuncin."


Cikin kika " in sha Allah zan yi yadda kuke so."


" Allah ya miki albarka, ya baki miji na gari, da Yaya masu albarka wa' anda zasuji kanki kema. In sha Allah bazaki taba dana sanin biyayyar da kikai mana ba. Ina alfahari da zamowarki ya a gareni. Na gode."


Rungume mahaofin nata tayi. " na gode daddy da adduarku garemu. Ina alfahari da zamowarki iyaye na gari a garemu."


Murmushi mommy Hauwa tayi ta dade tsaye a bakin kofar, amma basu kula da shigowarta ba. " in an gama tattaunawar tsakanin uba da yarsa, sai muje a ba ciki nashi hakkin." Murmushi hubby ta kakalo tare da ficewa daga dakin.


Da kallo iyayen suka bita cikin tausayawa. " akwai rikici fa!!! Sai kinayi kina bata baki."


Murmushi mommy Hauwa tayi " ummin ce wani lokaci Zuma ce, sai da wuta. Kasan tun sassafe har ta sa kayanta a mota? Gani kawai take data zo ta kallalameka zaka barta ta tafi."


Ajiyar zuciya Alhaji Munir yayi " kema da naki laifin ai. Ban son ki kara mata maganar Hussain tunda ta furta bata son sa shike nan."


" Allah ya zaba mata miji na gari, amma gaskiya naso wannan hadin. "


" mata kenan, kibar yarinya ta zabi wanda ranta keso. Kedai naki ki bita da addua."


" ai shi kenan, na farko ma ya akayi, balle na biyu. Allah ya mana jagora."


" amin" Alhaji Munir ya fada, a tare suka nufo part din mommy Hauwa don yin break fast kamar yadda suka saba.


Already su jafar, jabir, junaid sun halkara saman dinning table suna jiran iyayen nasu.


Toilet direct hubby ta wuce ta wanke fuskarta. Sannan ta nufo dinning din.


                *******************

Kwance take saman gadonta, sai sakawa da kwancewa take. Lallai ta yadda da maganar  da hausawa ke cewa mutuwa mai tonon asiri, tabbas haka maganar take, dabadon mutuwa da yanzu tana tare da mosoyinta, wata kilama harda da ko ya. Tunanin yadda zata iya zama da wani mijin ba Yusuf ba take.  "Yanzufa dole in auri wani? Dole yadda Yusuf ya sanni shima haka." Runtse idonta tayi hawaye mai zafi na bin kuncinta. Don ba abun dayafi daga mata hankali irin hada shinfida da wani ba Yusuf ba. To ita yanzu waye zata fitar? Hashim, suraj ko Munir.


Kai no!!! Ba dai  Munir ba, yaron da suka taso tare tasan kuruciyarsa yasan nata. After all ya mata yaro da yawa. Hashim kuma gaskiya tana tsoron zama da kishiya, don bata tashi ta ganta a gidansu ba. Balle yadda ake fadin hatsabibancin matarsa, gaskiya bazata sa kanta a shiga uku ba. Suraj yes!!! Zata iya aurensa don ta lura yana matukar sonta, sai dai tana ganin kamar ajinsu ba daya ba, zai yi wuya aurenta dashi. Don difference din is Claire.

Agogon dakinta ta duba 1:6 pm mikewa tayi ta dauro alwala, bayan ta idar da sallar azhahar ta dora da salatul istikhara, 2 rakaat. Rakaar farko fatiha da suratul khafirun, rakaa ta biyu fatiha da ikhlas. don neman zabin Allah

Bayan ta idar tayi tasbihi, da istigfar ta karanta adduar istikhara.


Allâhumma inni astakhiruka bi ilmika wa astaqdiruka biqudratika wa as’aluka min fadlikal-azimi, fa innaka taqdiru walâ aqdiru wa ta’lamu walâ a’lamu wa anta allamul ghuyubi. Allâhumma in kunta ta’lamu anna hâdhal amra (  bukata   ) khayrun li fi dini wa ma-ashi wa aqibati amri faqdir-hu li wa yassir-hu li thumma barik li fihi wa in kunta ta’lamu anna hâdhal amra(  bukata )  sharrun li fi dini wa maâshi wa aqibati amri fasrifhu anni wasrifni anhu waqdir liyal-khayra haythu kâna thumma ardini.


Wani natsuwa taji yana ratsata. Tana cikin ninke sallayar Aisha tayi sallama. Yar da sallayar tayi da gudu ta rungumeta tana mai matukar farin cikin ganinta.


Cike da farin cikin ganin juna kamar ba jiya suka rabuba. Aisha ta kalli hubby " sis meya faru? Kar dai maganar jiya ce, tasa kikayi zuru zuru haka? Kamar wadda ta kwanta cuta."

Tabe baki hubby ta yi " abubuwa sun kwabe, dama na rasa abokin shawara. Na gode Allah da kika zo at right time "


" tare da Yaya Ahmad muke, yazo ya baki hakuri, baiji dadi yadda kukayi dasu munaya ba. Muje in mun dawo sai mu tattauna."


Tsaki hubby ta yi " wallahi ban son ko ganinshi. Da zaki taomakeni ki ce masa bananan."


Harararta Aisha ta yi " laifin wani dai baya shafar wani. Meye laifinsa a cikin rikicinku? Ki tashi muje don sauri yake, mu samman yabar aikinsa don yazo ya baki hakuri,  muje."


Ba yadda hubby ta iya, haka ta zunbulo hijab dinta har kasa. Don Ahmad ya wuce ta masa wulakanci, saboda girma da mutuncinsa da take gani. Tabbas laifin wani baya shafar wani.


Sosai ya nuna rashin jin dadinsa, tare da bata hakuri. "Ba komai, yariga ya wuce" ta ce masa. Ya mata godiya sannan sukayi sallama ya tafi.


                ****************

Shiru sukayi kowa da abunda yake sakawa, bayan hubby ta gama zayyanowa Aisha matsalarta.


Nisawa Aisha ta yi " maganar su daddy gaskiya ne, lokaci yayi da zaki yi settling. Ni ina ga ki ba suraj dama ya turo. Gayen ya hadu, kuma yana sonki.after all da ganin alamunsa zai yi riko da addini."


" kayya dai!!! Baka ganewa a fuska"


"Haba ke kuwa, kina ganin tabon sallah a goshinsa, ai kinsan ko ba komai yana yinta."


" Allah yasa." Hubby ta fada


" naga alama kamar hankalinki yafi kwanciya da Dr Hashim. " Aisha ta fada tana dariya.


Harararta hubby tayi tare da Jan tsaki. " ni kam duk cikinsu ba wanda nake jin wani Abu a kansa. Sai dai kawai zan iya cewa na danfi ganin dama damar suraj, duk da dinbin matsalolin da nake hangowa."


" in haka ne, mai zai hana ki ba Hussain dama, wata kila in kin fahimce sa, kiga sabanin zatoki, kin San duk muskilancin mutun yakan dagawa matarsa kafa. Sai ki sha mamaki irinsu. Musamman akayi dacen yana sonki. Kuma kamar mommy hankalinta yafi kwanciya dashi."


" ina!!!!! Bada ni ba. Auren soja sa mutun ya shirya."


Dariya Aisha ta yi " nifa kike zagi da wayau."


" kinga zaki iya ne ai." Hubby ta bata amsa tana murmushi


" to koda Engr Sahabi za ayi." Duka hubby ta kai mata " Allah ya kyauta."


" maganar gaskiya dai ko suraj ko kuma salis. Don salis yayi gaskiya bashi da aibu."


" ke a tunaninki zan iya auren abokin Yusuf? Ko kadan don haka ki saka zancen wani salis a dustbin. "


" halacci ke nan aboki in ya mutu ko ya saki matarsa ka aura."


" Allah ko? To baa kaina ba. Don ni ko Wanda ya San Yusuf ban iya aura, don ina ganin kamar naci fuskarsa ne. Gara min bare inyi maneji."


" Allah ya zaba miki mafi alkhairi"

" amin."


Hirar bikin su Aisha suka fara, da yadda ya kamata komai ya kasance.


Sai 5pm Aisha ta masu  mommy sallama, hubby ta rakota compound dinsu, in da driver gidansu Aisha ke jiranta.


Tsayawa sukayi jikin motar, suna maganar fita da zasuyi gobe saboda wasu shirye shirye daza su fara.


Wata hadaddiyar fox jeep ce ta shigo compound din. Baka wuluk sai daukar ido take, gashi tasha tilted da bazaka iya ganin wanda ke ciki ba.


Da kallo su hubby suka bi motar. Aisha ta kalli hubby, hubby ma aishan ta kalla. Suka sake maida hankalinsu kan motar data parka kusa da motar su Aisha..........

Toh!!pa!!!! Suraj, ko Dr Hashim, Munir, ko Engr Sahabi, ko kuma salis...Wani hadadden half cover shoe army green  ya fara musu sallama, bayan kamshin da ya cika hancinansu, da kofar driver ta bude. Sanye yake da shadda mai matukar daukar ido, light green, kanshi na sanye da hula damanga, army green. Yayi matukar kyau ga kamshi, kamar ya fito daga shagon turare.+


Aisha ta kalli hubby " wannan hadadden guy din fah!!!" Da yake bata taba ganin shiba sai labarinsa da take ji.


Tabe baki hubby ta yi " suraj" ta fada a takaice, a hankali yadda bazai jiyo suba.


