YAKANA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YAKANA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

YAKANA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

- - Post a Comment

 YAKANA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

tare, har yanzu bani da lafiya". 


Da gudu suka mike daga jikinta suka nufi dakin su suna murnar zuwan Antin su da suke tsananin so. Alti ta yi sallama dauke da tray kanta a sunkuye ta ce da Hadiza, 


"Na ce sai na daina daura abinci a tebir?’ 


Hadiza ta yi murmushi mai hade da wani irin huci mai zafi, ta ce,

 


"Idan maigidan yana son hawa tebir din fa?" Ta fada tana kallon Sulaiman. Bai dago ya kalle su ba, haka bai tofa musu ba, duk da ya lura ta bakinsa suke son ji. Alti ta ajiye katon tray a gaban Hadiza ta juya ta fita. 


Tana ba da baya ya suri Hadiza a kafadar shi sai dakin barcin su. A hankali ya sauke ta a makeken ‘family bed’ din su, ya koma toilet ya cika baf da ruwa mai dumi, ya zuba dettol kadan ya dawo ya soma warwarewa Hadiza kayan jikinta, ya nade ta cikin towel ya sake sungumar ta ya yi toilet ya sanya ta cikin ruwan da ya hada. Ita 

karfin Sulaiman mamaki yake bata. Ya yi mata kyakkyawan wanka da kamsassan sabulun Zest, ya nado ta ya fito da ita. 


Yawancin kayanta a dakin suke, don haka ya shirya ta cikin riga da wandon pakistan ruwan goro (orange), ya dauki (kumb) ya soma sharce mata gashin kanta wanda rashin gyara kwana biyu ya sa shi duk ya cukurkude. 


Ta ce, "Da ka bari Sulaiman Fati za ta yi min”. 


Bai saurare ta ba ya ci gaba da abin da yake, amma da a ce ta kalli fuskarshi a lokacin, data lura da yadda ya dan hada rai, saboda ambatar Fati da ta yi, wato ta fi son Fati ta kula da ita fiye da shi. 


Ta yi murmushi ta ce, "Amma tunda ka hada ruwan wanka ka yi mai wuyar, zan iya wanka da kaina,sai Fati ta shirya ni koda yake ma zan iya shiryawa da kaina....... " 


"Is o.k Hadiza, ba tun yau ba na san 

kin fi son kanwar ki fiye dani. In ba haka ba ni amfanin me ke gare ni? Da ba zan kula dake ba a lokacin da kike cikin lalura?" 


Ta kama baki, don ba ta ji dadin maganar shi ta farko ba, amma sai ta share ta ce, "Yau da gobe ne sai Allah Sulaiman....... ". Can kuma ta yi rau-rau da ido kamar hawaye za su zubo, 


"Me ya kawo maganar na fi son Fati a kanka? Ban ji dadin nagetive response din ka ba". 


Ya ce, "To ai ke ce Hadiza da wani irin batu, amma ina so ki yarda da cewa, idan zan gaji da hidimar ki Hadiza, to zan gaji da_ hidimar Kaina...... " 


Ta ce, “Amma Sulaiman...... Ya kai hannu ya toshe mata baki, "Kina shakka da abin da na ce miki?" Ba ta son jan zancen da nisa, har ya yi tsayin da zai zamo bacin rai, sai ta ce, “Bana shakka Sulaiman, Allah ya bamu rai da lafiya”. 

Ya turo ta cikin kujerar ta suka dawo falon don cin abinci. Munib da Muniba suka shigo, fes dasu cikin kaya ‘yan kanti (pink colour) har Fati tayi musu wanka ta shirya su ta feshe su da turare. 


Suka saki baki cikin mamaki, ganin Daddy yana tura Mummy cikin kujera, abin ki da yaro, sai ba su kawo ma ransu komai ba, ko wani abu ne ya faru da Maman nasu, sun dauka haka nan dai yake tura ta don bata da lafiya. Sai suka sa rigimar ta tashi suma Daddy ya tura su. 


Haka Sulaiman ya sauke Hadiza a seater, ya dauke su su duka biyun ya aza a kujerar, ya yi ta zagaya falon dasu suna jin dadi, sai kyalkyatar dariya suke. 


Hadiza ta juya ta dube su, ganin abin nasu ba na kare bane ta ce, "Oya! Food is ready, maza ku zo ku ci kafin malamin lesson ya zo, ko kuna so ku yi latti ya yi muku bulala?" 


