ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 5  by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir

- - Post a Comment

 ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 5  by Sumayyah Abdul-kadirCikin dan lokacin nan mun tattauna abubuwa da dama mun kara fahimtar juna. Har zuwa lokacin na kasa tambayar shi sunan shi. Sai wurin karfe goma Haulatu ta fargar damu, da kyar muka katse hirar muka fito zuwa mota. 


Ina ganin Ummi da Haulatu na gulma suna rada da dariyar shegantaka ko kula su ban yi ba. Don na san da ni suke. A kan hanya ma hirar muke yi. Ya gaya min ya yi dukkan karatunshi ne a Taiwan inda ya karanta harshen Larabci ziryan. Shi da Abdullahi ‘ya’ yan family friends ne, haifaffun garin Dambatta. 


Da kyar muka iya yin sallama don sai da Ummi ta shige ta barmu. Sai shigowar hancin motar Yaya Mufty ne yasa muka yi sallama ya jira fitowar shi da yin parking din shi suka yi hannu, sannan ya shiga motarsa ya tafi. Har zai fita get ya dawo ya yi min horn na juyo “Phone no na manta Fa’izah”’. 


“Ni da Ummi bamu da waya”. 


“Saboda me?” 


“An hana mu rikewa ne”. 


Hannu yasa ya dauko tashi a gefe, “Ki rike wannan saboda ni Fa’izah. Na yi alkawari ba zan zamo mai hana ki karatu ba!” 


Ya cire layin ya miko min (Sony experia) sabuwa dal. Na rasa abin da ya hanani kin karba, na kuma rasa wanda ya sani yin godiya. Wala’alla soyayyar kenan? 


2B KK 


Fada na duniya babu irin wanda Aunty Rabi ba ta 

yi min ba a wannan daren. Ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, har sai da na saka kuka. Na farko daren da muka yi, na biyu tsayawa a waje da namiji tsayin karfe sha dayan dare. Na uku wayar da ta ganni da ita, da izinin wa na karbo ta? 


Don bakwa gaban iyayenmu ba zan ci amanarsu ba. Abin da ya zaunar daku gidana shine karatu ba (flirting) ba. Wannan wayar dole ki mai da masa abarsa gobe. Gaskiya ba dani ba, ba a gidana za a karya dokar A.B House ba, gara ma ku sake tsari. Gobe abu na farko da za ki fara da zarar kun shiga makaranta shine mayar da wannan wayar. 


Yaya Muftahu bai ce komai ba. Haka na kwanta zuciyata ba dadi da haushin Aunty Rabi. Duk kula mazan da Ummi ke yi ba ta taba yi mata fada ba sai ni da na yi sau daya, ni da nake da niyyar aure ma ba flirt irin na Ummi ba. Da zuciyata daya nake son malamina, da gaske auren shi zan yi in Allah ya yarda. 


I love you. If you hate it, kill with an arrow. But please not in the heart because that’s where you are. Gud night. 


Sakon da ya fara shigowa cikin wayar kenan da na saka layin da ya bani cikin kwalinsa. “Why will I hate it?” Na tambayi kaina cikin murmushi. “T do love it too!” Na baiwa kaina amsa. Don haka na baiwa 

Malami na amsa. 


“You inspire in me a love so deep and powerful that cannot be destroyed by any arrow! How I wish there is a way you could see into my soul. My love on you is far to strong Mallam!” 


Daga wannan na kashe wayar gaba daya. 


KE 


Washe gari tun asuba nice farkon yin wanka a gidan. Ban jira Ummi ba balle Yaya Muftahun dake sauke mu ya wuce office, na yi tafiya ta ni kadai saboda fushin da nake yi da Aunty Rabi, ban yi ko tunanin wani abu wai shi kalaci ba. Babban burina in dora idona a kan lecturer. Kusan nice farkon shiga laccarsa ta karfe goma ta safe. Kai! Ni Fa’izah na shiga uku!!! Don I become infatuated to him fiye da kima. Akwai wani sirri dake cikin kwayar idanunsa da ba duk maza Allah ya mallakawa ba. 


