ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 9 by Sumayyah Abdul-kadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 9  by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 9 by Sumayyah Abdul-kadir

- - Post a Comment

 ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 9

by Sumayyah Abdul-kadirwani abu guda daya, taura biyu ba ta tauno, tunda karatu kika zo yi ba rubutu ba ki mai da hankali ki yi karatun nan. In kin kammala kin san dai hajjah ba barinku zuwa jami’a za ta yi ba AURE za ta yi muku. Sai ki yi ta rubutun da za ki yi a gidan aurenki, ni kuma na dauki nauyin wallafawa”’. 


Na ce, “Yaya Aliyu na san wannan, amma komai da lokacin da na ware mishi cikin al’amuran rayuwata. Wallahi bana rubutun da malami cikin ajinmu, ko ana karatu sai a karshen sati (week end) da (prefs), a sa ilin da bani da ‘test’ ko ‘exams’ a kusa. Wato lokacin da ya kasance farko-farkon ‘term’. Inda bana karatu da ban kawo maka positions masu kyau ba ai”. 


Ya ce, “Shi kenan Fa’izah, ai ko lauya nan ya ganki ya barki wurin dadin baki da kawo hujja da_ persuation.Allah ya taimaka. All the best my sister. Cross word!” 


2K OK OK ok 


A shekarar aka nada wakilan malamai 

bayan tafiyar “yan aji shida, na yi mamaki matuka da aka kira ni Fa’izah Ahmad Bamalli Giwa a matsayin AMIRA! Aka kuma nada Ummi Gate Prefect. A hostel su Naja’atu Room-mates din mu ke yiwa Ummi dariya, domin ita Naja ta amshi dankwalin Head-Girl ne, ya yin da Haulatu Sani ta karbi Labour Prefect.. 


Ummi ta ce, “Aikin kawai, a rasa dankwalin da za a baiwa mutum sai na bakin kofa? Wani ya ce ina son mukami da za a hadani da gate?” 


Muka tuntsire mata da dariya. Haulatu ta ce, “Khadija Sabi’u ke ce baki sani ba, cika idonki ya sanya (Vice-Principal) baki wannan dankwalin, don kin san an ce alamar karfi na ga mai kiba, ta san za ki yi fada (Ummi na da jiki sosail) ga masu yin latti da ‘yan komawa hostel during school hours.Zaki cikawa dalibai masu latti ido da kwarjini. Yawancin mata masu jiki fada 


gare su’. Ummi ta yi tsaki ta ce, “A kan me za a 


bawa Fa’iza Ameerah? Wa ta fi tsoron Allah? Yarinya mai shegiyar tsiwar tsiya”’, 

Naja ta ce, “Ai kuwa Fa’izah ta cancanci dankwalinta. Dalili; 


-Duk da ta fimu nutsuwa da kula da addini. 


-Zuwa jam’i a kan lokaci. 


-Tun zuwanta Sarauniya Amina kullum sai ta share masallaci. 


-Ita take riga kowa zuwa masallaci da asubah. 


-Ta fi kowa iya Larabci, ta fi kowa iya karatun Alkur’ani, ta fi kowa iya kira’a da Tajweed. In ba a baiwa Fa’iza Ahmad “Amira” a makarantar nan ba ki gaya min wa Za a bawa?”’ 


Bakin Ummi ya mutu. Naja’atu ta ci gaba da cewa. 


“Duk fadin Sarauniya Amina babu mai tsantseni da addini irin Fa’izah”. 


Ummi ta ce, “Tana takurawa kanta ne kawai. Duk sanyi ba ta jin sa sai ta je masallaci da asuba. Da rana baka huta ba, da yamma baka huta ba haka dare. Ai ba zuwa masallaci yin sallah ne ke sanyawa Allah ya karbi sallarka ba”. 

Haulatu ta ce, “Kin yi kuskure Khadija, duk taku daya zuwa masallaci lada ne da babu wanda ya san adadinsa sai sarkin sarakunan dake ba da shi. Sannan sallar jam’i ladanta ya ninka ta mutum daya, ko taka ba ta yi kyau ba Ubangiji zai duba ta na kusa da kai ya baka ladan, ai ba ma za a kwatanta ba. Kiwa ce _ kawai_ take damunmu Allah ya yaye mana”. 


Ni dai ban tanka musu ba har suka gaji suka watse. 


