BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 9 by sumayyah Abdulkadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 9 by sumayyah Abdulkadir

BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 9 by sumayyah Abdulkadir

- - Post a Comment

 BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 9 by sumayyah Abdulkadir


lahi ba ta san mene ne a cikinta ba, ba ta san ya take ba. 


Tunda ta taso cikin gata ta taso, ba kwaba ba hantara, sai nasiha a inda aka ga za ta kauce hanya. Ta taso cikin rayuwar ‘yanci da sukuni. Mene ne kalubalen dake cikin rayuwar aure? Shine ba ta sani ba. 


Mami ta tsawatar ta tsoratar da ita sosai. Ta ce da ita, “Wata sabuwar rayuwa za ki fara wadda ta bambanta da wadda kika taso a ciki. 


Ita wannan akwai hakkoki da yawa a cikinta na wasu mutane masu yawa da suka hau kanki, wato uwar miji da ubansa, yayyensa da kannensa, kishiya da ‘ya’yansa. 


Duk dunkulesu za ki yi su zama naki, sannan ne za ki samu zaman lafiya a rayuwar aurenki. 


A cikin ita wannan rayuwa, baki da iko da kanki sai abin da mijinki ya karkata ki a kai, wato ya yi miki izini. 


Na san dai ba zai zamo mai tauye miki hakki ba, amma fa ba ke kadai ba ce. Dole ki bi tsarin a yadda kika same shi. 


Idan kika ce za ki kawo sauyi, ba lallai abokan rayuwar naki su karba ba. So ki karbi RAYUWA A DUK YADDA TA ZO, ki kasance mai tsarkakakkiyar zuciya a kan kowa. Sauran al’amura ki barwa ALLAH!” 


Hawayen dake makale cikin kwayar idanunta suka mirgino a hankali masu dumi. 


Lamido ya gigice, ya riko hannunta sosai yana share mata hawayen da habar babbar rigarsa. 

“Na shiga uku ni Lamido!. Taimake ni ki hadiyesu kada al’umma ta ce bakya farin ciki don Allah Safah!” 


Kwanciya ta yi sosai a kafadunsa da suka zamo waigi a gareta daga faduwa kasa. 


A hankali ta ce, “Mami....ni dai wajen Mami zan koma....”. 


Ya ci gaba da share mata hawayen kamshin jikinsa na sanyaya mata zuciya. 


Ya ce, “Wallahi ko gobe kike son ganin Mamin zan kai ki. Ni dai rokona gareki ki mai da hawayen nan kada abokaina su ce bakya so na....” Ba ta san sanda ta yi murmushi ba, shima ya shiga taya ta murmushin. Suka soma takawa zuwa cikin hall din. 


Ai kuwa masu mujallar Obasion da Delight, ‘yan jaridar New Nigeria, Daily Trust, Triump, Leadership, Weekly Trust, Present Nigeria, NTA Abuja, BBC London (Abuja Branch), ma’ aikatan gidan rediyon tarayya da sauransu suka taru suka ce da wa Allah Ya hada ku ba da mu ba??? 


Taro ya gudana kamar yadda aka tsara, cikin tsari da ilimi. Babu hayaniya. Karfe goma sha biyun dare garin Abuja hadari ya gangamo, sama ta daure kitikif da bakin hadari aka soma tsawa da walkiya da guguwa mai karfi. 


Zuwa lokacin da yawa jama’a sun tafi, wadanda angon ya saukar a hotel din duk sun bi matattakala da lifta sun nabba’a a dakunansu da aka kama musu. 


Mutanen Yola ne da na Kaduna, sai abokan huldarshi na wasu garuruwan, irin Legas, Fatakwal, 

Bayelsa, Benue da sauransu. 


Akwai kuma jama’ar sauran kasashe da dama da suka zo takanas domin halartar liyafar cin abinci, duk sun yi masaukinsu. 


