BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 1 by sumayyah Abdulkadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 1 by sumayyah Abdulkadir

BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 1 by sumayyah Abdulkadir

- - Post a Comment

 BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 1 by sumayyah Abdulkadir 

Www.bankinhausanovels.com.ng Allah ne ya kai Susan mai aikin Danejo dakin uwargijiyarta don ta gaya mata an harbi Oga tun dazu babu wanda ya ganta ta fito, ta duba falon ba ta nan sai ta nufi bedroom, nan ta jiyo muryar Danejo na cewa.

““Waye a nan? Bude ni don Allah”. 


Ta bude ta, ta ganta wujiga-wujiga dakinta kamar an sha dambe a cikinsa, nan da nan ta gane abinda ya faru.

May be Oga ya gaya mata ya yi aure daga dawowarta shine ta nemi kashe shi. Don ko su barorin gidan sun santa farin sani kan kishi, cikinsu babu wadda ta isa ta shigo in yana gidan sai in ya fita ta neme su. 


Sai ta kasa gaya mata komai ta ce dai an wuce da Oga asibiti basu ganta ba. Tsaki ta yi ta koreta. Tana kwafa ta ce, “Ai mutuwar kasko zamu yi, kar ka barni da rai, kamar yadda nima ba zan barka da rai ba’. 


Safah na cikin likitocin dake kula da Lamido, domin dai MBBS ta yi ( specialization dinta kawai shine dental surgery/dentistry). Sai da aka kwana uku ya samu kansa. Anyi dinki sosai an rufe wajen, kafadarshi ta dama ma ta kumbura sakamakon fitilar barcin da ta sauke masa a kafadar. 


Tun daga asibiti ya sai mata tikiti ya aika mata, sannan ya kirata a waya ya ce ta tattara ta tafi Yola shi ba zai iya wannan bala’in ba kafin ta kai shi kabari kwananshi bai kare ba, idan ta sake ya zo ya taddata a gidan zai sake ta. 


Wannan shine weakness din Danejo (saki daga 


Lamido). Don haka tana kuka ta debi wasu daga cikin kayanta ta tafi. Ta je ta shiryawa ‘yan’uwa da iyayensu karya da gaskiya ya ce in ba ta tafi ba zai saketa. Ya yi aure bata sani ba, don ta yi magana ya yi mata dukan tsiya ya koro ta. 


Hankalin Hajiya Nadeeya ya tashi kwarai, Malam kuwa bai yarda da ita ba, cewa ya yi sai ya ji ta bakin Lamidon. 


Ya yi ta kiranshi a waya amma dukkan wayoyinshi a kashe. Hajiya Nadeeya ta ce, “Ka ga abinda nake gudu ko Malam? Shi yasa raina bai kwanta da karin auren nan na Lamido ba, amma ka yi uwa ka yi makarbiya kai ga mai ‘yar’uwa. “Yar’uwar da saboda daular da take ciki ta daina neman ku, ta daina zumunci daku. Yarinyar da aka tabbatar tun kan ta je gidan miji ya saketa saboda sun gama watsewa da saurayin tun a titi, shekaru bakwai da rabuwarsu ba ta samu miji ba ya je ya kwaso ta, kai kuma ka goya mishi baya. Ga shi nan ai tun ba a je ko’ina ba ya koro uwar ‘ya’yanshi. To wallahi mu ba zamu yarda ba. Idan har Danejo bazata zauna tare da shi a Abujar ba, sai dai in ita ma Sakina take ko wa? Ta dawo nan su zauna tare da Danejo muna kallon takun kowaccensu, ba za a mallake min da ba, kamar yadda suke mulkar maza! Labarinsu kwandokwando babu wanda bani da shi”. 


Malam Abdulkarim bai katseta ba sai da ta dasa aya. Ya ce, “Nadiya! Nadiya!! Nadiya!!!” Har sau uku. 


“Ke ce ko ba ke ba ce? Ko wata me kama dake ce take yi min gizo da kamannin ki?” 


