BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 8 by sumayyah Abdulkadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 8 by sumayyah Abdulkadir

BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 8 by sumayyah Abdulkadir

- - Post a Comment

BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 8 by sumayyah Abdulkadir                 Www.bankinhausanovels.com.ng 


daidaito, kowanne wani tunani ne daban a ransa game da dan’uwansa bayan kuma duka abu guda ne wato, soyayyah. 


Shi Imam gani yake Safah ba ta son sa, bai san cewa in akwai wanda Safah ke so a duniya bayanshi yake ba. 


Kuskure ne da kuruciya kawai ta yi. Yanzu abinda ke gabana shine Allah Ya daidaita su kowa ya huta nima in dawo gida in samu miji in yi aure.....” 


Ta share hawaye da habar zaninta. 


Zahradeen ya girgiza kai, lamarin su abin tausayi ne. Allah Ya yi musu arzikin da su kansu basu san iyakarsa ba, gashi kuma Yana yi musu jarrabawa kala-kala wadda sai mai karfin imani ne kadai zai iya jurewa. 


Da kyar ya ce, “Mami addu’a zamu ci gaba da yi Allah Ya warware mana, ita kuma Allah Ya bata lafiya. 


Ga ‘yar’ uwarta ma ba ta cikin kwanciyar hankali tun tahowarku, hankalinta ya gaza kwanciya, cewa take idan an ce mata Safah tana jin sauki ba a taba hadasu a waya sunyi magana ba. Wai idan ita ma ta rasu ne ake boye mata, to ba a son ta. 


Ta ce Ibadan din ma ba za ta bini ba sai dai in tafi da Anisa ita nan za ta taho”. 


Mami ta yi murmushi ta ce, “Safah ta Marwah, me za ta zo ta yi mana? Ta zauna ta kula da ‘ya’yan da Allah Ya bata, ta ji kansu kamar yadda aka ji kanta. 


Ta yi bautar aure wanda shine bautar Ubangiji. Ga kishiya ta gari Allah Ya bata tana binta kamar 


ta yi mata sujjadah. Ga albarkar Uwa irin Inna Binta, ga gwarzo kuma sadaukin masoyi. Ka gaya mata wannan. Safah za ta kirata kwanan nan”. 


Cike da murmushin jin dadin yabon da ya samu daga surukarsa, Zahraddeen ya aje wayar Mami, ya juya ya dubi matarsa Marwah dake gefensa a kwance tana jin duk abinda suke tattaunawa shi da Mami, kasancewar murya a waje (handsfree) suke maganar. 


Ita ma sai da ta murmusa domin kalaman Mami sun sanyaya mata rai. Ta mike ta shige cikin kirjin Zahraddeen, gwarzo, sadauki in ji Mami. A hankali ya yi mata kyakkyawan masauki a kirjin 


nasa, duk da tirtsetsen cikinnata da ke tokare shi. ok 2K 


IMAM a Imam can ya tafi neman aure a wani kauyen Ingila Banbury. Akwai wani abokinsa Joseph da suka yi karatu tare dan asalin kasar Kenya, akwai wata kanwarsa Regina da ta like masa lokacin suna karatu sai ya aure ta. 


Ba irin wulakancin da bai yiwa Regina ba amma 


har yau da take da shekaru talatin da shida bata yi aure ba saboda ya ki auren ta. Tafi kama da black Americans fiye da Kenyanz, domin a nan iyayensu suka haife su. 


Ya hada kaya cikin karamar troller wadanda za su yi masa kwana uku. Ya ce da Mami zai yi balaguro na kwana uku. Mami ta kura masa ido ta kasa karanto komai cikin kwayar idanunsa. 


A sanyaye ya yi kasa da kansa, don har yau kunyar Mami ba ta sake shi ba tun ranar da ta kama shi drunkerd, red-handed. Ta juya ta ci gaba da abinda take yi idanunta cike taf da kwallah. Domin dai tunanin Mami ya ba ta zai yi tafiyar ne inda ba za ta sa masa ido ba ya kwankwadi barasarshi kwana uku, don ta tabbata a cikin gidan ya daina kam. 