Washe gari Yaya Hauwa ta zo har ajinmu ta shigo da kaya a leda da wasika, ta ce, ‘In bai wa Ummi daga Fa’iz, jiya su Hajjah suka dawo Ukrain, sauran kayan bai yiwuwa a kawo su makaranta, in mun koma gida ta gan’. 


Na ce, “Ayya! Yaya Hauwa da kin mika mata ajinsu don ni za ta bari da daukar kayan zuwa hostel”. 


Yaya Hauwa ta yi dariya ta ce, “Ahaf! Na manta fa kayan da suka fito hannun Fa’izAbubakar ne, abokin fadan Fa’izah. Ya 


kamata ki yafi dan ‘uwanki haka girma ya hau ku ku manta kuruciyar baya, haka nan 

‘yan’uwa kuke”’. 


Na yi dariyar yake kawai. A raina na ce, ‘“Meye zai kankare kiyayyar Fa’iz a zuciyata? Wallahi babu shi Yaya Hauwa! Fa’iz bai so na, bai son mahaifiya ta, bai ganin girmanta balle darajarta, ya ya kuwa za ayi in taba shiri da shi a rayuwata??? Mu dai irin tamu ZUMUNTAR KENAN! 


Na shigo dakinmu a gajiye tikis na ajiye (school bag) na zauna gefen gadona ina sabule socks (safar) kafa ta, na fada bayi na dan watsa ruwan sanyi a_jikina, kasancewar ana tsakiyar yanayin afi karshen watan Yuli. 


Na fito na sanya riga da wando na yadin (house wear) dinmu na dan kishingida ina hutawa. Ummi ta shigo da gudu-gudu da kaya da takarda ta fado min a jiki tana shesshekar wata irin dariyar farin ciki, ta kara min takarda a fuska bayan ta zube kayan a gadona. 


Sassanyan kamshin da takardar ke yi na turaren ‘Philips Lumea’ na daxe ban ji kwantaccen kamshi irisa ba, tun can wani lokaci mai tsayi da ya shude. Na lumshe 

gajiyayyun idanuwana a hankali na janye hannunta da takardar daga fuskata na dube ta cikin mutuwar jiki da ta zuciya gaba daya. 


Ta kwanta kusa dani fuskarta dauke da annurin farin ciki da zumudi bayyanan ne, irin dai wanda kika sani a duk lokacin da wata zuciya ma’abociyar bege ta samu sakon masoyinta bayan lokaci mai tsaho. 


Haulatu. da Naja suka _ shigo suka zazzauna a gadon Ummi dake fuskantar nawa, daidai lokacin da Ummi ke fitar da kayan ledar da ta shigo da ita da Yaya Hauwa ta bani in ba ta na ki karbowa. 


Littafin zane ne irin wanda su Ummi ke amfani dasu, alkaluman zane, penti kalakala “yan waje da agogon hannu (handwrist watch) samfurin (L’?OREAL) ruwan silver da zobe shima na silver dandasheshe mai kyau. Ummi ta sanya a yatsanta babban ya yi mata cif duk yadda ta juya hannunta sai ‘dot’ din zoben ya yi walainiya. 


Ta rungume su Haulatu tana dariyar dadi gani kashe ni. Haulatu ta ce, “Hala sakon 

Yaya Fa’izu ne da kullum ake bamu labari mai cin zalin Fa’izah?” Ummi murna take, bakin ya gaza rufo, ta zaro hotuna cikiin ambulan din wasikar jikinta na rawa da karkarwa ta bude suka fara gani. 


Kyakkyawa Fa’iz Giwa ne sanye cikin jibgegiyar rigar leda mai kare sanyi wadda ta sauko har gkwiwarsa, yana tsaye cikin dusar kankara baka ganin komai jikinsa sai fuskarsa, domin hatta hannayensa cikin bakaken safar hannu suke. 


Hoto na biyu sanye yake cikin uniform na masu koyon tukin jirgin sama _cikin karamin jirgi (jet) da wasu abokan karatunshi farare da bakake. Fuskarshi ta fi fitowa a wannan din sosai. “‘Yammatan uku suka ci gaba da kallon hotunan guda biyu suna kada kai kamar kadangaru, da kyar Naja’atu ta iya bude baki ta ce, “Khadija Yaya Fa’iz din ne?” 