Suka diro daga kujerar suka nufo 

abincin, Sulaiman ya zauna tsakanin Hadiza da Muniba, kafadun su na gugar na juna. Ta sa murya ta ce, "Fati!" 


Ta fito sanye da hijab, da alama sallah ta idar, kallo daya Sulaiman ya yi mata ya dauke kansa, ya ci gaba da cin abincinsa. Daga can bakin kofa ta tsaya ba ta karaso cikin falon ba, son addini irin na Fati yana matukar burge Hadiza ba kadan ba. 


Ta ce, "Taho mu ci abinci in kin idar da sallar". 


Ta yatsina fuska ta ce, "Na ci tun dazu, Alti ta zuba mini". 


Don jikinta ya yi sanyi da hararar da Sulaiman ke zabga mata, bayan ita ko da gida da mota aka hada ta dama ba za ta ci abinci da shi ba, don ta ki jinin mutum mai halin GIRMAN KAI. 


To a ganin ta halin Sulaiman kenan, babu wanda ke ganin walwalar shi sai 'ya'yan shi da matarshi, duk ilimin da ya ke takama da shi a ganin ta girman kai ba hali ne da ya dace da likita ba. 

Ba ta san cewa shi ma bekenta yake gani ba. 


Hadiza ta ce, "Don me ba za ki bari mu ci tare ba? Kada ki sake yin haka". Fati ta ce, "Haka nan na saba, ba zan iya cin abinci da mutane ba". Sulaiman ya balla mata harara, "Su waye mutanen? Bakauya kawai, saboda ni ne ba za ki ci ba. Na yi kama da rubabben saurayin ki ne? Dube ta da Allah kullum da zumbulelen hijabi kamar takari, gara ma ki rage wannan zuhudun ko kya samu mashinshini, don ko ni din nan aka bani ke ko da sadaka ne ba abinda zan yi da ke wallahi-wallahi ko mata sun kare a duniya". 


Fati ta harare shi ta zumbura baki kamar ta yi kuka, ta ce da Hadiza, "Kina jin shi ko?" 


Hadiza ta yi dariya ta ce, "Rabu da shi Fati na, Allah na tuba ko mutuwa nayi ai ya yi miki tsufa, me za ki ci da dan late thirty? Sai yaro sabon jini kamar ki". 

Daga Fati har Sulaiman, kalmar “mutuwa” da Hadiza ta ambatawa kanta, ta taba zuciyar su. Sulaiman ya tsame cokali daga plate ya aje gefe yana bin Hadiza da wata irin harara da ita kadai ta san ma’anar ta. 


Ita kuwa Fati ba ta kara tofawa ba, ta koma daki tana cewa cikin ranta, “kada Allah ya nuna min wannan ranar...., Yaya Hadiza sai dai ki yi min makoki, ba dai in yi miki ba’. 


Kwana bakwai cif Sulaiman yana gida cikin iyalinsa bai je ofis ba, yana kula da lafiyar Hadizar sa. Ta fuskar shan magungunan ta a kan lokaci, hidimar ta da walwalar ta, tare da ba ta karfin gwiwa na karbar rayuwa a duk yadda tazo, yana nuna mata kaddarar da ta same ta ba ta shafi ko kankani na daga soyayyar da yake yi mata ba. 


Ta yarda, ta amince Sulaiman mai son ta ne, kuma irin mazan da da wuya a samu kamar su a wannan zamanin wajen rike alkawarin soyayya da sanin 

darajar diya mace. 


A ‘yan kwanakin ta kara samun karfin jikinta, don haka ta kirkirowa kanta abubuwan debe kewa da _ dama, wadanda a da ba ta da lokacin su, kamar karatun jaridu da mujallu, “browsing’ da kuma kasancewa full-time da ‘ya'yanta suka kara shakuwa. 


Abu na hudu da take ganin zai taimaka ainun wajen debe mata kewa shi ne, rubuta tarihin rayuwar ta a matsayin story-writing cikin harshen Hausa. 


Da Sulaiman ya fahimci damuwar Hadiza ta ragu da 80%, sai ya samu kwarin gwiwa da jarumtakar fuskantar aikin sa. Ya koma aiki ranar monday cike da tausayin Hadiza, yana mai tuno lokutan zirga-zirgar su cikin asibitin don ceton al'umma, da matsalar ta mai magantuwa ce ba ya tsammanin in zai rasa duk abin da ya mallaka zai gaza wajen nema mata magani. 


