YAR TALAKAWA COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

 YAR TALAKAWA COMPLETE

YAR TALAKAWA COMPLETE

- - Post a Comment

 YAR TALAKAWA COMPLETE 


Tafe nake a cikin wata kasuwar fruits(kayan marmari),nazo wuce wata  rumfa,mai dauke da kayan marmari kala kala,  wata kyakkyawar yarinya na hango a ciki, sanye take da wasu

kodaddun atamfa riga da skirt,yarinyar ba zata wuce shekaru sha shidda ba, sai tsalle take tana fadin, kuzo ku siya, namu sunfi zaki, tana maganar fuskar ta dauke da murmushi,kumatun ta sun lotsa, mutane dayawa suka tsaya a wurin suna kallon ta,kwanin sha'awa, gata kyakkyawa, ta dauko lemu,ta dauko alaba da sauran fruits din, tana fadi musu anfanin su,dan kawai su siya.

Ni afrah nace bari na bi wannan yarinya mai siyar da kayan marmari, dan kwaso wa masoyana labari.

Wani mutuni na gani ya kira ta ciki, yarinyar na murmushin mai kara mata kyau, tace ya habu har zamu tashi ne, naga akwai sauran jama'a a kasuwar, mu dan kara jira kaji, ya habu ya kalle ta yace NI'IMATU, ke bakya gajiya ne , tun safe kike tsalle tsallen nan, niimatu ta dara, ta kai wa ya habu naushi a hannu, ni ban gaji ba Allah, mudan kara jimawa kaji, ya habu yayi dariya, ke kam da namiji ce , da anyi jarumi.

Niimatu ta daure fuska, ohh ni yanzu ba jaruma bace ashe ko? Ta turo masa dan karamin bakin ta, ya habu yadan dungurar mata da kai, yace a tsalle tsallen kike jaruma, ya wuce waje abunsa, niimatu taja tsaki, sannan ta murmusa itama ta bishi wajen.

  .

Umma !umma! Ina kike gamu mu dawo, umma ta fito cike da fara'a, niimatu tayi saurin ajiye ledar hannunta,tayi wurin umman ta rungume ta, umma tayi murmushi, niimatu bakya girma ko?, niimatu  tayi murmushin ta, tana kallon umman tace, umma idan dai a gaban kine ni har yanzu yarinya ce karama, koda na haifi yara dari ne, umma tayi dariya , ya habu ya karaso ciki, yace umma sannu da gida?, umma tace ko keda sannu habu.

Sunyi wanka sun ci abinci, suna zaune dan tsakar gidan su, wanda ko siminti babu,ga ginin gidan duk ya lalace duk da na bulo ne, amma da yake ya tsofa, duk ya zaizaye.

Ya habu yasa hannu cikin aljihun sa, ya fiddo wasu yan kudi, ya mikawa umman, ga wannan nasan malam sahabi yazo, umma tace yazo kuwa dazun da rana, dama yace gobe idan munsan bamu da kudin hayan  , toh kada mu sake ya iske mu anan, ya habu ya girgiza kai, Allah yana sane damu, kuma mun gode masa, daya barmu da ranmu da kuma lafiyar mu ,umma tace aini har yanzu ina nan ina wa bawan Allah nan daya baka rumfa , kuma ya baka kudin jarin nan addu'a, dan ba karamin taimakon mu yayi ba ,Ya habu yace nima ina masa addu'a har yanzu, umma.

.

Niimatu dake kwance kanta bisan cinyan umma, tana barci,sai munshari take, tana juye juye ,ya habu ya tafka mata bugu a baya, kee uwar munshari tashi ki koma daki. Niimatu ta mike ta kura masa ido tana smiling, ya habu yaja tsaki, ke wai bakya gajiya da murmushi ne, kumatun ki baya gajiya?, umma tace kyele ta habu ta huta, ba karamin kokari take ba,  niimatu tace nifa ba barci nake ba yaya, kuma yaushe nayi munshari?, ya habu ya mike yace umma sai da safe, ke kuma , ya nuna niimatu, saura kiyi ta barci, kada ki tashi ki shirya da wuri, niimatu ta washe baki, ta nuna kanta nifa jaruma ce yaya.... ya habu yayi dan tsaki ya fice abunsa, dan idan zai biye wa niimatu bazai samu barcin kirki ba.... 

.

Washe gari da safe,niimatu ta kumo safko,tayi wankan ta,ta shirya cikin wata rigar ta gown ce ta  shadda,shaddar kalar ja ce amma se ka rantse da Allah ba jar bace saboda kodewa, lekawa tayi cikin kicin dinsu na galan galan duk ya huhhuje ,hayaki ya turnuke shi,ummana ina kwana?,umma  da idon ta yadan canza kala don hayaki tace, niimatu har kin tashi,ai da kin dan kara jimawa tunda yayan naki ma bai tashi ba, niimatu tayi murmushin ta tace , inna ya habu fa raggo ne, ko a kasuwa sai yayita wani gyangyadi, ni ce ma fa karfin wannan sana'ar tamu,kuma ma..

Ya habu da shigowar shi kenan cikin gidan, dan shi dakin sa a waje yake, jin niimatu na gulmar sa sai ya lallabo, yana zuwa bayanta yasa hannu ya dungurar mata da kai.

.

Auuuuushshshs..ya ya habu!!! Umma data dauko dan bokitin koko a hannu ta,tace ni ku dan matsa daga kofar nan na wuce...niimatu ta matsa,ya habu ya samu wuri  ya zauna, niimatu tazo gaban sa tana dafe da kanta tace, ya habu mai na maka zaka dungure ni??? Ya habu yace gulmata na kama ki kina yi, niimatu ta tsoke baki, sannan tadan matso kusa da ya habu, tasa hannun ta a kansa taja gashin kansa kadan, habu yayi yar kara , keee miye haka?eyee!, niimatu ta kwashe da dariya, tace nima na rama ne ai, umma dake juya koko tace kai kuzo ku sha kokon ku tafi kasuwan kada rana tayi muku,.. su niimatu suka zauna suka sha kokon dawar su, dama shine suke sha duk safiya, sai idan Allah yadan huro sun dan samu ciniki sosai , suke sauyawa da wani abun.

Sun shiga kasuwa, niimatu taci gaba da advertising fruits dinsu, wasu dan kawai suga murmushin nan nata kawai suke zuwa siye a wurin su.

Da yamma ya habu ya kwala mata kira, tana daga dan cikin rumfar ta amsa, tace gani yaya, hijabin ta ya juye gefe guda, ya habu yayi dariya da gani an fara jin yunwa, dan naga anyi lauro, ba kuzarin tsalle tsallen da ake , ga hijabi kuma na kallon gabas itama, niimatu tayi murmushin ta, duk da eh da gasken yunwa take ji sosai, tun kokon safen da suka sha,  gashi yanzu, har karfe biyar na yamma, ai dole taji yunwa.

.

Ya habu yace kici ayaba kuda biyu, yasa hannu cikin aljinhun sa, naira hamsin ya dauko ya mika mata, ga wannan kije wurin laure mai shinkafa da wake ki siwo mana mu dan ba cikin mu hakkin sa, da sauri ta dauki ayaban ta fara ci kamar ba suke siyar wa ba, ya habu yace ci a hankali niina, niimatu ta cika baki da ayaba amma sai data murmusa, ta mika hannu kawo hamsin din, ya habu ya mika mata yana dariya,easy niina, ta amsa da sauri, sannan ta fice da gudu.

Tana tafe tana murmushi, duk inda ta wuce sai an kalle ta, yarinyar ce akwai kyau ga fara'a.

Tazo wuce mai sai da kayan lambo, bata ankara ba taji ta buge mutum, jakar matar ta fadi kasa, a fusace ta juyo cikin masifa da isa.. ta kalli niimatu kasa da sama, kee miye haka ko bakya gani ne, tana maganar tana yatsine fuska.

Niimatu ta dago kanta ta kalli matar, sakin baki tayi, ta shagala da kallon kyakkyawar matar, gashi tasha ado sosai cikin kayan alfarma, ga kayan kyele kyele a jikin ta, matar ta wanka mata mari, keee.. bakya jina ne??!!!,,, niimatu tayi saurin cewa kiyi hakuri, ban lura bane wlh, matar ta watsa mata harara, mai saida kayan lambo yace hajiya kiyi hakuri dan Allah ba halin yarinyar bane rashin kunya,da gasken nasan bata lura dake bane..

Matar taja tsaki, tace wuce daga nan plss, niimatu tayi saurin wucewa tana waiwayen matar tana murmusawa abunta, matar ta sake jan tsaki ,  YAR TALAKAWA kawai sai iya kallon mutum kamar zata cinye ka.....

.

Niimatu taje ta siyo musu dan shinkafa da waken su,ko mutum daya sai ya cinye bai koshi ba.

Sun tashi daga kasuwa da dan wuri,saboda ba yawan jama'a sosai a kasuwar, sun isa gida kenan aka kira sallar mangariba.

Niimatu na zaune tsakar dakin umma, litattafan makarantar ta ne take sake gyarawa,kusan kullum sai ta gyara su take yin barci.

.

Umma ta shigo dakin da fitila a hannunta,niimatu kin san dai ba wadda kika ajiye dazai kwashe miki kayan shanyarki ko?! Niimatu ta juyo tana kallon umma tana smiling, zan zo na kwashe yanzu umma, ina dan sake gyara jakar makaranta na ne, kinga damun samu kudin school fees din saina koma kawai , umma ta kura mata ido, yanzu ashe dama har yanzu niimatu bata cire rai da karatu ba?,! Yanzu a kalla an kusa shekara biyu da kuro ta daga makaranta, niimatu ce tadan taba umman nata, umma tunanin me kike, ko kinyi fushi ne dan banje na kwashe kayana ba a shanya??? Umma tayi murmushin dole, ta shafa kan niimatu, ni bana fushi da auta ta, ko nayi ma, wannan murmushin naki, zaisa na huce ai, niimatu ta wangale baki tace Allah umma??? Umma na neman zama a yar katifar su tace, eh mana murmushin ki nasa nI tuna mahaifun ku, niimatu tayi saurin zuwa ta zauna kusa da umma, shima haka babn mu yake? Yana son yin murmushi irin nawa? Umma ta kada mata kai, sannan ta jawo ta jikin ta, niimatu tace umma baki taba fada mana komai akan baban mu ba, sai a ringa cewa mu bamu da baba ne?? Umma tayi saurin share hawayen dake niyyar fitowa daga idonta, tace niimatu kuna da uba kinji, niimatu tayi smiling, na sani umma muna dashi, tunda ba yanda za'ayi ki haife mu ke kadai, umma tace hakane su auta an fara girma ashe, niimatu ta turo baki tana shure shuren shagwaba, ni ban fara girma ba umma , umma tayi dariya ta mike, ke ni tashi ki kwaso kayan ki dan ban manta ba.

****************************

Aysha shine asalin sunan umma, ba wanda zai iya fada maka daga inda take? Daga wane gari take, tazo garin suleja tun abubakar(habu) yana da shekara goma, lokacin niimatu na jaririya, a gidan wata tsohowa take zama, wadda ita ce ta taimake ta lokacin da bata da wurin kwana, a  tasha suka hadu, tsohuwar ce ta rika su har na tsawon shekaru bakwai, sai Allah yayi mata rasuwa,yaran ta sukazo dan rabon gado, sahabi shine ya samu kason gidan dasu umma ke ciki, ya bar musu amma da sharadin sai umma ta amince ta aure shi, umman ta ki yarda da sharadin nasa, sahabi yace toh fah sai dai su bar masa gidan  sa, umma ta roke shi ya bar musu gidan a haya, duk wata zasu ringa biyansa kudin sa.

     Umma ba karamin wahala tasha ba, wurin ciyar da yaranta, har habu ya samu ya shiga collage, ita kuma niimatu aka sanya ta pri, kullum cikin koro niimatu ake daga makaranta, dan bata da kayan karatun irin su textbook, books da sauran su ,habu na ajin karshe a collage dinsa  , aka bukatu wasu kudi daga garesu, na final year exams dinsu, umma tayi bakin kokarin ta dan ganin ta samo kudin amma inaa, duk inda take tsanmanin samu bata samo ba, haka habu yaci gaba da zuwa kasuwa yana dan samo musu na Maggie, karatu kuma tun daga lokacin ya fitar da ran yinsa,niimatu na jss2 , aka koro ta dan bata  taba biya kudin makaranta ba tunda ta shiga school din.

Itama tunda daga ranar bata sake komawa ba. Har habu ya hadu da bawan Allah nan daya taimake su, habu ya fara saida kayan marmari a kasuwar suleja, niimatu ta matsa wa umma ita tana son ta ringa bin habu kasuwa, umma da farko taki yarda, ganin yadda niimatu ta dage sai ta amince ta sanar wa habu, shine yanzu suke tafiya tare. 

.

Niimatu taje ta siyo musu dan shinkafa da waken su,ko mutum daya sai ya cinye bai koshi ba.

Sun tashi daga kasuwa da dan wuri,saboda ba yawan jama'a sosai a kasuwar, sun isa gida kenan aka kira sallar mangariba.

Niimatu na zaune tsakar dakin umma, litattafan makarantar ta ne take sake gyarawa,kusan kullum sai ta gyara su take yin barci.

.

Umma ta shigo dakin da fitila a hannunta,niimatu kin san dai ba wadda kika ajiye dazai kwashe miki kayan shanyarki ko?! Niimatu ta juyo tana kallon umma tana smiling, zan zo na kwashe yanzu umma, ina dan sake gyara jakar makaranta na ne, kinga damun samu kudin school fees din saina koma kawai , umma ta kura mata ido, yanzu ashe dama har yanzu niimatu bata cire rai da karatu ba?,! Yanzu a kalla an kusa shekara biyu da kuro ta daga makaranta, niimatu ce tadan taba umman nata, umma tunanin me kike, ko kinyi fushi ne dan banje na kwashe kayana ba a shanya??? Umma tayi murmushin dole, ta shafa kan niimatu, ni bana fushi da auta ta, ko nayi ma, wannan murmushin naki, zaisa na huce ai, niimatu ta wangale baki tace Allah umma??? Umma na neman zama a yar katifar su tace, eh mana murmushin ki nasa nI tuna mahaifun ku, niimatu tayi saurin zuwa ta zauna kusa da umma, shima haka babn mu yake? Yana son yin murmushi irin nawa? Umma ta kada mata kai, sannan ta jawo ta jikin ta, niimatu tace umma baki taba fada mana komai akan baban mu ba, sai a ringa cewa mu bamu da baba ne?? Umma tayi saurin share hawayen dake niyyar fitowa daga idonta, tace niimatu kuna da uba kinji, niimatu tayi smiling, na sani umma muna dashi, tunda ba yanda za'ayi ki haife mu ke kadai, umma tace hakane su auta an fara girma ashe, niimatu ta turo baki tana shure shuren shagwaba, ni ban fara girma ba umma , umma tayi dariya ta mike, ke ni tashi ki kwaso kayan ki dan ban manta ba.

****************************

Aysha shine asalin sunan umma, ba wanda zai iya fada maka daga inda take? Daga wane gari take, tazo garin suleja tun abubakar(habu) yana da shekara goma, lokacin niimatu na jaririya, a gidan wata tsohowa take zama, wadda ita ce ta taimake ta lokacin da bata da wurin kwana, a  tasha suka hadu, tsohuwar ce ta rika su har na tsawon shekaru bakwai, sai Allah yayi mata rasuwa,yaran ta sukazo dan rabon gado, sahabi shine ya samu kason gidan dasu umma ke ciki, ya bar musu amma da sharadin sai umma ta amince ta aure shi, umman ta ki yarda da sharadin nasa, sahabi yace toh fah sai dai su bar masa gidan  sa, umma ta roke shi ya bar musu gidan a haya, duk wata zasu ringa biyansa kudin sa.

     Umma ba karamin wahala tasha ba, wurin ciyar da yaranta, har habu ya samu ya shiga collage, ita kuma niimatu aka sanya ta pri, kullum cikin koro niimatu ake daga makaranta, dan bata da kayan karatun irin su textbook, books da sauran su ,habu na ajin karshe a collage dinsa  , aka bukatu wasu kudi daga garesu, na final year exams dinsu, umma tayi bakin kokarin ta dan ganin ta samo kudin amma inaa, duk inda take tsanmanin samu bata samo ba, haka habu yaci gaba da zuwa kasuwa yana dan samo musu na Maggie, karatu kuma tun daga lokacin ya fitar da ran yinsa,niimatu na jss2 , aka koro ta dan bata  taba biya kudin makaranta ba tunda ta shiga school din.

Itama tunda daga ranar bata sake komawa ba. Har habu ya hadu da bawan Allah nan daya taimake su, habu ya fara saida kayan marmari a kasuwar suleja, niimatu ta matsa wa umma ita tana son ta ringa bin habu kasuwa, umma da farko taki yarda, ganin yadda niimatu ta dage sai ta amince ta sanar wa habu, shine yanzu suke tafiya tare. 

.

Wani katon gida ne mansion, mai dauke da fulawoyi, ko ina , ga swimmingpool da garden babba , ko ina security ne, gidan kashi biyu ne duka iri daya ne , hawa bibbiyu, wasu motoci na hango manya manyan gaske, daga benz sai prado, cikin gidan nan suka nufa da jiniyar su.

Wasu matane su biyu naga sunyi saurin fitowa daga cikin gidan, sanye suke cikin kaya masu shegen tsada, sunci gayu kamar zasuje wani occasion, fuskar su dauke da murmushi, da gani cikin farin ciki suke.

.

Ana gama parking din motocin nan, wasu na gani da kayan sojoji sunyi saurin fitowa daga cikin daya daga hiking motocin nan, motar dake tsakiya naga sun nufa, bude kofar motar sukayi, sannan suka sara, (da gani dai ko waye a ciki soja ne shima)

wani kyakkyawan handsome ne ya fito daga cikin motar, sanye yake cikin wandon sojoji da farar top, yana da tsayi sosai, da ganin shi kaga jarumin namiji mai ji da kansa, fuskar shi ba alamun wasa, a daure take , idanun shi medium ne masu kyawun gaske, ya saka sun glasses, bakin sa dan karami, hancin sa nada tsayi mashaAllah, fuskar shi ba saje ko kadan da gani ya aske ne, dan akwai shaidar gashi a wurin,

(O.M.G ni kaina afrah sai dana kyasa wannan guy din)

.

Yan matan nan naga sunyi saurin zuwa wurin shi, daya mai haske kamar shi, sai daya mai dan duhu , a tare  sukace you are welcome ya "PRINCE!!"

Glasses din idon shi ya cire, yadan kalle su kadan, fuskar nan a daure, ya galla musu harara yayi cikin gidan.

Mai duhun tace, zarah kinga wulakancin da kika ja mana ko!, kalla a gaban sojojin nan ya disga mu, mai hasken tayi dan murmushi, ta dafa dayar tace zuby kin cika surutu, ke kanki kin riga kin san halin ya"PRINCE" ai, muje pls na sake ganin cute face dinnan tasa, taja hannun zuby sukayi cikin gidan suma.

WAYE PRINCE  ?????

.

Readers nasan kuma kuna son sanin waye shi, dan haka ku biyo afrah luv dan yanzu labarin YAR~TALAKAWA  ya fara.....

.

Zuby da zarah na shiga suka iske ya prince a zaune falo,tare yake da mum da mami, zama sukayI suma suna kallon shi yana gaisawa da iyayen sa, amma fuskar sa ko gizo.

Mum ta kalli prince tace , my son kana kuwa cin abinci a lagos dinnan?, mami tayi murmushi tace gaskiya baka cin abinci sosai prince, prince ya mike yana kallon su yace, mum, mami let me fresh up , yanzu yunwa nake ji,bazan iya duguwar magana ba, zuby ta kalli zarah, zarah ma ta kalli zuby, suka rike baki, ashe har iyayensu yana wa wannan miskilancin.

Yayi one step kenan, wani kyakkyawan yaro, mai kimanin shekaru shidda,ya fito daga wani daki dake kusa da falon da gudun sa,  PAPA! PAPA!, yake ta cewa, wata ce ta biyo sa , da gani dai mai aiki ce dan tana sanye da wasu uniform ne kalar baki da fari.

Yaron yazo ya rungume prince yana dariya, mum tace su AMEER  anga daddy yau sai aci abincin kirki, amir ya dago ya kalle ta , grany yau zanci ko me kika bani, mami tayi dariya, zan maka pancakes kuma dole ka cinye su, amir yayi dariya qibin hakorin sa ya fito, yace zan cinye grany mami.

.

Su zuby da zarah suka kura ido suka ko prince zai wa amir smiling, ga mamakin su sai suka ga ya shafa kansa kawai, ya rike hannun sa sun haura sama.

Zuby tace zarah ya prince bai canza ba ko kadan, see fa ko little amir dake mutuwar son ganin Papa dinsa amma baiko yi wa poor boy din smiling ba, zarah da tayi tagumi tana kallon zuby tace, halin ya prince sai shi amma ni yana burge ni a hakan ma, zuby ta mike, tashi muje daki kafin ya same mu anan kema kinsan sauran.

Prince a kwance a saman katoton gadon shi, mai laushi, yana hutawa kafin su dad su dawo yaje ya gaisar dasu.

Amir ne ya shigo dakin da gudu ya haye saman bayan prince, yana dariya cike da fara'a yace , papa papa! Yau zamuje ka kaini nasha ice cream  ko kai kuma kaci pizza??, prince ya kada masa kai kawai, amir ya mirgino ya kwanta yana kallon papa dinsa, yace papa kasan me, prince ya girgiza masa kai, yace jiya ko  grany mami tayi wa anty zarah fada a falo, prince ya ware ido yana kallon amir, amir yace kasan me tayi , prince ya girgiza kai, amir yakai bakin sa kunnen prince yace, wai taje party din frnd dinta da daddare.

Prince ya mike ya zauna, ya kalli amir yace da anty zuby sukaje?, amir ya girgiza kai, sannan ya sake matsowa kusa da prince yace papa, kasan me anty zuby tayi yau da safe? Prince ya girgiza kai, amir yace, grany ta kama ta tana wa uncle fahad rashin kunya.

     Prince yace good boy,ya shafa kansa, kai kuma mai kayi da bana nan, amir yayi saurin mikewa , yana zuwa bakin kofa yace papa, na samu 5/10 a math, yayi saurin gudu, dan yasan halin papa dinsa.

    Prince yace zamu hadu dakai kaima.

.

Prince bai fito daga dakin sa ba sai da yamma, ya shirya cikin kananan kaya,ba karamin kyau da kwarjini yayi ba, fuskar nan a daure yazo wuce falo dan zuwa babban falon dad dinsu, zarah ce a kwance tana kallon vampires diaries,bata lura da shigowar ya prince ba, kwata kwata,tsawa taji kawai a kanta,Kee!! Zarah tayi saurin mikewa tace na na'am, prince ya galla mata harara,da kyal ya  iya bude bakin sa yace,ki kira zuby kuje garden ina zuwa, zarah ta ware ido,tayi saurin cewa wayyo ya prince kayi hakuri.

Prince bai ko kalle ta ba yayi ficewar sa.zarah ta dafe kirjin ta yau mun shiga 10,dan 3 kadan ne.

.

Dad da abba ne zaune a falon, prince yayi sallama ya shiga.

Abba yace major an tuna damu kenan?, prince ya samu wuri a kasa ya zauna, dad ya kalle shi yace, kunzo wani aikin kenan nan abuja?, prince ya kada kai,dad ya kalli abba yace,na fada maka ai, abba yace, NA'IM ya kamata ka manta duk wani abu daya faru a baya, u most go on with your life,kowa ya maidaka kumurci, duk yaran nan da sunji zuwan ka hankalin su sai ya tashi , haba ! shekaru biyar kenan fa.

    Dad yaja tsaki,kai ma dai Usman baka gajiya wlh,kullum sai ka maimaita masa wannan maganar,ni nama gaji da masa fadan nan, dan shi ba yaro bane yanzu,he should knw by now he have to go on in life,prince dai kansa na sunkuye yana sauraron su,sun yi fadan su na kullum , sun gaji,prince ya mike yace dad,abba, dama muna da meeting da general ne a abuja, nan da kwana hudu zan koma inshaAllah, dad yayi banza dashi, abba ne yace toh Allah ya kaimu.

Zarah a goje ta shiga dakin zuby,ta iske ta tana chat a wayan ta, zuby tace yauwa zarah zo kiga guy din nan da nake fada miki,he's darm handsome,wlh kamar ya prince.

     Zarah tace kee  its nt time for dat nw, tashi fa tamu ta kare, zuby ta kalle ta, meya faru? Zarah tayi saurin amshe wayar dake hannun zuby , ta ajiye a gadon  tace, tashi muje garden, zuby ta kalli zarah tace me zamuyi acan din?, zarah tace ohhh har kin ma manta mai ke kaimu garden ko??, zuby ta ware ido ta dafe kirjin ta,tayi saurin mikewa, dnt tell ya prince....kafin ta idasa zarah tace, shine yace muje mu jirashi acan, zuby tace muje muje pls ban shirya tsallen kwado ba wlh.

.

Prince na barin falo wurin abba , direct garden ya nufa, as expected , ya iske su  a tsaye cikin garden din  suna jiran sa.

Prince ya zauna a wasu kayatattun kujeru dake tsakiyar garden din.

     Da hannu yayi musu nuni dasuzo kusa, cikin rawar jiki suka karaso, prince yace wato idan kunga bana nan , sai ku riga duk abunda kuka ga dama ko!!!!!

   Sudai sun sadda kai kasa kawai, prince ya daura kafar sa bisan table din dake gabansa yace, ke zarah, partyn dare, ya nuna zuby , ke kuma rashin kunya , ya daga murya yace Ko! Suka hada baki wurin cewa , bazamu sake ba ya prince.

    Prince ya mike yace, basai na fada muku me zakuyi ba,am sure baku manta ba, yayi hanyar gidan abba, dake kusa da nasu,yana cewa zan turo Sargent ema ya duba min ku.

.

Yana shiga kayatatcen falon gidan abba,komai da komai irin nasu ne,colour ne kawai ya banbanta, ya iske Fahad tare da amir suna zaune a three seater ,  suna temple run, a wayar fahad din.

     Prince na shiga ya samu kujera ya  zauna, fahad yace, ya prince sannu da zuwa, dama yanzu nake shirin zuwa gaida kai.

   Prince yace a takaice , ya service din? Fahad yace alhamdulillah,muna nan muna fama, prince yace Allah ya taimaka,fahad ya amsa da amin, prince ya kalli amir dake faman game dinsa yace , amir come here! Amir ya mikawa fahad wayarsa yace ok papa, har yazo kusa da prince sai ya tuna, da sauri ya koma bayan kujera yana cewa, am sorry papa, zanyi kokari next text dinmu na samu 10, prince ya mike ya nufi bayan kujeran, amir yayi saurin guduwa kicin yana kiran grany mami grany mami, mami ta rike hannun sa Zatayi magana prince ya shigo.

      Tace prince pls ka daina dukan yaran nan , yayi karami dayin wadan nan punishments din naka, prince yace mami kyele ni dashi,ai yasan mai yayi, yasa hannu zai kamo amir, mami tace prince bar kicin nan, daga dawowar ka zaka takura yaro, prince ya juya ya fita,yana kiran fahad.

.

Ya dawo daga masallaci kenan yazo wuce dakin zuby dake kusa da nashi, yaji suna gulmar shi, tsayawa yayi yana sauraron su.

    Zuby tace wai shin waye ya sanar wa ya prince ne,?, zarah tace kee mayb fa ya prince ya saka cameras a gidan nan, kinsan soja, zuby tace noo I dnt think yasa, zarah tace kodai ya fahad ne ya fada masa, zuby tace kila, amma ni wlh harna kosa ya koma wlh, zarah tace kedai bari mutum kullum fuska a daure,kamar an aiko masa da sakon mutuwa.

Prince yaja tsaki yayi shigewar shi daki.

Yau umman su niimatu ta tashi da ciwon kai, abu kamar wasa ciwo sai kara gaba yake yi, hankalin su ya tashi sosai, habu yace niimatu ina ganin mukai umma asibiti, niimatu data buga uban tagumi tace toh yaya, amma kudin fa?habu yace muje dai muji kome ke damun ta, akwai wasu kudi dana rantawa sanusi,sai na maso su, niimatu ta kada kai, sannan ta shiryawa umma sukayi asibitin.

Doctor ya duba umma, yace hawan jini ne ke damun ta , amma zai basu magungunan da zata ringa sha , inshaAllah zata samu sauki.

"Habu yaje ya amso kudin, suka biya komai suka dawo gida, ranar ko kasuwa basuje ba, suna nan tare da umman su suna kula da ita.

."Bayan kwana biyu jikin umman su niimatu yayi sauki.

,tunda sanyin safiya ya habu ya shigo gidan.

   Niimatu na tsakar gida, tana juya kunu a wani yellow bucket ,tace yaya harka shirya?habu yace na shirya yau zamu kasuwa ,kije ki shirya kema so nake yau mu dan samu ko dari shidda ne sai mu sake siyowa umma maganinta,tunda dama na kwana biyu kawai muka siya; niimatu ta mike da  kofin kunu a hannun ta,eh gara muje gsky dan, dan ragowar garin dake gidan ya kare ma, habu yace toh yi maza ki shirya mu tafi,niimatu tace toh ta shiga daki, a zaune ta iske umma,tace umma ga kukun ki,bari na shirya shaf shaf,yau zamu kasuwa, umma tace toh Allah yayi muku albarka,Allah ya kuma bada sa'a, niimatu na cire rigar jikin ta,tayi murmushi tace amin umman mu.

Suna shiga kasuwa,mutane sai tambayar yaya habu suke lafiya kwana biyu basu zo kasuwa ba?, habu ya fada musu rashin lafiyar umman su ne kwana kwana biyu , shiyasa ,sun tausayawa yaran kwarai,dan ba karamin kokari suke ba,dan kawai su ciyar da kansu.

.

Niimatu ranar ta kara dagewa  tana  ta advertising din kayan marmarin su,har yamma tayi,ya habu yace niina muje gida hakanan,kinga mun bar umma ita daya,  tunda dai mun  samu dari biyar sauran an biyo bashi a clinic din, niimatu tace toh, suka kulle rumfar su sukayi hanyar gida.

Suna cikin tafiya,niimatu ta hango wani mai naman tsire daga tsallaken hanyar da suke ,tace yaya mu saya wa umma dan tsire kona dari ne mana, tadan ji maiko maiko, ya habu yace tsire kuma?kinsan kofa kudin maganin basu cika ba, niina a bar tsiren nan,tunda dai ba sanin mu mai tsoren yayi ba, balle ya bamu bashi, niimatu tayi murmushin ta tace bari dai ka gani yaya, ina zuwa,tayi saurin tsallakawa titin,ya habu na kiran ta amma bata tanka ba,sai saurin take bugawa, tana zuwa wurin mai tsiren tayi masa murmushin ta mai sanyi ,sannan tace malam dan Allah ka bani tsiren nan sadaka, umma na zan kai wa bata da lafiya, mai tsire da farko bai so bata ba, mai ma so tanka mata ba, amma ganin innocent face dinta da kuma cute smile dinta, sai yace toh yan'mata,ya dauko tsinke daya yana washe baki, kamar gonat auduga, ya saka mata a takarda, yace gashi, ta amsa tana  murya sosai, Allah ya zunduma maka albarka nagode sosai, mai tsire ya washe hakoran shi yace ba komai yan'mata, amma ina ne gidan.........

.

Kafin ya karasa tayi hanyar tsallake titi, da gudu ta tasar wa titin, cike da murna, bata ko tsaya kallon ko akwai motoci maso zuwa ba, sai smiling take tana kallon ya habu dake tsallake,tana daga masa takardar naman,dan ya gani.

Ya habu ya hango wata mota ta taho cikin speed sosai, ya kwala wa niimatu kira, yana nuna mata motar,dan ta koma baya , amma me kafin ta ankara motar ta kwashe ta kiiiiiiiiiiiiii.......

Toh readers waye ya buge niimatu?

waye wannan prince din

Yana da mata kuwa?toh kuma gashi harda yaro?

Miye ya faru shekaru biyar da suka wucen da prince ya kasa mantawa?

Mai zai faru da niimatu yanzu?

Ku kasance  tare da afrah dan sanin amsar wadan nan tambayoyin.

Anan zan dan tsagaita muku da labarin YAR♡TALAKAWA, sai kuma Allah ya kaimu bayan sallah,inshaAllah zan ciga ba da sanbado muku ci gaban lbrn.

        godiya mai tarin yawa ga masoyan yar'talakawa, idan nayi wani kuskure a rashin sani a yafe ni.

.

Mutuwar tsaye yaya habu yayi,ledar dake hannun sa ta fadi,idon shi ya firfito,kallon niimatu kawai yake yi,dake kwance tsakiyar titi ba rai,duk jini ya bata mata jiki ta ko ina,kamar wadda aka tunkuda,da gudu ya isa gareta ya fasa wani irin razanannan ihu,yana kuka kamar ransa zai fita, mutane suka fara cika wurin,ana ta salati.

Wani alhaji ne ya fito daga Babbar motar data buge niimatu,hankalin sa a tashe ya karaso cikin jama'ar dake wurin, mai tsire shima yana nan ya buga uban tagumi, Allah kenan yanzun nan fa yarinyar nan tabar wurin shi.

