WA NAKE SO CHAPTER 3 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WA NAKE SO CHAPTER 3

WA NAKE SO CHAPTER 3

- - Post a Comment

WA NAKE SO CHAPTER 3


A rayuwar ta burin Aisha sam bana ta kyautata tata rayuwar da jin dadi bane sai na ta kyautata rayuwar jama'a ne.


Wannan burun nata kuwa tana rasa taya zai kasance duk da a rayuwar ta bata cire rai da kasancewar sa.


Sau da dama tana zama tai zurfi a tunanin ta wacce hanya burin ta zai cika. Amman sau da yawa bata samun amsar wannan tambayar.


Ita ba inda take zuwa daga makaranta boko sai isilamiyya da Baba ne ke koyar wa ma sai kuwa zaman gida ko gidan su Hauwa.


Baba kuwa aikin sa yai nisa dan wajen wata uku kenan suna aiki a gidan Major AK wanda zasu ce basu taba ganin sa ba.


Mai gadi ne kawai ke ganin sa shima ta cikin mota ko in ya fito yaga bayan sa.


A wata ukun nan Baba ya samu alheri da yawa a aikin da yake inda gida ma suka san da haka dan komai cikin wadata ake musu shi.


Major Ak, kuma gwamna a yanzu aiki yake wanda shi dai a kawo masa kwangila yai signing amman bai taba bin aiyukan ya gani yadda suke wakana ba.


Haka nan Hajara tayi tsamo tsamo a cikin siyasa dan sai yadda tace duk da Aliyu bai san abinda take yi ba.


Sai suyi sati bai gan ta ba tinda ba gida daya suke kwana ba ita ta ce sai gidan gwamnati shi kuwa ko a cikin gari ba kowa yasan da cewa ba agidan gwamnati yake kwana ba. Inda ba wanda yasan gidan da yake gidan sa ne.


STORY CONTINUES BELOW

Sai ddaga baya ne su Baba suka sani shima gwamna Aliyu sam bai san sun sani ba.


Haka rayuwa taci gaba da tafiya har Yai shekara akan kujerar gwamna yasa an gina makarantu masu kyau amman sam ba a dauka mutane sai masu hannu ko mai kudi.


Shi da bai damu da harkar jama'a ba wannan yasa bai damu da bincike yaga abinda yake wakana


Yau Baba da wuri ya baro gidan Majir Ak wanda a lokacin tashin sa bai ba ya tashi ne saboda zazzabi da ya rufe shi.


A lokacin kuma Major Ak ya dawo yace a tara masa mutanen dake aiki a gidan sa gaba daya.


Bayan an tara ya sa aka dibar masa list kowa da aikin da yake yai musu dadin albashi banda Baba da ya taho gida kuma basu lura baya nan ba.


Sai washe gari da Baba yaje aka fada masa wannan yasa, ya nemi ganawa da Major Ak.


An masa iso sai dai kwarjini irin na Aliyu yasa Baba kasa masa magana akan abinda ya kawo shi.


Sai da kyar ya ce,

"Ina daya daga cikin masu aiki a gidan nan kuma jiya bana nan akai....."


Bai karasa ba ya dakatar da shi.

"Ya isa!"


Shiru Baba yayi. Ya ce,

"Ni na riga da na gama sai dai kaje zuwa wani lokacin in za a kuma daukar ma'aikata."


Baba zai magana ya ce,

"Ya isa!"


Kudi ya debo ya mika masa. Amsa Baba yayi ya mike ya fito jiki a sanyaye dan dai yanajin dadin aikin gidan nan bama yadda ya rufa musu asiri sosai.


Haka Baba ya koma gida da yake ranar lahadi ne Aisha na zaune. Ya shigo jiki a sanyaye.


"Baba lafiya?"

Ta tambaya.


"Lafiya lou. Ina Ummahn taku."

Ummah ta fito daga bayi hannun ta rike da buta. karasowa tayi da sauri ta ce,

"Badai jikin ba."


Kai ya gyada dan yaga Aisha a gun.

"Dauko min tabarma Aisha."

Aisha ta dauko ta shimfida masa anan tsakar gida.


Kwanciya yayi Aisha ta koma daki. Ummah ce ta kalle Baba cikin damuwa ta ce,

"Amman kuma naga kana cikin damuwa fa."


"Uhmm kedai bari. Wai jiya da na taho ashe an kira gaba daya masu aiki an dau suna an dada albashi."

"Ahm toh Alhamdulilah!"


"To shine fa, da bana nan yau da naje na same shi amman yaron nan ya rufe ido kan cewa sai dai nayi hakuri kuma."

"Inna lillahi wainna illahir rajiun!"


Haka Ummah tai ta maimaitawa. Baba ya ce,

"Shine fa na taho dole yanzu na koma neman wani aikin."