Imam ya karasa gabanta ya kai gwiwoyinsa kasa, “Ki yafe min Mami ki yi min kyakkyawan zato. Na san abinda kike tunani, wallahi ba haka bane. Tafiyar da zan yi alheri za ta zame mana daga ni har ku, insha Allahu’’. 


Ta yi saurin kama hannunsa ta mikar da shi tsaye, “Ina za ka je?” 


Ya ce, “Banbury”. 


Mami duk yawonta a kasashen duniya ba ta taba jin wani gari Banbury ba. 


Ya ce, “Ba lallai ki san garin ba Mami, kauye ne”. 


Bata takura da bincike ba ko son kure mutum, tunda bai fadi abinda zai kai shin ba, baya bukatar ta sani ne. 


Ta ce, “Allah ya kiyaye hanya”. 


Yana sauka a Leads ya fiddo waya ya kira Joseph, ya zo ya dauke shi suka karasa a train. Karbar girma Mummyn Regina ta yi masa, sai dai bai ji dadin yadda ya riski Regina ba. 


Gaba daya ta lalace ta tsambare, duk da hakan kyanta yana nan, sai ya ta’allaka hakan da rashin wadatar da ya same su ciki, wai mahaifinsu ya yi retire yana kwance a gida ba shi da lafiya. 


Bai bata lokaci ba ya gaya musu abinda ya kawo shi. Ai kuwa kamar su cinye shi don farin ciki, suka yanke sadaki ya biya, amma ya ce sai dai suyi shiri dukkansu su tafi wurin iyayensa a Los Angeles a daura auren a can yadda addininsa ya tsara. 


Su dai da tsuntsu ya fado musu kasa gasasshe ai basu da ja. Tuni suka hau shiri har wanda ke kwance ba lafiyan suka taho U.S. 


Mami da Hajiya Mama suna bakin swimming a kan kujerun roba suna hira yaran makota dake shigo musu suna ta wanka cikin ruwan ta hanyar amfani da robobin da suke hana su nutsewa (float). 


Mota ta shigo farfajiyar gidan, sai ga Imam da jama’a da wata tsotsatstsiyar yarinya da in ba kanjamau ba, sai ko rashin nutrition. 


Da girmamawa suka karbesu suka yi musu jagora zuwa cikin gida. Gashi su abincin da suka ci tuwo ne da miyar kalkashi wanda ya ji naman talo-talo, don haka Mami ta shiga kicin ta soma kwaso musu abinda ta san za su iya ci da bata rabo dasu, wato snacks, fruits da soyayyun kaji (suyar Na


jeriya). 


Nan suka tashi da komai, aka sake gaisawa bakinsu kamar ya tsage don fara’a. A lokacin ne Imam ya yi mata bayaninsu idanunsa a kasa ya kasa dagowa ya dube ta, balle Hajiya Maama da ta yi kuriii da ido tana jiran jin daga ina ya kwaso musu wannan gayyar tsiyar tsirara dasu kamar bayin Turawa. 


Ya ce, “Mami iyayen Regina ne, wannan kuma yayanta ne abokina Joseph da muka yi karatu tare, amma shi baya aiki don ya yiwa hukumar jamzi’ar laifin da suka bata mai takardu. 


Suna zaune a kauyensu Bunbury, Regina mun dade tare shine dai yau na je na nemo aurenta. Sai ku shirya mai yiwuwa, ko da za a dauko Baffa Sufyan ma hakan ba zai zama matsala ba”. 


Ya yi shiru da ya kawo aya, kasancewar da Turanci ya yi maganar ita da su duk suna ji. Hajiya Maama ce dai da curiosity ya cikawa ciki ta ce da Mami. 


“Ke Zaynabu wai su waye wadannan kafiran?” Mami ta ce ( tana zazzare ido), “Matar da Imam zai aura ce da iyayenta”’. 