Yaya habu ya kasa tabuka komai,hawaye kawai ke fita daga idanuwan sa, ,alhajin na karasowa,yace subhanallahi,dan Allah ku taimaka asa ta a mota can sai mu kaita asibiti,ya kalli habu ya dafa shi yace kayi hakuri,yaya habu da idon shi yayi jaa,ya mike ya ciccibi niimatu,wasu samari suka taimaka masa, a bayan mota suka saka ta, habu ya shiga gaba sai gaba daya duk ya zauce, alhaji a mazaunin driver.

Jama'a sai Allah ya sawake suke fada.

.

Suna isa asibiti,alhaji ya kira police,aka sanar musu komai, likitoci suka shiga da ita emergency.

Habu ya kasa zaune ya kasa tsaye, hankalin shi a tashe yake kwarai, yasan umman su nacan na jiran isowar su, duk ya rikice,dan yasan idan umman su taji halin da niimatu ke ciki,ciwon ta na iya dawowa..

Alhajin dake zaune shima da gani hankalin nashi a tashen yake, ya kalli yaya habu yace, samari zo ka zauna,inshaAllah zata rayu,habu ya kasa gardamawa yazo ya zauna kusa da alhajin.

Wayar alhajin ce tayi ring, ya dauka bai dade yana magana ba ya kashe wayar, ya kalli habu, tundaga yanalin shigar shi ya gane cewar yaran ba masu hali bane,wata kodaddiyar shadda ce a jikin sa ,sai wando jeans duk ya yage, hakanan yaji ya tausaya musu.

Ya prince ne tsaye tare da wani sagent hamza,prince sanye cikin kayan sojoji,dawowar su kenan daga meeting,prince ya kalli sagent, we will be going out later kada kuyi nisa,sagent ya sara masa ok sir,prince ya juya zai shige cikin gida,dad ne ya fito a rikice, prince yace dad hope lafiya?, dad yace, abban  ku ne mukayi waya dashi dazun, yana hospital, prince yadan gyara tsayuwar shi yace asibiti!?, dad na tafiya wurin motocin dake compound,yace muje muje yace ya buge wata yarinya ne, prince yace dad kaje,bari nadan canzo kaya,zan same ku acan.

.

An fito da niimatu, doc ya samu abba da yaya habu, hankalinsu a tashe suka ce, doctor ya jikin nata?, doc ya dafa yaya habu yace, ku kwantar da hankalinku, mun samu mun tsaida jinin,kuma ciwokan duka anyi treating dinsu,Allah yaso ba karaya, dan haka nan da awa daya zata dawo conscious.

Abba yace alhamdullilah,yaya habu ya sauke ajiyar zuciya,yayi wa Allah hamdala,abba yace doc zamu iya mu ganta?, doc din yace yes zaku iya zuwa.

A kwance suka iske ta,duk bandeji an rufe ciwokan,yaya habu yayi saurin zuwa kusa da ita, yana hawaye, saboda tsire tsinke daya, hannun ta ya riko,abba ya tausaya musu sosai,hawaye yaji suna niyyar zubo masa, ya juya da sauri,wayar shi tayi ring,dad ne dauka yayi ya fada masa inda suke,yaya habu ya mike,ya samu abba,yace zanje gida na dawo,mun bar umman mu kuma bata jin dadi sosai itama, abba yace toh shikenan, dan'uwana ma na nan zuwa,kaje zamu kula da ita.

Yaya habu yace toh,yayi masa godiya,har ya kai kufa abba yayi saurin tsaida shi,kudi ne dubu biyu ya basa,yace kayi kudin mota,yaya habu yace a'a ka barshi,abba ya saka masa a aljihun sa,ya koma kusa da niimatu ya zauna, yaya habu ya juyo yace na gode,sannan ya fice. - dad a rikice ya shigo dakin, yayi wurin abba yace, hankalinmu ya tashi mutuka hope dai its not fatal, abba ya sauke ajiyar zuciya yace, alhndllh babu karaya, dad yace alhmdllh, bari na kira gida na sanar dasu dan kowa hankalinshi a tashe yake .

Yaya habu na komawa gida ya iske umma a zaune bakin kofa, ta buga uban tagumi tana tunanin halin da yaranta ke ciki har yanzu basu iso gida ba.

Sallamar da yaya habu yayi ya dawo da ita daga tunanin da take.  Mikewa tayi zumbur tana cewa, habu lafiya kukayi dare....bata idasa maganar ba ta lura ba niimatu a bayan sa; ina ita niimatun ne? Yaya habu ya share zufar dake goshin shi, yace, umma zauna ne tukun.

.

Umma ta zauna hankalin ta na kanshi tace, hala ta tsaya siyan kankarar data saba? Yaya habu ya girgiza kai, baya son ya fada wa umma jiyon ta ya tashi, gashi shi kuma baya son yayi mata karya, musgutawa yayi ya gyara zaman sa, sannan ya fada mata komai.

    Umma sai salati takeyi kawai, gaba daya hankalin ta a tashe yake, ta mike tana gyara zanin ta, tashi muje habu, yaya habu yayi kuri yana kallon ta, ganin dare ya tsala sosai.

    Umman ta daga murya tace" kana fa ji ina magana" yaya habu yace umma kiyi hakuri muje gobe mana; Allah mutumin yana da kirki zai kula da niimatu , umma ta harere shi, kai harma kasan yana da mutumci ko, baka san masu kudin nan da san kansu ba ko, yaya habu ya mike ya riko hannun ta, umma kada ki damu, har a zuciyata naji mutumin ya kwanta min. Da kyal habu ya samu umma ta hakura, amma duk daren sallah kawai takeyi, Allah ya bawa diyar tata lafiya.

Prince tare dasu zuby da zarah, sai mum ne suka shigo dakin dasu dad da abba suke, zaune suna jinyar niimatu dake kwance, har lokacin barci takeyi.

Mum ta karasa kusa da gadon, tana cewa, Allahu akbar, gata karama, abba yace yayan nata yace shekarunta sha biyar. Zuby dake neman zama kusa da niimatun tace gata very cute wlh, zarah tace gsky she is cute.

   Prince kuwa yana zaune a kujerar da dad ke zaune, tunda ya shigo yake amsa waya.

    Dad yace wa abba, sunce zata tashi nan da awa hudu amma gashi harda wasu mins.

   Abba ya mike yana cewa, let me call d doc, nima naga mins sun wuce, har yakai bakin kofa.

  Niimatu dake kwance ta bude idon ta a hankali, tana binsu da kallo, ganin bata san su ba, tayi yunkurin tashi, amma ciwokan dake jikinta suka mata zafi, tayi yar kara kadan.

   Abba ya juyo da sauri, mum tayi saurin cewa kwanta kwanta, kada ki fama ciwon ki, niimatu sai kallo kawai take binsu dashi, abba ya matso shima yace, niimatu ya jikin, jin ya ambaci sunan ta sai ta kura masa ido kafin tace a kasalance lafiya, dad yace sannu kinji yarinya, mum ta kalli su zarah, ku hada mata tea tasha.

   Dad ya juyo ya kalli inda prince yake, yana ta faman waya, yace kai idan waya ta kawo ka tashi ka tafi mun yafe, prince yadan juyo ya kalli abba, sannan ya mike ya fita, abba yaja tsaki shi dai yasan yaron shi ba haka yake ba, mai tausayi ne amma yanzu kwata kwata ya canza.

Sun kula da niimatu sosai, har sai karfe goma sannan driver yazo ya tafi da mum da dad da abba, aka bar su zuby su kula da ita.

Tunda safe umma ta shirya ta zauna a bakin kofa tana jiran habu ya shigo.

.

Yaya habu na shigowa umma ta mike ta rarumi pose dinta, yaya habu yayi yar dariya ya gaisheta, bata amsa masa ba tace muje, yaya habu yayi gaba sukayi hanyar asibitin, suna shiga dakin suka iske , zarah na kwance a kujera tana chatting,  sai zuby dake zaune kusa da niimatu tana rike da hannunta, ita dai yarinyar na mata kyau, duk da ta nura Yar TALAKAWA ce.

      Da sallama su umma suka shiga, niimatu na ganinta ta fashe da kuka, tana yunkurin tashi, umma tayi saurin zuwa gurinta ta rungume ta tana shafa bayanta, yaya habu dake bakin kofa yana mamakin ganin yan'mata a dakin ba abba ba.

   Zuby ta gaishe shi hakama zarah, ya amsa a sake sannan ya zauna shima. Ana haka su dad da abba da mum da mami, sai faruk dake rike da hannun ameer suka shigo, abba yayi saurin mikawa yaya habu hannu suka gaisa, hakama dad da yaya faruk.

    Mum da mami suka gaisa da umma a mutumce, . Bayan wasu yan mintoci, an gama gaisawa, su dad suka wuce office.

     ameer ne ya matso kusa da gadon niimatu yana kallon ta, ya juya ya kalli mum yace, grany, she looks like barbie ko? Duka dakin akayi dariya, mum tace ai kaine barbie din, zarah tace na mata duk boys na kallon cartoon din maza but you, sai nasu barbie da sofia the first, yaya faruk dake shirin zama yace kuma ga papan dinsa soja ba, aka sake kwashewa da dariya.

      

.

Satin niimatu daya a hospital, aka sallame su, kullum su mum da mami na zuwa hospital din, umma tun tana jan jikin ta dasu, ganin matan manya ne har dai ta saba dasu dan kullum suna zuwa harma dasu abban.

      , ameer kuwa ya saba da niimatu sosai gata dama uwar fara'a ,  duk family din suna son ta , prince kuwa tun ranar bai sake zuwa ba, yama koma lagos bakin aikin sa, dan a cewar sa bai ga dalilin da duk gidan suke tafiya hospital su tare a wurin Yar Talakawan nan ba.

Ranar da aka sallameta, yaya faruk da ameer suka kaisu gida, ba karamin tausaya musu yayi ba, ai kuwa yana isa gida yake fadawa su dad da abba. dad yaja lumfashi yace ya kamata mu taimaka musu dan na lura mutanen kirki ne, abba yace nima ina tunanin nan, amma taya zamu taimaka musun....abba na rufe baki mum ta shigo falon dauke da drinks,  mika musu drinks din tayi sannan ta zauna itama.

    Dad yace mai zai hana muyi sponsoring din abubakar din yayi karatu, abba ya kada kai hakan yayi tunda shine babba.

   Mum ta gyara zaman ta, tace maganar su neena kuke? Dad ya amsa da eh, mum tace yarinyar ta kwanta min sosai, mai zai hana mu dauke ta as nanny din ameer, naga jinin su ya hadu.

     Faruk yayi saurin cewa, yes mum hakan ma yayi sosai, abba yace toh ba matsala gobe sai kai faruk kakai ni gidan nasu nayi magana da umman tasu.

Haka kau akayi washe gari faruk yakai abba har gidan su niimatu, umma ba karamin murna tayi ba, gashi ance duk weekend niimatu zata ringa zuwan mata, yaya habu kuwa kasar Jordan zasu kaishi, murna sosai sukayi, ranar su abba sunsha addu'a a wurin umma.

.

Yau ne ranar farko da niimatu zata fara aiki a mansion din. Driver aka tura yaje ya daukota, da ledar ta, ta sako kaya kala uku da zata ringa maneji har na kwanaki biyar.

A babban falo driver ya ajiyeta, sannan yasa mai aikin gidan ta fadawa mum. Tunda ta shigo take waige waige, bata taba shiga gida mai shegen kyau irin wannan ba, maganar mum ce ta dawo da ita daga tunanin ta.

     Mum na murmushi tace sannu da zuwa neena, niimatu tayi mata nata murmushin tace ina kwana, mum tace lfy lau yasu umman naki, tace lafiya lau suna gaida ku.

  Mum tace, muna amsa tashi na kaiki dakin da zaki zauna.

   Sunje har wani katafaran dakin yayi kyau sosai, mum tace nan ne dakin ki, dakin dake kallon naki kuma na ameer ne, yana barci yau bazai je school ba, karfe sha daya lesson teacher dinsa ke zuwa, da yamma kuma yana islamiyya.

     Niimatu ta kada kai, tana murmushi, mum tace jummai zata zo ta kawo miki abinci, nizan wuce office,  Niimatu tace toh sai kin dawo.

.

Mum na fita ta zauna a bed side, ta sauke ajiyar zuciya, yau itace a irin wannan dakin, lallai ta gode wa Allah, tana cikin tunanin nan , jummai ta shigo dauke da plate na abinci, suka gaisa sannan jumman ta fita.

   Da kyal ta iya cin abincin, dan duk bata iya ci ba, tana yi tana matse fuska, a haka ta kammala.

Karfe goma ta nufi dakin ameer, yana kwance saman tautausan gadon sa, karasawa tayi cikin dakin tana kalle kalle tana murmushi,  can idon ta yakai pic din dake bisan side drawer din shi, dauka tayi tana kallo, woow ta furta a bayyane, prince dauke da ameer yana shekaru biyu, sunyi mutukar yin kyau, niimatu ta shafa pic din tana murmushi, mutum sai kace aljani.....

     "Hes my papa" muryar ameer taji...da sauri ta ajiye pic din tana kallon ameer, dariya yayi mata yace, my papa is cute ko? Niimatu tayi murmushi kawai, sannan ta mika masa hannunta, ya kama, tace muje nayi maka wanka, ameer ya make kafada, ni nake wankana....niimatu tayi dariya daga yau nizan na maka , ya sake make kafada

.

Murmushi niimatu tayi musu, tace dazu nazo, zuby ta mike rike da hannun ameer tana cewa, su little anyi new nanny,  ameer yayi tsalle yace, yes yes tafi sauran, wadan nan duka kazamai ne, yuks ya wani bata fuska, zarah dake shirin hawa sama ta kwashe da dariya, nawawo su little ansan tsabta, zuby tace kyeleshi haka zai tashi kamar babansa.

      Niimatu dake tsaye tana jinsu tayi murmushi, tazo ta mikawa ameer hannunta, lets go na sake koya maka leason dinka, ameer yayi dariya yayi waje da gudu, niimatu ma ta bisa tana kiran sunan sa.

.

Bayan kwana uku, mum ce ta shigo dakin ameer dauke da wata leda bag, lokacin niimatu na fama da ameer yasha custard dinshi amma yaki, sai gudu yakeyi yana hawan gado.

    Mum na shiga tayi mishi tsawa, come on dear idan baka shanye ba, I wont phone your papa today, ameer yayi saurin zuwa ya zauna kusa da niimatu, ya bude baki yace haaa, niimatu tayi smiling ya fara basa yana amsa, mum ta zauna a bed side, ta mikawa niimatu bag din dake hannunta, gashi zan aike ku gidan sister dina, tare da ameer sai ki bata wannan.

     Niimatu ta amsa tace toh shikenan.

     Tana gama  canza mishi kaya, sukayo kasa, a dinning suka iske zuby, tana cikin abincin rana, zuby tace wa ameer sai inaa little , yayi gunta yana dariya gidansu fu'ad zamuje, zuby tayi dariya, toh a gaida ikram ,ameer na tafiya waje yace okay.

.

Sun isa kantamemen gidan sister din mum, driver yayi parking , niimatu ta fito sannan ta budewa ameer shima ya fito, ameer ne ja gaba har kofar shiga gidan, sunyi knocking, ba'a fi minti daya ba aka zo aka bude musu.

Mai aikin gidan ce, niimatu ta gaishe ta, ameer kuwa ciki yayi da gudu yana kiran sunan fu'ad.

Wata kyakkyawar matashiyar yarinyar ce ta fito daga wani daki dake cikin falon, sanye take cikin wata english gown purple, bako dankwali a kanta, sai yanga take abunta, niimatu na ganin ta tayi saurin cewa, ina wuni? A tunanin ta ko yarinyar ce matar gidan, tunda tana da jiki.

.

Yarinyar ta juyo, ta wani watsawa niimatu kallon banza, ameer yayi gunta yayi hugging dinta, smiling tayi kawai tace dear, sai yau zaga daman zuwar mana? Ameer yace aunt ikram ina fu'ad? Da mummy?  Ikram na shirin zama tace fu'ad ya fita da ya moha mummy na sama je ka kirata.

   Ameer yayi saman da gudu, niimatu kuwa ta rasa yama zatayi, ita ba halin ta zauna tunda basu bata izini ba, gashi ita bata da jumurin tsayuwa.

       Ba'a dade ba ameer ya sauko tare da wata mata, da ganinta kasan hutu ya kwanta mata, taci ado abunta.

      Niimatu tayi saurin cewa, ina wuni, waigowa tayi ta wani kallo ta, ta yamutse fuska, sannan ta zauna, niimatu ta karasa ta ajiye mata leda bag din da mum ta bata , sannan ta koma ta tsaya. Mummy ta kwala wa mai aikin ta kira, lusy!!!! Lusy ta shigo cikin sauri yes ma, mummy ta nuna mata ledar da niimatu ta ajiye tace, ciro min kayan dake ciki, lusy tayi saurin ciro wa ta ajiye mata a centre table, mummy ta kalla sannan ta kalli niimatu kice mata sunyi, niimatu tace toh, sannan ta kalli ameer, muje little master,  ameer ya make kafada kije nizan jira fu'ad a nan, niimatu tace no muje akwai leason yau, ameer ya kara shigewa jikin mummy yana cewa no bazani ba, niimatu kuwa ta dage suje.

    Tsawa ikram ta mata, keeee ki kyele shi mana, or r u his mum ne, yace bazai biki ba sai ki tafi ai, niimatu ta saddar da kai kasa, sallama sukaji, da gudu yaron da suka shigo tare da wani saurayi yayi wurin ameer, shi kuwa saurayin yayi wurin mummy ya zauna a kasalance, ohh God, am darm tired, bazan sake gingin fita da yaron can ba, mummy ta shafa fuskar sa my boy, sannunka da kokari, just jiya ka dawo daga china, yau ka biyewa acicin nan kuje wani yawo.

Samarin ya tabe baki, ya na iya da rigimar sa, mummy ta kallo wurin da niimatu take a tsaye, kee shiga kicin kice wa lucy ta kawo wa moha drink yasha, niimatu tace toh tana murmushi  ta mai karawa fuskar ta innocent,  tayi hanyar inda taga lucy ta fito, tana tunani a zuciyarta, lallai wannan matar batayi halin mum ba ko da kwayar zarra, shi kuma kato dashi amma sai wani shagwaba yake mtsww

.

Taje ta kira lucy, aka kawo wa moha drink, sai kallonta yake, kallon rashin sani, ameer na haduwa da fu'ad sukayi dan wasa sai, yazo ya same ta a waje wurin balcony tana kallon flowers,  dan zaman cikin ya ishe ta, ko nace tsayuwar cikin. Aunt neena muje gida, smiling tayi tace toh ta mika masa hannu.

Yau watan ta daya da fara aiki, kullum weekend tana zuwar wa umma, yaya habu an gama masa komai na tafiyar sa shima next week zai tafi, umma a kullum tana godewa Allah daya kawo masu taimakon su.

Yau da yamma ci, suna falo ita da ameer da zarah da zuby, game sukeyi , irin wanda ake kullewa mutum daya ido sai ya nemo sauran, mum na wurin mami, suna firan su, dan duk yamma sai sun hadu sun gaisa, gwanin sha'awa kamar wasu sisters suke..

An kolle wa neena ido sai faman neman su takeyi, sai dariya suke mata dan sai karo take ci da kujerun falon.

       Bude kofar falon akayi, zarah dake kusa da kofar, ta kallo kofar zatayi masifa mai yasa ba'ayi knocking ba, aikuwa sukayi 4 eyes da ya Prince, har sai data sarke da miyau dan batayi tsammanin ganin saba, duk da yake ma idan zai zo baya wani sanar wa kowa. zuby ma ta kallo kofar itama taga ya prince, da sauri ta sauka daga bisan kujerar da take tana yiwa neena dariya, ameer ma sai da hanjin cikin sa sukayi kara , dan yasan halin papa dinsa.

.

Ita kuwa neena da ido ke kulle, sai faman neman su takeyi, har taje wurin kofa tana laluben ta, jin ta taba mutum sai ta hau murna, ta rirrike kam tana cewa, ya zarah na kama ki, now turn dinki ne, sai tattaba shi takeyi tana tsalle, wani kallo yabi ta dashi, daga kasa har sama, zani ne a jikin ta na atamfa, yadan koke, sai top data dan sha jiki itama ta fara fading, tabe baki yayi, ya wani yamutsa fuska , fuskar nan ta tamke, yasa hannun sa ya turar da ita , neena na faduwa tayi yar kara, ta bude idon ta, bayan shi ta gani yana hawa sama,  hes a tall n giant man, yana sanye da wandon soja da body hug fara, saboda yadda yayi building din jikinsa top din ta zauna masa sosai a jiki. yana tafiya cikin kasaita, WANNAN WAYE? shi kuma, neena ta furta, a tunanin ta a zuciyarta tayi maganar amma ashe a fili tayi, sai dai taji muryar ameer kusa da ita yace, he's my Papa......

Mikewa tayi tana wash, zuby tayi saurin mikewa tsaye tana wiki wiki da ido, zarah ta rike kugu, yau mun shiga uku, zuby tace tara ma muka shiga ba uku ba, kinsan yadda ya tsani ganin babba yana wasan yara!!! Neena ta mike itama tana kallon su tace, wancan shine papa din little master???, suka hada baki wurin cewa Yes shine, a zuciyarta tace lallai ashe akwai rigima, dan da ganin sa dan rainin wayo ne.

Da daddare a dinning,  dad da mum da zuby, suna cin abinci, prince ya sauko shima, dukawa yayi ya gaisar da iyayen sa, mum ce ta amsa masa a sake, dad kuwa daure fuskar shi yayi kawai, prince ya mike shima ya zauna.

    Gabadaya zuby hankalin ta a tashe yake, bata son ma su hada ido dashi, kee! Baki iya gaisuwa bane? Zuby har sai data kware da juice din da take sipping,  na'am ehh uhm ina wuni? Mtsw prince yayi tsaki, sannan ya kalli kujerar ameer yaga wayaam.

    Zuby ya kalla yace ina ameeer din shi?, mum tasa baki tace, yana daki da nanny dinsa, kasan yanzu baya cin abinci a dinning,  girki take masa suci a daki.

   Prince ya mike, nanny? ?? Wace irin nanny ce da za'a bari tana bawa yaro abinci a daki

.

Dad a fusace yace, idan baka son nanny ta kular maka  da yaro, mai ya hana kayi aure duk shekarun nan!!! 

      Mum da zuby sukayi saurin kallon dad, prince ya wani wuce fuuuu, ya haura sama, direct dakin ameer ya nufa a kule, wacece wannan da zata sa dad yayi masa maganar nan daya tsana a rayuwar sa"ace yayi aure".

Neena da ameer a daki, ta gama basa abincin sa, ta zo zata dauke plates din, ameer yayi tsalle ya haye bayan ta yana dariya, neena tayi dariya itama ta dauke shi, ta fara masa doki a bayanta. Sai dariya yake kyalkyatawa, suna cikin wasan dokin su, prince ya banko kofar ya shigo.

Tamkar wani zaki ya shigo musu, da sauri neena ta juyo dan ganin waye, ya shigo haka ba sallama balle knocking,  ganin wannan kyakkyawan mutumin nan tayi wanda kullum take yaba kyawun shi, idan ta kalli pic din nan dake ajiye a bisan side drawer din ameer, amma mai domin taga murmuahin nan nasa na pic, sai taga fuskar nan a hade gam.

.

Wani banzan kallo yabi da shi, ameer kuwa yayi saurin saukowa daga bayan ta, yayi wurin papa dinsa, papa papa,! Prince ya riko hannun sa, zai fita da yaron, neena tayi saurin cewa, lokacin barcin sa yayi...prince ya tsaya cak, lallai wannan yar kauyen nan  yar talakawan, shi take fadawa lokacin barcin dansa yayi, ita din ma bata wuce a raine ta.

Neena ganin ya tsaya sai ta matso, hannu ta mikawa ameer tace, little master,  its time to sleep, muje ka kwanta, ameer kuwa ya mika mata hannu.

    Prince ya juyo ya kalle ta, ta kuwa kura masa nata sexy  idanun, prince yace, kee wacece da zaki fada min lokacin barcin dana yayi? Neena tayi masa murmushin ta tace, saboda nice mai rainon sa, prince ya kara kulewa see dis small rat woo, hararta yayi yace, na kori nannies sunfi goma, dan bana son raini, da shishshigi, dan haka ya nuna ta da yatsa idan baki kiyaye ba, zakiyi..... ya nuna mata kofa.

     Neena tayi kasa da kanta kawai ta koma wurin ameer dake jiran ta ta kwantar dashi, prince yayi waje ya banko kofar, neena ta kalli kofar tace, an dai yi kyaun dan maciji.

.

Washe gari da safe, neena ta gama shirya ameer dan zuwa makaranta, ta kai shi har mota ta dawo, mum na saukowa dan fita zuwa aiki, neena ta gaishe ta sannan tace, ki shirya wa Na'im breakfast pls, ladi mai aiki bazata zo aikin safe yau ba, neena tace, toh mum, ta bude baki ta tambaya waye shi, amma har mum takai kofa dan cikin sauri take.

       Tana nan tsaye ta rasa mai zata girka , dan bata masan waye Na'im din ba, zuby ce ta fito tana gyara gyelen ta, da gani itama cikin saurin take, neena ta tare ta dan ta bata shawarar maia zata girka, tace anty zuby ina kwana? Zuby na saurin ta tace lafiya neena, nizan fita lecture sai da rana zamu dawo, neena tace anty zuby dan minti uku, zuby tadan tsaya tace neena zarah na waje tana jirana yi sauri, neena tayi saurin karasowa wurin ta tace, mai zan dafa na breakfast wai na Na'im? Zuby tace ki dafa masa abu mai sauki kawai tunda bawai kin kware bane, tayi saurin yin waje.

.

Neena ta rike kugu, abu mai sauki, miye mai sauki? Mtsww , kicin ta nufa , tayi tsaye tana tunani, can tace, bari nayi masa, koko da kosai , tayi murmushi abincin yaya habu kenan.

Ai kuwa niimatu tahau, hada kokon ta dama akwai kullun, kosai kuwa har fita tayi tabi layin su neman nika da kyal ta masu wurin da akeyi, aka mata ta dawo da sauri ta hada komai, tana gamawa ta wuce daki da sauri tayi wanka sannan ta dawo falo tana karatun wani book na uncle faruk daya manta.

.

Tayi awa daya amma shiru bako bai zo ba, can taji kamar tafiya daga bayan ta, saurin juyowa tayi, taga papa din ameer ne, prince bai ko kalli inda take ba, dinning ya nufa yaga wayam, ladi ya fara kwala wa kira, yaji shiru, neena tayi saurin zuwa wurinsa tace, ladi bata zo ba, ya wani yamutsa fuska, yace ina abincina? Niimatu tace nima ban sani ba, yaja tsaki ya ciro wayar sa ya kira mum, can ya kashe wayar ya kalli neena yace, ke! Tayi saurin kallon shi, yace mum tace abincina na wurin ki, niimatu ta girgiza kai, ni abincin Na'im akace nayi

.

A fusace prince yace, kee da Allah je ki kawo min abincina!!!, neena tayi saurin shigewa kicin dan yadda yayi mata tsawa ba karamin tsorata tayi ba.

Yana zaune a dinning, yana danna wayar sa, duk a kule yake yau dinnan, gashi suna da meeting da general yau.

.

Neena ta ajiye masa abincin, ta juya zata wuce, dan ta fara tsorata da shi, tsawar ya kara daka mata, ke! Zo kiyi serving dina!, neena  ta dawo kamar ta fashe da kuka.

    Ta fara bude flask ta zuba koko a cikin cup, da sauri prince ya matsa yana toshe hancin sa, ya mike yana nuna cup din, miye wannan haka dake da odour din nan, neena ta kalli cup din, koko ne lafiyayye tayi, tace koko ne, prince yace yuks, pls jeki zubar dashi pls, neena ta sauke lumfashi ,sannan ta dauke duk abunda ta kawo ta kai kicin, takaici ya ishe ta sosai, duk wahalar dasha ya zama a banza.

Washe gari Saturday ne, ranar zataje weekend dinta, kuma tayi sallama da yaya habu.

Sai data gama komai na hidimar ameer, sun fito falo ita dashi, uncle faruk, zarah, mum, da prince ke a zaune, da gani dai prince din yau shima baya da fita.

Suna shiga falon, neena ta gaishe su, hannunsu a sarke ita da ameer, mami tace, su ameer za'ayi kewar neena, mum tace aikuwa dai, ta bar mana rigima.

     Zuby ce ta shigo falon da cup a hannunta, wannan kokon fa a flask na ganshi, kuma da zafin sa, tayi one sip tace wow da dadi, neena tace ni nayi jiya, ta kalli prince da gefen ido, ya wani basar kamar baya wajen.

    Zarah ta mike ta nufa kicin din tana cewa, nima bari na zubo nawa.

    uncle faruk daya gama amsa waya yace, neena kawo min book din nan pls, neena tayi saurin zuwa ta kawo masa, tana mika masa tayi musu sallama ta tafi.

.

A tsakar gida ta iske umma, tana zaune suna fira da wata laraba, nan makotan su.

Da gudu ta shigo gidan cikin murnar ta, umma tace kee, kuma bako sallama? Neena tayi dariya dokin ganinki ya mantar dani umma na, laraba tayi dariya, tace niimatu har an shigo mana kenan?, neena na shirin zama tace ehh na shigo inna  laraba ina wuni?, inna laraba ta amsa da lafiya, sannan ta mike tayiwa umma sallama ta fita.

.'

Su niimatu sunsha fira sosai da umman ta, sai tambayar yaya habu takeyi, umma tace ai ya fita siyo wasu kaya dazai tafi dasu.

Bayan sallar mangariba, yaya habu ya shigo gidan, da gudu neena taje ta rungume shi tana murna, yaya habu yayi dariya, ke bakya girma, neena ta shagwabe fuska tace, baka missing dina, kullum nazo weekend ban cika fa haduwa dakai ba, yaya habu ya shafa kanta, ina missing dinki mana, ya mika mata wata leda, ta amsa tana murna, laaah fruits ne umma, umma tayi murmshi ai sai ki ta sha, sarkin kwadayi.

Washe gari da sassafe, yaya habu yayi sallama dasu, neena tayi tayi umma tabar ta ta raka sa amma umman tace a'a; har kuka tayi dazai wuce dan Allah ya hada jinin su sosai da yaya habu.

.

Ranar da neena ta tafi weekend, da daddare family na falo, abba daya dawo daga tafiya yace, su neena har an tafi weekend dinne? Mum tace ta tafi dazu da safe, dad yace ai yarinyar tana kokari sosai, faruk yace gaskiya kam, kullum tana nan tare da ameer tana kula dashi, ameer dake kwance kusa da zarah ya mike, yayi wurin mum yace, grany ina jin barci, mum ta kalli zuby, zubaida kai shi dakin shi, zuby na mikewa ameer ya make kafada, ni wurin papa zan kwana, dad yace toh kaishi wurin mahaifi  nasa, ai gara yadan taba rainon dan nashi, abba yace, na'im kam sai addu'a, dad yaja tsaki, ai ba biye masa zamuyi ba, shekaru har shidda, amma mutum ya kasa ci gaba a rayuwarsa, mami tace a kara masa hakuri yaya, mum tace, abun nasa ne ya wuce wuri dayawa, dad yace , ni na gama yanke hukuncin yi masa aure da koma wacece, mum tayi saurin kallon dad,"ita kam bata son ayiwa danta dole"

     Dad ya gyara zaman sa yace, idan faruk ya kammala bautar kasar sa, hadasu zamuyi ayi musu aure kowa ma ya huta, abba ya kada kai hakan ma yayi.

Zuby na kai ameer, ta iske prince a zaune yana amsa waya, da gani da ogan sa yake magana, dan yadda ya nustu.

     Tana kaishi tayi saurin barin wajen.

  Ameer ya samu wuri ya zauna, yana kallon papa dinsa dake waya, prince na gama amsa wayar ya kallo ameer, come n sleep dear, ameer ya mike ya karaso kusa dashi, yace papa sai an canza min zuwa kayana barcina, an wanke min baki, prince ya mike a gajiye yace , kaje kayi sai kazo mu kwanta cos am sleepy already,  ameer yaa make kafada papa, ni ban iya ba, prince ya tsaya daga cire rigarsa da yake yace, ohh god toh muje na maka.

Sunje dakin, komai a kimtse an gyara, prince ya dauko masa wasu green nighties,  ameer yayi saurin cewa , no papa green din na monday n friday ne, prince ya saki baki, kayan barci ake raba wa kwanaki, jawo amir din yayi yace, oya sa ni bana da time, amir ya turje yaki saka kayan shi na friday ne da monday, ai blue din ne na Saturday,  prince yajaa tsakk ya dauko masa blue din ya saka masa.

.

Oya muje toilet ayi brush din, zasu shiga amir yayi saurin tsaida prince, stop papa, ya dauko masa takalmin da neena ke sakawa idan zata shiga toilet din, sa wannan, sanna shima ya saka nashi, yana murmshi,  prince yayi dan mamaki, amma ya share kawai, yayi masa brush suka fito.

