WA NAKE SO CHAPTER 8 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WA NAKE SO CHAPTER 8

WA NAKE SO CHAPTER 8

- - Post a Comment

 WA NAKE SO CHAPTER 8

Sai bayan kwana biyu. Bayan ya shiga gidan gwamnati ya dan yi aiyukan sa.

Mikewa yayi ya shirya cikin Bakin glass ya saka da face mask din sa. Nan ya fito kawai ya nemi yan rakiya. Basu san da zasu ba sam sai direction da yake basu. Basuyi mamaki ba lokacin da suka gansu a makaranta domin tin daga shigar Aliyu suka gane zai je ganin wani aikin nasane. Ai kam illai.


A bakin gate ya sa aka ajiye sa yace nan da Minti talatin su shigo. Yana shiga ya gaisa da mai gadi. Staff room ya fara zuwa. Ba lafi ba mutane da yawa wannan yasa ya nufi ajijuwa. SS 2b ya fara zuwa ya tadda malami yana ta aikin sa. Har zai shiga SS 3 ya fara ya nufi SS 1 suma aikin ake masa.

JS Section ya nufa suma duk ajijuwan da malamai a ciki wannan yasa yayo shashen shugaban makarantar amman sai zuciyar sa tace masa yaje ajikin su Aisha. Kamar ba zashi ba sai ya juya ya nufi SS 2a. Yana zuwa kofar ajin motar da suka zo da ita guda uku suka shigo. Ajin ya shige ya tadda malami. Gaisawa sukai ya fara zagaye ajin yana bin sa da kallo.


Tana front sit dake tsakiya. Ido ya zuba mata itama jin ido akan ta yasa da dago tana kallon sa. Mikewa yan ajin sukai suka gaishe sa sannan suka zauna amman duk jikin Aisha ya bata kamar tasan wane wannan haka ta zauna ta dinga bin sa da kallo yana zagaye ajin yana kuma duba littafan wasu daliban. Ya duba a kowanne roll banda nasu Aisha wannan yasa yayo gaba yana zuwa sit din su ya tsaya.

"Show me ur books?"


Ya fada. Kallon sa take dan muryar sa kadai taji wannan yasa ta dago tana kallon sa. Ganin da malami a ajin yasa ta mika hannu. jakar ta dauko ta fara fito da littafai daya bayan daya tana mika masa kallan littafan yake amman kuma idon sa na kan Aisha.

Principal ganin motar ta shigo ya fito da kansa nan yaga sojoji karin bayani ya tambaya suka fada masa da wanda suke tare. Wannan yasa yayi ajin da suka nuna masa. Yana shiga lokacin ya mikawa Aisha littafan ta.


Da sauri principal ya karaso wajen  yana fadin

"Welcome sir!"


Ya kame masa. Hannu Aliyu ya mika masa sukai musabaha sannan suka fiice a ajin Principal yana rawar jiki hadi da bashi rahoto. Office suka nufa yana bincike game da staff da abubuwan da school din ke bukata. Ya jima a makarantar sannan suka mike suka fito Principal na take masa baya. Nan staff din masuka fito cikin girmamawa suna mika masa gaisuwa. Yadda ya yaba da ckul din a take ya rabawa staff din kudi dubu hamsin hamsin yaran kumanya bada a siyo musu lemo with biskit sannan ya bada littafai da biro with text books a raba musu kyauta.


STORY CONTINUES BELOW

Sosai daga malaman har dalibai su kai murna dazuwan sa. Nan ya juya ya shiga mota. Aisha tana taga ta zuba masa ido. Zuciyar ta na tambayar ta wane irin relation ne a tsakanin Yaa AK da Gwamnan. Domin kuwa suna matukar kama duk da ba fuskar sa ta kalla ba amman murya da kirar jikin sa irin daya ce.


Tana tsaye a taga ya juyo yana kallon ajin nasu idon sa ne ya kai kanta ta tsaya tana kallon sa. Hannu ya daga mata yana weaving nata. Kallon gun da take tayi ita kadai ce kan ta juyo da kallon ta inda yake har ya shige mota sun bar harabar makarantar.


Mamaki ya kamata haka ta tsaya tana kallon kurar da suka tayar. Suna fita suka dau hanya dan zaga gari. Wani karamin asibiti ya gani nan yace su shiga.

Suna shga yace su tsaya a gate ciki ya shiga. Wasu daga cikin likitocin na zaune suna ta hira ga marasa lafiya na layi. Amman a haka wasu suka zo akace rana tayi sai dai su dawo washe gari.


Kyauta ne kati amman yana gani suna siyar wa. Har likita in zaka gani sai ka bada wani abu. Yana tsaye yana kallon komai yana samun information daga wasu marasa lafiya yan rakiyar sa suka shigo. a take ya sallami likitoci da yawa sannan a lokacin yasa akayo posting din wasu wajen sannan ya saka musu doka akan kula da marasa lafiya.


Duk wanda yake cikin asibitin mara lafiya sai da ya samu kyautar dubu biyar sannan kuma yace a basu magani kyauta. Haka ya juya ya tafi ana ta saka masa albarka. Nan  da nan kuma aka hau duba su kan kace me har an gama an raba musu magani sun tafi ranar duk wanda yaje daga baya ba layi haka za a bashi magani kyauta kuma.


Gidan gwamnati ya koma ya cigaba da cike wasu abubuwa da yake son cikewa akan cigaban garin dai dan a yanzu ba da wani aiki sai na son ganin cigaban garin.


Ai kam yana wahalta musu kuma suma sun san da haka domin duk inda ka shia ba abinda zaka ji sai dai kai ana saka masa  barka shi da iyayen sa. Sosai yake jin dadin hakan domin komai na zuwa kunnen sa.

Ranar sam bai samu zuwa gidan su Aisha ba domin sai magariba ma ya koma gida a matukar gajiye. Wanka yayi yai sallah sannan ya shige daki ya kwanta bayan sunyi waya da gida.


*

Washe gari da ya dawo daga aiki ya shirya cikin wasu kananun kayan sa blue din wando ne da bakar riga yai kyau sosai a cikin su. Fitowa yayi yana tafiya a kasa yana bin garin da kallo. Shi kam Allah ya daura masa son garin nan.


Garin nan ya kawo masa sauyi da yawa a rayuwa gashi ya hada shi da burin zuciyar sa kai taimakon sa wacce ta cece  shi daga halaka. Hakika wannan garin yana da matukar tarihi a cikin rayuwar sa.


Domin yana daya daga cikin abinda ya yi a rayuwa da ba zai manta ba. Bai taba kawowa zai shiga harkar siyasa ba amman wai yau shine gwamna. Ikon Allah kenan. Haka yake tafiya yana ta tunane tunane. Fadi yake sai ma ya auri Aisha yar garin,  garin zai kara zame masa tarihi a rayuwar sa. Bama in ta haifa masa yara. Yana son Babies bama in suna jarirai da in suka tasa suka fara tafiya. Bare kuma ace sun girma.

Da wadan nan tunanin ya karasa gidan su Aisha. Yana zuwa ya aika ta zo fitowa tayi cikin shigar ta mai kyau da hijab har kasa. Aisha ta kara kyau bama da ta girma ta zama yan mata.


Murnushi suka sakar wa juna. Ta zauna akan dakalin tana fadin

"Yaa AK ina yini?"


"Lafiya lou yan mata ya makaranta?"

Fuska ta rufe da tafin hannun ta.


Murmushi yayi yace

"Ya dai kunya kuma?"


"Yaa AK jiya gwamna yazo school din mu. Ina ta Allah Allah na dawo kazo in baka labari amman baka zo ba."

Ta fada tana bata fuska.


"Am sorry ina can aiki amman kina cikin zuciya ta a ko wannen motsi na da tunani na."

Murmushi tayi tace

"Haka Yaa Mubammad yake ce min kullum wai ina cikin tunanin sa da zuciyar sa."


STORY CONTINUES BELOW

Fuska ya dan bata yace

"Ya kuke da Yaa Mubammad din nan naki ne?"


"Yaya nane?"

"Ur relationship."


Murmushi tayi tace

"In baka labari na?"


Kai ya gyada. Nan ta fara bashi labarin Maman ta da Abban ta tin auren su har lokacin da aka auren Umma da Baba. Ta bashi komai da komai rasuwar Abba da tafiyar Mama.


Hawaye ta share tana fadin

"Yaa Muhammad shi ya zame min komai nawa wanka na wanki na goyo na da komai nawa. Farin ciki na shine nashi  yana sona da yawa yana fada min yafi so na akan kansa. Ina son Yaa Muhammad nima."


"Shut up!"

Ya fada a zafafe. da sauri ta dago tana kallonsa. Kallon juna suke ido cikin ido sun kasa daina kallon juna su.

"Menene Yaa AK?"

"Labarin ne ya ishe ni."


Ido ta zaro tace

"Akan me?"


"Bana son kina yawan kawon zancen Yayan nan naki  ni na zata uwa daya uba daya kuke ashe ba haka kuke ba."

Da ido take bin sa.


Tace

"But Yaya nane fa?"


"Yayan naki fa!"

Mikewa tayi tana kallon sa da mamaki.

Kai ya girvgiza zatai magana kenan taji an ce

"Kanwata!"