Haba! Da Hajiya Maama ta mike kicin ta nufa, ta je ta dauko muciyar tukin tuwon Mami ta yi kansu aguje suka tarwatse a falon, domin sunyi zaton mahaukaciya ce. 


Da ta kasa cimmasu sai ta dawo kan Imam din ta rusa masa a baya sai da ya kai kasa. Sannan ta fasa kuka ta ce, 


“Wallahi in bai fitar mata da wadannan arnan daga gidan ba ita za ta bar masa gidansa, ko a 


kafa ne ta kai kanta Kaduna ta nufi Chikun ba zai kara ganin ko gawarta ba”. 


Haka Imam ya zuba su a mota ya fita dasu yana basu hakuri da cewa ba ta yarda ba, su bata lokaci ta huce zai Jallashe ta a hankali. 


Su dai sunyi mukus kamar ruwa ya cinye su. GA SAMU GA RASHI (In ji Aunty Dinan A Bari Ya Huce). 


Suka kwana a otel din da ya kama musu, washegari ya yi musu sha tara ta arziki har da mota zundumemiya zai tura musu ta jirgin ruwa, suka koma inda suka fito cikin jin dadi, ko ba komai basu yi zuwan banza ba. 


Tun daga ranar Imam ya daukewa Hajiya Maama wuta, Mami kawai yake kulawa. Hirar da yake zama suyi duk daren Allah ya daina, ya daina nemo mata goro da zogale da yake sayo mata wajen ‘yan Ghana mazauna Amurka. 


Sai ya koma shigo da ‘yammata Turawa gidan wai su gaisheta, ma’aikatansa ne don kawai ya bata haushi. 


Da yake ita ma ‘yar duniya ce sai take karbarsu hannu bibbiyu, ta yi ta basu dariya da labarin kuruciyarsa da Safah bata sonsa duk kyan nasa. Ita baka kirin. 


Mami ce mai fassara (translation) suyi ta shan dariya suna mamaki. Domin dai cikinsu duka babu wadda ba ta fatan Imam ya aure ta. 


Suke kuma zuwa da ita Hajiyan a motarsu wajen Safah su gaisa da ita, su kai mata katinan get well soon da fulawoyi. 


Da ya ga hakan ma wato zuwan nasu nishadi 


yake kawo mata, sai ya koresu ya ce kada wadda ta kara zuwar mishi gida. 


Da kyar Mami ta daidaita shi da matar tashi Hajiya Maama suka koma shirinsu. Sai kuma ya dauke kafa daga zuwa duba Safah, don ya san sarai ta warke sai jiran haihuwa amma ba ta mishi wata kwakkwaran magana banda gaisuwa. 


A wurinshi duka wannan nau’i ne na wulakanci da rashin so. Ita kuma bata san me za ta dinga ce mishi ba banda gaisuwar da addu’a cikin zuciyarta. Domin Allah kadai ya san iyakacin miliyoyin da ya kashe a kan lafiyar ta da ta abinda ke cikinta. 


EDD (Edpected Day of Delibery) dinta ya cika har ya wuce. Likitocinta sunyi meeting a kanta, sun tsayar cewa sakamakon kasusuwanta da basu jima da hadewa ba, ba za su bari ta haihu da kanta ba, za ta wahala, ko ta kasa saboda kasusuwanta da sauran ciwo, za su yi mata fida ne a washegari litinin. 


Sanda za a shige da ita dakin tiyatar, ita kuka Hajiya Maama kuka. Imam da Mami idanunsu kemadagas, amma fa addu’a suke yi a zuciyarsu, kar ki so ki tona zukatansu, wadanda ke cike taf da firgici, tsoro da taraddadi. 


Sai addu’a suke cikin zukatan nasu (masu karfin hali). Zuwa wannan lokacin Safah fa ta san Lamido ya rasu tuntuni. Zuciyar musulunci ce kawai ke rike da ita. 