Da safe kuwa, amir yaki saukowa daga kujera, shi sai an bashi hot milk da anty neena ke basa , prince yayi tsakin, yayi fadan amma amir yaki saukowan, can ya fita yana bala'i, a falo ya iske mum da zuby a zaune suna hada wasu takardu, mum wai ina wannan nanny din taje ne? Mum tace taje weekend,  prince ya rike kugu mum ta dawo gsky, mum tayi saurin kallon shi, ban gane ta dawo ba,? Prince yace yaron nan ya cika rigima wlh , ya kalli zuby, ke kai masa hot milk nina gaji, ya zauna gwajab a kujera, mum ta kalle shi tace, na'im ! Ta kira sunan shi, yes mum ya fada yana gyara zaman shi, mum ta gyara muryar ta, ya kamata ace by now ka manta da dik abunda ya faru baya, u should go on wit ur life my child,  kaga fa dad dinku ya gama shawarar yi maka aure tare da faruk, da sauri prince ya kalle ta "aure" mum ta tace aure mana, kullun mune hiring nannies,  ya kamata kodan amir kayi auren nan na'im, prince yayi shiru, mum ta matso kusa dashi tace, mai zai hana ka fara zuwa wurin ikram , 

Prince ya sake kallon mum ya maimaita suna "ikram!!!!!! Mum tace ai gara ikram din tunda baka san dawa dad din naku zai hada ka ba

.

Prince ya kura wa mum ido, mum ta sake muskutawa tace, u know bazan baka shawarar banza ba, ikram wayayyace, she is educated n social too, kawai dai kula da ameer dinne I knw bazatayi ba, prince ya tabe baki, yace den mum ba amfanin auren ta, cos ni kozan aure, zan auri wadda zata kula min da ameer ne kawai, bana da ra'ayin sake soyayya da ko wacce irin mace, yana maganar ransa a bace.

   Mum ta sauke ajiyar zuciya, kada ka damu, ni da mummy (mummy din su ikram kenan), mun yanke shawarar yadda komai zai kasance, ranar na aiki neena, nanny din amir, mummy ta ganta, kuma tayi mata , so mun yanke shawarar koda ka auri ikram, neena sai taci gaba da kula da amir din, kawai makaranta zaka nema mata taci gaba.

       Prince yashafi gefen fuskar sa, ya hura iskar bakin sa, sannnan ya kalli mum, toh shikenan ba matsala, amma gara dai ta san manufar auren mu, dan mum kin sani.....mum ta tsaida shi yayi na sani na gane, zan fadawa mummy komai.

Niimatu tayi kwanakin ta biyu tare da  umma, cikin gata dajin dadi , kamar kada su rabu.

Da sassafe ta shirya ta hau hanyar komawa aikin ta.

Ta shigo gidan ba kowa a falon, taji motsin ladi a cikin , lekawa tayi tace ina kwana inna ladi?, ladi ta washe baki, antyn amir kin shigo? Neena tace na shigo inna ladi, bari nayi sauri naje na tashe shi,kada ya makara, bakwai har tayi ma, inna ladi tace toh maza jeki, neena tayi saurin haurawa sama.

Tana shiga dakin amir taga wayam, ta rike kugu, ina yake kuma? Tayi dakin zuby ta murda ta shiga da sallama, zuby na kwance tana ta sharar barci abunta.

.

Niematu ta matso kusa da ita, tasa hannu tana dan tattabata, anty zuby, anty zuby,! Zuby ta murgina tace a muryar barci uhmm na'am, neena tace ina little master ya kwana? Zuby tayi hamma tace wurin ya prince, neena tace uhmm, kamar bata ji ba, zuby tace haba neena wurin papa dinsa nace, oh wurin papa dinsa, ta mike ta fito.

A tsaye ta tsaya bakin kofar dakin, ta kasa kwankwasawa, sai yawo takeyi bakin kofar ta rasa yadda zatayi , ga  time nata wucewa.

Mum ta fito daga lungun dakin ta, ta hango neena na kai wa da komowa, tace neena lafiya kike nana a tsaye, neena tayi saurin gaishe da ita,  mum ta amsa tace, kiyi knocking amir na ciki wurin papa dinsa, mum ta wuce abunta.

Neena tayi shahada tayi knocking kofar, taji shiru, ta sake , shiru, tayi dan tsaki, yanzu ya zanyi kenan ga time na wucewa, murda kofar tayi, aikuwa a bude take, ta tura ta shiga dakin.

Woooooah wooah ta furta, dakin katon gaske ne, ga bed mai shegen kyau da tsada, harda falo a ciki, da s gymnasium wurin motsa jiki, ga wasu pictures guda biyu  manya manya a like jikin bangon,  nashi ne dana amir, sunyi masifar yin kyau, sai kamshi da sanyin AC kawai.

.

Tana gama kalle kallen ta , ta nufi wurin gadon tana lallabawa kamar wata barauniya.

Tazo side din da amir yake kwance, ta wura masa iska a kunne, shiru bai motsa ba, ta dan kallo prince tana dubawa kada ya ganta, tasan kashin ta sai ya bushe.

Ta kara matsowa ta sakala hannunta , gashi sun bar space a tsakiya, da gani barci ne yayi barci suka rabu.

Tana ta kokarin ciccibar amir, taji lallausan hannun prince ya tamko hannunta, ware idanun ta tayi da sauti ta kallo shi, gabanta na faduwa, a tunanin ta koya farka ne.

Bata ankara ba taji an jawo ta, wani super da tayi , saura kadan ta fadowa amir.

Sai gata a tsakiyar gadon, gaba daya lumfashin ta ya kusan daukewa, sai wiki wiki takeyi da idoo, zata mike, ya sake jawota ya manna a kirjinsaa....

Hehe bari nadan tsagaita anan sai leta kuma - Kasa tabuka komai tayi, wani kamshi kawai ke fita daga kirjin sa, yana bugun hancin ta, dara daran idanunta   ta dago ta dan kalli fuskar sa, mashaAllah, tun daga cute pink lips dinshi ta fara kallo, zuwa pointed hancin sa, tana kara gaba takai eyes din sa, medium ne a lumshe suke sai zara zara eye lashes dinsa, ohh God kawai ku sinfantashi da (shakti arora ko arjun kapoor).

Amir ne yayi motsi, tabi  a hankali tadan  zare jikin ta daga nasa, kara jin hannun sa tayi ya jawo taaa , ta tafi luu, fuskukin su suka hade, da juna,  lips dinsu suka gaisa da junaaa....a take ta lumshe idanunta.....

Gaba daya lumfashin neena sai daya tsaya cak na wasu sankwanni, jin kamar amir na niyyar mikewa yasa tayi kokarin zare hannun prince ta mike,  a hankali ta sauko daga gadon, ai kuwa tana dira amir na bude ido, yana ganinta ya amir da sauri zai kira sunanta, tayi saurin zuwa ta rufe masa baki, taja hannun sa suka fito daga dakin.

Suna shiga dakin amir din, ya rumgume ta yana murna, itama murnar take , tace little master , muje nayi maka wanka time ya kusa, amir yace ok, suka shige toilet. 

.

Da rana wuraren karfe 12 neena ta gama gyarawa amir dakinsa, ta wanke toilet, ta fito dan taya inna ladi aiki, dan haka take kullum, idan ta gama nata sai taje tadan taimaka mata.

Tana shiga kicin ta iske zuby a bakin fridge,  zuby ta juyo tace neena, ashe ba sauran milk shake din amir , sai sauri nake nazo na dauki dayan daya rage, inna ladi dake yanka cabbage tace, aikuwa dai dazun faruku ya shigo ya dauka, wai yana jin shan wani abu mai dadi..zuby ta tare lumfashin inna ladi, shine sai kika nuna masa milk shake din.

     Neena tayi dariya, anty zuby bari nayi miki wani now, zuby ta ajiye bottle water din hannunta, inaaa bazai yiyuba, tayi hanyar fita tana cewa, bari naje na amso, shi ya faruk dinnan ance masa shi kadai keson kayan dadin, amso zanyi tayi kofa tana masifa, neena ta bita tana cewa anty zuby ki bar masa nayi miki wani, inna ladi kuwa mai zatai inba dariya ba, abincin amir akewa wannan hadamai.

Direct side din abba sukayi, neena na baya. Suna shiga suka iske zarah kwance tana kallon keeping up with the kardashians, zuby na shiga tace, sisi ina ya faruk, kafin zarah ta amsa mami da abba suka fito da gani fita zasuyi, zuby tayi gum ta gaida dasu, neena ma ta gaishe su, suka amsa musu a sake suka fice.

Zarah ta mike tana cewa, kee sisi lafiya kuwa, ji yadda kika fito fa, kayan barci a jikin ki, gashi kinsan Sargents din ya prince na around,  zuby taja tsaki, for goodness sake ina ya faruk?, zarah tace yana gym a garden.

Zuby tace good,tayi waje fuuu..su neena na biye da ita suna mata dariya (dama zuby akwai masifa, ga saurin yin fushi)

.

Suna isa ta shiga rumfar gym din a masifance.

   Aikuwa ta iske shi yana motsa jiki yana sipping din milk shake din.

      Tace haba ya faruk,! Sai ka dauki kayan.....bata karasa ba ta hango prince a kwance yana press up,  da kyal ta iya karasa "kayaaan"

Prince ya mike, fuskar nan kamar zaki a tamke, ya kalle su, yace da muryar sa kamar mai jin barci, kee baki da kunya ko! Kin kwaso jiki kinzo ki masa fitsara, ji ji, ya nuna jikin ta, wit those slping clothes kika wuce ko'ina kika zo nan! Zuby tayi wiki wiki kamar mai shirin yin kuka, su kuwa su neena baya baya sukayi,  suka sulale abunsu.

    Ranar kuwa zuby sai da tasha punishments a wurin prince, yaya faruk kuwa yana gefe yana mata gwalo danshi akwai shi da zolaya.

,

Ranar friday, da sassafe mum ta shiga shirye shirye, mami ta shigo itama sai taya ta takeyi, zuby suna daki tare da neena da amir, wani movie suke kallo a laptop din zuby din.

        Zarah ta shigo dakin a gajiye, sisi kinji dadin ki wallahi, yau munci uban mu wurin, dr Ak saleem, kinga uban questions , zuby ta kwashe da dariya, kai dan Allah, kice yau su sumzzy anci uban cin biro, zarah tayi tsaki ba sumzzy kadai ba yau wallahi harda wannan, saleem din kin gane shi ai, zuby ta sake kwashe wa dariya dont tell me mai yawan zuwa cafeteria dinnan.

   Sai firan su sukeyi, su neena kuwa hankalin su gaba daya a kallon da suke yake.

Sun sauko, suka iske falon an gyara shi sosai, zuby ta zarah, wai wane irin bakine zasuzo yau dinnan, zarah tace nida na dawo dazun..mum ce ta fito daga kicin tana kiran neena, neena! Neena! ,  neena ta amsa, na'am mum, mum ta mika mata kudi, ga wannan kije driver ya kaiki ki siyo min fruits , neena ta amsa kudin ta riko hannun amir muje ka raka ni.

Suna kai wa bakin kofa, su mummy suma suna saka kafa, ikram tasha ado sosai, cikin fitted gown red n green, tayi kyau sosai, sai fuad .

   Da sauri neena taja baya, ta gaishe su, basu ko amsa mata ba sukayi kici, amir ya yace da fuskar shi a shagwabe, anty neena kinga fuad yazo, naje muyi wasa,? Neena tayi murmushi, kai dai bakason rakani, ta saki hannun sa taje yaje suyi wasan da fuad din.

Tana fitowa wurin balcony,  sukayi karoo da MOHA da sauri taja baya tace, kayi hakuri ban lura bane, moha ya kalli fuskar ta, a zuciyarsa yace, she's cute really.....ya wani kura mata ido....

.

Neena ta zagaye shi tayi gaba, moha yayi murmushin yan duniya, ya shige cikin gidan.

Neena ta samu idi driver a zaune bisan benci suna fira da mai gadi, ta fada masa mum tace ya kaita garki market tayi sayayya.

Suna isa , taje ta siyo duk abunda mum tayi mata list. 

      Suna yin parking, ta fito ta zagayo wurin but, ta kwashi ledojin kayayyakin da suka siyo, ledojin sun mata yawa sosai a hannunta, da kyal take tafiya ma.

Faruk ne ya shigo side din, yana hango ta tana cicciban ledojin, yayi murmushi, ya daga murja yace, nanny!  Neena tayi saurin juyowa, tana ganin shi tayi murmushi,  yaya faruk" faruk ya karaso wurin ta, yasa hannu ya amsa ledaoji guda biyu, let me help, neena tayi smiling daka barshi ya faruk, faruk yace kaji ta sai kace zaki iya dauka ke day.

.

Suna cikin conservation dinsu, motar ya prince ta shigo cikin gidan, motoci biyu ne? Sojoji suka fito daga dayar motar, sukayi saurin zuwa suka bude wa prince kofar mota, yana fitowa sukayi saurin sara masa, fuskar nan kamar garwashi.

Yazo fuu zai wuce su faruk, faruk yayi saurin cewa ya prince harka iso, dama dad ne yace na kira ka, prince ya kada kai kawai ya shige ciki.

    Neena kuwa da kallo ta bishi, a zuciyar ta tace, shi kullum fuska a daure.

   

   Ta kofar kicin suka kai kayan, mami da inna ladi ne a ciki, mami tace wa faruk, na'im din ya iso ne? Faruk dake daukar apple a leda yace ehh yanzu ya shigo, mami tace kaima sai ka shiga dan su abba na falon, faruk yace toh sannan ya fita.

Neena kuwa zama tayi, ta shiga taya su mami aiki, ita dai tana son ta koya girkin zamani.

     

Bayan sun kammala komai da inna ladi, ta dauki abincin ta taci, sannan tace wa inna ladi, inna bari naje nadan watsa ruwa, tayi saurin ficewa.

Tana zuwa dakin ta, ta cire kayan jikinta, ta dauki zanin ta ta daura, dama toilet dinta ya samu matsala, dan haka sai ta saka hijabi ta fito ta shiga dakin amir, ba kowa a ciki su amir na side din mami tare dasu zuby.

Cire hijabin tayi ta shige toilet.

Bango kofar dakin yayi ya shigo, ya fada kan gadon yana sauke lumfashi, ya naushi gadon yace ohhh darm it !!! Ya zakayi su dad su masa haka, a fili ya furta a hate Woman, dey r all d same!!!!!.

Neena na kammala wankan ta, ta dauro zani ta bude kofa, prince najin ana bude kofa yayi saurin kallo kofar, sukayi for eyes da neena, da sauri ta koma toilet din tana dafe da kirjin ta.

Prince yaja tsaki, mtswwww ita kuma wannan fa, me zan gani a jikin ta, yarinya karama da ita sai shegen fi'ili, harda su yawo da hijabi, ya sake jan tsakin, ya gyara kwanciyar shi, idan bazata iya fitowa ba sai dai ta kwana.

Motsin bude kofar dakin yaji, yayi saurin rufe ido, a tunanin sa mum ce.

.

Ikram na shigowa dakin, ta zauna kusa dashi, tana yanga, prince najin kamshin turaren bana mum bane ya bude idon shi, ikram ya gani zaune kusa dashi ta kura masa ido," ita dai tana son prince kamar ranta, shiyasa ta matsawa mummy tayi wa mum maganar , gashi har zata mallake shi" 

     Kee, prince ya fada, dan yadda ta wani kura masa ido kamar zata cinye, ikram tayi fari da ido, tayi murmushi, ya prince dama su mum ne sukace nazo mu fahimci juna, prince ya yamuste fuska, bai ce mata kala ba, wayarshi tayi ringing,  ya dauka , sai da ya dauki mintuna yana magana a wayar, ikram haushi ya ishe ta, taso suyi fira.

Neena dake toilet kuwa tana jin duk abunda suke cewa, tabe baki tayi, tace, aikowa wannan ikram din zata sha fama.

Mikewa prince yayi daya gama wayar, ya kalli ikram, sai muje mu fada musu ko? Wani kolulu ya tsaya mata a wuya, toh mai zasu fada, bayan basuce komai ba. Prince yayi gaba ta mike ta biyo shi.

Neena najin sun fita, tayi saurin bude kofa ta fito, tai saurin zuwa ta bude kofa zata fice itama.

Dai dai lokacin shima prince ya bude zai dauko wayar sa daya manta, sukayi karoo gumm

   Allah ya taimaka, bata da tsayi , kanta ya bugi korjinsa, jin santsin kafar ta zai fadar da ita , tayi saurin sa hannayen ta ta riko shirt din prince ta kankame shi tsammmm

.

Wani yarr yaji, da sauri yasa hannun sa a kafadar ta, ya ture ta, tadan buge da bango, yayi saurin karasawa ya dauki wayar sa ya fice, neena tayi dan guntun tsaki, ya zata ko wacce mace ce zata so shi, dan kawai yana da kyau, tayi wucewarta daki, dan saka kaya.

Prince na saukowa kasa, ya iske su abba, dad, mum, mami, mummy, faruk da ikram duka zaune, yana saukowa, abba yace, yauwa na'im zo muji ya kukayi, dan bama so bikin ya dade.

Ikram ta mike tazo inda prince ke tsaye, tace, mun riga mun fahimci junan mu, kuma mun yanke shawarar, ayi bikin nan da wata biyu.

.

Falon ya dauki, alhamdulillah, mum sai dadi takeji, tasan ikram wayayya ce, zata ja ra'ayin prince ya sake.

Dad yace toh yayi, Allah ya kaimu, sannan ya kalli faruk, kai kuma fa, dis week zaku kammala nysc din ai ko?, faruk yace eh dad, abba yace munyi maganar da mamin su, mun yanke shawarar hadashi da DEEJA (diyar yayar mami), faruk yayi saurin kallon abba, yace but abba, mami ta zungure da kafa dama kusa suke, abba yace but wat? Bamu isa mu zaba maka mata bane?, faruk yayi shiru.

       MOha ne ya shigo rike da hannun  su amir da fuad, sunyi kaca kaca da milo, suna shigowa mami ta mike, ohh God yaran nan bazaku kashe mu ba.

      Dad da abba sai dariya sukeyi, yadda fuskokin yaran yayi dame dame da milo, shi kuwa prince yanan tsaye fuskar nan a tamke, haushin ikram yakeji kamar ya shake ta.

Mum ma ta mike tana cewa, moha ina ka gansu wadan nan kuma?, moha dake shirin zama yace, mum a bisan dinning din gidan abba, suna ta faman wasan su da kwankwanin milo.

     Mummy tace, ina nanny din amir, sai tayi musu wanka, dan yanzu muke shirin tafiya.

      Mum ta kwalawa neena kira, sai gata cikin sauri, mum tace kinga mutuminki ko?, neena tayi murmushi tazo taja su sama, moha sai binta da kallo yakeyi. Faruk ya mike yayi waje abunsa.

.

Side dinsu ya dawo, yazo zai shiga daki, yaji su zarah nata kwasar dariya, dakin ya nufa yayi musu tsawa," Kai da Allah kuyi wa mutane shiru abeg!!!!! Gaba dayan su suka kalle shi baki bude, ya faruk lafiya??! Faruk ya karaso cikin dakin ya zauna kwajab a kujera, wai ni za'ai auren hadi, ai ko da anyi wa ya prince, ni bai kamata ba.

Zuby ta mike auren hadi??? Zarah tace wai meke faruwa ne a gidan, faruk yaja tsaki, sanna ya fada musu komai, zuby tace lallai sisi ya kamata muyi maza mu fito da mazaje, kafin ayi mana irin wannan hadin, zarah tace aikuwa dai, dan ni bazan iya zama da wanda bana kauna ba.

     Nan suka zauna suna ta firan su, da kuma kwantarwa yayan nasu da hankali.

.

Prince kuwa bayan anyiwa su mummy,  rakiya, dakinsa ya koma, ya zauna yana nushin hannun sa, gaba daya garin da gidan suka ishe sa, mikewa yayi ya shiga hada kayan sa, gobe zai koma lagos, dan bazai iya zama mum na hada da wannan mayyar ba.

      Yana cikin hada kayan, amir ya shigo da gudu, yana fadin, papa papa!  Ni bana son asa min riga now, kace wa aunt neena kada ta saka min, kafin prince yayi magana, neena ta shigo itama, gaba daya ta manta ma, da wane dakine, so kawai take ta sakawa amir rigarsa.

    Amir ya fara zagaye dakin, sai binsa takeyi, prince yayi tsaye yana kallon su, can carpet din da ke yashe a kasan floor din, ya kwashe ta, ta tafi suuuu ta fadi gwajam.

Wani irin dariya faduwar ta, ta bawa prince, ya shiga kyalkyata dariya, hahahaha

Neena ta juyo ta kalle sa, wani radadi duwawunta keyi, wani haushin prince taji kamar mai....shi kuwa harda su zama dan dariya, hahaha yana nuna ta....

.

Neena tayi dan tsaki a zuciyarta, ashe dama yana dariya, idan yaga abun mugunta, mtsw, tayi yunkurin mikewa, wani azaba taji a hannunta data dafa, washshshs....

       Tayi ihun wahala, amir yayi saurin dawowa wurin ta, yace aunt neena, kinji zafi ne? Neena ta kalle da kyal tace, eh little master,  amir ya mika mata hannun sa, yace let me help u, ta rike hannun, zata mike ta sake jin azaba a bayan ta, da sauri ta zauna, har sai da tayi dan guntun hawaye.


Amir na ganin haka, yayi saurin mikewa yayi gun papa dinsa.

Papa stop laughing,  aunt neena taji ciwo fa, prince ya kalle ta da gefen ido, yaga yadda take hawaye, yaji dan tausayin ta, dan yasan tiles din dole mutum yaji azaba.

Ya kalli amir, boy wat should I do, ai ita ta jawa kanta ko?amir yayi saurin girgiza kai, noo papa, nina ja mata, aunt neena dont knw hw to run, pls papa help ha, yayi folding hannunsa, prince ya wani dauke kai, amir ya sake shagwabe fuska, help ha like d way u helped me, lokacin dana fadi a steps.

Prince ya juyo ya kalli ya kalli neena, sannan ya sake kallon amir yace, should I?" Amir yayi saurin kada kai, yes papa.

Prince ya mike yazo kusa da neena, sai daya dan dauki lokaci sannan , ya mika mata hannu, neena tadan kalle shi, kamar kada ta amsa, sai kuma taga bazadai ta iya mikewar ba ita daya.

.

Ta mika masa hannunta, ba karamin mamaki prince yayi ba, a zaton sa tunda YAR TALAKAWA ce, hannunta will b hard, amma sai yaji laushi, itama neena mamaki taji, danjin hannun prince da tayi laushi kamar ba aikin soja yake ba.

Ya taimaka mata ta mike da kyal, tazo zatayi one step, taji kafarta ta rike, da sauri ta sake komawa ta zauna, ta share hawayenta, sannan tadan jawo kafar ta duba.

Tadan bugu da centre table,  amir yazo wurin ta, ya turo bakin sa, kamar yayi kuka shima yace, sorry aunt neena, bari naje na kira grany, a kaiki asibiti, neena ta riko sa, a'a basai naje asibiti ba, idan nasa magani zai daina, ina da magani a daki.

Amir ya sake komawa prince, papa ka goya aunt neena, kamar yadda kamin ranan, she need to go to room, pls papa, prince ya juyo adan fusace, leave me alone kaje ka kira inna ladi ta taimaka mata.

.

Amir ya zauna, ya hade fuska da gwaiwa ya fara kuka wiwi.

Prince ya girgiza kai, ya mike yazo wurin amir, zan kaita daki, oya bar kukan, amir ya goge hawayen shi yace thank you papa.

Prince ya dawo ya tsaya a kan neena, amir yace, papa muyi sauri, prince ya duka, yasa hannunsa, zai ciccibi neena, tayi saurin matsawa , prince yaja tsaki, ya sunkuto ta, ta ware idon ta, yau itace prince ya dauka???????

Tayi saurin kallon fuskar sa, ya tamke ta tsam, neena ta kura masa ido, wani abu taji ya tsirga mata a zuciyarta, 

Tayi saurin dauke kai.

Har daki prince ya kaita, yana kaiwa wurin gadon, ya jefar da ita ya juya ya fice, neena ta murguda baki, kadai kawo ni din, tayi gwalo.

Sai da tayi ta jinyar jikinta har safe.

Da sassafen prince ya fito da akwatinsa, ya shiga wurin dad yace shi zai koma lagos, dad yace toh shikenan amma biki nan da 2months ya tabbatar ya dawo kafin nan..

Bayan wata biyu

Ana ta faman shirye shiryen, daurin auren su faruk da prince.

Iyayen biyu, mum da mami, kullum suna busy.

Zuby da zarah kuwa, lokacin suna semester exams, suma basa da wani time sosai.

Yanzu kuwa neena ta kara wayewa, dan zama da zuby dole mutum ya goge.

Duk kayansu idan sun matse su, ko sun gama yayi, sai ku tarkata su bata, dama neena akwai body, dan jikin ta yafi shekarunta.

Yau ake sa ran zuwan prince, dan sai da dad da abba, suka masa fada sosai, dan cewa yayi, shifa bazai samu zuwa va, suna da aiki a bayalsa.

Amarya ikram, sai shiri akeyi, ta shirya events sunfi biyar.ita kuwa amaryar faruk, Deeja, dama yan maiduguri ne, acan zasuyi komai,sai dai a kawo amarya kawai.

.

Neena tare da amir a garden, suna wasan buya, yanzu amir a dauke a matsayin uwa, idan bata nan ba mai iya shawo kansa, shi yasa yanzu sai wata wata take samun zuwa wurin umma, kuma ta wayar zuby take samun gaisawa da yaya habu, dan har chat suke da zuby din (toh fa)

Amir yace, aunt neena, yau papa dina zai dawo, neena na shirin bude baki, zarah ta kwala mata kira ta kofar kicin.

Da sauri ta karaso wurinta, zarah dake zuba abinci a plate tace, kije inji mum.

Neena na zuwa, ta samu mun da mami a daki, sun baje kaya a tsakiyar dakin, dama yau kwanan su biyu da dawowa daga Egypt.

Neena ta gaishe su tace mum gani, mum ta mika mata wasu kayan a dinke suke, kala har biyar, tace ga kayan biki kema, neena tayi murmushi, sannan ta musu godiya.

  Tazo zata fita, mum tayi saurin cewa, yauwa neena, neena ta juyo, tace kidan shiga dakin Na'im ki gyara masa, suzy na min aiki a BQ, neena tadan ware ido, dakin papa!!!!! Mum tace eh jeki pls, ya kusan isowa....

.

Neena ta fito, kamar waddda kwai ya fashewa a ciki.

   Dakin ta, ta shiga ta ajiye kayan ta, sannan ta fito ta nufi dakin prince.

    Tana cikin tafiya suka hadu da zuby, dauke da kedar kayan data amso musu daga wurin tela.

    Neena takai hannunta zata taimaka mata, tace barshi neena na kai, kinsan anjima zamu, family dinner,  yanzu saloon zamuje, mami tace muje dake, dan haka idan kin gama aikin ki, ki hau taxi kizo, kinsan ai wurin?? Neena tayi murmushi tace ehh na gane wurin, a wuse 2 ko, zuby dake tafiya tace eh nan ne kiyi sauri pls.

Neena ta shiga dakin prince, ta zo wurin gadon sa, ta tsaya, take ta tuna lokacin daya jawo ta jikinsa, ta runtse idon ta, ta bude a hankali, sannan tazo ta fara gyara gadon, kamshin bed sheet din, tamkar shine a wurin , haka nan ta samu kanta da rungume zanin gadon, ta shaki kamshin, ta tuna lokacin daya dauketa, haka jikinsa keta kamshi, tayi saurin ajiye wa, taci gaba da aikin ta, da taga zata fara tunane tunane, sai tace a'uzubillahi minal shaidanil rajim, Allah ka raba ni da tunanin mijin wata, ni duka shekaruna nawa, ni inshaAllah karatuna zanyi nima, na zama kamar mum, tayi murmushin ta taji gaba da aikin gaban ta.

.

Ta gama kimtsa dakin, ta shiga toilet,  woow ta furta, katon toilet ne sosai, gashi shima sai kamshin freshener yake yi.

Ta shiga wanke wa, tana gama wanke na farko ta shiga wurin shower, din, dan daban daban ne, amma duka a cikin toilet dinne.

Ta shiga ta gama wanke wa, tahau kalle kallen wurin, duk glasses ne, ga kuma remote,  neena ta shafa'a da kalle kallen ta.

Sai jin bude kofar toilet din tayi, ware ido tayi, waye ya shigo kuma????

Tayi sauri tadan leko, Prince ta gama a tsale gaban mirror,  shaving din kasumbar sa yakeyi, daga shi sai, rigar towel fara.

.

Da sauri neena ta koma cikin shower din, ta dafe kirjin ta, yanzu ya zanyi, nasan ya prince ya gabe ina nan ciki, zan shiga 6 ne bama 3 ba.

Ta rasa ya zatayi, sai wiki wiki take yi da idanunta.

     

Shi kuwa prince, yana kammala shaving dinshi, ya wanke fuskar sa, ya juyo yana kallon shower din , da gani nan yake shirin shiga , ya watsa ruwa.

Neena tension dinta ya lunku, dan wanda ke ciki yana iya ganin na waje, shi dake waje bazai ganta ba.

        

  Take wata idea tazo mata, tayi saurin lalubar, aljihun pakistani wandonta, tana tabo wayar dake ciki, ta sauke lumfashin ta.

Wayar amir ce daya bata ajiya, lokacin suna wata a garden,  tayi saurin lalubar numbar papa, aikuwa ta gani, Allah ya sota ta iya karatun ta.

Da sauri hannun ta na kyarma ta danna kiran numbar...........

.

Prince ya mika hannun sa zai bude kofar ya shiga, yaji karar ringing din wayar sa daga daki.


Mtsww, yayi tsaki, zuwa fa wurin nan ba dole bane, ya bude kofar toilet din ya koma daki.

Neeena tayi saurin sauke ajiyar zuciya, wai Allah na gode.

Fitowa tayi da sauri, tazo ta lekasa ta kofar, ganin shi tayi zai dauki wayar, tayi saurin rakubewa, ta fito tana bin bango, tana sando, kamar wata munafuka.

.

Prince ya dauki wayar, hello dear, am busy nw, zan neme ka anjima kaji, prince bai jira jin komai ba ya kashe wayar, ita kuwa neena hankalinta na, wurin kawai taga ta fice daga dakin.

Sai lallabawa take yi tana bin bango, prince na ajiye wayar ya juyo zai koma toilet,  sai ganin neena yayi ta lallabawa zata fice, ya saki baki, ita wannan kuma fa?! Kaman ya make ta yake ji, ya daka mata tsawa, kee!! Mai ya kawo ki nan?!!

.

Neena ba karamin tsorata tayi ba, ta jingine da hango tana kallon shi a tsoracen.

Prince ya karaso wurin da take a tsaye, ya nuna ta da yatsa sa, mai ya kawo nan?, neena ta kasa motsa harshen ta, dan nauyin da yayi mata, prince ya sake cewa da tsawa, ba da ke nake ba??!! Neena tayi saurin runtse idon ta, dan tsawar da yayi mata kamar zai hadiye ta.

Tayi kokarin motsa lips dinta, tace , ni ni uhm ni dama ni uhm, mum ce , uhm tace wai, nazo na gyara maka dakin, prince ya wani wurga mata harara, ya juya yace, get out!!!! Da sauri neena tayi gaba harda su tuntube.

Sunje salon, an musu gyaran gashi, su zuby sai yaba tsayin gashin neena suke, zarah kuwa na nan zaune sai waya take da mates dinta, wai ance mata zasuyi paper da yamma, shine take ta kira dan taji koda gaske ne.

Sun dawo gida karfe hudu na yamma, neena tayi dakin amir, a kwance ta iske shi tare da faruk, suna game da ipad.

Neena na shigowa tayi sallama, amir yayi saurin saukowa daga saman gadon, ya rungume ta, neena tayi murmushi, my little master, muje nayi maka wanka, amir yayi tsalle zanje naga fuad yau inji uncle faruk, neena tayi murmushi,  sanna ta kalli uncle faruk, ina wuni ya faruk? Faruk ya juyo ya kalle ta, yayi murmushi,  lafiya neena, har kun dawo ne? Neena tace eh yanzun nan muka dawo, faruk ya mike, bari na shiga wurin ya prince, ya fice.

.

A zaune ya iske prince, yasha wankan shi, cikin wasu tsadaddun kaya, farare, faruk ya samu wuri ya zauna, yace ya prince , su dad sunce idan mun kammala mu same su a can family house,  prince ya tabe baki, faruk yayi dariya ya mike, haba yaya kadan saki fuska, kada ka bawa amaryar mu tsoro, prince yaja tsaki ya jefe shi da remote din da ke kusa dashi, faruk ya fita yana masa dariya.

.

Neena zaune ta gama shirya amir, yayi kyau shima sosai, ta shafa fuskar sa, little master kayi kyau abunka, amir ya shafa fuskar ta itama yace, u r pretty like a barbie aunt neena, neena tayi dariya, nagode, oya maza je wurin su antu zarah su tafi dakai, amir ya make kafada, ni sai dake zan je, neena zatai magana, mum ta shigo tare da zarah da zuby.

.

Mum ta kalli neena , ya baki shirya ba neena, oya tashi tashi, kije ki shirya, dan dole sai ke amir dinnan. Amir ya rike hannun mum yace, grany da aunt neena zamu ko? Mum tace eh da ita zamu, sannan ta kalli neena tashi kije ki shirya. 

Neena ta saka, riga da skirt dinta, dinki zamani, sun zauna mata sosai, kamar ba ita ba, sai juyi take tana kallon kanta, wai dama umma na na nan, ta ganni cikin kayan nan, tayi murmushi.