Angon ne da amaryar kwance a bayan mota ‘Opel - Astra’, wani kurtun soja ne ke janta. Ko murmushi baya yi fuskarsa murtuk kamar hadari. A gaba mai kula da lafiyar Lamido ne ya sha bakar kwat wadda harsashi baya huda ta sai muzurai yake kamar ya ci babu, yana fama da wareless da na’urori kanana. 


Wannan lokacin Safah fuskarta a bude take ba kamar sanda aka kawo ta ba, tana kallon yadda wiper ke kore ruwan dake sauka da karfinsa a kan gilasan motar, har da karar kananan kankara, ta ko kasa hada ido da Lamido. 


Shima bai takura ta ba, tunda ya fahimci tana cikin yanayin da bai taba ganinta a ciki ba. Kamar bata san shi ba, zuciyarta Imam take tunawa ranar liyafar dinar aurensu da suka dawo yana tambayar Zahraddeen ko zai rage zafi su zaga otal? 


Daga baya duk sanda ta tuna wannan maganar sai ta yi dariya ita kadai, idan ta tuno yadda duk tsiwar su bakinsu ya mutu babu wacce ta ce uffan. Allah sarki, ashe iyakar auren kenan. Daurin aure da saki. To amma waye musabbabin? Ita ce. “Kina auren wani kina tunanin wani?” 


Wani bangare na zuciyarta ya tunatar. A take ta soma jan istigfari, sannan ta fashe da kuka tana rokon Allah Ya yafe mata kuskurenta. 


Abin fa ya soma taba ran Lamido, ya rufe wayar 

hannunsa ya dube ta sosai, ya ce, “Mami dai?” 


Ta girgiza kai. Ya sake cewa, “Kenan ba a farin ciki da aurena ni wane irin mara sa’a ne?” 


Da sauri ta girgiza kai. Ya lalubo hannunta ya rike cikin nashi, fatar hannunta kamar auduga don taushi, ga wani santsi da take yi. Bai san sanda ya kai fatar bakinshi gare ta ba, ya soma tsotson bakinta kamar zai tsinke harshen gaba daya ya huta. 


Irin wannan kissing bai taba yi a rayuwarshi ba. Domin dai Danejo bakinta bai taba daukar hankalinshi ba saboda mayuka da take amfani dasu na canza fata marasa dadin kamshi da cin uban jambaki, sun sanya bai son sakin jiki da dukkan gabbanta. 


Amma a nan wani irin cool kamshi ne ke fita a wasu irin soft-thin lips, da aka tausasa da wet-lips mai dadin kamshi kamar yana tsotson hubbabubba, cingum din nan mai dadin kamshi. 


Ita ce ta kwaci bakinta da kyar sakamakon kashe motar da direba ya yi, gilasan motar suka yi kasa gaba daya, wani irin sanyi da kamshin furanni mai ni’ima ya bakunce ta a harabar gidan gaba daya, zuwa lokacin ruwan ya tsagaita amma bai daina zuba ba. 


Ai suna shiga falon farko bai bari ta kuma takawa ba, daukar ta ya yi ya bi matattakalarsa, bai dire ta ba sai a lafiyayyen gadonsa. 


Da kanshi ya hada mata ruwan wanka, tsugunnawa ya yi daidai gwiwoyinta ya cire mata sarka, dan kunne da zoben hancinta irin na Kanuri, ya ajiyesu a gefe. 

Ya tayata rage nauyin leshin jikinta, ya zama sai doguwar riga mai santsi mara hannu (shimi), ya ja hannunta har toilet. 


Sai da ya tabbatar ta shiga kwamin sannan ya nufi kitchen da kansa, shi kansa kitchen din a cikin falon saman yake. 


Ya duba cikin micro wabe ya ga aikin da yasa kukun sa Abraham ya yi ya yi shi da kyau da ban sha’awa. 


Wato wani Dawisu (Peacock) an gashe shi irin gashin nan mai ruwa-ruwa da ya ji albasa da tumatir, har da dan attarugu. 


Sai ya dauko shi baki daya ya dora a katon fadika-mutu, ya dauko cokali mai yatsu, wuka, pepper, chips and scottish salad da ruwa da jusi ya koma bedroom din. 


