BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 7 by sumayyah Abdulkadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 7 by sumayyah Abdulkadir

BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 7 by sumayyah Abdulkadir

- - Post a Comment

BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 7 by sumayyah Abdulkadir


                     Www.bankinhausanovels.com.ng 
‘yan’ uwantaka suke? 


Tun iyayensu na raye take rike da Shatu, ita ta yi mata aure ta yi mata gadon daki. Lokacin da Baban Danejo ya rasu, ita ta ci gaba da rikonsu ita da ‘yarta, ta aurawa Lamido. 


In kana son ganin bacin ran Hajiya Nadeeya, ko kai wane to ka yi batanci ga Danejo ko ka fadi laifin ta. 


Lamido bai isa ya ce Danejo ta yi mishi laifi ba, yanzun nan za ta gwale shi, ta zage shi ta uwa ta uba. Wai duk duniya bayan iyayensa ba mai kaunar shi kamar Danejo, don tun ba shi da ko sisi take tare da shi. Yanzu da ya samu shine zai nemi ya tozarta ta. 


Lokacin da Lamido ya fara yin kwari, ya so ya kaita ta sauke farali amma ta ce sai Shatu da Danejo sun fara zuwa. 


An ba shi auren ‘ya’yan manya har ba adadi, ta hana shi karba saboda Danejo. Dubi tijarar da ta rika yiwa Malam a kan auren Lamido da Safah. Ba don Malam din namiji bane, da ba a yi auren nan ba. Tsakaninta da Shatu da Danejo sai Allah Ya yi musu hisabi. Wata shari’ar......SAI A LAHIRA! 


An cafke Danejo da yara biyu a Airport din kasar Neitherland. Shari’ar da aka yi ba doguwa ba ce, domin shaidu sun bayyana, yaran kuma sun tabbatar ita ce ta sasu, komai a rubuce yake da kwanan wata da sa hannunta. 


Taso ta yi gardama Shatu ta kwada mata mari ta 


ce, “Ke kika sa su, haka kawai da tsufana kinsa an daura min ankwa saboda mugun kishinki mara amfani, kin rabani da ‘yar’ uwata daya da ta saura mini a duniya”’. 


Sai tasa kuka. Danejo ta ce, “Idan ni na sasu ba ke kika gaya min yadda za a yi ba? Na taba cewa zan ci gadon Lamido ba ke kika ce mu ci ba? Kwadayinki ya ja miki amma ni son Lamido nake saboda Allah ba don abin da ya mallaka ba.....ko na kashe Lamido, wallahi a kan ina son shi ne, nima a kashe ni don ban ga amfanin sauran rayuwata ba tare da Lamido ba......” Tasa kuka. Haka Alkali ya gama rubuce-rubucensa, ya yanke hukuncin da shari’a ta bayar. Danejo da Shatu daurin rai da rai wato (life inprisonment). Sauran yaran kowa ya karbi hukuncin da shari’a ta ba shi. 


Wannan bai wanke zuciyar Abdulkarim da Nadeeya ba, karfin imani kadai ke rike dasu. Jigon gida ya tafi, babban bango ya fadi. Zuciyoyi sunyi duhu, idanuwa sun kode don kuka, kuzari Ya tafi, walwala ta dushe, baki yayi gummm! Sai zuciya ke azabta. 


In ka ga wannan family sai ka zub da musu hawaye, don kowannensu babu karsashi, farin cikinsu daya likitoci sun ce akwai yaron ciki a jikin Safah. 


Malam da Deputy sun hada dukiyar Lamido waje guda, kyautar da ya yiwa Malam da Safah malamai sun ce bata halatta ba, domin ya yi ta ne ba 


cikin hayyacinsa ba. Don haka duk an hadata waje daya. 


Babu wanda yake da tabbacin cewa Lamido ya saki Danejo kafin ya rasu ko bai sake ta ba. Don haka an zuba ido a ga abin da Safah za ta haifa kafin a raba gadon. Don haka Danejo tana cikin rabon gadon. ikin wannan lokacin gaba daya, Imam da Mami ke jinyar Safah. Marwah kan zo ta yi kwanaki ta koma. 