Zuby ce ta shigo dakin, neena kiyi sauri muje, tsayawa tayi tana kallon yarinyar, baki a bude, tace kin ganki neena, neena tayi murmushi tace kinyi kyau kema anty, zuby ta karaso ciki tace, sai dai bakiyi make up ba, kuma dankwalin ki, zuby ta sa hannu ta cire jakwalkwalon daurin da neena tayi, tace zauna na gyara miki.

Neena na murna ta zauna.

.

Zuby cikin mintuna kalilan, ta kammalawa neena simple but pretty makeup, woow zuby tace, kin ganki kuwa?, neena sai murmushi takeyi, dan tunda take ,daga powder sai mai , kawai take shafawa fuskarta, yau gashi harda su pink janbaki, tayi kyau mashaAllah, kamar ba ita ba.

.

Zarah ce ta shigo dakkn, cikin shiri itama, dinkin su kala daya da zuby, tace kuzo muje mana, su mum duk sun wuce fa.

Sakin baki tayi tana kallon neena, ta nuna ta da yatsa, who is dis sisi? , zuby tayi dariya, amir nanny,  zarah ta matso tace, dama kyaun neena yakai haka?, neena tayi murmushi tace anty kuma ai kunyi kyau, zarah tace toh matso muyi selfie kafin mu wuce, zuby ta matso hakama neena, zarah ta daga wayarta ta dauke su, sunyi kyau kamar wasu flowers (lols).

.

Sun isa wurin mutane a cike, duk family dinsu ne a wurin, amarya ikram tasha gayun ta, cikin wasu tsadaddun kaya, ga makeup an mata, tayi kyau sosai abunta, ango kuma ga kyaun amma ba fara'a, fuskar nan kamar kullum, a tsoke.

.

Neena ganin duk ba wanda ta sani, kuma duk inda tayi sai an kalle ta, wasu a zaton suma , irin ruwa biyun nan ce, dan a gaskiya neena farace soaai.

Neman su amir ta farayi dan ta tsare su, kada suje su tafka banna, mum ta hango ta, ta kwala mata kira, neena ta karaso wurin table dinsu mum, zaune suke su hudu, mami, mum, mummy,  sai wata mata, da ganin kaga su abba, dan kamannin su harya baci, neena ta gaishe su, mum ta mika mata car key, je ki dauko min, wasu kaya a mota, neena ta amsa tace toh.

Wannan matar mai kama dasu abba, tace asiya (mum) ina kika samu yarinya,? Mum tace nanny din amir ce, da sauri naga matar ta kalli mum, nanny? ? Shine taci gayu haka, bata da uniform ne ko me?, mami tace tana dasu, amma su abban faruk sunce kada ta ringa sakawa, matar nan dama da ganin ta yar masifa ce, dan fuskarta ba alamun wasa ko kadan, tace ban gane kada tasa ba, ita din yar Wacece??? Mummy dake jinsu tace yar wacece fa fashe _YAR TALAKAWA_ matar nan ta maimaita, yar talakawa, shine zasuce kada tasa uniform,  wannan yar yarinyar da ba'a gama rainon taba shine zaku bata rainon wani?, gata yar talakawa, ko karatun kirki batayi ba, tazo ta koya wa yaro tabi'a irin tasu?, toh wai ina professionals nannies,  dinda kuke masa hiring? .

Mum tace yaya B , wannan da kike gani duk tafi su wlh, yaya B taja tsaki, zamuyi dai maganar idan mun isa gidan.

.

Duk wannan maganar da yaya B keyi, neena taji, dan ta dawo daga daukar kayan taji ta tana aibata ta, a sanyaye ta kawo wa mum kayan, yaya B ta watsa mata kallon tsana, ta juya zata koma seat dinta, batasan lokacin da hawaye suka sauko daga idon taba, can baya ta samu ta zauna, ta buga uban tagumi, hawaye na fita daga idon ta, tunda tazo family duka suna sonta, amma da gani ranar tafiyarta ya kusa, wani kuka yazo mata, tayi saurin dukar da kanta, ita kam bazata iya rayuwa ba amir ba, haka takeji har zuciyarta.

Tana nan zaune gaji anyi kiran amarya da ango, ta dago kanta ta kallo su, sunyi mugun yin kyau , ta dauke kanta tace, ku kam kunji dadin ku.

Tana nan zaune har aka kammala family dinner din nan.

.

Su zuby suka fara neman ta dansu koma gida, sai suka hade da wasu cousins dinsu, meera da meena, nan suka fada firar yaushe gamo, ya faruk yazo yace musu suzo ya maidasu gida, nan suka bisa, suka ma manta da neena.

Amir kuwa yash neman neena bai ganta ba, su abba zasu koma suka tafi dashi.

Duk wurin an watse, neena ta mike ta shiga neman amir, amma duk wurin sai data duba bata kansa ba.

.

Tazo har bakin gate tayi tsaye, kowa ya tafi, ita tana can ta lula duniyar tunani, addu'ar ta daya Allah yasa amir ya bi wasu yana gida.

Can ta matso dan ta tari mai taxi, Allah ya taimake ta tana da sauran canjin dazu, data je saloon.

Wata bakar motace tayi parking a gaban ta, saurayin dake ciki ya fito, tana ganin sa, ta gane shi, Moha ne yayan ikram.

Ya fito ya nufo ta, sai wani layi yakeyi, da gani dai yayi dan shaye shayen sa.

.

A gaban neena ya tsaya kikam, tadan matsa kadan ta gaishe sa, ya amsa yana dariyar shakiyan ci, yace muje na kai ki gida, neena tace nagode amma kaje, zan hau taxi, moha ya sake matso ta zai kama hannunta, muje bana baby, neena tayi saurin ja baya tace da Allah malam nace kaje bazan bika ba!!

   

Moha ya kwashe da dariya, see dis village gal, ke harni zance kizo na baki lift kice bakyaso, who d hell r u, yar talakawa dake, bakauyiya.

Neena ta share hawayen ta, tayi gaba dan samun taxi, sai dai jin hannun moha tayi, ta cafko ta, yana neman rungume ta, ta fasa kara ta fara tura shi, dankwalin ta ya fadi, moha ya kurawa fuskar ta ido, ya yaye gyelen jikinta ya jefar , yasa hannunsa yana shafa gashin kanta, neena sai mutsu mustu take tana kuka, can taji kamar yana shirin zage mata zip, tayi kokari ta wanka masa mari, kai wane irin maye ne eyee, moha ya ciji leben sa yace yanzu zaki gane wane irin mayen ne ni, yayo kanta kadan kadan.....

.

Prince zaune a family house,  ajiye coffee cup din hannunsa yayi, ya mike, its over tunda naji shiru.

       Ya mike ya dauki, wayar sa ya fito, yasa key ya rufe gidan, sannan ya nufo gate dan a waje yayi parking din motar sa.

Tunda ya nufo gate din yake jin kukan mace, ya kara sauri, yana isa ya hango moha sai kokarin yage wa yarinya riga yakeyi, shi baima gane wacece ba.

Yana isowa moha na yage hannayen rigar neena, dan materials ne, ba wani wahalan yagewa gare shi ba.

Prince yayi saurin zuwa ya janye moha, ya wanka masa kyawawan mari kuda uku, sannan ya tsukomo rigar sa, ya nuna sa da yatsa, kada ka sake na kara maka ma moha, maza wuce jahili kawai, moha yayi saurin shigewa mota ya wuce fuu, dan yasan halin prince sosai, zai iya kai shi sell ne kawai ya rufe.

Juyowa yayi wurin yarinyar, yaga wayam sai gyelenta da  da dankwali, can ya hango ta tana tafiya kamar zata fadi.

Neena duk hankalin a tashe yake, gaba daya kwakwalwarta ta tsaya cak, ko prince dinma bata gane shi bane, tafiya kawai takeyi.

.

Harya shiga mota zai wuce abunsa, can ya fito ya dawo ya dauki, gyelenta da jaka da dankwali, ya koma motar, yaja yakai dai dai inda take, yayi horn, yaga bata tsaya ba, yajaa tsaki , shi kawai tausayi ta basa, ganin ta yar teenager,  ya fito yace kee!!! Neena taci gaba da tafiyar ta kamar zombie.

Prince yasha gaban ta, sai a sannan ta tsaya ta dago idanunta da suka rine zuwa jajaye, fuskar nan kamar tomatoe dan ja.

Prince ya kura mata ido, shikam kamar yasan wannan fuskar, take ya tuna dazun daya ganta a dakinsa, yace a fili nanny! !!! Toh mai ya kawo ta nan ? kuma ya akayi kowa ya tafi sai ita aka bari?? - Ya kura mata ido, da gani hankalinta har yanzu a tashe yake, yace da silent voice dinshi, muje ya nuna mata mota, neena tayi saurin ja baya, har tana faduwa, dan gani takeyi kamar har yanzu moha dinne.

Prince ya girgiza kai, yaja tsaki, wai meyasa ma ya tsaya taimakon ta, ya bude kofar motarsa zai fice abunsa, sai kuma ya nushi motar ya dawo wurin ta, har lokacin tana nan a kasa ta zauna rashe rashe , sai kiran sunan Allah take , da yaya habu da umma.

Prince ya duka daidai fuskarta, ya kura mata ido, yace come back to ur sense,  nine papa din amir, neena zata ja baya , prince ya rike ta , yace ba abunda zai faru dake, tashi mu tafi gida wurin amir, tayi saurin kallon shi, tace amir, prince ya kada mata kai, ta mike tace ka kaini wurin amir, prince ya mike shima sannan yace shiga muje toh, taki motsawa daga inda take, prince ya buga kafar sa , yace ohh darm it, ke nifa zan wuce abuna haba! 

   Neena ta kalle shi, prince yace nibar kallona da wani idon ki katoto, neena tayi one step dan zuwa shiga motar, duk ta takure dan sanyin da takeji, ga iska, ga kuma ba gyele a jikin ta bare dankwali, prince ya lira da hakan, sai ya biyo bayan ta dan ya bata gyelen ta rufa, aikuwa neena na juyowa, sukayi karo da prince, dago kanta tayi ta kalle sa, kamshin nan nasa yasa, tayi saurin kallon fuskarsa, tace Papa!!! A zaton ta a zuciya tayi maganar, sai dai taji yace, ke lafiyanki, dare keyi fa, neena tayi saurin shigewa motar, dan take ta dawo hankalinta, prince ya tabe baki ya jefa mata gyelen ta, ta window.

Suna ta tafiya shiru, ita duk ta takure wuri daya, sanyi takeji kamar mai, gashi ya kunna AC abunsa.

Yana lura da yadda take kyarman sanyin, amma saboda mugunta ta prince , sai ya share ta, wai dolene ma ya bata punishment,  tasa ya bata time dinsa, gashi yana da abunyi gobe da safe.

Sunzo bakin gate , amma a kulle, dan dare yayi sosai, karfe, sha biyu, yayi kiran wayar mai gadi, shiru sai ringing kawai takeyi, yaja tsaki mtsw...., neena tayi saurin kallo shi, ya sake kiran faruk shima tayi ringing harta katse ba'a dauka ba.

Duk yan gidan sai daya kirasu amma, ba wanda ya dauka, sai tsaki yake take ja, neena data kagara tabar motar, sai tace, papa ni zan shiga ciki, prince ya watso mata harara, sai ki shiga ai, neena tasa hannu ta bude motar, ta fita taje bakin gate din, sai kiran mai gadin take amma shiru, ga iska sai hurata takeyi, sai da tayi minti sha bakwai, sannan ta jingina da gate din, prince ya hurar da iskan bakin shi, yayi mata horn.

Ta kallo shi ,sannan  ta karasa wurin motar, shigo kawai prince yace mata, ta bude ta shiga, prince yaja motar suka bar unguwar.

Neena gaban ta yahau faduwa, ina zai kaita ne????

Toh fa nima afrah, na kunna motata nabi bayan prince, dan gano wa idanuna inda prince zai kai mana neena.

.

Sai sharar gudu yakeyi, ga titin ba kowa , saboda dare ya tsala sosai.

Bai zarce ko ina ba, sai family house din da suka baro.

Ya shiga yayi parking,  sannan ya fito ya nufi cikin babban gidan, neena ta bishi da kallo, harya isa babban balcony din gidan ya zura key a kofar yana budewa.

Ganin zai shige, ga tsoro har yanzu bai sake ta ba, yasa tayi saurin fitowa tabi sa ciki.

Babban falone sosai, can ta hango prince yana hawa benen, tayi sallama ta karaso falon, prince bai ko juyo ba ya shige wani daki dake kusa da benen.

Neena ta samu saman carpet ta rakube tadan kwanta, Allah yaso ta ma bata sallah ranar, sanyi takeji bana wasa ba, sai kyarma takeyi, ta rufa da dankwalinta amma inaa, sanyin yaki raguwa, tun tana kalle kallen falon, tana rawar sanyi har barcin dole ya dauke ta.

Prince ya sauko dauke da blanket a hannun sa, daga shi sai singlet,  shikam yana son lokacin sanyi sosai.

Yana isowa ya duka wurin da take a kwance, ya warware blanket din, ya rufa mata a jiki, yazo rufawa hannun ta, yaga karcewar akaifa, jini yadan bata mata gyelen data rufa dashi.

.

Mikewa yayi zai koma sama abunsa, sai kuma ya dawo, yaje ya dauko akwatin gaggawa, ya duka yasa hannu ya janye gyelen, farar soft fatar ta , ta fito, ya dauko auduga da dan spirit,  ya fara goge ciwon, neena taji dan zafi, ta muskuta ta juya, juyawan da tayi, ya bayyanar da kyakkyawar fuskarta, da tayi jaa, prince ya kura mata ido, sawon hannu ya gani a jikin fuskarta, ya kai hannunsa ya shafi wurin, ya tausayawa yarinyar gaskiya, gata karama (a yadda kake gani ba ).

Ya mike ya wuce saman ya kwanta shima.

Tunda asuba, daya fita sallah, ya barta sai sharar barci takeyi.

Yana gama sallah ya nufi wani dan boutique,  kusa da gidan, ya siyo riga da skirt,  masu kamar suwaita, amma gaskiya sun hadu karshe.

Yana komawa ya iske ta a zaune a kasan, tayi saurin gaishe shi, ya kalle ta kawai ya mika mata ledar hannunsa, ta amsa, tace miye?, prince yayi gaba bai ko amsa mata ba.

Neena ta bude ledar taga, kayan dake ciki, ba karamin kyau suka mata ba , ta mike ta fara neman inda zata shiga ta canzo kayan, amma duka kofofin a rufe suke, sai dai ta samu bayan kujera , ta fara cire skirt dinta , ta canza, sannan ta zage zip din rigarta , ta cire, ta dauko sabuwar ta saka kanta, harta zura hannayenta....

.

Prince ne ya sauko cikin dan sauri, ta bayan kujerar ya biyo, baima san akwai mutum a wurin ba...

Neena na ganin yayo wurin ta, ta saki ihuuuu...

Prince yadan tsorata, dan shima bai tsammanin mutum a wurin ba, ta juyo yana kallon ta....

   Neena tayi saurin juya masa baya, tana kare kirjinta, prince yaja tsaki, kee kiyi sauri ki same a mota, mu koma gida kafin kowa ya tashi.

Neena tayi saurin kada masa kanta, shi kuma fice, yana cewa idan kin fito ki rufe gidan.

Yana zaune a mota, ta karaso, wani irin kyau tayi a cikin English wears dinnan, prince yadan kalle ta ya kauda ido, neena ta shiga motar, suka hau hanya.

Suna isa mai gadi ya bude musu, suka shiga, yayi parking ya fito itama ta fito, yayi hanyar baya, itama ta bisa, yazo zai shiga ciki, neena tace, ga keys din, ta mika masa, tsayawa yayi, ya juyo ya mika hannunsa dan ya amsa...

Faruk ne ya fito daga side dinsu, yayi shirin tafiya motsa jiki, ya hango prince da neena a tsaye, wani abune ya tsaya masa a wuya, miye hadin ya prince da neena?, kuma ya akayi suke tare da sassafen nan?

Hannunsu ne ya hadu da juna, wani yarrrr sukaji a tare, kamar shocking,  prince ya juya ya shige, itama ta shiga.

Direct dakin amir ta nufa, Allah ya so su ba wanda ya farka a gidan, tayi masa hot milk ta kai ta ajiye masa, sannan ta koma dakin ta, ta cire kayan da prince ya bata, ta shiga tayi wanka ta saka wasu kayan. Wadan da ya bata kuwa sai ta linke su, tace idan mun sake haduwa sai na mayar 

.

Ikram kwance a makeken gadon ta, mummy ce ta shigo dauke da tray , ta zauna a bed side din.

Hannun tasa ta dan bubbuga ikram.

Wake up, tashi kisha maganin nan.

Ikram ta bude idon ta, da kyal, ta mike, tana hamma tare da mika.

Mummy,  nifa na gaji da shan wadannan magungunan da kike dirka min.

Mummy tadan buge bakin ikram, banason iya shege, duk ba taimakon ki akeyi ba.

Ikram ta turo baki, ni mummy toh ki daina bani mai dacin nan.

Mummy ta mike tace, gaya nan kisha, saura kuma nazo na iske baki shan ba.

Mummy ta fice.

Ikram ta mike ta sauko daga gadon , tazo ta dauki cup din tadan kurba, tana yamutsa fuska.

Wani daci daci taji yana yi, da sauri ta nufi toilet ta zubar, ta kalli na cup din tace, Allah ya sawake nasha wannan dacin yuks, ta tufar da yawo.

Family gaba daya sun taro a falon dad, breakfast sukeyi, prince na gefe yana shan tea, yaya B ta matsa masa ya zauna, dan shi har ya fito da shirin fita.

.

Yaya B ta kalli zuby, ina shi amir din yake?

Zuby tace tana cin soyayyen kwai, yana wurin neena.

Yaya B ta daure fuska, wacece neena?

Zuby tace nanny din amir din nan.

mum ta kalli mami, suka hada ido.

Yaya B ta kalli dad da abba, yaza ku kawo yar kauye, yar talakawa ta kula da amir?, yarinyar da ko ita ba'a gama rainon taba!? 

Abba yayi murmushi, yaya B ai taimako ne, kuma gaskiya yarinyar na kokari.

Yaya B taja tsaki, duk yawan professionals nannies din da akwai, sai ku rasa wadda zata kula da yaro sai yar karamar yarinyar nan.

Dad ya ajiye cukalin hannunsa.

Ya kalli yaya B yace, mu mun dauki yarinyar nan ne a matsayin yarmu ba'a mai raino ba.

Yaya B tayi saurin kallon dad, yar ku, kun hada dangi ne da ita? Ko kuwa dai kalan dangi?, toh bara kuji, idan har kuna son yarinyar nan taci gaba da kula amir, sai tasaka uniform,  kowa ya shigo yasan matsayinta, dan bakuji yadda yan'uwa jiya akai ta maganar ta ba.

Abba zai magana dad ya dakatar dashi.

Dad yace zata saka uniform,  shike nan ko? Yaya B ta juyar da kanta tace shikenan, kuma dole asa mata ido dan irin wadan nan yaran ba abun yarda bane.

Prince gaba daya maganar su yayaB kuleshi tayi, ya mike a hanzarce yace, am off, yayi gaba.

YayaB ta tabe baki, shi wannan har yanzu bakar zuciyar na nan? 

Duka falon sukayi banza da ita.

.

Neena ta gama bawa amir abinci, ta zauna taci nata.

Amir ya fita yaje ya gaida kakannin sa, yana dawowa yace wa neena kije YayaB na kiran ki, gaban neena ya fadi? Tasan wannan matar ce, amir ya dafa ta, tana da kirki, zata baki sweet.

Neena tayi murmushin dole kawai ta fice.

A hakimce ta iske yayaB a zaune saman seater.

Dakin ta babban gaske ne, neena ta durkusa ta gaida ita.

YayaB ta amsa a dakile, ta jefa mata leda, wadan nan kayan su zaki ringa sawa yanzu, neena tayi murmushin ta mai sanyi, tace toh.

Sannan ta mike ta fice.

Tana zuwa dakin ta, ta bude kayan, uniform ne, riga ja da black skirt, kala uku ne.

Neena ta cire kayan jikin ta, ta saka uniform din, tazo gaban mirror ta tsaya.

MashaAllah kayan ba karamin amsarta sukayi ba, dan jikin ta, mai kyau ne duk kayan data saka sai sun amshe ta.

Wani murmushi ta saki, tace , ni wadan nan dinma sunfi mani.

Anyi events biyu, amma duka na amarya ne da abokanta, ko su zuby basuje ba.

Yadda neena tayi tsammanin, yayaB zata takura ta, sai taga bata ma damu da ita ba, kullum tana dakin ta tare da amir, neena kuwa kullum cikin mata hidima take, dan ta lura matar nada son girma.

.

Yau ana gobe daurin auren su prince.

Gidan gaba daya a cike yake.

Neena ta shigo dakin yayaB, ta kawo mata farfesun kayan cikin data sata ta mata.ta ajiye mata a saman table, yayaB dake kallon news tace, zo nan , neena tazo ta zauna a kasan carpet, yayaB tace ina mahaifanki suke? Neena tace da mahaifiyata nake zaune sai yayana, yayaB tace ina mahaifinku? Neena tace muma bamu sani ba.

YayaB ta sauke lumfashi, zaman da tayi da neena ta gane cewa yarinyar mai shiga rai ce, kuma tana mata kamanni da wata data sani.

   Ta sauke ajiyar zuciya tace, kina karatu ne? Neena tace na fara amma ban kammala ba, yayaB ta kura mata ido can kuma tace , tashi kije, neena ta mike ta fita

Da daddaren ranar, prince ya shigo dakin yayaB dan amsa kiran ta.

.

Ya samu wuri ya zauna, yace gani, yayaB ta tabe baki, kai wai wane irin mutum ne eyee? Prince ya kalle ta yace, ni mutum ni irin ki, yayaB tayi dariya, Allah ya sawake na zama irin ka, prince yayi murmushi, yayaB tace duk wannan kumbure kumburen naka bazai hana gobe a daura auren nan ba na'im.

Prince ya daure fuska, wai maina tsare muku ne ?, yayaB tace, ja'iri kana so kana kaiwa kasuwa, yarinya irin wannan., prince ya dakatar da ita, ni zan tafi idan kin gama.

Ya nufi kofar fita, dai dai lokacin neena itama , ta sunno kai zata shigo.

tun ranar  nan rabun dasu hadu.

Prince yadan kalle ta ya dauke ido ya fice, neena ta karaso ciki , ta amsa sakon da mum ta aiko ta amsar mata wurin yayaB , tayi saurin kaiwa  mum din.

sannan ta koma daki cikin hanzari, ta dauki ledar kayan nan da prince ya bata kwanaki, ta nufi dakin amir, dan taga shigar prince ciki.

.

Ta bude kofar ahankali, dan tasan amir baya ciki, yana wurin faruk a waje.

Prince na shiga dakin yayi mika, mutum yana barcin shi, aka wani tashe shi, saboda wannan nonsense maganar, ita yaya B dinnan matsalarta kenan pock nosing , a cikin maganar da bata shafe taba, mtsww yaja taki, let me sleep here nasan ba wanda zai san ina nan balle su dame mutum.

Ya daga hannunsa, ya cire shirt din dake jikin sa, daga shi sai three quarter da singlet fara.

neena ta bude kofar ahankali ta shigo, prince najin bude kofa ya juyo, suka hada ido da neena, neena na ganin shi ba riga tayi saurin juya baya, prince irin mazan nan ne masu 6packs, yayi building din jikin shi sosai.

.

Neena ta dafe kirjin ta dake bugawa, maiya kawo ta, tayi saurin sa hannun ta jikin kofa zata gudu.

Prince ya daka mata tsawa, kee!! Neena ta tsaya amma bata juyo ba, prince ya mike yazo kusa da ita, bugan zuciyar ta ya karu, prince ya rike kugun shi, yace, kee mai kike zo yi anan?, neena ta fara kyarma dan yadda yayi maganar ba wasa, uhm uhm dama kayan nan ne zan mayar maka.

Prince yace wane kaya, neena ta mika masa ledar, prince yaja tsaki, ta haka ake mikawa mutum abu a kauyen ku? Neena ta girgiza kai, sannan ta rufe idon ta , ta juyo ta mika masa.

Prince ya tabe baki, sannan ya amsa ledar ya bude.

Kayan daya bata ne a family house,  ya mika mata ledar, mai zanyi dasu, ko kin taba ganina nasa kayan matane? Neena ta girgiza kai, yadda ta rufe idon ta, gashin idon ta masu tsawo suka karawa fuskar ta kyau, prince yadan kura mata ido, ganin girar idon ta, yayi wadda ta fado a kumatun ta, yadan kara one step zuwa gab da ita.

Neena ta sake matse idon ta, tana cewa , wayyo kayi hakuri, ban taba ganiba, a zaton ta bugun ta zaiyi.

.

Ya mika hannun sa, zuwa fuskar ta, zai cire gashin, zuby ta banko kofar dakin ta shigo, tana cewa neena neena, kizo ga ya abubakar dinku ya kira.....

.

Neena dake kusa da kofar ta tafi zata fadi, dan bude kofar da zuby tayi, ya turo ta ita kuma.

Da sauri ta ware idonta dan naiman ma kanta madafa, sai kawai taji ta a jikin mutum.

Ta shaki kamshin sa, zuby ta ware ido tana kallon su, wani mamaki da tsoro ya lullube ta, miye haka yake faruwa?

Prince ya ture neena gefe, da kyal ya iya ma turen tan, da duka gabobin sa sunyi sanyi.

Neena tayi saurin juyawa ta kalli zuby, na'am anty zuby.

    Zuby ta kalli prince, ya wani watso mata harara, yayi kan gadon ya kwanta, yace ku fice min pls!!!

Sukayi waje da sauri, har suna buge juna.

Zuby kasa tambayar neena tayi, sai dai tayi alkawarin yin investigation akan abunda idon ta ya gane mata.

Washe gari juma'a, 21 of November,  misalin karfe biyu da rabi na rana, dubun nan jama'a suka halarci _DAURIN AUREN_ na'im prince da Ikram isma'il.sai faruk da Deeja Aliyu.

.

Bikin ya tara manyan manyan yan siyasa, da masu hannu da shuni, sojoji dayawa sunzo dan a reception din har pareti akayi.

Da karfe 6 na yamma aka kawo amaryar ya faruk, deeja, ta sauka a gidan abba.

    Karfe 8 aka shigo da amaryar prince wato ikram.

Gidajen biyu sun cika sun batse, angwaye kuwa na family house da abokansu, sai washe gari zasu dawo gida ayi budar kai, sannan kowa ya dauki matarsa yakai, gidajen dasu dad da abba suka gina musu.

Umman neena tazo itama, amma basu hade da yayaB ba, dan ita tana family house wai dole ne yaran zamani asa musu ido, dan kada muyi barna.

Neena na kicin tana taimakawa inna ladi suna wanke wanke, bayan ta raka umman ta , tahau mota.

Zarah ta shigo kicin din, tace neena ga waya yayaB zatayi magana dake.

Neena ta goge hannayen ta, ta amsa wayar.

YayaB tace, niimatu kina ji ko, neena tace eh, ki hado min koko da tuwo , zan aiko a dauko minke, ina zan iya da abincin turawan nan duk maso sa basar ne, neena tayi dariya tace toh shikenan nan da awa daya zan kammala, yayaB tace toh kiyi dai sauri yunwa kamar ta zautar dani wlh.

Neena ta nemi taimakon inna ladi, da wata mata da tazo daga garin su dad, suna kwatanta mata har ta kammala duka ta saka a flask ta ruba a kwando.

YayaB na ajiye wayar, ta sauki dan samun wanda zata aika.

Samari ne su hudu a falon, tana saukowa suka gaishe ta, ta amsa, sannan tace musu, akwai wanda yasan gidan bikin cikin ku?, suka kalli juna , suka ce mama bamu kai ga zuwa can bama, yayaB tace hakane kusa baki ne, ina faruk ? Din ne? Sukace yaje siyo credit a waje, yayaB tayi dan tsaki ai shi dama yawo kamar yaci kafar kare.

Ta koma daki dan jiran faruk, amma inaa yunwa ta addabe ta.

Ta fito ta nufi dakin da prince yake.

A kwance ta iske shi, yana kallon sama, gaba daya baya cikin farin ciki, har kamar shi,  za'a aura wa wannan yarinyar da ko kamun kai bata dashi.

    Jin hannun yayaB yayi, ta riko kunnen shi, yayi yar kara yace, yayaB mai nayi maki, zaki cire min kunne .

     YayaB ta zauna tace, tashi na aike ka gida, prince ya zauna yana cewa, ni na gaji ki aiki faruk mana, yayaB tace ni kai nake so kaje min aiken ai.

   Sai da tayi ta rokon sa sannan ya yarda zaije.

Neena na nan a tsaye wajen gate, sai dube dube takeyi, amma shiru ba wanda taga yazo.

Can ta hango wata black benz ta nufu ta.

    Akayi parking a gaban ta, ta karasa wurin driver din, prince ya sauke mirror, neena tana ganin shi taji gaban ta yadan buga, wani irin kyau yayi mata , tace kodan yau auren shi, shiyasa yayi kyau abunsa.

Ta mika masa basket , ga abincin , prince ya dauke kai yace, waye dan aiken ki???

.

neena ta kalle shi, hankalinsa na wurin wayarsa, tace ban sanar wa mum ba, kuma zan kula da amir.

Prince ya juyo, ya wani watso mata idanunsa yace, nace kizo muje ne? Neena ta sadda kanta kasa, ita wallahi sometimes,  prince dinnan na kule ta, kullum sai iya gwale mutum.

Prince ya tada motarsa, neena tayi saurin cewa, ga abincin nan fa bansa a motan ba, yayi banza da ita.

Taga alamun dai wucewarsa zaiyi, ta bude motar da sauri ta shiga tare da kwandon , sai sauke ajiyar zuciya takeyi, inaa zata kuskure ya tafi, ta bani da masifar yayaB.

Tunda suka hau hanya, bai ko kalle inda take ba, sai tafiya sukeyi kamar kurame, har suka iso, yana parking motar ya fice abunsa.

Neena ta fito, ta dauki kwandon, tabi bayan sa.

.

A falon suka iske faruk da frnds dinsa, suna shiga yayi sama abunsa.

    Neena tayi tsaye dan bata san ina yayaB take ba.

  Ta gaishe da faruk da sauran dake wajen, sai kallon ta sukeyi.

   Faruk ya taso yazo wurin ta, yace wurin yayaB kika zone? Neena tace eh abinci na kawo mata.

Faruk yayi murmushi ya nuna mata dakin.

Tana shiga yayaB ta mike, yauwa , ta tari neena ta ajiye kwandon a table, neena ta zuba mata sannan ta samu wuri ta zauna.

       YayaB na kwasar girki tace, kince ummanki zata zo? Neena tayi murmushi, eh tama zo dazun harta tafi.

    YayaB ta kallo neena, shine baki fada min ba?, neena tace ai bakya gidan lokacin, amma tace a gaida ke, yayaB tace ina amsawa naso ai mu gaisa, dan na mata maganar rikon ki, kinsan zaman kadaici na ishe ni.

  Neena ta kalle ta da sauri, tace riko? YayaB ta ajiye cukalin hannun ta, tace, ko bazaki bini ba? Neena ta girgiza kai dan mamaki take ji.

YayaB tace, dana daya a duniya, kuma yanzu bama tare da juna, akwai wadda nake nema, nasan idan har na ganta takaicina zai ragu.

Neena ta jinjina kai tace, ina danki ya tafi? YayaB tace yana kasashen nasara, neena ta gyara zaman ta, azuciyarta taji tausayin yayaB, (yayaB ta manyanta sosai, amma jikin ta na nan gwanin sha'awa , yayaB kanwar mahaifiyar su dad da abba ce, itace auta a wurin maman su dad wato kakar su prince kenan wadda ta zasu lokacin haihuwar faruk).

Neena ta mike tace, zan koma, nasan amir nacan na nemana, yayaB ta kurbi ruwa, toh shikenan , na'im zaya maidake, bari na kira shi, neena kamar ta fasa ihu, ita dama ko ya faruk ne.

.

Ya fito daga wanka kenan, yaga kiran yayaB, yaja tsaki, wannan tsohuwar yar rigima ce wallahi.

Ya dauki wayar yace, kuma ya akayi ? YayaB tace kazo ka mayar da niimatu gida, ta kashe wayar.

Sai daya bata kusan awa da rabi, har neena ta fara gyangyadi ita da yayaB, sanna ya shigo.

     Sukayi saurin farkawa, yace muje kawai ya fita, neena tayiwa yayaB sai da safe ta fito.

Sun hau hanya, aka fara zuka ruwan sama.

Har suka isa ana kwara ruwa, neena ta bude kofa tana tsoron kada ruwan ya tabata, prince yadan kalle ta, ya juyar dakai abunsa.

Da kyal ta fito daga motar, dai dai lokacin wata kawar ikram ta fito da umbrella, da gani tafiya zatayi.

.

Prince sai kallon neena yake yaga ya zatayi da ruwan nan mai karfi, sai yaga tayi tsaye a bakin gate din .

Yaja tsaki wannan ita shes very slow at everything,  ya juya seat din baya, ya dauko umbrella ya fito.

Yazo har wurin ta, neena sai binshi takeyi da kallon mamaki, ya mika mata umbrella din.

    Kawar ikram ta kalle su, baki bude, ta shige motar ta.