Sai dai kuma cikin rashin sa’a bayan ajin ya cika (class-representer) din ya ce ya mai da ita (fixed) karfe biyu na rana. Kamar na fashe da kuka daidai lokacin da wayar da na jefa a jaka ta kama tsuwwa. Cikin rashin kuzari na amsa da tunanin yadda zan yi in mayar da ita din kamar yadda Aunty Rabi ta yi umarni. 


Muryar mace ke tambaya, “Dacta ne?” 


“A’a, ba shi bane, wace ce?” 


“Ke me maganar wace ce?” 


““Matarshi ce!” 


Sai ta kyalkyale da dariya ta ce, “Ki ce Haulatu 

Sani Galadanci na gaishe shi, kuma inda hali yana jiranki a office dinsa. Saboda ke ya dage laccar ku zuwa anjima. He can’t wait to see you.... cross sword....! Kunyar Haulatu ta kama ni ainun yadda ta yi ta canza murya ta shammace ni na yi tabargaza, na yi shuka a idon makwarwa. 


Jiki babu nauyi na nufi inda Haulatu ta kwatanta min cewa nan ne ofishin nasa. A ofishin akwai hoton gwamna mai ci a lokacin da na shugaban kasa, sai na Alh. Dr. Ado Bayero. Sanda na yi sallama rubutu yake yi amma bai kasa amsa min ba. 


Na samu kujera na zauna har ya kare, sai ya turo min folder din da yake rubutun nasa hannu biyu na amsa. Ko da na duba (note) dinsa ne da na yi missing har guda biyu cikin hand-writing dinsa mai kayatarwa da ban sha’awa. 


Idona ya kai ga dan karfen dake like saman kofar shigowa ofishin da ban rufe ba. Sunansa ne radau DR. NAZIRU SANI GALADANCI. Wato Dr. Yayan Haulatu ne uwa daya uba daya ta yi min irin wannan ninkewar? Kai abin da mamaki. 


Har mun yi sallama na kai bakin kofa sai na juyo na ce, “Na yi mantuwa ne”. 


“Ta me Fa’ izah?” 


Na dawo a nutse na ciro wayarsa daga jakata na mika masa, yasa hannu ya karba yana fadin “Ya kika dawo min da ita?” 


“Aunty Rabi tana ta fada ne, ita ce ta ce na dawo maka da ita, ba za a barni na rike waya ba sai na yi aure”’. 

Ya yi kasake cikin kallona da murmushi, “Sai na ji na kara son ki, na kuma kara yarda da cewa da ki kai ke din ‘yar babban gida ce. Abin da ban taba ji ba a wannan zamanin ‘yammata kamar ku a jami’a iyayenku sun hanaku rike waya, kuma kun bi, anyway. Ki ce ma Aunty Rabi ta yi hakuri, ba za ki sake rike waya ba sai kin zama matar Dr. Nazir insha Allahu”. 


Da sassarfa na karasa ficewa daga ofishin ina murmushi. 


Yinin ranar zungur na kare shi ne cikin tunanin Dr. Nazir da maimaita ambaton sunansa cikin zuciyata sakan bayan sakan, minti bayan minti, awa bayan awa son Dr. Nazir karuwa yake yi a raina. Yana kara habaka a birnin zuciyata. 


oh KKK 


Soyayyarmu da Dr. Nazir ta yi nisa da karfin da ta Zama sananniya a tsangayarmu. Tsegumi kam iri-iri an kawo min a kan yawan ‘yammatan da Nazir ke dasu cikin makarantar. Na kan toshe kunnuwana ne kamar yadda ya ce, ko in yi hannun riga da duk wanda ya kawo min tsegumin. 


Dr. Nazir ya ware muhimmin lokacinsa wurin yi min (extra class) bayan kowacce laccarsa. Nazir ya iya koyarwa. A dalilin koyarwar da yake yi min ‘points’ dina a jarrabawa ya kara karfi fiye da na baya. Nazir ba shi da karfin idanu (short sight), a dalilin hakan yake amfani da farin gilashi mai kara karfin gani (lenses) ya yin rubutu ko karatu, ko ba da lacca. Amma in ba fadi aka yi ba za ka yi zaton na kwalisa ne. Don yana mai 

kyau sosai. 