Ummi ta rungume hotuna cikin lumshe ido ta ce, “Yes, Fa’iz Bamalli kenan Naja’atu. Yau kinga yayanmu_ Fa’iz, tabbas Ya Fa’iz ne. Ni kaina ya canza min sosai fiye da yadda na san shi. Ya Fa’iz ya kara kyau kwarai, ya yi kiba da haske, ya 

kuma kara girma cikin shekaru uku kacal, kai abin da mamak.’’. 


Haulatu ta ce, “Amman yana da kyau fiye da ku duka, ko in ce fiye da dukkan zuri’ar A.B da na sani. Na so a ce yadda yake da kyau yana da mahadin sa wato kirki, amma kyau ba hali kyawun dan maciji ne Khadija’. (Can da jimawa Ummi ta sha basu labari na da Fa’iz tun daga kuruciya da rashin kirkinsa garemu). 


Ummi ta yi murmushi kawai, ta ce, “Haule yadda kika ji labarin Yaya Fa’iz da Fa’izah ne kurum ya sanya kika fassara shi da haka, amma yana da kirki in his own unique way! Da za ki ganshi a zahiri rantsewa za ki yi ba zai ko kusa da taba iya aikata abin da yake aikatawa ba. Ni kadai na fahimci Fa’iz ciki da waje, zan iya rantsewa babu wanda ya kai ni sanin Ya Fa’iz a gidanmu, akwai dalilin da yasa Fa’iz yake kyarar Fa’iza wanda babu wanda ya sani sai shi daya sai Allah da ya halicce mu. 


Amma _ wallahi ba _ gundarin halinshi kenan ba, koma da halinshi ne ni Ummi 

Khadija INA SON SHI HAKA! Zan iya jure kowane irin halinshi idan na yi sa’ar samun shi a matsayin mii. Ina son sa da yawa Haulatu, kamar yadda na fahimci shima yana sona kawai ba zai furta bane ko ya nuna kamar yadda Yaya Aliyu ke nuna ma Fa’izah. Ban san ina son shi ba Haule sai ranar da zai tafi’”’. 


Ta yi shiru tana kallon yatsar kafarta kafin ta yi murmushi a hankali ta ce, ‘“Wannan ya faru ne a dalilin babu auren na-gani-ina so cikin zuri’armu da family dinmu duka, sama da komai Fa’iz daban ne wajen halayya da dabi’a. Wanda zai ce miki ya san dukkan halinshi wallah ya fadi karya, saboda kullum sabon hali yake sakewa tamkar wahainiya mai canza launi daga wannan zuwa wannan. [rin wadannan mutanen ma’abota kaskantar da kansu ga abin da zuciyarsu ke matukar so tsiraru ne a cikin al’umma!”’ 


Ta girgiza kai. Su kuma kamar masu daukar darasin tarihi, sai gyada kai suke, don haushi kamar na hada kawunan nasu su duka ukun na gwara, da suka tsaya suna sauraren shirmen Ummi da ba ta san inda 

ke mata ciwo ba. 


Ta ci gaba da cewa, “Ni dai ku tayani addu’a Allah yasa Hajjah ta hadamu ni da Fa’iz, don in ba Yaya Fa’iz ta bani ba? Bana jin zan iya aure a rayuwata. Na gwammace in mutu haka nan ban yi aure ba. Zan jirayi Fa’iz ko da shekaru nawa zai yi bai dawo daga Ukrain ba in dai har Hajjah ba ta yi tunanin aurar dani ga wanin shi ba”. 


A hankali na juyo da kaina sashen da su Ummi ke zaune, na dube ta tsaf. Shin mafarki nake ko ko a farke (idona biyu)? UMMI NA SON FAV’IZ, FA’EEZ NA SON UMMI? 


“Wannan haka yake”. Daga can cikin wani sako na kwakwalwata aka bani amsar. Tabbas biri ya yi kama da mutum. Yawan zancen Fa’iz da Ummi ke yi har ya so ya baci. Bana jin akwai ranar Allah da za ta fito ta fadi, bakin Ummi bai ambaci kalmar “YA FA’IZ’ ba. Na kuma sha jin an ce ‘adadin soyayyarka da abu adadin yawan ambatonsa a bakinka.....!; 


“Amman Ummi_ kin cika _ banza, 

shashasha, dabba, mahaukaciya wadda ba ta san ciwon Kanta ba....... 1” 


Ban san sanda kalaman suka yo ambaliya daga bakina ba. Kafin hawaye su shimfido a kundukukina. Na soma shesshekar kuka sosai. Su duka suka dube ni a razane. Na mike tsaye na shiga nuna Ummi da babban yatsana, idona a rufe bana ko ganin abin da yake gabana, na surfeta tas da zagin da ba ta taba tsammani daga gare ni ba. 


