ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 3 by Sumayyah Abdul-kadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 3  by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 3 by Sumayyah Abdul-kadir

- - Post a Comment

 ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 3  by Sumayyah Abdul-kadir


hau jirgi mai zuwa Legas. 


Sai a wannan lokacin ne zuciyata ta soma turiri, tana kurma ihun yarda da zancen Zanirah ZAMANI YA CHANZA.... ya kamata Hajjah da ireirenta su ajiye traditional false beliefs su yarda love is a natural nature that cannot be totally eradicated. Yanzu ne na tabbatar na rasa Aliyu har abada! A lokacin da tayoyin jirginsu suka rabu da kasa. Sai na fashe da kuka a lokacin da wani bakon tunani ya bakunce ni, wato yanayin idanun Zanirah (oily eyes). 


Sau da dama Yaya Aliyu kan ce “Fa’izah ina ma kema irin kwayar idon Zanirah gare ki? Wallahi da na ji dadi na.....” 


Hawayena suka sake ninka na da.... Ga Zanirah nan complete din ta ka samu Aliyu. Hawaye na ya sake ninka na da, na kifa kaina a kafadar Ummi muka ci gaba da kukan tare. Inda wanda ya san sirrin son da nake wa Yaya Aliyu, to Ummi ce, don tare muka rayuwa a makaranta fiye da Zanirah dake Giwa a lokacin da muka mallaki hankalin kanmu. 


Babu irin tsarin da ban yiwa rayuwar aure na da Yaya Aliyu ba. Yadda za ta kasance, yadda zamu yi ta, yadda zamu gudanar da ita da yadda zamu tafiyar da ita, amma a yau Hajjah and her false beliefs (a ganina) sun rushe komai. 


Lokaci guda wata irin sabuwar zuciya ta shige ni mai dauke da sabon perception. Na san dadin ‘So”, haka na san dacin rasa shi. In Allah ya yarda ba zan yarda in auri wanda bana so ba! Ba zan yi auren zumuncin ba, ba zan yi auren A.B 

Family ba. Zan zamo mutum ta farko da za ta canza A.B Family, zan zamo mutum ta farko da za ta yi auren soyayya a cikin zuri’ar Abubakar Bamalli Giwa. 


Bare zan aura wanda zuciya da ruhina ke so da kauna, wanda zai jiyar dani dadin soyayya da zakin dake cikinta. Ko duk duniyar nan za ta taru a kaina ba zan yi auren A.B House ba sai wanda zuciyata ta aminta da shi. Nake so, yake sona da irin soyayyar da muka yiwa juna ni da Yaya Aliyu. 


36 2 2 


Yau wata guda kenan da tafiyar su Zanirah in har na lissafa dai-dai, amma babu ko duriyarsu. Aliyu dai ya yi waya wa Hajjah cewa yana bakin aiki a Ibadan, don haka ba zai samu zuwa gida karshen watan nan ba sai na sama, suna tare da amaryar a Ibadan. Uhm! Namiji kenan. In ji Umma Sulaiman Shu’aibu ‘Yan Awaki. Kudan zuma, indararon roba ta ko ina zuba kake. Allah ya gyara. Takurawar da Mansur Modibbo ke min a gida Giwa da Zaria yasa duk garuruwan suka fice min a rai. Domin dai ni tunda na rasa Yaya Aliyu bana jin zan iya wata aba wai ita soyayya nan kusa. So dai guda daya ne, na sha shi na warke, bana fatan Allah ya kara maimaita mini. Ko ina fatan hakan ba cikin garuruwan nan uku ba, Zaria, Giwa da Kaduna. He must be a stranger! Very far away!!! 


Ban gama jinyar wancan ciwon ba yake nema na da in dasa wani, “Shin shi wannan bai ma da 

tausayi ne Ummi?” Na tambayi Ummi a yammacin wata asabar. “Wai da me zan ji ne? Yeah! I would love to marry a stranger, but he must be from far..... and he’s a stranger but not from far...” 


Don haka na rika yin baya-baya da shi da kora da hali wanda ya fi kora da sanda, duk da mahaukacin son da yake min kuwa. Ba wai don yana da wata makusa ba, dukkan halayen shi ababen yabo ne. 


