ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 9 by Sumayyah Abdul-kadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 9  by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 9 by Sumayyah Abdul-kadir

- - Post a Comment

 ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 9

by Sumayyah Abdul-kadir


Na ce, “Kin bata wayonki Ummi, wallahi kika aure shi za ki kwashi kashinki a hannu. Na rantse mai hali.......” 


“Baya fasa halinsa fa Fa’izah!” 


Ta karasa tana min dariyar tura haushi. Ta kuwa tura din. Ta ci gaba da cewa, “A ganina wannan ba damuwar ki ba ce tunda dai ba ke za ki zauna min dashi ba, bai shafe ki ba kowacce irin rayuwa zamu yi ni da Ya Fa’iz, tunda abin sa-kai-ne. Ina SON SHI HAKA! 


Shine kadai ya tara dukkan abubuwan da nake so ga Da namiji, har ma ya zarta. Kafin a samu namijin da ya tara sura da ‘attributes’ din duk da ‘ya mace ke so irin Fa’iz za a jima Fa’izah. Don haka Fa’izah a yau ina mai farin cikin shaida miki cewa, ina son FA’IZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA!” 


Sai na ce, “Allah ya ganar dake Ummi. Kin riga kin yi nisa ba za ki ji kiran ba. Allah ya shirye ki, ya ganar 


i O < 

dake makiyinka baya taba rikidewa ya dawo masoyinka, ‘no matter what... sai in ya ga kiyayyar tasa ba mai ci ba 


“wai ke sai kira kike FA’IZ MAKIYI To makiyin wa? Ke ko mu? A lokuta da dama Yaya Aliyu kan ce bakya magana sai mai ma’ana da hikima a ciki, amma ga shi ni yanzu duk kin cika ni da rubbish (shirme). Wallahi duk kin isheni da surutu mara ma’ana. To wannan shirmen da kike shi zai sanya in tsani Fa’izun nima?” 


Ta yi dariya ta shiga tattare kayan ta cikin ledar da aka kawo su. Tabbas da da ne ba yanzu ba da GIRMA da HANKALI suka zo ba, babu abin da zai hanani rufe Ummi da dan iskan duka, yakushi da cizo irin wanda muka saba da zarar mun samu sabanin ra’ayi ko don in huce bakin ciki da takaicin da ta kunsa mini, amma ina! Girma ya zo!! In ma mun yi ba zai mana kyau ba!!! 


Sai na kyale ta na kwanta a gado na kama kuka mara sauti. Ni babban 


I Oo < 

bakin cikina da muka yi a gaban su Haulatu muka farke sirrin gidanmu a gabansu, shin da me za su fassaramu ba dabbobi ba? 


Wasikar da Fa’iz ya aiko abin da ya rubuta a ciki kawai “Ga Hankicina ki bawa Fa’izah, sauran kayan naku ne ke da Zanirah”. 


Wannan wasika ta bai wa su Ummi da su Naja dariya. Wato su tsaraba wadda za ta amfane su, Fa’izah da ba a so ‘HANKICI! Suka kyalkyale da dariya. 


Haule ta ce, “Kai zan so in ga Fa’iz dinnanface to face, am sure he will be vey funny”. 


Ummi ta harareta ta ce, “Me kika ce? Ki ganshi ki yi mai uwar me?” 


Suka kara kyalkyalewa da dariya. Naja ta ce, “Sorry Khadijan Fa’iz, ai mu Fa’iz ya wuce da ajinmu ba cewa zamu yi muna so ba. Wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa!” 


i O < 

SRR AK 


Tun daga ranar na fita harkar Ummi, na ma tattara kayana na koma hostel din su Naja da muka fi dasawa. Ummi ba ta gaya min Fa’iz ya ba ta hankici ta bani ba, kawai na _ tsinci kyakkyawan farin hankici cikin kayana mai dauke da _ kalmomin Larabci guda (7) ‘AHUBBIK’. 


Na kai hankicin karan hancina na sunsuna, sassanyan kamshin turare dan gidan (Philips Lumea) da hakincin ke yi ya haifar da wani takaitaccen nishadi a zuciyata, ya gusar da duk wani bacin rai na Ummi da nake fama da shi a cikin ranakun da bama ga maciji. Haka nan Allah ya sanya mani kaunar dan kyakkyawan hankicin a raina. 


Sai dai kamshin Philips Lumea da hankicin ke yi na kan so in san inda na san shi amma Allah bai bani ikon tunawa ba. Na tura shi cikin jakar littattafaina ko cigiya ban yi ba. A raina na ce “Ina zaune ai ya zo ya 


(i O < 

tadda ni. In mai shi ta yi cigiya na ba ta”. 