Fuskarsa cike da faraa ya nufo in da suke tsaye, Cikin takunsa na kasaita.


" u are lucky sis. Please don't let him go." Aisha ta rada mata kasa kasa.


Sallama ya musu, Aisha ce ta amsa masa fuskarta dauke da murmushi.

" what a lucky day. " ya fada yana kallon hubby da kanta ke sunkuye. Yau daya tun haduwarsu dataji nauyinsa.

Aisha ce ta gaisheshi, cikin mutunci suka gaisa. Sannan hubby ta gaishe shi.

Murmushi yayi  yana karewa hubby dake sanye da dogon hijab har kasa brown kallo. Ta masa kyau sosai duk da ba wani kwalliya ce a fuskarta ba.


" to hubby sai goben in mun hadu." Aisha ta fada tana kokarin shigewa mota.


Kallon hubby yayi yana murmushi " baki gabatar min da kawar tamu ba, har zata tafi."


Hannun Aisha hubby ta kamo. " Aisha Jamal Yusuf zubair Oregon, sister din su hayder, my Best friend and also sister. "

" masha Allah, best friend ya kike, ya hidimomi."

Murmushi Aisha ta yi " lafiya kalau, kazo lafiya."


Nan fa hira ya barke tsakanin Aisha da suraj, don shi mutunne mai saurin sabo, da alama yana da son hira.


Hubby dai yar kallo ta zama, sai mamakin Aisha take yadda ta sake dashi kamar sun dade da sanin juna.


" I have to go, nice to meet u." Aisha ta fada tana murmushi


Shima murmushin yayi " nice to meet u too friend. " sallama sukayi da Aisha ta shige mota suka yi gaba.


" bismillah." Hubby ta fada tana yin gaba. Binta yayi da sauri  suka jera.

Shuke shuke ne na fruit, sai kujeru singles kusan guda biyar. Wurin hirar su jabir ne da abokansu. Wurin yayi kyau. Daga wurin kana hango duk abin da ake a conpound  din, kamar yadda kaima ana shigowa zaa hangoka.


Sai da ta tabbatar ya zauna computable,. " bari in shiga gida 2 min, kar suga na dade."


Murmushi yayi " no problems, ko kwana kika ce inyi, ai an gama balle 2min."


Takunta mai matukar burgewa da daukan ido, duk da dogon hijab din amma yakan iya ganin yadda take yi, cikin natsuwa, da yanga, wanda yasan is naturally. Har ta bacewa kallonsa murmushi yayi tare da sauke ajiyar zuciya. Allah ya sani yana matukar son yarinyar. Akwai hankali da natsuwa. Ba irin rawar kan nan na matan zamani. Shi da badan ma yaji ta taba aure ba, a bakin da baya karya. Da ba zai taba yaddaba. Tanada karamin jiki, kuma jikinta nada kyau sosai. Don shi a yadda yake bata bazata wuce 20 zuwa 21 years ba.

Wayarsa dake faman ringing ya duba tare da answering.


A cikin natsuwa take takowa, dauke da wani kyakyakyawan trey golden. Ruwan faro, sai 7live da cups, sai wani bowl mai dauke da danbun nama. Anyi celling din shi da leader


Da sauri ya tashi ya amshi trey din. Kujerar kusa dashi ta jawo zuwa gabansa, ya daura trey din a kai. " thanks. " ya fada yana Mata murmushi mai kayatarwa.


Shiru sukayi na dan wani lokaci. Shi ya katse shirun " naje  kankiya jiya baki koma ba.?"


Cike da natsuwa, " I won't back to kankiya. "


Murmushi yayi " I known, Alhaji kawu ya min bayani. "


Ido ta zaro tana kallonsa cike da mamaki. " meya fada maka?"


Juice din ya tsiyaya, sai da ya yi sipping tukunna, idonsa a kanta, fuskarsa cike da annuri. " Notting much, ya tambayeni yadda mukayi dake, I tell him kinyi accepting dina as a friend. So murmushi yayi irin nasu na manya." Ya fada yana daga mata gira daya. " then he told me in turo magabatana nan da 2 weeks."

" what." Ta fada da dan karfi, idonta a waje. That means kenan duk abin da yake faruwa da saninsu.


Dariya ya yi " am so happy, jiya ko bacci ban iya ba, saboda dadi.  Kamar yasan na matsu Kwarai in ga na ajiye iyali. Wannan shine dalilin zuwana don in ji naki raayin. " do u really accept me as your husband? "


Kanta ta sunkuyar tana wasa da tsinken dake hannunta. Zuciyarta na faman bugun uku uku.  wannan shi ake kira abun yazo, in ji mai tsoron wanka.


" please ina son ji daga bakinki,. Kin yadda kin amince, zaki zama uwar yayan suraj kangiwa?"


Sai da taja numfashi tukunna, kanta a kasa " if that is what they wanted, it's OK by me."


" ba abunda suke soba, ke meye naki raayin? Zanfi farin ciki, ace ke kikayi accepting dina da kanki, ba wai under  pressure from you're parent ba."


" I accept. " ta fada tana kara sunkuyar da kanta.


Farin ciki wurin suraj baa magana. " Alhamdulillah, in sha Allah bazaki taba yin dana Sani,da zamowa ta miji, kuma uban yayanki ba. Zan baki farin ciki, iyakar iyawata, In sha Allah. Na gode sosai da kika bani dama in shigo rayuwarki."


Hira sukeyi cikin natsuwa, duk da yawancin maganar shi yake bata labarin daya dangan ce shi, da family dinshi. Yaji dadin yadda ta fara sakin jikinta dashi, duk da ya lura tana da kunya sosai,. Yau ma kamar yafi na ko yaushe.


Shigowar motar Alhaji Munir, yasa gaba daya hamkalinsu ya koma kansa. Mikewa yayi. " bari in je in kwashi gaisuwa." Ya fada yana nufar motar Alhaji Munir. Da driver ke kokarin bude masa Kofa. Tun shigowarsu ya lura dasu.


Sallama ya masa, tare da kokarin durkusawa don gaisheshi. Da sauri Alhaji Munir ya tareshi, tare da mika masa hannu. Cikin jin kunya, da nauyinsa ya mika masa nashi, sukayi MusaBaha.

Suraj yaji dadin yadda Alhaji Munir ya tarbeshi,cikin mutunci. Duk da haduwarsu ke nan ta farko ba,. Already sun San juna, sun sha haduwa a maban- banta wurare.

Ajiyar zuciya hubby ta sauke, lokacin da suraj ya isa wurin daddynta. Sai yau ta kare masa kallo. Tabbas bashi da makusa, ya hadu. Sai dai tasan bai kama kafar Yusuf dinta ba. 

" madam bari in kama hanyar kauyen mu." Suraj ya fada yana murmushi.


Tashi tayi ta rakoshi har jikin mota. Tare da masa fatan sauka lafiya. Har ta  juya zata tafi. " ji mana." Ya fada yana bude kofar motar. Dawowa tayi ta tsaya.


Wata hadaddiyar leader ya mika mata " please ba don ni ba, don Allah ki yi anfani da ita, bana jin dadin rashin waya a hannunki, ko ba komai zanji muryarki, wani abun ma zakifi sake jiki, ki min magana. Next week Saturday in sha Allah parents dina zasu zo."


Gadiya ta mishi, da alkawarin zatayi anfani da ita kamar yadda ya bukata. cike da farin ciki suraj ya bar gidansu hubby.


Sai bayan da ta idar da sallar magrib ta dauki leader din ta nufi dakin mommy Hauwa. A zaune ta sameta tana jan tasbaha. Sai da ta jira ta gama sannan ta mika mata leader din. " meye wannan." Mommy Hauwa ta tambaya

" nima ban Sani ba, shi ya bani." Ta fada kanta a sunkuye.


Kada kai mommy Hauwa tayi tare da bude leader. Kwalin waya ne ta fara cin karo dashi. A hankali ta fito da kwalin ta bude. Ido mummy Hauwa ta zaro, baki a sake tana juya wayar, tare da kara karanta sunan waya.


Goldvish (18 carat white gold & 120carat of vvs---1 graded diamond)


Mommy Hauwa ta kalli hubby da itama idonta na kan wayar. Tana ganin kyawawan waya bata taba ganin wayar data burgeta ba, kamar wannan. Gata yar dai dai, so cute.


" Ummi wannan ai customize phone ne?" Mummy Hauwa ta fada tana juya phone din.


Junaid ne ya shigo da sallama. " evening Anty. " ya fada yana zama kusa da hubby. " evening brother, daga ina?"


" hayders house. "


" aikin ke nan." Hubby ta fada

"Mommy Hajiya na gaisheki, wai ya taji shiru."

" or I totally forget. I call her."


Mommy Hauwa ta kalli hubby, tare da mika mata phone din. " kin tabbatar dai kina son shi ko?" Kai hubby ta sunkuyar cike da jin nauyin mommy Hauwa.


" naso Kwarai Ku dai daita da hassan, amma tunda kin ga bai miki ba, shi kenan, Allah ya musu  zabi na alkhairi."

Junaid ya amsa da " amin."


Shima ya yaba phone din. Leader ya bude wani kwalayen ya fito dashi. Daya smart watch, da yan perfumes ne different colours. Kananan kwalabe masu kyau.

"Woow!!! This is our collection." Junaid ya fada yana murmushi. Mommy da idonta ke kan set din perfume din ta ce " kamar Yaya?"