Ni da Ummi mun kasance cikin kewar Zanirah, kullum kamar wadanda aka yiwa mutuwa. Hajjah kanta daurewa take tana sabgoginta, amma rashin Zanirah a gidan ita ma yana dukan ta. Daga mu yi tagumi, sai mu kwanta. Mun daina barin yara su kunna T.V a gidan balle radio. Sai mu ce sun dame mu. Mun dai mai da gidan kamar gidan mutuwa, farin cikinmu ya takaita, ba Zanirah ba Aliyu. Muna cikin kewar da ba za ta misaltu ba, ko yaushe muna kwance a daki kamar tsumma. Don haka na ji dadi da Hajjah ta kawo shawarar wai mu tafi Kano gidan Yaya Rabi mu huta gajiyar baki kafin fitowar takardun karatunmu mu ci gaba da karatu. Dukkanmu ba karamin mamakin wannan magana ta ci gaba da karatu muka yi ba. Na yi tunanin ko Hajjah ta yi hakan ne don ta samu na manta da Yaya Aliyu gaba daya. Abin da ba ta sani ba shine, tuni na bude kundi na sanya Aliyu a ciki (as a past tense). Wallahi ko da zan mutu babu aure, babu huldar da za ta shiga tsakanina da mijin Zanirah (other than) ta ‘yan uwantakar da ta hada. 

Muka shirya tsaf sai Kano. Yaya Rabi mutum guda har da rabi don zumunci da son dan uwa. Zan iya cewa duk ‘ya’yan Hajjah babu wanda ya kaita kirki. Zama da ita da raha irin ta mijinta Yaya Muftahu ya wanke mana damuwa kakaf. Don sai ya zamanto Yaya Rabi ta cike mana gurbin Zanirah, Yaya Muftahu ya cike mana gurbin Yaya Aliyu. Sai muka kwantar da hankalinmu muka bude sabuwar rayuwa mai dadi. 


A irin hirarrakin da muke yi da Yaya Rabi ta kan so a Sako hirar su Zanirah, ko da wasa Yaya Rabi ba ta taba sanin mun so juna ni da Yaya Aliyu ba. Irin maganganun da take sakin baki tana fadi a kansu a gabana ya kan kona min rai ya tado wani kwantaccen ciwo da na riga na samu ya warke. 


Akwai sanda za ta ce, “Allah kadai ya san irin soyayyar da suke barzaa yana muzurai yana cewa baya so din” Ko ta ce, “Uhm! Su Zanirah ana can Ikko ana romansewa”. Ko ta ce, “A gaskiya Zanirah ta caba miji. Ga kyau ga kuma kyawun hali. Aliyu Mutum ne wanda zai shagwaba matarsa, ya bita da duk yadda yadda ta yi da shi, ba irin Bashir, Fa’iz da Mus’abu bane”. Na kan kau da kai ne kamar ban ji ta ba. Ummi ta yi dariya kawai. Haka nan ban taba tankawa ba sai Ummin. Tsakanina da Ummi yanzu mun koma mun dinke kamar da. Domin ta lura in har tana son hulda dani to fa sai ta ajiye zancen makiyina Fa’iz a gefe. Ba ta zancen Fa’iz a gabana kamar yadda duk hotunan shi da ire-iren kayan da yake aiko mata ta tattara su ta aje a wata katuwar jakar Hajjah a Giwa. Amma dai ai na ji TAKORI ta ce, 

“ZUCIYAR MUTUM, BIRNIN SA!” 


Daki guda Yaya Rabi ta ware mana mai dauke da bayan gida, kananan gadaje biyu, sai jar kilishi da ta malale ilahirin dakin da jan labulaye. Karamin bed-side fridge, sai mudubin dogon yaro mai sheki da kayan shafe-shafe da feshe-feshe, da kwabar adana suttura (wardrove) ta jikin bango. Kamar yadda mazan Kano samari da magidanta basa ganin kyawawan ‘yammata su kyale, to haka fita ta gagaremu ni da Ummi. Har suna aka sakawa gidan Aunty Rabi a layin wai Gidan Mallawa. 