Tana shiga ta kira ikram, ta kwashe gaskiya da karya ta fada mata.

Ikram ba karamin tashi hankalinta yayi ba, lallai kuwa sai ta gyarawa yarinyar nan zama.

Washe gari akayi budar kai, amaren biyu duka sunsha gayu abunsu.

  Neena kuwa ko fitowa bata samu yi ba.

   General dinsu prince sai ranar ya samu zuwa.

    A babban hotel aka saukar dashi, yazo har gida ya gaida su dad da abba, yana yaba irin gwazon prince a fanni aikin su.

     Prince gaba daya ranar busy yake, sai da yamma sosai , ya shigo gidan, ya samu mum a daki ita da mami.

    Sai daya gaishe su sannan ya samu wuri ya zauna.

   Mum tace anya kuwa kaci abinci ma yau kuwa? Prince ya girgiza kai, yace ban samu lokaci ba wallahi, sai dana kai  general waheed har airport sannan na samu dawowa gida.

   

Mum da mami sukace ai gaskiya mutumin nada kirki sosai, kalla fa kayan da ya kawo mana.

Prince yace haka yake, yana kyautatawa soldiers dinshi sosai.

     Mum tace Allah ya kara masa budi, mami ta amsa da amin.

  Prince ya mike yana cewa, ni na gaji ne over, let me go n hv a rest.

   Mum tace sannanu, sai kaje kaci abinci ka huta dan kuna da tafiyar safe gobe.

Su ikram dinma na side din mamin ku.

Prince ya wani dauke kai abunsa.

Mum ta mika hannu ta dauki wayarta, bari na kira zuby ta fada wa neena ta kawo maka abinci.

Prince ya juya ya fita, kamar ya shake mum yakeji.

Yana shiga daki, ya shiga ya watsa ruwa, ya fito ya saka kana nan kaya, ya zauna bakin gadon yana amsa waya.

Neena tayi sallama ta shigo, amir na biye da ita dauke da cup.

Suna ajiye masa, sukayi kofa dan fita, prince ya ajiye wayar hannunsa, yace zoki zuba min.

     Neena taji kamar ta ruga da gudu, dan tasan shi ba'a iya masa.

.

Ta dawo tazo, ta fara zuba masa, amir na gefen ta, yana wasa da dutsunan rigarta.

   Tana zubawa tace wannan yayi?, prince yayi kamar baiji taba.

  Neena ta kada kai, tace a zuciyarta, ai maza nata ci soaai, ya faruk ma idan yace na zuba masa, dayawa nake zubawa kuma ya cinye.

       Ta dauki serving spoon,  ta kara abinci, har sai daya yayi suro.

     Tace na zuba, ta rike hannun amir zasu wuce.

Prince ya daka mata tsawa, ke dawo !

Neena ta dawo ta tsaya,  prince ya nuna abincin yace, ni dawa zanci wannan?, neena tayi shiru, prince yace, kewai komai baki iya bane? Tayi shiru.

      Ya kara kulewa, yace, toh sai ki zauna, idan naci wanda ya isheni, sai ki cinye sauran.

    Neena ta ware ido, ni naci abinci dazu, prince ya jawo table ya faraci, amir yazo wurin sa yace, papa, anty neena taci nata ita, prince yace, sai ta kara wannan ai, amir yace papa, ya mata yawa, ita ba acici bane, prince yace sai ka taya ta kuci.

.

Suna nan tsaye, yadan tsakuri abincin, ya tura masa sauran, mai uban yawa.

    Neena ta dauka, tace amir muje, prince ya rike hannun amir yace, ba inda zaku, a nan zaki zauna ki cinye shi.

     Neena ta bata rai, ita da yanzun nan ta gama shan fura wurin yaya B ga cake din da su zarah suka bata, ko ita rumbu ce ai sai haka, toh ga kuma wannan uwar fried rice din.

    Kamar zatayi kuka, ta samu wuri ta zauna, daga waje, mami tayi kiran Amir.

    Yayi waje da gudu yana amsawa.

.

Prince ya haye gadon sa, wayarsa tayi ring.

Ya dauka bakuwar numba ce.

   Hello, 

  Ikram daga dayan side din ta kashe murya, tace hello dear,

  Prince yadan daure fuska, pls waye?

  Ikram taji wani daci a ranta, mijin ta amma ko numbar ta baya da.

     Ta dai yi murmushi tace, ikram ce.

  Prince ya tabe baki, ohh toh ya kike.

   Ikram ta amsa da lafiya, amma ina son ganin ka pls.

  Prince yace a gajiye, ganina ? Me zan miki?

  Ikram ta hade miyau da kyal, lallai ma, idan tana son ganinsa sai da dalili tab.

   Ta kara tsuke murya, yau frnds dina zasu tafi, suna so kuyi bankwana.

    Prince yace am really tired nw, bt zan duba dai.ya kashe wayar.

Neena dake zaune a kasan carpet,  tana tsakurar abinci, taji yana ta waya , kuma taji yace ikram, bt bataji ya sukayi ba, dan shi maganar sa silent,  ko wace albarka.

Hakanan taji wani abu a zuciyarta, ita dai idan tana tare da shi, she fills save.

Kodan ya taba taimakon tane oho.

Prince yace, kee! Ba tunani na ajiye ki, kimin ba.

  Neena ta samu kanta da shagwabe fuska, tamkar yadda takewa, yaya habu, idan ya matsa mata taci abinci.

Ni na koshi, Allah cikina zai iya fashewa idan na cinye wannan.

Prince ya kura mata ido, hakanan yaji dama, taci gaba da maganar.

   Ya mike ya nufi closet dinshi, ya dauko kudi bandir uku na dari biyar biyar.

.

Yazo gaban neena ya mika mata, ta ware ido, wannan kuma fa, ta furta a zuciyarta.

     Yace amsa mana, ta amsa, yace kije side din mami ki basu.

   Neena tace su wa? Prince yace ikram, sannan ya shige toilet. 

    Neena ta mike, ta kwashe kayan abincin, ta fita da kudin tayi side din mami.

A hanya suka hadu da zuby da zarah, sukayi barkwancinsu, tana zuwa taji firar yan mata, ta shiga da sallama.

Duka falon aka kallo ta, yan matane masu ji da kansu.

   Ta rasa wa zata tambaya ina amaryar, tunda amaryar faruk an kaita dazun ita.

Ta nufi kicin ta tambaye inna ladi, dan tana side din tana wa frnda din amaren girki.

Tana shiga dakin, ta iske ikram tare da kawayen ta su biyu.

Tayi sallama, ta gaishe su, duk suna zaune a bisan gadon, daya na chat, daya na waya, ikram na duba wani book.

.

Suka watso mata kallon raini.

Ta karaso ciki ta mikawa ikram kudi.

    Ikram ta harare ta, daya daga cikin kawayen tace, wannan ce fa yarinyar.

     Ikram tace na gane ta ai, ta mike, neena tace gashi inji ya prince.

    Ikram ta wani daure fuska, haushi kamar ya kasheta, wato bazai iya zuwa ba, sai na aiko wannan _YAR TALAKAWAN_

Kawarta tace , lallai ikram , kinyi sa'a mune anan, dakin bani da sharrin su teema.

     Ikram taja tsaki, ta kalli neena sama da kasa, sannan ta nuna ta da yatsan ta dayaji karin akaifa da jan barce.

     Ke kada na sake , na kara jin ko gani ki, tare da prince kinji ko, dama ko yan kauyen nan yaya _TALAKAWAN_ nan, aikin ku kenan snatching mazajen wasu.

    Kawayen suka kwashe da dariya, neena ta dukar da kai kawai, ikram taja hannun ta, ta tura ta waje, get out , dayar kawar tace mutum kamar bunsuru, tana shigowa dakin yahau wari.

     Neena na fita tayi garden da gudu, ta samu wuri ta zauna, wani kuka tari yazo mata, zamanta tare da family dinnan shekara daya kenan, (kenan shekarunta sha bakwai yanzu)

Ba wanda ke wulakanta ta, tasan ita ba yar kowa bace, tasan ita _YAR TALAKAWA_ ce, amma ai suma mutane ne.

Ta saki wani kukan, ita kam tasan ya prince , ba sonta yake ba, amma yanzu, itama kam ta fara kamuwa sa son sa, dan yadda yake taimakon ta.....

.

Hannu taji a kafadarta an dafa ta, a tsorace ta juyo dan ganin waye.

Prince ta gani a bayanta, ta ware ido, tana goge su , wai ko gizo ne yake mata.

Prince ya zauna a kusa da ita, (ya kasa barci shine ya fito shan iska, Allah yasa ya hango fitowar ta sashen mami tana kuka).

.

Yana zama neena ta mike da sauri, zata fice.

   Prince ya riko hannunta, ta tsaya cak ta kasa juyowa, prince ya mike ya kusanto ta sosai.

    Neena gabadaya taji lumfashin ta na neman ya tsaya, toh mai hakan yake nufi?

   Bata idasa tunanin da take yi ba, taji prince ya juyo da ita,  ta fada a faffadan, kirjin sa, ta ware ido a tsorace...

     Saukar  ajiyar zuciyar shi  ,  gabadaya gabobin ta, suka kasa yunkurin kwace kanta daga kirjin sa, ta shaki kamshin sa, ta lumshe idon ta, take taji kamar an dasa mata wani masifaffen sonsa.

YayaB ce tazo wurin window din dakin ta, neena ta manta bata kullo min windows dinnan ba yau.....

   Hango su prince tayi, da yake akwai , wutar lantarki ta wajajen, ta haska su.

  Ta kura musu ido tana kallo, taji mamaki kwarai, ashe akwai ranar da prince su wata banda nateefa, ta kullo windon ta dawo ta zauna bakin gadon ta tana tunanin wannan al'amari.

Sai da sukayi minti sha biyar a haka,sannan  prince yasa hannu yadan matsar da ita, yayi tafiyarsa zai shige cikin gidan, neena tabi bayan sa da kallo, har yakai kofar shiga ya tsaya, ya juyo, shi take kallo, ya sakar mata murmushin da tunda take dashi bata taba ganin yayi saba.

     Neena mutuwar tsaye tayi , bata san lokacin da kumatun ta da lips din ta, suka bayyanar da murmushi ba, prince ya juya ya shige ciki.

.

Yana zuwa dakinsa, ya dafe kirjinsa, sai bugawa yakeyi da sauri da sauri, ya runtse idanunsa, koda yayi soyayya da lateefa, bai taba jin wannan yanayin ba, ya dafe kansa, noo prince u cant fall inlove wit dat small gal, gata _YAR TALAKAWA_ yarinyar da bata waye ba, yarinyar dake matsayin mai rainon danka, yaja tsaki da yaji zuciyarsa ta fara zafi, ya mike ya dauko drugs dinsa ya sha, sannan ya kwanta, wani barci mai dadi ya dauke shi mai tattare da mafalkai masu annashuwa.

Neena ma daki ta koma bayan ta duba amir yayi barci, ta haye saman gadon ta, tana murmushi kamar bakin ta zai yage, ta mike ta zauna tsakiyar gadon, ta dafa kirjin ta, ta runste ido, ta shiga tunano duk wani moments da sukayi da prince.

   Can kuma tadan tsaya da murmushinta, mai yasa toh ya rungume ta, kodai tausayin ta kawai yaji, ba sonta yake ba, ta buga uban tagumi tace....

    Ya za'ayi kuwa ya prince yaso ta, _YAR TALAKAWA_ da ita, wadda a karatu ma ajin ta uku ta tsaya, ta sauke ajiyar zuciya, shi dake da mata kamar ikram ai bazai taba son mace irin taba ( ni kuwa afrah nace, kedai duba mirror _NEENA_)

   Tadan buga goshin ta  da tafin hannun ta, neena ki dawo daga duniyar tunanin ki.

.

ikram kuwa neena na wucewa , ta kira mummy dinta, ta fada mata komai tace, mummy ba inda zani da wannan karuwar yarinyar, gara ma kusan abunyi kafin gobe eheen.

    Mummy tace, haba ai koni bazan yarda ki tafi da itan ba, zan kira mum dinshi, zamuyi maganar, ba inda yarinyar nan zata biku.

   Ikram tace, ni mummy har amir din ma, bana so ya bimu, da rainon shi zanji ko da cin amarcina ( kuji fa mutum yana magana da uwarsa amma kamar yana yi da kawar sa zamani kam ya canza).

Mummy tace, hakane gaskiya bari na kira mum dinshi muyi maganar, ikram tace toh mummy , sukayi sallama.

Moha dake zaune kusa da mummy yace, mummy mai ya faru ne da ita ikram dinnan, uwar shaida.

   Mummy ta fada masa, ikram na zargin prince da mai rainon amir.

   Moha yaja tsaki, dama ashe akwai abunda ke tsakanin su, shiyasa ranar ya bata min show, mummy tace kasan suna tare kenan, moha yace eh mana mummy ranar family dinner, ya ganni tare da ita, shine yazo ya wani kora ni, ashe dama shike nemanta, mummy taja tsaki , kai kuwa mai zakayi da wannan aljanar yarinyar, ga yan'matan a gari, moha yayi murmushi, mummy Allah yarinyar ce akwai kyau, mummy tace ,kadai bi ahankali idan abban ku ya san da wannan banzan halin naka , bazakaji da dadi ba ( pls iyaye mata a kiyaye).

.

Mummy ta kira mum, suka maganar , mum bataji dadi ba ko kadan, tayiwa prince aure ne, dan amir ya samu wadda zai kira uwarsa, amma ba damuwa nan gaba sai yaje, dan maganar mummy tayi tasiri a zuciyar mum, da tace idan amir da neena sukaje, su ikram "bazasu sake da junan suba"

Washe gari da sassafe, aka taru family,  a babban falon dad.

Abba yace wa mum, ita neenan ta shirya daiko? Ikram tayi saurin kallon mum, suka hada ido, mum tace ai bada su zasu tafi yanzu ba.

Dad yace kamar yaya? Mum tace wai da idan sunyi dan watan ni sai akai su amir din , abba yace hakan yayi, ikram tayi murmushi ta kallo prince... - Prince ya dauke kai, yayaB ta gyara murya, toh idan dai bazata bi su na'im ba, nizan tafi da ita.

  Duka falon aka kallo ta, tace ku kalle ni dakyau, ta kalli abba , yau zamuje ka kaini gidan su, nayi magana da umman ta, ta bani rikon ta, nasakata makaranta tayi karatu itama.

   Dad yace , yayaB ai ko anan dinma zamu saka ta, amma raba neena da amir zaiyi wahala.

  Abba yace kwarai kuwa, kada ki damu indai karatu ne zamu saka ta tayi inshaAllah.

   YayaB tace toh shikenan, dan dai bana son amir yayi rashinta ne kawai zan barta anan.

   Abba ya kalli faruk dake zaune suna magana kasa kasa da zarah, yace kai faruk, makarantar nan dakayi service,  kaje ka nemawa neena, dad yace kaje ka tambaye ta inda ta tsaya.

    Faruk yace toh dad, yaci gaba da maganar su da zarah, yayaB ta kai masa duka, kaji ja'irin yaron nan, an maka magana amma ko tashi bakayi ba, faruk yace, haba yayaB zan tashi mana, yayaB tace ai fah, an zama ango har an fara rashin kunya, nan da jiyane ana fada zaka mike, saura ka zama mijin hajiya...

   Aka kwashe da dariya, amma banda prince, mikewa yayi ma zai fita, yayaB tace su oh oh kuma, sai bakin rai, ana so ana kaiwa kasuwa...

  Ikram tayi wani fari da ido, prince yace ehh din ina ruwanki, yayi ficewarsa.

  Mum tace, ikram muje ki dauko jakar ki , flight din 8 zaku bi, mami ta mike tana cewa, bara na daukowa na'im danbum naman sa.

Prince ya fito da jakar shi, ya bawa faruk yakai masa mota, dakin amir ya nufa dan yi masa sallama.

.

A zaune ya iske su, suna wasan *X* and *O* a ipad din zuby.

    Sai dariyarsu sukeyi, ya tsaya yana kallon su, amir yace anty neena banda cheating fah, neena tace little master,  kaima fa dazun kayi , amir ya amshe ipad din ya haye gado yana cewa, toh dukkan mu winners ne, neena ta fara binsa yana guduwa, tace ban yarda ba, dawo mu sake wani...

     Suna cikin wasan su, basu ma lura da prince dake tsaye bakin kofar ba...

   Sai da zarah tazo wurin tana cewa, ya prince ka fito inji su mum...sai sannan neena ta juyo ta ganshi a tsaye, tayi saurin tsayawa daga wasan da suke, amir yayi wurin papa dinsa, prince ya shafa kansa, ya riko hannun sa, suka fita.

Neena tabi bayan su itama.

   

  A waje faruk ne zai kaisu, mum, mami , zarah, zuby duka ana wajen, yayaB taki fitowa , wai barcin ta zata koma.

     Mum ta rike ikram, tace ki kula da kanki dear, ikram tace toh mum, zuby da zarah sukayi hugging dinta, sukace ki kula mana da yayan mu, ikram tayi murmushi, mami tace shiga ikram kada kuyi latti, ikram ta shiga, prince ya fito da amir, yace takecare my boy, amir yace I will papa, prince yazo yayi side hugging mum, tace Allah yayi maka albarka , ka kula da matarka da kanka pls, prince yace ok mum, yaje yayiwa mami, ta mika masa wata leda, ga danbum naman, prince yace a'a mami ki barshi, mami tace aikuwa sai ka tafi dashi, wahalar neena bazata tafi a banza ba...

    Ikram najin ance neena, ta kallo neena dake rike da amir ta balla mata harara, neenan ma bata san tanayi ba.

.

Prince ya juya yakalli neena, bata san lokacin da tayi masa murmushi dole ba, dan wani daci takeji a zuciyarta, yanzu idan ya tafi bazata gansa gobe ba, hakama jibi, wasu hawaye suka sulalo mata.

Prince ya amsa ledar yace nagoda mamina..

  ikram ta duba jakarta dan dauko chewing gum,  taga ba dayar wayarta data bari a dakin mum dataje dauko gyelen ta, tace laah! na manta wayana a dakin ki mum,mum  ta kwalawa neenah kira, jeki daukowa ikram wayarta a dakina yi maza.

Neena ta saki hannun amir tace toh, ta shige cikin gidan.

     Prince na ganin ta shiga yace oops nima na manta drugs dina, mum tace yi maza kaje ka dauko, prince ya juya shima ya shige cikin gidan, ikram ta tabe baki kadai gama yangar , sai ka dawo cikin tafin hannun nan nawa.

Neena ta dauko wayar ta fito, a lungun da zai fitar da ita zuwa benen suka hadu da prince, tafiya kawai takeyi amma hankalin ta baya jikinta.

      Prince ya kura mata ido tana tahowa tazo har zata wuce sa, taji kamshin nan nasa dasauri ta tsaya ta kallo shi, prince ya kura mata ido shima ya sa hannunsa a kyakkyawar fuskarta, neena zata ja baya, yasa dayan hannun sa ya riko hannun ta, ta kalli fuskar sa da sauri..

    Ya wani daure fuskar tana kallon shi ya karasa kai hannunsa kan kumatun ta, ya goge mata ziraren hawayen fuskar ta.

.

   Neena ta kasa controlling kukan daya zo mata, ita wai meyasa ya prince yake mata hakane, ya kuwa san hakan da yake mata yake sa tana kara sonsa, shi tunda ba sonta yake ba ya daina tausayin ta mana....

    Wani kuka yazo mata, ta saki kukan, gwanin tausayi, fuskar nan har ta fara yin ja, wani abu ya tsayawa prince a makoshi, kirjin sa na bugawa da sauri da sauri, shi ma kansa ya rasa mai yasa yake jin tausayin yarinyar, kwata kwata baya son yaganta cikin damuwa, ganin hawayen ta dazun shiyasa yayi karyan dauko magani dan  kawai ya lallashe ta..

    Neena ta janye daga rikon da yayi mata, taci gaba da tafiyarta, prince yayi saurin karasawa wurin ta, ya jawo hannun ta suka shige dakin zuby dake kusa da wurin..

Ya saki hannun neena ya juya mata baya, tayi tsaye tana share hawayen ta tana shashshekar kuka, prince yace da silent muryar sa, kee mai yasaki kuka uhm, neena tace ni ba kuka nake ba, prince ya juyo yace toh me kike? Neena tace ni hawaye nake, prince ya kalle ta mai ya saki hawayen?  Neena tace wani abune ya shigar min ido na.

Prince yadan naushi hannun sa, yaso ace neena ta fada masa cewar danshi take kukan, shi baya son raini dan haka koda son ta yake ma, bazai taba fada mata ba.

Yayi dan tsaki yazo ya bude kofar ya fice, neena ta saki wani kukan, tayi saurin lallashin kanta ta goge hawayenta tayi waje da sauri.

A wajen ta iske shi zai shiga mota, ta mikawa mum wayar ikram, mum ta bawa ikram  zuby tace wa neena, mai ya samu idon ki?  neena tace wani abune ya shigar min, ta riko hannun amir suka shige ciki.

Prince ya shige mota shima, faruk yaja suka tafi, su mum nata musu bye bye

.

Neena dakinta ta shige, amir na kiran tama bataji shiba, ta haye saman gado , tana rusa kukan da baya da dalili, ita wacece da zatayi kuka dan ya prince ya tafi, ko amir baiyi ba sai ita, wata zuciyar ta bata amsa da , ke masoyiyar sace, kuma mai kaunar sa, neena ta daga hannun ta sama.

Ya Allah kaine ka halicci, dukkan bayi ka, Allah kai ka saka min son wannan bawan naka, Allah nasan bankai matsayin yin soyayya da wannan bawan naka ba, ya Allah ka zaba min abunda yafi alkhairi, ta sha a fuskar ta, sannan ta mike ta dauro alwala, tazo tayi nafila raka'a biyu, a take taji wani sanyi ya ratsa zuciyarta.

Su prince sun sauka lagos lafiya, sojoji ne suka zo daukar su, ikram sai cika take tana batsewa, shi prince gaba daya ma ya kosa ya isa gida ya samu peace of mind, dan wani haushin ikram dayake ji, gaba daya bata burge shi.

.

Sun isa kantamemen gidan prince dake Victoria island, a lagos, gaba daya gidan sojoi ne, suna sauka a mota, duka sojojin dake wurin suka zo suka sara masa, ya daga musu hannu kawai ya shige ciki, ikram na biye dashi.

Dakin sa ya shige, ta biyo shi ciki, prince yace dakin ki na can a gaba, ikram zatayi magana ya shige toilet abunsa, ta sauke ajiyar zuciya, lallai sai tayi aiki wurin shawo kan prince dinta.

Da daddare ikram aka ki barci, sai jiran ango takeyi, amma har sha biyu shiru bata ko kyallin prince ba.

Ta naushi gadon ta, taja tsaki, ta mike ta fito zuwa nasa dakin, ta murda kofar taji ta a kulle, ta shuri kofar ta koma dakin ta.

Prince najin ta tana murda kofar, yayi tsaki, mayya kawai, sannan ya dauko ledar danbum naman da mami ta basa.

Ya bude, wani kamshi ya doki hancin sa, ya bude robar, yasa hannu ya dibo kadan ya saka baki, wani dadi yaji ya mamaye bakin sa, ya lumshe idonsa, take ya tuno dazun, daya juyo yaga hawaye a fuskar neena, ya bude idon sa , yayi dan tsaki, why do I care about ha?, yayi kansa tambaya, ba sonta kake ba , tausayinta kake, wata zuciyar ta basa amsar tambayar sa.

Ya mike ya koma kan gadonshi, ya jawo wayar sa, ya kai sunan mum, Ya sa kira.

Mum ta dauka, ya sanar mata sun iso lafiya, mum ta kara masa fada sannan sukayi sallama.

   Ya mirgina , yana tuna lokacin daya rungume neena, ya sauke ajiyar zuciya, sannan runtse ido, a haka barci yayi awon gaba dashi.

.

Sati daya kenan da zuwan su prince lagos, amma ba abunda ya shiga tsakaninsu, kullum prince na busy wurin aikin sa, ikram abun duniya ya taru yayi mata yawa, gashi duk aikin gida ita keyi, duk da bata wani iya ba, shiyasa prince a waje hake siyo abincin sa.

Yau dai hakurin ta ya kare, kullum ta fada wa mummy sai tace, tayi amfani da hikimarta ta mata ta jawo ahi jikinta, taja tsaki ita mummy bata gane bane, ni ina ma ganin sa ne.

Wayarta tayi ringing,  wata sharifa ce, kawarta ce dake zama a lagos, ta dauka sukayi fita kadan, shine take fadawa sharifat, din ko zata taimaka mata, dan sharifat, gogaggiyar yar duniya ce.

Sharifat ta fadawa ikram, gobe zata zo suje wurin wani, bayarrabe ya iya aiki sosai, ikram tayi murna sosai tace mata to sai tazo din.

.

Neena yanzu harta fara zuwa school,  tana ss1 yanzu, idan ta dawo sai ta shiga kula da little master dinta, kullum zata kwanta sai ta tuna da ya prince.

Faruk kuwa, suna zaune lafiya da matarsa deeja, duk Fridays,  sai ya kawo ta , yayaB ta koma itama, su zuby da zarah suna busy da makaranta, yanzu gidan kullum shiru, dad da abba sunyi tafiya hajji.

Sharifa tazo gidan ikram, Allah ya so su prince baya nan ma, ikram ta shirya, ta kwashi kudi sosai, cikin wadanda ta samu na biki, sukayi wurin bokan yarbawa.

Sunje wurin shi, tsoho ne mutumin, baki mummuna, ikram ta tsorata da farko sosai, sharifata ta fada masa bukatar su, yayi sundabaru yace, zasu kawo masa jinin ikram na hayla, sannan zasu biya kudin aikin aljani.

Ikram ta gwale ido, sharifat ta kara zurmiyar da ita, ikram tace ai yanzu ma tan _ON_ ne, bokan yarbawa ya bata wani kallo kallo, yace taje ta diga jinin a kai, ikram tayi yadda yace, sannan ta biya kudin aikin bakin aljanin da zasu turawa prince.

.

Komai an kammala, boka yace taje gida zata sha mamaki.

Duk wannan abun dare ya tsaya sosai, prince ya dawo bai iske ta a gidan ba, yaja tsaki ya koma nasa dakin, yayi sallah yadan kwanta yana rage gajiya.

Cikin barcin sa yayi mummunan mafarki, wai ga wata bakar mata nan tazo da wuka zata kashe shi, har tazo zata tsaka masa wukar, wata tazo cikin fararen kaya ta rike hannun bakar matar, bakar matar ta ture mai farin kayan sannan ta hadasu duka zata kashe, dai dai prince ya farka....

Yayi zufa sharkaf, da kyal ya iya furta, a'uzubillahi minal shaidanil rajim.

   Dai dai nan ikram ta shigo dakin cikin isa, prince na ganin ta ya mike, yayi saurin zuwa ya rungume ta, yana sauke lumfashi, ikram tayi murmushin samun nasara, sannan ta shafa kan prince...

.

Cikin kwana biyu, ikram ta maida prince bawan ta, komai tace yayi sai yayi shi yake samun sukuni, gaba daya yanzu baya da aiki sai nata, dan ma zuwa aikin shi ya zama dolene, mummy ta kirata taji ko abu ya daidaita, ikram tayi dariya tace lafiya lau mummy nayi yadda kika ce , komai ya daidaita yanzu, ta mikawa prince wayar, hannunsa na rawa ya amsa, ya gaida mummy.

Mum suna falo tare da mami, sai zuby da zarah suna kallo, a dinning kuma su neena ne suna assignment dinsu.

   Kiran mummy ya shigo, mum ta dauka suka gaisa, sai mummy take fada mata ai su prince sun daidaita kansu, mum murna sosai tayi .

.

Mami ta kalli mum, ya naga kina jin dadi, wani abun farin ciki ne ya faru? Mum tace kedai bari danki ya sauko, sun daidaita da amaryarsa, mami tayi hamdala, kice shiyasa bai kiramu ba kwana biyu, toh madallah. Zarah tayi dariya, su ya prince an shiga layi, zuby dake waya kasa kasa , tadan jefawa zarah littafin dake kusa da ita, pls rage muryan mana, zarah tayi dan tsaki, ku bakwa gajiya da wayane, Allah sai na tonaki, zarah tace, mum....zuby tayi super ta rufe wa zarah baki, mami tace Allah dai ya shirye ku, ku kam.

Neena dake assignment dinta, duk maganar su mum tanaji, wani daci taji a zuciyarta, ita kam tana tausayin kanta, soyayya da wanda tasan bazata taba samu ba.tayi tagumi, amir yace anty neena, kalla, neena ta sauke ajiyar zuciya sannan ta amsa book din amir din.

*Bayan shekara daya* 

.

Dad da abba tare da mum da mami a falo, dad yace ni kam na kasa gane abunda yaron nan yake nufi, abba yashafa gemun shi, ni kaina wannan al'amari ya dame ni, ka duba ka gani, ko da dayake cikin damuwa yana zuwa weekend ko wani aiki ya kawo shi, mum data buga uban tagumi tace, ni amir kawai nake tausayi, gashi ko ikram din bata kira , mami tace gaskiya ya kamata a je aga ko lafiya, suna cikin maganar, wayar mum tayi ringing. .mum tayi saurin dauka dan ganin numbar prince...

    Sun gaisa tace wai kuwa lafiya?, prince yace lafiya lau, amma zasuyi tafiya zuwa Australia,  zasuyi watan ni shida, mum ta sauke ajiyar zuciya sannan ta masa fada na rashin kiran su da baiyi ba.

.

Hankalin iyaye yadan kwanta, matar faruk deeja yanzu har tana da tsohon ciki, faruk shike kula da harkokin su dad yanzu.

Su neena yan makaranta yanzu an waye an kara kyau, su zarah da zuby na kula da ita sosai kamar kanwarsu, amir kuwa yanzu sun zama jini da hanta, yana son neena sosai, hakama ita.

Yau Saturday,  neena ta gama shiryawa dan zuwa gaida ummanta, ta shirya amir dan tare zasu tafi.

Dakin zuby ta shiga dan mata sallama, ta iske zuby tasha gayun ta da wani lace , tayi kyau sosai, tana ganin neena tace, ki jirani muje tare, neena tace toh, taga zuby ta yafa babban mayafi, sai mamaki take, zuby zataje gaida umma, shine sai tayi wannan gayun?

.

Zuby tace wa neena, nayi kyau ko? neena tayi murmushi kinyi masifar yin kyau ma , zuby tayi dariya nagode, wayarta tayi ringing,  ta dauka tana murmushi,  tace sadeeq, kai koh, sai yanzu ka tuna dani?  Sai wayarta takeyi cikin nishadi, ta miko wa neena wayar, gashi ku gaisa, bari naje dakin mum na sanyo turare.

Neena ta amsa, tayi sallama tace ina kwana?, muryar yaya habu taji yana mata dariya, ta ware ido, tace yaya habu?, yayi dariya, kwana biyu bamu gaisa ba, zubaida tace kina zuwa lesson ko?, neena tace wai yaya tsaya badai anty zuby kake....yaya habu ya kwashe da dariya, ko batayi bane?, neena tace tayi mana sosai, suka sha fira, daga bisani suka yi sallama, neena tayi farin ciki sosai, dan tana son zuby sosai.

Sunje gidan umman, tayi farin ciki sosai da gani su, sai kallon zuby takeyi, dan yaya habu ya kirata ya sanar mata da zuwan zubaida gaishe ta, yarinyar tayi mata sosai, dan yadda neena ke bata labarin ta.

Amir na jikin umma, dan ya saba da ita, zuby tayi mamakin ganin umma, kyakkyawa ce sosai, kamar su daya da neena, da sadeeq, dandai shi bai kaisu haske ba, sunsha fura , sunyi fira sai da yamma, suka mata sallama suka tafi.

Tun wayar da prince yayi wa mum, bai kara kiran su ba, har wata shidda ya wuce, ana neman wata takwas.

Dad da abba suka kira faruk a falo, lokacin kwana biyu kenan da haihuwar deeja, dad yacewa faruk ka shirya gobe kaje min lagos, ko hauka na'im yakeyi ni na fi shi.....

.

Faruk ya mike, toh dad, zanje yanzu nayi booking flight,  abba yace toh madallah.

    Faruk na fitowa ya iske mum a tsaye ta jingine da bango, ya karasa wurin ta ya dafa ta, mum ki daina tunanin nan pls, inshaAllah komai lafiya, nasan aiki ne ya rike shi.

Mum ta kalli faruk da idonta ya ciko da kwallah, faruk ina ji a jikina na'im na cikin matsala, faruk ya girgiza  kansa, mum ba komai kada ki damu zanje na duba su yau dinnan, mum ta rike hannun faruk, ka taimaka kayi booking flight dani faruk.

Faruk yace no mum, ki bari naje ni kadai pls, ki kwantar da hankalinki, mum tace ka taimaka faruk, wallahi kullum sai nayi mafarki da na'im.

Faruk yace toh ba damuwa , amma na yamma ne zan samu, mum tace ba damuwa, zanwa dad dinku magana.

Mum tayiwa dad maganar bin faruk lagos, da farko yaki yarda, sai da mami da abba suka saka baki sannan ya yarda taje.

   Faruk ma ya shiga sashen mami wurin deeja, dan tunda ta haihu ya maido ta nan, sunyi bankwana. Su neena, zuby da zarah na wurin ta, kullum a nan suke wuni.

