YAKANA BOOK 1 KARSHE CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YAKANA BOOK 1 KARSHE CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAKANA BOOK 1 KARSHE CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

- - Post a Comment

 YAKANA BOOK 1 KARSHE CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIRDa sauri Inna ta ce, 


"Ka ga Fati can tana tare mota, yi kwana mu dauke su". Ya yi kamar bai ji ba, ya karawa motar shi gudu. Inna ta yi salati ta ce, "Baka ji ni bane? 'Ya'yan ka fa ta dauko daga makaranta!”. Sai a sannan ya juya, tuni ta tare tasi suna kokarin shiga. Ya ce, "Ai sun shiga mota ma hadu a can”. 

Inna ta yi shiru tana mamaki, har suka iso gidan su Fati ba su shigo ba, don ba za ka hada motar gida da ta haya da ke yin tsaye-tsaye ba. 


Tun daga soron gidan yake jiyo kukan Baby Nana Khadijah. Ya rintse ido tsigar jikinshi na tashi. Inna ce ta yi sallama ya biyo bayan ta. Yaya suka tarar tana ta fama da Baby Nana, wadda ke ta tsandara kuka kamar ta tsaga gidan ta ki karbar madarar da take bata. 


Ta amsa musu sallama cikin sakin fuska da walwala, ta shimfida musu sabuwar tabarma, sannan ta mikawa Inna Baby Nana. Yaya ta dubi Sulaiman ganin yadda ya rame ya yi kasumba, sai ta ji hawaye sun ciko idon ta. 


Ta ce, 


"Me nake gani haka ni Sa'adatu? Sulaiman me ya yi zafi? Hadiza ba ta yi gaggawa ba, muma jiran namu wa'adin muke. Karbi 'yarka tunda ta zo duniya baka taba daukar ta ba, ita kuma laifin me ta yi? Ka zamo mai YAKANAH, wannan ba shi ne karshen rayuwar ka ba!!". 


Inna ta mika mishi yarinyar, ya fi karafin mintuna uku kamin ya karbe ta, ya kura mata ido yana mamakin kamannin shi da ita har sun fi nashi da Munib. 


Dai-dai sanda Fati da yaran suka shigo cikin sallama, tana sanye da katon hijabin ta har kasa mai hannaye, rike da lunch bod din yara da jakunkunan su. 


Cikin nutsuwa ta tsuguna har kasa ta gaida Inna, ba tare da ta kalli Sulaiman ba ta ce, "Ina wuni?’ Bai amsa ba, ita ma ba ta tsaya sauraron ya amsa 

ba ta wuce ciki. 


Ai Munib da Muniba suna ganin Baban su suka fada mishi suna ta tsallen murna, ya mikawa Inna Baby ya zaunar dasu duka a cinyoyin sa, suka soma ba shi labari iri-iri, duka rabi ‘AUNTY FATI’ ta yi mana kaza, ta yi mana kaza. Yana jinsu bai ce komi ba. 


Malam Ja'afar ya shigo hannayen shi rike da manyan ledoji yayo cefane ciki har da madarar SMA da Nana ke sha, ya kwalawa Fati kira ta fito ya bata. 


Sai a sannan ya lura da bakin takalma har da na namiji a kofar dakin Yaya, ya ce da Fati, "Waccan madarar ta kare ne?" Ta ce, "Eh, saura kadan". Ya ce, "To ki dinga gaya min kafin ta kare ba sai ta kare kaf a barta tana kuka ba". 


Ta ce, 


"Ai masassara take shi ne take kuka, amma dama gobe zan kaita asibiti". Ya ce, "To Allah ya sauwake, ke kuma Allah ya ba ki ladan hidimar da kike yi da 'ya'yan ki, ya sa suji kan ki kamar yadda kika ji kan su, ya kai rahama kabarin mahaifiyar su". 


Ta ce, 


"Amin Baba”. 


Shi ma Sulaiman da ke can daki yana jin su ya ce "Amin". A zuciyar shi. 


