ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 2 by Sumayyah Abdul-kadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 2  by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 2 by Sumayyah Abdul-kadir

- - Post a Comment

 ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 2  by Sumayyah Abdul-kadir
Malam Hassan. Ina jama’ar gidan suka tafi ne? Mantawa aka yi yau muke graduating? Babu wanda ya je mana daga Giwa, Zaria har nan cikin Kaduna?” 


Ya ce, “Hala mantawa kuka yi yau ake daurin auren Zanirah da Alh. Aliyu???” 


Wallahi baya ga wannan ban sake jin komai ba, ban sake sanin inda kaina yake ba. Sai tsintar kaina na yi a asibitin Jinya dake cikin garin Kaduna, Ummi na gefen kaina tana mini firfita. Na soma kokarin tuno abin da na ji (DAURIN AUREN ZANIRA DA ALTYU). 


Na fashe da wani gursheken kuka a cinyar Ummi, ita ma Ummi kuka take, na tabbata kukan tausaya mana ne ni da Yaya Aliyu, cewa take “Ya aka yi haka Fa’izah? Garin ya ya ni ban san zancen ba? 

Ya ya aka yi haka? Na dauka ke za a baiwa Yaya Aliyu?” 


Na mike zumbur ina layi na ce, “Ummi ya zama dole in je Giwa a yanzun nan, dole ne in je Giwa kada Zanira ta dauka ina bakin cikin auren ta da Yaya Aliyu ne, ta wuce haka a gareni, tashi mu tafi Ummi”. 


Ummi ta share hawaye ta mike, halin da nake ciki ne yasa ban bambance motar suwa muka shiga zuwa Giwa ba, ashe motar Yariman Zazzau ne Mansur Modibbo wanda ke biye damu da abokinsa tun daga Queen Amina har Jabi Road. A kan idonsu na fadi, kuma su suka kawo ni asibiti tare da Ummi. 


A hanyar mu ta zuwa Giwa Mansur ya ce, “Shin wace ce ita wannan Zanirah da labarin aurenta ke sumar da Fa’izah yake sanya Ummi kuka?” Maganar tashi sai ta bamu dariya har ni da ke cikin hali na kaka-ni-kayin zuciya. Ummi ta ce, “Duk wani bayani da zan yi maka a yanzu ranka ya dade ba za ka fahimta ba, Zanirah is our bloody sister’. Ya ce, “To na hakura da jin wace ce real Zanirah sai na dawo. Ni dai fatana Ummi don Allah ki rinka shigar dani kin ji? In na kai ku yanzu juyowa zan yi Sai sati mai zuwa zan dawo, saboda zan yi tafiya zuwa Abia State na san kafin lokacin Fa’izah ta dawo normal!” 


Ni kam kallon shi ma ban yi ba fuskata na cikin cinyoyina, tunda na rasa Yaya Aliyu babu abin da zan nema a wani Da namiji, domin ko kusa ba zan samu mai hali abin so da irin kyakkyawar zuciyarsa ba. It’s indeed a great loss! Addu’a nake a 

cikin zuciyata, “Ya Allah ka sanya min hakuri da dangana, ka bani juriya da karfin zuciyar fitar da Yaya Aliyu Haidar daga Zuciyata”. 


Dai-daikun jama’ar da na gani a harabar A.B Estate ya tabbatar min har an gama daurin auren Zanirah da Yaya Aliyu! Wayyo Allah ni Fa’izah na rasa Yaya Aliyu kenan, tabbas na rasa shin, na hakura har ga Allah daga yau na bar wa Zanirah Yaya Aliyu. 


Sunan Allah Ya zuljalali wal ikrami nake taunawa a harshe da hakorina. Babu shakka zuciyata ta yi sanyi illa jikina dake faman karkarwa, amma a kan fuskata farin ciki ne bayyananne. Ni kadai na yi sallama falon Hajjah domin na baro Ummi waje tare da su Mansur Modibbo wanda su da gaske suke neman iri suka zo gidan Bamalli. Lallai iska na wahalar da mai kayan kara (na fada cikin raina). 


