ALWASHI COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ALWASHI COMPLETE

ALWASHI COMPLETE

- - Post a Comment

 ALWASHI COMPLETE                     Www.bankinhausanovels.com.ng 

.

      ****

Gidane na marayu mai d’auke da tangamemen gate sannan ga katanga babba zagaye da gidan wanda tsawonta ma abin kallone,haka shima cikin gidan yake wawakeken gaske mai dauke da gine gine masu yawa wadanda suka hadar da ofisoshin ma’aikatan gidan da kuma wurin kwanan marayun da kuma duk wani abu na bukatarsu,

Duk inda ka hanga yarane zaune sunyi group group, masu wasa nayi sannan masu hira sunayi yayinda wasu kuma suke yan aikace aikacensu na yau da kullum,

Wasu yanmata ne guda biyu acan gefe su kadai wadanda akalla shekarunsu zasu kai shekaru 23,

Daya daga cikinsu tayi tagumi tana sanye da kodadden hijabi da wata kodaddiyar atamfa ajikinta haka itama dayar kayan jikinta duk sun gajiya,

.

“Hafsat wai wannan tagumin da kikayi na menene? Yau naga gaba daya yanayin naki sai ahankali tamkar wata marar lafiya…” Daya daga cikin yanmatan tafada bayan ta dafa kawar tata,

“Amina wallahi lafiyata kalau kawai dai ina tunanin makomar rayuwarmu ne acikin gidan nan, ba kasafai mutane suka fiya kulawa damu ba, hatta gwamnati tayi watsi da rayuwarmu sai lokaci zuwa lokaci take tunawa damu…” Wadda aka kira da suna hafsat tayi magana cikin karyewar zuciya,

“Amma dai hafsat wannan ai ba bakon abu bane awajenmu duba da tsawon shekarun da muka diba acikin wannan gida gashi har yau Allah bai kawo wanda zai daukemu ya fitar damu daga cikin gidan nanba ko muma mazamo yaya kamar kowa..”

“Amina kenan tayaya zamu zamo yaya kamar kowa alhalin babu wanda yasan asalinmu, Allah ne kadai yasan tushenmu dan haka kinga maganar amaida mu ‘yaya ma bata taso ba..”

“Hmmm babu komai koma dai yayane Allah yana tare damu…”

“Kai yanmatan nan kutaso kuzo muje..” Muryar daya daga cikin ma’aikatan gidan marayun ta ratsa kunnuwansu wanda hakane yayi sanadiyyar katse musu hirar da suke yi,

Mikewa sukayi suka karasa inda take,

“Yawwa kuzo muje, wannan bawan Allahn ne yauma yakawo muku agaji kamar yadda yasaba…”

Batare da sunyi magana ba suka bi bayanta, gaba daya an tattaro yaran gidan antarasu wuri guda gefe kuma wata babbar motace anata sauke kaya daga kanta wadanda suka hadar da buhunhunan kayan abinci da tufafi,

Wuri amina da hafsat suka samu suka tsaya suna kallon irin uba uban kayan da ake saukewa,

Kowacce acikinsu addu’a take acikin zuciyarta kan Allah yasakawa koma wanene wannan mutumin da alkhairi domin yajima yana yi musu hidima,

Kayan da aka sauke daga kan wannan katuwar motar ba dan kadan bane domin bayan kayan abinci da kayan sawa harda barguna da katifu,

Suna nan zaune sunyi tsuru suna ganin tulin kayan da aka kawo musu har aka kammala sauke kayan nan wakilin wanda yabada kayan akawo ya mike yadanyi jawabi,

_Kamar yadda muka sani kuma muka saba, wannan bawan Allah Wanda mukafi sani da suna baya goya marayu akoda yaushe yana iya kokarinsa wurin ganin ya kyautatawa rayuwar marayu sannan kuma ya sadaukar da dukiyarsa wurin taimakon musulunci, kamar yadda nadade ina fada muku shi wannan bawan Allah matashine ba tsoho ba kawai dai Allah ne ya albarkaceshi da halin manya dan haka muyita yimasa addu’a akan Allah ya albarkaci rayuwarsa da dukiyarsa da kuma iyayensa…._

“Amin…”

.

Dukkan jama’ar dake wurin suka amsa cikin farin ciki domin wannan bawan Allah ba karamin taimako yake yiba saboda kusan agarin ma shine lamba daya wurin taimakawa rayuwar marayu.

Saida aka gama rabawa marayun kayayyakin da aka kawo musu akan idon wakilin wannan bawan Allahn dake basu gudun mawa wanda suka dade da rada masa suna da baya goya marayu,bayan gama rabon kayan tsaf sannan wakilin baya goya marayu yatafi, sukuma yaran kowa ya kinkimi kayanshi ya nufi wurinda zai adana su, haka suke gudanar da rayuwarsu cikin wannan gida wanda a lokuta mafiya yawa sukan shafe sama da watanni biyu batare da sun samu wani tallafi ba indai ba wannan bawan Allahn ne ya aiko musu ba gashi kuma duk wannan hidimar da yake yi musu basu taba ganinsa ba balle har su gane kamanninsa.

***

  Kamar bazai taka k’asa ba haka yake tafiya, sanye yake cikin jar t shirt mai dogon hannu yasha d’amara da jar belt wadda ke d’amare ajikin bakin trouser din dake jikinsa, duk da wai ahakan sauri yake amma baisashi sauya salon tafiyar tashi ba,bak’in face din dake idonshi yadan gyara bayan ya maida hankalinsa kan agogon azurfar dake d’aure a tsintsiyar hannunshi, kamar koda yaushe fuskarshi babu alamun fara’a atare da ita,

.

K’ofar da zata sadashi da falon mahaifiyarshi ya bude ya shiga fuskar nan kamar zaice wayyo Allah dan tsananin fushi,

Ganin babu kowa aciki yasashi kara yin gaba, awani tsararren falo wanda aka tanada musamman domin hutawa ya isketa, tana zaune saman kujera daga ganinta bazata haura shekaru 45 ba aduniya, farace jajur mai dan jiki, tana sanye da wani leshi mai tsadar gaske, wuyanta da hannuwanta gamida kunnenta duk gwala gwalai ne sai walwali suke, haka yan yatsun hannunta ma duk sunsha zubunan gold,gefenta kuma wata yar matashiyar budurwa ce wacce zata kai shekaru 23 tana kwance tayi matashi da cinyar matar,

Sallama yayi wadda ba lallai su iya jiba domin aciki ciki yayita,

Dukkansu hankalinsu yana ga drama din da suke kallo atashar tauraron dan adam wanda har saida ya zauna sannan suka farga dashi…….

      ***

Fuska cikeda annashuwa mahaifiyar tashi ta kalleshi cikin fara,a yayin da shikuma sai faman cijar lebenshi nakasa yake yi fuska babu annuri,

“Yusleem…. Har anshigo?”

Mahaifiyar tashi ta tambayeshi da fara,a akan fuskarta,

Saida yasake hade rai idanuwansa na bisa screen din hadaddiyar wayar dake hannunshi sannan ya amsata dakyar,

,

“Ehh Mami…”

Wata fara,ar tasake yi sannan tayi magana,

“Nima dama tun dazu nake jiranka kazo saboda ina son ka sama mana visa nida surayya zuwa kasar chairo zan kaita medical check up…”

Shiru yayi batare da ya amsa ba yaci gaba da latsa wayarshi, idan da sabo to kowa nagidan ya saba da wannan mummunar dabi’ar tashi tayin shiru idan ana yimasa magana, ko mahaifiyarshi ce tayi masa magana sai yaga dama zai amsa gashi da shegen girman kan tsiya kamar shi yafi kowa,

.

Saida ya dauki fiyeda mintuna goma sannan ya daga manyan idanuwanshi wadanda suke tamkar kwai domin round eyes gareshi,surayya kanwarshi ya kalla wacce ke kwance akan cinyar mami tana sanye da English wears riga da skirt bakake kanta babu dan kwali,

Baiyi magana ba yasake mayar da kanshi kan screen din wayarshi,

“Mami…am dama ina son infada miki..”

Tattaro hankalinta gaba daya Mami tayi zuwa gareshi,

“To yusleem ina jinka..”

“Mami nasaki khadija yau da safe..”

Zaro idanuwa Mami tayi gamida dafe kirji, surayya kuwa dake kwance akan cinyarta zunbur tayi ta mike zaune, dukkaninsu kallonshi suke cikeda tuhuma gamida zargi iri iri,

“Nashiga uku ni siyama, innalillahi wa inna ilaihir raji’un….” Mami tafada tana tafa hannuwanta,

.

“Haba yusleem wai kai wanne irin mutum ne? Anya kuwa ba aljana ce ta aureka ba? Karfa ka manta ko watanni uku cikakke ba ayiba da bikinku kaida khadija amma shine yau kazo kake fada min wai ka saketa?

Yusleem mai ka dauki aure ne? Ka daukeshi ne a matsayin wasa, ko kuma abin wasa ko wasan yara?

Yusleem duk fa wannan dukiyar da kake ganin kana da ita bazata taba iya siya maka darajar da aure zai siya maka ba…!”

Dan jan numfashi tayi sannan ta dora,

“Kana yaronka dakai amma acikin shekaru biyar kayi aure sama da guda goma, haba yusleem wannan wacce irin mummunar dabi’a ce, ka mayar da sakin aure ba komaiba,saki da Allah ma baya sonsa amma kai kuma shine ka mayar tamkar sana,arka,

To agaskiya nidai nagama gajiya da wannan halin naka na auri saki, babu damar ka zauna da mace na koda shekara dayane?”

“Gaskiya Yaya bamuji dadin wannan labarin ba, yanzu anty khadijan ma ka saketa?”

Surayya ta fada idonta dauke da kwalla,ko kallonta baiyi ba bare tasa ran zai bata amsa,

Fada mami tasoma balbala masa ta inda take shiga bata nan take fitaba,

“Ni narasa gane kan wannan hali naka yusleem, kwata kwata baka dauki aure da daraja ba, sam baka son zama da mace, wannan wacce irin rayuwa ce,

Kuma bafa kowa kake watsawa kasa a idoba face ni tunda nice nake aura maka matan, yanzu abinda kayi ka kyauta kenan?”

Dan kishingida yayi kadan ya tsurawa wayarshi ido batare da yace komai ba,

.

“Dakai nake magana kayi min shiru, ka fada min dalilinka na auri saki, akalla ba a kasaru ba yusleem ka auri mata dai dai dai har guda goma sha…, baka da lafiya ne ko yaya?”

Saida ya dan shafi sajen fuskarshi sannan ya kalli mami,

“Mami ni lafiyata kalau sannan dama ai ban taba cewa ga wacce nake so ba, duk matan da nake aure kece kike samo min su ki aura min..”

“Wacce irin magana kake fada min yusleem? Dan bakai kagansu kana soba shikenan bazaka zauna dasu ba? Wannan dalilinne yasa ka dauki auri saki ba abakin komai ba?

Sau nawa ina baka dama domin ka fito da matar da kake so in aura maka amma sai kayi biris da maganar, kuma ni ai aganina nagama yimaka duk wani gata wanda yadace ace uwa tayiwa danta domin na nemo maka mata yan mutunci, yan asali, masu aji wadanda suka dace dakai amma daga karshe duk dai labarin iri dayane cewa ka sakesu, yanzu kaduba kaga yarinyar nan khadija da ka saketa ka rabu da ita, yarinya ce mai hakuri mai nagarta mai sanin ya kamata, yarinya kyakkyawa yar asali yar mutunci yar kawata hajiya fa’iza,ko wata biyar ba ayiba da bikinku amma kasaketa…”

Dan tsagaitawa mami tayi tana dubanshi cikeda bacin rai, har tsawon mintuna biyar babu wanda yasake magana acikinsu,

“Yusleem wai da me kake takama ne da har kadauki auri saki ba abakin komai ba?

Idan dan kyawun dakake dashi ne yasaka kake yin haka to ya kamata fa kasani akwai wadanda suka zartaka kyau amma basa yin haka,

Idan kuma dan arzikin dakake dashi ne to kasani akwai big millionaires suna nan ba irinkaba young millionaire ba kuma basa aikata wannan wulakancin dakake yi,

.

Inkuma kuruciyar da kake tare da itane yasaka yin wannan cin mutuncin to wallahi ka gaggauta farkawa daga wannan dogon baccin da kakeyi domin akullum shekarunka sake yawa suke bawai raguwa ba..”

Shiru mami tayi cikeda bacin rai tana huci saboda babatun da tagama yanzu,

Mikewa yayi sannan yayi magana ahankali,kamar mai ciwon baki yace,

“Kiyi hakuri mami..”

Ko amsa masa batayi ba yasaka kai yafice daga cikin falon, nan mami da surayya suka rakashi da idanu….

        ***

Dafe goshi mami tayi cikeda damuwa bayan fitar yusleem,nan tayi shiru tana jin wani irin bacin rai yana ziyartar zuciyarta,

.

Sunfi mintuna biyar itada surayya batare da wani acikinsu ya iya yin koda motsi ba,

Mami ce tayi karfin yin magana cikeda damuwa,

“Narasa gane kan yaron nan, agaskiya abin nasa yawuce tunani, yawuce hankali, gaba daya zagayen jahar nan harma da mak’ota kowa yasanshi awurin auri saki, duk yabi yabatawa kansa suna…”

“Mami wallahi nidai ban yarda yaya yusleem lafiyarsa kalau ba, duk inda akaje aka dawo acikin abubuwa guda uku to abu daya yana damunsa dole,

.

Kodai aljana ce ta aureshi, ko kuma yana shaye shayen kwayoyi aboye ko kuma kwakwalwarsa ta dan tabu batare da mun saniba…, wallahi mami ki kaishi adubashi” surayya ta kareshi zancen hawaye yana bin kuncinta,

Jinjina kai mami tashiga yi tana kallon surayya amma sai dai kafin takai ga yin magana tuni karar wayarta ta cika musu kunnuwa nan mami ta dauki wayar jikinta asanyaye saboda ganin sunan wanda ke kiran,

Jiki asanyaye mami ta kalli surayya,

“Kinga ni ko? Hajiya fa’iza ce ke kirana mahaifiyar khadija, yanzu ban san me zan fada mataba, ban san irin fushin da take cikiba..”

Kiranne yakatse wani yasake shigowa,

“Mami ki daga kawai..” Surayya tace da ita bayan ta tsura mata ido,

“Hajiya siyama ina fata dai kinji cin mutuncin da danki yayi mana, koda yake nasanma da saninki zai aikata hakan,yayiwa khadija saki na wulakanci batare da laifin komai ba…”  Jin abinda mahaifiyar khadija ke fadi yasa mami saurin katseta domin bata son amintakarsu da kawancensu yabaci ta wannan silar,

“Hajiya fa’iza dan Allah kiyi hakuri kijirani zanzo gidan, dan Allah karki yi fushi akan wannan abun da yafaru, kisani khadija yatace kuma bata da wani banbanci da yayan da nahaifa…”

,

“Ai hajiya siyama magana tariga da takare Allah yasa haka shine yafi alkhairi kawai kuma dama halin danki ne auri saki tunda ba akan khadija yafara ba, ita khadija kaddara ce kawai ta hauta har takaita ga aurensa…”

K’ittt mami taji hajiya fa’iza takashe wayarta bayan tagama wadannan maganganu,


“Yusleem bai kyauta minba, akansa zumuncinmu da muka dade muna yi da hajiya fa’iza yana neman baci..”

.

“Ai mami nafada miki wallahi acikin abubuwa guda ukun nan da na zayyano abaya akwai daya aciki wanda ke damunsa”

“Hakane surayya nima nayarda da batunki, indai kuwa hakane to yazama dole inbincike shi sosai har ingano matsalarsa…”

Shuru kowannensu yasake yi har na tsawon wani lokaci, surayya ce tafara mikewa ta nufi bedroom dinta ganin haka yasa mami itama tashi ta shiga nata bedroom din, mintuna kadan tafito cikin sabuwar shiga wacce tafi ta da,

Wani jan swiss lace ta dauro tayafa babban mayafi kalarshi,hannunta rikeda handbag dinta ta leka bedroom din surayya, kwance ta isketa da wayarta ahannu suna yin video call itada Abdul tana fada masa sakin da yusleem yayiwa khadija,

“Yawwa yaya Abdul ga mami…”

.

Karbar wayar mamin tayi tana kallon Abdul din,

“Mami haka yaya yasake karo wulakanci? Yanzu sury take fada min wai yasaki khadija yau..”

Ajiyar zuciya mami ta sauke,

“Abdul nikaina yanzu haka ban san da wacce kalma zanyi amfani da itaba wurin bawa mahaifiyar khadija hakuri duba da irin wulakancin da yayanku yayi, auren da ko watanni biyar  ba ayiba amma wai yau har anyi angama…”

“Ni mami narasa meye matsalar yaya wallahi, ko kadan baya son zama da mace..”

“Abdul koma dai menene matsalarshi yazame min dole intashi atsaye saboda na lura sam shi baisan zuru ba, yanzu haka gidansu khadijan zance inbawa mahaifiyarta hakuri sannan kuma innemi bikonta su taimaka su dawo da ita gidan mijinta..”

.

“To shikenan mami sai kin dawo..”

“Yawwa abdul sai nadawo, ina khalifa din kuma?”

“Mami shi yashiga school tun dazu yanada lecture ni yau banda class shiyasa nake gida”

“To Allah yabaku sa’a,idan yadawo ka gaidashi itama surayya zuwa nanda 3 weeks zata koma Malaysia hutunta yakare…”

“To shikenan mami Allah yakaimu”

“Amin, babu wata matsala dai ko?”

.

“Wallahi babu matsalar komai mami domin yaya yana turo mana da kudade akai akai..”

Jijjiga kai mami tayi, “yanada wannan kokarin kam,zama da mace ne bai iyaba”

Dariya abdul yafara nan ta mikawa surayya wayar tamike tana gyara mayafinta, jin surayya da abdul sun cigaba da hira yasata fadin,

“Surayya bazaki rakani bane intafi?”

“Mami kije kawai sai kin dawo..”

“Haba surayya da ina cewa sai ki kaimu kawai..”

“Mami bazan iya driving ba wallahi kin san cikina ciwo yake..”

“To bani key din motar taki inje Mamman driver yakaini..”

Hannunta ta mika kan drewar tadauko key din tabata takoma ta kwanta taci gaba da yin video call dinta itada Abdul yayinda ita kuma mami tafita,

.

Shu’aibu kuku ta iske acikin kitchen yana yin yan aikace aikacensa kamar yadda yasaba nan tabar mishi abinda take son yadafa mata kafin tadawo,sannan tadora da cewar ya leka bedroom din sury itama ya tambayeta abinda take sha’awar ci da daddare sai ya dafa mata,

Tunda tafito driver dinta wanda aka tanada musamman domin kaita unguwa yazo ya tareta tareda karbar key din motar dake hannunta, bude mata yayi tashiga owners corner ta zauna yaja suka tafi.


Kai tsaye gidansu khadija suka nufa koda sukaje mahaifiyar khadija wato hajiya fa’iza babu yabo babu fallasa ta karbi mami,gyaran murya Mami tayi sannan tace,

“Hajiya fa’iza mu taru muyi hakuri mu daidata yaran nan mu mayar da khadija dakinta dan Allah..”

Tagumin da tayi tagyara, “hajiya siyama ba ki nayiba amma kisani wallahi macen da zata iya zama da yusleem sai antona, kinga tunda khadija ta shigo gidan nan tana can ta kunshe adaki tana kuka, taki ci taki sha…”

“Ikon Allah, to me yayi mata?” Mami tafada cikeda damuwa,

“Waya sani, sai dai muje tare ko zatayi magana…”

Mahaifiyar khadija tafada fuskarta adaure.

       ***

Tashi mami tayi tabi bayan hajiya fa’iza zuwa dakin da khadija ke kwance tagama cin kuka ta koshi dan tsabar kuka yanzu ko hawayen ma bata iyayi,

Zama mami tayi agefen gadon da khadijan ke zaune ta dafata jikinta asanyaye,

“Khadija kiyi hakuri kinji, insha Allah komai zai daidaita sannan zaki koma gidan mijinki”

D’aga jajayen idanuwanta wadanda suka rine tayi ta kalli mami,

“Mami bazan iya komawa gidansa ba, nahakura da aurenshi, bazan sake iya zaman aure dashi ba wallahi”

Gaban mami ne yashiga dukan tara tara saboda jin abinda khadija tafada,

“Khadija wani abu yayi miki?”

“Mami ni babu abinda yayi min kawai wulakancinshi ne bazan iya cigaba da jurewa ba”

Dafata mami tasake yi,cikin sigar lallashi tace,

.

“Nasani khadija, kuma nasan kinada hakuri amma daurewa zakiyi  kisake yin wani hakurin ki koma dakinki…”

“Mami bazan iya komawa ba wallahi nidai nahakura”

“To kuma khadija idan Allah ya kaddaro da rabo a tsakaninku fa? Bana son ayi gaggawar yanke hukunci daga baya kuma azo ana dana sani”

Sai a lokacin hajiya fa’iza mahaifiyar khadija tayi magana,

“Ai hajiya siyama maganar rabo a tsakaninsu ma babu shi saboda tunda akayi auren bai taba shiga dakinta ba, ko kallo bata isheshi ba bare har ya kulata”

Tagumi mami ta rafka taci gaba da sauraron bayanin da hajiya fa’iza take yimata na irin zaman da yusleem yayi da khadija ta rufe maganar da cewa,

“Kawai dai muyi addu’a Allah yasa hakane mafi alkhairi, nanda sati biyu kuma zamuzo mu kwashe kayanta ki fada masa”

Ita dai mami jiki babu kwari ta mike bayan tagama bawa khadija da mahaifiyarta hakuri, jakarta ta dauka ta fita ranta babu dadi zuciyarta cike da bacin rai, wannan karon kam yazama dole ta nunawa yusleem fushinta akan abinda yajima yana aikatawa na sakin mata babu gaira bare dalili, babu laifin tsaye babu na zaune.

.

Har kofar gida hajiya fa’iza ta rakata suna cigaba da bawa juna hakuri musamman ma mami da take ganin laifin na yusleem ne domin shine yake nema yaja mata lalacewar zumuncinsu da matar da suka dade atare,

Mota Mamman driver ya bude mata tashiga ta zauna ya rufe suka tafi domin tuni hajiya fa’iza tajima da shigewa cikin gida.

Da tunani kala kala acikin zuciyarta suka karasa gida, cikeda damuwa take zayyanewa surayya abinda yafaru, suna tsaka da yin maganar sukaji shigowar yusleem,

Bai karaso cikin falon ba yatsaya a dining area, sanye yake da jar t shirt mai gajeren hannu sai black trouser, kamshin turaren lailatul abyad da na  real oud ne yake tashi daga jikinsa, fuskarshi tayi fes sai annurin kyaune yake fita daga gareta,

D’aga murya Mami tayi tayadda tasan zai iya jiyota,

“Kai…”

“Na’am ma…” Ya amsa yana kokarin bude jeren flasks din dake ajiye asaman table din,

“Zo nan..” Mami tafada bayan ta daure fuskarta, fasa diban abincin yayi ya tasamma cikin falon inda su Mami suke.

***

  Rayuwar Hafsat haka taci gaba da tafiya agidan marayu, yanzu haka ta maida hankali sosai wurin koyon sana’o’in hannu domin ana zuwa akoya musu, musamman aka ajiye musu wadanda zasu rinka koyar dasu,

.

Cikin lokutan da babu yawa ta kwarance wurin sak’a sannan tafara iya dinkin keke,haka kawarta Amina itama tana yi daidai gwargwado,

Kullum cikin yin sak’a suke itada Amina suna warwarewa sai su sake saka wani abun nadaban kamar hula, safa, ko riga,

Yau ma kamar kullum suna zaune a inda suka saba zama suna yar hirarsu kowaccensu tana rikeda koreshi tana yin saka,

Hirarsu ce ta katse saboda gano wasu manya manyan motoci da sukayi suna kokarin shigowa cikin harabar gidan,

Amina ce ta zunguri Hafsat da hannunta,

“Hafsat yauma da alama munyi baki, watakila mai girma governor ne yakawo mana ziyarar bazata..”

“Nima dai abinda nake tunani kenan Amina, koma dai menene kinga tashi muje ayi damu kin san bahaushe yace wai gani ya kori ji…”

Mikewa sukayi atare kowaccensu ta tukunkune zaren kulunta da koreshi suka nufi inda suka hango mutanen gidan suna tafiya….

      ***

Ahankali yake ratsawa har zuwa cikin falon mami inda suke zaune itada surayya,

Tunda yaga fuskarta yasan tana cikeda bacin rai,

Zama yayi acikin daya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun dake girke acikin falon,

Tamkar basarake haka yajingina da jikin kujerar ya kishingide,

“Yusleem kana son inyi maka mugun baki..?”

Mami tafada ahasale cikin fada, shiru yayi bai amsa ba hakan yasake tunzurata, cikin tsawa tasake yin magana,

“Ba dakai nake yin magana ba?”

Dan kallonta yayi,

“Mami laifin me kuma nasake yi?”

“Ban saniba, ohhh watonma tambayata kake me kayi? Harma ka manta abinda kayi kenan..?”

Jijjiga kai mami tashiga yi ta maida dubanta ga surayya wacce ke zaune tana jinsu,

“Lallai surayya gaskiyarki ne dole sai an binciki kwakwalwarsa, kinji yanzu wai tambayata yake me yayi, watonma shi har ya manta, dole ka manta mana tunda ka cimin mutunci a idon duniya, sannan ka nunawa duniya ban isa dakaiba, ka cuci yar mutane ka mayar da ita bazawara..”

Nunashi da yatsa tayi,

.

“To wallahi kaji tsoron Allah yusleem, ina fada maka kaji tsoron Allah domin wallahi bazai barka ba indai kaci gaba da wannan mummunar dabi’ar taka ta auri saki”

“Mami yanzu shikenan anty khadijan tatafi bazata dawoba?” Surayya tayi tambayar tana kallon mami,

“Surayya ai babu macen da za ayiwa irin wannan wulakancin ta yarda tasake dawowa, yayanku bashida hali mai kyau mugun mutum ne..”

Da sauri ya kalli mami, sai lokacin yayi magana,

“Mami muguntar me nayi? Ita khadijan ce tace miki ni mugune?”

Kallonsa mami tayi cikeda masifa,

“Ai basai ta fada minba, kai yanzu acikin halayenka har sai wata tafada min? Acikin halayenka wanne ne bansani ba?

Kai cikakken mugune, miskili, mai shegen tinkahon tsiya da girman kai,

To bari kaji infada maka, komai tinkahon mutum da girman kansa idan yashiga wurin matarsa kaskantar da kansa yake komai sarautarsa da kudinsa, amma kai hatta matarka wannan shegen kasaitar taka da girman kai kake nuna mata..”

Shiru yayi bai sake maganaba, yayinda mami taci gaba da zuba masa fada har saida tayi mai isarta sannan ta sassauta,

.

“Yusleem nakasa gane damuwarka, tun kana karami kai mutumne mai zurfin ciki, amma ai bakada wanda zaka iya fadawa damuwarka sama dani da na haifeka, idan wani abune yake damunka kasanar dani..”

“Nifa lafiya lau nake mami, babu abinda yake damuna” yabata amsa,

“Karya kake, tayaya zan yarda dakai bayan kana yin abu irin na marassa lafiya, tunda bazaka fada minba to ya zama wajibi agareni inkaika adubaka, yanzu maganar zuwa chairo da nayi maka dazu to harda kai zamuje, zan kaika kaima su bincika min kwakwalwarka agani domin inajin kasamu tabin kwakwalwa a wannan accident din da kukayi da mahaifinku..”

Murmushi yadanyi saboda maganar ta mami dariya taso bashi,

“Mami tabin hankali kuma? Nidin?”

“Kai kuwa, ai ni har yanzu ban tabbatar da cewa kanada cikakken hankali ba har sai kikitoci sun tabbatar da hakan..”

Mikewa yayi domin yunwa yakeji, dining ya nufa nan mami tabishi abaya,

“Kullum kai kenan azuwa cin abinci gidan nan, yanzu da kanada matarka kuma ka riketa da daraja da ba kana can ta hada maka dinner mai ban sha’awa ba”

Baiyi magana ba yaja kujera ya zauna yafara bude flask din dake jere agabanshi,

Surayya ce ta kwaso da gudu,

“Yaya Karka taba wannan nawane..”

Daure fuska yayi yabude flask din, farfesun dankali ne da hanta da kwai da alayyahu yasha curry sai kamshi yake,

.

Kamar bazaiyi magana ba,daga ido yayi ya kalli surayya sannan ya mayar da dubanshi ga mami,

“Mami zan fasa bakin yarinyar nan..”

“Akan me? Abincinta fa ka taba, da kayi zuciya ka rike aure ka rike matarka hannu bibbiyu ai da duk ba akai ga hakaba” mami tace dashi tana kokarin zuba tuwon accah miyar egusi,

Bai tanka ba ya debi farfesun dankalin acikin flate ya fara tsakura yana ci,

Cigaba da yi masa gugar zana mami tayi shi dai bai kulaba, wannan yana daya daga cikin abinda yasa mami take ganin ba kowacce macece zata iya zama dashi ba domin ko zaka shekara kana yi masa magana sai ya gadama zai amsa idan bai gadama ba har kayi ka gama bazai amsa maka ba, yusleem miskili ne nagaske,ahaka ya karaci cakule cakulen abincin yagama yatashi ya nufi gidanshi wanda ke can wata unguwa daban bata su mami ba.

***

    Daga can baya su Hafsat suka tsaya itada amina suna hangen bakin dake fitowa daga cikin motocin da suka zo yanzu,

Wata bakar jeep mai dauke da glasses masu duhu aka bude nan wani matashin saurayi ya fito, yana sanye da suit blue colour da bakin face idanuwanshi sakaye aciki wanda ya karawa fuskarshi haiba,ashekaru bazai wuce shekaru 30 ba zuwa 31,

Dan yatsina fuska yake kamar wani mace ko kuma kamar wanda yaga kashi,

Kallon hafsa amina tayi,

“Hafsat kalli wancan mutumin, yanzu dama aduniya akwai irinshi?”

“Uhm amina kenan, mu ai kinsan muna nan akumshe dan haka baza mu san me duniya take cikiba”

Jin anfara bayani akan bakin nasu da suka Kawo musu ziyara yasasu maida hankulansu can.

Bayani akayi sosai tareda gabatar musu da mutumin da ya jajurce wurin basu gudun mawa akoda yaushe, har akayi aka gama baice ko uffan ba, shugaban gidan marayun ne yayi jawabin godiya a madadin marayun tareda mika wasu tarin bukatunsu wadanda suke son gwamnati tayi musu ko kuma masu hannu da shuni,

Take awurin matashin saurayin Wanda suka sanya masa suna da baya goya marayu yabada gudun mawar naira biliyan goma, yana gama saka hannu ajikin cheque din da yabada yabude motarshi yashiga batare da yatsaya yaji karshen jawabin godiyar da jama’ar wurin keyi masa ba,

Shiru Hafsat da amina sukayi acikin zuciyoyinsu suna tambayar kansu to shi wannan wanne irin mutum ne mai alheri wanda baya bukatar go

     ***

Suna tsaye suna kallonshi motar tashi ta lula tabar wurin yayinda yan rakiyarsa suka yi hanzarin shiga nasu motocin suka mara masa baya,

“Mutumin nan Allah yasaka masa da alkhairi, dan haduwa ya hadu amma kuma nidai banji dadin yanda ya karbemu ba lokacin da ana gabatar masa damu..” Amina tace da Hafsat tana girgiza kanta,

“To in banda abinki amina mudai ina ruwanmu da yanda ya karbemu,mudai dama taimakonmu kawai muke so yayi kuma yana yi iya daidai gwargwadonsa sannan dama kin san masu kudi ance wulakanci garesu”

“Hakane Hafsat amma kuma ai daraja mutum ma wani abune mai muhimmanci..”

“Kedai amina korafinki kullum baya karewa, dadina dake kenan”

“To shikenan Hafsat nayi shiru..”

Amina tafada tana kokarin jan hannunta.

***

  Tunda yashiga cikin lafiyayyen gidan nasa yaja burki acikin kasaitaccen falonsa na alfarma wanda za a iya kira da aljannar duniya,

Kasa zama yayi dan haka ya mike yafara yin sintiri yana kaiwa da kawowa acikin falon nasa,

Yau kwata kwata baya jin barci sannan yasan barcin ma dama bazai zo gareshi ba saboda halin da yake ciki,

Maganar mami ce ta fado masa nacewa zata kaishi domin a binciki kwakwalwarshi,

.

Shi dai a iya saninsa yasan lafiyarshi kalau bashida wata lalura wacce keda alaka da tabin hankali,

Haka yaci gaba da ire iren wadannan tunane tunanen har dare ya raba, saida yayi sallar asubah sannan yasamu bacci yayi awon gaba dashi,

Misalin karfe 10 daidai nasafe yatashi, wanka yayi ya shirya yafito cikin bakaken suit wadanda sukayi mutukar karbarshi domin rigar da yasaka aciki ja ce shikuma red colour tana mutukar amsarshi,

Fita yayi zuwa wurinda aka tanada musamman domin adana motoci, motocine gasu nan ajere kala daban daban tamkar wurin saida motoci,

Wata dark blue ya bude yashiga yayi mata key yafita daga gidan, kamar ya biya ta gidan mami yayi breakfast sai kawai yawuce batare da yabiya ba domin yasan idan yaje ma fadan dai da take ta yi zata dora daga inda ta tsaya,

Kamfaninshi na sarrafa takalma da jaka ya nufa domin yana da meeting da ma’aikatan company din nan yabata lokaci mai tsawo bashi ya tashi ba sai 5 na yamma dan haka agajiye ya tasamma gidan mami,

.

Yana tafe yana kokarin cire necktie din dake wuyanshi daf da zai shiga falo su surayya suka fito itada kawarta wacce ta Kawo mata ziyara,

“Barka da zuwa yaya..” Surayya tace dashi lokacin da saka zo daf dashi, ko kallonta baiyi ba bare ya amsa mata sannun da take yimasa,

Dayake tasan halinshi sai ko damuwa batayi ba maimakon hakama sai murmushi da tadanyi ta waiwaya lokacin har yashige cikin babban falon,

“Sury wannan kuma waye?”

Kawar tata ta tambayeta tana dafa kafadarta,

“Wallahi billy brother nane..”

“Au wai dama kinada wani brother din bayan Abdul da khalifa?”

Murmushi surayya tayi,

“Wannan shine first born namu ai sunanshi yusleem”

.

Kada kai billy tayi tana dan murmusawa,

“Masha Allah, amma duk yafiku kyau, inama ace zaki bani shi..”

“A’a billy bazanyi Fatan ki auri yaya yusleem ba domin daga karshe kawancenmu dake sunanshi kararre”

“Meyasa kikace haka?” Billy ta tambayeta,

“Kedai kawai mubar maganar, idan mun koma school zamu karasa, nidai bazan samu komawa next week ba sai dai upper week”

“To shikenan Allah yakaimu”

Sallama sukayi billy tatafi ita kuma surayya tashiga cikin gida, akan dining ta iske yusleem yana cin abinci,

“Yaya wallahi kayi kasuwa..”

.

Banza yayi mata yaci gaba da cin abincinsa, bedroom din Mami ta shiga ta fara tsegunta mata maganar kawarta billy, ahaka yusleem yasamesu,

Agefen gadon mami yazauna yadan kishingida,

“Mami maganar visa dinnan inaga kawai kufara shiri domin nanda kwana 4 zata iya zama ready..”

“Allah yakaimu, Allah yayi maka albarka yusleem..”

“Amin mami”.

  Cikin kwanaki hudu visa tafito suka shirya suka tafi kasar chairo, bincike sosai mami tasa ayi mata a kwakwalwar yusleem dan agano mata abinda ke damunsa, cikin kwanaki 2 likitocin suka kammala sakamako yafito…

       ***

Mamaki ne  ya kama mami saboda ganin sakamakon dake jikin takardar, wurin surayya taje ta mika mata bayan ta zauna agefenta,

Itama surayyan mamaki ne ya bayyana akan fuskarta ganin wai yusleem lafiyarsa kalau bashida matsalar komai,

“To yanzu mami menene mafita kuma?”

Surayya tayi tambayar tana kallon mamin,

“Surayya mujira tukunna mu koma gida sai asamo mafita”

“To Allah ya kaimu”.

  Satinsu biyu suka koma gida nigeria, bayan sun hutane mami tasake sakashi agaba ta koro masa jawabi kamar haka,

“Tunda munje asibiti sun tabbatar mana da cewar kwakwalwarka lafiya lau take tofa akwai sauran bincike domin yanzu kuma malamin rukiyya zan samo yazo yayi maka rukiyya ya rabaka da wannan aljanar data aureka..”

Ware ido yayi ya kalli mami,

“Rukiyya kuma mami? Ni me ya hadani da rukiyya kuma?”

,

“Kai kuwa keda hadi da rukiyya yusleem domin dukkan alamu sun nuna cewar kana tareda aljana…”

“Wallahi mami ni banida wata aljana, lafiyata lau..”

“Ai bazan yarda dakai ba har sai masu bincike sun bincika sun tabbatar”

Mikewa yayi yafita, tun daga nan bai sake komawa gidan ba sai ranar da surayya zata koma makaranta,

Acikin kitchen ya iske mami itada kukunta suna soya dambun kifi da nama wanda surayya zata tafi dashi makaranta,

“Mami barka da aiki..”

Kallonsa mami tayi ta dauke idonta taci gaba da aikinta,

“Sai yau zaka zo gidan? Akan ina nemamaka lafiya shine kuma zaka daina zuwa gidan nan? Yayi kyau”

.

Shiru yayi baice komai ba dama kuma tasan ba komai din zaice ba,

Wucewa yayi zuwa cikin falo inda surayya take zaune tanata harhada kayanta wadanda zata wuce school dasu,

“Yawwa yaya dama kai nake jira, pls ka bani kudi zan sai phone wallahi kaga wannan din ta fashe jiya ina…”

Bai bari ta karasa ba yayi saurin katseta,

“Nawa kikeso?”

“Yaya duk abinda nasamu”

“Kijira zan turo miki anjima harda kudin karatunki, inyaso idan kikaje can sai kisiya”

“Nagode yaya, Allah yabaka mata tagari”

Wata uwar tsawa ya daka mata,

“Ke…..”

.

Saurin rufe bakinta tayi tai shiru, mami ce ta shigo tana rikeda dambun nama akan flate, yusleem ta ajiyewa agabanshi ta samu wuri ta zauna tana kallonshi,

“Gobe idan Allah yakaimu malamin da zai yimaka rukiyya zaizo zaku fara”

Baiyi maganaba illa idanuwansa da ya tsayar akan tv din dake kafe abangon falon tana aiki,

“Ko bakaji ne? Ina yimaka magana”

“Inaji..”

“Yawwa dan haka gobe da safe inganka agidan nan”

Dambun naman yaja yafara tsakura yana ci har surayya ta kammala shiryawa nan ya daukesu a motarshi itada mami ya kaisu airport, saida sukaga tashin jirginsu sannan suka dawo gida, bai shiga gidan ba ya juya ya nufi gidansa.

  Washe gari kamar yadda mami tace haka ya nufi gidan, lokacin har mai yin rukiyyar yazo, tun aranar aka fara amma shiru babu alamun aljanu atare dashi,

Tsawon kwana 7 aka dauka ana gudanar da rukiyyar amma babu abinda ya canja dan haka malamin yacewa mami daga ranar angama kuma lafiyar yusleem kalau,amma bai saniba ko aljanar kin bayyana tayi,

Shiru mami tayi tai tagumi tarasa abin fada amma har lokacin zuciyarta bata amince mata da cewar yusleem baya tareda aljana ba.

Sallamar malamin mami tayi ta zubawa yusleem ido,

“Yusleem ka fada min abinda ke damunka saboda ni har yanzu jikina yana bani da akwai wani abu”

“Mami babu abinda yake damuna”

“Da akwai yusleem, akwai abinda yake damunka, kafada min gaskiya idan baka da lafiya a matsayinka na d’a namiji?”

,

Dan sunkuyar da kai yayi yasoma shafa sumar kanshi saboda nauyin da maganar ta mami tayi mishi,

“Mami nifa banida kowacce irin matsala wallahi lafiyata lau”

“To shikenan tunda kafadi haka amma ina son daga yau dinnan kafara duba matar aure domin agaskiya bazan juri ganinka ahaka babu mata ba”

Kallonta yayi amma sai yayi shiru baiyi magana ba domin shi ba kasafai ya fiya son yayita magana ba, nasiha mami tashiga yimasa sai da tayi tagama sannan yatashi ya fita,

Tun daga ranar mami tashiga nemar masa matar aure domin acewarta bata son ganinshi haka babu aure,shikuma tasan ba samowa zaiyi dakanshi ba ko tabashi dama tunda abaya tasha gwada irin hakan amma abun ya faskara.

Cikin sa’a aka samo mata wata yarinya mai hankali Nusaiba yarinyar bazata wuce shekaru 20 ba domin ko jami’a bata shiga ba, duk da iyayenta sunji labarin irin auri sakin da yusleem yakeyi hakan bai sasu yunkurin hanashi aurenta ba domin suna ganin kamar wannan wata damace da suka samu wadda zasu dandani zakin arziki.

          ***

Tamkar zaiyi kuka yasa mami agaba yana rokonta akan ta janye maganar auren nan domin bashida burin sake yin aure nan kusa,

“Mami tunda dai sakin nan da nakeyi bakya so, shi yafi komai daga miki hankali to kiyi hakuri kibar maganar auren nan domin bana bukatarsa..”

“Kai ka isama? Ai ko bakaso sai nayi maka wannan auren domin cikar kimarka shine aganka da iyali, haba yusleem wacce irin rayuwa kake son yi ne? Haka kake so inzuba maka ido ka zauna babu mata atare dakai? Ina abinda bazai yuyu ba kenan..”

Bai sake cewa komai ba yaciro wayarshi dake cikin aljihun wandonshi yafara latsawa,

“Aikinka kenan latse latsen waya, babu dama ayi magana ta minti 5 dakai, ai dole ka rasa macen da zata zauna dakai…”

.

Nan dinma dai shirun yayi baice komai ba, nan mami taci gaba da mita tana tayi shidai yayi shiru har tayi tagama ta tashi takoma bedroom dinta bai sake cewa koda uffan ba,

Yadade zaune acikin falon kafin ya mike ya fita, washe garin ranar yan uwan tsohuwar matarshi khadija suka zo suka kwashe kayanta kaf basu bar koda cokali ba,

.

Ita kuwa mami shirye shirye nema masa aure taci gaba dayi, tuni har tabada sautin ahado masa lefe tun daga kasar dubai, amma har yau yusleem bai san koda kalar yarinyar da Mami keson aura mishi ba,

Neman auren saida yayi karfi sosai sannan Mami tace ya shirya yaje yaga yarinyar,

Baiyi musu ba yace to zaije amma kuma baije dinba, shiru shiru baije gidansu nusaiban ba har aka wuce sati biyu, kiranshi Mami tayi tace yazo ya sameta,

Lokacin da yatashi daga office yawuce kiran da mamin keyi masa, a falo ya sameta itada sa’ade mai yimata kitso da kunshi domin Mami irin matan nanne yan gayu shiyasa koda wasa bazaka taba cewa itace ta haifi yusleem dinba domin jikinta bai nunaba gayunta ya boye tsufan,

Zama yayi acikin daya daga kujerun falon yazaro wayarshi yasoma latsawa,

Gaidashi sa’ade mai kitso tayi ya amsa dakyar, saida mami ta sallami sa’aden tatafi sannan ta juya ta fuskanceshi.

.

“Yusleem meya hanaka zuwa wurin matar da zan aura maka? Tunfa rannan nace maka kaje ku gaisa amma shine bakaje ba?

To lallai lallai kaje yau”

“Mami yarinyar shekararta nawane? Tayi 22?”

Girgiza kai mami tayi, “banajin zatafi 20 gaskiya”

.

“To agaskiya Mami ni tayi min kankanta da yawa, ina laifin ma yar 23 zuwa 25,amma kawai ni akawo min wata karamar yarinya tazo tana yimin yarinta..”

“Kajishi sai kace wani abun arziki yake yiwa matan idan ankai mishi, ina ruwanka da kankantarta? Kaida duk aure auren nan da kayi bana jin akwai mace kwaya daya da zakace kunyi rayuwar aure da ita, duk fa sakinsu kake yi kafin wani abu yashiga tsakaninku…”

Kawar da kanshi yayi bai kalli bangaren da mamin takeba,

“Koba haka bane..?”

“Mami wai sune suka fada miki hakan?” Yafada yana kallon wani wuri,

.

“Kai kasani dai,nidai kaji abinda nafada maka yau dinnan kaje wurinta ku gaisa”

Bai amsa ba yatsiri danne dannen waya,

“Wai idan ana yimika magana sai ka hau danne dannen waya, kaji abinda nafada?”

“Naji mami…”

“Ba maganar kaji bane, dama ai nasan kaji, so nake ka aikata abinda nasaka, sannan idan kasan kanada matsala ka fada min tunda wuri sai in nemo maka magani…”

.

Sunkuyar da kanshi yayi yana murmushi, shi baya son yaji mami tana irin wannan maganar,

“Kaji abinda nace?”

“Naji, mami dan Allah kibar maganar nan nifa lafiyata kalau”

.

“Yusleem ai dole inyi wannan maganar domin tazama dole, idan ba marar lafiya ba wanne namiji ne za arinka aura masa kyawawan yanmata yazauna yana kallonsu sai ankwana biyu ka sakesu? Nidai har yau ina nan akan bakana nacewar kana tareda aljana dan haka ya zama wajibi inci gaba da nemar maka mafita”

Sajensa yafara shafawa kansa asunkuye idanuwansa akasa,

“Yanzu katashi kaje kaci abinci inyaso sai ka karasa gida ka shirya kaje can gidansu nusaiban”

Tashi yayi yaje yahau kan dining ya dan fara dudduba abubuwan da aka dafa, tuwon shinkafa da miyar ganye ya saka yadan ci ya mike, har lokacin mami na zaune acikin falo, lekata yayi yai mata sallama yafita,

Shi dai adole zaije wurin yarinyar nan, yasan tunda mami takafe akan sai anyi auren nan to ko me zaiyi bazata fasaba ba, da wannan tunanin yashiga cikin gidansa yaje yayi wanka ya shirya,

.

Kananan kaya yasaka dark blue din t shirt mai gajeren hannu da bakin jeans, fuskar nan ahade babu alamun fara’a,kamshin turaren albahrainil madina ne ke ta faman tashi daga jikinsa,

Saida yayi sallar magrib a masallacin dake kofar gidanshi sannan ya dauki mota yafita lokacin gari yasoma dan yin duhu,

“Mtswwww..” Yaja dogon tsaki, tsakin yayi tayi yana bin kwatancen da mami tayi masa har yasamu ya gano gidansu nusaiba,

Yana hakimce acikin motarshi ya tura yaro ya kirata, gidan yaketa bi da kallo yana daga cikin motar, gidan ba wani babba bane sai dai rufin asiri,

Yana daga ciki azaune ya hango ta tana fitowa daga ciki, kawar da kanshi yayi daga kallonta sannan kuma bai fito daga cikin motar ba har ta karaso,

Glass din motar ya zuge yayi kasa dashi yana kallonta fuska ahade….

      ***

Fuska adaure yusleem ke karewa nusaiba kallo aranshi yana mamakin wai shine zai auri wannan yar karamar yarinyar domin shi aduk matan da mami ke aura masa ma babu wacce take kasa da shekaru 23,

.

Muryar nusaiba ce ta katse masa tunaninsa,

“Ina wuni..?”

Sai da yayi kamar bazai amsa ba sannan ya amsa gaisuwar tata da kyar,

Daga nan yayi shiru itama shiru din tayi domin bata da abin cewa, kallonshi nusaiba keyi yana cikin mota a zaune ita kuma ya barta awaje atsaye saboda tsabar mulki,

.

Wayarshi ya dauka yafara latsawa zuwa can ya dan kalleta kamar wanda akayiwa dole,

“Sai anjima…”

Glass din motar yayi sama dashi nan ta matsa tabashi wuri yaja motarshi yayi gaba, bin motar da kallo nusaiba tayi acikin ranta tana yaba kyawun siffarshi amma kuma akwai iya tsare gida da dan karen wulakanci nan da nan taji auren nashi ya fice mata arai,

Shikam yusleem tun lokacin da yabar gidansu nusaiba yayi watsi da maganar aurenta domin gaba dayanta bata yimasa ba,

Bai samu zarafin zuwa gidan mami ba sai washe gari da yamma,

.

Acikin bedroom dinta ya sameta tana yin waya da su khalifa,

Wuri yasamu yazauna akan stoll din mudubinta yana kallonta,

Sallama tayi dasu khalifa ta juya tana fuskantarshi,

“Barka da hutawa mami..”

“Yawwa sarkin taurin kai.., yanzu kai haka dama ake yin zance? Kaje ka tisa yarinya agaba da harara, fuskarka adaure kamar mala’ikan mutuwa..”

Zamanshi ya gyara,

.

“Mami shiyasa nace maganar auren nan kibarshi kawai, yanzu ahakura da maganar auren wannan yarinyar, ki bani lokaci zanyi miki magana da kaina kuma da kaina zan gabatar miki da yarinyar da zan aura..”

Shiru mami tayi tana dan nazari,

“To yanzu baka jin idan nace afasa iyayenta zasu yimana kallon kananan mutane? Kuma ma duk ba wannan ba, kai dinnan ba tabbas garekaba, nasan ko na baka shekara azuwan ka fito da matar aure ba lallai ne ka iya yin hakan ba”

.

“Mami kidai bani damar ki gani nidai burina yanzu ki hakura da maganar auren nan wallahi yarinyar nan tayi min karama kofa surayya batayi ba ashekaru..”

“Ehhh to, bari dai sai nayi shawara”

“To shikenan mami Allah yasa ki amince da bukatata..”

“Ai bukatar taka ne bata alkhairi bace amma tunda ka dage zan duba nagani..”

“To mami..”

.

Mikewa yayi yafita Mami ta rakashi da ido ita yanzu tausayi ma yake bata saboda takamaimai ba asan abinda ke damunsa ba,

Aminiyarta hajiya fa’iza ta Kira wato mahaifiyar khadija matar yusleem tada wacce yasaka,

Shawararta mami ta nema dangane da auren da take nemarwa yusleem, ajiyar zuciya hajiya fa’iza ta ajiye sannan cikin sanyin murya tafara magana,

.

“Hajiya siyama nidai aganina ki rabuda yaron nan karki sake yimasa wani auren har nan da wani lokaci,

Abinda yasa kikaji nace haka shine, kinga dai nafarko sakin auren da yusleem yakeyi yayi yawa kuma hakan yana haifar da bacin sunansa acikin al’umma sannan kuma suma yaran da yake sakin kinga yana rage musu wata kima da daraja a matsayinsu na yanmata domin koda babu abinda yataba shiga tsakaninsu tofa da zarar ya sakesu sunansu zawarawa sannan iyayensu kamar fa anshiga hakkinsu shiyasa ni nake ganin ahakura da batun auren nan inyaso sai kici gaba da lallabashi har yasamu ya sanar dake matsalarshi…”

Itama mami ajiyar zuciyar ta sauke,

.

“Hakane hajiya fa’iza, hakika gaskiya kika fadi shikenan insha Allah zanyi yanda kikace”

“Babu komai siyama,Allah dai yabamu mafita”

“Amin ya Allah”

Sallama sukayi mami ta katse wayar, tabbas tasan abinda hajiya fa’iza tafadi gaskiya ne shiyasa ma ta kuduri niyyar zuwa gidansu nusaiba da kanta domin tayiwa iyayenta bayani,

Aranar da yamma taje gidan, lokacin da ta shiga dama ta iske Baban nusaiban da mahaifiyarta sun sakata agaba sai fada suke ta inda suke shiga bata nan suke fitaba saboda tace bazata auri yusleem ba ita tsoranshi takeji,

“Ko zaki mutu kuwa dolenki sai kin aureshi..” Inji mahaifin nusaiba, ganin mami yasa suka dakata daga fadan da suke yiwa nusaiba, nan mami ta sanar dasu anjanye maganar aure amma dukiyar aure wacce aka kai anbar musu,

Bacin rai da tashin hankalin da iyayen nusaiba suka shiga ba kadan bane itada dai mami nan tayi musu sallama tatafi tabarsu da mita.

***

  “Hajiya kubra dan Allah ki hakura kidaina kukan nan haka, haba kamar wadda aka yiwa mutuwa? Karfa ki manta tafiya ba mutuwa bace”

Dago da jajayen idanuwanta tayi tana kallon mai gidan nata wanda ke zaune kusa da ita,

“Haba Alhaji, dole nayi kuka ai, yanzu  bazan sake ganin amal ba sai nanda shekara daya..”

“Haba hajiya kubra sai kace yarinya, ya kike abu irin na yara ne, ai naga ga waya nan akoda yaushe zaku rinka gaisawa..”

Cigaba da kukanta tayi bata amsa ba, yana shirin sake yi mata magana wayarshi dake aljihunsa tafara ringing nan yacirota yaduba, ganin Wanda ke kiran nashi yasashi saurin mikewa yana kallonta”

“Hajiya kubra ina zuwa, Alhaji Abubakar ne yazo,dama munyi dashi zaizo yanzu, ina zuwa”

Bai jira amsarta ba yayi azamar ficewa daga cikin bedroom din nata yafita zuwa part dinshi…

.

      ***Amininshi Alhaji Abubakar ya hango tareda tawagarsa masu rufa masa baya domin ayanzu haka aminin nashi shine ke rike da mukamin mataimakin gwamna na wannan jiha,

Hannu Alhaji Sa’id yabawa Alhaji Abubakar tareda janshi zuwa cikin falonshi,

“Ya banga uwar gidan ba, ko taje unguwa ne?” Alhaji Abubakar ya tambaya cikin raha,

.

“Ai hajiya kubra yau zuciyar tata babu sauki ranka ya dade domin kuwa tunda amal tabar gidan nan ta tafi kasar India karatu jiya shikenan hajiya ta rasa sukuni acikin ranta..”

“Allah sarki, kasan ai rabuwa da d’a sai dole balle ma ita da bata da wasu yayan sai iya amal..”

“To amma ranka yadade ba hakuri akeyi ba? Dukkan al’amarin duniya ai hakuri akeyi,idan ma amal bata tafi wata kasar karatu ba to nan gaba wani garin zata tafi aure, kaga kuwa ai babu amfanin sakawa zuciya damuwa tunda ita mace ansan cewar komin daren dadewa zata bar gida…”

.

“Hakane Alhaji sa’id, abin dai sai hakuri kasan lamarin mata, yawwa kafin in manta, dama abinda yasa kaga nazo yanzu shine so nake kayi min rakiya zuwa wani wuri, amma ba jimawa zamuyi ba, yanzun nan zamu dawo..”

“Atoh indai hakane ina zuwa, bari inje in sanar da kubra cewar nafita, ina zuwa”

“Amika min gaisuwa dan Allah” inji Alhaji Abubakar,

Fita Alhaji sa’id yayi zuwa part din matar tashi wato hajiya kubra, tana zaune kamar yadda yatafi yabarta tana sharar hawaye,

Hakuri yasake bata sannan yayi mata sallama yafita,

Acikin mota akan hanyarsu Alhaji Abubakar ya dubi aminin nashi yace,

“Ni da sai nake ganin kamar inhada kayan inkaiwa wasu mutane daban magidanta wadanda ke fama da talauci”

“A’a ranka yadade, gidan marayun dai ya kamata mukai domin suna bukatar taimako mutuka, sannan kaga ni ina ganin gidan yari ma (jail, prison) suma suna bukatar taimakon ku domin suma suna cikin wani hali, ya kamata arinka taimaka musu da barguna da kayan sanyi idan lokacin sanyi ne, idan kuma da zafi ne shima arinka duba abinda yafi cancanta da ataimaka musu dashi..”

Murmushi Alhaji Abubakar yayi,

.

“Hakane Alhaji sa’id, agaskiya ka Kawo shawara mai kyau kuma mai amfani shiyasa akoda yaushe nake farin cikin kasancewata dakai domin baka bani gurguwar shawara, yanzu abinda za ayi to bari mufara kaiwa gidan yarin ziyara inyaso idan mun fito sai mu karasa sauran wuraren..”

Karya kan motar driver yayi yadauki hanyar gidan yari nan sauran motocin suka rufa musu baya,

Ba karamin kaya aka saukewa gidan yarin ba domin abun tausayi ne idan kagansu gashi suna fama da babu, bayan sun kammala da nan dinne suka kama hanyar zuwa gidan marayu domin suma abasu nasu tallafin,

.

Su Hafsat suna ta kiciniyar yin sak’a kamar yadda suka saba aka sanar dasu zuwan bakinsu,dukkan yaran dake cikin gidan aka tattara aka kai wurin da mai girma mataimakin gwamna yake,

Bayan ansauke kayayyakin da aka kai musu ne aka jerasu alayi mataimakin gwamna yafara basu sadakar kudi sabbi fifil fifil,

Amina da Hafsat sune akusan karshe domin dama yanmatan ba yawa garesu ba basufi su shida ba,

.

Dai dai lokacin da Hafsat takarasa dan karbar kudin idon Alhaji sa’id yasauka akanta jin gabansa yayi yafadi nan take zuciyarsa tashiga harbawa da karfi,

Binta yayita yi da kallo har ta karba ta matsa Amina ta maye wurin,

Da hannu ya yafito shugaban ma’aikatan gidan,yana zuwa ya nuna masa Hafsat yace abashi ita zai tafi da ita zuwa gidanshi ma’ana zai cigaba da riketa,

Saida Alhaji Abubakar ya kammala rabawa marayun kudin sannan Alhaji sa’id ya sanar dashi cewar yaga wata yarinya budurwa ya nemi izinin abashi ita zai tafi da ita gidanshi,

Ba ayi wani dogon cike cike ba shugaban gidan marayun yace anbawa Alhaji sa’id hafsat yatafi da ita duba da wanda suka zo tare dashi,

Hafsat da Amina sun dauki hanya kenan zasu nufi wurin da makwancinsu yake taji ana kwala mata kira,

Komawa tayi tabi ma’aikacin gidan wanda aka turo kiranta, suna zuwa shugaban gidan ya kalleta,

“Yawwa Hafsat ke yau Allah yakawo karshen zamanki agidan nan, gashi kin samu wanda zai cigaba da kula dake..”

Kafin tayi yunkurin magana tuni har anbude mata kofar mota saboda har su Alhaji sa’id sun shiga cikin mota, ita kawai ake jira,

Sakin baki tayi nan shugaban gidan ya daka mata tsawa babu shiri tafada cikin motar wacce mutum biyune kacal aciki daga driver sai wani sss guda daya agaban motar,

Babu bata lokaci motocin suka nufi hanyar fita, Amina kuwa kawar hafsa sai shugaban gidan ne yayi mata bayani cewar antafi da Hafsat, kuka Amina tasa domin sunyi mutukar shakuwa komai tare suke yi tun tasowarsu acikin gidan domin kamar kusan lokaci daya ma aka kaisu gidan.

***

  Koda Mami takoma gida bata nunawa yusleem cewar anfasa bikin ba shikuma sai faman bata rai yake yana shan kamshi,

Yau ma rai abace yashiga cikin gidan domin yau su khalifa da Abdul zasu dawo daga Malaysia,

Lokacin da yashiga gidan har sun dawo suna falon mami sunyi kaca kaca da kayayyakin tsarabar da suka zo da ita,

“Yaya yanzu muke cewa ko sai munje bikonka ne..” Abdul yafada yana dariya,

.

Wuri yasamu ya zauna yana kallonsu daya bayan daya, dukkaninsu samarine masu kamarshi sai ko dan banbancin da baza arasaba,

“Yaya lafiya kuwa?” Khalifa yace,

“Kuma dai kun san halin yayanku idan aljanunshi na rashin son magana suka motsa” Mami tafada tana bude dan karamin akwatin dake kan cinyarta wanda su abdul suka taho dashi,

“Yaya gafa babbar tsaraba mun Kawo maka, domin Mami tafada mana ka kusa yin aure..” Inji abdul,

Harara ya aika musu da ita,

“Yaran nan kun rainani ko? Wai ni sa’anku ne?”

“Haba yaya kagafa kayan da muka siyo mukace sai ka kara akan lefen da zaka hada” Khalifa yace yana gumtse dariyarshi,

Baice dasu komai ba ya gimtse fuska ganin haka yasasu fara gaidashi nan ya amsa yana ciccin magani,

Tabe baki Mami tayi,

“Ai sai ka saki fuskarka idan maganar aurece to anfasa..”

D’aga ido yayi ya kalli Mami batare da yayi magana ba….

.

.

      ***Gidan Alhaji sa’id tawagar mai girma mataimakin gwamna suka wuce direct, hafsat tana zaune abayan mota sai zazzare ido take yi domin bata ma san inda suka nufa ba kasancewar ba fitowa sukeyi ba,

.

Wani kayataccen gida taga sun shiga wanda ya tsaru mutuka fadin girman gidan kuwa bata baki ne,

Bude mata kofar motar akayi tafito tana bin gidan da kallo,

Wurinta alhaji sa’id ya karasa bayan sunyi sallama da aminin nashi wanda tuni har tawagar tashi tafara fita daga cikin gidan,

.

Atsorace hafsa take binsa da kallo saboda rashin sabo gashi kuma uwa uba bata taba ganinshi ba,

“Zo mu karasa ciki..” Yace da ita lokacin da yakarasa kusa da ita,

Kamar kurma haka tayi domin bata iya amsawa ba illah bin bayanshi da tayi tana mai cigaba da karewa gidan kallo,

Tana biye dashi abaya har zuwa cikin wani hamshakin falo wanda ya kayatu mutuka da kayan alatun more rayuwa,

Tunda suka shiga cikin falon alhaji sa’id yake kwallawa matarshi kira,

“Hajiya kubra…. Hajiya kubra…,hajiya kubra ko bakya kusa ne?”

.

Amsawar da yaji hajiya kubran tayine ya dakatar dashi daga kwalla kiran da yake yi mata, falon tafito tana magana muryarta adashe saboda kukan da ta dade tanayi,

“Alhaji gani, har kun dawo?”

“Mun dawo kuma munyi farar tafiya tunda harda tsaraba nakawo miki..”

Hafsat ya nuna mata da yatsanshi, ido ta zaro ta bude baki cikeda mamaki domin da lokacin da ta fito sam bata lura da Hafsat dinba sai yanzu da ya nuna mata ita,

.

“Alhaji a ina kasamo amal? Dawo da ita kasa akayi?”

Dan murmushi alhaji sa’id yayi, “kidai kalleta dakyau kigani..”

“Alhaji ai naganta, amal ce, ai bai kamata kace adawo da itaba tunda karatunta karuwarmu ce gaba daya.., amal meyasa kika dawo?”

“Hajiya kubra wannan fa ba amal bace mai kamada amal ce, ganin kin tada hankalinki kina neman tayar da nawa hankalin shiyasa na Kawo miki ita..”

.

Sai a lokacin hajiya kubra tafara bin Hafsat da kallo tun daga kafarta zuwa kayan dake sanye ajikinta, ko shakka babu wannan ba amal bace amma kuma bata da banbanci da amal din sai ko gayu da wayewa wadda amal din zata fita dashi amma hatta kalar fatarsu da komai iri dayane kawai hutu da jin dadi fatar amal zata nunawa ta Hafsat,

“Ikon Allah baya karewa,tabbas wannan babu abinda zai hanani karbarta a matsayin amal domin kamar tasu ta isa..” Hajiya kubra tafada tana takawa har izuwa wurinda Hafsat ke tsaye nan tashiga kare mata kallo,

.

“Yawwa tunda bukatata tabiya shikenan dama burina ki cire damuwar dake ranki akan amal ki karbi wannan amadadinta”

“Alhaji ina kasamo min ita? Wallahi yarinyar nan batada maraba da’yata..”

“Hajiya kubra zanyi miki bayani daga baya saboda kinga yanzu lokacin sallar magrib yakawo kai, amma abinda nake so dake shine wannan yarinyar nakawo miki ita amana duk da cewar nasan zaki kula da ita tamkar yar da kika haifa saboda tayi kama da jininki amal, yanzu kije kibata duk abinda ya kamata..”

Narai narai da ido hajiya kubra tayi ta kalleshi,

“Amma dai alhaji ba aro aka bani itaba ko? Saboda bana son itama kwana biyu azo ace za arabani da ita”

.

“Kisha kuruminki hajjaju wannan yarinyar babu abinda zai rabaki da ita domin tazama’yarki halak malak..”

Farin cikine ya bayyana akan fuskar hajiya kubra wanda har saida takasa boye hakan,

“To alhaji, amma naji dadin wannan maganar,nayi mutukar farin ciki..”

Juyawa yayi yanufi kofar fita, cikin farin ciki hajiya kubra ta kama hannun Hafsat tana kallonta,

Tana rikeda hannunta har suka fice daga cikin falon suka shiga wani tafkeken dakin bacci wanda ke dauke da Italian bed pink colour,haka komai na cikin dakin kalarshi pink domin hatta bed sheet din dake shimfide akan gadon pink colour ne,

“Ya sunanki?” Hajiya kubra ta tambayi Hafsat har lokacin tana rikeda hannunta,

Sai a lokacin Hafsat tayi magana tun shigowarta gidan,

“Sunana Hafsat..” Tabata amsa,

.

“Hafsat, kamarku daya da tilon ‘yata kwaya daya amal shiyasa lokacin da naganki naji ina sonki har cikin zuciya…, nan dakinta ne ina so ki daukeshi a matsayin naki, kiyi amfani da duk wani abu wanda kika ganshi acikin dakin nan ko kuma cikin gidan nan..”

Sakin hannunta hajiya kubra tayi tajuya tafita, kan Hafsat adaure tafara bin dakin da kallo tana yaba irin haduwar da yayi domin kamar akasar turai, kan gadon ta kalla nan taga wasu jibga jibgan teddies guda biyu a jingine, kan mirror din dake cikin dakin kuwa kayan make up ne jere tamkar wani dan karamin shago,

Kananan frames ta hango guda hudu ajiye akan bedside drewar nan ta nufi wurin domin tahango kamar akwai hoton wata budurwa ajiki, nan ta nufi wurin da Sauri……

.

,

       ***Gaban frames din hafsat ta karasa da sauri ta mika hannu ta dauki guda daya ta kura masa idanuwa tafara kallo,

.

Gabanta ne yafara faduwa zuciyarta tana bugawa da karfi da karfi Wanda har saida ta kaita da zama asaman gadon dake gefenta,

Ko shakka babu badan rayuwarta agidan marayu tayita ba to da zata iya yarda da cewar wannan ta jikin hoton itace, sake kallon hoton tayi akaro na biyu wanda yarinyar jiki ke sanye da english wears pink din riga da farin wando, kanta sanye da hula pink colour,

“Ikon Allah…” Tafada ahankali tana mai sake dauko wani hoton tafara kallo, nan ta lalace wurin kallon hoton batare data kosa ba.

.

  Kasa koda zama hajiya kubra tayi illah kaiwa da kawowa da take ta faman yi dan tsananin farin ciki, tabbas wannan wani al’amari ne daga Allah Wanda shi kadai yabarwa kansa sani,

Ganin zama yagagara yasata fita ta nufi part din alhaji, shima shigowarsa kenan daga masallacin dake kofar gidansa,

.

Zama tayi akan kujerar dake makotaka da tashi,

“Alhaji nidai kaganni tsabar farin ciki nakasa zaune nakasa tsaye..”

Murmushi alhaji sa’id yayi,

“To in banda abinki hajiya menene abin kasa tsaye da kasa zaune? Yanzu ina ita yarinyar take?”

“Alhaji dole inkasa zaune in kasa tsaye mana,ai farin cikin da nake ciki bazai barni inyi hakaba, tace min sunanta hafsat, tana can dakin amal nakaita tayi wanka ta shirya sai tafito muyi dinner..”

.

“Hakan yayi daidai hajiya kubra,nidai abinda nakeso dake shine dan Allah ki rike yarinyar nan bisa amana duk danasan zaiyi wuya ki gallaza mata tunda bata da maraba da amal to amma wani lokacin ku mata ana ganin kamar kunfi kowa tausayi da rauni sai dai akan gallazawa yaran da ba nakuba kunfi kowa nuna rashin tausayi da rashin rauni, dan Allah ki riketa amana tunda kinga daga gidan marayu na daukota wannan yana nuna cewar ita maraya ce…”

.

“Haba alhaji ai basai kayi min wannan nasihar ba domin ko wanine yakawo min wannan yarinyar wanda bakai ba wallahi zan kula da ita…”

“Nasani hajiya kubra, Allah yayi miki albarka, yanzu ina tunanin ai tagama ko?”

“Ehh to bari indubo ingani”

Tashi tayi tafita takoma part dinta, dakin amal ta tura tashiga nan ta iske hafsat zaune ta kurawa hotunan amal ido ko kifawa bata yi,

“Hafsat…” Ta kira sunanta bayan takarasa kusa da ita, dagowa hafsat tayi ta kalleta,

“Na’am”

.

“Ya bakiyi wanka kin canja kayan jikinki ba? Tashi ki shiga bathroom kiyi wanka indan kin fito ga drewar din kayan amal nan ki duba duk wanda yayi miki kisaka..” Ta karasa zancen tana nuna mata drewar din da dan yatsanta,

“To” hafsat ta amsa har lokacin tana cike da mamaki domin ganin abubuwan dake faruwa take yi tamkar acikin mafarki,

Fita hajiya kubra ta sake yi ganin haka yasa hafsat tashi ta shiga cikin bathroom din, komai wanda ake bukata akwaishi acikin bathroom din babu bata lokaci tayi wanka ta fito, man da zata dan shafawa fatarta ta shiga nema domin duk wadanda ke kan dressing mirror din lotion ne dan haka dakyar tasamu wani me dan kama da Vaseline tashafa,

Gaban drewar taje ta bude nanfa mamaki yacikata domin kayane iya ganinta shake acikin drewar din,

Wata doguwar riga kalar ruwan hanta ta zaro da dan kwalinta tasaka ta dauki hijabinta tayi salla,tana saman abin sallar azaune a inda aka kebe musamman domin yin salla hajiya kubra tasake shigowa fuskarta dauke da murmushi,

.

“Hafsa kin idar ne?” Tajiyo muryar hajiya kubra na tambayarta,

“Ehh na idar..” Tabata amsa tana kokarin mikewa,

“Yawwa to taso kizo muje wurin alhaji”

Bin bayanta tayi suka fita, tiryan tiryan tana biyeda ita har suka shiga falon alhaji sa’id Wanda ke zaune yana kallon labarai a tauraron dan adam,

Ganinsu yasashi rage volume din tv din ya fadada murmushinsa yana kallonsu domin sai yake ganin kamar hajiya kubra ce da amal suke dososhi kamar yadda suka saba akowanne dare domin yin hira,

“Alhaji…,labarai kake kallo?”

“Wallahi kuwa hajiya, keda ‘yar takine?”

.

“Ehh amma har yanzu dai banga alamar zata sake ta saki jiki damu ba saboda ganinmu take baki agareta” hajiya kubra tafada fuskarta da yar damuwa,

“To wannan kuma dama ai sai ahankali,kin san ai yau tafara ganinmu,sai asannu ko Hafsat?” Yakarasa zancen cikin barkwanci,

Hafsat kam shiru tayi takasa koda kallonsu, sai dai wani lokacin ta dan saci kallonsu ahaka har lokacin sallar isha yayi nan alhaji sa’id yafita masallaci yabarsu a cikin falon nashi,

Anan Hafsat da hajiya kubra sukayi sallarsu,suna nan zaune har alhaji sa’id yadawo dan haka hajiya kubra ta mike domin gabatar musu da abincin dare,

“Hafsat zo muje kitchen..”

.

Mikewa Hafsat tayi suka fita zuwa cikin kitchen wanda kallo kawai Hafsat ta bude ido tanayi saboda ita ba taba ganin irin shi tayiba,

Akan babban faranti hajiya kubra ta jera flasks din abincin nan Hafsat din ta karba ita kuma hajiya kubra ta debi filet da sauran abubuwan da suka kamata,

Zama Hafsat tayi bayan ta ajiye farantin, acikin dan madaidaicin filet hajiya kubra ta zuba musu abincin, tuwon semo miyar danyar kubewa,

“Hafsat zo muci abincin..”

Matsawa hafsa tayi tasa hannu ita a zatonta iya ita da hajiya kubran ne kadai zasuci amma sai taga sabanin haka domin shima alhajin saka hannu yayi saboda al’adarsu tare suke cin abincin tare dashi da hajiya da amal, Hafsat ji tayi kaunarsu ta fara darsuwa acikin zuciyarta, duk da cewar taki dan sakin jiki dasu amma hajiya kubra sai sakota take acikin hirar tasu dahaka suka kammala cin abincin.

.

  Suna falon alhaji sa’id azaune har misalin karfe 9 nadare lokacinne hajiya kubra ta mike ta kalli Hafsat,

“Hafsa taso muje ki kwanta naga kamar bacci kikeji ko?”