*Lagos*

Faruk da mum sun isa da daddare, suka samu mai taxi driver,  ya kawo su har victory island.

.

A gaban gate ya ajiye su, suka kwankwasa, soja ya bude musu, faruk ya masa bayanin, cewa shi brother din prince ne, sannan wannan , mahaifiyarsa ce, sojan nan yace yauwa, am glad I meet oga's family, ya kalli faruk yace, oga yana cikin damuwa kwarai kwarai, yau 2days kenan bama ganin oga, mum tambayi madam, tace wai miye namu ciki, sojan ya kalli mum, I think oga de sick Ma.

Faruk ya kalli mum, mum ta kalli faruk, hankalinsu a tashe , sojan yace su shiga, mum jikinta na rawa ta shige ciki.

Tun a bakin kofa, suke jin tashin music kamar gidan zai tsage, faruk ya shiga buga kofar amma inaaa ba'a zo an bude ba.

    Sojan nan ya karaso wurinsu, ma she no go hear wuna woo, kawai ku bude ku shiga ne, faruk ya murza kofar ta bude, mum ta shige da sauri, faruk na biye da ita.

.

Ikram suka gani, tare da kawayen ta , yan duniya ne na karshe, ga maza nan suma, an cakude ana ta kwasar rawa, ana zukar sugari, falon ya cika da hayaki kamar ana gobara.

Mum ta saki baki da ido, faruk ya tsaya cak yana kallon ikon Allah, mum ta kasa hakuri dan ganin ikram bata masan sun shigo ba.

Mum tace , *IKRAM*!!!!!!!!!

   Da tsawa, har sai da gidan yadan amsa.

    Da sauri ikram ta juyo, sukayi ido hudu da mum...

     Ta ware ido tana kallon mum, ta karaso cikin rawar jiki, mum tace a fusace ina Dana yake????

   Ikram ta nuna mata sama, mum da faruk sukayi saurin saurawa saman, ikram tajaa tsaki, sannan ta sallami duka kawayen shashan cinta.

.

Mum na shiga dakin, taga dakin duhu, ta kunna wuta, can suka hango prince, a kwance yana lumfashi dakyal dakyal, mum tayi saurin karasawa wurin sa, faruk yazo ya rike hannun prince, yayi baki ya rame, mum ta saki wani irin kukaa, ikram ta shigo dakin, mum ta mike a fusace, ta shiga wanka mata mari..., ihun da ikram tayi , yasa prince mikewa da kyal, yacewa mum, kada ki kara marin mum, da sauri mum ta juyo tana kallon shi, tace na'im ba hankalin ka daya ba, prince ya daddafa ya mike, yayi wurin ikram ya rike ta, sai kukan shagwaba takeyi, faruk yace ya prince, ciwon kane ya dawo?, Prince ya wani harare shi, ya nuna musu kofa, ku koma gida, zan zo...

    Mum ta kasa cewa komai, sai kallon prince takeyi.

Faruk ya rike hannun ta, yaja ta suka fita..

Wurin sojan suka dawo, yace ai nasan madam ba mutumin kirki bane, faruk yace wa mum, ya prince ba hankalin sa daya ba, kuma ciwon sa ya dawo, dan yadda naga yana lumfashi, sojan nan yace, eh mana an taba kai oga hospital yayi collapse,  hankalin su ya kara tashi, mum sai kuka takeyi, faruk yace, muje nayi miki booking flight,  ki koma gida ki sanar dasu dad komai, ni zan tsaya nan.

   Mum ta kada kai kawai.

Mum ta isa da daddare sosai, ta iska yayaB tazo dan lokacin an kusa babbar sallah.

    Hankalin kowa sai daya tashi ganin yadda mum ta dawo, ta kwashe komai ta fada musu, kowa hankalinshi ba karamin tashi yayi ba, neena dake labe itama tana komai, wani hawaye taji yazo mata, ba karamin tausayin prince tayi ba.

YayaB tace , wannan al'amari harda sihiri, amma na'im bazai taba aikata haka ba, abba yace gaskiya wannan al'amari abun a duba ne, dad yace aikuwa dani ake zancen, ya ciro wayarsa , ya kira numbar wani malami, daya koyar dasu prince din islamiyya.

Suna nan zaune jugum a falo, ya iso, malam ya zauna aka fada masa komai, yace toh su bashi dan da gobe da safe.

  

Da sassafe malam barau, bayan kowa yazo ana jiran bayanin sa, yayi gyaran murya yace, gaskiya,  wannan al'amari bayyi dadi ba, wato na'im dai _SIHIRI_ akai masa....

Gaba daya falon suka hada baki wurin cewa sihiri....

,

YayaB tace, bana fada muku ba, wannan aikin sihiri ne.

    Abba yace , yanzu yaza'yi kenan malam?

  Malam barau yace, bakin sihiri ne akai masa, dan haka dole ne sai an kawo sa nan.

    Dad yace, yanzu ya zamuyi mu kawo na'im nan?, mum tace gaskiya zaiyi wahala dan na'im zai iya hallaka wani dan ikram.

       yayaB tace, ku kira min faruk dai ku gani, mami ta saka kiran faruk ta mikawa yayaB.

YayaB tayi masa bayani, kamar yadda malam yayi musu, faruk yace da wuya ikram tabar ya prince ya biyo ni, yayaB tace , kace mata mahaifiyarta ba lafiya, idan kun iso airport,  ka make shegiya ka taho mana da na'im kaji!!? Faruk abun dariya yama bashi, yayaB taja tsaki,dadi nadai tsoro wlh, duka nawa take, faruk zai magana, yayaB tace  kai kayi maza da Allah, malam nada abunyi, ta kashe wayar.

Neena ranar gaba daya tana daki, sai karatun alqur'ani takeyi, tana wa prince addu'a.

Kamar yadda yayaB tace wa faruk yayi, haka kuwa yayi, da wayar soja John suka kira ikram, sukayi mata karya, kamar dai likita ne ya kirata mahaifiyarta na asibiti, hankalinta yayi mugun tashi, kuma Allah ya taimaka, duk numbars din data kira basa shiga, da yake da sassafe ne, lokacin  mummy ma basu kai ga tashi ba.

.

A take tayi booking flight,  tare da prince,  dake jin jiki, kokari kawai yakeyi yana binta.

   Faruk ma ya bisu, a jirgi daya suke, amma faruk bai yarda sun ganshi ba.

Suna isowa abuja, dama an turo driver, ikram na rike da hannun prince, daya koma kamar wawa sai binta yake kamar bindi, sukazo neman mai taxi, a inda suke tsaye, motar su faruk ta tsaya, fitowa faruk yayi, ya fisge hannun prince daga na ikram, yayi saurin turasa cikin motar duk da prince din na fisge wa, ikram ta shiga kuka, tana bin motar, amma inaa su faruk sun mata nisa.

Suna isa gida, faruk ya riko prince, prince na sauko da kafarsa, yaji kan sa ya sara masa, ya dafe kan, faruk na masa sannu, har suka karasa cikin falon, duka family suke mike , sun tausayawa prince mutuka, mace ta kusan hallaka shi.

Mum kuwa hawaye kawai take, dan ita taja masa, tunda dama bason auren yake yi ba, duk ita taja wa danta wannan wahalai.

Faruk ya zaunar da prince gaban malam, malam ya kurawa prince ido, ya taso yazo ya dafa kansa, yayi masa addu'a , sannan ya basa ruwan addu'ar , da kyal aka samu yasha, aka shafa masa a fuska, take prince ya fara yi kamar zaiyi amai.

.

Malam yasa zarah ta kawo ruba, ai kuwa prince ya shiga kwara aman wani irin bakin abu, yana gamawa ya fadi sai barci kuma.

       Malam yace ku kaishi daki, idan ya farka inshaAllah zai dawo daidai.

     Dad yayi masa godiya sosai, abba yace wa faruk, ya kira driver su kama sukai shi dakin.

     YayaB tace, malam ba wani maganin da zaka basa ne, mami  dake zaune shiru tace, eh malam ko ruwan addu'a babu?

    Malam barau yace, zan aiko a kawo masa anjima, akwai su duka, amma sai nan da yamma InshaAllah.

Sukayi wa malam godiya, akasa faruk ya maida sa gida.

Ikram kuwa hankalinta ya tashi, tasan dole ne iyayen prince suyi masa magani,tasan kashinta ya bushe,  gidan su ta nufa, kamar mahaukaciya, ta shigo falon, mummy, moha, fuad duka da abban su , suna dinning suna breakfast.

Tana shigowa ta zube a kasa, sai shure shure takeyi, mummy tayi kanta tana tambayar ta hankali tashe, tace, lafiya ikram da sassafen nan?, ikram tayi dariya, sai sushe sushen kai takeyi, ta fara zaiyana duk wani asiri da tayiwa prince.

.

Abbansu ya fusata sosai, mummy kuwa zaman dirshan tayi, moha ya kasa dauke ido daga kallon ikram, mamaki yakeyi, yauwa ikram tayi wayo da har tasan tayiwa wani asiri,  abbansu yahau dukanta kamar jaka.

  Mummy ta tashi tana basa hakuri, ya ture ta yana fada kamar zai cinye su, duk laifin mummy ne kawai yake cewa, bata bawa yayan ta tarbiyya ba, ranar ikram duka har sai da abban ya gaji ya ya fice cikin konar rai, nan kuma ta fara hauka, hankalin mummy in yayi dubu ya tashi, tasa moha ya kamata ya kai daki suka kulle ta, suka fita dauko likita.

Mami da mum kitchen suka shiga, suka shiga hadawa prince girki kala kala, hankalin su kwance, sai godewa Allah sukeyi.

Zarah da zuby tare da faruk su, aka bari dakin prince su kula dashi.

Neena da amir , kuwa turasu  akayi wurin deeja, dan kada kadaici ya dame ta.

Hankalin neena ya kasa kwanciya, ita kawai burinta shine, taga halin da prince yake ciki, deeja tace, neena kodai bakya jin dadi ne, yau ba ko fira, baby ma tayi missing din daukarta da kike.

Neena tayi murmushi, lafiya lau anty deeja, kawai dai tunanin waec dinnan zamuyi nakeyi, deeja tayi dariya, ba wani wahala gareta ba, indai kinyi karatu.

   Neena tayi murmuahi, ta mike tazo ta dauki babyn, tana cewa, bari ya faruk yazo, sunana za'a sawa babynah.

.

A hankali prince ya bude idonsa da sukayi masa nauyi, zarah tace ya faruk, ta nuna masa prince, faruk yayi saurin kama hannun prince, ya prince sannu, baka jin komai ko, prince ya motsa bakinsa, a hankali, dauko min drugs dina, faruk yace wa zuby, duba acan ki dauki drugs dinda abba ya kawo dazun.

Zuby ta kawo, zarah ta fita ta kawo masa ruwa, tare ta shigo dasu mum.

    Sai sannu suke masa, mum tace na'im badai inda ke maka ciwo ko?, prince yace a hankali, zuciyata nadan zafi, amma nasan idan nasha magani zai bari, kada ku damu.

Mami tace sannu dana, kai faruk taimaka masa yayi wanka.ku kuma muje ku dauko abincinsa.

Prince yayi wanka, ya saka kana nan kayansa, su zuby suka zuba masa abinci, yaci bana wasa ba, sai mamakin shi sukeyi, dan bai cika cin abinci haka dayawa ba.

Su neena kuwa suna sashen mami, tadan sake suna fira da deeja.

    Faruk ne ya shigo dakin da sallama.

   Deeja tace sannu , ya jikin yaya prince din, faruk na neman zama gadon yace, da sauki yama tashi yaci abinci, kinsan abun ya hadu da miskili, sai a hankali.

    Neena dake jinshi, taji wani sanyi a zuciyarta.

  Faruk yace, su neena yan waec ana dai karatu ko? deeja tayi dariya, tana nan tana tunanin exams dinma, faruk yace kiyi karatu ba wani wahala garai bane, neena tace karatu kam muna tayi, sai dai yaya ku taya mu da addu'a , faruk yace inshaAllah, yauwa munyi waya da sadeeq, yace gobe zai dawo daga Jordan. 

     Neena tayi murmushin jin dadi, at last zata ga yaya habun su, tace Allah ya kaimu.

.

Har yamma neena na sashen mami, suna kicin da zarah, abba yasa ta hada masa danwake, amma bata iya ba, sai tayi inviting neena ta taya ta, suna gama kwabin su, amir ya shigo da gudu, yaja hannun neena, anty anty, zo muje papa dina ya zo, neena tace ka bari muje anjima little master, amir ya dunga janta yana cewa noo noo muje yanzu, zarah sai dariya take musu.

Prince duk ya gaji da kwanciyar, ji yake kamar an dauke masa wani dutse mai nauyi daga kansa, tsana kyama da dana sani duk yake akan ikram.

Amir ya shigo da gudu, papa papa, ya fada akan jikin prince, prince ya rungume shi, my boy kaine haka, ka zama big boy fa, amir yayi dariya yace papa, ka manta dani, kullum anty neena sai tace min zaka zo, zaka zo, amma baka zo ba, prince ya dago kansa, ya kalli neena dake tsaye, ta kura masa ido, gaba daya tausayin shi take, yadda duk ya rame.

Prince ya kura mata ido shima, gaba daya ta canza, ta kara girma tayi wani irin kyau, yayi saurin dauke idon sa, ya shafa kan amir my boy am sorry koh, ka yafe wa papa, amir yace na yafe maka papa, sukayi hugging junan su.neena tayi murmushi itama.

.

Da daddare mum ta zauna kusa da prince, ta riko hannun sa, ka yafe min na'im duk ni na jawo maka....

Prince ya katse ta , noo mum bake bace, haka Allah ya kaddara, yayaB ce ta shigo tana fadin ina angon ikram?,

   Mum tace yayaB bama son jin sunan nan a gidan nan, yayaB ta zauna itama, tace sannu na'im, prince ya kada mata kai, ta kalli mum , yanzu ya za'ayi da auren?

Kinsan dai ba sakin ta yayi ba, mum tace sai gobe akayi maganar dasu dad dinsu, yayaB tace hakane, sannan ta mike, su na'im gara dai a maida jiki, dan jibi sallah, kadan fito da fasali, amma dai ko abinci bata baka ma ko?, prince ya mike yana kumbure fuska, kije yayaB ki tafi hakanan, surutun nan naki zai sani ciwon kai, yayaB na dariya ta fita, mum ta mike itama, inshaAllah bazan sake matsa maka da maganar aure ba, prince yace mum kada ki dauki wannan al'amarin ya faru ne saboda ke, Allah ne ya kaddara zai faru, mum tace toh my son, ka kwanta kayi barci ka huta.

Neena a kicin, ta hada wa amir hot milk dinshi, zuby ta shigo daukar ruwa, ta dauki roban hot milk din da yayi ragowa, yau dai rabona ne, neena tayi saurin kwacewa, anty zuby akwai mai shi, zuby ta tsaya kallon neena, da mamaki, dan ita take bawa sauran ko ta kai wa deeja, toh yau koma wa zata bawa?, 

   Zuby tace neena na waye, neena ta shiga zare zaren ido, uhm uhm na na, ya........prince

  Zuby ta kalle ta baki bude, ya prince.?? Zata kara magana, mum ta kwala mata kira..

Ta fita da sauri, neena ta sauke ajiyar zuciya.

Sannan ta dauki cups din guda biyu ta fita.

   Ta kaiwa amir nashi, sannan ta zauna da dayan ta rasa ya zatayi ta kai wa prince, amir yace anty wannan naki ne? Kisha mana kada yayi sanyi.

  Neena ta mike, ba nawa bane, ina zuwa little master, ta fice da sauri.

.

Tazo bakin kofar dakin ta tsaya, sai dataji kamar wani na tahuwa tayi saurin bude kofar ta shiga.

A kwance ta iske shi, yana karatun wani novel, yana jin bude dakin ya kalli kofar, yaga neena a tsaye.

   Neena da kyal take daga kafar ta, prince ya mike ya zauna, yace lafiya?

Neena ta miko masa cup din hot milk,  wannan na kawo maka, prince ya dan kalle ta, ya miko hannu zai amsa, neena tace da zafi, prince ya nuna mata kusa dashi, zauna, neena ta kasa gardama dasshi dan tausaya masa da takeyi.

Ta zauna, prince yace sai ki bani nasha , tunda ke baya miki zafi a hannun, neena ta kalle shi, taga ita yake kallo shima, tayi saurin dauke idon ta, tace toh.

   Prince yayi mamakin ta, ta kuwa miko masa cup din a baki, amma bata bari sun hada ido ba, yakai bakin sa yasha, wani dadi yaji sosai, baiso yasha dayawa ba, amma hakanan ya samu kansa dashan madarar sosai, yana sha yana kallon neena.

  Har saida madarar ta kare sannan neena ta mike, bata lura da akwai ruwa a kasa kusa da ita, sai dai taji lema a kasan, ruwan ya rube, skirt dinta ya tadiye ta, ta fadii luu akan gadon, kuma a jikin prince.

      Gabadaya sai da sukaji wani yarrr, neena ta kasa tabuka komai, shi kuwa prince , wani yanayi ya shiga, kirjinsa na bugawa da sauri, har neena sai data ji ma....ta kalle shi da sauri, zaton ta ciwon sane, ta mike da sauri.., tana cewa badai jikin bane ko?  Prince ya girgiza mata kai, ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta dauki cup dinta ta fice...

                                   .

Washegari da safe, duka family ana falo, neena da amir sun tafi school.

Dad ya gyara zaman sa yace, na'im ya jikin naka?

Prince yace  da sauki dad.

   YayaB tace ni yanzu maganar matarsa za'ayi, mum tace dazun munyi waya dama mummy din ikram din, ta bada hakuri sosai, tace bama da sanin ta bane, ikram ta aikata wannan danyen aikin.yanzu ma halin da take ciki ya ishe ta ishara, dan suna asibitin mahaukata..

      Duka falon aka hau salati, prince dai dauke kai yayi kawai, shi da zasu taimaka masa ma dasun daina ko ambatar sunan ta.

Abba yace ashsha, Allah ya kara tsarewa, ni ina ganin mu barwa na'im komai a hannunsa, idan yaji zai iya yafe mata suci gaba da auren toh, idan kuma ya gaji sai ya bata takardarta.

    Dad yace gaskiyane, yayaB tace, zaman na'im da wannan jahilar yarinyar ya kare...

Mum tace kwarai kuwa, gaskiya bazan sake yarda a kara cutar min da daba..

   Mami tace nima dai ina ganin rabuwar zata fi.

   Dad yace kudai ina ruwan a ciki, miji da matarsa..

  Abba ya kalli prince, na'im kaje kayi shawara kafin gobe kaji.

   Prince ya kada kai,ya mike ya fita, mum ta bisa da kallo, kodai bai dawo hankalinsa, miye abun tunani aciki, kawai ya bawa ikram saki kowa ma ya huta.

.

Ranar gaba daya neena na school,  sai da yamma ta dawo, cikin sauri ta shirya, ta shiga dakin mum, ta sanar mata zuwa gaida yaya habu, dan ya iso ranar daga jordan.

Amir yayi yayi ta tafi dashi amma taki, dan motar haya zata shiga.

Cikin murna ta shigo gidan, salamu alaikum, ina babban yayan yake?

    Umma da sadeeq suka fito, yayi wani haske, ya kara kyau sosai, ya kara wayewa, ga kayan jikinshi ma sun mutukar amsar sa, ya aje kasumba, sai murmushi yake sakarwa neena, shima din ba karamin ganin girman ta yayi ba, dan ma zuby na aika masa pics dinsu.

Neena ta ware idanun ta, umman waye wannan arab man din?

   Umman tayi dariya, waye kuwa, yayankine.

   Neena ta rike kugun ta, like seriously? , yayana kaine kuwa?

    Sadeeq yayi dariya, kaji yarinyar nan, harkin ma manta da yayan naki kenan?,

   Neena tayi dariya tayi saurin zuwa ta rungume sa, well come back yayan, sadeeq yayi murmushi yace my sis kin ganki kuwa, kinga yadda kika koma yan mata.

  Neena ta rufe fuskarta da tafin hannun ta, kai yaya ni har yanzu yarinya ce ko umma?

  Umma na shiga daki tace, ni rabani da shiga karyayyakin ki,

  Neena ta riko hannun sadeeq, muje ka bani tsaraba ta.

Sun shiga dakin umma, sai fira sukeyi, cikin nishadi da barkwanci.

  Neena ta matsa wa sadeeq sai ya bata tsarabar ta, yace kin cika damun mutum wallahi, oya jawo min akwatin can.

  Neena cikin zumudi ta jawo ta kawo masa a gaban sa, ya bude ya ciro wasu laces guda biyu da set din sarka da yan kunne masu tsadar gaske, ya mikawa umma.

    Umma tace harda ni kuma, toh an gode Allah yayi albarka.

    Ya ciro wasu materials guda uku, da arebians gowns guda biyu, sai indian set of yan kunne da sarka, sai waya kirar samsung A4.

Neena tace woah wooah , yaya duk nawa ne,?

  Sadeeq ya harareta, yace ga naki, materials daya, set din yan kunne da kuma waya A4 , neena ta daka tsallen murna, wayyo yaya nagode...

   Sadeeq ya dan yage muryar sa, wannan na inlaw dinki ne, da zara'u..

  Neena tace woow sun gode sosai, amma zaka zo gaida su dad ko?

   Sadeeq yace eh, nama kirasu na sanar dasu dawowa ta, faruk yace deeja ta haihu, yaushe ne sunan ma?

   Neena tace saura kwana uku.

  Umma tace ina ta cewa nazo barka, amma kuma sai ga, shamsiyar , jamila ta haihu itama, ina zuwa tayasu aiki.

  Neena tace ba damuwa ai, zan fadawa su mamin.

    Sunsha fira sosai, sai karfe bakwai neena ta baro gidan, dan gobe sallah, kuma mum tace ta dawo.

Mai taxi ya ajiye ta a gaban gate, ta biyasa kudin sa ta shigo, ta gaida mai gadi, tayi ta bayan gidan.

.

Hango ta yayi tana tahuwa cikin tafiyarta mai daukar hankali, prince ya kura mata, daga inaa take ?

    Ita neena bata ma san yana ta wajen ba, sai tafiyarta takeyi, dauke da ledojin kayan da sadeeq ya basu, sai murna takeyi yayanta ya dawo, kuma har waya ya siya mata.

Bata ankara ba , Sai dai kawai taji an jawo hannun ta, ba karamin  tsorata tayi ba.

, jikin bango ya jinginar da ita, ta kware  baki  ta saki ihuuu,  ga  wurin duhu ya mamaye bata ganin kowa sai inuwa.

.

Wayyooooo,ta furta a tsorace..... taji ansa hannu antoshe mata baki... - .

Ta ware manyan manyan idanunta, kirjin ta kuwa kamar zai bullo, fitsari kawai ya rage tayi, a tunanin ta barawo ne ya shigo musu gidan.

Prince ya jawo hannun ta da karfi, sukayi tafiya har wurin da kawai haske.

   Neena kuwa sai bin sa kawai take, gashi ya juya mata baya, bata gane ko wanene ba.

     Har sai da suka iso bangon kusa da kicin din mum, ya sake jawo ta ta dawo gaban sa, ya jinginar da ita da bango kamar dazun.

     Sai lokacin neena ta ganshi, amma har lokacin a tsorace take, mai ya prince keyi anan?

      Bata idasa tambayar kan  taba, taji yace da silent voice dinshi, ina kikaje?

Yayi maganar yana daure fuska, neena tayi blinking(kyafta) idonta sau biyu, ta nuna kanta da yatsan ta, Ni?

Prince yace a'a ni, neena ta hadiye yawu da kyal, gaba daya ya dawo mata prince dinshi.

    Yayi two steps, sai gashi dab da ita, bude kofar sukaji za'ayi , yayaB ce, ta fito rubar da ruwan zafin data gama kasa kafarta..ai ni zubaida kada ma kimin magana, har nace miki kizo ki kasan kafa, ki wani turo dan bakin ki kamar biro, dan kina amsa waya ko.....

   YayaB na maganar ne tana shirin fitowarta....kuma dole ne idan ta fito ta gansu.

Prince ya rike hannun neena, ya fisgota sukayi baya sosai, ga wurin yayi duhu sosai, ya jingina da bango, sannan ya jawo ta jikin sa, neena ta kware baki, dan yayaB taji ta, ta taimaka mata, a zaton ta prince sai ya bata punishment din dawowar dare da tayi, dan ta taba jin su zarah da zuby na fadin, idan sukayi dare ya prince na cin uban su.

.

Prince ya daure fuska yayi saurin rufe mata baki, ya sa dayan hannunsa a lips dinsa, meaning tayi masa shiru

Gaba daya ta kasa sukuni, sai neman kwace wa takeyi, prince yayi dan tsaki, ganin yarinyar zata tona shi, gashi wannan yayaB din surutu kamar radio. .yasan ta gansu, kowa ma sai yaji a gidan...

   Ya sake janyota sosai, har suna jin lumfashin juna, hancinsu na gogar na juna, idanunsu na kallon juna, take neena ta nutsu, dan wani irin kyau da kwarjini da prince yayi mata..

   Shima prince dai kawai controlling kansa yake, ya kasa dauke idonsa daga kallon cute face din neena, (shes darm a pretty dude) zuciyar prince ta fada masa... (ni kuwa afrah dake tsaye ina kallon ikon Allah,, nace make I play aashiqui song 4 dem"sunn raha hai" lolz).

Sai da sukayi minti 10 a haka , sannan sukaji rufe kofar yayaB, lock lock ta saka key ta rufe gaba daya tana cewa, sai ayi ta barin kofar nan a bude, bacin kowa na ciki mtsw, ta fice daga kicin din tana kashe wutar kicin din....

.

Neena ta fisge da karfi, daga rikon da prince yayi mata, tayi saurin karasawa wurin kofar tana bubbugawa, ta leka ta window tana kiran sunan zuby! YayaB! Amir! Mum!... amma shiru ba wanda yasan ma tanayi....

   Kamar zatayi kuka, ta saki kayan hanunta, tayi tsaye hawaye na fita, wayyo yau a waje zata kwana kenan?

Gashi bata da waya a hannunta, wanda ya sadeeq ya bata kuma ba caji bare simcard...

Prince kuwa tsaye yayi, sai data gama nata rakin , sannan yazo, ya murda yaji gam, yaja tsaki, ya leka windows yaga an ma rufe kofar kicin din, yazo wurin neena.

   Yace, ya zamuyi kenan? Neena kamar ta shake shi, duka bashi ya jawo ba, da yanzu tana daki abunta, ta rufa da bargonta mai laushi, dan sanyin wajen nan yayi yawa, gashi bata son sanyi...

    Bata san ma hararar prince takeyi ba, tana tunanin nan, shi kuwa, burge shi ma ta kara yi...har taso ta basa dariya, yadda duk ta wani shagwabe fuska, zata kuka..

Neena tace ya prince ka kira zuby please, prince yace gud idea, ya saka hannun sa cikin aljinu, yaji wayam...

  Neena ta kura masa ido, tace badai ka manta wayan a ciki ba?? Kamar zata fashe da kuka tayi maganar...

     Prince ya kada mata kai, neena ta kwashi kayan ledojin ta, bari naje sashen mami na duba ko basu kulle ba...

   Ta tafi da sauri, prince ya saka hannunsa a aljihu ya koma , wurin rumfar garden , ya zauna.

.

Neena taje taga sun rufe suma, kamar ta fasa ihu, ta sake dawowa, ta hango prince a zaune abunsa, mtsw shi bai ma ko damu ba, dan yana da jacket dinshi zata rage masa jin sanyin nan, ni fa, ta kalli jikinta...

   Gown ta saka, mai guntun hannu, sai gyele bamai kauri bane sosai, ko dan kwali bata daura bama, tana zangin zuwa wurin yaya habu...

  

A sanyaye tazo ta zauna itama, prince ya jinginar da kanshi a kujera ya lumshe idon shi.

Neena tasa gyelen ta, ta rufe jikin ta, still tana danjin sanyin, ta takure sosai...

     Sai data dauki minti sha biyar a haka, duk tsoro takeji, amma tana kallon prince taji she's save, tunda yana kusa, tayi murmushi , sannan tasa kanta a table, barci yadan dauke ta...

    Prince ya bude idonsa a hankali,

  Ya taso yazo wurin ta, gashin ta yadan sauko a fuskarta, sai barcin ta takeyi, amma a takure da gani dai tana jin sanyi..

    Prince ya cire jacket dinshi, ya rufe mata jiki, sannan ya jawo kujera, ya zauna dab da ita, ya sa hannun sa, yadan janye mata gashin daga fuskarta, ya kura mata ido, tun daga idanunta, gashin idonta masu tsayi, zuwa hancinta, medium, yayi fitting din fuskarta, zuwa cute pink lips dinta, suma sunyi daidai da fuskarta.

Prince yakai hannunsa ya shafi lips dinta, take ya sauke ajiyar zuciya...

      Ya mike kadan, ya sumbaceta a goshin ta, a hankali ya motsa bakin sa.

       Zai furta.......

Fans na bar muku amsar abunda prince zai furta....

Lols sai naji guesses dinku zanci muku gaba

Love u all muah....

.

Sai daya lumshe ido ya bude ahankali _yace_ ji yadda take barci so soundly a waje, is she dat careless?  yayi murmushi ya shafi gefen fuskarta,yace   sleeping beauty. ..

Ya matso da kujera, ya zauna dab da ita, ya kwantar da kansa yana facing din fuskar neena sosai ya jawo hannun ta ya rige gam, kamar wani zai kwace masa ita, yana ta kallon ta, har barci ya dauke sa...

Neena tajibwuyanta ya fara mata ciwo, ta bude ido a hankali sai ganin prince tayi dab da ita, ta ware ido👀, mai ya kawo ya prince nan?, tazo sa hannunta ta goge idanunta dan tabbatarwa kanta ko shine din?

Taji hannun kamar an rike, tayi saurin kallon hannunta taga prince ya sarke hannuwan su, ta sake kwalo ido, ta kalli fuskar sa,  ya prince ya hadu karshe, tayi murmushi Allah ya mallakamin kai my prince, ta zare hannun ta daga nasa a hankali, ta kai hannunta ta shafi gashin sa mai laushin gaske da yasha gyara sai kamshi yakeyi, ta shagala da shafar gashin nasa.... 

   

Prince ya bude idon sa ahankali sukayi ido hudu da juna...

Neena tayi saurin dauke hannunta, duk ta rikice tayi baya da sauri, kujerar ta ta tafi suuu....

    Ta fadi gwajab.....

Prince ya mike da sauri yana kallon ta...

Neena ta runtse idonta, oh God, ta matse bakin ta dan taji dan zafin faduwar...Duk kunya ta isheta...

Prince kuwa yadda ta runtsee ido ta matse dan bakin ta sai abun ya basa dariya...

   Ya hau mata dariya, neena ta daure fuska shi kuma kullum idan mutum ya fadi instead of  ya taimaka masa sai yahau masa dariya...

   Ta shagwabe fuska tace ya prince. ...

  Prince ya tsaida dariyar sa ya mika mata hannunsa, maganin marar gaskiya kenan ai..

  Neena ta kama hannunsa ta mike...

  Tace har yanzu dad bai fito sallah ba,, ko karfe nawa yanzu??

    Jin ta taka wani abu yasa ta kalli kasa, jacket din prince ne, ta duga ta dauka tana cewa mai ya kawo jacket dinnan nan? A zuciyarta tayi maganar...

   Prince ya amshe da sauri ya zauna abunsa, neena ta tabe baki itama ta zauna...

   Barcin ma fita daga idonta yayi, data dago ido sai suka hada da prince, tace kai Allah ya masa kallo..

   Prince shi kam mamakin kansa yake  baya gajiya da kallon ta ko kadan...

Suna nan zaune har karfe biyar tayi sukaji bude kofar dad...zai tafi masallaci...

Prince yace wa neena ki buya kasan table dinnan, neena tayi saurin boyewa shima ya shige karkashin table din...bugewa sukayi...sukace auuusshh... a tare kuma suka daurawa juna finger a lips shiiiish!...

     Abun kuma sai ya basu dariya sukayi wa juna murmushi. ..

   Dad na wuce wa suka fito

Prince yace ki shiga now, bari naje sallah nima..

  Neena ta kada masa kai ta dauki ledojin ta ta shige gidan...

.

Ranar da safe, _sallah_..

  Tunda safe suka shiga aiki, mum da mami da inna ladi ke abinci...

  Neena da zuby da zarah suna sashen mami, tare da deeja  suna ta hada snacks, neena tace ohh God na manta, ta mike da sauri ta tafi sashen mum..

Zuwa tayi ta dauko kayan da ya habu ya bata...

Tazo wurin su zuby, anty zuby gashi inji yaya, jiya ya bani yace na baku...

  Zarah ta amsa ledar, wooow.. zuby kalla  exactly irin wannan ne da muke nema..

   Zuby ta amshe, eh na sani ya tambaye ni ko inason irinsa, neena ta basu nasu, zarah tace gaskiya munayi da ya sadeeq..

Zuby tace da kuyi da kada kuyi dashi, ni inayi dashi...

Deeja da zarah suka kwashe da dariya...

An dawo sallar idi, faruk da sadeeq suka shigo falo..

  Sadeeq ya gaishe dasu mum da mami...suka amsa masa a sake...suna taya sa murnar kammala karatunsa.

Har yamma yana gidan, zubaida da shi suna compound sai fira sukeyi..

Neena dake zaune ita da amir a dakin yayaB.