Sunan ya nuna mata. ( 7 friends for ever collection) sai ainihin sunan turaren caron poivre.


1

" kai junaid ban son karya, yaushe kuka fara kasuwancin da har zaku fara collection na kanku.?" Mommy Hauwa ta fada tana harararsa.


Dariya yayi " da gaske mommy wannan turaren mu mukayi, design dinsu, sannan mu muka zabi ingredients din da muke son a hada mana dashi. Mu muka yi exporting dinsu to Nigeria. Its our oder"


" yaran nan kun fara bani tsoro fah!!" Mommy Hauwa ta fada tana tsare junaid da ido.


Dariya yayi " kar kiji komai mommy. Neman halas dinmu fa muke yi. Kin ga waannan ko wanne da kamshinsa da ban. Its made from expensive ingredients, zakiji dadin su sosai."


Harararsa hubby ta yi " in mommy ta yadda ka dauka nima yadda zanyi. Please stop lieying. Luke at is very care full its expensive perfumes. How do you people have that kind of money to do all this in short time. ?"


Kada kai mommy Hauwa tayi alamar gamsuwa da maganar hubby.


Murmushi junaid yayi. " it's OK. Amma kar Ku manta muna da irin su don Harris da business tycoon Alhaji omer Yusuf zubair, har kwa tambayemu in da muka samo manyan kudi?"


" haka nefa!!!." Mummy Hauwa ta fada tana kallonsa.


" dama na shigo in gaya muku amaryata ta iso." Ya fada yana murmushi


" Amarya kuma?" Hubby ta tambaya


"Mai kafa hudu ba." Ya fada yana dariya ganin kallon da mommy Hauwa ta masa.


Murmushi suka yi tare da masa Allah ya sanya alkhairi. Tare suka fito compound din. A jikin motar suka samu jafar da jabir, suma suna kallon new car din kanin nasu.


Cike da mamaki  mommy Hauwa ta ke bin motar dake gabanta da kallo


2008 BMW 7 Series.


" masha Allah brother, mota tayi kyau, Allah ya sa alkhairi, ya sa daka da alkhairin dake tattate da ita, ya kare ka daga sharrin dake tattare da ita." Su jafar suka fada, suna rungume dan uwan nasu, cikin farin ciki.


" ameen, na gode." Ya fada yana murmushin jin dadi.


Su mommy Hauwa ma sun tayashi murna da addua. Duk da zuciyarta na cike da tambayoyi.


" yarona fah?!" Mommy Hauwa ta tambaya


" power bike, da safe ya ce min zaizo ya nuna miki, da tare zamu taho, Alhaji babba ya kirashi."


Tabe baki hubby ta yi

" Allah ya kyauta, banda shirmen hayder me zaiyi da power bike." Mommy Hauwa ta fada


" ra ayi." Jafar ya fada yana dariya


"Sai kin ga power bike din yayi kyau sosai." In ji Junaid

" mako dai!!! Me mutun zaiyi da wani mashin in ba mako ba." Hubby ta fada tana hararar junaid


Ido ya zaro " kin San kudin bike din nan, kike cewa mako? Yafi kudin motar nan da kike gani nesa ba kusa ba."


Dariya hubby tayi " Haba yaro karka raina min hankali mana."


Kallon jabir junaid yayi " gaya mata brother. "


" is true bike akwai masu tsada sosai, duk da bansan irin wanda ya siya ba, amma zai iya kasan cewa yafi motar tsada." Jafar ya fada


"Aprilla ( Italian motorcycle brand )"

daga jafar har jabir kallon junaid suka yi cike da mamaki. " wow!!! Har kasa na kosa inga bike dinnan, kwanan nan friends dina na musu  tsakanin aprillia da kasawaki."

Murmushi junaid yayi " zakuwa ka ganshi yayi kyau sosai,"


Mommy Hauwa dake saurarensu murmushi tayi " ina ruwan yarona, komai nashi daban."


Jabir ne ya amsa da " I love the boy, he have a taste, komai nashi unique. Kam"


" gobe zaa bani Amarya in dana." Hubby ta fada


Murmushi junaid yayi, tare da amsar key din a hannun jafar ya mika mata.  " it all yours sis."


" thanks u are the best. " ido su jafar suka zaro cikin wasa " what about us." Dariya su hubby suka yi

" jealousy. " junaid ya fada yana dariya


" I love u all. " hubby ta fada tana shigewa ciki da gudu, kamar wata karamar yarinya.


Da kallo suka bita. Mommy Hauwa ta kada kai " Allah ka shirya, naga ranar da Ummi zata San ta girma."


Murmushi dukan su suka yi cike da son yayar tasu..........

Baka jin komai sai karar cukula da plate.+


Mommy Hauwa ta kalli Alhaji Munir. " sai ga yaronka da zukekiyar mota."


Murmushi Alhaji Munir yayi " na ganta Allah ya sa albarka."


Ajiye spoon dinta tayi " haka ma zaka ce? nifa abun ya fara bani tsoro, har yaushe suka fara business din, da zasu samu manyan kudi haka?"


Murmushi still Alhaji Munir yayi " ki kwantar da hankalinki. Shi kasuwanci sirrine, kashi casa'in na arziki yana kasuwanci. In Allah ya sa maka albarka sai kiga cikin lokaci kadan ka zama wani Abu. Kamar yadda suka fara nasu cikin nasara. Shekara uku da wani abu, ai ba yanzu bane."


" ehhhmm!! Haka dai kace."


Junaid Alhaji Munir ya kalla " kai baka mata bayanin kasuwanci naku bane?"


" na gaya mata, kawai bata yadda bane."


Alhaji Munir ya kalli mommy Hauwa "duk abun da suke yi is under our watch."


" shi kenan ai!!! Allah yasa albarka."


"Amen "  suka fada baki daya. A nan Alhaji Munir ke shaida musu za a je tambayar auren jafar, yana son nan da 5month a hada dana hubby gaba daya.


Kallon jabir mommy Hauwa tayi " kayi kokari nan da lokacin ka fito da taka a hada in huta. Don na kosa in dinga ganin yan dagwai dagwai a gidan nan."


Dariya suka yi gaba daya, banda jabir dake faman Sosa keya, yana murmushi kasa kasa. " tu kunna dai mommy. "


" ba wani tukunna, ni da zaka bani zabi dana hada ka da kawar amir, Zainab. Yarinyar akwai hankali da natsuwa. Ina son yarinyar. Don haka nake fatan ko kai ko junaid ya auro min ita."


" lala!!! Ban dani." Junaid ya fada yana dariya


" nima aa!" Jabir ya fada


Alhaji Munir ya kalli mommy Hauwa " wai ke me yasa bakya son zaman lafiya ne? Ki barmin yara su zabi abinda suke so."


" ai shi kenan, Allah baku hakuri." Ta fada tana yamutsa fuska


Dariya hubby keyi kasa kasa. Ita ta rasa wannan son hada zumunci na mommy. Gashi duka are in vain.


Harara mommy Hauwa ta maka mata. Ba shiri ta Mike ta nufi dakinta, kafin mommy ta kai mata mangara, bayan ba ita takar zomon ba.


               ***********"*******


"Lafiya meya samu kafar?" Ummu khulsum ta fada tana zama kusa da hubby.


Hubby da ta cika tayi tam. Don bata kaunar ko kwarzane a jikinta. Ta nunama ummu khulsum in data kuje har yayi jini kadan. " subhanallahi garin Yaya?" Tsaki hubby ta yi " wannan dan banzan yaron ne, ya so yabi ta kaina da gwangwanin banza mashin dinsa."


Baki ummu khulsum ta rike. " kar ki gayamin har yanzu kina nan kuna shirmenku."


" bar miskilin banza, sai na masa dukan kawo wuka, tukun na zai shiga hankalinsa dani, in farfasa gwangwanin banza kowa ya huta."


Ummul khair dake shigowa ta fashe da dariya, jin hubby na maganar yima hayder duka. Itama ummu khulsum dariyar tayi.


" gaskiya kam, don ya gama raina ki, wata kila in kin nuna masa tsohon kashi ya shiga hankalinsa." Ummu khulsum ta fada tana dariya


" kai uhtee!! Wannan ai zuga ne! Ina hubby ina hayder? Loma biyu kawai zai yi da ke, ko in ce hadiya daya. Ki daina shiga harkarsa kawai. Don yanzu kosu Yaya Ahmad ai basa ce zasu bugeshi ba, balle ke mace." Ummul khair ta fada


" laifinta ne ai, yayi ta hon taki matsawa, da ba dan na janyeta ba da ya karairayata, yadda ya taho da gudun nan." Ummu sulaim ta fada tana shigowa da fist aid a hannunta.


Harararta hubby ta yi cikin fushi, da jin haushin maganarta " duk filin compound din nan ya rasa inda zai bi sai ta inda nake tsaye?"


" Allah ya shiryeku, ke son girma shi son girma da raini. Sai kuyi tayi, wanda ya gaji ya sake." Ummu khulsum ta fada


Zama ummu sulaim ta yi ta na ma hubby dressing din inda ta kuje.


" daga yau da dorinata zan dinga zuwa gidan nan. Don ni bazan dauki rainin hankali ba. Dukan tsiya zan masa ko ya shiga hankalinsa. Don yaga yayi tsawon kafa, bashi zai bashi lasisin raina na gaba dashi ba. Don duk ta gina ne bata shigaba. Agric chicken kawai."


