BABBAN GORO BOOK 2 KARSHE CHAPTER 11 by sumayyah Abdulkadir END - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BABBAN GORO BOOK 2 KARSHE CHAPTER 11 by sumayyah Abdulkadir END

BABBAN GORO BOOK 2 KARSHE CHAPTER 11 by sumayyah Abdulkadir END

- - Post a Comment

 BABBAN GORO BOOK 2 KARSHE CHAPTER 11 by sumayyah Abdulkadir END

Www.bankinhausanovels.com.ng 


don ba zai iya hada ido da Inna ba. Ya fiddo mota ya bata wuta jikinshi yana rawa saboda firgita da mamakin wannan magana ta ‘yar yarinya Anisa. Ya soma jera horn don Marwah ta fito amma shiru. 


Marwah da Inna kuwa ko duban juna sun kasa yi, yarinya da gaskiyarta, ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne (In ji Marwah) wadda ke tadin zuci, ba ta san cewa a fili take yi ba. 


Ba ta iya hada ido da Inna ba wadda har zuwa lokacin take tafa hannuwa tana salati, ta sunkuyar da kai ta ce da Anisa. 


“Ki daina kuka, ki kwantar da hankalinki, anyi mai wuyar tunda kin zama matarsa halalinsa wadda Allah Ya dora hakkin duk wadannan abubuwa da kika lissafo a kansa. 


Amma yanzu baki da passport da biza, balle kuma ba dadewa zamu yi ba asibiti za ni. Na yi miki alkawarin da zarar mun dawo tare dake zamu wuce Abuja”. 


Ta dan tsurawa Marwah ido jawur tana kallon ta, ashe tana da kirki? Take fadi cikin ranta. A sanyaye ta yi kasa da idonta ta ce, “Ba komai, ku je Allah Ya kai ku lafiya Ya kuma sauke ki lafiya’. 


Haka suka kamo hanya ma’auratan, ba mai kallon dan uwansa ba mai ce da dan’uwansa komai, har suka shigo Kaduna. 


Suka shiga a gurguje suka gaisa da Mami da Hajiya Maama, ko zama basu yi ba, Mami ta hada musu abin karin kumallo a kwandon abinci, aka sa a kujerun bayan motar suka mika basu tsaya ba 

sai a Abuja. 


Haka ta ci abincinta ba ta kula shi ba, shima bai tanka mata ba, domin ya hango rikici mai yawa a cikin kwayar idanunta. 


A gidansu Safah suka yada zango, suka yi sallolin da basu yi ba a guest room, suka yi wanka suka ci abinci, a lokacin ne suka samu nutsuwa. Lamido da amaryarsa suka same su a guest room din ake ta hira, amma fuskar Marwah babu walwala babu bakinta cikin hirar, har Lamido ya gane. 


Ya ce, “Yar gidana ya aka yi ne? Garin ko jikin?” Tana girgiza kai cikin takaici. Ta ce, “Babu ko daya’’. 


Ya ce, “Na ganki ne rather-moody???”. 


Ta ce, “Yau da gobe ba ta bar komai ba”. 


Ya ce, “Brother na ne ko? Yau bai yi messaging kafar ba halan? Gata nan ta suntume”. 


Ta kyabe baki, 


“Yaushe ka zama dan’uwannasa? Ga _ dai ‘yar’uwarsa can amaryarsa ya baro a Zaria tana jiran shi mu dawo su barje amarci, har tana gaya min magana zan dauke mata miji, amma ku ya yi 


shiru ya ki fada muku”. 


Safah ta zaburo, “Yaya Deen da gaske aure ka yi?” 


Idanunshi na kan labarun CNN ya ce, “Daurowa ta yi”. 


Sai Lamido ya zungure shi, “Ka ce mun yi ekual, me ya kai cancada-cancadan mata dadi a duniya?” 


Ba tare da ya dauke idonsa a kan ‘Mu’azzam 

Kanti’ ba ya ce, “Babu abokina, tunda an hanani ‘yan’ uwantakar ka. Sai na abotake ka. Tana nan (sweet 16) kamar za ta mutu don soyayya”. 


Suka tafa suka tintsire da dariya. 


‘Yan biyun suka fusata kowacce ta soma huci kamar mesa, mai cikin saura kadan ta fadi saboda mikewar bazata da ta yi. 


“Idan baka koma ka daukota ka tafi da ita ba baka cika namijin ba. Ai ina lura da kai kana sonta kake mata wani muzuran banza. 


Ni dai na gaya maka, daga ranar da ka kama farcenta da sunan auratayya wallahi-wallahi na bar gidanka kenan”’. 