Ya samu har ta fito ta yi shafa’i da wutri, ba ta kai ga tashi daga sallayar ba, sai ya ajiye gabanta. Ta dago ta dube shi idanunta sun koma kanana saboda kuka, sai zafi suke mata. Ta ji duk tausayinshi ya kama ta. 


A hankali ta furta, ““Sannu da kokarv’. 


Sai ya yi murmushi kawai yana tsiyaya lemun Prime Lady cikin tambulan mai garai-garai, ya sa mata a baki. 


Karba ta yi ta sha sosai, don ba ta san ma tana jin yunwa har haka ba. Hatta naman shi yake yagowa da fork yasa mata a baki. 


Wannan kulawa da kyautayi ga babban mutum irinsa ya taba zuciyarta. Ba ta san sanda ita ma ta zage ta soma ba shi a bakin ba. 


Sai da suka tashi da Dawisun nan baki dayansa 

sai kasusuwa, don kowannensu bai san cewa ya tara yunwa ba sai yau. 


Abubuwa da yawa sun biyo baya, wato sallar neman albarkar aure. Hira mai dadi da karin fahimtar juna. 


Don haka da al’amura suka fara nisa ba ta da karfin gwiwar ko karfin zuciyar da za ta iya cutar da mijinta mai sonta, ashe ita ma tana da muradi irin na kowanne lafiyayyen dan Adam??? Batasan hakan ba sai yau dinnan. 


Sai dai a matsayinta na farin shiga, lamarin bai zo mata da sauki ba. Da ta san haka ne ma ai da ba ta yi saurin ba da kai bori ya hau ba. 


Karfe hudu da rabi na asubah amma dukkaninsu basu yi barci ba. Da idanunta ta ga Nasir yana share hawaye, ba kuma ta san dalilin zubarsu ba. Sannan ya mata kwarjinin da ta kasa tambayar shi. 


Tana daga kwancen take gaya mishi taimakon da zai yi mata; hada ruwan dumi da dettol a jacuzzi, paracetamol da ampicilline a first-aid bag dinta. Hakan ya yi, sai da ta fito wankan ta dora alwala, ya ba ta fresh milk ta sha, sannan ya ballo maganin ya ba ta kamar yadda ta yi zato ba hakan ce ta faru ba. 


Domin ta yi tunanin za ta yi regretting baiwa Lamido budurcin ta, ba ma shi ba, ko wani namiji sabanin IMAM. 


Sai hakan ba ta faru ba, har zuciyarta farin ciki ta yi da Nasir ya dauki barginity dinta da ta dade tana tattalawa Imam, domin ya cancanta. 


Ta kuma tabbatar abin da ya sa shi kuka kenan. 

Shi ya ja su sallar asubahi saboda babu masallaci a nan kusa dasu. 


Ko da suka koma suka kwanta don rama barci, hakan bai yiwu ba, saboda sabon fejin da Lamido ya bude gaba daya ya kara gigita ta. 


Haka ya ci gaba da shayar da ita mamaki, cikin fannonin kauna da soyayya daban-daban, da ba duk maza Allah Ke yiwa baiwarsu ba, don ita kam ko a litattafai da fina-finan Turawa bata taba yin karo da caring and lobing husband irin EFCC Naseer Lamido Abdulkarim ba. Ko kuma don 


tana son shi ne ta ga hakan? Ba zan iya cewa ba!!! 2K 


MUTANEN RUGAR ARDO I na Marwah ne da angonta Zahraddeen har aka yi biki bamu ji duriyarsu ba? To basa nan, suna cikin wani jeji gabashin garin Kaduna, cikin karamar hukumar Lere, suna jinyar Yayar Inna Binta da suka tarar babu lafiya rai a hannun Allah, dauke da cutar kansar nono (breast cancer). Saidai a kwantar a tayar. Sannan duk wani roko da lallashi sunyi don su taho da ita asibiti amma ta ki, ta ce wa’adinta ne ya zo, ba kuma taso ta mutu a ko’ina sai mahaifarta. 