Dariya sukayi gaba daya, banda hubby dake cika tana batsewa.


Ummu sulaim ta ce " ke yanzu ko cewa akayi ki bugeshi sai ki buga?"


Harararta hubby tayi " mai zai hana. Ki zuba ido ki gani, ya sake shiga gonata kiga yadda zamu kwashe."


Hayder ne ya shigo da sallamarsa, wucewa dakinsa yayi ba tare daya ko kallesu ba.


" tabdijamm!!! Anty khulsum bai fa gaishe kiba, ya wuce."


Murmushi tayi tana kallon hubby " ina zai gaisheni, bayan yanzu gani yake shine gaba damu, ya kwace girman Hajiya kuma ta goya masa baya."


" tabdijamm!!! Allah ya ragewa aya zaki, da anyi karamin yakin badar a gidan nan." Hubby ta fada


Ummul khair dariya tayi " ba abunda zakiyi ko ke din ce,. Don Hajiya ta daure masa kafa, harda wani shine uba, kuma yaya a garemu. Can u imagine, ke hatta su Yaya Ahmad shakkarsa suke. Don wani abun in yanayi har mamaki yake bani. Karfi da yaji ya kwace girman ya dora ma kansa."


Tabe baki hubby tayi " Ku kuka so, wallahi."


Hayder ne ya fito da niyyar fita. Hubby ta mike ta tareshi " dutse halan ka taka dasu ko? Kasan Allah duk randa ka kuskura ka kara aunani da gwangwanin  mashin dinka, sai jikinka ya gaya maka, sannan in fasa gwangwanin banza kowa ya huta." Kallon up and dawn ya mata tare da tabe baki ya bi ta gefenta ya wuce abinsa.


" miskilin banza, dani kake zan cen." Ta fada tana zama. Su ummu sulaim kam dariya hubby ta ba su yadda ta dage adole tana masifa.


Hirar zumunci, da na shirye shiryen biki suka kafa. Duk da already an gama duk kan wani shiri daya da ce. Lokacin bikin duka duka saura 10days.


             *********************


" kayi hakuri, kafi kowa sanin halin mahaifinka, wajen kafiya, munyi iya kar kokarinmu amma abun ya ci tura. Don haka ka daure ka amince da zabin sa shine zaman lafiyarka. Don ban taba ganin bacin ran Yaya ba irin wannan karon, har cewa yayi nida hajiyanka mune masu daure maka kafa, shiyasa kake son bujirewa zabinsa."


Cikin tashin hankali, suraj ya zo ya tsugunna a gabanta. " nasan kinyi kokari, amma sanin kanki ne ke kadai zaki iya sakko da daddy kan raayinsa. Na amince muddin ya yarda na auri zabin raina, zan auri doctor ita ma. Ko don in faranta masa rai."


Kada kai Anty tayi " ka kasa ganewa ne kawai. Amma wannan karon is different da sauran time din. Kafi kowa sanin mahaifinka ba zai aminta da auren bazawara ba, after all ba wani ilmi tayi mai zurfi ba. Sannan babban matsalan status din is far different."


Suraj da yake cike da tashin hankali da damuwa. Idon nan ya kada yayi jawur, shi kansa ya manta rabon da yasamu natsatsuwa da isashshen bacci. tun kan yakai maganar hubby gaban mahaifin nasa.


" wannan ba hujja bace Anty. Musulunci ya ce mu auri mata don kyanta, ko don kudinta, ko nasabarta, amma sai aka horemu da auren maabociyar addini. Me yasa  Ba a ce mu zabi maabociya dukiya da nasaba ba? Saboda wannan iyakarsa gidan duniya. Bazawara kuma, kun manta manzo SAW ma da bazawara ya fara. Kinga kenan nima nayi koyi dashi, meye aibu a nan?"


" ba aibu, suraj. Amma kasan halin mahaifinka fiye da kowa. Gobe in sha Allah zan je in sameshi, ka cigaba da addua, don ita ce kawai mafitarmu a yanzu."


Duk da tashin hankalin da yake ciki, bai hana bayyanuwar murmushi a fuskarsa ba, don duk cikin dangin mahaifin nasa ba wadda yake saurarawa sama da kanwartashi. In ya tuke ita kadai ke iya lallabashi.


" na gode Anty Allah ya biyaki da gidan aljannah. "


Murmushi tayi, tana mai fatan nasara. Zuciyarta cike da tausayin suraj, don ta tabbatar yayi nisa a son hubby.


               *****************

shakuwa ce ta shiga tsakanin hubby da suraj, don yanzu takan sake dashi a waya, susha hirarsu. Suraj mutun ne mai saurin sabo, ga ban dariya some times,. Satin daya yi alkawarin zuwan family nashi, basu samu zuwa ba, saboda uncle dinsa da ragamar tafiyar ke hannunsa baya kasar. So sai aka daga zuwa next week. Yanzu haka kwana uku kacal ya rage.


              ********************


Zaune yake a gaban mahaifin nasa. Kansa a kasa, zuciyarsa na faman bugu, don ya tabbatar yau zai samu duk kan amsarsa, in ma nasara da akasinta. Jikinsa yayi sanyi sosai ganin fuskar mahaifinsa daba wani annuri a tattare da ita. Sai dai duk da haka bazai yi saurin karaya ba.


Kallon da mahaifin nasa ya masa, yasa hantar cikinsa kadawa.


Gyara zama Alhaji saad kangiwa yayi. Cikin dakakkiyar murya  wadda ba wasa ko wargi a cikinta ya ce " na samu sakonka, sai dai ka sani ban lamuta ba, bazan taba yadda ka auro min yar talakawa ba," da sauri suraj ya dago yana kallon mahaifin nashi baki na rawa " Allah daddy babanta nada arziki dai dai gwargwado." Bai karasaba Alhaji saad kangiwa ya tareshi " rufa min baki, mutumin banza. Waye Alhaji omer Oregon, ballantana shi? Ina yaron sane? Me na sama ya ci balle na kasan?. Na gama magana, yanzu haka yan aike sun dade da isar da sakona ga iyayenta. Don haka kar koda wasa inji ance an sake ganinka tare da yarinyarsu. Bakai ba ita. Sannan maganar aurenka da doctor nan da sati mai zuwa, ya rage naka kaje Ku tsara yadda abubuwan zasu kasance ko kar kaje, ba fashi. Don na lura da take yakenka in na ci gaba da zuba maka ido, mutuncina zaka zubar."


Fadin tashin hankalin da suraj ya shiga a lokacin bazai faduba. Gaba daya jinsa yake kamar a sama yana plotting. Ga kirjinsa da ya masa nauyi kamar an daura dutse. Kallon mahaifin nasa yake. Gani yake kamar an canza masa shi. Mahaifinsa mai matukar son sa, da son farin cikinsa, yau shine da kansa yake son fatali da duk wani farin ciki na rayuwarsa. Don rabuwa da hubby tamkar rabuwa da wani bari na jikinsa ne.

" tashi ka ban wuri, kar ka manta nasa matakan tsaro a kanka, koda wasa ka kuskura kayi gigin tsallake umurnina, tamuce ni dakai."


Da kyar ya kawo kansa part din hajiyansa. Rungumeta yayi, ya saki kuka kamar wani karamin yaro.


Tasan dama zaayi haka, don daga kanta aka fara, Tausayin tilon yaron nata ne cike da ranta. Taso Kwarai  mahaifin ya masa adalci ya auresu gaba daya, amma yaki. saboda wani ra'ayi Mara tushe balle makama.


Lallashin suraj ta yi, tare da nuna masa muhimmancin biyayya ga iyaye, sannan ta kwantar masa da hankalin in har hubby rabonsa ce, to ba makawa sai ya aureta, in kuwa ba rabonsa bace to no matter how baza ka sameta ba. " I promise u, in har ka kwantar da hankalinka, bayan aurenka da doctor, zanyi iya yina in ga ya barka ka auri zabin ranka kaima. Amma hakan bazai samu ba, sai ka natsu ka nuna masa kayi naam da zabin sa."

Kallon hajiyansa yayi, da jajayen idonsa da suka kara kan kan cewa. " kina ganin baza suyi kokarin aurad da ita ba, kafin lokacin?"


Ajiyar zuciya tayi " shiyasa na ce ka dage da adduar ai. Sai kaga komai yazo da sauki."


" shikenan. Amma tayaya zan tari Habiba da wannan maganar? Dama da yaya na samu ta saurareni."


" yanzu kam na tabbata bayani ya isa ga iyayenta. Nasan zata nemi Karin bayani daga bakinka, then sai kayi anfani da hikimarku ta maza, ka bata baki, tare da shaida mata matsayarka."


" na tabbata gani zatayi kamar yaudararta zan kuma yi. I can tell her. "


" u have to tell her, this is the right thing."


" I will try." Ya fada in low voice.


                ***********


Zaune suke a falon Alhaji babba, bayan sun sallami bakinsu. Alhaji kawu ne ya kalli Alhaji babba, fuskarsa cike da bacin rai da damuwa

Zai yi magana, Alhaji babba ya katseshi.

" kar kace komai. Nasan abun da ciwo. Amma karka manta kullun cikin yima yaranmu addua ta gari mukeyi, mu dauka hakan wani alkhairi ne a garesu baki daya. Sannan ina neman alfarma kamar yadda na nema a baya, in har Habiba bata da wani tsayayye to ina son a hada da Abdul majid ko abdul Karim, kamar yadda na bukata a baya."


