YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 1 BY HARUNA USMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA  CHAPTER 1 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 1 BY HARUNA USMAN

- - Post a Comment

 YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA

CHAPTER 1 BY HARUNA USMAN


SABON LITTAFI DAGA WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

HAJI Hamidu dan Usman mutum ne da Allah Ya yi wa baiwar ilmi da aiki da shi, ga hankali da hakuri da riKon amana da kuma rashin girman kai. Daidai gwargwado kuma yana cikin rufin asiri. 


Babbar dacewa ita ce irin yadda Allah Ya albarkace shi da mace ta Kwarai, wadda samun irin ta sai an tona ta bangaren sanin ya kamata da hakuri da kyau da cikar halitta. Sunanta Ramlah. 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ma’‘auratan suna da 'ya'ya maza da mata, amma manyan da suka isa misali su uku ne. Babban sunansa Idrisu, mai bi masa kuma Abubakar wanda suke kira Habu, sannan sai Yahaya. Dukkan su sun sami ilmi daidai gwargwado. | 


Wani abin sha'awa shi ne irin yadda wadannan samari ba su bar komai na kyawawan halaye da siffofin iyayensu ba, hakan ya sa halayyarsu ta zama abar misali kuma kyan halittarsu ya zama abin tsegumi a gari. } 


Fara jin dadi da kuma taka wani mataki na ilmi ne 

suka sa wadannan matasa a rayuwa ba abin da suka fi bukata da kauna fiye da tsunduma cikin duniya don 


Karo sani. 


A karshe dai suka yanke shawarar tafiya din. Kuma saboda sanin muhimmancin ilmi da kuma daidai gwargwado aminta ko yarda da tarbiyyar ‘ya'yansu suka sa ko kadan iyayensu ba su ki yarda da wannan buKata ta tafiya ba, har maa karshe mahaifinsu ya kara da yi musu gargadin cewa, 


“Ya ku ‘ya'yana, babban abin da nake so in tunatar da ku kuma in gargade ku a kai shi ne, duk inda kuka tsinci kanku, to ku rike amana, kuma ku rika tuna sanadin fitarku daga gida, wato ~ilmi; jagoran _ rayuwa.” 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yara suka ce in Allah Ya yarda ba za su taba mantawa ba. 


A daya bangaren kuma akwai Bashari, shi ma wani yaro ne mai hankali, makwabci kuma abokin wadannan yara. Duk shirye-shiryen da ake yi na tafiya da shi ake yi, don irin shakuwar da ke tsakanin su. Shi ma ya nemi yardar nasa iyayen kuma sun amince. ” 


Su hudu ke nan. 


Bayan addu’o'in fatan alheri da sa albarka irin wadanda iyaye kan yi wa ‘ya'yansu, wadannan matasa suka yi sallama da jama‘arsu suka bi hanya. 


Kwana arba’in ba biyu suna tafiya, sai suka isa wata 


mararraba wadda hanyoyin da ke jikinta suka rabu hudu, Gabas da Yamma, Kudu da Arewa. A nan suka 


tsaya don shawartawa. 


Habu ya ce, “Ina ganin ya kamata daga nan sai mu rabu, kowa ya bi tasa hanyar, don in mun tuna daga cikin maganar mahaifinmu ta kwanakin baya, ya ce za mu fi kwazo in har ba ma ganin juna.” 


Ba tare da gardama ba suka yi sallama, suka rabu kowanne zuciyarsa cikin halin raurawa. 


Babbansu Idrisu ya fuskanci Gabas, shi kuma Habu ya doshi Arewa, Bashari ya tsinkayi Kudu, Yahaya 


kuwa Yamma ya nufa, kowa ya mika. 


IDRISU ya ci gaba da tafiya kwana da kwanaki ba tare da sanin inda ya ke nufa ba, ba dare ba rana, shi dai nutsawa ya ke yi. Bugun ruwan sama kuwa har ya zame masa jiki. 


Amma maimakon ya fara ganin alamar gari ko Kauye, kullum sai kungurmin daji ya ke sake kutsawa. Ya wuce wannan Korama, ya ratsa ta wancan tafki, ya sakala ta tsakanin wadancan duwatsu, namun daji iriirl ya yi ta haduwa da su, wadanda ya sani ko kuma ya taba jin labari da wadanda ko tunanin irinsu ma bai taba yi ba, manya da Kanana. Ba ya jin kukan komai sai zakoki da damisoshi da giwaye da sauransu, Allah dai Ya yi ta kiyaye shi. Wasu koke-koken ma sam bai 

 san ko dabbobi ko mene ne ke yin su ba, shi dai ya ci gaba da tafiya bai san inda ya ke nufa ba. 