Sun kasa tahowa su barta, kuma ta yi rantsuwa ko sun dauke ta ba cikin hayyacinta ba sun kaita an yanke mata nono Allah Ya isa ba ta yafe ba. 


Idan kaga Marwah da Zahraddeen a wannan jeji sai sun baka tausayi, sunyi wujiga-wujiga dasu. Inna Binta kam a tsaye take kan ‘yar’uwarta. Ba yadda ba ta yi ba su tafi su kyale su sun ki, ko don aikin Zahraddeen. 


Ya ce, ai cikin hutu yake, ya dau hutun shekara. Shi Daddy kuwa ba a magana, kafafunshi sunyi futuk da kaushi da faso, saboda yawo ba takalmi cikin rugage. 


Ko sau dubu uwar ta sa mishi takalmi sau dubu zai haka rami ya binnesu ya zo ya ce mata bai gansu ba. 


Shi kuma Daddy ba don komai yake hakan ba sai don ganin sauran yara na rugar tsararrakinsa da yake wasa dasu ba a sa musu takalmi, to shi don me za a sa mishi? 


Bukkar Badijo guda biyu ce, daya ta marigayin mijinta ce, daya tata ita da jikanyarta Anisa, wadda yanzu ta zama budurwa, domin sa’ar Rabi’a ce. 


A daya Bukkar ne Zahraddeen da matarshi ke ciki, dayar da Inna Badijo ke kwance ciki nan Inna Binta, Daddy da Anisa ke ciki. 


Sai dai fa Anisa sam ba ta shiri da Marwa, tana kullace da ita a kan labarin da Rabi’a take ba ta sanda suna makaranta na wulakancin da take musu. Duk da ita Rabi’a abin ya wuce a ranta har ta manta. 


Ko dansu Daddy bata kulawa, kiyayyar uwarshi 

ta shafeshi, kai ita a dan tsukin nan ma wata muguwar soyayyar Zahraddeen ke cinta a zuci. Duk da ta san ba ta kai matarsa a komai ba, amma ai dan’uwanta ne, zamansu waje daya yanzun ba karamin barazana ya zamewa rayuwarta ba. 


Anisa kullum sai ta tafi fadama ta wuni don kar ta ga Zahraddeen. A kwanakin ta daina cin abincin kirki, girkin ma da take musu ta daina sai Maman Daddy ke yi. 


Zan so ki hango min Marwa Dan Kasa diyar Aliko a gaban murhu suna hura itace ita da Zahraddeen, idanunsu na tsiyaya. 


Amma hakan bai sa ta ki yi musu girki mai kyau ba, naman zabbi da kaji gashi nan sai sun ture, don haka take sarrafashi nau’i-nau’i, wataran grilled (a turmi), wataran minced, wataran soya, wataran farfesu, wataran gashi (baking) a garwashi. 


Ta zubar da komai ko a lahira ta zabi ta zauna da mijinta ko da dan kanzo ne, balle ma shi bai daina gayunshi ba ita din ce dai duk ta sakwarkwace, amma ba abin da ya dame su. Wasa-wasa sai gasu sun kwashi wata biyu a Rugar Ardo, a wani dare Inna Binta da Badijo suna shirin kwanciya, Badijo ta fara shakuwa ta juya tana kallon ‘yar’uwarta. 


Ta ce, “Binta ki yi min alfarma ki sa Dini ya auri Anisa, wannan shine burina na karshe a rayuwar duniya”. 


Inna Binta ta yi zugum tana jinjina maganar, ko ita din ta so haka a baya, amma ban da yanzu da 

Marwah ta gama siye zuciyarta da kyawawan halaye da kauna ta hakika ga mijinta. 


Sun gina rayuwarsu ta zamo mai ban sha’awa abin alfaharin kowadanne iyaye, ba za ta so ta zama silar ruguje farin cikin dake cikin rayuwar aurensu ba. 