Malam ya daga labulen ya ce, "A'a! Ashe Inna ce, barka da zuwa kin sha hanya, ya ya aka baro Malam?" 


Ta amsa, suka ci gaba da gaisawa suna hirar ‘yan jikokin su, tare da kara yiwa juna ta’aziyya. 

Malam Ja'afar ya dubi Sulaiman sosai ya ce, 


"Ina maganar aiki ta kwana?" 


Ya yi shiru kanshi a sunkuye, can kuma ya ce, "Zan koma gobe insha Allahu". 


Malam ya ji dadi, ya kara mishi da nasiha mai sanyaya zuciya. 


Ba su baro gidan ba sai karfe biyar na yamma, bayan Inna da Yaya sun yanke shawarar yaran za su ci gaba da zama a nan saboda ya fi kusa da makarantar su. 


Har za su tafi ya dubi Yaya ya ce, "Duk abin da ake bukata Yaya, don Allah a gaya min”. 


Yaya ta yi murmushi ta ce, "Me ake bukata ban da madara? Bayan ita babu abin da zai gagara da izinin Allah”. 


Ya ce, 


"Duk da haka ina son sanin sauran abubuwan da ake bukata, ai ragi-ragi ne". 


Ta ce, 


"To ka tambayi Fati". 


Ba don ranshi ya so ba ya nufi kofar dakin nata. hijabin a jikinta, kwayar idanun su ta hadu, ya yi saurin dauke kansa don gani ya yi kamar Hadiza, hatta digon tauwadar Allah da ke kan tsinin hancin Hadiza akwai shi a tsinin hancin Fati. Zuciyar shi ta yi wani irin mummunan bugu, don gani ya yi tana rikide mishi Hadiza sak, kasancewar bai taba ganin ta babu hijabi ba. Ya tsaya daga bakin kofar hannun shi duka biyu zube cikin aljihu. Da kyar yake magana kamar an tilasta mishi, ba tare da ya kara kallon ta ba. 

"Na tambayi Yaya abubuwan da yara suke bukata, ta ce in tambaye ki?" 


Kanta a kasa ta ce, 


"Sai ko pampers da madara". 


Yace, 


"Bayan su ba wani abu?" 


Ta ce, "Eh, amma malamar su ta ce akwai prize gibing day ranar asabar kuma ana son iyayen yara su je". Sannan ta dauko report card na yaran na wannan zangon ta mika masa. 


Garin karba hannayen su suka gogi juna, sannan suka kara hada ido a lokaci daya babu wanda bai jia jikin sa ba. Ita tsoro ta ji, shi kuma ji ya yi kamar hannun Hadiza. Bai ce komi ba ya karba ya sanya a aljihun shi ba tare da ya duba ba, bai kuma ba ta amsar zai je ko ba zai je ba ya fita. Ya tadda Inna har ta fito suka tafi, ya bar Fati cikin tunani. Ta zauna a gefen gadon ta, ta sauko Nanah wadda ta samu barci ta rungume cikin hannayen ta, tana tunanin me Hadiza ke nufi da ta ce ta kula da Baban Munib? "\....Munib kulawar Uwa yake nema, Sulaiman kulawar MATA yake nema....”. Ta tuno kalaman Hadiza. To ai ita ba matar shi ba ce, ba gidansu daya ba, ta ina za ta kula da shin kada rashin Hadiza ya tagayyara shi? Wannan baudadden mijin nata dake yi mata kiyayya maras dalili? In har Hadiza na nufin ta auri mijinta ne wanda ba ta fito baro-baro ta fada ba, sai hannunka mai sanda da ta yi mata, ta hada 

ta da wani al'amari da ba zai taba yiwuwa ba. 