Bayan guzurin da ya riko ya Kare sai 'ya'yan itatuwa suka koma su kadai ne abincinsa, har dai ya zo cikin wani kungurmin daji da babu alamar ko dan Adam ya taba wucewa ta wurin ma. Kwatsam a cikin dokar daji sai ya rika jiyo haniniya, ya nufi inda sautin ke fitowa yana lellekawa har dai abin da ya ke zato ya tabbata daidai, wato doki ne. Shi dai Idrisu bai taba ganin doki mai kyau irinsa ba. 


Yanzu kam a cikin zuciyarsa ya tabbata cewa zai sami taimako ko kuma labari, kasancewar akwai alamar ya iso inda mutane suke. 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ya duba ko ina ko zai ga mai dokin amma abin mamaki babu alama ko daya. Ya Kara matsawa kusa, sai ya tarar ashe saiwar wata irin itaciya mai yado da sarkakiya a kasa ce ta rike wa dokin Rafa, amma ya kasa cirewa da kansa. Ganin Idrisu kusa da shi sai ya yi ta harbe-harbe, shi kuma yana ta lallabar sa yana matsawa kusa a hankali. Ya je ya samo masa ciyawa mai kyau ya mika masa don nuna cewa ba shi da mugun nufi gare shi. A haka dai har ya kai ga shafa shi. 


Idrisu ya zaro wuka daga kuibinsa ya yayyanke saiwar, ya janyo Kafar a hankali, wadda ya tarar ta dan yi rauni, kuma ba tare da bata lokaci ba ya yagi rigar 


jikinsa ya daure masa. Doki dai ya fahimci taimakon ,,. sa ake yi, saboda haka sai ya saki jiki. Idrisu ya hada 

 wata ‘yar bukka a wannan wuri ya yi kwanaki yana jinyar doki har Allah Ya sa ya warke garau. 


Shi ke nan ya sami abin hawa. Kuma yanzu ba ya samun wata wahala wajen hawa da sarrafa shi, kuma duk abin da ya umurce shi, to babu gardama ya ke aikatawa. 


Shi wannan doki da wahala duk yadda mutum ya taba ganin doki a ce ya ga mai kyansa, Kosasshe ne, fari, mai kwarjini. Dole ne idan ka yi sa'ar ganin sa ka dimauta da son sa. 


Ba da dadewa ba Idrisu ya fara tunanin irin sunan da ya kamata ya rada wa wannan ingarman doki nasa. Can yana cikin tunani sai kwatsam ya tuna da wata kalma da mahaifinsu ya yi amfani da ita a lokacin da za su bar gida, wato nunin da ya yi musu cewa ilmi shi ne jagoran rayuwa, saboda haka sai ya shafa jikin doki ya ce masa, “Sunanka Jagora.” Nan take dokin ya yi wata irin haniniya ta jin dadi kamar ya fahimci abin da ake nufi. | 


Bayan dukkan su sun sami isasshen hutu sai Idrisu ya cewa Jagora, “Ya kamata mu bar wannan wuri mu nufi inda Allah Ya kai mu.” Yau da kullum ta sa ya dauki wata dabi'a ta yin magana da wannan doki nasa kamar yana yi da mutum dan'uwansa. 


Haka nan babu sirdi ya hau Jagora ya sake tsunduma cikin daji, ya sa masa idanu sai inda ya kai shi, kuma duk inda ya nufa ba ya kwabon sa. 

Bai ankara ba sai ga su a bakin wani lambu cikin dokar daji, wanda tun da ya ke a duniya, bai taba mafarki ko jin labarin mai ban sha'awar sa ba, ga furanni masu Kanshi da launuka iri-iri, Korama tana kaiwa tana kawowa gwanin ban sha'awa, ga ‘ya'yan itatuwa nan iri-iri sai tsuntsaye suke ta wakoki da mabambantan sautuka masu natsar da zuciya. Kai a takaice dai irin wannan lambu da zarar ka gan shi, to tunanin da zai fara biyo baya shi ne, “Allah ba mu Aljanna.” 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Sai dai kuma lambun yana da wani abin mamaki. Shi kansa kungurmin dajin dai ba shi da alamar rairayi ko kadan a cikin sa, duk itatuwa ne da sarkakiya da sunkuru da duwatsu da Koramu, amma sai ga shi lambun ya fita daban. Ga yashi nan fari fat har da wasu ‘yan dunkulallun duwatsu na Karau masu ba da haske kamar fitilu a cikin sa. Daga gani ka san ba aikin mutum ba ne sai dai aljan. 