Gaba dayansu ‘ya’yan Hajja Hadiza su goma sha biyar in ka dauke Yaya Rabi auta dake Kano, Baba Muntari, Baba Na’ibi, Baba Ibrahim, Baba Barau, Baba Sadi, Baba Sani, Baba Salisu da su Yaya Hauwa, maza goma mata hudu kenan, duka zaune falon Hajjah wanda yake makeken gaske suna tattaunawa ko a kan mene ne oho! 


Na tsugunna na gaida su daya bayan daya. Hajjah ta ce, “Yar albarka, kuna raina wallahi, yanzu nake cewa a je a dauko ku don ita kanta amaryar yanzu ta shigo daga tata makarantar?” 


Ni dai na ce, “Uhm! A raina na ce, ‘dole ki ce min ‘yar albarka mana tunda kin san yankan bayan da kika yi min, kin barni da cizon yatsa.... 

ai dole kisa min albarka!’ 


Amma a fili sai na ce, “Wallahi kuwa mun yi mamakin rashin zuwa kowa, sai da muka je Jabi Road, Malam Hassan ke gaya mana daurin auren Yaya Aliyu da Zanirah ake yi, shi yasa ma bamu damu sosai ba muka taho da kanmu kawai”. 


Na mikawa Babana kyaututtukan da na samu cikin ledar Ghana must go da cheque din kudaden da na samu. Su Baba suka shiga dubawa suna kwararamin albarka tun karfinsu. Sai dai duk abin nan da ake na lura Yaya Hauwa na hankalce da duk motsina da na jajayen idanuwana, tana bina da kallon tausayi da karfafa gwiwa. 


Fuskarta cike da tausayi ta ce, ““Fa’izah duk wannan ramar ta mecece?” Ta fada tana taba kasusuwan wuya da suka bullutso min da hannun damanta. 


Na yi murmushi na ce, “Kai Ya Hauwa kin manta daga kurkukun jarabawa na fito?” 


Ta yi murmushi kawai irin nasu na manya. 


Ba zato Baba Na’ ibi ya ce, “Na yi zaton Fa’izah ce za ta zamo matar Aliyu?” 


Duk sai kowa ya yi tsit, yana mai jinjina maganar. Sai Hajjah ta bude baki a hankali ta ce, “Na’ibi!” Ya dago ya dube ta cikin amsawa. A nutsenta ta ce, “Ta ina Fa’iza ta dace da Aliyu?” Baba Na’ibi a dan daburce ya ce, “Ban gane ba Hajjah?” 


Ta yi murmushi ta ce, “Abin nufi a nan, shin Fa’izah ba mace ce mai tsiwa, taurin rai, ginshira, dagewa bisa duk abin da ta kudurtawa ranta (dertermination) kekasasshiyar zuciya a kan duk abin 

da ta tsana ko mutumin da ta tsana ko halayyarsa. So wanda ya wuce hankali ga duk abin da take so? Shin Aliyu da Zanirah ba mutane ne masu sanyin rai ba da saukin zuciya? 


Saboda haka sun dace da juna, za su zauna da juna lafiya, za su ji dadin zama da juna babu hayagaga. Amma halayen Fa’izah ba kowanne namiji ne zai iya zama da ita ba sai NAMIJIN DUNIYA, mai halaye irin nata ba mai sanyin rai irin Aliyu ba. Ma’abocin juriya da karfin jiki da na zuciya baki daya. 


Amma in an hada Aliyu mai sanyi da Fa’izah mai tsiwa da jumurda, bakwa tunanin Fa’izah ce za ta zama mijin, Aliyu ya zama matar saboda matsanancin son da yake mata? Wato ya zamo sai yadda ta yi da shi kenan saboda gudun fitinarta da bacin ranta? Kasancewar shi mutumin da bai son tashin hankali da hayagaga ko kankani? 


Kuna gani fa tun yanzu duk abin da Fa’izah ta gindaya mishi baya iya tsallakewa duk ya lalace a gindinta, bini-bini yana binta kamar bita-zai-zai wace kalar rayuwa kuke tunanin za su shimfida a gidan auren su? Baya iya musa abin da ta ce, baya iya tsawata mata in ta yi ba dai-dai ba, tun suna yara nake hankalce dasu. 