Kiri-kiri muna gani za a gayyaci Yaya Rabi biki ko suna amma mu haramtawa kanmu zuwa muna ji muna gani, domin muddin muka fita, to kuwa la-shakka ba zamu dawo mu kadai ba maza basu biyo mu ba. 


Kofar gidan Yaya Muftahu baya rabo da mota da vespa, wanda mu bamu saba hakan ba sam a namu garin sai hakan ya dame mu ya zamo mana sabo ya takurawa walwalarmu. A hankali na soma fuskantar Ummi na canjawa, ta fara saurararsu. 


Da na yi mata magana sai ta yi murmushi kawai har mulmulallun kumatunta suka lotsa, ta ce, “In mun koma inda muka fito ba shi kenan ba? Abu ne na dan lokaci. Namiji abokin rayuwar mace ne ba za ta taba rabo da shi ba”. 


Cikin watanni hudu a gidan Aunty Rabi jikina ya soma wani irin canzawa, tsayina ya fito na mike sosai. Yawan kaimu (Zaynab Saloon) da Ya Rabi ke yi a (Mukhtar Mohammed Link) yasa gashina 

ya ware ya yi tsayi da taushi duk da ba (relaxing) muke ba wankewa ne da (steaming) kawai. Haskena ya dan fito duk da bani da haske. Kamannina na Mallawan usli ya fito sosai, na yi kumatu subul-subul, saboda kwanciyar hankali. Kugu da kirjina duk sun canza kiyasi, tabbacin budurwa matashiya ‘yar shekaru goma sha takwas. Shin ma na taba gaya muku ko wace ce Fa’izah Ahmad Abubakar Bamalli Giwa??? Ban taba ba, illa kawai kun jera ni a sahun kyawawan Bamalli. To eh, ba zan yi musu ba a nan, sai dai akwai wasu ‘yan bambance which I didn’t clarify (da ban farrake ba) ga masu karatu na. 


Ni kaina ban san ina da wadannan qualities din ba sai da na shiga shekara goma sha takwas da zamana a Kanon Dabo. Duka A.B Family ni kadai ce mai duhu (choculate). A yau, kaina na tsurama ido cikin mudubin dogon yaron gidan Aunty Rabi bayan fitowa ta wankan la’asar. 


Ina da madaidaicin tsayi, wato ba doguwa ba ce ni, ba kuma gajeriya ba. Doguwar fuska mai dauke da mulmulallun kumatun hutu subul dasu masu nuna bana cikin wahalar rayuwa ko kadan, wadanda Allah bai halacci kwayar kurajen (pimples) ko daya a kansu ba. Idanuwana farare sol da bakin zanen ido mai walainiya na daukar hankali. Madaidaicin baki wanda ba kankani bane can-can ba kuma kato bane, jerarrun hakora farare sol, jere reras a cikin shi. Karan hanci siriri kamar an saka ruler an daidaita mata shi a tsakanin idanunta. Tunda ya taho daga sama a mike yake bai lankwashe ba ya dire kyam saman bakinta. Tsa

gin Mallanci 2-2 dake gefen fuskar Fa’izah su suka fitar da Mallancin ta sosai da an ganta babu tambaya zuriya’ar Abubakar Giwa ce. 


Sumar kaina kan sakko har bisa kafadu, ya kwanta lamban. Wanda kitson shi kwararriyar ma sai ta hada da dabara. Duk da haka kuma cikin kwana hudu ya warware da kanshi ba tare da ta sanya kibiya ta warware shi ba. Don haka ta hakurewa kanta yin kitso kullum sai dai ta kalmashe shi cikin ribbons (bound). 


In Aunty Rabi ta daddage ne take kalbace shi yaryar ta kama bakin ta matse da dutse da roba sannan yake zama. Ba ta taba tsugunnawa wata mace ta kama mata kai da sunan kitso ba tun tasowar ta baya ga Hajjarta. Yalwar gashin kanta shi ya taimaka wajen inganta gashin ido da na girarta. Hakan bai ishe shi ba sai da ya bi ya kwanta a fatar jikinta kafataninsa. Irin wadanda Sadanis basa yiwa (halawa) ya yin aure. 