Dan murmushin yake Hafsat tayi ta tashi ta kalli alhaji sa’id,

Dan rissinawa tayi, “Alhaji saida safe”

Cikeda fara’a ya amsa tabi bayan hajiya kubra suka fita,

“Abba zaki rinka cewa alhaji kinji, nikuma ummi saboda haka amal ke kiranmu, kinga tunda yanzu kema mune iyayenki..”

Hajiya kubra tace da ita akan hanyarsu ta zuwa part dinta,

“Tohh Ummi..”

Dadi hajiya kubra taji jin Hafsat ta kirata da Ummi,

Sai da safe Hafsat tayiwa hajiya kubra tashiga daki,zama tayi akan gado tana mai bin dakin da kallo….

Kasa bacci Hafsat tayi illa tunanin rayuwarta da take ta faman yi,


Ji tayi kamar ta fashe da kuka a sakamakon fadowa ranta da kawarta Amina tayi,


Duk da tasan abin atayata farin cikine saboda canjin rayuwar data samu amma duk da haka tana jin radadi acikin zuciyarta na rabuwa da gidan marayu da tayi domin tariga da ta saba da mutanen ciki,


Wadannan tunane tunanen da tarinka yi sune suka hana idonta bacci har aka fara kiran assalatu, a kunnenta aka shiga sallar asubah nan ta tashi tashiga bathroom ta dauro alwala tafito, salla tayi tareda addu’o’i masu yawan gaske, anan inda tayi sallar anan bacci ya kwasheta.


Misalin karfe shida da rabi na safe hajiya kubra ta shiga cikin dakin ganinta kwance tana bacci yasata juyawa tafita batare data tasheta ba domin ta fahimci cewar tayi sallar asubah,


Hafsat dai bata samu damar tashi daga wannan baccin ba mai cikeda mafarkai iri iri wadanda takasa tuno koda guda daya daga ciki lokacin data farka, ba ita tatashi ba sai misalin karfe 10 zuwa da rabi, hajiya kubra kuwa ta leka dakin yafi sau akirga,


Zama tayi tana bin dakin da kallo kamar yanzu ne tashigo ciki, daga bisani ta sauke idonta kasa ta mike, fita tayi acikin falo ta hango hajiya kubra tasha kwalliya cikin wata shadda kamfala tana faman jejjera abin Karin kumallo akan dining table,


Sam hajiya kubra bataji fitowarta ba har saida tayi magana,


“Ummi ina kwana..”


Cikeda farin ciki hajiya kubra ta juyo ganin Hafsat atsugunne yasata kamo kafadunta ta tada ita tsaye tana murmushi,


“Lafiya lau Hafsat, sai yanzu aka tashi? Ai na shisshiga dakin kinata bacci”

.

Murmushin yake Hafsat tayi,


“Ummi akwai abinda za ayi ne?”


“Kamar mefa Hafsa na?”


“Na aikin gida..”


“A’a Hafsa babu abinda za ayi, har ankammala gyara gidan ai, inada ma’aikata na masu yimin komai da kika sani, girki ne kadai nake yin abuna dakaina, yanzu kije kiyi wanka ki shirya ki fito mu karya lokacin abbanku shima ya fito”


“Toh” ta amsa tareda juyawa takoma cikin daki, wanka tayi ta shirya ta fito zuciyarta cikeda mamaki na irin tarba da soyayyar da hajiya kubra ke nuna mata wadda abisa dukkan alamu zata riketa amana kamar itace ta haifeta,


Atamfa ta saka dinkin riga da zanine pieces kalar atamfar kalar ruwan hoda, hijabinta da tazo dashi tasa ta fita,


Lokacin data fita tuni har su hajiya kubra sun hau kan table suna jiranta, durkuwa tayi tagaida Alhaji sa’id,


Fuska asake ya amsa gaisuwarta yakare maganar da fadin,


“Tashi, tashi, zo ga kujera ki zauna”


Mikewa tayi taje ta zauna akusa da hajiya kubra wacce tafara kokarin hadawa Alhaji tea,


“Hafsa babu wasu hijaban ne akayan amal naga kinata saka wannan?”


“A’a ban duba ba”


“To ai kuwa inajin tabar hijabai dan bata tafi da komai nataba duk agida tabarsu…”

.

“Ashe yar uwarta tabarwa bata saniba” Alhaji sa’id ya karbe zancen,


Dariya hajiya kubra tayi,


“Ai so nake idan ta sai sim ta kira inyi mata albishir”


“To ai kuwa da dai nine naso inyi albishir dinnan amma naga kina nema ki rigani..”


Dariya sukayi dukkaninsu inbanda Hafsat wacce dan murmushi kawai tayi,


Abinsu gwanin sha’awa suna karyawa suna hirarsu har suka kammala nan Alhaji sa’id ya mike yana gyara babbar rigar dake jikinsa domin wurin aiki zai fita,


“Adawo lafiya, Allah ya kiyaye hanya” Hafsat tace dashi tana rakube ajikin kujera,


“Amin Hafsat, nidai abinda nakeso dake shine ki saki jikinki ki dauka cewar nan gidanku ne sannan kuma mu iyayenki ne, kinji? Allah yayi miki albarka”


“Amin, amin…” Hajiya kubra ta amsa tana murmushi,


Juyawa yayi yafita hajiya kubra tana biye dashi ganin haka yasa hafsat tattare kayan da sukayi amfani dasu wurin karyawa ta nufi kitchen, tana tsaka da daurayesu hajiya kubra ta dawo daga rakiyar da ta yiwa alhaji,

.

“Ahh hafsat ai ban sakiba, waye yace ki wankesu? Nafada miki akwai masu aiki zasu yi har wanke wanken”


“Babu komai Ummi nima gani nayi babu abinda zanyi shiyasa nace bari in wanke..”


“To shikenan ai kin kyauta, ke baki da son jiki ba irin amal ba, amal bata son motsi nan da can koda yaushe tana nade akan gado kamar wata mage..”


‘Yar dariya Hafsat tayi taci gaba da wanke wanken yayinda ita kuma hajiya kubra taci gaba da bata labari akan amal wannan yasa Hafsat sake fahimtar cewar ba karamin so hajiya kubra ke yiwa yar tata ba domin magana daya biyu sai ta sako zancen amal,


Tsaf Hafsat ta gyare kitchen din bayan ta kammala wanke wanken, falo suka koma suka zauna suka fara kallo atashar tauraron dan adam,


Wannan zaman da suka yi shine yabawa Hafsat damar sakin jiki sosai da hajiya kubra domin ta dan warware suna yin hira har tana bata labarin irin yanda rayuwarta ta gudana agidan marayu…..


        ***


Sosai hafsat ta sake da hajiya kubra domin hatta girkin rana tare suka yi suka shiryashi akan table saboda alhaji sa’id yana dawowa cin abinci daga office,


Har dare suna tare suna hira afalon alhaji sa’id wanda kusan rabin hirar ta amal ce, yauma kamar jiya atare suka fita ita da hajiya kubra suka yiwa alhaji sai da safe,


Yauma saida tayi karfin hali sannan tasamu bacci ya dauketa domin har lokacin tana kewar gidan marayu da kuma kewar kawarta amina,


Washe gari da safe suna kan table suna karyawa amal ta kira mahaifinta,nan hajiya kubra ta shiga murna domin bakinta yaki rufuwa,


Mikawa hajiya kubra wayar Alhaji sa’id yayi bayan sun kammala gaisawa shida amal din, cikin farin ciki hajiya kubra ta fara yiwa amal albishir na zuwan Hafsat gidan, Hafsat tana zaune tanaji bata dai jiyo abinda amal din taceba kawai dai taga hajiya kubra ta mika mata wayar tana fadin,

.

“To shikenan bari abata..”


Karbar wayar tayi ta kara akunnenta nan taji muryar amal din kamar zata fasa mata dodon kunne dan tsananin kara,


Tamkar dama sun san juna haka suka gaisa gamida yin sallama,


Cikin fara’a Alhaji sa’id ya mike domin fita adawo lafiya Hafsat tayi masa, zama tayi shiru bayan fitarsu shida hajiya kubra,tunani tafara aranta na yanda kowa agidan ke sonta da kaunarta tabbas ta yarda Allah shine kadirun ala man yasha’u domin ya sauya rayuwarta ya kuma juyata acikin lokaci kankani,


Yanzu kam ta warware sannan tagama sakewa da hajiya kubra, abu dayane kawai ke damunta shine kewar Amina tare da sauran jama’ar da ta dade da sani arayuwarta,


Haka dai ta rinka boye damuwarta taci gaba da zama tareda su hajiya kubra har tayi sati biyu agidan, kullum da daddare sai hajiya kubra ko Alhaji sa’id sun kira amal angaisa da ita, ita kuwa idan aka bata wayar domin su gaisa amal cewa take tana ta dokin ganinta saboda taji yanda su umminta ke zuzuta tsananin kamanninsu da Hafsat din,


Duk da cewar tana jin dadin zaman gidan kuma babu abinda ta nema tarasa amma hakan bai hanata shiga damuwa ba, tana yawan tuna rayuwarta ta baya wadda tayita acikin rashin gata da rashin galihu sannan uwa uba cikin maraici,wannan dalilin ne yasa take burin ta bada tata gudun mawar domin aganinta wannan wata damace ta samu wurin taimakon yan uwanta marayu,

.

Ganin kamar tana cikin damuwa yasa hajiya kubra tambayarta koda akwai abinda ke damunta, bata boye mata ba ta sanar mata da gaskiyar bukatarta na son zuwa kaiwa kawarta Amina wacce ke gidan Marayu ziyara,


“To ai duk wannan mai sauki ne Hafsat, idan kin shirya kiyi min magana sai insa driver yakaiki..”


“Toh Ummi nagode madalla Allah yasaka da alkhairi, Allah ya…”


Dakatar da ita hajiya kubra tayi,


“Bana son godiyar nan Hafsat, duk abinda nayi miki kaina nayiwa, yanzu me zaki kaiwa kawar taki?”


“Ummi girki kawai zanyi mata inkai mata domin wallahi hatta abinci wahala yake mana acan..”


“To shikenan gashi nan sai ki zabi abinda zaki dafa mata,duk abinda zaki bukata da akwai kuma kin san wurinda yake..”


Daga haka hajiya kubra ta juya tawuce cikin falo domin lokacin acikin kitchen suke Hafsat tana wanke wanke saboda sam bata son zama batare da tayi dan wani aiki ba,

.

Shinkafa da miyar kaji Hafsat ta dafawa Amina cikin manyan food flaks guda biyu, wanka tayi ta shirya cikin wata shaddar amal kalar ruwan toka,farin hijab tasa tafito ta iske hajiya kubra zaune tana karanta wani English novel,


“Hafsat anfito?”


“Ehh Ummi nashirya”


“To driver yana waje yana jiranki, yanzu idan kin tafi sai yaushe zaki dawo?”


“Ummi zan dan jima saboda kinga rabona da Amina an kwana biyu..”


“To shikenan sai kin dawo Allah ya kiyaye hanya..”


“Amin” ta amsa tareda fita ta shiga kitchen ta debi girkin da tayiwa aminan tafita compound din gidan inda salisu driver yake jiranta,


Har wani nushadi takeji yau haka kawai saboda zataje taga Amina da sauran mutanen dake gidan marayun.


****


  Tunda yusleem yaji mami tace masa anjanye maganar aurenshi shikenan yasaki jiki yayi watsi da maganar bai kara bi takanta ba amma ita mami abun yana nan aranta domin har yanzu kullum cikin tanadin kayan aurenshi take, duk inda taji ankawo kaya masu kyau ko masu tsada na mata sai ta siyo kuma zata nuna masa tace matarsa ta siyawa wacce zai auro nan gaba, shidai baya magana sai dai yayi shiru amma kuma shine zai biya kudin kayan da ta siyo wannan kam ko nawane baya shayin biya kuma bai taba musu ba,


Yauma hakance tafaru lokacin da ya shigo gidan ya isketa afalo ita da wata mata wacce ta Kawo mata kaya daga dubai, wasu dogayen riguna ne masu adon stones ajiki hadaddu,


Daga rigunan mami taci gaba dayi tana jujjuya su, bayan sallamar da yayi bai sake yin magana ba  yasamu wuri ya zauna,


“Yusleem kaga rigunan nan daga dubai aka kawo kuma sunada kyau nayi sha’awarsu mutuka ko zaka siyawa matarka..?”


Yaji sarai abind mamin tace amma bai amsaba, kasancewar tasan halin abinta yasata daukar kala biyu, ja da kuma baka mai adon golden ajiki,


“Gashi na daukar maka guda biyu, duk guda daya 35 thousands ahakanma ragi tayi min amma bahaka take sayarwa ba..”

.

Gyada kai yayi har lokacin baice komai ba saboda shidai baiga amfanin kayan nan da mami ta dage taketa siya ba,


Saida mai kayan tatafi sannan yadubi mami wacce ke zaune har lokacin tana ta dudduba rigunan tana yaba kyawunsu,


“Wai mami dan Allah meye amfanin wadannan kayan da kiketa siye?”


“Amfaninsu? Amfaninsu kake tambaya? Kaifa mukayi dakai zaka nemo matar aure, ko kamanta? Ai zuba maka ido nayi ka gama zagaye zagayenka ka Kawo min wacce kakeso idan kuma hakan ya faskara to ni bazan gajiya ba wurin sake nemo maka wata..”


Shiru yayi ya lumshe manyan idanuwansa tareda jingina da jikin kujerar da yake zaune batare da yayi magana ba….


      ***


Lokacin da Hafsa takarasa gidan marayun ba karamin dadin ganinta Amina tajiba domin bata taba tsammanin sake yin tozali da itaba acikin rayuwarta,


Kebewa sukayi suka samu kasan wata bishiyar darbejiya suka zauna suka fara tattaunawa,


“Hafsa har kinyi kyau, ki ganki yanda kika sauya lokaci daya” Amina tace da Hafsat tana bin jikin Hafsat din da kallo,


“Amina kema insha Allah canji yana nan zuwar miki ai tunda mukayi hakuri da rayuwar da muka samu kanmu to da izinin Allah zamu dace da samun babban rabo..”


“Hmmm abar kaza dai kawai acikin gashinta hafsa, yawwa baki bani labarin yanda akayi ba rannan da kika tafi..”

.

Kwashewa duk yadda akayi hafsat tayi tafadawa amina da irin gatan da take samu yanzu,


Sun dade suna hira domin sai da la’asar liss sannan hafsat tatafi nan dinma kamar kada su rabu da amina saida hafsa tace ai zata rinka zuwa akai akai sannan hankalin amina ya kwanta.


Lokacin da hafsat takoma gida har alhaji sa’id yadawo daga office yana zaune a falon hajiya kubra shida ita bayan ya kammala cin abinci kasancewar yau bai dawo yin lunch ba,


Sallama tayi tashiga bayan sun amsa mata,


“Hafsa yau kuma ziyara aka kai?” Alhaji sa’id ya tambayeta yana murmushi,


“Ehh Abba” tabashi amsa,


“To ai yayi kyau, kin kyauta mutuka wannan ya nuna min cewa bazaki manta dasu ba duk abinda kika zama nan gaba”


“Ai da alama kam hafsat bazata manta dasu ba” hajiya kubra ta karbe zancen ta hanyar bawa alhajin amsa,


Zama hafsat tayi acikin falon tana sauraren hirar da su alhaji keyi wanda basu suka tashiba sai da sukaji anfara kiran sallar magrib.


.

  Satin hafsat uku agidan amma kai idan kaganta zakace wata uku tayi domin tayi kiba tayi bul bul sosai, domin tana samun kulawa sosai daga iyayen rikon nata ga gata da suke nuna mata kamar sune suka haifeta,


Malamai guda biyu musamman alhaji sa’id ya daukosu domin su rinka koyar da ita karatun boko da na Arabic, sannan kuma yayi mata register a wata center ta mata wacce ake koyar da sana’o’i saboda tana son tasake samun kwarewa sosai akan sakar da ta iya,


Wadannan abubuwan da tasaka agaba sune suka saka bata da lokacin kanta yanzu koda yaushe tana da abinyi amma hakan bai hanata ware lokaci na ziyartar kawarta amina ba,


A fannin sakar ma tafi maida hankali domin hajiya kubra tafada mata cewar idan har ta gwanance to zata siyo mata keken saka kuma tanada shagon saida kayayyaki zata bata jari tafara saka kaya ana kaiwa shagon ana sayar mata wannan dalilin ne yasa ta bada himma sosai har ta samu kwarewa kamar yadda hajiya kubran keso,


Satinsu shida aka yayesu domin sun iya sosai, alkawarin da hajiya kubra ta daukar mata ta cika ta hanyar siyo mata keken saka harda sabuwar wayar hannu dambasheshiya mai kyau kirar kamfanin LG,


Murna wurin hafsa sai wanda yagani, samun keke da tayi sai yasake rike lokacin ta koda yaushe tana kai tana aiki acikin satittika kadan ta saka kaya masu yawan gaske, kayan sanyi na yara da towel da safa da hula,


Diban kayan akayi aka kai shagon hajiya kubra na kasuwa acikin satin aka Kawo kudin kayan domin har sun kare,


Kiranta hajiya kubra tayi itada alhaji sa’id domin suji ra’ayinta dangane da kudin,


“Hafsat kudin naki ajiyewa zakiyi a banki ko kuma wani abu zaki siyo ki ajiye?” Alhaji sa’id ya tambayeta,

.

“Abba ba ajiyewa zanyi ba, kaya nakeso insiya inkaiwa gidan marayu gudun mawa” tabashi amsa idonta yana kallon kasa,


Murmushi Alhaji sa’id yayi,


“Allah sarki hafsat hakika ke tagari ce kuma kinada hankali da nutsuwa, Allah yayi miki albarka, yanzu abinda za ayi shine, gobe idan Allah yakaimu zan hadaki da driver sai yakaiki kasuwa ki siyi duk abubuwan da kike ganin zaki siya sai kuje ki kai musu..”


“Allah yabaki lada ya biyaki da gidan aljanna kinji..” Hajiya kubra tayi magana cikin marerecewa,


Tashi hafsa tayi tafita domin malamin dake koyar da ita karatun arabi duk yamma yazo yana jiranta.


Washe gari kamar yadda alhaji sa’id ya alkawarta haka yasa driver ya dauketa yakaita kasuwa tayi siyayya wadda saida ta karar da kudin tass ko kwandala baiyi saura ba, daga nan gidan marayu suka wuce, koda sukaje kuma akaga irin gudun mawar da takai saida kowa yayi mamaki domin kayane na amfanin yau da kullum irinsu sabulun wanka da na wanki, omo, sugar, man shafawa da makamantansu,


Rungumeta Amina tayi tana kukan farin ciki tareda yi mata addu’ar alkhairi, bama Amina kadai ba kowa addu’ar da yake yi mata kenan….


         ***


Haka rayuwar Hafsat taci gaba da tafiya akoda yaushe burinta shine taga ta taimakawa yan uwanta marayu wadanda basu samu gataba suke zaune acikin gidan marayu,


Rikon da hajiya kubra keyi mata kuwa rikone na tsakani da Allah wanda ko yar cikinta iya abinda zata iya yimata kenan,

.

Kasancewar Hafsat din ta maida hankali akan karatuttukan da ake koya mata yasa malamin dake koyar da ita fadawa Alhaji sa’id cewar lokaci yayi wanda yadace asata a makaranta duk da cewar bata faro karatun daga tushe ba amma yana kyautata zaton cewar zata iya, shawarar malamin Alhaji sa’id yabi aka sa Hafsat din awata makaranta ta day,


Zuwanta makaranta yasata sake samun gogewa da wayewa domin ta hadu da yan mata irinta wadanda suka fita wayewa,


Haka rayuwarta taci gaba da gudana sannan duk da ta shiga makaranta hakan bai hanata cigaba da yin saka ba tana saidawa idan ta hada kudin sai taje kasuwa tayi siyayya kamar yadda tasaba ta kai kayan gidan marayu.


Kwanci tashi har Amina kawarta ta samu mijin aure daya daga cikin ma’aikatan gidan marayun ne zai aureta,ba karamin dadi Hafsat tajiba domin Amina itama zata bar rayuwar kunci da talauci gamida maraici, tareda ita aka gudanar da komai aka daura aure suka rakata gidan mijinta wanda keda makobtaka da gidan marayun.


Akwana atashi ahaka Hafsat tashiga aji biyar na secondary domin dama a aji hudu aka sakata, kuma acikin wannan lokacin ne amal tazo gida hutu daga kasar Malaysia, kai idan kagansu kamar wasu yan biyu domin ko Alhaji sa’id dakyar yake iya banbance su musamman ma idan suka saka kaya iri daya domin hajiya kubra tun zuwan Hafsat gidan iri daya take yimusu dinki tareda amal bata taba banbantawa ba,


Saida amal tayi wata uku sannan takoma makaranta tana cike da kewar Hafsa domin komai tare suke yi gashi jininsu ya hadu sosai, itama Hafsat din tana mutukar kewarta.


***


   Abangaren yusleem kuwa har yanzu bai fitar da matar aureba duk kuwa da irin Matsin lambar da Mami keyi masa akan ya zabo matar aure amma shiru to shi girman kanshi ma bazai barshi ya tunkari mace da maganar soba,


Kullum idan yaje gidan Mami sai ta tisashi agaba da tambayoyi amma sai dai yayi mata shiru daga karshe ma sai cemata yayi shifa har yanzu bai samu budurwar ba, kyaleshi Mami tayi ta zuba masa ido domin ta dade da sanin cewar aljana ce ta aureshi.


***


  Misalin karfe 2:30 narana agogon hannunta ya nuna, dan karamin tsaki taja ta fito daga cikin motar tata ta kulleta ta tsaya bakin titi tana jiran adaidaita sahu,kallo daya kawai zaka yimata ka fahimci ko wacece ita domin sanye take cikin atamfa exclusive purple colour da mayafi shima purple sai takalmi da jaka duk purple colour,

.

Bakowa bace face Mami wadda ta dawo daga al hikima clinic dubiyar yar kawarta hajiya maryam wacce aka yiwa cs adaren jiya, ganin motarta ta bata matsala yasata tsayawa tanata kiran driver dinta amma bata sameshi ba wannan dalilin ne yasata barin motar awurin ta zabi tasamu adaidaita sahu yakaita gida inyaso daga baya sai drivern yazo ya dauki motar,


Adaidaita sahu ta tare tashiga yaja suka tafi, akan hanyarsu ne daidai queen ihsan restaurant akofar wata private school ta hangi wata yar budurwa tana tsaye sanye da uniform wanda yayi mutukar karbarta tana tare adaidaita sahun,


Da a niyyar Mami ta dauki drop yakaita gida kawai amma ganin budurwar wacce da alama itama agajiye take sannan ga rana yasa mami barin mai adaidaita sahun ya tsaya yadauki budurwar,


Lokacin da budurwar ta shigo ciki saida tagaida mamin, binta da dan kallo mamin ta yi tana yaba hankalinta,

.

“Hajiya ina zan saukeki..?” Mai adaidaita sahun ya tambayi budurwar,


“A titin fahad mangul zan sauka..”


“Ok to sai nafara sauke wannan hajiyar kenan saboda ita a madaci road zata sauka”


“Babu damuwa” inji budurwar,


Suna tafe dukkaninsu sunyi shiru saiko karar radio din da mai adaidaita sahun ya kunna dahaka suka karasa gidan mami, hand bag dinta ta bude ta fito da karamar jakar hannunta ta fiddo naira dari biyar ta mikawa mai adaidaita sahun, key din motarta da yafadi ta dauka ta fita tana gyara mayafinta,


Saida sukaje kofar gidan su wannan budurwar tana shirin fita bayan tabawa mai adaidaita sahu kudinsa sai kawai tayi ido hudu da yar karamar jakar hannun Mami wacce ta Jefarta aciki bata kulaba lokacin da zata dauki key din motarta,


Batayi magana ba tasa hannu ta dauki jakar tafita batareda tabari mai adaidaita sahun yaganiba….


          ***


Tana makale da jakar acikin hijabinta ta shiga gida, afalo ta iske ummi tana lissafin wasu kayan yara da aka Kawo mata domin ta sara,


Ganinta yasa ummin yin murmushi,


“Hafsa na yau kam nayi miki laifi driver baije ya daukoki ba na aikeshi bakin kasuwa shagona yaje yakai kayan nan da aka Kawo jiya kinga shine har yanzu bai dawoba..”


Murmushi Hafsat tayi tazauna tana cire takalmi da safar dake kafarta,


“To ai babu komai ummi tunda gashi nadawo..”


“Ame kika dawo?”


“Adaidaita sahune dama kuma inada canji acikin jakata, kinga ma har na tsinci jakar wata mata wacce muka zauna tareda ita aciki” takarasa maganar tana nunawa ummin jakar,


“Yarwa tayi? To yanzu taya zaki ganta har abata, kodai cikiya zamu kai gidan radio?”


“Ai naga gidanta ummi, naga gidan data shiga koda ace ba gidanta bane tunda dai nan taje idan naje ai zan sameta”


“To shikenan tunda kinga gidan da taje sai kije ki kai mata koda gobe ne”


“To ummi Allah ya kaimu”


“Amin, kije kicire uniform din ki shiga kitchen akwai abinci yana nan”


“Toh” ta amsa tareda mikewa ta shiga bedroom dinta.


  Washe gari da yamma ta shirya bayan tayi wanka, wani jan leshi tasa mai adon blue ajiki, farin hijab tasa tafito tana rikeda jakar data tsinta,

.

A balcony tasamu hajiya kubra zaune ta dan kishingida tana sauraren radio,


“Ummi bari inje indawo”


“To hafsa sai kin dawo, zaki gane gidan dai ko?”


“Ehh zan gane, to kije ku tafi da salisu driver sai yakaiki”


“Toh ummi” ta amsa tareda wucewa,


Abakin gate ta iske drivern yana zaune wurin mai gadi suna hira, ganinta yasashi tasowa domin yagane unguwa zasu fita, gidan baya yake kokarin bude mata taki tahanyar bude gidan gaba tashiga ta zauna.


  Mami kuwa tunda ta koma gida take faman duba yar karamar jakarta domin makudan kudi ne aciki sannan uwa uba akwai muhimman abubuwanta aciki irinsu katin shaidar dan kasa, gashi ATM card dinta yana ciki,

.

Ganin bata ganta ba ya tabbatar mata da cewar jefarwa tayi, zama tayi tasoma kiran wayar yusleem amma shiru bai daga ba har takatse tasake kira, saida ta kirashi sau uku bai dauka ba,


Tana kokarin tashi taji shigowarshi domin shi shigowarsa cikin gidan ma daban banci dana kowa saboda awani hankali yake bude kofa ya rufeta,


Yana shigowa ko zama baiyi ba tafara magana,


“Kana inane haka nayita kiranka bakai picking ba? Nafita da mota ta dazu tabani matsala akusa da al hikimah clinic naje duba yar gidan hajiya maryam”


Saida ya zauna yadan jingina kanshi da jikin kujera sannan ya kalli mamin yayi magana,


“To amma mami meyasa zaki fita ke kadai? Meyasa baki tafi da driver ba? Saboda irin wannan na ajiye miki driver fa”


“Yusleem drivern ai baya nan yatafi gareji gyaran daya motar tawa shine naga basai na jirashi ba gara kawai naje nadawo”

.

“To meye matsalar motar?”


“Ina zan sani, tana can nabarta awurin ai saboda taki tashi, ni duk ma ba wannan ba, jakata na yar ahanya ko akofar gidan nan ko kuma acikin adaidaita sahun da nahau.., Kiran da naketa yi maka dama shine so nake kayi maza kaje bank kakai repot saboda ATM card dina yana cikin jakar”


“Mami shiyasa ai nace kidaina yawo dashi..”


“Babu komai, kai ai ba a ketarewa kaddara”


“To Allah ya rufa asiri, bari naje”


Tashi yayi yafita ita kuma ta mike zuwa cikin bedroom dinta.


  Har mami ta fidda rai da samun wannan jakar kwatsam washe gari da yamma tana falo zaune tana kallo gabanta kuma snacks ne ajiye tana dauka jifa jifa tana ci taji sallama,

.

Amsa sallamar tayi tadan gyara zamanta tana jiran wanda keyin sallamar yashigo,


Wata yar budurwa tagani wacce kamar ta dan san fuskar amma dai bazata iya tunawa yanzu ba,


Ciki Hafsat ta shiga ta tsugunna tagaida mamin,


“A’a tashi mana, tashi ga kujera nan ki zauna” ita Mami ma duk tunaninta ko kawar surayya ce,


“Hajiya dama jiyane bayan mun saukeki a adaidaita sahu mun tafi yakaini gida sai naga jakarki kin mantata aciki shine nakawo miki yanzu…” Hafsat ta kammala zancen tana mikawa mami jakar…..


         ***


Cike da mamaki Mami take kallonta bayan ta amshi jakar tata daga hannunta,


Tabbas wannan jakar tace nan tayi hanzarin bude jakar tafara duba kudinta da abubuwanta dake ciki,


Tsawon mintuna biyu tayi tana duban cikin jakar kafin ta dago fuskarta kunshe da mamaki saboda yanda ta yasar da jakar haka take babu abinda aka taba bare har acanja masa muhalli,


Ita kam Hafsat komawa tayi ta zauna bayan tabawa mami jakar, hankalinta kwance lokacin da taga mamin tana kokarin duba jakar saboda yanda ta tsinceta haka ta ajiyeta bata kara koda tabawa ba sai yau dinnan da zata Kawo mata,


“Yan mata ya sunanki?” Mami ta tambayeta fuskarta dauke da fara’a,


“Sunana Hafsat hajiya”

.

“Hafsat gaskiya kadanne irinku yanzu aduniya domin ba kowane zai tsinci makudan kudi da sauran muhimman abubuwa ya mayarwa mai kayanba sai wanda yake mutukar jin tsoron Allah, dama ni tun farkon ganin da nayi miki wallahi nayaba da hankalinki da nutsuwarki sannan lokaci guda naji kin shiga raina,nagode madalla…”


Dan murmushi hafsa tayi akaro nafarko domin jin dadin yabon da mami tayi mata,


“Ai babu komai hajiya, nima nagode Allah yabar zumunci”


“Ai nice da godiya hafsa, wallahi naji dadi mutuka domin ATM card dina yana ciki niduk dashi nafi damuwa ma wallahi saboda yarana sun koma makaranta last week to kuma yayansu account dinshi yadan samu problem babu damar ya tura musu kudi shine yasaka musu kudin a account dina inyaso sai atura musu tanan…”


“Ayya Allah sarki Allah yabasu sa’a”


“Amin amin, ai da har natura shi ma bankin yaje yakai musu report saboda kar asamu matsala sai gashi kuma kin Kawo min, wallahi nagode miki mutuka”


“Hajiya wallahi babu komai dama tunda naganta nace taki ce domin mu biyu ne aciki..”


“Allah sarki, kuma sai kika gane gidan nawa ma”

.

“Ehh dama nace koda ace banan ne gidan nakiba to zan Kawo saboda nasan kila idan nayi musu kwatance su ganeki..”


Murmushi mami tayi ta mike cikeda fara’a akan fuskarta,


“Allah sarki,Allah yayi miki albarka..”


Dining area taje,jimm kadan sai gata ta fito rikeda dan madaidaicin farantin silver,


Agaban Hafsat ta ajiye farantin tasake komawa ta dauko mata cup da juice na roba takawo mata,


Kallon farantin Hafsat tayi taga dambun nama ne da snacks,


“Ga lemo nan kisha kinji ‘yata, ai ni danaga kin shigo nazaci kawar yatace surayya”


“Au Allah sarki ai inajin ma banma santa ba..”

.

“Ehh gaskiya bazaki santa ba saboda ba anan takeba tana can akasar Malaysia tana karatu yanzu haka saura shekara daya da yan watanni ta kammala, akwai kuma yayunta maza guda biyu Abdul da khalifa suma suna outside suna karatu sai babban yayansu shi yana nan anan..”


“Allah sarki” Hafsat tafada tana kallon agogon wayarta,


“Hajiya bari inje intafi saboda mamana tace kar injima”


“To ai hafsa bakici snacks dinba kuma ko juice dinma baki shaba”


“Babu komai hajiya, akoshe nake wallahi nagode madalla”


“To tsaya, ina zuwa” mami tafada tareda mikewa tashiga bedroom dinta tafito,


Kitchen ta wuce Jim kadan ta sake fitowa,


“Hafsat to ai sai ki fada min a inda gidanku yake ko saboda inason zan hadaki kawance da yata surayya, koda yake bari sai insa driver yakaiki kinga sai yagano min gidan ko”


Fuskar hafsa da murmushi tace,


“Hajiya nima driver ne yakawoni, kuma gidan namu ma bashida wuyar kwatance”


“To duk da haka dai zansa driver yabiku ya gano gidan naku”


“To shikenan hajiya nagode”


“Yawwa ga wannan babu yawa”


Dan tsorata Hafsat tayi saboda ganin girman ledar da mami ke mika mata,

.

“A’a hajiya bazan karba ba, nagode madalla amma kibarshi”


“Haba Hafsat karki maida hannun kyauta baya mana”


Dakyar dai mami tasamu har Hafsat ta karbi kayan, rakiya mami tayi mata har compound din gidan, nan sukayi sallama Hafsat tashiga mota drivern mami yana biye dasu suka fice daga gidan,


Kallon Salisu driver Hafsat tayi bayan sun hau titi sakamakon wasu kaya da tagani a sit din baya,


“Wannan kayan fa?”


“Nakine, daga ciki wannan matar tasa aka fito dasu tace asa miki acikin mota”


Sake waiwayawa Hafsat tayi ta kalli kayan nan taga katan din juice guda daya sai na biscuit shima guda daya sai snacks da dambun nama cikin wata leda mai dan kyalli, murmushi tayi tana yaba kirkin mami acikin zuciyarta wato duk abinda takai mata da bataci ba shine saida aka biyota dasu,


Har gida drivern mami yarakasu saida yaga shigarsu ciki sannan yajuya yake


        ***


Da murna akan fuskarta ta shiga cikin falon hajiya kubra, zaune ta sameta akan carpet tana goge wata doguwar rigarta mai dan santsi,


“Ah Ummi akan kibari nadawo sai ingoge miki shine kike yi da kanki?”


Hafsat tafada bayan tayi yozali da hajiya kubran,


“A’a Hafsat to ai bawani aiki ne mai yawaba, zaman kadaici ne ya isheni shine nadauko ina gogewa, abbanku ma kinga har yanzu bai dawoba nayi masa waya yace yana gidan abokinshi sunje meeting”


“To Kawo in karasa miki..”


Mika mata iron din hajiya kubra tayi tana cewa,

.

“Abinda yasa ban hada da ita acikin kayan gugar nanba bana so akona min itane tunda kinga tanada santsi…”


“Wannan kam sai anbita ahankali”


Bude kofa akayi aka shigo, Salisu driver ne yashigo bakinsa dauke da sallama,


Kayan da Mami tabaiwa Hafsat yashigo dasu ya ajiye yafita,


Saida Hafsat tagama goge duguwar rigar sannan ta tashi taje ta kinkimo kayan takawo gaban ummin tana fadin,


“Ummi kinga wai daga zuwa shikenan matar nan ta hadoni da wadannan kayan..”


Cikin fara’a hajiya kubra tafara bude babbar ledar da mami tabawa hafsan,


Manyan turarruka ne masu kamshi guda biyu irin na larabawa sai mansu da sabulai suma masu kyau sai abin hannu da sarka fation amma kuma mai mutukar kyauce,


Kallon kayan Hafsat keyi cikeda mamaki haka itama hajiya kubra mamakin ne ke bayyane akan fuskarta,

.

“Hafsa anya kuwa duk murnar mayar da jakar nan zatasa matar nan tabaki wadannan uban kayan? Anya kuwa?”


Murmushi Hafsat tayi ta gyara zamanta,


“Wallahi Ummi nima dai haka nace to amma yanda naga ta sake dani tanata yimin hira tana bani labarin yaranta sai nima nadan saki jiki domin harfa cemin tayi wai tanada yarinya budurwa tana kasar waje tana karatu idan ta dawo zata hadamu kawance..”


“Kawance…?” Hajiya kubra ta tambayeta tana dariya,


“Wallahi haka tace Ummi, kinga fa har drivern ta taturo ya biyomu wai yazo yagane mata gidanmu..”


“Allah sarki ai akwai mutane masu kirki a duniya, wasu sunada son jama’a..”


“Wannan kam tanada son mutane wallahi Ummi, kinga snacks din wai dan banci ba shine ta hado min dashi”


Jan kayan sukayi suka ciro suna dubawa, cake ne da meat pie da sauran tarkacen snacks,


Ajiyewa kayan sukayi har saida Alhaji sa’id yadawo suka nuna masa, tun daga wannan rana ita hafsa tama manta da batun mami amma ita kam mami Hafsat tana makale aranta,


Ranar alhamis da rana ta dawo daga super market siyayyar kayan amfanin gida ta biya ta gidansu Hafsat,


Hajiya kubra tana kitchen tana kokarin sauke girkin rana da tayi taji sallamar mami, da fara’a ta karbeta tamkar dama ta santa tayi mata jagora zuwa cikin falonta,


Ruwa da abinci da juice takawo mata sannan tazauna suka fara gaisawa,


“Hmm nace yarinyarki kuwa tana nan?”


“Wacce daga ciki?”

.

Murmushi mami tayi ta daga kanta takalli hoton amal wanda ke kafe ajikin bangon dakin wanda sak bashida maraba da Hafsat,


“Wannan, gata nan ajikin hoto” mami tafada tana murmushi,


“Ayya to ai tana makaranta, tatafi school tun watanni hudu da suka wuce”


“A’a, anya kuwa? Ai naga last week takai min jakata dana yar acikin adaidaita sahu..”


“To ai shiyasa nace miki wacce aciki domin su 2 ne kuma duk kamanninsu daya,wannan wacce kika nuna amal ce..” Hajiya kubra tafada tana dariya,


“Allah sarki to ba wannan nake nufiba, dayar nake nufi wacce taje gidana tace min sunanta hafsat”


“Ehh,itama tana makaranta amma karfe 2 zata taso..”


Kallon agogon hannunta mami tayi, karfe 12:30 narana,


“To gashi nikuma sauri nakeyi, idan tazo agaisheta, zanje intafi”


“Insha Allah zataji, gashi bakici abincin ba”

.

“Alhamdulillah, nagode sosai”


Tashi tayi tafita nan hajiya kubra ta bi bayanta ta rakata har bakin gate mami kuwa sai jaddadawa take cewar agaida Hafsat idan tazo,


Koda hafsat tadawo hajiya kubra tafada mata murmushi kawai tayi batace komai ba, ita harkokin gabanta kawai takeyi yanzu daga makarantar boko sai makarantar islamiyya kuma cikin hukuncin ubangiji duk tana fahimtar karatun nako wanne fanni,


Bayan sati biyu da zuwan mami tasake komawa ranar laraba da yamma amma ranar ma bata samu hafsat ba domin tatafi islamiyya,


Sam bataji dadin wannan sabanin da suke yiba wanda har hajiya kubra saida ta fahimci haka,

.

“Hajiya kiyi hakuri insha Allah zan turo miki ita gobe ko ranar juma’a, hafsan ce wallahi uzururrukanta yawa garesu amma insha Allah zata zo miki..”


Sai lokacin damuwar dake kan fuskar mami takau har ta maye gurbinsa da murmushi,


“To ina jira amma dai dan Allah hajiya kicika alkawari kuma ranar juma’a ma yakamata ki turo min ita yanda zamu dade muna hira..”


“To insha Allah zata zo, agaida mutanen gida”


Sallama sukayi mami tafita tatafi, kamar yadda hajiya kubra ta alkawartawa mami haka ta cika alkawari ta hanyar saka driver yakai Hafsat gidan ranar juma’a da musalin karfe 1 narana,


Lokacin da Hafsat taje gidan mami tana cikin bedroom dinta zaune agefen gado suna yin waya da surayya jin sallama yasata fita ganin Hafsat dince tace ta karaso, har cikin bedroom dinta takaita tace ta zauna agefen gado amma fur hafsa taki zama sai akasa ta zauna kan dan madaidaicin carpet din dake shimfide akusa da gadon,


Wayar hannunta ta mikawa Hafsat,

.

“Ungo amshi ku gaisa da yar tawa surayya, ina zuwa bari inkawo miki ruwa kafin ku gama”


Karbar wayar Hafsat tayi tana murmushi tafara kallon screen din wayar saboda video call ne, surayyan ma daga can kurawa screen din ido tayi tana kallon Hafsat nan suka shiga gaisawa kamar dama can surayya tasanta domin hira sosai take yimata,


Mami tana cikin kitchen tana warming din abinci yusleem ya shigo yana sanye da farar shadda mai mutukar tsada kai idan kaganshi zaka dauka sabon ango ne saboda tsananin kyawun da yayi dama kuma shi haka ka’idarshi take baya taba saka manyan kaya sai ranar juma’a sai ko wani babban muhimmin abu,


“Har kadawo daga masallacin?” Mami ta tambayeshi tana kokarin sauke tukunya daga kan wuta,saida yaje yadan jingina da jikin bango sannan ya amsa mata da,


“Ehhh, ina kukun naku yake naga kina girki dakanki mami?”


“Ba girki nakeyiba dumame ne nayi bakuwa ne shine zan kai mata abinci”


“Ok” shine kawai abinda yace yajuya zai fita, dakatar dashi mami tayi,


“Bazaka shiga ku gaisa da bakuwar tawa ba?”

.

“Ina zuwa mami, ai ba tafiya nayiba” daga fadin haka yasaka kai yafice,


Filet mami ta dauko ta zubawa Hafsat abincin, macaroni da miyar danyen kifi sai abinsha da fruits, har mami takoma su Hafsat suna ta hira itada surayya wani dadi mami taji wanda ita kadai tasan ma’anarsa acikin zuciyarta,


Saida mami ta karbe wayar tace Hafsat taci abinci sannan hirar tasu ta katse, kasa cin abincin tayi saboda kunyar mami wanda har mamin saida ta fahimci haka, dakyar dai tadan ci ta tattara kayan zata fitar mami ta hanata,


Wuni guda tayi domin sai la’asar sannan hajiya kubra taturo driver yadauketa, mami kam wannan karon kaya sosai ta hada mata domin acikin kayan da take ajiyewa na auren yusleem ta dauko mata duguwar riga dark blue da takalmi da turarruka,


Kin karba Hafsat tayi amma mami saida tasaka mata acikin mota tatafi da kayan,


Lokacin da takoma gidan hajiya kubra taga kayan rasa abin cewa tayi sai can ta nisa tayi magana,


“Hafsat wannan matar haka zatayi ta miki hidima batareda wani abu aranta ba? Nifa ina tsoron rayuwar yau domin wallahi akwai ayar tambaya aciki”


Murmushi Hafsat tayi,

.

“Wallahi Ummi babu komai sai alheri domin yau munyi waya ma sosai da yartata..”


“To shikenan tunda hakane”


Koda suka nunawa Alhaji sa’id kayan fada yashiga yi sannan yace kar Hafsat takara zuwa gidan shi bai yadda da mami ba,


Tun daga wannan rana Hafsat bata sake zuwa ba amma da aka kwana biyu ita mamin sai gata tazo, ranar kuma tayi Sa’a Hafsat din nagida tana kan keken sakarta tana dinki,


Kyakkyawar tarba hajiya kubra da Hafsat din sukayi mata, ta dan jima agidan kafin tayi musu sallama tatafi, sai bayan tafita ne maigadi yashigo da kaya wanda takawowa Hafsat,


Kayan makulashe ne da turaruka masu tsada, ita kanta hajiya kubra yanzu tafara kuma wani tunani akan mami Wanda dai tabarwa zuciyarta bata furta ba.


Lokuta zuwa lokuta mami kanzo ganin Hafsat kuma duk lokacin da zatazo bata zuwa haka sai ta Kawo mata kayan makulashe irinsu biscuit, chocolate, sweet da sauransu banda mayukan shafawa da turaruka, akwai wani lokaci da taje dubai tadawo tsarabar da takawowa Hafsat abin ba acewa komai domin akwati guda medium ta ciko mata taf da kayan sawa,


Shiyasa tun su ummi na zargin akwai wani abu aran mami har sun dawo sun daina daga ita har Alhaji sa’id din,


Haka mami taci gaba da yiwa Hafsat hidima baji babu gani, lokacin da watan azumi yakama kaya sosai mami tabada aka kai mata kamarsu fruits, madara, sugar da dai sauran kayan hada tea da tarkacen kayan da akafi amfani dasu a lokacin azumi,


Ranar da aka kai azumi na 10 bayan ansha ruwa Hafsat ta shirya taje yimata sannu da shan ruwa, suna zaune ita da yusleem yatashi yafita, yana fita Hafsat ta shiga, ba karamin dadin ganinta mami tajiba nan ta cikata da kayan abinci iri iri,

.

Har Hafsat tabar gidan tatafi yusleem bai dawoba, da salla tazo kuwa mami kaya ta dinkawa Hafsat kala biyar daya materia, daya leshi daya shadda biyu atamfa super masu kyau da tsadar yan gaske kuma kowanne da takalminsa da mayafinsa banda turare da sarka da abun hannu, wannan sallar saida Hafsat tasamu kaya kala goma domin agida ma kala biyar Alhaji sa’id yayi musu itada amal,


Ranar salla kwalliya Hafsat taci bayan sun gama aikin Gida da hajiya kubra tace mata zataje gidan kawarta Amina nan tatafi mata da abincin sallar da Ummi tayi wainar shinkafa da miyar agushi,


Acan gidan Amina tawuni sai bayan sallar magrib driver yaje ya dauketa yamayarta gida tana zuwa taga wasu sabbin food flasks zama tayi tafara budewa tana gani, fried rice ce da kaza guda daya akai gasasshiya sai sinasir da miyar ganye wanda yaji kaji,


“Ummi wannan abincin fa?”

.

“Daga gidan mamanki hajiya siyama aka Kawo miki abincin salla”


Murmushi tayi ta mike,


“Allah sarki mami kinga ni namanta ma ban kai mata abincin salla ba”


“Gobe ai sai ki kai mata idan zaki mayar mata da kwanukanta”


Washe gari hajiya kubra tayi girki musamman saboda mami shinkafa da miyar kaji Hafsat ta shirya bayan taci kwalliya tatafi kai mata,


Da murna mami ta tareta tayi mata iso har cikin dakinta,

.

Zama tayi suka fara hira kamar yadda tasaba yi da Hafsat idan tazo mata, wuni cur Hafsat tayi sai yamma tatafi.


Ahaka rayuwa taci gaba da wakana mami tana mutukar kaunar Hafsat kuma tana kyautata mata wanda harsu hajiya kubra sun yarda da hakan adalilin hakanne ma zumunci mai karfi yashiga tsakanin hajiya kubra da mami domin kawance sukeyi sosai,


Sannu sannu Hafsat ta kammala makarantar secondary wannan dalilinne yasa yanzu bata zuwa ko ina sai makarantar islamiyya saiko dinkin sakarta wanda tasaka agaba,


Cikin weekend tashirya takaiwa mami ziyara,


“Hafsat ankammala karatu ko? Yanzu kuma me kikeda ra’ayin yi?”

.

Murmushi hafsat tayi,


“Mami karatu zanci gaba dayi”


“To hafsat banki ba amma dai da zakiyi aure shiyafi, idan kikayi aurenki sai kiyi karatunki agidan mijinki”


“Hakane mami amma to wazan aura? Nida ko zance banay..”


“Dana zaki aura hafsat, yarona nakeso ki taimaka min ki aureshi, dan Allah kiyi min wannan taimakon….!.

Cikeda mamaki Hafsat ta kalli mami saboda jin abinda tafada,

“Kidaina mamaki Hafsat sannan kuma narokeki dan girman Allah kada ki k’i amsar bukatata domin yin hakan na iya zama dalilin faruwar abubuwa da dama ciki kuwa harda dawwamar bacin rai da bakin ciki acikin zuciyata…”

Sunkuyar da kai Hafsat tayi tai shiru takasa yin magana acikin zuciyarta kuwa tunani takeyi shin shi yaron mamin da take burin hadata dashi shine yaganta yake sonta ko kuwa kawai mamin ce keda burin yin hakan a matsayinta na mahaifiyarsa domin ita tunda take zuwa gidan bata taba ganin daya daga cikin yaran mamin ba kuma surayya kadai ta sani har suke yin waya da ita,

“Hafsat ya naji kinyi shiru? Kodai bakya son dan nawa?”

Muryar mami ta katse mata tunaninta da takeyi,

“Mami to ai bai taba ganina ba kuma nima ba taba ganinshi nayiba..”

Murmushi mami tayi,

“Hafsat kenan ni awurina duk wannan ba wani abu bane kuma abune mai sauki domin na isa da dana duk abinda nasashi baya k’in bin umarni na, matsalar dai kawai kece idan baiyi miki ba,ga hotonshi nan akafe abango ta bayanki, juya ki gani…”

Waiwayawa Hafsat tayi cikeda mamaki ta kalli wurin domin tunda take shigowa bedroom din mami Allah bai taba bata ikon damar kallon wurinba bare har taga hoton,

Hadadden saurayi tagani zaune akan kujerarshi ta office wanda abisa dukkan alamu acikin office dinshi akayi masa hoton,

Farine kyakkyawa mai daukar hankali wanda baduk macece zata ganshi takau da idonta a lokaci guda ba,fuskarshi zagaye take da saje mai hadeda kasumba,bakaken suit ne ajikinshi wadanda sukayi mutukar amsarshi domin sun sake haska farar fatarshi,
,
Manyan idanuwanshi farare tatass ta zubawa ido har ta gangaro izuwa kan dogon hancinshi mai tsini wanda yake daf da bakinshi dan madaidaici mai dauke da zagayayyun lips wadanda suka kasance jajaye jur,

Ita kanta bata san tsawon mintunan data dauka tana karewa halittar yusleem kallo ba,

“Masha Allah, tsarki ya tabbata ga ubangijin halittu wanda ya kawata halitta da surar wannan bawan nashi..” Ta fadi hakan acikin zuciyarta wanda har lokacin takasa dauke idanuwanta daga kallon hoton,

“Hafsat…” Taji mami takira sunanta sai lokacin ta iya tunawa ma da ashe mamin na zaune wurin, cikin sauri ta dauke idonta daga kan hoton ta sunkuyar da kai cikeda jin kunya,

“Hafsat ko baiyi miki bane?”

Shiru Hafsat tayi bata amsaba tasake sunkuyar da kanta kasa,

Juyin duniya haka mami tayi tana tambayar hafsat amma taki amsawa tayi shiru,

Murmushi mami tayi,

“To Allah dai yasa hasashe na yazama gaskiya hafsat idan har kuwa hakan ya tabbata to nasan zanfi kowa farin ciki…..”

Dan murmushi hafsat ta kuma yi cike da kunya,

“Insha Allah zanzo gidan gobe goben nan muyi maganar da umminki kafin asan ta inda za afara kuma”

Mami tafadi hakan cikin jin dadi, ita hafsat yanzu sai taji tana jin kunya da kuma nauyin mamin shiyasa taji duk zaman ta takura,

“Haba hafsat ai tsakaninmu babu yar surukunta, ki dauka cewa kece yata ba yusleem ba, ko aurenku ya tabbata karkiji kunyar sanar dani laifinsa matsawar yayi miki ba daidai ba..”

Shiru hafsat tayi takasa cewa komai,har mami takaraci maganarta ta gama bata iya daga ido ta kalleta ba daga karshe ma sai cewa tayi zata tafi duk kuwa da cewar ba wannan lokacin tayi niyyar tafiyar ba amma wannan maganar da sukayi da mamin itace ta tilasta mata barin gidan.

Ko drivern gidansu bata zauna zaman jiraba sai mami ce tasa drivern ta yakaita gida,

Hatta ummi saida tayi mamakin ganinta a lokacin saboda bata zaci zata dawo dawuri hakaba,

Tambayarta ummin taringa yi akan dalilin dawowarta da wuri haka bayan kuma ba haka tasaba dawowa ba idan taje,

“Hafsat ko unguwa hajiya siyaman zataje ne shiyasa kika dawo?”

“A’a Ummi babu inda zataje tana nan..”

“To meya faru?” Tasake tambayarta,

“Babu komai, tace zatazo wurinki gobe ma”

“Amma dai lafiya ko?”

“Ehh lafiya lau”

“To shikenan Allah yakaimu..”

Acikin zuciyarta ta amsa amin din bata bari ummin tajiba,

Ita kanta bazata iya fassara yanayin da zuciyarta ta karbi yusleem ba kawai dai tanajinta cikin nishadi wanda bata san dalili ba,

Daren ranar tayishi ne batare da tayi isasshen bacciba.

Washe gari da safe misalin karfe 11 daidai nasafe mami tayiwa gidan sammako lokacin Alhaji sa’id na nan ko fita baiyiba,

Jin zuwanta yasa Hafsat jin wata irin faduwar gaba duk sai taji jikinta yayi sanyi dan dakyar ma ta iya zuwa suka gaisa daga nan ta koma daki ta kule bayan ta gabatar mata da ruwa,

“Hajiya kubra yau dai zuwana yasha banban da wanda nakeyi ada domin dalilin zuwana yau shine neman auren yata nazo.. Wato Hafsat”

Murmushi hajiya kubra tayi ta kalli mami,

“To ai bakiyi min gwari gwari yanda zan ganeba”

“Kamar yadda nafada miki nazone in nemarwa dana yusleem auren yarki Hafsat idan har babu alkawarin wani akanta domin wallahi ina mutukar kaunarta kuma ina son inhada jini da ku..”

Murmushi hajiya kubra tayi,
.
“To ai kema yarkice, amma yanzu abinda nake ganin za ayi shine abbanta yana nan bai fitaba bari inje insanar masa”

“To shikenan”

Tashi hajiya kubra tayi tafita zuwa part din Alhaji sa’id mintuna Kadan sai gata tadawo,

“Hajiya to bismillah zo mu karasa wurin alhajin”

Tare suka shiga suka iskeshi zaune kan kujera hannunsa rikeda jaridar weekly trust,

Gaisawa sukayi da mami tayi masa bayani kamar yanda tayiwa Ummi nan Alhaji sa’id yace babu komai indai har Hafsat din ta amince domin ba za ayi mata doleba kawai abinda za ayi shine suje su daidaita ita da yaron,

Cikeda farin ciki mami tayiwa Alhaji sa’id godiya ta mike tafita acikin ranta tana ganin yanzu saura abu daya yarage shine tashawo kan yusleem….

*
   ***Falon hajiya kubra mami takoma tazauna tana jiranta zuciyarta cikeda farin ciki wanda kana iya gane hakan karara idan har ka kalli kan fuskarta,

Tana nan zaune har ummi tafito daga sashen alhaji nan sukayi sallama ta rakata tatafi, saida Hafsat taji fitar mami sannan tafito daga daki tazauna akusa da ummin tana dan kallonta domin jin karin bayani amma kuma sai dai kunya takeji,
.
“Mamin naku tatafi yanzu nakaita wurin abbanku sunyi magana akanki keda danta, abbanki yace yaron yazo ku daidaita mutukar kun amince kuna son juna to shi bashida wata matsala…”

Shiru Hafsat tayi ta dan sunkuyar da kanta kasa tana murmushi,

“Nida naso kema kiyi karatu kamar yar uwarki amal to amma kin san kowa da yadda Allah yake tsara masa rayuwarsa.., sai dai muyi fatan Allah yasa hakan shine yafi alkhairi”

Har dai ummi tayi maganarta tagama Hafsat bata iya cemata ko uffan ba.

    Cikin farin ciki marar misaltuwa mami taje gida tana shiga ta nemi wurin zama ta zauna tafara lissafin abubuwan da ya kamata ta siyo ko ta hado domin bata bukatar bikin nan yawuce watanni biyu masu zuwa kacal,

Paper da pen ta dauko ta zauna tana rubuta abubuwan da takeso tasiyo da adadinsu,

Yusleem ne yaturo kofar falon ya shigo yana sanye da farar riga jersey da blue din trouser hannunshi rike da key din motarshi,

A kusa da mamin ya zauna ya jingina kamar yadda yasaba domin shi haka dabi’arshi take kamar wani mai sarauta akoda yaushe cikin iko yake,

“Mami ina kwana..?”

Dagowa tayi ta kalleshi bayan tacire farin medical glass din dake kan fuskarta,

“Sai yanzu katashi ko? In ba hakaba yaushe za akira karfe 12 da safiya…” Takarasa maganar tana murmushi,

“To ai mami weekend ne..”

“Ehhh tunda weekend ne sannan kuma kai kadaine baka da mata ai dole kayita bacci har rana ta fito”

Murmushi yayi yana shafa kasumbar dake fuskarshi,

“Mami yunwa nakeji wallahi dan yunwar ce ma tafito dani daga gida”

“To me zakaci?”

“Abani tea banda bread, soyayyiyar agada da dankali amma banda egg”

Murmushi Mami tayi tana kallonsa,
.
“Ai matarka zata sha tsaraba kai idan katashi karyawa baka karyawa da abu guda biyu kuma abin haushinma idan anbaka ba na kirki zakaci ba”

“Mami wallahi nima ina son infara cin abinci dayawa amma narasa meyasa bana iyawa, but ina tunanin nanda 2 weeks zanje london so zan biya ta chairo naga dr dina”

“Da dai yafi maka amma mutum yarinka cin abinci kamar wani karamin yaro…”

Bai kara maganaba yaciro wayarshi daga aljihu yasoma latsawa, mikewa mami tayi tafita takira kuku ta fada masa aikin da zaiyi tadawo wurin yusleem tazauna,

“Wai mami rubuce rubucen me kikeyi ne haka?”

“Ai zan fada maka, kwantar da hankalinka..”

Murmushi yayi yatashi yakoma kan 3 sitter ya kwanta,

Mintuna kadan kuku yashigo dauke da faranti wanda ya dorowa yusleem kayan breakfast din akai,

Akan center table ya dora mishi yajuya yafita, tashi yusleem yayi yaja table din gabanshi ya hada tea yasoma karyawa yanayi yana kallon mami wacce ta dukufa akan rubutun da takeyi,

Saida ya kammala sannan mami ta dago ta kalleshi,

“Yusleem ya maganar auren da nace ka nemo, har yanzu baka samo yarinyar da tayi maka ba ko kuma yaya?”

Dama tun shigowarshi saida jikinsa yabashi maganar aure mami zatayi masa,

Sai da yadan ja lokaci sannan yace,

“Mami meya faru kuma?”

“Babu abinda yafaru inaso ne inji idan har kasamo sai afara maganar auren idan kuma baka samoba to ni nasamo maka…”

Sunkuyar dakanshi yayi yana nazari batare da yace komai ba, tabbas shikam yanada farin jinin yanmata domin babu wahala yanzun nan budurwa tace tana sonshi sai dai kuma sam shi baya bukatar auren ne,
.
“Yanaji kayi shiru?”

“To mami ai nazaci mun gama maganar nan”

“Dawa? A’a bamu gamaba, nidai ina son kasani nasamo maka yarinyar da zaka aura nanda watanni biyu dan haka saika fara dukkan shirye shiryen da yadace amma wannan karon kasani banyi maka aure dan ka sakar musu yarinya ba,

Sannan kuma inaso ka sama mana visa mutafi umarah domin muje inyi maka addu’a akan Allah yarabaka da wannan aljanar da take tareda kai kuma yasa ayi auren nan cikin sa’a yasaka albarka aciki”

Tunda mami tafara maganar baice uffan ba har tagama,

“Ina fata kaji maganganun da nayi maka kuma sun shiga cikin kunnenka?”

“Ehh naji”

“Yawwa to Allah yayi maka albarka Allah yasa ayi cikin nasara”

Bai amsaba yatashi yafita mami tarakashi da ido,

Kamar yadda mamin tafada acikin lokaci kankani yasamo musu visa suka tafi umarah addu’a sosai mami tayi masa kan auren da zatayi masa bayan sun kammala umarah ne yawuce London yabarta anan bayan tafiyarshi da kwana uku itama tawuce dubai domin karasa hada lefenshi da siyan sauran abubuwan da za ayi amfani dasu abikin dan hatta kayan da amarya zata saka duk saida tasai mata,
.
Saida ta kammala siyayyarta tsaf sannan tadawo Nigeria shikuwa yusleem har lokacin bai dawoba, dawowarta babu jimawa tatura wakilan yusleem sukaje nemar masa auren Hafsat agidan Alhaji sa’id wanda basu tahoba saida ranarsu, domin Alhaji sa’id ya yanke ranar aure saboda ya fahimci cewar Hafsat din tana son yusleem,

Wannan abu ba karamin dadi yayiwa mami ba dan tsananin dadi aranar da daddare taje gidan tayi godiya,

Aminanta da kawayenta ta gayyato suka kai lefen Hafsat wanda tsayawa fadar kayan ciki bata lokaci ne, domin mami ta yiwa Hafsat lefe na alfarma irin lefen da tunda yusleem yake aure ba ataba yin irinshi ba,

Yanzu gidajen guda biyu ko ina shirin biki sukeyi gadan gadan, Alhaji sa’id ya sakarwa ummi kudi domin yiwa yartata siyayya, ita dai Hafsat bata katabus saboda har yau bataga angonba kuma shima bai gantaba tana jin tsoron kar yaganta ya rainata yace batayi masa ba domin tasan dama auren hadin mami ne,amma shikam bata tunanin akwai wata ya macen da zata ce baiyi mataba,
.
Yusleem kuwa tunda ya Lula yatafi bai dawoba gyaran gidanshi ma wanda za ayi sai yaronshi na office yasa yatsaya akai akayi aka gama aka gyara gidan tsafa aka sake fenti,

Saida biki yarage saura kwana takwas sannan yadawo lokacin hatta kannenshi su Abdul da surayya har sun zazzo daga makaranta, mami taso tayi masa fada amma kuma dayake acikin farin ciki take sai ta shareshi taci gaba da harkokinta,

Surayya kam kanwar yusleem tattarawa tayi takoma gidansu Hafsat saboda acewarta ita abangaren amarya take ba bangaren ango ba, Hafsat ba karamin dadi tajiba domin dama ita kadaici kwal agidan take harkokinta domin Alhaji sa’id bai bar amal tazo ba duk da tayi niyyar zuwa amma yahana,

Surayya ce taraka Hafsat akayi mata komai kama tun daga kunshi gyaran jiki da gyaran kai wanda duk mami ce tadauki nauyin yin hakan,
.
Ana igobe daurin aure yusleem yaje gidansu Hafsat din wanda wannan dinma mamice ta tilastashi, kamar zaiyi kuka yashirya yatafi bayan sallar isha,

Surayya yayiwa waya tana dauka taji yace,

“Ke turo min wannan yarinyar”

Sarai surayya tagane abinda yake nufi amma sai tayi fuska tace,

“Uhm yaya wafa?”

“Oho miki” yafadi tareda katse wayar,

Kallon Hafsat tayi tana murmushi,

“Angonki ne yazo yana waje yana jiranki”

Saida gaban hafsa yafadi saboda jin abinda surayya tace,hijabi tadauka ta kalli surayya,

“Zo ki rakani dan Allah”

“Zan dai kaiki amma ina zuwa dawowa zanyi”

“Nayarda”

Fita sukayi gaba dayansu, afalo suka iske su ummi ita da jama’arta wadanda sukazo suna yan aikace aikace,
.
Kanshi yana durkushe akasa yana latsa wayarsa dan haka ko fitowarsu bai ganiba bare yaga zuwansu, surayya ce ta kwankwasa masa glass din dake saitinshi hakan yasashi yin kasa da glass din yana kallonta, gaban Hafsat ne yashiga dukan tara tara haka kawai domin gani tayi yusleem yafi kyau afili kuma tabbas shine mutumin da yake taimaka musu lokacin da tana gidan marayu domin yataba zuwar musu sau daya sun ganshi,

“Ina wuni..” Hafsat tace dashi tana kallon kasa,

Ko kallonta baiyiba ya amsa da “lafiya”

Daga haka babu wanda yakara magana acikinsu ganin haka yasa surayya tajuya zata tafi dominated tabasu wuri nan yadakatar da ita yadauko rafar yan dubu dubu guda daya ya mika mata yaja motarshi yayi gaba,

Hafsat ji tayi ko ajikinta balle abin ya dameta,

Washe gari aka daura auren Hafsat da yusleem da misalin karfe 2 narana akan sadaki naira dubu hamsin.

*
        ***Aranar da aka daura auren aranar alhaji sa’id yace aje akai Hafsat gidanta duk da hajiya kubra bata so hakaba domin ita taso ace sai washe gari za akaita amma tunda ga abinda alhaji sa’id yace dole babu yadda ta iya dan haka aka fara shirin kai amarya dakinta,
.
K’arfe 9 daidai aka fito da Hafsat din daga sashen alhaji sa’id bayan ya kammala yimata nasihar da ta dace duk wani uba yayiwa’yarsa a lokacin da za akaita gidan miji, haka itama hajiya kubra ba abarta abaya ba wurin yiwa Hafsat fada akan tabi mijinta kuma ta kyautata masa,

Inbanda kuka babu abinda Hafsat keyi domin tasan su hajiya kubra sunyi mutukar kokari akanta kuma sun taka muhimmiyar rawa acikin rayuwarta wanda har abada bazata manceba kuma bata da abinda zata iya biyansu da shi,
.
Wata tsadaddiyar mota ta alfarma kirar Lexus new series 2017 aka bude mata tashiga, nan kannen hajiya kubra suka sakata atsakiya yayinda surayya kanwar yusleem tashiga gaban motar,

Direct gidan mami aka wuce da ita inda mamin nacan ita da jama’arta suna zaman jiran zuwansu,

Yanayin farin cikin da mami ke ciki abin bazai misaltu ba domin kana ganinta zaka gane irin dunbin farin cikin da take ciki,

Har tsakiyar bedroom dinta aka shigar da Hafsat wacce ke tukunkune cikin wani babban mayafi dark blue kalar leshin dake jikinta,

Rungumeta mami tayi tana fara’a,

“Barka da zuwa cikin zuri’ata ‘yata,ubangiji Allah ya baku zaman lafiya ya kauda fitina da duk wani sharri daga gareku, Allah yabaku zuri’a dayyibah, nidama tun can a matsayin ‘ya na daukeki kuma yanzun ma kina nan ahaka baki sauya ba, insha Allah zamu rikeki amana”

Jin abinda mami tafada yasa kawayenta dake baibaye da ita sakin guda,basufi minti talatin agidan mami ba aka wuce da Hafsat gidanta wanda ke can wata unguwa da ake kira da babbar inuwa domin gaba daya mazauna unguwar shaharrun mutane ne wadanda sukeda hannu da shuni,

Shi kanshi yusleem fadin girman gidansa da tsarinsa abune mai wahala domin gidan yatsaru iya tsaruwa,

Cikin babban bedroom dinta aka shigar da ita ta zauna akan gefen makeken gadonta samfurin Italy,

Saida yan Kawo amarya suka fita sannan Amina kawarta da surayya suka shiga cikin dakin,

“Amarya kinsha kamshi, nidai bari inje intafi..” Inji Amina,

Dago jajayen idanuwanta Hafsat tayi ta kalleta,

“Haba Amina bazaki bari angwayen suzo ba?”

Dariya surayya tayi tareda bararrajewa akan gadon,

“Waye zai Kawo miki angwaye? Indai yaya yusleem ne Allah shi kadai zai zo gidan nan garama kibarmu muje mu tafi, nidai dama kin san gobe da sassafe zanyi miki asubanci…”

Jin abinda surayya tace yasa Amina tashi tsaye,
.
“To shikenan bari intafi, Hafsat sai nadawo ganin gida lokacin kin dawo cikin nutauwarki domin nasan yanzu bakya tareda ita…”

“To Amina nagode, Allah yabar zumunci, nagode”

Tashi surayya tayi tabi bayan Amina suka fita tare,

Tsuru Hafsat tayi tana bin dakin da kallo wanda yasha furniture’s na alfarma kalarsu dark purple, duk tsoro yabi ya cikata saboda babu motsin komai agidan, ta wuri daya hankalinta ya kwanta shine tasan akwai masu gadi acikin gidan wanda yanzu haka suna can gate suna aikinsu,nan tazauna taci gaba da zuba idon ta Inda zataga shigowar angonta.

   K’arfe 10:30 yusleem yashiga gidan mami kasancewar yan biki suna nan basu tattafi ba yasa gidan inbanda hayaniya babu abinda kakeji kamar dare baiyi ba,

Fitowa mami tayi wurinshi ta tsaya tana kallonsa, gaba daya ta fahimci bashida wata walwala,

“Yusleem…” Ta kira sunanshi tana kallonsa,

“Na’am..”

“Kasan abinda nakeso dakai? Na hadaka da girman Allah yusleem ka rike Hafsat amana, dan Allah karka cutar da ita, sannan ka taimaka ka rufa min asiri karka sakar musu ‘ya, yusleem idan ka aikata daya daga cikin wadannan wallahi bazan yafe makaba sannan ka nemi wata uwar amma baniba, Allah yayi maka albarka ya baka zuri’a tagari”

Hannayenshi duka suna cikin wandon farar shaddar dake jikinsa yana tsaye yana jin mami har ta kammala,

Gyada kai yayi batare da yace komai ba ya sunkuyar da kai,

“To kaje katafi mana”

“Ehh yanzu zan tafi, inasu Abdul suke? Ko shi ko khalifa wani yazo muje yayi dropping dina saboda dama shu’aibu yaron office dinane yakawo ni kuma yawuce”

“To bari nakira maka daya daga cikinsu, ina zuwa”

Juyawa mami tayi ta nufi sashen samarin,da khalifa tafara yin arba dan haka shi takirawo ta nuna masa yusleem a inda yake tsaye ya cire hularshi yana lanlankwasa ta,

Batare data koma wurinshi ba tawuce zuwa ciki shikuma khalifa ya nufi wurinsa daga nan wurin da aka tanada domin adana motoci sukaje khalifa yadauko guda daya yusleem yabude yashiga suka fita daga cikin gidan,

“Yaya ka siyi yan abubuwanne?”

Kallon khalifa yusleem yayi,

“Mefa?”

“Wai da yaya ina nufin dan nama haka da sauransu..”

“Kaima yanzu bakada kunya kamar Abdul ko?” Yafada yana kallon titi,

“A’a yaya bahaka bane,nayi tunanin ko kamanta ne shine natuna maka”

Bai sake cemasa uffan ba har sukaje gidan nan yabude kofa yafita ya nufi ciki yana takawa ahankali…..

*

        ***Ahankali yaci gaba da takawa yana tafiya tamkar wani marar lafiya ko kuma wanda yake jin tausayin kasar,

Hularshi yatura baya zuwa keyarshi ya zuba hannuwanshi acikin aljihun wandonshi domin wani dan dari dari yakeji,

Babban falon dake girke atsakiyar part din guda biyu yabude yashiga, hanyar da zata sadashi da bedrooms din Hafsat yabi har ya isa ga dakin da take ciki,tana kishingide ta dan fara gyangyadi amma ba bacci takeyi ba,

Ahankali yatura kofar dakin yashiga, daga bakin kofa ya tsaya bayan yasake zuba hannuwanshi acikin aljihun wandonshi,

Dan gyaran murya yayi kadan wanda hakan yayi sanadiyyar bude idon Hafsa ta tashi zaune da hanzari,
.
“Zo….” Shine kawai abinda yace da ita cikin sanyayyiyar muryarshi yajuya yafara tafiya, tashi tayi tasauka daga kan gadon tabi bayanshi,

Saboda irin yadda yake daga kafa dakyar yana tafiya ahankali yasa harta cimmashi awani dan madaidaicin corridor, cikin falonta suka shiga,

Kan dining ya nuna mata,

“Ga abinci can idan kina jin yunwa..”

Daga haka bai sake cewa komai ba yajuya yafita ya nufi part dinshi,

Cikeda mamaki Hafsat take binshi da kallo, lallai wannan yusleem din ba kanwar lasa bane yanzu dama akan kawai zai nuna mata abinci ne yasa yatasota?

Kan dining table din takarasa, bakaken ledodi ne cikeda fruits daya ledar kuma kaji ne gasassu guda uku sai juice da fresh milk,
.
Dan yunwa kam tabbas tana jinta domin rabonta da cin abinci tun lokacin da aka fara hidimar bikin nan bata iya zama taci abinci ta koshi ba,

Zama tayi ta bude ledar tafara yagar kazar tana ci saida taji ta koshi sannan ta mayar ta rufe ta tashi,

Bedroom dinta takoma tashiga bathroom ta wanke hannunta da bakinta tadawo ta kwanta, Sam bata kara jin duriyar yusleem ba har asuba tayi gari ya waye,

Wanka tayi ta shirya tayi kwalliya tasaka wani jan Swiss material,

Fita tayi zuwa falo tana bin ko ina da kallo domin dukiyar da aka zuba afalon da shi kansa tsarin falon ba kadan bane,

Haka taci gaba da zama shiru har surayya tazo, shigowa tayi tana dauketa kulolin abinci,

“Amarya bakya laifi..” Surayya tafada cikeda tsokana,

“Ni dan Allah zubo min abincin nan inci yunwa nakeji”

“Ai dole kiji yunwa amaryar mu, yanzu kuwa zan Kawo miki..”

