WANNAN RAYUWAR CHAPTER 12 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WANNAN RAYUWAR CHAPTER 12

WANNAN RAYUWAR CHAPTER 12

- - Post a Comment

 WANNAN RAYUWAR CHAPTER 12Karfe uku da Rabi an gamai Mata kwalliya amarya tayi kyau cikin peach kala material Wanda akai wa Dinkin doguwar riga sai mayafin kayan da aka dauro Mata a ka aka makele shi. Shigar Tai Mata kyau Kuma Bata nuna tsiraicin ta ba Dan dogon hannu ne Kuma ta bude. Su kansu masu makeup din Basu ta kwalliyar da ta burge su kamar ta Ummu ba. Tayi kyau har ba a magana.+


Sallah tayi tana zaune aka ce anzo daukar ta lokacin hudu da kwata. Mai makeup din da kanta ta rakata har bakin wajen. Wata sabuwar mota ta gani fara tas a wajen tsayawa sukai zata Kira number ya bude motar ya fito.


Sanye yake cikin milk din shadda wacce take kyalli ta Masa kyau ya sa bakin takalmi sau ciki ya daura hula Mai kyau da tsada a Kansa. Hannun sa daure da agogon azurfa sai zuba Kamshin yake.

Tin da ta daga Kai ta kalle shi Bata Kara dagowa ba Dan yai Mata kyau ba kadan ba. A hankali ya karaso ya kamo hannun ta. Suka wuce wajen mota.


Shiga tayi Shima ya shiga sai ya tsaya kallon ta.

"Baby Mie Kinga yadda kikai kyau kuwa!"


"Ka fini kyau Yaa Muhammad!"

"Wa ya fada miki ban taba ganin make up din da Tai kyau kamar Taki ba. Komai naki da ban ne Habibty nah."


Murmushi tayi yazaro waya yai musu picture ya nuna Mata yace

"Kinga fa?"


Amsa tayi tana kallon yadda sukai kyau suka Dace da juna. Mika masa tayi yace

"Ibrahim Kai mu Ai Mana pictures kan mu karasa wajen!"


"To Yaya!"

Yace

"Ina yini Anty?"


"Lafiya Lou! Ya kake?"

"Alhamdulillah!"


"Masha Allah!"

Ya tada motar suka bar wajen. Gun hoto ya kai su mai kyau da tsari nan akai musu wajen kala goma aka turo masa sannan aka basu copy din suka fita.


*

Karfe biyar suna compound din wajen har an fara lectures. Anty Zainab ce ta karaso itama taci kwalliya cikin wani rantsatsen less tayi kyau sosai. Motar ta leka tana ganin Ummu ta saki mutmushi tana godiya ga Allhah.


Fitowa sukai akai musu jagora zuwa wajen da aka tanadarwa amarya da ango zama sukai aka daura faga inda aka tsaya a lecture din. Lecture ake mai ratsa zuciyar mai sauraro akan aure da biyayya ga miji. Kowa yai shiru yana sauraron lecture din.


Gefe na kalla naga tawagar su Mamah ce da su Rukayya da Sailuba sun ci kwalliya sun cakare ba laifi sai buda hanci suke gaban su plate ne na abinci sai bowl na pepper soup dayan kuma snack ne da lemo da ruwa an ajiye musu kowa abinda ke gaban sa kenan.


Can kuma su Umma ne da wasu daga kawayen ta suma sun ci kwalliya mai kyau kowa da mayafin sa akai. Sai gefe kuma dagin Abba da Umma ne sai wasu daga kawayen Ummu tin na isilammiyya har da wanda sukai university ma. Daya bangaren kuma dangin Hajiyar Muhammad ne da abokan sa daga can gefe. Kuma kowa an ajiye masa abincin sa a gaba.

Sannu a hankali kuma aka fara rabon kayan da Anty zainab ta bayar ayi. Shima dai lemo da ruwa ne a jakar sai cake da springroll da donot sai memo da aka rubuta suna  su da kur'ani da jaka. Kowa haka aka dinga bashi.

STORY CONTINUES BELOW

Daga wannan malamar ko malamin ya gama wani zai amsa yayi kuma sosai aka karu dan sun kawo hadisai da ayoyi na hujja ga abinda suke fada. Karfe shida da arbain aka tashi saboda ana kiran magariba. Karasawa sukai Ummu ta gaida Hajiyar Muhammad sannan suka je aka gaisar da Ummah.

Wajen Mamah suka karasa Rukayya na ganin sunyo wajen ta mike ta bar wajen zuciyar ya na bugawa dan tinda taga Muhammad taga ya canja ya kara kyau da girma sai zuciyar ta ta karye. Gaisawa sukai suka bar wajen ya nufi masallaci itama masallacin mata taje tayi sallah. Sai da suka idar sannan ya kira ta dan zai mai da ta gida kan azo kai amarya.

Karfe takwas suka karasa gida ta bude mota zata fita yace

"Baby!"

Juyowa tayi yai mata murmushi itama murmushin tai masa ta fita ta shige gida. Tana shiga ta tadda Anty Zainab a dakin su. Tana hada mata ruwan wanka. Tana fitowa tace

"Yauwah shiga kiyi wanka dare nayi Ummu!"

Kayan ta ta cire ta shiga tai wanka ta fito ta shafa mai. Hoda kawai Anty Zainab ta shafa mata sai magic lipstick wanda in an saka yake canja kala sai kwalli. Tai mata turaren wuta na musamman sannan ta bata kayan ta wata atampa ce Red wacce akaiwa adon red da blue. Ta saka ta dauko mata laffaya blue kala itama ta saka. Ta dauki flat shoe blue ta saka tai mata wanka da turaruka kala kala sannan ta hade mata kaya ta tas. Sallah isha'i tayi sannan ta kama hannun ta suka nufi dakin Mamah.

Mamah na zaune da su Rukayya suka shigo. Zainab tace

"mama tazo miki sallama"

"To Allah kiyayye!"

"Amin!"

Ta kamo hannun ta suka fita. A dakin Abban suka samu Umma. Zama sukai Abbah yana kallon Ummu fuskar sa dauke da farin ciki yana fadin

"Alhamdulillah!"

Gaishe shi sukai ya amsa sannan yace

"Yanzu nake magana naga har takwas da rabi ba akai ta ba."

"Wallahi Abbah yanzu muka dawo ne amman ai an gama sai tafiya motoci ma suna waje."

"Masha Allah!"

"Ummu duk abinda zan gaya miki na riga na fada miki su a bayabsai dai kawai in kara fada miki kalmar da zaki rike ta a rayuwar ki wato Hakuri mai hakuri shike da riba a komai. Ki zama mai hakuri da biyayya ga mijin ki ina alfahari dake kuma zan ta alfahari dake. Allah ya baku zaman lafiya yayi miku albarka Allah kema ya baki masu miki biyayya"

"Amin !"

Suka amsa sannan Umma tace

"Allah ya kai ki lafiya ya bada zaman lafiya Ummu!"

Rumgumr Umma tayi tana fadin

"Umma ki yafe min!"

"Baki min komai ba Ummu Allah miki albarka."

Gaban Abbah ta karasa zata durkusa ya dago ta ya rumgume tana fadin

"baki min komai ba Ummu Allah miki albarka."

"Amin!"

Ya kamo ta a haka suka fita ya saka ta a motar da za'a dauki amarya. A motar Daga kanwar Umma sai ta Abbah. Anty Zainab kuma a gaba haka suka tafi Ummu sai kuka take suna ta lallashin. Ta.

Duk wanda yaje yaga gidan sai dai kaji yana sa albarka da addu'ar Allah bada zaman lafiya. Haka aka kai ta dakin ta akavzaunar sukai mata nasiha sannan suka taho.

Kasancewar ba wasu kawaye ne da ita ba ya rage Anty Zianab ce kadai. Gyara gidan ta kara ta sakabturaren wuta sannan ta kira Muhammad yace gashi nan yana hanua. Mikewa tayi tace

"To Ummu ni zan tafi."

Da sauri Ummu ta mike ta rumgume Anty tana kuka tana fadin

"Anty kinyafe min ina bata miki."

"Baki min komai ba Ummu ina alfahari dake Allah yai miki albarka ya baki zaman lafiya."

"Amin."

Ta jata ta zaunar akan gado ta fadin

"Kiyi biyayya sannan kiyi duk abinda na saka kaki kinji. Allah bada zaman lafiya."

Ta mike zata tafi tace

"Anty ki tsaya ya shigo."

"A'ah Ummu ai yana hanya yanzu zao karaso kinji."

STORY CONTINUES BELOW

Kai ta gyada ta mike tace

"Na tafi."

Ta fita kuka Ummu take tna addu'a a cikin ranta kawai.


*

**

***

****

*****

******

*******

Ranar walima.

Karfe biyu su Khaleel da Sakina suka zo. Da aka shiga da ita wajen su Hafsa ta ganta sai kanta ya kulle. Basu jima da zuwa ba Ahmad ya dire duk suna tare da Muhammad a sashen sa.


Kan lokacin walima yayi. akai mata makeup mai kyau. Amarya ta saka ash kalar less mai ado da maroon kalar zare ta saka alkebba tai kyau. Wajen da aka tanada dan ita aka kai ta aka zaunar.

Muhammad ma yasha shadda Ash kala sai kyalli yake gefen maza ya zauna. A haka aka yi taro mayan malamai sukai wa'azi sosai jikin kowa yai sanyi na wajen.


Sai gab da magatiba aka tashi anci an sha an raba gift da duk wanda yazo. Kowa ya tafi dan yin sallah. Fauziyya na idarwa kanwar Ummi ta shigo ta sa tayi wanka. Wasu sabbin kaya aka kawo mata ta saka farar atamfa ce mai adon golding. Haka alkebbar ta ma fara ce da adon golding tai kyau. Aka dauke ta aka tafi da ita wajen Ummi da Abbi. Nasiha sukai mata sannan aka shige da ita sashen su.


Ginin kadai abin kalla ne dan ya tsaru kuma an zuba komai mai kyau da tsada. Dakin ta aka kai ta aka zaunar sannan suka tafi suka barta. Sai Sakina da Hafsa a wajen ta.


Karfe tara ango da abokan sa da Khaleel da Ahmad suka shigo.  Nan aka danyi barkwanci akai addu'a sannan sukaiwa Amarya da ango fatan alheri suka tafi tare da Sakina da Hafsa.

A kofar part din Ummi suka tsaya suka sha hirar su. Sai goma sukai sallama kowa ya tafi dan kwanciyya.