Mikewa ya yi ya riketa a gabansu ya toshe masifaffen bakinta da nasa. Kissing yake passionately kamar babu wani mahaluki awajen bayan su. Lamido ya rufe ido da tafukansa, cikin lalube ya lalubo hannun matarsa dake kusa dashi ya finciki hannun ta suka tafi. 


Tuni bakin masifa ya mutu, sai dai Allah ya jikansa, ya koma sambatu na soyayya mai ban mamaki a tsakanin ma’auratan. Daga karshe sai ta koma kuka tana rokonsa kada ya karya zuciyarta, kada ya hada jiki da kowacce mace a duniya bayan ita, zai karya mata zuciya daga ranar da hakan ta faru. 


Ya taimake ta ya bar Anisa ta ci gaba da zama kamar Rabi’a, don za ta yi mata raini na karshe duk ranar da ta ga gadon barcinta. (Anya uwargida baki so kanki ba)? Takori. 


Basu dawo cikin hayyacinsu ba sai karfe goma da rabi na dare. Wata irin sassanyar kaunace suka 

gudanar a yau mai tsayawa a zuci. Sun yarda, sun amince, rabuwarsu ko na minti daya na nufin shigar rayuwar kowannensu cikin garari. 


Alkawuran da Zahraddeen yai mata a yau ba za ta taba mantawa dasu ba. Shin wane irin miji ne cikin dubu ubanta ya zabo ya ba ta? Son da take masa, sai dai ya bi bayan wanda mahaifiyarsa da Ubangidansa ke masa. 


Shi kuma son da yake mata, ya zarta wanda ya yiwa Safah tun daga ranar da ya dora hannu a jikinta, ya dauki budurcinta cikin GIRMA da girmamawa. 


Safah da Lamido su suka kaisu har Airport, basu dawo gida ba sai da suka ga tashin jirgin su. Suna tafe a hanya Lamido na tunanin nashi borin dake jiransa wanda ya zarta na Marwah mai karamin kishi. 


Domin dai gobe ne Danejo za ta dawo daga boyon da ya yi mata a Sydney (Australia) ya yi auren sa ya barje amarcinsa. 


Yara dama suna makarantar kwana (Nigerian Turkish) da ke Kano, anguwar Tarauni. Itama Safah ya gaya mata gobe ne Maman Fahad za ta dawo. 


Sai ta samu kanta cikin rashin sukunin zuciya tun daga lokacin. Har suka iso gida daga Airport bai ga fara’ ar amaryar tasa ba. 


Ya girgiza kai, “Mata! Mata!! Mata!!! Sai a barsu, tunda burinsu su haramta maka abin da Allah Ya halatta maka saboda son kansu. 


(Don Allah mu dinga tunani, ko zamu yi kishin kada mu yi wanda zai dagula nutsuwar maza

jenmu, haka Allah ya ce suyi, don su tserar da kansu daga dattin zina da cikar kamalarsu da mazantakar su, ba yin kansu bane, ba kuma umarnin kansu bane, na UBANGIIJI ne). 


Yana shan tea a gefen gado yana satar kallon ta, sai wani ciccin magani take tana doddojewa. Ta dauki filo ta jefa a sofa ta yi kwanciyarta, wato (yau tunda matarka za ta dawo ba zan hada makwanci da kai ba). 


Sai ya girgiza kai, ya aje kofin, bai bita yana lallashinta ba sai ya zuba mata ido. Ya yi wanka yai sallah, ya yi lazimi yana sauraron kira’ar Abdurrahaman Sudaith cikin ‘yar kankanuwar na’ura cikin Suratul Nisa’i. 


Yana jin umarnin da Ubangiji yake yiwa mata da alfarmomin da yai musu, da umarnin da Ubangiji ya yi a kansu wajen rabon gado. 


Amma sun ki hankalta. Da ta san tashin hankalin da zai shiga a gun Danejo da ta sassautawa tata zuciyar ta tallafe shi. 


Ya koma ya kwanta shi kadai a gadon ya yi light up, amma ya kasa barcin. Yaya ga mata cancadediya Allah Ya bani zan kwana gwauro? Barcin nata ma ai na karya ne don ta kasa. He is someone she lobe and respect most! Idan zuciyarta ta jure gangar jikin ba za ta iya jurewa ba. Don haka ne da ta ji ta a hannunsa ya maida ta gadon sai ta mika wuya ga bautar Ubangiji. 


Da safe tana cikin bargo tana rama barcin da Nasir bai barta ta yi ba a daren jiya baki dayansa (throughout), ta ji alamar shigowar sako (tedt) 

cikin wayarta. 


Lokacin Lamido ya tsufa a office, domin 8 0’clock a cikin office take mishi kafin ya rage ayyuka ya tafi taren Danejo wadda za ta sauka karfe hudu na yamma. 