Kullum bana iya barci ba tare da na shaki kamshin daddadan hankicin nan ba, haka in na fito aji ana rana, na kan rufa shi ne a fuskata zuwa hostel, bana ko tsoron mai shi ta gani. Kuma abin mamaki har kwanaki suka ja, aka debi wata kamshin da hankicin nan ke yi bai gushe ba. 


Wannan ya tabbatar min da ba karamin turare ne a jikinsa ba. Duk sanda zan wanke uniform sai na wanke shi, amma babu abin da ya ragu na daga kamshinsa kullum kamar ina kara fesa masa turare dan gidan (Philips Lumea) ne. 


A karshen watan Yaya Hauwa ta zo ganinmu, ta bani letter daga Yaya Aliyu, kuma wai lallai-lallai in rubuta amsa in ba ta a take. Don a satin ya zo gidanta ya fi a kirga yana tambayar amsar wasikar tana cewa ba ta zo ba, yana ta yi mata mita. 


Na yi dariya na ce, “Yaya Hauwa 


Wl O < 

tadda ni. In mai shi ta yi cigiya na ba ta”. 


Kullum bana iya barci ba tare da na shaki kamshin daddadan hankicin nan ba, haka in na fito aji ana rana, na kan rufa shi ne a fuskata zuwa hostel, bana ko tsoron mai shi ta gani. Kuma abin mamaki har kwanaki suka ja, aka debi wata kamshin da hankicin nan ke yi bai gushe ba. 


Wannan ya tabbatar min da ba karamin turare ne a jikinsa ba. Duk sanda zan wanke uniform sai na wanke shi, amma babu abin da ya ragu na daga kamshinsa kullum kamar ina kara fesa masa turare dan gidan (Philips Lumea) ne. 


A karshen watan Yaya Hauwa ta zo ganinmu, ta bani letter daga Yaya Aliyu, kuma wai lallai-lallai in rubuta amsa in ba ta a take. Don a satin ya zo gidanta ya fi a kirga yana tambayar amsar wasikar tana cewa ba ta zo ba, yana ta yi mata mita. 


Na yi dariya na ce, “Yaya Hauwa 


Wl O < 

kyale Yaya Aliyu kawai, rigimar shi yawa gare ta. Yanzu haka duk zancen in bar rubutu in yi karatu ne bai san tuntuni na ajiye shi a gefe ba”. 


Ta ce, “Ah toh! Sako-makoko na dai isar don haka ragowar can ta matse muku kun fi kusa, wai harshe da hakori. Ban tambaye ki me ke cikin wasikarku ba”. Na rufe fuska da tafukana ina dariya cike da jin kunya. 


Ban bude wasikar Yaya Aliyu ba sai a washegarin talata da daddare bayan na gama komi da ya zamo min al’ada kafin kwanciyar barci. Na_ saka (nighties) na saki net (gidan sauro) na shige ciki. Sannan na bude wasikar Aliyu; 


“A gida, Giwa


Fa’izah, ko kin san mene ne abin da na dade ina cewa ba ki yi girman da za ki fahimta ba? To ba wani abu bane strange. Abu ne da ya zamo (known) ga kowa a Giwa, Zaria, Kano da Kaduna. Idan har zuwa yanzu shekaru 


i O < 

goma sha bakwai baki yi kwakwalwar da za ki fahimtar ba sai in ce zan yi A BARI YA HUCE..... 


Yayan is in love! Fa’izah Aliyu is in love!! Please save a soul..... ki taimaki “tuzurun” yayan ki ki zama zabin Hajjah gare shi nan da watanni uku wato bayan kammala jarrabawarku ta karshe. Hajjah ta yi rantsuwa nan da watanni uku ko na shirya ko ban shirya ba za a daura min aure, ta gaji da karatun da ba shi da karshe. Don haka ne na ga tunda wuri gara mu fito fili mu bayyana kanmu maimakon hannunka mai sanda. Babu zancen fahimtar juna sai cika burin zuciyoyin da suka dade suna ragaita. 


-Aliyu-Na’ibi. 


Wata irin murna marar misali na shiga yi tare da dariya-dariya da ni kaina ban san irinta ba. Abin da kunnuwana suka dade suna jiran ji daga bakin Yaya Aliyu. Gaskiyar Mama Asma’u ne da ta ce, “Sannu


Wl O < 

sannu ba ta hana zuwa, sai dai a dade ba a je ba”. 


Sai na kwanta a rigingine zuciyata da ruhi cike taf da begen AliyuHaidar. Kwakwalwata ta _ shiga wassafo min irin kyakkyawar rayuwar da zamu shimfida ni da Yayana Aliyu, irin kyawawan yaran da zamu haifa kasancewar Aliyu fari tas Fa’izah choculate colour. Na tabbata za suyi kyau, kyau mai suna kyau da babu irinsa cikin zuri’ar Abubakar Bamalli Giwa. 