*

Muhammad na rufe kofa ya juyo ya dawo. Dago Fauziyya yayi ya yaye mata mayafin yace

"Su Ummi duk sun mai da min mata sabuwar amarya ni dai kada kiji kunya ta kada ki manta munyi watanni da tarewa."

Ya fada yana rumgume ta.


Kai ta make tace

"Ai kuwa dole duk abinda ake a ranar amarcin mutum a sake min."

"Ke kici tudu biyu kenan."


Kai ta gyada. Daukar ta yayi yace

"Baki da matsala muje muyi sallah mu sake godiya gareshi sai kuma na ciyar dake daga nan sai kuma!"


Ya kanne mata ido daya. Ta shafa kansa suka shiga alwala tayi suka fito sukai sallah suna idarwa ya dauko naman da suka shigo dashi a baki ya bata hayan sun gama ya shiga suka wanke bakin su. Sannan ta fito ta canja kayan baccin ta.


Shima bayan ya saka ya hau gadon. Ta juyo tana kallon sa yace

"Kashe mana fitilar."


Kashewa tayi ta nufi gadon ta haye kan sa. Rumgume ta yayi yana kissing goshin ta. Yace

"I love you Baby!"


"I love you more."

"I need you."


Shiru tayi sai tace

"Nima."


"Da gaske?"

Kai ta gyada yace

"Baby wallahi ina bukatar ki."


Kansa ta kama tace

"Ai ni taka ce!"

"Da gaske?"


Kai ta gyada. Nan ya hade bakin su. Daga haka ya fara romancing nata tana maida masa da martani. A haka har ya raba ta da komai na jikin ta shima haka. Tin daga yaddavtaji yana aika mata sakonnin da bata taba jin irin su ba jikin ta ya fara sanyi. Dan ta yadda yana matukar bukatar ta bama yadda taga yana ta rawar jiki ido kawai ta lumshe wani ta taya shi wani kuma ta share. Lokacin da taji yana laluben inda zai shiga sai da abun ya bata mamaki domin ta yadda da gaske Muhammad bai san taya ake abun ba amman cikin hikima da ilimi ya nemi hanyar sai da ya gane sannan ya fara addu'ar saduwa da iyali.


Ido kawai ta runtse dan tana tuna ranar da Kamal ya fara raba ta da mutumcin ta lokacin bata san ma yanayi ba saboda maganin da ya saka mata. Wasu hawaye ne suka zubo mata. Jin yana kokarin shiga wajen bai bashi dama ba yana ta kara dannawa sai ya bata tausayi. A haka da kyar ya samu ya danna wanda daga ita har shi sai da suka saki wani ihu ita na azaba shi kuma da dadi.


Yana shigar ta ya saki wata ajiyar zuciya nan ya fara having sex da ita. Yi yake yana jin sa a wata duniya ta daban da bai taba shigar ta ba. Dan ya kasa jin ya hakura da ita. Sai da ya dauke wajen awa uku yana abu daya da kyar ya samu ya zare jikin sa ya rumgume Fauziyya wacce take kuka. Shima kukan ya sakar mata domin abun da yaji ya matukar kashe masa jiki domin bai taba zaton samun abunda ya samu ba. Sai kuma ya hau tambayar kansa anya da gaske Fauziyya ta taba bin maza kuwa domin shi a yau ji yayi kamar a leda ya bare ta bama da yadda ya shige ta.


Fauziyya ganin yana kuka sai ya kara karya mata zuciya kila yana kukan bata kawo masa budurci bane dan haka sai ta kara sakin wani kuka. Cikin tashin hankali ya matso yana fadin

"Innalillahi wainna illahir rajiun Baby menene kike kuka ko ban miki bane? Ko ban kai yadda kike so bane?"


Kai ta hau girgizawa ya dago ta ya rumgume yana fadin

"Fada min kukan me kike?"


"Muhammad ina kuka akan dalilai da yawa na farko kai kukan me kake?"

"Kukan farin ciki na samu abunda ban taba zaro ba dan Allah Baby ke ba virgin bace? Ni dai wallahi ji nake a budurwa na sameki."


Sai ta kara fashewa da kuka. Hankalin sa ne ya tashi yace

"Menene Baby me kuma nayi ya saki kuka?"


Kai ta girgiza tace

"Ina kuka na yau zakayi danasin aure nane."


Hannu ya daura a bakin ta yana fadin

"Ba zan taba danasani ba. Fatana ki zama uwar ya'ya na har abada mu hadu a aljanna cikin gida daya."


"Ina son ka My Honey love."

"Nima ina son ko Baby."


"Yau naji abunda ban taba ji ba. Having sex with you once yasa na samu nustuwar da ban taba samu ba yasa naji dadin da ban taba ba. Dan Allah kada ka barni dan Allah kada ka guje ni."

"Ba zan taba ba Baby ki kwantar da hankalin ki kuma ni ji na nake na sameki a budurwa dan Allah ki daina tuno da abin baya."


Sai kawai ya fara kissing nata ta ko ina itama nan ta fara mada masa da martani. Nan suka kara komawa ruwa. Kiran sallah shi yasa suka tsagaita ba dan sun gaji ko sun koshi ba.


Daukar ta yayi sukai bandakin su wanka sukai sannan ya fito sukai sallah dan har an idar da sallar. Suna idarwa suka koma gado.

Washe gari da safe kan su tashi an jere musu kayan break. Sai karfe goma suka tashi tare sukai wanka makale da juna. Shi ya shirya ta suka fito sai da suka karya. Falo suka dawo suka zauna. Ta kalli Muhammad tace
"Kai na yana duhu har yanzu!"+

Ya kamo hannun ta yace
"Na sani Baby."
Sai yai shiru can yace
"Da farko dai ina mai baki hakuri da rashin fada miki asalin wanene ni!
Na duba na hanga na hango a rayuwar nan ba a fiya so dan Allah ba sai in kana da wani abu ko kudi,  kyau,  mulki da sauran su.
Tin ina makaranta na gane haka domin kyau na yasa da yawa yan mata ke so na. lokacin da aka san wanene ni baki ga yadda yan mata ke hauka akai na ba. Ni kuma sam Allah bai dauran son su ba ko kadan mace ma bata damen ba kallo bata ishen ba.
A haka na gama karatu na wanda a lokacin da su Ummi suka farai min zancen aure sai ya kasance zaba min suke saidai kawai suce naje naga yar wane? Ko yar wancan? Duk yayan masu kudi ne ko mukani. Wanda da naje kan na yaba sunin waye ni suke aminta ni kuma abinda bana so kenan na fiso a soni a yadda nake ba a matsayi na na dan wani ba."

Yai kissing hannun ta yace
"Na farai miki bayani ban fada muku asalin wanene ni ba ko?
To ni Muhammad ni kadai ne da namiji a wajen Abbi wanda Abbi shine sarkin wannan garin namu ana min lakabi da Yarima mai jiran gado. Tin asali ina da sanyin hali abin duniya bai damen ba wanda hakan yasa bana daukar kaina a matsayin wani. Wannan ya kara sa mahaifina ke sona da alfahari dani.
A makaratun ya'yan talaka nai karatu har na gama na fara jami'a ban fita waje ba a kasa ta nayi cikin garin mu. Bani da abokai dan ban fiya son ba saboda da yawa ba sa zama dan Allah da mutum kana zaune dasu ne suna cin dundunuyar ka. Aboki na basu wuce daya zuwa biyu ba suma ya'yan yan uwa ne sune kadai zance miki abokai na."

Ya dago ya kalle ta yace
"To ni a lokacin da naga haka shine na nemi Ummi nai mata bayani ta gane wacce irin mace nake so. Dan bana son a soni dan ni waye ko dan mahaifi na wannan shine yasa na taho garin ku.
Watana uku a garin ku ina bulayin neman matar da zan aura dan Ummi ta bani shekara tace in ban fitar ba kowa ta samu zara aura min.
A wata ukun nan na hadu da yan mata wanda wasu in na tsayar wulakanci suke min sun rainani da sauran su.
Wata rana ina zaune akan layin ku naga fitowar ki da hijab har kasa daga kallo daya zuciya ta, ta kamu da son ki tin daga ranar na fara bibiyar rayuwar ki na samu tarihin gidan ku da abinda ba zaki zata zan sani ba domin har Kamal sai da na shigewa na san halakar ku dashi.
Wanda farkon fara magana ta dake lokacin kika fito duk da baki tsaya munyi magana ba amman fuskar da kika bani kadai ya kwantar min da hankali. Wanda daga lokacin ban kara saki a ido ba har na lokaci mai tsa6i kuma hakan bai hanani nemanki ba har kika dawo nazo wajen ki da soyayya ta.........."

Ya numfasa yace
"Kinji komai duk halin da ake ciki Ummi ta sani amman ban fada mata halaiyar da na sameki a ciki ba."

Ta sauke ajiyar zuciya ta shige jikin sa tace
"Tayaya akai Baba ya yadda da maganar auren mu."
"Kamar yadda na fada miki na bibiyi rayuwar ki sosai anan na gane matsalar Baba ba auren ne baya so yayi muku ba kudin da zai kashe ne wannan yasa da naje neman auren ki na nuna bana bukatar komai wannan yasa ya yadda ya aminta."

STORY CONTINUES BELOW
Kai ta kwantar a jikin sa yace
"A gida kuma na fada musu cewar mahaifin ki yana daga cikin mutanen da basa son lefe sai dai miji yaiwa yarinya kayan daki kuma baya son taron biki kinji yadda akai."

Kai ta gyada tace
"Nagode Honey Love hakika kana sona dan Allah ba dan ina da abunda za a soni ba"

"Waya fada miki. Ga abubuwan so na birjik a wajen ki da farko yadda kika tuba ya ban mamaki ya kuma burgeni. duk da wannan tsohuwar ta ban tarihin komai na tausaya miki sosai da halin da kika shiga.
Sai yadda kika amshe ni a mara shi kika rufan asiri wannan ya kara samin son ki da kaunar ki.
Kina da dabiu masu kyau Baby ga tarbiyya na gane komai da ya faru dake kaddarar kice.
Ke kyakyawa ce ga baiwa da ni'ima hakika kina da abin so Baby."

Hawaye ta fara yace
"Menene na kukan to?"
"Ina kukan farin ciki da Allah ya bani kai. Kullum tunani na tayaya zan kare rayuwa wa zan aura da zai iya zama dani. Allah nagode maka da ka shiryar dani Allah nagode maka da ka bani Muhammad a matsayin miji. Allah ka bamu zaman lafiya ka kade mana fitina ka shirya kanena."