Nazir mutum ne da ya iya tsara magana da hafizin harshen da Ubangiji ya hore masa. Iya maganarsa da kirkinsa ya taka rawa mai yawa wajen sanya zuciyata ta zamo kangararra, bana ji bana gani. 


Da kaina in ban ganshi ba sai na bishi office, har sayayya mu kan fita wasu lokutan. Tun Ummi na hana ni har ta gaji ta rabu dani. Wai ni Fa’izah tsatso daga A.B House nice mai bin saurayi har office, nice mai fita da saurayi. Wannan ba karamin kona ran Ummi yake ba. Har ta gaji ta tseguntawa Aunty Rabi. 


Aunty Rabi ta samu Yaya Mufty take sanar da shi, inda ya ce, “A kawo mishi sunan Nazir cikakke zai yi bincike a kansa. In mutumin kirki ne a kyale ni, kwana nawa ne zamu gama karatun mu koma gaban iyayenmu? Domin Hajjah ta soma fadan mu dawo gida haka karatun ya ishe ta. Abu ya ki ci ya ki cinyewa tamkar cin kwan makauniya”’. 


Aunty Rabi ta ce, “In kuma ba mutumin kirkin bane ba fa Mufty?” 


Ya ce, “Zan san abin yi a kai’. 


Ni kam duk surutunsu da harare hararen su basa damuna, na yi nisa a son Naziru. 


Wani irin so nake dandana mai wuyar fassarawa, wanda ya zarta na Yaya Aliyu fintinkau! Idona ya rufe a son Naziru, lokutana baki daya na Dr. Nazir ne. 


Tambayar da jama’ar dake tare damu ke wa Ummi shin Fa’izah ta san Dr. Naziru (use and 

dump) ne? Ta ya ya yarinyar ‘yar gidan mutumci wadda ta san ciwon kanta irin Fa’izah ta yarda cewa Dr. Nazir auren ta zai yi? Shin Fa’izah ta san yawan “‘yammatan da Dr. Nazir ya yaudara ya watsar a Kano? Shi fa dama duk inda kyakkyawar mace take nan idonsa yake, zai nuna mata so ya yi ta yi mata facaka, amma da an ce ya fito ayi aure ba kya kara ganin keyarsa’”’. Ummi ta kan girgiza kai, don bakin ciki ta rasa me za ta ce, sai dai ta ce, “Fa’izah kam ta yi nisa ba za ta ji kiran ba”. 


A yammacin wata talata mun dawo daga Ado Bayero Mall (Shoprite) ni da Nazir ya sauke ni dai-dai inda ya ga su Ummi a zaune a (seaters) na dalibai karkashin wata bishiyar dalbejiya mai inuwa, bai ko tsaya sun gaisa da su Ummi ba don ya san Ummi ba ta goyon bayan tarayyarmu daga ita har shakikiyarshi Haulatu, ita ma ta bi sahu don tsoronta na kar mutuncinta ya zube idon su Aunty Rabi dake matukar ganin mutuncinta, ranar da Nazir ya yi (dumping) dina. 


Ko ba don wannan ba Nazir baya sakar ma dalibanshi fuskar da raini zai shiga tsakani. Ko mata da yake nema tamkar bunsuru ba dai cikin tsangayarmu ba can a wasu tsangayoyin ko waje yake neman abinshi. 


Na yi musu sallama duka suka amsa min a sanyaye, na aje ledar hannuna gefen Haulatu ina fadin “Wash Allah! Na gaji da yawa. Dr. N (sunan da nake kiransa) ba dai yawo ba, shi dai a je shopping burinsa kenan”. 


