WA NAKE SO CHAPTER 5 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WA NAKE SO CHAPTER 5

WA NAKE SO CHAPTER 5

- - Post a Comment

 WA NAKE SO CHAPTER 5
Tin daga ranar kullum major AK na dawowa daga gidan gwamnati yake tafiya gidan su Aisha Wanda wani lokacin ma a hanya suke haduwa su karasa tare.+

Sosai suka shaku da juna, Dan kullum zai zo ya koya Mata karatu Wanda In har kana son Aisha ta so ka ko tana kula ka to kana kawo mata zancen makaranta.


Wata Ranar alhamis Mamah ta manta Bata bawa yayen Aisha su yo nika ba. Dan har sai da ta daura ruwan tuwon sannan taje Dan ta debo gari tayi talge amma Sai taga Babu wannan yasa ta bawa Aisha taje tayo nika.


Amsa tayi tana fita Major AK na karasowa. Murmushi yayi tace

"Ina yini?"


"Lafiya Lou. Ina zuwa?"

Baki ta Dan turo tace

"Nika Zan Kai baka ga layi ba Kuma."


Murmushi yayi yace

"Shine zakiyi kuka Kuma? Muje na rakaki."


Nan suka fara tafiya suna Hira jifa jifa. Can Aliyu ya kalli Aisha yace

"Kanwata ina son ki fada min dalilin ki na son ganin gwamna.


Kallon sa ta tsaya Yi sai Kuma ta cigaba da tafiya tana fadin

"Baka manta ba Ashe!"


"Tayaya zan manta bayan shine dalilin haduwar mu."

"Haka ne!"


Suka cigaba da tafiya can Kuma tace

"Hakika nin gaskiya shugabanci bala'i ne, Wanda ba Zan so wani nawa yayi ba Amman Kuma in har hakan zai zama hanyar da za a kubutar da wasu daga wani Hali Abu ne Mai kyau."


"Uhmm!"

"A gaskiya abinda gwamna yayi wa mahaifina ya tsaya min a Rai....."


"Wane gwamnan?"

Ya katse Mata maganar ta.


"Dan uwanka!"

"Nasan mahaifin ki ne?"


Yai Mata maganar dan shi bai san ma  yayi ba kuma shi ba wanda ya sani a garin ba.

Kallon sa Aisha take da Mamaki sai kuma tace

"Gwamna nace!"


Dan basar wa yayi yace

"Ina nufin yasan mahaifin ki ne?"


Kallon sa ta danyi sai kuma ta dauke kai tace

"Mahaifina yana daya daga cikin masu masa aiki a gidan da kake. Wanda Ranar da ya nemi ganin ma'aikantan a lokacin mahaifina yana Jin zazzabi ya taho gida wannan yasa a washe gari da yaje ya je Dan ya bashi hakuri Amman kasan bai saurare shi ba sai ya kore shi"


Ta dago tana kallon Aliyu Ido cikin Ido tace

"Shin haka shugaba ya Dace suyi a matsayin sa na shugansu da suke aiki a gidan su ai ya kamata yaji uzurin sa akan ya zartar da hukunci. Shin yasan ladan da yake samu na daukar mahaifina aiki da yayi. Hmmm! Kasan me zai ciyar da marainiyya ya tufatar da ita ya ilimantar da ita bayan haka iyalan sq suma duk zai musu haka. Baka zaton duk da Mahaifina aiki yake. Aba Biyan sa Amman shima zau samu lada Dan ya taimaka masw ya ciyar da iyalan sa."


STORY CONTINUES BELOW

Wajen nikan suka karasa ta ajiye a layi sannan suka matsa gefe tana fadin

"Wannan shine dalilin son ganin gwamna da nake Yi ina son in masa nasiha akan duniya da mulki Amman tin da gaka zan maka Kai Kuma kaji tsoron Allah tin da kana tare dashi. Ka fada Masa gaskiya ya kula ko ta wannan sanadin ya tsira."


Aliyu Sam ya Manta da ya kori wani bare har ya tuna wanene ma. In ya kalli Aisha yaga yadda take magana with full of confidence ba tsoro tana burge shi. Dan da yawa mutane na da sanin gaskiya amman tsoro da son abin duniya Sai ya hana su fadin gaskiyar. Lallai Aisha ta wuce tunanin sa da sanin sa. Zama da ita zai Ankara da Kai abubuwa da dama.


Duk Yana wannan tunanin ne a lokacin da ya zuba Mata Ido.

"Kallon fa?"


Ta fada tana fadin

"In har mutun na son mulki na gaskiya Sai ya cire son zuciyar sa daga neman azurta Kansa daga dokiyar talakawa Dan dukiyar dake hannun sa ba tashi bace ta talakawa ce. Sai ya sa wa zuciyar sa cewar aljannar Sai zai nema daga wannan mulkin in ba haka ba kuwa son duniya zai rude shi Amman in har ya San aljannar sa zai neman zai cire son zuciya ya bautawa ubangiji.

Akwai hadisin da Annabi yake cewa

"Shugaba makiyayi ne, Kuma za a tambayar shi Akan kiwon sa."

Kasan me hakan yake nufi kuwa? Dole ne ko wanne shugaba ya kula da mutanen da yake jagorantaka saboda a gobe kiyama Allah zai tambaye shi tayaya ya mulki Al ummar sa.

Yanzu da aka ce shugaba bawan Al umma ne, hakan Yana nufin Sai yayi aiki tukuru dan ganin ya kula da ko wacce Al umma dake karkashin sa.

Yana da kyau shugabanin mu su San cewa akwai gobe kiyama Ranar da Allah zai tsaida ka Dan Jin yadda ka kula da Al ummar ka.

Meyasa idon mu ke rufewa in Jin dadi ko mulki ya same mu ne? Mu manta komai sai duniyar bayan duniyar ba matabbaciyya bace."


hawayen idon ta ta goge tana fadin

"Bayan lahira ita ce gidan mu tabbatace wanda ya kamata muyi iya yin mu Dan samun shi Amman ina Sam bama ta shi ta duniyar Muke kawai. Bayan duniyar gidan banza da wofi gidan da ba zamu taba dauwama a cikin sa ba. In kuka Tina ciwo zamu gane Lallai duniya abar banza ce mu nemi lahira ingantaciyya. Sai kana da lafiya lokaci daya ciwo ya same ka a lokacin zaka ji tsoron Allah domin in Allah yayi duk maganin da zakayi ba za a taba warkewa ba sai mutuwa. Mutuwa kadai Aya ce wacce zata tsorata duk wani Mai hankali da tunanin. Bayan mun mutu anan wata ayar take. A da  Kai kake wanka Kai tafiya amman a lokacin sai dai ai maka. Abinda yafi wannan Kuma kwanciyyar kabari in da za akai ka a baro ka daga Kai sai halin ka. Ya salam acan fa abin yake acan danasani take ga wanda ya aikata ba dai dai ba kenan. to kada mu kuskura mu kasance cikin masu danasani a cikin kabarin mu muyi aikin da zai raba mu da yin danasani.

Sai Kuma final stage inda in a nan zamu tafi gidan tabbatace wanda in munyi aikin dai dai mu shiga aljanna in Kuma munyi aikin ba dai dai ba mu shiga wuta Wanda ba Wanda zai so shigar ta ko kafiri bare mu musulmai da ake kwadaita mana aljanna da tsoratar da mu da wuta.

Yana da kyau shugabanin mu su kasance suna koyi da kalifofin mu kamar Umar, Usman, Aliyu da Abubakar. Ba irin mulkin wadan nan shugabanin ba da kansu kadai suka sani ba."

Tin da ta fara magana yake kallon ta. Lalai Allah yai baiwa a gun Aisha. Wani matsayi yake ji ya Bata na daban Wanda bai taba bawa wata irin da ba.


Hakika abinda yake so ana tunasar dashi Kenan Amman ba Mai masa haka Sai iyayen su. Matar sa da tafi kusa dashi a yanzu Bata tabai masa nasiha akan yaji tsoron Allah ba haka mabiyan sa.

Hakika ba zai taba barin Aisha tai masa nesa ba domin kuwa Aisha abar so ce da son kasancewa da ita ce.


Sosai jikin sa yai sanyi da Wanda Nan kalaman Aisha. Aishan ma tsoron duniya duk ya Kara kamata. Ganin an nika Mata yasa ta dauko shi ya amsa suka tafi sai dai. Yanzu tafiyar kurame ake ba me cewa uhm bare uhm uhm kowa magana yake da zuciyar sa.

A haka suka karasa gida lokacin har shida saura. Kallon sa tayi tace

"Yau dai ba karatu Dan da alama zamuyi dare a abinci zan je na taya Mamah. Nagode Alah saka da alheri Sai da safe!"


STORY CONTINUES BELOW

Kai ya gyada tayi cikin gida. Kasa tafiya yayi Sai zama yayi Akan dakalin gidan Yana zaune yana tunanin a zuciyar sa na kalaman Aisha da duk ba karya a cikin su Sai ya Kara Jin tsoron Allah da duniyar.


A haka akai sallah yaje yai sallah har akai isha'i sannan ya tafi gida jiki a matukar sanyaye. Yana zuwa ya fada saman kujera Yana bin gidan da kallo wayar sa ce tai Kara Yana dubawa yaga Maman sa ce wannan yasa ya dauka murya a matukar sanyaye.


"Ina yini Mama?"

"Lafiya Lou Baba na ya kake? Me yake damun ka?"


"Mamah tsoron duniya shi yake damu na."

Dan murmushi tayi tace

"Yana da kyau ko da yaushe kana tsoron duniya domin duniya abar tsoro ce. Kuma Jin tsoron duniya shi zai sa ka kasa aikata aiyuka na gari bama da Allah ya baka wannan mu'kamin dole kayi taka tsantsar da wadan da ke gefen  ka sannan ka samu amintacce a cikin wanda kuke tare da zai na nusar dakai. Ina Fatan sirika ta tana baka kulawa tare da kwarin gwiwa ko?"