A can daga gefen lambun kuma wasu dakuna ne ake iya hangowa, guda biyu masu kyau; babba da karami, su ma suna da launuka iri-iri gwanin ban sha'awa. A tsakanin su da lambun akwai wata Korama wadda ruwa ke gudana gwanin ban sha'awa. A cikin ruwan ga kifaye nan masu kyau iri-iri da mabambantan launuka Karara ana kallon su. Da Idrisu ya tsallake Koramar sai ya saki Jagora karKashin inuwar itace, shi kuma ya nufi inda katon dakin nan 

yake. Ya yi sallama, “Assalamu alaikum.” Abin mamaki sai ya ji an amsa, “Wa’alaikumus salamu, shigo.” 


Shigarsa sai ya ga ashe wannan daki Kato ne kamar wani dan karamin gida. Wani dattijo ne a ciki mai yawan shekaru, ga dogon gemu da saje da gashi fari fat mai kyau. Da ganin sa ka san yana da wata daraja da Allah Ya yi masa saboda tsananin kwarjinin fuskarsa. 


Yana zaune a kan wani farin buzun rago zagaye da litattafan karatu iri-iri, masu tarin yawa. 


Idrisu ya Karasa kusa da shi ya gai da shi cikin girmamawa da tausasa murya. Dattijo ya kalle shi wanda kuma a cikin kallon ya nazarci cewa yaro ne saurayi kyakkyawa mai alamar natsuwa. Ya ba shi damar zama, sannan ya ce, “Ya kai wannan saurayi mene ne sunanka? Daga ina ka fito? Me kake nema? Kuma inazaka?” 


Cikin natsuwa ya mayar da amsa, “Sunana Idrisu dan Hamidu, na fito daga garinmu Dutsen-ruga ne don neman ilmi, tafiya kawai nake ba tare da sanin inda nake fuskanta ba har Allah Ya kawo ni nan.” 


Bayan ya gama shaida wa dattijo labarinsa sai shi ma ya tambaya cewa, “Ya kai wannan dattijo mai daraja, kai kuma mene ne naka labarin? Mene ne labarin kasancewarka a wannan kungurmin daji kai kadai? Kuma mene ne labarin wancan lambu mai ban mamaki?>” 


Dattijo ya ce, “Ya kai Idrisu ina so ka sani, ni sunana Ibrahim dan Yahaya, kuma labarin kasancewa ta a nan da kuma labarin lambu kada ka sake tambaya ta. Ina so in shaida maka wata magana, in ka yarda, to zan koyar da kai abin da ka fito nema, wato ilmi, in kuma ba ka amince ba, to sai ka ci gaba da tafiyarka.” 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Sai Idrisu ya ce masa, “Allah gafarta malam ai sai ka shaida mini, in abin da zan iya yarda da shi ne in yarda, in kuma ba wanda zan iyaba ne in tafi.” . 

Dattijo [brahim ya ce, “Ya kai Idrisu, mutane suna lissafta ni daga cikin mashahuran malaman wannan zamani don irin dumbin ilmin da Allah Ya yi mini baiwa da shi.”


Ya ci gaba da bayani, “Ya kai dan Hamidu, na dade a cikin wannan Kungurmin daji, sai dai kuma labarina a cikin sa da kuma labarin shi kansa wurin yana da tsawo, kuma ba zai yiwu ka ji shia yanzu ba, sai dai ko’ watakila nan gaba. 


Sharadi na farko da zan ba ka shi ne, daga yanzu komai ka gani kada ka tambaya. Abu na biyu kuma shi ne, lokacin da za ka shigo ka wuce ta wurin wata rijiya ko? To abin da nake so shi ne a kullum ka je ka debo ruwa daga cikin dan rafin can kana zubawa a cikinta har na tsawon yawan kwanakin shekara daya babu fashi, kuma kada ka manta na ce maka babu tambaya, kai dai aikata abin da na ce kawai. Ga daki 

A can ka rika kwana a ciki, kuma kada ka kuskura a tsawon kwanakin shekarar nan ka makara har in riga ka fitowa. Sauran abubuwan da za ka rika gani in dare ya yi kuma, sai ka san yadda za ka fitar da kanka. 


In har ka yarda da wadannan sharudda, to zan karantar da kai har na tsawon shekara daya. Kar ka damu da maganar abinci, wannan akwai shi. 