Don haka a kullum Fa’izah cikin (shower-shaving) take duk sati biyu zuwa uku don fitar da kyan fatar jikinta da kwantaccen gashi ke boyewa. Idan tana tafiya kai ka ce rangaji take, komai ya yi masha Allah, komai nata danye ne sharaf. Jikinta kamar mai shiga wankin fata a inji, domin jikinta ya fi fuskarta haske. 


Ga zazzakar murya kamar diyar Shata, Fa’izah mace ce mai tsiwa, don in ta fara tsiwarta da mitarta har hacinta tsattsafar da gumi yake yi. Ba a yi mata ta kyale. Tana da kafiya da taurin rai, ba kankanin abu ke sanyata kuka ba. Tana da wuyar lankwasuwa a kan abin da ta kudurtawa zuci

yarta. 


Watanni hudu kenan muna zaman garin Kano, ko in ce zaman jiran fitowar jarabawa, zama mai dadi da ma’ana. Hankalinmu a kwance, rayuwar baya duka ta zama tarihi, komai ya zamanto kamar bai faru ba. 


Don yanzu har na kan iya zama ayi hirar su Zanirah dani ayi dariya ba tare da na ji komai a raina ba. Zan iya cewa, soyayyar Yaya Aliyu babu ita ko kadan ta bace daga raina. 


Zamanmu da Yaya Rabi (accounter) a bakin G.T na Gyadi-Gyadi (branch) mun karu da abubuwa masu yawan gaske. Ga dai girke-girke na zamani muna koyo, kwalliya kala-kala, tattalin miji da nuna masa soyayya mai tsafta mai tafiya da ZAMANI da CHANJE-CHANJEN sa, tsafta, kissa da tarairaya, duk mun nade su cikin kanmu daga gidan Yaya Rabi. 


Wai yanzu ma kokari muke Hausar mu (accent) dinta ya yi dai-dai da na ‘yan Kano, domin masana luggogin Nigeria sun tabbatar da cewar Hausar Kano ita ce mafi karbabbiyar Hausa a Nothern Nigeria baki daya. Domin a lokuta da yawa in muna magana Yaya Rabi da Yaya Muftahu da dansu Abdul dariya suke mana, wai “Kauyawan Giwa”. Shi yasa muka yi zuciya muka koya a hankali. 


Yau lahadi, daga Yaya Rabi har Yaya Muftahu basa zuwa aiki. Mu kan kasance ne wunin ranar da yamma a shagunan Breirut Road irin su Captano, Arebian Sweets da ire-irensu, ko manyan shagunan Kano irin su Country Mall, Ado Bayero 

Mall ko Grand Square da Well-Care don yin sayayyar amfanin gida da ta kayan makulashe. 


To yau ma hakan, dawowar mu gidan kenan, muka kai ledojin hannayenmu kitchen ni da Ummi, muna adana kowanne a freezer masu bukatar firinji, muna saka su. Yaya Hauwa ta kira wayar Ya Rabi ta sanar da ita jarrabawar mu ta fito. Amma dole ana neman mu a makaranta zamu karbi ‘testimonial’ da ‘statement of result’ ko da zamu duba ‘online’ ne. 


Don haka washegari muka nufi Kaduna da direban Muftahu. Abdulrahaman ma ya saka naci sai ya bimu saboda su Junior autan Maman Kaduna mutanensa ne. Muka tattara duka Kaduna ta diba, su kuma kowanne ya nufi office a safiyar litinin kenan. 


A Jabi Road komai ya canza, tun daga bakin gate na tabbatar Baban kaduna Allah ya kara masa budi da falala hade da nasara cikin al’ amarinsa. Hyundai, Jeep-Jeep har guda uku sai neman fashewa suke yi don koshi da kyalli a harabar adana motoci. Haka korran (grass carpet) sun malale harabar gidan da furanni kala-kala masu dadin kamshi. Komai na falon ya canza sai kyalli yake yi. Ita kanta Mama ta kara kirbewa dama ga ta masha Allah tun-tuni, kamar za ta tsage cikin (sofa-bed). Kai! Wadannan mutane suna cikin daular da babu wani cikin A.B Family dake cikin rabinta. 