Ta mika hannu ta dauki wayar ta duba. 


“We are in a train between Suisra and Paris, lub you ma Sis....”. 


Nan ta gane sun sauka lafiya. Ta mayar mata amsa da 


“Lub you too Sissy....... Allah Ya sauke ki lafiya”’. 


Sannan ta mike ta shiga wanka. 


2K 2K KK 


L amido da Danejonsa kwance a bayan mota ‘Ferrari has come’ Isaac direbansa na kwarara gudu dasu a kan manyan titunan Abuja. Lamido rike da hannun Danejo, ita kuma ta kwace hannunta kada su Isaac su ce miji ya kama hannunta. Ire-iren wadannan kauyancin na Danejo ko shekara sittin ta yi a birni irin haka ba za ta daina su ba. 

Da zumudinsa yake mata barka da zuwa, ya ta baro Sydney? How does it look like? How does she feel libing there? Don shi bai taba zuwa Australia ba. 


Ire-iren tambayoyin da yake mata kenan cikin Turanci tana mayar mishi da Fulatanci, don ba ta sO ya ci gyaranta ko ya yi mata muguwar dariya in tana kwabo Turanci. 


Sai magariba suka iso gida. Safah ta daga labulen dakinta dake saman bene sakamakon horn din Isaac da ta jiyo. 


Gumsu kurtun soja ne shi ke kula da gidan Lamido, shi ya bude get Isaac ya sanyo hancin motar cikin gidan 


Ya kame ya yiwa oga barka da zuwa, ya amsa. Kasancewar harabar gidan tarwai take da fitilu masu tsananin haske kamar kana Dubai, ya sanya ta ga fitowar Danejo da Lamido. 


Fara sol mai kyau gajeriya mai dan jiki. Ta ce, Lamido na da mace mai kyau haka me ya gani a jikinta ita baka ya kasa sukuni sai da ya same ta? Ta yi saurin sakin labulen a lokacin da Nasir ya dago suka hada ido. Ta fada a gado tana numfarfashi kamar wadda ta yi gudun famfalakin mita goma. Kai kishi bala’i ne, ya Allah Ka rage mana. 


A can side din kuwa Lamido sai nan-nan ake da Danejo, sai da ta ci abinci ta koshi, sai dai babu alamar Daddy (yadda take kiran shi saboda su Fahad dake kiranshi da hakan). Ya yi missing din ta, dan ko rungumarta bai yi ba sai tadi yake ta zuba mata na mutanen Taraba. 

A yadda ta san Daddy in ta yi tafiya irin wannan ta dawo ya fara barin jiki kenan kamar wanda ake kadawa gangi. 


Yau dai Daddy hirar su Fahad kawai yake yi, ita ta sauke kunya ta soma mishi abin da ta san yana so, amma Daddy ko gezau. 


Cewa ma ya yi, “Bari Dijah, am not in the mood wallahi’. 


Ta ce, “In baka cikin mudun ni ina ciki, watanni biyu ba kwana biyu bane. Na yi kewarka Daddy, na yi kewar soyayyarka yadda baka zato, don Allah Daddy”. 


Tausayi ya kama shi ya rungume matarsa don sauke hakkinta da Allah ya dora masa, amma ba don yana cikin sha’awa ba. 


Wayyo! Dole mata su ki kishiya, ba kishiyar suke gudu ba, wacce iri za a kawo musu shine abin tambayar. Ya take? Kowacce mace da irin baiwar da Allah ya yi mata. 


A yau EFCC Lamido ya tabbatar mata masu sunan mata Allah ne kawai yake halittarsu, ba za ka taba bambancewa a fuska ko a launin fatar jiki ba. 


Ji yake kamar yana cin tuwon tsaki (biski) ba tareda miya ba, ashe shi da, (prebiously) maza ya rako duniya bai san wace ce diya mace ba. 


A daddafe aka daddage aka farantawa Danejo saboda kyakkyawar zuciya irin tasa. Hakan bai sa zuciyarsa ta yi kudurin wulakanta Danejo ba. Tausayinta ma ya ji sosai. 


Sai da ta nutsu take nazarinsa, gaba daya ya canza kamar ba shi ba ya daina dokin ta. A 

lokacin ma shi hankalinsa ya koma ga amaryarsa wadda ya baro tun safe tana barci, wunin yau zungur bai ganta ba, bai neme ta a waya ba, ko daren jiya bakidayansa. 


Danejo ta taso ta dawo jikinsa ta zauna ta yi shiru. Ya juyo ya dube ta tausayi ya rufe shi, nata da nashi baki daya. 


A haka ya karar da samartakarsa ta shekaru goma a baya da macen da ba ta isa ba a sanyata a jerin mata, bai taba yin zina ba, balle ya san bambanci sai ‘yan abubuwan da ba a rasa ba, wadanda sharrin kudi da mukami ke sawa. 