Haka ba za ta iya bijirewa bukatar Yayarta ba, musamman a wannan hali na rai kwakwai-mutu kwakwai da take ciki, ba za ta mance hidimar Badijo ga Zahraddeeni ba a lokacin da yana yaro. Ita ta karbi haihuwarsa, ta yaye shi, ta yi masa shayi (kaciya) da sauran hidimomin da ba za su lissafu ba. 


To amma wane bayani za ta yiwa Marwah da Zahraddeen su fahimta ba ta da hannu ko niyyar shiga rayuwarsu? 


Dabara ce ta zo mata yadda za ta fita ko ba sabulu. 


Mikewa ta yi tsaye ta ce, “Jirani Badijo”. 


Ta dauki fitilar aci-bal-bal bayan ta sauke Daddy bisa katifar auduga wanda ke kwance cinyarta yana barci. 


Ta fito ta nufi bukkar su Zahraddeen, ba ta shiga kai tsaye ba, su ma sun kunna aci-bal-bal din amma sun rage haskenta tabbacin sunyi shirin kwanciya. 


Sallama ta yi tare da cewa, “Kun kwanta ne?” Daga ciki har suna hada baki wajen cewa, “A’a, Inna muna dai shirin kwanciyar ne”’. 


Ta ce, “To ku zo dukkan ku Badijo ta yi magana wadda ta girgiza ni, shine nake so ku zo ku tayani jinta don ku tafi shafa ba ni ba”. 

Gaba daya suka fito suna tambayar me ya samu Badijon? Zahraddeen har yana karo da asabari sabida tsayinsa ya zarta na ‘yar kofar bukkar. 


Ta ce, “Rikici na tsufa da zafin rashin lafiya kawai’”. 


Suka ce, “Har da zafin ciwo”. 


Dukkansu suka gurfana gaban Badijo wadda ke kwance kan katifar alawayyo. 


“Badijo ga Zahraddeenin ki gaya mishi da bakinki tare da matarsa, na shaidesu kan cewa su dukkansu masu biyayya ne a gare ni, idan na furta aikatawa ce kawai tasu ko suna so ko basa sO. 


To amma bana so in takura musu don suna min biyayya, duk abin da ya shafi Dini ya shafi matarsa, don haka ki gaya musu da bakinki”. Badijo ta ce, “Ai ba sai kin yi haka za ki tabbatar min matar Dini ta shanyeku ta siyeku ba, kamar yadda nake jin labari, saboda su masu arziki ne. Ta yadda har ba za ki iya yin sirri dani ba a matsayina na shakikiyarki, kuma ba za ki iya yin umarni ga danki ba, sai kin hada da yardar matarsa. 


Duk wulakancin da ta yi muku kin shanye kin manta saboda suna da kudi. Kai Dini, saurareni da kyau bar ganina rai a hannun Allah, har yanzu ina nan a Badijo na, mai bala’i kuma mai kirki ga wanda ya yi mata kirkin. 


Na baka auren Anisa na bawa uwarka amanarta, ko bayan raina ka wulakanta ta marainiya ce Allah zai saka mata, ka karba ko baka karba ba?” Da sauri ya ce, “Na karba Badijo, ni dai fatana 

Allah ya baki lafiya. Amma in kina so in ji dadi, to ki goge fassarar da kika yiwa Innata da mai dakina. 


Baki taba yin kalaman da suka yi min ciwo irin wadannan da kika furta yanzu ba. 


Innata mai sonki ce da girmamaki Badijo, babu ranar Allah da za ta fito ta fadi ba ta ambace ki ba. Tun kan ki yi wannan hasashe Innata ta yi a kan Anisa, ni ne na yiwa maganar birki. 


Mai dakina kuwa kome kika yi hasashe a kaina game da ita kin yi daidai. Ta shanyeni, ina gudun bacin ranta, tana da arziki, ni bawanta ne kuma mai kula da dukiyarta. 


Amma fa ba ta fi karfina ba, sannan karkashin ikona take. Don haka kar ki kara wannan magana’. 