Ajiyar zuciya Alhaji kawu yayi, tare da kai kallonsa kan Alhaji Jamil, da abokan Alhaji Munir su biyu, sai Alhaji Jamal, da abokan shi kansa Alhaji kawu su biyu dake falon. Ya maida kansa kan Alhaji babba.


" bamu bukatar sake mai maita wannan kuskuren. Don haka koma da wanne ne a ciki na amince. Zuriata da zuriarku tamkar Abu daya ne, ko da dana bukaci a bata dama, ganin ita a yanzu bazawarace musulunci ya bata damar zabar abokin rayuwarta. Sai dai yanzu iya sanina duk masu son nata matasa ne, marasa aure, bana son a maimaita yar gidan jiya. daya ne mai iyali, shi kuma akwai dalili daya dazai hana in bashi auren Habiba. Dama mun so a hada dana dan uwanta,."


Murmushi Alhaji babba yayi irin na jin dadi. " alhamdulillah wannan Abu ya min dadi. Ban son ko kadan Habiba ta fita daga zuria ta. Shiyasa tun farko na bukaci ka yarje min in hada ta da daya daga cikin jikokina. Don haka ba fashi, nan da lokacin da akasa auren, muna fatan su samu fahimtar juna."


Duka yan falon addua sukayi da fatan alkhairi.

Taro ya watse kowa na cikin farin ciki da annashuwa, kamar ba wani abun bacin rai daya faru.


Abokan Alhaji Munir suka fara masa bayanin abunda ya faru, kafin ya koma gida, Alhaji kawu ma ya mayar masa da yadda abubuwan suka kasance. Ran Alhaji Munir ya baci sosai.  Addua yayi Allah yasa haka ya zama mafi alkhairi garesu baki daya.


So koda ya koma gida mommy Hauwa kawai yama bayani, sannan ya bukaci datayi shiru tukun na, har suji daga bakin Alhaji Jamal kan wanda zaa hada dashi. Mommy Hauwa bata ji dadin wannan lamari ba, duk da dama ta dade da hasaso hakan. Don wata aminiyarta ta shaida mata akwai yar abokin kangiwa da akeson a hadasu tun shekaru biyu da suka wuce, ya ki. So ta dauka maganar ta wuce ne,ko kuma sun hakura tunda shi ya nuna baya so. Fatan alkhairi tama yarta da kudurce kara dukufa da yi mata adduar zabin nagari........Yau ne Alhaji Jamal ya Tara iyalansa, da yaransa maza. Ahmad, Abdul Karim da hayder. Abdul fatta bai samu zuwa ba, saboda yanayin aikinsa.+

Alhaji Jamal ya kalli iyalan nasa bayan ya tabbatar da duk hankalinsu na tare dashi, don jin abun da yasa ya tarasu.


" ina son tsakanin Abdul Karim da Abdul fatta daya daga cikin su, ya auri Habiba don maye gurbin dan uwansa, bai kamata ina da samari a gida ba ace nabar irin wannan natsatstsiyar yarinyar ta fita daga zuriata. Don haka na tara mu a nan don muyi shawarar wanda ya dace ya maye makwafin marigayi a cikin su biyun nan."


Kallon kallo aka fara tsakanin matan, su Ahmad dai Kansu na kasa. Mmn Yusuf ce tayi karaf ta cafke da " Abdul Karim din dai, don wannan karon bazan taba yadda amin abinda aka min wancan karon ba."


Da ido Alhaji Jamal ya tsareta " ko zaki gayamin abinda kike ikirarin an mikin?"


Cikin jin haushi ta ce " in maye ya manta, ai uwar diya bazata manta ba. Wan can karon naji Yusuf da kansa yaki nafisa, ka daure masa kafa, to a wannan karon an samu akasi, don Abdul fatta da kansa ya bani damar zaba masa mata, kuma na zabo masa, har sun aminta da juna. Don haka abi wani sarkin ba dai yayana ba."


Still idon Alhaji Jamal a kam Mmn Yusuf. " Allah ko? Duk da yaushe akayi hakan bani da labari?" Ya tambaya


Shiru tayi tana dan ture turen baki.

Numfashi ya ja " gidana ne, yaya nane, nike da ikon kafa doka a gidan nan kuma dole abi. Don haka ki bini a hankali"


Hajiya ce ta amshe da " aa gaskiya ta fada, kamar yadda kake da iko da Abdul itama tana dashi, a matsayinta na uwa. Ya kamata a mata uzuri, tunda ya samu mata, ba matsala Allah ya sanya alkhairi yasa ayi damu."


Harara Mmn Yusuf ta dallawa Hajiya, murmushi Hajiya tayi. Don bata manta gashin kuman da sukawa hubby a wan can karon ba, bata fatan ta kuma kasan cewa a kalkashinsu kuma. Ita hakan ma dadi ya mata.


Alhaji Jamal ya maida kallonsa ga Abdul Karim da ke zaune gefensa, kansa a kasa. " to Abdul Karim magana ta dawo gareka, ya kake gani? Zaka iya cika min wannan burin nawa ko kai ma ka samu wadda kake so?.'"


Shirune ya biyo baya, kowa idonsa na kan Abdul Karim, yana jiran yaji mai zai fada.


Mmn Yusuf ce ta katse shirun da " a bashi lokaci yayi tunani ai ko?"


Harararta Alhaji Jamal yayi, dauke idonta tayi tana fadin " Allah baku hakuri da ga fadar gaskiya."


Mmn samira da tun da suka zauna sai yanzu ta yi magana. " ka bashi lokaci yayi nazari tukunna."


Da tsananin mamaki Hajiya tabi Mmn samira da kallo. Bata taba tunanin ko a mafarki Mmn samira zata samu second true akan hada Habiba da daya daga cikin yaranta ba. Ganin yadda suke zaune kai a hade, sama da shekara talatin. Kin yadda su hada ido Mmn samira ta yi, duk yadda Hajiya taso su hada idon.


" zan cen banza, ba maganar shawara a ko aa, kawai nake son ji." Alhaji Jamal ya fada, don shma jikinsa ya fara sanyi da lamarin iyalan nasa.


" ka bashi lokacin kamar yadda suka bukata, sai dai ina son Ku Sani Habiba, bawai ta rasa manema bane, so karkuyi tunanin wai kunyi favoring dinta ne." Hajiya ta fada

Dariya Mmn Yusuf tayi " munga alama ai.?" Ta fada cikin gatse.


" ya isa haka!! Ban kiraku don Ku daga min hankali ba, don Ku baa taba abun arziki daku. Kaje na baka nan da rana ita yau, ina jiran amsa daga gareka, sai dai karku manta baku kadai bane yayana, in Ku kunki min wannan alfarma akwai masu bukata ido rufe, sai dai an ce so so ne amma son kai yafi. Ku tashi Ku tafi."


So ko a cikin gida, gaba daya Mmn samira daukewa Hajiya wuta tayi, ganin haka Hajiya ta fita a hanyarta. Sai dai mamakin Mmn samira har yanzu bai barta ba. Ita kam ko a jikinta, don ta tabbata koda Abdul Karim ko bashi hubby bazata rasa mijin aure ba. Da badon yadda take kin sauraran masu sonta ba da tun tuni ta dade a gidan mijinta. Addua da fatan alkhairi ta bi lamarin dashi, sannan ta sata cikin adduainta na musamman.


                *******************

Koda suraj ya kira hubby ya mata bayani, don ya tabbatar bata da labarin abinda ke faruwa. Bata wani nuna masa damuwarta ba, duk da deep down she is broken. Ba wai tana son shi bane, aa, amma shine mutun na biyu data bashi damar shiga cikin rayuwarta.

Tattara komai tayi ta ajiye a gefe, don dama bawai auren bane a gabanta. Ta wani fanninma dadi taji, don ta dan Shana kafin su kara bijiro mata da wani zan cen aure."


Su ummu sulaim da sauran friends dinta suma abin bai musu dadi ba, amma suka bita da fatan alkhairi.


             *****************

Abdul Karim Jamal Yusuf zubair Oregon. Kani ga Ahamad, Shi ke binshi a dakinsu. Ya yi degree dinsa na farko Dana biyu a Malaysia, in da ya karanta architecture yanzu haka yana aiki da ministry of works abuja. Yana da rufin asiri dai dai kwargwado  Kyakyawa ne,  duk gidan in ka dauke Yusuf da hayder to ba ya shi.  Dan gayune na karshen zamani, cikakken womanizer, amma a boye yake alamuransa. Sai sigari da yake busawa time to time, wannan kam kowa ya San dashi. Yana son wayayyar mace mai ilmi, don duk yan matan da yake muamala dasu wayayyune, wanda ilmi da kudi suka zaunama. Burinshi duk in da matarsa ta fita a San yes ya iya zabe, ya kere sauran maza.


Hubby no way!!! She is alliterate, sannan bata waye ba ko kadan, ba irin Matar da yake muradin ajiyewa a gidanshi bace. Yasan she is beautiful and wealthy, amma shi is not his type.

 

            *******************

Hidima ake ba kama hannun yaro. Yau gidan kamar an yashe, duk suna wurin lunching. daga iyayen amare sai  tsoffi da suke ganin wurin ba wurin zuwansu bane. 