Da sauri ta jiyo jin muryar Yaa Muhammad  gun sa tayi tana murna Aliyu da Muhammad kallon juna suka tsaya  Aisha ita ta daukewa Muhamnad hankali ta ja jakar sa wannan yasa sukai ciki bata kara bi ta kan Aliyu ba  komawa yayi ya zauna yana dafe kan sa  hakika ya kamata ya fadawa Aisha yana son ta but tayaya Aisha yarinya ce karama kar ta daina ganin girman sa in taji abinda yake tafe dashi.


Da sallama suka shiga gida. Aisha tace

"Umma Ummah Yaya ya dawo."


Ummah ta fito a daki tana fadin

"Aisha kenan!"


Nan Muhammad ya durkusa yana gaishe da Ummah. Mikewa Aisha tayi ta kawo masa ruwa sannan ta zauna suna hira. Ji tayi gaba daya hankalin ta ya kasa kwanciyya ta rasa ko akan menene wannan yasa ta tuno da ta bar Aliyu a waje. Da sauri tayi waje. Da kallo Muhammad ya bita.

Aliyu yana zama ya mike yana kallon kofar gidan ya jima a tsaye sai ya juya ya fara tafiya jikin sa a matukar sake. Bai jima da fara tafiya ba da fito da sauri ta fito ta hangeshi yana tafiya.


Tsayawa tayi tana kallon sa. Can ta daga murya tace

"Yaa AK!"


Da sauri ya jiyo jin muryar Aisha. Ido suka kurawa juna. Hannu ta daga masa tana masa bye bye hadi da sakar masa murmushi. Shima bai san lokacin da ya sakar mata murmushi ba. Wannan yasa ya juya. Tsayawa tayi yana tafiya yana juyowa yana kallon ta har ya daina hangen ta.


Ta jima a wajen duk da ya tafi amman ta kasa komawa ciki har Yaa Muhammad ya fito dan har an kira magariba zai tafi masjid.

"Me kike anan?"


Ya tambaya yana wuce ta. A firgice ta juyo tana cewa

"Uhm ba komai."


Sai kuma tayi cikin gida da sauri. Alwala ta wuce daki ta tada sallah. Tana idar wa ta zauna aikin tunanin Yaa AK nata. Ta rasa me yasa take jin kamar bata kyauta masa ba ta tafi ta bar sa dan Yaa Muhammad yazo. Duk abinda Yake mata bai kamata tai masa haka ba. Meyasa bata hada shi da Yaa Muhammad sun gaisa ba. Haka tai ta tunani dai.


Can kuma sai ga tunanin gwamna da tace zata tambaya shi yaya suke dan kamanin su sunyi yawa. Kan kafita ta fada ta kwanta tana mai lumshe ido. Fuskar Yaa AK ta gani tana mata murmushi da sauri ta mike tana fadin

"Yaa AK!"


Sai kuma ta saki murmushi tana mikea jin ana kiran sallah isha'i. Tana idar wa kuma ta haye katifar ta ta dasa daga inda ta tsaya a tunanin Yaa AK dinta. Da Muhammad ya dawo sallah ya shiga dakin ya zata tayo bacci domin idon ta a umshe suke wannan yasa ya juya ya koma.


Ummah tace

"Ina Aishan?"


"Bacci take."

"Bacci kuma anya? Bata ci fa abinci ba. Je ka ka taso ta taci abinci in baccin zatai sai ta koma tayi."


Komawa dakin yayi ya hau kiran ta da

"Aisha Aisha!"

Yana dan bubbuga katifar da ta ke kai. Da sauri ta bude ido tana fadin

"Yaa AK!"


Ganin Yaa Muhamnad yasata daura hannu akan bakin ta. Da ido yake bin ta ta mike zaune tace

"Yaushe ka dawo?"


"Na shigo naga kina bacci ai. Ummah tace ki taso kici abinci."

Mikewa tsaye tayi. Yana kallon ta yace

"Waye Yaa AK?


Kallon sa tayi zatai magana kenan Ummah tace

"Wai bata tashin bane?


"Ta tashi gamu nan."

Yaa Muhammad ya fada yana yin gaba bayan sa tabi suka fita a dakin. Abincin kadan taci ta mike tai musu sai da safe.


Da kallo Muhammad ya bita yana girgiza kai. Tin wancan zuwan yaga sauyi daga Aisha har yanzu kuma yana ganin sa a tare da ita me kenan. Da yayi tunani ko girma da ta yi ne amman ya fara tunanin ba haka bane wani abu ne dai kila.

Aliyu na komawa gida sallah ya shiga masallaci yayi bai fito ba sai da akai isha'i yana fitowa ya shige cikin gidan sa. Wanka yayi ya kwanta akan gado  kwalkwalar sa ta kasa kawo masa tayaya zai sanar da Aisha abinda ke ransa.


Tunani yake ya kasa bawa kan sa mafita. Kwakwalar sa tafi a aiki da bashi tsaro amman a irin wannan fanin bai san komai ba shiyasa abun yake hade masa yai masa zafi a ransa.


Faisal ne ya fado masa a rai da sauri ya dauki wayar sa ya fara neman layinsa. Faisal na zaune shi da iyalin sabkiran wayar Aliyu ya shigo.

Da sallama ya dauka yana fadin

"Barka da yamma Mai girma gwamna kuma sarki mai jiran gado."


Tsaki Aliyu yayi dan a rayuwar sa ba abinda ya tsana kamar ace masa mai jiran gado bai son kujerar sarki sam baya son damuwa.

"Ina sauraron kai Mai girma Gwamna."


"Please ka ajiye wasan nan a gefe ina da damuwa!"

"Damuwa kuma? Kai kam me zai dame ka a duniya Aliyu? Bayan kana da kudi mulki sarauta jin dadin rayuwa komai ka tara."


Wani murmushi mai ciwo Aliyu yayi yace

"Haka ake wa masu kudi wannan kallon amman abin ba haka bane. In kana da kudi wani lokacin bacci ma kadai gaggarar ka yake yi dan wata damuwar kudi ko mulki duk basa maganin ta kamar yadda tawa take."


"Me yake faruwa to?"

"Akan Aisha ne!"


"Wacce Aisha?"

"Yarinyar da ka ce ina son ta."


Dariya Faidal yaui yace

"To bason nata kake bane?"


STORY CONTINUES BELOW

"Uhmm shi nake."

Murmushi yayi Faisal yace

"Menene matsalar?"


Ido Aliyu ya lumshe yace

"Tayaya zan sanar mata?"


"Me zaka sanar mata?"

Wani tsaki Aliyu ya saki yace

"Ina son ta mana."


Kai Faisal ya girgixa ya mike adakin ya fita compound din gidan. Sai da ya tsaya yace

"Kai kaga ta gama yi maka?"


"Wane irin magana kake haka?"

"Eh nufi na tana da qualities din duk macen da kake so?"


Shiru Aliyi yayi yace

"Kasan ni ba zalamame bane. Abinda nake son mace dashi bai wuce ilimi da tarbiyya ba ban son mace mai son abin duniya ita da iyayen ta. Da farko na zata duk masu kudi sun fi raini da rashin ji. Amman aura da nayi yasa nangane wasu daga cikin ya'yan talakawar ma ko ince masu rufin asirin ma duk kanwar ja ce. Dan na gane su akwai su da son abin duniya."


Kai Faisal ya gyada yana sauraron sa sai da ya gama sannan yace

"An zo wajen. Abinda nake so shine yanzu yana da kyau kafara gwada yarinyar akan abinda kafi tsana ana  zaka gane ya suke ita da mutanen ta. Bayan sai ka sanar da ita."


"Alright but tayaya zan fada mata uhmm?"

"Yana da kyau kana nuna mata damuwar ka akan ta da kulawar ta. Sannan a sannu ka gane me take so? In ka gane sai kana mata wannan abubuwan sannan a sannu sai ka fito mata fili ka sanar da ita me kake ji a wajen ta. Kana mata abinda take so shine ta yadda zaka kara sace zuciyar ta. Sannan ita yaya reaction nata yake a wajen ka?"


Kai ya gyada ya lumshe ido yace

"Tana damuwa dani da na dawo baka ga a halin da na same ta ba. Duk ta damu har rama. A tym din naga har kunya na take yi."


"Wow kaga da wannan kunyar taka da take ji nasan akwai wani abu a kasa. Da tana jin kunyar ka ne?"

"A'ah!"


"Hmmm ni fa nasan ba macen da zata ki ka wallahi. Ka cancanci a so ka kana da qualities din da ko wacce mace zata so ka sai wannan miskilancin naka amman nasan Aisha zata rage maka shi. Shawara dai kabi abinda nace. Allah bada sa'a."

"Amin Amin. Nagode Faisal."


"Ba komai kar ka damu."

Wayar sa ya kashe ya koma ya kwanta. Sake sake yake yi na yadda zai gane abinda Faisal yace ya duba. Ga Aisha dai yasan sam abin duniya bai gaban ta zai gwada iyayen ta. Dan in ita bata da ra'ayin in iyayen ta na dashi to zasu na takura mata akan lamarin.

"Allah yasa kar haka ta faru."