Na hango tahowarka daga nesa a kan zakakurin dokin nan wanda daga ganin yadda ya ke takawa ma kawai duk mai lura zai iya gane cewa yana da wata baiwa ta musamman, wato ba gama-garin doki ba ne, 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

amma sai ga shi kai kana sarrafa shi yadda ka ga dama,


ya zama KarKashin ikonka. Shi yasa nake zaton akwai nasara a cikin lamarinka. Ina jaddada maka cewa lallai ka riKe shi da mutunci don zai taimake ka taimako mai yawa.” 


Dattijo ya ci gaba da yi wa Idrisu bayani, “Ya kai dana babu shakka za ka yi gwagwarmaya da yawa a cikin tafiyarka.” 


To, da Idrisu dan Hamidu ya ji wannan zance na dattijo sai ya ce, “Ya kai wannan dattijo mai daraja, na ji abubuwan da ka ce, kuma na yarda na amince, sai dai kuma na ba ka amana, ina fata kada ka yaudare ni. 


Kuma ga shi ka ce kada in yi tambaya, ba don haka ba, ina da tambayoyi masu yawa da nake matuKar bukatar amsoshinsu daga gare ka.” 


' Dattijo ya ce, “A'a kada ka yi, da sannu za ka zo ka 

san komai.” 


Idrisu ya nemi Karin bayani, “Idan muna karatu har abin da ya shige mini duhu ban gane ba kada in tambaya?” 


Sai dattijo ya ba shi amsa cewa, “A‘a banda in an zo fagen karatu, ai karatu babu tambaya ya zama labari ke nan.” 


Dattijo kuma Shaihin malami Ibrahim ya Kara da cewa Idrisu, “Ya kai wannan kyakkyawan saurayi, in dai karatu ka zo nema, to kuwa ka samu in dai har za ka tsare Ka'idoji. Bayan ka kammala karatu a wurina na shekara daya, za ka je ka ci gaba da karatu a wurin wasu. Amma kafin ka sadu da su jan aiki ne.” 


Yana matukar bukatar sanin abin da dattijon ke nufi, amma kuma ya tuna cewa babu tambaya, sai ya yi shiru. | | 


Sai ya cewa dattijo, “Babu shakka zan yi iyakacin Kokarina in kiyaye dokokin da ka sa mini, in Allah Ya yarda.” 


Cikin annashuwa dattijo ya ce, “To sai ka je ga dakin can ka shiga ka gani, a ciki za ka rika kwana, kuma ga wata ‘yar Karamar rumfa can a jikin dakin ka rika daure dokinka. Kuma shi wannan daki akwai komai da dan Adam zai buKata. In Allah Ya kai mu 


gobe, sai ka fara debo ruwa daga rafin kana zubawa a cikin rijiyar. Kada ka manta a kullum za ka zuba tulu goma ne, kuma kana kammalawa sai ka zo mu fara karatu.” 


Ya yi wa dattijo godiya, ya nufi inda daki ya ke, ya shiga ya tarar akwai gado da kujera da komai na more " rayuwa fiye ma da yadda ya ke zato. Ya zauna bakin 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

gado yana ta tunanin maganganun da suka yi, musamman ruwa da zai rika zubawa a cikin rijiya maimakon ita rijiya a debi ruwa daga cikin ta, amma an ce kada ya tambaya. Kuma ga irin wannan lambu mai ban mamaki. Sannan kuma babu wani mutum ko daya a wannan wuri sai dai wannan dattijo, duk dai an ce kada ya tambaya. | 


Tun da Asubahin fari ya dauki tulu ya fara debo ruwa yana zubawa a cikin rijiya kamar yadda aka umurce shi, har sai da ya zuba tulu goma daidai. | 


Bayan ya kammala sai ya je wurin dokinsa Jagora ya 


shafa shi, shi kuma dokin ya yi haniniya mai kamar gaisuwa kafin ya juya ya shige cikin daji kiwo abin sa. Shi kuma Idrisu sai ya nufi dakin malam ya yi sallama aka amsa tare da umurnin cewa ya shiga. Ya gai da malam cikin girmamawa shi kuma ya amsa cikin murmushi irin na Kauna. 


Idrisu ya ce, “Na zuba ruwan.” 


Dattijo ya amsa, “Ai na sani.” 


Idrisu ya yi mamakin yadda aka yi ya sani alhali kuwa ba ya fito ba ne, sai dai kuma babu dama ya yi tambaya. 