"Uhmm Mamah ina Maryama da Abbah?"

"Suna nan lafiya. Abban ka yana bangaren Mamin ku."


"Alright zan kwanta Mamah a cigaba da samu addu'a Allah ya bamu ikon yin adalci "

"Insha Allahu Baba na. Allah ya taimaka ya taya riko kaje ka kwanta sai da safe!"


Wayar yakashe ya lumshe ido Aisha kawai yake gani tana goge hawayen idon ta. Kai ya girgiza yana mai jin wani abu na ratsawa tin daga kasan zuciyar sa. Lallai dole ya rike Aisha domin kuwa ta silar ta ya kara shiga hankalin sa da tunanin lahirarsa duk da yana yi amman ta kara zaburar dashi dole ya mike yai taka tsantsan da mulkin nan nasa duk da bai so amman yana addu'a Allah yasa ya zama silar kubutarsa.


Ranar bai bacci ba tunanin sa mulkin sa shin yana yin adalci kuwa shi dai a yadda ya sani ana yawan yin aiyuka dan ana kawo masa takardun amsar kudi za'ai kaza za'ai kaza kenan anayi din.

Washe gari da ya shiga gidan gwamnati PAn sa ya sama akan aje gidan su Aisha a bawa mahaifin ta rumfa a kasuwa sannan a bashi jari masu yawa.

Baba yana gida yana shirin fita aka aiko ana sallama dashi yana fitowa PAn Aliyu ya mika masa hannu suka gaisa. Bayan sun gaisa ne yake fada masa aiken daga mai girma gwamna ne sannan yazo suje yaga shagon da aka bashi.


Ba musu suka tafi a take aka bashi takardun shagon da kudaden. Murna wajen Abbah kamar me a lokacin ya koma gida lokacn da Aisha a dawo daga makaranta kenan ta samu wannan labarin hakikanin gaskya taji dadi sosai. Sai ta fara tunanin keman magabar ta taje wajen Gwamna lallai in har taje gwamnan nan yana da daukar shawara lallai ba yadda ta dauke shi ba

Ranar wani nishadi ta jinga ji tare da farin ciki duk wanda ya ganta a take zai gane hakan. Karfe biyu da kwata tatafi isilamiyya.

Aliyu kuwa yana can office yana ta aiki yana gano aiyikan da ake gudanar wa kamar yadda takadu ke nuna masa shi kuma yasa hannu aje a amshi kudi. In yai duba da hakan yana ganin ai bashi da matsalar komai dan haka sai yaji damuwar sa ta ragu amman a ransa akwai wani target da yake dashi wanda da kan sa da kuma dukiyar sa yake son yanayi.


Hudu nayi ya bar gidan bayan yai sallah la'asar garin ya hau zagayawa sai dai a yadda yake jin ana aiki sam sai yaga kamar ba abinda ake ba titi ka bayan hawan sa an ce anyi titika sunfi hamsin amman tin da ya hau zagaya gqrin bai ga wani sabon titi ba. Har biyar da ashirin tayi sannan yayo hanyar gidan su Aisha dan ko gida ranar bai da niyyar komawa.


Yana daga cikin motar tasa ya hango ta tana tafe cikin uniform din ta tai kyau ga annurin fuskata duk dadu. Kallon ta ya tsaya yi yana jin wani sanyi da nishadi har ta gota motar zata shiga gida yai saurin bude murfin kofar ya fito.


Tana ganin sa ta kara fadada fara'ar kan fuskar ta tace

"Ina yini?"


"Lafiya lou Aisha ya gida da makaranta?!

"Alhamdulillah! To je kicire uniform kizo muyi watacmagana yau ba lesson."


Baki ta washe tana fadin

"To ina zuwa!"


Tafiya tai cikin gida bin ta yayi da kallon yana mai girgiza kai hadi da shafa sumar kan tashi sai kuma ya lumshe ido. Shin me yake ji game da Aisha ne? Yana jin abubuwa masu yawa wanda ba zai iya misaltasu ba.

Bata jima ba ta fito fuskar ta dauke da murmushi wanda yasa kumatunta lotsawa. Kallon ta ya tsaya yi. Hannu ta tafa masa tace

"Kallon fa?"


Murmushi ya saki. Shi kan sa Aliyu yana mamakin kansa. A baya ba ruwan sa da shiga abinda ba ruwan sa dashi amman daga kan Aisha komai ya canja masa. Shine zai zauna yai ta magana ko Aishan ta cika shi da surutu amman bai ji ta gudure shi bare ta saka masa ciwon kai.


Shi da bai kallon mace amman yanzu idanun sa ba abinda suke so da muradin kalla kamar Aisha. Jin matsayin Aisha yake a jikin sa kamar yar uwar sa. Haka na matsayin ta azuciyar sa ya kasa ganewa.

Ido ya lumshe sannan ya bude ya sauke akan ta tare da sakin wata ajiyar zuciya. Itama kallon nasa take da murmushi akan fuskar ta

"Ya dai?"


Ta fada tana dage girar ta  Murnushi yayi yace

"Normal!"


"Kace za muyi wata magana!"

Shi har ga Allah ya ma manta da ya fada mata.


"Zauna mana."

Zama tayi tana kallon sa. shima ita yake kalla. Ita tai karfin halin janye idon ta.


Murmushi ya saki yace

"Tambayar ki zanyi Ayshh!"


Juyowa tayi jin yadda ya ambaci sunan ta. Kai ya gyada mata. Kai ta dauke dan wani abu ta gani a idon sa wanda ta rasa gane menene shi.


Murmushi yayi yace

"Ya kike ganin mulkin dan uwa na? Shin yana aiki ko kuwa?"


"Ba zance ba a aiki ba Yaa AK amman a gaskiya in ma anayi wani wajen basu san da anayi ba. Ilimi yana daga cikin manyan abubuwan da ya kamata gwamnati tana taimakawa amman abin sam ba haka yake ba. Zan so kazo makarantar mu kaga babu cikakun malamai, ba wajen daukar karatu mai kyau ba kayan daukar karatu duk abin sai a hankali bayan ana son kan a dau darasi ya zamaba environment din is well established with all teaching and learning material wanda zasu taimakawa yaran su gane abinda ya dace su gane, hmmmm did u know wai nan mu yan secondary ne, ina ga primary school student su tayaya kake ganin zasu samu abinda ake so for god sake. Tayaya ake ganin zamu zama wasu ko mu taimakawa al umma bayan muma ba atsaya mana akan mu zama hakan ba. Yaa AK their is problm on education in our state."


Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon sa tace

"Ilimi ya zama koma baya bayan shi ya kamata ya zama abu na farko da za a taimaka mana dashi............

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon sa tace
"Ilimi ya zama koma baya bayan shi ya kamata ya zama abu na farko da za a taimaka mana dashi.
Sai abu na biyu asibito cin mu. Yaa AK ranan da aka kai ni asibiti bani da lafiya ga malaman jinyar basa zuwa da wuri kuma in sun zo sai dai su tsaya sagadar sagadar ba zasuyi abinda ya dace ba a lokaci sai lokaci ya kure su duba mutune kadan suce an tashi bayan wani tin asuba yaje amman baza su gashin ba. Gashi sam ba sa aikin da ya dace kawai kansu suka sani ba tausayi bayan abun da ya kamata su fara kenan tausayi."1

Idon ta ne ya cika da kwalla tace
"Dalilin da yaza malam kamis na kusa da gidan mu ya rasu kenan sun kasa bashi taimakon da yake nema duk da abin yazo da karar kwana amman da gangancin su yanzu a haka zamu cigaba da rayuwa kenan.
After all kaje kaga asibtin kamar ba asibiti ba ba gyara ba tsafta gini bakyau kuma ba kayan aiki. Tayaya ba zamu na mutuwa ba ka fadamin a haka muka san an bawa garin mu jiha har an bamu gwamna da zai kula da matsalolin mu."

Murmushi tayi tace
"Da shine bai da lafiya kasar waje zai je a duba shi wannan yasa sam shugabanin mu basa damuwa da inganta abubuwan damu talakawa ke so ha. Saboda ya'yan su basa karatu a cikin mu talakawa sai dai akai su makarantu masu kyau ko a fitar dasu waje. Haka nan asibiti ma basa zuwa na gwamnati sai dai a kai su private in abun yai gaba a fitar dasu waje ka fada min tayaya zasu damu da samar mana ingantattu malami da likitoci da kayan aiki."

"Kalli matasan mu ba aikin yi wasu sun gama secondary amman ba mai daukar nauyin su har su tafi gaba da secondary sai zaman banza. wannan ba shi ke kawo bata gqri ba yan fashi yan ta'ada yan shaye shaye da sauran su. Duk da an basu abin yi zasu concentration on what to do to achieved their goals but an dakusar dasu suna ganin ba zasu taba cimma burin su ba kaga sai yi komai yazo musu.
Bamu da ruwan famfo tuka tukan ma guda daya ne damu a garin nan in kaga layi kamar me ai ta fada.
Ga ba wuta sam na manta rabon da naga wutar Nepa. Shin shi yasan da rashin ruwa da wuta da ya kunno famfo ruwa yazo haka wata 24 hours bata daukewa. Amman mu ko masallacen mu ba wuta bare generator da za'a  na kunnawa. Yan unguwa su suke dan hada kudin mai yau in akwai gobe babu a haka ake gangarawa.
Kana bin titi nan mu kuwa? Titi nan mu sun zama kamar hanya ba alamar wata coalter akai.
Yaa AK garin nan na da matsala yana matukar bukatar gyara kana bawa dan uwan ka shawara dan naga mai daukar shawara ne."

Dagowa tayi tana kallon sa tace
"Yauwah dan Allah kai masa maganar Abba nane?"

Shiru yai yana kallon ta. Tace
"Dazu aka zo aka bashi rumfa a kasuwa har da jari naji dadi naji dadi sosai amman kasan me akwai mabukata da suka fi Abbah na, bukata. da su aka taimakawa da yafi samun lada."