Ya fada a ransa yana mai gyara kwaciyya.Hajara da Alhaji Lukman kuwa sun dinke domin har gidan sa take zuwa dsai dai duk yadda yaso ya rinjaye ta akan su kulla wata mu'amala taki yadda. Domin tasan hukuncin wanda yayi zina da auren sa. Wanda jifa ne. Shin tayaya zata tunkari mahallicin ta da wannan kazantarbin ta mutu tana aika zinar.

Duk da haka bai fasa nna mata bujatar sa da son tona mata asiri ba. Amman shima ganin tana ba shi kudiduk lokacin da yake son kudi zai fada mata haka nan dole ta kawo masa. Wannan yasa ya ke bi da ita a sannu.


Cikin lokaci kadan ta fara rasa abubuwan ta dan a lokacin bata da hanyar samu dan duk hanyar da zata samu Aliyu ya toshe yanzu komai shi ke sawa ayi ko ya hana. Sai dai ta roke shi. Wanda da ya fara bata sai yaga abin bana karau bane ba a kwana biyu bata ce ya bata dubu dari ko hamsin ba abin yana bashi mamaki me take da kudi har haka dan ga kanya komai nan a gidan wannan yasa ya daina bata sai dai duk wata ya dire mata domin komai akwai ba abinda zata nema.


Ganin haka tace yana bata kudin kayan abinci da amfanin gida zata na bayar wa ana kawo wa. Bai kawo komai ba wannan yasa duk wata zai mata transfer. Wannan yasa ta fara farfadowa dan ba karamin kudi take ja a cikin kudin cefane ba. Sam bai san me ake ciki ba tinda shi ba abincin gidan yake ci ba.


Ma'aikatan ta ne dai suka ga sauyi duk da komai akwai amman ba kamar da da kayan abinci wani wata zai tadda wani ba ko kuma nama ya kai wata bai kare ba. Gashi tai ta tara mata ana shan hira a yi musu uban abinci da kaji kamar ba a san zafin nema ba.


STORY CONTINUES BELOW

Itama haka zata ce a dafa mata abinci yafi kala biyar amman a ciki in taci guda biyu baifi half plate ba. Sai ciye ciyen banza da wofi.
***********************************************************************************************************************************


Fu'ad na fita daga gidan ya dau hanyar sa ta barin garin kano. Tafiya yake idanun sa na zubar da hawaye har baya iya ganin gaban sa wannan yasa ya gangara titi ya faka motar kan sa ya kifa akan sitiyarin mota. Yana kuka mai taba zuciyar wanda duk wanda ya saurara sai ya zubar masa da hawaye. Kuka yake yana fadin

"Ban so ba. Ban so ba Fateema. Ki yafe min ki yafe min."


Abinda yake iya fada kenan cikin rawar murya. Ya jima a haka sai da kyar da ya fara ambaton Allah sannan ya samu nustuwar ta fara zuwar masa. A hankali ya dago yana kallon inda yake. Kaduna State yake. Wani masallaci ya hanga wannan yasa ya mike ya fito a mota ya nufi masallacin.


Alwala yayi ta la'asar sannan ya shiga yai sallah. Yana idar wa yai addu'a akan Allah ya bashi hakuri da juriya sannan ya shafa ya mike ya fito mota ya koma ya dauki hanyar sa.****

Ranar yini sukai hira tana bawa Momy labari kamar wacce ta shekara basu hadu ba sallah kadai ke tada ta. Can da yamma sai ga Suraiyya nan suka shige daki suna hira.

Can Suraiyya tace

"Ya kuke da Fu'ad kuwa yanzu?"


"Komai normal ina kokarin cire komai a raina sosai. Yanzu ba abinda na saka a gaba sai son farantawa Fu'ad amman kinsan me?"

Kai Suraiyya ta girgiza.


Fateema tace

"Yanzu na kasa gane kan Fu'ad ya canja min tin ranar da na dau damarar ganin na canja a ranar shima na ga ya canja."


"Ke kuma baki tambaye shi ba?"

"Na tambaye shi mana. Amman sai yace min wai ni ce damuwar sa bai son ganin damuwa ta."


"Uhmm Allah Fatrema sam baki kyauta ba yadda Fu'ad ke son ki amma kin sashi a wani halin wallahi. Gaskiya ki gyara yanzu "

"Insha Allah yar uwa daga yau ba zan kara sa masa damuwa da damuwa ta ba zan cire komai na rumgumi miji na kinsan dai nima ina son sa ai."


"Haka ne ni nayi mamaki ta yadda akai Yaa Fauwaz yazo ya shiga tsakanin ku. Kowa na sha'awar ku kuna burge kowa amma gaskiya kin yi wasa da damar ki. Kada ki kuskura hakan ta kuma faruwa"

"Insha Allah!"


Yanzu yaushe zai zo ku tafi."

Kafa ta mike tace

"Zan kwana biyu a gida fa. Ya tafi Abuja."


"Allah sarki. Allah tsare hanya."

"Amin! Kinsan bam ma kira sa ba bari naji ya hanya hira da Momy ta mantar dani Kalbi na"


Dariya Suraiyya tayi tana fadin

"Anya kuwa kalbin ne?"


"Ya wuce kalbi ma wallahi."

Sukai murmushi sannan ta dauki waya tana neman layin sa amman a kashe. Tace

"Uhmm shifa haka My yake in zai tafiya ya kashe waya dan Allah haka ake yi?"


Ta fada da damuwa a ranta.

"Gaskiya dai bai dace ba bama da tafiya zai yi ya kamata ya bar ta a kunne ko dan ki samu kiji ya hanyar tasa."


"Uhmm!"

Ta fada tana ajiye wayar tana fadin

"Ke ya shirye shiryen bikin ne?"


"Alhamdulilah. Me kike ganin za ayi?"

"Me angon yace?"


Daga haka suka dinga hira akan bikin Suraiyya. Sai da akai magariba sukai sallah suka ci abinci sannan Suraiyya ta tafi.

Har karfe goma suna Falo dan har da Baba uwani ta dawo. Sai sha daya sannan kowa yai dakin sa. Daki na a da na shige. Dakin nabi da kallo ina sakin murmushi tuna irin rayuwar da nayi a ciki.

Ciki na shige na cire kaya na na daura towel sannan na shige bandaki. Wanka nayi da ruwan dumi sannan na fito na bude wardrobe dina akwai wasu kayan nawa har lokacin ciki dan haka na dauka na saka na bacci.


Kan gado na fada ina salati. Ji nayi gadon duk ba dadi. Murmushi nayi a raina nace

"Lallai ko yaushe na saba da kwana acan."


Ido na lunshe tuna da tini yanzu ina jikin Fu'ad a kwance tunawa da haka yasa na mike na janyo jaka ta waya na dauko sai naga takardar da Fu'ad ya bani fito da ita nayi ina juya ta a hannu na.


Gaba na naji ya fadi wannan yasa na ajiye ta ina kunna wayata nayi mamaki ganin har tym din ba missed call din Fu'ad. Shiru nayi sai kuma na fara nema layin sa amman har tym din a kashe. Tagumi na zuba na rasa tunanin me zan yi. Shin yaya Fu'ad yake.


Komawa nayi na kwanta ido na na zubar da hawaye. Haka nake abun kuka baya min kadan bai min yawa. Ganin na kasa nutsuwa yasa na mike na shiga bandaki na dauro alwala. Nazo na hau kan sallaya na jima ina sallah daga baya na zauna ina zaune ina tasbibi bacci ya dauke ni.


Karfe biyar dai dai na bude ido jin kiran sallah asuba yasa na fara kallon a inda nake a kasa nayi bacci wannan yasa na mike da sauri na shiga bandaki. Ruwa na watsa sannan na dauro alwala na fito. Sallah nayi na idar ina yin addu'a na shafa na mike ina kara duba wayata ko zan ga missed call ko text din sa amman shiru. Take tsoro ya mamaye ni.


Wanda sai da zuciya ta ta buga da karfi wanda hakan yasa na dafe ta take kaina ya sara. Nasan kome nake bacci bazai dauke ni a yanzu ba dan haka na mike na fita. A kitchen na samu Momy dan haka na shiga na gaishe ta na fara taya ta aiki.


Karfe bakwai da rabi mun gama komai na gidan dan haka na shiga daki na. Gadon na fara gyarawa sai ga takardar da Fu'ad ya bani ta fado dauka nayi na kara juya ta sai na ajiye akan bedside durowa. Dakin na gyara na shige bandaki.


Wanka nayi na fito na tsane jiki na sannan na shafa mai. Wata bakar doguwar riga na saka banyi kwalliya ba naje daukar wayata dake kan side durowa sai ido na ya kara sauka akan takardar da Fu'ad ya bani.

Take zuciya ta ta kara bugawa. So nake na bude naga menene a ciki amman kuma tsoro nake ji ba san ko tsoron me ba. Zama nayi a gefen gado sannan na mika hannu jiki a sanyaye na dauki takardar.


Budewa na fara kirji na na bugawa. Rubutun Fu'ad ne ya bayyana akai wanda yake mai kyau dashi kamar computer ce ta rubuta shi. Shafa rubutun nayi sai kuma na maida ido na kan farkon takardar.