A wani bangaren kuma yana tunanin shawarar su Dr. Ruth ne da suka ce 

Hadiza za ta iya komawa aikin ta a haka. Da ya tuntube ta, ta nuna ba ta yi naam da shawarar ba, don ba ta yanke kauna da rahmar Ubangiji ba, za ta zauna a gida ta yi zaman aure, wanda a da ba ta yi ba. Ta ga shi kuma wace irin riba ce a cikin sa, tunda ta yi aikin, ta ga ribarsa da rashin ribar sa? A wautar Hadiza, tunda wannan lalura ta same ta shikenan Sulaiman ya daina sha'awar ta, wato ya daina mu'amalar aure da ita, tunda ta nakasa ba ta da abin da za ta ja hankalin sa. Ba ta yi la'akari da cewa soyayyar ta a cikin jinin Sulaiman take ba, ba’a abun jan hankali ba. 


Kwata-kwata sati biyu cur da fitowar ta daga asibiti, sai labari ya sauya, Sulaiman soyayya har ta fi ta baya, kamar wanda ya je ya kara yin course a kan (lobe-making). Watakila da da hali da ya tsaga kirjinsa ya sanya ta a ciki, mai yiwuwa sannan ne zai zamo (contented). 


Sai da komai ya lafa ya fahimci 

Hadiza kuka take, ba kuma kukan komi take ba, ....kukan rashin yarda da kai ne. 


Amma shi duk sai ya rikice, kukanta da hawayen ta ba karamin daga mai hankali ya yi ba. 


Ya tarairayo ta ya dora a kan kirjin shi, cikin sassanyar murya yake tambaya, "Did I hurt you Hadizahh?' Ta girgiza kai, cikin shesshekar kuka ta ce, 


"Sulaiman kai ne?" 


"In bani bane wane ne?" 


Sai ta yarfar da hawaye da hannun 


daman ta, ta ce, "Ni dai ka kara AURE!" 


Sai ya janye jiki daga jikinta cikin mutuwar jiki da sagewar gwiwa, "Kafin in baki amsa Hadiza, ko in bi umarnin ki, ina so in san mene ne dalilin ki na cewa hakan?” 


"Saboda Hadizar da, ba ita ce yanzu ba, wannan nakasasshiya ce, ba ta cancanci wannan dimbin soyayyar 

ba". 


Ya dade yana kallon kyakkyawar fuskarta a dan hasken asubahi da ya soma keto shara-sharan farin labulen dakin, kamin ya yi murmushin takaici ya zauna sosai ya ba ta baya. 


"Hadiza tafiyar ki ce ta sa na aure ki? Ko ko yanga da kwarkwasa kika yi min na ji ina son ki?" 


Ta girgiza kai, "babu ko daya. Amma son da nake maka Sulaiman, ba zai barni in kware ka ba, idan ka ci gaba da zama dani ni kadai, na kware ka, a matsayin ka na _ lafiyayye kuma cikakken namiji. Idan ka kara aure zan ji dadi, zuciyata za ta sake. A kalla ina da tabbacin baka cikin kwaruwa, amma yanzu sai nake ganin, na kware ka........ " 


Ya daga mata hannu ya ce, "Ya isa, ya isa Hadiza...." Ya ma rasa me zai ce don takaici, sai ya karkada kai ya fita ya bar mata dakin. 


Kwanaki uku suna kan wannan takaddamar. Hadiza ta dage ta ja tunga a 

kan bakanta, in ya yi fushi sai kuma ya sauko ya yi dariya don mamaki. Ba ya son duk wani abu da zai bata ranta a dai wannan lokacin da_yake angwancewa da kuma yin la’akari da halin da take ciki. 


Don haka a rana ta biyar da ya ga ba zai iya jure wannan horon da ta tsiri yi mishi ba, don ba shi da juriyar a wannan fannin ta inda take samun weakness din sa kenan. Sai ya cafki hannayen ta ya langabar da kai kamar karamin yaro, idanuwan nan sun juye sun rikide zuwa........ 