Ina rayuwar aure za ta yiwu tsakaninsu ba tare da raini ya shiga tsakani ba? Aliyu da Zanirah kuwa da wuya za a ji kansu, za ku ga irin rayuwar da za suyi ta namijin da ya isa da gidansa, za ku ce dama na gaya muku ne”. 


Gaba daya suka yi shiru suna masu jinjina maganar, haka nima ina mai gaskata kowacce kalama a 

cikin zancenta. Tuni na gane hikimar hada auren Zanirah da Aliyu da tsohuwar mai tarin hikima da fasaha ta yi. Wato muddin na auri Yaya Aliyu ba zai iya lankwasa ni ba ko kadan, saboda matsanancin son da yake min. Tana masa gudun zama mijin ta-ce ne kawai gara ta ba shi wadda zai iya da ita don son zamar da shi mai kima da karfi a gidansa. 


Amma Zanirah halinsu daya (simple personality) wadda ba ta zafafawa cikin al’amuranta. Tabbas halayen Zanirah baki daya irin na Yaya Aliyu ne, hakuri, sanyin rai da sanyin zuciya. Abin da babba ya hango yaro ko ya hau ganuwa da Dala da Gwauron Duste ba zai hango ba. 


Sai dai ta wani bangaren Hajja ta yi (underestimating) dina. Ni ina son Yaya Aliyu ne saboda kirkinshi, halayensa da mutuncinsa da son addini. Ban taba tunanin in yi amfani da son da yake mini in mun yi aure in mai da shi sahoramin miji ba (mijin-ta-ce). 


Sai na bude baki a gaban Babannina duka na ce, ‘“Hajjah kina da gaskiya. A da kam mun so juna da Yaya Aliyu so ba na wasa ba. Sai dai daga yau wallahi na hakura, na barma Zanirah da zuciya daya, zan kuma ci gaba da binsu da kyakkyawar addu’a Allah ya karkatar da son da yake mini kanta. Ban ga laifin ki ba Hajjah, Allah ya basu zaman lafiya.....” 


Hawayen da suka shimfido min su suka sanya na mike na yi daki aguje ina kuka wiwi. Yaya Hauwa ta taso za ta biyo ni ta rarrashe ni amma Hajjah ta ce ta kyale ni kawai in yi kukan zuciy

ata za ta yi min sanyi, kukan sabo ne da fitar SO. Na ci kuka na a gado na share hawaye, na jiyo zubar ruwa a (toilet) wanda ya tabbatar min Zanirah wanka take yi. Idona ya kai ga abin da na jima ina fakon Zanirah don in dauka sai yau na hange shi cikin kwabar kayanta wato ‘DIARY’ dinta. Na yi hamzarin daukowa ban yi nawa ba wajen bude shafin farko. Kwanan watan ya nuna Zanirah ta yi rubutun nan ne tun muna JSS (karamar sakandire). 


“Ban san abin da ke damuna ba, amma kamar son Yaya Aliyu nake in na yi la’akari da yawan tunaninsa da nake da mafarkinsa cikin barcina, da kwadaituwa da son ganinsa akai-akai. Me kenen hakan ke nufi? 


Sai na shiga bude sauran shafukan a gurguje. Duk yawanci abin da ya shafi kuruciyarmu ne. Sai wani da ya dauki hankalina wanda kwanan watan ya tabbatar min Zanirah ta yi rubutun ne ranar 10/10 wato ranar da muka je Area One ni da ita (Zaria). 


“Dole ne in yi jihadin fitar da Yaya Aliyu a raina, domin ina son shi ne a yayin da na fahimci zuciyarsa, rayuwarsa, ruhinsa da gangar jikinsa sunyi nisa a soyayyar ‘yar’uwata (Fa’izah.) Fa’izah da zumunci basu cancanci in yi tarayya dasu a son komai a duniya ba. Yadda nake son Fa’izah bana son abin da zai sosa ranta. Na tabbatar da Fa’izah ta san ina begen Yaya Aliyu, babu abin da zai hana ta bar mini.... zan ci gaba 

da lallamin zuciyata har sai ta mance da Yaya Aliyu.... in har Fa’izah za ta iya yi min wannan halacci ni me zai hana na kasa? In anyi duniya don Rasulillahi daga yau na cire son Aliyu a raina domin Fa’ izah.......” 