Suka dubi juna suka kau da kai. Cikin nutsuwar 

da ban san tana da ita ba Ummi ta ce, “Fa’izah rayuwar da kika zabawa kanki kenan? Tarayya da maza irin su Dr. Naziru? Yau da Hajjah za ta ji wannan mummunan labari ina kike tunanin za ta tsoma ranta? Da kin sa zuciyarta ta yi bugawar farat daya. 


Wallahi-wallahi tun wuri ki sake hanya tun dare bai yi miki ba. Nazir ba dai-dai yake da tsarin rayuwarki ba, kuma aurenku ba zai taba yiwuwa ba. In kin manta kin fito daga zuri’ar A.B ne nake tuna miki”. 


Haulatu ta cafke “Ina mai matukar jin kunyar ranar da Yaya Naziru zai yi dumping din ki, (as if you had never been in existance), shi yasa nake so ki kwaci kanki tun kafin zuwan wannan ranar, domin mai hali baya fasa halinsa, kuma sannu ba ta hana zuwa sai dai a dade ba a je ba. 


Nazir dai dan uwana ne, karewa ma shi ya sha nono ya saki na kama, uwarmu daya ubanmu daya. Amma bana goyon bayan ki mallaka mishi soyayyarki. Abin dai da baki son a ta da to dole ne a fadi, ba auren ki zai yi ba”. 


Na yi murmushi na ce, “Kun gama? Shin ina kaunar da kuke ikirarin kuna yi min din Haulatu da har ba za ku so abin da nake so ba don cikar farin cikina? Kuna kina da Dr. N ne don tsoron kada ya yi min yadda yake yiwa sauran ‘yammatan da ya nema a baya, shin ku Allahn musuru ne? Kun san gaibu? Kuma shin shi halin dan Adam baya canzawa ne? 


Dr. N ba munafuki bane irin yadda kuke zato, tun ranar da muka hadu ya gaya min abin da kuke 

gudu din, ya kuma tabbatar min daga kaina ya daina, ina rokon Allah ya taimake shi ya dainan. Manzo mai tsira da aminci ya ce, “ku kyautatawa mutum zato domin zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya’. 


Kuma duk iskancin da kuke tsammana mishi wallahi bai taba kai hannunshi jikina ba ko bisa kuskure. Bai taba ba. Wannan ya nuna Dr. N son Allah da Annabinsa yake yi mun, ba kuma zai gwada iskancin nasa a kaina ba saboda ba yaudarata yake da niyyar yi ba. Zancen mutuncina da kuke, kada Allah yasa a ga mutuncin nawa in har sai na bar Dr. N. 


Ke kuma Haulatu yadda kike aibata dan uwanki don tsira da naki mutuncin wallahi kin bani mamaki, in kin yi ne don ki burge wallahi baki burge ni ba. Ai naka-naka ne komin lalacewar shi, hannunka baya taba ribewa ka yanke ka yar. Ku zuba ido tunda duk kun zama ‘yan adawa da yardar Allah kunya za ku sha”. 


Na suri ledar shopping dina na bar musu wurin, na barsu suna kallon-kallo a junansu an rasa mai karfin halin musawa ko maida martani. 


3 AS BK 


Abdullahi ya ce, “Ka rufa min asiri Naziru, Haulat ta zo min tana kuka in rokeka ka rabu da kawarta in ba auren ta za ka yi ba. Naziru ka yiwa Allah ka rabu da yarinyar nan ko don zumunci da sanayyar dake tsakani”. 


Dr. Nazir Sani Galadanci sai ya yi murmushi 

yana harhada takardun daliban dake bisa tebirinsa. “Wata fuskar..... ta fi gaban mari. Za ka sha mamaki na Abdullahi’. 


2K KK 


Ranar da muka kare zana jarrabawar zangon karshe na aji uku (300 level), ranar muka yi shirin tafiya Giwa, a dalilin dan uban aiken da Hajja da Baban ABU suka ishemu da shi lallai mu zo gida ana neman mu. 