Na girgiza kai tare da sallama, da gudu na karasa jikin Mama a (sofa-bed) muka rungume juna domin mun jima bamu hadu ba, tun bikin Zani

rah, ga kuma soyayya mai karfi tun fil’azal wadda ta zarta ta jini kawai, har ma da haduwar jini da Allah ya hada a tsakaninmu. 


Mama ta ce, “Oh! Su Fa’izah an gudu Kano don ba Zanirah ko duriyarku ba a ji, ko waya babu, kun kyauta kenan?” 


Na ce, “Kin san Baban ABU ya hanamu rike waya Mama, kuma na je ne don na huta na samu nutsuwa. Amma wallahi Mama kullum kina raina”. 


Ta ce, “Na sani, na kuma yarda Fa’izah”. Ta dubi Ummi ta ce, “Sai tsohuwa!” 


Ummi ta shagwargwabe fuska ta ce, “Allah Mama ki bari...” 


Muka sa mata dariya ganin yadda ta yi da fuska kamar za ta barke da kuka. Mama ta ce, “Mutuminki kullum ya yo waya korafinsa daya, yaushe za ki baro Kano? Yau dai ga Ummi a gidan nan, anjima zai yo waya bakina ya huta cewa, ban sani ba”. 


Cikin matsananciyar murna Ummi ta makalkale Mama tana dariya kamar ba surukar ba, ta ce, “Allah da gaske Mama Ya Fa’iz na tambaya ta? Don Allah Mama ya muryarshi ta koma? Ban taba magana da shi a waya ba tunda ya tafi”. Mama ta ce, “Muryar Fa’izu ta karye (kwatakwata) da Ukrainian language da Belarusian. Da kyar nake fahimtar Hausar shi. Su Shu’aibu ba ma sa ganewa gara ma in yana Larabci ko Turanci”. 


Ummi ta yi zugum (her passion for him heightened). Tana duban Mama hannuwa tallabe da 

fuska ta ce, “Kin san Allah Mama, na yi dana sani tunda fari da na san haka ne da na shiga Arabic Club da Fa’iza tayi-tayi dani in shiga a makaranta na ki, don a ganina yawa ne in tsaya koyon Larabci tunda ba a fiya amfani da shi a nan Nigeria ba”. 


Mama ta ce, “Ayya! Kin yi babban kuskure, domin Larabci shine harshe mafi soyuwa a wurin Ubangiji da ya zabe shi a cikin harsunan duniya ya saukar da Alkur’ani da shi. Har yake cewa, “An saukar da shi Alkur’ani BALARABE....” Kuma Annabi (S.A.W) ya ce, “Ku so harshen Larabci saboda uku. Na daya ni Balarabe ne, na biyu Alkur’ani Balarabe ne. Na uku harshen ‘yan Aljanna shine LARABCI!” 


Ummi kamar ta fashe da kuka, na yi dariyar mugunta na ce, “Rabu da ita Mama, ba zan taba manta sanda su Ummi suke min dariya don ina Alifun Ba’un ba. Wahid-Ithna-thalatha ban iya 123 da ABCD ba, ga shi na muku wayo. 


An ce ana jifan tsuntsu biyu da dutse daya, don a ci amfaninsa. Yau Ummi Turancin me za ku nuna min? Sai dai in nuna muku LARABCT”. Na yi mata gwalo. 


Ummi ta yi zugum, da alama kalma ta kare a bakinta. Na yi dariya mai isata har cikina ya kulle. Ummi ta zo iya wuya ta tashi ta fice daga dakin, muka ci gaba da yi mata dariya. 


Mama ta ce, “Sai yaushe za ku je wa Hassanar ku ne?” Tana nufin Zanirah. 


Na ce, “Kai-kai! Mama so soon haka? Ai ba a zuwa gidan amare sabon aure sai sun haihu’”. 

Mama ta lakace min hanci ta ce, “Ai su da yake sun damu daku zuwan su uku duk kuna Kano. Ba kuma don kowa suka zo ba sai don su ganku”. 


Na ce, “A’a Mama, da da gaske sun damu damu da sun bimu inda muke. In babu jirgi akwai mota, tsakanin Kaduna da Kano awa biyu ne kacal. Ke dai basu gama amarci bane ma je suna in da rabo”. 