Kitchen ta shiga ta dauko filet tazubo mata wainar shinkafa da miyar agushi wacce taji kaji domin inbanda kamshi babu abinda takeyi,
.
“Ga abinci, ina yayan? Ko bai tashiba?”

Shiru Hafsat tayi saboda ita bata sanma me zatace ba domin rabonta da ganinshi tun jiya da daddare,

“Duk yunwar ce ne ta hanaki magana?”

Murmushi Hafsat tayi ta gutsuri wainar tafara aikawa cikinta, kan dining table surayya takoma taje ta kinkimo ledar kajin da yusleem yakawowa Hafsat jiya,

“Ai wannan baku ci bama, kun tsaya jin kunyar juna ko? To ni bari inci”

Hafsat najinta bata tankaba domin ita yusleem yayi bala’in daure mata kai saboda ko atarihi bata taba jin angon da yayiwa amaryarshi hakaba, ace kazar ma bata da darajar da zai dauka yakai mata har sai ya kirata tazo ta dauka da kanta,
.
Abincinta taci ta koshi ita kuma surayya tana faman yagar kazar da ta rage jiya, bayan sun gama ne surayya tajata,

“Zo muje kiga sauran bedrooms din”

Fita sukayi daga falonta suka shiga corridor din da zai sadaka da dakunan baccinta wadanda suke guda biyu ajere sai can gaba dasu daga karshe wata kofa ce itama daban, bayan sun gama dudduba dakunan ne suka shiga wannan kofar, wani lafiyayyen falo Hafsat tagani mai mutukar kyau wanda yasha kaya masu tsada sannan akwai wata babbar kofa wacce tafita tawaje har zuwa kan wata katuwar balcony,

Coffee & milk colour ne gaba dayanshi sai wani kamshi yake na musamman,

Zama surayya tayi acikin daya daga cikin kujerun falon,

“Wash kafata, kinga bedroom din can leka kigani saboda wallahi nikam nagaji..”
.
Batare da tunanin komai ba Hafsat ta nufi bedroom din ta murda kofar ta shiga, dakine babba wanda girmansa zaiyi girman falo, wani babban royal bed ne agirke aciki sai kamfacecen mudubi da sauran kayayyaki, kamar ance ta kalli gefenta tana kallon wurin taga wata babbar kujera mai kamada dan karamin gado, yusleem ne kwance akai ya rungume pillow akirjinsa idanuwansa arufe abisa dukkan alamu bacci yake yi,

Tafi minti biyu tana kallonshi kafin tajuya zata fita harta bude kofar taji maganarshi cikin muryarshi mai mutukar sanyi da zaki,

“Zo nan…”

Cikin tsoro ta waiwaya ta kalleshi, bude idanuwanshi yayi yana kallon sama bai kalleta ba,

Mayar da kofar tayi ta rufe takarasa inda yake,

“Gani..”

“Menene ya kawoki?”

“Babu komai..”

Shiru taji yayi baiyi magana ba sannan har lokacin bai daga ido ya kalleta ba maimakon hakama sai yajuyar da kanshi da yayi yana kallon wani wuri,

“Ina kwana..?” Tace dashi saboda tunawar da tayi bata gaidashi ba,
.
“Lafiya..” Taji ya amsa,

Tana nan tsaye shiru bai sake yimata magana ba dan haka tajuya tafita,

Gani tayi surayya bata inda tatafi tabarta, wucewa tayi takoma part dinta acan ta iske surayya ta kunna  makekiyar tv din dake manne abangon falon ta kamo tashar zee world,

Ganinta yasa surayya fara yin dariya kasa kasa,

“Amarya da alama dai jiya yaya bai gayyaceki dakin nashi ba shiyasa har nakaiki baki san can bane”

Zama Hafsat tayi tana yamutsa fuska,

“Dama kin san dakinsa ne shine kika ce inshiga ko?”

Dariya surayya tayi,

“To ba gashi kinyi gaisuwar safe ba..”
.
Kyaleta Hafsat tayi batace komai ba amma yanzu ta fahimci miskilin mutum Allah ya hadata zama dashi,

Haka suka cigaba da zama itada surayya har yan uwan hajiya kubra suka zo suka tafi suna tafiya yan uwan mami da kawayenta suma suka zo, duk wanda yazo gidan sai yasa albarka kuma sai yaji yayi sha’awarsa domin yayi sosai, amma wasu daga cikin kawayen mami da sukazo suka ga gida sannan suka ga Hafsat saida tausayinta yakamasu domin sun san itama kwana nawane yusleem zai tarkatata yakorata da saki dai dai dai dai har uku.

Har dare surayya tana gidan sai bayan sallar isha dasu khalifa suka zo tace zata bisu tatafi,

Hafsat kallon samarin tayi wato Abdul da khalifa duk da bata taba ganinsuba amma tasan dai kannen yusleem ne domin ga kama nan sai dai duk cikinsu shine fari domin har surayya batafi Hafsat din fariba shikuwa yusleem farine sol,

“Kinga kannen yaya, yakika gansu? Sunfishi kyau ko?”

Murmushi Hafsat tayi, “ke kika sani”

Gaisawa sukayi daga nan sukai mata sallama suka tafi,

Tunda suka tafi kuma tazauna shiru ita kadai daga karshema taji tsoro yafara shigarta dan haka ta tattara takoma bedroom dinta tayi shirin bacci ta kwanta.

.
  Tun daga wannan ranar bata sake saka yusleem acikin idonta ba,kullum tareda surayya suke wuni har dare, da haka har tayi sati daya agidan,

Rabonta da ganin yusleem kuwa tun ranar da surayya tazo last wanda yashigo falon yace mata gobe kukun da yasamo mata zai fara zuwa tace a’a zata rinka girkinta da kanta, juyawa yayi gurin surayya tatashi ya maida ta gida, tun daga ranar Hafsa bata kara ganinshi ba gashi yanzu surayya bata nan sati biyu kenan da tafiyarta Kaduna gidan kanwar mami,

Haka take wuni ita kadai babu abokin hira, bata san fitar yusleem ba bare tasan dawowarsa.

Ranar alhamis da safe misalin karfe 11 saiga mami tazo gidan,

Da murna Hafsat ta karbeta, bayan sun gaisa mamin ke tambayarta yusleem din tashi tayi tafita tace bari ta kirashi,

Faduwa gabanta yafara yi lokacin data doshi dakin nasa, ahankali ta tura ta shiga, tayi sa’a kuwa yana nan,

Yana kan gado akwance yana bacci,

“Yaya… Yaya..” Tafara kiranshi, bude idonshi yayi, kallo daya yayi mata ya maida idanuwanshi ya rufe,cikin sanyayyiyar muryarshi mai dadi yace,

“Menene?,idan ina bacci ba a tashina”

“Mami ce tazo shine tace inkira ka,amma kayi hakuri”

Ganin bashida niyyar amsa mata yasata juyawa zata fita, har takai bakin kofa taji muryarsa,

“Zo..” Komawa tayi wurinshi,

“Bude drewar dinnan ki miko min t shirt dina”
.
Budewa drewar din tayi ta dauko masa t shirt guda daya ja ta mika masa,

“Ajiye anan”

Ajiyewa tayi ta juya zata fita,

“Kinga…”

Dawowa tasake yi,

“Kin iya dafa tea?”

“Ehh na iya”

“Ki dafa min, kicewa mami ina zuwa”

Da “to” ta amsa tajuya tafita tana mamakinshi acikin ranta domin sam bashida alkibla tarasa gane inda yasaka gaba……

*

     ***Tagumi Hafsat tayi tai shiru tama rasa abin cewa domin bata san ta inda zata faraba,

“Baiwar Allah karki tashi hankalinki, nidai kawai abinda nakeso kisani shine yaya yusleem fa ba dutse bane mutum ne dan haka duk taurin kansa wata rana dole ya bukaci mace, dan haka daurewa zakiyi ki zage kiyita shisshige masa har yazo hannu kin gane ai?

‘Yar rangwadar nan, kwalliyar nan, tsabtar nan…” Surayya tafada tana dariya,

Kallonta Hafsat tayi idanuwanta har sunyi ja,

“Surayya kenan da alama baki gama fahimtar yayan naki ba, yaushe ma ya zauna agidan bare har insamu damar yi masa wadannan abubuwan? Kedai kawai Allah yabani mafita”

“Amin, zaima baki cikin ikonsa”

Haka suka cigaba da tattauna maganar har tsawon wani lokaci,yauma kamar koda yaushe saida da daddare sannan surayya taja motarta ta tafi,
.
Tafiyarta yasa Hafsat jin gidan yayi mata tsittt, part din yusleem ta shiga baya cikin falon dan haka ta nufi bedroom dinshi nan dinma baya ciki, har zata fita tajiyo motsin ruwa acikin toilet alamun wanka yake nan tajuya tafita,

Bata kara sashi a idonta ba tun daga ranar,dan haka kullum wunin kadaici takeyi wannan dalilin ne yasa tayiwa Ummi waya tace a Kawo mata keken sakarta domin ko babu komai zai rinka dan debe mata kewa idan babu abinda takeyi sai tarinka hawa tanayi,

Washe gari hajiya kubra taje gidan takai mata keken da sauran kayan da zatayi amfani dasu wurin sakar, wannan shine karo nafarko da ummin taje gidan nata shiyasa murnarta takasa boyuwa,

Ita ason ranta ma ummin ta zauna ta wuni amma fur taki ko minti talatin batayi ba tatashi zata tafi,

Bin bayanta Hafsat tayi ta rakata anan hajiya kubran ke fada mata cewar ai yusleem sau biyu yana zuwa gida gaishesu bayan bikin, mamaki ne ya kama hafsa saboda bata zaci zai iya zuwaba duk da tafi zaton cewar mami ce zata tilasta shi yaje, sallama sukayi da ummin tatafi ita kuma takoma cikin gida.
.
Samun keken sakar nan akusa da ita shine dalilinta yanzu na rage zaman tunani duk da wani lokacin tana ganin anya kuwa rayuwarsu ita da yusleem zata yiyu ahaka? A matsayinsu na mata da miji ace sai suyi kwana 3 basu ga junaba, sannan bai damu da yaci abincinta ba balle har magana ta shiga tsakaninsu,

Gama wannan tunanin keda wuya ta mike ta nufi falonshi, baya ciki dan haka takarasa dakin baccinsa can dinma baya nan amma ga laptop dinshi nan a ajiye akan gado, karasawa tayi ta dauke laptop din ta gyara gadon daga nan ta zarce da gyara dakin gaba daya,

Bathroom tashiga nan taga ya jika kananan kayanshi acikin bocket da dukkan alamu so yake su jiku yasa acikin washing machine yawanke domin tasan bazai taba yin wanki da kansa ba tunda itama da ba kowan kowaba an ajiye mata injin wankin sai dai ita bata ma fiya amfani dashiba tafi ganewa tayi abinta da kanta,

Tsayawa tayi ta wanke masa kayan tass tadauka tafita ta shanya, tana cikin shanyawa yadawo yana sanye da kananan kaya jeans da t shirt,

Binshi cikin falon tayi bayan ta kammala shanyar kayan,

“Sannu da zuwa…”

“Yawwa…” Ya amsa mata aciki ciki daga nan bai kara koda kallon bangaren da takeba bare tasa ran zaiyi mata sannu na aikin da tayi masa,dan haka tawuce takoma part dinta,

Wadannan abubuwan dake faruwa sune suka hanata bacci adaren yau har misalin karfe daya idonta biyu, tanata juyi tajiyo kamar alamun tafiya atsakar gida a tsorace ta tashi taje gaban window ta daga labule tafara lekawa ahankali, kasancewar tsakar gidan akwai haske tal kamar rana shiyasa tasamu damar hango yusleem din wanda ke kokarin bude kofar motarshi,

“Ina yaya yusleem zaije acikin daren nan?” Ta tambayi kanta,
.
Kafin ta iya bawa kanta amsa tuni har yashiga motar mai gadi ya bude masa yafice, ita tsoro ne ma ya kamata domin duk atunaninta agidan mami ne wani abu yafaru nan takoma ta zauna jugum tanata nazari amma motsi kadan sai tatashi ta leka ko yadawo amma shiru,

Haka takasa bacci sai sake sake da haka har asubah tayi a lokacin ne taji dawowarshi da kamar taje wurinshi taji abinda yafaru sai dai tafasa,alwala taje ta dauro tazo ta tada salla.

Misalin karfe 8 tashiga falonshi bayan taci kwalliya cikin wata dark purple din shadda,

Kwance ta sameshi yana bacci akan doguwar kujera yana sanye da farar t shirt da bakin boxer, karasawa dakinshi tayi ta gyara masa tafito, lokacin da ta fito kuma yana zaune yana danna wayarshi, gaisheshi tayi ya amsa daga nan yaci gaba da abinda yake yi, jin baice mata komai ba yasata fita takoma falonta taci gaba da harkokinta,

Tana kan kekenta tana karasa hada rigar data fara jiya taji sallamar Amina kawarta, da murna ta tari aminan wacce ke daga kafa dakyar domin cikinta yadan fara tsufa,

Ba karamin dadin ganin aminan tajiba nan suka baje a falonta suka hau hirar yaushe gamo, wuni cur Amina tayi mata sai yamma ta tafi,

Haka taci gaba da zaman kadaici agidan domin surayya ma takoma makaranta kuma bazata sake dawowa ba har saita kammala, yau watanta biyu da wani abu agidan kuma tunda tazo bata taba fitaba shiyasa yau ta kuduri niyyar tambayarshi zuwa ganin gida,
.
Yana kokarin fita tayi gaggawar tsayar dashi, tsayawa yayi batare da yajiyo ba,

“Yaya dama yau ina son zuwa gidanmu ne”

“Allah kiyaye hanya, idan kin shirya akwai driver”

Daga haka yayi gaba abinshi, shiryawa taje tayi tafito tana dauke da rigunan jariran da ta saka wanda zata tafi dasu takaiwa Ummi domin asayar mata,

Kamar yadda yusleem yace haka ta tarar da driver yana zaman jiranta nan ya dauketa yakaita gida, murna wurin hajiya kubra abin ba acewa komai nan tashiga yin nan nan da ita, Hafsat ba ita tabaro gidanba sai dare domin saida tajira alhaji sa’id yadawo suka gaisa,

Daren yauma kamar rannan kasa bacci tayi can taji fitar yusleem daga gidan agogo ta kalla karfe 2 saura na dare,

“To wai shi wannan ina yake zuwa cikin talatainin dare haka?”
.
Sake saken zuci tayita yi har saida asuba takawo kai, awannan lokacin ne taji dawowarsa azamar sauka daga kan gadonta tayi tanufi part dinshi da sauri domin tana son taga awanne yanayi yake,

Acikin falonshi ta buya a bayan labule, ahankali taji ya bude kofa yashigo, lekashi tayi nan taganshi acikin nutsuwarshi yake ita tayi zaton zata ganshi cikin maye ko makamancin haka, zama yayi ya bude wani dan karamin akwati nan taga kudi fall kuma duk daloli ne ba naira ba,

Mayarwa yayi ya rufe ya tashi yashiga bedroom dinshi, sadadadawa tayi tafita takoma dakinta tana tambayar kanta to daga ina yaya yusleem yake?

Wasa wasa kullum cikin dare sai taji fitarsa kuma bashi zai dawoba sai aubah ashe dama can haka yakeyi sanine batayi ba saboda lokacin da zai fita tayi bacci shiyasa har yaje yadawo bata saniba, kasa gane inda yake zuwa tayi domin fitar tasa kusan kullum ne tamkar ibada kuma baya tashi fita sai tsakiyar dare,

Yau kam ta daura aniyar binshi taga inda yake zuwa domin tunaninta yanzu yafara bata cewar ko yaya yusleem dan fashi ne?
.
Hana idonta bacci tayi har karfe dayan dare tana jira taji motsin fitowarsa amma shiru, karfe biyu shiru har da rabi duk shiru, hakura tayi ta kwanta nan bacci ya dauketa can cikin baccinta taji dirin motarshi agigice ta tashi ta leka abin haushi wai sai ganinshi tayi yafito daga cikin mota alamun yadawo daga wurinda yaje,

Da haushin wannan abun ta wuni da yamma sai gashi ya shigo cikin part dinta yana sanye cikin farar shadda mai mutukar kyau da tsada dinkin tazarce sai jar hula da yasaka,hannunsa daure da agogon fata fari kafarshi kuma yasa farin takalmi half cover tsaf dashi fadin irin kyan da yayi abun ba acewa komai,ita bama tafiya ganinshi da dogayen kayaba sai dai idan ranar juma’a ce tayi wannan kam yanasa manyan kaya amma idan bahaka ba kullum cikin kananan kaya yake,

“Zanyi tafiya zanje America daga can zan wuce India saboda akwai likitan da zan gani acan,idan akwai abinda kike bukata ki duba cikin bedroom dina akwai kudi…” Yace da ita cikin muryarsa mai sanyi,

“Allah ya kiyaye hanya yadawo dakai lafiya”

Bai amsaba yajuya yafita,bayan tafiyarshi part dinshi taje ta shiga bedroom dinshi tahau binciki wai ko zataga wata alama wacce zata tabbatar mata da gaskiyar abinda take zargi amma babu abinda tagani haka ta hakura ta mayar da dakin ta gyara ta fita,
.
Washe garin tafiyarshi mami ta turo driver ya dauketa can ta zauna har tsawon sati 2 sai ana gobe zai dawo sannan takoma gidanta kuma sosai taji dadin zama tareda mami domin tana mutukar kaunarta tareda kulawa da ita,

Tunda yadawo take bibiyarsa tana fakonsa saboda so take sai tagane inda yake zuwa cikin dare da abinda yake yi, kullum bata bacci har tsawon kwana biyar da dawowarsa saida ta sakankance ranar da tayi bacci aranar ya fita daf da asuba kuma sai gashi yadawo,

Wani haushine ya cika mata ciki gashi kuma tun daga ranar bai kuma fitaba, duk da haka bata hakura ba haka taci gaba da saka masa ido,

A wata ranar lahdi har zata kwanta sai tajiyo motsinsa, tashi tayi ta sadada tafita har yabude motar zai shiga ko me ya tuna oho sai yafasa yanufi ciki amma dai yabar motar a bude, ganin haka yasata lallabawa tabude bayan motar tashiga ta makure ta buya,

Tafi mintuna talatin aciki bai dawoba, tana shirin fita sai taji alamun tahowarsa nan takoma tasake makalewa ta yadda bazai ganta ba,

Shiga cikin motar yayi yatadata ahankali ya murza ya doshi gate din fita…….

  _Sakon fatan alkhairi ga yan group din Duniyar littattafan Hausa, tabbas kunfi kowa son alwashi…_

*

      ***Sake lafewa Hafsat tayi a lungun kunjerun baya wato wurinda ake ajiye kafa, tana jinsa yana driving din yana dan jan karamin tsaki, titin emirs palace yahau,

Gaba daya garin tsitt yake babu motsin kowa sai haushin karnuka wadanda idan sun ji motsi suke kaurewa da yi,

Wayarshi ce tadanyi kara nan taga ya dauka yakara a kunnensa, cikin sansanyar muryarshi taji yace,

“Am on my way….” Wani dan tsakin yaja bayan ya kammala wayar ya ajiye,
.
Haka yaci gaba da yin driving ahankali shi kadai atsakiyar titi domin hatta jami’an tsaro masu yin patrol sun gama aikinsu sun tafi,ita mamakinshi ma takeyi ganin ko tsoro bayaji shi kadai a titi kamar aljani,

Wata hadaddiyar atishawa ce ta tahowa Hafsat batare data shirya ba nan tayi hanzarin toshe bakinta da hancinta amma duk da haka saida yar kararta ta fita,

“Atshhh…”

Jin sautin yasa yusleem wanda ke yin driving dan juyowa nan tayi saurin sake kwantawa abayan kujerar, maida kallonsa titi yayi yaci gaba da tukinshi,

Jin alamun yatsaya yasata dan dago kanta domin ganin ko inane, bata san ko ina bane amma tana dan iya jiyo maganganun mutane, dukar da kanta tayi har saida taji fitarsa sannan ta dago tafara kallon wurin,

Wani babban hotel ne mai tsananin kyau wanda yakeda fiyeda hawa 20,harabar wurin kadai ta isheka nishadi da kallo domin itama kawace take da abubuwan saka nishadi, wurin haske ne tarwal kamar rana sannan ga mutane nan sunata hada hadarsu mata da maza,
.
Hango yusleem tayi ya nufi cikin hotel din nan tayi yunkurin binshi amma abin haushi ya kulle motar kuma babu yadda zatayi ta iya budeta domin motar tashi ba kamar sauran motoci bane, motarshi motace mai tsada wacce ta amsa sunanta domin ko a zagayen garin bata tunanin akwai wanda yake da irinta,

Dukan kujera tayi cikeda haushi, damuwa gamida bacin rai domin taso ace tabishi abaya taga karshen gudun ruwansa,

Tana nan zaune tana kallon yanda mata da maza ke zuwa suna shiga cikin hotel din kamar bazasu kareba domin maimakon ma su ragu sai sake karuwa suke,

Tagumi Hafsat tayi aranta tana tunanin ko mahukunta suna ina hakan take faruwa?,

Tana nan zaune tana jiran taga ta inda yusleem zai bullo amma shiru sai misalin karfe 5 saura sannan ta hangoshi yana fitowa daga cikin hotel din, saurin komawa maboyarta tayi ta lafe, saida yadan jima awaje bata san me yatsaya yiba sannan yabude motar yashiga ya tadata,

Tana jinsu suka hau titi suka nufi unguwarsu, karar bude gate taji alamun sun iso gida lokacin anfara shiga masallaci sallar asubah,

Kasancewar gidane yasa yusleem bai kulle motar ba fita kawai yayi yatura kofar yanufi ciki, saida yajima da fita sannan hafsat ta lallaba ta fita,
.
Ganin kamar giftawar mutum yusleem yayi lokacin da yake tsaye agaban window dinshi bayan yadauro alwala, da sauri yafita yabi ta kofar da zata sadashi da part din hafsat,

Bai taba shiga bedrooms dinta ba sai yau, wannan shine karo nafarko da yataba takawa zuwa dakunan barcinta,

Bedroom din farko yafara shiga nan babu kowa aciki har cikin toilet yaduba amma babu kowa, rufe dakin yayi yakarasa dayan yana shiga tana fitowa daga bathroom da alama alwala tayi,

Ganinta yasashi juyawa yafita, dan lekashi Hafsat tayi,

“Ohh Allah, Allah kasa dai ba ganewa yayiba..” Tafada acikin zuciyarta,

Tana idar da salla ta kwanta ramuwar baccin da bata samu tayiba tunda ta kwanta kuma ba ita ta tashiba sai misalin karfe 10 nasafe, wanka tayi tashirya tasaka wata doguwar riga ta leshi pink colour da stones ajiki, kitchen tashiga ta dora breakfast sannan ta dafawa yusleem tea tanayi tana addu’ar Allah yasa karya gwasaleta,

Saida ta kammala yin breakfast dinta taci sannan ta dauki nashi ta nufi part dinshi,

Yana kwance akan tsakiyar fankamemen gadonshi yana ta bacci, abisa dukkan alamu har yanzu bai tashiba,

Dan karamin stoll tajawo ta dora masa akai ta tsaya tana kallonsa,

“Menene kika tsaya min aka kina kallona??” Taji yafada batare da ya bude idonsa ba, ita tsorata ma tayi saboda ganin tun lokacin data shigo dakin idanuwanshi a rufe suke,

“Ahhh babu komai…, dama breakfast nakawo maka..”
.
Murmushi taga yayi akaro nafarko tsakaninta dashi domin tun ranar data fara ganinsa bata taba ganin murmushinsa ba sai yau,

“Shiga toilet ki hada min ruwan wanka..”

Taji yasake fada ahankali,

“Toh” bude bathroom dinshi tayi tashiga, saida tafara dauraye toilet din sannan ta hada mishi ruwa acikin bathtub tasaka salt nawanka da turaren wanka domin duk gasu nan tanade asaman wata yar madaidaiciyar kanta wacce ke daure ajikin bangon toilet din,

Lokacin da tafito atsakar dakin ta sameshi yana tsaye yana yin mika nan tabashi hanya yawuce yashiga ita kuma tasoma gyaran dakin tana yi tana yan kalle kalle ko Allah zaisa idanuwanta su gane mata wani abu, har kasan gado ta leka amma babu abinda tagani,

Tana kammala gyara dakin shi kuma yana fitowa fita tayi tabashi wuri domin yashirya, a falonshi ta zauna tana nan zaune har yafito,zama yayi ya dauki remote ya kunna tv,

Ita dai Hafsat tana zaune tana binsa da kallo duk inda ya motsa, har azahar tayi bata bar falonba saida taga yafita salla sannan taje takwashe kayan da ta kawo masa breakfast aciki takoma part dinta amma data kammala lunch ma can tasake komawa sukaci gaba da zaman kurame.
.
  Abin mamaki tamkar yasan shirin da Hafsat keyi akansa ko kuma yanada masaniyar abinda take shirin yi sai ya canja taku, acikin kwanakin gaba daya baiyi fitar dareba sai dai amma idan yafita kafin sallar magrib baya dawowa sai 1 ko 12:30,kuma ranakun suna dan sassabawa domin wata ranama da rana yake fita to bazai dawoba sai 1 wata rana kuma tun safe idan yafita office baya dawowa sai 12 wata rana kuma sai yayi zamansa agida ko nan da kofar gida bazai fitaba sai dai idan time din salla yayi yafita yaje masallaci yadawo, gaba daya yasa Hafsat acikin wani yanayi domin takasa fahimtar ta inda zata gano abinda yake aikatawa aboye wanda abisa dukkan alamu babu Wanda yasani,

Yafi sati biyu yana wannan shifting din daga rana zuwa dare ko kuma daga yamma zuwa dare,

Ganin kamar idan aka cigaba da haka Hafsat bazata samu abinda takeso ba yasata yimasa dabara,

Tea ta dafa masa takai mishi ta zauna acan nesa dashi, saida yadawo daga sallar azahar sannan yasha, nan yaji duk kasala ta rufeshi, wannan dalilin ne ya hanashi fita gaba daya ranar domin har salla agida duk yayi,

Karfe 2 nadare daidai yayi shirin fita nan yaje wurin da yake ajiye keys din motocinshi yasoma dubawa, yayi neman duniya amma baiga na BMW dinshiba shikuma yafi son yaje da ita domin sabuwar motace dan haka ba kowa bane yasanshi da itaba sabanin sauran motocinshi,

Wani key din yadauka yafita, Hafsat da tun jimawa take cikin bayan motar a boye tasake gyara buyan da tayi ganin ya nufo parking space din amma abin haushi koda yazo sai taji ba motar da take ciki yashiga ba wata daban yabude yashiga yayi reverse zai fita haushi ne ya cika mata ciki domin fa saboda haka ta dauke key din BMW dinshi ta boye saboda kar taje yasake kulleta kamar yadda yayi mata rannan tanaji tana gani yafice daga gidan batare data bishiba,
.
Ciki takoma tana cizon yatsa wato duk shirin data dade tanayi Yatashi abanza kenan,tsabar takaici bata ma san lokacin da yadawo ba.

  Ganin tarasa mafita yasata tambayarshi cewar zataje gidansu bai hanataba kamar yadda tayi tsammani dama, koda taje gidan acan tawuni amma yamma tanayi tacewa Ummi tafiya zatayi, nan ummin tayi tayi da ita akan tajira salisu driver yadawo yakaita amma taki,

A perfect guys & ladies hotel ta sauka ta biya mai adaidaita sahu kudinsa tatafi can cikin wasu shuke shuken flowers ta tsaya, har akayi magrib bataga alamun daya daga cikin motocin yusleem ba tana nan tsaye har akayi isha alokacin ne ta saddakar da bazai zoba,

Fitowa tayi takama hanya zata fita tana zuwa gate din hotel din tahango motarshi tana dosowa kamar a mafarki babu shiri tajuya tabi ta bayan wasu bishiyoyi ta nemi mafaka duk da tasan ba lallai ne yaganeta ba saboda bazai taba  tsammanin ganinta awurinba,

Tana ganinshi yafito bayan ya rufe motarshi ya nufi ciki yana yin waya yana sanye cikin kananan kaya, lababawa tayi tasoma binsa abaya abaya har zuwa ciki, akofar wani daki taga yatsaya mintuna kadan aka bude masa yashiga,batayi kasa agwiwa ba tabishi har kofar wannan dakin,
.
Tsayawa tayi tana tunanin ta ina ya kamata tafara, tafi minti goma atsaye daga karshe kawai ta nufi kofar ta murda abin mamaki abude tajita nan tashiga ahankali, wani dan madaidaicin falone wanda yacika da sanyin air condition, leken cikin bedroom din tafara yi amma kuma bata iya hango komai nan tadan tura kofar ahankali ta zira kanta ta leka, abinda tagani shine yayi sanadiyar sulalewarta awurin ta suma bayan ta kwalla kara mai mutukar firgitarwa…..

  _Tofa ko me Hafsat tagani? Nidai Ummi Shatu banida wannan amsar…_

*

         ***Ahankali tafara bude idanuwanta wadanda suka yi mata nauyi ga wani irin ciwo da kanta ke faman yimata kamar zai tsage,

Dishi dishi take gani kafin daga bisani ta dan fara ganin dishi dishin yana washewa har ya b’ace gaba daya,

Mami ta hango zaune saman wata kujerar roba ganin ta bude idonta yasa mamin matsawa gareta,

“Sannu Hafsat…, sannu kinji, Allah yabaki lafiya…”

Runtse idanuwanta tayi take wasu zafafan hawaye suka gangaro daga cikin idanuwanta, ko kadan bata burin ta sake ganin yusleem ayanda taganshi dazu kuma ko tunawa bata son ta kara yi domin wannan shine mafi munin gani da idanuwanta suka taba yi tunda tazo duniya,

“Sannu Hafsat, kukan me kikeyi kuma?” Mami ta tambayeta tana dafata,
.
“Kukan ciwo mami, kukan ciwo nakeyi mami ba kukan komai ba domin kaina wani nauyi naji yayi min banda azabar ciwon dake addabata…”

“Sannu, sannu Allah yabaki lafiya, ina zuwa bari inkirawo likita saboda yace idan kin bude idanuwanki inkirashi..”

Fita mami tayi daga cikin dakin nan Hafsat tasake mayar da idanuwanta ta rufe tana hawaye, a hakikanin gaskiya abinda tagani ne yasata wannan kukan bawai ciwon kan da take tareda shi yanzu bane,

Tana nan kwance tana hawaye taji shigowar mami da dr,

Gaban gadonta likitan yakarasa yakai hannunsa kan goshinta ya taba,

“Sannu, yanzu me kikeji yafi damunki?”

“Dr ciwon kai ne kadai ke damuna..”

“To insha Allah shima zai daina nan da dan wani lokaci..”
.
Dukufa likitan yayi yafara rubutu ajikin wani dan madaidaicin file saida ya kammala sannan yadago ya mikawa mami takardar,

“Ga magungunan da za asamo mata tasha bayan taci abinci, Allah yakara bata lafiya..”

Karbar takardar mami tayi shikuma likitan yasaka kai yafice daga cikin dakin,

Wayar yusleem mami tasoma nema ringing biyu zuwa uku ya dauka,

“Kana inane? Kai nake jirafa..”

Kashe wayar tayi batare da Hafsat tajiyo abinda yusleem din yafada ba,

Ba afi mintuna biyar da gama wayarsu da mami ba sai gashi ya turo kofa yashigo, kawar da kanta hafsat tayi daga gefen da yake ta mayar zuwa wani gefen,

“Wannan shine mijin kaddara…” Tafada acikin zuciyarta,

“Wai kai me yasameta? Inata tambayarka abinda yasameta harta suma haka amma kaki yimin bayani..”

“Yanzu dai mami ai ba lokacin yin wannan maganar bane, abinda kuke bukata nake son ji”
.
“To kaga dai magungunan da dr yace asiyo tasha bayan ta ci abinci amma gaskiya ni ina ganin idan har takara kwana biyar bataji sauki ba gara ka kaita chairo…”

Dan sajenshi ya shafa ya karbi takardar dake hannu mami,

“To shikenan bari nasamo drugs din indawo..”

Yana fita hajiya kubra na shigowa hannayenta dauke da babban basket din abinci,

“Hajiya siyama ya mai jikin? Nifa kalau muka rabu da ita saida ma nayi nayi da ita tajira salisu yadawo yakaita amma furr taki ashe tsautsayi ke janta..”

“Ehh haka Allah yake ikonsa ai, nima wallahi sai waya kawai yusleem yamin wai yakaita asibiti…”

Ajiye kayan hannunta hajiya kubra tayi ta matsa wurin Hafsat tana yimata sannu,

“Wai ya akayi haka tafaru? Hafsat garin yaya..?”

“Ummi kaddara da tsautsayi, nima ban san abinda ya sameni ba kawai jina nayi nafadi,shi lokacin da abin yafaru ma yana office inajin sai wayata aka dauka aka kirashi…” Ta karashe maganar hawaye na bin kuncinta,

“To Allah ya rufa asiri ya kiyaye gaba..”

“Amin summa amin, Allah yatashi kafadunta yabata lafiya…” Inji mami,
.
“Tashi kici abincin to, tuwon shinkafa ne miyar zogale..”

Dakyar Hafsat ta iya tashi ta zauna saboda irin yanda kanta ke tsananin sarawa, tafara cin abincin kenan yusleem ya shigo dauke da magungunan da likita ya rubuta mata,

“Mami gashi…”

“Yawwa ansamo, to bari tagama cin abincin sai tasha, ashe kaima baka gida lokacin da abun yafaru? Tace kana office sai awaya aka kiraka..”

Kallonshi Hafsat tayi domin taga irin yanda zai karbi maganar,

Shiru yayi baiyi magana ba saima bude kofa da yayi yafita,

Tunda yafita bata sake jin motsinshi ba,ita kanta tasan daren ranar bazata iya bacciba ba don Allah ya taimaka anhada mata da magungunan bacci ba acikin maganin da aka bata,

Tareda mami suka kwana a asibitin ita kuma ummi tatafi sai da safe ta dawo takawo musu abincin karyawa,
.
Kwananta uku a asibitin dr yace zasu iya tafiya gida, duk da ta dan samu saukin ciwon kan dake addabarta amma ta gagara daina kukan da takeyi wannan kam yazame mata kamar ibada wani lokacin sai suna zaune kalau sai kawai aga tana hawaye gashi daga mamin har Ummi sunyi tambayar duniya amma taki fada musu damuwarta wacce ke sata kukan,

Yanzun ma da zasu bar asibitin hawaye ne ke faman bin kuncinta ganin haka sai mami tace kawai hajiya kubra tatafi da ita gida ta dan sake warwarewa,

Tunda suka koma ummi ta tisata agaba tana yimata tambayoyi,

“Hafsat kin dai san yanzu aduniyar nan bakida wanda yafini daga ni sai Alhaji, ki sanar dani abinda yake damunki, idan baki fada minba wa kike dashi wanda zaki fadawa?”

Murmushin karfin hali Hafsat tayi,

“Ummi wallahi bafa kukan wani abu nakeyiba, kawai wani abin mamaki da ban tausayi nagani ranar da nabar gidan nan…”

“Me kika gani?”

“Ummi wata matace suke tafiya da yarta, tana rike da hannun yar fa yarinyar ta kwace ta ruga da gudu zata dauko wani abin wasa da ta hango ashe tsautsayi ne saiga mota tabi takanta gaba daya ta tanitseta, wannan abun shinefa ya hadda samin wannan suman da nayi…”

Dafata hajiya kubra tayi,

“Allah sarki Hafsat to ai dama idan ajali yayi kira ba makawa sai antafi, Allah yajikanta mukuma yasa mucika da kalmar shahada..”

“Amin Ummi”
.
Tashi hajiya kubra tayi tafita, tana fita Hafsat ta kifa kanta ajikin pillow tasoma kuka mai sauti domin da duk kukan zuci take yi wanda yafi nafili ciwo,

Kwananta biyu agida amma kullum sai mami tazo dubata yusleem ne kadai bai taba zuwa ba, aranar da tayi kwana uku mami tace tashirya su tafi inyaso idan takarasa warwarewa awurinta sai takoma gidanta, shiryawa tayi suka tafi gidan mamin nan mami tasoma bata dukkan kulawa domin dakin surayya tabata ta zauna aciki wanda yake dauke da dukkan abubuwan jin dadi irin wadanda ba agidan kowa ake samuba sai gidan wadanda suka amsa sunansu masu naira,

Dukkan abinda take so shi ake Kawo mata domin ga ma’aikata nan agidan kashi kashi ita kanta mamin babu abinda takeyi sai dai idan tana bukatar abu tayi waya kawai akawo mata shiyasa koda yaushe cikin ado zaka sameta tasha kwalliyarta ta zubawa jikinta gwala gwalai,
.
Dawowarta gidan mamin ma bai hanata daina kukan da ya zame mata jiki ba domin kullum cikin yinsa take,

Kwananta biyar agidan mamin amma bataga yusleem ba nan tafara tunanin to kodai tafiya yayi ne?

Tana cikin wannan tunanin tajiyo maganar mami a falo kuma da alamu yusleem dinne yazo, runtse idonta tayi tafara zubar da hawaye wanda har mami tashigo bata san tashigo ba,

“Hafsat, wai me yake damunki ne, kukan nan naki yayi yawa kuma nasoma zargin cewar akwai abinda ke saki kukan, ki fada min gaskiya karki boye min..”

“Mami babu komai, wallahi babu abinda ke damuna, wannan kukan ni kaina ban san meyasa nake yinsa amma nasan bazai rasa nasaba ba da accident din da naga anyi rannan ba”
.
“To hafsat ai sai hakuri, haka rayuwar take sai dai Allah yasa mucika da imani, ki shirya anjima mijinki zai zo ya daukeki ku tafi..”

“To mami..”

Ai mami nafita hafsat ta rushe da kuka saboda yanzu ita bata son ganin yusleem kwata kwata kuma da alama shima yagane haka domin tun rannan bai sake rab’ar inda takeba.

Misalin karfe 8 nadare yazo daukarta, kuka mami ta sameta tanayi nan hankalinta yatashi ta fara tambayarta,

“Hafsat ko wani abun yusleem din yake yi miki?”

Jijjiga kai tayi, “a’a mami babu abinda yake min”

“To ko bakya son komawa gidan nashi ne yabarki anan?”

“A’a mami zan koma”

Zama mami tayi agefenta,
.
“Hafsat kar muyi haka dake, ki fada min gaskiya idan har akwai abinda yusleem yake yimiki karki boye min”

“Wallahi mami babu komai, ni babu abinda ya taba yimin muna zaune lafiya dashi,kukan rabuwa dake kawai nakeyi mami da kuma irin soyayyar da kike nuna min nasan duk duniya nafi kowa yin sa’ar surika tagari mai sona”

Rungumeta mami tayi tasoma shafa kanta,

“To hafsat ai kema surakace tagari shiyasa dole in kaunaceki kuma wallahi ina sonki irin soyayyar da nake yiwa ‘yayan da na haifa,yanzu dai shikenan tashi kizo muje dan yazo yana jiranki share hawayenki daina kukan”

Akwatin kayanta tadauka tareda yin karfin halin tsayar da hawayen dake zuba a idonta tafito suka fita da mami domin shi har yajima acikin motarsa,kasancewar ranar juma’a ne shiyasa yake sanye da dogayen kaya na ash colour din shadda mai tsadar gaske,

Gaban motar tashiga batare da ta kalleshiba amma kamshin turarensa na beautiful oud sai cika hancinta yake sallama sukayi da mami tanaji mamin nace masa yakula da ita sosai sannan banda matsanta mata,kuma indai taji yayi mata wani abu to sai ransa yabaci, kasancewar yan miskilancin suna kusa ko amsawa baiyi ba,
.
Jan motar yayi suka fita suka nufi gidanshi babu wanda ya kalli wani bare har yayi magana nan tafara tunanin to ko shima fushin yake?

Lokacin da suka karasa gidan, trolley dinta taja ta nufi ciki batare data dubi side din dayake ba,gidan tsaf tsaf taganshi kamar tana nan, a bedroom dinta tazauna kan bed side drewar tayi tagumi sai kuma tafara kuka,

Handbag dinta wacce tafita da ita ranar data bishi hotel ta suma ya dauko yabita dakinta, cilla mata jakar yayi saman kan bed dinta yajuya zai fita,

“Yaya yusleem…”

Takira sunanshi, cak yatsaya batare da yajiyo ba,

“Meyasa ka zabi wannan mummunar sana’ar acikin rayuwarka? Duk sana’o’in duniya karasa wacce zakayi sai wannan? Kasan kuwa irin mummunan tanadin da Allah yayiwa masu irin wannan sana’ar? Meyasa ka zabi duniyarka akan lahirarka?”
.
Ahankali yajuya yafara takawa ya nufi inda take tana zaune hawaye nafaman bulbula daga idonta kamar anbude fanfo…..Agabanta ya tsugunna yana kallon fuskarta karo nafarko a zamantakewarsu da ya tsaya ya kalleta,

“Yaya yusleem ko kasan kuwa tarin zunubin da yake kan duk wani wanda yake aikata irin wannan dabi’ar? Irinfa wannan laifin al’umar wani annabi sukayi Allah ya halakar dasu sannan acikin littafinsa mai tsarki ya sanar damu nau’o’in azabar da ya tanadarwa duk wani wanda ya kasance yana aikata irin wannan halayyar….”

Tausassun hannayensa yakai yadora akan nata har lokacin dai idanuwansa suna kan fuskarta sannan sun juye daga farare zuwa jajaye,

“Ba laifina bane, karki ga laifina, komai yana faruwa ne da dalili, wallahi irin rayuwar da na tsinci kaina abaya ta kunci, talauci, tsangwama, tsana da kuma kyara itace tayi sanadiyyar fadawata cikin wannan mummunan halin…”
.
Kallonta yayi da jan idanuwanshi tareda kwantar da kanshi bisa cinyarta yanajin zuciyarshi tana yi masa zafi wanda bai taba jin irinsa ba,

“Yaya yusleem nikuma sai nake ganin wannan ba dalili bane ko hujja da har zaka jefa kanka cikin halaka…”

“Wannan daliline mai karfi NANAH….”

“Nikuma agareni ba dalili bane domin wannan abun da kake aikatawa yafi dukkanin abubuwan da ka zayyano muni,haba yaya yusleem kamanta labarin wani mutum da annabi yafada mana mai tsawaita tafiya yana mai gizo mai k’ura k’ura yadaga hannayensa zuwa sama yana cewa ya ubangiji ya ubangiji amma annabi yace ba a amsa masaba saboda abincinsa haramun ne,abin shansa haramun, tufafinsa haramun sannan yayi guzuri da haram….”

Dago da kanshi yayi ya kalleta sakamakon jin saukar hawayenta akan wuyanshi,

“NANAH arayuwar baya na tsinci kaina cikin mawuyacin hali, mahaifinmu Alhaji Ahmad Mela mu Goma Sha biyar ya haifa sannan matanshi uku kowacce tanada yara biyar,

Ya mutu ya barmu tun muna kanana, acikin yaransa mu ukune manya daga Shu’aib sai Mukhtar sai ni, dukkaninmu kanmu daya, kasancewar dama gidan ba azaman lafiya yasa tun rasuwar mahaifinmu kowa ya kama ‘yayanshi  yarike bayan anraba gado,kuma kin san zumuncin yanzu yanda yake na ganin ido ne,

Nanah a lokacin wallahi duk da ni yarone ban wuce shekara 24 ba ina yin iya bakin kokarina wurin nemowa mahaifiyata da kannena abinda zamuci amma mami bata gani kullum cikin kusheni take da zagi cewar ni banida zuciya zan bari wai talauci ya kasheta,
.
Nayi iyakar iyawata ganin na fahimtar da ita amma taki fahimta ita kawai burinta lokaci daya inyi kudi inzama millionaire dan kawai ta bawa kishiyoyinta haushi,

Idan kinga irin sana’o’in danayi makaskanta sai kin tausaya min, har turin baro wallahi nayi, na saida pure water, nayi kanikanci,nayi jiran shago duk wai dan inrufawa kaina da yan uwana asiri amma mami bata gani koda yaushe bata da magana sai nacewa, ita bazan burgeta ba muddin ban tashi nanemo kudi duk inda yake nazama mai kudiba,mami duk tabi ta tsangwameni ta tsaneni akan kawai ban zama mai kudiba,

Da wannan kananan sana’o’in nasamu nakammala degree amma abin haushi babu aikin yi dole nakoma gareji naci gaba da gyaran mota,

Sau da dama ku mata kune kuke cusawa mutum ra’ayin da baiyi niyyaba nanah, a lokacin idan nasiyowa mami abu nakawo mata ko atamfa ko takalmi sai ta raina kiri kiri zata nuna min ban burgeta ba kuma bata ji dadiba wani lokacin ma har takara da fadin “ni ba irin wannan harkar tsiyar nakeso kayimin ba, ni so nake karinka Kawo min kaya masu tsada akwati akwati yanda nima zan fantama, amma kai kullum abubuwa ba arziki kaki katashi kayi arziki yanda mahaifinku ya mutu bai bar muku komaiba kaima haka zaka mutu baka bar komai ba?”
.
Irin Wadannan  maganganun da mami kemin sune suke tsaya min araina inji zuciyata takasa samun nutsuwa saboda ni aganina ina iyakar kokarina amma komai nayi bata gode min kuma bazata samin albarka ba,

Acikin wannan yanayin wan mahaifinmu yabani yarsa Rahina in aura, sam Rahinan bata sona saboda kawai banda abin hannu sai rufin asiri,

Dakyar ita da uwarta suka amince akayi auren saboda babu yanda zasuyi, bayan aurenmu da Rahina nashiga matsanancin hali saboda zan siyo mata kayan cefane in aiko mata dashi daga gareji amma wallahi nanah yanda aka Kawo kayan nan haka zan dawo insamu kayana tabarshi awurin bata taba ba, idan abin lalacewa ne to sai dai ya lalace, bazata yimin girki ba idan nayi magana tace ita bazata dafawa matsiyaci abinci ba mai k’ashin tsiya wanda bashida rabon arziki,

Bazata yi sharaba,baza tai wanke wanke ba babu abinda takeyi abinci ma mahaifiyarta ce ke aiko mata daga gidansu batare da mahaifinta yasaniba, kullum idan naje gaida mami dakyar take amsawa, idan nadawo gida Rahina ta tareni da masifa da bakaken maganganu wani lokacin ma sai tace bazan shiga dakinta ba ita ubanta bai siya mata gado da katifa dan matsiyaci ba dama kuma tunda akayi auren bata barni na kusanceta ba domin kullum da wuka akasan pillow take kwana wai duk ranar da nayi yunkurin zuwa inda take sai ta kasheni,
.
Kullum a falo nake kwana ita kuma tana cikin daki wata rana ma idan bata gadamaba rufe kofa take sai dai inkwana awaje idan nafadawa mami sai ta goyi da bayanta tamkar ba itace ta haifeni ba, duk da irin wannan abubuwan da Rahina kemin bai hana zuciyata fara sonta ba amma ita hankalinta ba akaina yakeba domin haka mahaifiyarta zata zo har gida su hadu su zageni tass suna kirana da matsiyaci marar arziki,

In takaice miki zance daga karshe sakani agaba sukayi saida nasaki Rahina duk da ina sonta ashe wani mai kudi tasamu suke soyayyarsu da aurena, aranar da nasaketa sukazo suka kwashe kayanta Hafsat nayi kuka irin kukan da ban tabayiba domin ina sonta duk da rashin kyautatawar da take yimin,

Kwana biyu nadauka agida ban fitaba saboda damuwa, da daddare ina kwance ni kadai adaki na dauki wayata nashiga facebook nan naga wani yaturo min da friend request babu bata lokaci nayi accepting,

Bayan mun gaisa yake cemin a ina nake nafada masa, sai yacemin wai ina dan harkoki nace masa ehh to ana dan tabawa saboda ni ban gane abinda yake nufiba haka mukaci gaba da yin hira yace shi dan majalissa ne awani gari yakamata inje in sameshi,

Wallahi nanah ban taba sanin mutumin nan bana kirki bane saboda nayi tunanin ko aiki zai bani tunda nafada masa nagama karatu babu aikin yi,
.
Sallama nayiwa mami nashirya natafi wurinsa da takardu na amma koda naje sai labari yasha banban lokacin da yanuna min karara abinda yake son yi dani ashe gay ne ban saniba, a lokacin ban aminceba amma koda nazauna nayi tunani nahango irin tsangwamar da mutane kemin akan bani da arziki da irin halin ko inkula da mami ke nuna min da kuma yadda aka rabani da rahina sai kawai na amince shiyasa nace miki amafi yawan lokuta ku mata kone kuke zama silar faruwar komai domin dayawa daga cikinku bakuda godiyar Allah burinku kawai mutum yayi arziki batareda kun damu da sanin halalcin arzikin ko haramcinsa ba,

Kwanana uku awurinshi aranar da zan dawo yabani wata kyakkyawar mota banda tsabar kudi dubu dari biyar,
.
Tunda mami taga nafara arziki shikenan tahau murna tana cewa burinta yakusa cika sukuma mutane sai cewa suke Allah ne yayi min nasibi dare daya ya azurtani, wallahi nanah ko sau daya mami bata taba tambayata a ina nake samun kudiba ita kawai tunda nace mata wani uban gida nasamu yake buda min shikenan tahau murna tana saka min albarka,

Kuma har yau dinnan da nake miki magana mami bata taba tuhumata akan arzikin da nake dashiba gashi kuma acikin lokaci kankani na mallaki komai na jin dadin rayuwa kama tun daga gidaje, kamfanoni, motoci da komai da kika sani na jin dadin rayuwa domin mutanen dake cikin harkar nan masu fada ajine daga senators sai Reps sai Governors….”

Zamowa daga kan bedside drewar din Hafsat tayi tazauna dirshan akasa cikeda tashin hankali, matsawa kusa da ita yayi yasake dora kanshi akan cinyarta yafashe da wani kuka mai ban tausayi,

“Yaya yusleem daina kuka dan Allah, shi Allah mai yawan gafara ne domin yace yana gafarta zunabai gaba daya komai yawansu mutukar muka tuba kuma muka nemi gafararsa, nidai dan Allah so nake kabar aikata wannan dabi’ar domin bata dace dakai ba, kazanta ce, masu aikatata sun tabe duniya da lahira..”

Hannunta yakama ya matse cikin nashi,
.
“Nanah na daina, amma nasan rayuwata tana cikin hatsari domin wallahi sawa zasuyi akashe ni saboda zasuga kamar zan tona musu asiri ne kuma mafi yawansu manyan mutane ne..”

“Yaya yusleem insha Allah babu abinda zai sameka, insha Allah Allah zai kareka…”

Baiyi magana ba illah kukan da yaci gaba dayi mai tsuma zuciya,

Rarrashin duniya Hafsat tayi masa amma baiyi shiruba, ranar haka suka kwana azaune ido biyu har gari yawaye,

Alwala yayi yafita masallaci idanuwansa akunbure sunyi jajur, ita kanta Hafsat din kukan da tayi ba kadan bane,

Acikin sujjadarta kuwa tajima tana yimasa addu’a, tana zaune akan abin sallar tayi tagumi ta jingina da jikin gado sai gashi yashigo akusa da ita ya zauna yajingina da jikinta, hannu tasa ta rungumeshi,

“Yaya yusleem kadaina kukan nan haka dan Allah..”

“Hafsat wallahi natsani kaina, natsani rayuwata, ni yanzu mutuwa kawai nake s….”

Saurin rufe masa baki tayi,

“Yaya yusleem babu kyau fatan mutuwa, karkayi sabo dan Allah kayi shiru..”
.
“Nanah mami ta illata rayuwata, bata min adalciba..”

Sake rufe masa baki tayi, “kadaina fadin haka, mami mahaifiyarka ce bata cancanci haka daga gareka ba domin tafi kowa sonka..”  Shiru yayi baice komai ba saboda jin abinda tace.

Haka suka ci gaba da zama har rana tafito karfe 12 narana yayi, tashi Hafsat tayi taje kitchen ta dafa musu indomie da kwai ta hado tea takawo musu, ko kallon abincin yusleem baiyi ba bare tasa ran zaici, ta rarrasheshi iya rarrashi amma yace bazai iya ciba,

Haka suka wuni da yunwa har dare,

Yau ma bacci baiga idonsu ba sai jikin asubah ya daukesu yana kwance akan cinyarta.

Karfe 8 nasafe suka farka, salla sukayi tace bari takawo masa tea, girgiza mata kai yayi alamun bazai sha ba, dawowa tayi tazauna akusa dashi takamo hannunshi,
.
“Yaya yusleem haka zaka zauna jiya bakaci komai ba yauma kaki ci?”

“Nanah bazan iya cin komai ba musamman ma wanda aka siya da wannan kazamin kudin …”

“To idan nabada aka siyo maka wani abun nadafa maka zaka ci?”

Girgiza kai yayi alamun a’a, tashi tayi taje cikin drewar din gadonta ta dauko dari biyar,

“Wallahi wannan ba irin kudin ka bane, ranar da naje gidane Abba yabani 5000,gashi zan bawa mai gadi ya siyo maka indomie indafa maka”

Baiyi magana ba tasaka kai tafita, tunda tafita bata dawo cikin dakinba har sai da tadafo indomie din,

Agabanshi tazauna ta diba takai saitin bakinshi, kawar dakai yayi,

“Please yaya yusleem…”

Dakyar yayarda yayi 5 spoon daga haka bai karaba, ita kanta cokali biyu kacal tayi tabari tature gefe.

Har kwana uku suna cikin wannan hali yusleem dai dai da ruwan gidan yaki sha bare yaci abinci, aranar tun sassafe yafice daga gidan batareda yasanar da itaba, bashi yadawo ba sai la’asar,

Tana falo tayi tagumi yazo ya sameta, hannunta yakama ya matse cikin nasa,kallonshi tayi cikin tausayawa domin har ya dan fada yayi wani iri kamar bashiba,
.
“Yaya yusleem ina katafi haka tun safe,lafiya kuwa?”

“Zan fada miki, yanzu kitashi kije ki debo kayanki gidan nan zamu bari, yau bazamu kwana agidan nan ba..”

“Lafiya?” Ta tambayeshi tana zaro ido,

“Kidai je ki kwaso kayanki kifito mu tafi, nasayar da gidanne bama shi kadaiba komai nawa da kika sani nasayar..”

“To me zakai da kudin?”

“Nasaka acikin asusun marayu, yanzu banida ko kwandala nanah, banida komai yanzu, su kansu kayan sawata wallahi dan babu yanda zanyi dasu ne amma da bazan kara sakasu ba..”

Hawayen dake makale acikin idanuwanta sune suka silalo tajuya ta nufi cikin bedroom dinta,

Lokacin da tafito rikeda babbar trolley dinta shima har ya fito yana kulle part dinshi, jakarta yakarba yahada da tashi yaja suka fita,

A bakin gate taga wasu mutane guda  3 suna jiransu, kulle gidan yayi da wani babban padlock yamika musu key din yarike daya awurinshi domin yafada musu da sauran kayansu aciki,

“Ina mai gadin kuma?” Ta tambayeshi,

“Na sallameshi tun safe”

“To yanzu ina zamuje?”

“Allah ne yasani domin nikaina ban saniba gashi nafada miki babu ko naira daya atare dani domin hatta account dina na rufeshi…”

Trolley dinsu yasoma ja yayi gaba nan tabi bayanshi suka fara tafiya batare da sunsan inda zasuje ba…..

*
       ***Bin bayanshi tayi suka fara tafiya batare da sun san inda zasuje ba har saida suka danyi nisa da gidansu sannan Hafsat ta dakatar dashi,

“Yaya yusleem yanzu ina wai muka nufane takamaimai?”

“Ai nafada miki ni kaina banida masaniyar inda zamuje…”

“To tsaya inkira ummi inada kudi awurinta sai inje in karbo kaga ko babu komai zai dan rage mana wani abun..”

Shiru yayi baice komai ba illah tsayawa da yayi akarkashin wata bishiyar mangwaro,

Wayarta ta zaro tasoma kiran Ummi, saida suka gaisa sannan tayi mata maganar kudin kayan sanyin da ta saka kashi biyu,

“Hafsat kin san ban fiya son in ajiye kudi agida ba amma anyi sa’a ga dubu talatin zan bawa Salisu yakawo miki yanzu…”

“To shikenan Ummi dan Allah kice yayi sauri saboda amfani zanyi da kudin yanzun nan…”
.
Sallama sukayi ta katse wayar takarasa kusa da yusleem ta tsugunna,

“Yi dan hakuri kadan yanzu ummi zata aiko min da kudin”

Daga mata kai yayi baiyi maganaba da alama miskilancin ne ya motsa kuma hakan bazai rasa nasaba da irin damuwar da yake ciki ba,

Bayan kamar mintuna 15 suna zaune sai ga motar gidansu ummin tana dosowa da sauri hafsa ta tashi ta tsayar da salisu driver ta karbi kudin tana kallonsa sam bata son ya fahimci wani abu bare idan yakoma yafada,

“Kaga nima baki nayine yan uwan mijina ne suka zo daga can wani kauye kuma baya nan shine zan basu kudin mota”

“Allah sarki to Allah ya kiyaye hanya”

“Amin”

Saida taga bacewar motarsa sannan takoma wurin yusleem wanda ke zaune shiru yana tunani,

“Yaya yusleem tashi mutafi to..”

Mikewa yayi yaja akwatunansu suka fara tafiya,

Adaidaita sahu suka samu suka tare bayan sun fara tafiya mai adaidaitan ya tambayesu wurinda zai kaisu,

“Bawan Allah idan akwai unguwar da kasani wacce za a iya samun dakin haya ayanzu kawai kaimu can…” Inji Hafsat,
.
“Ahh za asamu mana hajiya, unguwar da nake akwai gidajen haya sosai bari muje…”

Yar tafiya mai tsawo kadan sukayi sai gasu cikin wata unguwa, kallon yanayin unguwar dukkansu suke yi domin da alama ta talakawa ce saboda ko titi babu gashi gidajen awani cunkushe suke babu tsari,

“Yawwa ga gidan alhaji Bashari yanada gidajen haya har guda uku bari inyi muku sallama dashi”

“Yawwa mun gode”

Kafin dan adaidaita sahun ma yafita saiga mai gidan yafito,

“Yawwa ga alhajin ma”

Fita Hafsat tayi mai adaidaita sahun yana biyeda ita,

“Alhaji barka da yamma, dama wadannan ne suke neman dakin haya..”

Dan jimm alhajin yayi sannan yace,

“Ai inajin dukka gidajen nan akwai mutane aciki..”

“To alhaji yanzu ya za’ayi?” Inji Hafsat,
.
“Yawwa natuna jiya wani yafita sakamakon transfer da akayi masa ta aiki amma gidan ba anan layin bane a layin gabane”

“Alhaji nawane kudin dakin”

“Dubu ishirin ne”

“To shikenan yanzu zamu baka dubu goma, nanda kwana biyu sai mu cika maka”

“To babu laifi, babu laifi Kawo”

Kirgar kudin Hafsat tayi tabashi suka koma cikin adaidaita sahu suka nufi layin da gidan yake,

Fitowa sukayi suka shiga cikin gidan nan suka ganshi babba domin dakuna sun kai goma sha biyar can gefe kuma rijiya ce gefenta wasu mata ne kimanin su 8 zaune suna hira masu kitso kuma sunayi,

Dakin da zasu zauna aciki gashi nan abude duk sumintin ya dan farfashe,kayansu suka shigar ciki takalli dan adaidaita sahun,

“Bawon Allah a ina zamu samu motar da zata debo mana yan kayayyakinmu?”

“Hajiya nima ai ina yin dakon kayan, bari inje indauko akori kura..”
.
Fita yayi ita kuma ta tsaya tana karewa dakin kallo wanda yake da dan girma amma ba canba, gabanta ne yafadi sakamakon tunawa da tayi da matan da ta hango atsakar gidan ita fatanta daya Allah yasa ba bathroom guda daya bane agidan,

Ji tayi andafa ta, ahankali ta juya, yusleem tagani,

“Tunanin me kikeyi?”

“Yaya yusleem fata nake Allah yasa bathroom din gidan nan ba guda daya bane”

“Idan guda dayane mezai faru?”

“Takura zamuyi, kuma bana son idan kafito daga wanka mutane suyita kare maka kallo..”

Kafadarta ya dafa yayi mata nuni da hannunsa bayan yadan saki murmushi,

“Kinga bathroom nan acikin dakin nan..”
.
Sai lokacin ma ita takula da kofar bathroom din amma sam da hankalinta bai kai nanba, zuwa tayi ta bude nan taga bathroom din dan kuf dashi,

“Wannan dinma duk da haka babu laifi..” Tafada acikin zuciyarta.

Babu jimawa dan adaidaita sahun nan yadawo da mota ta diban kaya fita tayi suka koma gidansu ta bude tashiga yan kayayyakin da tasan zasu bukata ta debo musu irinsu kwanukan cin abinci tukunyar girki, bargo, bedsheet,labule sai katifarta sannan bata bar keken sakarta ba shima ta hado dashi,

Wurin biyar da rabi suka koma gidan hayar nan aka sassauke kayan ta biya kudin diban kaya Dubu biyar, har ciki mai adaidaita sahun nan ya taimaka musu suka shigar da kayansu,

Share dakin tayi ta karkade ko ina suka shigar da katifar ta shimfidata wacce ta cinye fin rabin filin dakin gashi babu ko leda atsakar dakin sai simintin dake shimfide kawai,
.
Yar madaidaiciyar dardumar data dauko musu ta shimfida agaban katifar sannan ta shimfida bedsheet akan katifar tajera musu filillika guda biyu,

Yusleem ta kalla wanda ke kokarin kafa musu labule,

“Yaya yusleem bari indebo ruwa inwanke mana toilet din..”

“Kibari ingama sai na debo”

“A’a kayi wannan din idan kagama sai ka yi alwala kaga fa ko salla bamuyi ba”

Bucket ta dauka ta fita taje bakin rijiya inda matan nan ke zaune,

“Sannunku..”
.
“Yawwa sannu da zuwa..” Matan suka fada har suna hada baki,

Ruwa taja ta cika bucket din ta dauka ta koma daki, wanke toilet din tayi tasake komawa ta debo wani ruwan ta cika daya bucket din sannan ta ciko wannan din ta ajiye,

Alwala sukayi sukai salla,

Kan katifa taje ta kwanta saboda gajiyar da take tareda ita, shikuma yana kan carpet azaune yana tunanin rayuwa domin ko a mafarki bai taba tunanin wai zai yi irin wannan rayuwar ba amma dayake Allah shine mai cancanja al’amura sai gashi rayuwa ta canja ya tsinci kanshi acikin wannan halin,

“Yaya yusleem baka jin yunwa ne?”

Juyawa yayi ya kalleta,

“Inaji amma sam bana sha’awar cin komai”
.
“Duk da haka daurewa zakayi kaci, bari ayi sallar magrib sai mufita mu samo abinda zamu ci”

Har bayan sallar magrib Hafsat takasa tashi saboda gajiyar da tayi, saida akayi sallar isha sannan ta iya mikewa,dakin duhu didim yake saboda babu wuta ga uban sauro banda zafi da yake addabarsu,

“Gaskiya yaya yusleem muyi sallar nan muje mu samo abinda zamu ci daga nan sai mu taho da maganin sauro..”

Suna idar da sallar suka fita, gasasshiyar kaza Hafsat tace asiya nan yusleem ya kalleta,

“Yanzu fa ba lokacin cin abin dadi bane, kibar kazar nan muje shagon can mu sai gari da sugar..”

“A’a yaya yusleem, gaskiya gari bazai shiga ba wallahi, mudai siyi kazar..”

Son ranta yabi suka siyo gasasshiyar kazar daga nan suka karasa shago suka siyi maganin sauro da candle guda biyu da ashana sai sabulun wanka give sinki daya da soson wanka da brush da maclean sai man shafawa Vaseline,

Gida suka koma ya kunna candle din ya ajiye sannan ya kunna musu maganin sauro,

Kasancewar yunwar tasu taci ta cinye yasa baifi rabi suka ci kazar ba, Hafsat ce tafara tashi ta bude trolley dinta ta dauki zani tadauki soso da sabulun wanka da brushes dinsu da maclean ta shiga bathroom, wanka tayi tafito ta dauki kayan baccinta takoma cikin bathroom din,Riga da wando ne red colour masu santsi, rigar tana da dan guntun hannu yayinda wandon yake dogo,doro hijabinta tayi akan kayan tafito tahau kan katifa ta kwanta,

“Bari nima inje inyi wankan tunda kin fito” yusleem yafada tareda tashi tsaye ya shiga cikin toilet din, yajima aciki kamar wanda zai sake fata dama Hafsat tasan dadewarshi a wanka shiyasa tafara shiga,

Saida yayi kusan minti 30 sannan yafito yana rikeda rigarshi yana tsane ruwan kanshi,
.
Gaban kayansu ya karasa ya bude trolley dinshi yaciro yar t shirt da boxer,

Ta dan hasken candle din da suka kunna Hafsat take kallonshi lokacin da yake kokarin sauya kayan jikinshi,

Rufe idanuwanta tayi saboda wannan shine karo nafarko da zata kwana dashi akan katifa guda daya,

Juyowa yayi ya kalleta bayan yaje ya dauke kakkauran labulen kofar dakin yabar mai shara sharan,

“Ko ke bakya jin zafin ne?”

“Inaji mana yaya yusleem, wallahi akwai zafi kila hadari ne agarin”

Candle ya dauka yakarasa gefen katifar yazauna,

“Bama kila bane ga gari nan anata yin walkiya, kalli waje ki gani”

Sai lokacin talura da ashe asaitin kofar daki ta kwanta nan ta mirgina takoma barin da yake,

“Anan zan kwanta, kai kakoma can barin”

Tashi yayi yakoma bayan yakashe candle din,duhu didim dakin yayi,

“Shine ni kika turo ni kofar daki ko inyaso abin tsoron idan yazo ni ya kamani”

Murmushi tayi ta zare hijabin dake jikinta,tana jinshi ya kwanta agefenta bayan ya matso da filonshi jikin nata filon sabanin da dayake ajiye acan karshen katifa…..

*

        ***Dukkaninsu shiru sukayi kowa da abinda yake tunani acikin zuciyarsa,

“Nanah…” Taji yusleem yakirata, dan juyawa tayi acikin duhun ta kalleshi,

“Yaya yusleem menene?”

“Babu komai dama nayi zaton ko kinyi bacci ne”

Juyawa tayi ta dan gyara kwanciyarta,

“A’a banyi ba”

“To kiyi..”

Lumshe idanuwanta tayi,

“Saida safe”

“Allah ya tashemu lafiya”
.
Shiru suka sakeyi wanda har bacci ya dauke Hafsat amma shi yusleem sam yakasa baccin inbanda sake sake babu abinda zuciyarshi keyi masa, yasaka wancen ya kunce yasaka wancan har garin yayi tsit dare ya raba bai iya yin bacci ba,

Hafsat kuwa cikin barcin da takeyi tafara wani mafarki marar dadi domin wasu manyan mutane tagani suna bin yusleem aguje kowannensu rikeda katuwar wuka mai kaifi sai kyalli take zuwa can yusleem din ya fadi daya daga cikinsu ne ya cimmasa ya daga wukar zai daba masa tayi firgigit ta farka,

Cikin duhun tafara lalubenshi akan katifar amma bata jishiba hakan yasata rudewa,

“Yaya yusleem,yaya yusleem…!”

Shiru tayi sakamakon jin ya amsa daga bakin kofa inda yaje domin saukar da labulen dakin domin yanzu garin yadauki sanyi duk da ba ayi ruwa ba amma wata iska mai sanyi ake kadawa,

Karasowa yayi kan katifar, tun kafin yakarasa hawowa taje ta rirrikeshi,

“Yaya yusleem babu abinda yasameka…?”

Riketa yayi ya kwantar da ita awurinda take kwance dafarko,

“Menene yafaru nanah? Lafiya lau nake.. Mafarki kikayi?”

Hannuwanshi ta makalkale cikin nata,

“Yaya yusleem wani mummunan mafarki nayi wallahi…”
.
“To ai mafarki ba gaskiya bane nanah, ki koma kiyi baccinki kinji…”

D’aga mishi kai tayi kamar yana ganinta tareda tallafe kumatunta da hannunshi guda daya,

Duk da taga azahiri babu abinda ya sameshi amma sai takasa komawa baccin, shi kanshi yusleem din shima yakasa yin barcin,

“Yaya yusleem..”

“Na’am…”

“Tunda mun kasa yin bacci katashi muyi alwala muyi sallar nafila watakila sai Allah ya amsa ya rangwanta mana masifun da suke tunkaro mu…”

“To nanah, bari natashi naje..”

Saurin rikeshi tayi, “yaya yusleem mu tafi tare”

Taren suka shiga toilet din kasancewar duhu ne alwala sukayi suka fito suka fara sallolin nafila wanda har saida suka yi sallar asuba sannan suka kwanta bacci, bacci sukayi sosai sai 12 saura sannan Hafsat ta farka, yusleem takalla wanda ta rirrikeshi yana kwance agefenta,

Tashi tayi tashiga wanka har tafito ta shirya bai tashiba tunanin abinda zasu karya dashi tafara, mikewa tayi tashiga bathroom ta dauko bucket domin debowa yusleem ruwan wanka,

“Nanah ina zaki..?” Taji yace da ita idanuwanshi suna rufe,

“Ruwan wanka zan debo maka…”

Tashi zaune yayi,

“Dauko wani bucket din inbiki mu debo tare”

“Kabarshi zan debo”

Tashi yayi dakanshi yaje yadauko bucket din yabita domin ita tuni tajima da fita, kamar jiya yauma matan gidan suna zazzaune akofar dakin daya daga cikinsu, ganin Hafsat tafito duk sai suka maida kallonsu gareta, gaishesu tayi kamar jiya sannan takarasa bakin rijiyar,

Gugar yusleem ya karba daga hannunta,
.
“Kawo inzuba miki..” Yayi maganar ahankali duk da dama maganarshi bawai cika karfi tayiba,sakar mishi tayi yafara janyo ruwan yana zuba mata acikin bucket din,

Ganin hankalin matan ya komo garesu yasa duk taji ta tsargu musamman ma dataga kamar sunfi karkata ga kallon yusleem, saida ta jirashi ya cika nasa bucket din sannan suka dauka suka tafi,

Acikin bathroom din tabarshi bayan ta ajiye ruwan tafito,

Keken sakarta ta kinkimo ta zauna agefen katifa tasoma saitashi domin so take tafara yin sakar kayan sanyi, jin tafiyar yusleem yasata juyawa ganinshi tayi babu riga sai iya boxer dan haka tayi saurin maida kanta ta sunkuyar,

Kanta yana sunkuye har yagama shiryawa yasaka kayanshi yadawo kan katifar ya Zauna,

“Yaya yusleem ga guntun naman jiya can bari indauko mana..”

Kafin yabata amsa har tatashi taje ta dauko,

“Kaga cewa nayi ko inje insaida kujeru na sai insiyo zaren bulu da sauran kayan da zamu bukata, kaga dole sai mun siyo risho da kayan abinci..”
.
Shiru taji yayi baice komai ba, dagowa tayi ta kalleshi,

“Yaya yusleem bakace komai ba”

“Nanah gaskiya akaina bazaki rabu da kayanki ba, karki saida ko cokali naki”

Murmushi tayi,

“To ai ba saboda kai zan siyarba, saboda nida kai zan siyar”

“To ban goyi baya ba”

“Shikenan tunda baka amince ba”

“Ba amincewa ne banyiba kawai dai idan narabaki da kayanki ne banyi miki adalci ba”

“To magana tawuce,yanzu kasan me? Kafadawa mami cewar zakayi tafiya ta gaggawa zuwa wani state din mai nisa saboda kasan zata nemeka idan kuma har ta nemeka bata sameka ba hankalinta tashi zaiyi, idan tayi maka maganata kace tare zamu tafi kaga hankalinta zaifi kwanciya sannan tunaninta bazai taba Kawo mata cewar da akwai matsala ba..”

“To amma iyayenki fa? Sukuma me zan fada musu”

“Sudinma hakan zan cemusu munyi tafiya zuwa wani gari mai nisa, koma kawai muce Niger muka tafi..”

Hadaddun wayoyinshi dake ajiye akasan trolley dinshi hadeda laptop dinshi yadauko ya kunna,

Number mami yayi dialing babu bata lokaci ta dauka, dakyar ya saita nutsuwarshi yayi mata bayani bayan sun gaisa, fatan alkhairi tayi musu daga nan sukayi sallama,

“Nima bari inkira Ummi infada mata kaga shikenan daga nan mun gama da matsalar gida sai mu fuskanci wata rayuwar kuma”
.
Tata wayar itama ta dauka ta kira Ummi ta sanar mata daga nan takashe wayar amma shi yusleem tashi wayar abude yabarta saboda yasan abokan harkarshi zasu nemeshi.