STORY CONTINUES BELOW
Kai ya gyada yana nazarin Aisha. Aisha tayi 100% tin da yake bai taba ganin aibun ta ba kullum cikin iya zance a hikima da hankali da nusar da mutun take sam bata da son kan ta tafi son wasu akan ta.

"Muje naga tsarin wajejen naku!"
ya mike ta bi bayan sa. Suna tafe tana nuna masa unguwar tasu haka suka karasa wajen tuka tuka nasu inda yake cike da mutane kamar kasa. Ya jima yana kallan yadda ake layi wasu suyi fada wasu na wasa wasu hira haka dai. Daga nan sukai gaba har wajen da samarin su marasa aikin yi ke zaune wannan ya buga tagumi wannan yana bacci wasu na hira wasu karta haka dai abin ba dadi.

Kan su gama zageye unguwar jikin Aliyu yayi sanyi lakwas. Sai da suka je asibiti ma suka ga yada ma'aikantan jinyar ke wulakanta marasa lafiya. Wata mata aka shiga da ita tana labour amman kememe suka ce bazasu amshe ta ba sun tashi.
Aisha da Aliyu na tsaye suna kallon su. A hankali cikin hikima ya janye Jikin sa ya nemi a fada masa sunayen likitocin asibitin ya amsa sannan yai rubutu ya bawa wanda suke tare da me nakudar takarda dan akai wacce ke labour din asibitin cikin gidan gwamnati. Duk Aisha na tsaye tana hawaye bata san me ake ba. Har ya dawo yace
"Mu tafi!"

Daga nan makatatun su suka isa suma ba kyan gani wai anan ake karatu shi inda yai karatu ko wani student bencin sa daban with loka da komai su nawa ne a ajin basu fi goma ba ga kayan aiki komai akwai a ckul ban da kayan wasa da zasuyi refreshing mutum amman nan ko kallo ba zaka so kayiwa environment din naka ba.  Ginin duk ya zama biskit ba fenti wannan da damina tsaf zai fadi kuma ace a haka yara suke katatu a ciki.

Suna cikin tafiya suka zo wucewa ta bakin wani police station. Kallan Aisha yayi yace
"Tsaya anan ina zuwa."

Ya shiga ciki yana tsaye yana kallon yadda suke amsar na goro da cin hanci a dannewa mai gaskiya gaskiya a bawa mara ita gaskiya. Ya jima a gun sannan ya juyo suka kama hanyar komawa gida.
Gari ne mai kyau da ni'ima amman sam ba a gyara shi ba da ya samu gyara za aji dadin garin.

Tin da suka fara tafiya ba wanda yace da dan uwan sa kala. Shi Aliyu tunanin sa ina kudaden da ake amsa da sunan aiki suke. Shin daman ba aikin suke ba. Ransa yai mugun baci dan jijiyoyin kanza duk sun tashi idon sa yai jajir. Suna zuwa gida ana kiran magariba dan haka ta kawo masa ruwa yai alwala sukai sallama ya tafi madallaci.

Ya jima yana addu'a akan Allah ya bashi ikon yin aiki da adalci har akai isha'i sannan ya tafi gida ransa a gajule.

Bayan yai wanka yana kwance yana kallon news wanda kallon yake amman gaba daya hankalin sa baya wajen. Karar wayar sa ce ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula. Wayar ya dauka yana dubawa yaga Abban sa ne. Mikewa yayi zaunw yana mai yin sallama
Amsawa Abbah yayi yana fadin
"ya gida da iyali da jama'a?"

"Alhamdulillah!"
"Masha Allah.!"

Nan Abbah yake tambayar sa harkokin garib Aliyu yana bashi amsa. Can Abbah yace
"Allah taya riko ina son fada maka sai kana sa ido akan masu taimaka maka duniya ta baci kai kana zaton suna aiki in bakai wasa ba zakaga ba abinda suke dan haka sai ka yi takatsantsan kanaji na ko? Domin kome ake ciki kai ne a ciki dan kai ne shugaba. Allah ya shige gaba ya taya ka riko ya sa sanadin wannan mulkin ka shiga aljanna."

"Amin Abbah nagode. Ina Mamah?"
Wayar ya mikawa Mamah ta amsa tana fadin.
"Baba na ya kake?"

"Ina yini Mamah?"
"Lafiya lou. Ya iyali da jama'a?"

"Alhamdulillah! "
"Masha Allah. Babana ka dage da addu'a fa kasan baka sanin makiyin ka. Addu'a ita zata na kare ka da tsareka."

"Insha Allah Mamah ina Maryama?"
"Maryama tana cikin gida."

STORY CONTINUES BELOW
"Agaishe da ita."
"Zataji sai da safe to!"

"Allah tashe mu lafiya."*********************************************************************************************************************************

Tin daga lokacin Yaa Fauwaz ke bani dukkan nin wata kulawar sa sai dai sam bai kawon zancen soyayyar sa, wanda a lokacin ita kawai nake muradi.

Kwana biyu da rashin lafiya ta, ina kwance a falo na idona a lumshe, Momy ce ta shigo tana fadin
"Fateema bacci kike?"

Mikewa nayi zaune ina fadin
"Aah Momy."

"Fu'ad ne yazo!"
Wata faduwar gaba naji ta buge ni.
Momy bata lura ba ta mike tana fadin
"Ki tashi kije kada ya gaji da jiran ki."

Kai na gyada na mike na shiga daki hijab na dauko na saka sannan na fito. Momy na falo nace
"Momy na fita."

Ta amsa min da toh na fice. A sitting room na same shi da sallama na shiga yana gani na ya mike yayo guna. Hannu na ya kama ya zo ya zaunar dani akan kujera a kasa ya zauna ya zuba min ido yace
"Fateema me yake faruwa ne? Wayar ki bata shiga kwata kwata ."

Kai na a kasa ido na ya ciko da kwalla. Dago kai na yayi take yaga ramar da nayi nan fa hankalin sa ya tashi bama da yaga hawaue ga ramar da nayi. Yace
"Fateema nah baki da lafiya ne?"

Sai na fashe masa da kuka domin kuwa ina jin tausayin Fu'ad sosai yadda yake so na da damuwa da danuwata dole naji tausayin sa.

Jana yayi jikinsa yana lalashi na.
"Haba yan mata na ki daina kuka ki fadan me yake faruwa?"

Hawayen ido na na goge nan ya cigaba da goge min sannan yace
"Kiyi shiru kinji?"

Kai na gyada yace
"Me yake damun ki?"

"Uhmm nayi ciwo Fu'ad kwana biyu shyasa ban kunna waya ta ba."
"To saboda me? Baki san rashin kunna wayar taki yafi komai tadan hankali ba. Ina ta sake saken ko lafiya? Jiki na ya bani baki da lafiya Fateema. Yanzu ya kike ji?"

"Naji sauki."
"Sannu Allah kara sauki!"

"Amin!"
"Me kike so?"

"Ba komai!
"Kin tabbata?

Kai ta gyada masa. yace
"To yanzu in tafi kije ki huta ko?"

Kai na girgiza yace
"Zan dawo anjina!"

Kai na gyada na mike ya biyo baya na ya rako ni har kofar falo. Yaa Fauwaz ne ya fito daga falon da kallo ya bimu sannan ya dauke kai ya wuce bakin gate.
'Sai anjiman!"
"Toh!"

Na daga masa hannu. Lokacin da Yaa Fauwaz ya dawo kenan ya bini da kallo sannan ya dauke kan sa. Bayan sa nabi kai na na sarawa ni kam dai na gaji.

Na shiga ban tsaya a falo ba nayi cikin daki na. Ina shiga na fada saman gado ina sakin wata ajiyar zuciya Dan kuwa na kasa kukan ma. Ina kwance naji ana Kiran magariba wannan yasa na mike na shiga nayo alwala nai sallah.

Ina zaune har akai isha'i ina kan sallaya Basma ta shigo kallon ta nayi tace
"Anty Yaa Fu'ad ne yazo."

"Je kice ina zuwa."
Na Mike na fito suna falo ko kallon su ban ba na fice. Mai aikin mu naga ya taho da Kaya Niki Niki katon din maltina da ruwa da lemo da wata Leda yace
"Hajiya gashi inji Alhaji "

"Shiga dashi"
Na fada ina karasa wajen Fu'ad dake tsaye a jikin motar sa.

Murmushi ya sakar min. Nima nayi masa yake nace
"Mu shiga ko?"

Kai ya girgiza yace
"Dare yayi ai tafiya zanyi "
Su Yaa Fauwaz na zaune Ismail ya Kai kayan Momy ta kalle shi tace
"Daga ina?"

"Alhaji Fu'ad ne ya ce na shigo dasu."
"Allah sarki. Ajiye anan angode."

Yaa Fauwaz ne ya kalli Yaa Kalmal yace
"Tashi mu tafi."

Mikewa yayi sukai wa Momy sallama. Momy yace
"Ku dauki maltinan Mana "

Waje Fauwaz yayi Yana fadin
"Ni kam nagode "

Yaa Kamal ne ya dauki maltinan ya na fadin
"Angode Sai da safe."

Fuska na Dan Bata na make kafada. Kallona yake murmushi akan fuskar sa yace
"Yau shagwabar ce ta motsa ne?"

Kafada na make ina murmushi. Dai dai lokacin da Yaa Fauwaz ya fito. A lokacin da Fu'ad ya matso Yana fadin
"Ki kwantar da hankali ki na kusan dauke ki ma gabadaya ki dawo gida na."

Fuska na rufe ina murmushi nace
"Kai Fu'ad ni fa ba haka nace ba."

"Ba haka Kika ce ba Amman ai abinda kusan kike nufi Kenan tinda bakya son na tafi na barki "
Yaa Fauwaz kamar ya hadiye zuciya haka yake ji Dan haka da saurin sa ya shiga mota.