Da na kawo nan sai na rushe da kuka sosai, hawaye na zuba a kan littafin. Dai-dai lokacin da Zanirah ta bude kofar toilet ta fito, kukan da ta tarar dani ina yi ya kara tsuma raunanniyar zuciyarta. 


Ta tsuguna nan a bakin kofar ta shiga rera kuka ita ma, muka taru muka yi ta yi kamar akuyoyi. Cikin gunjin kuka Zanirah ta ce, “Fa’izah ki yafe Ni...... wallahi ban ci amanarki ba.... Ban taba sanin Yaya Aliyu ne mijin da za a daura mana aure ba..... da na san shine wallahi da na bar garin da in zauna in ga wannan rana.... wallahi ban san cewa Yaya Aliyu bane ban sani ba Fa’ izah.... ban san za a daura ba.....” 


Na mike da azama da sassarfa na isa ga Zaniraha muka rungume juna muka ci gaba da rusa kuka tare ba mai jin na wani. 


Na ce, “‘Zanirah kada ki ce haka, (waman qaddarralahu haqqan qadrihi.) Kada ki kara fadin haka Zanira, ban taba zargin ki da wannan ba, mune muka yi kuskure, kuskurenmu ne ni da Yaya Aliyu da muka yarjewa zuciyoyinmu muka basu fili a kan abin da suke so, alhalin muna da masaniyar ko in ce mun kwana da sanin cewa babu auren soyayya a zuri’ar A.B muka bi ta kai muka take. So we are to be liable for the out

come, ban zarge ki ba ko kadan Zanirah. Baki da wani laifi, babu wata amanata da kika ci. Addu’ ata da fatana Allah ya karkato da son da Yaya Aliyu ke mini da wanda nake masa kanki, ya baku zuri’a dayyaba... Ya bani miji kamar naki Zaneerah...!” 


KKK 


Yaya Aliyu bai tashi zuwa Giwa ba sai karshen wata kamar yadda ya saba, wanda ya yi dai-dai da sati biyu kenan daurin auren shi. 


Tun daga gidan mahaifinsa, mahaifinshi Baba Na’ ibi ya kira shi ya yi masa gamsasshen bayani. Ya kara zancensa da cewa, “Aliyu ka bi Hajjah da duk yadda take so in har kana so ka taimakemu mu rabu da ita lafiya. Hajjah mahaifiyarmu ce da ta tsuguna ta haife mu daya bayan daya. Bamu da ikon bijirewa tsarinta da mahaifinmu Allah ya ji kan rai ya dorata a kai, ka sanyawa zuciyarka hakuri da dangana tamkar kowane Da cikin gidan nan da ka budi ido ka gani. 


Domin a yadda Hajjah ta dage a kan auren nan naka da Zanirah, ta kuma kawo hujjojinta masu ma’ana mu kanmu mun ga gaskiyarta mun mika mata goyon bayanmu wanda a baya bamu bayar ba. 


Ta sanya tariya sati biyu masu zuwa, na biya sadaki dubu sittin, ga lefe kuma da Babanka Ibrahim ya yi maka, su Hauwa ya tura Kano suka hado komai, gobe in Allah ya kaimu za su Zaria (gidanmu kenan). Don Babana ne alwalin Za

neerah.” 


Aliyu Na’ibi a zaune yake bisa kilishi dai-dai kafafun mahaifinsa, amma sai ga shi tsaye gaban Baba Na’ibi ba tare da ya san lokacin da ya yunkura ya mike tsayen ba. 


Wani kakkauran gumi ya wanke shi daga kwanyar kansa har zuwa yatsar kafarsa. Ya bude baki zai yi magana yawu ya kafe kat, a bakinshi. Bakin ya bushe fayau! Iyaka kokari Ali ya yi wurin tattaro kalma daga can_ kasan makoshinsa...... 


“Don me kuka yi min haka Baba?” 