Tunda ta iya ta karbi rashin DADDY na wane ne ba za ta iya karba ba? But it is still painful...... 


yeah so painful! 


Wannan dalilin ne ma yasa ba abinda ke burgeta a duniya balle ya sata nishadi. Haka nan take zaune ba doguwar magana, babu hope babu shiryawa kai future. Babu zabi cikin rayuwa. Duk yadda Allah Ya yi da rayuwarta daidai ne. 


A yau ta tuno da Lamido kan abubuwa da yawa, wato ranar da za a ciro mishi dan shi daga jikinta. Da yana nan Allah kadai Ya san irin sallamar da za suyi, gigicewa zai yi da tarairaya concern da emotional pity. 


Watakila da zai iya da ya haifo mata abin da ke cikinta, ba tare da an yanka ta ba. Ba irin wannan kallon ko in kula da Imam da Mami ke mata 


Wasu irin hawaye masu dumi suka barko daga idanunta. Ta ce a fili amma a hankali. 


“This life has changed.....and we go our separate ways Lamido....... but you’ ll still be in my heart till my dying days.....my world has neber meet a person like you........ ” 


Har aka tura keken da take kai zuwa dakin tiyata ba ta bar nanata wadannan kalaman cikin zuci


yarta ba. 


oko ok 3k 


A n fiddowa Safah kyakkyawar baby girl kwabo da kwabo da Haj. Nadeeya, kalarta ruwan ‘yan Sudan, ba ta yo hasken fatar Lamido ba, ba ta yi kama da uwar ba ko uban, sai ta tsallakesu ta dauko kakarta. Daga uwar har diyar lafiya lau, don haka bayan dogon rubutu da gwaje-gwaje asibitin suka ba ta sallama. Sun hadasu da Nurse wadda za ta ke kula da ita a gida, amma Mami ta ce basa so, ita zaman me take? A hankali Mami ke gasa mata jiki da tawul, kada ta fama wajen da aka yanka. Ta gama ta yiwa baby wanka ta shirya ta cikin suttura kyakkyawa da Imam ya je wani shagon jarirai ya jibgo musu. Ta gasa mata cibi ta rufe ta cikin tawul mai dumi da kauri, ta sanya ta cikin gadonta. Ta gasawa Safah nama ta hana ta cin abincin gongoni, ta hana ta shan kowanne ruwa sai tafasasshe wanda ya sha iska. Ta dama mata kunun kanwa irin wanda ake kaiwa cikin ledarsa daga Nigeria a sayar a kantuna. Sau hudu take mata gashin jikin kullum. Cikin wata guda sai ga Dr. Safah Dan-Kasa ta mike ta girgije ta tsaya da kafafunta. Jaririyarta ta yi 


kubul saboda samun isasshen ruwan nono da abinci mai lafiya da mahaifiyarta take ci kullum. Tun ranar da aka yi haihuwar Mami ta bugawa Malam Abdulkarim da Hajiya Nadeeya, har kukan baby ta saka musu sun ji. 


Malam ya ce, “Sun yanka mata rago da suna (Nadiya). Su aiko musu da inbitation letter da za su kai wajen bisa su zo as bisit zai fi saukin samun bizar U.S da wuri, za su zo shi da Hajiya da Aliyu. 


Wata guda da haihuwar Nadiya (Shukrah) su Malam suka sauka a Los-Angeles, Imam da Mami su suka je suka debo su a filin jirgi. 


Sun ga tarba ta girma da mutunci. Hajiya Nadiya ta yarda a ranta cewa wannan Safah din, ba kwadayi ya kawo ta hannun Lamido ba ikon Allah ne kawai da soyayya ta gaskiya da kuma abin nan da ake cewa, ‘matar mutum kabarinsa. 


Sun wuce gidaje da kasashe da yawa kafin su iso, amma ba ta ga wani waje ko gidan da ya kama kafar wannan da suke ciki ba. Wato ko a Turai din ma gaba da gabanta, BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE. 