Misalin karfe 2 narana ta dauki dan madaidaicin food flask, fita tayi domin yusleem bacci yakeyi, tsakar gida taje inda matan nan ke zazzaune ta tambayesu inda ake sayar da abinci,

“Me kike so? Kawo amir yasiyo miki” inji wata mata wacce ahaife da alama bazata girmeta ba,

“Yawwa nagode dan wanke nakeso”

Naira dari tabayar yaron yatafi siyo mata, daki takoma tazauna tana lissafi domin kudin da yayi saura yanzu baifi dubu goma sha daya da yan canji ba gashi kuma bukatunsu nada yawa domin basuda kayan abinci kuma zasu cikawa mai gidan haya kudinsa gashi tana son ta siyo zaren saka,
.
Yanke hukuncin zata sayar da kujerunta kawai tayi batareda yusleem yasaniba, jin muryar amir yana sallama yasata tashi taje ta karbo abincin ta danka mishi naira goma,

Bata tashi yusleem ba saboda tasan daren jiya bai samu bacci ba har saida ya tashi dan kanshi lokacin karfe 3:32 na yamma,

Dan waken tasa musu suka ci bayan sun gama tace mishi zata fita kasuwa domin siyo zaren kulu da dan abubuwan da ba arasa ba, acikin dakin tabarshi tafita,

Direct wurin wasu kafintoci tawuce tayi musu tallen kujerunta sukace zasu siya amma sai sun gansu nan tace to zuwa gobe zatazo suje sai sugani,

Daga nan kasuwa tawuce tasiyo zarirrukan kulu kala kala sannan ta siyo musu dan karamin risho ta hado musu kayan tea da babban bread guda daya,

Ana kokarin yin sallar magrib tadawo gida, akan katifa tasamu yusleem yana zaune,

“Sannu nanah..”

“Yawwa yaya yusleem sannu nabarka kai kadai ko”

Murmushi yayi, “ai kece da sannu”

“Kaga abubuwan da nasiyo, ga risho amma kalanzir dinne na dari biyu kawai nasiyo nasan zai ishemu mu rinka dan dafa ruwan zafi”

Tausayinta yaji yakamashi saboda irin rayuwar da suka samu kansu aciki yanzu wacce yasan shine silar jefata aciki,

“Allah yayi miki sakayya da gidan aljanna..” Shine abinda yafada kawai ya mike yashiga toilet domin yin alwala,
.
Tea tadafa musu da daddaren suka sha suka kwanta, wayarshi ce ta hau vibrating nan yadaga,

“Yusleem kayi gaggawar kashe wayarka domin su oga nemanka suke ido rufe, idan baka kashe wayarka ba zasuyi tracing wurinda kake…” Wannan shine abinda kunnuwan yusleem suka ji wanda bai gane ko muryar waye ba kitt yaji wayar takatse nan yakashe wayar gaba daya,

Sam baya son Hafsat taji bare hankalinta yatashi nan yaki fada mata gaskiyar abinda yake faruwa domin tun lokacin data fita suke fafatawa shida abokan harkar tasa domin sun ce mutukar yace yabar wannan harkar to sai dai wani bashi ba saboda sun san tona musu asiri zaiyi,

Jin baice komai ba yasa Hafsat bata Kawo komai acikin ranta ba daga karshema tashi tayi ta kunna candle tahau keken sakarta tafara saka kayan sanyi na yara, sai wurin  12 sannan ta hakura ta kwanta.

Washe gari dakyar da dabara yusleem yabarta tafita, wurin masu siyan kayan nan da sukayi alkawarin siyan kujerunta ta nufa daga can suka wuce gidan yusleem nada tabude musu sukaje suka gani, ganin kyawun kayan da irin tsaruwar gidan sai masu siyan kayan suka nemi fasawa domin gani suke kamar karya take banata bane ko kuma ba mallakinta bane dakyar tashawo kansu akayi cikini dubu 50 suka siya duk da kayan sun wuce haka,

Fita sukayi da kujerun tamayar gidan ta rufe ta nufi kasuwa da kudin, komai da tasan zasu bukata na kayan abinci saida ta siya musu, data gama siyayyar kuwa adaidaita sahu ta nema ta zuba kayan yakaita har kofar gida.

Yusleem na kwance agefen katifa bayan ya kammala dafa musu ruwan zafi wanda zasu sha tea sai gata tashigo niki niki da kaya, manyan idanuwanshi yazuba mata,

“Daga ina haka?”

“Ina zuwa yaya yusleem ai zan fada maka”

Tashi yayi ya taimaka mata suka karasa shigo da kayayyakin,

Kudin hannunta ta ajiye ta zare hijabin jikinta ta zauna,

“Yaya yusleem nagaji sosai gashi ina jin yunwa”

“Bari inhada miki tea..”

Kafada ta makale,

“Gaskiya ni bazan sha tea da wannan uban zafinba, tunda ga kayan abinci sai ka dafa min abinci inci”

“To ai baki fada min a inda kika samo wadannan kayan abincin ba..”

“Zan fada maka kafara bani abinci inci tukunna mana”

“Nifa ban iya girki ba sai dai kiyi guiding dina”

“To fara kunna risho din ka mayar da ruwan zafin can ka dora..”

Kamar yadda tace haka yayi, yanayi tana kwatanta mishi har yadafa musu farar taliya yasoya mai,
.
Acikin filet ya zuba musu yakai gabanta inda take kwance, hannunshi ya mika mata amma sai tayi kamar bata ganiba ta tashi zaune cikeda kunya,

Saida suka gama cin abincin sannan ta fada mishi duk yanda akayi,

“Yanzu ga 10 thousands din wannan alhajin cikon kudin hayarshi idan yazo sai abashi, wannan kuma 9 thousands din sai mu ajiye..”

Rasa abinda zaice yayi yatsaya kawai yana kallonta saboda yasan acikin mata dari dakyar za asamu irinta guda goma, Hafsat tayi masa halacci acikin rayuwarsa, ta rufa masa asiri, tayi sanadiyyar fitarshi daga cikin halaka, gashi tana zaune dashi a lokacin da bashida madafa har tana salwantar da abubuwan data mallaka saboda shi,

“Nanah banida bakin da zan gode miki illah…”

Tashi tayi tabar dakin ta wuce toilet saboda bata son yayi mata godiyar abinda tayi,

Cikin dare ta tasheshi tana makale da cikinta saboda wani irin ciwo mararta keyi mata, riketa yayi acikin duhun da suke yana tambayarta menene,

“Yaya yusleem cikina ne yake ciwo”

“Ciki kuma? Sannu to yi hakuri”

“Bani ruwa insha..”

Ruwa ya Kawo mata takarba tasha takwanta, candle ya kunna yajata jikinshi yadora kanta akirjinshi ya rungumeta yasoma rarrashinta hannunshi yakai kan cikin nata nan tayi saurin ture hannun,

Kwanciya luff tayi ajikinshi sakamakon duk gabobinta ciwo suke yimata, tambayar duniya yayi mata akan tafada mishi abinda yasa mata ciwon cikin amma tayi shiru saboda kunya takeji tace mishi period pain ne,

Ajikinshi ta kwana har asuba tayi sai lokacin tasamu saukin ciwon da marar tata keyi bacci yadan dauketa kwantar da ita yayi ya nufi toilet,

Sai wurin karfe 6 sannan tatashi daga baccin nan tarasa yadda zatayi tana son tafada mishi kuma tana kunya, komawa tayi ta kwanta ta kalleshi,

“Yaya yusleem kira min amir dan gidan maman amir..”

“Meya faru?”

“Aikenshi zanyi..”

“Toh bari naje”

Tashi yayi yafita ita kuma ta rakashi da ido…

*.
        ****Bai wani jima da fitaba sai gashi yadawo, kusa da ita yakarasa ya tsugunna agabanta,

“Su maman amir din basu bude kofar su ba inaji basu tashiba..”

Gyada mishi kai tayi taja bargo zata lulluba, rike bargon yayi,

“Kitashi kiyi salla mana kafin kisake kwanciya”

Shiru tayi masa tasake yunkurin lulluba, kara maimaita maganarshi tafarko yayi,

“Ba yanzu ba..”

Ganin ta dage taki tashi yasashi rabuwa da ita tasake lulluba takoma barci, gefenta yaje ya kwanta,

K’arfe 8 tafarka ta kalli yusleem wanda ke gefenta akwance,
“Yaya yusleem dubo min ko su Maman amir din sun tashi..”

Tashi yayi yafita jim kadan sai gasu sun dawo tareda amir din,

“Yaya akwai biro awurinka?”

“A’a babu”

“Amir jeka wurin ummanka kace tabani aron biro da yar paper kaji”

Tafada tana ciccije lebenta, fitar amir tasa yusleem komawa wurinta,

“Har yanzu ciwon ne?”

Daga mishi kai tayi,

“To ko asibiti zamuje?”

“A’a”
.
Shigowar amir yasa sukayi shiru dukkaninsu, karbar takarda da biron tayi tana daga kwance ta rubuta mishi abinda zai siyo mata ta kalli yusleem,

“Yaya yusleem bashi dari biyu acikin kudin nan”

Tashi yusleem yayi yadauko kudin yabashi, sake gyara kwanciyarta tayi ta tukunkuna har amir yadawo kasancewar yusleem yana tsaye bakin kofa yasa amir bashi ledar pad din,karba yusleem yayi ya leka cikin ledar, sai yanzu ya fahimci abinda yake damunta,

Tana kokarin tashi domin yin wanka ya dakatar da ita,

“Tsaya indafa miki ruwan zafi sai kiyi wankan dashi zaki fi jin dadin jikinki”

Komawa tayi tasake kwantawa shikuma ya dora mata ruwan zafin bayan ya kunna risho,

Bathroom yashiga ya dauko bucket yazo ya juye mata ruwan aciki yakai mata cikin toilet tareda sirka mata shi,

“Ga ruwan wankan can nakai miki, tashi kije kiyi”
.
Dakyar ta tashi tajuya ta dan kalleshi ganin ba ita yake kalloba hankalinsa yana kan ruwan da zai sake maidawa ya tafasa yasata saurin tashi bayan taja zanin wankanta tashige cikin bathroom.

  Bata dade sosai ba tafito lokacin har yusleem ya kammala hada musu abinda zasu karya dashi, kallonshi take kasa kasa saboda duk yau atakure take,shi kansa ya fahimci haka shiyasa ma yajuya mata baya bayan ya kwanta bisa katifa,

Ganin baya kallonta yasata dan sakewa tashirya tasaka wata blue din atamfa dinkin riga da skirt wanda dayane daga cikin irin dunkunan da mami tayiyyi mata,

Zama tayi abakin katifa wanda yayi sanadiyyar juyowar yusleem,

“Kin gama?”

“Uhm” tabashi amsa,

Tashi yayi ya debo mata tafasasshen ruwan zafi acikin cup,

“Kisha wannan ruwan zafin zai dan rage miki radadin ciwon da marar taki keyi”

“Ni ba ciwon Mara nakeba ciwon cikine”
.
Murmushi yayi ya mika mata cup din,

“Ashe dai ke dinma kin iya karya ban saniba, meye hadin period da ciwon ciki? Ai nazaci mahaifa a mara take ba acikin cikiba ko ke taki acikin ciki take?”

Karbar cup din tayi tasoma kurbar ruwan zafin batare da tayi magana ba har saida ta shanye,

“To ga abinci kuma taliya”

Girgiza masa kai tayi ta kwanta babu jimawa sai bacci, rasa abinda zaiyi yayi saboda dama idan tana ido biyu ne suke yin yar hira, shi dinma kwanciyar yayi tun yana yan tunane tunane har bacci ya daukeshi,

Hafsat ce tafara farkawa yanzu taji dadin jikin nata sannan kuma ciwon ma yaragu sosai sai kadan kadan, ganin yusleem din bacci yake yasata zuba abincin ita kadai ta danci tana gamawa yatashi, fita tayi tace mishi zataje wurin maman amir,

Dayake mata babu wuyar sabo tunda taje suke hira da maman amir din kasancewar itama mijinta baya nan dama kuma police ne,
.
Yau duk taki sakewa ta zauna wuri daya da yusleem saboda kawai yagane abinda ke damunta, da tashiga dakin zata fice takoma wurin maman amir shi kanshi yusleem din ya lura da ita,

Tun azahar da tashiga wurin maman amir sai yamma lis tadawo wannan dinma dan wanka zatayi ne, yana kwance ta shigo taki kallon inda yake tadauki abinda zata dauka tashiga wanka bakar ledar da tasaka pad din data cire da rana taga ya dauke yadora akan window din bathroom din, acikin toilet din tashirya dan haka koda tafito iya kaya kawai tasa tashafa dan mai tagama tafita.

Wasa wasa har karfe 8 nadare tana dakin maman amir saboda ita so take sai yusleem yayi bacci sannan zata koma dakin, shi kuma yau duk kadaici yakeji saboda bata cikin dakin ganin har 8 ta dan gota yasashi fita yanufi dakin maman amir daidai lokacin da aka dan fara yayyafi yif yif alamun ruwa yana daf da tsinkewa,

Abakin kofar dakin yatsaya,ahankali yayi magana,

“Nanah..!”

“Na’am”

Hafsat ta amsa tareda tashi, kallonta maman amir tayi,

“A’a keda wa? Banji magana ba sai ji nayi kawai kin amsa”

“Yaya yusleem ne yake kirana”

“Anya kuwa? Kodai kunnenki ne”

“Wallahi shine, bari inje”
.
Duk da haka maman amir bata yarda ba saida ta leka nan taga ashe shidinne kuwa yana tsaye akofar dakin,

“Lahh ashe dagaske shine, kinga kuwa ni banji maganarshi ba, mijin naki ne ma ni sai inga kamar baya magana”

“Dama ai nafada miki shine, bari inje, saida safe”

Fita tayi lokacin har ruwan yadan soma karfi, wucewa yayi tabishi abaya, suna shiga daki yajuya ya kalleta,

“Da ban kiraki ba sai yaushe zaki dawo?”

“Sai anjima”

“To ke haka akeyi mata da mijinta kije ki zauna musu adaki tun rana”

“Mijin nata fa baya nan”

“To amma ai ke naki mijin yana nan ko? Shine zaki kama hanya kitafi kibarshi”
.
Shiru tayi bata amsaba, maimakon ma tazauna sai kawai ta dauki kayan baccinta tanufi toilet, shi yau yarasa wacce irin kunya takeji sam taki sakewa dashi shikuma yafi son tasaki jiki dashi sosai tadaina jin kunyarshi,

Yana nan zaune tafito sanye da rigar bacci wacce tadora zani da hijab akai,

“Ga abinci nan ko zaki ci”

Girgiza masa kai tayi, “Allah nakoshi tun abincin da naci da rana”

Maimakon tazo ta kwanta sai yaga tadauki candle ta tafi kan keken sakarta, nan ta farayi babu ji bare gani, yana kwance yana kallonta har 11 nadare kuma har lokacin ba adauke ruwan da ake tsugawa ba,

Lumshe idanuwanshi yayi yabudesu akanta take zuciyarshi tafara kissima mishi siffarta, baka ce yar doguwa sannan ita ba ramammiya bace kuma bata da kiba can, tanada round face mai dauke da madaidaitan idanuwa sai dan dogon hanci wanda yake daf da dan karamin bakinta, tanada gashin gira sosai da gashin ido haka kuma gashin kanta ma yanada dan yalwa,
.
Ido ya tsura mata domin ta dade da cire hijabin dake jikinta dan haka daga ita sai wata rigar bacci cotton mai hannun shimi milk colour mai digon fari da ja da baki da pink da blue duk dai kaloli ne aka diddiga ajiki, sai hula mai santsi kalar ruwan siminta dake kanta saboda duk tunaninta yusleem yayi bacci, sakarta takeyi bil hakki da gaskiya tana son ta kammala rigar da tafara kafin ta kwanta bacci gashi har candle din data kunna yakusa cinyewa shiyasa taketa sauri takarasa kafin ya mutu,

Tashi yusleem yayi sadaf sadaf ya nufi wurinta baki yasa ya hure candle din take ya mutu ita kuma ya daukota cak daga inda take zaune, tsorone ya ziyarceta hankalinta yatashi domin bata taba zaton yusleem bane kokarin kurma masa ihu take yayi saurin rufe mata bakinta da hannunshi ahaka suka karasa kan katifa ya kwantar da ita, laluben hannunshi tafara domin tananne kadai zata gane idan shine cikin sa’a ta lalubo zobenshi na azurfa wanda ke sanye cikin babban dan yatsanshi na tsakiya,

Duk da tagane shine gabanta bai daina faduwa ba sannan kuma jikinta bai daina rawaba domin tayi mutukar tsorata,

Pillow yaja yadora kanta akai,cikin maganarshi mai sanyi ahankali yace,

“Ke yau bazaki yi bacci bane?”
.
Dan matsar da jikinta take kokarin yi amma ya hanata saboda irin yanda ya manne gefen jikinshi da nata domin hatta kanshi yau akan pillown ta yake,

“Yaya yusleem wata riga naso da inkarasa kafin inyi baccin..”

“To kiyi hakuri kibari sai gobe..” Yayi maganar asaitin kunnenta ahankali,

“Amma wallahi kabani tsoro, kaji yanda na tsorata kuwa?”

“Kin zaci wanine yazo saceki?”

“A’a nazaci ko aljanine saboda fa lokaci daya naga candle din ya mutu sannan anyi sama dani..”

Murmushi yayi yaja bargo ya lullubesu,

“Sanyi akeyi ne kuma wallahi inajinsa sosai kekuma kin tafi da dumin kin barni shiyasa na dauko ki”

Shiru tayi saboda kunya bata amsa ba, sarai yagane kunyace ta hanata magana,
.
Jikinta taji ya shige sosai yadora kanshi atsakiyar kirjinta,

“Yaya yusleem….” Takira sunanshi,

“Na’am nanah..”

“Gaskiya to banda juye juye ka ajiye kanka wuri daya dan wallahi kirjina ciwo yake” tayi maganar cikeda shagwaba kamar zatayi kuka,

Murmushi yayi saboda yagane abinda take nufi,

“Nasani ai, bazan fama ki ba, kiyi barcinki”

Shiru tayi takasa magana,shi dinma shirun yayi amma dai aranshi yana jin cewar kullum haka zai rinka yi mata har tasamu tasake dashi yadda ya kamata,

Saida yaji tayi bacci sannan shima yasamu zarafin yi. Dayake kusan kwana akayi ana ruwa sai karfe 6 harda wani abu ya iya tashi,

Yana zaune bayan ya idar da salla Hafsat tatashi, brush tashiga bathroom tayi tafito ta kunna risho ta dora ruwan wanka,

Sam takasa kallon koda gefen da yake zaune,

“Masak’iya babu magana? Ya saka?”

Murmushine ya subuce mata saboda jin abinda yace sai yanzu tagane ashe shidinma ya iya tsokana,

“Ai wallahi jiya ka tsoratani”

Murmushi yayi yakoma ya kwanta,

“Ke dince ai gani nayi kinfi bawa sakarki muhimmanci fiyeda barcinki..”
.
Ruwan wankanta ta juye ta dora wani tashiga wanka.

Duk da dai yanata janta da magana amma bata sake dashi ba sosai saboda yanzu har ma tafi jin kunyarshi fiyeda jiya, tashi tayi da niyyar fita zuwa dakin maman amir,

“Ina zakije?” Taji ya tambayeta,

“Dakin maman amir zanje”

“Shikenan to nima bari intashi inleka kofar gida inzauna tunda kema fita zakiyi”

Murmushi tayi tafita, tashi shidinma yayi yasa takalminsa yafita kofar gida wanda bama wai taba fitowa yayiba tun zuwansu unguwar sai yau,

Kan wani dan dutse yasamu yazauna, yana zama ko minti  5 baiyi ba wasu mutane sukazo a mota kimanin su biyar suka kamashi suka saka a mota suka tafi dashi……

*

         **Hafsat tana dakin maman amir bata san abinda ke faruwa ba domin duk tunaninta yusleem yana daki baima fita ko ina ba,

Tajima adakin maman amir kafin ta mike ta nufi dakinsu,lokacin data shiga taga baya nan duk tunaninta ko yana cikin bathroom amma kuma koda ta dan jira yafito sai taji shiru hakan yasata zuwa ta duba nan taga wayam,

“Hmm lallai yaya yusleem kenan wajen yafita da danshin nan baya tsoron sanyi ko..?” Tayi maganar afili tana kokarin gyara bedsheet din dake shimfide akan katifarsu,

Dakin tagyara ta hau keken sakarta tasoma kokarin karasa sakar da tafara yi adaren jiya tanayi tana rera yar wakarta,
.
“Tunda nai nisa ankirani baza najiba, naki inkosa hidimarka bazan gajiba, bani inlasa Zuma ta sonka bazana ki ba, yau nake taku wata rana baza nayiba….”

Har ta kammala hada sakar nan yusleem bai shigoba, kan katifa tahau ta kwanta domin ta dan huta, tana nan kwance har rana tayi bata farga ba sai jin kiran sallar azahar tayi nanne kuma taji hankalinta ya koma ga yusleem dan haka tatashi ta dauki hijab dinta tafita amma abin mamaki baya nan, bata koma cikin gidan ba ta mike tabi hanyar da zata sadata da bakin titi,har bakin titin taje amma bata ga koda alamarshi ba nan hankalinta yatashi mutuka,
.
Duk wanda tagani sai ta tsayar dashi ta tambayeshi ko yaga yusleem amma duk wanda ta kwatantawa kamanninsa sai yace bai ganshi ba, kasa komawa gida tayi taci gaba da tafiya tana nemanshi amma har yamma tayi bata ganshi ba,

Gidan tasake komawa wai ko bayan fitarta yadawo amma yanda tatafi tabar dakin haka tadawo ta iskeshi, hankalinta atashe tana kokarin sake fitowa daga cikin dakin sai ga maman amir tashigo rikeda wani kwano wanda takawo mata alalan gwangwanin data dafa,

“A’a ko fita zakiyi..?”

“Maman amir yaya yusleem ne ban ganiba tun safe lokacin da nabaro dakinki baya nan..” Tayi maganar hawaye na gangarowa akan kumatunta,

“Kodai wani wurin yatafi?”

“Da wani wurin zaije ai da zai fada min, wallahi ina jin saceshi akayi saboda tun safe nake nemansa ban ganshi ba”

“Sacewa kuma? Sai kace wani karamin yaro”

“Wallahi kila saceshi akayi saboda dama yanada wadanda ke nemanshi, gashi kuma sun samu dama sun daukeshi watikil ma su kasheshi…”

Jin abinda Hafsa tace yasa maman amir zaro ido, ajiye kwanon hannunta tayi ta kalli Hafsa,

“Kinga to zo muje ga Baban amir can yadawo yarakaki division dinsu kikai report..”
.
Bin bayanta Hafsat tayi tana aikin sharar kwalla, maman amir ce ta yiwa mijin nata bayani daga nan yadauki Hafsat din abayan babur dinsa suka tafi office dinsu,

Dukkan wani bayani da ake bukata kuma ya kamata aji Hafsat tafada nan yan sandan sukace tayi hakuri takoma gida zasu yi iya kokarinsu insha Allah,

Tun a police station din take kuka har suka koma gida, gaba daya dakin yayi mata kunci, maman amir ce ke tare da ita take bata baki,

Tunani Hafsat tayi kodai taje tafadawa Mami abinda ke faruwa saboda kar nan gaba mamin ta rinka ganin kamar itace tayi sanadiyyar salwantar yaronta,

Wani sabon kuka tasake fashewa dashi jin har mangariba tayi amma yusleem bai dawoba, yanda tatashi tun safe bata sakawa cikinta komai ba har yanzu takasa shan koda ruwa babu abinda yake cikinta sai iya ruwan zafin da tasha da safe, idanuwanta kamar jan gauta saboda uban kukan data sha,ita addu’ar da take Allah yasa kar su kasheshi.

Tana zaune ita kadai acikin duhu bayan maman amir tatafi misalin karfe 10:30, taji motsin mutum, zaune tatashi cikin dasasshiyar muryarta tayi magana,

“Waye…?”
.
Kamar acikin mafarki taji muryar yusleem,

“Nanah…”

Zabura tayi ta nufeshi acikin duhun,

“Yaya yusleem”

“Na’am..”

Rungumeshi tayi ta kankameshi, shi dinma rungumetan yayi,

“Yaya yusleem ina katafi tun safe? Kasa duk hankalina yatashi..”

Daukarta yayi zuwa bakin kafita ya zauna yadorata ajikinshi gaba daya ma ita ta manta da cewar akwai wata aba wai ita kunya sai shisshigewa jikinshi take,

“Yi hakuri kinji, kuka kikayi ne naji muryarki ta dishe?”

Kwantar da kanta tayi bisa kirjinshi,

“Haba yaya yusleem ba dole inyi kukaba, tun safefa nake nemanka har yamma ban ganka ba…”

Kanshi ya dora akan nata ya zagayeta da hannuwanshi,
.
“Wallahi Hafsat ba laifina bane, dama nafada miki mutanen nan bazasu barni ba…”

“Yaya yusleem me suka yimaka? Sunyi maka wani abu?” Tafada tana lallaluba jikinshi,

“Babu abinda suka yimin amma sunce mutukar na tona musu asiri zasu kasheni…”

“Nida cewa nayi ko infadawa abbanmu gaskiyar abinda yake faruwa? Saboda ayi muku tsakani dasu yaya yusleem inma wurin yan sanda zakuje ayi muku tsakani sai kuje tunda har gunsu dazu naje nakai report..”

Murmushi yusleem yayi yashiga shafa gadon bayanta alamun rarrashi,

“Nanah mutanen nan fa sunada gatan da bakowa keda shi ba, sunada fada fiyeda yadda kike tsammani, koda kayi kararsu to daga karshe kaine zaka kwana aciki shiyasa ni bazance zanyi kararsu ba, tunda dai bukatarsu kar intona sirrinsu to shikenan bazan taba tonawa ba tunda Allah yana kallonsu shi yasan yanda zaiyi dasu”

“Hakane, shikenan Allah yakara kareka daga sharrinsu..”

“Amin nanah..”

Hannunshi yasa ya shafo cikinta,

“Kinci abinci kuwa?”

Girgiza masa kai tayi,

“Meyasa?” Ya tambayeta har lokacin hannunshi yana kan cikinta,

“Taya zan iya cin abinci alhali ban ganka ba? Ni ko girki ma banyi ba, maman amir ma takawo min alala amma ko budashi banyi ba”

“Wallahi nima banci komai ba kuma sun Kawo min abincin amma naki ci..”
.
“Allah ya shiryar dasu, kasan duk inda ka kai da son wani ya shiryu bazaka iyaba mutukar Allah bai nufeshi da shiriyar ba domin shiryarwa awurinshi take..”

“Amin Hafsa, Allah yaganar dasu suma, ya ciwon marar taki?”

Sake lafewa tayi ajikinshi,

“Da sauki,dayake ina cikin damuwa ma ni harna manta da wai banda lafiya”

“Allah sarki nanah, sannu kinji, bari in dafa miki ruwan zafi kisha sai kici abinci”

Kwantar da ita yayi yakunna candle sannan yakunna risho ya dora ruwan zafi, taliyar da yadafa musu da safe tana nan ayanda take batayi komai ba dayake sanyi ne dan haka ya dumama musu ita,

Acikin cup yazuba mata ruwan zafin yasa sugar dan kadan yajefa Lipton,

“Tashi kisha ruwan zafin sai muci abinci ko?”

Tashi tayi ta amshi tea din ta kurba,
.
“Ya haka dalam babu sugar?”

Murmushi yayi,

“To keda bakida lafiya inake ina shan zaki? Ko kina son kiyita bleeding ne?”

Shiru tayi taci gaba da kurbar tea din har ta shanye,

Taliya yazuba musu suka ci, bayan sun gama ta shiga toilet ta dan gyara jikinta ta fito sanye da kayan bacci riga da wando, kwance ta sameshi ya dan jingina da jikin bango yana wasa da candle din dake hannunshi yana d’isa ruwan candle din a hannunshi,

Kusa dashi takarasa ta kwanta jikinta ajikin nashi,

“11 fa tawuce bazaka kwanta ba?”

Hannunta yakamo ya disa mata ruwan candle din, zabura tayi ta tashi zaune tana yarfe hannun, diff taga yabushe candle din,

“Yaya yusleem da zafifa, wallahi ka kona ni”

Kamota taji yayi zuwa jikinshi, bargo yaja ya rufesu ya kamo hannunta wanda ya disa mata ruwan candle din,

“Sannu, kawo mugani…, nimafa kinji inda ya diddisa a hannuna taba kiji”

Kanta ta kwantar agefen wuyanshi numfashinta yana sauka akan wuyanshi…..

*
           ***Lumshe idanuwanta tayi tana jin yanda yake hura mata iskar bakinshi awurin da ya diga mata ruwan candle,

“Wai dagaske kin kone ne..?”

“Ehh..”

“Kai nanah banda karya dai, naji anacewa bakar fata tafi fara kwari to ya akayi ni ban koneba sai ke?”

“To ai kai namiji ne”

Murmushi yayi yaci gaba da busa mata wurin,

“Da ban dawo ba shikenan sai dai ki kwana ke kadai ko?”

Dayan hannunta takai ta dora akan bakinshi,
.
“Yaya yusleem dan Allah kadaina fadin haka, bana burin wani dare yazo wanda zan kasance ni daya ba tare da kai ba…”

Murmushi yayi yajuya ya rungumeta tsam tsam,

“Gobe akwai maganar da nake son muyi tare dake amma yanzu kiyi bacci ki huta..”

Makale kafada tayi kamar yana ganinta,

“Uhm, uhm muyi yanzu mana..”

“Meyasa bazaki bari sai goben ba?”

“Ni bana jin bacci yanzu”

“Nikuma kinga bacci nakeji sosai dan har idanuwana rurrufewa suke saboda tsananin bacci…”

Hannu takai tafara laluben fuskarshi har ta tabo idanuwanshi wadanda ke rufe,gangarowa tayi har zuwa kasumbarshi wadda ta dan fara taruwa,

“Yaya yusleem gaskiya gobe ya kamata inkaika kayi aski, jifa yanda kafara zama wani tsoho..”

Murmushi yayi yadora hannunshi akan nata wanda ke bisa kasumbar tashi,
.
“Nine nafara zama tsohon? Har yanzu fa ni saurayine nanah…”

Jin abinda yace yasata boye fuskarta cikin kirjinshi,ahankali yasake magana,

“Askin ma sai kin kaini…?”

“Ehh mana..”

“Kina tsoro kar su oga dalma su kara kamani ko?”

“Insha Allah ai bazasu ma sake ganinka ba bare su daukeka,yanzu dai muyi maganar da kace zamuyi”

“Ai nace miki sai gobe saboda yanzu bacci nakeji”

“Tom shikenan tunda dai bazaka fada min yanzu ba…”

Zamewa tayi daga jikinsa ta juya daya bangaren, matsawa yayi ya rungumeta ta baya mintuna kadan taji yayi bacci,
.
Ita kam kasa yin baccin tayi sai tunane tunane barkatai da kwakwalwarta ke yi daga karshe itama bata san lokacin da baccin ya dauketa ba.

K’arfe 6:30 ta bude idanuwanta, yusleem tagani zaune akasa ya bude laptop dinshi yana latse latsen da bata san ko na menene ba,

Bathroom ta shiga tayi brush tafito ta karasa wurin kayan sakawarsu, kayan da yasaka da wanda tasaka taware zata wanke,

Har ta dibi kayan ya daga kai ya ganta,

“Ina zakije kuma daga tashinki?”

“Wanki zanyi wai kafin rana tafito”

“To ai nace miki zamuyi magana ko kin manta?”
.
“Gani nayi ai kaima akwai abinda kakeyi shine zan yi kafin kagama”

“A’a zo mu gama maganar tukunna..”

Ajiye kayan tayi takarasa inda yake, daukar laptop din yayi suka koma saman katifa,

“To ina jinka..”

“Sana’ar yi nake son ki zaba min sai infara..”

“Yaya yusleem Sana’a kuma?”

“To nanah zanyi ta zama hakane? Ai yakamata insamu abinyi komai kankantarsa”

“To shikenan amma dai banda aikin karfi da sauran ayyukan wahala”

“Meyasa? Bakya son karfina yakare ne?”

Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta cike da kunya, janta jikinshi yayi ya dora hannunshi akan kafadarta kyass taji karar camera, dago da idonta da sauri tayi nan taga ya kuma daukar wani ajikin laptop din,

Kallonshi tayi, “yaya yusleem wannan wanne irin hoto ne da kayan bacci?”

Sake dauka yayi yana murmushi,

“Kinyi kyau ne shiyasa, kuma kinga kayan baccin ma sunyi miki kyau..”

Kokarin tashi tayi yahanata ta hanyar matseta ajikinshi,
.
“Ki tsaya mugama mana, so nake muyi hotuna kamar guda 50 ayanzu..”

“Sai har charge yakare kenan..”

“Waya fada miki zai kare?” Yakarasa maganar yana cusa fuskarshi tsakiyar kirjinta,

Tureshi tayi tana murmushi,

“Kai yaya yusleem,dan Allah kabari..”

“Au bakya son hoton?”

Kallar screen din laptop din tayi nan taga har lokacin da yasaka fuskarshi a kirjinta saida ya dauka,

“Dan Allah ko goge wannan.. Idan wani yagani fa”

“Sai infada mishi nida matata ne”

Ta bude baki da niyyar sake yin magana taji lebenshi kan nata dolenta tayi shiru, kan kumatunta yakoma daga nan yakoma goshinta, habarta, wuyanta,
.
Zamewa tayi, “nidai gaskiya hoton nan ya isa haka”

“To shikenan, zo ki gansu”

Matsawa kusa dashi tayi tasoma kallon hotunan tun daga kan nafarko, wani idan tagani ma kunya ce take lullubeta domin har lokacin da yake kissing dinta duk ya dauka,

“Lahhh kaga namanta bari inje infadawa Maman amir tafadawa baban amir kadawo..”

“To amma karki dade”

Hijabi ta dauka tafita bata jima ba sai gata tadawo,

Kayan wankin data hada ta nufa zata diba,

“Zo nanah..”
.
“Yaya yusleem ni kabarni inyi wankin nan”

“Ehh zan barki kiyi, zo kigani”

Fasa diban kayan tayi takoma wurinshi nan suka shashance awurin suna kallon hutananshi wanda ya dauka lokacin yanada arziki kuma yana tsaka da cin daula domin mafi yawansu akasashen turai ne idan yaje sai wadanda yadauka anan gida nigeria tareda mutanenshi ada wadanda suke harka tare wanda mafi yawansu manyan mutane ne kalilanne yara irinshi, haka suka lalace wurin kallon hotunan daga karshema kashe laptop din yayi ya kwantar da ita ajikinshi babu bata lokaci bacci ya kwasheta, ahankali ya zare jikinshi yatashi bayan ya kwantar da ita, kayan yadiba yadauki sabulun wanki ya shiga bathroom, bucket guda biyu ya dauka yafita rijiya ya debo ruwa yadawo yashiga bathroom din ya fara wanke kayan, shi kansa yasan bazai iya tuna ranar da yayi wanki da hannunshi ba sai dai da washing machine,

Kafin Hafsat tatashi har ya gama wankin domin dama bamasu yawa bane, yana cikin yin dauraya sai gata tashigo,

“Yaya yusleem me kakeyi?”

“Daga tashinki?”

Bokitin ta kalla wanda yake dauraye kayan aciki nan idonta yasauka akan kayan baccinta wadanda tasaka shekaran jiya sukayi staining, sannan ga bra guda biyu,Kunyace ta lullubeta ta mika hannu ta janye bokitin,

“Menene haka?” Ya tambayeta yana kallonta,

“Kabarshi inkarasa”

“To ai nagama”

“Ehh katafi dai zan karasa”
.
Fita yayi yabarta acikin bathroom din takarasa dauraye kayan ta kinkima zuwa tsakar gida wurin igiyar shanya, shanya kayan tayi takoma daki,

“Yaya yusleem wallahi koko da kosai nake sha’awa, zaka sha?”

“Zansha mana”

“A’a idan baka so dan Allah kafada min”

“Wallahi ina so”

Daukar flask tayi da kudi,

“Bari to inkaiwa amir yasiyo mana”

Kai yagyada mata yabita da kallo har ta fice, shi kansa bazai iya fassara yanayin da zuciyarshi ke cikiba gameda ita.
.
Idanuwanshi ya lumshe nan yaji hannuwanta akan kasumbarshi tana shafawa, bude idonshi yayi ya kalleta,

“Baban amir ne yake magana dakai yana waje..”

“Toh bari inje”

Tashi yayi yafita, yana fita ta dan gyara dakin ta dora ruwan wanka,

Tana fitowa daga wankan yusleem nashigowa cikin dakin rikeda koko da kosan da ta aiki amir ya siyo,

Fita yasake yi domin yabata damar shiryawa saboda yasan indai yana cikin dakin takura zatayi,

Saida ya daidaici cewar tagama shiryawa sannan yakoma, tana zaune tana shafa mai akafarta bayan ta saka kayanta atamfa pink colour riga da zani,

Akusa da ita yazauna, “nima bari inyi wankan ko?”

“To ga ruwan zafin can”

Girgiza mata kai yayi,

“Nida ruwan sanyi zanyi”

“Kai yaya yusleem”
.
“To aini babu abinda zaiyi min, kece dai zaiyi miki illa idan kika fiya amfani dashi especially ma yanzu da kike period, ku mata idan kuna period anfiso ku yawaita amfani da ruwan zafi sannan ku yawaita shan shi..”

“To ai yanzun ma da ruwan zafin nayi wankan” tace dashi kanta akasa,

“To ki diba kisha idan kin gama”

“Toh..”

Bai sake magana ba ya tashi ya shiga bathroom, maganar Maman amir tajiyo awaje dan haka ta tashi ta fita domin da ita kadai suke yin shiri amma duk sauran matan gidan gaisuwa ce kadai ke hadasu.

Lokacin data koma cikin dakin yusleem yana saka kaya, juyawa tayi zata koma ya dakatar da ita,

“Ina zakije?”

“Waje zanje”

“Me akeyi?”

“Babu komai”

“To dawo ki zauna”
.
Komawa tayi ta zauna batare da ta kalli wurin da yakeba, har saida ya kammala yazo kusa da ita ya zauna suka fara karyawa,

Abaki yasa mata kosan yana kallonta kawar da kanta gefe tayi tana murmushi,

“Au bazaki ci ba? To ni bani inaso”

Kasa bashin tayi dan haka lokacin data dauko takai bakinta yayi gaggawar rike hannun nata yakai bakinshi maimakon bakinta,

“Nanah wai wannan kunyar duk ta menene uhm…?”

Hannunta nahagu tasa ta kare fuskarta,
.
“To indai baki saki jikinki kin daina jin kunyata ba zamu bata dake”

Murmushi tayi batace komai ba, da haka suka gama cin abincin duk tana takure,

“Yaushe zamuje kayi askin?”

“Sai dai idan zakiyi min”

Waro ido tayi ta kalleshi,

“Dame?”

“Shaving stick”

Kanta ta cusa cikin pillow tana dariya, binta yayi ya dora kanshi akan bayanta.

Kan keken sakarta tahau tana yin sakar hula shikuma yana kan katifa yana gyara farcenshi da nail cutter,

“Yaya yusleem albishirinka”

“Goro”

“Hula nake saka maka da sunanka ajiki..”

.
Ajiye nail cutter din yayi yanufi inda take, abayanta ya tsaya yasaka hannuwanshi ya dafe jikin keken sakar bayan ya dan rankwafa yayi mata runfa,

“Shine baki kirani na tayaki ba?”

“To ai baka iyaba”

“Basai ki koya min ba”
.
Murmushi tayi taci gaba da sakarta yana tsaye yana kallo da haka har ta kammala hada mishi hular wanda ajiki ta rubuta sunanshi,

Karba yayi yasa ya kalleta,

“Dame zan biya?”

“Ni kyauta nayi maka”

“To zo ki kwanta ki huta”

“A’a ba yanzuba saboda maman amir tace inyiwa amir kayan sanyi zata siya mishi”

“To ki dan huta sai kiyi”

Hakura tayi takoma kusa dashi ta kwanta nan kuma yasoma cakulinta, daga ita har shi dariya suke wanda bata taba ganin yayiba sai yau,

Sai yanzu ta tabbatar da rayuwa cikin rufin asiri shi yafi komai dadi fiyeda azauna cikin daula amma babu farin ciki.
.
  Daren ranar ta matsa mishi suje tarakashi aski amma yaki yace itace zatayi masa dole babu yadda zatayi haka ta yadda sukaje shago suka siyo shaving stick suka dawo, candle ta kunna suka shiga bathroom, sabulu ya mika mata bayan ya lumshe idonshi yana jiran yaji tafara……Saida ta rintse idanuwanta sannan ta goga mishi sabulun ajikin kasunbar tashi bayan ta shafa ruwa,

Ahankali tasa shaving stick din tafara shaving kasumbar tashi wacce take bala’in burgeta domin itace takara kawata fuskar tashi,

“Nanah tunanin me kikeyi ne kike nema ki hada da fatata…”

Taji muryarshi bayan yarike hannunta, sai lokacin tadawo daga duniyar tunanin data tafi, dan murmushi tayi,

“Babu komai…”

“Ban yarda ba”

“Saboda me?”

“Saboda nasan ba gaskiya kika fada ba”

Cigaba da yimasa shaving din tayi tana murmushi,

“Ohh yaya yusleem..”

“Ohh nanah…”

Dariya tayi, “angama”

“Inji wa?” Ya tambayeta yana shafa habarshi,

“Allah angama ko sai nakawo maka mirror kagani?”

“A’a tunda kince angama shikenan”

Candle din tabar mishi tafita, tana zuwa tsakiyar dakin taga ankawo wuta, ita sai yanzu ma ta tuna da wata wutar nepa domin tunda suka dawo wannan gidan ba ataba kawowa ba sai yau,

Wurin da zasu kwanta ta gyara musu ta shirya ta kwanta,
.
Maganar yusleem ce tasata dan juyawa ta kalleshi,

“Nanah shine baki fada min ankawo wuta ba?”

“Au dama baka saniba? Ai nazaci kwan ban dakin akunne yake..”

“Inajin dai wutar cikin ban dakin batayi gaskiya..”

Kaya yasaka ya dauki laptop dinshi yajona charge, da Hafsat har ta kwanta amma ganin wuta yasata tashi taje zata dan rage sakar dake gabanta,

“Wai ke bakya gajiya da sakar nanne?”

“Ina gajiya mana, amma yanzun dai ban gajiba…”

“To asauko lafiya..”

“Amin yaya yusleem..”

Kunna laptop dinshi yayi yafara game ita kuma tana kan keke tana sakarta amma dan jefi jefi suna yar hira,

Wata wak’a taji ya kunna yanabi ahankali,

_”Ehh shin yanzu idan kika barni ina zan kwana….,so naki yake tab’a raina, nagane da cewa yanzun so ne asalina,ki aminta dani alkawari mu rikewa juna,inhar nabarki inane zansa kaina,kimin uzuri kome nai sone sanadina,duk mai kaunarki sahibine ni awurina….”_

Shiru tayi tana sauraren yanda yake bin wakar yanayi ahankali cikin muryarsa mai sanyi, da zarar wakar takare sai taji yasake dawo da ita farko yanabi kamar mai yin hadda, murmushi tayi,

“Yaya yusleem dama ka iya waka?”

Rage volume din wakar yayi,

“Ban iyaba amma nakoya saboda wata yarinya guda daya…”

“Lallai….”

“Ina son wakar nan Allah nanah, duk lokacin da nake jinta jinake kamar danni mawakin yayita…”

Murmushi Hafsat tayi,

“To akunna min nima inji mana”

“Gata kiji, na sadaukar miki da ita”

Volume din wakar yakara yanda zata jiyo sosai nan yaci gaba da bin baitikan wakar har takare yasake kunnawa,

Har Hafsat tagama hada rigar da take yiwa amir tataso bai daina jin wakar ba yana kwance laptop din nakusa dashi,

“Yaya yusleem akashe wakar nan haka zanyi bacci..”

“Inkunna mana american film dai mu kalla..”

“To shikenan kunna kafin bacci yayi gaba dani..”
.
Kwanciya tayi ata bayanshi tadora kanta akan pillow tana kallonshi yana kokarin lalubo film din da zai kunna musu,sai taga yakara kyau saboda gyaran fuskar da tayi mishi, fuskarshi tafito fes sai kyalli take,

Black men shine film din da yasaka musu, juyawa yayi ya kelleta,

“Wannan ai nakare miki bakya gani..”

Janta jikinshi yayi yadauki kanta yadora akirjinshi suka cigaba da kallon wanda yakaisu har karfe 1 nadare sai lokacin bacci yasace Hafsat baima san tayi baccin ba saida yayi magana yaji shiru,

Kashe kallon yayi ya kashe laptop din yasake gyara mata kwanciyarta ajikinshi.

  Rayuwarsu haka ta kasance, Hafsat ta hanashi yafita ya nemi aiki idan yayi magana sai tace to me suka rasa ai basu rasa komai ba, shi kansa yasan babu abinda suka rasa din amma wani lokacin yakan zauna yayi tunani tunda bazasu dawwama ahaka ba gashi lokuta da dama kewar maminshi data yan uwanshi tana damunshi domin yana mutukar sonsu sannan ya shaku dasu sosai,

Hafsat koda yaushe cikin kwantar mishi da hankali take tana nuna masa cewar wannan halin da suke ciki shine kadai marufar asirinsu da zarar sun koma wurinsu Mami to asirinsu zai tonu asan abinda yafaru, hakura yayi ya zauna bai fita ya nemi aiki ba koda yaushe suna daki shida ita tana aikin sakarta shikuma yayi musu girki ya kunna wakar da yazamar da jinta kamar ibada , yana bi yana abinda yake yi, hatta sauran matan dake haya agidan sun saka musu ido koda yaushe suka zauna gulmarsu sukeyi wai su jarababbu ne kullum suna daki basa rabuwa kuma baya barin Hafsat tana fitowa,

Da dan kudaden sakar da Hafsat takeyi suke samun na cefane kuma duk da haka suna zaune cikin rufin asiri basu da wata damuwa saita rashin danginsu atare dasu.

Yau tunda safe yusleem da rashin lafiya yatashi domin yajima baije yaga likitansa ba kuma akwai magungunan da yakesha wanda yajima baisha ba shiyasa lalurar ta tashi mishi tun daren jiya amma yayi kokarin boyewa kada Hafsat tagane, haka ya lallaba suke Yar hira sama sama har abin yafara fin karfinsa domin wani zazzafan zazzabine ke yimasa sallama….

*
      ***Daurewa yusleem yaci gaba dayi bai bari ta fahimci komai ba har tagama shiryawa ta fita kitso wurin maman amir,

Kafin tadawo tuni har zazzabin ya rufeshi, akwance tadawo ta tarar dashi yayi ruf da ciki,
.
“Yaya yusleem kayi salla kuwa…?”

Shiru taji nan tayi tunanin kodai barci yake yi dan haka ta nufeshi da niyyar tashinshi,

Agaban katifar ta zuba gwiwowinta ta dan kai hannu da niyyar taba jikinshi amma sai tajishi zafi zau,

Cikin rawar jiki ta daddafa shi,

“Yaya yusleem menene? Baka da lafiya? Meya sameka?”

Juyo da kanshi yayi ya bude idanuwanshi wadanda sukayi jajur ya kalleta,

“Nanah cikina ke ciwo gashi zazzabi ya kamani..”

Zama tayi agefenshi fuskarta kamar zata fashe da kuka,

“Sannu yaya yusleem, to yanzu wanne magani zan samo maka? Ko paracetamol zaka sha?”
.
“Uhmm Kawo min insha to”

Har tatashi sai tadawo ta zauna,

“To ai bakaci abinci ba”

Girgiza mata kai yayi,

“Bazan iyaci ba bana sha’awar kowanne irin abinci, zan dai sha ruwan zafi”

“Yaya yusleem amma da ka daure kaci abincin komai kankantarshi…”

Daga mata kai yayi alamun to saboda ganin yanda tadamu ta daga hankalinta lokaci daya,

Shinkafa da wake da mai da yaji ta zubo mishi dama ita ta dafa tunda safe,
.
Zaune ya tashi  ta gauraya masa shinkafar tasoma bashi, cokali uku kacal yayi ya mike yashiga toilet da sauri nan yafara kwara amai baji bare gani, da sauri tabishi cikin toilet din inda yake aman ta rikeshi, bayan yagama amayar da abincin da yaci dinma bai daina aman ba,

Ruwa ta zuba masa ya wanke bakinshi bayan ya gama, rikoshi tayi suka koma cikin daki hawaye suna zuba daga cikin idanuwanta,

Kwanciya yayi yadan bude idonshi ya kalleta ganin tana hawaye yasashi rikota zuwa jikinsa ya kwantar da ita tareda dora kanta bisa kirjinshi,

“Menene na kuka?”

Shiru tayi bata amsa ba, amma kuma hawayen basu bar fita daga idanuwanta ba,
.
Kokarin kwantar mata da hankali yayi ta hanyar zame dan kwalin dake kanta,

“Baki nuna min kitson da akayi miki ba…”

Goge hawayen fuskarta tayi tana jinshi yana kirga adadin yawan kitson duk da cewar acikin karfin hali yake yi amma ita tadan ji sauki acikin zuciyarta saboda ganin ya dan ware,

“Kayi salla ne?”

“Banyi ba, dafa min ruwan zafi insha sai nayi alwala saboda naji ruwan kamar da sanyi”

Tashi tayi ta dafa masa ruwan zafin ta zubo masa a cup tasa Lipton da sugar tabashi yasha sannan takai masa wani ban daki ta rakashi yaje yayi alwala yafito,

Kwanciya yayi ruf da ciki bayan ya idar da sallar yaja bargo ya lulluba, tagumi Hafsat tayi tana kallonsa idonta fal fal da hawaye,
.
Haka suka wuni acikin wannan hali har dare yayi tunda dare yayi kuma bacci yagagari idonsu domin wani irin shassheka yusleem yakeyi kamar wanda yayi gamo, kuka Hafsat tasashi agaba tanayi ga kakarin amai da yaketa yi amma kuma yakasa banda zazzafan zazzabin da yake jikinsa gashi dama throughout yau baici komai ba cokali ukun da yayi ma a shinkafa da waken data dafa saida ya amayar da ita tass ruwan zafi kadai ya iya sha,

Rirrikeshi hafsat tayi tana kuka domin ita bata ma san yanda zatayi ba ganin dare yayi sosai bare tace su tafi asibiti,

Addu’a take ta tofa mishi afuskarshi zuwa can bacci ya daukeshi, lullubarshi tayi tazuba masa ido tana kallonsa, har asubah tayi bata runtsa ba,

Tashi tayi tai salla zuwa can taji kakarin amai alamun yatashi, tashi tayi da sauri taje ta rikeshi,

“Sannu yaya yusleem, sannu…”

Kai yake daga mata har yasamu yadaina kakarin aman,

Ruwan zafin data dora mishi ta je ta sauke ta zuba mishi yayi alwala yayi salla tabashi tea yasha, kwanciya yayi yadora kanshi akan cinyarta jikinsa zau dan zafi,

Bacci taji yasake komawa nan ta zame tatashi taje ta harhado kaf kan kudadenta dake cikin dakin wanda ta lissafasu Dubu goma sha daya ne da dari biyar,
.
Tagama yanke hukuncin zasuje asibiti idan gari ya waye saboda wannan rashin lafiyar ta yaya yusleem da karfinta tazo idan ba atareta da wuriba gaba sai azo asha wuya,wurinshi takoma ta zauna ta taba jikinshi har lokacin akwai zafi da alama zazzabin bai sauka ba.

K’arfe 9 suka gama shiryawa domin tafiya asibitin,

“Wanne asibitin  zamuje?” Yusleem ya tambayeta,

“Private mana yaya yusleem”

“Private akwai tsada nana, muje general”

Girgiza masa kai tayi,

“Yaya yusleem general hospital babu confidential saboda asibiti ne na kowa da kowa yanzu idan mukaje can wallahi sai kowa yasan abinda ake ciki nikuma bana son sirrinmu ya fita amma kaga idan private ne babu ruwan kowa da mu balle har musa ran wani zaiji maganar”

“Shikenan tunda kince haka”
.
Tashi tayi ta rikeshi yatashi yasa takalmi suka fita, maman amir ta biyosu tana yimusu Allah ya kiyaye hanya,

Sai da sukaje bakin titi sannan suka samu keke napep nan ta tare musu suka shiga suka nufi wani private hospital,

A reception yusleem ya zauna taje ta bude mishi polder dubu biyu sannan za abiya kudin ganin Dr dubu biyar,sannan sai anfara yimishi general test na komai da komai domin ayi saurin fahimtar matsalarshi daga nan sai aturashi wurin likitan da yadace yaganshi dan haka sai ta biya kudin test dubu biyu, duk haka ta biya takoma wurinshi suka nufi laboratory,
.
Babu bata lokaci akayi masa duk gwaje gwajen da za ayi aka basu result sannan aka nuna musu wurinda zasuje suga likita,

Zama sukayi suna jiran na ciki yafito bayan yafito ta rikeshi suka shiga cikin office din wanda ajiki anrubuta sunan likitan wato Dr Sufyan,

Dan siriri ne likitan baki kyakkyawa yana sanye da bakaken suit da farin glass a idonshi,

Bude sakamakon da suka Kawo masa yayi yaduba kafin yadago yana kallonsu bayan ya cire farin glass din dake idonshi,

“What…” Yafada ahankali yana kallon paper din,

Maida kallonshi garesu yayi, yajanyo wani dan karamin card yafara rubutu,

“Me yasameshi? Tun yaushe ne bashida lafiya? Yana iya cin abinci?,ya kakejin ciwon cikin? Menene yafi yimaka ciwo ajikinka?”
.
Duk wadannan tambayoyin yusleem ne ya amsasu da kanshi, card din Dr yamika musu bayan yagama rubutun da zaiyi,

“Ok ga wannan kuje pharmacy Ku siyi magani, zai rinka shan guda daya kwal akullum..”

Karba sukayi suka fita, a reception tabar yusleem tatafi pharmacy domin siyo maganin, takardar ta mika domin abata maganin,

“Hajiya kwali daya ko biyu?”

“Abani kwali biyu”

“Ok kudinki yakama dubu dari da sittin”

Idanuwa Hafsat tazaro,

“Dubu dari da sittin?”
.
“Ehh ai duk guda daya dubu tamanin ne”

“Ok tom ina zuwa bani takardar”

Karbar takardar tayi tafita tanufi office din Dr sufyan, knocking tayi sannan tashiga,

“Madam ya akayi?”

“Dr maganin naje zan siya naji ance wai dubu tamanin ne guda daya”

Gyara farin glass dinshi yayi yanuna mata kujera ta zauna,

“Kin san mijinki gay ne?”

“Ehh nasani likita..”

“To wannan maganin shine kadai maganin da zai rinka sha domin samun lafiyarshi saboda idan bakuyi kokari yasamu maganin nan yana sha ba komai zai iya faruwa dashi,dan haka am advising you kiyi kokari ku mallaki wannan maganin duk tsadarshi..”

“To shikenan likita za asiya insha Allah”

“Ok Allah yabashi lafiya”

“Amin, nagode”

Tashi tayi tafita tanufi wurin yusleem zuciyarta cikeda tunanin inda zataje ta samo kudin domin ita yanzu dubu biyu ne da dari biyu da hamsin kacal awurinta…..

 
*

      ***Kafin ta k’arasa wurin yusleem tayi karfin halin tsaida hawayen dake yi mata ambaliya akan kuncinta,

Murmushin karfin hali ta kakaro tayi lokacin da ta isa wurin yusleem,
.
“Yaya yusleem tashi muje…, anjima zan dawo na sai maka maganin saboda yanzu kudin hannuna bai kai ba”

Kallonta yayi yana jingine ajikin kujerar dake jere acikin reception din,

“Nawa ne?”

“Ka tashi muje kawai yaya yusleem…”

Bai sake yin magana ba yatashi, hannunshi ta rike suka fita, suna fita suka samu keke napep suka shiga,

Lokacin da suka koma gida ruwan zafi kadai ta dafa mishi domin baya iya cin abinci komai yaci sai yayi amansa, tana kokarin fita maman amir ta aiko mata da dan wake,

Kasa zaunawa taci tayi saboda idan har ba kudin nan taje ta nemo ta siyowa yusleem magani ba hankalinta bazai taba kwanciya ba,
.
Wurin kafintocin da suka siyi kujerunta takoma tasake kai musu tallar dayan kujerun nata na babban falo babu bata lokaci suka tafi gidan taje ta bude musu,

Duk haduwar kujerun nan da kyawunsu amma sai kafintocin sukayi mata tayin wulakanci wai dubu 60 zasu siya, kin siyarwa tayi nan suka kara dubu goma yazama dubu saba’in,ganin kudin basu cikaba yasata fito musu da wani show glass dinta wanda aka zuba mata humra da turaren wuta aciki, dubu goma sha biyar suka siya,

Saida suka fitar da kayan sannan ta rufe gidan tatafi, kai tsaye asibitin da sukaje da yusleem ta koma taje pharmacy ta siyo mishi maganin sachet daya,
.
Lokacin data koma gidan samunshi tayi yana bacci dan haka ta ajiye mishi maganin ta shiga wanka tafito, harta shirya bai tashi ba sai da ta idar da salla sannan taji motsinshi, juyawa tayi ta kalleshi,

“Sannu yaya yusleem”

“Yawwa, kin dawo?”

“Nadawo lokacin kana bacci..”

Mikewa tayi taje kusa dashi ta zauna,

“Yaya yusleem ga maganin nasiyo maka”

Kallonta yayi bayan ya gyara zamansa,
.
“A ina kika samo kudin da kika siyo?”

“Yaya yusleem kujerun nan naje nasiyar, lafiyarka yanzu ni tafi min komai..”

Hannunshi ya dora akan nata,

“Amma meyasa kika zabi sayar da kayanki? Ba ga nawa kayan ba wayoyina da laptop dina”

Girgiza masa kai tayi,

“Nawa kayanma naka ne, sannan nasan yanzu aduniya baka mallaki komai ba sai wayarka da laptop wannan dalilinne yasa bazan bada goyon bayan mu siyar dasu ba..”
.
“Nanah agaskiya ban san da wanne baki zan yimiki..”

Saurin rufe masa baki tayi bata barshi yakarasa ba,

“Inbaka maganin kasha yanzu ko zaka dan ci abincin da Maman amir ta Kawo min?”

“Bazan ci komai ba, bani maganin kawai nasha”
.
Tashi tayi ta dauko mishi ta hado da ruwa, abin mamaki kwata kwata kwayoyin maganin kwallo 6 ne aciki bamasu wani yawa bane sai dan karen tsada abinda yayi mutukar tayar da hankalin Hafsat,

Saida taga yasha maganin sannan ta dauko dan waken da maman amir takawo mata taci,
.
Hannu ya mika mata bayan tagama cin abincin ya kwantar da ita akusa dashi, kasa kasa yake yi mata magana suna yin yar hira.

Tunda Hafsat taga yakusa shanye maganin hankalinta yatashi nan tasake komawa wurin kafintoci ta sayar musu da gadajenta gaba daya taje ta siyo mishi magunguna saboda sam bata son ta doshi umminta ko abbanta da lalurar yusleem domin tasan asirinsu yana iya fallasa,

Haka taci gaba da daga kayanta tana sayarwa tana siya masa magani wanda yanzu haka bata da komai domin hatta su fridge dinta da sauran kayan kallonta duk ta siyar ta hada kan kudin ta ajiye wani kuma ta saiwa yusleem magani, yanzu abu dayane ke damunta shine kullum yusleem yana shan magani amma sauki baya samuwa kuma har yanzu baya iya cin abinci sai ruwan zafi gashi kusan  3weeks da zuwansu asibitin,
.
Sake shiryawa sukayi suka koma asibiti ganin dr sufyan, bayan yagama dudduba yusleem sun kama hanyar fita har sun kai kusa da gate Hafsat ta dakatar da yusleem,

“Yaya yusleem tsaya zo mukoma wurin dr akwai abinda nake son fada mishi”

“To Nana shiga kifito mana, bari injiraki anan”

Komawa office din dr sufyan Hafsat tayi, zaune tasameshi yana rikeda cup yana kurbar tea,

“Madam ya akayi?”

“A’a babu komai likita dama cewa nayi ko zaka sauya mana wani maganin saboda wannan din yayi tsada da yawa kuma har yanzu bai warkeba gashi baya iya cin abinci…”
.
Tunda tafara jawabi ya kura mata ido baya ko kiftawa har saida ta gama, ajiye cup din dake hannunshi yayi ya dora hannuwanshi akan table,

“Wato madam abinda zaki fahimta shine mijinki dan homo sexual ne wanda kusan lalurar ma taci karfinsa so dole sai magani mai karfi zai rinka sha, wannan maganin ba ako ina ake samunsa ba saboda tsadarshi dan inajin ma gaba daya garin nan baifi chemists guda uku zaki samu ba wadanda suke kawoshi, amma ni zan taimaka miki zan rinka baki maganin free mutukar zaki amince da abinda zan fada miki..”

“Likita ni sassauci nake son kayi mana ka sauya mana wani maganin wanda bai kai wannan tsada ba..”

“To ai madam condition din da mijinki yake ciki yanzu dole irin wannan maganin zai rinka sha,amma ni zan taimaka miki..”

“To nagode dr, nagode madalla..”

“A’a ai ba wani abu bane, zan baki card wanda yake dauke da address din gidana dake cikin G. R. A. Governor road..” Yakarashe maganar yana lasar lips dinshi,

Sai lokacin Hafsat ta fahimci inda maganar tashi ta nufa,

“Dr aini ba yar iska bace sannan banyi kamada matan banza ba wadanda zasu iya cin amanar mazajensu ba…”

Hannu ya daga mata,

“Amma shi mijin naki meyasa yaci taki amanar yaje maza suka bata masa rayuwa? Shifa da maza yan uwanshi ma yarinka alaka,Bari infada miki gaskiya kidaina wahalar da kanki akan mijunki domin situation din da yake ciki yanzu bazai taba kallonki a matsayin mace ba bare har ya iya kusantarki saboda lalurar dake tare dashi, gaba daya bayanshi yakusa lalacewa domin sperm din dake shiga ciki babu wurinda zai fice shine sai yarinka taruwa yana taruwa har idan yakai wani stage sai wurin ya lalace har tsutsotsi su rinka fita ta wurin dan haka kidaina wahalar da kanki abanza, ni zan rinka bashi magani kyauta duk da tsadarshi mutukar kin amince da bukatata domin nan asibiti nane wadannan magungunan kuma tun daga India nake iyo ordersu ake kawo min…..!”

Sassauta muryarshi yayi cikeda yaudara da son janyo hankalinta,

“Kinga maimakon ki zauna kina yimasa wahala bayan bazai iya amfana miki komai ba gara kisamu wanda zai rinka debe miki kewa duk lokacin da kika so…!.

*
     ***Cikeda tsana da takaici hadeda bacin rai wanda ya bayyana fushi mai tsanani akan fuskarta Hafsat take kallon Dr sufyan wanda yake zaune bisa kujerarshi yana dan juyawa ahankali abisa dukkan alamu ko auren farima dakyar idan yayi duba da yanayinsa haka kuma ahaife yusleem bazai girme mishiba,
.
“Madam bakice komai ba, abinda nake son ki fahimta shine wallahi idan kika cigaba da zama da wannan mijin naki dan homosexual to zaki nak’asa rayuwarki ne domin babu abinda zai amfana miki saboda yanzu shi yamafi bukatar dan uwanshi namiji sama dake domin masu aikata irin wannan mummunar dabi’ar akwai wani stage wanda idan har suka kai wannan level din to wallahi zai zamana bama sa kaunar mace kwata kwata bare har suyi sha’awarta, mijinki ayanzu dai haka presently bazanyi saurin yanke hukunci ba but yana daf da karasawa wannan stage din muddin baku dage da bashi wadannan magungunan yana sha ba..”

“Likita ni dama sassauci nazo nema wurinka bawai maganar banza ce takawo ni ba kuma har tunda sassaucin bazai samuba to babu matsala amma kaji tsoron Allah…”

Takarasa maganar cikeda fushi ta mike saurin dakatar da ita dr sufyan yayi,
.
“Haba yar kyakkyawa kyakkyawa, wallahi kinada kyau dan Allah…”

“Allah ya shiryeka tunda bakada aiki sai fasikanci da matar aure…”

Bata sake jiran abinda zai fada ba tafice daga cikin office din gabanta yana tsananta faduwa domin babu Wanda yataba tunkurarta da maganar banza irin wannan sai Dr sufyan, ko yusleem da yake mijinta bai taba yimata magana makamanciyar wannan ba,

Jan kafarta tayi zuciyarta tana yimata wani irin kunci da radadi, kamar amafarki ta jiyo muryar dr sufyan abayanta yana yimata magana da alama sake biyota yayi bai hakura ba da mugun nufinshi,

“Hajiya tsaya kiji, dan Allah kibani 5 minutes kacal infada miki wata magana..”

Afusace tajuya ta kalleshi,

“Dr nahadaka da girman Allah karabu dani, kadaina bina, yanzu idan mijina yaga kana bina me zai yi zargi?”

Jin yanda ta bude murya tana neman tara masa mutane yasashi tsayawa, ahankali yafurta,

“Zan barki amma bawai dan nahakura ba..”

Juyawa yayi yakoma ita kuma tabishi da kallon mamaki zuciyarta tana harbawa da karfi,

Wurin yusleem ta tasamma komawa kwakwalwarta abirkice saboda abinda taji dr sufyan yafada gashi kuma nanda 2 weeks dole su sake dawowa asibitin domin za asake checking din yusleem agani,

Awurinda tatafi tabarshi anan tasake samunshi yana tsaye ya dafa gate din asibitin yana jiranta,

Hannunshi takama tarike acikin nata,

“Yaya yusleem mutafi ko..”
.
Kallonta yayi yana dan murmushi,

“Au kin dawo?”

“Nadawo muje gida kawai abinda naje nema bai samuba dama nufina wai asauya maka maganin nan zuwa wani tunda naga har yanzu babu wani improvement..”

“To me likitan yace miki?”

Cewa yayi wai wannan din dai shine zaka cigaba dasha..”

Shiru yusleem yayi har suka samu adaidaita sahu suka shiga baice komai ba, daidai lokacin da zasu tare keke napep din khadija tsohuwar matar yusleem wacce yasaka last kafin ya auri Hafsat tana cikin motarta tadawo daga makaranta tacikin glass ta hangi wani kamar yusleem parking tayi da niyyar komawa wurinsu amma kafin ta juyo har sun shige keke napep din sun tafi,

Bata hakura ba tabi bayansu acikin motarta, ahankali take binsu ta yanda babu wanda zai gane cewar su takebi har suka shiga layin unguwar da suke,
.
Tsananin mamaki ne yakama khadija domin har wata zuciyar tana cemata wannan ba yusleem bane yayinda wata zuciyar kuma take gasgatata cewar shine,

Adaidai kofar gidan da suke suka sauka bayan hafsat tabaiwa mai keke napep din kudinshi, hannunshi rikeda na Hafsat suka fito zasu shiga ciki, saurin fitowa daga cikin motarta khadija tayi tabisu da sauri,

Dakin da suka shiga ta tasamma shiga domin yau ta rantse kuma ta dauri aniyar sai taga kwakwaf,
.
Suna shiga cikin dakin akan katifa suka yada zango, tunani Hafsat takeyi shin tafadawa yusleem yanda sukayi da dr sufyan ko tayi shiru saboda bata san abinda zaije yazo ba sannan bata son kuma tayi shiru wani abun yasake bullowa tarasa mafita,

Kanta taji yusleem yana shafawa ahankali yana yimata magana,

“Wai meke damunki ne?”

Kakaro murmushin dole tayi ta kalleshi,

“Babu komai yaya yusleem kawai dai nagaji ne”

Kafin wani acikinsu yakara magana tuni muryar khadija ta karade cikin kunnuwansu wacce ke tsaye akofar dakin tana doka musu sallama, Hafsat ce ta amsa sallamar sannan tatashi daga jikin yusleem inda take kwance ta tafi duba ko wacece ke sallamar domin ita duk atunaninta ma daya daga cikin yan hayar gidanne ke sallamar……

****

Kallon mamaki Hafsat ke yiwa khadija lokacin da ta fita kofar dakin domin ganin ko wacece ke sallama ganin khadijan yasata shiga cikin mamaki domin bata taba ganinta ba,

Dan gyara tsayuwarta kadan khadija tayi bayan ta zubawa Hafsat idanuwanta tana yimata kallon kurulla domin tun daga kafarta tafara kallonta har zuwa samanta,

“Baiwar Allah wakike nema?” Hafsat ta katse shirun nasu ta hanyar tambayar khadija,

“Ammm yusleem nagani shine nabiyoshi saboda ina son yin magana dashi..”

Shiru Hafsat tayi kafin tasake yin magana,

“Ok to amma daga ina kike kuma wa zance mishi?”

“Anan garin nake, kice mishi khadija mu’az ce..”
.
“To ina zuwa..” Hafsat tace tareda juyawa takoma cikin dakin,

Bin dukkan lungu da sako na gidan khadija keyi da kallo tana mamakin yanda akayi har yusleem yake iya yin rayuwa acikin wannan gidan na haya wanda babu komai na alatun more rayuwa aciki,

Acan cikin daki kuwa koda Hafsat takoma wurin yusleem zama tayi agefenshi gabanta yana faduwa,

“Yaya yusleem watace tazo nemanka wai sunanta khadija..”

Dan damm taga yayi kafin ya yunkura yatashi zaune,

“Yanaji kayi shiru ko akwai matsala ne? Ni tsoro nakeji kar asirinmu ya tonu,kar taje tafadawa mami..”

“Babu abinda zai faru insha Allah, ki shigo da ita”

Tashi Hafsat tayi ta sake lekawa inda khadija ke tsaye tana faman touching din phone dinta,

“Yawwa bismillah shigo..”
.
Tare suka shiga cikin dakin, ganin yanda dakin yake awani takure yasa khadija sake shiga cikin tsananin mamaki,

“Yusleem… Dagaske kaine anan? Me yafaru? Lafiya kuwa? Me yakawoka rayuwa a irin wannan gidan?”

Duk wadannan tambayoyin khadija ta jero sune cikeda mamaki lokacin da take yunkurin zama akasan carpet din dake dan shimfide agaban katifarsu,

“Yusleem wai dagaske kai dinne kodai idanuwana ne kemin gizo..”

“Khadija nine nan..” Yusleem yabata amsa yana kallonta,

Jijjiga kai tayi tagyara zamanta,

“To meya faru dakai har kazo nan? Saboda ni ban san wani abu yafaru dakaiba domin ko jiya agida da yamma muna tareda mami agidanmu..”

“Khadija wata matsala aka samu babba wadda ta tilasta min dawowa nan..”

“Amma dai mami bata saniba ko?”

“Ehh to gaskiya ban bari tasani ba har yanzun nan danake yimiki bayani saboda wani dalili..”

“To amma yusleem meyasa zakazo nan wurin kazauna? Irin wannan rayuwar sam bata dace dakai ba, dubi yanda duk kabi kasauya ka dawo wani kala…”

Murmushi yusleem yayi,

“Khadija kenan kin san dai ai komai yana faruwa ne da dalili, kawai dai ki kalli wannan a matsayin wata kaddara wacce take tawa kuma dole saita sameni..”

Jijjiga kai tayi,

“Hakane, to Allah ya rufa asiri.. Sannan insha Allah nayi alkawari zan baka gudun mawa dari bisa dari acikin rayuwarka..”

“Nagode khadija amma ni babu wata gudun mawa da nake nema daga gareki..”

Jin abinda yace yasa Hafsat saurin kallonshi, tashi khadija tayi tai musu sallama tafita, har kofar daki hafsat ta rakata bayan taga fitarta ne takoma wurin yusleem,
.
“Yaya yusleem gaskiya banji dadin abinda kafada ba, ai ni sai nake ganin ko babu komai wanda ya nuna yanayi dakai yafi…”

Bai barta takarasa ba yajata jikinshi ya rufe mata baki da hannunshi yana kallonta,

“Nanah akwai dalilin dayasa kikaji nafadi haka, wallahi ba dan Allah khadija zata taimaka mana ba, akwai wata manufa atare da ita..”

“Taya kasani?”

“Saboda khadija matatace ada, saida muka rabuda ita sannan na aureki..”

“To ai ba lallai bane abinda kake zargi yazama gaskiya ba, nidai dan Allah idan tasake dawowa next time karka yi mata irin wannan..”

Kura mata ido yayi saboda jin abinda tafada, lallabashi takoma yi har ya amince,

Washe gari da safe misalin karfe 11 saiga khadija tasake dawowa gidan lokacin hafsat na gyarawa yusleem farcenshi, da fara’a Hafsat ta karbeta suka gaisa, fuskar yusleem kuwa babu yabo babu fallasa,

Cigaba da yimishi gyaran farcen Hafsat tayi yayinda ita kuma khadija ta zauna tana kallonsu aranta tana tunanin yanda akayi har Hafsat tasamu irin wannan damar awurin yusleem domin abisa dukkan alamu tasamu fada mai girman gaske awurinshi sabanin su da ko kallo basu isheshi ba lokacin da yana tareda su,
.
Ajiyar zuciya ta dan sauke sannan ta kalli yusleem wanda idonshi ke kan hannayensu shida Hafsat wanda ta rike nashi cikin nata acikin zuciyar shi kuwa dan murmushi yakeyi saboda ganin yanda kalolin fatarsu guda biyu ta hadu tashi fari tata kuma bak’a,

“Uhmm yusleem dama cewa nayi bari nabiyo na dubaku saboda naga kamar baka da lafiya ko? Domin duk ka sauya”

Kafin yayi magana Hafsat ta amsa,

“Ehh wallahi zazzabi yake fama dashi amma hakanma da dan sauki..”