Da karsashi da tausayin da ake son boyewa Karfi da yaji ya ce, “Don mun isa daku dukkanku”. Aliyu ya ce, “Bana son Zanirah da irin soyayyar da kuke nufinmu da ita, ban taba sonta da aure ba Baba”. 


Baba Na’ibi ya mike tsaye idanunshi tinjim da kwallah ya ce, “Aliyu babu bambanci tsakanin Zanirah da Fa’izah, abin da ya yi Fa’izah shi ya yi Zanirah. Uwar da ta haifi uban Fa’izah ita ta haifi uban Zanirah. Tare suka taso tun suna kanana, komai nasu iri daya ne sai a halayya da suka bambanta. Ka yi hakuri ka jure sauyin da Allah ya yi maka ka yi koyi da mai sunanka”. 


Ya ce, “Matsalata Baba ba zan iya daina son Fa’izah ba.....” 


Sai a wannan lokacin hawaye suka sakko bisa kundukukinsa. 


Baba Na’ibi cikin dimuwar wai yau Aliyu ke kuka a gabansa, kukan ma a kan mace. Sai ya ce a harkuze, 

“To Aliyu ka yi yadda kake so, ka yi duk abin da kake ganin shine dai-dai, tunda mu bamu san daidai ba. Sai dai ina tabbatar maka da abu uku, na daya muddin ka wulakanta Zanirah sai Allah ya saka mata, domin ita ma yadda ka tsinci al’amarin haka ta tsince shi bakin iyayenta. 


Na biyu muddin ka tsinka igiyoyin nan guda uku da muka damka maka sai dai ka nemi wasu iyayen amma ba cikin zuri’ar A.B ba. Na uku muddin ka dagawa gyatumar mu hankali tsakanina da kai sai Allah ya bi min kadina na haifar ka da na yi na raine ka har ka yi girman da za ka soka wa uwata tsinke cikin idanu”. 


Hawayen Aliyu na zuba ya ce, “Ta ya ya Baba za a daki mutum sannan a hana shi kuka?” 


Baba Na’ibi ya ce, “Har karya shi za ayi a ce in ya yi nishi Allah ya isa! Na dai gaya maka daga yau babu sauran wata hulda tsakaninka da Fa’izah sai ta ‘yan’uwantaka. Zanirah kuma idan ka wulakanta ta don kanka, sai dai a kullum kake tunawa ita ma ba ta taba cewa tana sonka ba dole a kai mata. Amma da yake ita mai biyayya ce ba ta dagawa ubanta hakarkari kamar yadda ka daga min ba’. 


Haka ya fice daga dakin Baban cikin mummunan yanayi da ba zai misaltu ba. A take ya zari mota ya bar garin kwata-kwata ya koma inda ya fito (Ikko), fadi yake kamar zararre, “Ku rike amaryarku can bana so...... Ta ya ma Za ayi na auri Zanirah?” 


Gidan babban amininshi Isa Kaita ya aje motarshi. Isa ya kai shi filin jirgi ya bi jirgi zuwa La

gos. Mu muna can dakinmu na ‘yammatan gidan muna jiran ango ya shigo ya bamu kudin alibidi da lancin din da zamu yi a Zaria da Walima a gidan Baban A.B.U. Labari ya iske mu ai Yaya Aliyun ya zo ya kuma koma Lagos ba tare da ya kwana ba ma. 


Ban da salati ba abin da Hajjah ke yi tana fadin “Zai ZO ya same ta”. Amarya Zanirah ta yi kamar ba ta san ma me ake cewa ba, ta yi bakam. Ta dauki remote ta karo sautin wakokin yaran Larabawa na (Ad-difl - wal-bahr). 


A take na gano matsalar Yayan namu, wato ya ji labarin wannan rikitaccen al’amari na Hajjah. Ni kam da na mai da al’amurana ga Allah da addu’a, nafilfili dare da rana da addu’o’i na musamman cewa, in soyayyar Aliyu ba alkairi ba ce a gareni Allah ya sanya min hakuri da dangana, ya yi min zabin alkhairi mafi kyau, domin zabinsa shine zabi. Abin da nake maimaitawa kenan cikin sujjada ta a ko da yaushe. 