Yaa Kamal na fitowa yace
"Masoyan asali"

Murmushi mukai gaba dayan mu. Ya Mikawa Fu'ad hannu suka gaisa. Yaa Fauwaz Da ya gama kuluwa ya Danna Masa wani mahaukacin horn. Juyowa yayi yace
"Bari mu tafi sai da safe "

"Allah bamu alheri."
Ya fada. Ni kuwa hankali na Naga Yaa Fauwaz ina tunanin a Halin da yake.

A yadda ya fita da motar ma kamar zai tashi sama. Da Ido muka bishi dai dai shigowar motar Dady kenan.

Fu'ad yace
"Wayoo Dady ya dawo."

Dariya nayi inai Masa gwalo. Lokacin da Dady ya fito kenan har kasa Fu'ad ya durkusa Yana gaishe shi. Dady ya Kamo hannun Yana fadin
"Aah tashi tashi Fu'ad ya gidan?"

"Alhamdulillah!"
"Masha Allah "

Ina gefe nace
"Sannu da zuwa Dady!"

"Yauwah fateema!"
Ya fada Yana yin cikin gidan.

Fu'ad na kalla yadda ya nutsu Dan yadda yake Jin kunyar Dady nace
"Hey Man ya dai!"

Dan harara ta yayi Yana fadin
"Sai na kawo Miki Hajiya ta."

"Am sorry love. Kaje kawai nagode da kulawar ka da soyayyar ka "
"Bana ce Banda godiya ba"

Kai na make alamun shagwaba. Yace
"Ni dai na fada."

"Ni a'ah ina so "
"To ni nace A'ah ai closing matter "

Ido na nayi raurau dashi take hankalin sa ya tashi yace
"To naji na yadda Kar kiyi kuka."

Murmushi na saki ina Masa gwalo. Kallo ya bini da shi yana fadin Zan Rama ne."
Dariya nayi nace
"daga baya kenan "

"Ko?"
Na gyada Masa kai.

"Shikenan dare yayi ki shiga ciki Alah kara sauki. Take care."
"U too bye!"

Na daga Masa hannu na shige cikin Shima ya shiga motar sa ya bar gidan.
Ina shiga nayi hanyar dakin Momy tace
"Kizo kiga abinda ya kawo Miki man "

Matsawa nayi ina budewa, a ledar shawarma ce da meatpie da spring roll. Shawarmar na dauka da maltina guda daya nayi cikin daki ina fadin
"Momy wannan ya ishe ni."
Tin daga Ranar Yaa Fauwaz bai Kara zuwa gidan mu ba duk na damu Amman a fili Sai na nuna ban damu ba. Dan ba wanda zai gane na damun kuma ko Yaa Kamal dake zuwa shima ban tambaye shi yana ina ba. A zuciya ta Kuma ina ta tunanin halin da yake ciki na kasa nutsuwa.+

A lokacin Kuma har mun koma makaranta inda saura semester daya mu gama karatun mu gaba daya. Dan haka sosai na mai da hankali akan harkar karatu na. Tin a lokacin Dady ya fara Gina min wani asibiti a nan unguwra tamu. Inda muna fara exam har an gama an zuba min duk abinda zan bukata.

A lokacin shakuwa ta da Dady ta Karu. Dan har zai zauna Yana zancen biki na inda yake so da na gama karatu kan na tafi service yake son ayi komai a gama.

Duk wannan tsawon lokacin ban ganin Yaa Fauwaz Dan bai zuwa Sai ya tabbatar da bana gida yake zuwa.  Kan na dawo Kuma ya tafi. Abin na damu na Amman haka na danne Dan ma Fu'ad na bani dukkan kulawar da nake bukata daga gareshi.

*A gurguje*
Yau muka gama exam din mu ta karshe inda mukai celebration ni da Class mate din mu. Ranar riga mukai Orange sai black siket. Muna fitowa daga Exam hall kowa ya saka kayan sa. Bakin mayafi nayi rolling dashi ban wani yi make up ba dan bata fiya damu na ba. Muna tsaka da hutuna sai ga Fu'ad nan. Tare mukau komai dashi dan sai bayan la'asar ya dauke ni ya mai dani gida.

Mun shirya zamuyi dinner Ranar Friday inda tin da mukai graduation ba zama dan hada Hadar yin dinner. Shi kansa Fu'ad bai samu time dina. Domin kuwa kullum sai mun fita kasuwa.
Haka nima Dady ya sa akai min bags da buks da cups dan in raba ga yan uwa da abokan arziki.
Ranar dinner kuwa. Da yamma mai make up tazo har gida tai min kwalliya. wani pink less da akai wa ado da maroon duk jikin sa white stone. Fadar irin kyan da nayi bata baki ne dan duk Wanda ya kallen Sai ya Kara kallo na Kuma duk hasadun iza hasadin yasan nagama yin kyau.
Fu'ad ne yazo ya dauke kafin su Momy su taho da abubuwna da na bayar Ayo mana. Muna zuwa aka fara abinda ya hada mu a wajen. Manyan Baki lectures din mu har da provost duk sunzo wajen ya cika da manyan yan Boko da graduate yan gayu.

*
A gida su Momy na Shirin fitowa Yaa Fauwaz yazo. Momy ya kalla yace
"Unguwa zakuje ne?"

Momy tace
"Ai kawai shige muje."

Ba tare da ta fada masa inda zasu ba. Shima bai tambayi ina zasu ba tini yabi bayan su har suka shigo wajen da muke gudanar da Dinner tamu. Shigowar su tayi dai dai da Kiran da akai Akan nazo na yiwa manyan Baki barka da zuwa.

STORY CONTINUES BELOW
Nan na fito cikin tafiya ta a hankali na karasa kan stage din.
Tinda na fito Yaa Fauwaz ya daura idon sa a Kai na ya kasa sukuni wani sabon so na da kauna ta suka Kara mameye zuciyar sa.
Fu'ad ma kallo na yake yana kara jin so na da alfahari da kasancewar sa tare dani.
Tin da na fara magana daga shi har Fu'ad suka kura min Ido kamar Basu sanni ba. Yaa Fauwaz ina gamawa ya lumshe Ido ba abinda yake gani Sai ni.

Yana bude Ido ya hange ni tare da Fu'ad ana mana picture ba karamin kyau da dacewa da Juna mukai ba. shi kansa ya ga hakan Amman kishi ya hanashi ya yadda da hakan.
Ana gamai mana nayo gun su Momy fuska ta dauke da murmushi Sam ban kula dashi ba sai da na hau step din da su Momy suke ban aune ba naji nayo baya wannan yasa cikin zafin nama ya taro ni na fada jikin sa. Kallon juna muka tsaya yi, dukkan mu mun kasa dauke idon mu daga kallon juna.

Wani hawayen ne suka fara zubo min a idanu na wannan yasa yai saurin janye ni muka fita a wajen.
"Menene na kukan?"

Ya tambaya bayan mun fita daga cikin hall din da ake gudanar da abun.
Ai kamar yace in Kara wani kuka na Kara sakin wani kuka.
"Am sorry nasa ki kuka on dis special day ko? Amman sorry dama ban zo ba tinda har Zan saki kuka kiyi hakuri bari na tafi "

Ya juya zai tafi hannu na,  na saka na Kamo nashi wannan yasa ya juyo yana kallon na ban San lokacin da na fada jikin sa ba ai kam Shima ya rumgume ni ina kuka yana lallashi na.

Duk abinda ya faru akan idon Fu'ad ne dan lokacin da Fu'ad yaga fitowar mu Sai hankalin sa ya kasa kwanciyya wannan yasa ya biyo bayan mu yana fitowa ya same ni rumgume da Yaa Fauwaz abinda ya daga Masa hankali kenan. Kasa jurewa yayi kawai ya nufi motar sa ya shiga ya kifa kan sa a akan sitiyari yana sakin wani irin kuka mai taba zuciya.

Ya Jima Yana kuka sannan ya dago Yana Mai daga hannayen sa sama Yana fadin
"Yaa Allah in Fateema rabo nace Kuma alheri ce a gareni Yaa Allah ka mallaka min ita."

Har ya bude mota zai fito Sai Kuma ya koma ya zauna yana dafe da kirjin sa. ya Jima a haka sannan ya tada motar ya fita daga compound din makarantar a guje

Yaa Fauwaz kuwa lallashin Fateema ya fara Yana fadin
"Haba Teema nah please ki daina kukan Mana. Kina son Nima nai kukan ne?"

Kai na girgiza yace
"Toh please daina kukan kinji today is one of ur special day u support to be happy not crying kinji."

Kai na gyada ya sharen hawayen sannan yace,
"Toh smile!"

Murmushi na saki ya amshi jaka na ya bude ya dauki powder ya mikon yace
"Amshi ki gyara face dinki."

Amsa nayi na shafa yace
"Yauwah ko kefa?"

Ya kama hannun na mukai cikin hall din muna shiga muka karasa wajen su Momy Nan aka dingai mana pictures.
Sam na manta da wani Fu'ad Dan yadda Yaa Fauwaz ya dinga Nan Nan dani naji dadin Ranar Dan na samu gift sosai daga malamai har yan uwa na dalibai.

Bamu muka koma gida ba Sai karfe Sha dayan dare. Ina shiga Yaa Fauwaz ya biyo ni da tulin kayan da na samo anan kan kujera ya ajiye kayan da kallo ya bini, Sai ya karaso inda nake,
"Zan tafi Baby Sai gobe?"

Kai na gyada Masa yai hugging dina sannan ya juya ya fita. Da kallo na bishi har ya fice sai na lumshe Ido. A zabure na Mike tunawa da Fu'ad da nayi.
Waya ta na dauka Nan na fara Kiran number sa Amman har ta gama ringing bai dauka ba, Kara Kira nayi Shima shiru wannan yasa na tura Masa da sakon Amman no reply.

Take naji ba Dadi Dan ban kyauta ba ban Kara bin ta Fu'ad ba. Jiki a sanyaye na tashi na shiga bandaki nai wanka na fita ina Kara kiran sa Amman Sai naji wayar tashi a kashe ma.
Kan gado na fada ina sakin wani irin kuka Mai taba zuciya. Shin Wai me yake damu name? Wacce irin zuciya ce dani me ya Hau Kai nane?