Ta dauki jaririya ta tsura mata ido, hawayenta na gudu suna zarya a kundukukinta. 


“Allah Ka ji kan LAMIDO! Ka albarkaci zuri’ar da ya bari, ka yalwata makwancinsa da haske da kamshi. Ka raya wannan yarinya da halin mahaifinta”’. 


Sai daki ya koma kamar dakin zaman makoki. Hajiya Nadeeya na kuka, Mami na yi, Safah na yi, jaririya ma na yi, amma uwar ba ta da karfin 


daukar ta, balle ta bata abincin ta. 


Hajiya Maama, Malam Abdulkarim da Imam dake falo ne suka jiyo kukan jaririyar ya yi yawa. Imam ya ce musu bari ya je ya gano. 


Tsayawa ya yi a bakin kofar dakin yana kallon ikon Allah, 


“Matar mamaci da iyayen mamaci”. 


Ya fadi a ransa. 


“To ya zaku yi? Hakuri ne naku, muma Allah Ya bamu masu son mu haka, kowa ma ai zai mutu”. Abinda ya fadi kenan cikin ransa. Ya shiga har inda Safan take ya dauko ‘yar ya fito da ita ya kawowa Mal. Abdulkarim. Ya karba ya dora ta a kafadarsa. 


Zancen da suke da Malam da Hajiya Maama a falon na gado ne, sun kawo gadon Safah da na ‘yarta. 


Imam ya ce na yarinya su barshi wurinsu su hada da na ‘yan’uwanta ko share ne a saya mata, ko a juya mata. Na Safah za su karba, Allah ya ji kan Nasir. 


Satinsu biyu a guest house din Imam, ana i jibi za su tafi ya kaisu babbar kasuwar Los -Angeles (Grand Central Market) ya yi musu sayayyar tsaraba, musamman kayan yara, manya da kanana ya ce a kai wa ‘yan’uwan Shukrah. 


Har Aliyu ba a yi mishi karamar kyauta ba, daloli aka danka masa ya sayi abinda yake so. Shi kuwa ya ce me zai saya banda ya hada lefe ranar da Allah Ya kawo matar aure ya kai mata. 


Suka yi ta yi masa dariya wai har yanzu da sauransa bai isa aure ba. Ya ce, ““Wallahi na isa 


har na yi yawa”. 


Safah ba ta manta da Zahra’u da Abubakar ba, kayan kawa na mata da jewelleris, shoes and handbags, laces (swiss) da materials haka ta shake mata akwati guda dasu, har sun fi lefen da Aliyu ya hada. 


Ya ce bai yarda ba sai dai ayi musanye, nata sun fi kyau. To dama ina za ka hada zaben Safah da na Aliyu? 


Sannan ta kai baby studio aka yi mata manyan enlergements da na sanyawa a frame duk ta aika musu ita da Abubakar da Talatu. Abubakar mota ce (Honda City 2014). 


Haka bakin suka dawo da sha tara ta arziki. Su da suka kai sai ga shi an maido musu da rabin abinsu cikin lumana in a bery nice way.. 


Kayan sun zowa Zahra’u a daidai za ta tafi Kuwait karatu, sai ta dinka na dinkawa, ta hadasu cikin luggage dinta tana godewa Allah da Ya bata ‘yar da zata ke tuna mata da Yaya Lamido, tana kuma godewa Maman Nadeeya (sabon sunan da tasa mata). 


2K KR AK awowar Safah gida, Mami sai ta zuba ido tana kallon wani sabon film koko in ce lobe drama da suka fito da shi. Shi dai haka nan Allah ya dora masa son Shukrah kamar shi ya haife ta. 


Baya iya fita office bai duba ta tana barci ba. Haka idan ya je baya awa uku bai kira Mami ya ji yadda take ba. Ko magana basa yi a junansu, ba 

Post a Comment for "BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 8 by sumayyah Abdulkadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...