Hajiya ce sai manyan aminanta biyu, Hajiya Balkisu da Hajiya Fatima. Suna zaune a falon hajiyar ana hirar duniya. Daga can suka fara jiyo magan ganu na tashi daga tsakar gidan da ya hada part dinsu.


" lafiya kuwa?" Hajiya Fatima ta fada tana kallon kafar falon.


" muryar Hajiya kaka ne, Allah yasa lafiya." Hajiya ta fada tana mikewa don ta gano abinda ke faruwa. Kafin ma ta isaga fita Hajiya kaka da kanwar Mmn samira, Hafsat suka iso bakin kofar Hajiya.


" ina kike, yar ayi ba yar a rababa. Dama tun da naga kina shishshigewa yarinya nasan kin kulla tuggun cuta. Ita kuma da yake sakarya ce, Mara tunani take biye miki, kina cutarta. To wallahi bazata sabuba. Bazan taba yadda da wannan hadin cutar ba eheee!!!." Gaba daya su Hajiya suka fito don jin ba'asin zance.


" lafiya dai ko Hajiya? " Hajiya Balkisu ta tambaya, don bata gane kan maganganun da Hajiya kaka ke fada ba.


" ina fa lafiya, ana son cutata, a cuci zuriata. Ta ya zaa dauki second hand a ba jikana, babban abun ma Mara haihuwa? Yarinyar da shekara kusan hudu ko batan wata bata taba ba, har mijin ya koma ga Allah baiga kwansa ba, saboda an asirce shi, an hanashi auro wadda zata Haifa  masa yaya. Shine ni ake son a lallaba a cuci jikana ko? To wallahi bazai taba yiyuwa ba, matukar ina raye. Ni da nake fatan ganin yayan jika zaa min sagegeduwa don rashin imani."

" Haba hajiya!! Ba girmanki bane, koma menene, ki bari a warwareshi a tsanake, be kamata kina daga murya haka ba, kefa babbace." Hajiya Fatima ta fada cikin murya mai taushi, ganin yadda Hajiya kaka ta hakikance tana zuba ruwan balai, ga bakinta sai kunfa yake fitarwa.


Hafsa ce ta amshe da "haka dama ake fakewa da cin girma a cuci mutun. Ai gaskiyar Hajiya kaka ne, tana son yadda ta mallake yaya Amina, sai abunda ta ce, ta mallake mata dan da take ji dashi. Gara tun wuri ki sake lale, a nemi wani sarkin."


" ni kike gayawa wannan maganar? Ki Sani in Hajiya kaka ta fada na kyale, ke kam gidanku zanci, har kina da bakin da zaki gayamin zan cen banza? Ina abun yake?" Hajiya ta fada cikin fushi da bacin rai


Yan uwan Mmn Yusuf dake tsaye suna kallon ikon Allah.


Innani ta ce " meye laifin Hajiya a wannan magana? Sai ki jira Alhaji Jamal shida yake son hadawar kuyi dashi. Amma gaskiya wannan ba dai dai bane.


Agi ta harari innani " zancen banza kenan!!! Ai maganar Hajiya kaka a kan hanya take. Karki yarda haka ina ji ina gani, jikana har ya koma ga Allah banga kwansa ba, baya ga mallakeminshi da akayi, baya ganin kowa da gashi in ba su ba. Me ake da wannan hadi? Ko cuta? "


" ta ina zan yadda da wannan danyan hukunci? Shima Abdul Karim din ya ce bai so, don haka babu dole. A kara gaba, a sakarma jikana mara yayi fitsari, kar inji kar in gani, in fa ana son zama lafiya."


" wai gaya muku a kayi neman kai ake da ita ne da kuka, ishi jamaa da tashin hankali? Yau ya ce baya so, dubunsa nanan na jira. Meyayi zafi? Ko an ce dama dole sai jikanki ya aureta, sannan zata ci gaba da rayuwa.? Hajiya Balkisu ta fada rai a bace.


" ya dai rage naku, in gaskiya ake son kullawa, ba cuta ba, ai itama ta haifi namijin, shi ya aureta mana. Amma da yake ba Allah a ciki, zaa cuci dan kishiya." Hafsat ta fada tana barin wurin.


" aiko fadi ki kara, na haifi da daya tamkar da dubu, ke kanki kinsan hakan." Hajiya ta fada


Ido Hajiya kaka ta zaro " to in kin cika yar halas, cikin Uwale da ubale, shi ya aureta. Amma ba jikana ba."


Murmushi agi tayi " gaskiyarki Hajiya kaka tunda Allah ya raba yaba kowa, kinga tuwona maina kenan. Kai wannan abu yayi kyau." Ta fada cikin izgili


Iska Hajiya ta busar daga bakinta, ta sauke ajiyar zuciya, ta dade rabon ranta ya baci irin na yau. Murmushi tayi.


" na gode da shawararki, in sha Allah gobe iwar haka Habiba ta zama mallakin Aliyu hayder, zan nuna miki tabbas nidin yar halasce,. In kin cika ki nemowa jikan naki wadda tafi Habiba a gobe."


" gasu nan kamar jamfa a Jos, takin ce dai baa so. Tunda kun janye falillahil hamdu, aniya bi aniya. " ta fada ta juya ta nufi part din yar tata tana faman surutai.


                    ****************

Sanye take da ankon cotton material milk sai design dark blue, dinkin riga da skert 8picess yasha adon dark blue less da yazo da material din. Dinkin ya zauna das a jikinta, tasha make-up yau kan make-up sosai ta tsaya aka mata, ga daurin head irin wanda ake yayi, gashinta da yasha gyara ya fito sosai yayi tim a bayanta. Karamin gyale ne, Mara nauyi dark blue da takalmi da jaka to match. Tayi mugun kyau, kai kace ita ce amaryar. Kana ganinta kasan tana cikin farin ciki, ga abokansu da sukayi secondary tare sunzo, sai kashe selfie suke ana shafta baka jin komai sai karar sautin DJ da dariyarsu


Kasan cewar wurin duka mata ne, yasa hubby sake jikinta.

Daga inda suke tsaye da Anty samira yana iya hango hall din, da jamaar dake ciki. Tun yana fahimtar abinda Anty samira ke fada har ya daina jinta. Gaba daya hankalinsa ya koma kan wata hadaddiyar yarinya da yake hangowa daga inda yake tsaye. Ba abunda ya kara tafiya dashi irin dirin jikinta unique, kamar murmushinta da dariyarta. Gaba daya wani irin yanayi ya tshinci kansa a ciki, mai wuyar fassarawa. Ya hadu da mata iri iri, yayi muamala dasu, amma bai taba cin karo da irin abunda idonsa ke hango masa ba. Ba abunda ya kara tayar masa da hankali, irin lokacin data tashi ta nufi wani table din dake kusa da inda take zaune. Takunta da yadda jikinta ke juyawa. Ajiyar zuciya tare da wani nishi gaba daya ya sauke lokaci guda. Da sauri samira ta kalleshi. Rufin asirinsa yana sanye da dark glass a idonsa. Da ta gama dagoshi.


" lafiya ahehh!!! Ina magana kayi min Shiru?"


Kanshi ya shafa, yana kokarin saita natsuwarsa. " ba damuwa in kin dawo ma karasa maganar, I have to go. " ya fada cikin rawar murya


" are u OK?" Ta tambaya tana tsareshi da ido, ganin yadda ya koma lokaci daya.


"I'm OK."

" shi kenan sai mun hadu a house, ka kwantar da hankalinka, komai na hannun Hajiya kaka, nasan she will handle it."


" thanks sis, shi yasa nake sonki da yawa."


Dariya tayi cike da jin dadi. " in dai ina raye ba mai makala maka abinda baka so."


" thanks " ya fada yana murmushi. Cikin dabara ya daddauki picture din yarinyar da gaba daya ta tafi da imaninsa.

Har Anty samira ta juya zata tafi, ya kirata, yarinyar ya nuna mata " waccan fah, gani nake kamar na santa, a wani wuri.?" Kallonta takai kan yarinyar, sannan ta kalleshi. Ganin ba wani alama a tattare dashi, he ask normal yasa ta tabe baki tare da Jan tsaki. " habiban da ake son manna maka ce, kasan bawai kwalliya take yi ba, kullun tana lullube kamar Matar liman, shi yasa ba lallai ka ganeta ba."


" what." Ya fada da karfi. Ganin hankalin Anty samira ya dawo kansa tana masa kallon tuhuma, ya dan wayance. " good for her. Ni na wuce." Ya fada cikin basarwa.

Da ido ta bishi har ya fice a wurin. Allah yasa ba sonta ya fara ba, don ta lura da canjin yanayinsa. Musamman yazo don su tattauna hanyar da ya dace yabi ya kubucewa auren hubby, amma gashi ko gama maganar basuyi ba ya kawo excuse, ya tafi. Bari zasu hadu a gida koma menene taji. Allah ma yasa Hajiya kaka ta aiwatar da abunda ta ce zata aiwatar, A wuce wurin. 

Tafiya yake, amma gaba daya hankalinsa da tunaninsa yana kan hubby. Tabbas yaso ya cuci kanshi, bai taba tunanin haka yarinyar take ba. Wannan ai irinsu ne ake kira matan Niima. Murmushi yayi yana shafa tattausar sumar kansa. Tabbas yayi mata, ta nunawa saa, irin Matar da ko a mafarki bai yi zaton zai ci karo da ita ba. A tunaninshi is just fairy Tell ne kawai. But its real.