Watanni uku kenan da kammala masters din Yaya Aliyu a jami’ar Legas a kan (Agricultural Engineering), cikin lokacin kuma ya samu aiki da ma’aikatar gonaki ta kasa. Sun aje shi reshen jihar Legas matsayin mataimakin M.D. Gida cikin lekki da motar shiga ta zamani da matasa masu matakin rayuwa dai-dai da tashi suke hawa. 


Il O < 

RK 


Shin wace irin amsa zan rubutawa Yaya Aliyu ne? Wallahi ban sani ba. Na shafa ko ina ban ji amsar da ta dace cikin kwakwalwata ba saboda kunya. Kuma wadda zan saka ta yi min gayyar ta watse (Khadija-Ummi) anyi ta ba dadi. Ina kuma ganin faduwa ce babba gareni in je ni neman sulhu. Sai dai in mu koma gida a haka amma ba zan ba da kaina ba ta kara kular dani a banza, don da alama babu sauran mutunci cikin al’amarinta in dai a kan wannan dan’uwan nata ne Musa a fuska, Fir’auna a zuci. 


A kullum sai na karanta wasikar Yaya Aliyu a kalla sau cikin carbi. Aike na duniya Yayan ya yi in ba da amsa na ki, don tsakanina da Allah da gasken ban san me zan rubuta mishi ba. Don haka ne wat na bari ayi hutu tunda ya matso in yaso sai mu rubuta ni da Zanirah. 


Yau saura sati biyu hutu Yaya 


(tt! O < 

Hauwa ta shigo makarantar wajen kawayenta) malaman makarantar. Bayan ta gama abin da ya kawo fa, ta yi kirana staff office ta ce, “Fa’izah na gaji! Zaryar Aliyu gidana ta ishe ni, wai amsar me za ki ba shi ne? Ki yiwa Allah ki bani takardar nan in ba shi in huta ya sarara mini”. 


Na ce, “Yaya Hawwa ki kyale Yaya Aliyu don Allah sai mun zo gida. Saura kwana goma sha hudu ya rage”. 


Ta ce, “Ai shi kenan, ni tausayin shi nake ji wallahi. Ya damu fiye da zaton ki, wayar safe daban ta dare daban, ga ayyuka masu tsauri a_ gabanshi. Yarinya karama sai tamaula kike da ‘yan maza, ki ji tsoron gamuwarki da Allah Fa’izah ki tausayawa Da na”. 


Na kyalkyale da dartya na ce, “Yaya ni ba ‘yarki ba ce sai Yaya Aliyu kadai?” Ta ce, “A’a, ni na fara cewa haka? Duka daya kuke”. 


A ranar ne kuma_ hukumar makaranta ta sanar cewa, babu ‘yan set dinmu a masu zuwa hutu saboda 


MI O < 

karatun bita na jarrabawar karshe. Sai dai wadanda ke cikin Kaduna ne kawai za su fita su dawo sati daya jal. 


Muka debi kayan sawa uku cikin jaka muka yi gidan Yaya Hauwa. Tsakanina da Ummisai _harara. Kwanana daya gidan yaya Hauwa gidansu Ummi kenan, duk na kasa sakewa sakamakon rashin sabo da gabar da muka tsira a junanmu. 


Sai dai duk iyaka kokarina na yi Yaya Hauwa ba ta gane ba, don ko da Za ta ji din na tabbata ni za a daurawa rashin gaskiya duk da nice mai gaskiyar, da rashin dadin zuciya ya isheni na dau wanka na sha atamfa super da mayafi, na yiwa Yaya Hauwa sallama da niyyar za ni gidan Baban Kaduna Jabi Road. 


Ta ce, “To dai kada ki sake ki je Giwa, kin san dai dokar makarantar nan, iyakacinku cikin gari. Ga ummi ta shiga wanka ki tsaya ta fito ku tafi tare mana”. 


i O < 

Na ce, “Ai kwana zan yi, kin san kuma Ummi ba za ta yarda ta kwana gidan Baban Kaduna ba_ saboda abokin fadanta (Junior)”. 


Ta yi dariya ta ce, “Yiwa Idi direba magana ya kai ki yana nan cikin lambu wajen tsintsaye yana basu abinci’”. 


Shigarmu harabar gidan ke da wuya idona ya kyallo mani motar Yaya Aliyu fake a harabar adana motoci. Gabana ya fadi, tabbas na yiwa Yaya Aliyu laifi babba kuwa, na yiwa Aliyu Haidar babban laifin da ban san (punishment) din da zan fuskanta ba, bani kuma da uzuri ko hujjar kare kaina. 


Na gyara murya zan ce da Malam Idi mu koma na hango fitowarsu shi da Baban Kaduna yana rike da brief case din shi. Dole na fito, duk gwiwoyina sunyi sanyi kalau. 