Budewa na fara kirji na na bugawa. Rubutun Fu'ad ne ya bayyana akai wanda yake mai kyau dashi kamar computer ce ta rubuta shi. Shafa rubutun nayi sai kuma na maida ido na kan farkon takardar.+


"Assalamu alaikum ya ma'abociyar kyau nustuwa....."

Kofar dakin naji an budo wannan yasa na juyo. Yasmeen ce tsaye cikin shirin ta na makaranta.


"Ina kwana Anty?"

Murmushi na saki na mike nace

"Lafiya lou har kin fito?"


"Eh Momy tace ki fito mu karya."

Waya ta na dauka na bi bayan ta muka fice na bar takardar akan gado.


A falo na samu Baba Uwani na durkusa na gaishe ta ta amsa tana fadin

"Kin tashi lafiya?"


"Alhamdulilah."

Nan muka karasa dining muka karya. Muna gamawa Yasmeen ta mike ta fita driver ya tafi kai ta. Anan falo muka zauna muna hira dasu Baba Uwani har da Momy.


Har karfe sha biyu muna zaune. Bana minti goma ban kara trying number Fu'ad ba har Momy ta lura tace

"Lafiya dai ko?"


Fuska ta cike da damuwa nace

"Momy number Fu'ad ne bata shiga."


"Ke kuma da saka damuwa da fargaba ko? To ai kika sani ko ba charge ne ko aiki yai masa yawa shiyasa."

"But Momy tin ......"


"Please Fateema ki kwantar da hankalin ki yana lafiya kinji ko? Nasan zai kira ki da ya samu dama."

"Shikenan."


Na fada ina mikewa. Kallon Baba Uwani nayi nace

"Baba me zan dafa mana ne?"


"In abinda nake so ne wahala zaki sha,  gashi kuma kamar kina da yaron ciki."

Ido na zaro nace

"Kai Baba ni ba ni da komai."


Dariya Momy tayi tace

"Me kike so Baba?"


"Dambu nake sha'awa wallahi."

"Nima shi nake sha'awa."

Na fada.


Momy ce ta kallen tace

"Je ki daura dambun akwai barzaziyar shinkafa a store."


Kitchen na tafi ina murmushin maganar Baba wai ina da yaron ciki. dariya nayi nace

"Ni da ba abinda ya shiga tsakani na da Fu'ad din ma."


Baba tace

"Dan Allah Huwaila ba ciki ne da Fateema ba?"


"Me kika gani Baba?"

"Gani nayi tayi haske sai yar ramar da tayi shiyasa nake zaton hasken ciki ne da ramar."


"To wa ya sani ni dai bata fada min ba."

"To Allah ya inganta."


"Amin!"


*

Ina shiga kitchen na dauko barzaziyar shinkafar na wanke sannan na dauko tukunyar dambu. Wanke barzaziyar shinkafar nayi na zuba a cikin tukunyar dambun bayan na zuba ruwa a kasa na daura akan wuta.


STORY CONTINUES BELOW

Attaruhu na dauka na yanka albasa sannan nayi greating. Kifi na dauko na gyara na daura akan wuta na zuba masa jajjagagen attaruhu da albasa sannan na saka masa kayan kamshi da magi da curry navrufe shi.


Ina cikin aiki Momy ta kawo min gyararen zogale na wanke shi na ajiye. Tukunya nan bude naga ya turara dan haka na sauke na dauko wannan jajjagagen attaruhun na hada a cikin turarraiyar barzaziyar shinkafa na zuba gyada da magi da curry sannan na kawo zogalen na zuba na zuwa wadataciyar albasa ta na mai da kan wuta.


Ina duba farfesun kiifin naga ya dahu dan haka na sauke. Zobo na tafasa na saka masa kayan kamshi. Sannan nayi blending cocumber na tace na zuba akai na saka suga da kankara na maida cikin firji


Bayan minti goma na bude dambun naga har ya gama dan haka na zuba a cikin kula na wanke duk abinda nai amfani dashi sannan na fitar dasu na kai dining. Anan falo nayi sallah dan lokacin har biyu tayi.

Ina idar wa muka hau dining muna cin abinci. Lokacin Yasmeen ta dawo bata cire uniform ba tayo dining tana fadin

"Wow yau dambu akai mana."


Ta zauna tana yi mana sannu da gida sannan aka zuba mata abincin ta fara ci. Muna gamawa ta shige tai wanka ta shiryo ta tafi isilamiyya. Kayan da muka ci abibci na wanke sannan na dawo falo.


Momy na sama nace

"Zani gidan su Surayya na gaida Uncle."


"Kin fadawa Fu'ad ne?"

Kai na gyada nace

"Eh na fada masa tin a gida."


"Shikenan ki gaishe su."

Nan na shiga daki nayi wanka na canja kaya sannan na fito nayiwa Momy da Baba sallama sannan na tafi.


Ina shiga gidan kanne na suka fara murna ga amarya ga amarya ni har suka ban kunya. Suraiyya ce ta fito a daki tana gani na ta saki murushi tace

"Ashe kece!"


Muka shiga dakin Mama na gaishe ta tana tambaya ta ya gida na amsa da

"Alhamdulilah. Uncle ya dawo?"


"Yanzun nan ya dawo!"

"Ok bari naje na gaishe shi."

Na mike na nufi dakin sa.

Sallama nayi ya amsa sannan na shiga. Murmushi a saman fuskar sa ya saki da ya ganni yace

"Fateema kece."


Kai nayi kasa dashi naxe

"Ina yini?"


"Lafiya Alhamdulilah ya gidan da mai gidan?"

"Alhamdulillah!"


"Ina fatan ba wata matsalla dai ko?"

Kai na gyada yace

"To Allah yayi albarka ai ta hakuri Allah baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka."


Shiru bayi kai na a kasa nan yai tai min nasiha mun jima a daki dan har akai sallah la'asar sannan na tashi na fito shi kuma ya tafi masallaci.  Alwala nayi na shiga dakin Suraiyya. Sallah nayi kan na idar ta cikan gaba da kayan dadi. Nan na zauna muna ci muna hira duk yawan ci akan bikin tane.


Ban an kata ba sai kiran sallah Magariba naji ido na zaro nace

"Lallai lokaci na gudu yau."


Alwala nayi nai sallah sannan nace gida zan tafi amman Mama tace sai na tsaya naci abinci. A falon ta muka zauna muna cin abinci muna hira sai takwas na koma gida.


Ina komawa nai sallah sannan na dawo muka zauna hira. Har sha daya muna falo ana ta hira da Baba Uwani tana bamu labarin da dana kakan mu. Ni da Yasmeen sai dariya muke.


Duk wannan sakewar da debe kewar da na samu hakan bai sa na cire tunaninvFu'ad ba domin duk tunani na da komai nawa yana ga Fu'ad. Ina basar wane dan Momy kada tace ban dauki maganar ta ba.


Bayan mu koma daki wanka na shiga nayi na fito ina tsane jiki na. Gaban mudubi na karasa ina kallon Kai na a jikin mudubi. Ido na lumshe saboda tinawa da kwana biyu da suka wuce baya.

*

Bayan na fito daga wanka Fu'ad ya shigo dakin sam ban san yana dakin ba ina fito na tsane jiki na gaban mirror nayi na dauki mai ina shafawa. Towel din jiki na bude ina shafa mai a kirji na. Kallon mirron da zanyi naga Fu'ad ya zuba min ido.


STORY CONTINUES BELOW

Ido na zaro nai saurin dukewa. Dariya ya fashe da ita sannan ya taso ya dauki man da nake shafawa ya lakata a hannun sa sannan ya hau murza min a gadon baya na da yake a bude saboda towel din yana kugu na.


Tsigar jiki na naji ta mike dan wani yar naji wannan yasa naja Towel dina dagowa nayi ina kallon sa nima shi yake kalla. Mun jima a haka jiki na yai mugun sanyi. Man ya kara lakuta ya durkusa yana yaye towel dina yana shafa min daga cinya ba. Ido na runtse ina mai sauke wata ajiyar zuciya.


A haka ya gama shafa min mai ido na a rufe sai da ya gama ya dago ni,  Towel dina ne ya zame zai fadi da sauri ya dafe min towel din. Rigar bacci na dake kan gado ya dauka ya zura min sannan ya janye towel din. Pant dina dake kan gado ya miko min da sauri na amsa nayi cikin toilet.


Dariya ya saki yana mai shafa kan sa. Kan gadon ya kwanta yana mai sakin murmushi. Na jima da saka pant din nawa,  na tsaya a toilet ina sauke ajiyar zuciya. Da kyar na fito a bandakin ganin shi a kwance yasa na wuce kan gadon ina kwaciyya a gefeb sa.


Ina kwanciyya ya yo guna yai min rumfa. Kallon juna muka tsaya yi yace

"Teemah na nifa mijin kine wannan kunyar taki tayi yawa yau satin mu hudu da aure fa yaci ace by now kin sake dani ko?"


Ya fada yana kanne ido sa daya. Ido na lumshe ina sakin murmushi. Peck yai min a kumatu na yana fadin

"Zan ga ranar da Baby na zai fito ta wannan dan cikin naki."


Ya fada yana shafo min ciki na. Wani iri naji a jiki na tsigar jiki na na tashi. Mirginawa nayi  ya kara mirginowa. Dago kai na yayi yana fadin

"Teemah nah i will miss u Badly!"