“Ayya Allah yakara bashi lafiya..”

“Amin..”

Kallo na tsanaki khadija ta rinka bin dakin dashi aranta tana mamakin tayadda akayi wai yusleem yadawo haka duk da cewar jiya yayi mata bayani amma gaskiya har yanzu bata gamsu da bayanin dayayi mata ba duba da irin tarin dukiyarshi da matsayinshi ada,

Mikewa tayi tsaye tana murmushi,

“Yawwa bari naje na tafi sai wani lokacin idan nadawo..”

Cikeda fara’a Hafsat ta kalleta,

“Zaki tafi? To mun gode madalla Allah yasaka da alkhairi..”

“Nagode khadija, sai anjima” yusleem ya fada yana damke hannun hafsat acikin nashi, fita khadija tayi tana fita yusleem yaja hafsat jikinshi yana murmushi, lakuce mata hanci yayi,

“Yau fa banga kinci abinci ba?”

“Kaima ai bakaci ba, gara ma ni amma kai yaushe rabonka da abinci”

Murmushi yayi ya matse kanta akan kirjinshi tayanda har tana iya jiyo bugun zuciyarshi,
.
“Hafsat wani tunani nafara gameda ke da rayuwarki…, ni ina ganin kodai in sawwake miki ne kitafi gidanku kije kici gaba da rayuwarki cikin kwanciyar hankali saboda nasan na takura rayuwarki da yawa ba kadanba…”

Jin abinda yafada yasa gabanta mummunan faduwa bayan zuciyarta ta harba da karfi, dagowa tayi ta kalleshi idanuwanshi sun danyi ja kadan, ganin ta kura mishi ido abinda bata taba yiba yasashi sake mayar da kanta ya kwantar bisa kirjinshi,

Daga shi har ita shiru sukayi babu wanda ya iya cewa uffan domin kowa da abinda yake sakawa acikin ransa.

  Abangaren khadija kuwa bayan tafita daga wurinsu yusleem tafi minti goma sha biyar tana tsaye ajikin motarta takasa shiga, tunani take anya kuwa yadace tabar yusleem acikin wannan halin?

Girgiza kai tayi,

“Am sorry yusleem dan gaskiya yazama dole nasan abinyi…”

Shiga motarta tayi tai mata key tafita daga unguwar, fitarta keda wuya bata zame ako inaba sai gidan mami mahaifiyar yusleem, cikin sa’a kuma mamin na gida bata fita ko inaba,

Lokacin da khadija ta shiga kawataccen falon na mami mamin na cikin bedroom dinta tana shiryawa kamar me shirin zuwa unguwa, jin sallamar khadija yasata fitowa falo,

Kallo khadija ta dan bita dashi, tana sanye cikin wani swiss les dan gaske golden colour sannan tasaka sarka da earrings da warwaro duk golden gashi tasha jan lalle kai idan kaganta bazaka taba cewa ta ajiye samarin yara ba,zama mamin tayi tana murmushi saboda ganin khadija……

 
         ***

Gaisar da mami khadija tayi bayan sun gaisa ne khadijan tafara tunanin ta inda ya kamata ta bullowa da mami maganar yusleem, zuwa can dai ta dan nisa tace,

“Mami nikuwa yusleem yana kasar nan..?”

Murmushi mami tayi,

“Yusleem baya nan khadija, nikaina rabon da inyi magana dashi kota wayane anjima, daga yin tafiya shikenan shine har yau…”

Jijjiga kai khadija tayi,

“Ai kuwa Mami naga yusleem, yana nan agarin nan babu inda yaje domin naganshi da idona kuma har magana munyi dashi jiya da yau, yanzu ma daga wurinshi nataho nan..”
.
Mamakine ya bayyana akan fuskar mami,

“A ina kika ganshi khadija? Yaushe yadawo..?”

“Ai dama mami babu inda yusleem yaje yana cikin garin nan kawai dai wurin zama ya sauya, agaskiya mami na tausayawa halin da naga yusleem aciki..”

“Meya sameshi khadija? Dan Allah fada min idan wani abune ya sameshi” mami tayi maganar cikin rudewa,

“Ba wani abun tada hankali bane mami, kawai dai muje inkaiki gidan da yake ki ganshi da idonki..”

Da hanzari mami ta tashi tashiga bedroom dinta ta dauko mayafi ta fito jikinta har wani yar tsuma yake saboda taraddadin halin da zataje taga yusleem aciki,

Acikin motar khadija suka fita, ganin irin yanayin unguwar da khadija ke kokarin shigar dasu yasanya mami fara kokwanton anya kuwa khadija yusleem dinta tagani kuwa? Kasa hakuri mamin tayi har saida tayi magana,

“Khadija anya kuwa idanuwanki sun gane miki gaskiya?, me yusleem zaizo yayi anan? Sannan tayaya za ace waima yadawo kasar nan amma ni a matsayina ta mahaifiyarshi inkasa sani…”
.
“Mami ai magana kam takare tunda gamu munzo kofar gidan da yusleem ke ciki, zaki ganewa idonki komai”

Shiru kawai mami tayi amma bawai dan ta yarda da khadija bane a’a sai dan dai kawai ba abokiyar yin mahawararta bace shiyasa bazata yita jayayya da itaba,

Bude kofa kowaccensu tayi ta fito daga cikin motar, nan suka tasamma cikin gidan gadan gadan bayan khadija tarufe motarta,

Wani mamakin ne yasake lullube mami lokacin da suka shiga cikin gidan saboda yanda taga tsarin gidan yake dakuna ratata banda kaca kacan da gidan yayi sannan ga mata nan atsakar gidan kowacce tana harkar gabanta, watama ko riga babu saiko daurin kirji,

Kofar dakin da su yusleem suke khadija ta karasa dasu suka tsaya khadija tafara doka sallama,

Cikin barcin da ya daukesu sama sama kunnuwansu suka fara amsar sallamar da khadija keyi,

Hafsat ce ta dan bude idonta gamida sake kankame yusleem wanda take kwance ajikinshi,

Jin ansake kwada sallamar da karfi yasanyata tashi tana jan dan karamin tsaki, shi kanshi yusleem din shima baiji dadin wannan katse mishi baccin da akayi ba, juyi yayi yasake gyara kwanciyarshi ita kuma Hafsat ta dauki dan kwalinta tafita,

Tana yaye labulen tayi arba da mami da khadija wadanda ke tsaye akofar dakin, tamkar acikin mafarki haka Hafsat tagani, take kuma gabanta yashiga faduwa,

Tunda mami taga Hafsat tasan abinda khadija tabata labari gaskiyane dan haka yanzu bata da sauran kokwanto kuma,

Cikin rawar baki Hafsat tace,

“Mami…”

“Na’am Hafsat, ashe dagaske kuna nan kuna rayuwa batare da sanina ba..?” Mami tayi maganar cikin sanyin jiki,

“Mami shigo daga ciki”
.
Shiga cikin dakin mami tayi bayan tacire takalminta, cikeda mamaki take bin kowacce kusurwa ta cikin dakin da kallo wanda take ganinshi kamar dakin girki irin na kauye,

Har lokacin da suka shigo yusleem baisan cewar mami bace domin baccinshi yakeyi hankali kwance amma jin maganarta yasashi juyowa da sauri bayan yatashi,kallon mamin yakeyi fuskarsa dauke da mamaki gamida al’ajabi,

“Mamie…” Yakira sunanta yana mutsutstsuke ido,

“Yusleem wacce zuciyarce tabaka wannan mummunar shawarar har kazo nan kake rayuwa batare da sanina ba? Meyasa zakayi min karya?”

Wadannan sune tambayoyin da mami ta jefo masa batare da ta amsa kiran da yayi mata ba, fuskarta kunshe da fushi da bacin rai take kallonshi…….

        ***

Rasa abinda zaice yusleem yayi illa kallon mamin da yakeyi wadda itama shi take kallo kafin daga bisani ta mayar da kallonta kan Hafsat wacce ta sunkuyar da kanta kasa,

Dakin nasu mami takoma tafara kallo kusurwa bayan kusurwa,

“Mami dan Allah kiyi hakuri wallahi akwai kwakkwaran dalilin da yasa kikaga hakan tafaru, zamuyi miki bayanin komai….” Hafsat tayi karfin halin yin magana,

Mami bata bawa Hafsat amsar maganarta ba illa sake balbale yusleem da fada da tayi,
.
“Ka dauko yarinyar mutane kazo ka ajiyeta anan kana wahalar da ita, dubi yanda takoma, kalli kaima yanda ka zama duk kabi ka rame kayi baki daga gani kana cikin mawuyacin hali, to da ace khadija bata ganku taje ta fada minba da sai yaushe zaku nemeni? Da sai ka kashe musu ‘ya sannan zakaje min da mummunan labari? Yayi kyau”

Mikewa mami tayi ta kalli khadija wacce ke zaune ta sunkuyar da kai tana sauraren duk abubuwan dake faruwa,

“Tashi mu tafi khadija”

Kallon yusleem mami tayi,

“Kai kuma na baka nanda mintuna 20 ku tattaro duk kayanku kuzo gida ku sameni, idan kuka wuce haka to ina mai tabbatar maka ranka sai ya baci..”
.
Fita mami tayi daga cikin dakin khadija ta rufa mata baya,

Kallon yusleem Hafsat tayi bayan mami tafita,

“Yaya yusleem katashi mu bita, idan munje gidan sai muyi mata bayani atsanake kaga kamar fa tayi fushi…”

Dafe kanshi yayi wanda ke yimasa wani irin ciwo,

“Kibari kawai muci gaba da zama anan idan ta huce sai muje mu bata hakuri”

Girgiza kai tayi bayan ta rike hannunshi cikin nata,

“A’a yaya yusleem, mubi umarninta mu tattara kayanmu muje, bai kamata muyi watsi da maganarta ba..”

Tashi tayi batare da tajira abinda zaiceba ta shiga tattara kaya dama kuma kayan ba wadansu masu yawa bane, cikin toilet ta shiga ta kwaso inner wears dinsu dake shanye tazo ta zuba acikin trolley, har lokacin yusleem na zaune baiko motsa ba,

Kayan da tasan bazai yiyu su tafi dasu yanzuba ta tattara wuri daya ta adana sannan tafita daga dakin taje dakin maman amir tayi mata sallama, kasancewar sunyi sabo maman amir harda kuka, ita kanta Hafsat din da hawaye tadawo cikin dakin,
.
Tashi yayi ya rungumota jikinshi yana murmushi,

“Menene na kukan kamar ance bazaku sake haduwa ba…, sorry..”

Har lokacin hawayen basu bar zuba a idonta ba,

“Ya isa haka, kiyi shiru dan Allah”

Dakyar ta iya tsayar da hawayen yusleem ya dauki trolley dinsu suka fita acikin ranshi yana mamakin mata su babu wuya yanzun nan zasuyi maka kuka,

Har waje mutanen gidan suka rakasu duk da ba wai wani zumunci mai zurfi sukeyi ba,

Adaidaita sahu suka shiga yakaisu har gidan mami,
.
Gidan yana nan kamar da babu abinda ya sauya sannan ga ma’aikata nan kowa yana aikinsa kamar yanda suka saba, ganin su yusleem yasa masu gadin gidan saurin amsar kayan dake hannunsu suka shigar musu dashi ciki,kowa sai sannu da zuwa yake yiwa yusleem domin duk atunaninsu daga doguwar tafiya yadawo,

Acikin falo suka iske mami tana zaune tana shan ruwan lipton sannan ga soyayyen chips with kidney sos tana dan tsakura kadan kadan tana ci da dukkan alamu sai yanzu take yin breakfast,
.
Jin sallamarsu yasanyata dagowa ta kallesu bayan ta amsa, akasa Hafsat ta zauna yayinda yusleem yazauna akujerar dake kusa da ta mami,

“Hafsa ga abinci can maza tashi kije kici kinji…”

“Wallahi mami munci abinci sai dai idan anjima..”

Shiru mamin tayi batace komai ba taci gaba da kurbar ruwan tea dinta, suna nan zaune shiru babu wanda yasake magana har mami ta kammala cin abincin,

Sunkuyar da kai Hafsat tayi tasoma bawa mami hakuri,
.
“Mami dan Allah kiyi hakuri da abinda yafaru, wallahi ba laifinsa bane laifina ne domin nice nabashi wannan shawarar kuma nima nayi hakanne dan gudun kada mu tayar miki da hankali, amma dan Allah kiyi hakuri..”

Ajiyar zuciya mami tayi ta kalli yusleem sannan ta kalli Hafsat,

“To shikenan Hafsat nahakura, amma meyake faruwa? Nasan dai duk yanda akayi akwai abinda ke faruwa daku”

“Ehh mami da akwai, bashin banki yaya yusleem yaci sukuma kin san dokarsu idan baka biyasu ba sai sun sayar da komai naka, to shima yaya yusleem din hakance tafaru kuma lokacin nasan idan kikaji hankalinki tashi zaiyi shiyasa nace mubari tukunna sai zuwa wani lokaci sai mu fada miki…”
.
Tafa hannuwa mami tashiga yi tana salati,

“To garin yaya?”

Kallon yusleem tayi,

“Kai agarin yaya kaciyo bashin banki batare da sanina ba?”

“Mami tsautsayi da kaddara, saboda dama tun asali da wannan bashin nasu nayi arziki, komai da kika sani nasune, nikuma nayi hakanne dan incika burinki inzama mai wadata kamar yadda kike muradi…”

Katse shi mami tayi cikin fada tace,

“Ungo nan..” Dakuwa tayi masa sannan ta dora da cewa,

“Shikenan kuma dan ina son kayi arziki sai kaje ka aikata ba daidai ba? Ai ni bance kayi kudi kota halin kaka ba, haba yusleem meyasa zakabi shawarar zuciya? Ko dan gaba karka sake aikata makamancin wannan, yanzu da ace sun kamaka sunje sun daureka me gari yawaya?”
.
Dan zamewa yayi ya jingina bayanshi da jikin kujerar ya lumshe idanuwansa,

Kallon Hafsat mami tayi,

“Bashida lafiya ko?”

“Ehh mami amma da sauki, matsalar dai baya iya cin abinci”

Shiru mami tayi ta danyi tagumi,
.
“Hakika wannan wata jarrabawa ce daga Allah, domin ni dinma duk kudaden dake cikin account dina na turawa yan makaranta domin sun kusa dawowa, gashi na sissiyo kayan abinci wadanda zasuyi mana 1 month,ma’aikatan gidan nan ma wallahi wannan watan ko albashi ban biyasu ba nace suyi hakuri sai yusleem yadawo..”

“To ai babu komai mami duk wannan ba wani abu bane Allah zai bamu mafita” inji Hafsat,

“To hafsa rashin lafiyar tashifa? Ni duk ita tafi daga min hankali”

“Mami babu komai insha Allah zai samu lafiya, gobe zamu sake komawa asibitin ma ayi masa test…”
.
“To wai menene ke damunsa?” Mamin ta tambaya cikin damuwa,

“Mami harda ulcer dai saboda baya cin abinci wallahi”

“To Allah yabashi lafiya, goben sai muje asibitin mugani”

Shi dai yusleem yana jinsu baiyi magana ba da zaman kujerar ya isheshi ma dakin surayya yashiga wanda yake makotaka da na mami yaje ya kwanta akan gadonta,

Ita kuma mami afalo duk tabi ta damu sai jajanta rashin lafiyar yusleem takeyi, Hafsat dince ma mai karfin halin kwantarwa da mamin hankali tana cewa babu komai,

Saida lokacin salla yayi sannan Hafsat ta dauki kayanta ta nufi bedroom din surayya, akwance ta samu yusleem amma ba bacci yakeyi ba,

“Yaya yusleem tashi kayi salla…”
.
Tashi yayi yana kallonta,

“Hafsat meyasa baki fadawa mami gaskiyar abinda yafaru ba? Saboda ko dan nan gaba ya kamata ace tasani”

Zama tayi kusa dashi,

“A’a yaya yusleem fadar bata da alfanu hakan dai da akayi shine daidai”

“Shikenan..” Abinda yace kenan yatashi zai fita, bin bayanshi tayi zuwa falo ta dauki trolley din kayanshi tabishi, part dinsu Abdul ya bude yashiga, bedrooms biyu ne aciki sai falo domin suma samarin kowa da dakinshi, dakin khalifa yashiga tana biye dashi, juyawa yayi ya kalleta,

“Wai kina nufin ke adakin surayya zaki zauna?”

“Ehh mana”

Murmushi yayi ya karbi trolley din hannunta,
.
“Ashe dama karya kike da kikace bazaki iya kwana babu niba..”

Murmushi ne ya kwace mata tajuya zata fice yayi hanzarin rikota,

“Debo kayanki kidawo nan”

“Tohm” ta amsa amma bawai aikatawar zatayi ba domin tana jin nauyin mami ba kadanba,

Sakinta yayi tafita shikuma ya nufi cikin toilet.

Koda takoma part din mami salla tayi tafito falo nan ta hango kuku yana shirya lunch akan table, fitowar mami ne ya katse mata tunaninta,

Kan table suka hau, fried spaghetti da salad kukun yadafa sai kunun shinkafa, suna ci suna hira har suka gama, kunun Hafsat ta dauka tatafi kaiwa yusleem ko zai iya sha,

Akan carpet din salla ta sameshi yana tura sako ta email dinshi ackin laptop,

“Yaya yusleem ga kunu..”
.
Dagowa yayi ya karba ya dan kurba, zama tayi agefen gado, babu laifi yadan sha kunun ganin haka yasa taji dadi sosai, maganinshi ta dauko mishi ya karba ya hadiya daga nan tatashi tafita.

Wayarta ta Kunna bayan ta koma, ko minti biyu ba ayiba Ummi takirata, cikeda zumudi ta dauka suka gaisa nan take fadawa ummin cewar yau suka dawo amma suna gidan mami,

Suna gama waya da ummin kiran Amina yashigo, ita dinma korafin bata samunta awaya tayita yimata gashi ta jima da haihuwa mijinta yanata zuwa gidan domin yafada mata amma baya samunsu, Allah yaraya Hafsat tayi mata tace sunyi tafiya ne amma tunda sun dawo tana nan zuwa,

Komawa wurin mami tayi bayan sunyi sallama da Amina, nan take fadawa mami yusleem yadan sha kunun da takai masa tunda hakane zata rinka dama masa kullum.

Misalin karfe 8:30 nadare suna zaune afalo suna kallon tashar zee world itada mami sai gashi yashigo da cup din kunun data kaimasa, zama yayi yasoma kurbar kunun, Hafsat da mamine ke dan yin hira lokaci zuwa lokaci yana zaune yana jinsu,

Yana kallo hafsat ta shige daki bayan tayi musu saida safe, itama mami ba ajima ba tashiga nata dakin suka barshi afalo shi kadai, sai wurin 11 yakashe tv da sauran kayan wutar dake cikin falon, dakin surayya wadda Hafsat ke ciki ya shiga ya maida kofa ya rufe, gani yayi harta jima da yin bacci, bargon yabude yashiga yayi kwanciyarshi tareda mannuwa ajikinta.

Said a asubah sannan Hafsat tasan yana cikin dakin, tashi tayi tashiga bathroom tayi alwala tafito, ahankali tafara tashinsa saboda bata son mami ta jiyo,
.
Tashi yayi yana lullumshe ido alamun baccin bai isheshi ba,

“Yaya yusleem katafi saida safe…”

Hammar da yafara ya karasa sannan ya kalleta,

“Ina zan tafi?”

“Masaukinka…”

Baice komai ba yasauka daga kan gadon yanufi toilet, lokacin da yafito har ta idar da raka’atanul fijr tana kokarin tada ikamar sallar asubah,

Tashi yayi yakoma kan gadon ya kwanta bayan ya idar da sallar, yana kokarin lulluba da bargo Hafsat ta bazamo tazo tana masa magana kasa kasa,

“Dan Allah yaya yusleem katafi..”

“Ina?”
.
“Dakinka mana, bana son mami tazo taganka”

Kafin yabata amsa suka fara jiyo knocking abakin kofa da sauri Hafsat ta diro, maganar mami tajiyo tana cewa,

“Hafsat, Hafsat kitashi asubah tayi..”

“Na’am mami”

“Au ko kin tashi ma?”

“Ehh mami”

“To shikenan..”

Daga nan tajiyo alamun tafiyar mami,hannu ya mika mata yana daga kwance,kafada ta makale ta kwabe fuska, shi dinma hakan yayi kamar yadda tayi,

“Zo dan Allah”

Kan gadon ta hau ta mika masa nata hannun, kama hannun nata yayi yajata ya kwantar da ita yaja musu bargo.

  _Fatan alkhairi ga Hajjaju, Chuchu, Maman sultan, pheey, Maman humy, Anty sis, Dshanty, Reane_Gh,meela adeel,meernah parrot,khadija sadeeq,Billy s fari, Billy s jega, ummu abrar, anty Baraka, Maman mujahid da duk wadanda ban ambata ba, wannan shafin nakune kyauta domin jin dadinku._

*

       ***Misalin karfe 9 Hafsat tafarka daga bacci, juyawa tayi ta kalli yusleem wanda ke rike da hannunta yana kanannade da ita, dakyar ta iya tureshi daga jikinta ta tashi,

Wanka tashiga tayi tafito ta shirya agurguje, falo ta leka tagani ko mami tafito domin sam bata so mamin ta fahimci cewar yusleem awurinta ya kwana, ganin mami bata fito ba sai masu aiki dake faman mopping din falon yasata sakin ajiyar zuciya,

Juyawa tayi tasake komawa cikin dakin, tashinsa tasoma yi tana dan bubbuga gefen pillow din da kanshi ke kai,

“Yaya yusleem…,yaya yusleem katashi”

Ido guda daya ya bude ya kalleta,

“Me zan yi miki?”

“Safiya fa tajima dayi dan Allah katashi”
.
Mayar da idonshi yayi ya rufe yajuya mata baya yasake jan bargo ya lulluba, tashi tayi tafita, kuku ta hango yana jera musu breakfast akan dining,

Zama tayi acikin falon tama rasa me zatayi, ajiyar zuciya tayi aranta tana fadin dama matsalar gidan masu kudi kenan ko katashi da wuri karasa abinda zakayi,

Tana nan zaune tana kallon shirin gari yawaye a tashar arewa 24 har mami tafito, kamar kullum mamin tasha kwalliya kamar me shirin zuwa gidan biki,

Sauka kasa tayi tagaida mami, cikin fara’a da sakin fuska mami ta amsa domin tana jin son Hafsat tamkar na yar da ta haifa,

Kan dining suka dunguma suka fara karyawa,suna daf da gamawa mami ta kalleta tace,

“Shi wannan sarkin baccin bai tashi bane? Ai da yatashi saboda maganar zuwa asibitin ko”

“Ehh gaskiya kam, bari nagama sai inje in tasoshi..”

Kafin Hafsat ta rufe baki sai gashi ya bude kofa yafito yana yamutsa fuska, sunkuyar da kai Hafsat tayi kamar ruwa ya cinyeta, mami kuwa dubanshi tayi ta kawar da kai,

“Ka manta da maganar zuwa asibitinne kaki tashi da wuri?”
.
“Wallahi ina sane mami, ban manta ba” yakarasa maganar yana kallon Hafsat ta gefen ido wadda yasan ba haka tasoba,

“To ai sai kaje kashirya..”

Wucewa yayi yafita zuwa part din su khalifa, wanka yayi yafito ya zauna domin shafa mai, yana zama Hafsat tashigo hannunta rikeda jug dan madaidaici,

“Ga kunun…”

“Babu gaisuwa?”
.
Yafada lokacin da yake shafa man a hannayenshi,

“Ina kwana?”

“Ni bazan amsa ba, zo nan..”

Dan sake matsawa tayi tana kallonsa,

“Gani..”

“Kinsa Mamie tana yimin fada ko, bayan kuma kece kikayi sanadiyyar makarata saboda dumin jikinki da naji”

Juyawa tayi zata fita daga dakin fuskarta dauke da murmushi,

“Zo nan, Allah karki fita”

Dawowa tayi ta tsaya, tana nan tsaye har yagama shiryawa ya dauki kayanshi yasa,
.
Kunun da ta Kawo mishi yasha sannan suka fita domin Tafiya asibiti,

Afalo suka iske mami cikin shiri nan suka dunguma domin tafiya amma kuma suna fitowa compound din gidan sai ga motar khadija ta kunno kai kuma tareda mahaifiyarta suke wannan dalilinne yasa mami fasa zuwa asibitin tace da yusleem da Hafsat kawai suje driver yakaisu ita kuma takoma ciki itada hajiya fa’iza da khadija,

Ganin irin gaisuwar da yusleem sukayi shida khadija yasa Hafsat yimasa magana domin daurewa khadija fuska taga yakeyi bayan kuma ita bataga laifinta ba, ganin baya son maganar yasata yin shiru ta kyaleshi.

Lokacin da sukaje asibitin Hafsat kin shiga office din dr sufyan tayi tai zamanta awaje sai yusleem ne yashiga shi kadai, ya dan jima aciki kafin yafito,

“Yaya yusleem ya kukayi?”

“Yace nanda 4 days nakara dawowa lokacin result din taste din da yayi min yafito..”

“To Allah dai ya jiyar damu alkhairi”
.
“Amin, muje mu tafi gida tunda babu abinda yayi saura, Dr din yana tambayarki wai yau banzo da matata ba nace tare ai muke kina waje wai ai dama yasan bazaki barni nazo ni daya ba…”

Dan murmushin yake tayi batace komai ba amma acikin ranta fadi take “Dan iskan Dr”,

Lokacin da suka koma gida sai mami ita kadai domin su khadija sun tafi, ganin sun dawo da wuri mami tace Hafsat ta shirya taje driver yakaita gidansu tagaisa da iyayenta,

Garin dakakkiyar busasshiyar kubewa da kuka da daddawa wanda Maman khadija ta Kawo wa mami su mamin tabawa Hafsat tace takaiwa umminta tsaraba,
.
Yusleem yana kwance akan kujera mami na kujerar kusa dashi Hafsat din tafito zata tafi,

“Mami idan nadawo zan biya ta gidan amina kawata, haihuwa tayi shine zanje inga babyn..”

“To sai kin dawo, Allah ya raya.. Ki gaida hajiya kubran”

“To mami zataji”

Fita tayi nan yusleem yatashi yabita, tana daf da fita daga cikin kitchen yayi saurin rikota,

“Mami zaki tambaya unguwa saboda itace take aurenki ko? To gidanku kadai na amince kije daga nan karkije ko ina”

Juyawa yayi zai koma falo tayi saurin rikoshi,

“Dan Allah kayi hakuri yaya yusleem.. Kaji”

Shiru yayi mata ita kuma taci gaba da yimasa magiya, dakyar ya amince yace taje.

Acikin kitchen ta iske Ummi lokacin dataje gidan, ba karamin dadin ganinta hajiya kubra tajiba nan suka baje suka fara hira irinta uwa da ‘ya da haka har Alhaji sa’id yazo ya samesu yadawo daga buga bugarsa domin shima ya haduda jarrabawa irinta rayuwa sai dai  ita Hafsat bata saniba har saida ummi tayi mata bayanin abubuwan da suka faru na iftila’in da ya afkawa alhaji sa’id din bayan ya sayar da kadarorinsa ya tura asiyo masa kayayyaki amma har yau kayan basu fitoba gashi saboda rashin kudi kwangilar ma ba samuwa takeyi ba dan dai kawai yanada amini ne mai fada aji,
.
Kuka Hafsat tayi ba kadanba dalilin jin wannan labarin da hajiya kubra ta bata amma kuma tasan jarrabawa ce daga Allah shiyasa ma bata daga hankalinta ba,

Dayake sun dade basu hadu da umminba yasa Hafsat takasa tafiya da wuri har saida aka kira sallar magrib, bayan tayi sallane tatafi  lokacin driver yazo daukarta, ko gidan aminan ma bataje ba gida ta wuce direct,

Mami kadai ta tarar afalo tana waya da surayya nan ta zauna har mami ta kammala wayar itama tabata suka gaisa domin rabonsu da juna tun lokacin da surayyan takoma school,

“Hafsa kin dawo? Ya kika baro mutanen gidan?” Mami ta tambaya tana kokarin ajiye wayarta,

“Lafiya lau mami, suna nan lafiya, Ummi tana gaidaki tace ayi miki godiya…”

“Babu komai wallahi, kayan ma nawa suke..”
.
Zama sukayi dan shiru suna kallon tv zuwa can Hafsat ta mike ta nufi bedroom, tana shiga ta iske yusleem akwance,

“Lafiya kuwa yaya yusleem?” Ta tambaya,

“Wallahi zazzabi ke damuna hafsa”

Ahanzarce takarasa kusa dashi jin jikinsa zafi zauuu tayi gashi yana dafe da cikinsa wanda ke ta faman murda masa,sannu ta shiga yimasa yana amsawa dakyar, zuwa can taji ya kamo hannunta ya dora akan cikin nasa,

Jikinta rawa yafara saboda ganin yanda yusleem yake yin murkususu gashi bata son taje tafadawa mami hankalinta yatashi,
.
Ruwan sanyi ta dauko tasoma shafa masa acikin nashi nan yaji ciwon yafara lafa masa ahaka har bacci ya daukeshi, ganin yasamu bacci yasa ta fita wurin mami wadda take zaune akan abin salla ta idar da sallar isha tana jan carbi,

“Hafsa ga tuwo can, wallahi yau shi naji ina sha’awa shine nace kuku yayi..”

Murmushin yake Hafsat tayi ta girgiza kai,

“Kafin nataho ma agidan Ummi saida naci abinci,wallahi na koshi..”

Wuri tasamu ta zauna amma lokaci zuwa lokaci tana dan shiga bedroom din taduba yusleem sai dai har 10 tayi bai tashiba, har sukayi sallama da mami tashiga dakinta itama ta shiga daki yusleem bacci yake,

Akusa dashi ta kwanta tana kallonshi yana rike da cikinshi, sai wurin 11 sannan yatashi yayi sallar magrib da isha wadanda ke kanshi domin bai samu damar yiba,
.
Kalau yayi sallar ya idar tana zaune tana kallonshi yana idarwa kuma yace sai ta dama masa kunu yasha yunwa yakeji, tare suka fita zuwa kitchen din ta tafasa ruwa ta dama masa kunun suka koma daki, saida yagama sha sannan suka kwanta, tana ji yafara tsokanarta kamar bashi bane dazu yake murkususu kamar zai mutuba,
.
Bata San lokacin da yagama tsokanar tataba domin bacci tayi tabarshi, can tsakiyar dare kuma kamar acikin mafarki take jin kakarin amai nan tatashi taganshi kwance yana juyi yana rikeda cikinsa, ruwan sanyi ta debo tafara shafa masa amma yanzu ji yake kamar ruwan zafi tafasasshe take Shafa masa, kunun da yasha kuwa saida yayi amansa gaba daya,rikeshi tayi nan ya kuwa kankameta kamar zai koma cikin cikinta daga shi har ita babu wanda yasake runtsawa har asuba tayi ita dai agaba tasashi tana hawaye,
.
Ganin abin yayi yawa gashi yana yin wani irin amai kore kore yellow yellow yasa hafsa zuwa ta sanarwa da mami lokacin karfe 5:30,

Driver mami tayiwa waya kasancewar a B/Q yake zaune, nan da nan yafito suka kama yusleem suka nufi asibitin Dr sufyan dashi,

Kallo daya zaka yiwa mami da Hafsat kagane acikin tashin hankali suke domin kowannensu fuskarshi kunshe take da tashin hankalin,

Emergency aka kai yusleem bayan kamar mintuna 30 Dr mufid yafito dauke da file din yusleem domin lokacin Dr sufyan bai fitoba,binsa mami da Hafsat sukayi abaya domin jin abinda zaice,

“Hajiya in my opinion ni ina ganin cewar is better for u idan kuka fitar da patient dinku kasar Cairo ko kuma India saboda sincerely speaking yana cikin bad condition domin cutar dake tattare dashi itace take cousing din wannan ciwon cikin da yake fama dashi, and kuma akwai wani aiki da zasuyi masa wanda mu bazamu iyaba, so idan zai yuyu in the next 3 days ku samar masa visa sai ku fita dashi domin magana tagaskiya bama karbar patients wadanda lalurarsu tazama chronic kuma worst saboda kinga nan is private hospital dole sai mun zama muna him takatsantsan…”

Yana ida wannan bayanin yagyara farin glass dinshi yayi gaba, sororo mami da Hafsat sukayi kowannensu yana tunanin hanyar da za abi har akai ga fitar da yusleem kasar waje….Daga mami har Hafsat ji sukayi kamar ruwa ya cinyesu dalilin jin bayanin da dr yayi musu nan hankalin kowanne acikinsu yakai kololuwar tashi,

Mami ce tafara magana fuskarta cikeda murmushin yake,

“Hafsat babu komai kinji, karki daga hankalinki insha Allah zamu samu yanda zamuyi…”

Wasu hawaye ne suka zubowa Hafsat tasa gefen hijabinta ta share batare da tayi magana ba,

Kama hannunta taji mami tayi suka bar wurin suka koma reception,

“Yanzu Hafsat ina zuwa bari naje gida nadawo kinji…”

“To mami sai kin dawo, Allah kiyaye hanya..”

Tashi mami tayi tafita, yayinda ita kuma Hafsat taci gaba da zama awurin zuciyarta kunshe fal da tarin tunani.

   Tana nan zaune tarasa abinda yake mata dadi tahango dr sufyan yana kokarin shigowa cikin reception din hannunsa dauke da wata yar madaidaiciyar bag, ko kallonsa batayi ba ta dauke kanta takaishi can gefe, shikuwa kura mata ido yayi har ya bace ya nufi office dinshi,
.
Kimanin mintuna 30 da tafiyar mami sai gata ta dawo, tun kallon farko da Hafsat tayi mata ta fahimci cewar akwai damuwa a tattare da ita amma dai sai batayi magana ba domin daga ita har mami din kowa ba son yin maganar yake ba,

Emergency suka shiga wurin da yusleem ke kwance yana bacci, gaban gadon sukaje suna kallonsa,

“Ni wannan abu ya daure min kai, wai menene takamaimai abinda yake damunsa ne? Ni duk ban fahimci bayanin da Dr yayiba hafsat…” Mami tayi maganar idanuwanta na kan yusleem wanda yake kwance yana fitar da numfashi,

“To nima dai mami maganar dr ta daure min kai amma a iya sanina dai wannan ciwon cikin shine ke damun yaya yusleem”

“To ko komawa zanyi wurin Dr din insake tuntubarsa inji?”

“A’a mami da dai mun hakura kawai munyi yanda yace din..”

“To yanzu hafsat ina zamu samu kudaden da zamuyi hakan? Hafsat yanzu ba babu abinda muka mallaka inbanda wannan motar kwaya daya da nake hawa sai ko gidan da muke ciki…”

“Babu komai mami ki kwantar da hankalinki insha Allah komai zai zama daidai saboda Allah baya taba dorawa bawansa abinda bazai iyaba”

Ajiyar zuciya mami ta yi suka fita daga cikin emergency room din suka koma waje suka zauna,

Wuni guda cur yusleem yana bacci sai yamma yafarka, hafsat ce ta karasa wurinsa domin ita mami tatafi gida ta dawo wanda tafiyar tata bazata rasa nasaba ba dayin wanka sannan da shiryo abinci,

“Sannu yaya yusleem..”

Kai ya daga mata ya lumshe idanuwansa,

“Yaya yusleem zaka sha kunun?”

Girgiza mata kai yayi bayan ya bude idonsa, kicin kicin yaga tayi tabata fuska kamar zata saka kuka, ganin haka yasashi daga mata kai alamun zaisha,ita kanta tana lura dashi sam yanzu baya son yaga bacin ranta,
.
Dan murmushi tayi ta tsiyayo masa kunun acikin cup ta zauna agefen gadon, yunkurawa yayi yafara kokarin tashi ta taimaka masa, duk da cewar dakin basu kadai bane akwai mutane da yawa aciki amma haka ta rinka bashi abaki yana kurba idan kuma ya disa sai ta lashe, kallonta kawai yake yi da idanuwanshi wadanda suka dan firfito har tagama bashi duk da dai bai shanyeba amma yadan sha dayawa,

Taimaka masa tayi ya kwanta ta gyara masa kwanciyar, ta zauna tana kallonshi, hannunta taji ya riko acikin nashi tareda lumshe idanuwanshi ahaka har wani baccin ya sake daukarshi.

Zuba mishi ido tayi takai hannunta bisa kuncinshi tasoma shafawa ahankali tana jin wani irin tunani yana ratsa zuciyarta, ahaka Mami ta dawo ta isketa jikinta sukuku wanda daga gani ranta abace yake gaba daya,

Jugum sukayi babu wanda yake yin magana acikinsu har tsawon wani lokaci domin kowa shi yasan tunanin da yakeyi,sai can Mami tayi karfin halin yiwa hafsat magana,

“Hafsa kitafi gida kije kiyi wanka sai kidawo..”

Duk da bata son tafiyar amma bata musawa Mami ba haka tayi mata sallama tatafi bayan ta leka yusleem ta window nan taganshi har lokacin bacci yakeyi ga drip nan ahannunshi wanda ba ajima da daura masa ba domin duk jikinshi yayi yaushi,

Mami saida ta tabbatar da cewa hafsat tatafi sannan tatashi ta nufi office din Dr sufyan,

Kimanin mintuna samada arba’in mamin ta shafe acikin office din na dr sufyan sannan daga bisani tafito, tana zama hafsat nadawowa,
.
Zama suka cigaba dayi har zuwa dare, lokacin ne aka fito da yusleem daga emergency aka kaishi wani daki wanda gado ne guda daya aciki irin na marassa lafiya sai fridge dan karami sannan ga yar karamar tv nan daure ajikin bango sai dan madaidaicin bathroom aciki,

“Hajiya wannan dakin kwana uku kadai zamu bashi muna treating dinshi domin dama narigada nafada miki cewar fitar dashi outside shine kadai solution agareku, therefore nan da 3 days zamu baku sallama so sai kuje gida kuci gaba da kula dashi idan kuma before time din kun sami kudin fitar dashi outside sai ku fitar dashi..” Dr mufid yafada yana sunkuye yana rubutu ajikin file din yusleem,

Kallonshi Mami da hafsat sukayi har ya kammala jawabin sannan yafita,

“Hafsat wuce kije kitafi gida ki kwanta inyaso idan Allah ya nuna mana gobe sai musan abinyi..”

Girgiza kai hafsat tayi ta kalli mami,

“A’a Mami kibarni anan din ke kitafi gida, ni zan kwana tare dashi..”

“Hafsat kije ki huta kinji, babu komai”

“Dan Allah mami kibarni kitafi, wallahi ko naje gidan ba iya barci zanyi ba”

“To shikenan tunda kinki, bari ni naje natafi, Allah yabashi lafiya”

“Amin mami”

Saida mamin tasake duba yusleem din sannan tayiwa hafsa sallama tatafi,tana fita harabar asibitin tahango dr sufyan tsaye ajikin motarshi kirar Benz new series 2017 yana sanye cikin kananan kaya, wurinshi mami takarasa dama abisa dukkan alamu ita yake zaman jira, bude mata kofar motar yayi tashiga tazauna sannan yazagaya side dinshi bayan yarufe yaja motar suka bar harabar asibitin.
.
Cikin dakin hafsat tashiga ta zauna akan wata kujera tana kallon yusleem wanda keta faman barci, lokaci daya ta tashi zunbur ta isa gefen gadon ta zauna, bude idonshi taga yayi,

“Sannu yaya yusleem”

Kai ya daga mata sannan yadanyi murmushi,

“Yaya yusleem ko kana bukatar wani abu ne..?”

Kanshi ya girgiza har lokacin fuskarshi tana dauke da murmushi, shiru tayi ta dan jingina da jikin bango, gyangyadi ta dan soma yi amma da zarar baccin yafara daukarta zatayi firgigit ta bude idonta,

Matsawa yusleem ya danyi yakamo hannunta, idonta Wanda yake cike da barci ya bude domin daren jiya bata samu tayi ba,

“Kizo ki kwanta…”

“Bari inshinfida hijabina akasa kawai sai in kwanta saboda kar intakura maka”

“Gashi na matsa miki”

Girgiza kai tayi zata sauka daga kan gadon, tashi shima yayi da niyyar sauka tayi saurin rikeshi,

“Haba yaya yusleem kaida bakada lafiya,dan Allah kakoma ka kwanta”

Dakyar ya kwanta din hannunshi rikeda ita dole ta hakura ta kwanta akusa dashi,
.
Sassafe saiga mami tazo, office din dr sufyan tafara zuwa amma lokacin bai fitoba, wurinsu hafsa taje, hafsat din tana zaune akan kujera shikuma yusleem yana kan gado akwance,

Tare da mamin suka cigaba da zama har karfe 9 tayi lokacinne driver yakawo musu abinci amma ita mami bata samu damar cin abincin ba domin hankalinta yana can office din Dr sufyan, hajiya kubra da alhaji sa’id ne suka zo duba yusleem din bayan an dan gaggaisa mami ta zare jikinta ta fita, office din Dr sufyan tashiga wanda yake abude alamun yana ciki,

Lokacin da hafsat tafito domin raka su hajiya kubra sukayi kicibus da mami, godiya mami tayiwa su hajiya kubra sukayi sallama suka wuce ita kuma tanufi dakin da yusleem yake,

Hafsat kam saida ta rakasu har wurinda motarsu take sannan tajuya ta takoma, tana shiga cikin dakin ta iske mami tana shirya kudi rafa rafa sabbi kal yan dubu dubu acikin jakarta wadanda zasu doshi samada naira dubu dari tara, cikeda mamaki hafsat ta karasa gaban mami wacce ke zaune akan kujera…..

  _Fans kuyi hakuri da jina shiru da kukayi kwana biyu, kun san jiki da jini amma alhamdulillah naji sauki sosai, hakika bani da bakin da zan gode muku,duk wadanda suka kirani suka gaisheni da wadanda suka min text nagode Allah yabar zumunci._

*
Gaban Mami hafsat takarasa ta tsugunna fuskarta cikeda mamaki,

“Mami wannan kudin fa?”

Fadada murmushi mami tayi batare da ta dago ta kalli hafsat ba domin hankalinta yanaga kan kudin da take lissafawa,
.
“Hafsat wani al’amari ne ya gudana wanda yayi sanadiyyar samuwar wannan kudin, kinga dr kwana uku kacal yabamu yace daga nan sallamace zata biyo baya to shiyasa naga gara fa intashi atsaye innemo kudi duk inda yake domin mu fitar da yusleem kasar Cairo..”

“Hakane mami, amma yanzu kin san kudi yana wuyar samuwa shiyasa nace garin yaya aka samo wadannan kudaden masu yawa..”

Rufe handbag din mami tayi ta maida hankalinta gurin hafsat da niyyar yimata bayani amma kafin takai ga farawa sukaji anturo kofar dakin da suke ciki anshigo, dukkaninsu maida idanuwansu wurin sukayi domin ganin wanda zai shigo,

Khadija ce ta shigo hannunta rikeda basket din abinci, tana sanye cikin bakar doguwar riga ta yane kanta da mayafin rigar inbanda kamshi babu abinda take zubawa,

“A’a khadija ce? Sannu da zuwa” mami tayi maganar tana fadada fara’arta,

“Yawwa sannu mami” khadija tafada tareda ajiye basket din hannunta ta durkusa kasa tagaida mami,

“Mami ina kwana? Ya mai jikin? Allah yabashi lafiya”

Cikin raha mami ta amsa gaisuwar, kallon khadija hafsat tayi tayi mata sannu da zuwa sannan suka gaisa,
.
Gaban gadon yusleem khadija takarasa amma har lokacin bai tashi daga bacci ba dan haka tadawo wurinsu mami ta zauna suka cigaba da zaman tare,

Zuwa can bayan yan wasu mintuna nurse tashigo ta dan dubashi tayi rubutun da zatayi tafita, fitarta babu wuya yusleem din yatashi, idanuwansa fess yasaukesu akan hafsat wacce ke zaune kusa da khadija, ita kuma khadijan sai danne dannenta takeyi awayarta,

Tashi hafsat tayi taje wurinda yake itada mami,

“Hafsat taimaka min inje bathroom..”

Ba iya hafsat dince kadai ta rikeshi ba harda mami suka taimaka mishi yasauko daga kan gadon suka rirrikeshi,

Tasowa khadija tayi tana cewa mami,

“Ayya mami barshi, kawo intayata..”

“Lahh babu komai khadija da kinyi zamanki kin huta” inji mami,

“A’a mami dan Allah barshi kije ki zauna”

Hade fuska yusleem yayi bai bari khadijan takai ga rikeshi ba yafada cikin toilet, dukkansu sororo sukayi banda khadija da ke yin dan murmushin yake,

Dukkansu komawa sukayi suka zauna hafsat ce kadai ta tsaya tana jiran yafito, bai jima sosai ba yabude kofa yafito yana faman bin bango, rikeshi hafsat tayi har zuwa gefen gadon,

“Salla fa nake son yi” yace da hafsat,

“To bari in shimfida maka dan kwalina sai kayi..”
.
“A’a inada carpet acikin mota bari inkawo..” Khadija tace sannan ta mike tafita, dan satar kallonshi hafsat tayi har lokacin fuskarshi kicin kicin take babu walwala,

Karbar dardumar hafsa tayi bayan khadija ta Kawo ta shimfida masa,yahau yatada salla,

Tashi yayi yakoma kan gadon bayan ya idar da salla, gaishe da mami yayi tai masa sannu sannan suka gaisa da khadija,

Tea Hafsa tatashi ta hada masa takai masa,

“Yaya yusleem wannan bata fuskar duk na menene? Ka saki ranka mana”

Hannunta yariko tareda cup din ruwan zafin yana dan murmushi,

“Ai kece kika sani yin fushin..?”

“Saboda me?” Tafada tana dan zame hannunta daga nashi,sake rike hannun yayi yaki saki,

“To ai gani nayi kunyi min rufdugu alhalin ke daya ma zaki iya rikeni…”
.
Murmushi tayi ta dan kalli wurin dasu mami ke zaune nan taga hankalinsu ma kwata kwata ba akansu yakeba domin hirarsu sukeyi itada khadija,

“Yaya yusleem kenan…”

Cup din da hannunta yahada yarinka kaiwa tea din bakinsa yana kurba har yakusa kammalawa, muryar mami ce ta katsesu,

“Hafsat ina zuwa bari mu fita tareda khadija tayi dropping dina saboda ayau zuwa gobe nake so agama komai na tafiyar yusleem ban son abun yadauki lokaci..”

“To shikenan mami sai kin dawo, Allah yasa adace”

Sallama sukayi da khadija suka fita tareda mami, kwanciya yusleem yayi ya tallafe kumatunsa da hannunsa guda daya yana kallonta,

“Kici abincin ki tayani wanka”
.
Sunkuyar da kanta tayi taci gaba da tsiyayo tea acikin cup,

“Uhmm, ko bakiji ba?”

“Naji yaya yusleem”

Ido ya tsura mata lokacin da tafara kurbar ruwan tea din, ganin ya kafeta da ido yasata tashi ta bar wurin ta matsa can nesa dashi, murmushi yayi ya lumshe idanuwansa.

Tunda mami tatafi bata samu dawowa ba har yamma abincima sai khadija ce takawo musu kuma yanzun ma kamar da safe bataga sakin fuska awurin yusleem ba amma hafsat ita kam ta karbeta hannu bibbiyu domin bataga aibunta ba,

Alla Alla hafsat tarinka yi mami tadawo domin ta kosa taji hanyar da mamin tabi tasamo makudan kudade haka masu wuyar samuwa.

Mami bata samu dawowa ba sai bayan sallar isha, lokacin Dr yazo ya rubuta musu sallama bayan mami ta bibbiya kudaden da yakamata su biya asibitin,
.
Driver ne ya daukesu suka nufi gida kuma dama jikin yusleem din yadanyi sauki ba kamar ranar da sukazo ba domin yanzu ko aman yadaina,

Afalo suka zauna dukkaninsu hafsat tagama matsuwa da son jin abinda mami zatace amma taji mamin tayi shiru sai lissafe lissafen kudi taketa faman yi,

“Yusleem nasamu munyi nasara komai ya kammala insha Allah nanda kwana biyu zaka tafi kasar Cairo domin ance visa din kasar tafi saurin samuwa fiyeda ta kasar India..”

“To mami Allah yasaka da alkhairi Allah yakaimu lokacin”

“Amin, Allah yasa asamo abinda akaje nema Allah yabaka lafiya”

“Amin mami, bari inyi wanka” yace da mami bayan ya mike yana yiwa hafsat kallon zo ki rakani, taganshi sarai amma saita dauke kanta tayi kamar bata ganiba dolenshi yajuya ya fice shi kadai,

Bayan fitarshi hafsat ta kalli mami,

“Mami kodai gwala gwalanki kika siyar?”

Dakatawa mami tayi daga yin abinda take ta kalli hafsat,

“Hafsa ai ni yanzu banida gwalagwalai, jiya  darana bakiga nakoma asibiti raina abace hankalina atashe ba?
.
Wallahi infada miki dawowa nayi na iske safe dina wurin da nake ajiyar gold din abude an kwashe babu komai aciki, koda nakira mai gadi na tambayeshi sai yace min wai bakuwa nayi kuma yace mata babu kowa agidan amma tace ehh zata shigo ta jirani, ban san wacece ba amma duk yadda akayi itace ta sace min wadannan gold din kuma dama iya saiti daya gareni sauran duk nasayar bana gasken bane..”

Zaro ido hafsat tayi saboda jin satar da akazo har gida aka yiwa mami,

“Mami Allah ya kiyaye gaba, Allah yamayar miki da alkhairi, yanzu kuma ya akayi?”

“Shine naje nasamu shi shugaban asibitin wannan yaron sufyan nace masa zan sayar da kodata (kidney)guda daya sannan suma su khalifa shida Abdul idan sun dawo za aciri tasu guda dai dai tunda dama guda dayace ke amfani ajikin dan adam..”

Zabura hafsat tayi ta zazzaro ido, cikin rawar baki tace,

“Haba mami, ya za ayi kisayar da kododinku? Ai bai kamata dan za agyara wani kuma abata wani ba..” Takarashe maganar hawaye nabin kuncinta,
.
“Ai magana takare hafsat tunda shima sufyan din yabani shawara ta hanyar cewar idan inada wata kadara kamar gida ko fili gara insiyar akan insaida kodata data yarana, to kinga yanzu bamuda wasu kadarori inbanda wannan gidan kwaya daya shine yace to mahaifinsa zai sai gidan kuma insha Allah zaiyi mana taimako ta hanyar bamu aron gidan muci gaba da zama har zuwa ranar da zamu mallaki namu,adaren jiya mukazo muka ga gidan bayan ya debo dillalai kuma sunyiwa gida kudi, ansiya miliyan daya..” Mami takammala maganar tana dan murmushin yake domin zuciyarta wani zafi takeyi mata.

Hafsat ji tayi tasamu yar nutsuwa saboda jin bayanin mami,

“Allah ya rufa asiri mami, Allah yasa adace kuma”

“Amin hafsat, kinga yanda rayuwa ta juya mana ko? Mun kawoki kinata faman shan wahala”

“Dan Allah mami kidaina fadin haka, ai yanda Allah ya tsara min kenan..”

“Allah yayi miki albarka, insha Allah gobe zamu yi signing atakardar gidan daga nan sai inbasu copy..”
.
Shiru hafsat tayi tana jin tausayin mami yana kwaranya acikin ranta domin tasan karfin hali kawai mamin keyi amma ita kadai tasan yanayin da take ciki,

Ganin mami ta tashi tashiga cikin bedroom dinta yasa itama hafsat tatashi tashiga dakin surayya,

Kayan jikinta ta cire tashiga wanka, lokacin da tafito ta hangi yusleem kwance saman gado yayi d’ai d’ai, hijabinta ta janyo ta saka tana kallonshi, shi dinma juyawa yayi yana kallonta daga kasa har sama……

*
D’auke kanta tayi daga kallon yusleem taje gaban mirror tafara shiryawa, shikuwa sai faman binta da idanuwa yake domin duk wani motsi da zatayi akan idonshi ne,

Tashi tayi da niyyar ta dauki kaya tasa amma ganin ya kafeta da ido yasata shiga bathroom tasa kayan sannan tafito,

“Yaya yusleem dan Allah katashi katafi,ni wallahi bacci nakeji, kaga dai 2 days banyi bacci ba…” Tafada cikin shagwaba bayan ta zauna agefen gadon, hannunta ya kamo yarike cikin nashi,

“To ai yanzu ba hanaki baccin nayi ba, zo ki kwanta”

“Ni gaskiya katafi, bana son mami ta…”

Saurin katseta yayi ta hanyar jawota jikinshi,

“Karyar kunya kikeyi nanah, saboda Kinga mami fa tajima da sanin cewar tare muke kwana tunda ko lokacin da tararmu agidan haya muna zaune adaki daya ta tarar damu ba dakuna biyu ba..”

Jin ya ambaci gidan haya yasa taji Maman amir ta fado ranta,
.
“Kaga kuwa dazu da rana Maman amir ta kirani tana gaisheka tace inyi maka sannu…”

“Ina amsawa kawar Maman amir…”

Murmushi tayi tafara kokarin zamewa daga jikinsa amma ya riketa gam,

“Ba kince bacci zakiyi ba, to kiyi mana”

Shiru tayi domin dama bawai baccin takeji ba ita dai kawai tana kunyar mami tasan anan yake kwana,

“Ya kukayi da mami? Ta fada miki a inda tasamo kudaden nan kuwa? Saboda wallahi sam hankalina yaki kwanciya” yayi maganar cikin raunin zuciya yana shafa kanta,

“Ehh ta fada min yaya yusleem, wannan gidan ta saida kasan lafiyarka tafi komai muhimmanci agaremu yanzu…”
.
“Hakane to amma…”

Katseshi hafsat tayi ta hanyar kai hannu ta rufe masa baki, shiru yayi yana jin yanda take shafar kasumbarshi dake baibaye a fuskarshi,

“Ai yaya yusleem babu abinda yakai uwa dadi, kowacce uwa tana son danta acikin kowanne irin yanayi koda kuwa duk duniya zata ki shi to ita zataso kayanta, kasan meyasa nafadi haka?”

Girgiza kai yayi alamun a’a,

“To da mami kidney dinta tayi niyyar sayarwa da tasu Abdul…”

Gani tayi idanuwanshi sun firfito waje ya yunkura yana kokarin tashi, mayar dashi tayi ya kwanta takoma jikinshi ta dora kanta akirjinsa,

“Ka kwantar da hankalinka ai bata sayar ba, gidan nan ta siyar shine aka samu kudaden da zaka tafi Cairo…”

Ajiyar zuciya yayi yakai hannu ya rungumeta,

“Dole hankalina yatashi hafsat, idan mami da yan uwana suka sayar da kidney dinsu menene ribar? Babu riba at all saboda nan gaba za azo ana facing problems a lot,tunda kinga akwai kidney disease ko wani abu mai kamada haka”
.
“Hakane amma tunda Allah ya takaita abin ai shikenan karka daga hankalinka, Allah yabaka lafiya, ni yanzu babban burina shine inga kasamu cikakkiyar lafiya kamar kowa”

Murmushi yayi ya kamo hannuwanta,

“Kin kosa insamu lafiya ayi wacce za ayi ko?”

Dariya tayi ta boye fuskarta akirjinsa,

“Kai yaya yusleem ni wallahi ba abinda nake nufi ba kenan”

“To me kike nufi?”

“Ni kawai inganka lafiya kadaina wannan zazzabin da amai da ciwon ciki shine kadai burina”

Kanta yafara shafawa yana murmushi,

“Nikuwa kin ga babban burina shine idan nasamu lafiya inbawa matata dukkan hakkoki wanda addini ya rataya min awuyana, sannan inmaidata mace sosai…”

Boye fuskarta tayi tana dariya,

“Kai yaya yusleem..”

“Kai nanah hafsat, da kin zaci zamu zauna ahaka ne? Uhm”

Shiru tayi masa tana dariya har lokacin bata bari yaga fuskarta ba,

“Uhmm?” Yasake tambayarta, shirun tasake yimasa, hannunta yakama yakai bakinsa yayi kissing dinshi, ji tayi ya rungumeta tsam tsam,
.
Kunyace ta lullubeta domin abin na yusleem yau yagirmama duk da dai dama yasaba rike hannunta ko ya dafa kafadarta ko yaja mata yan yatsun kafarta ko kuma yadafa kafadarta amma bai taba yunkurin kissing dinta ba sai yau,

Wasu wasanni masu nauyi yau yake yimata wanda bai taba yimata ba, sun jima cikin wannan yanayin kafin ya rungumeta yana fitar da numfashi ahankali, kwanciya tayi luf ajikinsa da haka har bacci ya dauketa domin dare yayi sosai.

Tunda tafara baccin  ba ita ta tashi ba sai karfe 7,ita kanta tayi mamakin makarar da tayi, dudduba gefenta tayi nan taga babu yusleem babu alamunsa,

Wanka tashiga tayi agurguje tafito tayi salla taci gaba da zama shiru, tana zaune akan abin sallar taji shigowar mami,

“Hafsat yau makara kikayi ne? Naji shiru baki fitoba”

Tashi Hafsa tayi tana ninke dardumar da tayi salla,

“Ehh wallahi mami, ina kwana?”

“Lafiya lau, idan kin shirya kifito ga breakfast nan yana jiranki”

“To mami bari inzo..”

Fita mami tayi ita kuma ta tsaya tana nazarin ta yadda zata fita falo domin bata son su hadu da yusleem, ta dade tsaye akofar dakin tana ta tunani kafin daga bisani tayi kuru tafita,
.
Akan kujera ta hango yusleem kwance yana kallon tv ita kuma mami tana zaune tana hada ruwan zafi,

Kin kallon yusleem tayi taje kusa da mami ta zauna itama tasoma hada ruwan zafin,

“Kai yusleem bazaka yi breakfast din bane?”

“Mami sai zuwa anjima yanzu ruwan zafi kadai zan Sha”

“To bari akawo maka”

Hada masa tea din hafsat tayi ta dauka takai mishi, zaune yatashi yana kallon fuskarta amma saita kawar da tata fuskar,

“Yaya wankan safe…?” Yafadi lokacin da zai karbi cup din, shiru tayi masa tayi hanzarin barin wurin aranta tana tunanin yanda akayi yazama marar kunya tsakanin daren jiya zuwa yau,
.
Misalin karfe 10 nasafe suna zazzaune acikin falon sai ga khadija tashigo, tana sanye da orange colour din atamfa da mayafi kalar atamfar da yar karamar hand bag,

Duba yusleem tayi tatafi bayan sun gaggaisa, bayan tafiyar khadija mai gadi yashigo yace anyi baki wai masu siyan gidane suka zo, mamice tafita bayan ta dauki wasu takardu,

Wasu mutane guda biyu tasamu tsaye a compound din gidan suna jiranta amma yau babu dr sufyan,

“Sannu alhaji, wadannan sune takardun gidan gashi..”

Karbar takardun wani dan dattijon mutum yayi yafara dubawa, yajima yana nazarin takardun kafin ya dago yana kallon mami,

“Hajiya wannan wanda sunansa yake jiki shine mai gidan?”

Jijjiga kai mami tayi,

“Ehh shine yarona ne”

“Yana ina yanzu?”
.
“Yana ciki”

“Zan iya ganinsa?”

“Me zai hana, bisimillah zo mu karasa”

Yusleem yana zaune a falo ya tisa Hafsa agaba yana tsokanarta sai gasu mami sun shigo tashi yayi daga kusa da Hafsa yakoma wata kujerar ya zauna,

“Yusleem ga bakinka” inji mami, cikeda mamaki ya kalli mutanen nan yaga babu wanda yasani acikinsu, zama wannan dattijon yayi ya kalli yusleem,

“Yusleem baka ganeni ba ko?”

Daga kai yusleem yayi alamun eh,

“Zaka iya tunawa shekaru shida da suka wuce kaje neman aiki a wata ma’aikata ta yada labarai? A lokacin anyi maka interview daga baya kadawo akace maka baka samu aikinba”

Murmushi yusleem yayi alamun ya tuna,

“Ok sai yanzu natuna ai dayake shekarun an dan kwana biyu”
.
“To yusleem tun lokacin da kayi interview kasamu wannan aikin kuma abangarena wato department dina, nine nan nahanaka aikinka nace baka samuba amma gwamnati ta daukeka sannan duk watan duniya tana biyanka albashi na naira dubu hamsin da biyar banda allowances d sauran alkhairan da baza arasaba, nine na rinka rike kudin ina harkokin gabana dasu har lokacin da zaka samu promotion daga grade level 9 zuwa grade level 12,haka na rinka ninke kudinka ina kasafin gabana har saida naji wani malami yayi wa’azi akan mutane masu aikata laifi irin nawa, to tun daga nan nasoma binciken hanyar da zanbi insadu dakai inbaka hakkinka da aikinka amma kuma duk lokacin da nakira wayarka bata shiga, daga karshe danaga narasa yanda zanyi inganka sai narinka tara maka albashinka ina ajiye maka kuma ina juya maka acikin kudadena na kasuwanci wanda yanzu haka duk dukiyata tamuce nida kai, kayi hakuri yusleem ka yafe min domin na danne maka hakkinka kuma na cutar dakai…”

Jin maganar yusleem yayi kamar acikin mafarki, bashi kadaiba hatta su mami abin yabasu mamaki mutuka amma kuma duba da irin zamanin da muke ciki yanzu sai mamakin nasu baiyi yawa ba domin yanzu zalunci awurin mutane ba abune mai wahala ba,

“To ai alhaji ni banma san me zance ba domin gaba daya kaina yagama daurewa..” Yusleem yayi maganar yana kallon mami wadda ita dinma shi take kallo zuciyarta kamar kankara dan farin ciki domin arzikin danta da alama yakusa dawowa,
.
“yanzu tashi zakayi kazo muje inkaika kamfanoninmu da gidajenmu da kuma shagunanmu wadanda ake sayar mana da kayayyakin da kamfanin mu yake sarrafawa, yusleem wallahi kullum da kai nake kwana acikin raina inata addu’ar Allah yasa sai mun hadu nabaka hakkinka kafin na amsa kiran ubangijina, gashi yau burina yacika, zan sauke babban nauyi, zan baka albashinka na shekaru shida sannan kuma zan raba dukiyata gida biyu inbaka taka, haka kuma zamuje can ministry of information domin abaka office dinka wanda yake can yana jiranka.., yanzu tashi mu hanzarta mu tafi”

Farin cikine ya lullube Hafsa nan tasoma yiwa ubangiji godiya acikin zuciyarta, ji take kamar ta zuba ruwa akasa tasha dan farin ciki,

Alhaji musa mori bai bar yusleem yasake wata magana ba yasashi agaba suka fita yace zaije ya sauke nauyi,

Har tsakar gida mami da hafsat suka rakasu saida suka ga fitarsu sannan suka koma ciki cikeda farin ciki da murna, dan murna ko abincin rana kasa ci sukayi suna jiran suga dawowar yusleem amma har dare bai dawoba gashi kuma washe gari da safe zai tafi kasar Cairo,
.
Yusleem kuwa tunda suka fita basu samu zamaba suna can sunata yawo ana nunnuna masa filayensa da gidaje da shaguna da kamfanoni, basu suka samu Kansu ba sai karfe 9 nadare nan alhaji musa yagayyaceshi suje gidanshi suci abinci amma yusleem yaki yace gida zaije domin gobe da safe zai tafi kasar Cairo nan suka rabu da alhaji musa akan sai bayan yadawo sannan zasu karasa duk wasu abubuwa wadanda suka dace, suka kawoshi gida suka ajiyeshi.

Afalo yasamu su mami zaune suna sauraron zuwanshi kowannensu da gani babu tambaya yana cikin walwala da farin ciki, zama yayi agajiye kusa da hafsat yana murmushi,

“Wallahi yau nasha wahala mami, munyi tafiya sosai har wasu yan kauyuka mukaje..”
.
“Ikon Allah, Allah mai yadda yaso, Allah yasanya alkhairi dai” inji mami,

“Amin” ya amsa mata tareda kwashewa yadda akayi yasanar da ita, murna dukkansu suka rinka yi sai lokacin suka iya cin abinci, faten wake da kifi yaji albasa da manja, acikin faranti babba hafsat ta zuba musu suka hadu gaba dayansu sukaci harda mami,

Mamince tafara tashi tawuce bedroom dinta tabarsu awurin, kallon hafsat din yakeyi yanda taketa wani sussunne kai ita adole kunyarshi takeji, bai kulata ba yatashi yafita, wanka yaje yayi ya duba kayanshi yasa domin har hafsat ta hada masa yan kayan da zai tafi dasu,
.
Saida yashirya tsaf sannan yanufi part din mami, dakin da hafsat take ciki yatura yashiga, tana tsaye gaban mirror tana shafe jikinta da turare mai dan karen kamshi da dadi,

Abayanta yatsaya yana kallonta yana shakar kamshinta wanda yatasamma rikita masa kwakwalwa,

“Ashe nidinma dan gatane tunda gashi nan ana shirin yimin tarba ta musamman” yafada cikin tsokana,
.
Shiru tayi bata tanka ba, ji tayi yadauketa yayi saman gado da ita, rungumeta yayi yana bata labarin abinda yafaru tun daga fitarsa har Kawo dawowarsa,

“Yaya yusleem ai Allah yaga sadaukarwar da kayi kuma yaga irin tuban da kayi shiyasa bazai taba barinka katabe ba..”

“To ai da taimakonki hakan yafaru madam, Allah yayi miki albarka..”

Kasa amsawa tayi domin tuni taji yasoma yunkurin irin wasannin da yayi mata adaren jiya,

Duk da yanata maganar yagaji yagaji yau amma hakan bai sashi yayi barci ba, yanda sukaga rana haka sukaga dare har asuba tayi, saida sukayi salla sannan suka kwanta bacci.

Itace tafara tashi lokacin karfe 9 nasafe tayi wanka tafita wurin mami, bayan sun gama breakfast tana shirin taje ta tasoshi sai gashi yafito, kamar ta nitse dan kunya duk da tasan yanzu mami tagama gane adakin yake kwana, tagefen ido ta kalleshi lokacin da yana gaida mami,

“Yusleem karfe 11 fa zaku tashi, kayi sauri kashirya muje mu rakaka” mami tayi maganar tana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta, tea kawai yasha yatafi shiryawa,

10:30 daidai yafito tsaf cikin shirinsa natafiya, yasha kananan kaya, iya hafsat ce kadai acikin falon tana jiran mami tafito tana tsaye gaban wani console tana ganin fuskarta, abayanta ya tsaya, yariko kugunta nan tayi saurin juyowa,

Murmushi yayi yakai mata kiss saman bakinta tayi saurin gocewa, hannunta yariko,

“Jiya baki ki ba yau kuma tsabar gulma ce tasaki kin yarda?”

Hannu tasa tarufe fuskarta, jin mami na kokarin fitowa yasashi sakinta nan suka dunguma suka tafi, motar mami suka shiga driver yaja suka fita daidai lokacin motar khadija ta Kawo kai nan tayi reverse tabi bayansu…..

_Gaisuwar fatan alkhairi ga Anty A’isha (mama 4),Anty Aisha (maman minal),Maman sultan, & Hawy yanmata_

*
.
Ta cikin mirror din saitinshi yake hango fuskar hafsat wacce ke kunshe da abubuwa guda biyu wato farin ciki da kuma sabanin haka,

Mami kuwa tamkar tafi kowa farin cikin wannan tafiyar ta yusleem domin zaka gane hakan idan har ka kalli fuskarta,

Tafiyar mintuna 15 zuwa 20 ne yakaisu airport din suna yin packing saiga khadija itama tayi packing din tata motar akusa dasu dan haka kusan atare suka firfito,

Cikeda fara’a ta karaso wurinsu tasoma gaisar da mami, cikin fara’a mami ta amsa domin acikin farin ciki take, dan kallon yusleem tayi taga hankalinsa ai bama anan yakeba domin yana tsaye shida hafsat suna yin magana,

Tsayawa dukkaninsu sukayi ajikin mota suna jiran su,

Hawayene suke kokarin zuba a idon hafsat yusleem yayi saurin kama hannunta suka bar wajen, can dan nesa dasu mami sukaje yafara rarrashinta,

Hannuwanta duka biyu yarike yana kallon fuskarta,

“Haba nanah karki zama raguwa, kiyi hakuri kinga da ace tun farko kudin nan sun fito dawuri to da tare dake zan tafi…”

Hawayen da taketa kokarin hana zubowarsu ne suka zubo sharr nan yakai hannunshi ya goge mata,

“Daina kuka, me kike so inkawo miki idan zan dawo..?”

Shiru tayi idanuwanta na kallon kasa,

“Abin dadi?, ko kayan kwalliya?”, taji yasake tambayarta, girgiza masa kai tayi alamun a’a,

“To me kikeso?”

Nunashi tayi da dan yatsa,

“Ni kaina…?” Yayi maganar murya kasa kasa,

Kai ta daga masa,

Hannuwanta taji ya matse tareda janta zuwa kirjinsa bata fargaba tajita rungume ajikinshi,

“Yaya yusleem su mami…” Tafada tana kokarin zamewa, sassauta rikon da yayi mata yayi yana murmushi,
.
“Ki kwantar da hankalinki idan nadawo zaki sameni har sai ma kin gaji dani”

Murmushi tayi ta zame jikinta tana kallonshi, shi dinma kallon fuskarta yake yana murmushi, wurinsu mami suka koma yayi musu sallama ya dauki yar jakar kayanshi yawuce,

Saida sukaga tashinsu sannan suka bar airport din suka dunguma suka koma gida har khadija.

Bayan komawarsu gida harkokinsu sukai tayi amma da zarar hafsat tashiga daki sai taga kamar zataga yusleem, haka taitajin kewarsa har dare yayi, duk irin baccin da yacika mata ido amma lokacin da tazo ta kwanta sai taji ta kasa baccin kwata kwata, sai uban juyi data rinka yi tana tuno mijinta, dakyar tasamu bacci ya dauketa bayan dare ya raba.

Washe gari da safe bata samu damar fitowa da wuri ba sai wurin misalin karfe 11 lokacin da ta fito mami na shiri fita dama ita take jira,

“Hafsa ga breakfast can ni fita zanyi, ina son zanje gidan hajiya Sarah amma ba dadewa zanyi ba”

“To mami Allah ya kiyaye hanya sai kin dawo”

Fita mami tayi tatafi ita kuma ta nufi dining area, zama tayi ta karya duk da abincin bawani mai yawa taciba, falo tadawo tazauna ta kamo tashar b4u tana kalla domin zaman shiru babu dadi,

Har bacci yadan fara daukarta sama sama taji sallamar khadija wacce abisa dukkan alamu yanzu ta mayar da zuwa gidan kullum tamkar ibada,
.
Tashi zaune hafsat tayi tana murmushi,

“Sannu da zuwa..”

“Yawwa hafsa, ko mamin bata nan” inji khadija wacce ke sanye cikin wata doguwar riga ta atamfa,

“Ehh mami ta dan fita wallahi” hafsa tabata amsa bayan tatashi zaune,

Zama khadija tayi, bayan sun gaisa suka dan fara hira kadan kadan,

“Hafsa kowa yayi mamakin yadda akayi kika samu kan yusleem har kuka kai wannan lokacin tare, saboda yusleem baya iya zama da mace..”

Murmushi hafsa tayi,

“Baya zama da mace kamar ya? Aini ban san wannan labarinba ko a mafarki”

“To kuwa a lissafi kece mace ta fiyeda goma da ya aura, kuma saida ya sakeni sannan ya aureki, ni kinga bamufi wata biyarba tare”

Jijjiga kai hafsa tayi alamun tausayawa,

“Allah sarki, Allah yarufa asiri kin san ai dama lamarin aure sai hakuri domin shima rai gareshi…”

“Hakane amma nida ina zargin ko aljanu gareshi ko kuma da saninsa tsabar cin mutunci ne, shiyasa ma ni yanzu wallahi auren yagama fitar min daga raina domin kin san naji dadi shine gari bawai nasaba ba..”