Mun yi sallama da Aunty Rabi da alkawarin ita da kanta za ta rako iyayen Nazir Giwa a duk lokacin da suka bukaci hakan, domin Aunty Rabi ta tsinke da irin kaunar dake tsakanina da Dr. N, duk da binciken da Yaya Mufty ya yi ya nuna cewa Dr. Naziru Sani Galadanci yana layin samarin da iyaye ke tsoron ya dora mayaudaran idanunshi bisa ‘ya’yansu a fadin garin Kano da jami’ar Bayero. 


To an ce fadan da ya fi karfinka sai ka mai da shi wasa. Don haka dukkaninsu suka koma lallabani da bina da siyasa. Ashe abin da ban sani ba a nufin Hajjah karatun daga iya nan an barshi kenan mu da Kano sai zuwa da yawo babu wanda ya gaya mini. 


Na ga dai Ummi cikin damuwa, da zamu tafi kuwa sanda Yaya Mufty ya kunna mota kuka take yi wiwi har da sharbe, ni kuwa sai na ji gabana ya yi wani irin mummunan faduwa a sa’ilin da Yaya Mufty ya hau kan titi. 


Kaduna muka fara isa. A sa’ilin da Yaya Mufty ya sanya hancin motar cikin gate din gidan Baban 

Kaduna, a sa’ilin ne na ji wani irin faduwar gaba da ban taba ji ba a rayuwata. 


Muka yi sallama a babban falo, duka ‘ya’ yan Hajjah in ka dauke Rabi auta dake Kano babu wanda babu a falon. Suna zaune duk sunyi jigumjigum. Da na juya ido zuwa mahaifina Ahmadu A.B sai na ganshi cikin jan ido kamar gauta. Babu abin da ya zo raina face mutuwa ga tsohuwa Hajjah. Idanuna suka yi kwalkwal na dubi Maman Kaduna cikin hawaye. 


“Hajjah ta mutu ko Mama?” 


Na rushe da kuka bana ji bana gani, kuka mai tsananin gigitar da zuciya ma’abociyar imani. Wata irin tsawa Baban ABU ya daka mini, “Ke bama son sakarcin banza. In mutuwar ta yi abin da za ki yi mata kenan? Sakayyar da za ki yi mata kenan zubar hawaye?” 


Baba Barau ya ce, “Ita Hajjah din za ta so ta mutu Fa’izah ba ta rungume ‘ya’ yanku ke da Ummi ba tunda ta rungume na Zanirah?” 


Sai ga mai kuka na dariya bayan ga hawaye shabe-shabe a fuskar “Zanirah ta haihu Mama?” Gaba daya na basu dariya ban da Baban ABU. Na ce, “Amma Mama shine baku gayawa Aunty Rabi ba mun zo mun ga danmu?” 


Mama ta ce, “Mace ce, ai abin bana yau bane. Ita Rabi ta sani lokacin kuna jarrabawa shi yasa ta ce ba za ta gaya muku ba murna da doki za su hanaku karatu in kun zo kwa gani, to kin ji. Yau shekarar (FA’IZA) daya tana gudunta ko ina”. 


Na yi shiru cikin tunani, wato sunana Yaya Aliyu ya sanyawa diyarsa da Zanirah. Na ce cikin mur

mushi, “Allah ya raya takwara, zuwa Lagos ya kama mu kenan”’. 


Ni sai a lokacin idona ya kai ga huhunan goro da alawa dake jingine gefe guda wani a kan wani. Na ce, “A’a, wannan kuma fa? Auren Maryam za ayi ko Hanifa?” 


Baban Kaduna da Baban ABU suka kau da kai kamar basu ji ni ba. Baba Ibrahim ne ya ce, “Auren Ummi ne ya tashi gobe insha Allahu, don haka makaranta ta kare babu sauran komawa Kano”. 


Ummi ta zare ido cikin firgici da kaduwa. Ni kuwa sai na rungumeta ina murna ina fadin “Don Allah Mama waye angon?” 


Mama ta ce, “Da masoyinta mana mai sonta tun tana karama”. Babu wanda zuciyata ta kawo min sai FA’7EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BaAMALLI GIWA!” 


Ban san sanda na ce, “Amma a rasa wanda za a bawa Ummi sai Fa’iz?” 