Suna gama karya kumallo sai Shehi Ibrahim ya ce, 

“Ya kai Idrisu, kafin mu fara, ina so ka ba ni dalilin da ya sa kake so ka sami ilmi ko ta halin Kaka, ko kuma a takaice ince ba ni labarin muhimmancin ilmi.” 


Sai Idrisu ya ce, “Ya kai wannan malami mai daraja, ni dai yaro ne, saboda haka na san cewa lallai kadan ne kawai abin da na sani game da muhimmanci da amfanin ilmi. 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ilmi yana fitar da mutum daga duhu, ya yi masa jagora zuwa ga haske, kuma in kana da ilmi, to kana da mutunci, kuma komai ikonka, dukiyarka da kwarjininka in ba ka da shi, to da kai da jaki bambancinku halitta, kawai kai mutum ne shi kuma sunansa jaki. | 


Ilmi bargo ne da duk wanda ya lulluba da shi ba ya tozarta. Sai ka ga mutum dan talakawa amma matukar ya sami ilmi sai ya zama babban mutum mutane suna ba shi girma har ma ya iya rike mukaman da mai unguwarsu bai taba mafarki ba. 


ilmi shi ne babban makamin da ko lahira za ka tafi, to tare za ku, kana tafiya yana yi wa rayuwarka jagora, kuma duk inda za ka shiga, to kana gani radau don ko idanunka ba sa budewa, to kai ba makaho ba ne, wato ko idanunka a rufe suke matukar dai kana da ilmi, to kafi jahili wanda idanunsa ke bude sau dari. Wannan wani abu ke nan daga cikin abin da na sani na daga

 muhimmancin ilmi.” | To, da Shaihi Ibrahim ya ji zancen saurayi Idrisu sai 

 ya ce, “Lallai ka ambaci dan kadan daga cikin _ muhimmancin ilmi. Amma duk da haka ka yi Kokari, = kuma a hankali za ka yi ta Kara gani da fahimtar muhimmancin na ilmi. » Yanzu sai ka Kara da sanin cewa shi ilmi takobin ~~ 


yanke jahilci ne. In kana son ganin bakin cikin duniya, ne to ka zauna da jahilci, kuma yadda ilmi ya ke jagora, to shi ma jahilci babban jagora ne, amma fa ta 


Bangaren halaka.  Jahilci ne rawanin girman kai. Jahili ne kan soki . kansa da kansa amma ko kadan bai sani ba. A takaice dai innaci gaba da baka maganar jahilci  sai mu yi kwana da . kwanaki muna yi. Yanzu sai mu ci gaba da karatu.” ‘ Lokacin Sallah ya yi suka tashi suka gabatar, suka ci > abinci sannan suka sake komawa fagen karatu. In banda Sallar La‘asar ba su tsaya ba sai gab da Magriba Ne lokacin da malamin ya ba dalibinsa damar yin  tambayoyi a game da karatun da suka yi a ranar, daga nan suka yi Sallah suka ci abinci, kafin su kammala | 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

lokacin Sallar Isha'i ya shiga. Suka gabatar da ita daga 


nan sai dattijo ya ce, “Mun kammala na yau, yanzu sai ka hanzarta ka koma dakinka, kuma kada ka kuskura “ ka sake zuwa wannan daki nawa sai gobe da safe. Kuma kamar yadda nake jaddada maka komai ka gani kada ka kuskura ka yi mini tambaya.” _


Idrisu ya yi sallama ya tashi. Yana shiga dakinsa sai ya tsunduma cikin tunani 

 tare da mamakin irin abubuwan da ya ke gani daga wannan dattijo, musamman irin yadda abinci ke 

zuwa masa. Ga shi babu wani mutum a kusa da shi, ballantana a ce shi ke kawowa, sai dai kuma an ce banda tambaya. 


Ya dai Kare tunane-tunanensa ya shiga bitar karatun da ya dauko. Yana cikin nazarinsa sai ya ji dattijo a bakin dakinsa yana kira, nan da nan ya fita cikin gaggawa. 


Dattijo ya ce, “Na manta in shaida maka cewa lallai ka lura da dokinka, muddin ka ji yayi haniniya, to babu shakka yana yi maka nuni da wani abu ne, saboda haka sai ka kula.” 