"Amin!"
Ya rumgume ta shiru sukai can tace
"Ina neman wata alfarma a wajen ka?"

"Ina jin ki Baby!"
"Kanne na suna son aure bama Hafsa, Sakina da Halima ina son kaje wajen Baba ka nuna zakai musu komai ya yadda da auren su ni zan musu duk abinda ya dace na kayan daki da saura......"

Hannu ya daura akan bakin ta yace
"Wato baki dauken miji,  yaya,  aboki,  dan uwa ba ko?"
"Kamar yaya?"

"In xaki gane a gida nayi wasu abubuwan ne dan gwadaki Baby banyi dan bani dashi ba. Ina da halin da zan aurar da mata goma a yanzu kowacce nai mata kayan dashi abinda ya dace. Ni nai miki alkawarin zan aurar da dukka kannen ki kuma nai alkawarin kula da gidan ku har karshen rayuwa ta. Iyayen ki iyaye nane kannen ki nawa ne ba zan so su wahala ko su shiga wani hali ba. Komai kikaga ya kama ki fada min. Zancen karatun Auwal zan yi magana dan Allah Baby ki dauken a marsayin Yaya aboki da miji duk abinda ya taso ki fada min. In na taimako ne a matsayin Yayan ki zaki fada min. In na neman shawara ne a matsayin abokin ki. In na rayuwar aure ne a matsayin mijin ki kada kina dauka ta a miji kadai kina sauya matsayi na zan zama mai cika miki buri da saki farin ciki da kawar miki da damuwa. Ni dai buri na ki soni ki zauna dani ki kuma haifa min ya'ya kyawawa kamar ki."

"Dame zan saka maka? Inama na kawo maka budurci na......"
"Baby kin bani abunda yafi wannan. Kuma to me u give me your pride that is your virgin dan haka kada ki damu ki dauka kin bani shi."

Rumgume shi tayi tana sauke ajiyar zuciya kawai. Yace
"Eh Ki fada wa duk wanda ya ke son aure a kanne na su fadawa mazajen su turo ni kuma zan samu Baba muyi maganar."

"Nagode Honey Love."
Bakin ta ya cija yace
"Ba godiya a tsakanin mu."

Ta dafe bakin tana kykan karya nan ya hau lallashin ta. Haka suka  dinga tattaunawa  sannan sukaje gaishe da su Ummi da ban gajiya ga mutane gidan.

Suna gaisawa Fauziyya ta koma part din ta tare da kannen ta da cousin din mijin ta. Muhammad kuma ya tafi wajen Ahmad da Khaleel. Tare sukai sallah azahar sannan suka ce zasu tafi.
A bangaren fauziyya suka ci abinci sannan sukai sallama da Fauziyya Khaleel da Sakina suka tafi. Ahmad ma sukai sallama suka fita shi da Hafsa. Kamar kar su rabu da kyar ya tafi dai.

*
**
***
****
*****
******
*******
********
Kabir yana barin nan gidan su Sadiya ya tafi duk mood din sa ba a dai dai ba. Yana zuwa security suka tsaida shi wajen wa yazo ya fada musu sannan suka ce sunan sa. Ya fada kiran ta sukai tace a barshi ya shiga. Kan yai parking ya hango ta ta taho. Sanye take da doguwar riga orange kala ta yafa blure kalar mayafi hannun ta rike da wayar ta. Kafar ta sanye da flat shoe blue.

STORY CONTINUES BELOW
Tana karasowa ta saki murmushi tana fadin
"Barka da zuwa."

"Yauwah Dr ya gidan?"
"No mu karasa ka zauna sai mu gaisa ko?"

Tayi gaba yabi bayan ta. wani waje suka karasa inda aka kawata wajen da kayan alatu wajen shan iska ne an saka kujeru da kayan kallo har da firij. Zama yayi ta dauki waya tayi cikin gida. Kan kace me an cika gaban sa da kayan morsa baki.

Kallon sa tayi tace
"Ina yini?"
"Lafiya lou ya gidan?"

"Alhamdulillah ya aiki?"
"Alhamdulillah ya naki?"

"Same!"
Ta zuba masa lemo ta bashi. Amsa yayi ya kurba yace
"Thanks!"

Tai murmushi. Haka suka dinga hira abinsu. Sosai Sadiya take jin ta tana having fun in suna tare. Bata taba haduwa da na mijin da ya burge ta ya kwanta mata kamar Kabir ba.

Kan ya tafi Dad dinta ya dawo ta kai shi suka gaisa sannan ta rakashi ya shiga kota suka rabu.
*
Gaba daya kasa bacci yayi ranar tsananin tausayin Haluma ya gama cika zuciyar sa. a baya ya so ya cire ta a ransa amman Allah bai bashi iko ba kenan hakan yana nufin zai taimake ta yanzu ya aurenta. Shin zai iya da wanne idon zai na ganin ta abokin sa ya gama lalata da ita.

"Auzubillahi minna shaidanir rajim!"
Ya kori shaudan dake son saka masa wannan bazan tunani domin ya yadda auren Halima tamkar jahadi ne zai taimaka mata ta samu farin ciki ya ceto ta kada ta fada halaka domin yarinya ce karama.

*
Kwana biyu dukka tare suke karewa da Sadiya sosai take nuna masa kulawa.

Kwance yake akan gadon sa.Text ne ya shigo wayar sa ya fara karantawa kamar haka
"Ka daina shishigewa Sadiya domin Sadiya tawa ce wallahi sai na aure ta dan haka kama daina shige mata dan na fara ganin take raken ka."

Tsaki yayi yace
"Iska na wahalar dame kayan kara."
wayar ce ta dau kara ya dauki yaga Sadiya ce dauka yayi tayi sallama sannan ya amsa tace
"Ya kaje gida?"

"Alhamdulillah ya na baroki."
"Lafiya naji dadin zuwan ka ya sani nishadi har yanzu ina cikin farin ciki."

"Haka nake so."
"Kabir haduwa na da kai ya fara sauyan lissafi na. Ban taba jin son wani da namiji ba Kabir amman akan ka zuciya ta ta gaza hakura. Nasan ni macece bai dace na fito na fada maka ba amman wallahi Kabir ina so ka.
Lokacin da na gane haka nasha mamaki kuma nayi kuka dan ban san tayaya zaka dauka ba amman kai naga sam baka gane 8nda na dosa ba. Dan Allah Kabir kar kace baka so na."

"Innalillahi wainna illahir rajiun!"
Ya fada a rasa sam Saidiya bata da aibu kyakyawa ce ga kyan hali ga ilimi yasan zai so Sadiya amman kuma Halima fa.

"Kabir kayi shiru!"
"Am dama... Am kisan...."
Ya fara kame kame. Tai murmushi tace
"Shikenan kagi hakuri."

Ta kashe wayar. Kasa bin ta yayi ya kira sai kawai sake sake yake ta ina zai fara wa ya dace ua aura wa ua kamata ya taimakwa.

wayar sa ya dauko ya fara kiran layin Halia amman har ya kira sau uku bata dauka ba. Hajara ya kira ta dauka sika gaisa yace
"Ina Halima?"

"Tana daki!"
"Kai mata wayar."

A kwance ta sameta tace
"Anty Halima?"

Ido ta hude da sukai jajir ta kalle ta. Mika mata wayar tayi tace
"Yaya kabir zai kura."

Amsa tayi kan Hajara ta fita ya kira. Dauka tayi ta kai kunne yace
"Halima ina wayar ki ina ra kura baki dauka na.,"

"Ah haba dai gata nan fa a hefe na."
"Kuma gana general!"

"Eh!"
"Me kike to baki ji ba?"

"Ina kwance kawai!"
"Kina tinani ko?"

Kai ta girgiza yacr
"Dan Allah kada kisa damuwa zan samo mafita kinji."

"No Kabir ka kyale Isma'il kawai Abinda yai min Allah zai saka.min daman sata shari'ar sai a lahira. Ni yanzu nasan rayuwa ta ta gama.rugujewa. mutuwa ta kawai nake hukata ita ce zata zama.hutu a rayuwa ta."
"A'ah Halima bakinsan me.Allah ya tsaraiki ba kila.kina zaune Allahnta kawo.miki wani mai som naki!"

"Kayya Kabir a halin tanzu ba.mai amsa ta a matsayin Matar sa domin na gama zubar da mutunci na me zan kai masa. Nasan ko ya auren ba abinda zan tarar sai bacin rai da tsangwama. Ni nasan ba zan samu mai so na ba."
"Ki daina fada haka. Akwai masu son ki da yawa."

"Da sun ji ya nake zasu daina sona."
"Sai dai ba son gaskiya suke miki ba."

"Daman duniyar ai duk ta canja ba son gaskiya a cikin ta. Sai na dadin baki bare kuma ni da nayi wasa da damata."
Ta fashe da kuka yace
"Haba ki daina kukan nan please."

"Dole nayi kuka Kabir. Nasan kuka ne kadai zai zama abokin rayuwa ta a yanzu."
"A'ah ki bar fadar haka. Ki saka a ranki zaki farin ciki kuma zaki ji dadi rayuwa."

"Da Allah Ka daina fadan abinda nasan ba zan samu ba."
"Zaki samu Halima ni na fada miki."

"Hmmm nagode Kabir da kulawar ka sai da safe."
"Allah bamu alheri amman dan Allah ki daina kuka da tuannain nan bana so wallahi."

"Zan daina insha Allah."
"Allah ya yadda ba abinda kike bukata?"

"Babu."
"To sai da safe."

"Allah tashe mu tafiya."
Ya kashe wayar ya koma ya kwanta yana mai runtsa ido. Hakika Halima na bukatar taimakon sa. Kuma yana son Halima. Amman Sadiya fa. Yaya zaiyi da ita. In ya barta kar ta amshi Isma'il me xai yi.
Wa zai aura Halima ko Sadiya?
A bakin gate suka hadu da Anty Zainab ya fito a mota ya leka ya mikawa Yaa Suleiman hannu yana fadin
"Sannu mun gode da dawaiyya!"+

"Kar ka damu ai kanwata ce."
Ya kalli Anty Zainab yace
"Shine kika baro ta ita kadai?"

"Ko na koma ciki mu zauna tare?"
"Da dai yafi amman kuma ai Yayan mu."

Sukai dariya. Yace
"To Antyn mu mun gode Alah huce gajiya ku gaida gida sai mun zo ban gajiya."

"To muna zuba ido."
Yaa Suleiman yace
"Aci amarci lafiya."