Tuni nake da tabbacin Ubangijin nan maji rokon bayinsa ya amsa mini, zuciyata sarai, duk wani duhu da kunci sun gushe. Babu abin da zuciyata ke kwadayi kamar ganin daidaituwar auren Zanirah da Aliyu. Na kudurtawa zuciyata zan yi amfani da mahaukacin son da yake min in ciyo galabarshi a kan Zanirah. 


Na dauki wayar Hajjah na yi kofar gida can inda babu kowa tsakanin motoci, na danna lambobin Yaya Aliyu wadanda tuni na haddace su. A washegari kenan da tafiyar shi. 

Ta yi ringing har bakwai bai daga ba. Kafin ya daga a fusace a na takwas, “Wai wane ne? Mene ne?” 


Wani sanyi da ya ratsa zuciyata ya tabbatar min har yanzu ina son Aliyuna, na kasa magana. So shu’umi ya rugurguza duk wata kalma ta bakina. Aliyu ya sake cewa, “Hello! In ba wani abu ba kuma sako bane zan ajiye ina sauri zan tafi Ibadan ne”. 


Cikin jarumta na ce, “Yaya Aliyu, kana da ikon zuwa Ilorin, Abeakuta, Benue da Akwa-Ibom ma amma bayan ka zo ka dauki Zanirah kun tafi tare. Ni wannan wane irin so ne da kake neman lika min kashin kaji cikin ‘yan’uwa? Yanzu kowa ya bude baki cewa yake, “Aliyu ya ki Zanirah ne domin Fa’izah”’. 


To muddin son da kake ikirarin kana yi min na gaskiya ne ba kuma ka kaunar tashin hankali na da kasancewata cikin zargin jama’a, to ka dawo ka tafi da matarka yau ko gobe. Ko da baka son Zanirah ba haka ne hanyar da za ka nuna ba Yaya Aliyu. Wannan hanyar da ka bi ka nuna cewa ka ki bin abin da iyayenmu ke son ka da shi ne. Ka yi butulci ga alkhairin da suke hango mana ta hakan. 


In kuma don ka batawa Zanirah rai ne ka yi hakan, wallahi Zanirah baka gabanta, harkokin gabanta take. Dakacen auren take yi, sai don ba yadda za ta yi ne. Ni din dai nice cikin damuwa..... tunda ni dangi za su tsana, ni zan shiga bakin duniya...!” 


Da fadin hakan na kashe wayar baki daya ba tare 

da na tsaya sauraron amsar da zai bani ba, wadda na tabbatar ba shi da ita din. 


kK 


To Ali kam ya nuna ya haifu cikin uwarshi Zainabu, da ubanshi Na’ibi, kuma mai son farin cikin Fa’izah. A washegari ya dawo Giwa, inda ya saki kudi aka yi shagulgulan al’adarmu namu na Mallawa. Ya nuna tamkar komi bai faru ba, kamar Zanirah zabin shi ce ba zabin iyaye ba. Amma zuciyar ta fi duhun dare duhu. Babu yadda ya iya fadan da ya fi karfin ka aka ce sai ka mai da shi wasa. Iyayen nan bashi da saman su, Hajjar nan ta fi karfin komi a garemu in har muna da iko, in har bamu da shi, zamu yi iya kokarinmu mu nemo masu shi suyi mata. 


Sai dai abu ne da har illa masha Allahu ba zai taba kankaruwa daga zuciyarsa ba wato SON FA’IZAH! In ka ga ramar da Yaya Aliyu ya yi kamar wanda ya taso daga gadon asibiti bayan doguwar jinya. Jirgin karfe taran dare aka ajiye za su bi zuwa Lagos. 