Idrisu ya ce, “Na gode malam, kuma in Allah Ya so zankula” 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Dattijo ya koma dakinsa, ya bar Idrisu cikin tunani, “To ni ko ina cikin garin aljanu ne? An ce kada in yi tambaya, kuma ga abinci mai dumi muna ci ban ga mai dafawa ba, shi ma an ce kada in tambaya, dokina kuma in ya yi haniniya wai yana yi mini ishara ne, shi ma babu halin tambaya, kuma komai na gani a cikin dare kada in yi tambaya. 


A gaskiya ba don tsohon nan Musulmi ba ne, to lallai da na gudu daga wannan wuri, amma na tabbata dai ba zai yaudare ni ba daga dukkan alamu dai... to, zan zauna in ci gaba da bin umurninsa.” 


Ya shige ya haye gado ya yi kwanciyarsa. 

Can cikin dare bayan barci mai nauyi ya dauke shi, kamar a cikin mafarki sai ya ji ana rera waka, kuma lallai muryar ta mace ce mai dadin gaske kuwa, kuma tun da ya ke a rayuwarsa, bai taba jin waka da kidan molo mai dadi irin wannan ba. 


Ya farka a firgice, ya bude idanunsa amma sai ya ci gaba da jin wannan kida da waka wanda hakan ya tabbatar masa da cewa lallai da gaske ne ba mafarki ba. Hasali ma ba molo kadai ba ne, akwai wasu sauran kayan kade-kaden dake tashi a hankali. 


Ya tashi ya leKa waje daga cikin dakinsa, ai kawai sai ya ga lambun nan na kusa da su ya dauki-wani irin haske Kau da wasu irin fitilu masu launi iri-iri gwanin ban sha'awa, kuma ga wasu ‘yan mata nan su goma sha hudu, sun yi ado iri daya, ta cikon sha biyar din ce kayanta daban a cikin su, kuma ita ce ke ba da waka 


suna amsawa. 


Ita wannan yarinya duk ta fi sauran kyau, kamar dai yadda ake iya hango wata a cikin taurari, duk inda Sarauniyar kyau ta kai, to ba ta kai ta ba, kuma duk inda wani mai gani ya ke ganin kyau bai taba ganin mai kyanta ba, komai rashin begenka, idan ka gan ta, to dole sai ta dama maka tunani. Sa'arka dai kawai ba ka gan tadin ba. 

Kasance da www.bankinhausanovels.com.ng 

Idan ta sako waka sauran suka amsa, sai ya ji kamar zai narke saboda tsananin dadi. | 


Idrisu ya tabbatar da cewa ko mafarkinsa bai taba 

nuna masa wata yarinya da ta yi kusa da ita a fagen kyau da cikar halittar jiki ba. Abin da ya fito daga cikin bakinsa shi ne, “Tsarki ya tabbatar wa Ubangijin talikai. Ni na tabbata wannan yarinyg Sarauniyar kyau ce ta aljanu.” 


In yarinyar ta sake ba da wata waka sai Idrisu ya jj kamar ya tashi ya tsallake ‘yar Koramar da ke tsakanin, su ya isa wurinta, amma sai wata zuciya ta tsawatar masa ya fasa. Can dai da ta rero wata waka wadda dadinta ke ratsa sasannin Kwakwalwaar Idrisu bai san lokacin da ya tashi ya yi waje ya nufi wurinsu ba, yana KoKarin duba ta gefen da zai tsallaka Koramar ke nan sai kawai ya ji Jagora ya yi haniniya, ai nan take sai hankalinsa ya dawo jikinsa ya tuna cewa haniniyar dokinsa ishara ce a gare shi. Ya fahimci lallai zuwa wurin wadannan ‘yan mata ba alheri ba ne a gare shi, sai ya dawo ya shige daki yana mai ci gaba da sauraren wakoKinsu. , 

Lokacin da Asubahi ta kusa sai ya ji shiru, ya tashi ya leka amma sai ya ga babu kowa, duk ‘yan matan sun bace tare da dukkan fitilun, sai dai lambun kawai. 


Mamaki ya sake rufe shi, “Da ma na san wadannan ‘yan matan aljanu ne.” Kwanciyarsa ke da wuya sai barci mai Karfin gaske ya dauke shi har sai da dokinsa ya zo ya yi haniniya sau biyu. Nan da nan ya farka. Ya tashi ya yi sallah ya roki Allah nasara da kariya, kuma cikin gaggawa ya dauki tulu ya tafi yana debo ruwa 

 

Hmm ko mai zai faru kudai kuci gaba da kasancewa da wannan website www.bankinhausanovels.com.ng namu don samun ci gaban wannan kayataccen littafin

Post a Comment for "YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 1 BY HARUNA USMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...