Ganin al’amuranshi na shirin durkushewa a dalilin rashinsa, sai ya yi magana da likitocin Safah kan zai fita da ita. Suka shirya takardun komai, ya hada passport din Mami da na Hajiya Mama ya nufi Abuja. 


Cikin sati biyu su Mami suka yi sallama da kowa, ‘yan’uwa da abokan arziki, Marwah na kuka ‘ya’yanta na yi. Gidan rufe shi akai da manyamanyan (padlocks) domin tafiya ce da babu ranar dawowa. 


Ya dai yi alkawarin zai kawowa su Malam Abdulkarim abinda Safah ta haifa su ganshi da zarar haife shi. Da an yaye shi/ta za a basu jikansu kamar yadda suke so. 


Hajiya Nadeeya da Mami sun sha kuka. Zahraddeen kansa ya koka har ya gode Allah. A duk sanda ya tuno Lamido da halin rai kwakwai mutu kawai da Safah ke ciki, kuma cikin kudurar Ubangiji wai da ciki. 


Don haka a ganin Zahraddeen rangwamen Imam ne rashin sanin Lamido! Sai dai ya ji a bakin Mami, Shahida da maigidanta sune ‘yan rakiya don su ga muhallinsu. 


Ranar alhamis ashirin da tara ga watan Mayu suka daga Amurka. Sun sauka birnin New York jirgi ya huta, sannan suka daga Los Angeles a yammacin ranar juma’a. Lafiya suka sauka a babban airport din Los-Angeles.. 


Motocin da suka zo dibarsu kadai da bakake da jajayen ma’aikatan sun basu tsoro. Domin in ka kalli Imam din a haka yadda ya maida kansa Sufi (Sufism) ba za ka ce ya mallaki naira goma ba. 


Da suka shiga farfajiyar gidansa a Beberly - Hills, Hajiya Maama kuka ta saka, ta ce, “Anya Almustapha ba cinikin sassan jikin mutane kuke yi ba?” 


Shahidah da Hafizu suka sa dariya. Imam ko kallon ta bai yi ba, abinda ya dame shi ya dame shi, wato halin da Safah ke ciki a asibiti. AllahAllah yake a sauke su ya bude musu gidan su shiga ya juya. 


Domin tun daga filin jirgi motar asibitin Good - Samaritan (daya daga cikin manyan asibitocin Los-Angeles) ta yi gaba da Safah cikin ambulance aka dora a inda aka tsaya. 


Kwanan Shahidah da Minister Hafizu bakwai a guest house din Imam suka juya gida Nageria. Suna masu yiwa Safah fatan alheri da samun lafiya. 


Kowannensu da dalleliyar mota kirar jiya-jiya 


(2015 Sonata Genesis) wadda bata kai ga isa kowace kasa ba, daga kamfanin Dan-Kasa Motors. 


Gida ya rage sai Mami da Hajiya Mama, wadda ita ma kwararrun likitoci ya debo mata har gida suke kula da ita. Don ta ce ba shegen da zai kaita asibiti, ajalinta take jira ya risketa a daki cikin bautar Ubangiji, ba akan gadon turawa ba. 


Imam kan ce da ita, 


“Wai ke wa ya ce dake shekaru sune mutuwa? Kina ina jarirai ke mutuwa su bar tsoho? Kina ina ‘ya’ yanki masu kuruciya suka mace suka barki? Kina ina Da yake mutuwa a cikin uwarsa tun kamin ya zo duniya??? 


Don haka don Allah don Annabi ki saurara mana da zancen mutuwa haka nan muji da abin da ya 


dame mu”. 2K ok ok ami da Hajiya Mama rayuwar dadi da kwanciyar hankali suke yi. Cikin ‘yan watanni Hajiya Mama ta yi kwari tana takawa da kafafunta ta shiga ko’ina a gidan aljannar duniyar da suke ciki. Lallai gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta, idan suka tuno gidansu na Kaduna. Aikin Mami a gidan kawai shine GIRKI, ta dafa musu abincin da suke so traditionally (a gargajiyance) ba kwabe-kwaben Turawa ba. 