Ido na bude ina kallon sa nace

"Wane irin Missing after all i am with u all days.


Ajiyar zuciya na sauke yace

" In time din yayi zaki sani."


Baki na turo ina mikewa zaune. Mikewa yayi ya janyo ni yace

"Menene to?"


"Bari na zakayi?"

Ya tambaye ni.

"Tayaya zan barki Fateema. In har kinga na barki to ki sani ba yadda zanyi ne kuma ba dan yin kai na ba sai dai dan faran ta miki Teemah na. Komai zanyi dake nake yi kuma dan ke zanyi. Ki sani in har na barki to dan samuwar farin cikin ki ne?"

Dagowa nayi ina kallom sa domin kusan two days abinda yake fadan sam ban ganewa kalaman nasa.


"Fu'ad me kake nufi ne?"

Na fada ina kwanciyya akan kirjin sa. Kai na yake shafawa yana fadin

"Nothing more fa. Zaki gane a sannu. Samuwar farin cikin ki shine nawa dan haka i can do anything to makes u happy. I love u Teemah i really do so."


"I love u more My!"

Yai hugging dina. Iska ya fara huran a cikin kunne take na fara mika hadi da lumshe ido na. Yadda yake shafan kai na da baya na yasa bacci ya dauke ni.


*

*

Kai na nake kalla a mirrow ido na na kawo ruwa hakika ko a iya two days nayi missing Fu'ad sosai da sosai. Fasa shafa man nayi na wuce na dauki riga ta na zura sai na tuna lokacin da ya sakan rigar.

Kan gado na kwanta tsigar jiki na na tashi dan yadda nake jin wani mahaukacin feeling dan ji nake duk abinda ya faru tsakani na da Fu'ad kamar a yanzu ya faru. Pillow na janyo na rumgume a jiki na. Matse shi nayi sosai ina juyi akan gadon. Takardar da na ajiye da safe naji a kasana wannan yasa na mike zaune ina daukar ta.


Kallon ta nayi na zuba mata ido sannan na bude ta.

"Assalamu alaikum ya ma'abociyar kyau nustuwa. Da fatan na barki tafiya cikin farin ciki da kwanciyyar hankali.

Fateema abinda zan fara fada miki shine ki kwantar da hankalin ki,  ki nutsuwa sannan ki fara karanta wanna takardar."


Ajiyar zuciya na sauke na girgiza kai kirjin na na tsanan ta bugu. Cigaba da karantawa nayi Kamar haka.

"Nasan a lokacin da zaki duba takardar nan na jima da yin nisa dake kuma a lokacin nasan kina cikin kadaici da damuwar ina na shiga domin nasan kin nemi wayata duk a kashe to kiyi hakuri ban yi haka dan na bata miki rai ba. Nayi hakan ne duk domin farin cikin ki.

Sam kar ki damu da halin da nake ciki kawai kisa a ranki ina nan lafiya ba abinda ya samen naje kuma inda zani lafiya da izinin Allah. Allah zai kare ni ya kiyaye ni. Kema ina fatan Allah ya cigaba da karen ke da kiyaye min ke a ko da yaushe.

Fateema na ki sani a duniya bayan mahaifiyya ta a yanzu ban da wacce tafiki kuma bana fatan na samu wacce zata fiki. Zuciya ta da rayuwa ta duk naki ne. Ki sani komai kika ga na aikata a rayuwar nan dan ke nake yin sa a yanzu.

Samuwar farin cikin ki shine nawa. Fateema ke kyakywa ce wacce ko wanne da namiji zai yi burin sama a matsayin na matar auren sa. Kina da hankali nustuwa wanda duk wanada ya same ki ba zai yi sanya wajen kukawa dake ba. Kina da ilimi da tarbiyya wanda ba wanda zai so rasa irin ki a rayuwar sa domin wanda ya same ki ya gama dace a duniya sauran sa kiyama. Kuma ance mace ta gari ita ke taimakawa mijin taya shiga aljanna. Ina mai bakin cikin rabuwa da ke ina bakin takaicin rasa wannan baiwar ina yiwa ya'ya na bakin cikin rasa ki a rayuwar su."


Kirjina ne ya tsanan ta bugu amman bana jin zan daina karanta wannan takardar dan sam ban gane me Fu'ad ke nufi da wadan nan kalaman ba. Dole na cigaba da karantawa ko dan na gane me takardar ke nufi. Wannan yasa na mai da kai ina mai cigaba da karanta takardar. Amman fa gumi duk ya gama wanke jiki na ban san na menene ba.

"Fateema kiyi hakuri da duk abinda zan aika ta miki *son ki shi ne sanadi" faruwar duk abinda zan aikata miki. Ba tin yau ba na dauki alkawarin cewa zan samar miki farin ciki ko da zai kasance rasa rayuwa tane. To wannan alkawarin yana nan dan haka a yanzu nake son na sauke nauyin wannan alkawarin ko na samu nutsuwa dan nasan zaki kasance cikin farin ciki na har abada.

Duk da a yanzu nagabe sai dake duniya zana more rayuwa. Domin daga lokacin da aka daura auren mu na kara jin ki a cikin jinin jiki na. Domin son ki a  jini yake,  ko naso ko kar naso nasan zan shiga damuwa duk da nasan farin cikin ki shibe nawa. Kuma in dai nayi tunanin kina cikin farin ciki nima zan ji farin ciki na saka wacce na fi so farin ciki. Na amince akan hakan kwarai.

Nayi burin zama dake da'iman a rayuwa. domin tin da na same ki na fada miki kika zamen min kamar jini ko, ko ince idanuwan gani domin zama na dake ya haskakan rayuwa na samu alherai na dan zaman da mukai. 

Ni dai nasan a duniya ba macen da zan kuma kalla da sunan mace domin duk ka mata basa da kwarjini,  kyau,  cikar hallita ba tin yau ba na jima da gane hakan domin kuwa  duk garin nan na bincike ni a  guna kadai nake gani a matsayin 'ya mace.

A fagen son ki bana faduwa na komai zanyi ba zan fadi ba. Na sadaukar da rai ake ko dani zana rasa rayuwa. Kece sarauniya ta wacce ke mulkin zuciya ta. Nasan har abada ba wacce zata kara shiga zuciya ta domin makullin ta na wajen ki kin burne a cikin jikin ki inda ba wanda yasan a inda yake. Duk hankali na gun ki ya karkata. Sunan ki shi zai tsaya min a zuciya.

Zuciya ta tana ta damuwa akan wannan ranar ta rabuwar mu.

Kiyi hakuri ki yafe min,  ki yafe mjn ni baki min komai ba in ma kin min na yafe miki duniya da lahira nima ina fatan ki yafen in na bata miki a tsawon zaman mu."


Ina zuwa nan naga alamar jikewa wanda ko ba a fada ba nasan hawayen Fu'ad ne. Ban an kara ba naga nawa ma na diga,   sam ban san kuka nake ba. Hannu na sa ina shafo fuska ta.. Ruwan hawaye na shafo wanda suke bin kuncin na suke zuba a jikin na dago takardar shi yasa ya dinga a inda na Fu'ad ya diga. Juyo da takardar nayi ina mai cigaba da karantawa amman hannu na gaba daya rawa yake.

"Ba zan fasa nemab yafiyar ki ba Fateema nah......

Amman kiyi hakuri Fateema na sauwake miki igiyoyin aure na dake kan ki gaba daya uk.……"

Washe gari da safe Momy kadai ce ta yi aikin abin kari ta gama ta gyara gidan ta hade shi da turaren wuta. Yasmeen ta tasa tai wanka ta shirya sannan tasa ta zo ta tashe ni.+


Da Sallama ta shigo dakin Gani na tayi kwance akan gado wannan yasa ta kira sunana

"Anty! Anty!!"


Jin ban amsa ba yasa ta fita. Momy tace

"Ta tashi?"

Kai Yasmeen ta girgiza tace

"A'ah bacci take!"


"Zauna ki karya ki wuce kada ki makara."

Nan ta hada tea ta nufi dakin Baba Uwani. Tana zaune akan sallaya tin asuba bata tashi ba. Zama tayi tana fadin

"Baba ina kwana?"


"lafiya lou. Kin tashi lpy?"

"Alhamdulilah! A kawo miki abincin nan ne?"


"A'ah barshi yanzu zan fito so nake nayi walha gaba daya sai na fito. Ina Fateema ne?"

"Yau bacci take yi bata tashi ba"


Momy ta mike ta fita tana kara gyagyara gidan. Karfe goma Baba Uwani ta fito sannan ta karya.

Abin ya basu mamaki domin har sha biyu ban fito ba. Momy tace

"Bari naje dai naga wane irin Bacci haka yau Fateema take haba har sha biyu."


Baba Uwani tace

"Ai na fada miki kila ba ita kadai bace."


"Uhmm!"

Kadai Momy ta fada tayo daki na. A kife ta sameni akan gado wannan yasa ta karaso da sauri tana fadin

"Fateema lafiya kuwa?"