Yanzu kam baiga wanda zai hanashi auren hubby ba. Sauri yake ya isa gida, don ya samu su tattauna da Mmn samira da Hajiya kaka, don yasan dukansu are against the marriage.


" Habiba Abdul Karim Jamal Yusuf zubair Oregon " ya fada yana murmushi. ga picture dinta daya bude yana kallo, yaci saa kuwa lokacin tana murmushi, kyawawan hakoranta farare masu dauke da siririyar wushirya sun fito tar, saboda zooming din da yayi lokacin da zai dauka, abinka da babbar waya, kamar yana gabanta ya dauka...........amma gaskiya mutanen nan basu da mutunci. Yanzu duk yadda kuke da Hajiya Amina, da abunda zasu saka miki kenan." Hajiya Fatima ta fada bayan sun koma falon Hajiya.+


Hajiya Balkisu ta karba, bayan ta rike haba irin na mutun yaga abun mamaki. " ai ni kam jikina yayi sanyi, dama an ce baa ba kishiya amana, ko ba dade ko ba jima, sai ta dagaki sama ta nana da kasa, ki ganta sumi sumi, da ita kamar bata yiba. Shiyasa kullun nake gayawa Hajiya ta yi taka tsantsan, amma sai tace ai anzama daya. Mutanen yanzu baka taba sanin zuciyarsu. sai abu ya sameka."

Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke " tun da dama Alhaji yayi maganar nan, na lura da take taken su, amma ban dauka abun yayi zafi haka ba. Ni a tunanina koda Habiba kwantai tayi, ita mai rufamin asiri ce, Ashe ni ban Sani ba, burun burun ake min. Allah na gani alkhairi nake nufin dukkansu dashi, ya rage nasu yanzu."


" to ke da kika ci alwashi, ba tare da dogon nazariba, abun fah da kamar wuya!!! kina ganin hakan zai yiyu?" Hajiya Fatima ta fada

" nima abinda na gani kenan, kin San a girme Habiba ta girma hayder tayaya zakiyi, wannan hadin. Da kin barta kawai baki amsata ba."


Murmushi Hajiya ta yi " she karu ba komai bane face numbers. Hayder dai ni na haifi abuna, in sha Allah ba niba har su sai sunyi alfahari da auren hubby da hayder. Alhaji yaso su da alkhairi sun bujire, ni kam zan amsheshe da hannu bubbiyu. Ko ba komai tuwona maina kamar yadda suka fada. Ina son Habib tamkar yadda nake son yayan cikina,. Kamar yadda duk duniya a yanzu, banda mijina, bani da kamar Hauwa. Nasan kuma in sha Allah hayder yayi mata, irin Matar da nake masa fatan samu, zuwa gaba  in sha Allah zaiyi alfahari da zamowarta mata a gareshi, kamar yadda itama zatayi alfahari da zamowarsa miji gareta."


" Allah yasa albarka ya kade fitina."


"Amin" Hajiya da Hajiya Fatima suka amsa.


" bamuga ta zama ba!!! Auren auta." Hajiya Fatima ta fada tana murmushi


" ba zama kam, yanzu meye abun yi?" Hajiya Balkisu ta tambaya


" eh!!! To!!! Maganar neman gidane zai zama matsala, saboda kurewar lokaci, don so nake a hada bikin gaba daya a wuce wurin. "


" wannan ba matsala bane, yanzun nan zan kira kanin megidana, harkar gine gine, yake yana bada haya. In ji ko akwai available. " Hajiya Balkisu ta fada tana lalubo wayarta.


Murmushi Hajiya Fatima ta yi tare da rike baki " ammafa ya kamata kafin mu fara gudanar da komai, aji ta bakin maza, tukunna."


" haka ne kam, amma dai buga muji maganar gidan, don in sha Allah ba fashi auren nan." Hajiya ta fada tana kallon Hajiya Balkisu.


                ******************

A tare suka sauke ajiyar zuciya, kada kai Alhaji Jamal yayi ya juya zuwa part dinsa.


Hayder da kansa ke faman juyawa, ga wani bugu da zuciyarsa keyi kamar zata faso waje. Bakin ciki, da takaicin magan ganun da  Hajiya kaka ke yi. Wanda duk akan kunnensu shida Alhaji Jamal. Suna tsaye suna magana, suka fara jin hayaniya, da sauri suka nufo part din matan, jin muryar Hajiya kaka yasa Alhaji Jamal Jan birki, ganin haka shima hayder din ya kasa shiga.


Ba abunda ya kara daga hankalin hayder irin furucin Hajiya. " in sha Allah gobe iwar haka Habiba ta zama Matar Aliyu hayder. " me hakan ke nufi? Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, allahumma ajirji fi musibayi wakhlufli khairan minha. Ya furta a saman labbansa. Da kyar yake daga kafarsa, ya nufi part din su Abdul Karim, yayi sa'a ba kowa a dakin. kwanciya yayi dafe da kansa, dake barazanar tarwatsewa. Yana jero adduai a saman labbansa.


Alhaji Jamal na shiga part dinsa ya kira Hajiya Amina (Mmn samira) a wayarsa. Zama yayi Yana huci cike da bacin rai da damuwa.


A hankali ta tako zuwa cikin dakin, daya daga cikin kujerun dake kusa dashi, tama kanta masauki. Tare da gaishe shi. Shiru ya mata ba tare daya amsa gaisuwar tata ba. Ido ya zuba mata, wanda ta kasa jure kallon da yake mata ta maida kallonta gefe. " meke faruwa a gidan.?" Ya jeho mata tambaya


Cikin alamun rashin gaskiya ta kalleshi tare da kauda idonta " ba abinda ke faruwa, ko wani ya fada maka wani abu ya faru ne?." Takaici ne ya cika Alhaji Jamal ganin yadda take son raina masa hankali


" ba gayamin akayi ba, da kunnena naji duk abinda Hajiya kaka ke fada."


Tabe baki tayi " meye laifi to don ta fadi gaskiya?"

Baki sake Alhaji Jamal yabi Mmn samira dashi cikin tsananin mamaki. He can believed Mmn samira ce da kanta.  " kin ban mamaki, ban taba tsammanin haka daga gareki ba, ko don kusancin dake tsakaninki da Hajiya. Sannan da dai nawa ne? Koyana so ko bayaso jibi in sha Allah zaa hada danasu Aisha, kun dade baku daga hankalinku ba."


Wani kallo Mmn samira ta zuba masa, da tun aurensa da ita bata taba masa ko makaman cin saba.


" kamar yadda yake danka, haka zalika yake dana, haka kurun bazan zauna a ci gaba da cutata ba, abin baima tsaya kaina ba, sai an hada da yarana? Abdul da kansa ya ce baya sonta, banga dalilin da za'a masa dole ba, shima a barshi ya zabi abinda yake so kamar sauran yaran. Tayaya za'a jona masa bazawara?, bazawarar ma juya? Sannan a ce kar in yi magana?, ina kallo a cukeni a cuci dana. Naga in da namijin ne itama tana dashi, in gaskiya ne, shi ya aureta man. Za'a zo a kitsa maka abu ka hau ka zauna, Nasan duk ita ce mai wannan kinbibin hadin, don haka ta hada da danta badai dana ba."


Alhaji Jamal mamaki gaba daya ya cika shi. Tabbas abin ya wuce inda yake zatonsa. Mmn samira zai ce tunda ya aureta bata taba daga masa murya ba irin yau. Don haka mamaki da bacin rai yasa ya kafeta da ido.


Kin kallonsa tayi sai data kai inda taso kaiwa sannan ta yi shiru tana huci da huhhura hanci.


" shi Abdul Karim din da bakinsa ya ce miki baya sonta?" Ya tambayeta


" so sai ma, kaima ya kamata kasan baya sonta tun ranar daka taramu a nan. Don da yana sonta nan take zai amsa maka."


Kada kai Alhaji Jamal yayi " shi kenan tashi kije." Haka ta fice a dakin tana faman hura hanci. Da ido ya bita yana mamakin mutanen duniya, Tabbas in da ranka kasha kallo.

Fita yayi, ya nufi gidan Alhaji babba.


                    ****************


So koda Abdul Karim ya iso gida, bai samu shiga wurin Mmn samira ba. Don ya samu compound din gidan cike da abokan Ahmad sai engrn Sahabi da salis. Gefe kadan kuma su Hafiz omer, junaid, amir, alim, da Hafiz ne suma jikin motar amir suna nasu hirar.


Direct wurin su Ahmad ya nufa, bayan bayan ya paka tashi motar. an gaggaisa ya dale motar salis dake kusa data Ahmad in da wasu na jingine a jiki, wasu na kan kujerun roba. Kasan cewar Abdul Karim ya saba da yawancinsu, kusan duk ana tare, yasa shima ya shiga aka ci gaba da hirar dashi. Duk da deep down his heart tunanin hubby ne dankare a ransa, da son sake sakata a idonsa.


A hankali get man ya wangale kofar get din. Motoci ne suka fara shigowa dan kare da mata. A hankali ta sawo kan motarta cikin compound din. Wanda gaba daya hankalinsu Ahmad yana Kansu. Ita da yusra ne a gaba, sai mutun biyu, kawayenta na islamiyya, da suka mata kara, sai humaira ta uku. Hira suke sha da dariya don akwai daya mammy mai ban dariya a cikinsu.