Nayi kuka har wajen asuba Ido na biyu. Ina mamakin ta yadda zuciya ta take min irin haka ace ina son mutun biyu a lokacin daya. Shine wacce irin zuciya gareni kenan.

---------------------------------
Tin safe Yaa Fauwaz yazo dan haka tare muka yini.

A Ranar ya tino min da soyayyar mu Mai dadi wacce na mance yaushe rabon da Yaa Fauwaz ya kula dani kusan wata shida kenan. Amman yanzu yadda yake mun kamar zai maidani cikin sa.

Gaskiya na yadda Yaa Fauwaz na so na sai da yana da kishi da zuciya wannan yasa in ya hau dokin zuciyar yake daukar komai da zafi. Amman Yaa Fauwaz ya iya soyayya da kulawa da mutum.
Ni kam Zan Yi fatan kasancewa ta dashi Dan ya iya kulawa da mace Wanda nasan ko wacce mace ke fatan samun miji da zai kula da ita.

Ban Kara neman layin Fu'ad ba sai da dare da Yaa Fauwaz ya tafi. Amman har lokacin wayar tashi a kashe take na shiga tashin hankali ina tambayar Kai na lafiya kuwa Dan Fu'ad ba ma'abocin kashe waya bane.

Haka nai wanka na kwanta da tunanin Fu'ad a rai na. Ina mamakin zuciya ta in ina tare da wannan ina Jin kewar dayan.

Duk da nasan soyayyar ko wacce daban take a zuciya ta Wanda hakan shi janyowa na kasa hakura da daya Wanda nasan duk Daren dadewa Dole da mutum daya zanyi rayuwar.

Shin in Fu'ad na aura ya kenan? Tayaya Zan na ganin Yaa Fauwaz in mun hadu Dan da na aure shi da ban aure shi ba Dole muna tare tin da jini nane Yaya nane.

In kuwa Yaa Fauwaz na aure ba dole ne ina ganin Fu'ad ba. Ina tunanin tayaya zan Yi rayuwar ba tare da son daya a cikin su ba.

Hakika son Fu'ad son Allah ne Wanda shi ya saka mana son junan mu da taimakon shakuwa ya kara zurfi da zafi.

Son Yaa Fauwaz kuwa Shima son Allah ne Dan Allah shi ya daura min son sa Dan Yana burge ni, sai Kuma jinin mu da yake daya shi ya Kara Mana zafi da zurfi soyayyar mu.

Lallai ni Kuma tawa *Kalar kaddarar* kenan Akan soyayya soyayyar na ta mutane biyu. Allah kai ka dauran son Fu'ad da Fauwaz Allah nasan Yana cikin *kaddarata* Allah ina rokar ka ka sassauta min ka dauran abinda Zan iya. Amin na shafa ๐Ÿ™๐Ÿป hawaye na kwaranya a idanuna.๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ

Juyi nake akan gado ina tuna rayuwar mutane da *kalar kaddarata* su wacce ni Kuma tawa take daban da ta su.
Ina godiya ga Allah da ya bar ni da Mahaifina da mahaifiyata Kuma ya bani masoya Allah ka bani ikon cinye jarabawa ta. Amin๐Ÿ™๐Ÿป


Washe gari ina zaune a falo Yaa Fauwaz ya shigo murmushi na saki ina fadin
"Kayi kyau My Hero!"

"Haba beauty na ai kin fini kyau. Ya kike ya gidan?"
"Alhamdulillah!"

"How was ur nyt?"
"Alhamdulillah!"

"Masha Allah!"
"And ur's?"

"So lonely."
Ido na zaro nace
"Why?"

"Saboda Babu ke a cikin sa."
Ido na na rufe saboda ya ban kunya.

Murmushi yayi yace
"Teemah ki bani Dana na aiko a saka mana rana muyi auren mu tinda yanzu kin gama karatu."

"Yaya nah na baka dama."
"Da gaske?"

Kai a gyada Masa.
"Alhamdulillah! Ashe dai Zan zama zabin ki Fateema?"

"Haba Yaya na tinda na amshi soyayyar ka ka zama zabin rai na."
"I love u Baby love. I really love u."

"Love u more honey love."
Muka saki murmushi.

Yaa Fauwaz kenan ya gama yi 100% sai Abu da ba a rasa ba.

*** ***** ***
Abin mamaki kwana daya kwana biyu kwana uku dukka ba Kiran wayar Fu'ad kullum Zan Kira Amman a kashe abin fa ya Dagan hankali Dan Momy ma sai da ta gane.+
Ina zaune a falo na sanye da wani sea green less wanda akai masa a do da brown and yellow. Dinkin riga da siket ne ba dan kwalli akai na sai gashi na da na faka yake kwance har a baya na. Ban yi kwalliya ba daga mai sai hoda da kwalli da na saka wanda ya kara fito min da kyau idanu na kuma sauka kara girma. Gashin ido na yai gazar gazar sai kace na saka gashin ido ko mascara. Baki na kuwa man lebe na saka sai kyalli yake. Daga kallo daya zaka gane ina cikin damuwa domin kuwa na zuba tagumi na lula can duniyar tunani. Har Momy ta shigo dakin ta gama kallo na ban sani ba. Wannan yasa tazo ta zauna a gefe na  tana fadin
"kwana biyu na rasa meke damun ki kina yawan shiga damuwa!"

Hawaye ne ya zubo min Dan me neman kuka ne aka jefe shi da kashin tumaki.

"To menene na kuka daga tambaya?"
Jikin Momy na fada ina fadin
"Momy yau kwana uku kenan bamuyi waya da Fu'ad ba kullum na Kira wayar a kashe!"

"Fada kuka Yi ne?"
Momy ta tambaya.

Kai na girgiza nace
"A'ah Momy tin Ranar dinner mu fa."

Kallo na Momy tayi sai tace
"Ki kwantar da hankalin ki Yana lafiya kinji."
"Momy na kasa yadda da hakan na kada cire tunanin hakan domin kuwa ba mu taba irin wannan jimawar bamu yi waya ba. tunani na Yana bani ko bai da lafiya. Momy dan Allah kije kuga ko lafiya Kinga Sani baya gari "

"To naji zani Amman ki daina kuka sannan ki taso muje falo gasu Fauwaz can sunzo."
Momy ta fada tana mikewa.

Naji dadin zuwan nashi Dan shi ke deben kewa Dan haka na Mike ina goge hawaye muka fito.

Ina fitowa na tadda Yaa Fauwaz zaune akan kujera sanye da black wando da blue black din riga mai long sleeve. Yai kyau idon sa makale da glass. Ina karasowa falon mu yai dai dai da Aiko yaron gidan.
Sallama yayi muka amsa sannan ya kalli Momy yace
"Alhaji Fu'ad ne yazo yace a fadawa Anty Fateema yana waje."

Ban tsaya Bata lokacin ba ko jin me Momy zata fada ba kawai na fice da sauri na. Daga Momy har Yaa Fauwaz da ido suka bini.

Ina fita naga motar sa a bude wannan yasa nasan yana cikin mota. Wajen motar na karasa na same shi zaube a cikin motar sanye cikin blue black din yadi yai Masa kyau. Sai tashin Kamshi yake.
kallo daya zakai Masa ka gane ya rame sosai. Kallon sa nayi da fuskar tausayi Ido na yana kawo ruwa,
"Ina ka shiga? Ina ka tafi ka bar ni?"

Na fada ina fadawa jikin sa tare da fashewa da kuka. Rumgume ni yayi Yana sauke ajiyar zuciya yana Kara Jin Sona da kauna ta na Kara shigar sa.

STORY CONTINUES BELOW
Mun Jima a haka ya dago Kai na yana gogen hawayen Ido na. Yana fadin
"My Princess please stop crying kinsan I can't do without u ko? Ban da lafiya shiyasa kwana na biyu a asibiti yau aka sallamoni na kasa zama Sai da nazo Dan na ganki. I love u princess u are my life my happiness rasaki a rayuwar ta kamar rasa rayuwar tane. I love u My Moonlight please don't ever leave me."

Ajiyar zuciya nake saukewa ina kallon sa. Tabbas kalaman sa da komai nasa da gaske yake ba wasa a cikin kalaman sa Sam.
Son sa da kaunar sa hadi da tausayin sa ne suka Kara rufar min. Ido na lumshe hawaye na zubo min. Hannun sa ya saka yana gogen idona tare da girgiza min Kai alamun in daina kukan.

Jikin sa na fada dan na rasa abin fada. Hannun sa ya saka yana lallashin na. Da kyar nai shiru.

Mun Jima a tare yana lallashin na abinda ban sani ba komai akan idon Yaa Fauwaz ya faru Wanda ban San da hakan ba ma. Sai da Fu'ad ya tafi na shiga gida anan naji Momy tace ai ya Jima da tafiya. Daki na nashiga na kwanta kawai.


Da dare Muna zaune akan dining muna yin dinner Dady ya kallen yace
"Fateema ina son ki fadawa Wanda kike so ya turo ayi komai Amman in na dawo daga tafiyar da zanyi. Dan gwara na aurar da ke tin ban mutu ba."

"Kai Dady insha Alalhu ba zaka mutu ba har sai kaga jikokin Basma."
"Kayya Fateema. Na tsufa fa. In samu Inga auren naki ma."

"Allah ya Kara muku lafiya da nisan kwana."
Na fada ina langwabar da kai na.
" Amin."
Basma da Momy suka ce.

Basma ce ta dubi Dady tace
"Dady ina zakaje?"

"Zanyi tafiya zuwa Abuja kwana biyu zanyi Zan dawo."
"To Allah ya tsare."
Na fada.

"Amin!"
Dukka muka amsa a tare.
"A jirgi zaka je ne?"
Na tambaya.

"A'ah muna da yawa a mota zamuje."
"Ni Dady ban son tafiyar motar Nan bama da hanya Bata da kyau."