—_ 


Ta karkace kai, ‘““Gaskiya ai daci ne da ita”. Malam ya yi murmushi ya ce, “To yanzu in ya tattaro matan nasa ya kawo miki shi ya tafi shi kadai me za ki yiwa matan nashi? 


Za ki ije musu larurar aure ne ko za ki dauki nauyin su?” 


Ta yi shiru, don ta rasa amsar da za ta bashi. 


Ya ce, “Da girmanki, da mutuncinki kika share mazauna kika zauna ana gaya miki gulma a kan mutanen da basu da hakkin ki. 


Wallahi ki ji tsoron Allah, Allah ba azzalumin kowa bane. In kin ki ji ba kya ki gani ba’. Ya karkade babbar rigarsa ya fita. 


Kwana bakwai din da suka biyo baya, babu waya daga Lamido ko ji daga gare shi. Don haka Malam Abdulkarim ya yi shiri ya bi dansa don hankalinsa ya gaza kwanciya. 


Ta jirgi ya taho, dan haka cikin dan lokaci ya isa Abuja, ya yiwa Isaac waya ya je filin jirgi ya dauko shi. 


Suna tafe a hanya Isaac yake gaya mishi ai Oga yana asibiti yau sati guda, mai yiwuwa ma yau a sallamo shi. 


Malam jiki a sanyaye ya ce, “Me ya same shi?” Isaac ya ce, “Mu kanmu ba zamu ce ba, lafiya na dauko su a filin jirgi shi da Maman su Fa’ik, muka shigo gida lafiya. Ta dade a Sydney sai ranar ta dawo. 


Ba a fi awanni biyu da shigarsa gida ba sai Madam karama ta soma ihun kirana. Wallahi wani abu aka luma masa a tsakar ka kamar bullet saboda zurfin da ya yi. 


Dan Allah ya rubuta yana da sauran shan ruwa a gaba da ba za a same shi ba. Har yanzu likitoci suna hasashen Allah yasa kwakwalwarsa ba ta samu matsala ba, za su tura shi wani asibitin a Miami, likitan kwakwalwar da babu kamarsa a Africa da Turai ya duba shi sosai, Dr. Al-ameen Bello Makarfi (Siradin Rayuwa). 


Don haka duk da bai fada ba, sai dai in a tsakanin Madam babba da karama ne wata ta yi mishi wannan aika-aika wallahi, don mu dai bamu ga kowa ya zo ba, kuma babu wanda ya shiga, don babu wanda ya isa ya karya security din gidan nan kwamfuta bata nuna shi ba”. 


Malam ya girgiza kai, tuni ya gano bakin zaren al’amarin. 


Ya samu Lamido ya ji sauki sosai, sai dai asibitin cike yake da ma’aikatansa da abokan arziki har da mataimakin shugaban kasa. 


Lamido ya ji dadin ganin mahaifinshi. A lokacin aka sallame su suka nufi gida motoci bila’adadin biye dasu. 


Lamido mutum ne na jama’a, kowa son shi yake. Shi ba dan siyasa bane amma yanada siyasar sa akankaran kansa, wadda ke sayo mishi kauna daga al’ummar Nigeria kabilu da hausawa. Yana rike da hannun Malam, Safah na biye dasu rike da jakar Malam din karama, basu tsaya ba sai falonta na kasa. 


Lamido bai ambato Danejo ba balle ya ce ita ta yi mishi wannan aika-aika, cewa ya yi tsautsayi ne wanda ba a sa mishi rana. 


Malam din ma bai takura sai ya kure shi ba, shi 


—_ 


dadi ma ya ji Lamido zuciyar ‘yan Aljannah gare shi, ya rufawa iyalinsa asiri shima Allah Zai rufa masa. 


Malam don haushin Danejo ko zancen zuwanta Taraba bai masa ba. Ita tana can ta hada shi da mahaifiyarsa da ‘yan’uwansa, shi ga shi yana rufa mata asiri, don ya tabbatar bai yi aure don baya son Danejo ba, ko don ya wulakanta ta ba. Washegari Malam ya yi sammako ya yi komawarsa. Bayan ya saka musu albarkar hidimar da suka kwana suka yini yi da shi kamar sun hadiyeshi shi da Safah. 