“To ai ba duk aka taru aka zama dayaba khadija, sai kiga nan gaba kin samu inda zakiji dadin hankalinki ya kwanta…”

“Kayya hafsa, kin san ai duk wanda miciji ya sareshi to idan yaga tsumma gudu yake, hafsa arayuwar aurena tafarko ban tsinci komai ba face bakin ciki da bacin rai da takaici, shiyasa ko zan kara wani auren gaskiya ba yanzu ba sai zuciyata ta nutsu tukunna”

“Ubangiji Allah yazabi abinda yafi alkhairi, babu komai ai jarrabawa ce daga Allah”

“Amin..”
.
Haka sukaci gaba da yin hirarsu har azahar tayi sai lokacin khadija tatafi, tun daga wannan rana kuma kullum zatazo susha hirarsu da hafsat wani lokacin ma harda mami, ita hafsa tausayin khadija takeji domin irin labaran da take bata na kuncin rayuwa da rashin samun farin ciki wanda ta rinka fuskanta agidan aurenta nafarko, shiyasa take tausayinta domin tasan irin wannan rayuwar tunda itama tashiga makamanciyarta abaya, koda yaushe yanzu khadija tana gidan haka kuma idan bataje da safe ba to zataje da rana ko da yamma wani lokacin harda daddare ma zuwa take tamaida gidan mami kamar gidansu haka ta dauki hafsat a matsayin yar uwa kuma abokiyar shawara domin ko sabon bazawari tayi saita fada mata,

Yauma kamar kullum hafsa tana zaune tana tsifar kai ita kuma mami tana gyaran farcenta saiga khadijan tashigo da alama daga sch take domin karfe 2 saura narana,

Da mami kawai suka gaisa tahaye dining ta zubo tuwon shinkafa miyar zogale tadawo wurin hafsat ta zauna,

“To inbanda abinku kuma ga tsifar gashi ga abinci?” Mami tafada tana murmushi,

Dan kwali hafsat ta dauka ta rufe kanta, “bari inbarshi anjima na karasa idan tagama”

Tashi mami tayi ta shiga kitchen domin tajiyo buruntun kuku aciki,

Mami natashi khadija ta dubi hafsa dama da labari tazo mata,

“Hafsa inata son inbaki labarin wani guy Al’amin, saurayi ne fa amma yadage sai ya aureni duk da nace masa nataba aure”

Murmushi hafsat tayi, “to kibashi dama mana kigani, wallahi khadija kiyarda indai kinga baida problem”

Murmushi khadija tayi ta yanko laumar tuwo tasa abakinta,
.
“Shikenan zan gwada ingani, bari inyi sauri ma domin munyi dashi zaizo da yamma”

“To Allah ya tabbatar da alkhairi”

Saida khadija taji tayi nak sannan ta hada nata yanata tatafi, kullum hakace take faruwa domin acewarta dama gidan mami gidansu ne domin dama aminiyar mahaifiyarta ce.

Tunda yusleem yatafi basuji duriyarsa ba saida yayi sati biyu sannan yakira su murna ranar awurin mami da hafsa ba acewa komai, sun jima suna hira dashi yana yimusu bayanin abubuwan dake faruwa sannan sukayi sallama,

Haka da daddare ma saida ya kuma kira suka kwashe awanni shida hafsat suna hira, yanzu har tasan lokacin kiranshi domin kullum sai yakirasu da safe da daddare,

Satinshi 7 acan yafara shirye shiryen dawowa amma idan yadawo bayan wani lokaci zai  sake komawa,

Hafsat tunda taji zai dawo tarasa inda zata cusa kanta dan murna wanda hatta mami saida ta fahimta, saloon mami takaita aka wanke mata gashinta aka gyarashi, bayan sun dawo gida mai kunshin dake yiwa mami tazo ta zane mata kafafunta da hannaye da bakin lallai mai adon ja,

Tarba ta musamman mami da hafsat suka shiryawa yusleem,karfe 3:30 jirginsu yasauka nan mami da driver suka tafi daukoshi banda hafsa wacce tazauna domin karasa girke girken da aka dora sabodayau tace itace zatayi girkin da yusleem zaici…..

       ***

Lokacin dasu mami suka dawo gidan hafsat tana cikin daki tana shiryawa, saida ta kammala sannan tayi sallar la’asar domin lokaci yayi,
.
Tana tsaye gaban mirror tana gyara fuskarta bayan ta idar da sallar ta hango wulgawar mutum ta cikin mirror atsorace ta juya amma abun mamaki bataga kowa ba, tsorata tayi takama hanya zata fita daga dakin taje falo wurinsu mami,

Ji tayi anyi mata wata irin damka, tuni numfashinta yafara neman daukewa, ajikin mutum tajita anrugumeta tabaya tayadda bazata iya ganin fuskar mutumin ba, kara taso fasawa amma ina bata samu zarafin yin hakanba domin ji tayi anrufe mata baki da abinda bata san ko menene ba sai daga baya sannan ta fahimci cewar da bakinshi ne,

Wani sanyayyen kamshi ne mai dadi yake ratsa kofofin hancinta gaba daya,

Sassauta rikon da yayi mata yayi ya dago da fuskarta yana kallonta,

“Nanah hafsat…”

Firgigit tayi tabude idanuwanta akan fuskarsa ganinshi yasata daka tsalle ta rungumeshi na tsawon wasu mintuna,

Riketa yayi yana dan juyi da ita ahankali, dago da fuskarta tayi ta kalleshi, tabbas yaya yusleem dintane amma kuma tamkar wanda aka canjashi domin farar fatarshi tasake haskawa farin yakaru, gashi fatar tashi tasake laushi lubus kamar ta jarirai, kyakkyawar fuskarshi kuma tasake cika da kyau, annuri, da farin ciki,

Ji tayi gaba daya tagama raina kanta saboda yusleem yafita tako ina ita sai take ganinma ayanzu haka ai bata da wani abu atare da ita wanda take ganin zata iya jan ra’ayinshi domin yafita kyau yafita komai na rayuwa,

Hancinta taji yaja domin har lokacin tana dale ajikinshi hannayenta sakale awuyanshi,
.
Bude idanuwanta tayi daga dogon tunanin data lula ta kalleshi, ji tayi ya rike fuskarta yana kokarin sake saita bakinshi akan nata, shi kansa bakin nashi da lips din dake jiki da fararen hakoran dake jere aciki tasan abin kallone, lumshe idonta tayi tana jiran taji saukar lips dinshi akan nata amma sai taji sabanin haka maimakon yayi kissing din bakinta sai tajishi asaman kirjinta, saurin tureshi tayi tasoma kokarin kwacewa tana dariya,

Riketa yayi shidinma yana yin dariyar kasa kasa,

“Bakiyi min ko sannu da zuwa ba..”

Tana shirin yin magana suka jiyo maganar mami tana nufo kofar dakin,

“Hafsa har yanzu baki idar da sallar bane? Idan kin idar kifito ki hada salad din saboda nace kuku yahada yace kece kika ce karya taba sai kin fito…”

Bude baki tayi zata amsawa mami amma takasa saboda shakewar da muryarta tayi, rufe mata baki da hannunshi yayi yabawa mami amsa da,

“Mami har yanzu fa bata idar da sallar ba..”

“To idan ta idar kafada mata, sannan ku fito muci abincin…”

“To mami…”

Saida ta tabbatar da cewar mami tatafi sannan ta kalleshi,

“Kuma da tashigo taganmu fa gashi kace mata wai salla nake yi..”

Murmushi yayi ya lakuce mata hanci,

“Ai bazata ma shigo ba saboda tasan nidake yau tamkar tif da taya zamu kasance….”

“To kazo muje kar taga mun dade tayi zargin ko wani abu muke yi..”

Murmushi yayi ya dauketa nan tasoma mutsu mutsu, ajiyeta yayi ta fice shikuma yashiga toilet yayi alwala yafito yayi salla,
.
A falo ya samesu ita da mami sun baje girke girken da aka wuni anayi saboda shi, akusa da mami ya zauna yana kallon hafsa wacce ke tsugunne tana hada salad wanda zasu ci abincin dashi,sai lokacin wai ya lura da kunshin dake hannunta duk hidimar dazu idonshi bai kai kan kunshin ba,

Tashi mami tayi zuwa kan dining domin debo wasu kwanuka,

Hannunshi yakai kan na hafsa,

“Ya akayi dazu banga kunshin nan ba sai yanzu? Koda yake ai ni yau dinne gaba daya amaryar tawa tagama rudani, ta dauke hankalina”

Murmushi hafsat tayi saboda jin abinda yace, janye hannunta tayi daga jikin nashi saboda taga mami na kokarin fitowa ganin haka shikuma ya wayance da lakuto salad din yakai bakinsa,

Kamar koda yaushe a cikin babban faranti yauma suka zuba abincin suka hadu suna ci, idan yusleem yafaki idon mami sai ya kwace abincin hafsa ya kai bakinsa,

Tun daga yanayin cin abincinsa mami da hafsa suka gane cewar lafiya ta samu domin yau yaci abinci sosai wanda rabon da yaci irinshi har anmanta,

Komai da suka girka saida yaci, kallonshi kurum hafsa keyi saboda ganin yanda ya bude ciki ya narki abinci,
.
Kan kujera yaje ya mike, mami na zaune kusa dashi suna dan yar hira dangane da tafiyarsa da dawowar tashi yana sanar da ita abubuwan da suka wakana,

Hafsa kam wurin da suka gama cin abinci tashiga gyarawa tana kwashe na kwashewa tana kaiwa kitchen ba zuwa tayi tasasu agaba ba domin tasan tsakanin d’a da mahaifi dole akwai abubuwan da zasu tattauna atsakaninsu,

Saida ta kalkale wurin tass sannan ta kunna turaren wuta lokacin har 6 tayi, tashar zee world ta kunna tazauna tana kallo bayan ta dora dan karamin pillow din kujera akan cinyarta,

Tana ta kallonta sam hankalinta baya kansu mami, pillown taji anzare an kwanto akan cinyarta,

Saurin kallon wurin dasu mami ke zaune tayi nan taga mamin bata nan, kallonshi tayi lokacin da yake kara gyara kwanciyar kanshi akan cinyarta,

“Wai yaya yusleem yau da me kazo ne? So kake sai mami tafito ta ganmu?”

“Mami bazata fito yanzu ba ai, tashiga bedroom dinta kuma kin san idan tashiga bata fitowa sai bayan tayi salla”

Shiru tayi, hannunta ya kamo ya hada da nashi yana gani,

“Kinyi kyau…”
.
Shiru tasake yi domin sai tana ganin kamar gatse yake yi mata, shikuma tsakaninshi da Allah har cikin zuciyarshi yake fada,

“Yanaji kinyi shiru? Uhm”

“Babu komai”

“Ban yarda ba” yafada yana murza babban dan yatsanta,

“Lokacin salla yayi fa..”

Tashi zaune yayi yana kallonta,

“Tashi muje to muyi”

Tashi tayi tabi bayanshi zuwa cikin bedroom din,

“Kishiga ki fara yin alwalar”

“Nifa inada alwalata”

Murmushi yayi ya matsa kusa da ita,

“Allah karya kike, infada miki gaskiya? Wallahi ko tsarki bakida shi garama kije ki sake kiyi alwala..”

Tamkar kasa ta tsage ta shige haka taji dan kunya, ganin yana kokarin sake yimata wata tabargazar yasata juyawa da sauri ta fada cikin bathroom din ta turo kofa, murmushi yayi ya cusa hannuwanshi cikin aljihun wandon jeans din dake jikinsa……

_Fans aci gaba da yimin uzuri domin har yanzu ban gama warwarewa ba, fatan alkhairi agareku all…_

        ***

Yana tsaye ya bawa kofar bathroom din baya hafsat ta fito hannunta rikeda dan kwalinta tana kokarin daurawa,

Juyowa yayi yana kallonta, ganin gashin kanta wanda yasha gyara da yayi yasashi karasawa gabanta ya rike dan kwalin,

“Yanmata harda su gyaran gashi shine ba anuna min tuntuni ba?”

Hancinshi yakai kan gashin wanda har hafsat na iya jin dumin numfashinsa wanda ke sauka akan gashin nata,

Hannunshi tarike tana mai bata fuska,

“Yaya yusleem dan Allah kabari, Allah lokacin salla zai wuce..”
.
“Da yaushe ma aka kira sallar? Da sauran lokaci ai baby..”

Ribom din dake daure da gashin nata ya warware yasoma baza mata shi akan kafadarta,tamkar mai yimata tafiyar tsutsa haka taji,

Rike hannunshi tasake yi,

“Nikam gaskiya yaya yusleem alwalata…”

Murmushi yafara wanda yakarashe shi da dariya,

“Ta karye?”

Girgiza masa kai tayi alamun a’a,

“A’a dai baby hafsa fada min gaskiya, ta karye?”

Runtse idonta tayi tana rikeda hannunshi,

“Dan Allah kabari kar time din salla yakure mana..”

“To bari naje masallaci…”

Har yasaketa yasake rikota,
.
“Bari kawai nakarasa karyata inyaso sai kisake sabuwa”

Kafin takai ga yin magana har ya kama lips dinta,

Mintsininshi tayi a hannunshi nan yasaketa yana dariya, fita yayi daga cikin dakin zuwa bathroom din dake cikin falo anan yayi alwala yatafi masallaci.

Koda hafsa ta idar da sallar magrib kin fitowa tayi anan inda tayi salla ta kwanta har saida lokacin sallar isha yayi sannan tatashi ta gabatar da sallar isha da shafa’i da wutri,

Batare da ta cire hijab din da tayi sallar ba tafita falo wurin mami,

Mamin nazaune da carbi a hannunta tana ja sannan kuma tana kallon labarai a tashar BBCW,

Tana zama yusleem yana shigowa, kin kallonshi tayi tamaida idonta kan tv, a kusa da mami ya zauna wato kujerar dake kallon ta hafsa,

“Hafsa akawo abinci ko?” Mami tayi maganar tana kallonta,

“To mami bari nakawo muku nidai nakoshi..”

“Nima gaskiya na koshi amma zansha kunu” yusleem yayi maganar yana zaro wayarshi daga aljihun jeans dinshi,
.
“To shikenan adama mana kunun gaba daya sai musha” inji mami,

Tashi hafsa tayi zuwa kitchen, mintuna kalilan ta damo kunun ta dawo falo dauke dashi,

A cup ta zuzzuba musu ta dauko sugar da madara tasa musu,da kafarshi ya tabota kasancewar tana zaune akasa kusa da kujerarshi, dagowa tayi ta kalleshi,

“Wannan na waye kike zubawa?”

“Nakane..” Tabashi amsa,

“Yayi yawa ai, rage”

Sauka kasan shima yayi kusa da ita,

“Bar sugar dinnan haka, amma ki kara milk da yawa”

“Duk wannan wadda nasa batayi ba?”

“Nifa ke nake yiwa gata yarinya, ko bakya so indaina?” Yayi maganar cikin rada rada tayadda mami bazata jiyo ba domin tana dan nesa dasu,

Shiru tayi masa saboda tagane abinda yake nufi, ita yau mamaki yake bata domin kamar zuwansa Cairo dinnan rashin kunya yaje ya koyo domin tunda yashigo cikin gidan yau yaketa yimata abubuwa masu nauyi,

Tura masa gwangwanin madarar tayi gaba daya da kunun nashi tadauki na mami takai mata tadawo ta zauna tasoma shan nata kunun,

Tana jinshi yanata dungurinta tarabu dashi daga karshe ma tashi tayi tawuce cikin daki tayi kwanciyarta, wayarta ta jawo nan taga miss called din umminta, kiranta tayi suka gaisa suka dan taba hira daga nan sukayi sallama.
.

  Tana kwance lullube cikin bargo taji shigowarshi, rufe idonta tayi kamar mai yin bacci, akusa da kafarta ya zauna yakama yan yatsun kafar yasoma jansu daya bayan daya suna yin kara, duk da tanajin zafi shiru tayi masa ita adole bacci take yi,

Jin tayi shiru yasashi haurawa saman gadon, abayanta ya kwanta bayan ya dan ture bargon da take ciki,

Kamshin turarenshi da taji shine ya haifar mata da kasala, luf tayi tana jinshi yana baza mata gashin kanta,

Juyo da ita yayi tana fuskantarshi, jikinta ne yabata cewar kallonta yake domin tsawon mintuna biyar zuwa shida tajishi shiru baiyi koda motsi ba kuma tasan ba bacci yake yiba, ahankali ta bude idonta guda daya kadan ta kalleshi ai kuwa kamar yanda ta zarga ganinshi tayi ya zubawa halittar kirjinta manyan idanuwanshi ko kiftawa bayayi, ganin yana kokarin kai hannu yasata saurin juya masa baya kamar mai bacci, juyo da ita yasake yi,

Rike masa hannu tayi tabude idonta,

“Keda kike yin barci ya akayi kikasan abinda ke faruwa?”
.
“Dan Allah nidai ka kashe hasken nan”

Murmushi yayi ya kalleta,

“Bakya son inganki ahaske? Nikuma da nafi son inkare miki kallo sosai”

Jan bargo tayi ta rufe har kanta, sauka yayi daga kan gadon yaje yakashe hasken yadawo amma abin mamaki koda yahau kan gadon ji yayi babu ita babu alamunta nan yafara shashime amma bai jitaba,

“Hafsa, hafsa, dama wayo zakimin kenan..”

Jin bata amsaba yasashi sauka daga kan gadon yafara bin bangon dakin yana lalubenta domin bai zo da wayarshiba,

Shiru bai jitaba sai can yajiyo kamar motsinta awurin gaban mirror, ahankali yataka yaje wurin, hannayenshi ya mika da niyyar damkota amma sai aka samu akasi suka sauka akan abunda yaketa zumudin samu yanzu,

“Wai wai yaya yusleem…” Tace dashi tana rike hannunshi,

Rikota yayi ya dagata yadorata akan kafadarshi ya lulubi gado ya hau har lokacin tana kan kafadarshi,

“Allah ne yaga zuciyata shiyasa yabani cikin sauki..” Yace da ita yana kokarin kawar da sleeping gown dinta,
.
“Dan Allah kayi bacci kaga daga tafiya kadawo…”

Murmushi yayi mai sauti wanda har sai da ita kanta taji,

Bata kara jin muryarshi ba har tsawon wani lokaci,

Duk da cewar bacci yacika mata ido amma haka tahakura,

A tsakiyar kirjinta ya kwantar da kanshi ahaka bacci ya daukesu,

Dakyar ta iya tashi da asuba saboda tsabar bacci, komawa tayi ta kwanta bayan ta idar da salla,tana kwanciya yazo ya matseta ya kwanta abayanta.

K’arfe 10 tatashi, wanka tayi ta shirya tasa atamfa blue ta fita, iya mami ce kadai a falon tana duba jaridar daily trust, durkusawa tayi tagaida mami sannan tahau kan dining tahada tea tasha,

“Yafada miki yafita ko?” Mami ta tambayeta,

“A’a mami ai sai yanzu natashi”

“Hakane kuma, can yatafi gidan alh musa mori zasu karasa wannan yawon ganin kadarorin nasu wanda suka fara rannan”

“To Allah yadawo dashi lafiya”

“Amin amin”.

Koda yusleem yafarka daga barci bathroom yashiga yayi wanka yafito, ganin hafsat bata tashiba yasashi fita zuwa part dinsu Abdul, acan yashirya cikin farar shadda kal da ita yasa agogon azurfa yafito bayan yashafe jikinsa da turare, sauri sauri yashiga part din mami yasha tea domin alh musa nacan yana jiranshi, wurin hafsa yakoma har lokacin bacci take gagarumi bata da ranar tashi, yan yatsun kafarta yaja, ganin ko motsi batayi ba yasashi yiwa dan madaidaicin bakinta kiss da wuyanta,shi baisan dalilin da yasa baya iya dauke idonshi daga jikinta ba musamman ma kirjinta idan yazuba mata ido shagala yake, saida yakai hannunshi wurin sannan ya iya kwantar da kwalamarshi yafita,

Yana fitowa daga dakin itama mami nafitowa daga nata,
.
Keyarshi yadan fara sosawa sannan ya durkusa yagaida mami, sallama yayi mata yakarbi key din motarta yafita,

Lokacin da yaje gidan alh musa dake unguwar millionaires estate aharabar gidan ya ajiye motarshi wadda tafito a matsayin bare acikin sauran motocin dake farfajiyar gidan domin duk sunfi tashi aji da matsayi,

Wata zukekiyar budurwace tafito sanye da wata hadaddiyar bakar gown, hannunta rikeda hand bag da key din mota tasha takalmi mai mutukar tsini tasa bakin face afuskarta, ashekaru zata kai 30 sai kamshinta ne ke kai kawo acikin iskar dake kadawa a compound din gidan, hango yusleem tayi yana fitowa lokacin da take kokarin bude motarta sabuwa dal,

Fasa shiga cikin motar tayi ta tsaya tana karewa yusleem kallo domin ko acikin finafinan India tasan ba kasafai aka fiya samun handsome, classic guy kamarshi ba…..

      ***

Tsayawa yusleem yayi ajikin motarshi bayan yafito, wayarshi ya zaro daga cikin aljihun wandon shaddarshi yasoma kiran hafsat saboda yasan yanzu may be tatashi daga baccin da yataho yabarta tanayi,

Har tayi ringing takatse bata dauka ba da alama bata kusa, sake kira yayi domin yasan bazai samu nutsuwa ba har sai yaji muryarta,

Kiranta yaci gaba dayi amma shiru bata dauka ba domin bata cikin bedroom din tana falo tareda mami, saida yayi mata 5 miss called, ana 6 dinne tashiga cikin bedroom din, wayar na daf da tsinkewa ta daga tareda zama agefen gado,

“Yaya yusleem lafiya…?” Tace dashi bayan ta kara wayar a kunnenta,

“A’a…” Yabata amsa yana murmushi,

“To meyake faruwa?”

“Ji nayi ina tsananin son jin muryar matata saboda nabarota tana bacci, ko har yanzu baki tashiba?”

Murmushi tayi najin dadi,

“Natashi, gashi har naci abinci naje wurin mami muna hira”

Murmushin shima yayi,
.
“To nima idan nadawo za ayi hirar dani”

“Allah yadawo dakai lafiya, Allah ya tsare ka ya kare mana kai”

“Amin, sai nadawo”

Katse wayar yayi yana murmushi, wayar tashi yamaida cikin aljihu ya nufi kofar da zata sadashi da falon bakin alh musa mori,

Duk wadannan abubuwan da yusleem keyi akan idon wannan matashiyar budurwar ne domin tamkar tv haka ta tsaya tazuba masa ido tana kallonshi, ganin ya shige tadaina hangoshi yasata fasa fitar da zatayi ta juya takoma cikin gida domin har ga Allah tanada bukatar sanin ko waye wannan kyakkyawan saurayin, gentle mai aji,

Ta kofar dake cikin part dinsu ta bi tashiga falon mahaifin nata,

Shi kam yusleem baima san da itaba domin lokacin da yagama wayarshi kansa tsaye yanufi wurin alh musa,

A falo ya iskeshi yana karyawa, durkusawa yusleem yayi yagaida shi sannan yatashi yazauna akan kujera,

“Yusleem ga abinci kazo kazuba kaci, ina so kadauki nan gidan a matsayin gidanku domin bakada shamaki atare dashi”

Murmushi yusleem yayi,

“To alh nagode, Allah yasaka da alkhairi”
.
Duk da bashida sha’awar cin abincin amma yadan hada ruwan zafi rabin cup yana kurba,

Wani kamshine mai mutukar ratsa zuciya ya dokeshi kafin zazzakar muryarta ta cika kunnuwansu,

Cikin nutsuwa tashigo cikin falon mahaifin nata ta durkusa agabanshi tana gaidashi kanta akasa,

“Hafsat baki fita ba yau?” Alh musa yayi maganar cikeda kulawa, jin an ambaci hafsat yasa yusleem kallonta, kyakkyawa ce iya kyau saida yaji gabansa yafadi,

“Ehh abba dama saboda naji umma tace katashi baka jin dadi shiyasa ma ban fitaba”

“To ai babu komai kin san jikin tsufa dama hakane..”

Gaida yusleem tayi cikin nutsuwa da ladabi, ya amsa mata fuska asake,

Dauke idonshi daga garesu yusleem yayi yana sauraren tattaunawar tasu har suka gama,

Mikewa tayi tafita yayinda alh musa yajuya ga yusleem,
.
“Yusleem wannan itace babbar yata hafsa, itace babba tanada kanne guda hudu daya mace uku maza”

“Allah sarki..” Yusleem yafada yana murmushi,sake kallon alh musan yayi yace,

“To alh ni ina ganin tunda baka da lafiya ma kawai mubari gobe idan Allah yakaimu sai nazo muje, dama dan ban san bakada lafiya bane da bazan zo ba sai gobe”

“To shikenan Allah yakaimu, nagode yusleem”

Sallama sukayi yusleem yafita, gaba daya kamshin turaren nan dayaji yatada masa da kwalamar hafsanshi,

Shiyasa yake sauri yasamu yaje gareta ko zaiji sauki, bude motar tashi yayi cikin sauri yashiga yayi mata key yafita daga gidan,

Tun daga fitowarshi har fitarshi duk akan idon hafsat hakan yafaru saida taga fitarshi sannan takoma ciki.

Lokacin da yusleem yakoma gida, afalo ya iske hafsat da khadija suna hira da alama mami bata nan, gaidashi khadija tayi ya amsa batare da yatsaya ba yawuce dakin hafsa,

Kallon hafsa khadija tayi,

“Bari nakarasa tunda maigidanki yadawo sai wani lokacin zan sake dawowa..”
.
“To shikenan Allah yadawo dake khadija, nagode”

Rakata kofar falo hafsa tayi tajuya ta nufi wurin yusleem, a kwance tasameshi yayi rigingine yana kallon sama, hannu ya mika yarikota zuwa jikinsa ya kwantar da ita,

“Harka dawo? Amma kamar fa kadawo dawuri…”

Shiru yayi mata yana laluben zip din rigarta,shirun itama tayi aranta tana tunanin to ko dama abinda yadawo dashi kenan?

D’an dukan kirjinshi tayi, “yaya yusleem kayi magana mana”

Sake rungumeta yayi yana shakar kamshin dake tashi daga jikinta,

“Matata naji ina bukata shiyasa nadawo gareta…”

Murmushi tayi aranta tana mai jin farin ciki yana ratsata sai dai kuma har yau takasa banbance shin halaccin da tayi masa ne yake sashi kyautata mata ko kuma zuciyarshi ce tafara kaunarta?

Kasa lalubo amsa tayi dan haka tayi gaggawar kawar da tunanin acikin ranta, mirginata kasa taji yayi shikuma yana samanta,
.
Soyayya mai mutukar sanyi yashiga nuna mata cikin nutsuwa domin komai nashi dama a nutse yake aiwatar dashi babu baragada, kissing dinta yajima yanayi har zuwa wani lokaci,wasu wasanni masu sanyaya zuciya yashiga yimata wanda saida yaji yasamu nutsuwa sannan ya sarara mata,

Rungumeta tsam tsam yayi yana jin wata irin nutsuwa tana saukar masa, fatar kunnenta yakama da hakorinshi yana ciza ahankali yana hura mata iska awurin,

“Wai yaya yusleem dama abinda yadawo dakai kenan?”

“Hafsa sau nawa zan amsa miki ne? Nace miki eh, eh, ehhhh…”

Murmushi tayi tarike hannunshi duk kunya tagama baibayeta kawai daurewa takeyi,

“Ina mami tatafi?”

Sai lokacin hafsat ta tuna da cewar mami na iya dawowa ako wanne lokaci dan haka tafara kokarin zame jikinta, riketa tsam yayi,

“Mami fa ba nisa tayiba dan Allah kabari karta dawo ta samemu…”

“Kin kusa ai kibar mamin dan wallahi daukeki zanyi inkaiki inda zamu rayu mu biyu babu mai katse min hanzarina..”

Murmushi tayi tasamu ta zare jikinta dakyar tatashi tana yimasa dariya kasa kasa saboda ganin yanda duk shaddar jikinsa tayi wani arnen squeezing,

Rikota yayi lokacin da take kokarin sauka daga kan gadon, hannuwanta duka biyu tasa ta kare fuskarta tana yin wata dariyar ahankali…..

   _Gaisuwar fatan alkhairi ga maman fati, ina mutukar kaunarki mamana…_

       ***

Ahankali ya tashi zaune har lokacin yana rikeda ita,

“Menene kike yimin dariya?”

“Babu komai..”

“Ban yarda ba”

Wata dariyarce tasake subuce mata,

“Nasan abinda kike yiwa dariya shikenan, anjima ki shirya zaki rakani unguwa”

Dadine taji ya kamata shiyasa fuskarta tasake fadada da farin ciki,

“Tom Allah yakaimu, amma ina zan rakaka?”

“Zance…” Yabata amsa tareda kokarin sauka daga kan gadon, saurin rikoshi tayi saboda jin abinda yace,

“Zance?” Ta maimaita abinda yace cikin sigar tambaya,

“Ehh ko bakya son inyi miki kishiya?”
.
Shiru tayi masa tasakeshi, dan kwalinta da rigarta da sauran kayanta wanda yayi mata fatali dasu tabi ta tattara ta nufi wurin drewar kaya ta tsaya,

Dan kallonta yayi yasaki murmushi domin bai taba ganin fushinta ba sai yau,

Tashi yayi yaje gabanta tana tsaye tana kokarin saka riga, kunnuwanshi duka guda biyu ya rike,

“Am sorry nanah hafsat…”

Bata kulashi ba taci gaba da abinda takeyi, hannuwanta yarike,

“Nace kiyi hakuri wallahi dawasa nake yi miki..”

“Ni kadaina bani hakuri saboda ba fushi nayiba”

Rungumeta yayi gaba daya ajikinshi yana murmushi,acikin kunnenta yafara yimata rada,

“Gidan su Ummi fa nake son ki rakani daga nan sai muje gidansu kawarki Maman amir”
.
Duk da taji dadin zata je gidansu da gidan su maman amir hakan baisa ta saki fuskarta ba,sassauta rikon da yayi mata yayi,

“Baby ashe haka kike da kishi shine ban saniba?”

Sake bata fuska tayi ta zame daga rikon da yayi mata, fita tayi gaba daya daga cikin dakin tanufi falo tana tafiya tana kokarin zuge zip din rigarta, tana zama mami na shigowa,

Sannu da zuwa tayi mata ta karbi kayan dake hannunta, kinkimar kayan da mamin tazo dashi hafsat tayi takai cikin dakin mami tafito lokacin har yusleem yafito yana zaune kusa da mamin,

Ko kallonshi batayi ba tawuce tazauna, dan kallonta yayi ya rausayar dakai alamun ban hakuri, dauke kanta tayi taki kallonshi,

“Mami dan Allah kibawa yarinyar nan hakuri naga sai fushi take dani daga yimata wasa…..” Tajiyo yusleem yana fadawa mami,

“Ahh fushi kuma?” Mami ta tambaya, juyawa tayi ga hafsa,

“Hafsa meya faru??”

Murmushi hafsa tayi cikeda jin kunya tace, “Allah mami ni babu komai ba fushi nakeba”

“Wallahi mami karya take yi fada mukayi saboda wai kawai nayi mata wasa nace zata rakani zance wurin budurwata…”

Jin abinda yace yasa mami yin murmushi tatashi ta wuce kitchen wurin kuku tabarsu afalon saboda ta fahimci maganarsu ce ba tataba,

Ganin mami tafita yasa yusleem kallonta yana gyarawa hularshi karinta,

“Wallahi Allah hafsa wasa nake yimiki, wallahi ni banida wata budurwa kin san dai bazan rantse miki akan karya ba..”

Jin abinda yace yasata sakin ranta kadan amma bawai dan ta huceba sai dai ko babu komai zuciyarta ta danyi sanyi domin ta tabbatar da gaskiyar abinda yafada tunda har ya rantse mata,

Tashi yayi yafita saboda jin batayi masa magana ba, tunda yatafi bata kara jin motsinshi ba har karfe  2 narana, suna zaune suna cin abinci taji yakira mami awaya,

“To shikenan bari mugama sai tazo, ehh tana nan zuwa” mami tafada sannan takatse wayar tajuya tana kallon hafsa,
.
“Yusleem ne wai idan kin gama kije ki karbo mana kayan tsarabarmu, kiji wani kinibibi tun dasafe bai bamu ba sai yanzu…”

Murmushi hafsa tayi saboda tagano wayonshi kawai son ganinta yake shine ya bullo tanan,

Saida mami tasake tuna mata bayan sun gama cin abincin sannan ta tashi tatafi, baya cikin falo dan haka tawuce ciki, akan gado ta hangoshi zaune yana daddanna wayarshi,

“Mami tace kana kirana, gani..”

“Zo…”

Karasawa tayi gaban gadon ta tsaya batare data kalleshiba tun bayan kallon farko da tayi masa saboda daga shi sai gajeren wando da farar vest iya shaddar da yasaka kawai yacire,

Hannunshi ya mika ya kamo nata ya fisgota da karfi, babu zato tajita tafada kanshi, matseta yayi yana kallonta fuskarshi dauke da murmushi, sam baya gajiya da lalubarta dan haka nan take yafara,
.
Duk da tana dan fushi dashi amma hakan baisata juya masa baya ba,soyayya ya nuna mata sosai ita har mamakinshi ma tayi,

“Baby wallahi bana gajiya dake,kefa kina gajiya dani…?”

Shiru tayi masa ta dauke kanta cikeda kunya,

Hancinshi yagoga ajikin nata,

“Uhm…?”

Shirun tasake yimasa, hancinta yaja tareda lakuce mata shi yana murmushi,

“Bacci nake son ki dan tayani baby zuwa anjima sai kitafi wurin mamin ko?”

Bai jira amsarta ba ya rungumeta tsam tsam ajikinshi yana shafa sumar kanta wacce tasha gyaran saloon……
Saida hafsat ta tabbatar da cewar yusleem yayi bacci sannan ta zare jikinta ta fice, cikin sa’a lokacin da tashiga falon babu kowa mami tana cikin dakinta tana hutawa, ita dinma nata dakin tawuce ta kwanta,

Bata samu zarafin tashiba sai misalin karfe 3 na yamma, wanka tashiga, bata wani jima sosai ba tafito daure da zani daurin kirji sam bata san yusleem yashigo ba sai ganinshi tayi tsaye gaban mudubi yana jingine,

Ji tayi kamar ta juya ta koma amma saita daure duk da tasan yau tsokanar da zata sha awurinshi mai yawace,

Kallo yabita dashi tun daga kan gashinta wanda ke jike jalaf da ruwa har izuwa dukkan jikinta,

“Su hafsat haka aka girma?” Taji yafada cikin sigar tsokana, rabuwa tayi dashi taje zata dauki mai, rike hannunta yayi bayan ta dauki man suka koma gefen gado,

“Wai wankan me kikayi?”

Shiru tayi masa ta lukuto man zata fara shafawa ya kwace daga hannunta ya lukuta zai shafa mata,

“Babyn mami kinaji ina tambayarki shine kikayi min shiru?”

Bata fuska tayi,

“To me kakeso ince maka?”
.
“Ai ke kikasan abinda zakice min nidai kawai tambayarki nayi nace wankan da kikayi na menene?”

Kunyace ta kamata amma tasan idan bata bashi amsa daidai da tambayarshi ba yau tsuyeta zaiyi yasata agaba yayita tsokanarta domin yusleem ya iya tsokana,

Daga kan wuyanta yafara shafa mata man zuwa kafadarta,

“Kodai bashida suna?” Yasake tambayarta cikin tsokana,

“Da akwai mana” tabashi amsa tana rike daurin zanin dake jikinta,

“To wanne irine?”

“Irin wanda kayi….”

Murmushi yayi ya matsa kusa da ita,

“Waya fada miki ni nayi wanka?”

“Allah kaima kayi, kalli fa kasake kaya da ai ba wadannan bane ajikinta…” Takarasa maganar tana nuna brown t shirt din dake jikinsa da bakin trouser,

Hannunta yarike,
.
“To tunda kince haka shikenan nayarda yanzu bari sai musake yin wani tare”

Girgiza masa kai tayi,

“Why?” Yace da ita yana matsa tafin hannunta, zare hannunta tayi ta lakuci man zata ci gaba da shafawa ya hanata,

“Bari mana inkarasa shafa miki…”

Lakutowa yakuma yi yana kallonta, “oya to kunce zanin”
Ki tayi ta girgiza kai, “ni basai ansa anan ba”

“Inji wa? So kike kiyi fururu…”

“Ehh”

“A’a to ni bana so”

Da wayo da wayo yasamu yayi kasa da zanin, kunyace ta lullubeta gaba daya saboda hakan bai taba faruwa ba sai yau, ita yau gaba daya takasa gane kan yusleem domin yahanata sakat,

Sam gaba daya ma shi yamanta da cewar wai mai yake shafa mata domin tuni yagama shagala da abinda yake yi,

Ganin lamarin yana neman yin nisa yasata kokarin  dakatar dashi,
.
“Dan Allah yaya yusleem kabari”

Batare da ya iya bude idanuwanshi ba ya shafo fuskarta,

“Haba baby….”

“Nidai Allah kabari”

Shiru yayi mata,dakyar tasamu ta kwace jikinta daga gareshi,

Zanin taja ta daura tana zumburo baki, murmushi yayi ya kishingida agefen gadon yana fitar da numfashi ahankali,

“Yau sau uku kina bata min jikina”

Yi tayi kamar bataji abinda yace ba saboda nauyin da maganar tayi mata,

“Yanzu sai kinsa nasake alwala bayan nayi alwalata ta sallar la’asar”

Tashi yayi yafita bayan yaja hancinta, saida tasake komawa tayi alwala sannan tafito tazo takarasa shiryawa, riga da skirt na leshi ruwan kwai tasaka sannan tayi salla tafita bayan tagyara fuskarta,
.
Mami da yusleem tahango zaune, shi yana cin abinci yayinda ita kuma mamin ke karanta jarida wanda yazama dabi’arta domin kullum saita tura ansiyo mata,

Ruwan sanyi ta dauko acikin fridge ta zauna akan kujera, yusleem ta kalla wanda ya kafeta da ido yana kallonta yana cin abincin dake gabanshi,

“Su yaya yusleem jaraba, ashe kai dinma jarababbe ne ban saniba” tafada acikin ranta domin gani tayi yasake kayan dake jikinsa maimaikon bakin wando yanzu blue ne ajikinsa kuma ta tabbata wannan kallon da yadameta dashi kari yake nema,

Idanuwanshi ya lumshe mata sannan yabude su akanta, kawar da kanta tayi tamayar kan tv,

“Yawwa ni ina tsarabar tamune naji shiru ba ace gataba bayan kuma tunda rana naji ance aje akarbo” mami tafada tana murmushi,

Daga shi har ita sai lokacin ma suka tuna da maganar domin har sun manta ma da makasudin zuwanta dakin nashi saboda shagalinsu kawai suka sha,

“Mami zan baku dazunne ban ganiba amma bari ingama sai inje indubo”

“To adubo akawo mana” inji mami,
.
“Wallahi mami kinga wacce ta sa namanta wurinma da na ajiye” yayi maganar yana nunata da spoon din da yake cin abinci.

“A’a wallahi mami babu ruwana” tafada tana harararshi, murmushi mami tayi tace,

“Rabu dashi hafsa ai nasan ba dagaske yakeba..”

Ajiye filet din dayake cin abinci yayi yamike yafita babu jimawa sai gashi yadawo dauke da wasu yan madaidaitan gold case guda biyu wadanda basu da girma, mikawa mami yayi yazauna akusa da ita,

Karba tayi fuskarta dauke da murmushi tasoma dubawa, wasu hadaddun Indian gold ne kanana ba manya canba sai faman walwali suke suna daukar ido,

“Mami ga tsarabarku…”

“Ai kuwa gashi munsha tsaraba, kai da kaje neman lafiya shine harda su tsarabar daham?”

“Babu komai mami dama da niyyar siyo muku natafi shiyasa ma natafi da kudin..”

“Cancadi, Allah yakara lafiya yayi albarka, hafsa matso kigani”

Tashi hafsa tayi taje wurin mami nan ta mika mata sarkokin da earrings dinsu da dan karamin ring aciki, bin sarkokin da kallo hafsa tayi nan taga guda daya harda wani dan siririn rubutu anrubuta harafin H ajiki,daga gani itace tata,
.
“Wow…., yaya yusleem mun gode madalla Allah yakara lafiya da arziki mai amfani”

“Amin hafsa, idan kin gama murnar gani kitashi muje unguwar mudawo” yace da ita yana kashe mata ido,

Mikawa mami tata tayi ita kuma tanufi cikin daki da tata,

Tana tsaye gaban mirror tana kokarin saka sarkar sai gashi yashigo, hannu yasa yakarbe daga hannunta ya saka mata dan kunnen sannan ya sa mata sarkar a wuyanta, hannu yakai yashafi wuyan nata,

“Kinyi kyau sosai, sarkar ta amsheki”

Murmushi tayi har hakoranta suka bayyana,

“Nagode yaya yusleem”

“Shirya kizo muje mugaida su ummi mudawo”

Juyawa tayi ta kalleshi, “kace ai zamuje gidansu maman amir sannan idan mun fito ina son naje gidan kawata amina”

“A’a banda wadannan su kyaje su daga baya”

Rakwarkwabe fuska tayi, “dan Allah yayana…”

Murmushi yayi, “naki”

“Haba sweetheart”

Dariya yayi yajuya zai fita,

“Yau harda su canja min suna saboda za akware ni ko? To naki wayon”

Kafin tabashi amsa har yafice daga cikin dakin murmushi tayi ta gyara fuskarta tasaka hijabinta tafita bayan ta fesa turare,

Atsaye ta iskeshi afalo yana jingine ajikin bango yana yin game awayarshi,

Bedroom din mami ta leka tayi mata sallama ta fito, har lokacin yana tsaye kamar yadda tabarshi yana yin game din,

“Yaya yusleem muje to”

Shiru taji yayi dan haka ta leka screen din wayar nan taga game din angry birds yake yi,

Pause yasa ya kalleta, “muje,banso ne wannan game din na fadi”

“Kawo incigaba da yimaka”

Hanata yayi tarike hannunshi,har suka fita daga cikin falon bata iya karbar wayar daga hannunshi ba, saida suka shiga cikin mota sannan yabata,

Gidansu hafsat suka fara zuwa,ba karamin dadin ganinsu Ummi tajiba dan haka ta karbesu da murnarta, tunda hafsa taga yanayin gidan ta fahimci cewar canji yasamu ai kuwa tunaninta yabata gaskiya domin koda suka shiga cikin daki ummin ke fada mata cewar kayan mahaifinsu da customs suka rike ansakosu sun fito yanzu haka mahaifin nasu yana can wurin hada hadar kasuwancinsa, murnar awurin hafsat kamar zatayi me domin babban farin cikinta shine taga su Ummi cikin walwala,nan ta nunawa ummi itama sarkar gold din da yusleem ya siyo mata, ummi albarka tasa tareda yimusu fatan alkhairi,
.
Sun dan jima agidan Ummi sannan suka yimata sallama suka fito, gidan hayarsu nada suka hara,gidan nanan kamar yadda yake ada matan gidan gasu nan zazzaune suna hira kowacce tana girkinta nadare akofar dakinta, hafsat ce tashiga ita kadai, duk cikin matan gidan babu wanda yaganeta har saida tayi musu bayanin cewar sune masu waccan dakin dake rufe, da gudu Maman amir tafito tazo ta rungumeta suka shiga daki,

Daga gani babu tambaya Maman amir tasan hafsat hutu da jin dadi yasamu domin gaba daya ta sauya fatarta ta goge,

Fitowa tayi bayan sun gama gaisawa da Maman amir tafita wurin yusleem yashigo suka shiga dakinsu nada wanda suka zauna aciki, rungumeta tabaya yayi yana bin dakin da kallo yana tuno abubuwa da dama tsakaninshi da ita wadanda suka faru acikin dakin,

“Yaya yusleem ya zamuyi da wadannan kayanne?”
.
“Kibarwa kawarki su”

“Nima haka nace araina amma fa banda keken sakata domin tsakanina dashi amanace”

Murmushi yayi yasaketa yaje ya ciro mata shi daga cikin shirgi, sallama suka yiwa su Maman amir bayan sun fada mata cewar sun bar mata komai nasu dake cikin dakin,
.
Gidan amina kawarta yakaita acanma tayi sallar magrib domin lokacin salla yayi, daga nan kuma suka wuce gida, lokacin da sukaje gida sun tarar da mami suna zaune suna hira da khadija, yusleem ko shiga baiyiba yawuce part dinsu khalifa yayinda ita kuma hafsa takarasa wurin khadija,nan suka shantake sai wurin 8 sannan khadija tatafi gida.

Daren yau kam duk da hafsa bata son zuwa part dinsu khalifa saida yusleem yakaita, kallo ya kunna musu a laptop dinshi daga karshe anan tayi bacci dan haka acan suka kwana saida asuba sannan ta tuna a inda take, kokarin guduwa tayi domin komawa part din mami amma ya hanata saboda akwai bukatar da yake bukata.

Sai da karfe 8 sannan tasamu tagudu takoma part din mami danma tayi sa’a mamin bata fitoba, nan tasake kwanciya tasha baccinta saida 11 tayi sannan tatashi tayi wanka tashirya tana shirin fitowa gogan yashigo yasha wani farin lallausan yadi mai kyau,

Harde hannuwanshi yayi yana kallonta,

“Yaya yusleem ina kwana?”

“Kin tashi lafiya?”

“Lafiya lau”

Hannunta Yakama yana kallonta,karan hancinta yaja,

“Dama zuwa nayi infada miki wata muhimmiyar magana mai muhimmanci dan haka ina son ki nutsu ki saurareni kuma ki fahimceni…!”

   ***

Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi,

“Ina sauraronka ya yusleem”

“Hakuri zan baki akan rashin baki hakkinki da banayi wannan yana faruwane bisa umarnin da likita yabani saboda har yanzu akwai sauran bacteria atare dani so idan nace zan baki hakkinki to zan iya cutar dake ta hanyar maidaki victim, shiyasa nake mai baki hakuri da kikara dan bani lokaci har zuwa time din da zan koma Cairo naga likita nasan insha Allah lokacin komai yazama normal ina dawowa abinda zan fara yi shine insauke hakkinki inbaki kayanki…”

Juya masa baya tayi cikeda kunya tana murmushi saboda ita dataji yace zasuyi magana a tunaninta wata muhimmiyar magana ce ashe wai wannan zai sanar da ita,
.
Rungumeta ta baya yayi hancinsa yana shakar daddadan kamshinta,

“Banji kince komai ba Nana hafsa”

Jin tayi shiru yace,

“Uhm?”

“To yaya yusleem me zance? Ni wallahi nazaci wata muhimmiyar magana zaka fada ashe wannan zakace..”

“Wannan ba muhimmiya bace? Wannan maganar ai ni aganina tafi kowacce magana da zan fada miki ayanzu”

“Ni bahaka bane gaskiya”

Murmushi yayi ya juyo da ita,

“Tsakaninki da Allah bakya son inbaki hakkinki?”

Zame jikinta tayi zata fita daga cikin dakin yasake rikota,

“Ai babu inda zakije sai kin amsa min tambayar da nayi miki”

“Kai yaya yusleem, nifa yunwa nakeji”

“Ehh zakice min ko a’a”

“To ehh”
.
“Ohh dagaske bakya so din kenan ko? Shikenan to bari Indaina wahalar da kaina na sai nasamu lafiya, basai nakoma Cairo dinba sai kawai inzauna muci gaba da zamanmu haka”

Dasauri ta dago ta kalleshi bayan ta zaro idanuwa,

“Haba ya yusleem, haka zaka yita zama da cuta ajikinka?”

Murmushi yayi yaja hancinta,

“Dama ashe karya kike ba gaskiya kika fada ba”

“Nifa ba wannan nake nufiba”

“Ai nariga da nagane wayonki”

“Allah ya yusleem ni bahaka nake nufi ba”

“To naji, ke bakya bukatata kenan?”

Kwacewa tayi daga jikinshi tajuya tana bubbuga kafa, “nidai Allah yaya yusleem kabari”

“Shikenan nabari amma gaskiya ni kullum acikin bukatarki nake”

Hannayenta tasa tarufe fuskarta taki juyowa,

“Tunda ni ba a bukatata bari natafi..”

Juyawa yayi zai fita tabi bayanshi,
.
Tea tahada masa sannan tazuba mishi sauran kayan soye soyen wanda aka tanada dan karin kumallo,

Har yagama karyawa mami bata fito ba, kallon hafsa yayi,

“Nabar hulata adakinki, jeki dauko min”

Tashi tayi tanufi cikin dakin taje ta dauko hular tadawo,

Hannu ya mika zai karba ta hanashi,

“Zan gwada sa makane ingani ko na iya”

“Tom gwada ingani…”

Wayarshi yazaro saboda jin yar tsuwwarta daga cikin aljihunsa, ganin alh musa mori ne yasashi saurin dagawa, saka masa hular tayi tazaro turaren data boyo tasoma fesa masa ajikinshi, hannunta yarike bayan tagama fesa masa turaren yajata kan cinyarshi, kokarin kissing dinta yake duk da bai gama yin wayar ba, kanta ta ajiye akan kafadarshi tana shafa kasumbarshi, hannun yarike yakai bakinshi,

Zumbur ta mike daga kan cinyarshi saboda jiyo maganar mami da tayi tana kokarin fitowa daga bedroom wanda da alama waya take yi,

Akan kujera tazauna itama mami tazo ta zauna har lokacin bata gama wayarba, saida yusleem yajira tagama sannan yagaidata yafita yana yiwa hafsa wani kallo, “adawo lafiya” tafada ahankali wanda shi kadaine yaji, binshi da kallo hafsa tayi har yafice daga cikin falon.

Acikin mota yazauna yana kallon fuskarshi tajikin mirror, hular da hafsa tasaka mishi yake kallo domin ba karamin kyau yayi ba, tada motar yayi fuskarshi kunshe da murmushi har yaje gidan alh musa,

Kamar jiya yauma hafsa yar gidan alh musa tana tsaye asaman upstairs awani dan corridor tana jiran ganin zuwan yusleem cikin sa’a kuwa saiga motarshi ta kunno kai, murmushi tayi lokacin da taga yafito daga cikin motar yana duba agogon dake daure a hannunshi,
.
“Fine boy” tafada ahankali tana kallonshi, bata iya dauke idonta daga kanshiba har saida taga kulewarshi sannan ta nufi hanyar saukowa.

Kamar jiya yauma yusleem afalon alh musa ya sameshi yazauna bayan sun gaisa, tashi alh musan yayi yashiga ciki yabar yusleem zaune afalon,

Hafsa ce tashigo dauke da wani kyakkyawan faranti sai fitinannen kamshine ke fita daga jikinta,

Doguwar riga tasa ja mai gajeren hannu tayafa dan karamin bakin mayafi akanta,

Agaban yusleem ta ajiye abincin,

“Ina kwana…?”

“Lafiya lau, yagida”

“Alhamdulillah,bismillah ga abinci”

“Alhamdulillah”

“Haba dai, dan Allah kaci ko babu yawa, please” ta karashe maganar kamar zatayi kuka,

“Ok to nagode”

Juyawa tayi tafita baiyi niyyar cin komai ba amma yahada coffee yasha yana gamawa alh musa na fitowa dan haka babu bata lokaci suka dunguma suka fita.
.

Karfe 8 nadare suka dawo domin daga yau sun gama zagayen da yakamata suyi saboda duk inda ya dace suje sunje kuma yusleem zai fara fita aiki nanda sati mai zuwa domin alh musa ya gabatar dashi,

Gaba daya hankalin yusleem yayi gida saboda yau wuni guda baiga hafsanshi ba dan haka suna dawowa yaso tafiya gida amma alh musa yahana yace sai sunyi dinner haka ya zauna ba don yasoba, hafsa ce takawo abincin yanzu blue din doguwar rigace ajikinta da dan mayafi, tuwon semo miyar ogu ta kawo musu,

Filet ta dauka ta zuzzuba musu sannan tafita, kadan yusleem yaci yayiwa alh musa sallama yafita,

Abin mamaki koda yaje motarshi saiyaga tayoyin gaba daya sun sace babu iska motar tayi kasa, tsayawa yayi yana duban motar cikeda mamaki,

“Ya yusleem lafiya kuwa?” Yajiyo zazzakar muryarta daga bayanshi,juyawa yayi ya kalleta,

“Lafiya lau, tayoyin motar ne suka sace…”
.
“Ayya to yanzu ya za ayi? Gashi dare yayi balle inkira maka bakanike dinmu..”

“Ah babu damuwa bari kawai zanje insamu keke napep so gobe sai nazo da bakanike”

“A’a kabari inyi dropping dinka mana ko kuma inbaka motata sai katafi da ita gobe ka Kawo min”

“Karki damu babu komai”

“A’a wallahi gaskiya bazaka hau keke napep ba da daren nan,ka karbi motata dan Allah katafi da ita, haba mana ya yusleem yaushe da ajinka da komai zaka wani tafi a keke napep…”

Tsayawa yayi yana kallonta yanda ta tubure sai yatafi da motarta, shi abinma dayafi bashi mamaki yanda akayi ta rike sunanshi tamau abakinta tamkar itace ta rada mushi ga wata shagwaba da take yimasa,

“Ya yusleem please say something..”

“Am ina ganin basai na karbi mot…

“Please ya yusleem don’t say bazaka karbi motata ba, please ban son wani abu yafaru dakai”

Daga mata kai yayi alamun takawo key din, juyawa tayi zuwa cikin gida mintuna kadan sai gata tafito, yana tsaye yana bin tangamemen tsakar gidan da kallo wanda ya wadatu da shuke shuke da hasken fitilu kamar rana,
.
“Gashi” ta mika masa tareda dan rissinawa, karba yayi yana jiran ta nuna mishi motar,

“Ga motar can, the last one din”

Parking space din yaje wanda ke dankare da lafiyayyun motoci hadaddu, takarshen ya bude kamar yadda tafada, ash colour ce motar kirar Mercedes Benz mai bakaken glass,shiga yayi yabawa motar wuta ya fito, tana tsaye  tana kallonshi har yazo saitinta, kasa yayi da tintac glass din yaleko,

“Nagode sai goben, thank you”

“Don’t mention it, Allah yakaimu”

Sai da taga fitarshi daga cikin gidan sannan tanufi ciki cikeda murna domin dama tana neman hanyar da zata samu tayi magana dashi sai gashi tasamu cikin sauki….

       ***

K’arfe 8:30 yusleem yashiga cikin gidansu daidai lokacin da yashiga yahango hafsat itada khadija suna tsaye jikin motar khadijan suna hira,
.
Fitowa yayi hannunshi rikeda robar ruwa, jikinshi gaba daya ya kamu da daddadan kamshin dake cikin motar Hafsat domin wani irin fitinannen kamshi ne shi ba turaren wuta ba shi ba perfume spray ba,

Ganin yusleem yasa hafsa jin mamaki domin a iya saninta yanzu basuda mota irin wannan,

Wani kallo khadija tabishi dashi lokacin da yazo daidai kusa dasu, gaisheshi tayi ya amsa batare da yatsaya ba bare ya kalli inda take, dan jijjiga kai tayi tana mamakin takamarshi domin har yanzu wannan jijji da kan nashi yana nan bai sauka ba saima karuwa da yasake yi,

Sallama sukayi tatafi ita kuma hafsat tawuce ciki, a bakin kofa taganshi tsaye da alama ita yake jira, tana zuwa kusa dashi taji ya rungumeta, kissing dinta yafara yi,

“Ya yusleem daga dawowa?”

“Ehh mana barka da dawowa nake baki ko bakya so?”

Murmushi tayi tarufe fuskarta, hannunshi yasakala a kugunta yana fuskantarta,
.
“Yau wuni guda ban gankiba, ke amma babu ruwanki ko, ko ma damuwa bakiyi ba”

“To ai nasan duk acikin aikine, naganka ma da sabuwar mota tawaye?”

Shiru yayi yarasa amsar da zai bata domin yasan idan yafada mata gaskiyar abinda yafaru kila za a iya samun matsala,

“Uhm yaya yusleem?” Tafada tana wasa da clips din dake jikin rigarshi,

“Motar gidan alh musa ce na aro saboda ta mamin da naje da ita tayoyinta sun sace..”

Murmushi yaga tayi tareda jan dogon hancinshi abinda bata taba yiba,
.
“Ban yarda dakaiba” shine abinda tace tareda kokarin tafiya, sake kankameta yayi yana sinsina wuyanta,

“Duniya tazo karshe tunda gashi hafsa tafara karyata ni”

Dariya ce tazo mata saboda jin abinda yace

“Ni ban isa inkaryata yaya yusleem ba, yanzu ni duk bama wannan ba zo muje kayi wanka sai kafito kaci abinci”

Jin abinda tace yasashi dan murmusawa,

“Yawwa Nana hafsa na, zo muje tare to”

Tana makale ajikinshi suka nufi part din su Abdul, suna zuwa balcony yayi sama da ita yabude part din suka shiga, har cikin bedroom yaje da ita ahaka, asaman gado ya ajiyeta tareda binta,

“Gaskiya wata yarinya tafara nauyi, mami tana bata abinci tana koshi”

Murmushi tayi tashafo kanshi wanda ke kwance bisa kirjinta,

“Kuma kaga ko rabinka banyi ba fa”

“Ahh karya kike da ace akwai scale da angwada”

“To agwada”
.
“To agwada mana” yafada tareda dago kanshi yana kallon fuskarta,

“Tayaya?” Ta tambayeshi,

“Zamuje agwada kibari sai nasamu lokaci, yanzu tashi ki hada min ruwan wankan…”

Tayar da ita zaune yayi tashiga cikin bathroom shikuma yasoma cire agogon hannunshi, fitowa tayi tasameshi tsaye yana jiranta bayan tahada mishi ruwan,

“Sauranki cire wannan..” Yayi maganar yana nuna mata kayan jikinshi, kunya taji ta kamata domin bata taba cire mishi kayaba amma saita daure, clips din rigarshi tasoma cirewa nan taji ya matseta ajikinshi har suna jiyo bugun zuciyar junansu,

“Yaya yusleem easy mana..”

Sassauta rikon da yai mata yayi,cire mishi kayan tayi tabarshi da na ciki kadai.

Ahankali taji yafara zuge zip din dake jikin rigarta,saurin kallonshi tayi,

“Lafiya?”
.
Langabar da kanshi yayi,

“Tare zamuyi dan Allah karkice a’a”

Kasa tayi da kanta nan ya kinkimeta yayi cikin bathroom din da ita, duk jinta tayi atakure saboda sam bata shiryawa wankan ba shiyasa abin yazo mata kwatsam,

Dadewar da sukayi acikin bathroom din ba kadan bace daga karshe dai shine yarigata fitowa yazo yatsaya agaban mudubi yafara goge sumar kanshi da dan karamin towel,

Yana cikin shafa turare yahangota tana fitowa,sunkuyar da kanshi yayi yana murmushi yaci gaba da bulbulawa jikinshi turare domin shi arayuwarsa yana tsananin son kamshi ko nawane zai iya kashewa ya siyi turare komai tsadarshi,

Ji tayi gaba daya dakin ya kaure da kamshin turarukan da yake shafawa wanda yawancinsu oil ne masu karfi,

Ta gefenshi tabi ta dauki turaren zata shafa,

“To kinga ai na taimaka miki kinyi wanka yanzu kina zuwa sai dai kawai kisa kayan bacci ki kwanta”

Turo baki tayi tana harararshi, kunnenshi guda daya ya kama,

“Nadauki laifin, yi hakuri…”

Murmushi tayi batace komaiba har ta gama shiryawa tasa kayanta, koriyar t shirt yasa da boxer, ba karamin kyau taga yayiba wanda harta shagala tana kallonsa bata saniba, hure mata ido yayi da bakinshi,
.
“Ko wankan bai isheki ba akara wani?”

Makale kafada tayi,

“Kyau kamin”

“Kema haka”

“Nagode”

Murmushi yayi bai bata amsaba illa kama hannunta da yayi suka tasamma kofar fita, shirun itama tayi aranta tana jin wani irin babban lamari agame dashi, jin har suka fita baiyi magana yasata fahimtar yan miskilanci nashi sun motsa,

Har saida sukaje cikin part din mami sannan yayi magana,

“Zo inji cikinki kinci abinci kuwa?”
.
Zame hannunta tayi tagudu tarigashi shiga cikin falon,

Mami nazaune tana cin tuwon shinkafa miyar lalo,

“Yau hira tayi muku dadi keda khadija, sai yanzu tatafi?” Mami tace tana murmushi,

“Ehh mami..”

“Mami karya take tun dazu khadija tatafi” yusleem yafada lokacin da yake shigowa,harararshi hafsat tayi ita kuma mami tace,

“Kajishi ko taya yasani shida baya nan”

Murmushi hafsa tayi gamida yimasa gwalo,

Tuwon hafsa tazuba yazo yazauna akusa da ita yasa hannu aciki, duk da tasan sun saba cin abinci tare amma saida taji kunyar mami sai dai ita mamin babu ruwanta bata ma san sunayi ba domin ta maida hankakinta akan labaran da take kallo atashar NTA hausa.

Hafsat tariga kowa tashi daga falon saboda ciwon da taji cikinta yanayi, kwanciya taje tayi acikin bedroom,
.
Daga mami har yusleem babu wanda yakawo wani abu dan haka suka cigaba da hirarsu har wani lokaci, sai wurin 10 sannan mami tashiga dakinta, saida yusleem yabari bayan shigar mami kamar da mintuna 15 sannan shima yatashi yanufi wurin hafsa,

Akwance ya sameta dafe da cikinta zuwa mararta,

“Lafiya?”

Girgiza masa kanta tayi, “cikina ne ke ciwo”

“Da kuma mararki ko?”

Daga mishi kai tayi bayan tarufe idonta, zama yayi yadauketa yadorata ajikinshi yasoma shasshafa mata cikin nata har zuwa mararta ahaka suka raba dare har saida bacci yadauketa sannan ya kwantar da ita shima ya kwanta.

Washe gari tariga shi tashi har ta shirya bai tashiba,

Tana tsaka da fesa turare ya bude idonshi ya kalleta,

“Har kin tashi? Marar taki tadaina ciwo?”

Kai ta daga mishi, “tadaina, naji sauki”

“Har yazo kenan”

Shiru tayi masa,

“Zo inji kamshin wannan turaren saboda wallahi kamshinne yatada ni…”
.
Ajiye turaren tayi takarasa kusa dashi, cusa fuskarshi yayi ajikinta har na tsawon wani lokaci, dakyar yabarta yatashi yafita,shiryawa yaje yayi yafito yazo tabashi breakfast yaci wanda kusan ma tare suka ci, zama yayi suka fara yin game din temple run awayarshi, saida yajira mami tafito suka gaisa sannan tarakashi zai tafi,motar yabude yashiga bayan yaja hancinta, ramawa itama tayi ta hanyar jan nashi, zama yayi acikin motar yasauke glass yana kallonta, leka cikin motar tayi nan tahango takalmin mata mai tsini ajiye akan kujerar gaba,

Dauke kanta tayi ta daga mishi hannu yaja motar yafice, tunda taga wannan takalmin sai kuma taji hankalinta yakasa kwanciya, wani irin zafi takeji acikin zuciyarta, da wannan takalmin tawuni aranta.
.
Yusleem kuwa lokacin da yaje gidan alh musa mori samu yayi har angyara mishi tayoyin motarsa an wanke motar tas sai wani sheki takeyi, packing yayi yafito yana kokarin rufe motar yasoma jiyo takun tahowar hafsat domin dama tana tsaye tana sauraren zuwanshi, juyawa yayi,tana sanye da bakar doguwar riga da dan mayafi kamar kullum wannan fitinannen kamshin nata yana yawo acikin iska,

“Barka da zuwa ya yusleem”

Dan murmushin yak’e yayi, “yawwa, ga motar nagode fa,thank you”

Karbar key din tayi ta dan shagwabe fuska,

“Ni ya yusleem kadaina yimin godiya dan Allah, saikace wanda nayi maka wani babban abu?”

Murmushi yayi yajuya yafara tafiya,

“Duk da haka nagode”

Tsayawa tayi tana kallon yanda yake tafiya yasa hannunshi guda daya cikin aljihun wandonshi, akan idonta yashige cikin sashen Alh musa mori….

*
***

Tsaye tayi tana kallonsa da murmushi akan fuskarta,har ya bacewa ganinta bata iya yin kwakkwaran motsiba,

Tana nan atsaye har yafito daga sashen mahaifin nata sai lokacin ta dauke idonta daga kallon kofa tamayar kan kyakkyawar silbebiyar wayar dake rike a hannunta,

Har ya nufi motarshi sai yafasa yanufi wurinta,

“Sai yanzu nakula ashe ma angyara min tayoyin…”

Batare da ta dago ta kalleshi ba tayi magana cikin aji da yauki,

“Uhm karka damu..”

“To nagode, bari naje”

“Am bakaji ba, phone number dinka nake so saboda wata rana”

Murmushi yayi, “babu damuwa”
.
Wayarta ta mika masa ya amsa ya rubuta mata sannan ya wuce, motarshi ya dauka wacce keta faman tashin daddadan abin kamshin da aka saka aciki,

Kansa tsaye banki yawuce wanda kusan acanma yau yabata lokaci domin sai bayan sallar azahar sannan yagama dasu, duk wasu kudadensa wadanda ke hannun alh musa ayau yaturo masa kayanshi sannan zai mallaka masa takardun gonakinsu da na filaye,

K’arfe uku da yan mintuna ya koma gida, iya mami kadai ya tarar afalo tana kishingide tana hutawa, samun wuri yayi yazauna cikeda alamun gajiya atare dashi,
.
“Ya akayi naganka duk kayi la’asar?” Inji mami,

“Mami wallahi nidinne agajiye nake, yanzu haka daga banki nake”

“Sannu, bari akawo maka abinci”

“To mami, ina yar taki tayi naji banji motsinta ba?”

Dan murmushi mami tayi bayan ta tashi domin Kawo masa abinci,

“Tana ciki inajin bacci ma take yi”

“Lallai tana hutawa”

Murmushi mami tayi bata sake magana ba tawuce dining area ta zubo masa abinci ta Kawo masa, fried rice with chicken salad sai coconut juice mai dan banzan sanyi,

Diban abincin yayi acikin filet ya nufi cikin bedroom din hafsa, tana kwance akan gado tana bacci, agefenta ya zauna yaja babban yasanta na kafa,

Har yagama cin abincin bata motsa ba, yana shirin ja mata hanci yaga tana kokarin yin juyi, riketa yayi nan ta bude idonta ta ganshi,

“A’a yaushe ka dawo?”

“Tunda jimawa, nazo kinata bacci”
.
Murmushi tayi ta mika masa hannunta yarike ta tashi zaune,

“Yau kadawo da wuri”

“To ai yawon yau bai kai najiya ba”

Murmushi tayi tai shiru saboda tarasa ta inda zata fara,

Ji tayi ya matsa gareta sosai,

“Sai naga kamar akwai abinda kike son fada,hakane?”

Murmushi tayi,

“Hakane amma bana son fada yanzu”

“Saboda me?”

“Saboda kar ka ga kamar banda juriya”

Murmushi yayi yasa hannuwanshi duka ya tallafo kumatunta,

“Bazan yi wannan tunaninba dan haka karki ji tsoron komai fada min”

Shiru tayi tasaki fuskarta ta kawatata da murmushi,

“Dama cewa zanyi har ka mayar mata da motar tata?”

Dan dam yayi jin abinda tace, cikeda mamaki ya kalleta,

“Wacece?”

“Ita wadda ta baka aron motar mana”

Murmushi yayi yasake matsarta,

“Kece kika santa amma nidai ban san wata mai bada aron motaba”

“Ohh dama nima hasashe nayi saboda naga takalminta aciki shiyasa nazaci ko…”

“Ko me? Ni ban san motar ko ta macene ko ta namiji ba saboda nidai kawai bani aro akayi”

Murmushi tayi ta kalleshi,

“To shikenan magana tawuce,kuma har hankalina ya kwanta”
.
Murmushin shima yayi ya kalleta yana nazarin maganganunta duk da bata fito fili ta fada ma amma yafahimci kishi ne fal zuciyarta saboda takalmin hafsat dataga acikin motar,

“Yanaji kayi shiru?”

“A’a babu komai, kawai dai tunanin fara fita aiki inbarki ke daya nake”

Murmushi tayi, “to basai muna tafiya tare ba”

“Hakama za ayi”

“Ko?” Tace tana murmushi,

“Ehh mana”

Zamewa tayi zata kwanta ya riketa ya langabe Kai, babu yanda ta iya dole sai tare suka kwanta.

Acikin yan kwanakin ya dauketa suka fita ta zazzabo masa kayan sawa nafita office tun daga kan kananan kaya, suit, shaddodi,yadika da takalma, banda turaruka da sauran kayan bukata,

Cikin lokaci kankani yusleem yadawo yusleem dinshi na ainihi dan gaye mai ji da kwalisa,

Wata Lafiyayyiyar mota sabuwa mai tsada yasa aka Kawo masa yasiya saboda zuwa office,
.
Ranar Monday yafara fita bayan mami da hafsa sunyi masa addu’o’i masu tarin yawa, ciki suka koma bayan sunga tafiyarshi, laptop dinshi hafsat tadauka wacce yabar mata aro tayi game domin debe kewa kafin yadawo,

Tana cikin bedroom azaune tana yin game din wizo taji sallamar khadija,da murna tatareta domin yanzu khadija yar gidace ba bakuwa ba nan suka bude babin hira har hafsat ke sanar da khadija yusleem yafita office,

K’arfe 3 hafsa tashiga kitchen da kanta ta hadawa yusleem abinci, shinkafa da salad da miyar dafaffen kwai,

Shirya masa abincin tayi akan table taje tayi wanka tafito tashirya bayan ta hade jikinta da turaruka masu kamshi,doguwar riga ta atamfa tasa wacce ta tsuke daga kirji sannan ta baje daga kasa,

Yusleem bai samu dawowa gidanba sai karfe 5:30,tana tsaye cikin falo taji kamshin turarensa, cikin nutsuwa da jan hankali tajuya ta kalleshi tana yimasa murmushi, shi dinma murmushin ya aika mata dashi,dauke kanta tayi taci gaba da abinda takeyi har ya karaso kusa da ita, kafadarshi yasa ya bugi tata,

“Babu sannu da zuwa baby nanah..?”

Murmushi tayi ta dubeshi,

“Da akwai mana, sannu da zuwa…”

Hular kanshi yacire yana shafa sumarshi,

“Mami fa?”

“Yanzu tafita, baku haduba?”

“A’a bamu haduba, kuma naji dadin jin hakan domin ko babu komai zan dan sake da ke before tadawo, kima fara shiri mun kusa barin gidan nan..”

“Ko zamu bari amma ai kabari kaje Cairo kadawo tukunna ko?”

Murmushi yayi ya lakuce mata hanci,

“Kafin sannan dinma inada bukatar kasancewar mu mubiyu..”

Kawar da zancen tayi ta hanyar fadin,
.
“To zo muje kayi wanka sai kazo kaci abinci…”

Bai musa mataba yabi bayanta suka nufi part din da yake, itace ta taimaka masa yayi wanka yashirya cikin kananan kaya bakar t shirt round neck da bakin boxer,part din mami suka koma tazuba mishi abinci tasoma bashi abaki, hannunta yarike cikin nashi yana yin wasa dashi domin har acikin ranshi yana yaba irin kulawar da take bashi batare da nuna gajiyawa ba,

“Baka bani labarin office ba”

Hadiye abincin dake bakinshi yayi,

“Zan baki amma ba yanzu ba sai dare yayi idan munzo yin bacci”

“Kai wai ya yusleem baka da magana sai ta dare”

“To ai lokacin ne nafi samun nutsuwa”

Kawar da kanta tayi ta ci gaba da bashi abincin har ya koshi nan kuma ya kinkimeta ya dorata bisa cinyarshi suka fara buga game,

“Meyasa aka yimiki wannan zip din tabaya? Arinka yimiki tagaba..”

Hannunshi tarike cikeda kunya,

“Ta gaba kuma sai kace wata mai shayarwa…”

Dariya yadanyi ya hade hannuwanshi da nata,

Ahaka mami ta dawo ta iskesu, bayan sallar magrib yakirata wai ta rakashi unguwa, a motarshi suka fita domin zaga gari kawai, basu suka koma gidaba sai 9, kullum haka ce take faruwa kamar doka sai sun fita yawon zaga gari da daddare,

Tuni cikin kankanin lokaci harkokinshi suka soma mikawa suna hababbaka, alh musa kuwa ya maidashi tamkar mahaifinshi domin har mami yadauka taje ta gaidashi, kusan kullum sai yaje gidan saboda yazama tamkar dan gida, hafsa kuwa akullum da tunaninsa take wuni take kwana saboda zuciyarta da ruhinta sun yaba dashi kuma sun aminta da nagartarsa,

Yau kam kasa daurewa tayi dan haka ta kuduri aniyar sanar dashi sirrin dake cikin zuciyarta wanda ya jima yana azabtar da ita,

Waya tayi mishi tace abbanta na son ganinshi domin yau throughout baizo gidan ba, cemata yayi gashi nan zuwa nanda 20 minutes, cikin sauri tafada bedroom dinta tasoma shirin tarbarshi…..

 
       ***

Sauke manyan idanuwanshi yayi masu mutukar haske akan fuskar hafsa wacce ke zaune tana hada masa green tea,

“Yaya yusleem ina zakaje?” Ta tambayeshi tana juya tea din da spoon,

Kafarshi ya dora akan hannunta dake ajiye yadan taka ahankali,

Yar kara tasaki ta runtse idonta,

“Ahh sorry, zo mugani” yace da ita yana murmushi kasa kasa,

“Ya yusleem Allah da saninka ka takani..”