Mama ta ce, “Kamar mai gani har hanji an zo ana ta laulayin ciki kamar wadanda suka yi tuntube da shi a dokin kofa. Ku yaran yanzu ko kadan cannot excercise patience. Mu zamanin mu sai amarya ta shekara biyar dakin miji ba ta samu ciki ba”. 


Duk da zuciyata ta dan sosu ban bari Mama ta gane ba. In Aliyu bai son Zanirah, ai ita Zanirah tana mutuwar son shi. Za ta san duk hanyar da ta bi ta janyo hankalin abinta gare ta. Sai na samu kaina a yau ina mai dan KISHIN Zanirah Mukhtar Abubakar Bamalli Giwa! 


Karfe tara na dare duka al’ummar gidan na bisa tebir suna cin abincin dare, har mu da muka bakunci gidan. Da tuwon laushi miyar alayyahu da aka wadata da naman Turkey (talo-talo) aka kuma shirbine ta da man shanu dan asalin GIWA. Na lura Abdul zubi kawai yake ba kakkautawa, ban san sanda na yi dariya ba. Yahya mai bin Fa’iz ya ce, “Kalau kike dariya ke kadai?” 


Na ce, “Baka ganin yadda yaro ya samu abincin zage-zagi ya rude baya so ya bari ya fara hadiye na bakinsa kafin ya kara loma?”’ 


Abdul ya yi murmushi, ya san da shi nake. Can 

kuma ya ce, “Yanzu ba zan ce miki komi ba sai mun koma Kano kina cin bandashe (gurasa da kuli-kuli) tukunna”. Kowa yasa dariya. 


Daga daki Mama ta fito tana fadin “Ku yi sauri Fa’izah, cin abincin ne kuma ya koma hira da shewa? Aiken ku zan yi unguwar Sarki ku amso min ankon ‘yar Hajiya Saratu da kun gama, dare yana yi’. 


Karar wayar landline dake gefe ya sanya kowannensu yin wurgi da cokalinsa ya nufi inda wayar take, kokawa fa ta kaure domin Ummi, Yahya, Shu’aib da Junior kowanne ya ci alwashin shi zai fara daukar wayar ko ta halin kaka. 


Mama ta ce, “Yau ina ganin sakarci, to bari in raba gardamar nan. Duk cikinku babu mai tabbacin kiran nasa ne ko ba nasa bane, tsammani kuke Fa’izu ne, kuma ba lallai ya tabbata shi din bane haka ne?” 


Duk suka tsaya suna tsuma, ta ‘kauna’ da ‘doki. “Don haka ke babbar Yaya (ta nuno ni) dauki wayar ki jiye mana waye kamin wani ya dauka don a raba gardamar”’. 


Na yi dariya cikin ginshira na tsiyaya ruwan FARO mai sanyi a tambulan na soma kwankwada. Sanyin ruwan na sanyaya makogarona, yana taimakawa wajen digesting (narkewar) daddadan tuwon da na ci. Na yagi tishu na goge baki da hannu. 


Ummi ta kufula ta ce, “Kina gani fa Mama sai ta gama yi mana yanga”’. 


Mama ta ce, “Kai, dadina dake gajen hakuri Ummi”. 

Na yi murmushin tura haushi sannan na mike na nufi wayar landline da har lokacin ba’a bar kira tana tsinkewa ba, wayar na daga na amsa da “Assalamu Alaykum!” 


Shiru kake ji, ga shi da alama ba a ajiye ba. “Hello!” Shima shiru. Na sake sallama aka yi shiru, ina shirin mikawa Mama wayar cikin kufula da mamakin wannan ikon Allah, ka kira waya kuma ka yi shiru kudinka na tafiya a banza. Muryar mai cike da ginshira ke tambayar “Impertinence Fa’izah ko?” (Fa’izah mai tsiwa?). culating dinshi ga sassan jiki sun tsaya cak! Da ba da aiki. Jijiyoyin cikin kai masu ba da doka da oda su ma sun yi yajin aiki na (temporary). Muryar da ba zan taba mantawa da ita ba, muryar dan uwa amma MAKIYI. Muryar FA’EEZ, HAFIZIN HAJJAH, FA’IZU MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA. 