Da ya dawo gida ma bakinshi ya ja ya yi gum bai ce dasu komai ba. Ta zauna gidan in ta zama ‘yar ta’adda kar ta kashe masa rabin zuciyarshi Lamido. 


Tambayar duniya Haj. Nadeeya ta yi Malam ya ki ce da ita komai. Da ta dame shi da tambaya sai ya ce. “Dana bai ce min ga laifin da Danejo ta yi masa ba”. 


Ta ce, “Rashin arziki ne kenan ka gani ko? Don haka gobe a sai mata tikiti ta koma dakinta”. 


Ya ce, “Bani da hali’”’. 


Ta ce, ‘Ni ina da shi zan bata’. 


Ta shuri kwanukan abinci ta fita. 


Zahra’u ta shigo ta tadda mahaifinsu cikin tagumi, Zahra’u ita ce autar su Lamido. Akwai shiri sosai tsakaninta da dan’uwanta da take so fiye da kowa a gidan. 


Shekarunta sha bakwai ta gama sakandire tana jiran fitowar jarabawa, don Lamido ya ce Malaysia 


zai kaita ba yanzu zai yi mata aure ba. 


Ta gaida Malam, ta yi masa barka da dawowa. Sai ta koma gefe ta takure ta yi shiru, idanunta suka ciko da kwalla. 


Malam ya maido hankalinsa kanta da ya gane cikin damuwa take, ya ce, “Fadima (sunan da yake kiranta) me ya faru ne?” 


Hawaye ya zubo mata ta matsa kusa da shi sosai, kamar zata shige jikinsa jikinta yana rawa, 


“Baba tun muna yara ka hane mu da yin labe (sauraron maganar mutane), kuma wallahi ban taba yi ba’. 


Ya girgiza kai alamar ya yarda ba ta yi din. Ta ci gaba da cewa. 


“To jiya Hajiyarmu ta fita Inna Shatu (mahaifiyar Danejo) ta zo, lokacin ina barci a uwar daka tashina kenan, amma ban fito ba sai na ci gaba da kwanciya. 


Sai na ji Aunty Danejo na gayawa Inna Shatu fasa kan Yaya Lamido ta yi da tsinin takalminta”. Ta share idonta da hanci. Ta ci gaba da cewa. 


“Ta gayawa Inna Shatu wallahi sai ta karasa shi in dai bai rabu da matar da ya aura ba. Ita ba gado take so ta ci ba, don ita ma ta shirya tafiya lahirar suje can su zauna su biyu, ko hurul’ini Allah ya ba shi sai ta rabata da numfashinta”. 


Malam ya kadu sosai ya firgita. Zahra’u ta ci gaba da cewa, “Sai Inna Shatu ta hau yin dariya, ta ce mata ai a lahira ba a mutuwa. 


Ta yi hakuri ta zauna su ci gado, ta danne shi da filo kawai ko ta zuba mishi abin da zai tsitstsinka mishi hanji bakinsu alaikum, ba kishiya kuma ga 


gado daga ita sai ‘ya’yanta, karkari a bawa amarya tumunin takaba, su Malam da Nadiya ma dan abin da za a tsakura musu a ciki bai taka kara ya karya ba.....”. 


Zuwa wannan lokacin Malam ya mike tsaye. “Tsakanin ki da wa kike magana Fadima? Mai sunanki ba ta karya”. 


Ta ce, “Idan na yi musu karya kada Allah ya sunsuna min kamshin Aljanna”. 


Ya ce, “Jeki, ki kwantar da hankalinki barni dasu, ba abinda zai samu dan’uwanki da_ yardar Ubangiji. 


Mutane na gari Allah yana kare abinsa a ko’ina. Balle wadanda albarka da addu’ar iyaye ta yi 


musu lullubv’’. ok kK 


T un daga ranar Malam ya daukewa Hajiya 


Nadeeya wuta a kan zancen komen Danejo. Gargadi ya yi mata mai zafi cewa kada ta sake ya ji ta maida Danejo dakinta sai mijinta ya bukaci hakan, ya kuma zo da kansa daukan nata. Wannan ba karamin tada ma Hajiya da Danejo hankali ya yi ba, sai dai ita Danejo ta fita tashin hankali, musamman idan ta tuna Lamido na can yana barje amarcinsa da watanta. 