Jin shiru yasa ta girgiza ni sai a lokacin ta lura da kamar bana numfashi. Cikin tashin hankali Momy ta hau kiran suna na tana saka hannun ta a kofofin hanci na. Tare da girgixa ni. A kideme ta fice a dakin tayi hanyar waje.


Baba Uwani na ganin ta fita ta mike tana fadin

"Lafiya?"


Momy bama tasan tana yi ba ta fice dan kira driver. Tana fita ta ci karo da Yaa Kamal zai shigo wannan yasa tai saurin kamo hannun sa tana fadin

"Zo ka gane min Fateema kamar bata da rai."


Haka tai ta jan hannun sa har dakin da Fateema take kwance. Baba Uwani suka gani a kai na tana shafa min ruwa a fuska amman sam ko gezau ban ba. Yaa Kamal bai tsaya wata wata ba kawai ya dauke ni. Momy da Baba Uwani suka biyo bayan mu. A mota ya saka ni muka wuce asibiti emergency.

Muna zuwa aka amshe ni suka shige daki dani. Momy na zarya hawaye na zubowa a idon ta addu'a take Allah ya tashi kafadu na kawai. Baba Uwani na zaune sai salati take tana fadin

"Jiya fa har sha daya muna zaune a falo muna ta hira sun cikan ciki da dariya ita da yar uwar amman jibi yau yadda muka dauke tankamar gawa. Kai Allah dai ya gajarta wahala. Yanzu in mutuwa ce ma shikenan. Inna illiahi eainna illahir Raji'un. Kai Allah dai ya tashi kafadun Fateema. Allah ka bata lafiya."


STORY CONTINUES BELOW

Abinda Baba Uwani take ta fadi kenan. Ba a minti bata ce

"Oh jiya fa har sha daya muna tare."


Haka tai ta jimami Momy kuwa gaba daya bata cikin nutsuwar ta. Suna ganin yadda Nurses ke kaiwa da kawowa a dakin da aka shiga da ni hankalin Momy ya dada tashi domin tin karfe daya saura har akai la'asar ba wani bayani daga likitoci dan nurses ke gani kawai suna kaiwa da kawowa.


Abi har magariba sannan suka ga Nurse da likitocin sun fito. Doctorn bai tsaya ba ya wuce office din sa. Sai da yai sallah la'asa da magariba sannan ya nemi yaga iyaye na.


Baba Uwani da Yaa Kamal ne suka zaune amman Momy ta kasa zama tana tsaye a bayan Baba Uwani duk idon ta ya zurma na yini daya kawai.


Bayan Likita sun gaisa da Yaa Kamal yace

"Ya kuke da ita?"


"Doctor please ka fada mana me yake damun 'ya ta?"

"Ki kwantar da hankalin ki."


Yaa Kamal yace

"Wannan Maman ta ce."

Ya nuna Mommy sannan ya nnuna Baba Uwani yace

"Wannan kuma Kakar ta ce. Sai ni cousin nata ne?"


Kai doctor ya gyada yace

"Da can tana da hawan jini ne?"


Kallon kallo su Momy da Yaa Kamal suka tsaya yi. Can Momy ta girgiza kai tace

"A'ah gaskiya."


Ajiyar zuciya ya sauke yace

"A gaskiya a yanzu ba zamu ce komai ba domin dai na duba naga jinin ta ne yai mugun hawa sai wani abu da ta gani ya firgita ta har ya sa zuciyar ta a wani hali. Allah ya takaita wahala bata buga ba amman gaskiya tana cikin hatsari dan haka nake son naji ko akwai abinda kuka san na damun ta."


Hawaye ne ke zubowa a idon Momy tace

"Innalillahi wainna illahir rajiun. Ni kan Fateema bata ce min tana da damuwa ba ko Baba da tazo kinga alamar tana da damuwa?"


Kai Baba ta girgiza tace

"Gaskiya babu."


"Shikenan. Yanzu dai ta shiga comma. Munyi iya yin mu dan ta dawo amman a gaskiya abin sai addu'a. Yanzu zamu tsaya har lokacin da zata farga sai muga me ake ciki. Ku kwantar da hankalin ku zata farka da yaddar Allah."

Momy dai kasa magana tayi.


Yaa Kamal ne ya iya magana yace

"Mun gode Doctor!"


Sannan ya mike Momy da Baba Uwani suka biyo bayan sa. Dakin da aka kwantar da ni suka shigo. Duk kansu sai dasuka tausaya min domin da kanganni kamar gawa. An saka min oxygen ga drip dake sauka a jiki na.


Durkusawa Momy tayi ta kama hannu na. Sai ta fashe da kuka. Kasa magana tayi sai kuka da take yi. Baba Uwani ta karaso wajen Momy ta dafa ta tace

"Ki daina kuka addu'a zaki mata."


Kai Momy ta gyada. Suna zaune akai sallah isha'i wannan yasa Yaa Kaamal ya tafi masallaci. Su Momy sukai anan dakin. Sai karfe takwas ya dawo da abinci daga gidan su.


Sam Momy kasa ci tayi. Wajen karfe tara suka tafi da Baba Aka bar Momy a waje na. Bayan ta fadawa Baba Abubuwan da zata hado Yaa Kamal ya kawo mata.************************************************************************************************************************************

Shawarar da zuciyar sa ta bashi shi ya fara amfani da ita. Dan har kasuwa ya aika aka dauko mahaifin Aisha. Bayan yazo suka gaisa cikin mutunci da girma. Anan Baba ya samu damar masa godiya bayan sun karene. Aliyu ya kalle shi cikin jin kunya yace

"Baba daman Aisha nake so shine nace ya kamata na fada maka kafin na isa wajen ta."


Baba kallon mamaki yake shin a ina Aliyu yasan Aisha har da yake son ta.

"Amman a ina kasan Aishan?"


"Nasan Aisha a lokacin da sukai sauka naje makarantar su. Anan na ganta kuma naji ina son ta shine nake son na fada maka ko zaka ban dama wajen zuwa gareta."

Shiru Baba Yayi yana nazari. Can yace

"Aisha tana da wanda yake son ta. Amman hakan ba zai hana na baka dama ba dan ban san me Allah ya hukunta ba. In har Aisha ta amshi soyayyar ka to ni ba abinda zanyi sai dai nace Allah tabbatar da alheri in kuma bata amsa ba sai dai nace kayi hakuri"


STORY CONTINUES BELOW

Jin jina kai Aliyu yayi dan tin daga wannan kalaman ya san tabbas Abba bai da son abin duniya da yana dashi a take zai ce ya bashi ba sai ya tambayi Aisha ba. Dan haka yace

"Toh Baba nagode amman dan Allah ina da wata bukata"


Kallon sa Baba yayi yace

"Tame fa?"


"Bana son ka fadawa Aisha koni wanene na fison ta amshi soyayya ta a yadda zan je mata."

Murmushi Abba yayi a ransa yace

"Kayi dabara dan da kyar in tasan waye kai ta amshi soyayyar ka."


A fili kuma yace

"Ba matsala!"

Nan Aliyu yayi godiya sannan ta mike da kansa suka fita da Baba. Shi da kansa ya mai da Baba har gida sannan ya debo kudi masu yawa ya mika masa amman sam Baba yaki amsa duk yadda yayi Baba yace ya amsa ki yayi yace

"Kayi hakuri nagode. Allah buda."


Aliyu bai ji dadi ba amman haka ya hakura ya koma gida.

Baba na zuwa gida ya fadawa Ummah duk yadda sukai. Shiru Ummah tayi tace

"Amman kasan Muhammad shike son ta ko?"


"Na sani Masa'uda. Ya kamata mu bata dama itama ta fitar da zabin ranta. In har ta kula Wannan ta nuna bata son Muhammad in kuma taki amsar sa ta nuna Muhammad take so. Ni ba zan wa Aisha auren dole ba. Zan bata miji nagari wanda take so. dan ko ta zabi wannan din in har bai da halaiya mai kyau a gaskiya ba zan bashi ita ba."

Kai Ummah ta gyada. Tace

"Toh Allah zaba abinda yafi alheri."


"Amin Amin."

Sam Baba ma baiwa Aisha magana ba.

Tin daga ranar da Muhammad yazo sai ya dauke kafa daga zuwa gidan su Aisha duk yadda zuciyar sa ke azalzala shi da yaje amman fir yaki ya amince da hakan. Domin yana son ya fahimci rashin sa a tare da ita da rashin ta a tare dashi.


Yini yake tunanin ta da zancen ta ya kasa aikin komai dan a iya kwana daya da yayi bai je gare ta ba ba karamin hali ya shiga ba dan sosai ya damu da son yaje ya ganta. Amman ya danne yaki yaje din.


Wannan yasa yake making kan sa busy sosai dan yana son kar tunanin ta yana damun ta dan in ya tafi gidan gwamnati ma baya komawa gida sai bayan isha'i da ya komai yai wanka ya ci abinci ya kalli news wani lokacin yai waya da gida amman duk da haka da yaje kwanciyya bacci tunanin ta zai dabaibaye zuciyar sa.


Hatta Maryama da taji basa waya da Aisha kwana biyu sai da ta tambaye sa amman yace bata nan ne. Da tace Wacce Aisha sai yace 'yar wani makwabcin sa ne.