Ba ta fata, kuma kada Allah ya tabbatar ta yi tarayya da Hadiza a kan abin da take so, ta tafi ta bari ba don ba ta so ba, sai don hukuncin Allah wanda ya fi karfin dan adam ya yi jayayya da shi. Hakika ta dauki alkawarin da ba ta san yadda za 


ta yi ta sauke shi ba. kK 


WwW 


ashegari da yamma sai ga Inna ta kara dawowa, Dr. Sulaiman ya kawo ta, Hamza da Abdulyassar suka shigowa Fati da katon na madarar SMA, katon na diapers da himilin shopping na kayan masarufi da kayan biskit da choculate da su Indomie wanda su Munib ke zuwa makaranta da su. Ta adana kowanne a inda ya dace, Inna ta ce ya je sai dare ya zo ya dauke ta. 


A lokacin Malam Ja'afar ya iso da shi da Inna da Yaya suka kule a daki, suka sakayo kofa, me suka ce me suka ce oho, sun dai dade suna magana kafin ya dawo ya dauki Inna su wuce, kasancewar a gobe zata koma Bakonri, ya biya ta Jifatu ya yi mata sayayya mai yawa kamar yadda ya saba, ita da Malam da sauran kannen shi, suka wuce gidan sa. 


Inna ta tuka mishi tuwon semobita da miyar ganye ya ci, ta takura mishi ya bude wayoyinsa. Yana budewa sakonnin ta'aziyya daga |\ikitoci 

‘yan uwansa da sauran abokan arziki ya soma tittidowa cikin wayar. Sannan ana neman shi a ofishin (Chief Medical Director) na AKTH ranar litinin. 


Don haka yana kai Inna Bakori suka gaisa da mahaifin shi bai tsaya ba. Da zai tafi Inna ta ce, 


"Ni kuwa akwai wata magana muhimmiya da nake so mu yi, ga shi na ga alamar kana sauri". Yace, 


"Gaskiya kam ina cikin sauri, sai ko idan na dawo". Ta ce, 


"Shi ke nan Allah ya kiyaye hanya, ya kara maka hakuri da YAKANAH, ya shige maka gaba a kan al'amuran ka, ya yi maka musayan alheri”. 


Har ransa ya ji dadin addu'o'in Inna, wata nutsuwa ta kara shigar shi, son mahaifiyar shi ya kara shigar shi. Ta ce, 


"Ina so zuwa sanda za ka dawo in ga canji, kamar yadda ka yi min alkawari, in ganka a likitanka ba mai sunan Malam ba". 


Murmushi ya yi, wanda rabon shi da yin shi tun wani karni can da ya shude. 


RR KK 


itinin, ya isa ofishin CMD, sun dade suna tattunawa a kan wani aiki na dashen zuciya da za a yiwa ministan lafiya. Yana daya daga cikin likitocin da zasu gabatar da aikin. Ya koma office dinsa ya daidaita komai ya ci gaba da aikin sa, cikin karfin zuciya da neman rinjaye a kanta. Sai ya zamto yana jin dadin aikin sosai, don yana debe mishi kewa, yana hana shi zama shiru har maraicin matarsa ya gallabe shi. Ya tarar da tulin ayyuka da yawa, don haka ya zamo busy a satin gaba daya. 


Ranar alhamis ya saci jiki ya je yayowa ‘ya’yan shi siyayya ya biya ta makarantar su ya gansu, lokacin da aka fito cin abinci, a karkashin wani benci ya zauna ya rungume su suna ta labari, ya bude ‘kit-kat’ yana basu suna ci suna yi mishi hira. Tun suna damuwa da rashin Momin su har sun hakura sun dangana sun daina tambayar ta. Munib ya ce, 


"Daddy ba ka zo (prize gibing) din mu ba, kowa Baban shi ya zo banda mu". 


Ya kama kunnen shi cikin nunawa yaron amsa laifin sa, ya ce, "I am bery-bery sorry..... aiki ne ya yi min yawa. To wa ya kawo ku?" Suka ce, "Aunty Fati, ta yi mana kwalliya ta kawo mu”. Ya ce, 


"Aunty Fati ta kyauta!". 