Sai bayan na fada ne na tuna cewa, UWA da UBAN da suka tsugunna suka haifi Fa’iz ne a gabana. Suna zaune ne idanuwansu cike da kauna, kuma suna son dansu kwatankwacin yadda kowanne iyaye ke son dan da suka haifa duk munin shi ko munin halinshi. Ya yin da ni nake kokarin aibata musu shi a gabansu. 


A sanyaye na ce, “Allah ya sanya alkhairi”. Cikin sanyin jiki na wuce daki zuciyata cike da sakesake. Wani bangaren tausayin Ummi nake ji. A ganina sun cuce ta sun aura mata mutumin da bai cancanci a hada auren shi alkhairi ba. Sai na tuna 

Ummi fa na son Fa’iz, kuma so hana ganin aibu. Yadda nake son Dr. N da tabban da yake da shi, haka Ummi ke son Fa’iz da kowanne tabo mai alaka da shi da halinsa. Iyayenmu suka bini da kallon nazari ganin yadda yanayi na ya sauya gaba daya a lokaci daya. 


Wajejen karfe hudu na yamma masu aikin gidan ke ta kaiwa da komowa sun kasa zaune sun kasa tsaye. Suna diban katon-katon na lemuka suna jerewa a firizan dake dakunan Baskwata (boys quaters) guda biyu dake like da juna. 


Na dan matsa na leka, ko falon dan ‘Prince Charles’ sai haka. Kwata-kwata falon bai yi kama da sauran falukan da na saba gani ba a wurare daban-daban. Komai na falon cream colour ne in ka dauke kayan kallo bakake samfurin SONY, hatta ‘curtains’ (labulaye) cream colour ne. Haka sauran kayan alatun dake falon. 


A.C har biyu, ta tsaye (standing A.C) da ta manne a bango (split), sai sassanyan kamshin (Bakhour) da Yahya ya sanya a dakin ke tashi. Kujerun (leather) ne suma cream colour masu_ laushi. Yadda wannan dakin yake, haka na kusa da shi yake komai da komai, sai bambancin kala. Na daya dakin ruwan makuba ne (grey). 


“Shin Yahya Baba amarya ya yi ne?” 


Sai ya kyalkyale da dariya, “Mama ce za ta bari Baba ya yi amarya?”’ 


“Yo ina na sani? Na san dai ba naku bane, duk da gasu a Baskwata”’. Ya kara kyalkyala dariya, “Kin manta ne gobe su Yaya Bashir da Yaya Fa’eez za su dawo? Sai dai 

Bashir ya kammala, Fa’iz ma’aikaci ne ganin gida kawai zai zo”. 


Na ce, “Hummm! Lallai. Ni za ni in kwanta, anjima in su Baba za su koma Giwa kasa a tashe ni don Allah’. 


Ya ce, “Insha Allah’. 


Na juya zuwa cikin gida zuciyata cike da sakesake. Da mamakin kaunar da Baban Kaduna yake yiwa ‘ya’yansa (beyond comment) sunan wani ganyen shayi. Abin haushin dukkansu babu na gari, don gara ma Bashir din shi shaye-shaye kawai yake. Shi dayan munin hali har ba a magana. 


Sai dai duk yadda na so in yi barcin Ummi ba ta barni ba. Hakika tana cikin farin ciki da ban taba ganinta cikin irin shi a duniya ba. Murnar auren ta da masoyinta Fa’iz Allah ya cika musu burinsu. Ta yi kukan dadi, ta yi na sosai. Duka dalilin daurin aurenta da Fa’iz gobe......” 


Na yi murmushi na ce, “Ki yiwa Allah ki barni in yi barci, ki bari ya dawo sai ku yi tare tunda karfe daya baya amo. Ki barni da abin da ya dame ni fargabar zuwan iyayen Dr. N, don ban san irin tarbar da Hajjah za ta yi musu ba”. 


Ta ce, “Matsalarki ce wannan”. 