Tuni an sallami kukun Imam. Duk da yanayin kayan abincin akwai bambanci babu irin abincin Hausawan da bata iya sarrafawa da nasu kayan abincin. 


Lokaci-lokaci Imam kan kaita ta ga Safah wadda a hankali take samun sauki. Duk wani ciwo na jikinta ya kame sai tabo, kumburin kanta saboda buguwa ya sace, fuskarta ta sabe. 


Kasusuwan kafarta ne basu gama daidaituwa ba. Cikinta watanni takwas ya fito kuru-kuru cikin dogayen rigunan da ake sa mata tana daga kwance, yana ta wutsilniyarsa a dalilin good antinatal care da yake samu. 


A lokacin ne suka soma koya mata tafiya da karafa. Safah na ganin Imam da Mami ta kuma san a asibiti suke na jar fata, amma bata san ina ne ba. Wa ya kawo ta? Yaushe Imam ya dawo? Ina Lamido? Tambayoyin da take yiwa kanta kenan cikin zuciyarta amma ba ta taba furtawa ba. Iyakacinta da Imam, 


“Ya kike jin jikin? Mobement din baby fah?” “Alhamdulillahi, yana ta motsi”. 


Daga haka sai ido. Ya kalleta ta kalle shi, ta kau da kai ko ya kau da kai. Ba cewa ta tafas bayan wannan. 


Amma tana hira da Nurses dinta sosai, musamman Mrs. Wilson wata Baturiyar Moscow, aiki ya kawo mijinta Dr. Wilson asibitin, ita din kuma ta yi karatun Nursing a nan Los Angeles da ta gama ya samar mata aikin take yi. Za su yi shekaru daya da Safah. 


Yau ma Mrs. Wilson ce ke koya mata tafiya da sanduna, dai-dai lokacin da motar Imam ta sawo kai asibitin. 


Mami na zaune a gaba, tun daga nesa Mami ta fara fara’ar ganin Safah na tafiya. Ta fito dauke 


da kwandon kayan abinci, Imam ya karbe ta suka doshe su, bakin Mami ya ki rufuwa. 


Imam tsayawa ya yi jikin motarsa ‘Ford -Mustang’ yana kallon Safah ta cikin glasses din idonsa farare sol, a lokacin da Mami ta cika tambulan da kunun gyada tasa mata a baki. 


Babu abinda ya canza na halittarta daga yadda ya santa, kullum kuma kamar kara mata kuruciya ake. (She is looking fresh and youthful). Tun dawowarsa bai taba yi mata kyakkyawan kallo ba sai yau. 


Yarinyar da ta juya duniyar rayuwarshi, ta sanya mishi bakin cikin da babu wanda ya taba sanya mishi ko da misalinsa, amma matsayinta a zuciyarshi daidai da rana daya bai taba canzawa ba. Yarinyar da ta hana mishi dandana ni’imar da Allah Ya yiwa aure. Ita tana can ta yi aurenta da wanda take so, suka ci kuruciyarsu, har ga rabo Allah Ya basu. 


A duniya akwai wanda ya karya zuciyarsa kamar yadda Safah ta karya? 


Hankici yasa ya dauke hawayen da suka tsatstsafo a idanunsa yana mai tausayin kansa. Bai da Uwa, bai da Uba, baida Alh. Aliko, bai da sa’a a soyayyah.....!!!. 


Mami sai neman motar Imam ta yi a filin wajen ta rasa, ba ta ga kuma lokacin da ya tafi ba, tunda motar ba ta da hayaniyar komai. 


Mami da dare ya risketa a asibitin, sai public bus ta bi ta koma gida. Tana kakabin ina Imam ya shiga babu amo babu labari. 


