ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 11 by Sumayyah Abdul-kadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 11  by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 11 by Sumayyah Abdul-kadir

- - Post a Comment

 ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 11  by Sumayyah Abdul-kadir

BOOK 1 KARSHE 
amince ayi aurenmu da zarar kin yl graduating?” 


Na langanar da kai na ce, “Haba Yaya Aliyu”. 


Ya yi murmushi ya zauna, nima na zauna, muka dubi juna, sai muka sa dariya a tare. 


“Ke fa shu’uma ce Fa’izah, in mun yi aure zan sha wahalarki”’. 


Na kau da zancen cikin jin kunya da cewa, “Zanirah fa tana ciki Yaya Aliyu in kirawo ta?” 


Ya ce, “In mata me? Ke, ina fa da abin yi, za ki bani amsata ne ko kuwa?”’ 


Na yi rau-rau da ido kamar mai shirin kuka na ce, “Haka ake ba da amsar Yaya Aliyu kamar a fagen fama? Don Allah ka yi hakuri na amsa duka laifuffukana”’. 


Ya saki rai ya ce, “Ok!” 


Na koma kicin na kawo mishi wani ruwan, har da cake da dambun naman kaza ya soma ci yana hararata ina share fasasshen kofin tangaram ina murmushi. Na kammala na koma daki 

na dauko takarda na dunkule a hannuna na fito. 


Zuwa lokacin Yaya ya gama, na ce, “To Yaya Aliyu rufe idonka’”. Ya mai da manyan idanunshi ya lumshe zarazaran gassun girarsa. Ya bude su duka a kaina ya ce, “An ki a rufe, in rufe ki caka min wuka, tunda ba kya SO NA?” 


Ido waje na ce, “Lalala! Sharrin da za ka yi min kenan Yaya Aliyu?” Na jefe shi da takardar na yi daki a guje tare da kullo kofar har da murza key. 


Zanirah na tarar zaune bakin gado tana rubutu cikin karamin ‘DIARY’ din ta. Tana ganina ta boye shi cikin filo ta mike tana fadin “Fa’izah har yanzu Momi ba ta dawo bane?” 


Na ce, “Nima na rasa abin da ya tsare su, amma lokacin dawowarsu har ya wuce tuni’”’. Ta ce, “Ke da wa kuke ta magana ne haka a falo?” 


“Yaya Aliyu ne Zanirah, amma na ji tashin motarshi yanzun nan ya tafi, kina toilet sanda ya zo”. 

Jikinta a sanyaye ta koma gadon ta kwanta tana fadin “Zan dan kwanta in samu bacci kafin kiran sallah, in sun dawo don Allah ki tashe nv”. 


Wai Zanirah ta dauka kwanciyar nan da ta yi ban san cikin damuwa take ba. Damuwar ce ta yi mata yawa ba ta so na gane shine dalilin da yasa ta zabi ta kwanta din a dalilin dauriya da juriyarta sun kare. Umh! Na fa soma tunanin akwai wani abu tsakanin Yaya Aliyu da Zanirah, kai to mene ne.... kai babu komi.... to mene ne ma zal shiga tsakanin nasu? Oh! Ni Fa’izah! Anya ba son Yaya Aliyu Zanirah take 


sees Ina kammala makaranta zan kawo mata mijin..... Ki rike Yaya Aliyu da kyau, ki yi mai _ rikon magnet..... Yaya Aliyu ba irin mazan da ake yiwa rikon sakaka bane..... He has all the qualities and all the attributes to be loved upon.... ina da kyakkyawan zaton cewa, muddin Yaya Aliyu ya zamo miji a gare ki babu ke babu ganin wulakancin namiji 

da ‘yan’uwa mata ke suffering... Saboda Yaya Aliyu na daban ne.... domin Aliyu uwa ne, uba ne, aboki ne, dan’uwa ne.... miji ne abin so da duk wata diya amce za ta yiwa kanta burin samu...... Imagine Fa’izah, yadda za ka zauna da wani alhajin zuciyarka da tunaninka, ruhi da gangar jikinka duka suna ga kaunar wani can daban.... Na tuno kalaman Zanirah! 