Yai dariya yace
"Nagode!"
Sannan suka tafi ya koma motar sa ya shigar ya dauki bags din da ya shigo dasu ya kai dakin ana falo ya dire sannan ya dawo ya fara shiga da akwatin nan dake bayan motar sa.
Anan falo ya gama ajiye su sannan ya nufi dakin ta. Tana zaune rufe da fuska ya shigo bakin sa dauke da sallama. Gaban ta ne ya fadi murya na rawa ta amsa. Ya shigo ya durkusa a gaban gadon yana bude fuskar ta.
"Tsarki ya tabbata ga ubangiji da ya hallici wannan yarinya."

Ya fada a fili ba tare da ya san ya fada ba. Hakika Ummu tayi kyakyawa ce ya rasa da yaushe tafi masa kyau dan wannan kyan na yanzu wani cool ne mai ratsa zuciya.
Hawayen da ya gani a kumatun ta yasa ya dawo daga tunanin da ya tafi yasa hannu ya goge mata yana fadin
"Barka da shigowa gidan Muhammad hakika ina farin cikin da ban taba yin sa ba a rayuwa. Ina addu'a Allah ya bamu zaman lafiya yasa ni dake mutuwa ce zata raba mu."

Ya mike yana fadin
"Ki daina kuka dan gidan nan babu bakin ciki sai farin ciki insba Allahu kuma abinda kike so shi za ai miki dan haka ki daina damuwa kinji kanwata."

Kai ta gyada yace
"Yauwah!"
Yanzu taho muje kici abinci ko sai muzo muyi sallah ta godiya ga Allah."

Ya fada yana kamo hannun ta mai laushi da taushi. Falo suka isa suna shiga taga akwatuna jibge a gefe. Ya zaunar da ita yace
"Ina zuwa!"

Kitchen ya shiga ya dauko plate da cups ya wanke sannan ya taho dasu. Naman da ya siya ya juye a ciki sannan ya zuba musu lemo ya matsa kusa da ita.
Naman ya dauka yayii bakin ta dashi yana fadin
"Bismillah!"

Dagowa tayi suna hada ido tai kasa da kai ta bude bakin ta a hankali ta fara ci tana ci yana ci har suka gama sannan ya kwashe ya kama hannun ta sukai daki. Ban daki suka shiga sukai alwala suka fito ya shinfidda sallaya ya tada sallah.

Tare sukai raka'a biyu sannan ya zauna yai musu addu'a sosai ya juyo ya dafa kan ta yana mai fadin
"Allahmma inni as'aluka kharaha wa khaira ma jabalta alaihi,  wa'a'uzu bika min sharriha wa sharri ma jabalta alaihi!"

Yana gamawa ya dauke hannu yana mai mata murmushi. Nan yai mata tambayoyi akan addini game da tsarki da sauran su. Bai yi mamaki ba dan yasan wacece Ummu malama ce tana da sani sosai dan in akace kure za ai zata iya kure shi baya tamtama da wannan.

STORY CONTINUES BELOW
Hannun ta ya kamo ya mike da ita sannan ta saka hannu ya kunce mata lifayar ya rage daga ita sai riga da zanin da ta saka. Kallon ta ya tsaya yi sai ya bata kunya ta juya ta nufi gefen gado ta zauna. Yace
"Bazaki saka kayan bacci ba?"

Kai ta daga ya saki murmushi ya fara ninke mata liyafar sannan ya fara cire kayan jikin sa. Gajeren wando kawai ya bari da singlet ya nufi makunnin dakin ya kashe kwan dakin sannan ya taho ya kama hannun ta yace
"Wannan kunyar ko?"

Sai yai shiru yace
"Ummu!"

"Uhmm.. Na" am.."
Yace
"Ke ba yarinya bace haka nan nima ba yaro bane munsan menene aure ina fatan zaki bani hadin kai wajen gina rayuwa mai tsafta?"

"Insha Allahu!"
"Nagode Ummu ina son ki kuma ina Alfahari dake."

"Nima ina son ka Yaa Muhammad!"
"Da gaske?"

Kai ta gyada masa. Ya matso ya rumgume ta yana fadon
"Nagode Ummu nagode da soyayyar k,  shiyasa Abba yake fada min na samu canji mai alheri yana fada min Ummu daban ce a cikin mata domin ko a yarana na Ummu daban take ban taba zaton zaki amshi auren bazawari mijin yayar ki ba."

"Haba Yaa Muhammad menene to? Indai dan nayiwa Abbah biyayya ne ba abinda ba zan iya ba."
"Amman Ummu da can baki da samari!"

"Yaa Munammad bana kula su samari basa burge ni!"
"Nifa ina burge ki."

Kai ta gyada yace
"Fadi gaske dai!"
Jikin sa ta fada tana fadin
"Yaa Muhammad ban taba ganin mutumin da yake burge ni ba kamar ka. Kaima daban kake komai naka daban yake ina sonka ka mijin na."

"Nima ina son ki matata!"
Ya dago habar ta ya hade bakin su. A hankali yake kissing nata cikin salon da yake kashe mata jiki hannun sa ta saka a hankai ya kuncemata zanin jikin ta dayan hannu kuma ya saka ya zuge zip din rigar ya. Sannan ya zare rigar daga jiki ta. Haka ya balle bra din jikin .........................................................................
Wannan sirrin Ummu da Muhammad ne wanda suka ce na boye musu shi a matsayin siiriin su. Amman Tabbas Muhammad ya yadda da yayi dace ya kuma yadda da ake cewa mata suna suka tara ya kuma yadda da ake yawan fada masa Ummu daban take ya tabbatar da haka dan ya samu abun da bai taba zaton ko tunanin samun sa a duniya ba. Ya samu abunda bai san ana samu ba ya samu abinda ya kusan zautar dashi.

Ni'imar Ummu daban take wacce zakin ta ta kasa barin bakin sa wanda ya kasa misalta a wane hali ya tsinci kan sa wanda ya kasa sanin me ya faru shi dai yasan bakin sa yana ta sakawa Ummu Albatka.

A bangaren Ummu ma ba zata iya cewa ga komai ba domin taji maza amman Ummu yarinya ce mai dauriyya da hakuri wannan yasa batai masa raki ba aduk abinda taji haka ta barsa ya gama abun sa sai hawaye da ke zuba a idon ta kawai. Sai ajiyar zuciya da yake saukewa kawai. Amman jin irin yadda yake saka mata albarka da mata addu'a yasa taji komai ya wuce a gunta taji ko a lokacin ya bukata xata kuma bashi kanta ba zata hana shi ba.

Shi kansa Muhammad bayan ya dawo hayacinsa yaga abinda yai mata sosai ta bashi tausayi wani son ta da kaunar ta da sha'awar ta na daduwa amman ba zai iya kara kusantar ta ba dan yai mata abinda ko bazawara sai haka ya manta da sam Ummun tasa sabuwar shiga ce.
A daren nan sun raya su da farin ciki Ummu tasha Albarka kai bama Ummu ba dagasu Abba da Umma har Anty Zainab duk sun sha addu'a wajen Yaa Muhammad. Ya kuma godewa Allah. Da kyar ya tashi yai wanka ya hadawa Ummu sannan ya dauke ta ya gyara mata jikin ta yadda ya kamata. Kayan bacci ya saka mata masu dumi dan yaji yadda jikin ta ya dau zafi ya lullube ta ya zauna yana lallashin ta. Sai da tai bacci ya mike ya hau kan sallaya. Kwana yayi yana addu'a da kai kukan sa ga Allah yana godiya da ya musanya masa da Ummu kwana yayi yana saka mata albarka da iyayen ta.

STORY CONTINUES BELOW
*
**
***
****
*****
******
*******
********
Zaman lafiya suke kowa na buri da kokari farantawa dan uwan su. Muhammad sai dargwaje amarci yake san ransa domin Fauziyya batai masa iyaka dan haka ya kara son ta da kaunarta.

Zaune yake a gefen gado daga shi sai gajeran wando ko riga babu Fauziyya na ciki tana wanka. Wayar sa ce tai karaya mika hannu ya dauko. Text akai masa budewa yayi ya fara karantawa kamar haka
"Kai kuwa mai zakayi da karuwa wacce ta gama rabarwa kadangarun bariki. Hakika ka dauki jaraba dan Fauziyya ba alheri bakuma nasan ta aure kane dan kai wani ne ba dan haka ba bazata aure kaba. Ta aure ka killa dan ta kashe ka ta ci dukiya dan haka ina mai baka shawara ka sauwake maga tin wuri......"

Tsaki ya saki 6a goge text din gaba daya. Kai ya dafe fauziyya ce ta fito ta yarfa masa ruwan hannun ta da sauri ya dago. Ta saki murmushi tana fadin
"Ya dai?

Murmushi ya saki yana binta da kallo. Daure take da towel iya cinyar ta. Mai ta shafa ta shafa turare ta gama ta wuce zata gun wardrobe.
"Baby zo!"

"Bari nasa kaya."
"Amman nace bana son kwana da kaya ko?

" baby naga ba bacci zamuyi ba yanzu."
"No taho ni bacci zanyi amma kan nan sai ki ban zuma ta na sha."

Ya mika mata hannu ta karaso. Dayan hannun yasa ya kunce towel din kallon ta ya taaya yi. Sai kuma ya janyo ta jikin sa. Kwai ya kashe ya ja musu bargo.

*
Washe gari da safe yana zauna akan dining Fauziyya na tsaye cikin wani less tai kyau tana hada masa tea. Text ne ya shigo kamar jiya ana bata Fauziyya. Mikewa yayi a zafafe yana bin wayar da kallo sai ya fara dailing number amman me a akashe. Tsaki ya buga ya koma ya zauna. Fauziyya ta dago tace
"Lafiya Baby?"

"Ba komai"
"Amman...."

Hannun ta ya kamo ya zaunar a cinyar sa ya fara bata tea da dankalin tana ci. sai da suka gama suka koma falo ta kwanta a jikin sa tace
"Baby akwai abinda ke damunka!

"No Baby ba komai."
"Ka tabbata?"

Kai ya gyada. Tace
"Thats my wish."
Yai kissing lips din.
*
Tin daga ranar kullum sai an turo masa da irin wanna sakon in kuma ya kira yaji wayar a kashe. Duk ya damu dan baya so ransa yana baci yadda ake bata masa mata.