“Bada sanina bane baby nanah, zo ingani”

Tashi tayi tana yarfe hannun taje wurinshi inda yake zaune agefen gado, riko hannunta yayi ya zaunar da ita bisa cinyarshi yakama hannun yana hurawa,

“Yi hakuri bazan sake ba”

Daga masa kai tayi,

“Ina zakaje? Naji kamar kana yin waya kana zaka fita”

“Ehh ba jimawa zanyiba, gidan alh musa zanje, yau banje na gaidashi ba shine yake nemana”

“Zan bika…”

Murmushi yayi yasoma shafa bayanta,
.
“Ai nima ba jimawa zanyiba, yanzun nan zaki ganni nadawo”

Makale kafada tayi,

“Nidai ban yarda ba zan bika”

“Kai nanah irin wannan rigima haka, ashe kema rigimammiya ce”

“To kace zakaje dani”

“Bazaki bani tea din bane insha sai yahuce?”

“Lahh mantawa nayi…” Zumbur tayi taje ta dauko masa tea din takawo tazauna a inda tatashi, abaki tarinka bashi yana sha har ya shanye,

Wata mika yayi sannan yasauke idanuwanshi akanta,

“Ga lafiya iya lafiya ga karfi amma sai dai inyita kallonki…”

Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi,

“Bawani kallona da kakeyi bayan akwai abunda kake y…”

“Wannan ma ai sake takurani yake idan baki saniba… Danke fa nakeyi, tsaya ma yanzu…”

Yunkurin tashi tagudu tayi yayi saurin riketa yana dariya,

“Daga magana sai gudu?” Yayi maganar yana shafa cikinta daga nan yafara yimata cakulkuli babu shiri tafara dariya tana kokarin kwacewa,

Tashi yayi da ita ajikinsa ya isa gaban drewar, ajiyeta yayi,

“Canja min kaya saboda wannan sunyi kananu da yawa bazan iya zuwa dasu ba”

Wata ash colour din shadda sabuwa fil ta ciro masa, tayashi sakawa tayi taciro masa hula tasa masa, gaban mirror sukaje ta dauki turare ta fesa masa,

“Irin wannan kwalliya haka baby nanah kamar mai shirin zuwa zance?” Yafada yana rungume da ita agefen jikinshi bayan ya kalli mudubi,

“Ina sone duk inda mijina yaje arinka jin yana kamshi kuma aganshi fes fes, nafi son kafi kowanne namiji kyau da kwalliya..”

Murmushi yayi ya manna mata kiss a goshinta,
.
“Allah yayi miki albarka, Allah yasaka miki da gidan aljanna”

“Amin,muje katafi karka yi dare, dan Allah karka juma”

Sake rungumeta yayi suka fita, har gaban motarshi ta rakashi, saida taga fitarshi sannan ta juya takoma cikin gida.

Yana driving ahankali yana wani tunani acikin zuciyarsa,

Kome yatuna oho sai kawai yadan saki murmushi, yau jinsa yake acikin farin ciki banda nishadin da yake ciki,

Kamar koda yaushe yauma kansa tsaye yatura hancin motarsa cikin gidan yanufi parking space, saida yadan jima acikin motar sannan yabude kofa yafito yana fitowa yashaki daddadan kamshinta wanda ya yakawowa harabar wurin sumame babu bata lokaci ko ina yadauka,

Ahankali take takowa Kwas kwas cikin takunta na hamshakan mata masu ji da aji,

“Barka da zuwa jarumin maza…” Tafada daidai lokacin data karaso gab dashi,

Dan bude lumsassun idanuwanshi yayi ya kalleta, yau wani kyakkyawan leshi purple colour tasa dinkin riga da skirt ta yafa purple din mayafi marar nauyi atakaice dai irin shigarsu tayi ta yaran masu kudi,

“Waye yace miki ni jarumi ne?…” Yace da ita yana kokarin rufe motarshi,
.
“Ai basai anfada minba domin zan iya tabbatar da hakan batare da wani yafada ba…”

Murmushi yayi yajingina ajikin motar ya zuba hannuwanshi cikin aljihun rigarshi,

“To yau dai na fuskanci tsokana kikeso..”

“Ko daya bahaka bane, gaskiyata dai nafada maka..”

Dan murmushi yayi,

“To yagida lafiya?”

“Lafiya lau, ya aiki?”

“Aiki babu dadi hafsat”

“To ko zaka kawo intayaka?”

Murmushi yasakeyi ya kalleta,

“Me zai hana idan har zaki iya”

“Zan iya mana, ka kawo kagani”

“To shikenan, yanzu dai bari inshiga wurin abba saboda naga idan nabiyeki anan zan bata lokaci”

“To ai abban baya nan, yau baima wuni agari ba…” Tafada tana danyi masa dariya,

“Amma da ai kece kika fada min yana nan”
.
“To ai son ganinka nake yi kuma nasan idan ba hakan nayiba yau bazan samu ganinka ba bayan kuma ni zuciyata bazata iya jurewa ba”

Idanuwa yazuba mata yana kallonta tsawon mintuna biyu yayinda ita kuma ta sunkuyar da kanta tana wasa da zobunan gold din dake sanye cikin yan yatsunta.

Saida ya sauke ajiyar zuciya sannan yayi magana,

“Sai dai kuma hafsa ban gane abinda kike nufiba..”

Kunyace ta dan kamata har tasa mayafinta ta rufe gefen fuskarta,

“Wallahi har cikin zuciyata naji kana burgeni tun farkon ganin da nayi maka wannan dalilinne ma yasa na kuduri niyyar baka amanar zuciyata..”

Bugun da zuciyarsa keyi yaji ya tsananta batare da yasan dalili ba,
.
Kafin yayi mata magana wayarshi dake cikin aljihunsa tafara kara, zarota yayi nan yaga hafsat ce,

Cikin sanyin murya ya daga,

“Hello baby ya akayi?”

“Ya yusleem kaje lafiya?” Hafsat tafada daga can bangaren,

“Lafiya lau, yagidan”

“Lafiya, dama mami ce tace ka taho mata da maganin tari idan zaka dawo, nima kuma ina son ka taho min da maganin ciwon mara”

“Toh, dama har yanzu baki warware ba amma kika ki fada min?”

“Saura kadan amma naji sauki, sai kadawo dai”

“Korata kike yi hafsat?”

Jin yakira hafsat yasa hafsat din dake tsaye kusa dashi tayi saurin dagowa ta kalleshi,

“A’a ba korarka nakeyi ba, sai kadawo dai”

“Toh sai nadawo”
.
Katse wayar yayi ya maida cikin aljihu yayinda hafsat tunani fal yacika zuciyarta banda tarin tambayoyin dake ta faman kai kawo acikin kwakwalwarta,

“Wannan hafsat din da yusleem yakira wacece ita? Meye alakarshi da ita? Wanne matsayine da ita awurinsa? Sonta yake? ….” Wadannan tambayoyin su taketa jerowa acikin ranta har maganar yusleem takatse mata tunani,

“Hafsat am…, bawai fahimtarki ne banyiba, na fahimci abinda kike nufi sannan kuma babu wani namijin da zai ki karbarki a matsayin matarsa, sai dai kuma ni ahalin yanzu inada mata…”

Dagowa tayi da sauri ta kalleshi idanuwanta jajur,

Girgiza mata kai yayi alamun sake jaddada mata abinda yafada,

“Inada mata hafsat, sunanta hafsat”

“To ni yanzu menene makomata da matsayina agareka? Baka sona? Baka kaunata? Bazaka aureni ba?…”

Batare da tajira amsar tambayoyin da tayi masa ba takwasa gudu gudu sauri sauri ta nufi cikin gida, tana jinshi yana kiranta amma bata tsaya ba,
.
Yajima tsaye awurin kafin yashiga motarsa jikinsa asanyaye yafita daga gidan, tukin ma kawai yana yinsa ne cikin wani irin yanayi wanda shi kansa bai san abinda ke damunsa ba, a wani chemist ya tsaya yasaiwa su mami magungunan da suka bashi sako sannan yawuce gida,

Kasancewar mami bata jin dadi mura tasakota agaba shiyasa lokacin da yakoma gida bai sameta afalo ba iya hafsat kadai yatarar tana zaune tana kallon wani Indian film kites,

Jiki asabule yazauna akusa da ita ya mika mata maganin ta karba tana kallonsa bayan tahada ledar maganin da hannunsa ta ruke,

Jingina da jikinta yayi ya ajiye kansa bisa kafadarta……

   
       ***

Hular kanshi ta cire tasoma shafa sumarshi ahankali, dan lumlumshe ido yafara yana sake nanuka jikinta domin wani kamshine yake fusgarsa,

“Yaya yusleem lafiya kuwa?” Tace dashi tana rike hannunshi,

“Lafiya lau baby, kamshinki ne yake neman tada min da hankali…”
.
Saurin juyowa tayi ta kalleshi,

“Meyayi? Ko kamshinsa ne baiyi maka ba?”

Murmushi yayi yadafa kafadarta,

“Easy, ba abinda nake nufi kenanba, tsananin dadin kamshinshi ne ke neman juyar min da kwakwalwa…”

Murmushi tayi ta tureshi ta tashi tanufi dakin mami domin kai mata maganin da yasiyo mata,

Mintuna kadan tafito ta dauki ruwa roba daya tasake komawa, wannan karon ta dan jima sannan tafito, amike taganshi kwance kan doguwar kujera,

Durkusawa tayi akasa ta dora hannuwanta ajikin kujerar,

“Ba yanzu zaka shiga ka kwanta ba?”

Hannuwanta duka ya riko yajata kan ruwan cikinshi,

“Gani nayi kinje wurin mami kinyi zamanki shiyasa na kwanta anan…”

“To ba gashi nafito ba”

Yana kokarin kai hannunta guda daya bakinshi mami tafito,

Tashi hafsat tayi gaba daya kunya tagama lullubeta domin tasan mami tagansu, sum sum tawuce cikin bedroom batare da tayi magana ba,

Zaune yatashi yana kallon mami wacce tawuce dining area batare da ta kalli wurin da yakeba,

Handset dinta yaga ta dauko wanda da alama mantata tayi awurin,

“Sannu mami, yajikin naki”

“Yawwa sannu, dasauki”
.
Mami tace dashi tareda wucewa bedroom dinta, yajima zaune awurin kafin ya mike ya nufi bedroom wurin hafsat, tana gaban mirror daure da zani tana shafa wasu dadadan turaruka, khalta maryam,da musk altahara,

Ajiye mata ledar maganinta yayi yatsaya kawai yana kallonta,

Juyawa tayi ta kalleshi itama,

“Ya yusleem ya akayi?”

Hannunta yariko cikin nashi yazauna agefen gado ya zaunar da ita ajikinshi,

“Yau basai kinsa sleeping dress ba” yarada mata acikin kunnenta, kunyace ta rufeta, dan dukan kirjinshi tayi ahankali, ta cusa kanta agefen wuyanshi,

“Kaga dazu ma haka kasani naji kunya”

“Da nayi me?”

“Da ka sa mami tazo taganmu mana”

Mikewa yayi ya kwanta ya kwantar da ita ajikinshi yana murmushi,

“Ai ba laifina bane”

“Laifin waye?”

“Laifinki mana”

“Laifina fa kace”

Lumshe idanuwanshi yayi yana sake matseta ajikinshi,

Sun jima ahaka zuwa can bata san meya faruba sai ji tayi ya sassauta rungumar dayayi mata yafada kogin tunani,

Kin bari yayi ta fuskanci cewar akwai abinda yake damunsa nan ya lallabata bacci ya dauketa, kwantar da ita yayi yatashi zaune yayi shiru yana nazari,
.
Jin zaman ya gundureshi yasashi tashi tsaye yafara kai kawo acikin dakin, sam yau bayajin bacci sannan yarasa dalilinsa na damuwa da lamarin hafsat yar gidan alh musa, haka kuma yana jin wani irin abu mai kamada tausayi tausayi yana yimasa yawo akirjinsa gameda ita,

Kukan da yaga tatafi tanayi shine yafi komai tsaya masa arai,kusanma shine makasudin rashin baccinsa, yarasa ta inda zaibi ya bullowa wannan al’amari domin shi dai ara’ayinsa baida niyyar kara aure, yafi son ya zauna da Hafsat ita kadai ya nuna mata soyayyar da sauran mata basu samuba to amma kuma ita rayuwa kana nakane Allah yana nashi kuma komai mukaddarine daga gareshi,

Bude idanuwanta tayi nan taganshi tsaye yayi shiru abisa dukkan alamu baiyi bacci ba,

Sauka tayi ahankali daga kan gadon tanufi wurinshi, dafa kafadarshi tayi nan yayi saurin juyowa yana kallonta,

“Ya yusleem…., meke damunka? Menene ya hanaka bacci? Tunanin mekakeyi?”

Kago murmushin dole yayi yasa tausasan yan yatsunshi ya kamo nata,

“Babu abinda nake tunani baby nah, baccin ne naji yaki daukata shine kawai nataho nan nake dan zagayawa”

Murmushi tayi ta dan sake yin kasa da muryarta,

“Kafada min gaskiya dai, kodai?”

Murmushin shima yayi mata ya dauketa cak yanufi makwancinsu da ita,

“Kema kindai san idan nace miki bata damuna karya nake yimiki….”

Mayar da fuskarta gefe daya tayi tana murmushi aranta tana tunanin abinda zaije yazo duk ranar da aka tabbatar masa da yagama samun lafiya domin shima taga kamar fitinanne ne,

“Yanaji kinyi shiru?”

“Ehh bacci nake son komawa”
.
Mirginata yayi takoma kasa yayi pillow da kirjinta, tun tana dan shafa sumarshi har yaji shiru alamun tayi bacci, shikam dakyar yasamu ya iya bacci cikin wannan dare.

  Tunda wannan maganar ta shiga tsakaninsu da Hafsat shikenan bai sake ganinta ba koda yaje gidan sai dai kusan kullum yana ganin massage dinta taturo mishi,

Bayan kamar sati biyu da faruwar al’amarin da wani yammaci yaje gidan bayan sun gaisa da alh musa yafito ya hangeta tsaye jikin motarshi tana wasa da key din motarta wanda da alama dawowarta kenan taga motarshi,

Dan hade rai yayi yanufi wurin,

Ganinshi haka yasata yin dan murmushi,

“Ya yusleem menene abin bata ran? Dama kawai tsayawa nayi mugaisa sannan in tambayi lafiyar takwarata da na yaranta”

Batare da yasaki fuskarshi ba yace,

“Tana lafiya”

Bashi wuri tayi ta tsaya tana kallonshi bata kara maganaba yashiga motarsa yafita daga gidan, yana cikin driving yaji karar shigowar text massage,
.
   _Ya yusleem insha Allah sai na aureka kuma zakace nafada maka…_

Cilla wayar kan kujera yayi yaci gaba da driving dinshi bayan yagama karanta sakon.

Akasalance ya karasa gida,babu kowa afalon mami dan haka kai tsaye yawuce cikin bedroom dinta nan dinma bata nan sai lokacin yatuna da cewar baiga motarta ba lokacin da yashigo, dakin hafsat yawuce ita dinma bata ciki, fitowa yayi yana tunanin to kodai tareda mamin suka fita da wannan tunanin yakarasa cikin bedroom,

Zaune yaganta tana goge mishi kananan kayanshi data wanke ta kunna laptop dinshi tana sauraren wakar dayake muradin so wadda kusan koda yaushe sai yajita,

Tsaye yayi yana kallonta yana dan murmushi domin yasan bata san yashigo ba,
.
Ahankali ya sadada yarufe mata ido da hannuwanshi ai kuwa ta kurma wani uban ihu tana salati,

Dariya ce taci karfinshi ya fada jikinta yanayi bayan ya bude mata idanuwan,

Kashe iron din tayi tahau dukanshi, hada hannayenta duka guda biyun yayi ya rike yana yimata dariya,

“Allah ya yusleem sai nafawa mami abinda kayi…”

“Yi hakuri hafsat, ke dince kika bani dariya sosai”

“To bakaine ka tsorata ni ba”

“To kiyi hakuri, kinga anjima dama ina son ki rakani anguwa”

Fadada murmushinta tayi,

“Tom shikenan, yanzu bari inhada maka ruwan wanka idan ka shirya sai muje kaci abinci”

“To tashi ki hada min”

Tashi tayi tashiga bathroom kafin tafito yayi sauri ya cire kayan jikinshi yabita ciki dole sai tare sukayi suka fito tanata kumbura fuska,
.
“Shikenan bazan karaba tunda bakya son ladan, kiyi hakuri”

Kin kallonshi tayi yayinda shikuma ya kafeta da nashi manyan idanuwan, bai san daliliba bakar fatarta tana yimasa kyau,

“Gaskiya koda ace mata hudu zanyi to duk bakake zan aura”

Dan harararshi tayi taci gaba da shafa masa mai,

“Kullum kuma sai kaita ganin kala daya babu canji?”

“Ehh mana ai tafi kyau”

Shiru tayi masa takarasa shiryashi takoma shirya kanta, kananan kaya yasa dark blue din t shirt da blue din jeans iya gwiwa,

Tattarawa sukayi suka nufi part din mami lokacin tadawo tana zaune tana waya dasu Abdul wadanda zasu dawo wani satin,

Zama sukayi takawo masa abinci yaci sannan suka yiwa mami sallama suka fita,
.
Ac ya kunna musu acikin motar ya rufe gaba daya glasses din ya kunna wata waka ta turanci _you are my African queen…_,ahankali wakar take tashi yanabi yana makale da hannun hafsat guda daya acikin nashi yana driving da dayan,

Wata hamshakiyar unguwa tamasu fada aji taga yakaisu, wani tangamemen gida suka shiga mai manya manyan part har guda hudu sannan kowanne upstairs ne,kuma daga can gefe B/Q ne,

Nafarkon yabude suka shiga nan taga tangamemen falo da kitchen da store sai dining area, saman kuma bedrooms ne guda biyu masu dauke da bathroom acikin kowanne,

“Kinga gidan da na sai mana zamu dawo nan bada jimawa ba domin har nabada asiyo furniture’s,nafi son ina dawowa daga Cairo insauka anan”

“Wai amma gidan ya hadu yaya, ga girma komai awadace..”
.
Murmushi yayi yariko hannunta suka fito, “kin dai k’i zancen ko?”

Murmushi tayi,

“To amma yanaga part din guda hudu?”

“Daya namu, daya na mami, daya nasu Abdul”

“To dayan fa?”

“Na amarenki”

Duka takai mishi,

“Allah kabari”

Dariya yayi yabude musu motar suka shiga batare da sun shiga sauran part dinba domin gaba daya parts din tsarin gininsu da komai iri dayane,
.
Saida suka gama yawonsu agari sannan suka koma gida.

Washe gari hafsat gidan umminta tatafi tawuni acan, misalin karfe 2 narana mami nazaune tana yin lunch taji sallama, har cikin falon mai sallamar tashiga sai faman budada kamshi take nan ta durkusa tagaida mami,

“A’a tashi ki zauna, sannu da zuwa”

Saida mami ta gabatar mata da abinci da abubuwan sha sannan ta dubeta da fara’a,

“Sai dai kuma ban ganeki ba” inji mami,

“Ehh ai momy baki sanni ba, sunana hafsat kuma ni yar gidan alh musa ce ubangidan ya yusleem”

Sake fadada fara’arta mami tayi ta dubeta….

_Fans kuyi min uzuri zakuji ni shiru kwana biyu saboda wani uzuri da ya taso min na gaggawa amma insha Allah nanda sati daya zaku cigaba da jina ina fata zaku yimin afuwa…_

     ***

Sake fadada fara’arta mami tayi tadubeta cikin murmushi tace,

“Allah sarki ya kika baro mahaifiyar taki da yan uwanki, duk suna lafiya ko?”

“Lafiya lau suke…”

“Madalla, ai kin kyauta da kika zo” inji mami,

“Ah babu komai wlhi ai an zama daya…”

Sun dan jima suna hira kafin hafsat tayiwa mami sallama tatafi, har waje mami ta rakata wurinda motarta take saida taga tafiyarta sannan takoma ciki.

   K’arfe 6 yusleem yatashi daga aiki, Hafsat yakira daidai lokacin da yaje gaban motarshi,

“Ya yusleem…”

“Uhmmm, matata kina ina?”

Murmushi yaji tayi saboda sunan da ya kirata dashi,

“Da waye yace ba matarka bace?”

Cikeda alamun gajiya yabude motar yashiga ya zauna amma baiyi mata key ba,
.
“Nidai nasan matatace koda wanima zai ce ba tawa bace, dan Allah kina ina? Wallahi agajiye nake sosai”

“Ina gidan Ummi”

“Wai har yanzu dama baki koma gida ba?”

“Ai yau anan zan kwana”

Yar dariya taji yayi,

“Yanzu zanzo in daukoki ki shirya”

Yafadi yana daura sit belt ajikinshi,

“Ko baka zo ba ma ai zan dawo anjima”
.
“A’a ban yarda ba, gara inzo indauki abata intafi da ita ina jinta agefena”

Murmushi tayi tace “sai kazo” tareda katse wayar,

Mintuna ishirinne suka kaishi gidan, awaje ya tsaya ya kirata babu jimawa sai gata tafito rikeda jakarta da wata leda yar babba,

Bude mata kofar yayi tashiga ta zauna, mika hannu yayi ya rufo kofar yana kallonta, gaba daya wani kamshin dadine yaji ya cika cikin motar,

“Ummi tana gaisheka…”

“Ina amsawa, kefa? Bakya gaidani ko kina gaisheni?”

Murmushi tayi ta rike hannunshi wanda ke yawo acikin rigarta,

“Ina gaisheka, dan Allah kabari”
.
Murmushi yayi yatada motar yasoma tuki yana kallonta,

“Na fuskanci duk ranar da kikazo gidan Ummi bakya son komawa gida da wuri,meyasa?”

“Hirarce ke yin yawa bata karewa shiyasa” tafada tana murmushi,

Yan yatsunta taji ya kama,

“Me kike sha’awa yanzu mubi insiyo miki?”

Lumshe ido tayi, “Duk abinda kake kwadayi nima ina so”

Murmushi taji yayi kasa kasa yace,

“Ni ke naketa kwadayin samu kuma nagagara, kefa?”

Dauke kanta tayi ta mayar gefe saboda abinda taji yace, murmushi yayi ya dan kalleta,

“Yanaji madam tayi shiru?”

“Muje gida kawai basai mun tsaya ko inaba”
.
“Dama ai gidan zamuje”

Shiru tayi saboda yagama kashe mata bakinta, ita da zarar yayi mata magana makamanciyar wannan sai taji duk bata da bakin yimasa magana,

Juyawa yayi ya kalleta, “menene wannan haka mai kamshi ummi tabaki?”

“Turaren wutane da humra aka kawo mata daga Sudan shine tabani…”

“Ta kyauta kuwa dan naji kamshin irin wanda nake so ne”

Kawar da maganar tayi tahanyar cewa,

“Yaushe zaka je chairo dinne?”

“Zamuje dai, ai tare zamu tafi yanda muna dawowa mami zata fahimci cewar andace nagama warkewa”.

Murmushi kawai tayi masa batare da tace komai ba saboda idan taci gaba da biye masa kunya zai ta sata tanaji,

Wurin wani mai sayarda balangu da tsire taga ya tsaya nan yafita yaje ya siyo yadawo, ledoji biyu yariko ya mika mata,

“Amshi wannan, na mami daya namu daya…”

“To angode, Allah yakara budi”

“Amin, me zaki bani tukwici?”

Shiru tayi masa takai hannu zata kunna radio, dora nasa hannun yayi akan nata yana lalubo mukunnar radio din,
.
“Ko babu abinda zaki bani? Naji bakice komai ba”

“Uhmm”

“Uhm fa kikace? Lallai, to ashe bazaki cimin balangu na ba tunda hakane”

Kallonshi tayi tasaki dan murmushi,

“Dama bada zuciya daya ka siyo ba kenan?”

“Wallahi da zuciya biyu nasiyo, kici balangu ki bani tukwici”

Rasa abinda zata fada masa tayi dan haka taja bakinta tayi shiru, shikuwa sai sake nanatawa yake yi dahaka har sukaje gida,

Part din da yake yawuce yayinda ita kuma tawuce part din mami, mamin nazaune tana lazimi da alama sallar magrib ta idar, ciki Hafsat tawuce taje ta dauro alwala tafito, saida ta idar da sallar sannan suka gaisa da mami ta fito da kayan da Ummi tabata da kuma naman da yusleem yasiyo,

Tuwo da miya tazubo musu ita da mami,sun fara ci kenan yusleem yashigo,

“Mami ni baza ajirani ba inzo shine kuka wareni”
.
Murmushi mami tayi,

“Kai ai kayi girma da yawa Yanzu babu mai wani riritaka”

Samun wuri yayi yazauna kusa da mami yana murmushin shagwaba,

“Gaskiya mami a’a”

“Basai kayiba kuma” inji mami,

Dariya Hafsat tayi ta dan kalleshi nan suka hada ido dama shidinma ita yake kallo,

“Am yawwa kafin namanta, dazu wannan yarinyar Hafsat tazo yar gidan alh musa…” Mami tayi maganar tana kallon yusleem,

Saida yaji gabanshi ya fadi saboda jin abinda mami tace,

“Mami lafiya? Meya kawota gidan nan? Tace miki wani abune?” Duk ya jerowa mamin wadannan tambayoyin lokaci guda,

“A’a ni babu abinda tace min, kawai dai zuwa tayi agaisa, akwai wani abune tsakaninka da ita da kake tambayar me tace?”

Kallon hafsat yayi amma ita bashi take kalloba tuwonta kawai take ci sai dai gaba daya tasauya ta danyi wani iri tana sauraronsu, ita dama bata sawa ranta cewar ita kadai zata zauna dashi ba tunda tasan watakila shima akan kansa nan gaba zai bukaci kara auren,daurewa tayi tai watsi da duk wata damuwa taci gaba da cin tuwonta batare data bari bacin rai ya ziyarci zuciyarta ba,

Kallon mami yusleem yayi bayan ya tsame hannunshi daga cikin kwanon tuwon da suke ci,
.
“Mami ni banida wata alaka da ita, kawai dai abinda nasani shine ina zuwa gidansu wurin mahaifinta kuma tana girmamani”

“To ai shikenan hakanma yanada kyau, Allah ya rufa asiri..”

Bai amsaba yasaci kallon Hafsat, balangun da yasiyo musu yaga tabude tafara ci,

“Baby nanah babu ko bisimilla?”

Murmushi yaga tayi tatura masa gabanshi,

“Haba ya yusleem taya zan hanaka bayan kaine ka siyo, gashi muci”

Tashi mami tayi tawuce domin wanko hannunta, ganin haka yasashi rage murya,

“Nidai sai dai kibani abaki…”

Tun kafin yarufe bakin nashi ta dauki naman tasaka mishi, murmushi yayi yarike hannunta,

“Yawwa matata…”

Dariya tasaki saboda jin abinda yace,

“Ni kana bani dariya idan naji kafadi haka, wai waye da yace ba matarka bace?”

“To laifine dan nasake jaddadawa?”

Hannunta tazare daga cikin nashi saboda jin tahowar mami,sake rage murya yayi,

“Ya kamata fa kitashi muje mu kwanta saboda yau jina nake asama sama…”

Sunkuyar da kanta tayi batare data tanka mishiba har mami takaraso cikin falon ta nemi wuri ta zauna,

Hira sukeyi kadan kadan shida mamin yayinda ita kuma hafsat ta tattare kayan da suka ci abinci tafita dasu bayan tagama cin naman dayake gabanta,

Dawowa falon tayi itama ta zauna tana kallo sannan tana dan sauraren hirarsu mami wadda yanzu akan dawowarsu Abdul ne,
.
Da ido yusleem yake yiwa Hafsat alamun ta tafi bedroom zai biyota,

Makale kafada tayi, kallonta yayi yadan jijjiga kai alamun zan kamaki ne, murmushi tayi gamida yimasa gwalo, hakan da tayine yabashi dariya,

Gani yayi sam bata da niyyar tashi domin lokacin har karfe 9:30 tayi gashi mami itama yau hirar takeji saboda tana nan zaune bata motsa ba,

Dan gyangyadin da taji yana fusgarta ne yasata tashi badan tasoba tawuce bedroom, binta da kallo yusleem yayi har ta shige,

Wanka ta shiga bata dauki lokaci ba tafito tana daure da towel din surayya wanda dakyar ya ritsata saboda dan jikin da tayi,

Humrar da ummi tabata yau ita tabude tasoma shafe jikinta babu bata lokaci dakin gaba dayanshi ya gauraye da daddadan kamshi,tana rufe kwalbar yusleem yaturo kofa yashigo, da sassarfa yakaraso gareta sakamakon kamshin da yakaiwa hancinsa ziyara ya ratsa har cikin kwakwalwarsa…….Wata lafiyayyiyar runguma yayi mata bayan yacusa fuskarsa awuyanta yana sinsinarta,

Towel din dake jikinta tarike gam yayinda shi kuma yasake tsananta rukon da yayi mata,

“Ya yusleem….”

Kasa amsawa yayi illa gyada mata kai da yayi alamun yana jinta,

“Ya yusleem kabarni inshirya….”

Sake kankameta yayi yana janta ahankali har suka dangano da gadon dake cikin tsakiyar dakin,
.
Makaleta yayi sosai ajikinsa ya shimfidar dasu nan yasake bada himma wurin isar mata da sakonnin da yafara bata tun suna tsaye, sosai yau taga ya fice daga hayyacinsa sakamakon yakai makura wurin bukatarta, wani zazzafan numfashi yake fitarwa yana sauka ajikinta,

Sun dauki lokaci mai tsawo cikin wannan yanayin wanda shi yusleem jinshi kawai yake yashiga wani wahalallen hali maimakon yasamu relief daga azabtuwar da gangar jikinshi da rushinsa ke ciki, badan yana jin tausayinta ba kuma yana tsoron kar ya cutar da itaba da ayau dinnan ba gobeba babu abinda zai hanashi zama cikakken ango,sake kankameta yayi yana faman jujjuya kanshi,
.
Shiru Hafsat tayi tana saurarensa cikeda jin tausayinsa, dakarfi da karfi take jin fitar numfashinsa har yasoma fita ahankali ahankali dahaka har yadawo fita normal sai lokacin ya iya barin jikinta ya matsa gefenta amma har lokacin yana makale da hannunta kamar wadda za adauke masa ita,

Jin yadan sassauta rikon da yayiwa hannuwanta yasata zaton cewa bacci ya daukeshi,tashi tayi ahankali tawuce bathroom, ruwa takama tadawo tadauko rigar baccinta tasaka takoma kusa dashi ta kwanta tana faman runruntse idanuwanta saboda irin dakumar da yayiwa kirjinta har wani irin radadi takeji yana damunta,

Dakyar ta iya yin bacci awannan dare, shikam yusleem tunda yasamu bacci ya daukeshi bashi ya farkaba saida asuba wannan dinma Hafsat ce ta tadashi, wata wawiyar mika yayi sannan yashiga bathroom din, yajima aciki kafin yafito domin saida yayi wanka,

Lokacin da yafito Hafsat tana zaune akan abun salla tana lazimi, kallonta yayi yai magana ahankali,

“Bari naje part din can…”
.
Rike kafarshi tayi saboda bata son yafita domin zasu iya haduwa da mami afalo,

“Dan Allah ya yusleem karkaje kayi sallarka anan…”

Murmushi yayi yasake rage murya kamar wanda baya son wani yaji abinda zai fada,

“Wallahi kayana bazasu yi salla ba saboda gaba daya sun baci…”

Cikashi tayi batare da ta kalleshi ba, wucewa yayi yaje yabude kofa yafice, aranta tanata addu’ar Allah yasa kar mami tafito taganshi, kwanciya tasake yi bayan ta kammala addu’o’in da takeyi,

Baccine yasake daukarta saboda jiya bawani mai yawa tayiba, ba ita tatashiba sai karfe 8 nasafe, wanka tayi tashirya cikin doguwar riga tawani jan material, turarrukan jiya tafesa ta hade jikinta da kamshi mai dadi tafita.
.
  Abangaren yusleem kuwa dakyar ya iya komawa bacci bayan ya idar da salla, juyi kawai yarinka yi akan gado daga karshe wani wahalallen bacci ya daukeshi, karar wayarshi ce ta tasheshi lokacin karfe 8 saura nasafe,

Hannu yamika yadauko wayar idanuwanshi arufe, muryar Hafsat mori yaji tana magana cikin kasalalliyar murya da alama ita dinma daga baccin ta tashi,

“Ranka yadade ina fata ban tasar dakai ba a bacci?”

Batare da yabude idanuwanshi ba yayi magana,

“Meya faru? Dama ina son yin magana dake..”

Shiru tayi, jin baiyi magana ba yasata fadin,

“Ina sauraronka”
.
“Meya kawoki gidanmu jiya? Hafsat nafada miki fa inada mata, bakya tunanin zuwanki yana iya haifar da matsala tsakanina da iyalina? Dan Allah na rokeki karki sake zuwa gidanmu…”

Bai jira abinda zata fadi ba yakashe wayar kittt, daga nan tashi kawai yayi yashiga toilet yayi wanka yafito yanaji Hafsat mori nata kiranshi awaya amma yayi fuska yaki kallon koda wayarne,
.
Farin wani lallausan yadi yasaka yasha turare yadauki wayarshi yafita da hularshi ahannu, a tsakiyar falo ya hango Hafsat tana shirya jaridun mami akan centre table ita kuma mamin tana kitchen ita da kuku, wucewa yayi bayan sun gaisa da mami yashiga cikin falon, da kafadarshi yadan bugeta, murmushi tayi batare data juyo ba saboda tagane cewar shine domin kamshinsa yasanar da ita,

“Morning Nana hafsat”

“Morning ya yusleem” ta amsa mishi bayan ta dago amma bata kalleshi ba,
.
“Kinga irin wahalar da nasha dazu da asuba bayan nabar dakinki? Acikin week dinnan gaskiya zan koma chairo, wallahi nagama kaiwa karshe atakura”

Shiru tayi masa acikin ranta tana hangowa fitinar da yusleem zaiyi duk ranar da yagama samun lafiya,

“Yanaji kinyi shiru? Ko bakya son nawarke ne?”

Murmushi tayi tadago tana kallonsa saboda jin abinda yafada,

Kafin tayi magana tajiyo mami na kwalla mata kira daga kitchen, gefenshi ta raba tawuce batare data sake kallonshi ba,

Kayan breakfast tadauko tazo ta ajiye ta zuba mishi, da kallo yake binta yana kurbar tea din dake hannunshi amma yana lura da ita sai wani dan yayyatsina fuska takeyi, saida ya kammala breakfast din sannan yaja hannunta zuwa bedroom,
.
“Nanah meyake damunki naga alamun damuwa atare dake?”

Shiru tayi tasunkuyar da kai,

“Fada min Mana”

“Babu komai”

Murmushi yayi yakai hannu jikinta dasauri tarikeshi,

“Ya yusleem dan Allah kayi hakuri..”
,
Murmushi yayi yajuya yafita saboda ya fahimci abinda ke damunta, cikin falon tabishi tasameshi tsaye rikeda hularshi, karbar hular tayi tasaka mishi yajuya yafita, tana jiyoshi yana yiwa mami sallama domin har lokacin tana cikin kitchen saboda tafara shirye shiryen tarbar yan makaranta wadanda zasu dawo.

Wurin mami taje suka cigaba da aiki tare bayan ta kammala yin breakfast, har azahar tayi suna cikin kitchen suna aikace aikace zuwan khadija ne yasa Hafsat barin kitchen din suka shiga falo,

Yar hira suke tabawa bayan hafsat ta gabatarwa da khadija abinci shinkafa da doya da miya,

“Amarya ta ango” khadija tace da hafsat cikin wasa,

“Yanzu ai kece amarya khadija” hafsat tafada tana murmushi,

“A’a kedin dai”

“Zancen kike so” inji hafsa, maganar yusleem tajiyo acikin kitchen yana cewa mami,

“Yunwa ce ta dameni shine nadawo inci abinci”

Murmushi hafsat tayi saboda tasan ba gaskiya bane abinda yafadawa mami shidai kawai fitinarsa ce tadawo dashi, cikin falon yashigo ganin khadija yawani hade rai sama sama ya amsa gaisuwarta yawuce cikin bedroom,

Tashi hafsat tayi tashiga kitchen, abinci tahado masa ta dauka ta nufi cikin bedroom din har lokacin khadija tana zaune tana cin abincinta,
.
Kwance taganshi agefen gado idanuwanshi alumshe, ajiye abincin tayi taje kusa dashi,

“Lafiya kuwa ya yusleem?”

Bai bata amsaba illa kamota da yayi ya sadata da jikinsa ya kwantar da ita, fuskarta zuwa wuyanta yake sinsina da fuskarshi,

“Ni dama nasani” tafada acikin ranta,

Cigaba da birkitata yayi har zuwa tsawon wani lokaci dakyar ya iya barinta ya tashi domin cin abincin da ta Kawo masa saboda zai koma office,

Zuba mishi tayi ya dauka yafara ci yana kallonta,

Sunkuyar da kanta tayi taki kallonshi, dan murmushi yarinka binta dashi har yagama,

Fitowa sukayi bayan ya gama cin abincin nan taga khadija bata nan da alama tafiya tayi, saida ta rakashi har wurin motarshi taga tafiyarshi sannan takoma ciki.

  Cikin yan kwanakin gaba daya busy hafsat take itada mami saboda aikace aikacen da suke yi na karbar baki, ranar laraba da yamma su Abdul suka dawo shida khalifa,

Bakin mami kasa rufuwa yayi sai murna take tana fadin “saura yar autana surayya itama tana tafe”

Tunda su khalifa suka dawo sai hafsat ta dauke kafarta da zuwa part dinsu wurin yusleem duk da cewar har yanzu yana nan adakin Abdul sukuma samarin sunyi skwatin adakin khalifa kafin akoma sabon gida,
.
Duk da bata zuwa amma shi kowanne daren duniya adakinta yake kwana,

Dawowar su Abdul da sati biyu itama surayya tadawo, murna hafsa tashiga yi harda rungume surayya nan suka kafa dandalin hira har karfe 11 nadare,

Wasu hadaddun English wears surayya tadawo dasu akwati guda, kallonta hafsa tayi tana murmushi,

“Wai ke sury bakida kayane sai wadannan…?”

Dariya surayya tayi,

“Wallahi ban iya saka wasu kayan inba wadannan ba, ke nifa atamfa da sauran kayan gargajiya gumi suke sani, ga uban nauyi shiyasa ma bana iya sawa”

“Amma kuwa kin hadu da aiki” inji Hafsat,

“Babu wani aiki, kema ai nakawo miki tsarabarsu kisa ki kashe ya yusleem”
.
“Bakida kunya…”

Karar wayar hafsa ce ta katse musu hirarsu,

“Ya yusleem ya akayi?”

“Zo ina jiranki awaje”

Tashi hafsa tayi bayan ta dauki hijab, kallonta surayya tayi tana murmushin shakiyanci,

“Saida safe kenan”

“Ahh kin manta sai jibi” hafsat tafada tareda ficewa daga cikin dakin, hannunta yakama lokacin da tafita yanufi part dinsu khalifa,

“Ya yusleem…”

“Bana son gardama”

Shiru tayi har suka shiga falon, su Abdul din suna zaune kowannensu dauke da laptop dinshi suna danne danne, kunya ce ta kamata hafsat saboda ganinsu abdul amma shi ko ajikinsa, sakata yayi agaba suka wuce ciki yamaida kofa ya rufe harda sa key,
.
“Haba ya yusleem…”

Bai kulata ba yacire rigar jikinshi ya kwanta,

“Idan kin gama mitar sai kizo ki kwanta..”

Yace da ita bayan ya lumshe idanuwanshi, ta dan jima atsaye daga karshe dai taje gefenshi ta kwanta, dama kamar jira yake yajawota jikinshi ya kwantar.

Koda asuba hanata tafiya yayi bai barta tatafiba sai da gari yawaye,ai kuwa tasha tsokana awurin surayya dan tun tana mayar mata har dai tayi shiru ta rabuda ita daga karshe tace,

“Bari yayan naki yafito sai nafada masa”

Jin haka yasa surayya yin shiru tabar zancen, tun daga ranar kowanne dare sai yazo ya tisata agaba yatafi da ita baya barinta tadawo sai gari yawaye,
.
Yau kam takasance weekend suna zaune adaki ita da surayya, sury tana karatun novel a wattpad ita kuma tana gyara farcenta tana sanye da hijab ajikinta duk da acikin dakine domin wata yar karamar rigace ajikinta pink colour da yar karamar skirt iya cinya, kwata kwata bata saba irin shigar nanba surayya ce tasata dole saida tasa gashi bahaushe yace zama da madaukin kanwa shike kawo farin kai, knocking akayi sannan aka shigo yusleem ne yana sanye cikin kananan kaya,

“Zo Hafsat…” Yace da ita yana kallonta, kasancewar babban hijab ne ajikinta yasata tashi tabishi,
“taho min da ruwan zafi”

Acikin kitchen suka tsaya ta dauki ruwan zafin suka fita, part din su Abdul suka shiga, dukkansu suna falon suna kallo,

“Kai me kuke yi?” Yusleem ya tambayesu,

“Yaya kallo muke” inji khalifa,

“To ko ku koma daki ko kuma ku fice ku koma part din mami”

Yana kaiwa nan yawuce cikin daki Hafsat tana biye dashi tana ji kamar kasa ta tsage ta nutse dan tsananin kunya…….

 
        ***

Tsaye tayi a bayanshi batare da ta motsa daga wurinda take tsaye ba,

Juyowa yayi ya kalleta, ganin taki motsi yasashi karasawa gefen gado yazauna yasake juyowa ya kalleta,

“Bazaki bani tea din bane?…” Taji ya tambayeta,

Sai lokacin ta motsa ta nufeshi fuskarta adan daure ta mika mishi cup din ruwan zafin dake hannunta,

Hannu ya mika ya karba yahada da hannunta yazaunar da ita akan cinyarsa,
.
“Fushin na menene nanah? Uhmm?”

Yafadi yana kokarin zare hijabin dake jikinta,

Boye fuskarta tayi saboda ganin ya yaye hijabin,

“Wowwww….., baby nanah kinyi kyau”

Kallonta yaci gaba dayi yana murmushi,

“Insha Allah dai mun kusa tafiya chairo saboda idan naci gaba da zama anan haka kina iya zautar dani…., sury ne ta koya miki saka kananan kaya ko?”

Shiru tayi sai rufe fuskarta da tayi da tafukan hannunta, cigaba da zuzuta kyawun da tayi yayi yana faman sinsinarta.
.
  Daren ranar lokacin da tayi shirin bacci kashe wayarta tayi domin tasan yusleem zai iya kiranta yace sai taje sun kwana tare,

Tana nan kwance suna yar hira itada surayya suka ji bugun kofarshi, saurin rufe ido hafsat tayi tace,

“Surayya dan Allah kice nayi bacci”

Tun kafin surayya tayi magana yabude kofar yashigo,

“Yaya tayi bacci fa”

Harararta yayi,

“Zata tashi yanzu ko kuma indauketa”

Dariya sury tayi tabishi da ido, wurin hafsat yaje yakamo hannunta,

“Tashi ko indaukeki…”
.
Jin abinda yace yasa Hafsat tashi tana faman zumburo baki, bai kulataba yaja hannunta suka fice.

Kasancewar angama hada komai na bukata agidan da zasu koma yasa suka fara tattara kayayyakinsu domin komawa sabon gida, duk wannan hidimar da khadija akeyi kullum sai tazo ta tayasu tattara kayan,

Shikam yusleem yanzu fafutukar samun visa yakeyi domin zuwa kasar chairo saboda yana cikin matsanancin hali na bukatuwa amma kuma visa din samunta yayi wahala,
.
Kusan kullum sai yaje gidan alh musa mori domin yagama zama cikakken dan gida yanzu danma wani lokacin baya son zuwa saboda Hafsat yar gidan alh musan domin tagama takura masa ita adole shi takeso ta aura duk da yayi mata bayanin baida burin kara aure amma taki hakura koda yaushe cikin yimasa waya take, gaba daya jinta take tagama tsanar Hafsat dinshi saboda tasan saboda itane yaki amsar soyayyarta wannan dalilinne yasa bata son Hafsat ko kadan duk da cewar basu taba ganin juna ba.
.
  Ranar juma’a suka gama kwashe kayansu suka koma sabon gida wanda ya cancanci da akirashi da aljannar duniya saboda yanda aka kawatashi kuma aka zuba masa dukiya wacce bazata kididdugu ba, ba karamin kudi yusleem ya kashewa gidanba,

Sai daf da magrib Hafsat da sury suka gama gyarawa mami dakinta,agajiye Hafsat ta nufi part dinsu itada yusleem wanda ya hadu karshen haduwa, zama tayi afalon kasa tana bin falon da kallo yanda ya shiryu kamar aciki za a dawwama baza a mutuba, dan murmushi tayi saboda tunawar da tayi wai harfa agidan haya sun zauna itada yusleem,
.
Ganin zaman bazai kaita ko inaba yasata tashi ta nufi cikin bedroom dinta tayi wanka da ruwan dumi tafito ta shirya cikin wata doguwar riga yar kanti roba mai hannun shimi bayan ta shafe jikinta da turarurruka da humra masu dadin kamshi,

Sallar magrib tayi daga nan tasauka kasa tana rikeda wayarta sanye cikin hijab,
.
Yusleem tagani zaune afalon yana latsa wayarshi, sakon da Hafsat musa taturo masa yake karantawa wanda kusan kullum ne sai taturo masa,

Zama Hafsat tayi akusa dashi, mayar da wayar tashi cikin aljihu yayi yamika hannunshi ya kamo nata yajata jikinshi,
.
“Da abinci kibani? Yunwa nakeji…”

Murmushi tayi ta kalleshi,

“Da akwai, zakaci tuwo?”

“Zanci indai kece kika bani” yaceda ita yana faman shakar kamshinta,

Da dabara tasamu ta zame daga jikinsa saboda itama yunwar takeji gashi tagaji sosai,

Tuwon shinkafa miyar zogale wacce tasha naman zabuwa tazubo musu a faranti takawo gabanshi ta ajiye tasake komawa tadauko abin sanyaya makoshi ta kawo musu,

Sauka kasa yayi ya zauna yana kallonta bayan yasoma cin abincin,
.
“Nanah ina son sanar dake wani abu amma dan Allah ki fahimceni…”

Kallonshi itama tayi wanda har lokacin ita yake kallo,

“Haba ya yusleem ai ni mai fuskantarka ce acikin kowanne lokaci, kawai kafada min wallahi babu komai…”

“Kiyi hakuri hafsat saboda alkawarin da nayi miki natafiya chairo tareda ke bazai samuba domin anrasa visa, amma nayi miki alkawari idan har nadawo zamuje kasashe guda hudu tareda ke wanda kece nan zaki zaba da kanki, so sai kifara zaba tun daga yanzu…”

Wani murmushi tayi tana mai farin ciki,
.
“To ya yusleem nagode madalla, Allah yakaika lafiya yadawo dakai lafiya…”

“Shikenan addu’ar da zakiyi min? Bazaki min tasamun cikakkiyar lafiya ba wadda ina dawowa sai harka kawai…”

Fuskarta tarufe cikeda kunya tana cewa,

“Kai ya yusleem dan Allah”

Murmushi yayi suka cigaba da cin abincin su.

   Washe gari da safe khadija tazo gidan domin gani, tsarin yanda aka shirya part din Hafsat ba karamin burgeta yayiba nan tashiga addu’ar Allah yasa alkhairi,
.
Cikin yan kwanakin yusleem sai shirye shiryen tafiyarshi yake yi domin saura kwana uku yatafi,

Sanar da hafsat yayi cewar akwai wasu alkawarruka guda biyu wanda yayiwa zuciyarsa akanta amma bazai sanar da itaba sai har yadawo daga tafiyar da zaiyi,

Ana igobe zai tafi sai korar sury yayi daga part dinsu saboda koda yaushe tana part din nasu wurin Hafsat,

Harararshi Hafsat tayi tana dan tutturo baki,

“Ya yusleem kaida zaka tafi kuma meye na korar min yar tayin zamana?”
.
Janta jikinshi yayi yana dariya,

“Yi hakuri ai zata dawo idan natafi…, yau so nake tabarmu mu dan wala kafin natafi”

Shiru tayi masa tana karbar sakonninshi adaidai wannan lokaci.

Ahanzarce tatashi saboda jin kiran sallar la’sar,ganin babu yusleem akusa da ita yasata gaggawar shiga bedroom dinta, wanka tayi tafito daure da towel, ganinshi tayi zaune agefen gadonta yana yin waya,

Da kallo yabita sannan yayi murmushi, sunkuyar da kanta tayi taki kallonshi saboda tasan dalilinshi nayi mata wannan kallon dan yaga gashin kanta ajike jalaf da ruwane,
.
Tasan zata sha tsiya awurinshi yau shiyasa ta tsare gida ta shirya ta tada kabbarar salla, har lokacin yusleem bai gama wayar da yakeyi ba, duk da ta bata fuska hakan bai hanashi sakata agaba da tsokana ba, rabuwa dashi tayi tai shiru abinta.

Daren ranar kuwa da fitina ya addabeta idan tayi magana sai yace wai gobe iyanzu baya nan,yanda sukaga rana haka suka ga dare har asuba, kayanshi ta kintsa masa bayan tayi sallar asuba, daga nan kitchen tawuce ta hada masa breakfast,
.
Karfe 8 ya kammala shirinsa cikin farar shadda da hula, tare suka shiga part din mami, dukkansu suka dunguma zuwa airport din domin yi masa rakiya,

Hafsat ji take kamar zatayi kuka amma haka ta daure sukayi sallama duk da tasan zatayi missing dinshi ba kadanba,

Saida sukaga tashinsu sannan suka dawo gida, tunda suka dawo kuma surayya ta tattaro tadawo part dinsu Hafsat nan suke kwana su wuni tare,
.
Aranar da yatafi da daddare yakira Hafsat wanda sun jima suna hira sannan tace ya kwanta yahuta itama bacci takeji, tun washe garin tafiyarsa mami ta gayyato wata mata tafara gyarawa Hafsat jiki, gyaran jiki ake yimata nagaske banda kayayyakin da ake dura mata,

Kullum sai sunyi waya da yusleem babu ranar da bazai kirata ba, cikin yan kwanaki kadan fatar jikin hafsa tayi laushi lubuss kamar auduga banda kyallin da take faman shekawa,
.
Yusleem baisan tanadin da mami keyi masa ba amma duk da haka hankalinsa yagama komawa kan Hafsat musamman ma da Dr dinshi yace yanzu komai yazama normal zai iya kebewa da iyalinshi,

Hafsat yakira domin yayi mata albishir, fitowarta daga wanka kenan taji kiranshi,

“Nanah hafsat, kina jina? Kifara shirin karbata acikin kowanne lokaci domin ina nan tafe gareki nanda dan lokaci kankani….”

“To ya yusleem sai kazo, ai akullum cikin zuba idon ganinka muke”
.
“Ba wannan nakeso ba, idan nadawo me kika tanadar min? Me zaki bani?”

“Duk abinda kake so shi zan baka”

“Sai nadawo zan sanar dake abinda nake so din, ko kin sani?”

“A’a, sai kadawo dindai zaka sanar dani…”

Murmushi yayi, “har yau bamu taba bawa junanmu wani abu mai tsada ba amma nidai nayi alkawarin baki aranar da nadawo,kema kimin alkawarin zaki bani”

“Nayi, Allah yadawo dakai lafiya”
.
Sun dan jima suna hira sannan sukayi sallama, shiryawa tayi tafita falo wurin khadija da sury domin kusan kullum sai khadija tazo.

Ana saura kwana daya yusleem yadawo mami takira mai yimata kitso da kunshi tazo tayiwa hafsat kananan kitso samada guda dari domin ranar akusan zaune suka wuni sannan akayi mata kunshi, sai bayan magrib sannan tasamu kanta, surayya sai faman tsokanarta take wai miji zai dawo sai rawar jiki take,

Daga ita har yusleem daren ranar baccinsu kalilinanne, asubar fari ta tashi tasoma shirye shiryen abubuwan da zata girka masa domin ita bata da kuku tace da kanta zata rinka girkinta, mami ce kadai keda kuku,

Tareda surayya da khadija suka hadu suka yimasa tarin girke girken da ta shirya yimasa kafin 12 sun kammala domin yace karfe 2 daidai zasu iso,

Tafiya gida khadija tayi bayan sun gama aikin, ita kuma hafsat tashiga tayi wanka tashirya cikin wani hadadden leshi golden tafito rikeda wayarta tana faman tashin kamshi, surayya tana mike afalon kasa akan three sitter,

Ahankali take saukowa daga kan steps din kamar wacce aka kifo sai jinta tayi anhantsulota tafado nan tasoma mirginowa tana buguwa da karafen dake gefen steps din, jin kararta yasa surayya zabura tatashi tanufi wurinta aguje…..

         ***

Hankalin surayya ne yayi masifar tashi saboda ganin yanda jini yake zuba daga goshin hafsat, gaba daya goshinta duk ya fashe idanuwanta akafe alamun ta suma,
.
Kafin surayya tayi wani yunkuri taji sallamar Khadija wacce ta manta phone dinta a dining area tasaka charge kafin tatafi, ganin yanayin da Hafsat ke ciki yasanya Khadija rudewa cikin hanzari suka tarairayeta suka fita da ita zuwa motar Khadija agaggauce surayya tafada part din Mami tana kwalla mata wani matsanancin kira,
.
Mami suna zazzaune afalonta nakasa itada su khalifa suna jiran zuwan yusleem yasauka suje su daukoshi suka fara jiyo kiran da surayya keyi wanda da alama ba lafiya ba,mamice tasoma mikewa wacce ke sanyi cikin wata lafiyayyar exclusive,

“Surayya lafiya?”

Kankame Mami tayi jikinta yana rawa,

“Mami anty Hafsat ce tafado daga upstair bakiga yanda taji ciwoba…”
.
“Tana ina?…” Mami ta tambaya cikin rawar baki,

“Gata can amotar anty Khadija zata kaita asibiti”

“Tsaya nazo muje”

Dukkansu suka tafi asibitin Dr sufyan wanda shine mafi kusa fiyeda sauran asibitocin,

Har lokacin jinin dake fita daga goshin Hafsat bai tsayaba duk yabata cikin motar Khadija da jikin mami wacce ke rungume da ita,

Emergency aka shigar da ita har lokacin bata farfado ba, kowa acikinsu shiru yayi yana tunani,
.
Babu wanda ya iya matsawa nan da can acikinsu har saida yusleem yakira khalifa yace ya karaso amma yanata kiran Hafsat da mami bai samesuba sukuma Abdul da Surayya,babu wanda ya dauka,

Alama mami tayiwa khalifa da yace gasu nan zasuzo su daukeshi yanzu, hakan kuwa khalifa yafada masa sukayi sallama,
.
“Khalifa jeka kadauko shi amma dan Allah karka sanar dashi abinda yake faruwa, idan kunje gidan kace masa muma unguwa muka tafi amma ba jimawa zamuyi ba saboda bana son hankalinsa yatashi”

“To shikenan mami…”

“Ka bashi abinci yadiba yaci”

Fita khalifa yayi yanufi airport domin dauko yusleem yabar su mami zaune a reception suna ta jajanta abinda yafaru da hafsat wanda har yanzu tana nan kamar yadda aka kawota bata farfado ba acewar likita sai sunyi mata allurar bacci tasamu bacci nawasu awanni,

Koda khalifa yaje daukar yusleem tuni har yusleem din yafito yana saurarensu, duk yabi yadamu saboda rashin samun Hafsat da mami awaya,
.
Koda wasa khalifa bai fadawa yusleem abinda yake faruwaba har suka karasa gida,

Part dinsu zaije khalifa yayi gaggawar dakatar dashi,

“Yaya kazo kafara cin abinci mana a part din mami kafin su dawo…”

Fasa zuwa nasu part din yayi yawuce na mami saboda dama girke girken da Hafsat tayi duk can aka kai,

Zama yayi ya debi abincin yaci yayi alwala yai salla saida ya idar sannan khalifa yace yatashi suje wurinsu mami domin ta kirashi awaya tace suje,

Tunda yaji abinda khalifa yafada yasan akwai abinda yake faruwa dan haka ya kalleshi,

“Khalifa waye baida lafiya? Mami ko Hafsat?”
.
“Yaya dukkansu lafiya suke kawai kazo muje dai kagani…”

Binsa yusleem yayi bai kara cewa komai ba amma aransa yanata tunanin to waye baida lafiya agidan? Da wannan tunanin suka karasa asibitin Dr sufyan,

Mami da Abdul da sury suka samu domin ita khadija tatafi gida tadawo amma da tare suke tun lokacin da aka kawo Hafsat din,
.
Tunda yaga kowa baiga Hafsat ba jikinsa yabashi Hafsat ce batada lafiya, wurin mami yaje fuskarta dauke da alamun damuwa da tashin hankali,gashi duk jikin gyalen mami jini ya babbatashi,

“Mami…. Me…. Yasameta..?”

Tashi mami tayi cikin sigar kwantar da hankali ta dafashi,
.
“Karka daga hankalinka yusleem bawani abu bane dan buge goshinta tayi shine likita yabata gado domin yadubata amma insha Allah ma nasan nanda jimawa idan tatashi zai sallamemu…”

Ajiyar zuciya mai nauyi yasauke domin sai yanzu yasamu yar nutsuwa da mami tayi masa wannan bayanin.

Cigaba da zaman jiran farfadowarta suka zauna sunayi amma shiru har la’asar tayi koda suka tuntubi likita sai sukace allurar da akayi mata ne yasata yin bacci mai nauyi,

Duk yusleem yashiga cikin damuwa, dakyar yaje masallaci yayi salla yafito, lokacin da yake tahowa ya hango khadija tana packing din motarta aharabar cikin asibitin, jin wayarshi tasoma kara yasashi dubawa sunan hafsat musa yagani nan yaja dan siririn tsaki ya maida wayar aljihu batare da ya dauka ba,
.
Karasowarshi tayi daidai da fitowar khadija daga cikin motarta nan suka gaisa tayi masa sannu da zuwa sannan ta jajanta masa akan abinda yafaru, tare suka shiga ciki wurinsu mami suka cigaba da zaman jiran tashin Hafsat amma ba ita tafarka ba sai bayan sallar magrib,

Gaba dayansu suka shiga cikin dakin kowa yana kokarin yimata sannu,da ido duk take kallonsu tana dafe da goshinta wanda yake nannade da bandeji, yusleem ne ya nufeta yana yimata sannu tareda kokarin kai hannu jikinta, cikin wata irin kara da karaji ta dakatar dashi fuskarta kunshe da tsanarshi gamida jin haushinshi karara,
.
Kowa dake cikin dakin saida mamaki ya lullubeshi, tashi zaune tayi tana binsu da kallon tsoro daya bayan daya kamar wacce taga doduna,

“Hafsat sannu, duk zafin ciwon ne hak…” Inji mami, sai dai amma tun kafin mamin takarasa Hafsat ta toshe kunnenta ta callara wata kara wacce ta karade asibitin,

“Bana son ganinku kufice daga dakin nan…”

Yusleem wanda zuciyarshi keta faman tafarfasa yana tambayar kansa meyake faruwa, juyawa yayi yafita yanufi office din likita wanda shine on duty yau wato Dr zayyad,
.
Tare suka koma cikin dakin da Hafsat take wato emergency inbanda kara da buge buge babu abinda takeyi, kowa yayi tsumu tsumu yana kallonta, cewa likitan yayi dukkansu sujira awaje, jugum mami tayi banda yusleem wanda yama kasa koda maganane sai jan da idanuwanshi sukayi kamar gauta,

Khadija ce ke dan kokarin basu baki amma baya ga ita babu wanda ke iya magana acikinsu.

Haka suka cigaba da tsaiwa cikeda alhini kowa zuciyarsa babu dadi duk sunyi jungum jungum, suna gani likita yazo yawuce babu wanda ya iya binsa domin duk acikin damuwa suke,

Karfe goma saura suka sake komawa wurinta lokacin ta tashi daga baccin da tayi na bayan magrib,
.
Cikeda kulawa mami takarasa gefenta tazauna, awani iri take kallon mamin kamar yau tafara ganinta,

“Sannu Hafsat tashi kici abinci kinji…”

Sake bin mami da kallo tayi kafin tamaida kallonta ga kofar shigowa inda surayya tashigo rikeda basket din abinci sai khalifa da Abdul wadanda ke biyeda ita yusleem kuma yana bayansu,

Runtse ido tayi tasaki wata razananniyar kara tana nuna yusleem da yatsa,

“Sannu Hafsat, meke damunki ne? Kiyi hakuri kinji”

Hawaye ne suka soma zuba daga idonta,
.
“Bana son ganinku, bana son ganinku musamman ma shi….”

Mamakine yakama mami ta riketa,

“Yi hakuri kici abinci…”

Ki tayi har saida yusleem yafita daga dakin sannan aka dan fara samo kanta.

Damuwa sosai yusleem yashiga saboda ganin abubuwan da Hafsat keyi idan har taganshi kamar wacce taga wani dodo haka take zama, tagumi yayi idanuwanshi jajur,

Bayan fitar yusleem mami ta debo abincin a filet da spoon ta mika mata,
.
“Yi hakuri ki karba kici kinji hafsat…”

Kallon mami tayi,

“Sunana Hafsat? Yaushe aka saka min wannan sunan?”

Idanuwan mami cikeda kwalla takai spoon din bakinta batareda tabata amsaba ba,

Cikin lallashi da lallami mami take bata abincin tana ci kamar wata karamar yarinya, kowa acikin dakin tsuru tsuru yayi yana jin yanda Hafsat ke tayiwa mami wasu tambayoyin shirme,
.
Dai dai lokacin da mami tagama bata abincin nurse tashigo ta bata magani tasha, watsar da maganin Hafsat tayi ta toshe kunnuwanta ta zuba wata kara nan mami tayi saurin riketa tasoma rarrashi, dakyar da sudin goshi ta karbi maganin tasha tana daddafe goshinta wanda ke nannade da bandeji,

Inbanda shirme babu abinda takeyi kamar wacce ta bugu, da haka aka samu barci ya dauketa, saida tayi bacci sannan su mami suka fita daga cikin dakin, jin cewar tayi bacci yasa yusleem shiga wurinta,

Tunda yadawo sai yanzune yasamu yazo kusa da ita datayi bacci, agefenta ya zauna yakai hannu ya kamo nata idanuwanshi fal kwallah…….

       ***

Hannunshi yasa yadafa goshinta yana jin wani tausayinta yana ratsashi domin abin atausaya mata ne duba da irin kaddarorin da suke ta samun rayuwarta,binta da kallo yarinka yi saboda ganin yanda tasauya gaba daya, fatar jikinta sai sheki da kyalli take banda wani laushi da tayi, gashi kanta yasha kananan kitso masu mutukar kyau banda jan lallen da aka zana mata atafin kafarta da hannuwanta, ko ba afada masa ba yasan shi tayiwa wannan tanadin sai gashi kuma kaddara ta afku,
.
Yana nan zaune kusa da ita har su Mami suka shigo,

“Yusleem zo kutafi gida kaje ka kwanta ka huta inyaso gobe da safe sai kadawo…”

Girgiza kai yayi,

“Mami kuje kawai ni zan zauna inkwana awurinta”

“A’a yusleem kai da kadawo daga tafiya ai kana bukatar hutu, jeka ka huta ni zan kwana awurinta”

Tamkar zai fashe da kuka haka yamike yafita, dukkaninsu tafiya sukayi Mami kadai aka bari awurinta ta kula da ita.
.
Koda yusleem yaje gida kasa bacci yayi inbanda juyi babu abinda yakeyi wai duk irin burin da yaciwa ranar nan tayau yatashi a iska, goshinsa yadafe saboda wani irin radadi da kansa ke faman yimasa, kwanan zaune yayi har asuba tayi idonsa biyu Wanda damuwa ce fal ranshi musamman ma idan yatuno yanayin da Hafsat ke shiga aduk lokacin da taganshi,

Sai bayan da yayi sallar asubah sannan yasamu bacci ya dan daukeshi, karfe 8 saura yatashi yashiga part din mami, dakin sury yashiga ya tadata domin ta taya kuku su hada abincin da zasu kai asibiti domin da wuri yake son suje,

Karfe 9 daidai yafito bayan yayi wanka yashirya cikin kananan kaya, idanuwan nan nashi sunyi ja gashi sun dan canja daga halittarsu domin rashin bacci,

Shida surayya ne suka tafi asibitin a motarshi, suna tafe ahanya yana yiwa sury tambayoyi dangane da yadda abun yafaru har Hafsat taji irin wannan ciwon,
.
Lokacin da suka shiga cikin asibitin tuni har Khadija ta rigasu zuwa takai shiryayyen breakfast dinta, acikin filet ta zubawa Mami sannan ta zubawa Hafsat taje wurinta tana bata, tana tsaka da bata dinne su yusleem suka shiga, daga dan baya baya yatsaya yana leken Hafsat saboda ganin yanda fuskarta da idanuwanta suka kumbura tamkar an bubbugeta awurin,

Tun kafin taganshi yayi saurin komawa yafice daga cikin dakin, yana tsaye yanata kaiwa da komowa Mami tafito ta sameshi, durkusawa yayi yagaida ta sannan yatashi fuskarsa fal damuwa,

“Mami kodai wani asibitin zan canja muku ko kuma infitar daku outside? Wallahi rashin lafiyar nan ta hafsat ta tsaya min arai saboda irin yanda naga bata koda son ganina ne, why?”

Dafashi Mami tayi ita dinma fuskarta cikeda damuwa banda yar kwallar da taciko mata idonta,

“Yusleem ni kaina abin ya daure min kai, saboda jiya bamuyi bacciba daga ni har ita inbanda buge buge babu abinda takeyi daga bacci ya dauketa zakaga ta zabura tafarka tamike tana buge buge, dakyar bacci yadauketa bayan wata nurse tazo tayi mata allura…”

“To wai Mami kunyi magana da Dr din?”

“Har yanzu likita baice damu komai ba tukunna…”
.
“Ai kuwa yakamata ya sanar damu domin musan abinyi, bari idan yashigo zan tuntubeshi inji”

Tsayuwa suka cigaba dayi awurin har su Abdul suka karaso daidai lokacin Dr zayyad yashiga emergency wurin da Hafsat take, saida ya kammala duba marassa lafiya sannan yafito, bin bayansa yusleem da Mami sukayi zuwa cikin office dinsa,

Zama dukkanninsu sukayi suna fuskantar juna,

“Am Dr dama muna sone muji menene takamaimai abinda yake damun patient dinmu? Saboda har yanzu mu mun kasa fahimtar condition din da take ciki tunda tana behaving kamar wata wacce ta tabu….”

“Agaskiya patient dinku tana cikin wani irin yanayi wanda har yanzu muma bamu gama tabbatar da abinda muke zargi ba, amma dai abinda nasani shine, buguwar da tayi akanta kamar yaso ya taba lafiyar kwakwalwarta da tunaninta, acikin kai akwai wani abu da muke kira a turance da….”

“Dr buguwar da tayi har nawa take da za ace brain dinta ya tabu?” Yusleem yafadi cikin fushi,

“Calm down abokina….” Dr zayyad yafada yana dafashi,
.
“Buguwar da baiwar Allahr nan tayi bafa kadan bace kamar yadda kuke tunani, tunda kunce daga steps din bene tafado tarinka buguwa, wannan buguwar itace ta gurbata mata tunaninta amma insha Allah zata samu lafiya tunda muna bata magungunan da suka dace da ita”

Ajiyar zuciya mai karfi yusleem ya ajiye ya sunkuyar da kai, sam yakasa magana sai Mami ce tayi magana suka karasa maganganun da likita daga nan takamo hannunshi suka fito, sury da Khadija dasu abdul suka samu zaune a reception, bai tsaya awurinsu ba ya nufi wurin Hafsat tana kwance idanuwanta arufe kanta babu dan kwali, da sauri yaje yadauki dan kwalin zai daura mata saboda ganin dakin harda maza aciki, bude idonta tayi ai tana ganin yusleem tafasa wata uwar kara tafara buge buge kamar wata zautacciya, Mami ce tashigo ganin abinda ke faruwa yasata tura yusleem waje tace yafita, dan kwalin ya mika mata,

“Mami ki rufe mata gashinta kinga akwai maza awurin”

Murmushi mami tayi takarba takoma ciki saboda tasan kishine yasashi fadin haka amma inbanda haka matar da bata da lafiya ina ruwan wani da ita kowa yana takansa,

Saida mami ta lallabata sannan tafita wurinsu yusleem, kallonsu tayi,
.
“Ya kamata mukira iyayen Hafsat mu sanar dasu koba hakaba? Bai kamata muyi musu shiruba bamu sanar dasu rashin lafiyar yarsu ba, ya kamata mu sanar musu tunda wuri susan halin da ake ciki…”

“Gaskiya kam afada musu susani….” Acewar khadija,

Waya mami ta dauka takira hajiya kubra tasanar mata amma ta boye mata lalurar hafsat din domin gudun shiga cikin tashin hankali,

Shiru sukayi dukkaninsu bayan mami ta kammala yin wayar.

Bayan kamar mintuna 30 sai ga hajiya kubra itada Alh sa’id, kowa fuskarsa awurin kunshe takeda damuwa da bacin rai, mamice tayi musu jagora zuwa wurin Hafsat din nan suka isketa tana bacci duk tafita hayyacinta,
.
Dawowa reception din sukayi suka zauna suka cigaba da jajanta abun,

Sai daf da sallar azahar sannan Khadija tayi musu sallama tatafi,sukuma suka cigaba da zama, shima yusleem yana wurin azaune Hafsat mori sai faman kiranshi awaya take tayi bai daga ba ita kuma son ganinshi take domin ji take kamar ta shekara bata ganshiba,

Ganin ta dameshi da kira yasashi tashi ya matsa gefe ya daga wayar akufule,

“Sweet yusleem me yak….”

Tun kafin takarasa ya katseta cikin fada,

“Wai menene kiketa kirana ne? Baki san abinda yake damunaba kinbi kin uzzura min da kiranki marar amfani…”
.
“Ayya yusleem kayi hakuri dan Allah, meke damunka?”

“Babu ruwanki da abinda ke damuna, kawai dai ki saurara min haka…”

Daga haka yakatse wayar ya maidata cikin aljihu yakoma wurinsu mami ya zauna.

  Karfe 2:30 narana khalifa da sury sukaje gida domin dauko abinci saboda kuku yayiwa Mami waya yace yagama, kafin su dawo har Khadija tazo asibitin da wani babban basket shake da abinci, nan Mami tashiga yimata godiya saboda irin dawainiyar da taketa yi akansu,

“Mami ai babu komai, Hafsat tawuce haka agareni, tazama tamkar yar uwata ba kawata ba, fatanmu dai Allah yabata lafiya…”
.
“Amin,amin, Allah yakara zumunci” inji hajiya Kubra,

Sai da la’asar tayi sannan mami tatafi gida ita da yusleem, wanka mami tayi sannan ta debowa Hafsat wasu kayan, bayan sallar magrib suka koma asibitin shima yusleem din yasake wanka yasaka kananan kaya blue din jeans da farar t shirt ta polo,

Suna zuwa wurin su hajiya Kubra suka sanar musu da cewar ansauyawa Hafsat daki an kaita wani daki nata ita kadai, mami da yusleem ne suka nufi dakin wanda yake dauke da gado guda daya aciki,

“Asauya mata kayan ko?” Inji mami,

“To mami”
Mika masa tayi tafita, ahankali yazauna agefenta yafara kokarin cire mata rigarta ahankali, duk da yana cikin damuwa saida yayi ta maza sannan ya iya jurewa yasaka mata rigar, skirt din jikinta yacire yasa mata wani, yana cikin gyara mata dan kwaline mami tashigo, wani kamshine ya bayyana tareda mamaye cikin dakin,

“Yusleem kunyi bakuwa, Hafsat ce tazo duba Hafsat”
.
Dagowa yayi nan idanuwansu suka sarke da na juna, Hafsat mori yagani sanye cikin bakar abaya,dan hade rai yayi sannan yayi magana,

“Ok sannunta da zuwa”

Har wurin Hafsat din suka karasa, sai yau ma ita Hafsat taga matar tashi, kallonta ta danyi na wasu yan mintuna daga nan tayi musu fatan Allah yabata lafiya ta juya tafita, kasancewar da driver tazo sai ga drivern yashigo hannunsa niki niki da kayayyakin dubiya, kowa dake zaune awurin bin kayan yake da kallon mamaki…..

_Fatan alkhairi ga dumbin masoyana masu karanta wannan labari musamman ma yan kungiyar haske writers, haskakkun marubuta masu haskawa aduniyar rubutu….._
Wani takaici yusleem yakeji kamar zaiyi me dan bacin rai, tashi yayi yabi bayan Hafsat tana tsaye jikin motarta tana yin waya tabashi baya,

“Gaskiya aiki yayi kyau, nagode madalla, ladan aiki kuma sai na zo….”