A karshe na kare zancena da cewa, secees °*Ummi in har kin yarda ki auri Fa’iz, ki sani karshen zumuncina dake ya zo, ko a hanya muka gamu babu gaisuwa tsakaninmu. Fa’iz kike so Ummi? Kyawun fuska ne zai rude ki ki manta da waye Fa’iz? Fa’iz Bamalli? Fa’izun_ gidan Babllan Kaduna ne fa, kyawun fuska zai rude ki? Mugu azzalumi, makaryaci, masharranci, mugun da bai san girman zumunci da girman iyaye ba. Mutumin da ya nuna mana kyara da tsangwama irin wanda wani dan’uwa bai taba nunawa wani dan’uwansa ba, Fa’iz HAFIZIN HAJSJAH shi kike so Ummi?’ 

Muryata har dakushewa ta yi a wannan lokacin. Na dube ta da dukkan idanuna na ce, “Ummi kin manta baya? Kin manta duk abubuwan mugunta da tsanar da Ya Fa’iz yai mana? Shin farar fata koko zuwa Rasha ya rudeki ga son Fa’iz Ummi? Ko kuwa tukin jirgi da yake koyo.....?” 


A nan ne ran Ummi ya yi mugun baci, domin da kallona kawai take kamar ta ga mahaukaciya. Ta ce, “Ke Fa’izah dakata, cin mutuncin naki ya isa haka, ya ishe ki kin ji ko? Kada ki kara don kuwa ni ba ‘yar cikinki ba ce da za ki sani gaba kina min wannan hayagagar ba tsoronki nake ba. 


Da kin ki da kin so Fa’iz dan’ uwanmu ne jininmu ne, ko me Fa’iz ya yi miki ya ci a ce kin manta haka nan as time goes on.... Haka kike da riko da gaba wanda ya wuce na musulunci? Wai ke baki san kuruciya bane? Ke abu baya taba zuwa ya wuce a wurinki? 


Fa’izah ina son Fa’iz fisabilillahi na fada a yau na kara da babbar murya I LOVE FA’EEZ! Kuma insha Allahu shine mijina, 

ki yi duk abin da za ki yi, kada Allah yasa ki kulanin, kada Allah yasa mu _ yi zumuncin. In na auri Fa’iz don Allah kada ki zo gidana, in na haihu da Ya Fa’iz don Allah kada ki zo barka, kada kuma ki kawo riga ki ce a sawa dan ko atamfa in yi zanin goyo! In ce dai shine zumuncin? 


Ni babu abin da Fa’iz ya yi min baya ga yanke gashi wanda daga baya ya zo ya zame min alkairi, domin ya zamo silar da na yi gashi irin wanda ban taba zaton zan yi ba (Fa’iz ya taba yankewa Ummi duka jelunan kitsonta da ya kamata a dakinsa ta dauki hotonsa ta boye cikin hijabi za ta fita). 


Wata mugunta ko cin mutunci ko wulakanci kika ce ke ya shafa, matsalarku ne. Tsakanina da Fa’iz daban, tsakaninki da Fa’iz daban, ban ga dalilin da zai hada ki yi mana jimilla cikin al’amarin ba. Don haka ni a wajena komai ya wuce lafiyalafiya, lafiyar Allah muka rabu ni da Ya Fa’iz cike da begen juna da fahimtar juna. Insha Allah sai kin goya ‘ya’ yana da Fa’iz, kin ji Ko Fa’izah?” 

Ta fada cikin karaji da zazzaro idanuwa, duka a lokaci daya tamkar zararriya, ta daga hoton Fa’iz ta kai bakinta ta sumbata, ta kuma rungume a kirjinta ta ce, “Fa’izah, kin ce farar fata da kyawun Fa’iz ya rude ni ga son shi? Shin kin manta nima fara ce ba baka kamar ki ba? Kyawu na Bamalli duk ina da shi? Kina kuma tsammanin zuwan Ya Fa’iz Ukrain da tukin jirgi ne ya karkato zuciyata ga kaunarshi? Kin yi kuskure da wannan tunanin naki mara tushe Fa’izah. Bari in gaya miki sirrina da ko uwata da shi kansa Ya Fa’iz basu sani ba. Na fara son Fa’iz ne daga ranar da ya dauko ni a Gusau ya taho ya barki......” Wata irin sarawa kaina ya yi na rasa me zan cewa Ummi don bakin ciki. Da dai a gida ne ba makaranta ba daura hannuwa zan yi a ka in fasa mata kururuwa ko in rufe ta da duka. Tunda babu damar yin ko daya daga ciki sai na ce, “Kaico! Kin cuci kanki Ummi tunda kika sanyawa zuciyarki soyayyar wanda bai cancanta ba, bai san mutuncin dan Adam ba balle dan’uwansa na jini. Na tausaya miki Ummi, muddin 

kika Yatda kika auri wannan mugun 


Mutumi ; 3 


Ta 10 ha rantse sunanki sorry.... 