*
Tsakanin sa da Fayziyya soyayya suke sha daga ita har shi sunkara kyau sunyi haske sunyi kiba abin su. Hafsat na wajen Ummi itama tayi dumi dumi da ita.
*
Watan su daya suka fara shirin tafiya amman Abbi bai so ba Muhammad ya bashi hakuri kan abu zasuje suyi da komai ya dai dai ta zasu dawo gaba daya ya koma bakin aikin sa fatan alheri sukai musu duk sai suka ji ba dadi domin kuwa sun saba. Ummi ma ji tayi kamar tabisu. A haka suka tafi.
*
Wani katon hadadden gida aka kai su wanda haduwar sa da tsarin gidan ya wuce tunanin mai tunani babu ce kawai babu a ciki. Suna shiga kowa yai daki sa dan su watsa ruwa. Kan su fi5o har an tanadar musu kayan abincin su.
Zama sukai suka ci. Anqn falo suka baje suna hira abinsu. Tsakanin Hafsa da Ahmad soyayya suke sha sosai abinsu wanda suka dada shakuwa da juna. Hannah ba laifi in yau tai masa mutunci gobe sai akasin haka saboda kawaye masu zuga ta.

Dan yau in ta kula dashi gobe da kyar yake samun kallon arziki. Duk wannan bai damun sa shima sai ya share ta kawai. Bama da yake da Hafsa me debe masa kewa.

Bangaren Khaleel da Sakina mabsoyayya suke sha abin su kamar ba gobe. Kulawa yake bata sosai dan kullum suna tare yana kawo mata abubuwan bukata tin tana hanawa har ta daina dan fada yake sosai.

Tayiwa Anty Fauziyya magana tace ta jira ta dawo wanda jiran dawowar tata suke dan Khaleel ya kagu yaga ya mallaki Sakina

*
Yana zaune a compound din su. Fauziyya na matsa masa kafafun sa wayar sa tayi kara da sauri ya dauka sakon da akavl saba ne bai karanta ba ya hau neman layin ai kuwa yaci sa'a ya shiga. Har ya kusan tsinkewa aka dauka yace
"Ina mai maka ka shedi akan in ka kara aibata min ko yin mummunan furuci ga matata sai na sa anciremaka harshe. Naji na gani ko ya matata take ina sota kai ko a yanzu in tana bin maza ina son ta bare yanzu ta daina.
In ma so kake na sake ko wani abu kun makara dan haka ina mai baka shawara da ka kiyayi haduwa ta dani da kai koma waye"

Yaa kaiwa nan yakashe wayar. Fauziyya kallon sa ta tsaya ta kasa gane me yake nufi. Number wani dan sanda ya kira yai magana akan abunda yake fuskanta. Police din yace ya turo number. Yace
"Ok gata nan yanzu zan turo ina so ayi tracing agano waye aje a kamashi mu hadu a court kawai."

"Angama ranka ya dade."
Ya kashe waya. Fauziyya ta mike tace
"Me yake faruwa ne?"

"Ba komai!"
"Tayaya zakace min ba komai dan Allah ka fada min.

" ya zancen Sakina da kika farai min kuwa yakamata a hade ita da Hafsa ko?"
Eh har ma da Halima nake so a hade."

Shikenan ba gobe zamu gida ba sai a tattauana aji ko?"
"Eh hakan ma yayi nagode."

Ya zaunar da ita akan cinyar sa yace
"Nike da godiya da yadda ake sona da kula dani.
Ta kwantar da ka ta a kirjin sa tana mai yin murmushi kawai.Zaune yake yayi nisa a cikin tunanin sa abubuwa sun masa yawa ya rasa yaya zaiyi ya zaiyi da Halima kuma ya zaiyi da Sadiya?+

Hakika zai auri Halima ko dan taimaka mata ya fitar da ita daga halin da take dan yana tausaya mata yasan a irin wannan lokacin tana iya yin koma. Bama yai duba da karancin shekarun ta to yanzu yaya zaiyi tayaya mahaifin ta zai barta tayi aure a yanzu.

Wayar sa ya zaro ya fara neman layin Hajara. Tana dauka yace
"Hajara number wayar Yaya Hafsa nake so."
"Ok bari na turo."

"Aha ina Halima?"
"Tana daki!"

"Duba kiga me take?"
Mikewa tayi ta shiga ta same ta tana kwance tace
"Tana kwance."

"Bata wayar!"
Mika mata tayi tace
"Yaya kabir ne."

Amsa tayi tare da mikewa zaune sallama yayi wanda yasa gaban ta ya fadi. Da kyar ta daure ta amsa. Yace
"Me yake damun ki?"

"Ba komai!"
"A'ah ga muryar ki nan ta nuna damuwa a ciki. Bana hanaki saka damuwa da tunani ba."

"Tayaya zan daina damuwa da tunani Kabir?"
"Ta godiya ga Allah da dogaro dashi sai kiga ya kawo miki mafita nan take."

"Allah ya kawo min to."
"Yauwah koke fa! Kika sani ko Isma'il ya dawo yace yana son kk."

"Haba Kabir yanzu kai in yazo yace yana so na sai ka yadda!"
"To menene a ciki."

"Baka ganin abinda yai min. Bama wannan ba kana zaton Isma'il xai ga kimata in munyi auren ne nasan ba zai taba ba. Na riga na rasa kimar da ko wanne namiji ya auren zai gani a tare dani yaya zanyi ka fada min tayaya zan gyara wannan barakar."
"Ta komawa ga Allah sannan ki daina cire tsammani."

"Banda aiki sai neman gafar Allah."
"Haka nake so ina neman wata alfarma."

"Ina jin ki!"
"Dan Aah kada ki kara kuka."

Shiru tayi yace
"Kinji?"
"Naji!"

"Yauwah Allah miki albarka. Kinci abinci?"
"A'ah!"

"Why?"
"Na kasa ci."

"Ko a kawo miki wani abu ne?"
"A'ah zanci."

"Yauwah kici kinji."
"Nagode Kabir."

"No no kada kiyi wata godiya. Sai jima."
Ya kashe wayar. Ido ya lumshe yana mai sakin ajiyar zuciya.  Karar sako ne ya shigo wannan yasa ya bude ido. Number Hafsa ce.

Dauka yayi ya kira tana dauka suka gaisa yace
"Kabir ne!"

"Wanne?"
"Abokin saurayin Halima."

"Au Kabir ya kake ya gida?"
"Lafiya lou. Yaya Hafsa daman ina son na ganki ne?"

"To yaushe kenan?"
"Ko zuwa gobe ne."

"To Allah kaimh."
sukai sallama ya ajiye wayar take yaji wata matsalar ta kau. Sadiya ce ts fado masa wacce tin jiya da ta kashe waya take yaji wani iri nan da nan ya fara neman layin ta.
STORY CONTINUES BELOW
Kwance take zazzabi ya rufe ta saboda kukan da rasha jiya. Ya saukar mata da zazzabi wayar ta ce taike kara tana ji bata dauka ba jin ta katse an kara kira yasa ta mika hannu ta dauka bata damu da duba wayqr ba takai kunne tayi sallama da dashshiyar muryar ta.
"Subhanlallah me yasamu muryar taki sadiya!"

Ido ta lumshe tin da ji muryar sa ta fara jin wani dadi na ratsa jikin ta.
"Sadiya ko baki da lafiya ne?"

Kai ta gyada kamar yana wajen sai kuma tace
"A'ah."
yace
"Kunje asibiti?"

"A'ah."
"Haba saboda me? Gani nan zuwa."
Yana kashe waya ta mike zaune hawaye na bin kumatun ta na tausyain kanta.
Bai dauki minti ashirin ba yace yana compound din su. Hijab ta saka har kasa ta fita. Tinda ya hango ta yaji gaban sa na faduwa. Zuciyar sa tai rauni tausayin ta ya kamashi. Sai da ta karaso yaga yadda idon ta ya kumbura yai jajir.

Bai tsaya magana ba ya bude mata mota yace
"Shiga."
Ba musu ta shiha ya zagaya ya shiga ya tada motar. wani private asibiti suka je suka yanki card suka shiga ganin likta. Dr yai mata tambayoyi ta bashi amsa yace
"Ciwon kan kila har da rashin bacci sannan jinin ki ya dan hau ki rage tunani kinji ko ki samu hutu."

"Nagode!"
Aka rubuta magani suka taho. A fita ya ajiye ta yaje ta shiyo maganin. Gida ya maida ta. Mota ya bitada kallo yace
"Meya hanaki bacci jiya?"

Kai tayi kasa dashi yasa hannu ya dago kanta yace
"Kalli idon ki kukan me kikai?"
Shima shiru tayi ya kamo hannun ta yace
"Ki min magana mana."

Baki ta bude zatai magana sai kuka ya kubce mata.
*
**
***
****
*****
*******
********
**********
Washe gari da safe bayan sun gama komai suka shirya suka nufi gidan su Fauziyya. Muhammad ne ke driving har suka kusa wani super market ya tsaya ya shiga. Bay jima ba ya dawo ya koma mota ya zauna. Kayan abinci aka zuba a boot ya basu lada ya tada motar sukai gida.

Yana parking ta balle murfin motar zata fita hannun ta ya kamo yace
"Ke kin fa girma yanzu ji gudu fa kike ao kiyi abinda ko Halima ba zatai ba."

"Haba Baby nayi kewar kanne na fa."
"To ki tafi a hankali."

"Naji!"
Ya sake ta ta fita. Tana shiga soro ta kara ciki da sauri. Ya saki murmushi yana fadin
"Baby kenan."

Fita yayi ya kira wasu yara yasasu shiga da kyana abincin. Buhun shinkafa ne da katon din taliya,  macaroni, cus cus,  semo,  alkama da mai. Duk suka shuga. Yaba taaye  a bakin motar sa Baba ya fito. Tana ganin sa ya karasa ya duka har kasa. Fara'a ya saka yace
"Ah ashe kai?"

"Wallahi Baba ina kwana?"
"Lafiya lou ya kaka ya gidan?"

"Lafiya lou!".
" madallaj!"

Muhammad yace
"Baba daman ina son na ganka!"
"To to ina fatan dai lafiya ko?"

"Lafiya lou Alhamdulillah!"
"To ina ji!"

"Baba daman Hafsa,  Sakina da Halima ne suka fito da miji suke son suyi aure!"
"Kaji yara nawa suke da har zasu dauko maganar auren."

"Nima na ga hakan amman ganin suna so yasa na ce zan maka maganar!"
"To ni dai Muhammad ka kyale su kawai dan ban da kudin da zan aurar dasu bayan haka ma nawa suje ko sakina dake babar su bata kai sha biyar bafa."