Ya ce, “Danejo ki saurareni, na yi aure bayan tafiyarki’. 


Sai ta kyalkyale da dariya, “Daddy ho! Yau kuma da wannan za a tsokane ni?” 


Fuskarshi serious ya ce, “Am not teasing you Madam, and I’m not joking. Abin da nake so shine, ki zama uwargida ta gari abin koyi ga na kasa dake. 


Sai kin rike girmanki zan samu kwanciyar hankali madawwami. Kinga dai ban hada ku ba, kowacce na side dinta balle ta yi kukan daya ta yi mata ba daidai ba. 


Safah ba ta da matsala, am sure za ta zauna dake lafiya ta baki girmanki, ke kuma ki rike girman don Allah”. 


Danejo ta yi kukan kura ta wawuro fitilar jikin gado ta maka masa a baya. Ta sake yin wani kukan kuran ta bishi ta shake. 


“Daddy sai dai mu kashe juna kafin daya ya 

kashe daya........ Ya kama hannuwanta ya rike gam-gam, sannan ya zuba mata wani lafiyayyen mari a hagu da dama, sakamakon wata azaba da ya ji a kwakwalwarsa a dalilin takalminta mai tsini da ta kantara masa a tsakar ka. 


Marin ya shigeta sosai, don daina ji da gani ta yi na wucin gadi. 


Ya mike ya fita bayan ya kulleta a dakin ba tare da ya zare mukullin ba. Sassan Safah ya nufa jini na diga daga kansa. 


Tana kwance a falo ta rungume filo ta kashe fitilar falon sai hasken talabijin dake aiki, sai danjar A.C dake dan haskaka falon. 


Don haka ba ta ga halin da yake ciki ba, ita ma bai yi mata magana ba kai tsaye ya wuce toilet ya saki shower a kansa, yana ganin jinin jikinshi na bin ruwa. 


Jiri ya ji yana kokarin kama shi don haka dole ya nemi taimakon ta, duk da ya lura ita ma nata buhun bala’in yana nan yana jiransa, sai dai ya san ba na hauka da rashin imani irin na Danejo ba. Ita iyakar nata fushin shine ta ki yi masa magana ko ta raba makwanci da shi. 


Yana dafe da bangon bandakin ya ce, “Ki zo ki taimaka mini ina bleeding........ ”, 


A sukwane ta mike ta kunna fitila, ta ga Lamido tsamo-tsamo cikin jini. 


Ta ce, “Subhanallahi! Nasir (karo na farko da ta kira sunansa na ainihi) ‘yan fashi ne suka shigo?” Girgiza mata kai ya yi kwayar idonshi na shagidewa za ta bace daga cikin idanunsa. 

Akwatin taimakon farko (First Aid Bod) dinta ta nufa da gudu ta kungiyar (red cross). Kafin ta iso har ya kai kasa. Ta yi azamar tallafo shi ta rungume a kirjinta ta fashe da kuka. 


Kokarin tsaida jinin ta fara yi, yana bukatar dinki a kan domin ya yi rami sosai na dunduniyar takalmin mace. Kana iya hango kwakwalwarsa da jinni ya lullube. Don haka dole a dangana da asibiti. Bata taba shiga tashin hankali irin na yau ba. 


Taga (window) ta nufa tana kiran “Isaac...! Isaac...!! Gumsu”. 


Isaac wanda ke kasan benen yana shan taba ya jiyo ta, amma Gumsu bai ji ba don yana can yana baiwa karensa abinci. 


Sai ya haura da gudu yana fadin “Madam....Madamm, gani nan what happen?” 


Da ya shigo falon kara yayi, “aaaah! Oga!!! Sai ya kinkime shi ya yi kasa yana nishi kamar zai kifa, don ma yana da karfi. Bayan mota ya yi, kan ka ce meye wannan ma’aikatan gidan duk sun fito suna neman ba’asi, wasu sun ce saidai in bullet ne ya huda masa kai, to amma waye mai pistol a cikin su? Cikin kowannensu ya duri ruwa. Isaaac bai bi ta kansu ba, yayi asibiti da ubangidansa shida escourt dinsa yana tafe yana ta kiraye kirayen wayar Likitan Lamido yana kuka riris yayi asibiti da shi ba tareda yasan bayanin da zai yiwa likita ba. Haka likitoci suka rufu a kanshi don ceto lafiyar shi data kwakwalwarsa. 


Mu karasa a littafi na 3. Kuma na karshe insha-allahu. 


Post a Comment for "BABBAN GORO BOOK 2 KARSHE CHAPTER 11 by sumayyah Abdulkadir END"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...