Aliyu ya dubi Hajjah ya ce, “Tunda har anyi mai wuyar Hajjah, ba a bari in koma ni kadai in shirya in dawo in dauke ta? In gyara muhallina daga na saurayi zuwa na mai iyali. Saurin da gaggawar na mene ne? Cikin abokan aikina duka babu wanda na sanar mawa na yi aure kawai sai a ganni da mata kamar na sato ta? Yanzu haka a tsakiyar aiki nake zuwa Ibadan a bani lokaci ko da sati daya ne in je in dawo don Allah.....” Hajjah goyon Mahillah diyar Baba Barau take a 

bayanta ba ta ko dube shi ba. Ta sunkuci fidarta dake shake da cereal ta yi daki tana bambamin fada har da kumfar baki. Ta ce, “Karewar gyaran gida mai da gidan fadar shugaban kasa. Karewar rashin so Aliyu sayar da kan Zanirah garin Yarabawa. Amma kafarka-kafar Zannura”’. 


Aliyu ya yi tsit! Na fashe da dariya, Zanirah ko tsabar takaicin yadda Hajja ke mai da ta matar cushe kamar jakar da ta rasa miji na san shi yasa ta zub da kwalla. 


Kamar za ta fashe da kuka ta ce, “Ni dai gaskiya Hajjah ki daina ce mun Zannura.....” 


Hajjah ta ce, “Zannuraini an fada, ainahin sunanki kenan (ma’abociyar haske biyu)”’. Zanirah ta zumburi baki ta ce, “Hajjah Zunnuraini sunan namiji ne (Usman kenan)”. 


Hajjah ta ce, “Allah ya bamu albarkacinsa. Abin da yasa na saka miki suna Zannura saboda an haife ki Ranar Arfah, kuma kwanan watan ya yi daidai da ranar da Najeriya ta karbi ‘yancin kanta daga hannun Turawa, ga ki fara kal kamar auduga, ga kyau ga kyan hali. In baka so Zanirah ba ina jin babu zuciya da mazantaka a tare da kai”. 


Kalaman Hajjah sun girmi kunnuwan dukkanninmu daya bayan daya muka zame kowa ya bi hanya daban mai billar da shi wani sashe na gidan. Yaya Aliyu kuwa tunda ta dauko bayanin asalin sunan Zanirah ya bar dakin don haushi. 


Ta fannina nima na nuna ni ‘yar halas ce, nayi ma Zanirah gudunmmuwar (kayan amfanin kitchen) masu karko da tsada ‘yan Japan. Turare mai tsada 

‘versace’ da ‘hugo boss’ na ango Yaya Aliyu, na ce, “A sha kamshin amarci lafiya Aliyu da Zanirah”, 


Sai a wannan lokacin ne Yaya Aliyu ya dago ido ya dube ni da wata muguwar harara da ban tsammana ba. Zanirah dake gefen shi cikin farin (swiss lace) mara nauyi mai yarfin (silver) dinkin buba da zani, kunshi baki sidik ya kama tafukan hannaye da kafafunta. Gashin nan ya sha relaxing ya kara baki ya kwanta a dogon wuyanta, amarya dai sak! 


Ta dago kanta a hankali daga kan yatsun kafarta ‘yan sirara itama ta harare ni. Ga mamakinmu duka sai cewa ta yi, “Wanea irin amarci kike fade Fa’izah? A ya yin da zuciyoyi biyu basu dai-daita da juna ba? Auren da ake lallashi da takurawa mijin ya so ka, shi kike ambatawa amarci Fa’izah? Kaico da auren da ake roko da lallashin mijin ya dauki amaryar yana gudu. 


ZAMANI YA CHANZA, ya kamata iyaye da kakanni irin Hajjah su gane hakan, su ajiye traditionality su bi modernity in dai ba fadar Allah da manzo bane. Domin maimakon a gyara zumuncin sai a bata, ko a zalinci daya a kasa kwatar masa hakkinsa don a dorar da zumunci”. 


Ta mike ta yi waje tana mai fidda zafafan hawaye. Na kasa cewa komi sabanin Yaya Aliyu da ya kyabe baki ya gyara kwanciyar sa cikin kujera. Tsam! Nima na mike na bar wurin. Ummi ta bimu da kallon tausayi baki dayanmu. 


Karfe shida saura minti talatin, iyakar rakiyar mu dasu Zanirah filin jirgin saman Kaduna, inda suka 


Post a Comment for "ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 2 by Sumayyah Abdul-kadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...