Suka yi murmushi. Ya ce, "Nedt year ba zan sake ba". Aka kada kararrawar komawa aji, suka fella da gudu suka nufi ajinsu, ya bisu da kallo yana 

murmushi cike da kewar su. 


Hakan yake yi duk sanda ya samu sararin aiki, ya daina zuwa gidan don kar ya ga Fati, tana tuno mishi da wasu al'amura msu yawa a kan Hadiza. Sannan ba ya son wata alaka take shiga tsakanin su, shi ma kuma bai san mai ya sa ba, ya danganta hakan da rashin haduwar jini. 


Ita kuma ta danganta hakan da wulakanci da raina mata wayo, yana ganin ta kamar ba ta san abin da take yi ba, bayan in da wanda ya san ciwon kansa a duniya to ita ce. Sai dai tsarin rayuwar su da ya banbanta, kowa da irin nashi tsarin rayuwar, don haka ita ma ta yi kamar ba ta san yana zuwa makarantar yaran ba, bayan kuma suna gaya mata. 


Ana i gobe sadakar arba'in din Hadizah, Malam Sulaiman, Inna Halima da Baffanin Sulaiman guda biyu, Malam Surajo da Alhaji Umar suka iso gidan Sulaiman a Kano, a daren suka bukaci ya kai su Karkasara. In da ya ajiye su da daddare ya wuce asibiti, da cewar zai dawo ya dauke su. Manya sun kule a falon Baban Hadiza, wato Malam Ja'afar suna magana ta hankali har da Yaya da Inna. Yaya ta ce, "Ni bana jin Fati sai shi Sulaiman, anya zai yi na'am da al'amarin nan?” Malam Sulaiman ya yi murmushi ya ce, "Kune baku san Sule ba har yanzu, yana da wani hali tun yana yaro, abin da zai so sai ya fara kin shi tukunna. 


Ga yadda mahaifiyar shi take bani labari, babu jituwa ko ya ya tsakanin sa da Fati, ita kuma ta kama kanta ba ta shiga shirgin shi. Mu dai burin 

mu ku bamu hadin kai, Allah ya gani muna son zuri'ar gidan nan, muna son zumunci ya ci gaba da gudana kamar yadda aka faro. 


Fati ita ta fi cancanta da ta rike 'ya'yan ‘yar uwar ta, don a wannan zamanin da wuya a samu macen da za ta rike maka 'ya'ya har uku duk son da take maka. Sannan mun yaba da hankali da tsarin rayuwar Fati, muna sa ran yara za su tashi da kyakkyawar tarbiyya har zuwa girman su. 


Fati ba za ta dauwama a gida tana bautar 'ya'yan ‘yar uwarta ba, dole watarana za ta yi aure. Ranar da hakan ta faru ya ya Sulaiman zai yi da yaran nan? Ga shi suna karatun su mai kyau a nan balle mu tafi dasu Bakori. Fati ita ta fi cancanta da ta maye gurbin ‘yar uwarta a zuciyar Sulaiman. 


Don haka muna neman hadin kanku, yardar ku da amincewar ku Malam Ja'afar. Shin an bamu Fati? Da karfin mu muka zo, gobe muke so bayan an shafa addu'ar Hadiza a daura auren Sulaiman da Fatima". 


Malam Ja’afar ya ce, 


"Tun kafin ku yi wannan tunanin na riga ku yin sa, kun dai riga ni furtawa ne. Tabbas duk matar da Sule zai aura nan gaba ta rike mishi marayun shi ba kamar Fati ba, wadda ta san ciwon su, tasan ciwon ‘yar uwarta. 


Sannan Hadizah ta yi wani abu a ranar da za ta koma ga mahaliccinta, wanda ya tsaya min a rai kwarai, ta kama hannun Sulaiman ta hada da na Fati, sai dai ban ji me suke cewa ba. 