Da ta iso gida Hajiya Mama ma cewa ta yi ba ta 


ganshi ba. Amma ta ji shigowarsa. Kusufa-Kusufa Mami ke lekawa na gidan har lambu da swimming pool babu Imam. 


A wani dan karamin daki dake matsayin rest room dinsa ta same shi ko kayan jikinsa bai cire ba. Ya yi barci kamar barcin mutuwa, kwalaben giya birjik ga wani irin amai da ya sharkaba a gefe, da shishar wiwi da lofe ta Turawa. “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’ un!” 


Kawai Mami ke ambato, tareda toshe hanci. Da sauri ta koma dakinta ta rufe, ta jingina da kofar tana hirji da kokarin daidaita numfashinta. 


Ya kamata tuntuni ta yi tunanin wasu muhimman al’amura tun dawowar Imam gida, amma ba ta yi ba sakamakon wadannan al’amura marasa dadi da suka yi ta faruwa da su. 


Mene ne ya hana Imam yin aure? Mene ne ya lalata suffarsa da walwalarsa alhalin yana cikin wannan daular rayuwa? Idan neman mata yake tunda suka zo ba ta taba ganin alama ba, idan neman maza yake babu wanda ya taba biyo shi gida nemansa, daga gida sai ofis babu inda yake zuwa. Duk wanda yake mu’amala dasu mutanen kirki ne masu tyall. 


To me ke kuenching physiological need dinsa? “Giya!”. 


Zuciyarta ta bata amsa a hankali. 


Mami ta dauki abin shara da abin kwashewa ta nufi dakin hutawar tasa. Ta share aman, ta kwashe kwalaban, ta bude dan karamin firjin ta gansu a jere kala-kala masu karshen tsadar duk ta 


kwashe su ta kai bola. 


Ta dawo tana goge dakin da omo mai kamshi saboda hamamin da karnin aman da yake yi. 


Tana cikin gogewar Imam ya farka. Bai fahimci komai ba, don garau ya tashi babu damuwar komai a tare da shi. 


Ya ce, “Haba Mami, wannan ba aikinki bane, ki bari Suzana ta zo ta yi mana”. 


Mami kanta na kasa sai a lokacin ya ga hawaye ke diga daga idonta. Ba ta kuma bari sun hada ido ba ta dauki bokitin omon ta fita. 


Sai jikinsa ya yi sanyi, ya soma wani tunani daban kuma. (A asibiti ya baro ta, ya zo ya yi ta drinking). 


Ya kama kansa da hannayenshi biyu dake neman tsagewa. A fili ya ambaci “Lahaula wala kuwwata illabillahil aliyul azeem!” 


Da gudu ya bude firjinsa ya ga wayam! Bari kawai ya je ya amsa laifinsa, ya ba ta hakuri. Ya yi alkawarin daga yau ba shi ba giya, insha Allahu!!!. Sai dai soyayyah da kishin su halaka shi. Ya murda kofar dakin Mamin cikin sallama, tana sallah bisa sallaya, sallar da ita kanta ba ta san adadin raka’o’in da take yi ba, addu’a kawai take cikin sujjadarta a fili. 


“Ya Allah bani na haifi Imam ba, amma amana ne a gareni. Fushina da shi hakika za ka iya kama shi da shi. Na roke Ka, Ka sassauta fushina a kansa, ka daidaita rayuwarshi kada ka kama shi da laifin da ba halinsa ba, zuciya ce ta ingiza shi. Ya Allah wannan bawa naKa maraya ne, mai ne


man kauna da tausayin iyaye. Ina kaunarsa ina tausayinsa yadda harshena ba zai iya bayyanawa ba. 


Ina rokonka ka bani ikon kawo farin ciki cikin rayuwarsa, ka fahimtar da shi zuciyar Safah a 


Iya abinda ya iya ji kenan, sai ya yi baya ya kulle kofar ya koma dakinsa. Ya bude firjin babu giya, Sai ya zaro taba ya soma tada gajimare. Mami ta yi fami a kan gyambon da ake fama da shi. 