Da kyar ya iya kwana biyar a wannan halin amman ji yake tamkar yayi sati biyar ko wata biyar bai ganta ba. Gaba daya zuciyar sa da kwakwalwar sa ta shiga damuwa.


*

Aisha kuwa washe gari tana saka ido da ganin sa amman taga shiru haka next day ma abin fa ya bata mamaki dan kwata kwata bata zaman tsakar gida sai daki ga wasan yar buyar da ta fara da Yaa Muhammad da taji shi zata kwanta kamar mai bacci haka zai shiga dakin in ya ganta a haka ya juya ya fita. Dan sai ya zata bacci take.


Lokacin da akayi kwana biyar ba Aliyu duk ta gama jigata da rashin da dan sosai tayi rama ta rasa me take ji a game dashi har kuka take in ta tsinci kanta da tunanin sa ta rasa me yake mata dadi kwata kwata zuciyar ta tai mata zafi da kunci.

Abun ya hade mata ne ga son sa ga yadda Yaa Muhammad ke saka ta a gaba duk da tana boyewa gareshi amman bai fasa ba. Wannan yasa abin ya hade mata ga bata da wanda zata fadawa ga yarinta dake damun ta a bangaren.

Yau ana tashi a isilamiyya ta nufi gidan sa tana zuwa taga Mai gadi. Gaishe shi tayi ya amsa yana murmushi. Shiru tayi can tace

"Baba ya dawo kuwa?"


"A'ah bai dawo ba."

"Sai yaushe yake dawowa yanzu?"


"Gaskiya yana kai wa wajen Isha'i."

Murmushi tayi tace

"Nagode sai anjima!"


Ta juya tana tafiya tana sake sake. Kuka kawai take son tayi dan idon ta ma yayi jajir tin kan ta fara kukan. A kofar gida ta hadu da Yaa Muhammad bata kula shi ba tayi cikin gida da kallo ya buta can kuma sai ya mike yabi bayan ta.


Tana shiga tayiwa Ummah barka da gida sannan tayi cikin dakin ta. Tana shiga ta fada saman katifa tana fashewa da kuka. Yaa Muhammad da ya biyo ta ya tadda ta a wannan halin tsaya kallon ta yayi na mintina sannan ya shiga dakin. Dago ta yayi tana ganin shine ta fada jikin sa tana mai sakin wani sabon kukan.


"Ya salam me ya ke damun ki Aysher na?"

Kai ta hau girgiza masa. Komai bata boye masa na rayuwar ta amman yau sai taji tana kunyar sanar da shi wannan halin da take ciki.


Rumgume ta yayi yana lallashi ta can yace

"Kada ki manta nine kadai mai baki shawara Aisha dan Allah ki daina kukan ki fadan me yake damun ki kinsan zan fiki shiga tashin hankali da damuwa ko?"

Tasan da haka dan haka ta hadiye kukan. Kallon ta yayi yana fadin

"Fada min me yake damun ki. Tin last time zuwa na nagane kina cikin damuwa akwai abinda ke damunki nayi shiru nevdan naga ko zaki fada min amman naga abin sai gaba yake kara yi. Please Aisha ki fadan me yake damun ki ko naji sanyi na taimaka miki. Kada ki manta nayiwa Mamahn ki alkawarin kulawa dake tamkar ita tamkar yadda ta kula dani shin yanzu in tazo ta ganki a wannan halin me kike zaton zata ce ko zata tsammani?"


Shiru tayi tana tunanin ta inda zata fara can dabara ta fado mata tace

"Yaya ina son ganin Mamah na. Yaya ni Mamah bata so nane ta tafi ta barni tin ina yarinya bata kara waiwayo ni ba."


Dago kanta yayi yana kallon cikin idon ta da sauri ta lumshe idon ta. Shima lumshe na sa yayi ya bude a hankali sannan yace

"Wannan ba ita kadai bace damuwar ki. Naji kina kewar Mamah ki kuma nasan Mamahn ki zata zo koman daren dadewa kuma nima na miki alkawarin kai ki gare ta."


Kai ta gyada tana sauke ajiyar zuviya ya ce

"sai me ke damun ki?"


Kai ta girgiza murmushi yayi yace

"Yanayin ki yana nuna na alamun kina cikin wani hali Aisha. Ko dai...?"


Sai yai shiru. Dagowa tayi tana kafe shi da manyan idanun ta tace

"Ko dai me?"


Murmushi yayi ya zura hannun sa a aljihu ya zaro wata karamar waya tecno ya mika mata yace

"Ga waya nan na siyo miki in na tafi makaranta mana gaisawa ko?"


Amsa tayi tana murmushi tace

"Kai Yaya na nagode Allah kara budi. Nagode sosai."


"Banda godiya kanwata."

Tai murmushi tana juya wayar a hannun ta. Kallon ta yake yana murmushi bama da yaga ya korar mata damuwar ta. Jin ana kiran sallah yace

"Kinga an kira magrib tashi kije kiyi alwala bari na tafi masallaci."


Ya mike itama ta mike tana cire hijab din jikin ta.

Yana fita ta cire uniform din ta sannan ta dauki wani dogon siket baki ta saka da wata orange kalar bodyhuge. Sannan ta fita ta dauro alwala. Tana dawowa daki ta saka wani brown hijab din ta ta tada sallah.


Tana idar sallah ta zauna akan sallayar har akai isha'i tana idar wa ko shafa'i da wuturi ba tayi ba ta mike ta dauki wani littafi ta saka a cikin rigar ta sannan  tayo waje.

Ummah da ta mike zata yi shafa'i da wuturi ta ganta tayo wajen ta da sauri.

Kallon ta tsaya tana karasowa tace

"Lafiya?"

Kai ta hau sosawa tace

"Ummah daman littafi na zan amso wajen Fadila dake can kasan layi."


Kallon ta Ummah tayi tace

"Da ki bari Yayan naki ya dawo sai ya rakaki."


"Ummah sauri nake so nake da ya dawo ya koyan kar dare yayi gobe Malam zai amsa ne."

Ta fada tana yin kasa da kai.

Ummah tace

"Shikenan kiyi sauri kar ki jima."


Kai ta gyada ta fice da sauri. Tana fita ta dauki hanyar gidan Aliyu. Tafiya take da sauri dan bata son Ummah taga ta jima duk da gidan su Fadila da tazara amman dai tafi son taje ta dawo a yadda ta fada din.


Tana isa ta tsaya tana hakki dan yadda tai saurin. Baba mai gadi yana masallaci dan haka ta shiga ta tsaya tana mai da numfashi. Kamar daga sama ta gano hasken motar sa. Baba Mai gadi da fitowar sa a masallaci kenan ya taho da sauri ya bude masa gate.

Boya tayi a bayan wata mota. Yana parking ya fito a matukar gajiya da galabaita dan rashin Aisha ya saukar masa da kasala da galabaita ta yadda yake jin sa kamar mara lafiya. Motar ya rufe Baba Mai gadi na masa sannu da zuwa ya daga masa hannu kawai yai gaba.


Yana zuwa gun motar da take ya tsaya. Sanye yake cikin Brown kalar wando da orange kalar riga kayan sun amshe shi. Sai tashin kamshi yake. Ganin ya tsaya yasa ta fito ta tsaya a gaban. Ido ya zaro ganin ta a gaban sa. Domin wajen akwai haske kamar rana. Kallon sa take idon ta ya cika taf da hawaye shima kallon ta yake cikin so da kauna wanda bai san yana mata irin su ba.


Bai aune ba sai ganin hawaye yayi yana bin kuncin ta nan da nan hankalin sa ya tashi. Kai ya hau girgiza mata sannan ya saka hannu yana goge mata amman sai tai sauri ta juya masa baya. Da sauri ya koma gaban ta yana fadin

"Menene to?"


Baki ta turo irin na shagwabar nan kamar zatai kuka tace

"Me nayi maka ka daina zuwa gidan mu?"


Hannun sa ya zura a aljihu yana bin ta da kallo. Abinda ya kara harzuka ta tace

"Au Kallo na ma ka tsaya ina tambayar ka?"


Sai kawai ta juya zata bar wajen cikin zafin nama ya saka hannu ya kamo hannun ta ya finciko ta ta fado kansa. Dagowa tayi suka tsaya kallon juna sun yi minti biyu ahaka sannan tai saurin janye jikin ta daga nashi.


STORY CONTINUES BELOW

Ido ya lumshe sannan ya bude a sanyaye.

"Kiyi hakuri aiyuka sukai min yawa ne."


Baki ta dan turo tace

"Shikenan daman nazo naga ya kake ne kawai?"


Ta fada idon ta na kawo hawaye domin abun da take ji game da shi da kewar sa da tayi.

"Sai da safe!"


Ta juya zata tafi. Hannun ta ya riko sannan a hankali ya taka ya karasa gaban ta. Kan ta a kasa wannan yasa ya saka hannu ya dago da kan nata. Kallon juna suke suna sakar wa da junan su murmushi.

"Muje na rakaki dare yayi."

Tai gaba ya bi bayan sa. Mai gadi yayi mamaki ganin Aisha dan sai a sannan suka gaisa ta fice. sai yai zaton ko tare suke da shi.

Suna tafe kowa yai shiru yana sake sake a zuciyar sa. Can yace

"Tayaya kika samu kika fito a yanzu?"