Kunya ta kama Badijo, sai ta hau kame-kame, “Ai nima na san hakan uwar taka ce ta bani haushi’. 


Suka mike suka yi bukkarsu, ko kallon shi Marwah ta kasa. Katifarta ta bi ta kwanta ta soma kuka. 


A gefen katifar ya zauna kawai kansa a kasa ya harde hannayenshi guda biyu, kukanta na cin zuciyarsa. 


Ya juyo ya kama hannunta ta fizge, ya bita ya kwanta a bayanta ya rungumeta ta soma kicikicin kwatar kanta, amma karfin ba daya ba, sai kici-kicinta ya ba shi damar rungumeta sosai. Ya kanainayeta. 


Ta bishi da cizo da duka duk ya shanye bai cika ta ba, sai da ta yi mai isarta ta gaji ta kyale shi. Ta 

ci gaba da kuka a hankali. 


Sai ya yi amfani da wannan damar ya shayar da ita farin cikin da bai taba shayar da ita a rayuwar aurensu ba. Shi hawaye ita hawaye. 


Ba kuma don komai yake hawayen ba sai don tunawa da DADDY, da alkawarin da ya yi masa na karin aure, wannan ne dalilinshi na amsa maganar Badijo farat daya, amma ba don abin da ta furta ba (jan idonta ko masifarta). 


Sai da ya bari suka samu nutsuwa sosai, sannan ya soma yi mata bayanin hujjarshi da dalilinshi na auren Anisa don ya cika alkawarin Daddy ne ba don maganganun Badijo ba. 


Ita dai ba ta yi magana ba, tunaninta Badijo ba ta sonta kawai, kuma wannan yarinyar mai kafirin girman kan tsiya da nuna mata kiyayya, ita ce Zahraddeen ya amsa zai aura. 


Duk iya kokarinsa ya yi wajen lallashi, ban baki da alkawarirrika amma Marwah uffan ba ta ce mishi ba. Ita gara ya auro ko mai digiri uku ce da wannan yarinyar ‘yar rainin hankali. 


Ya ce, “To shi kenan, tunda duk bayanin da na yi miki kin ki yarda dani. Wallahi yarinyar nan ko farcenta ba zan taba kamawa ba, don ni kaina karshen raini ne hakan a gare ni. 


Gobe zamu bar garin nan tunda Badijo ta bata miki rai’. 


Wannan karon ne ta yi magana, “Ni na gaya maka? Kai ka bata min rai ba Badijo ba”. 


“Da na yi me?” 


“Da ka yi maza ka amsa mana babu tunani babu shawara kamar dama kiris kake jira. Ai ko rashin 

shiga sabgar yarinyar nan da kake na san sonta kake, ita ma kuma munafuka sonka take, in ba haka ba mene ne za ta dauki tsanar duniya ta aza a kaina ni da Daddy? 


Ko jiya ina wanka na hangota ta bayan danga tana kwakkwada masa mari don ya zubar mata da ruwa a buta”. 


Shi dariya ma ce ta kama shi, don bai taba jin Marwah na yin korafi ba a rayuwarta, lallai kishi ba dama ne. 


Ya ce, “To ta mareshi ke ina ruwanki tunda ba ke ta mara ba danta ta mara?” 


Ta zaro ido ta ce, “Sanda nake nakudar haihuwarshi ta taya ni? Na ce ta taya ni?” Ta hayayyako masa kamar ta rufe shi da duka. Sai ya fizgota ya makalkale ta, “Cool down, ...apple of my eyes, take it easy..... biyu kyautar Allah....na tuba, na bi Allah na bi ki...”. 


Ta ture shi, “Ku maza wallahi munafukai ne, algungumai marasa alkibla. Sai ka tafi goben don ni ba zamanka nake yi ba, ita ma Badijon ba zamanta nake ba. Inna na rako”. 


Ya dan yi fuska don jin za ta wuce kima. Bai sake tanka mata ba, ta kara kuluwa sai ta sake fashewa da kuka. 