Kai Muhammad ya gyada yace
"To Baba zancen baka da kudi a ajiye a gefe ni naji zan musu komai na aure. Sai batun shekaru. Baba menene dan an musu aure suna sha biyae naga ba laifi bane. Iyayen mu duk a nawa akai musu aure. Ko Nana Aisha shekarar ta tara fa aka aura mata Annabin mu. To suma ayi musu hakan su raya sunnar ma'aiki SAW"

"Ah to indai zakayi ai ba komai ko Hajara da kannen ta in sun shirya ai sai ayi "
"Yauwah Baba zan yi wa maneman nasu magana in yaso duk yadda mukai zan sanar maka."

"To shikenan ni zan tafi kasuwa."
Hannu Muhammad ya zura a aljihu ya zaro bandir din yan 1k ya mika masa yana fadin
"Baba gashi wannan ba yawa!"

Da sauri ya amsa yana fadin
"Madallah ai shine mai yawan. Allah saka albarka. Nagode sai na dawo."

"A dawo lafiya."
Ya tafi ya shiga motar
*
Hafsa da Fauziyya suna shiga sukai wajen Umma nan suka gaishe ta. Daki suka.shiga wajen Sakina suka manta da Muhammad dake waje. Sai can Hasa ta tuna ta fita da sauri ta shigo dashi. Gaisawa sukai da Umma da zai tafi itama ya ajiye mata bandir din 1k tace
"Haba Muhammad ka.dauke ai wahalar tai yawa."

"A'ah Umma ki sa mana albarka kawai dan Allah!"
"To Allah yayi albarka."

"Amin Umma nagode!"
Ya mike zai fita. A tsakar gida ya tsaya ya bawa dukyaran dari biyar biyar. Fauziyya tafito ta same shisukai soro. Kudi ya debo ya mika mata tace
"Name?"
"Kina gida kina bukatar kudi kar a bukaci wani abu."

"Haba Baby me za a bukata?"
Hannun ra ya kama ya saka yace
"Sai yamma ko?"

"Baby dare dai!"
"Kinsan bana son kiyi nesa daniko?"

"Baby yau dai daya. Kuma ina son naje  Wajen Baba Ni'ima."
"To ki gaishe ta."
Ya zura hannu a aljihu ya zaro kudi yace
"Ko zata bukaci wani abu!"

Ya mika mata tace
"Baby wannan ma ya isa."
"Ki amsa dai please "

Tasa hannu ta amsa tace
"To Allah dada budi. Allah kiyaye hanya."
"Amin!"

Ya juya ya fita tabi bayan sa a bakin mota ta tsaya tace
"Allah tsare to?"
"Amin!"

Ya tada motar ya tafi tana daga masa hannu. Yana fara tafiya wayar sa tai kara ya duba yaga police din da ya saka yayi tracing number ne. Dauka yayi yace
"Ya ake ciki?"
"Wallahi mun duba ba wanda yayi register ke amfani da sim din ba."

"Yanzu ya za ayi?"
"Zamu cigaba da tracing har a kamo ko wanene."

"Yauwah na gode."
Sukai sallama.
*
Fauziyya na komawa ta dauki Hafsa suka tafi gidan Baba Ni'ima. Gidan duk ya dada lalace wa ba kowa a tsakar gidan suna ta sallama har sun juya zasu tafi suka jiyo tarin ta. Da sauri suka shiga dakin wari ne ya doke su. Suka toshe hanci. Baba Ni'ima ce kwance cikin kashi da fitsari bata gane kowa dake kan ta ma.
Nan da nan suka gyara ta suka gyara wajen sannan suka nemo me adai dai ta. asibiti suka kai ta suna kai ta aka bata gado kaia farai mata karin ruwa. Sai da komai ya dai dai ta sannan ta kira Muhammad ta fada masa bai jima ba yazo asibitin. Shi ya biya kudin koami a lokacin.

Ranar tatr suka kwana Hafsat da Fauziyya. Kan safiya sai ga Baba Ni'ima tana gane su Fauziyya dab ta samu kulawa sosai. Kwanan su biyar a asibitib aka sallame su. Suna komawa suka ga An gyara gidan an saka mata gado da katifa da sauran kayan gida. Sannan aka nemo mai kula da ita za ana biyab ta kudi duj wata zata ba gyara gidan da musu girki.
Baba Ni'ima sai kuka take tana saka musu albarka. Fadi
"Take bata haihu ba amman Allah ya bata masu jikan ta. Allah suma ya basu masu musu."
Ba kalar addu'ar da basu sha ba.Duk yadda ta ji maza hakan bai hana ana kiran asalatu ta mike ba. akan sallaya ta hango shi wannan yasa ta koma da sauri ta kwanta yana ganin haka ya mike ya karaso yana fafin
"Sannu Ummu na Alllah miki albarka yasa ki gama da duniya lafiya!"+

Kai tayi kasa dashi. Yace
"Zaki sallah ko?"
Kai ta gyada masa ya shiga ya kara hada mata ruwan zafi ta kara gasa jikin ta ta dauro alwala ta fito sai da ya sata akan sallaya sannan ya fita nasallaci. Ta jima akan tana addu'a Allah basu zaman lafiya ya kau da duk wata fitina bayan ta gama tayi azkhar ta dauki alkur'ani ta fara karantawa.

Karfe shida saura ya shigo tinda ya nufo dakin ta ya jiyo ta tana karatun alkur'ani ido ya lumahe ya karaso. Ya zauna a gaban ta. Tana kai aya ta rufe tana fadin
"Ina kwana?"

"Lafiya lou Zuma ta!"
Dagowa tayi da sauri yace
"Eh mana kin bani zumar ki a jiya wacce har yanzu baki na akwai zakin ta tamkar yanzu na gama sha."

Ido ta rufe ya daga ta yace
"Taso ki kwanta ki huta ai kin gaji da yawa ga gajiyar jiya gashi na saukar miki da wata."
Sukai kan gado suka kwana take bacci ya dauke su.

Basu suka farka ba sai goma da wani abu. A tare suka tashi. Ya shiga ya hada musu ruwan wanka ya fito ya dauke ta sukai ciki sai nonnoke masa take a haka yai mata wankan shima yayi suka fito. Shi da kansa ya shirya ta cikin wata atamfa sea green da ja tai kyau dinkin riga da siket ne ta saka fashion ja ta kwalliyar ta mai kyau.

Shima ya shirya cikin sea green din shadda sukai kyau sai tashin kamshi sukeyi. Dakin ta fara gyarawa ya dauke ta ya kai ta falo yace
"Wanna ni xanyi ai!"

Ya koma dakin. Ya gyara falon ta dinga bi da kallo tana fadin
"Yanzu duk nan daki nane. Allah sarki Abbah na Allah bani ikon yi maka biyayya. Allah kara budi."

Bai jima ba ya fito ya nufi kofa ya dauko basket din da Anty Zainab ta aiko musu da kayan abinci. Anan Falo suka baje suka karya bayan sun gama ya dauke ta ya goya yace
"Muje kiga gidan ki kan muzo kiga kayanki abinda kike bukata sai ki magana a siyo ko?"

Ita dai murmushi kawai tayi. Haka ya zagaya gidan da ita tama ta yabawa ba inda yafi burge ta kamar garden wajen yai kyau da saka nutsuwa.
Sallah azahar da aka kira ira tasa suka baro garden dim. Alwala sukai ya tafi massalaci ita kuma tayi sallah anan. tana idarwa taji ana sallama fitowa tayi taga an kawo musu abinci amsa tayi ta ajiye zata shiga daki ya shigo tsayawa tayi ya karaso yana fadin
"Kinyi sallah?"

"Nayi!"
"Kin mana addu'a?"

"Na mana!"
"Me kika romar mana."

"Zaman lafiya Allahbkauda mana fitina. Ya buda maka."
Yai murmushi yace
"Amin!"

Hannun ta ya ja suka nufi wajen akwatinan saukewa ya hau yi. Akwatinane mai set goma yai kyau nan ya hau bude mata kaya ne masu yawa da tsada ido ta zaro tace
"Wai kayan waye wannan?"

"Na Zuma ta ne!"
"Haba Yaa Muhammad ai wannan wahala ne sai kace ban da kaya."

"Amman ya zama dole dai nai miki lefe ko Ummu?"
"Ba dole bane Yaa Muhammad da dole ne ai Abba zasuyi magana kaga kayan da akai min a gida ne duk na kai wannan ina to ni?"

STORY CONTINUES BELOW
"Duk rabon kine."
"Amman su Abba sukaji zasuyi Fada Yaa Muhammad!"

"Kada ki damu suma ba zasuyi ba."
"Bari na kira Anty Zainab tazo ta gani sai su kaiwa Abbah ko?"
"Duk yadda kika ce haka za ai!"

Ya rufe Babbar akwati ya bude mabiyar ta wanda ba komai bane a ciki sai kananun kaya masu kyau da tsada wanda da kan sa ya siyo mata su a saudiyya. Wasu in ya dagama kunya yake bata. Yace
"Ina son wannan shigar Zuma ta."

"To zan na maka."
Haka ya dinga bude mata akwatuna tana gani na under wears na dogayen riguna takalma jaka fashion komai dai babu ne kawai babu a ciki har akai la'asar suna zaune a gaban kayan. Shi ya kai kayan dakin ta sannan ya tafi masallaci.

Itama sallah tayi tana idarwa ta dauko wayar ta kunnawa tayi taga sakonni da yawa Anty Zainab ta kira. Tana dauka tace
"Antyna ina yini?"

"Lafiya lou Ummu ya gida?"
"Alhamdulillah! Kinsan me?"

"Sai kin fada."
"Tin jiya Yaa Muhammad ya shigo da wasu akwatuna. Sai yanzu ya bude min Anty wai lefe ya hada min fa."

"Ikon Allah."
"Shine nace kizo ki kaiwa Abbah ya gani ko?"

"Eh to anjima daman zan je nai masa sallama zan biyo sai mu kai masa."
"Wai Anty har tafiya zakuyi!"

"To me zamu zauna muyi Ummu munyi abinda ya kawomu ai sai ya koma aiki ko?"
"Haka ne amman zanyi missing yaushe zaku tafi!"

"Jibi muke son mu tafi."
"Amman ai kwazo.ku yinar min ko?"

"A'ah Ummu nazo daga baya gobe gidan su Yaa Suleiman zamu mu yini."
"Shikenan sai anjima in kinzo din!"

"Allah kaimu!"
Ji tayi an rufe mata fuska tai murmushi tace
"Ai nasan kai ne!"

"Tayaya?"
" wa zai min in ba miji na ba."

Ta fada tana mikewa janyo ta yayi ta fada kansa yace
"Ina zaki?"