Karfe bakwai na magariba muka bi Baban Giwa sai Giwa, Yaya Mufty ya wuce Kano. Tun daga gate din A.B Estate gaba daya komai ya canza, an sake fasalin ginin an mayar na zamani sosai, haka cikin gidan Hajjah an canza komai sabo dal kamar gidan amarya. An sake fenti gida kamar ba a cikin garin Giwa ba kamar a Lagos ko Abuja. 

Irin wannan sauyin na A.B Estate na faruwa ne a duk lokacin da A.B family za su yi wani gagarumin biki. Na ce, “Uhm! Ummi ana ji da aurenku tabbas”. Ta ce, “Fadi da babbar murya”’. 


Abin da ya bani mamaki yadda su Inna Kubra, Indo da su Kaltume da sauran kannenmu na Giwa ke min oyoyo da (AMARYA).... Ka ga amaren sai kyallin goshi suke.... ni dai murmushi kurum nake ina cewa cikin raina ‘“Auren Ummi guda ai dole a kiramu Amare, tunda mune Amara kirazan biki”. 


Idona bai hasko min kowa a falon ba sai Zanirah, rungume da buleliyar ‘yarta tana shayar da ita. Yaya Aliyu na gefenta yana waya. Habawa! Da Zanirah ta cizge ‘yar a nono ta dangware masa a cinya ta yi wani tsalle muka dire a tare muka makalkale juna bayan mun shararo a guje muka shiga juyi a tsakar falon Hajjah. 


Wai! TAKORI ta ce, TUNA BAYA SHINE RIKO! 


Yaya Aliyu ya mike rike da ‘yarsa ya hau Zanirah da fada..... “Wai ke baki da hankali ne? Kashe min ‘yar za ki yi? An girma ba a san an girma ba, kuna abu kamar kananan yara? Ko su Hanifa ba za suyi wannan shirmen da kuke yi ba....” Zanirah aka kwantar da kai aka shiga lallashin maigida... “Haba Baban Fa’izah! Shekaru uku currr! Ni, Fa’iza da Ummi???” 


Yaya Aliyu ya yi murmushi yana ci gaba da jijjiga Fa’izar don ta koma barcinta da hayagagar mu ya katse mata, don shi dama fadan whatshi baya nisa. Ya koma ya zauna ya ce, “Fa’izah ya 

karatu? Shi kenan an kare ko?” 


Muka dubi juna ni da Zanirah da Ummi duka muka yi murmushi. Na mika mishi hannu ya bani diyata kuma takwarata Fa’izah. Na dauke ta na sumbace ta na kura mata ido. Allah kareem dani yarinyar take kama sosai, ko da yake dukkanmu kamar tamu daya ce. 


Na ce, “Ya Allah ka raya mana little Fa’izah”. Kowa ya yi murmushi ya ce, “Ameen”. 


Yaya Aliyu kallona kawai yake, na san ba zai wuce mamakin kyakkyawan girman da na yi ba. Na samu Yaya Aliyu a kofar gida kan fararen kujerun roba yana yiwa ‘yar shi wasa, na labarta mishi zuwan dangin manemin aurena Dr. Nazir gobe. 


Yaya Aliyu ya yi shiru yana mai nazarin zancena. Akwai wani yanayi a tare da shi ya kada min ‘ya’yan hanji, wani yanayi da na kasa fassarawa. Yanayi ne mai nufin “BA ZAI TABA YIWUWA BA!” 


Na yi zugum! Ina dubansa hannuwa a kumatu zuciya cike da taraddadi. Ya yi ta maza in ji mata ya ce, “Fa’izah kin yi babban kuskure da kika saka soyayyar Dr. Nazir a ranki, alhalin kina sane da cewa babu auren (na gani ina so) cikin zuri’armu. Balle auren bare, wanda ba a taba ko da wasan kwatantawa ba. Tun bayan na mahaifiyarki wanda ko shi tunda ran A.B ne. 


Shin abin da ya faru a baya ni dake bai ishe ki ishara ba? Ki guji mu’amalar soyayya da kowa ki baiwa Allah zabi cikin al’amuran rayuwarki baki daya?” 

Post a Comment for "ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...