Ko kadan baya son zubar hawayenta, domin tamkar digar dalma yake a zuciyarsa. Kwanciya ya yi a kan cinyoyinta shi da tirtsetsen cikinta da ya zungure shi. 


Cikin ya rungume yana sumbata, “Ya Allah kada kasa babyna ta yo KISHI irin na Mamanta, Allah kasa ta yo halin SAFAH.....” 

Ai kuwa ta kara kunnuwa....... “Dadin abin dai SAI BAYAN RAINA......” 


Dafe kai ya yi, cikin razana, don jin yadda ta fassara maganarsa da wata manufa daban ta baya da ta riga ta dade da shudewa a zuciyarsa.............. “Ina rokon Allah ya sa ni zan fara mutuwa in barki, idan har tunaninki kenan’’. 


Iyakar abinda y ace kennan. Ya sa kai ya fita daga bukkar ya barta da binshi da harara. Zahraddeen saboda bacin rai fadama ya nufa ya samu wani katon dutse luwai-luwai da shi ya zauna ya harde hannunsa a tsakanin guiwoyinshi yana tufka da warwara. 


Ya rasa mata wadanne irin mutane ne, duk hankalinsu da iliminsu idan aka zo maganar kishi in suka kwaboma wata maganar sai ka ji kamar ka hadiyi zuciya ka mutu don haushi. 


Yana nan zaune yana kallon yadda ruwa ke ninkaya da ambaliya a katon kogin, wanda an tabbatar da cewa ya bullo ne daga Riber-Niger, sai ya samu kansa da diban tsakuwoyi yana cillawa cikin ruwan daya bayan daya. 


Marwah ta bata mishi rai sosai. yana nan zaune har yamma, sannan ya tashi ya nufo gida, zuciyarsa ta yi sanyi a lokacin. 


A hanya ya ga Daddy da yara 'yan'uwansa kowannensu hannunsa rike da katon dodon kodi mai rai da lafiya. 


Tsigogin jikin Zahraddeen suka tashi, shi kuwa yaron yana hango shi ya soma fadin. "Daddy....Daddy zo ka gani mun samo dodon kodi". 

Ya karaso ya bubbuge hannunsa dodon kudin suka zube suna ta motsi. Ai kuwa Daddy ya tsinke da ihu. 


Ya dauke shi kafarsa ba ko takalmi ya yi gida da shi yana ihu yana zillo sai ya dauko dodonninsa. Inna Binta ce ta fara jiyo ihunsa ta fita daga bukkar Bajido da sauri don ganin abin da ke sa shi wannan ihu. 


Uwar shi na gindin murhu tana suyar zabbi, Inna ta ce, "Anya Dini ba zaka bar mai sunan Alhaji ya yi wasa da tsararrakinsa ba yadda yake so kamar a kanka aka fara haihuwar da? Kai ba irin rayuwar da ka yi ba kenan, me ya same ka?" 


Ya ce, "Inna dodon kodi fa suke daukowa?" 


Ta ce, "Meye da shi? Ba abinci bane a gurin wasu?" 


Ya ce, "A'a, ban da ni wallahi, kuma idan ba zai zauna a gida ba daure kafafunsa zan yi". 


Inna ta kama baki. Marwah na jinsu tana ta dariya a boye, dan yajin da ya yi mata tun safe ba ta ganshi ba, yasa duk ta damu, sai yanzu da ta ji muryarsa. Dadi ya lullubeta. 


Ta saci kallonsa yana ta wankewa Daddy hannu da omo, kafarshi futu-futu da yashi. Sai ta ji kamar ta lashe shi don so. Ta manta da wata sa'insa da suka yi da safe. 


Ta cika ruwa a buta ta je gabanshi ta tsugunna ta soma wanke mishi kafafun ba tare da ta bari sun hada idanu ba. 


Anisa na gefe zaune a kan katon kunkuru (tortoise) tana satar kallonsu kamar ta shaketa ta mutu don kishi. 


Post a Comment for "BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 9 by sumayyah Abdulkadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...