Na tallabi kaina da hannayena biyu sakamakon wata irin kwankwatsa da yake yi min tamkar zai dare gida biyu. Ko da yake an ce az-zannu zambun, wato zato zunubi ne bai kamata in yi saurin gaskata hasashena ba, har sai na ga diary din Zanirah da take boyewa, sai na ga abin da ta rubuta dazu, sai na ga damuwarta ta shekara da shekaru wadda a kullum ke zane a fuskarta. Ko mene ne mi zan yi kokari in magance mata damuwarta in har ba soyayyar Yaya Aliyu bane, zan taimake ta insha Allah ta fita daga halin damuwar da take ciki. 


seen Shigowar Walida ya_ katse tunanina. Ta ce, “Yaya Fa’izah, Yaya 

Aliyu ke kiranki yana cikin mota zai tafi’’. 


Duk da ina jin nauyin Aliyu ba zan iya kasa yi mishi sallama ba. Na rufe kaina da mayafi na bishi. Yana zaune cikin mota duka kafafunshi suna waje, ya jingina da makarin kujerar idonshi a runtse. 


Har na karaso bai bude idon ba, sai da na kwankwasa gilashin kofar motar ya bude dukkan manyan idanunshi a kaina, sun kada sun yi jajir har sai da na ji gabana ya yanke ya fadi, ko amsar da na ba shi ne ya tayar da hankalinsa maimakon ya yi farin ciki? 


Kallon juna muka yi cikin ido na ‘yan sakanni, kafin mu_ saki ajiyar zuciya a tare. Cikin sassanyar murya ya ce, “Abin da kika fada_ cikin 


takarda Fa’izah haka yake ‘heart and soul!” 


Kunya ta rufe ni, na rufe ido da yatsuna goma ina dariya...... 


Ya ce, “Na gode, na gode kin ji Fa’izah. Ina fatan lokacin da na yanke 

ayi aurenmu bai zamo takura a gareki ba, wato watanni uku masu zuwa bayan kammala jarrabawar ku ta karshe?’’ na yi shiru. 


‘“Akwai babban dalilin da yasa na yanke wannan lokacin duk da bana so na takura ki, akwai dalilin da yasa na yi hakan”. 


Na kara yin shiru idona a kan kananan duwarwatsun da suka rufe harabar gidan, da gaske ne_ har zuciyata ban shirya aure yanzu ba. A ranar na cika shekara goma_ sha takwas. A ra’ayina in samu_ ko karamar Diploma ne in yi kafin aure. To amma bana iya yiwa Yaya Aliyu musu saboda matukar so da kaunar da nake masa, ina son shi fiye da tunanina, fiye da tunanin duk wani dan adam. 


Bana iya musa mishi duk abin da ya umarce ni, don ina da tabbacin ba zai yi umarnin da zai zama cutuwa a gare ni ba sai wanda zai amfane ni. Har sau tari na kan ga kamar son da nake wa 

Yaya Aliyu ya ninka, ya dame ya shanye wanda shi yake mini. 


Wani lokacin na kan yi tunanin muddin muka yi aure ba zan iya batawa Yaya Aliyu rai ba ko inyi masa ba dai-dai ba daidai da kwayar zarrah, ko da shi ya bata min abu kadan zai yi ya shafe laifin daga idanuna da zuciya, komin GIRMAN sa. 


To amma dole in ji dalilin gaggawar tunda an ce ba a son garaje cikin aure, don gaggawar daga shaidan ce. Kamar wadda za ta gudu? Na ce, “Shin Yaya Aliyu to saurin na mene ne haka?”’ 


Ya saita kwayar idanunshi cikin nawa cike da damuwa ya ce, “Saboda SONKI Fa’izah! Na kai na kawo a sonki da kaunarki da son ganin mun zamo abu guda, na mannu da fatar jikinki which is always hunting my 


99 


Na rufe fuska cikin jin kunya. Na ce, “Yaya Aliyu ai ba inda za ni, kullum muna tare. Ina laifin bayan candy da shekara daya? Bani da_ tunanin 

kowanne da namiji a duniya sai kai Aliyu Haydar......” 