"Yaya baka ci abinci bafa?"
"Ni bana jin yunwa ke fa?"

"Uhmm nima haka. yanzu na kira Anty Zainab anjima zata gida zata biyo ta dauka."
"Madallah."

"Yaya nagode Allah kara budi ya saka da alheri."
"Amin Ummu amman ai hakkin kine."

"Duk da haka nagode."
*
Da yamma da zasu wuce ta biyo suka dibi kayan suka tafi. Abbah da ya ga kayan kasa magana yayi waya ya dauka ya kira Muhammad yana dauka ya hau fada yana fadin
"Yanzu Muhammad sai da ka takurawa kanka akan me sai da nace kada ka damu da cewar sai ka hada wani lefe ko?"

"Abbah kayi hakuri amman ai ina da hali shiyasa dan Allah kayi hakuri kasa albarka."
"Shikenan Allah yayi albarka ya gidan ba dai matsala.ko?"

"Babu Abba ina godiya Allah kara girma da daukaka Allah ya kara kwana."
"Amin Muhammad nagode sai anjima!£

Ya kalli Zainab yace
"Je ki kira min Iyayen naki da yan uwan ki so zasu sakawa yar uwar su albarka suma."

Mikewa tayi ta nufi dakin Mamah ta samu Rukayya da Mamah a dakin ta gaishe da Mama tace
"Mama wai kuje inji Abbah kuga kaya."

"To!"
Ta fita ta fadawa Umma tare suka shiga da su Mama suna shiga Abbah yayi gyaran murya yace
"Gashi nan kayan Ummu ne Muhammad yai mata sai da nace ba sai yayi ba amman yace yana da halin yine dan haka kusa mata albarka."

"Wai dama kiran kenan ina wani abu an tasoni"
Ta mike ta fice. Rukayya kuwa jiki a sanyaye ta dan daddaga kayan sannan ta mike ta fita. Mamah bata taba komai ba sai Anty Zaib da ke daga maga a haka ta gani ta sa albarka sai Khaleel dake ta yabon kayan yana fadin
"Masha Allah Anty Ummu!"

Haka aka gama aka maida motar Zainab dan mai da kayan gida.
*
**
****
******
*******
*********
***********
*************
***************
Ya kamo hannun ta yace
"Ki min magana mana."

Baki ta bude zatai magana sai kuka ya kubce mata. Yace
"Oh my God. Wallahi Sadiya bana son kukan nan naki jin sa nake har kasan zuciya ta."

Dagowa tayi tana kallon sa. Ya gyada mata kai yace
"Eh kina ji abinda likita ya fada kuma kema likita ce amman kuma bakya kiyayewa."

Hawaye ne ya zubo mata ya dauki tissue ya goge mata yace
"Kukan to na menene?"

Ido ta runtse tace
"Na maraici nane Kabir!"
"Kamar Ya? Ai ke kin tashi daga marainiyya. Saboda kin girma kema me rike maraya ce. Kina da aiki da.rufib asiri kukan maraincin me zakiyi?

"A jiya kadai na kara maraicin Ummi na domin da tana nan zata ban shawara akan abubuwa da yawa zata tsaya min ganin samuwar farin ciki na sannan in ta ganni a damuwa zata damu har ta kawon mafita."
"Wacce damuwa kika shiga?"

"To duk ba akan ka bane!"
Ta fada tana rufe fuska da hannu tana mai cigaba da kuka. Yace
"Akaina kuma?"

Kai ta gyada. Ya gyara zama yadda zai kale ta ya juyo yace
"Me nayi to?"

"Ban taba ganin wani da namiji da na ya burge ni ba sai kai ban taba jin son wani da namiji ba sai kai amman a lokacin da na fada maka a lokacin ka nuna baka so na. Da Ummi na na nan nasan ba zata bari na aikata haka ba sai da na aikata na fara danasi tinda ba zakai accepting dina ba gwara na bari a zuciyata ko mutuwa zanyi na mutu. Dole jiya na kwana ina kukan rashin me ban shawara da ya zanyi da soyayyar ka da kuma abinda na aikata. Hakika bansan so ba ance yana da dadi yana da wahala. Ni na yadda da wahalar sa saboda daga jiya da na fada komar sa ya jefa rayuwa ta a hatsarin da ban taba shiga ba."
Wani murmushi ya saki ya kamo hannun ta yace
"Sadiya kenan. Ni nace bana son ki?"

Kai ta girgiza yace
"To amman kika ce bana sonki."
"Uhmm ka nuna kace."

Yai murmushi yace
"Sadiya kenan. Dole naso ko waye me sona saboda nima na fada a komar da kika fada son wani abu daban. Amman ke ki godewa Allah na sani.
Sadiya ba zan boye miki ba ina da wacce nake so na aura......"

Da sauri ta dago ta zuba masa ido. Yai kasa da kai yace
"Eh ina son ta. Amman kema yadda kike so na zan baki dama sai na hada ku ku biyu na aura in har kin yadda kenan."

Kai ta hau girgizawa tana fadin
"Kana da wacce kake so ka aura. Kenan kana son ta ni kuma fa?"
"Kema haka. Domin ranar da na fara kallon ki naji wani abu a tare dake. Lokacib da muka zauna na kara sanin ke yarinya ce mai hankali da ilimi wanda duk wanda ya same ki ya gama morewa a rayuwa."

"Bana so ka soni dan wani abu da nake dashi."
"Shiyasa na fada miki a ranar da na fara ganin ki a ranar na ji wani abu a tare dake wannan ya nuna tin kan mu zauna dake kenan. Kinga kenan tin ban san ki ba na fara son ki. Hakika ba dan komai nake son ki ba domin in naso ki dan wani abu in ya gujr ya kenan zan iya rabuwa dake kenan. "

Yaja ajiyar zuciya. Yace
"Mami na ta jima tana so nayi aure ammab Allah bai ba. Ita wacce nake so ma sam bata sani ba amman nayiwa zuciyar ta da tawa alkawarib aure.
Ban taba tunanin auren mata biyu ba sai gashi a lokaci daya tunanin ya fara zuwar min.
Hakika Sadiya ina son ki kamar yadda nake son Halima dan haka in zaki yadda ni zan hada na aure ku a rana daya. Halima uwar gida ke amarya ina fatan zaki amince da haka ni kuma nai miki alkwarin muku adalci insha Allahu. Fatana da ni daku muyi farin ciki kuma mu rayu cikin aminci mu hadu a aljanna.
Dan haka Sadiya ki bar kukan akan kin fadamin kina so na. Ki cire haka a ranki kisa a ranki ni na fara fadin ina son ki kuma ki cire maraicin ki domin zan zamar miki ramkar uwa a gareki. Dan Allah Sadiya ki bar damuwa sam bana son naga wani a damuwa bare kuma masoyi na kinji."

Kai tayi kasa dashi tana murmushi yace
"Yauwa ko ke fa kinfi kyau dashu. Abinda nake son na ganki kuma dashi kenan."
"Nagode Kabir. Nagode sosai Allah ya tabbatar mana da alheri amman ya kake gani ita ba matsala in ka hadamu?"

"Babu insha Allahu!"
"To Allah tabbatar da alheri."
"Amin! Yanzu kije kici abinci kisha magani ko?"
Kafada ta make tace
"Muje tare ka kula dani naga tin yanzu ko zaka iya kula dani."

Ya bude mota yace
"Muje to!"
Ya zagaya ya bude mata ta fito ya dauki ledar magani. Daya daga ciki falon gidan suka nufa. Suna zama ta kira waya kan a kawo mata abinci. Kan kace me an cika musu gaba da kayan abinci kala kala da drinks fruits da sauran su.
Shi yai serving nata abunda take so ya mike mata ta fara ci kadan taci ta ajiye tasha magani shima tace yaci bai ci ba sai fruits da ya dan sha.
Har yamma yana gidan sai ga Sadiya ta ware kamar ba ita ba sai hira suke sha a bar su.
Sai biyar ya mike yace zai tafi tare suka fito dan zatai masa rakiya. Mota ya shiga ta tsaya tana daga masa hannu. Yana zuwa bakin gate yaga Isma'il a bakin gate an hana sa shiga. Kai ya dauke kawai ya bar wajen.

Rokar su Isma'il ya dinga yi nan daya daga cikin gatrman din yace
"Favour daya da zan maka shine na kira ta a waya in ta yadda shikenan."
"Eh naji."

Nan ya fara kiran Sadiya wacce ta juya zata koma cikin gida ta tsaya tana duba wayar ta. Dauka tayi yace
"Ranki ya dade wani ne yazo ya takura sai ya shigo ya ganki wai."

"Waye shi?"
Ta tambaya. Kallon sa yayi yace
"Ya sunan ka?"

Isma'il dake tsaye yace
"Isma'il!"
Shima ya fada mata. Tace
"Barshi ya shigo. Gani nan."

Aka bude masa gate ya shiga. Ya fito yana bin harabar gidan da kallo. Daga nesa ya hango ta ta taho tana tafiya kamar ba zata taka kasa ba. Hijab ne a jikin ta amman yai mata kyau. Blue black wanda ya kara sa hasken ta ya fito. Gaban sa tazo ta tsaya ta harde hannu a kirji. Sai tai masa kwarjini yai kasa da kai ya fara kame kame.

Murmushi tayi dan ta saba haduwa da maza irin haka wanda kallo kawai take musu suke rikicewa.
"Sannu bawan Allah!"

"Yauwah. Ina yini?"
"Lafiya lou!"

Sai sukai shiru can tace
"Lafiya kake nema na?"

"Uhmm da uhm daman daman kawai na ganki ne nake son na kulla friendship dake!"
"Dani?"
Ta fada tana nuna kan ta.

Kai ya gyada kamar kadangare. Tace
"Am sorry bana abota da namiji dan da an fara abota dasu suke canja salon ta. Ni na zata taimako ka zo nema ko wani abu da aka ce ka nace in fito. Ni zan koma ciki in ba wata maganar."

Shiru yayi ta dago ta kalle shi tace
"To sai anjima!"
Ta juya tayi ciki ya bita da kallo kamar yaje ya kamo ta.

Tana shiga falon gidan su ta fada saman kujera tana jin wani sanyi domin Kabir ya amshi soyayyar ta itama zatai aure kamar yadda kowa keyi zata samu miji nagari da izinin Allah. Tinda ita dan Allah take son Kabir ba dan komai ba dan bata san waye uban sa ba ko shi kan sa.

Ranar duk wanda ya ganta daga masu aiki har yayen ta sun sha mamakin yadda suka ga tana farin ciki.