Wannan tunanin ba karamin tada mata hankali yake yi ba. Aka debi sati biyu babu Lamido babu wayarsa. 


Sai ta soma hada kayanta kawai kamar mahaukaciya a hantsin safiyar lahadi ta fito jaye da trolley, ta samu Hajiya a madafi ta ce. 


“Ni zan wuce Abuja Hajiya, jikina na bani Daddy ba lafiya ba, don bai taba yin irin wannan fushin dani ba”. 


Hajiya ta yi dan jum! Ta ce a ranta, “Danejo kishi ya maida ta mahaukaciya”’. 


Kamin ta ankara Danejo ta fice. A zaure ta hadu da Abubakar, ta ce, “Yauwa Bukar, dauki akwatin nan ka rakani Airport”. 


Abubakar ya cika da mamaki, ya ce, “Aunty Danejo babu mukullin motar Malam a hannuna, kin san kuma ba zan goye ki a babur ba”. 


Ta ce, “Tasi zamu hau”. 


Ya kama baki yana mata kallon wani abu na motsi a kwakwalwarki, sannan ya ce, “Da izinin Yaya Lamido zan dauke ki a tasi in kai ki filin jirgi?” 


Ta lailayo wani ubansu ashar ta mirgina masa, ta ce, “Shi da Yaya Lamidon su raba, zai rakata ko 


ba zai raka ta ba?” 


Da gudu Abubakar ya yi cikin gida ya shige kuryar dakin Hajiyarsu yana cewa, “Hajiya! Hajiyal!” 


Ta aje ludayin da take damun kunun gyada da shi ta bishi dakin zaninta na kwancewa, ta ce, “Lafiya Abkar”. 


Ya ce, “Wallahi Aunty Danejo kanta da motsi”. Ta ce, “Nima na ga alama”. 


Suka dunguma soron suka kama jakar suna lalJaminta ta koma gida ta jira Malam ya dawo ya ba da mota sai a kaita. 


Sai ta fashe musu da kuka, daidai lokacin Inna Shatu ta sawo kai soron. 


Ta ce, “Lafiya?” 


Hajiya ta ce, “To da sauki dai, Danejo ba ta jin magana, har yau matar Lamido take ba ta gama sanin halinsa ba’’. 


Da kyar suka lallabe ta da taimakon uwar suka koma cikin gida. Hajiya Nadeeya ta ce, “Ki bar ni in bai zo ba karshen satin nan ni da kaina zan maida ke dakinki. 


Bai isa ba wallahi, har yau ba a haifi diyar da za ta rabaki da Lamido ba. Ba ‘yar’uwar Malam ba, ko ‘yarsa ce ta cikinsa’’. 


36 2K OK 


A nasu bangaren, komawar Lamido gida daga asibiti ta zo da sabon sauyi wanda ke nuna lallai Lamido na bukatar ganin likitan kwakwalwa. 


Da farko al’amuran basu damu Safah ba, don tana danganta hakan da zafin ciwo, tunda raunin 


bai gama warkewa ba. Abu na farko, idan Lamido ya shiga wanka baya fitowa sai ya yi awa biyar. Tana mamakin me yake zama yana yi haka? Rannan dai ta ga zaman jiranshi a bakin gado ba zai yi mata ba, sai ta bishi bandakin ta ga me yake yi kwanan nan a bandaki? Sanda ta murda kofar ta shiga sai ta ganshi yana matsa (gilette shabing cream) a kan burushinsa, ya hau wanke baki da shi. A gefe kuma ya tara kumfa a baf ta omon Ariel ya shiga ciki ya soma bathing. Yana ninkaya cikin rowan. Yana mai yin soso da hularsa. As a proffessional medical Doctor, sai ta soma obserbing kwayar idanunsa, a juye take gaba daya. Sanda ta fito, zama tayi kan duwawunta a gefen bandakin a dandaryar tayal tasa hannuwanta cikin gashin kanta kamar ta kurma ihu, ta rasa inda za ta sa ranta. Sai ta ga ya fito daure da tawul ya nufi ma’ adanar kayanta ya fiddo best dinta fara sol ya soma kicikicin sakawa amma ta ki shiga jikinsa. Da ya takura sai ta tsage gida biyu, ya yi ta tsaki ya yar da ita ya dauki wandon farin boyel ya saka, tazugen na reto har kusa da gwiwarsa. sai ya kawo suit baka ya dora. Ya kawo hula zannabukar ya Saitata a goshinsa. Ta mike da gudu ta rungume shi ta baya, 