Na fada. Momy tace
"Allah zai tsare "

Daga Nan Falo muka koma. Dady suna Hira da Momy akan in sunzo lokacin kadan zai saka. Momy tace
"Alhaji ka dai shirya ko?"

"Bikin 'yar fari ai na gama shiri lokacin kawai zamu jira."
Mikewa nayi na nufi dakii Dan kunya ma suke bani.

Kan na shiga daki naji Momy Tana fadin
"Ni ban San wa zata bawa dama ba Fu'ad din ne ko Fauwaz?"

Ciki nayi ba tare da naji abinda Dady zai fada ba. Sai dai nima ina shiga na fara tunanin Wanda Zan bawa damar Nan.
Har nai bacci ban zabi Wanda *nake so* ba Dan na rasa *wa nake so?* wa Kuma zance ya turo.

*
Washe gari da safe su Dady suka tafi bayan mun Masa rakiya har compound din gidan mu. Duk Sai muka ji kamar Kar ya tafi Dan sai da mukai hawaye ya janyo Ni da Basma ya rumgume sannan yace
"Allah muku albarka."

Sannan ya sake mu ya shigan mota Yana daga Mana hannu. Ciki muka koma duk ba Dadi ga hankalin mu a tashe.

Ba mu samu nustuwa ba sai da Dady ya Kira yace ya sauka. Sai lokacin muka hau hada Hadar gida.


*
Ana gobe su Dady zasu dawo Muna zaune da Momy ta kalleni tace.
"Fateema *wa kike so?* Kuma wa Zaki bawa damar ya turo?"

Kai nayi kasa dashi. sannan nace
"Nima ban San *Wa nake so?* A cikin su ba ko Wanda Zan zaba ba dukkan su ina son su Kuma nasan hakan ba dai dai bane Dan Dole mutum daya Zan aura."

Dafa kafada ta Momy tayi tace
"Ki zauna da zuciyar ki, ki ga *wa kike so?* Dan da matsala in har Baki auri *wanda kike so ba* Mu baza muyi Miki auren dole ba, Kuma aure *Wanda kike so* shi zai Baki nutsuwa da kwanciyyar hankali. Dan haka ki daure ki zabi *Wanda kike so*  ba matsawar wani a cikin su ba. Duk cikin su ba Mai aibu kowa ya cancanci a so shi ina Miki addu'a samun miji na gari in Kinga abin ya Miki tsauri ki Kara istihara. Allah zaba Miki miji nagari. Amman zabin *wanda kike so* a gaba zaki ga alfanun sa domin zaki kula dashi kuma zaku samu fahimtar juna ba kamar in bakya son wani ba ba dole ne kina daukar duk abinda zai miki ba in kuwa ina son sa sai kiga ko yai miki abu kin shanye kuma zaku samu farin ciki dauwamame dan zaki bashi kulawa da soyayya. Allah ya zaba miki mafi alheri."

STORY CONTINUES BELOW
"Amin!"
Na fada ina lumshe Ido. Tokare kowanne irin tunanin nayi da zai zo min akan su. Na bar zuciya ta ta nutsu zuwa anjima nayi tunanin Hadi da istihara amman ina tunanin sai da yaci karfi na,  na fada fafatawa akan Wanda Zan zaba.
(Reader help me choose *wa nake so?* Ko wa kukaga yafi so na?)
*********************************************************************************************************************************

Washe gari da kwarin gwiwar sa ya mike dan ya daura damarar kwatarwa talakawa yancin su. Yana wanka ya fito ya shirya cikin kakin sa wanda suke dada masa kyau da kwarjini. Ya saka bakin space a idon sa duk wani mara gaskiya da yayi tozali da AK dole ya tsorata.

Yana fitowa ma'aikaran gidan tin daga falon sa suka fara gaisuwa amman da yake yau ya tashi a Aliyun nasa da hannu kadai yake amsa musu gaisuwar suma sun tsora ta dashi dan rabon da su ganshi a iri wanan yanayin tin farkon fara aikin su wanda yanzu a kalla sun debe shekara daya da doriya a gidan.

Yana fitowa ya nufi motar sa ya shige a 360 ya tashe ta ya fice da ita mai gadi ya bishi da addu'ar Allah ya tsare. 
A can gidan gwamnatin ma daga yadda sukaga shigowarsu kowa ya shiga cikin hankalin sa. Yana fitowa sojoijn dake harabar gidan suka kame masa.

Ko kallon su bai ba ya saka kai ta nufi hanyar da zata sada shi da offishin sa. Yana shiga ya zauna ya dauko jadawalin aiyukan da ake yi da sa hannun duk da akai na tura kudi. Har da aiyukan da akayi wanda aka amshi makudan kudade da adadin su yake da yawa sosai amman ace shi baiga ko daya ba. Ya jima yana nazartar abin kan ya ajiye lokacin da PA'n sa ya shigo a lokacin ne ya dago yana kallom sa.

"Ina son a tara min meetng yanzu nan na bada minti goma kowa ya hallata."
sara masa yayi ya juya ya fita dan gudanar da abinda ya saka shi.

Map din garin ya dauka yana fitar da unguwanin da titi da komai. Cikin minti goma kowa ya halallata acan meeting room din su lolacin da PA'n ya shigo dan fada masa an taru a lokacin yake fitar da abunda yake bukata
Dan haka tsayawa yayi yana jiran ya gama dan ya fada masa. Dan yasan halin ogan nasa ba a katse shi in yana yin aiki. Sai da ya dauki awa daya sannan ya gama ya dago yana kallon sa.

Kamewa yayi sannan yace
"Kowa ya hallata."

File din gaba sa da ya gama hadawa ya mika masa sannan ya mike yai gaba yana take masa baya. Yana fitowa daga Office din sojoji biyu dake bakin ofishin suka yi gaba  biyu da PAn sa na bin sa a baya ahaka suka karasa meeting room din.

Suna shiga suka tsaya a gefen sa PA ya gyara masa wajen zama ya zauna sannan shima ya zauna daga gefen sa.

File din dake hannun PA ya ajiye a gaban sa.
"Ayi salati ga Annabi!"

"Sallalahu Alaihi wasalam!"
Kowa ya amsa.
"Allahu Sali ala Muhammad wa'ala Ali Muhammad kama salaita ala Ibrahim wa ala Ali Ibrahim fil alamina innaka........ Allahu Salli Allah sayyaduna Muhammad wasalim. Allahu sali wa Salim was barik ala hazaratul nabiyyi nurul ala nur."

Ya fada Yana karanta ayyatul kursiyyu da falaki da nas da kulhuwallahu ahad. Ya rufe da Salatin Annabi sannan ya shafa.

File din gaban sa ya janyo ya bude yana nazartar abun cikin ya jima sannan ya dago ya fara magana cikin harshen turanci wanda yake magana kamar bature.
"Alhamdulillah dukkan yabo da gpdiya sun tabbata da Allah mai komai da kowa da ya ara mana rayukan mu har muke raye a yanzu. To Alhamdulillah Allah karawa Annabi daraja."

"Amin!"
Kowa ya amsa a cikin dakin taron.

File din yake kalla fuska ba walwala yace
"Yau muna shekara ta daya da fara mulkar wannan garin wanda a tsarin gwamnatin taraiyya shi kuma yake kan shekara ta uku wato sauran shekara daya ya gama mulkin sa muma muna sa ran daga lokacin mun gama mulkin nan da yaddar Allah."

Ya gyara zama yana bude page din cikin file din dake gaban sa sannan yace
"Kamar yadda muke sani a wannan state din muna da local government guda ashiri. Alhamdulillah tin da muka amshi garin nan muke gudanar da aikin mu, dan haka a yau nake son naga evidence da schedule na aiyukan da duk muka gabatar."

Shiru dakin taron ya dauka. Can daya daga cikin su ya mike yana fadin
"Mai Girma gwamna yanzu basa tare damu sai dai aje a dauko zuwa gobe."

Kai Major AK Ya girgiza ya kunna system din sa dake gaban sa. Ya umarci PAn sa yayi connectng yadda kowa zai ga komai. Sai da ya hada masa ana ganin screem din system din  sannan ya mike yace
"Ina da komai anan!"

Nan ya fara nuna takardar da aka fara kawo masa na neman za ai titina a dukka local government din da suke dashi guda ashirin. In da aka nemi makudan kudi biliyoyi kuma aka fitar duk sai daya nuna har alert ta banki da aka tura musu. Haka ya dinga nuna musu duk abubuwan da akan gudanar a cikin shekara dayan nan inda akai amfani da makudan kudaden da suke da yawan gaske.
Sai da ya gama nuna musu da bayani sannan ya koma ya zauna. Yai relaxe akan kujera yana bin yan wajen da kallo kowa a firgice yake bai san mai shugaban nasu zai yi ba. An jima wajen shiru sai Karar AC dake a wajen. Sannan ya dago yace.
"Akwai mai magana?"

Commisioner Tsaro ne ya mike yana fadin
"A yadda aka nuna komai hakan ya nuna mun ci riba kuma mun gudanar da abubuwa masu yawa. Dan haka muna rokar Allah da ya saka da alheri ya kara tayaka shugabanci."

Duk yan wajen suka amsa da Amin. A haka suka dinga tashi suna yabo aikin da ake gudanarwa da kara kwarin gwiwa da shawara. Sai da suka gama gaba daya yana jin su yana kallon kowa sannan yai gyaran murya yace
"Ina son ganin Evidence akan ko wacce kobo da ta fita a asusun talakawa. Kama daga kudin da aka bawa yan kwangila da komai with the work they do "

Jikin kowa ne yai sanyi yace
"A yanzu nake so!"

"Sir but ba mu san abinda ya tara mukenan ba bamu zo dasu ba."
Kallon su yake daya bayan daya da wani murmushin da suka kasa gane ko na menene yace
"Bana bukatar soft copy I need to see hard copy dan haka zan hada ku da amintattuna na baku nan da hour!"

Ya fada yana kallon agogon sa biyu saura. Yace
"To Three ina son kowa ya dawo with hard copy daga ma'aikata nan."