A kusa da motar ummu khulsum ta faka tata motar.


" dadina da zuwa gidan nan akwai hadaddun samari, mai powder ta dan miko min in dan murza, kafin na fita ko nayi ciniki."  Dariya suka kwashe dashi suna kallon mammy data hakikance sai sun bata powder.


Yusra ta mika mata " gashi Allah ya kawo kasuwa, musha biki."


Murmushi tayi ta amsa tana " amin."


Tsaki hubby ta ja, hango su Engr da suka kafe motarsu da ido.

Kallonta yusra tayi, tare da kallon su Engr tayi dariya " gafa muta nenki?"


" na gansu, ban son gaishesu wallahi, dana San suna gidan nan ba abunda zai shigo dani yanzu." Hubby ta fara


" gaisuwa ai dole, ko baku gaishe suba ni sai na gaishesu

don na hango new catch dina." Mammy ta fada tana murmushi


" wanne a ciki?" Dayar ta tambayeta


" anki gaya miki, salon amin snatching. " dariya sukasa jin salon data amsa din.


" wannan shine riga malan masallaci, tun kan catch din yazo hannu, ana tsoron snatchers. " yusra ta fada, tana balle murfin motar ta fita. Hubby ta Gyara zaman gyalen after dress dinta tayi da kyau. Kamar ta sani ana gama lunch zaa taho ta dora after dress dinta a kan kayan.


Fitowarta yayi dai dai da isowar su junaid, gaisheta sukayi, cikin mutunci tare da tambayar kayan lunch. Key ta mikawa hafiz, akwai abubuwa a but, in kun kwashe a kawo min key dina.


"Sai Anty!! Allah ya bar mana ke." Hafiz omer ya fada yana murmushi.

Dole ta inda su Ahmad da tawagarsa zasu wuce, zuwa part din su Hajiya. Tun suka doso idon salis, engrn da Abdul Karim na kan hubby, harta iso. Yaya Ahmad ta fara gaisarwa, kafin ta musu jam'u cikin sitiriyar miryarta mai zaki, da dadin sauraro. Sauran ma gaishesu sukayi, suka wuce ciki.


A jiyar zuciya dukan su suka sauke a tare.

" engr wai ya maganarku da hubby ne ta kwana?" Daya daga cikin abokansu ya tambaya


Murmushi Engr Sahabi yayi " Ku tayani da addua, yarinyar akwai kafiya wallahi, ina nan ina kokarin shawo kanta, sai dai lamarin suraj kangiwa dake nemanta yasa jikina ya fara sanyi."


" haba faduwar gaba, asarar namiji, sai dai in dama ba sonta kake yi ba." Daya daga ciki ya fada


" kasan irin son da nake mata kuwa? Ina sonta fiye da yadda labbana zasu iya misaltawa, ina sonta, ina son halayyarta, after all duk Wanda ya samu wannan ya gama dace da mata tagari, I known how happy she made my friend, when they are together. Ya fada yana smiling


" gaskiya kam ta hadu ba karya. Amma ya kamata kai da salis daya ya hakura ya marama daya baya, ta haka zakufi saurin shawo kanta, akan dukkan Ku kuce kuna sonta at the same time. "

Kallonsa Engr Sahabi yayi " do'sen matter, an ce kasowa dan uwanka abinda kake sowa kanka, duk kanmu muna da reasons da yasa muke son aurenta, Duk Wanda ya samu a cikinmu we are happy. Abinda kawai zai bakanta mana shine, wani can daga waje yazo ya aureta."


" haka ne kam. Amma ina ganin kamar da wuya ta amincewa dayanku." Dayan ya fada


" we keep on trying." Salis da sai lokacin ya samu bakin tofa nashi ya fada.


" ammafa duk laifin Ahmad ne! Naga suna mutunci sosai, da zai shiga maganar da komai yazo da sauki." Daya ya fada


Harararsa Ahmad yayi " ka rufa min asirina, kai da bakinka kace muna mutunci? Hubby duk Wanda zai mata maganar aure yan zunnan duk mutuncin da kukeyi zaku bata. Ni kuma I don't want that."


" nifa ban gane maka ba? Ina da question mark da yawa a kanka? Anya!!" Salis ya fada yana tsare Ahmad da kallo


Murmushi Ahmad yayi. " koma dai menene kowa tashi ta fishshe shi."

Kowa dake wurin ido ya zubama Ahmad da yake ci gaba da danna wayarsa, kamar bai San abunda suke yi ba.

Engr ya kalli salis " dama na fada maka ai! Ko ban fada ba?"


Salis ya sauke ajiyar zuciya " ka fada kam" ya fada a takai ce.


" kai amma yarinyar nan tayi kasuwa, kana ganin yadda kangiwa ya haukace a kanta? Kusan a sati in bai zo garin nan ba yazo sau biyu, da da sai ya kwashe fiye da 2month bai shigo garin Kaduna ba, duk da iyayensa na cikinta." Daya ya fada yana jin jina kai


" shawara!!; Ku samu manyanta da maganar don kowa yasan matsayarsa, tunda ta wurinta ba nasara, nasan in sha Allah su za suyi nazari sosai kan abun." Daya ya fada


" ka kawo shawara mai kyau, nima nayi tunanin haka." Salis ya fada


Abdul Karim kam ya zama photo,sai kallonsu yake one after the other. Shi a tunaninsa hubby rasa mai aurenta tayi, yasa daddy son hadashi da ita. Yanzu ya gane manufar daddyn akan son dayansu ya auri hubby. In har abokan Yusuf zasu so su maye gurbin Yusuf saboda sanin kyawawan halin hubby, ina ga su kannensa. Shi duk zaman Yusuf da hubby bai da wani cikakken labari a kai, don lokacin da akayi yana Malaysia, in yazo Hutu yawanci yana Lego's gidan uncle omer zuwanshi gidan Yusuf sau daya, zuwansa bayan auren, da yaje ganin daki, tare dama yayansa Allah yasa albarka. Saboda bai samu damar zuwa lokacin bikin ba.


Sai lokacin yake tuna tarba ta karamci da hubby ta musu a lokacin, shida arif fist born din Alhaji omer. Da yadda sukai tayiwa yayan nasu dariyar ya auro Small girl, gashi da alamar bata waye ba, saboda zunbulelen hijab data sako har yana Jan kasa, "ga gida har gida, amma ba mata" kalaman arif ya tuna a lokacin.


Kalaman yaya Ahmad ne suka dawo masa bayan fitowarsu daga part din Alhaji Jamal " a matsayina na dan uwanka, shawara daya zan baka. Karka kuskura ka bijirewa wannan auren, ka karbeshi da hannu bibbiyu, na tabbata zakayi alfahari dashi. Karka biyewa kyale kyale, kyawun zuciya da addini shine abun lura. Hakika daddy ya maka zabe mai nagarta, wanda duk cikinmu ba wanda ya dace da hakan. Damarka ce wannan, in kayi wasa ta kufce maka, na tabbata zakayi dana Sani mara iyaka, lokacin da ba zai maka anfani ba."


Amsar daya bashi a lokacin ta dawo masa. " in haka ne mai zai hana kai ka aureta, naga kana da space na mutun uku, a gidanka. Ko ba komai kai ka taba aure, kaga bazawari da bazawara kenan. Kunfi mach ma,."


Murmushi Ahmad yayi masa " kai din saurayine? Karka dauka bansan duk sharholiyar da kake yi a abuja da Lego's ba? Gara ita ta hanyar auren sunna ta rasa budurcinta, kuma ga jininka. Kai fa? Allah kadai yasan yawan matan da kayi tarayya dasu. Kaga kenan kai ne baka dace da ita ba. Da kake fadin in aureta, Wait and see ka ce baka so ka gani."


Kunyar Ahmad ce ta kamashi a lokacin, bai taba tsammanin yasan abinda yake aikatawa a boye ba,no wonder ko waya sukayi ya dinga masa waazin yaji tsoron Allah, ya tsare dokokinsa, kar yaga ba idon yan'uwa, ya aikata duk abinda yaso, yasan Allah na kallonsa, kuma yana jiran dukkan bayi a mada kata. Ba abunda yake boye a gareshi game da bawa, don haka ka yawaita tuba, tare da nisantar miyagun ayyuka.


Kallon sa yakai kan Ahmad dake faman daddanna wayarsa. So da kaunar dan uwan nasa yaji ya kara ratsa zuciyarsa. In sha Allah zai karbi auren hubby da hannu bibbiyu, sannan zaiyi iya kokarinsa ya kyara tsakaninsa da mahaliccinsa. Ya tabbatar Ahmad na son hubby sosai, sai dai ya kasa gane abunda yasa ya zabi ya hakura, don ya tabbata daya gayawa daddy yana sonta ba wanda zai sakosu a ciki.


Kamar Ahmad yasan shi Abdul Karim ke kallo, ya dago suka hada ido, murmushi ya masa da kallo mai nuni da kaga maganata ko?" Lumshe ido Abdul Karim yayi tare da jin son hubby na kara ratsa zuciyarsa. Allah Allah yake dare yayi ya samu Daddy ya shaida masa ya amince da auren hubby, don bazai iya jira har nan da 5days ba, kamar yadda daddy ya diba masa, don yayi shawara ba.......

Post a Comment for "DA KAMAR WUYA CHAPTER 3 BY ZULAIHATIDRISMISAU"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...