Da dare mahaifin ta na dawowa ya wuce bangaren ta. A falo ya same ta tana kallo. Yana sallama ta mike tana fadin
"Barka da zuwa Abbi na."

"Ah ai jiki yai sauki masha Allah."
Ya zauna itama ta zauna tana fadin
"Bafka da dawowa Abbi ya aiki?"

"Alhamdulillah Daughter ya jikin?"
"Abbi naji sauki."

"Mamin ta kai ki asibiti?"
"No Abbi Kabir ne yazo ya kai ne aka bani magani ya siyon na sha yanzu bana jin komai."

"Masha Allah."
Ta mike ya kawo masa ruwa da lemo tace
"Abbi na kawo maka abincin da na dafa dazu."

STORY CONTINUES BELOW
"Kawon naci daman na jima banci girkin ki ba kuma in ina ci na kanji kamar marigayiya ce ta girka."
"Allah sarki Ammi na. Allah masa rahma."

"Amin. Yar aljanna kenan. Ki daure in kinyi aure ki xauna lafiya da mijin sa ki masa biyayya zaki samu ribar haka."
"Insha Allahu Abbi."

Tayi kitchen ta hado masa abincin anan kasa ta jere masa ya sauko ya zauna ta baki roba ya amsa ya tara hannun sa ta fara zubo masa ruwa a ciki ya wanke yai bismillah ya fara cin abinci.

Yana loma daya ya lumshe ido yaba fadin
"Nayi missing abinci ki!"
"Abbi ko ina maka ne?"

"Ai kuma baki da time."
"Indai Abbi naso zan samu time din da zan na masa."

"A'ah a'ah kiyi hutawar ki."
Tai murmushi  yakara ci yace
"Wallahi kamar Ammi ki ce tayi girkin kin dauko hannu ta. Mijin ki kema ya huta."

Tai murmushi yace
"Ammin ki yar aljanna ce. Ban taba fushi da ita ba a koda yaushe farin ciki take bani ba ta da fada akwai hakuru ga ilimi ga sanyin hali. Akwai son taimako kanar yadda kike shiyasa nake kara son ki domin abubuwa da yawa naki irin na Ammin kine. Allah ya sa ki daure a haka "

"Amin Abbi"
Kofar dakin aka budo aka shigo. Mami ce cikin shiga ta alfarma ta shigo tana fadi
"Au yau ana kake cin abinci?"

"Eh ina cin abincin Daugther mai dadi."
Ta dan tabe baki tace
"Ai na zata jikin ne shine nazo na gani naga ka dade!"

"Meyasa baki kai ta asibiti ba."
"Wallahi abubuwa sukai min yawa."

"Kin kyauta."
"To Alhaji ba gashi taji sauki ba."

"Eh Alhamdulillah!"
Ya mike yana fadin
"Daughter ni zan tafi ba abinda kike bukta?"

"Babu Abbi. Sai da safe!"
"Allah tashe mu lafiya. Allah miki albarka!"

"Amin Abbi."
Ya fita Mami tabi bayan sa. Kayan wajen ta kwashe ta wuce daki dan yin wanka.
*
**
***
****
*****
******
*******
********
Fauziyya ce zaune sai Hafsa da Sakina. Fauziyya ta kalli Sakina tace
"Ke ya kuke ciki da Khaleel din?"

Kai tayi kasa dashi tace
"Daman ke nake jira ki dawo saboda yana son ai abun nan kusa."

Kai ta gyada ta kalli Hafsa tace
"Ahmad fa?"
"Anty ni na dakatar dashi!"

"Saboda me?"
"Bai jima da aure ba amman wata uku nace yanzu munci wata biyu da sati biyu."

Kao ta gyada tace
"Yayi kyau. Allah tabbatar da Alheri. Bari Muhammad yazo yace zai ga Baba muji ya sukayi!"

"To Allah yasa a dace."
"Amin duk yadda mukaji zamu basu dama su turo manyan su sai muji wane lokaci suke so a saka."

Ta kalli Hafsa tace
"Kira min Halima dan tare nake so a hada ku. Ki taho da Hajara muji in itama tana da manemi;"

Ta mike ta fita. Tare suka shigo da Halima wacce ta sauya tai sanyu ta rame sosai. Ta zauna ta hade kai da gwiwa. Hajara ce ta shigo ta zauna. Fauziyya tace
"To Halima lafiya?"

Ta dago tace
"Kai na yake ciwo ne!"
"Sannu kinsha magani?"

"Nasha kusan kwana uku kenan kan yaki daina ciwo."
"To bati na kira Muhammad sai muje asibiti ko?"

"To Yaya."
Ta dauki waya ta fara neman layin sa. Yana zaune yaga kiran ta dauka tace
"Kana ina ne?"

"Ina gida!".
"Hafsa ce bata da lafiya nake so muje asibiti."

"To ki bari nazo na kai ku mana."
"Shikenan!"

Ta kashe wayar tana fadin
"Gashi nan xuwa."
Sai kuma tace
"Ya zancen Isma'il din?"

Gaban Halima ne ya fadi tace
"Anty na fasa auren sa!"
"Saboda me?"

Idon ta ne ya kawo ruwa. Kai Fauziyya ta girgiza mata tace
"Kada kiyi kuka dan Allah."
Hannu tasa ta goge idon ta. Halima tace
"Yaya na yadda da abinda kuka ce daman kunce Isma'il ba zai auren ba  dan haka yanzu bama tare ya nuna baya so na."

"What wallahi bai isa ba. Xai gane ya tabo mu. Dan iskanci yace ba xai aure ki ba bayan ya gama lalata rayuwar ki!"

Hawaye ne ya zubo. Halina tace
"Yaya ki kyale shi kawai yanzu me zakiyi?"

"Kara zan kai shi akan ya lalata rayuwar ki."
"Yaya in kin kai shi kara kamar kin tonan asiri ne kuma ni ba tsoron tonan asirin duniya nake ba amman abun zai shafi kanne na da iyaye na. Na biyu ina muke da shaida akan Isma'il zai iya karya tasa dama dai na haihu ne ko wani abu. yaya dan Alla ki barshi da Allah duniya ce Allah zai saka min. Tinda ni ban zalunce shi ba."

Sai duk jikin su yai sanyi. Fauziyya tace
"Insha Allahu sai yaga sakamako tin aduniya yaje shi da Allah."
Tai murmushi. Fauziyya tace
"Kiyi hakuri."

Ta kara murmushi kawai ta kwanta a wajen. Hajara ta kalla tace
"Ke kuma fa Hajara ba ki da wanda ya fito miki yana son ki?"

"Akwai shi Yaya amman na nuna bana son sa saboda nasan Baba ba barin na kula shi zai ba in ma yazo zai ce ban isa aure ba."
"Haka ne a ina yake?"

"Yazo service makarantar mune amman sun gama tin last two year wanda yanzj yake lecturing."
Kai ta gyada tace
"Ok yanzu kina son ai miki aure?"

Kai ta gyada. Tace
"To Ya kuke gani Hibba da Izzatu da Hajiya suna da wanda suke neman su."

"Yaya ai basuyi graduation ba."
"Duk da haka naga Hibba da Izza shekarar sha takwas fa. Kuma naga nan da watanni zasuyi waec da neco. Hajiya ce ma sai next year.  Da ai irin tamu gwara ai musu auren in zasu cigaba da karatun sayi a gidan mazajen su. Duk me son karatu ya fada min ni kuma zan tsaya masa da yaddar Allah."

"Haka ne Yaya amman a bari su gama din ko?"
"Shikenan Allah kawo mazajen na gari!"

"Amin."
Wayar tace tayi kara tana dubawa taga Muhammad ne dauka tayi yace
"Ina waje."

"Gamu nan."
Ta dauki mayafin ta ta yafa ta kalli Halima tace
"Tashi muje."

Sakina ce ta kamo ta suka fita suka shiga baya ita kuma ta shiga gaba. Muhammad yace
"Sanni Halima."

"Yauwah Yaya ina yini?"
"Lafiya lou ya jikin?"

"Da sauki."
"Allah kara sauki!"

"Amin!"
Suka gaisa da Sakina sannan ya tada motar yana fadin
"Baby wanne asibiti zamu?"

"Ko wanne!"
"Amman ya kamata a budewa su Halima file ko?"

"Su da zasuyi Aure!"
"Haka ne amman su Umma da kannen mu sa na zuwa ko?"

"Haka ne!"
Suka cigaba da tafiya suna hira jefi jefi har suka karasa. Umar Specialist Clinic. Yai parking ya fito ya shiga. Kati ya yanka aka bude musu file sanna aka tura su inda zasuga Likita. Mota ya mota yace su taho. Tare suka karasa office din Dr Auwal.

Ya basu waje Muhammad da sakina suka fita. Halima da Fauziyya suka zauna. Suka gaisa yace
"Me yake damun ki?"

Nan ta fada masa duk yadda take ji da rashin bacci da komai. BP ta ya auna yaga jinin ta ya hau. Sosai yai fada yana fadin
"Tayaya yarinya kamar Halima za a barta jinin ta ya hau me ake mata me take so?"

Nan ya sasauta murya yace
"Fata min 'ya ta me yake damun ki?"
"Ba komai Dr!"

Yai murmushi yace
"Shikenan amman zan baki shawara dan da yawa yan mata irin ku akan soyayya ne. Wallahi ki nutsu ki rumgumi rayuwar ki da lafiya sune dahir in kika biye ta namiji zai kai ki ya baro ki a wahale. Shi yana can rayuwa daga baya ma ya barki. Dan haka ki kiyaye ba acekada ka so mutum ba amman kasan yadda zaka so shi."

"Nagode Dr!"
"Ba komai!"
Ya fada yana rubutu ya gama ya miko mata yace
"Kisha maganin nan in kin kwana hudu ki dawo Allah kara suaki."

"Amin mungode!"
Suka fito. Suna fitowa Muhammad ya mike ya karaso yaxe
"Sannu ta gyada kai."

Ya amshi papper magani ya bata key ya tafi phermacy ita kuma suka koma wajen mota ta bude suka shiga ita kuma ta tsaya a bakin motar.

Hajiyar su ce ta shigo asibitin tai parking ta fito kamar ance ta kallu gefe taga Fauziyya tsaye jikin mota tana danna waya. Da sauri ta karasa tana fadin
"Fauziyya!"

Fauziyya ta dago da sauri tana kallon ta. Hajiyar ta saki murmushi tace
"

Post a Comment for "WANNAN RAYUWAR CHAPTER 12"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...