YayaB tace neena jeki wurin zarah kice ta bani lemon nan na madara..

   Neena tace toh ta mike, taci gayun ta cikin riga da skirt sun amshe ta sosai, hips dinnan ya fito, ga shi ta gyara gashinta yayi das dashi cikin daurin dankwalinta, zuby ta mata simple makeup, amma tayi kyau kamar a sace..

.

Ta fito zuwa side din mami, ta iske zuby da ya sadeeq suna soyewar su, tayi murmushi, yaya ashe baka tafi ba..

     Ya sadeeq yayi murmushi, ina nan tare da mrs sadeeq taki barina na tafi, zubaida ta mike bana son sharri sadeeq, ta nufi cikin gidan ina zuwa 2mins...

Neena tadan zauna a kujerar da zuby ta tashi tace yaya kayi dacen mata fa...

Sadeeq yace itama tayi dacen miji ba...

Neena ta kwashe da dariya...

Dai dai lokacin prince ya shigo gidan tare da wani frnd dinsa mahmood..

Hango neena yayi zaune da wani sai washe baki takeyi tana dariya....

Neena tace yauwa yaya muga wayar ka, ta kai hannu jikin sadeeq....

Prince ya fusata sosai...

Tana daukar wayar tayi selfie, yaya ka nunawa umma wannan, sai nazo mata yawo gobe...ta mike tsaye, ta mikawa ya sadeeq  hannu daman sun saba shaking hands abunsu...

Ya Sadeeq ya mika mata nasa shima...

Prince bai ma san lokacin daya karasa wurin su ba, yana lumfashi kamar wani zakiii...

    Wace _wat d well r u doing_

.

Neena da ya sadeeq sukayi saurin kallon shi, prince ya karaso wurin su, ya nuna sadeeq, kai kuma daga inaa?

Neena tace ya prince , yayana ne fa..

Prince ya kalle sadeeq, sai lokacin ya lura da kamarsu da neena harta baci.

Dai dai nan zuby ta karaso tana cewa, ke neena yayaB nacan na jiran ki fa..

    Neena tayi saurin wucewa tana cewa, oh God na manta ma wallahi..

   Zuby ta kalli prince dake tsaye, fuskar nan a tamke, tace ya prince ga yayan neena ku gaisa..

     ya sadeeq yayi murmushi, ya mika masa hannu, prince yadan sake kadan ya basa hannu suka gaisa, sannan yaja abokinsa suka shige ciki..

    Sadeeq ya kalli zuby, yace, ya prince dinku amma soja ne ko? Zuby tace lah ya akayi a gane?

  Sadeeq yayi dariya, kowa ya ganshi zai gane ai...

   Amma akwai wani abu tsakanin su da neena ne?

    Zubaida tace babu komai, amma nima na taba zargin nan, sadeeq ya kada kai kawai, amma kuwa yaga kishin neena karara a idon prince.

   Sadeeq har dare yakai, suna tare da faruk , sai fira sukeyi, an kawo masa baby ya gani, ya kuma bawa deeja abun arziki.

Washe gari tunda safe neena ta shirya dan zuwa wurin umman ta.

    Ta samu dad da mum da zuby tare da amir a dinning,  ta duka ta gaishe su, dad yace har an gama shirin ne neena..

    Neena tayi murmushi ,eh na gama dad, mum tace saboda zangin ganin umma ko breakfast baza'ayi ba kenan.

    Neena dake shafa kan amir, tayi murmushi, dad ya kalli mum, ya maganar da mukayi da yayaB jiya..kin sanar mata kuwa?

   Mum tace aff na manta ma wallahi, neena zo nan ki zauna, mum ta nuna mata kujerar dake kusa data zuby..

    Neena ta kalli mum da sauri, zuby ta jawo hannunta, zauna mana ke kuma, neena dai sai binsu takeyi da ido, mum tace, daga yau _kin tashi daga nana_ din amir, daga yau kin zama yar mu..

     Neena ta saki da ido da baki da hanci...ta nuna  kanta, niiiii..

   Dad yayi dariya yace kwarai kuwa, mami da abbanku sunyi sunyi mu basu ke, hakama yayaB, amma sai nayi musu shigar sauri...

  Jiya naje wurin umman ku, munyi magana sosai da ita, tace ita kam ta bamu ke halak malak, dan halaccin da muka mata,

    Neena da hawaye suka fara zuba daga idon ta, tace mun gode kwarai da taimakon da kuke mana, bamu hada komai daku ba, amma kuma kun dauke mu a matsayin yan uwan ku, kowa na kirana *Yayan Talakawa*  da b'asan asalin su  amma...ku...kuka ya kufce mata, zuby ta rungumo ta tana lallashin ta, mum tace is ok my daughter, komai ya wuce yanzu, dad yace zubaida, jeki kira zarah kuzo kuje, kuyi mata shopping ko?, mum tayi murmushi, yau za'a kawo gadonsu ma, sai a gyara musu dakin zuby , tunda yafi girma, zuby ta rike hannun neena, tashi muje daga can sai muje mu gaida umman ko...

.

Sunje sunsha shopping sosai, duk wanda ya gansu sai sun burge shi, dan sai ka rantse da Allah yan gida daya ne..sun fito daga supermarket din kenan, neena taci karo da wani sausari, yaci gayun sa cikin suit mai tsadar gaske, kayan hannun ta duka suka zube...

    Zuby tace malam baka gani ne ko mai?

  Neena ta tsaida zuby, anty zuby ba laifin sa bane shi daya, harda ni daban kalli gabana ba, saurayin ya kalli neena, yayi murmushi, maganar da tayi yasa yaji ta kwanta masa,   ya duka zai kwashe mata kayan, neena ta duka itama, noo ka barshi pls. Zan kwashe...

    Ya dago kansa ya kalle ta, itama lokacin ta kalle shi...

Guy din ya hadu gaskiya, yayi mata smiling,  yace no I have too...

   Tare suka kwashe kayan, ya mika mata , ta amsa tace thanks, suka tafi wurin motar su..

   Har zata bude ta shiga, saurayin nan ya dawo da sauri..

   Amm pls ya sunanki? Neena uwar saukin kai, tace neenah,yayi murmushi, sunana naseer, pls zan iya samun num dinki?

   Neena tace I dnt hv a sim tukun, zarah ta leko, tace neena shiga mana muje, neena ta bude ta shige abunta...shi kuwa saurayi ya bita da kallo...

Sun kusa isa gidan umma, zuby dake driving ta kalli side mirror , tace, wannan guy dinfa mu yake bi..

Zarah tayi dariya, ai naga alamar sis din tamu ta tafi da zuciyarsa, neena tayi murmushi, ni ba ruwana anty zarah...zuby tayi dariya, guy din ba laifi hes cute...neena ta rufe kunnen ta, nidai ba ruwana am nt even present here.....

Sun iso gidan umma, suka gaishe ta, sannnan suka shiga fira sosai, neena tace ina yaya sadeeq? Umma tace yaje wurin saka furnitures din sabon gidan sa, neena ta ware ido, sabon gida? Yaushe ya gina? Umma tace tun yana jordan aka fara,Ginin , neena ta kwanta jikin umma, shine ni ba'a ko fada min ba, umma ta shafa kanta, aike yanzu ba yar nan gidan bace ba, na bawa mum, neena ta shagwabe fuska kai umma, ni gida biyu gareni fa, kuma iyaye biyu kin ga ni yar baiwa ce..yanzu koh?...

  Aka kwashe da dariya. .

  Sai yamma suka bar gidan, har lokacin naseer na biye dasu...

.

Suna isa gida, yayi parking shima, ya shigo compound din gidan, su zuby da zarah suka kwashi kaya sukayi ciki...

  Neena tazo daukar ragowar, taji an mata sallama, ta amsa ta kalle shi, mai yasa kake ta bin mu ne?

Lafiya dai ko? 

Naseer yayi murmushi. .

Eh lafiya dai ba lafiya ba.

Neena ta gyara tsayuwarta, ban gane lafiya ba lafiya ba..

   Naseer yace, tun haduwar mu dazun, naji kin kwanta min, can be frnds pls?

  Neena ta tabe baki, duk wani namiji baya burge ta, prince dinta kawai ke burgeta...

   

Prince ya fito kenan daga gymnasium (dakin motsa jiki) ya hango neena tsaye da wani, yaja tsaki, wannan yarinyar wai meyasa bataji ne uhm, wani haushi yaji kamar yaje ya shake naseer...

     Neena nacikin tunanin nan, ta kyallo prince, tsaye bakin kofar gymnasium, tace a zuciyarta, sai shegen girman kai, ai kuwa zan maganin ka...

   Ta sakar wa naseer murmushi, hmm ba damuwa, amma nifa har yanzu secondary school nake, naseer ya washe baki, noo ba damuwa ai, neena tace okay yanzu zan shiga ciki, nasan sisters dina nacan na jirana..

  Naseer yace ok sai gobe ko, ya daga mata hannun, neena ta daga masa itama, sannan ta kwashi kayanta tayi ciki...tana shiga falo ta kwashe da dariya...dan yadda taga yanayin fuskat prince, yayaB da amir dake kallo a falon suka kura mata ido, sai dariya take kamar zararriya...

    Tana juyowa taga ita suke kallo, ta hadiye dariyar ta haura sama.

   YayaB ta kalli amir, shima ya kalle ta, suka tabe baki sukaci gaba da kallon su...

   

.

Prince yayi tsaki, mtsw mai yasa na kasa share sha'anin yarinyar nan ne? Ya dunkule hannun sa ya naushi dayan...sannan ya yafa karamin towel dinshi a kafada ya nufi cikin gidan.

An gyara dakin zuby sosai, gadaje biyu ne yanzu, masu kyan gaske, sannan an sake musu closet (wurin ajiye kaya) zuwa babba, dakin gwanin sha'awa, dai dai na yan'mata.

Washe gari akayi liyafar suna, an saka wa baby suna, fatima (sunan mami) bt zasu ringa kiran ta intesar.

Da daddaren ranar ana falo gaba daya, mum, dad, mami, yayaB, zuby, zarah, faruk, deeja da babyn ta intee, sai neena da amir dake zaune a kasan carpet tana koya masa homework, prince ne kawai baya nan, yaje shopping din kayan coffee dinshi .

Inna ladi ta shigo falon, tace sannun ku da fira, abba yace yauwa sannu inna ladi, dad yace inna ladi sai kije kema kiyi hutu gobe da jibi ko, inna ladi ta washe baki, ai kuwa na gode sosai, mum tace lafiya dai ko inna ladi? Ko naman har yayi ne?

   Inna ladi tace, uhm uhm , yama yake da suna, hamza mai bawa fulawoyi ruwa, yazo yace nayi wa niimatu, magana wai ko tana da bako,neena ta dafe kirji, inna ladi ni kuwa, kodai sis zarah?

    Inna ladi ta soshi kanta, a'a ke yace niimatu..

   mami tace, tashi dai kije ki gani, neena ta mike a kunyace ta fita, dan dama da hijabi a jikin ta...

   Zuby tace , sisi kodai wannan guy dinne na supermarket jiya?

   Zarah tayi dariya, ai kuwa dai mayb shine, yayaB tace toh sarakan gulma, faruk yace aikin su kenan.

.

Neena na fita, ta fara yan dube dube, tana tsaki, yanzu haka wannan naseer dinne..

Ai kuwa sai gashi ya karaso dauke da murmushi..

   Neena tayi dan murmushin yake, ina wuni?

  Naseer yace lafiya cutie, ya kike ya daren..?

  Neena tadan gyara tsayuwarta lafiya yau, naseer yace ya sisters dinnan naki fa?

  Neena tace suna lafiya lau, naseer zai yi magana motar prince ta shigo compound din..

   Neena na ganin shine, tace great, mr girman kai ya dawo, ta saki murmushi, tace wa naseer, ammm kai daga wane state ne?

   Naseer yayi murmushi, ni dan yola ne, amma a nan nake aiki...

Neena ta sake murmusawa, lokacin prince ya fito mota dauke da leda..

    Ya wani watsa musu harara, gaba daya ya neme calmness dinsa ya rasa..

   Wani abu ya tsaya masa wuya, ji yadda take wani washe wa banzan cen baki...mtsww I hav to do something really. ...

Ya karaso wurin su, a fusace ya kalli naseer, kai kada na sake ganin ka a gidan okay????

Neena zatayi magana ya fisgo hannunta da karfi.....

  Ya nufi cikin gidan da ita...

  A bakin kofa ya tsaya yana sauke lumfashi sama sama...

  Ya jawo ta ya hada da bangoo..

Duk wannan abun bai ma lura da mutane a falon ba...

Kishi ya rufe masa idoo..

     Ya nuna ta da yasta...kee mai saya bakya jine uhm..

  Nasani tun ba yau ba, kina sona...

  girman kanki da yanga ya hana ki fada....

   Neena ta ware ido,

Ta tabe baki, ni bana sonka, prince ya kasa controlling din kansa, dan yadda yaji kalmar ta rasta zuciyarsa, _bana sonka_ bai san lokacin da ya wanka mata mari ba....

Dad da abba suka hada baki wurin cewa, prince!!! Lafiyarka..

  Prince ya juyo fuskar nan tayi jaaa, an bata zuciyar maza...

YayaB tace kajimin yaro, mai ta maka zaka mare ta uhm.?

   Prince yace iske ta nayi tana fira a wajee..har kamar ta duka nawa take..?

   Dad yace idan batayi fira ba, ita zata auri kanta..?

    YayaB tace atooh, dan kuwa neena tare dasu zuby zamu hadata muyi mata auree....

    Prince ya juyo da sauri ya kalli yayaB idon shi kamar zai zazzago....

Yace ba wanda ya isa ya aure neena, *nine nan mijin ta*ya nuna kansa....

Haha (maza kenan)

.

Gaba daya suka ware ido suna kallon prince..

   Neena kuwa kafafunta kasa daukarta sukayi..

   Sulale wa tayi kasa ta zauna gwajab, bata taba tunanin prince zai iya furta sonta a gaban kowa ba...

YayaB tace kaji min yaro, hausawa fa sunce mace allura ce a cikin ruwa, mai rabu ka dauka..

   Dad ya kalli abba, sukayi murmushi, sannan suka fice zuwa falon dad..

  Mum da mami, suka zo wurin prince, na'im kwantar da hankalinka, prince ya kalle su kawai ya haura sama, yana kallon yayaB..

   YayaB tayi tsaki, ni bari kallona..

  Zuby da zarah harma da faruk, duka mamaki sukeyi, prince ke son neena?, kuma baiji kunyar kowa ba ya fada...

   Deeja tace, ya prince manya, sannan ta kalli neena dake zaune bakin kofa..

  Neena tashi mana, neena ta mike da kyal, tazo zata haura sama, yayaB tace munafuka, harda wani cewa bata son shi, ranar nan fa na taba hango su suna fira a waje...

   Zuby tace nima haka na taba ganin su...

  Faruk yace haka nima..

  Zarah tace tab ashe ni kadai aka bari a duhu....

  Suka kwashe da dariya dukkan su...

Sa safe abba da dad, tare da yayaB suka zauna meeting, mum da mami suka shigo tare da umma, da suka dauko dan tattauna maganar...

Umma na shiga falon idon ta ya sauka akan yayaB, dake zaune tana shan tea...

     Umma ta ware ido, tana ja baya...

Mum ta rike ta, lafiya Aisha??

Lokacin yayaB ta kallo bakin kofar, suka hada ido da ummma.....

Ta mike da sauri, har tea din da ta rike ya rubar mata a jiki, amma bata damu ba...

    Ta nuna umma, aisha! Aisha! Kece nake gani ko kuwa gizo kike mini.....

Umma ta saki kuka, ta karaso wurin yayaB ta duka a kasa, tana kuka tana cewa, ki yafe ni goggo, ki yafe ni.....

     YayaB tayi saurin dukawa kusa da umma...

  Aisha tashi tashi, ba lokacin kuka bane, kuma nice zan nemi gafarar ki...

   Ki yafe ni , kuma ki yafe wa almustafa..

  Umma ta kalli yayaB tana zubar da hawaye...goggo ina almustafa? YayaB taja lumfashi ta dauke ido daga kallon umma, tace, almustafa yana kasar Italy,ni kaina rabun dana kansa shekaru wurin ishirin kenan....

Dad da abba, mum da mami sai kallon ikon Allah sukeyi, dad yace yayaB dama kinsan umman neena?...

YayaB ta mike da sauri, ta nuna umma, aisha ce umman neena daman....

Abba yace kwarai kuwa, itace...

Dad yace, ya akayi umman neena tasan yaya almustafa? 

    YayaB ta zauna tace, bazaku shaida aisha ba, dan lokacin da almustafa ya auri aisha, kuna kasar Egypt. ..

   

,

Almustafa ya hadu da aisha ne, a garin kano, lokacin daya je wani aiki acan..

  Yaso ta sosai, yazo yake bani labarin ta, marainiyace, wanda kawunta ke rikon ta, amma kuma matansa ke azabtar da ita..

    Na tausaya wa aisha tun kafin na ganta..

   Almustafa yace yana son ya aure ta, dan ya taimaka wa rayuwarta..

  Nace masa nima na amince.

   Bayan wata daya, na tura kawu ku maringayi isma'ila.

   Sukaje akayi komai, bayan sati daya aka dauro aure , aka taho da aisha.

  Bayan ansha fama da matan kawun nata.

   Sun zauna cikin kwanciyar hankali, kullum aisha cikin kyautata mana takeyi..

   Saboda ita, rayuwar mu ta samu kyakkyawan canji..

   Har Allah ya bata ciki, ta haihu abubakar, munyi farin ciki sosai.

   Almustafa kuwa ba wanda yakai sa farin ciki, bayan wasu shekaru..

   Ya samu karin girma, kuma aka mayar dashi lagos..

  Yayi yayi aisha ta bisa taki, dan bata son nayi zaman kadaici...

   Tofah tunda yaje lagos, sai yayi watanni shida har bakwai bai zo ba...

  A haka muke ta zaman mu, duk da aisha bata nuna tashin hankalinta ba, ni na gane yarinyar na cikin damuwa kwarai...

   Ranar da almustafa yazo, nayi masa maganar, ya tafi da aisha nizan dauko yarinya daga kauye mu zauna tare..

  Sai ya hau bala'i da masifa...

    Toh fa tunda ya koma lagod dinnan, bai dawo sai bayan shekara, hankalina a tashe, dan ganin da wata bayarrabiya da nayi...

    Yace mana matar sa ce, hankalinmu ya tashi, take ma aisha ta fadi a sume...

    Baiko damu ba, nice nan na rika mutane aka kaita asibiti, likita yace ai tana da shigar ciki...

   Mun dawo da farin ciki dan sanar wa almustafa, sai iske takarda mukayi...

    Ya tafi kasar Italy aiki, kuma ya saki aisha saki biyu....

     Hankalinmu ba karamin tashi yayi ba, gashi duk bakwa nan a lokacin, cikin satin isma'ila ya rasu..

    Na tafi kauye zaman makoki, dawowar dazanyi na iske wata takardar, aisha tabar min..

   Wai ta tafi......kuka yaci karfin yayaB...

   Umma ta ta shiga rera nata....

  Mum da mami suka shiga lallashin su...

   Neena da zuby da zarah dake bakin kofa , sunzo fadawa iyayen su zasu saloon, suka iske yayaB na bada wannan labarin...

.

Kuka sosai suka sha, su abba da dad ma dan goge hawaye....

Prince da faruk ne suka shigo..

  Suka iske falon duk anyi jigum, neena na jikin umma tana kuka...

YayaB tace komai ya wuce yanzu, duniya zata koya masa hankaliii....

  Umma tayi saurin cewa a'a goggo kada kiyiwa almustafa baki...

    Dad da abba sukace, zamu nemo yaya inshaAllah...

  Amma yanzu, umma da sadeeq zasu dawo nan gidan da zama, abba yace kwarai kuwa, har sai mun nemo yaya, sannan asan abunyi...

YayaB tace sai muyi maganar data kawo mu koh..

Dad yace ku kuma sai kuzo ku zauna ko, kukayiwa mutane tsaye..

   Prince da faruk suka karaso ciki...

   Abba yayiwa umma bayani...

    Zatayi magana, sadeeq yayi sallama ya shigo...

  YayaB ta mike da sauri, fuskar sadeeq ba karamin tuna mata da almustafa tayi ba..

  Tazo ta rungume sa...

Sadeeq ya tsaya kamar status. .

   

An zauna, dad ya sake bawa yaran labarin da yayaB ta basu..

   Kowa ya tausaya wa umma...

  Umma tace komai ya riga ya wuce,  ni kuma na yarda *na bawa na'im ,neena har abada*....

   .

*Bayan wata biyu*

.

Neena ta kammala exams dinta, zarah ta fito da wani saurayinta, mai suna Yusuf, yana aiki a banki,  sadeeq  da faruk ke tafiyar da aikin company dinsu dad da abba.prince na bakin aikin sa a lagos, kullum suna busy.

Yau ana gobe daurin aure....

  Prince ya shigo garin, direct family house ya  wuce anan ya samu su faruk da sadeeq, da abokinsa mahmood.

Mum da mami, sun dage wurin gyara yaran nasu.

   YayaB da umma ma sun dawo gidan, sai kuma bayan biki su koma.

   Kullum cikin hidima suke.

  .

Neena, zuby, da zarah anbar musu sashen mami, da kawayen su, kawar neena daya mai suna batool.

     Mum ce ta shigo dakin da suke, tace wai ko maiyasa bakwa jine uhm, wannan maganin tun yaushe mamin ku ta kawo shi.

    Zarah tace nidai nasha nawa mum ta haye kan bed abunta, neena tayi saurin boyewa bayan wata suhaila kawar zuby, zuby tace nima nasha nawa I think neena ce bata ba....

     Mum ta shiga neman neena, ina neena take, daman nasan sai ita ai...

    Neena ta mike da sauri zata fice, mum ta cafko ta, dawo nan sai kinsha shi..yarinya kamar shazumami..komai sai da zaki zata sha shi.

   Mum ta mikawa neena , neena ta wani kuntse fuska, tana sha kamar zatayi amai, har sai data shanye, mum tace ko ke fa...

Prince suna zaune a falo, sadeeq yace wa abokinsa, bari na kira mrs sadeeq,duk  yau bamuyi magana ba, I fill like seeing ha ryt nw wlh, abokin yayi dariya, yace nawawo dis  kind of love...

     Faruk yace, ai yayaB ta kwafsa muku wallah, bikin mutane uku, amma bako dan party...

   Mahmood abokin prince, yace, ai kakus din taku, da gani malamace..

  Prince yayi tsaki, yayaB ko rigima, bakuji yadda take bala'i ba..

  Wai nace inason aure amma, naki zuwa, wai sai ta hana auren...ma

   Aka kwashe da dariya...

Faruk yace ai kaine yaya, bafa wanda yayi tsanmanin kanason neena...

Ni nan da da ita zanyi second wallahi..

   Prince ya wurga masa harara...

  Faruk yayi dariya, amma seriously speaking, neena will b a good wife, she will be far better than,  *LATEEFA*......prince yayi saurin kallo faruk..

  Mahmood yace harka tuna min, na hadu da lateefa ma a turkey,  ta dame ni da tambayar ina prince ina prince, u knw I hated dat bitch, tace mata aure ma zakayi..

Prince ya mike a fusace ya saura sama abunsa..

  Sadeeq yace, wacece lateefa???

Faruk yace lateefa matar ya prince ce, amma fa ex-wife dinsa.....

.

Washe gari dubun nan jama'a suka shaida daurin auren *NA'IM NAFI'U alkali  AND NIEMA ALMUSTAFA*

         SAI

_ZUBAIDA NAFI'U alkali AND ABUBAKAR ALMUSTAFA_

          *DEN*

_ZARA'U SA'EED  alkali AND YUSUF ASHAFA_

Bikin daya tara mutane, masu  kudi , , masarauta da ma  yan kasuwa..

Karfe bakwai aka fara daukan amaren...

  Neena zata zauna a gidan prince na abuja..wanda ke maitama.

    Zarah zata zauna gidan yusuf dake gwarinfa.

   Sai zuby da zata zauna a wuse 2 gidan angon ta sadeeq.

Alhamdulillahi, ankai amaren lafiya, mum da mami sai da suka rubar da hawaye, zasuyi missing lovely daughters dinsu, yayaB da umma ma sun dan share nasu hawayen.

.

An kai neena dakinta, basu taho da amir ba, sai bayan kwana biyu mum tace za'a kawo shi.

Neena tunda kowa ya tafi aka barta ita daya, gaban ta nata faduwa, tana nan zaune shiru, taji an bude kofar dakin.

   Bugun gabanta ya karu..

Tana jin kamshin turaren ta gane prince ne..

  Ya zauna kusa da ita, ya sa hannunsa ya riko nata hannun, dayaji hennan lalle mai kyaun gaske..

   Neena ta sauke lumfashi...

Prince ya shiga murza yan yatsun ta, yana cewa, at last sai da kika mallake ni ko?

     Neena dake cikin mayafi, tadan kalle shi, sai data mallake sa?mai yake nufi..?

   Prince ya dago kai, suka hada ido...

  Ya dan daure fuska, eh mana, nasan kin dade kina addu'ar Allah ya mallaka miki ni....

  Neena ta turo baki..

Prince ya yaye mayafin, yace , ki kara turo min bakin nan ki gani.

   Neena ta juyar da kanta, prince yayi murmushi, anyways,  tunda kin same ni, ni zanyi dan maneji dake...

   Neena ta tsoke baki, tace , kai fa da bakinka kace wa yayab ranar"ba wanda ya isa _ya auri neena  saini_ ta kwaikwayi yadda yayi maganar...

Prince ya kwashe da dariya...

Neena ta juyo tana kallon shi cike da mamaki, dariya har yana faduwa..

   Ya mike ya zauna yace, ni din nan nace haka?

  Neena ta kada kai eh man..

  Prince yace no way, wazai soki, ni ya nuna kansa, god forbid. ...

    Neena ta sauko daga gadon, ta rike kugu tana kallon shi, tadan harare shi, tayi hanyar fita daga dakin...

     Prince ya mike shima, dawo kisha barcin ki yarinya, ni dakina zani...

   Neena ta juyo ta kalle shi, yace taga dan handsome ta makale, ta kara bata fuska kamar zatayi kuka...

   Prince ya fice yana mata dariya...

  Yana zuwa dakin sa, ya fada kan bed, she look much cuter idan tana fushi...yayi mirmushi, I wont force ha..amma for sure after shekara daya, by den mun shaku sosai, *I will make her mine*...

Yayi dariya ya murgina ya jawo wayar sa, pic dinda ya dauke ta dazun nan ne, lokacin daya shigo dakin, bata lura ba cos tana kallon kasa..