Daidai lokacin yusleem yazo wurinta, afusace yake kallonta,

“Me yakawoki nan? Waye yasanar dake inda muke da har kika samu kikazo? Nifa Hafsat kifita daga hanyata domin banida bukatarki acikin rayuwata, kin takura min, wai ni kadai ne namiji da zaki bi ki damu?”
.
Tunda yafara wadannan jawaban batayi maganaba illa binsa kawai da takeyi da kallo tana dan murmushi, sai da yagama sannan tayi magana,

“Allah yahuci zuciyarka, ai ban san zuwana zai haifar da matsala ba da bazan zoba amma kayi hakuri insha Allah hakan bazai sake faruwa ba sannan daga yau dinnan ni Hafsat ina mai farin cikin sanar dakai cewar kamar yadda kace bakai kadai ne namijiba to zanje injira har insamu rabona….”,
.
Tana kammala fadin haka tabude bayan motarta tazauna taja tarufe kofar da wani mugun karfi alamun yin fushi, nan driver yaja suka wuce daga harabar cikin asibitin,

Komawa ciki yusleem yayi zuciyarsa dankare da bacin rai domin ji yake komai na duniyar yagama isarshi,

Haka suka cigaba da jinyar Hafsat amma kuma kullum abun babu sauki har suka shafe satittika a asibitin, Khadija kuwa tareda ita ake jinyar Hafsat domin kullum tana asibitin, ganin sauki bai samuba yasa aka sallamesu daga asibitin domin su koma gida, damuwa sosai yusleem yashiga saboda har yau baya iya zuwa koda kusa da Hafsat ne mutukar idonta biyu sai dai idan bacci take shine zai samu ya rabeta,

Gidansu aka kaita domin hajiya Kubra tace gara itama mami tahuta saboda dawainiyar asibiti da tasha, duk da yusleem bai soba haka ya hakura domin yana ganin kamar za anisanta shi ne da farin cikinsa,
.
Batun Hafsat mori kuwa tun daga ranar yusleem bai kara ganin kiranta ba bare sakonta kamar yadda tace.

Ranar da aka tafi da hafsat gida yusleem yakasa zaune yakasa tsaye, kiranshi mami tayi tace yadebi kayan Hafsat nasawa yakai gidansu inji hajiya Kubra,

Kala biyar kacal ya diba saboda baya son tadade bata dawo ba,

Zuciyarsa babu dadi ranshi abace yanufi gidan su Hafsat din, lokacin da yaje an idar da sallar magrib dan haka saida yatsaya a masallaci yayi salla sannan yashiga cikin gidan lokacin da yashiga hajiya kubra na falo azaune hannunta rike da carbi Hafsat tadora kanta akan cinyarta tana tofa mata addu’a idanuwan hafsat din alumshe,
.
Jin sallamarsa yasa Hafsat kokarin tashi daga cinyar Ummi, saurin dakatar da ita Ummi tayi taci gaba da tofa mata addu’a, ahankali yusleem yashiga cikin falon yazauna, runtse idanuwanta hafsat tayi saboda bata son koda ganin yusleem ne, juye juye tafara yi da kanta tana ciccije lebe, ganin haka yasa Ummi tasar da ita tsaye takamata suka shiga bedroom dinta, kwanciya tayi akan gado sannan ummin tafita falo wurin yusleem,

Sauka kasa yayi yagaida ta fuskarsa dauke da damuwa,

Itama hajiya kubran cikin damuwar ta kalleshi,

“Yusleem kadai sake kara hakuri kaji, hakika Hafsa tana cikin mawuyacin hali, ni nakasa gane kan wannan ciwon nata kamar yadda asibiti suka kasa fahimtar komai, shiyasa ma ni nake wani tunani domin kamar abin akwai alamar tambaya aciki duba ga irin yanayin lalurar tata, kodai akwai wata ko wani wanda wani abu yahadasu ko kuma kai yahadaku shine akabi ta wata hanya aka cutar da ita Hafsat din…”

Shiru yusleem yayi zuwa wani lokaci kafin yadago ya kalli Ummi,

“Hakane Ummi insha Allah zan bincika domin akwai wanda nake zargi..”

“To Allah yasa adace, Allah yabata lafiya”
.
“Amin” yusleem ya amsa, nan yaci gaba da zama har isha tayi,

Sama sama ya danci tuwon da ummi takawo masa daga nan yatashi yashiga wurin Hafsat,

Akwance ya sameta tana bacci tunda lalurar nan tasameta koda yaushe acikin bacci take, zama yayi akusa da ita ya dafata yakamo hannunta,

“Hafsat bazan iya nisantarki ba kamar yadda kike so, bazan iya zama batare dake ba, kiyi min wannan alfarmar kibarni na rab’u dake ko zanji sanyi, ko zan samu sassauci araina….”

Kwallar dake kokarin sauka a kumatunsa yagoge, cigaba da mammatsa mata hannunta yayi sannan yatashi yafita bayan yayi kissing din goshinta.
.
Tunda ummi tayi masa wannan maganar suka shiga neman magani babuji babu gani amma kuma har lokaci mai tsawo ba adaceba domin duk mai maganin da aka kai masa Hafsa sai yace bai gane abinda ke damunta ba, gashi yusleem yana son yafitar da ita kasar waje amma su ummi sun hana sunce ciwon kamar ba na asibiti bane,

Abubuwa duk sun taru sunyi masa yawa nan aka hakura aka zubawa sarautar Allah ido amma ana neman maganin duk inda akaji labari.

  Yau kimanin watanni uku kenan da fara rashin lafiyar Hafsat, cikin satin yusleem yayi tafiya ta kwana biyu koda yatafi duk hankalinsa atashe yake domin yafi son kullum yarinka ganin Nana hafsanshi,

Kwananshi biyar yadawo, aranar da yadawo Alh Musa mori yayi masa waya yace yana son ganinshi, bai jeba saida yafara biyawa ta gidan su Hafsat domin idanuwanshi suna masifar son ganinta saboda kwana biyun nan da bai ganta ba ji yake kamar anzare masa lakka, shi sai yanzu ne da bata da lafiya yagane cewar yana mutukar kaunarta,

Tunda yashiga gidan yajishi gaba daya ya canja sai wani kamshi yake,
.
Cikin falon ya tasamma nan ya tarar da Ummi zaune sai Hafsat akusa da ita tasha english wears pink colour, riga da skirt, ta kama kanta da wata hula baka mai santsi, murmushi yai mata ga mamakinsa sai yaga itama ta maida masa da martani, nan ta mike tafita, suna cikin gaisawa da Ummi sai gata tashigo rikeda babban tire takawo masa juice da bottle water,

“Sannu….” Yace ahankali can kasan makoshinsa,

“Yawwa…” Ta amsa tareda yimasa murmushi, hamdala yafara yi acikin ranshi domin wannan kadai ya tabbatar masa da cewar hafsanshi tasamu lafiya,

Maganar Ummi ce takatse masa tunaninsa,

“Yusleem dama alh nason ganinka, tunda kazo bari inyi masa magana…”

Wayarta ta dauka takira alh sa’eed cewar yusleem yazo, shikuwa yusleem sai kallon Hafsat yake yanata faman aika mata da sakonni kala kala ta idanuwanshi, ita dai sai dai tayi murmushi ta sunkuyar da kanta.
.
Mintuna kadan alh sa’eed yashigo cikin falon yasamu wuri ya zauna, sauka kasa yusleem yayi ya gaidashi, bayan sun gaisa alh sa’eed yayi gyaran murya yace,

“Alhamdulillah ala kulli halin, yusleem damu dakai mun san komai daga Allah yake,sannan duk abinda yafaru da bawa mukaddari ne daga Allah, nasan kayi namijin kokari wurin ganin matarka Hafsat tasamu lafiya amma abin yaci tura, to duba da irin yananin da take ciki shine muka taru muka yanke wata shawara,

Muna son kasaki Hafsat inyaso ka auri yar uwarta *AMAL*  domin basu da banbanci ko awurin halitta…”

Cikin sauri yusleem yadago yakalli abban su Hafsat,

“Abba, wanne irin saki kuma? Wacece amal?” Bakinsa yana rawa yayi wannan maganganun,

Nuna masa amal abba yayi da yatsa,

“Gata nan kusa da hajiya Kubra”

Arazane yusleem yakalli wacce ada yake tsammanin hafsanshi ce, tabbas ko shakka bayayi wannan Hafsa ce tawarke duk da yaga takara fari sosai, to kodai wasa abba yake masa?

“Abba dan Allah karka cemin wannan ba Nana Hafsat bace…”

“Yusleem wannan amal ce yar uwar Hafsat, tare muka haifesu, yan biyune, Hafsa tana cikin daki…”
.
Dasauri yatashi yanufi dakin dan bai yarda ba, yana shiga yahangeta kwance tana bacci kamar yadda tasaba, da sassarfa yakara kusa da ita ya tsugunna yakamo hannunta kawai sai yafashe da kuka tamkar wani karamin yaro, dakyar yayi ta maza ya tsaida kukan yatashi yafita yana kallon amal wacce ko kadan batada maraba da hafsanshi,

“To yusleem yanzu dai kaje gida kuyi shawara da mahaifiyarka domin yabawa mukayi da nutsuwarka da kuma kokarinka shiyasa muka musanya maka da amal amadadin Hafsat….”

“To abba bari naje…”

Shine kawai abinda ya iya fadi yatashi yafita, kansa yawani yimasa nauyi da haka yaja mota yanufi gidan alh Musa mori domin sai waya yaketa yimasa,

Acikin falonsa ya tarar dashi zaune shida matarsa, da fara’a suka karbeshi bayan sun gaisa alh Musa yadubeshi da fara’a yace,

“Yusleem, nasan kasan irin matsayin da nabaka na dan da kamar nine na haifeshi, sannan na doraka akan dukiyata fiyeda yadda na dora yayana na cikina, to kayi hakuri zan sake dora maka wani nauyin akaro na biyu, domin zan aurar da yata Hafsat agareka mutukar ka amince….”

Yusleem ji yayi hankalinsa yatashi, gaba daya jikinsa babu kwari domin indai da halacci to da kunya yadubi idon alh Musa yace baya son yarsa ta cikinsa,

“Yusleem yanaji kayi shiru…?” Inji alh Musa,

Sake sunkuyar da kai yusleem yayi, ya ce,
.
“To alh nagode, Allah yasaka da alkhairi, yanzun ne sauri nake domin agida ana jirana, bari naje”

Sallama sukayi yafito zuciyarsa nawani irin tafarfasa cikin sa’a sai ga Hafsat ta danno motarta cikin gidan tana makale da waya, hade rai yayi yaje har gaban motarta yabude kofa ya kalleta cikeda tsana,

“Dama saboda kina son in aureki shiyasa kika yiwa matata asiri? To wlhi kiyi gaggawar zuwa ki karya asirin nan domin bazan taba aurenki ba, ni bakiyi minba bana sonki, mace daya nake so itace matata….”

Tafiya yayi yabarta baki bude mamaki bayyane akan fuskarta,

Aguje yake tafiya har yakarasa gidansu, part din mami yashiga, tana cikin bedroom dinta tana hutawa dan haka yabita ciki, agefen gadonta yazauna,

“Yawwa yusleem gara da Allah yakawoka, yanzun nan hajiya fa’iza tatafi mun gama yanke magana da ita zaka mayarda Khadija dakinta kafin Allah yabawa hafsat lafiya…”

Shiru yayi ya tallafe kansa da hannayensa wanda yake juya masa ga wata hajijiya dake daukarsa…….

*
        *Gaisuwa ga dunbin masoyana masu karanta littafin alwashi musamman ma masoyan yusleem & Hafsat, hakika banida kalmar da zanyi amfani da ita wurin mika muku sakon gaisuwata gashi kuma yawanku yasa bazan iya lissafo sunayenku ba amma akoda yaushe kuna nan acikin zuciyata…*

     ***Tsawon mintuna biyar yusleem yana rikeda kansa yakasa tabuka komai domin ji yake tamkar kansa zai rarrabe gida dari dan tsananin ciwo,

Wasu zafafan hawayene suka fara zubowa daga idonsa,

“Yusleem yanaji kayi shiru….” Mami tafada tana daga kishingide akan gado,
.
“Mami nashiga tsaka mai wuya, bazan iya auren wata maceba inbanda Hafsat, Hafsat itace sirrina she’s my  everything, Hafsat itace macen da tasoni tsakani da Allah, tasha wuya ta, tashiga kuncin rayuwa saboda ni, Hafsat itace macen datafi cancanta insota kuma inrayu da ita koda kuwa zataci gaba da tsanata da kyarata,

Mami bazan iya rabuwa da Hafsat ba sannan bazan iya yimata kishiya acikin wannan halin ba, mami zan cigaba da zama da Hafsat ahaka koda hakan na nufin rayuwata zata kare cikin kunci da damuwa da bakin ciki saboda abaya Hafsat ta zabi zama cikin kunci da talauci saboda ni, Hafsat itace tayi min sanin da ko mahaifiyata bata yimin shi ba, sannan ta lullube sirrina bayan ta maidani cikakken mutum nagari….”
.
Zaune mami tatashi tana sauraren yusleem,

“Yusleem duk naji bayananka kuma nafika son zamanka da hafsa amatsayin mata, idan baka manta ba nice nan nanemo maka ita a lokacin da baka santa ba kuma na jajurce har sai da tazama matarka, to yanzu tunda lalura tashigo ciki yana da kyau kasamu nutsuwa tahanyar auren wata matar…”

“Mami i can’t, wallahi bazan iyaba, bazan iyaba mami, mutukar nayiwa Hafsat kishiya tana cikin wannan halin ban kyauta mata ba, kamar yadda ta zauna dani acikin halin lalura to nima yazama wajibi inzauna da ita aduk halin data tsinci kanta, mami naci ALWASHIN zama da Hafsat ahaka kuma zan yi iya bakin kokarina wurin nemo mata lafiya domin hakan kadai shine zai bayyanarwa da duniya matsayinta da muhimmancinta agareni…”

Hawaye na bin kumatunsa yajuya yadafa mami,

“Mami ko kin san da ni dan luwadi ne? Mami da ni gay ne wanda bansa komai agaba ba face rashin tsoron Allah da aikata kazantar da Allah yai hani da ita, mami Hafsat da idonta taganni ina aikata luwadi amma ko uwar data haifeta bata fadawa ba haka tazauna dani, to danme yanzu ni zan kasa zama da ita? Mami akan me? Why….?, mami babu aurefa tsakanina da khadija domin saki 3 nayi mat”

Mikewa yayi tsaye nan wani jiri mai karfin gaske ya kwasheshi, sai gashi akasa, mami dake zaune ta daskare awurin takasa ko motsi saboda jin maganganun da yagama fada mata yanzu, dakyar tatashi tafita takira su Abdul, akan gadonta suka dorashi takira Dr Nabila domin abashi taimakon gaggawa,
.
Wani matsanancin ciwon kai yakeji tunda yafarka, bude idanuwansa yayi wadanda suka yimasa nauyi,

“Mami bazan auri kanwar Hafsat ba, bazan auri Hafsat ba, bazan auri khadija ba domin babu aure atsakaninmu saki 3 nayi mata mami, idan ku kun manta ni ban manta ba, cikinsu babu wanda zan aura mami, zanci gaba da zama da matata har mutuwata, wallahi mami bazan iya auren wataba, mami dan Allah kije ki dauko min Hafsat, ni ina son zama da ita koda zata cigaba da tsanata….”

Wadannan surutan yai tayi baiyi shiru ba, kowa dake cikin dakin shiru yayi yana saurarensa, saida mami taji yana shirin sake bada labarin da yabata dazu sannan tayi saurin zuwa tazauna tarufe masa baki da hannunta tana fadin,

“Ya isa haka yusleem, yi shiru zanje zan kawo maka ita, kayi hakuri…”

Karin ruwan dake hannunsa ya kalla sai yadafe goshinsa domin baya zama yaci abinci sam tunda yaga halin da Hafsat ke ciki wanda wannan kadai ya isa ya sashi rashin lafiya,
.
Rarrashinsa mami taci gaba da yi har tasamu allurar da aka yimishi tasoma aiki aijikinsa nan bacci ya daukeshi,

Nan suka koma falo suka barshi acikin bedroom din yana bacci, mami kam duk jikinta yamutu yayi sanyi kalau saboda jin labarin da yusleem yabata wai ada shi gay ne amma ita bata taba saniba? Lallai indai hakane to ta tabka babban kuskure abaya domin indai uwa tagari ce zata kasance mai bibiyar al’amuran yaranta da sanin abokan mu’amularsu da wurinda suke zuwa da kuma dabi’unsu,

Tabbas yanzu kam zata goyawa yusleem baya kamar yadda yaci ALWASHI na rayuwa da hafsanshi ita kadai kwal agidansa, tagumi ta rafka wanda har  bata jiyo maganar da surayya ke yi mata,

“Mami inata magana, tunanin me kike yine…?”

Firgigit tayi ta kalli sury,

“Wallahi surayya tunanin yayanku nakeyi domin yana cikin wani hali…”
.
“Allah zai bashi lafiya mami, kidaina daga hankalinki, me za adafa masa?”

“Kiyi masa faten wake da kifi da ganye, tunda kinga baya cin abinci sosai…”

Tashi surayya tayi tafita zuwa kitchen ita kuma mami taci gaba da zama bayan ta rafka tagumi.

Misalin karfe 10 yusleem yafarka har lokacin kansa bai daina wannan azababben ciwonba, mami ya kalla da kannensa wadanda ke zaune,

“Mami tana ina?”

Soma kwantar mishi da hankali mami tayi, dakyar ta lallabashi yaci abinci yakoma bacci,

Bar mishi dakin mami tayi takoma bedroom din surayya suka kwana tare.

Sai da yusleem yayi kwana uku akwance, akwana na hudu yadan samu lafiya har ya samu yafito daga bedroom din mami yazauna a falo, aranar mami taje gidansu Hafsat domin taho da ita nan Ummi ke fadawa mami shawarar da suka yanke na aurawa yusleem amal kanwar Hafsat domin ta maye gurbinta, jijjiga kai mami tayi taceda Ummi,

“Hajiya kubra ni ina ganin kar asoma yin haka domin yusleem ahalin yanzu yanuna min babu wadda zai zauna da ita idan ba Hafsat ba, mu hakura kawai muyita addu’a har Allah yabata lafiya, yanzu haka ma ni zuwa nayi domin natafi da ita…”
.
“To shikenan hakan yayi ai duk dayane da amal din da Hafsat din domin nice nan duk na haifesu, amma maganar komawar Hafsat adan bamu lokaci domin muna son muyi mata magani na gida, sannan yanzu haka ma andorata akan wasu addu’o’i wadanda nake yimata kullum safe da daddare, insha Allah da zarar ta soma samun sauki zamu dawo masa da matarsa…”

“To shikenan Allah yasa mudace, Allah yabata lafiya, shima yanzu yana can akwance bashida lafiya amma yadan soma warwarewa”

“To Allah yakara masa lafiya…”

“Amin” inji mami, nan mamin tayiwa Ummi sallama tatashi domin tafiya,amal dake labe ajikin labule akofar dakinsu tana sauraren duk abubuwan dasu mami suka tattauna akai wasu hawaye ne na bakin ciki suka shiga zarya da Kai Kawo akan kumatunta, cikin bedroom tawuce dagudu tana kuka, Hafsat dake zaune akan gado tabita da kallo ta zuba mata ido, cikin toilet amal tashiga tarufo kofa tana wani irin kuka mai tsuma zuciya wanda ita kadai tasan ko kukan me takeyi.
.
Daga gidan hajiya kubra mami gidan su khadija tawuce taje tasamu kawarta hajiya fa’iza suka tattauna dangane da maganar da sukayi na komawar khadija anan mami tabata hakuri tasanar da ita cewar yusleem bai aminceba yace saki uku yayiwa khadija abaya kuma bashida niyyar kara aure zai cigaba da jiran matarsa har tasamu lafiya,

Murmushi hajiya fa’iza tayi sannan tace,

“Ayya wallahi mun sha’afa ne, ashefa babu aure atsakaninsu yanzu tunda saki 3 ne, Allah yasa haka shiyafi alkhairi to”

“Amin hajiya fa’iza” ummi ta amsa,

Duk da khadija tana zaune awurin bata ko damuba balle aga sauyin fuska atare da ita, mami ta dan jima agidan sannan tatafi,
.
Lokacin data koma gida afalo tasamu yusleem yayi wanka yasa green din t shirt da farin trouser yana zaune yana cin biscuit da fresh milk, zama mami tayi tafada masa duk yanda sukayi da su hajiya kubra da hajiya fa’iza,

“To mami yanzu saura abu daya, dan Allah kisamu lokaci kije gidan alh musa kifada masa bawai kin auran yarsa nayiba, inada mata kuma yanzu ni hankalina ba akwance yake ba…”

“Shikenan insha Allah zuwa gobe sai inje”

Sanyi yaji aransa domin yanzu wannan matsalar yasamu damar kawar da ita.

  Bayan sallar isha yatafi gidansu hafsat saboda kwana ukun nan da yayi batareda yaganta ba yayi mutukar jigata,

Kayan kwalam da makulashe ya siya mata sannan yakarasa gidan, dukkansu suna falo banda Hafsat din wacce yanzu zaman daki ya zame Mata doka,
.
Bayan ya gaisar dasu Ummi ne ummin tace yashiga, tashi yayi yashiga wurin Hafsat wacce bata gajiya da bacci domin yanzu ma shi takeyi,

Zama yayi agefenta yana kallon fuskarta wadda duk da acikin halin rashin lafiya take amma tayi kiba, gashin kanta atsefe,

Fuskarta yake shafawa ahankali, dayan hannun kuma yarike hannunta daya, amal tana tsaye akofar daki tana kallonsu hawaye nabin kumatunta suna wanke mata fuska, jin alamun fitowarsa yasata saurin barin wurin tafada bedroom din Ummi.

Kwanaki sunci gaba da tafiya ahaka Hafsat har yanzu sai dai godiyar ubangiji amma sauki bai samuba, koda yaushe yusleem yana kan hanyar zuwa gidansu, har umarah yaje ya iyo mata addu’a akan Allah yabata lafiya,

Wata ranar alhamis dukkaninsu suka tafi dubota kamar yadda suka saba shida su mami, sury, Abdul da khalifa,dama duk sati sai sunje dubota duka gidan amma shi yusleem arana ma sai yaje gidan sau hudu duk da bata son ganinshi,

Suna falo azazzaune bayan angama gaggaisawa alh sa’eed na kokarin fita yafasa sakamakon sallamar da sukaji anyi, kowa maida hankalinsa kan kofar shigowa cikin falon yayi domin ganin wacce ke sallamar,

Hafsat mori ce tashigo fuskarta akumbure duk ta kukkuje an nadeta da bandeji, haka kanta ma an nannadeshi da bandage, hannunta daya yasha bandeji sannan an sakaleshi ajikin wuyanta alamun karaya, kafarta duk auduga amammanne,

Yusleem takalla tayi magana cikin dasasshiyar murya irin ta marassa lafiya,

“Yusleem gashi…”

Kowa bin abinda ke hannunta yakeyi da kallo domin wata bakar ledace marar kyan gani,

“Daga gidanku nake aka ce min kun taho nan shine nabiyoku nan din, wannan shine asirin da akama matarka gashi ka dauka ka kona shi yanzun nan mutukar kana son ta warke…”

Ajiye ledar tayi tajuya zata fita yusleem yayi gaggawar shan gabanta, bai yi la’akari da daddaujewar dake jikin fuskarta ba ya dauketa da mari, dafe kuncinta tayi da hannunta mai lafiya hawaye nabin kumatunta,Murmushin karfin hali tayi ta kalleshi,

“Nidai gashi nan na ajiye maka, kadauka ka kona da hannunka domin mutukar bakai ka kone wannan asirin ba to matarka zata dawwama har abada acikin hauka….”.

      ***

Kowa acikin falon tsitt yayi banda khadija da amal wadanda suka zazzaro ido suke kallon Hafsat mori,
.
Da wani gudu amal tataso tazo ta cukumi wuyan Hafsat mori tana jijjigata,

“Kece kika haukata min yar uwa ko? Wallahi bazamu yarda ba sai kema na haukataki….”

Yusleem ne ya bambareta yacireta daga rikon da tayiwa Hafsat din,

Khadija kuwa dake zaune har lokacin idanuwanta awaje suke, cikin daga murya tace,

“Gaskiya Hafsat kinyi asara, kirasa hanyar da zakibi ki cutar da baiwar Allah saita hanyar haukatata?”

“Ai bata kyauta ba kuma Allah ya isa tsakaninmu da ita…” Ummi tafada tana kwalla,

Mami dai bin kowa take da kallo tama kasa magana, banda surayya wacce tayi jugum tai tagumi tana kallon kowa,

“Duk dai yanzu abar wannan maganar, kai yusleem kayi yanda tace kadauka kaje waje ka kona…”

Juyawa Hafsat tayi zata tafi yusleem yayi saurin fincikota wanda har saida tatafi taga taga zata fadi,
.
“Babu inda zakije har sai nakona asirin nan sannan sai nakira hukumar yan sanda nayi report sunzo sun tafi dake domin wallahi bazan taba yafe miki ba har sai munyi shari’a dake….”

Wani murmushi Hafsat tayi irin ko ajikina dinnan tawuce kan kujera ta zauna, wata uwar harara khadija ta wulla mata,

“Andaiyi asara, wallahi sai kin je prison tunda kika cutar da baiwar Allah haka kawai…”

“Ba nace ya isaba? Kar nasake jin maganar kowa, kai yusleem dauki muje…” Alh sa’eed yafada yana nunawa yusleem kofa, tare suka fita dashi suka zagaya bayan gidan suka kunna wuta suka kona abun, nan wani bakin hayaki yaringa fita har yazama ja daga nan yakoma kore daga karshe yazama fari tass,

Saida sukaga yadaina hayaki alamun yagama konewa kurmus sannan suka koma ciki, abin mamaki suna shiga cikin falon saiga Hafsat tafito daga cikin daki dafe da kanta,yusleem ta zubawa ido tana kallonshi cikin wani irin shauki na so,

Kowa ita yake kallo ganin haka yasata karasawa tsakiyar falon ta matsa kusa da amal ta zauna wacce tafara hawaye tun ganin fitowar Hafsat din,

Waya yusleem yazaro daga cikin aljihunsa zai kira police alh sa’eed yayi gaggawar dakatar dashi,

“A’a yusleem, katsaya dai mubi komai ahankali mu warwareshi, kabari tafada mana dalilinta nayin haka..”

“Babu wani dalili abba kawai shirmene da hauka da mugunta irin nasu na mata….”

“Kadai bari muji daga gareta”

Juyawa ga Hafsat mori abban yayi,

“Baiwar Allah kiyi mana bayanin abinda yafaru, ni bana son zuwanki wurin hukuma domin hakan tozarcine ga rayuwarki…”

Wani shu’umin murmushi Hafsat mori tayi sannan ta daga kanta sama alamun tunani…..

*FLASHBACK*

Afusace yaja motarsa yabar harabar gidan bayan yagama gasa mata bakaken maganganu yanda yaso,

Cikeda mamaki baki abude take binsa da kallo har ya bacewa ganinta,

Ahankali taja kafarta tabar wurin tashiga cikin gida kasa tabuka komai tayi dan haka tawuce cikin dakinta ta zauna agefen gado,

“Anyiwa matarsa asiri? Kuma yana zargina da aikata hakan?”

Sunkuyar da kanta tayi daga nan kamar wacce aka tsikara ta mike ahanzarce tadauki key din motarta tafita duk da agajiye take, kai tsaye asibitin da aka kwantar da Hafsat kafin asallameta tanufa,

Dakyar tasamu ganin Dr zayyad ta hanyar dan uwanta Dr sufyan domin cousin brother dinta ne, bata samu damar barin asibitin ba sai misalin karfe 9 nadare,
.
Agajiye liss takoma gida lokacin kowa dake gidan yakwanta bacci,

Zama tayi akan teburinta na karatu wanda yake cikin dakinta ashirye kamar libry, mintuna kadan tatashi tashiga wanka tafito, ruwan Lipton kadai tasha tasake zama awannan teburin tana faman bincike acikin wasu tuma tuman littattafai har karfe 3 nadare tadauka zaune tana faman bincike sai 4 saura sannan ta kwanta,

Washe gari da sassafe ta tashi tashirya tafita ko karyawa batayi ba,

Unguwar Garara ta nufa nan tasamu dakyar ta binciko gidan da take nema, wani dan karamin gidan kasa tashiga tana kwada sallama, daga can wata yar dattijuwa ta amsa mata bayan tafito, gaisawa sukayi,

“Baba nazo wurin Malam audu ne mai gidannan”

“Lale lale, sannu da zuwa sai dai kuma yafita yatafi gona amma kijirashi yanzu zai dawo” Yar dattijuwar tafada tana kokarin shimfida mata wata yar guntuwar tabarmar karauni,

Zama Hafsat mori tayi tazaro wayarta wacce take tamkar faranti dan tsananin girma nan takunna ta tashiga latsawa,

Tsawon mintuna talatin sai ga alh audu yashigo sabe da fartanya akan kafadarsa,

“Yawwa Malam sannu da zuwa dama tun dazu bakuwa take jiranka”

Ajiye fartanyar yayi yana murmushi,

“Allah mai iko, lale da bakuwa…”

“Yawwa sannu da zuwa Malam…”

Zama yayi akan wani dan dutse wanda ke kafe abakin kofar dakinsu,

“Sai dai kuma yarinya ban ganekiba, daga ina?”

Murmushi Hafsat mori tayi,
.
“Baba ni sunana Hafsat m mori, ni kwararriyar lawyer ce mai zaman kanta, nazone domin ina neman wasu bayanai daga gareka saboda zamuyi wani aiki dakai, dan Allah baba kabani hadin kai, kataimaka min”

“To yarinya bawai ki nayiba amma wanne irin aikine wadannan, sannan wadanne bayanai kike nema daga gareni?”

“Baba abaya kayi aiki agidansu wani Matashi wanda ake kira da yusleem, shin baba zan iya sanin alakarka dashi wannan matashi? Tsawon wanne lokaci kadauka agidansu kana aiki? Shin yanzu kanada wata alaka dasu ko babu? Wanne irin bayani zaka yimin dangane da halayya ko dabi’un shi yusleem din”

Gyara zama Malam audu yayi yana kallon Hafsa,

“To yarinya nidai tsawon shekaru 4 nadauka ina aiki agidansu shi yusleem, sannnan nabar aikine agidan shekaru uku baya…”

“Ko menene dalili baba?”
.
“Ehh saboda girma yakamani shiyasa mai dakina tanemi da indawo gida inzauna inhuta haka”

“To baba yanzu kenan bakada wata alaka dasu?”

“Ehh gaskiya babu amma duk da haka wata rana nida mai dakina mukan shirya mu ziyarcesu”

“To baba mai kasani dangane da yusleem?”

“Yaron kirkine mai ganin girman manya, har nabar aiki agidansu ban taba ganin ya yi wani abu wanda bai kamata ba…”

“Har yanzu baba da kake ziyartarsu ko sau daya bakaji wani mummunan abu dangane dashiba?”

“Gaskiya banjiba”

“To baba lokacin daka bar aiki waye yakarba?”

“Malam ilu ne yakarba”

“Yanzu yana ina?”
.
“To inajin dai acan kauyen madaci yake domin shima yanzu yabar yimusu aiki”

“To baba nagode, idan nasamu lokaci zan dawo, nagode madalla”

“Ah babu komai yarinya, sai kin dawo”

Sallama tayi musu tafita, tana fita matar Malam audu ta dubeshi,

“Malam wannan yarinya da tambaya take? Aba kamar na’urar nasara?” Dariya dukkaninsu sukayi shida ita,

Da fitarta motarta tabude tashiga bata zame ko inaba sai kauyen madaci domin ayau dinnan take son ganin Malam ilu.

Tasha mutukar wahala Kafin tasamu gidan malam ilu, lokacin da tasamu gidan tashiga baya nan yatafi kasuwa sai matanshi da yaranshi, kasuwar tabishi wurin da yake sayar da kayan masarufi,

Acikin rumfarsa ta zauna ta fara gabatar masa da kanta, dukkan tambayoyin da tayiwa Malam audu shi tayi masa yana bata amsa har akazo wurinda take son ji domin tanan ne kadai zata samu saukin binciken da take yi,

“Malam ilu tun lokacin da kake zaune agidansu yusleem baka taba ganinshi da wani hali ko dabi’a wadda take bata gariba?”

“Ehh hajiya gaskiya nidai ban sanshi da wani hali marar kyau ba amma dai wata rana ina cikin falon mahaifiyarsa domin karbar albashi na naji ya bugo mata waya amma banji abinda yaceba nadai ji ita tanata fada tana cewa baya son zama da mata domin wannan itace mace ta goma da ya aura yasaki acikin kasa da shekera biyu… To wannan dai itace matsalarshi ina jin amma bayaga wannan agaskiya ban sanshi da wani mummunan haliba…”
.
“Nagode baba ilu sai nasake dawowa akaro nabiyu domin da yuyuwar zan kara dawowa”

“Shikenan yarinya Allah yadawo dake”

Sallama sukayi tashiga motarta tafita lokacin misalin karfe 1:30 narana, inbanda yunwa babu abinda takeji saboda ko breakfast batayi ba tafito da sassafe,

Kai tsaye gida tawuce tana zuwa tashiga kitchen tazubo abinci, tana zama hajiya mahaifiyarta nashigowa,

“Hafsat ina kikaje ne yau tun safe?”

Murmushi tayi takalli hajiyarta,

“Hajiya ina wani bincike ne akan wani case da zanyi…”

“To ai ku dama lauyoyi kullum aikinku kenan investigation, bakuda wani batu sai wannan, Allah yabada sa’a amma ina fata case din ba akan kisan kai bane ko maita dan bana sonki da karbar irin wadannan case din domin hatsarinsu yawa gareshi…”
.
“Bashi bane hajiya amma zanyi miki tambaya, hajiya mutumne yakeda matarsa sai tafara ciwon hauka kuma ance asirine to da yataba auren wasu matan kafin ita, dan Allah waya kamata azarga?”

Shiru hajiya tayi zuwa can tace,

“To zato dai zunubi ne amma babu tabbas ko acikin kishiyoyinne wata tayi mata asirin..”

“Hakane hajiya nima abinda nake tunani kenan amma dai bari zan bincika”

Abincin da take ci ta ajiye tawuce bedroom dinta, wanka tayi tai salla tazura wata bakar doguwar riga tayi rolling fuskarta babu makeup tafito, motar hajiya ta dauka tafita da ita, can tsohon gidansu yusleem tawuce kai tsaye B/Q din gidan tashiga inda malam hassan driver da matarsa Hadiza ke zaune,

Malam hassan baya nan domin har yanzu yana aiki dasu Mami sai matarsa ta samu nan tazauna suka gaisa ta gabatar mata da kanta,

“Malama Hadiza a iya tsawonki da Mami da yusleem mata nawa kikasan ya aura?”

“Gaskiya ban san adadinsu ba amma sunfi goma”

“Kuma duk shi yagansu yana so har ya auresu?” Hafsat ta jefa mata wata tambayar,

“A’a gaskiya duk mahaifiyarsa ce ke wahalar nemo masa”

“To meyasa yake sakinsu?”

“Saboda yace baya sonsu,ita kuma mamin bata hakura har sai ta sake yimasa wani auren”

“Wacece matarsa tafarko?”

“Wallahi namanta amma dai anan garin take”
.
“Daga cikin matan da ya aura waccece kike ganin kamar tafi sonshi?”

“Gaskiya duk suna sonshi shine dai baya sonsu”

“Zaki iya fada min guda uku daga cikin matan da ya aura?”

“Ehhh zan iya”

“Yawwa nagode”

Tsawon wani lokaci suka dauka suna tattaunawa sannan tayiwa Hadiza sallama tatafi, tana driving tana share zufar datake keto mata duk da cewar ta kunna air condition acikin motar,bata taba yin case mai kalubale irin wannan ba duk da cewar tajima tana yin cases daban daban to amma wannan yazo mata da wani salo daban,

Yanzu tunaninta shine inda zata samu matan da yusleem ya aura abaya domin amsa mata wasu tambayoyi, gida takoma domin magrib tayi, koda taje gidanma bata hutaba kwakwalwarta sai kaiwa da komowa takeyi domin gano ta inda yakamata tafara.

  Washe gari gidansu kamal tayiwa tsinke wanda shine kukun da yake dafawa mami abinci, yana daf da zai fita taje,

Bayan tagabatar mata da kanta ne tasoma yimasa tambayoyi,

“Ranki yadade ni babu abinda nasani dangane dasu yusleem domin aikina shine kawai dafa abinci”

Murmushi Hafsat mori tayi,

“To amma kasan matarsa bata da lafiya ko?”

“Kamar yadda nafada miki nifa ban san komai ba”

“To shikenan nagode”
.
Sallama sukayi tafita tanufi motarta, chamber din Barrister Aminu ta tafi amma koda taje akofar office dinshi tasameshi yana kokarin fita alamun cikin sauri yake,

“Barrister da zuwa nayi kamin wani taimako”

“Gashi kuma barrister kin sameni akan hanya domin wata tafiya zanyi yanzu zanje bayelsa state domin yin wani case kuma gaskiya zanfi 1 month acan, amma abinda za ayi zan hadaki da barrister aiman insha Allah zai baki duk wani taimako kamar yanda zan baki”

Godiya tayi masa takarbi number din barrister aiman din tatafi amma duk jikinta yayi sanyi.

Tsawon 3 weeks ta dauka tana bincike amma har yau bata samu wata matsaya guda daya ba ganin lokaci yana kurewa yasata neman barrister aiman nan ta gayyatoshi gidansu domin bata sanshiba kuma bata taba ganinsa ba,

“Barrister narasa ta yanda zan bullowa case dinnan, wacce shawara zaka bani?”

“Barrister gaskiya case dinki yana bukatar dogon bincike, amma ke wakike suspecting?”

“To ai yanzu barrister kowa ma abin zargine harda ni kaina, yanzu bincike sai yabi takan kowa ciki harda ni, sannan ya auri mata da yawa abaya narasa tayanda zan samosu balle har inyi musu tambayoyi”

Murmushi barrister aiman yayi wanda kyawunsa ya bayyana domin kyakkyawan matashine wanda shekarunsa 32 kacal aduniya,
.
“Karki damu insha Allah zan taimaka miki, just give me 3 days i will find out duk wani information da muke bukata”

“Nagode barrister”

Hira suka dan taba daga nan yatafi, duk da barrister aiman yayi mata alkawari bata saki jikiba, itama cigaba yin nata binciken tayi cikin sa’a tasamu damar gano mata uku daga cikin matan da yusleem ya aura,

Lokacin da barrister aiman yadawo yazo mata da information masu yawa nan itada shi suka fara bibiyar tushen faruwar rashin lafiyar Hafsat amma sun kasa ganowa har bincikensu yaje karshe yanzu yarage iya gidansu yusleem kadai,sai ko kadan daga cikin matan da ya aura wadanda basu ganosu ba,

Samun barrister aiman tayi cikin sanyin jiki tace,

“Barrister nagama karaya, ina tunanin duk yanda akayi wanda yayi wannan abun nagida ne domin kaga yanzu duk mun gama bincikar kowa amma babu alamun laifi atattare dasu, yanzu kawai gidansu yusleem zanje inji yaushe abun yafaru,suwaye suke gidan alokacin,kai har ma wanda yashiga gidan aranar sai na bincikeshi koda kuwa dabbace..”

Dariya barrister yayi yace,

“Idan kikaje dakanki kuma ai magana ta lalace kibarni nine kawai zanje so sai muyi amfani da hidden camera kirinka ganin duk abubuwan da zamu tattauna dasu”

“Shikenan barrister amma fa ka binciki kukun nan dakyau domin ban yarda dashiba last time ma ni kin amsa min tambayoyi yayi”

Sallama sukayi tatafi, aranar da daddare tana tsaka da shiryawa barrister aiman tambayoyin da zaiwa su mami gobe taji wayarta na kara nan tadauka saboda ganin shine,
.
“Ansake samun wani information, akwai wata mata da ya aura guda daya bari zan turo miki massage ta whatsapp yanzu”

Katse wayar tayi tajira sakonshi, sunan da matar ke amfani dashi shine Big girl, nan tayi searching dinta a Facebook tayi adding dinta domin da pic da komai nata barrister aiman yaturo kawai matsalar sun rasa sunanta nagaskiya, creating din sabon account na facebook Hafsat tayi acikin wannan daren,

Friend request Hafsat tatura mata nan tayi accepting suka fara gaisawa, kamar yadda suka shirya da barrister aiman haka tayi tanuna mata cewar ita kawarta ce wadda suka dade basu haduba da ta tambayi Hafsat sunanta sai tace sunanta na’ima Abbas ashe kuwa big girl din nada kawa mai wannan suna nan tayita sakin baki suna hira har taturowa Hafsat sabuwar number dinta ta whatsapp,

Tsawon 3 days suna chaten nan Hafsat tafara tambayarta wurin wanne boka take zuwa yanzu, kamar wacce ke jira tafara fada mata cewar a Niger yake amma tabari sai zataje sai su tafi tare kuma abin haushi tun daga wannan rana bata kara ganin big girl ba ko a online gashi wayarta bata shiga,

Barrister aiman tasamu tafadawa yace sujira har big girl din tadawo online nan Hafsat ta girgiza kai tace,

“No barrister gaskiya bazamu jiraba, ni aganina muje office din masu sim din datake amfani dashi tana chat gaba daya atattaro mana chat dinta wanda tayi da kowa da kowa”

“Kuma fa kin Kawo idea barrister, tashi muje”

Office din masu layin da big girl ke amfani dashi sukaje nan aka tattara musu komai aka basu domin tunda sukayi bayanin kansu ma’aikatan suka karbesu hannu bibbiyu amma kuma wani abun mamaki hatta register sim din da take amfani dashi namijne yayi shiyasa babu damar ganin information dinta,
.
Gida Hafsat takoma tashiga daki tarufe ta nutsu tafara bincikar chaten din big girl daya bayan daya har tazo nakan wani malam Dahiru Niger, nan taga chaten dinsu, daukar number dinshi tayi dasafe takirashi tace kawarta ce ta turota wurinshi yayi mata kwatance zai musu wani aikine, nan yafayyace mata yanda zata ganshi idan tazo Niger, sallama sukayi barrister aiman nazaune yana jinsu daga nan suka fara tsara yanda zata shirya tafiyarta zuwa Niger.

Ajirgi tatafi aranar da taje bata samu ganin Malam Dahiru ba domin yana can maradi, saida ta kwana sannan washe gari tashiga mota tatafi maradi,
Bayan sun gaisa tayi masa bayanin cewar kawarta ce taturo ta akan asirin nan da tasashi yayi yakarya shi nan yarike kai yace,

“Ai nafadawa big girl din shifa wannan asirin bazai karyeba har sai mijin shida kansa shine yakona”

“Ehh tasani shiyasa ma tace kabayar atafi dashi akarya acan”

Tashi yayi suka tafi makabarta domin acan ya binne asirin, acan aka tono asirin yabata,duk abinda ke faruwa akan idon barrister aiman ne wanda ke zaune yana gani ajikin laptop dinshi domin hafsat tana makale da wata yar karamar hidden camera ajikinta,

Tana komawa hotel din data sauka ta tattara kayanta domin dawowa Nigeria saboda jikinta yabata cewar akwai abinda zai biyo baya……

   _Gaisuwa da fatan alkhairi ga makiyan Hafsat mori domin nasan bata da fans ni kadai ke yinta….. Lol!

       ***

Kamar yadda Hafsat ta zarga hakance kuwa tafaru domin bayan tahowarta daga wurin malam D’ahiru sai ga wayar big girl takirashi da wani sabon layi saboda akwai wani sabon aiki datake son yayi mata cikin kankanin lokaci nan yake sanar mata da cewar kawarta wacce taturo yabata wannan sakon yabata har tatafi nan big girl tayi zumbur tana tambayarsa wanne sako domin ita dai a iya saninta bata turo kowaba, ai kuwa hankalinta ba karamin tashi yayiba lokacin dataji abinda yafada wai asirin da akayiwa matar yusleem tuni takashe wayar tasoma neman mafita, wayar na’ima kawarta takira domin taji ko itace amma koda na’iman ta dauka sai tama nuna ita sam bata san da wannan zancenba, hatta chaten dinsu da maganganun da sukayi a facebook duk na’iman ta nuna bata san anyiba,hankalin big girl kara tashi yayi nan jikinta yabata cewar koma wacece wannan dabara tayi mata ta shammaceta domin tacika nata burin,idan kuwa hakane yazama dole tadauki fansa akan koma wacece tayi mata wannan shisshigin akan yusleem.

   Kasancewar Hafsat agarin dake makotaka da jaharsu tasauka daga nan mota tahau zuwa garinsu, ba karamar tafiya suka shaba domin har misalin karfe 10 nadare suna kan hanya, daf da zasu shiga garin yan fashi sukayi niyyar taresu nan drivern yaki tsayawa garin guduwa yan fashin suka harbi tayar motar guda daya nan motar ta nufi cikin jeje taje tarinka bugar bishiyoyi da duwatsu tana dungurawa, sai da mutanen cikin motar suka jigata sannan motar takife, bayan kamar rabin awa da faruwar abun sai ga jami’an tsaro, sune suka dauki su Hafsat zuwa asibiti wanda saida tashafe tsawon kwanaki biyar acan, daga asibitin ta tafi gidansu yusleem amma koda taje sai mai gadi yace basa nan nan ta matsa masa da tambaya har saida ya sanar mata inda suka tafi shine tabiyosu,
.
Shiru kowa yayi acikin falon bayan Hafsat ta kammala basu wannan labarin,

Cikin sanyin jiki tareda nadamar irin cin mutuncin da suka yiwa Hafsat din dafarko Ummi tace,

“Lallai kin cika yar halak sannan kin cancanci kowacce irin jinjina, amma ni abinda nake fatan sani kuma na matsu da insani shine wacece big girl?”

Ajiyar zuciya Hafsat mori tasauke tana wani tunani acikin ranta, kukan amal ne yacika cikin falon wanda yabawa kowa mamaki banda Khadija dake faman fitar da kwalla tana kuka marar sauti,

“Bayan wannan accident din da nayi, big girl tanata kokarin ganoni domin tadauki fansar abinda nayi mata amma cikin ikon Allah barrister aiman yana bibiyarta shima sannan yana sane da duk wani yunkurinta, har asibitin da nake taje bayan taganoni wanda barrister aiman ne yashirya mata kofar rago har tazo hannu yanzu haka tana can ahannun hukuma domin kotu zamu shigar da ita…”
.
“Bata fada miki sunanta ba? Ko kuma wacece itaba?” Alh sa’eed yabukata,

“A’a ai ban samu zarafin ganinta ba ma bare har nayi mata interview, munyi magana da barrister dai yace min har yau taki amsa masa ko ita wacece…”

“To yanzu tashi zakuyi muje muganta domin musan ko wacece” inji Mami,

Amal kowa keta kallo wacce tadage sai kuka take, rungumeta Hafsat tayi tana hawayen itama,

“Kiyi hakuri amal ai gashi nasamu lafiya”
.
“Sister abubuwa da yawa nake yiwa kuka ciki kuwa harda yunkurin rabaki da masoyinki na hakika dasu Ummi sukayi niyyar yi tahanyar aura masa ni, nakanyi kuka mai yawa aduk lokacin da naga irin kulawar da yake baki da irin kaunar da yake yimiki, yau ina cike da farin ciki marar misaltuwa, wannan kukan da kikaga inayi wallahi nafarin cikin kin samu lafiyane zaki koma ga mijinki kuma masoyinki”

“Babu komai amal haka Allah yashirya, ni nasan su Ummi bazasu taba yin abinda zai raba kawunanmu ba ko ya cutar damu ba…” Takarasa maganar tana share hawayen dake kwaranya a idonta,

“Ku hanzarta kutashi mutafi” inji alh sa’eed,

Mikewa sukayi dukkaninsu suka dunguma har hafsat mori, kai tsaye police station suka wuce lokacin da sukaje aka fito musu da big girl, dukkaninsu basu santaba illa Mami da yusleem ne kadai suka santa,

“Rahina…..” Yusleem yakira sunanta cike da al’ajabi,

“Yusleem…” Big girl ta amsa tana mai daure fuska,

“Dama kasanta ne?” Hafsat mori ta bukata,

“Ehhh itace matata tafarko da nafara aura wacce aka yimana auren zumunci da ita, cousin dinace”

“Amma Rahina kin bata wayonki, meya kaiki cutar da yarinyar mutane?” Mami tafada idanuwanta fal kwalla,
.
Ita dai Rahina shiru tayi tana kallon kowa daya bayan daya, Hafsat itama kallonta take saboda ko kadan bata taba ganinta ba,

“Bari naje asibiti” Hafsat mori tafada domin kanta wani irin ciwo yake mata,

“To bari muje mu kaiki” Hafsat ta amsa mata tana kallon yusleem,

Tare suka fita domin mayar da Hafsat mori asibiti, sit din baya tashiga yayinda Hafsat tashiga gaba yusleem yaja motar suka tafi, babu wanda ke magana acikin motar sai da sukayi nisa sannan yusleem ya tambayeta wanne asibiti zasuje nan tafada masa,

Har Room din da aka kwantarta suka rakata daga nan suka fito suka tafi,

Kallon Hafsat yusleem yayi cikeda so,

“Muje gida basai mun koma gidansu ummi ba ko?”

“A’a mu koma kaga munbar su Mami acan”

Murmushi yayi yashafi sajenshi,
.
“Babu damuwa muje ai yau ango nake”

Murmushin itama tayi batace komai ba har suka koma gida, dukkansu suna cikin falo azaune kamar da farko,

Zama Hafsat da yusleem sukayi domin sun iske su ummi sunata jajanta abinda Rahina tayi wadda shi yusleem dinma yajima da mantawa da ita,

Gyaran murya alh sa’eed yayi yafara jawabi,

“Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah, hakika Allah shine abin godiya domin yabawa yarmu lafiya a lokacin da bamu tsanmata ba, agaskiya yusleem kayi namijin kokari sosai wurin jajurcewa har matarka ta samu lafiya, sannan abaya da muka umarceka daka auri yar uwarta bamuyi haka dan fifita wata akan wata ba domin dukkaninsu yayanmu ne, lokacin da tana wannan rashin lafiyar likitoci sun bincika jininta da komai nata ansamu sakamako cewar jininmu ce kamar yadda muka tsanmata domin dama tun asali mahaifiyarsu yan biyu ta haifa amma sai akace daya namijin Allah yayi masa rasuwa aka bamu gawar jariri ashe ba haka bane dayake Allah shine gwanin iya tsara rayuwa sai gashi ya hadamu da yarmu jininmu agidan marayu wanda bamu san waye yakaita canba, koma dai wanene mu yanzu muna cike da farin ciki domin yarmu tadawo garemu kuma tasamu lafiya, Allah yasake hada kanku yabaku zaman lafiya, ke kuma Hafsat kamar yadda kika daukemu a matsayin iyayenki to hakanne mune iyayenki na ainihi….”

Shiru kowa yayi inbanda Hafsat dake hawayen farin ciki,

“Abu yayi kyau Allah yakara tsaremu,Allah yakiyaye gaba, yanzu sai kutashi mutafi”  Mami tafada tana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta,

“Mami kuje kawai ni zamu taho da Hafsat” inji yusleem,

“Haba yusleem kabarta mana zuwa gobe sai arakota”

“Mami gara dai kawai mutafi da ita din”
.
“Tunda yafiso kutafi taren babu komai ai sai tatashi tashirya kutafi” Alh sa’eed yafada yana murmushi,

Tashi Hafsat tayi tashiga daki amal tabi bayanta tana cemata,

“Sister mijin nan naki yanaji dake, yadamu dake wallahi kirikeshi dakyau karki yi wasa…”

Murmushi Hafsat tayi,

“Amal kenan, insha Allah zanyi yanda kikace”

Yan kayayyakinta tadebo tafita amal na biye da ita, sai lokacin tafahimce cewar Khadija bata nan tun lokacin da sukaje police station kila tatafi gida,shidai yusleem duk sai binta da kallo yake yana jin tausayinta yana shigarsa saboda jin wai agidan marayu ta taso,

Sallama sukayiwa su Ummi suka dunguma zuwa gidan Mami, suna shiga part din Mami sukaga ankawatashi da decoration mai kyau banda kayan cima da kayan sha wadanda aka tanada musamman saboda murnar dawowar Hafsat, kowa baki yasaki yana kallo saboda mamaki sam basu san lokacin da yusleem yasa ayi hakanba,

“Yaya kabamu surprise fa…” Khalifa yafada yana daukar wani biscuit zai ci,

Sury dake rungume da Hafsat cikin murmushi tace,

“Nidai yau nafi kowa murna, yar kwanana tadawo…”

Harara yusleem ya wurga mata, aranshi yace “zakiga yar kwana” afili kuwa sai yace,

“Mami walima nashirya mana ta farin cikin dawowar Hafsat”

Cikin fara’a da so mami takarasa tazauna bayan tadauki cake guda daya,

“Allah yasa albarka, gashi muma zamu ci musha ai…”
.
Nan walima tafara gudana su Abdul aka kunna music suka fara cashewa tun yusleem yana musu fada yana cewa shifa ba party yashirya ba walima yashirya har yagaji yahakura daga karshe shima yashiga ya dan taka, Hafsat sai dariya take yimasa,

Dakin sury tashiga tayi wanka bayan surayya tawanke mata gashinta domin tasan yusleem ba barinta taje saloon zaiyi ba,

Tana tsaka da shiryawa Sury nayi mata kwalliya yashigo cikin dakin lokacin karfe  5 saura na yammaci,

“Me kukeyi ne haka? Hafsat fito mutafi”

“Ina?” Ta bukata,

“Part dinmu mana”

Hada ido sukayi itada surayya tacikin mirror sukayi dariya,

“Haba ya yusleem, mubari sai zuwa dare mana”

Murmushi yayi yajuya yafita saboda surayya nawurin,

Kasa suka sauko bayan surayya tagama tsarawa Hafsat kwalliya, yusleem sai binta yake da ido kamar yaune yafara ganinta, wata sabuwar walimar ce tasake tashi domin order din kalolin abinci yasake yi daga wani hotel,

Har dare suna shagali sai wurin karfe 9 saura sannan suka fito domin shiga part dinsu, sury ce tabiyosu,

“Yaya inzo intayata kwana?”

Banza yayi da ita yakama hannun Hafsat tareda karata agefen jikinshi suka nufi part dinsu cikin rada rada yace mata,

“Yarinyar nan sury taraina ni saboda taga yanda na matsu inkebe dake shine wai harda tsokanata”

Murmushi Hafsat tayi tare da sake lafewa ajikinsa…..

      ***

Tana rungume agefen jikinshi har suka karasa part dinsu, budewa yayi suka shiga cikin falon wanda yake ta faman tashin kamshi na turaren wuta da sanyayyan air freshener,lumshe idanuwa kawai Hafsat tayi saboda kamshin yayi masifar ratsata ga wani irin sanyi na musamman da ya gauraye falon, idanuwanta alumshe kafin ta farga sai ji kawai tayi yusleem ya ciccibeta, ahankali yarinka hawa steps din har yasamu ya isa falonsu da ke sama, kai tsaye bedroom dinshi yawuce dasu,

Agefen gadonshi ya ajiyeta ya durkusa agabanta yana kallonta fuskarshi dauke da murmushi wanda idan fassarashi za ayi yanada ma’anoni masu yawan gaske,

Tausassan hannunshi yakai bisa kan nata ya dafe,

“Baby Nanah…”

Kasa amsawa tayi saboda yanda yakira sunan nata yau dabanne da sauran lokutan da yakirata abaya,

“Nanah kinga kaddarar da Allah ya jarrabcemu da ita ko? Amma nasan insha Allah alkhairai ne masu tarin yawa zasu biyo baya ciki harda rayuwa dake da zanyi har abada da kuma yara masu yawa da zaki haifa min…”

Jin abinda yace yasata juyawa dasauri tabashi baya cikeda kunyarshi, tashi yayi yarabu da jikinta ya kwanta abayanta bayan yariko hannayenta,

“Nanah tun dazu tausayinki da tausayin irin rayuwar da kikayi abaya nake tayi, kibani labarin rayuwarki agidan marayu…”
.
Sai lokacin ta iya yin magana bayan tayi nasarar mayarda kwallar data cika idonta,

“Ya yusleem hakika kaima ka cika dan halas domin amal tabani labarin duk dawainiyar da kasha dakuma ALWASHIN da kadauka nazama dani aduk yanayin da nake ciki, insha Allah nima nadaukar maka ALWASHIN cigaba da rayuwa dakai duk rintsi…”

Katseta yayi ta hanyar mirgino da ita jikinshi, akan ruwan cikinshi ya kwantar da ita yana shafa bayanta,

“Zan iya yin komai saboda ke baby, Allah kadai yasan adadin irin son da nake yimiki acikin zuciyata, i love you…”

Tsabar farin cikin jin abinda yace Hafsat hawayene suka fara zarya akan kumatunta, tashi yayi yana rike da ita yarada mata akunnenta,

“Zo muje muyi wanka muzo muyi shirin bacci ko?”

Kai tadaga masa hakan yabashi damar kokarin fara tubeta, rikeshi tayi,

“Ya yusleem towel dinfa?”

Hannu yamika ya dauko yana murmushi,
.
Kinkimarta yayi zuwa cikin bathroom din ya kunna ruwa, wanka sukayi da sabulai masu mutukar dadi da kamshi kun san mutumin naku akwai son kamshi shiyasa tuni ya rikice mata,

Sun dauki lokaci mai tsawo acikin bathroom din sannan suka fito yana goye da ita, abakin gado yadireta yajuya ya dauko mata wasu zafafan turare guda hudu sannan yakoma ya dauko mata sleeping gown light purple mai kamada abin tace koko domin bata kauri sam,

“Ya yusleem wannan rigar…”

Zaman da yayi akusa da itane ya hanata karasawa,

“Ai salla zamuyi mu mika godiyarmu ga Allah da baki lafiya da yayi, amma da bacci zamuyi ma basai kin saka ba”
.
Murmushi tayi takarba cikeda kunya tasaka, shi dinma farar jallabiya yasa bayan yasaka boxer, wurinda yakebe musamman domin yin ibada yajata bayan tasaka katon hijabi nan suka fara sallolin nafila har dare yaraba,

Agogo ya kalla yaga karfe 3 nadare, kallonta yayi ya kama yan yatsun kafarta,

“Nanah tashi muje muyi wata ibadar, wannan ta isa haka..”

Hararar wasa tamishi ta dauke kanta,

“Nifa bacci nakeji kuma nagaji”

“To ai dama gajiyar zan rage miki”

Shiru tayi masa bata kara maganaba nan ya mike tsaye yana rike da ita, kiciniyar cire babban hijabin dake jikinta yashiga yi daga bisani kuma yadireta akan gado,

“Yaya yusleem Allah bacci nakeji”

“Nima haka” yace da ita yana mai lalubar dukkan sassan jikinta, ayanda taga take takenshi yau kam bai hakura har sai ya amsa sunansa na cikakken ango,

Duk da irin lallabatan da yayi da kuma tausayinta da yakeji hakan bai hanata shiga mawuyacin hali ba, zufa ce tarinka karyo mata duk da sanyin air condition din dake ratsa dakin,
.
Lokacin da aka fara kiraye kirayen sallar asubah lokacin hankalin yusleem yadawo jikinsa, wata runguma mai tsauri yayi mata yana share kwallar dake fita daga idanuwansa wanda shi kansa bai san ko ta menene ba, ita kam Hafsat tuni bacci yayi gaba da ita saboda tarin gajiyar dake tattare da ita.

Tunda tafara bacci bata ko motsa ba sai da karfe 7 tayi, tana kokarin tashi daga kan gadon yusleem yashigo cikin dakin, wani kyau na musamman taga yayi domin ya gyara fuskarshi sosai sannan wani sheki fuskar tashi keyi, yana sanye da farar t shirt mai gajeren hannu da blue din jeans, ganinshi yasata komawa ta kwanta, cikin sauri yakarasa gareta,

“Ayya amaryar daren jiya, sorry, tashi ahankali muje kiyi wanka kizo kiyi ramuwar sallar safe” yakarashe maganar cikin tsokana,

Shiru tayi masa tasoma kokarin tashi,

“Kabani towel to”

Yana guntse dariyar da ta taho masa yamiko mata, kallonshi tayi ganin yanda yaketa kawar da fuska alamun son yin dariya,

“Wai menene? Ai Kaine abin dariya baniba ya yusleem”

Sai lokacin yasamu damar yin dariyar,

“Nifa ba dake nakeba”
.
Shiru tayi tasauka tanufi toilet tana takawa sannu sannu,

“Inzo…?” Yace da ita yana murmushi,

“A’a” tafada tana turo baki, bedsheet din gadon ya cire da zummar yabar na kasan domin guda biyu yashimfida amma duk guda biyun sunyi staining nan yaciresu gaba daya,

Yana kokarin shiga toilet din tabude tafito, ganinshi rikeda zannuwan gado yasata dauke kai tayi gaba shikuma yashiga ciki, dakanshi yawanke wurin da ya baci din sannan yafito dasu da niyyar yaje yasasu acikin washing machine,

Dakin yadawo lokacin ta idar da salla tana goge kanta da towel,

“Ina kwana?” Tafada batareda ta kalleshi ba,

Zuwa yayi ya durkusa agabanta,

“Lafiya lau baby, ya wankan safe?”
.
Rabuwa tayi dashi taci gaba da abinda takeyi shikuma sai faman murmushi yake bakinsa yaki rufuwa ya gonar auduga,

“Inata magana kin rabu dani…” Yafada cikeda tsokana,

“Nifa bacci nakeji gaskiya”

Jin abinda tace yasashi sunkutarta zuwa kan bed ya kwantar da ita yana cewa,

“Kibari mana kisha tea, naga kamar harda yunwa bayan baccin ko?”

Daga mishi kai tayi nan yasauka yafita zuwa kitchen, mintuna kadan yahado mata tea mai kauri da wainar kwai yakawo mata lokacin har baccin yafara daukarta sama sama,

Tashinta yayi yabata tasha tea din sannan takoma ta kwanta, gefenta ya raba ya kwanta shima bayan ya rungumeta,

“Kaifa bazaka sha tea dinba?” Ta bukata idanuwanta arufe,

“Ni na koshi, abu daya kawai nake bukata..”

Bata sake bi takansa ba tayi baccinta, shima ganin haka yasashi yin baccin bawai dan yasoba.

Wuni sukayi suna barci sukuwa su Mami basu nemesu ba,

Karfe 1 saura suka tashi, wanka suka yi suka fesa kwalliya, ita wata maroon din atamfa tasa dinkin doguwar riga shikuma yasha kananan kaya sai kamshi suke,

Part din Mami suka nufa bayan sunyi salla, suna tafe yana rikeda ita suna yar hirarsu har suka shiga, su mamin dukkaninsu suna zaune suna kokarin yin launch,
.
Zama sukayi suma akayi dasu bayan sun gama suka koma part dinsu, Hafsat ce tace masa yakamata suje su sake gano jikin Hafsat mori, baiyi musu ba yayarda suka dauki surayya suka tafi, saida suka fara biyawa ta kings center suka yimata siyayyar kayan dubiya sannan sukaje asibitin,

Tana zaune akan gado tana waya da barrister aiman bayan fitar mahaifiyarta hajiya, ganinsu yasa tafadada murmushinta ta ajiye wayar tana yimusu sannu da zuwa,

Cikeda sakin fuska dukkaninsu suka gaisa da juna suka dubata, sun kai kimanin mintuna 30 sannan suka tafi bayan sun ajiye mata kayan dubiyar da suka Kawo mata,

Gidan Ummi suka wuce daga asibitin domin gaidasu, lokacin da sukaje sun tarar da ummin itada amal suna aiki a kitchen nan Ummi tashiga yiwa yusleem fada tana cewa daga tafiyarsu jiya shine zai biye Hafsat sudawo yau,

Har magrib suna gidan saida sukayi salla sannan suka tafi gida, a part din Mami suka yada zango suka bude babin hira har karfe 9 nadare sai lokacin suka koma part dinsu.

  Yana zaune agefen gadon dake cikin bedroom dinta tafito daga wanka tana daure da towel saida gabanta yafadi lokacin data ganshi,

Tagefen ido yarinka kallonta yana murmushi har ta kammala shiryawa, jawota yayi yadora akan cinyarshi,

“Zo kigani..”

“Nifa gaskiya…..”

“Kefa gaskiya me?”

Shiru tayi masa tana tutturo baki, daukarta yayi daga ita sai towel din yakaita dakinshi, wasu akwatuna guda biyu shake da kananan kaya da kayan bacci tagani sai sauran kayan shan iska nan tazauna tarinka duba kayan tana yaba kyansu duk da cewar bamasu nauyi bane,

“Haka nake son kullum kirinka saka min su ina hango kayana daga nesa,shiyasa nakawo miki tsarabarsu daga chairo”

Kunya taji maganarshi tabata dan haka tarufe fuskarta,

Da wayo da wayo yasamu ya lallabata har yakai ga cimma muradinshi.

   Kullum sai sunje sun dubo Hafsat a asibiti sannan koda yaushe Hafsat da Hafsat mori take yin girki idan zasuje sai su tafi mata dashi dahaka har tafara samun sauki domin karayar dake hannunta ma tawarke,
.
Ranar alhamis aka sallameta daga asibitin takoma gida,washe gari ranar juma’a da daddare Hafsat tayiwa yusleem wanka,

Sabbin kaya tasaka masa milk colour din shadda mai tsadar gaske inbanda kyalli babu abinda takeyi tafesheshi da turaren silver man sannan tashafa masa farar powder tasa masa lipstick abakinshi bayan tagyara masa girarshi da brush,shidai kallonta yakeyi har tagama,

“Ina zamuje ne?” Ya bukata,

“Zance zakaje wurin Hafsat…”

Murmushi yayi domin bai ganeba,

“Zance kuma?”

“Kwarai kuwa, ya yusleem nasan Hafsat har yanzu tana sonka sannan kuma kasan tayi mana halacci, ni wallahi nayarda kaje ka nemi aurenta kakawota ka hadamu nida ita mu zauna akarkashin inuwarka”

Kallonta yayi cikeda mamaki zaiyi magana tahana taja hannunshi suka fito,

“Idan har kana sona karka yimin gardama kaje kawai”

Baiyi magana ba har tasashi acikin mota, tana ganin fitarsa tashige part din Mami domin bata son tazauna ita kadai shaidan yasamu damar ribatarta,koda taje bata fadawa su mami inda yatafi ba kawai cemusu tayi yaje unguwa.

Har yusleem yaje gidan alh Musa mori zuciyarsa bata gushe daga mamakin matarsa Hafsat ba, wani sabon sonta yakeji yana shigarsa domin yagane bata da mugunta da hassada saboda yanzu ba kowacce macece zata iya yin abinda tayiba, sam kishi bai rufe mata ido yasata manta alkhairin Hafsat mori agareta ba,
.
A parking space yayi parking yatura daya daga cikin ma’aikatan gidan yakirata, mintuna goma zuwa 12 sai gata sanye da bakar doguwar riga kamar koda yaushe kamshi na faman tashi daga gareta,

Kallon kallon suka shigayi shida ita daga karshe yasaki dan murmushi yace,

“Wannan kallon fa kamar yau kika fara ganina”

Itama murmushin tayi tace,

“To kila hakanne, lafiya naganka da wannan daren?”

“Nazo zance ne wajenki”

Murmushi tayi, “Ko?”

“Kwarai kuwa”
.
Shiru tadanyi shima yayi shirun zuwa can yace,

“Hafsat nasan abaya nayi miki wasu abubuwa wadanda basu daceba amma ina mai neman yafiyarki sannan ayanzu nashirya aurenki mutukar kin amince”

Murmushi hafsat tayi sannan ta kura masa idanu na tsawon wasu mintuna Wanda har saida shi kansa yaji ya tsargu da kallon,

“Yusleem kenan ai kuma ka makaro domin wani yarigaka,duk da nasan ba yin kanka bane tunda ada baka kaunata”

“Hafsat ai da kikace, ayanzu kinyi min abinda dole zuciyata ta amshi sonki”

Girgiza masa kai tayi,

“Nagode kuma naji dadi amma kayi hakuri bazan iya auranka ba domin nasamu miji daidai dani”

Zai sake magana ta katseshi,
.
“Nabarka lafiya agaida madam sannan gobe za afara zaman kotu domin saurarar kararku wadda nashigar akan tsohuwar matarka rahina, idan kasamu time zuwanka Nada mutukar amfani”

Tana gama fadin haka tayi gaba tabarshi awurin, ganin tashige cikin gida tabarshi yasashi shiga motarsa yakoma gida,

Bai samu Hafsat a part din mamiba dan haka yawuce part dinsu, acan ya isketa ta caba kwalliya tanata zuba kamshi tazauna zaman jiranshi,

Lokacin da taganshi da fara’a tatashi ta taryeshi tashiga jikinshi ya rungumeta,

“Sannu da zuwa, ka barota lafiya?”

“Lafiya lau baby, tana gaidaki”

“Ina amsawa, ina fata dai kayi nasarar sace zuciyarta da dadadan kalamanka”

Kai yagirgiza alamun a’a nan ta langabar dakai alamun neman karin bayani,bai boye mata komaiba domin Hafsat takasance wani sirri na rayuwarshi kuma ma ayanda ta nuna mishi to bazai iya boye mata komai ba saboda irinsune matan da miji baya iya boye musu sirrinshi, hannunshi takama,
.
“Ya yusleem wallahi banji dadiba ko kadan amma Allah yasa hakan shi yafi alkhairi”

“Amin” yafada yana jan hancinta.

Washe gari sun sami halattar kotun inda aranar aka gama shari’a aka yankewa Rahina hukunci daidai da laifinta,kwatanta irin godiyar da Hafsat tayiwa Hafsat mori abin ba acewa, tuni suka kulla zumunci mai karfi, haka itama Khadija har yanzu tana ziyartar Hafsat akai akai amma ba kamar da ba.

  Soyayya mai wuyar fassarawa yusleem ke nunawa Hafsat wannan dalilinne yasa daga shi har ita suka manta da kowa sai junansu, ita Hafsat yanzu dadin da take ciki yasa tadade da manta wuyar da suka sha abaya sai yanzu tayarda da cewar komai lokacine gashi yanzu tana zaune cikin kwanciyar hankali da jin dadi,

Umarah yusleem yabiya musu shida ita suka tafi tacan suka wuce birnin london domin yawon bude idanu, watansu daya suka dawo, batare da tasaniba ya nemar mata admission a university nan yafara koya mata mota cikin lokaci kankani ta kware dan haka ya tura aka Kawo mata lafiyayyar mota mai numfashi yar yayi ta zamani,

Babu bata lokaci tasoma halattar makaranta inda zata karanci micro biology, kullum tare suke fita da yusleem dasafe tayi driving dinsu zuwa school dinsu idan sunje sai tafito tabashi motar daga nan yawuce office idan tatashi yazo ya dauketa,
.
Tsakiyar semester dinsu tafara wani bacci mai kashe jiki ga yawan cin abinci da takeyi hakan itada yusleem yabasu damar fahimtar cewar lallai sun samu karuwa, murna dukkaninsu suka shiga nunawa junansu bama yakamar yusleem wanda ya dauki son duniya da tattalinsa ya dora akan ta itada abinda ke cikinta,koda yaushe cikin bata kulawa yake hatta girki shine yake yimata.

Cikinta yanada wata biyar lokacin har ya bayyana suka fara shirye shiryen bikinsu surayya dasu Abdul, khalifa zai auri amal kanwar Hafsat shikuma Abdul zai auri Mimi kawar sury ita kuma surayya zata auri Dr faruk kwararren likitan kwakwalwa, Hafsat ita tayi ruwa da tsaki har aka kammala biki aka kai amare gidajensu,

Agajiye tazauna abakin gado tana nishi saboda gajiyar dake tattare da ita ga kuma ciki, ahankali yusleem wanda ke kwance yatashi zaune ya fara yimata tausa yana danna mata kafafunta,

“Ya yusleem yakamata gobe mukaiwa barrister Hafsat mori da mijinta barrister aiman ziyara kaga mun kwana biyu bamu haduba”

“Duk yadda kikace hakan za ayi gimbiyata”

Murmushi tayi taja karan hancinshi, shima murmushin yayi ya yi mata masauki ajikinshi cikeda so da kauna.

    Alhamdulillah

.
Godiya ga Allah subhanahu wata’ala da yanuna min karshen wannan littafi lafiya, ina addu’ar Allah ya yafe mana kura kuren dake ciki ya taramu acikin ladan gaba daya Allahumma amin. Godiya marar adadi ga dunbin masoyana masu bibiyar labarina akoda yaushe, hakika banda kamarku kuma akoda yaushe da bazarku nake rawa, duk wata masoyiyar ummi A’isha wacce take jinta aranta ko nasanta ko ban santaba to tasa aranta nima ina kaunarta, Yabo da jinjina ga yan kungiyar Haske writers Asso, tabbas kudin nadabanne agareni ina addu’ar Allah yakara hada kanmu yakara mana dunbin basira da fasaha,Masu karatu sai mun hadu acikin labari nagaba idan Allah ya nufa.

.

Post a Comment for "ALWASHI COMPLETE "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...