Ya ce, "Hadiza na baki wuka da nama, ke ce mijin ke ce matar, ki zabo min duk yarinyar da kika ga ta dace dani, don bani da idon kallon wata diya mace, tun daga lokacin da Allah ya mallaka min ke......" 


Ta cira kai a hankali ta dube shi, sai ya ba ta tausayi, don numfashi kanshi a wahale yake furzar da shi da sauri da sauri. Ganin yadda jidalin ta ya ramar da shi kwanaki biyar kacal, sai ta kara 

jin tausayin sa. 


Amma jan ajin mu na mata, sai ta balla masa harara wadda in ka lura ba komi ne cikin ta ba face tsananin son mijinta da matsanancin KISHI, ganin daga karshe ya sauko ya bi ra’ayinta kamar yadda take so. 


Kamar ta yi kuka ta ce, "Nice ma zan nemo maka matar? Ashe you are not serious...!" Ta juyar da kai, sai ga hawaye sharrr! Sun zubo a kan kundukukin ta. 


Kiris ya rage dariya ta kubce masa, amma ya danne kada ya kara laifi. A gicciye ba tare da ya dube ta ba ya ce, "Wai ko a cikin student din ward din ku, irin ‘yan yara-yaran 'yammatan nan? Ko rikakkun 'yammatan likitoci irin su Dr. Surayyah". 


Haushi ya kama Hadiza, don ta lura ya mai da abin zolaya. Ta yi shiru ba ta ba shi amsa ba. 


Ya rungumota ta baya, ya dora kan shi a kafadun ta, yana sakin ajiyar zuciya mai nauyi. A sanyaye ya ce, 

"Ko kin daina sona ne Hadizahh? Kike neman kai dani? A da ko kallo na wata ta yi, kallon da bai yi miki ba, sai kin kwana bakya yi min magana, amma yanzu duk kin daga hankalin ki wai in yi aure. Which mean....... na gundire ki.... kina neman mataimakiya don ki huta..... 


Ni ina ruwana da wasu kafafun ki tunda ba su nake aure ba? Inda nake aure zam-zam yake. Da aka yi accident din ma, kamar an kara masa armashi. Kafafu? Ni ba ina da su ba? Kuma ba ina daukar ki dasu ba? To meye damuwar ki? 


In gaya miki gaskiya, ba zan iya sharing kaina ba, saboda ina da kyama, ba kowacce mace zan iya hada jiki da ita ba. Babu, ban taba ba, bana fata, kada ki tursasa ni, don ba zan iya ba, ba zan iya adalci ba. An ce kuma in ba za ku iya adalci ba, to ku zauna da daya. Amma in kin gwammace ranar kiyama in tashi da shanyayyen barin jiki, all the same, sai in auri Surayyah! 

Kinga daga nan sai ku kara dankon zumunci........ Ta ture shi da sauri, duk da jikinta ya yi sanyi da maganganun sa, ta tabbatar iya gaskiyar shi yake fadi, don shi bai fadin abin da ba haka bane a zuciyar shi. Don kaji dadi, ko don ya faranta maka. In haka ne kenan Sulaiman da gaske za ka iya auren Dr. Surayyah?" Sai hawaye suka zubo. 


Magana take a zuci, ba ta san cewa a fili ta yi ba. Ya sauka daga gadon ya zauna dabas a kan kafet, ya dauki hannu ya rafka uban tagumi, "Ni SuJaiman na shige su, duk yadda na yi, ban iya ba. To ki fadi yadda kike so, ni kuma mijin ta ce ne!" 


Idon ta fal hawaye ta dube shi cikin ido, abin da bata yi sai rana ta kure, "Ka gaya min gaskiya Sulaiman, Surayyah kake so?" 


Ya yi murmushi ya shafi siraran lebbansa, "Ya ya ba zan so ta ba tunda tana son ki, tana son 'ya'yana?" 


"Ni ba wannan son nake nufi ba........ 

Ya mike tsaye ya bata baya zai fice, "Koma wanne kike nufi shi ne, yarinyar nan rikicinki ya ishe ni, son ta nake na soyayya, soyet. Ki yi kulikulin kubura dani, ko ki yi ta kuka, har hawayen ya kare........ " 


Duk da kuka take ba ta san sanda ta yi dariya ba, ganin kuma ya dawo ya cafko ta yana son a sauya hirar da irin wacce ya fi so ayi, mai ma’ana da tsayawa a zuci, hadi da dimbin lada. Ba ta da zabi (she habe no choice) ban da ta rungumi mijinta, mai son ta, mai kaunar ta. Ta nuna mishi son shi kawai ya sani, bai san nata ba. Duk hasashe take, amma ita ma ta san ba za ta iya raba Sulaiman din ta da kowa ba. 