“Lamido kada ka karya min zuciya, bayan ta mika wuya ga kaunarka!!!”’. 


Kokarin rabata yake da jikinsa, bayan ya bata kyawawan mari guda biyu a kuncinta na dama. Zafin marin ne yasa ta yi baya ta yi taga-taga ta fada gado. 


Ya fice yana ce da ita, “Ki yi maza ki dama min koko da ‘yar tsala, irin wadda Hajiyata ke mini ina tafiya dasu makaranta”. 


Fitowarsa ke da wuya Isaac ya jawo mota har gabansa, haka mai tsaron lafiyarshi na tare da shi suka nufi office, kowannensu fuska muzance da shigar da Ubangidansa ya yi. Amma wa ya isa yayi Magana? 


Isaac na tuki yana sharar hawaye, lallai maganar likitocin sa ta tabbata. 


A cikin office abubuwa suka ci gaba da gudana abnormally, a fuska dai Oga lafiyarsa kalau, amma abubuwan da yake yi sun sha bamban da wadanda yake yi a baya. 


Abu na farko da ya fara yi shine, transferring gaba daya kudin dake cikin account dinsa zuwa account din Safah (na bankin GT kenan). Na First bank zuwa account din Malam Abdulkarim. Na kadarorinsa kuwa zuwa account din Fahad da Fa’ ik. 


Sannan ya rubuta wata latter ya tura ta zuwa email din mataimakin shugaban kasa mai dauke da cewa a sauke shi daga mukaminsa zai koma kasar Saudiyya da zama, a nemi wani a bashi kujerar shi ya yi retire. 


Sako ya shigo ‘Economic and Financial Crime 


Commission’ cewa ga mai girma Deputy zai shigo ma’ aikatar yanzu. 


Nan da nan kowa ya mike tsaye aka karbi mai girma Deputy. Bai tsaya ba kai tsaye ofishin Lamido ya nufa. A lokacin Lamido kuka yake yi, ya kifa kai a teburinsa. 


Har mai girma ya shigo bai san ya shigo ba, sai da ya fiddo waya yana magana da Mr. President sannan ne Lamido ya dago. 


Ko gurin zama bai bashi ba, shi ya yiwa kansa mazauni a kujerar dake fuskantar Lamidon. 


Ko gaishe shi Lamido bai yi ba balle ya mike tsaye don girmamawa. Kallonsa kawai yake da juyayyun kwayar idonsa, shine ya sassauta murya ya ce. 


“Lamido baka gane ni bane?” 


Ya ce, “Idan na sanka sai me za a yi? Aikinku ne na ce bana yi, to me ka zo ka yi min?” 


A daidai lokacin da jiniyar sojoji ta cika ma’aikatar, sai ga mai girma Mr. President ya zo da kansa. Suka kulle kansu su uku a office. 


A Turance suke magana a tsakaninsu da mai girman da mataimakinsa. Nasir sai harararsu yake, ya soma tunanin ma bari kawai ya gwara kansu dukkansu munafukai ne. 


Ai da suka ga ya mike ya nufo su a fusace daya ne ya bi ta kan daya ya cimma kofa. A nan ne kuma likitan Lamido ya danno kai, sai Mr. President ya bi ta kansa ya yi gefe guda shi da jakar aikinsa, bai tsaya ba ya tsallake shi ya cimma jama’arsa a kofar ofishin yana haki yana zazzare ido da kokarin nuna komai is normal. 


Post a Comment for "BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 1 by sumayyah Abdulkadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...