   Yayi kissing wayar ya furta *I LOVE U MY NEENS* - 

Bayan kwana biyu, kullum prince cikin tsokanar neena yake, har abun ya fara koleta, ta kira mum tace a kawo mata ameer yau dan Allah.
Prince na falo a zaune, yana amsa wayar gadon shi, amir ya shigo da gudu cikin falon, yana kiran papa! Papa!...
Prince ya saki baki, yanzun nan yake da niyyar tashi yaje ya dauko shi.
    Inna ladi ce ta shiga falon itam..
   Neena dake daki, tana duba last question pepper din da sukayi, taji karar amir..
   Da gudu ta fito daga dakin..
Tace da karfi, my little. ...!
Amir ya saki papa dinsa, yayi gurin ta da gudu yana dariya..
   Inna ladi tace, a'a gida masha Allah, Allah ya kawo zuri'a tayyaba..
  Prince ya kallo neena, yaga ko a jikinta, tace inna ladi zauna mana na kawo miki juice. ..
  Inna ladi tace a'a barshi, gadai abincin ku na dare nan...inji mamin ku..
  Neena ta amsa basket din tace mun gode, ki gaida min su..
Da daddare, prince yaji su neena shiru, da kamar yanzu tana fitowa kallon wani series, amma yanzu yaji ta shiru..
   Ya mike ya nufi dakin ta...
Yana bude kofa, neena na tullo pillow, pilon ya buge masa fuska..
   Yadan daure fuska, miye haka kukeyi?
  Amir yace, wasa muke papa, ai grany mami tace yanzu anty ta zama momma dina, shine muke celebrating. ..
Prince karaso cikin dakin, yazo dai dai wurin neena, yasa hannun yaja mata kunne kadan...
  Babba dake kike biye wa amir ko, ji yadda koka yamutsa dakin...
   Neena tayi yar kara kadan, zan gyara ai...
  Prince ya saki kunnen ya fice...
  Amir daya kura musu ido yace, a zuciyarsa.
I wil make momma n papa, friends. .ya kalli neena yaga tana luliya kunnen ta...
    Ya turo baki, momma na jin zafi kuma papa ne ya jawo...
  Yazo wurin ta, yaja hannunta, ya zaunar da ita a gado, ya hawo gadon yazo yana luliya mata kunnen, neena taji son yaron ya karu a zuciyarta..ta jawo sa jikin ta, ta rungume shi...tace I will always be wit u my little.
Da sassafe, sunday, amir ya riga su tashi, yaje ya hawo kujera ya bude kofar baya, ya dauki leda, yaje ya samo kyankyaso guda biyu, dama yasan neena da tsoron kyankyaso...
Ya dawo cikin gidan ya shiga toilet, dinta ya ajiye kyankyasan a wurin da take ajiye brush da sabulu..
    Ya dawo dakin prince ya kwanta dama acan ya kwana...
Neena ta tashi, tace ohh God, nayi latti yau, ta mike, daga ita sai singlet da wando iya cinya, kanta duk ya barbaje saboda barci...
       Amir ya bubbuga prince, papa papa! Prince ya mike yace miye ne?
Amir yace zanyi brush, prince yace kaje toilet kayi mana, amir yace brush dina na dakin momma..
  Prince ya mike yana cewa, ka cika rigima wallahi...
Ya nufi dakin neena, dama kusa ne da nashi..
.
Neena kuwa na shiga toilet, ta kwabe kayan jikin ta, dama ita first thing da takeyi da safe, tayi brush tayi wanka...
   Tana gama daura towel, ta nufi wurin ajiye brush, tazo dauka, taga wasu kyankyaso a ta wurin suna yawo...
   Ta saki kara...wayyo Allah na.....da karfi tayo waje..
Dai dai nan prince ya shigo dakin...
  Tayi wurinsa tana nuna toilet din...
  Prince ya ce miye ke kuma?
  Neena ta kankame shi tana nuna toilet, akwai akwai uhm kyankyaso a ciki wlh...
    Prince din yadda take kamkamesa, duk sai yaji wani yarrrr, da kyal ya iya saita kansa...
   Ya banbarota, ya rike ta..
  Is ok, bari na cire...
  Ya shiga toilet din, ya dauko su guda biyun..
   Yaje ya yarda ta window..
Neena na nan tsaye...ya dawo yace ki shiga kiyi wankanki na cire...
   Ta make kafada, ni bazan shiga toilet dincan ba yau...
Prince ya wani kura wa surar ta ido...
  Yadda taga yana wani kallon ta, up n down..
  Ta kalli jikinta, da sauri...
Tana ganin towel ne kawai ko cinyarta bai rufe duka ba..
  Ta ware ido ta kalli prince..
Tace miye kake ta kallo nahaka, tayi saurin jawo hijab dinta dake saman sofa, ta rufe jikin ta..
Ranar dai a toilet din prince tayi wankan.
Washegari, amir da neena na falo suna breakfast. .
Prince ya sauko shima,
  Ya zauna, ya shiga zuba abincin yana ci..
  Amir ya kalli neena ya juyo kuma ya kalli prince..
Ya mike yace after breakfast lets pay a game..
  Prince yace noo..
Amir ya turo baki pls pls, neena tace zamuyi little dont worry..
Prince ya kalli neena zamuyi? "Zamu" meaning?  Ta amsa dani kenan.
    Amir ya hau murna..
Suna gama cin abincin..
  Aka shigo falo, amir yace momma n papa group dinku daya..ni ne zan nemo ku..
  Ya rufe idon shi.
Ku boye kafin nayi counting 10.
Prince da neena sukayi wani tsaye...
  Sai jin amir sukayi yana fara kirgawa abunsa..
   Har yakai 5...6....7....
  Yana kokarin cewa 8..
Suka bazu neman wurin boya...
  Neena ta boye a bayan table, taga dai zai ganta ta mike..
Prince ya boye bayan kujera yaga dai nan ma za'a ganshii..
Suka mike a tare suka kalli juna..
  A tare idea din boyewa karkashin dinning table yazo musu. ..
   Amir na 9.....sukayi gudu da sauri suke shige karkashin table din..
Dai dai amir ya tsaya...
Prince da neena suka kurawa juna idoo..
Prince yace a hankali, meyasa kika biyo ni nan?
Neena tace, na tuna dana boye a karkashin table din garden, dad bai ganmu ba..
    Prince zai yi magana, ya hango jelar gyelen neena yadan fita waje, amir zai iya gane suna wajen...
   Yayi saurin jawota, ta matse dashi sosai, har bugun zuciyarsu suna ji...
     Prince ya dago fuskarta, yana kallon cikin idonta...ya fara matsowa da fuskarsa kusa da nata...
  Yazo dab da fuskarta sosai, har lumfashin su na cin karu dana juna...
  Ya kai lips dinsa kan nata..
Da sauri ta runtse idonta...
  Prince yayi kissing din ta....
Neena taji duk jijiyoyin jikinta sunyi sanyi, kirjinta kuwa sai bugawa yake..
_Dis is my first kiss_.......
Amir ya gansu da dadewa, amma bai musu magana ba, sai ma komawa yayi falon ya saka cartoon dinshi yana kallo..
Karar TV din ta dawo da su daga duniyar da suka lula...
   Neena tayi saurin matsawa ta fito..
Haka shima prince....kasa yiwa amir  magana sukayi ma...suka koma dakinsu.
Da daddaren ranar, amir yana ta kalon prince, yana aiki a computer, harya gama amir na nan na game..
   Ya cire kayansa, ya  shige toilet,  amir yayi murmushi, I took away his towel, ya dauko towel din daga under pillow ya ajiye kan bed din..
Dama yasan papa dinsa, idan yayi wanka to towel yake kasawa ya fito..
Baya iya maida kayan daya cire....
Amir na nan zaune, prince yace daga toilet. ..
  Amir.... miko min towel dina, I forgot na shiga dashi...
Amir ya mike da gudu..
Ya fita zuwa dakin neena.
Ya iske ta suna waya da zuby..
Yace momma, papa yace kije yana kira..
Neena tadan hade yawo, ta mike ta fita..
Tana shiga taji yana kiran amir...
Give my towel son, jin amir ya masa shiru, yaja tsaki, mayb ma yayi ficewar sa...
  Ya bude kofar toilet din....
  Ya fito....daga shi sai wandon ciki..
   Neena najin bude kofar ta kalli wurin
Sai ganin prince tayi ba kaya...
  Ta saki ihuuu...
Tayi saurin rufe idon ta..
Ta juya zata gudu...
  Amir dake tsaye wurin kofar, ya kulle da sauri ya saka key...
Yayi murmushi, momma da papa, sai kun shirya zan bude ku...I saw it in a cartoon, d bad guy n good guy, an kulle su a wuri daya, kafin gobe suka zama gud friends. ..yayi murmushi ya wuce dakin neena yaci gaba da game..
.
Neena jin kofar a rufe..ta tsaya ta kasa juyowa.
Prince yace waya ce ki shigo dama..
   Neena tace bakai ka kira ni ba..
  Prince na saka kaya yace , ni ban kira ki ba..kice dai kinzo wurin mijin ki kawai...
  Neena ta runtse ido...
Ni ka bude min na fita..
Prince na gama saka kayan barcin sa..
Ya tako wurin ta...
Yazo ya sagala hannun sa a kugun ta..
  Ta ware ido da sauri..
  Prince ya kwantar da kansa a kafadarta..
  Naso da , na barki sai nan da one yr, amma tunda kika kawo kanki I cant help it....
  Neena tayi saurin cewa, ni ban kawo kaina ba..kai fa ka kira ni...jikinta na rawa..
    Prince ya juyo da ita, ya daura yatsan sa a lips dinta...
Shiiiiiiish....
   Kada ki damu, it wont hurt dat much....
  Neena ta kware baki, wayyo ya prince..., ni wlh bani na kawo kaina ba, ka barni na tafi pls, naji one yr din yayi......
Prince yayi dariya....ya sauke ajiye zuciya, ya shafi hancinsa...
   One year, let me see 🤔....neena ta kura masa ido tana jira taji mai zai ce...
Ya kalle ta, na fasa ma gaskiya. ..I need a baby...amir kuma kani zamu basa..or maybe kanwa ko? Nasan ku mata akwai son baby gal..
Neena ta sake kware baki, wayyooo ya...kafin ta karasa..prince ya jawo ta, ya hada bakin sa da nata....
    Neena sai mutsu mutsu takeyi...
    Prince ya rungume ta tsam a kirjinsa.....
  Ya rada mata a kunnen ta...
*I love u so very much my neens*  
I know kema kina sona koh? Yayi saurin tasowa ya kura mata ido...
  Neena ta kasa furta komai, dan harshen ta dayayi mata nauyi, prince yace idan baki amsa ni ba, I will...ya matso da bakin sa..kiss u...
  Da sauri tace _I love u too_
Prince yayi dariya..I know  ai ya shafi fuskar ta tunda am gud looking. ...neena ta turo baki, wasa nake nima, I dont.....
  Bata karasa ba taji bakin prince a kan nata...
    A nan ya dauke abarsa, ina ganin ya ajiyeta a kan makeken gadon sa...
     Nace abun yazo fa
Make I find my way. ..
    .
Da asuba ya taimaka mata, tayi wanka tayi sallah, ya bata magani tasha, sannan suka koma barcin su, prince gaba daya yana cikin farin ciki.
Karfe 8 ya farka, yayi wanka ya zauna amsa wayar general.
Harya gama neena bata tashi ba..
Ya dawo ya zauna wurin ta yana kallon kyakkyawar fuskarta.
Ya kai bakin sa goshin ta..
Ya sumbace ta..
    A nan yaga idonta sai rawa yakeyi...
Kamar dai idan mutum na barcin karya...
Yayi dariya...
   Ki bude idon ma na gano ki..
Neena ta sake runtse idon ta ja blanket ta rufe kanta a ciki...
Har mintina sha takwai  neena na cikin blanket, taki fitowa..prince ya rike kugun sa, mrs Na'im alkali, get up nw...or else. ...kema kin sani, second round....bai gama maganar ba.
  Neena tayi saurin ture barkon...ta fito....ta shagwabe fuskarta....ya prince wallahi bana soo...
    Prince ya kwashe da dariya...oh really....ya haye saman gadon shima..
   Mrs Na'im alkali, na zata ke jaruma ce ai....but tunda rakguwa ce....zan nemo wata sweet hrt din...
    Ya daure fuska yana jawo wayarsa...dama akwai wata chick..data dame ni wai tana sona..let me call ha nace nayi accepting. .
.
Neena ta turo baki, nii nii taga dai da gaske  kiran zaiyi...ta hannu ta kwace wayar.....
  Prince yace bani wayata.!. Neena taki basa..
Prince ya shiga neman wayar a jikinta...
   Neena kara boye wayar tana cewa, ya prince Allah har nw inajin zafi stop it....prince yayi banza da ita...can ya fara mata cakulkuli....
  Ta fara kyalkyata dariya...
Amir na fitowa faga dakin neena..yaji muryarta tana dariya..
Yace yes" momma n papa sun zama frnds nw..
  Yaje ya saka key ya bude kofar dakin....
   Ganin su yayi suna wasan su a a saman gado...shima yaje da gudu ya haye...
  Yace papa...I will help u...ya shiga taya prince suna ta yiwa neena cakulkuli..tana ta dariya harda hawaye...
Bayan sati biyu, prince da neena sun shaku da juna, kullum suna manne da juna, amir baya takura su, cos mai lessons dinsa na zuwa.
Kullum tana waya dasu mum da mami, harma dasu  zuby da zarah, umma da yayaB suna kiranta suma...
Hankalinta a kwance, tare da mijinta da yaronta..
  Kullum cikin sata farin ciki suke..
  Yau suka shirya ziyarar zarah da zuby..
Sai da tayi ta rokonsa sannan ya amince zai kaisu..
.
Sun samu su zarah da yusuf lafiya, sai cin amarci akeyi..
Daga nan suka leka wurin zuby, tayi farin ciki sosai da ganin su...
  Neena sai tambayar yayan takeyi..zuby tace kedai ko wurin sa kikazo ba wurina ba...
Neena tayi dariya ta rungume zuby...wurin sis dina nazo.
  Sun shiga daki...zuby tace..ya yayan nawa ni, hope kuna zaune lafiya?
   Neena tace lafiya lau, ai duk yadda kuka dauki ya prince Allah ba haka yake ba, hes cool n.....zuby ta rufe mata baki, I knw I knw...
  Dama yanzu kina crazy inlove dinshi...ai bazaki fadi bad side dinsa ba...
Daga wurin zuby, amir yace, papa muje wurin baby intee, nagan ta, neena tace yes...pls...ta hade hannayen ta..
Prince yace like mother like daughter. ...
Yakai su gidan faruk, deeja taji dadin ganin su sosai...
  Neena na rike da intee sai wasa take mata..
Prince yadan karkato wurin ta..
Yace very soon
Zamu samu namu ko..neena tayi saurin kallon shi.
Ya kashe mata ido daya
Ta dauke kanta tana murmushi....
Bayan wata daya da auren su, results din neena sun fito ta samu grades masu kyau, prince ya koma bakin aikinsa, kullum sai sunyi yawa sau 20 or fi ma...
    Amir na mutukar kaunar ta, suna zuwa gaida mum da mami every Friday,  sannan suna zuwa gidan da sadeeq yabar wa su umma da yayaB..yana zama da zuby a gidan da company suka bashi...
Yau juma'a prince zai zo weekend. ...
  Neena ta shiga gyara gidan ta....
  Ta shiga dakinsa, ta shiga gyara sosai...
Dan ya jima baizo ba..
  Tazo wurin computer dinshi, books dinta ke wajen ta dauko, uhmm bari na maidasu a laka, tana dauka, wani picture ya fado daga cikin daya daga cikin books din..
  Ta duka tasa hannu ta dauka....
   Wata kyakkyawar mata ta gani...
  Ta dauka tana kallon matar, kamar ta taba ganin ta...
  Ta samu bed side ta zauna..
Ina ma na taba ganinta?
Ta kurawa pic din ido
Yes a kasuwar fruits dinmu..years back...
Matar nan data kirani *YAR talakawa* ya akayi pic dinta yazo nan?
Kuma wacece?
kuma ya akayi my prince charming ya samu pic dinta?.....
.
Tana juya bayan pic din taga an sa, *lateefa* ta mamaita sunan, lateefa???
Can a kasa falo taji sallamar zuby, amir na gaishe ta..
   Neena ta ajiye pic din a bed din prince ta fita.
    Da murna ta tari zuby..suka koma dakin ta, ta kawo wa zuby ruwa da juice ta ajiye mata..
    Zuby tace neena lafiya dai ko, naga fuskar ki kamar kina cikin damuwa...
    Neena ta zauna a bed gwajab, tace yaya zuby, nima bansan meke damuna ba, pic din wata na gani a dakin ya prince dazun, zuby tayi murmushi, kishi akeyi kenan, wacece ita? Neena tace bansan taba amma naga ansa lateefa a bayan pic din..
     Zuby tadan ware ido, lateefa?
Neena tayi saurin mikewa, kin san tane?
   Zuby tace dauko pic din na gani, neena ta mike ta koma ta daukowa zuby pic din..ta mika mata.
    Zuby ta kalli pic din tace, wannan itace....sai kuma wayarta tayi ringing, neena ta kasa sukuni, wacece wannan?
   Ta kagara zuby ta gama wayar..
Sai tada dan dade sannan ta ajiye wayar, tace yayanki na gaishe ki..
Neena tace ina amsawa, wacece wannan anty zuby?
     Amir ne ya shigo dakin, da gudu, yana cewa, momma I will be going to garden malam yazo..
  Neena tace ok my little, pls behave ur self kaji, amir ya kada kai ya fice..
 
Zuby tace _lateefa_ itace matar ya prince da suka rabu shekara da shekaru, lateefa itace mahaifiyar ameer...
     Gaban neena ya buga duuuum dumm, ta runtse idonta...tace tana raye daman?
  Zuby ta dafa neena tace *Eh tana raye* neena ta sulale kasa gwajab, ta dafa kanta, zuby ta sauko ta rungume ta, sis kada kisa damuwa a ranki, ya prince yana kaunar ki sosai, kuma lateefa bata ma a kasar nan yanzu...
.
Neena ta dago idonta daya fara canza launi, anty zuby, meyasa ba wanda ya sanar dani?
    Zuby zatayi magana wayar ta ta sake ringing, ta dauka tace,my hrtbeat ina nan fitowa yanzu...
   Zuby ta lallashi neena sosai, sannan ta tafi...
Gaba daya hankalin neena ya kasa kwanciya, da kyal ta kammala abinci, ta saka turaren wuta..
  Ta koma dakin ta ta kife a gado..
Mai ya faru suka rabu? Bacin har karuwa sun samu?
Da yamma prince ya shigo gidan, amir kawai ya iske a falo, amir ya rungume sa yana masa sannnu da zuwa.
  Prince ya shafa kansa, ina momma dinka?
  Amir yace tana dakin ta, prince ya haura sama..
  Yana mamakin rashin zuwa tarbarsa da batayi ba..
 
A kwancen ya iske ta, yazo ya zauna kusa da ita, ya hura mata iska a ido..
   Taki motsawa, gaba daya haushin sa takeji, mai yasa bai taba fada mata ba?
   Prince ya tallabo ta, taki ko motsawa, idon ta ma a rufe suke, ya zaunar da ita ya jinginar jikinsa, ya matso da fuskar sa daf da tata, yace mrs Na'im alkali, wat is wrong uhmm?
   Kimin magana pls, neena ta bude idon ta, prince yace subhanallah, mai ya sami idon haka, yayi ja, neena tayi banza dashi, ya mike ya cire jacket dinshi ta kayan soja, sai farar shirt dinshi ya bari ta ciki..
    Ya riko hannunta, tashi muje asibiti, neena ta kwace hanninta, ta juya masa baya...
  Dama maman amir tana nan? Dama ba mutuwa tayi ba? Dama....ta saka ida sawa sai kuka ya kufce mata...
Prince ya runtse idonsa, dan kukan har cikin ransa yakeji, ya zauna a bed din, ya jawo ta ya rungume tsam, tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa....
    Ya dago da fuskarta, suna kallon cikin idon juna..
  Zan fada miki komai, amma bana so bayan nan ki guje ni, kinji...
Neena ta kada masa kanta..
Yace yauwa, amma sai na fara yin wanka, naci abinci koh?
Neena ta kada kai, yace good gal, muje toh a taya ni..
Kuma ki daina sa damuwa a ranki,..
  I love u...I love u...n I am for u alone...
Kinji?
   Tayi murmushi...prince yayi back hugging dinta, yayi mata kiss a kumatu, mrs Na'im alkali, bakice kina sona ba ke?
Neena ta rufe fuskar ta, tace I love u too so much my prince charming. ..ta juyo ta rungume shi..
.
Sai da prince yayi wanka, ya kwashi girki, sannan yajawo neena dakinsa...
     Ya zaunar da ita a saman gadon, sannan shima yahau ya kwanta, ya dora kansa a cinyar neena..
Neena ta shafa gashin sa,tana jiran mai zai ce, prince ya jawo hannunta ya sumbata..
Sannan yace, mrs Na'im alkali, nasan kin kagara, kiji yadda muka rabu da lateefa ko?
Ta kada masa kai...
Ya runtse idonsa ya bude..ya saukar da lumfashi...
.
kafin na fara aikin soja, nayi nayi da su dad su barni naje makarantar sojoji, amma suka ki, sukace sai nayi decree dina da masters.
A kasar china, sha daya ga watan June, 2008, a wani restaurant, na hadu da lateefa, ta siya abincin amma ta manta credit card dinta, kuma bata da kudin biyansu, inajin su da masu restaurant din, tana rokon su, amma sunki yarda, na mike naje na biya duka tare da ita, cos yadda naji masu shop din na cewa sai ta musu wanke wanke.
   Bayan na biya mata, tazo tamin godiya sosai, har mukayi exchanging nums.
.
A university din da nake karatu, anan muka sake haduwa da ita.
   Munyi mamakin ganin junan mu sosai...
    Anan muka san school daya mukeyi..
   Mun fara shakuwa da juna sosai, har muka fara sanin sirrin junan mu, muka shaku sosai da juna...
Babanta , babban dan kasuwa ne, mai kudin gaske a kaduna..
  Amma mahaifiyarta ba mutuniyar arziki bace, yar business ce sosai.
  
Munyi shekaru biyu muna soyayya da lateefa...
Har na kammala masters dina a shekarar 2010, na dawo gida, nayi applying neman soja..
   Na samu  su dad  na fada musu aure nake so, sunyi bincike akan family dinsu lateefa sosai, mum tace bata yarda ba, saboda irin halayen  maman lateefa da takeji....
  Su abba ma suka ce basu yarda ba, na hakikance ni sai sun aura min lateefa.
   Da kyal suka yarda, akayi bikin mu da ita.
   Watan mu daya na samu aikin soja, aka maidani lagos, kullum muna kan aiki ba hutu, lateefa kullum cikin complaining take.
har dai mahaifiyarta ta gano halin da muke ciki, tazo ta ringa daukar diyar ta suna yawon kasashe suna business dinsu...
   Abun nan ya dame sosai, har su dad suka zo sukaji lbrn.
  Ba karamin fushi sukayi dani ba.
  Ana cikin haka, mukaje libya wani aiki, na kamu da ciwon zuciya da kidney failure. ..
Saboda tunani da yayi min yawa, da kuma rashin cin abinci.ga aikin karfi da muke.
An maido ni abuja wurin iyayena.
, abun haushin ma, su lateefa na kasar Cyprus lokacin.
   An min treatment sosai, amma shiru rashin lafiya sai karuwa take, dan basu gano kidney dina bata da lafiya ba..
An kaini india, anan suka gane, har koda ta sai an cire.
, sun min kedney transplant, lateefa zuwan biyu kawai dubani, saboda yanzu idonta ya bude da manyan masu kudin da suke business dasu.
  Mahaifiyarta ta zuga ta sosai, gashi lokacin tana dauke da cikina, ni banma saniba.
An maido ni gida nigeria,ina ta jinya, har wurin watanni biyar, na rame nayi baki, saboda yadda nake jin jiki.
  
Na dan fara samun sauki, dan iyayena na kula dani sosai, mami da mum suke jinya ta, lokacin zuby da zarah da faruk na makaranta.
  Ba karamin haushin lateefa naji ba, ko zaman jinya ta batayi ba? Zuwa gaishe ni sau uku kawai tayi, wai tana da abunyi..
    Ina wata na 9 da cinya, ta kawo yaro jinjiri ta bawa mai gadin mu, tare da letter
.
   Abun nan ya bala'in bawa iyayena haushi, suka tsaya akan na bata takarda kawai, dan rashin imanin ta yayi yawa, aikuwa, na rubuta takarda aka bawa wani ya kai musu kadunan.
    Mum da mami suka ci gaba da kulan min da amir, bayan dad yace aje ayi test a duba ko jini na ne.
Test ya nuna amir dana ne.
  Bayan na samu sauki na koma bakin aikina.
Toh har yau da nake baki labarin nan bamu kara haduwa da lateefa ba.
.
Neena ta share hawayenta, ta rike hannun sa, insha Allah bazan taba gudun kaba my prince charming, ko wane irin ciwo kayi, ko wane irin aikin kakeyi, I will always be by ur side....
   Prince ya mike ya zauna, ya rungume ta, yace I knw mrs na'im alkali, bazata iya kyamata ba, ko a wane irin hali nake zata kaunace ni.
   Neena ta kada masa kai, ta kara matse shi a jikinta, ba karamin tausayawa amir da prince tayi ba, ta dauki alkawarin kula dasu har karshen rayuwar ta....
.
.
Bayan sati biyu, su amir suka samu hutu.
Prince yazo weekend, suna falo suna kallo abunsu, amir ya juyo ya kalli papa dinsa, papa can we go for a vacation?
Neena ta kalli prince tana jiran taji mai zai ce, prince yace no son, ur momma wil start school, next week.
  Amir ya shagwabe fuska,plss papa, ai zamu iya zuwa for 1 week, plss
   Prince ya kalli neena, tayi saurin dauje idon ta daga kallon shi, yace okay okay zamuje....
   Amir yace papa, lets go to Italy. ..
Neena taji gaban ta ya fadi, take ta tuna da mahaifin su daya barsu..
  Prince yace yess son nice one, amir ya kawo hannu sukayi high five..
Prince ya nemi hutun sati daya..
Sunje gidan su umma da yayaB sun masu sallama, sannan sukaje wurin su mum da mami, sukayi musu suma, anan suka iske deeja da zarah, suka danyi fira sannan suka wuce.
Washegari, sadeeq da zuby suka zo suka kai su airport.
     By 9 jirgin su ya tashi....
  Sun isa Italy lafiya, prince ya sama musu hotel mai tsadar gaske...
Kwanan su biyu suna hutawar su a hotel din, suyi games dinsu har su gaji.
Yau sun shirya fita ganin gari, neena taci gayun ta, cikin English wears, riga three quarter sai wando skinny jeans. .tayi rolling gyelen ta, ta dauki gucci side bag dinta..
    Prince da amir ne suka shiga cikin dakin, amir yace momma kinyi kyau.
Neena tayi murmushi, ta duko tayi masa peck a goshin sa...
Prince yace saura papa shima..ya miko mata bakinsa ya kulle ido....
   Neena tayi murmushi, ta jawo hannun amir suka yi saurin ficewa daga dakin suna masa dariya..yana bude idon sa yaga sun gudu, yaya murmushi yace zamu hadu dake ne...
.
Sun sha yawo sosai ranar, sunyi pictures ba adadi...
   Sunje wani side fast food restaurants.
   Prince yace musu, ku jira ni a nan, ya shige cikin shop din..
   Suna nan tsaye suna fira da amir..
   Wani mutumi yazo shiga shop din, dai dai wurin su neena, ya dafe kirjin sa, sai ganin sa sukayi ya fadi a sume....
Neena ta rikice, tazo wurin sa tana bubbuga shi, mutumin da ganin sa dan nigeria ne...suna nan a wurin mutane sun zagaye su, prince ya fito daga shop din dauke da ledoji kuda biyu...
   Yana ganin halin da ake ciki, neena tace my prince mu taimaka wa bawan Allahn nan, da gani sa kasar mu daya..
   Please yadan tsaya na wasu minutes, sannan ya nemi taimakon wasu suka saka shi a taxi dinsu, suka tafi kai shi asibiti....
An musu bayanin cewa mutumin ya kamu da ciwon zuciya saboda tunanin da yayi masa yawa...
Sun tausayawa bawan Allahn sosai..
  Suka shigo dakin da aka kwantar dashi..
  Lokacin yama farka, ameer na basa labarin yadda momma dinsa da papa dinsa suka taimaka masa..
Suna shiga mutumin ya kurawa neena ido...
  Sukayi masa sannu..
Ya amsa yayi musu godiya..
Prince ya shiga tambayarsa ko dan nigeria ne.
Yace kwarai daga nigeria yake..
Prince ya fada masa abunda likita ya fada musu.
Sai ganin shi sukayi yana kuka.
Prince da neena suka shiga lallashin sa.
Prince yace idan ba damuwa suna so su san maike damun sa.
   Mutumin ya fada musu, yayi wani babban kurkure ne a rayuwar sa, yanzu abun ya dame sa amma yasan wadan da yayiwa da wuya su yafe masa.
Sun tausaya masa sosai.
Prince yace kada ya damu, zasu taimaka masa da addu'a amma yaje ya nemi gafarar mutanen nan.
Ya amsa da toh, inshaAllah cikin satin nan zai koma nigeria.
Prince ya amsa card dinsa, shima ya amsa na prince din.
sannan suka masa sallama suka tafi..shidai sai kallon neena yakeyi, itama sai kallon sa takeyi.
Sun sha hutun su, cikin jin dadi, sun yo wa yan'uwa tsaraba sosai.
Ranar da suka dawo,gidan su mum suka sauka, sai farin ciki sukeyi, kowa yazo gida ana ta fira da barkwanci.
    Sai dare dukka yaron suka yiwa iyayen su sallama suka tafi gidajen su..
.
Bayan shekara biyu...
   Neena na gani za'a shiga da ita dakin haihuwa, mum, mami, umma, yayab, zuby da wata yar baby a hannunta, sai zarah da tsohon ciki, deejah da intee dinta, suna ta zarya a bakin labour room din...
Faruk da sadeeq suka shigo, suka tsaya wurin mami suna tambayrta ko an haihu lafiya, mami tace tukunna dai...
   Prince duk ya rikice, yana kan jirgi dan zuwa ganin yanayin da matarsa ke ciki, sai kiran su faruk yakeyi....
Ya sauka daga jirgi, yazo daukar mai taxi, dan ba wanda yazo daukarsa..
    Wata katowar mota ta tsaya a gaban sa...
   Aka sauke mirror, prince na kallon cikin motar yaga wannan mutumin da suka hadu a Italy, mutumin ya sakar masa murmushi, yace shigo mana Na'im...
   Prince ya shiga shima yana murmushi..
  Mutumin yace, naji dadin kara haduwa dakai, dama a abuja kuke ne? Prince yace eh, yanzu ma matata na asibiti zata haihu...
Mutumin yace Allah ya sauke ta lafiya, nima nazo neman mahaifiyata ne, da kuma yan'uwana...
Prince yace Allah sarki, Allah yasa ka gansu toh, mutumin yace amin, muje na kai ka asibitin a ina ne?
  Prince yace a maitama ne.
.
Ya ajiye prince a bakin gate, suka yi sallama, prince ya basa address dinsa.
Prince na cikin buga sauri dan zuwa wurin matarsa...
   Sukaci karo da *Lateefa* wani irin burki suka ci a tare...
  Lateefa na ganin sa ta zube a kasa...
Ta saki wani irin kuka, wanda suke tare yace, lateefa lafiya, lateefa ta rike hannun sa, hafiz hafiz, wannan shine Prince shine na'im, din da muke nema....
Hafiz ya kalli prince, yace na'im ka taimaka ka yafewa matata, I know she did wrong u, pls ka yafe mata...
    Lateefa dake kuka kamar ranta zai fita, tace prince, ka yafe min ka yafe min nasan banyi daidai ba, ka yafe min ko Allah zaisa na sake ganin tsatso na.....
Prince ya tsaya tsak yana kallon ta, ya kalli hafiz, yanzu ina cikin sauri ne, matata na labour room...
Hafiz ya rike hannunsa, yace pls abokina...
   Prince ya sauke ajiyar zuciya, na yafe miki lateefa, amma ki nemi yafiyar danki shima...
   Ta mike da sauri, tace ina yake yanzu.
  Prince yace ga address dinmu, kuzo gobe inshaAllah....yaya saurin tafiya, har yana hadawa da gudu.....
Neena ta haifi diyarta mace, kyakkyawa sosai, kamar su daya da prince....
.
Sun koma gidan su mum.
Dad da abba na falo suna fira da yayab da umma dasu mum da mami, faruk ya shigo ya sanar musu sunyi bako..
Abba yace shigo dashi mana...
   Faruk ya fita ya shigo da bakon...
  Gaba dayan su suka mike..
Yayab tace almustafa kai neh!!!!??
Almustafa ya iso gaban su ita da umma ya shiga neman gafarar su...
Ansha kuka, kafin nan aka yafe wa juna...mum tace bari a kira yaran ku gaisa ..
Taje dakin da neena ke jego, ta kirasu duka..
Suna zuwa neena tayi ta mamakin ganin mutumin da suka taimakawa..
Prince da safeeq suka shigo suma..
  Shima prince yayi mamakin ganin mutumin...
    An dai aka sanar dasu ko waye...
  Neena da sadeeq, suna hawaye sukaje suka rungume baban su...
    Sai sallamar su lateefa sukaji...
  Gaba daya falon anji mamakin ganin ta, ta duga gaban su dad ta basu hakuri...
Hakama mu mum da mami...
Kowa ya yafe mata, yayaB ta nuna mata neena tace ga matar na'im...
   Suka kalli juna, lateefa tayi mata murmushi...
  Sai ga faruk ya shigo da amir...
  Lateefa na ganinsa tayi gunsa ta rungume sa,....
   Ya kalli neena yace who is she momma. ...
   Neena tace shes ur momma also..
Amir yayi murmushi,  lateefa tayi ta kallon yaron, tana sumbatar sa...
   Sai da sukayi mangariba sannan suka tafi, mijin lateefa yace idan ba damuwa, suna so amir ya ringa zuwa musu hutu kaduna...
  Prince yace ba damuwa, sukayi exchange din contacts, ya raka su har gate suka tafi....
.
Ansha suna, an sawa baby suna aysha, amma zasu ringa kiranta hanan.
     Zubaida ta haihu ta samu yaro namiji  ahmad suna kiransa Ayman.
    Zarah na dauke da tsohon ciki...
Baban su neena almustafa, ya kara gyara gidan sadeeq kuma ya dawo da kasuwancin sa nigeria, ya saka sadeeq a matsayin CEO, ya sai wa neena mota har biyu, sannan ya sake musu kayan daki dukkan su harda su zarah da zuby dama deeja.
.
Bayan shekaru ashirin.......
  Na sake cin gayu na naje dan kara samo wa masoyana rahoto..
Wani handsome sarauyi na gani yana saukowa daga jirgi....
  Na goge idanuna...like seriously wannan Amir ne....
Oh my G, ya girma ya zama cikakken saurayi.....
Ya amir ya amir! Over here brother. .....
Wasu pretty flowers na hango, babbar su yar shekaru 22(intee), sai mai binta mai kimanin shekaru 20 (hanan) sai dayar mai shekaru 19 (diyar zarah mai suna salma)
Gaba dayansu sunci gayun su cikin black arabian abaya...
.
Ameer ya karaso wurin su yana murmushi...
     Hanan tayi tsalle ta rungume shi, ya manna mata kiss a kumatu...
    Babbar ta cire sun glasses  dinta, tace welcome back brother,  amir ya kura mata ido, d little intee...ta shagwabe fuska brother kai koh...
   Karamar su ta juya masa baya tana kumbure kumbure...
   Ameer ya kallo ta Oh Oh, matar ya akayi ne?
  Salma tana dariya yeeh. Welcome brother ta rungume sa itama, intee tadan buge ta oh wasa ma kike yi da brother ko? Sukayi dariya duka..
Ameer yace gals lets get going na kagara naga momma dina....
Sun isa babban gidan su dad da abba da suka canza.
Kowa da kowa na gidan lokacin ana jiran babban jika ya dawo..
  Neena na hango sanye da riga gown ta yafa babban gyele a jikinta sanye da glasses. ..sai faman girke girke takeyiwa danta...
   Prince ne ya shigo kitchen din ya dan manyanta daka ganshi  kaga tsohon soja....
.
Yazo yayi bag hugging neena, wat is mrs na'im alkali still doing? Neena tayi murmushi ta juyo tana kallon shi, my prince charming, ta manna masa kiss. ina ka shige ne yau? Yayi murmushi ina tare da Aiman a garden....
    Neena tace nidai kun maida ni maman maza, anty zuby ta kwace hanan...
     Prince yace oh yes, kina da yaro lawyer, ga kuma Aiman soja....
  Neena tayi dariya prince ya janyota jikinsa, yakamata muyiwa hanan sister fa...
   Neena takai masa dukan wasa, shiiiiish a kicin muke...
Prince yayi dariya.....shigowar yayab sukaji, tana cewa ni faruk da sadeeq zasu hadewa kai, har zubaida da deeja zasu shige wa mazan su...
    Nima inada jikata ai, neena neeena, prince ya shige bayan kofa, toh matar nan uwar surutu zata shigo....
    Neena tayi dariya....
Babansu neena da umma, mum da mami, dad da abba duka suna falo suna firan su.....
     Aiman ya shigo cikin murna, grannies guess what?
    Mum tace Amir is back?
Aiman yayi dariya oh yes, my big bro is back yahau tsalle, zubaida tana saukowa kasa falon tace maza ka fadi....
    Amir ne ya shigo falon tare da yan'matan...
   Yayi wurin zuby ya rungume ta aunty, ta shafa kansa, our amir congrats an gama karatu..
   Yayi murmushi ya karasa wurin kakanninsa, ya shiga rungumar su suna sa masa albarka...
   Ya tsaya tsakiyar falon, ya rike kugun sa ya kalli nan ya kalli can...
    Ina dr ? Where's my momma, our dr....?
Neena ta fito daga kitchen din cikin sauri, my son an dawo, amir na korarin rungume ta, yayaB ta shige tsakani....
Ta rungume amir tana washe baki...
  Sannu da dawowa dan albarka....
Amir yace granyB mun same ku lafiya...?
.
Ya janye jikinsa ya rungume neena, ta shafa kansa....my son Allah yayi maka albarka..
Prince ya fito shima, amir ya karasa ya rungume sa...
  Deeja da zarah suka shigo gidan suma, tare da faruk da sadeeq, amir gaba daya cikin farin ciki yake....
Yayi wanka ya fito ya iske kowa da kowa  ana fira, intee ta mike da sauri ta kawo masa abincinsa...
   Salma ta mike itama ta kawo masa juice. ..
Hanan ta kalli aiman sukayi dariyar gulma...
Suna cikin firan su akayi sallama, mummy tare da ikram...
Mum, mami, neena, zuby, zarah, faruk, deeja, dad, abba, yayab suka mike...
   Mummy ta karaso cikin falon...
Ikram taje gaban prince ta duka har kasa ta nemi yafiyar sa, neena tazo ta mikar da ita tace mijina ya yafe miki ikram....
   Duka falon sukayi murmushi.  hanan, intee, da salma suka ringa damun amir, brother who's she?
  Ameer yace ur auntie. ..
  Sallama aka kara yi....lateefa da mijin ta hafiz, tare da diyarta minal suka shigo...
    Duka yaran sukayi gunta suka rungume ta....
  Ameer ya rike hannun minal, ta rungume sa itama tace welcome brother, dad yace woo ameer kai kam kannen ka har sunyi yawa...
Gaba daya falon suka kwashe da dariya....
Nima Afrah na murmusa....
  Sannan na bawa phone dina hot kiss, thanks for all your hard work durling...
.
Alhamdulillahi anan muka kawo karshen wannan littafin , sai kuma mun hadu a wani.

Post a Comment for " YAR TALAKAWA COMPLETE "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...