2K OK 


a wannan Sulaiman ya kashe bakin Hadiza da maganar ya kara aure, saboda ita ta nakasa. Don ta san cewa zai yi zai auri Dr. Surayyah, ita kuma in da abin da ta tsana ya fito daga bakin sa, to bai wuce wannan furucin ba. 


Surayyar ba ta watsar da Hadiza ba, ta kan zo in ta samu sararin aiki kuma suna yawan yin waya. Tayi-tayi Hadiza ta koma aiki in ya so sai Fati ta dinga kula da zirga-zirgar ta amma ta ki. A ganin ta ita Fatin zaman ta kenan ba za ta yi nata auren ba? Ko ko haka za ta karar da rayuwar ta wajen hidimar ta alhalin bata kai ga cimma komai a rayuwa ba? 


Gara ita ta kai ga matakin da duk dan adam ke burin samu; tayi ilmi, tanada kwali, tayi aure, ta hayayyafa. Don ta zauna gida a halin yanzu babu komi. 

Ta ce, "Surayyah mune bamu gane ba, ko da yake mu namu aikin mai tushe ne daga addini. Amma ba abin da ya kai mace ta zauna a dakin mijinta ta yi biyayyar aure dadi da kwanciyar hankali, amma ina amfanin da auren ki da mijin ki da 'ya'yan ki amma kin watsar dasu kin barwa mai aiki kullum kina titi, bayan mijin ya tsare miki dukkan bukatun ki na rayuwa?" 


Surayyah ta ce, "Ke din ce dai kawai kin yi sa'a Hadiza, amma ba ko wadanne maza ne irin Dr. Sulaiman ba". 


Kishi ya motsawa Hadiza ta hadiye shi mukut, amma ta san Surayya gaskiya ta fada, Sulaiman is unikue, akwai wani simpleness a tare da shi wanda maza da yawa basu da shi. Hadiza ba ta samu kwanciyar hankali ba sai da Dr. Surayyah Yahya ta kawo mata katin auren ta da Dr. Bashir Bunza, cike da shakiyanci ta nunawa Sulaiman. Ya karanta ya ciji yatsa, "Shege Bunza, ya kasa ni". 

Ta kyalkyace da dariya ta ce, "Eh, to kai ne ka tsaya sanya". 


Ya harare ta da idanun kauna, "Haka ma za ki ce? Bayan ke kika kashe min gwiwa, ai da tuni na karkata hula nasa kai, wallahi da ni zan kasa shi". 


Ta sake yin dariya ta ce, "Oho dai, sai abi wani sarkin ba Ado ba". 


2K KK OK 


A sabar ce sassanya mai dauke da wani irin lullumi mai sanya nishadi a zukatan dan adam, ana saura kwana biyar a kama azumin watan Ramadan, kamar kowacce asabar din karshen 

wata. Dr. Sulaiman ya zuba 'ya'yan shi a mota suka nufi Bakori ainihin gidan iyayen shi kamar yadda suka saba, can za su wuni, wani zubin har yamma ko dare. To yau ma hakan. 


Gidan ya rage daga Hadiza sai Fati, don Alti ta je kauyen su Kukawa ganin gida za ta yi sati biyu tunda yaran ma cikin hutu suke. Fati ta tura Hadiza_ kitchen kamar yadda ta bukata, ita tana girki Hadiza na mata hira. 


Ta ce, "Fati yau shekara guda cur da faruwar al'amarin nan, nayi-nayi ki kara neman wani admission din amma kin ki, kina nufin haka za ki yi ta zama kina yi min bauta ba karatu ba aure? In don nice wallahi bana cikin matsala a halin yanzu I can take a good care of myself (zan iya kula da kaina) ko daa ce ni kadai ce a cikin gidan nan". 


Fati ta sauke tukunya ta dora wata, ta yarfar da hannu don zafi. Sannan ta dubi 'yar uwarta, "Yaya Hadiza ba zan iya barin ki ke kadai in tafi makaranta 

 


Post a Comment for "YAKANA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...