Ban amsa ba. “Kaif halikum Fa’izah? How are you Fa’izah?” Maimakon na amsa sai na yi azamar cire wayar daga kunnena na mikawa Ummi jin wani mugun fushi ya taso min wanda duk kokarin zuciya ba za ta iya boye shi a gaban kowa ba, including UWA-MAHAIFIYA dake gabana tana karanta duk wani motion dina a kan wayar danta da kyawawan idanunta, masu cike da matsananciyar kauna gare ni. Irin kaunar nan da baki baya iya bayyana ta, domin Allah ne ke assasa ta. 


Sai na zare wayar sannu a hankali daga kunnena na mikawa Ummi, tare da zare jikina daga 

cikinsu na yi dakin Mama don bakin ciki kamar in rushe da kuka. 


In da abin da na tsana a duniya to abin da zai tuna mani da shekarun da na kasance cikin fargaba da ukubar Yaya Fa’iz ne. Balle ya tuna min da shi kansa. To gaba daya yau muryarsa na ji a cikin kunnuwana, muryarshi ta dawo min da ranakun can baya marasa dadi da na rufe babin su ta dawo da tsanarsa danya a zuciyata. 


Haka na yi sallar isha ina ta sake-sake. Da na idar na bishi da muguwar addu’ar Allah ya gama shi da masifar duniya da ta lahira a can inda yake. Yasa a fatattako shi daga karatun ko garin tukin jirgin, jirgin ya fado ya ragargaje da shi. Amin summa amin. Don kam hakika ni mai bakin ciki ce da duk wani ci gaban FA’IZ GIWA kamar yadda yake a gare shi shima. 


A daren Ummi hanani barci ta yi da labarin hirarta da Fa’iz. Da hanzari na taka mata birki.... “Excuse me please. Shin Ummi ina ruwa na ne? Me ya shalle ni cikin wannan al’amarin naki? A duk lokacin da za ki yi hira, ki yi wadda ta shafe ni ban da ta Fa’iz! Na tsani Fa’iz!! Na tsani duk wani abu da ya shafe shi ban da iyayen da suka haife shi da ‘yan uwansa wannan (Individualistic matter) ne (sha’anin mutum daya). A duniya bani da abin ki, abin tsana, abin neman tsari da kariya daga sharrin sa bayan shaidan, sai Fa’ezz Bamalli’”. 


ok 6 6K 


Washe gari karfe goma na safe Queen Amina 

College ta yi mana, inda muka hadu da malamanmu da muka jima bamu gani ba. ALHAMDULILLAH, takarduna sunyi kyau har fiye da na Ummi, na tashi da Credentials a gaba dayan ( 9 Subjects) dina. Ummi tana da seven credits, sai dai tana da A a Fine-Art. 


A shekarar duka muka samu gurbi a jami’a, inda Yaya Aliyu ya samarwa Zanirah gurbi a jami’ar Lagos (UNILAG), inda za ta karanci likitanci (Medicine). Daga Baba na har mahaifin Ummi babu wanda bai yi mamaki da umarnin Hajjah ba na ta amince a nema mana gurbi a jami’ar Bayero ni da Ummi mu koma Kano da zama wajan Aunty Rabi, sai hutun karshen kowanne zango ta amince mu je Giwa da sauran garuruwan Zaria ko Kaduna. 


Yaya Muftahu shi ya shiga ya fita ya samar mana gurbi a fannin da kowacce take so, inda aka bani B.A Arabic, Ummi kuwa B.A Hausa. Duka a Faculty daya wato (FAIS) sai dai tsangaya (Department) da suka bambanta. 


BAYERO UNIVERSITY KANO Rayuwar mu cikin jami’ar Bayero, sabuwar rayuwa ce a garemu da ta zo da sabon salo irin na kowanne JJC (Joiny Just Come) a jami’a. Abubuwa da yawa (which are normal) ga sauran daliban jami’ar (is abnormal to us), irin su shan hannu da maza da wasu matan marasa kamun kai ke yi da sunan jami’anci, shan taba sigari da samari da matasa ke yi wanda ba a yi sam a A.B Estate. Shan lemo a shago a tsaye ga matan aure 

Post a Comment for "ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 3 by Sumayyah Abdul-kadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...