Me ya kawo ambaton Safah cikin addu’arta? Wato Mami ta fahimci har yanzu yana SON Safah? Soyayyar Safah ce ta tsunduma shi a gurbatacciyar rayuwa???. 


Me take nufi da Allah Ya fahimtar da shi zuciyar Safah a kansa? Tana nufin Safah na son sa? A’a, ba zai taba yarda ba. Muguwa ce, azzaluma ce, kanta kawai ta sani. Ba ta da tausayi ko miskala zarrah. 


Ban da ta zame masa dole kuma mijin ya rasu, babu abin da zai sa ya taho da ita, balle ta dawo cikin rayuwarshi. Ta je can ta karata da wanda take so. 


KK ashegari bai nunawa Mami komi a fuska ba, gaishe ta kawai ya yi, ya yi kalacin da ta shirya masa na funkaso da miyar kaji da kunun tsamiya. Bai ce komi ba ya wuce ofis, zuciyarsa na cewa ‘Kaddara Mami an amsa addu’arki, babu ni babu GIYA, insha Allahu. Safah ko ita ta yi saura a ‘ya’ya mata bata da abin da za ta birgeni da shi, ba abinda zan yi da ita. Kwanan nan zan yi aure insha Allahu kafin ta fito daga asibiti. 


“Auren huce haushi????” Wani bangaren na zuciyarsa ya yi gaggawar halarto da wannan tambaya. Tsaki ya yi, “Koma na mene ne zan yi aure, budurwa ba bazawara ba wadda wani can da bai san darajarta ba ya gama kwashe alfarmar ta”. Mami ba ta gayawa Hajiya Mama wannan zance ba, ta barshi a ranta tana ta ci gaba da addu’a. Sunyi waya da Zahraddeen a ranar yake tambayar lafiyar Safah, ya kuma gaya mata an yiwa Daddy shayi (kaciya), an kuma yiwa Fati Birthday one year. Yanzu haka kuma suna nan suna ta shiri za su koma Ibadan daga Lagos zasu yi wani aiki da refinery na Ibadan. Mami ta yi fatan alheri cikin wasa kuma ta ce, “Kada a kai min maigida garin Yarabawa ya taso 


da Yarabanci. Ita wannan kodaddiyar dai a tafi da ita”. 


Zahraddeen na dariya ya ce da Mami, “Ai kishiyoyin naki yawa garesu, wannan scan din ma ya nuna baby girl ce”. 


Mami na jin kunyar wai wani cikin Marwah ke da shi amma shi Zahraddeen ko a jikinsa don idan yana tare da Mami ji yake kamar Yayarshi. Baya iya boye mata komai. Yanzu ma wata muhimmiyar magana yake gaya mata. Ya nutsu sosai ya ce. 


“Wallahi Mami wani al’amari ne ya sawo kai, wato Deputy President abokin Lamido......... » Mami ta ce, “Sulaiman?” 


Ya ce, “Haka sunan yake, Sulaiman Yakasai. To ya yi tattaki ya taddani har Lagos da wata muhimmiyar magana”. 


Mami ta ce, “Uhm!” 


Ya ci gaba, “Ya zo ne yana kamun kafa dani in kawo shi gareku yana son auren Safah da zarar ta haihu idan Allah Ya bata lafiya”. 


“Wata sabuwa!” In ji Mami. 


Ta ce, “Zahraddeen bari zancen nan ka ji, ni kadai na san halin da nake ciki a yanzu.......ka bashi hakuri domin mutumin kirki ne, mun kuma yaba da kaunar da yake yiwa Lamido. 


Zamu ci gaba da yi mishi addu’a Allah Ya saka mai da mafificin ALHERIN Sa. Amma Safah bazata yarda ta aure shi ba tana ganin Imam single. 


Shima kuma ba zai yarda ba kada in je ya halaka kansa a banza. Sai dai zuciyoyinsu sun ki 


Post a Comment for "BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 7 by sumayyah Abdulkadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...