sa Katse ni da cewa, “Ki ce ma sunana Tal asarar duniya ba sorry ba, ‘to be 


frank’ 


yanzu na saka danba a son FA’IZ 


MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA 29 


Na ce, “Kin bata wayonki Ummi, wallahi kika aure shi za ki kwashi kashinki a hannu. Na rantse mai halli.......” 


“Baya fasa halinsa fa Fa’izah!” 


Ta karasa tana min dariyar tura haushi. Ta kuwa tura din. Ta ci gaba da cewa, “A ganina wannan ba damuwar ki ba ce tunda dai ba ke za ki zauna min dashi ba, bai shafe ki ba kowacce irin rayuwa zamu yi ni da Ya Fa’iz, tunda abin sa-kai-ne. Ina SON SHI HAKA! 


Shine kadai ya tara dukkan abubuwan da nake so ga Da namiji, har ma ya arta. Kafin a samu namijin da ya tara sura da ‘attributes’ din duk da ‘ya mace ke so irin Fa’iz za a jima Fa’izah. Don haka Fa’izah 


a yau ina mai farin cikin shaida miki cewa, ina son FA’IZ MUKHTAR ABUBAKAR 

BAMALLI GIWA!” 


Sai na ce, “Allah ya ganar dake Ummi. Kin riga kin yi nisa ba za ki ji kiran ba. Allah ya shirye ki, ya ganar dake makiyinka baya taba rikidewa ya dawo masoyinka, ‘no matter what.... sai in ya ga kiyayyar tasa ba mai ci ba ce.....” 


“wai ke sai kira kike FA’IZ MAKIYTI! To makiyin wa? Ke ko mu? A lokuta da dama Yaya Aliyu kan ce bakya magana sai mai ma’ana da hikima a ciki, amma ga shi ni yanzu duk kin cika ni da rubbish (shirme). Wallahi duk kin isheni da surutu mara ma’ana. To wannan shirmen da kike shi Zai sanya in tsani Fa’izun nima?” 


Ta yi dariya ta shiga tattare kayan ta cikin ledar da aka kawo su. Tabbas da da ne ba yanzu ba da GIRMA da HANKALT suka zo ba, babu abin da zai hanani rufe Ummi da dan iskan duka, yakushi da cizo irin wanda muka saba da zarar mun samu sabanin ra’ayi ko don in huce bakin ciki da takaicin da ta kunsa mini, amma ina! Girma ya zo!! In ma mun yi ba zai mana kyau ba!!! 


Sai na kyale ta na kwanta a gado na kama 

kuka mara sauti. Ni babban bakin cikina da muka yi a gaban su Haulatu muka farke sirrin gidanmu a gabansu, shin da me za su fassaramu ba dabbobi ba? 


Wasikar da Fa’iz ya aiko abin da ya rubuta a ciki kawai “Ga Hankicina ki bawa Fa’izah, sauran kayan naku ne ke da Zanirah”’. 


Wannan wasika ta bai wa su Ummi da su 


Naja dariya. Wato su tsaraba wadda za ta amfane su, Fa’izah da ba a so ‘HANKICI! Suka kyalkyale da dariya. 


Haule ta ce, “Kai zan so in ga Fa’iz dinnanface to face, am sure he will be vey 


funny”. Ummi ta harareta ta ce, “Me kika ce? Ki 


ganshi ki yi mai uwar me?” 


Suka kara kyalkyalewa da dariya. Naja ta ce, “Sorry Khadijan Fa’iz, ai mu Fa’iz ya wuce da ajinmu ba cewa zamu yi muna so ba. Wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa!” 


2K 2K ok ok 


Tun daga ranar na fita harkar Ummi, na ma tattara kayana na koma hostel din su 


Post a Comment for "ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 9 by Sumayyah Abdul-kadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...