Fati yarinya ce mai biyayya, ba za ta tsallake umarnin mu ba, amma kamar yadda Sa'adatu ta 

ce ne, da kyar idan shi Sulaiman din zai amince. Sannan ya wuce matsayin da za ace za a yi mishi aure ba tare da sanin shi ba”. 


Alhaji Umar ya ce, "Kubar wannan a hannun mu, kamar yadda Fati take mai biyayya, shi ma Sulaiman mai biyayya ne, iyayen shi basu taba saka mishi kara ya tsallake ba. Ina da yakinin zai yi biyayya ga mahaifin shi, kuma a daren nan zamu sanar da shi ba sai gobe ba. 


Ga sadaki naira dubu ishirin ga goro, daga aljihuna ni waliyyin sa. Jikina ya bani alheri ne zamu kulla, don irin wannan auren na son zuciyar iyaye ba karamar falala ake samu a cikin shi ba”. 


Kowa ya jinjina kai. Yaya ta ce, 


"Nima a daren nan zan sanar da ita insha Allahu”", Da haka taron ya tashi, ya yi dai-dai da sallamar Sulaiman a falon, dukkanin su suka amsa fuskar kowannen su cike da walwala da annuri. 


Malam ya ce, 


"Faduwa ta zo dai-dai da zama kenan, ita ma Fatiman a kirawo ta”. 


Yaya ta tashi ta fita don kiran Fati. 


Tana yiwa su Munib shimfidar kwanciya goye da Nana, Yaya ta yane labulen dakin ta ce, "Fati kin kwanta ne?" "A‘a, ina harama dai". "To biyo ni dakin Malam yana son magana da ke". Ta sauke goyon ta zurma hijabin ta, ta bi bayan Yaya har dakin Malam. Ta sha mamakin ganin taron dakin har da Baban 

Munib, wanda ke can sunkuye da kai a gefe. Ta yi sallama cikin sassanyar muryar ta dukkan su suka amsa, ban da Sulaiman wanda ya fara shan jinin jikinsa kan wannan taron domin shi aka yi. Jikinsa ya yi sanyi, gaban shi ya soma faduwa, haka nan gwiwoyinsa ya jisu kamar an rarrade su da murfin kwano. 


Ta samu gefen Inna ta zauna, ita ma jikinta ya soma kyarma don ba ta son a tirke ta a cikin mutane. 


Iyayen dai na duban su suna nazarin kowannen su, sun fahimci dukkan su a firgice suke, amma firgitar ta fi karfi ga Sulaiman. Wannan taro na mene ne? Malam Sulaiman baya _shiga kankanuwar magana. 


Sai da suka tabbatar sun dan samu nutsuwa sannan Malam Sulaiman ya dubi dansa ya ce, 


"Mai sunana wani abin alheri ne za mu yi maka, da fatan za ka karba hannu bibbiyu". 


Bai yi magana ba, amma ya dago ya dubi mahaifin sa. Ya ci gaba da cewa, 


"Muna kara yi muku ta'aziyya, sannan muna so ku sani cewa, duk abin da Allah ya tsara akwai hikimar yin hakan a cikin sa. 


Mun zauna mun yi tunani, mun yi shawara mun yanke cewa, Fati za ta maye gurbin ‘yar uwarta a gare ka, ku ci gaba da raino da_tarbiyyar ‘ya'yanku kamar yadda mahaifiyar su ta fara yi musu, kuma ‘yar uwarta ta karbe ta. 


Allah ya riga ya hada mu, zuri'a ta hada mu. Don haka Sulaiman bana son ka da wani aure in dai ba jinin gidan nan ne ya kare ba. Za mu yi alfahari 

daku idan kuka taushi zuciyoyin ku kuka yi mana biyayya. Allah zai nunawa Hadiza har cikin kabarin ta cewa, ke Fati kin rungumi iyalinta, kin rungumi mijinta baki bar rashin ta a rayuwa ya tagayyara shi ba. 


Sannan kai Sulaiman Hadiza za ta yi farin ciki idan har ya zamto ka rungumi amanar rayuwar ‘yar uwarta ta hanyar aure, muna neman hadin kan ku, za mu samu Fatima da Sulaiman?" 