Wata takarda ya mikowa PA'n sa yace
"Ka duba ka hada kowa da wanda zasu je ayo min vedio,  pictures and magana da ma'aikatan da kuma mutanen wajen. I need a real things"

Ya fada yana mikewa tare da nufar kofar dazata sada shi da office din sa. Daya daga cikin sojojin dake bashi tsoro yana tsaye yana jiran sa dan ya samu kiran sa tin kafin zuwan sa haka yana shiga ya kame masa.

Zama yayi. Sojan ya kara kame masa. Hannu Aliyu ya daga masa yace
"Kaje ka bawa kowa umarnin ai min aikin ba wasa ba."
Haka kawai ya fada ya juya kan system din da ke kan table din ya cigaba da dannawa. 'Kame wa yayi sannan ya juya ya fita. Yana ganin fitar sa ya mike ya shige toilet ya dauro alwala yana fitowa yai masallaci acan yai nafila sannan aka tada salah azahar.
A can dakin taro kuwa kowa ya sha jinin jikinsa. Haka PA sa ya rabawa kowa da wanda zasu sannan ya mike ya fice ya barsu. Kasa tashi sukai kowa yana tunanin ta ina zai fara ganin lokaci na kurewa yasa suka mike suka fice. Kowa ya nemi wanda zasu je su gudanar da aiki.
A can dakin taro kuwa kowa ya sha jinin jikinsa. Haka Pan sa ya rabawa kowa da wanda zasu sannan ya mike ya fice ya barsu. Kasa tashi sukai kowa yana tunanin ta ina zai fara ganin lokaci na kurewa yasa suka mike suka fice. Kowa ya nemi wanda zasu je su gudanar da aiki.


*
Karfe uku kamar yadda ya fada kowa Yana cikin dakin taron Yana jiran isowar Shugaba ja gaban yazo suji yadda za ai. Bai nufi dakin ba Yana zaune Yana ta aiyukan da ya saka a gaba. Kai ya daga yana kallan agogo karfe uku da arba'in lokacin sallah yayi kenan. Wannan yasa ya Mike ya nufi masallacin. Yana zuwa aka tada sallah. Ya Jima a ciki dan har sai da yayi azkhar sannan ya fito lokacin karfe hudu har da rabi.

Agogo ya kalla ransa ya baci ganin hudu da rabi Yana cikin gidan bai tafi ba kenan ba zai samu damar zuwa yaga Aisha ba. Dan yasan indai abinda take son ya gudanar ne a yanzu zai iya daukar sa awa biyu zuwa uku Wanda by then lokacin zai iya kaiwa magariba kenan.

Hanyar da zata sada shi da dakin taron yayi Yana shiga suka Mike hannu kawai ya nuna musu alamar su zauna Dan shi ya tsani ana Masa irin haka tinda dai duk daya suke Amman ai ta nuna shi da ban ne.

Zama yayi akai addu'a sannan fara kallon su daya bayan daya. Sai da ya gama ya kalli PA'n sa yave
"Je ka Kira min su."

Nan da Nan cikin minti na kadan sai ga shi da ta wagar sojoji na duk kan su kedare dasu jikin su a murde fuska ba wasa.

"Show me the evidence!"
Ya fada yana kallon cikin system din dake gaban sa.

Na farkon ne ya fara Mikawa PAn sa wayar sa da wani file. Wayar akai connecting da computer. Titinane da ba a karasa ba wajen guda biyar ko wanne ba a karasa aikin ba.

Sai hirar da sukai da masu aikin titin wadan da aka bawa kwangila suka ce kudin ne ba karasa basu wannan yasa suka tsaya a aikin.
Sai Yan gari da akai magana dasu suke fadin
"Dan Allah a taimaka a gyara musu titina dan in zasu fita aiki suna wahala gashi in damina tazo, hanyar duk ta jagwale suna wahala wajen fita aiki. Wasu kuma suka ce rashin gyaran titin ya hana su kasuwancin da suke akan titin domin kurar titin na damun su ga shi kuma kayan su yai ta datti masu kayan abinci na siyar wa ma suka ce shiyasa suka daina sa'ana dan duk baci abincin yake.

Anyi Hira da mutane wajen biyar Amman abinda duk haka suke fadi.
File din aka Mikawa Aliyu Wanda akai yarjejeniyar da akai da Yan kwangila da masu bada kwangilar. Amsa yayi ya duba sannan ya ajiye a gefe.
STORY CONTINUES BELOW
Dayan ne ya Mika nasa Akan wutar nepa ne suma an bada kudin transformer Amman sunkai rabi sauran sun cinye. Haka dai suma akai magana da masu raba hasken wutar da Kuma jama'a wurare da yawa.

Haka aka dinga Yi kowa Yana kawo evidence Wanda duk babu aikin da zaka daga ka kalla ka yaba kaji Dadi.

Lokacin karfe shida da rabi. Idon Aliyu yayi jajir dashi, saboda tsabar ciwon kai da ua rufe shi ta yadda aka Bata Masa Rai. Lallai Aisha ta taimake shi da yanzu Yana cikin duhu bai San yadda ake gudanar da mulkin sa ba sai kudi da suke amsa kamar me.

Dafe kan sa yayi. Jin har an fara Kiran sallah magariba yasa ya Mike zuciyar sa na zafi da radadi. PA'n sa ya kalla yasa ya debe masa tulin files din da suka kawo Masa daga Nan ya wuce masallaci.
Yana zuwa yai alwala ya shiga aka tada sallah. Yana idar wa ya Mike yai addu'a sannan ya zauna yana lazimi. Zuciyar sa ta bala'in karyewa da wadan da suke tare. Tsoron duniya ya shige shi na yadda zai je ya tadda Allah akan abinda magoya bayan sa keyi bai sani ba.

Yana mikewa ya nufi motar sa ya shiga. Sai da ya shigan ya Kira shugaban sojoji akan a kama dukkan commissioners a kulle su sai ya neme su.

Sannan ya tada motar ya bar gidan gwamnatin. Karfe bakwai saura ya shigan cikin gidan sa Mai gadi ya bude masa kofa sannan ya taho gun sa da sauri Yana fadin
"Barka da dawowa ranka ya dade!"

Hannu kawai ya daga sannan ya wuce ciki Dan ransa a matukar bace yake. Kai Mai gadin ya girgiza yace
"Alhaji Kenan duk da halin ka haka yake Amman yau dai an tabo ka."

Yana shiga bai zarce ko Ina ba sai cikin bathroom shower ๐Ÿšฟ ya sakar wa kan da. Sai da ya Jima tana jika sa sannan ya zare kayan jikin sa ya zuba a washing machine din dake cikin bathroom din sannan yai wanka ya fito daure da towel.

Zama yayi a gefen gado Yana Mai dafe kan da. Ba abinda yake son a yanzu in ba yaji yai kuka ba Amman kukan Sam yaki zuwa. Sai idon sa da yai jajir zuciyar sa na 'Kuna.

Wayar sa ce ta fara Kara sanin me Kiran ne Yasa shi janyowa ya dauka Yana yin sallama.
Mamah cikin tashin hankali ta amsa Hadi da fadin
"Wa'alaikum Salam. Lafiya Baba na me take damun ka."

"Mamah."
Sai Kuma yayi shiru. Abbah ne ya amshe wayar Yana fadin
"Aliyu lafiyar ka kuwa me take damun ka."

Kuka ya fashe dashi, take hankalin iyayen ya Kara tashi Nan suka hau tambayar lafiya amman sam ya kasa magana.
Wayar Abbah ya kashe. Yana mikewa. Mamah tace
"Me yace Yana damun sa."

"Bai magana ba. Ina Jin yanzu Zan tafi can."
Ido Mamah ta zaro tace
"A wannan daren?"

"Ba inda zaka ka Bari da asuba sai aje a dauko shi."
Komawa yayi ya zauna yana fadin
"Allah ka kiyaye min Aliyu a duk inda yake."

Ranar dai haka suka Kwana ba a cikin kwanciyyar hankali su ba.
Kamar yadda Aliyu ma bai runtsa ba tunanin mafita kawai yake yi.

*
Aisha kuwa tin Yamma take zaune tana jiran zuwan Aliyu Amman shiru har akai magariba Wanda hakan ya haifar Mata da bacin rai da kunci.
Ko da Abba ya dawo ma tana cin abinci ta shige daki. Kwanciyya tayi kawai sai hawaye wanda batasan dalilin yin kukan ba. Amman a ranta tana tunanin shin ko Ina Yaa AK din ta ya shiga tibda yau kusan wata uku Yana koya Mata karatu Amman bai taba fashin zuwan ba.

Anya lafiya kuwa. Ko dai bai da lafiya ne. Abin da ta dinga juyi dasu a ranta kenan. Daga baya Kuma sai hawaye a haka Kuma bacci ya dauke ta.

Washe gari tin asuba Yan Aiken Abbah waro Mai martaba Alhaji Kabir suka iso Dan Mamah ta hana Abbah tahowa.
Lokacin da ya fito daga masallaci sanye da jallabiyya ya tadda motar gidan su yai mamaki. Yana shiga suka taho suka zube tare da masa kirari.

STORY CONTINUES BELOW
Hannu ya daga musu nan suka gaishe shi cikin girmamawa suka fada masa sakon Mai martaba kan yana son ganin sa. Ba Bata lokacin ya shigan ciki dan ya shirya. Kan ya gama kuma ya bada sakon a hadawa bakin abincin Kari.

kan ya shirya har sun karya dan haka suna fitowa suka dau hanya.

*
Jiki a sanyaye ta tashi da safe Dan ta rasa me yake Mata dadi a haka Tai wanka ta taya Ummah aiki. Da kyar ta Sha Kunu sannan ta tafi makaranta. Duk Wanda ya kalle ta Sai ya tambaye ta me take damun tane? Sai dai tace Babu komai.

Karfe daya na rana suka shiga cikin gidan sarautar. Yana Isa Mai martaba da Fulani suka fito cikin shiga ta alfarma  suka tare shi. Hannun Abbah rike da na Aliyu suka Yi cikin gida. Sai da suka shigar dashi bangaren sa sannan suka fito Dan ya kintsa.