Littafin jikin ta tafito dashi tace

"Haka nace zanje amsar littafi na."

Tsayawa yayi yace

"Wato kin kasa zama sai kin ganni ko?"


Fuska ta rufe da hannu tana murmushi yayi murmushi yace

"Ai na zata ba a bukatata ne ma?"


Fuska ta bude tana bata rai tace

"Yaa AK ka min abu da yawa a rayuwa ta da yasa ba zan taba mantawa da kai ba. Ka koyar dani ka bani kula da farin ciki nima dole na damu da son sanin a halin da kake."

Murmushi yayi yace

"Aisha kenan."

"Aisha in nace zan fada miki yadda nake jin ki a rayuwa ta da komai nawa zaki zaton karya nake. Amman Aisha ki sani rasa ki a rayuwa babban matsala ce a gareni."

Dagowa tayi taga shima ita yake kalla saurin dauke kan ta tayi zatayi gaba yace

"Bakya son rakiyar."

"Barni a nan kar Yaa Muhammad ya gan mu tare a daren nan yace daga ina nake."

Murmushi yayi ya zura hannu a aljihu wata karanar waya ya fito da ita ya mika mata yace

"Amshi zan kira ki anjima."


Ido ta zaro ta girgiza kai tace

"A'ah Yaa AK nima dazu Yaa Muhamnad ya kawon waya"

"Bani number?"

Ido ta zaro wanda ya zame mata kamar jiki duk abinda zatai sai tayi da ido ko da gira dan haka tace

"Tab ai bam masan number ba."


Pen ya ciro a aljihun sa ya kamo hannun ta ya rubuta mata number  kallon numberlr tayi taga special ce nan da nan ta haddace ta kalle shi tace

"Bari na tafi sai da safe."

"Ki kirani in kinje gida."

Kai ta gyada kawai tai gaba. Tsayawa yayi yana kallon ta har ta bace masa da gani sannan ya juya ya koma gida.

Ta haka kadai yasan Aisha ta damu dashi. Kuma kamar yadda faisal ya fada masa ya samu gamsuwa wajen Aisha sauran sa sanar da ita kawai.


Gida ya koma yai wanka ya zauna kallo. Yau jin sa sakayai kamar bashi ba duk nauyin dake kan sa na lokaci da suka wuce babu shi.************************************************************************************************************************************

Satin na daya ban san a wane hali nake ba. Amman kullum cikin min allurai da saka min ruwa ake. Momy ta rame sosai dan ko abinci bata ci.

Kullum Suraiyya zata zo dan sai dare take tafiya. Baba Uwani ma da yamma take zuwa da dare Yaa Kamal ya mai dasu ita da Yasmeen.

Ranar da nayi kwana takwas a ranar na farka likitoci kuwa sukai min caa a ka domin kuwa sunfi awa hudu akai na sannan sukai min allurar bacci.


Suna fitowa a dakin Momy ta karasa wajen su tana kuka tana fadin

"Ya jikin nata?"

Murmushi Dr ya sakar mata yace

"Mama ki kwantar da hankalin ki. Fateema taji sauki zata farka nan da anjima insha Allahu."

STORY CONTINUES BELOW

Hannu biyu Momy ta daga tana fadin

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Allah ka bawa Fateema lafiya ka tashi kafadun ta."


Ta rufe fuskar ta tana mai zubar da hawaye. Suraiyya ta dafa ta tace

"Muje Momy dan Allah kibar kukan nan."


Kai kawai ta gyada sannan suka dawo dakin suka samen a kwance kamar me bacci. Zama sukai Momy dai sai addu'a take a cikin ranta.

Suna zaune akai magariba suka mike suka yi sallah. Lokacin da Yaa Kamal yazo ya tafi da Suraiyya.

Karfe goma sha biyu dai dai na bude ido na. Momy na gani zaune a gaban gado na rike da alkur'ani tana karantawa. Ido na lumshe sannan na bude hannu na daga na daura akan hannun ta da sauri ta juyo tana rufe alkur'anin.

Murmushi ne ya saki a fuskar ta hawaye na zubo mata tace

"Sannu Fateema!"


Sannan ta mike tana fadin

"In tashe ki ne?"


Kai na gyada mata nan ta tayar dani ta saka mun filo a baya sannan ta fita. Bata jima ba sai gata da nurses guda biyu sun shigo nan suka duba ni sannan suka Komai normal a bani ruwan dumi na sha. Sannan ai min wanka da ruwan dumi.


Suna fita Momy ta shiga ta gada ruwan dumi ta fito ta kamani muka shiga. Ita tai min wanka muka fito ta shafen jiki na da mai sanna ta nufi gun flask din tea ta zubo min ta hada min tea.


Da kanta ta dinga bani. Kadan nasha na koma na kwanta ina mai lunshe ido na. Da sauri na tashi tinawa da nayi cewar Fu'ad ya sake ni. Sai na fashe da kuka. Momy tayo guna tana fadin

"Menene?"

Amman sam naki yin magana sai kuka da nake har numfashi na na daukewa. Sai kuma na dinga yin tari ina dafe kurji na da sauri Mony ta fita ta tafi gun doctor tare suka shigo nan ya hau min sannu da kyar na lafa da tarin amman hawaye bai daina zuba a ido na ba.


Allurar bacci ya karai min dan a lokacin yana duba BP na yaga ya kara hawa sosai. Komawa Momy tayi ta xauna itama tana mai sakin kuka. Doctor bayan ya gamai mun abinda zaimin ya dago ya kalle Momy yace

"Hajiya ki kwantar da hankalin ki komai zai xama normal."


Kai Momy ta gyada tana fadulin

"Allah yasa."


Sam ranar Momy bata runtsa ba to daman can ai ba ta samun baccin amman yau akan sallaya ta kwana. Sai asuba na farka nima. A kan gado nai alwala nai sallah sannan na koma bacci ya kuma dauke ni.


Bani na farka ba sai da Doctor ya shigo. Zaunar dani nurses sukai suna min sannu na amsa ido na a lumshe. BP na ya kara auanawa yaga ya sauka akan jiya da daddare dan haka a lokacin ya hau min tambayoyi.


"Sannu Fateema!"

"Yauwah!"


"Ya jikin?"

"Da sauki!"


Ajiyar zuciya ya sauke yace

"Shin akwai abinda kika gani ya razana ki ne?"


Ido na lumshe hawaye na zubo min. Kallo na ya tsaya can yace

"Kiyi hakuri ki kinji. Komai na duniya fararre ne kararre. Ki mika komai ga Allah Allah yana tare dake insha Allahu."


Kai na gyada yace

"Wani abu ne ya razanar dake ko?"


Kai na gyada har lokacin ido na zubar da hawaye. Yace

"Daman kina da Hawan jini ne?"


Kai na gyada masa.

"Wane maganin kike sha?"


Nan na fada masa ya karai min wasu tambayoyin daga karshe ya kare maganar da

"Me yake miki ciwo yanzu?"


Kirjina na nuna masa. Ya gyada kai yace

"Kan ki fa?"


Kai na gyada masa domin daga kai na har wuyana duk ciwo suke min ido na kuma kamar me nake jin sa dan zafi.


Rubutu yayi ya mikawa nurse yace

"Wadan nan magungunan za a siyo mata ta fara amfani dasu mu gani."


Sannan ya mike yana kallo na yace

"Ki daina saka tunani a ranki sannan kina shan magani insha Allahu komai zai zama normal."


Kai na gyada na kwanta kurjina na suya da radadi. Ban jima da kwanciyya ba Momy ta shigo dan haka ta hadan ruwa nai wanka na fito na saka kaya. Tea kadai nasha na kasa cin komai. A lokacin ma kukan kasawa nayi amman jin wani abu nayi ya tsaya min a makoshi wanda nake tunanin da in nai kuka zan ji ya fada min.

Kwanciyya nayi na lumshe ido. Ban jima ba naji sallamar su Baba Uwani da Suraiyya da Yaa Kamal har da Basma da taki zuwa ckul duk da yai asabar bata je tahfiz ba.


Tana shigowa tayo kai na tana fadin

"Antu!"


Na juyo ta rumgume ni sai hawaye ni kuwan nama kasa kukan. Hannun Suraiyya na kama ina mai kallon ta. Tace

"Sannu ya jikin?"


"Alhamdulilah!"

Na kalli Baba Uwani nace

"Ina kwana?"


"Lafiya Sannu Fateema ya jikin?"

"Alhamdulilah!"


Yaa Kamal ma ya matso yana fadin

"Ya jikin?"


"Da sauki."

Na bashi amsa. Basma na bani labari. zuwan su ba karamin dadi yai min ba dan ko na fara tunani zasu tabo ni da hira da abin dariya.


Muna zaune Maman Suraiyya ta shigo da abincin rana nan ta min ta jiki. Bata jima ba sai ga Umman su Yaa Kamal nan itama da abincin kullum haka suka kawo na rana da na dare har da na safe ma.


Sun ji dadin gani na a kwance. Basu tafi ba sai dare wanda ya rage dagani sai Momy na. Naga tarairaya gun ta da wadan da suka zo gaba dayansu.Post a Comment for "WA NAKE SO CHAPTER 8"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...