A dai-dai motocin Baba dake jere a cikin rumfar adana motoci na tsugunna har kasa na gaida Baba. 


III O < 

Kallon da Yaya Aliyu ke min a yau ya kara sanya min mutuwar jiki da sanyin gwiwa har muryata karkarwa take ina gai da Baban. 


Ya ce, “Faduwa ta zo daidai da zama, yanzu Mamanku ke cikiyarku game da shirin da za ku soma na bikin da za ku sha nan da watanni uku. Ina kika baro Ummin?” 


Na ce, “Ummi na gidan Yaya Hauwa. Biki kuma Baba? Na wa?” 


Ya yi dariya ya ce, “Na Hassanar ku”. 


Ido warwaje na ce, “Zanirah?” 


Dariya ya yi, “It sounds like a film ko (kamar a shirin fim), to ya za a yl? Hajjah ta tada hankalinta aure za ta yiwa Zanirah, kinga kuwa babu mai ta cewa. Ko akwai?” 


Da sauri na shiga girgiza kai, na ce, “Babu kam, babu Baba”. Na mike da sassarfa zan shige Baba ya ce, “Baki ga Yayanki bane babu gaisuwa?” 


Yaya Aliyu ya ce, “Kyale ta Baba ai ta je kwaleji ta waye ne, kada ki sake 


MI O < 

ki bar gidan nan sai mun dawo Giwa yanzun nan”. 


A hankali na cira kai na dubi Yaya Aliyu, sanye yake da shadda (Hilton) ruwan toka mai gautsi. Sai sheki take cikin hantsin na safiyar Asabar. Ya rame sosai ya dan yi duhu, in ban yi kuskure ba sai in ce ko (ulcer) ce ta tashi ta kwantar da shi muna makaranta. Dara-daran idanunshi sun fada sun yi ciki sun yi ja ainun. Muka yiwa juna wani irin kallo na sakan biyu a hankali na ce, “Ina yini?” 


Ban damu da ya amsa ko bai amsa ba na wuce da sauri, har ina tuntube da kofar shigewar. 


Gaba daya yara suka diba ga Fa’iza, ga Yaya Fa’izah. Daya bayan daya nake daga su tika-tika dasu ina direwa. Na tambayi Junior Mama ita da waye? Ya ce ita da Yaya Zanirah ne sun zo su tare da Yaya Aliyu tana ta kuka wai za a yi mata aure. 


Na yi sallama a falon, Mama ce ta amsa. Zanirah na hango ta hade kai da 


III O < 

gwiwa can a kusurwar falon tana rusar kuka. Na ce, “Wai Mama da gaske?” 


Ta ce, “Ni gara da kika zo, na kasa ma Zanirah, ni yanzu da ta zo ta sani a gaba tana rusa min kuka me zan yi a kai don Allah? Sanin kanku ne in Hajjah ta yi hukunci Babanninku basa musu. Wannan kukan duk aikin banza ne Zanirah kike yi ba zai sa ba, ba kuma zai hana ba”. 


Cikin kuka Zanirah ta ce, “To waye Mama? Waye mijin? An ce wa Hajjah yanzu ma irin zamaninku ne da ake irin wannan auren a kwashe lafiya? Ni ba aure nake ki ba, karewa ma ina da wanda nake so. Ta yi hakuri mana mu kammala makaranta zan kawo mata mijin’”. 


Ni sai Zanirah ma ta bani dariya, don ni dai tun tasowar mu ban santa da wani saurayi ba. Na samu wuri gefen Mama na zauna na ce, “Wallahi Mama ni dama na san dole ne tsayin Zanirah ya dami Hajjah, duba ki ga 


III O < 

duk ta fimu cika ido ga tsayi, Hajjah na yawan cewa “doguwa hankalinki a gwiwa, ni kar ki fado min a ka”. 


Mama ta yi dariya Zanirah ta zabga min harara. Mama ta ce, “Daman Zanirah ai ta girmeku, shekaru biyu ta baki kwarara, ke kuma kika bawa Ummi watanni biyar. Ni kam ban ga laifin Hajjah ba don an yiwa Zanirah aure yanzu, shekarunta goma sha tara ris, sai dai tunanin wanda ta baiwa auren. 


Na yi iyaka tunanina amma hankalina bai bani ba. Baban ku ma ya yi tambayar duniyar nan amma ta kafe sai ana saura kwana uku daurin auren sannan kowa zai ji’. 


Na ce, “Kai wannan tsohuwa da rigima take, ke Zanirah to mene ne abin kuka? Muma muna tafe, kin sani dai ko ba yanzu ba mawuyaci ne Hajjah ta kyale ki zuwa jami’a da shekaru kusa da ashirin, kai Hajjah ta yi dai-dai....” 


I) O < 


Post a Comment for "ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 9 by Sumayyah Abdul-kadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...