Sai bayan na fada na san abin da na fada. Juyawa na yi zan tafi, Aliyu ya riko gefen mayafina. 


Ban juyo ba don haka ban san halin da yanayinsa ke ciki ba, ya ce, “Idan haka ne barshi a yadda na ce Fa’izah, watanni uku masu zuwa’”’. 


“Saboda me Yaya Aliyu? Gaggawa daga shaidan ce”. 


“What target do you have for making it longer haka Fa’izah? Wata babbar matsala ke neman fatali da farin cikinmu”’. 


Ban san sandana juyo gaba daya ba, na ce, “Matsala? Wacce irin matsala ce Yaya Aliyu?” 


Idonshi cikin nawa sun kada sunyi jajir, muryarsa a dushe ya ce, “Kina nufin baki sani ba? To Hajjah ke son in auri ZANEERAH!” 


Ji nayi wani abu ya kwashe ni yuuuu! Zai maka da kasa, na yi kokarin kama hannun Yaya Aliyu dake jikin motar gam-gam na rike. Muryata na rawa 

harshena na sarkewa na ce, “ZA-ZAZANIRAH Yaya Aliyu? Haba! Biri ya yi kama da mutum....” 


Na durkushe a gabansa kaina cikin cinyoyina, kamar in yi yekuwa a Zo a tallafi rayuwata. Shi kansa Yaya Aliyu ya yi nisa a tunani, bai tanka min ba. Kowanne sakar da yake yi _ cikin zuciyarshi daban da na dan uwanshi. Kafin wata juriya da imani su shigeni ciki da bai dina. 


Na dago a hankali idanuna taf da kwalla na ce, “Ka je Yaya Aliyu Allah ya kai ka lafiya”’. 


Ya dago ni daga durkushen da nake muka fuskanci juna. Don karfin hali irin na Aliyu murmushi ya yi min, nima ban san sanda na mayar mai da lallausar murmushi ba. 


‘“Kada ki sa abin a ranki fa. Everything will be alright. Don Baban Giwa (Barau), Baba Sadi da Baba Ibrahim da Yaya Hauwa basa goyon bayan zancen sam”’. 


Na yi shiru ban yi magana ba, a 

zuciyata cewa nake, “Ni da kai kuma Yaya Aliyu ai sai wani babban ikon Allah, wanda in haka ta faru na tabbata na yi asara wadda ba mayarwa”’. 


Zuwa can na ce, “Wallahi ka je 


kawai Yaya Aliyu, ni ba zan damu ba”. 


“How sure are you ba zaki damu ba.....” 


Na ba shi amsa muryata na gab da barkewa da kuka. 


“Tam sure!” 


Ya gyada kai. Ya sanya hannu cikin aljihun motarshi ya dauko daurin kudi ‘yan naira dari biyu sardauna sabbi kar ya miko min. Na bata fuska gab nake da rushewa da kuka, don ji nake kamar sallamar karshe muke yi ni da Yaya Aliyu, kamar babban shinge na shirin shiga tsakaninmu, kamar wata sabuwar rayuwa zamu bude wadda dukkaninmu bamu taba tsammaninta ba. 


“Kada ki min musu, ki karba kawai. Ban da yau na taba dauko naira 

tsurarta na baki?” 


Na mika hannu biyu na karba. 


“Yaya Aliyu na gode, Allah ya kara bud’. 


Ya yi murmushi a cikin kallona ya yi min alama da hannunsa in tafi. Har na juya na soma tafiya ya ce, “Au! Fa’izah!” 


Na juyo hawaye shimfide a fuskata wasu na korar wasu. 


“Kika ce ba za ki damu ba, to meye na kuka?” 


“Ni ba kuka nake ba hawaye ne”’. 


Ya yi murmushi, “Hawaye?” 


Nima sai na yi dariya, ga hawayen fal a fuskata. 


