WACECE NI COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WACECE NI COMPLETE

WACECE NI COMPLETE

- - Post a Comment

 WACECE NI COMPLETE Garin Kano garine me cike da albarkar mutane da kasuwanci garine da ake alfahari dashi a nahiyar Africa gabadaya saboda gudummawar da yake badawa wajen habaka tattalin arziqi kada na cikaku da surutu bari mu gangara cikin asalin labarin mu.
Gidan marayu na tudun Murtala nanne na leqa inda na hango wata matashiyar budurwa kyakkyawa me qarancin shekaru wadda idan muka dauketa muka azata a mizani bazata wucce 16 going to 17 years ba, hanunta riqe yake da tsintsiya da alamun shara takeyi tana sanye cikin wata baqar atamfa me ratsin jan zane da dadewa yasa ta kode ta jeme ta zama toka toka.“Marwanatu! Marwah!! ke  Marwah dan ubanki ba mgn akeyi miki bane shegiya karfa me qashin tsiya arziqi yana kiranki tsiya tana maidake baya ni bantaba ganin muguwar yarinya me tamola da arziqi irinki ba" qwass ta me maganar ta zuba mata ranqwashi tare da cewa “ja'ira da idanunta irin na aljanu kije Hajiyan nan ce ta dawo taji amsarki idan kuma naji kince mata aa wlh saina kasheki saidai uwar da tayi cikinki ta haifeki a titi ta qara haihuwar wata shegiya annamimiya makira" 
Sumsumsum  ta shige dakin tana sharar hawaye ta cake a bakin qofar tana kuka mecin zuciya tanajin dama baa halicceta a wannan gantalalliyar rayuwar ba mara tagomashin farin ciki kona gamin gafara.
Shigowar Nanny Indo ne yasata shiga dakin da sauri ta durawGarin Kano garine me cike da albarkar mutane da kasuwanci garine da ake alfahari dashi a nahiyar Africa gabadaya saboda gudummawar da yake badawa wajen habaka tattalin arziqi kada na cikaku da surutu bari mu gangara cikin asalin labarin mu.
Gidan marayu na tudun Murtala nanne na leqa inda na hango wata matashiyar budurwa kyakkyawa me qarancin shekaru wadda idan muka dauketa muka azata a mizani bazata wucce 16 going to 17 years ba, hanunta riqe yake da tsintsiya da alamun shara takeyi tana sanye cikin wata baqar atamfa me ratsin jan zane da dadewa yasa ta kode ta jeme ta zama toka toka.“Marwanatu! Marwah!! ke  Marwah dan ubanki ba mgn akeyi miki bane shegiya karfa me qashin tsiya arziqi yana kiranki tsiya tana maidake baya ni bantaba ganin muguwar yarinya me tamola da arziqi irinki ba" qwass ta me maganar ta zuba mata ranqwashi tare da cewa “ja'ira da idanunta irin na aljanu kije Hajiyan nan ce ta dawo taji amsarki idan kuma naji kince mata aa wlh saina kasheki saidai uwar da tayi cikinki ta haifeki a titi ta qara haihuwar wata shegiya annamimiya makira" 
Sumsumsum  ta shige dakin tana sharar hawaye ta cake a bakin qofar tana kuka mecin zuciya tanajin dama baa halicceta a wannan gantalalliyar rayuwar ba mara tagomashin farin ciki kona gamin gafara.
Shigowar Nanny Indo ne yasata shiga dakin da sauri ta durqushe a qasa cikin rawar murya tace “ga...gani.." kafin mutanen dake ciki suyi magana Nanny Indo ta cafe da cewa “makira me qashin tsiya gatanan daqyar na tanqwasata ta amince zata biku amma da sharadi daya kada ku kuskura ku fadawa shugabannin gidan cewa ga dalilinku na tafiya da ita kawai kuzo musu da sigar temako zakuyi dama yaran sunyi yawa gwabnati babu kula neman kai muke dasu balle wannan kinibabbiyar yarinyar sumumu kasau data addabi kowa duk saaninta mun auradda su amma ita kowa baiyi Mata ba saikace bugun iska" miqewa yar gajeriyar matar fara me bayyanannen kyau tayi sabanin marwa da take chocolate me sihirtaccen kyau tace “bakya gajiya da surutu Nanny nidai kin biyani dole zanyi miki ihsani nasan wannan hanyar ita kadaice zata kaimu ga inda mukeso mukai Ummah zo muje mu gama dasu ai kudi ba yaran da basaji mijina ya nuna yanason yin boyayyen aure dake yarinya dole zakuyi badon komai ba saidon mu kwashi albarkar jikinki ki bamu sanyin idanu mu sallameki"Gurin shugaban gdan marayun sukaje baayi wani dogon turanci ba suka gama komai aka basu ita tana kuka tana komai suna kyararta suka fito tana turjewa amma don rashin imani harda hada Mata da duka saida ta shiga motar sannan suka qyaleta ta hada kanta da gwiwa ta rungume yan tsummokaranta tana kuka me tsuma zuciya haka suka lula cikin garin Kano kanta yana qasa bata dagoba saboda koda ta dago ma babu abinda zata fahimta sai sunayen abubuwa tunda ba sanin ko Ina tayi ba kullum suna kulle a gdansu saida wasu tsirarun mutane masu sauran imani su kawo musu ziyara badan kada Marwah tayi qaryaba zata iya cewa tunda aka halicceta bata taba fitowa wajen gdan marayun ba sai yau.
Sunyi tafiya me tsayi sannan suka shiga cikin wata babbar unguwa me suna Badawa Layout cikin Nassarawa L.G.A gaban wani katafaren gida suka tsaya matar da taji an kir dazu da Hajiya Ra'isah tayi horn aka bude mata ta shiga wasu zunduma zunduman motoci ne a harabar gdan itama ta samu guri tayi parking ta bude ta fito wacce aka ambata da Ummah ta fito ta bude qofar baya ta finciko hanun Marwah tace “ke dallah malama kiyiwa mutane shiru banza kawai ai da gaske qashin tsiyarce dake badon hakaba meye abin kuka an raboki da waccen qazamar rayuwar ta gdan marayu" yatsina fuska Hajiya Ra'isah tayi tare da tsartar da yawu tace “nifa wlh kallonta kadai dagamin hankali yake naji amai yana tasomin" wata qofa suka shiga itadai Marwah tana tsaye sororo cikin hawaye ji takeyi dama ta bude idonta taganta a gdan marayun data baro tsawa taji an daka Mata data sanya ta sakin fitsari saboda firgici tace “kewai wacce irin banza ce to ubanki kika tsaya kinayi anan daidai lkcn data dago kanta daidai lkcn da wani matashin magidanci yake fitowa daga cikin wata mota dake tsaye a gurin ya kalli Marwah sheqeqe ya tabe baki ya wucce ciki itama kama hanyar shiga tayi tabi bayansa yana taka qafarsa ita taka tata ya juyo ya dubeta ya kawar dakai yace “lfy?" Baya tayi da sauri daidai lkcn da Hajiya Ra'isah ta fito daga daga wata qofa ta nufoshi da sauri suka rungume juna da sauri Marwah ta rintse idonta tajuya baya da sauri saboda iyakar saninta hakan iskanci ne haka Nanny Indo take fada musu kullum.

Post a Comment for "WACECE NI COMPLETE "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...