Da a ce Malam Sulaiman ya lura, da ya ga irin jibin (zufar) da ke ambaliya a fuska da jikin Sulaiman, yayin da gudun jini ya katse a jikin Fati, idanuwanta suka juye suka kada suka yi jazur, hanjin cikinta ya dunkule waje daya ko dan yatsanta ta kasa dagawa balle ta motsa bakinta. Tana addu'a cikin zuciyarta idan mafarki take Ubangiji Allah subhana ya yi gaggawar farkar da ita. 


Sai dai a bangaren shi Sulaiman, ya so a ce shi da iyayen shi ne kadai su kai wannan maganar, da a take zai ce dasu idan kasa da sama za ta hadu bai amince ba. To an ce wai ko mutuwa tana kunyar iyaye, balle iyayen Hadiza? Ya zai yi ya iya ya budi baki a gabansu ya ce baya son jinin Hadiza? Shi tunda ya rasa Hadiza bai kara tunanin nan gaba zai kara yin aure ba, bai kara tunanin wai yana da future ba, balle ya yi tunanin yin aure. Kuma a rasa wadda za a aura masa sai wannan yarinyar da bai san a matsayin da ya ajiye ta a zuciyar sa ba. 


Duk da yadda take hidima da 'ya'yansa, Fati ba ta taba burge shi ba, Allah bai sa masa kaunar ta a 

zuciyar sa ba, sannan kuma wai auren ma daga yin arba'in din Hadiza? Sannan da shakikiyar ta? Fati ba ta taba burge shi ba balle ya so ta, bai taba tunanin irin ta a matsayin matar shi ba. Ya ya ma za ai wannan kidahumar yarinyar 'yar sakandire ta maye gurbin Hadiza? Ta ya ya mahaifan shi suke tunanin zai iya rayuwa da kanwar Hadiza? Ya yada girman sa ya yi mu'amalar aure da ita? Kwarai ya fahimci abin da Hadiza ke nufi tsakanin shi da Fati a ranar da Allah zai dauki ranta, amma (he is sorry to say) ba zai iya cikawa Hadiza burinta ba. 


In don 'ya’yan shi ne a ba shi abinsa ya rike ko ya bai wa Inna, ba sai an makala mishi auren da bai san ya ya zai yi da shi ba. 


Malam Ja'afar ya ce, "Duk kun yi shiru, ko da yake shirun alamar amincewa ne, To ku tashi ku je Allah ya yi muku albarka, dama mun sanar daku ne kada sai gobe ku ji an daura aure ku ce ba a sanar daku ba. In kuma akwai mai magana to ya yi, a shirye muke da mu bai wa kowannen ku hakkin sa”. 


Inna tana murmushi ta dubi Sulaiman ta ce, 


"Ni na san mai sunan Malam ba zai ki abin da muke so ba”. 


Jikinsa ya yi sanyi kalau, ya nemi duk wata hujja da zai bayar ya neme ta ya rasa. Zuwa lokacin Fati ta mike za ta fita, juwa na kwasar ta, da dafa bango ta samu ta bar falon. 


Ta yi dakinta ta dauki ‘yar jaririyar ta wadda ke ta tsala kuka a dalilin ta manta ba ta sa mata gidan sauro ba ta fita, sauro ya hana mata barci. 

Shi ma bai yi magana ba yana jin su suna ta kida suna rawar su na addu'o’'l, sa albarka da fatan alheri a gare shi. Gwiwa a salube ya fito jikin mota ya baro su suna ta sallama. 


Mu tara a littafi na 2. Kuma na karshe inshallahu. Wanda tare suke da dan uwansa. Maman Safah da Marwah ce, ke yi muku fatan alheri. 


c a 


_=> 


- = 


- —= 


_= 


—= 


- > 

Post a Comment for "YAKANA BOOK 1 KARSHE CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...