“Su zuba kawai suke, kuka kuwa zuciya ke yin sa”. 


‘Na yarda dake”’. 


Ya miko hannu. 


“Wannan kyakkyawan hankicin na hannunki za ki bani mana?” 


Na girgiza kai na ce, “A’a!” 


Da mamaki Aliyu ya ce, “Dalili?” 


Na ce, ““Wallahi haka nan kawai nake 

son hankicin bana son rabuwa da shi, ina son kamshin sa’. 


“Wa ya baki?” 


“A dakin su kawata Naja na ganshi a hostel dinsu cikin kayana, wallahi ban San na waye ba”. 


“Mu gani?” 


Na mika masa ya karanta rubutun (AHUBBIK (I love you!’’) 


‘WA ANA AIDHAN (me too)” Na mayar masa muryata na karkarwa. 


Ya miko min hankicin na juya da gudu na karasa cikin gida, ban san tsawon lokacin da ya diba kafin ya bar gidan ba. 


ok 2K 2K 


Ban tashi sanin fitinar so ba sai a wannan ranar. Ban yarda it is injurious ba sai a wannan ranar. Ban san cewa its unbearable pain ba sai a wannan ranar da na tabbatar zuciyata ba za ta samu abin da ta dade tana SON ba, wato Ali Na’ibi. 


A gaskiya so abu ne mai dadi in ya zo da matsala marar dadi. Kamar 

yadda Ya IM ya ce na (GIRMA YA FADD “It’s so sweet, yet so painful”. 


Wai sai na kama jin haushin ‘yar’uwata Zanirah (kishi), a ganina duk ita ta yi saurin girman da ya gundiri Hajjah har ta yi tunanin aurar da ita, kuma ta rasa wanda za ta likawa duk gidan sai Aliyuna, Yaya Aliyu, Aliyu Haydar Na’ibi A.B Giwa. 


Daga ni har Zanirah, kowacce ta kasa barci sai juyi a kan gado. Da abin ya isheni kawai sai nasa kuka wiwi. Tunanin in na rasa Yaya Aliyu, idan ba Aliyu ne ya zamo mijina abokin rayuwata ba shin ya ya rayuwata za ta ci gaba da kasancewa? Ya Allah kada ka baiwa MHajjah_ ikon _ karfafa zumuncin akan wannan, ya Allah ka fidda Aliyu zuciyar Zanirah. Don na laluba na duba na hanga ko ina ban ga ta hanyar da zan iya cin kankanta in bar mata ba in ita ba ta ci girma ta bar min ba, sai dai duk mu rasa, ko duk mu samu. 


Zanirah ta mike ba zato ta kunna 

fitila dakin ya gauraye da haske. Ta shiga kallona tsaf, ba ta ce komai ba sai ta shiga toilet ta dauro alwala ta zo ta burma hijab ta hau doka nafilfili. 


Hankalina ya kara dugunzuma ya tashi, don a ganina Zanirah na rokon Allah ne a kan ya mallaka mata Yaya Aliyu ni ya hanani. Sai na_ kara rikicewa da kukan tun karfin gunjin da zan iya a hankali yadda _ sauran jama’ar gidan ba mai ji na. 


Ba shiri Zanirah ta sallame sallarta ta ce, “Fa’izah wai lafiya ne?” 


Na dan saurara da kukan na ce, “Na fara kukan rabuwar mu ne Zanirah....” Da alama ba ta yarda ba har zuci, sai ta yi murmushi ta ce, “Allah yasa hakan ne har zuciyarki. Da sai in ce rabuwa ta zama dole ai, tunda babu yadda za ayi mu dauwama tare a matsayin mu na ‘ya’ya mata. In babu aure akwai mutuwa, akwai kuma kaddarorin Ubangiji iri-iri’”’. 

BOOK 1 KARSHE MU HADU A BOOK 2 DOMIN CI GABA DA KARANTA WANNAN KAYATACCEN LITTAFIN 

Post a Comment for "ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 11 by Sumayyah Abdul-kadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...