Wanka yayi sannan ya saka wata ash kalar shadda wacce tai masa kyau kamar ka dauke shi ka gudu. Kula ya saka akan sa ya kara fito da kyan sa. Wanka yayi da turare sannan ya fito. Kai ba kace Aliyu yana da damuwar komai. Yana fitowa ya samu kayan abinci. Kadan ya ci sannan ya Mike Dan yaji ana Kiran sallah.

A masallaci suka hadu da Mai martaba sukai sallah suna idar wa sukai bangaren Mai martaba bayan ya aika a Kira Masa Fulani Rashida.
Zaune suke dukkan su a falon Mai martaba Wanda take cikin gida. Aliyu zaune a kasa gefen mahaifin nasa. Bayan sun gama gaisawa ne Mai martaba ya daura da fadin
"Aliyu hankali na ya kasa kwanciyya tin jiya da naji kana kuka ban San har me zai saka kuka ba. Ka fadan me yake damun ka?"

Kasa yayi da kansa. Yai shiru. Mamah ce yace
"Ka fada Mana damuwar ka. Shin in baka fada Mana ba Wa zaka fadawa?"

"Abbah akan ragamar garin can ce.'
"Me akayi a garin?"

"Abbah duk wadan da nake tare dasu Basu da amana Sam. Saboda duk aiyukan da suke kawo min na saka hannu a Basu kudi Ashe Sam Abbah abin ba haka bane domin kuwa Basu yi komai ba. Abbah ya zanyi da Rai na. Na gama aminta dasu, Ashe su ba haka bane. Abbah ya zanyi duk laifi nane fa Allah ni zai kama. Yanzu da na mutu me zanje na ce da Allah. Ina Zan Kai hakkin talakawa na. Wannan abun shi ke damu na. Wanda ta dalilin wata yarinyar duk nasan da wadan Nan matsalolin. Ashe matsalar tafi yadda nake Zato. Abbah ya zanyi shiyasa tin farko ban son wannan shugabanci."

Ya fada yana rufe fuske sa da hannayen sa. Sam ya kasa ma kukan sai Idonsa da yai jajir hannayen sa da fuskar sa duk jijiyon su sun tashi alamar Yana cikin tashin hankali da bacin rai.
Daga Abbah har Mamah shiru sukai.

Abbah ne ya ce
"kana da gaskiya amman Aliyu ai daman duk inda mulki yake sai kasamu irin haka Kai kan ka in baka Kai zuciyar ka nesa ba zaka iya tsintar kan ka a wannan halin.
A ko da yaushe ina godiya da Allah da ya bani Kai saboda kana da hankali da dabi'u masu kyau kullum addu'a ta Allah ya cigaba da kiyaye min Kai tare da cire maka son abin duniya Kuma wannan mulkin ya zama silar shiga aljannar ka.
Dole wadan nan a hukunta su Kuma Kai ma ba a barin Abu a sa Masa Ido. Dole ana Yi ana binsa in da laifin su to kaima da laifin ka. Dan haka ka kula yanzu da yadda komai zai na gudanar Akan mulkin Kuma Kai ma Dole kana aiki da kanka tare da saka tsaro sosai."

"Haka ne Baba nah Dole ka sa Ido ka Kuma dage da addu'a akan Allah ya baka ikon ya taya ka shugabanci. Dole kana addu'a sosai. Domin ita ce makamin mumini domin kana naka wani Yana tasa kai baka Riki kowa ba Amman shi Kai ka tsokane maka Ido. Allah ya kiyaye ya Kare man Kai.

Numfashi Mai martaba ya suake yace
"yanzu wane hukunci ka yanke?"

"Na bar su wajen sojojina Kuma nace ai musu horo Mai tsanani bayan Nan Kuma Dole ne su dawo da kudin gwamnati.
"Hakan yayi kyau. Allah kiyaye gaba."

"Amin!"
"Yauwah ya zancen company Nan na Abuja."

"Wallahi Abba tin da na taho ban Kara lekawa ba Amman ina son naje. Kar ka damu Wanda abin ke hannun sa bai da matsala na yadda dashi dari bisa dari."
"To ai shikenan Allah ya taimaka."

STORY CONTINUES BELOW
"Muje na Samar maka abinda zaka ci ko?"
Mama ta fada.

Mai martaba ne yace
"Kije ki kawo Mana akwai abinda zamu tattauna."

"Shikenan Ranka ya Dade!
Ta fada tana mikewa.
Bayan fitar ta Abbah yace
"Ya iyalan naka kuwa?"

"Alhamdulillah!"
Kai Mai martaba ya girgiza Dan yasan Aliyu da zurfin ciki wannan case din ma ya fada ne Dan ya caja Masa Kai Amman da ba abinda zai sa ya fada musu sai dai daga baya suji. Bai san ya zaman sa da iyalan sa yake ba Sam.

Jiya sukai magana da Mama da take cewa matar Babanta shiru ko da cikin?"

Mai martaba yake cewa
"To kinsan dai shi ba fada zai ba.,"

"Haka ne. Allah ya kawo zuri'a Mai albarka dai."
"Amin!"
Suna zaune Maryama da Mujahida suka shigo hannun su dauke da manyan tray. Maryama na ganin Aliyu ta washe Baki tana fadin
"Yaya nah oyoyo."

Kallon ta yayi Yana fadin
"Ya kike?"

"Alhamdulillah ya hanya?"
"Lafiya."

Mujahida Kuma Ido ta zuba Masa. Sai da Maryama ta dungure ta ne sannan ta juyo suna hada Ido ta kanne Mata Ido da ta gyada Mata Kai.
Ajiye tray din hannun ta tayi tab fadin
"Sannu da zuwa Yaya!"

"Yauwah!"
Ya fada Yana danna waya ba tare da ya dago ya kalle ta ba.

Maryama ce tayi gefen mahaifin ta tana fadi
"Barka da hutawa Abbah!"

"Yauwah Maryama ya gidan?"
"Lafiya Lou."

Mujahida ma gefen sa tayi tana fadin
"Barka da hutawa Abbah!"

"Yauwah Mujahida ya gidan ba dai matsala ko?"
Kai ta gyada Tana satar kallon Aliyu.

Mikewa sukai zasu fita Amman Mai Martaba yace
"Kuma ki zauna aci daku."

Zaman sukai. Suna zaune sai ga sallamar Momy Nan da sha'awa. Shigo sukai. Sha'awa na ganin Aliyu aka fara wata karairaya da iyayi.

Maryama tana kallon ta tana ta murmushi. Mujahida kuwa kishi kamar ya kashe ta. Momy ce tace
"Barka da Hutawa Ranka ya Dade! Baya Goya marayu."

"Barka kadai Fulani da fatan Kuna lafiya "
"Alhamdulillah!"

"To madallah "
Mai martaba ya fadi.

Sha'awa tace
"Ina yini Abbah?"

"Lafiya Lou Sha'awa ya gidan da fatan ba wata matsala dai ko?"
"Babu Abbah!"

"Madallah!"
Aliyu bai San me suke ba Dan yayi nisa a aikin da yake a cikin wayar sa Sai ji yayi an zauna kusa dashi. Bai dago ba yaji an make murya ana fadin
"Barka da Hutawa Yayan mu Allah Kara lafiya da nisan kwana. Allah yayi jagora, Allah...."

Da hannu yayi Mata nuni da ya isa. Sannan ya cigaba da abinda take Yi. Daga Momy har sha'awa sun ji ba Dadi Amman suka maze sai Momy ce tace
"Saukar yaushe Aliyu ba labari."

Dagowa yayi fuska ba yabo ba fallasa yace
"Ina yini?"

"Lafiya Lou d'ana ya hanya?"
"Alhamdulillah!"

Bai Kara tanka Mata ba. Sha'awa kuwa kamar Tai kuka Dan bakin ciki da takaici. Mujahida kuwa Dadi taji a ranta. Dan ita tasan halin Aliyu bai fiya son wannan kirarin ba ita Kuma sha'awa gani take in tana Masa zai ji Sonta tinda tana kodashi.
Zaman shiru akai sai Maryama da Mai martaba dake Hira akan makarantar ta. Mujahida da Sha'awa kuwa idon suka kurawa Aliyu kamar su cinye shi. Momy kuwa bakin ciki da takaici ya cika ta.

Suna zaune Mamah wato Fulani Rashida ta shigo dakin cikin takunta nan kasaita  ta da shigar alfarma. Tana shigo suka hada Ido da Momy wacce kirjin ta ya buga Dan sosai Momy ta Mata kere duk da yadda take Daukar kan ta.

Ido ta dauke Mamah Kuma ta saki murmushi tace
"Barka da Hutawa!"

Murmushi yake ta saki sannan tace
"Yauwah!"

Ta kalli sha'awa tace
"Tashi mu tafi."

Mamah ce tace
"A'ah kuyi zaman ku ayi daku."

"A'ah ina da abin yi."
"Ni Zan zauna Mamah."
Sha'awa ta fadi.

"Yauwah sha'awa Yi zaman ki."
Mamah ta mike ta fice ba tare da ta Kuma magana ba.

"Maryama zubawa kowa!"
Janyo tray tayi ta bude Kular Kai. Plate ya dauko ta zuba musu gasasshen hadin nama da akai da lemo sai snacks, kowa ta zuba Masa ta mika Masa.
Ci suke suna Hira Banda Aliyu da ke ta danne danne. Sai da ya gama ya wanko hannu sannan ya fara ci. Kadan yaci ya janye hannun sa.

Mikewa yayi Yana kallan iyayen yace
"Zanje na dawo!"

"Allah ya tsare!"
Mamah ta fada.

"Amin!"
"Sai ka dawo. Allah kiyaye!"

Abbah ya fada. Haka ya fice Mujahida da Sha'awa suka bishi da kallo.Post a Comment for "WA NAKE SO CHAPTER 5"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...