"To Malam Allah yasa haka shine mafi alheri amman dan Allah kada kasa damuwa. Kowa da tasa irin kaddarar."

"Ba komai nagode."


Aisha dake daki tana jin duk abinda suke yasa a ranta ta ce,

"Daman haka masu kudi suke sam basa daukar uzuri."


Tin daga lokacin ta ke jin haushin wannan da ya kori mahaifin ta daga aiki.

"Allah kai min arziki aga yadda ake mulki da son talakawa."

Ta fada a zuciyar ta.


Har da kukan ta. Abin bai kara bata tsoro ba sai da taji Baba yana fadawa Ummah cewa gidan Gwamna na ne inda yake aiki baya son a sani ne.


A ranta ta ce,

"Gwamna!"


Tai shiru ta fara sauraron Baba. Ya ce,

"Kinsan soja ne."


Ummah ta ce,

"Ah ba mamaki ai mu godewa Allah da ba mu shiga uku ba. Kasan mulkin soja wuya gare shi "


Fateema dake daki ta ce,

"Au wai gwamnan ma haka suke da son zuciya ashe."


A ran ta ta kuduri niyya sai taje wajen gwamann nan ta fada mai gaskiya ko da zai harbe ta ne

STORY CONTINUES BELOW

Ita a rayuwar ta kudi ko mulki ko wani abu duk basa burge ta ko bata sha'awa indai ba taimako zatai ba.


A ranta ta ce,

"Allah kamin arziki amman in har bazan taimakawa yan uwa musulmai ba Allah ka bar ni a yadda nake."


Sam Aisha bata da kwadayi, tsoro, duk girman mutum yai ba dai dai ba sai ta fada masa ko waye shi.


Wannan yasa ta kuduri niyyar tambayar Baba inane yake aiki kawai dan ta je taga wannan gwamnan.


Da dare bayan sun kare cin tuwon daren su suna zaune Baba yana mata karin Fikihu yana mata bayani akan jinin haila da yadda ake wankan tsarki kasancewa Aisha yanzu ta kara girma shekaru sun ja yanzu shekarun ta goma sha daya.


Duk da bata fara al ada ba amman yana da kyau kafin a fara mutum ya kasance yana da sani sosai akan sa.


Sai da suka gama ta dube Baba ta ce,

"Baba wai a wane gida kake aiki ne?"


"Can saman mune."

Kasancewa batayin can waje ne yasa ta ce,

"Baba ya gidan yake."


Murmushi Baba yayi ya ce,

"Yar gidan Yaya kenan. Gidane babba mai kyau "


Kai ta girgiza ta ce,

"Yauwah wai Baba ka taba zuwa gidan gwamnati?"


Kai ya gyada mata ya ce,

"Nadai wuce ta kofar gidan."


"Yauwah Baba dan Allah ya gidan yake?"

Murmushi yayi ya ce,

"Duk gidan gwamnati zaki same shi katon gaske dan kusan dan akwai bangarori da yawa har akwai gidajen da ake ginawa banda dakunan taro da sauran su."


"Baba kato sosai fa kace."

Kai ya gyada ya ce,

"Eh zai iya yin rabin gari ko kwatan gari guda"


Baki ta rufe da hannu ta ce

"Tab Baba kuma duk mai ake a ciki "


"Akwai ofisoshi na mutane da yawa akwai dakunan taro akwai na matar gwamna banda gidan gwamna da wasu daga cikin yan cikin gwamnatin."


Kai ta gyada ta ce,

"Baba ina sha'awar siyasa. Amman ba dan komai ba sai dan na kwatowa kasa ta yan cin ta."


"Hakan na da kyau. Amman kinsan dai mata basu fiya siyasa ba ko?"

Kai ta gyada ta ce,

"Ina addu'a Allah bawa Yayanah ne yadda zamu gyara kasar nan. Baba siyasa bata dace da masu son rai ba kwata kwata. In ka zama mai mukami aikin ka kawai ka biyawa al umma bukatun su amman Baba kalli yadda rayuwar mu take, kalli yadda karatun mu yake, kalli yadda titinan mu suke ka kalli ko famfo bamu dasu tuka tuka daya gare mu fa Baba, amman a yadda nake ji kudaden da ake bayar wa dan bukata mu duk ina suke tafiya. Baba kenan su suke cinyewa. Mene amfanin cin kudin al umma Baba. Hakkin wasu ne fa. Bayan su suna cikin rayuwar jin dadi amman Baba suke kuntata mana ta mu. in sun inganta rayuwar mu da me zasu ragu bafa kudin su bane. Gaskiya Baba na tsani wanna gwamnan ba shi kadai ba Baba har shugaban kasa. Dan suna zalumtar mu.

Baba ko a gida na kwana banci abinci ba laifin na gare ka. to in kai kuma ka fita nema baka samu ba a ina laifin yake kenan. Baba yana hannun shugbannin mu fa. Baba wai basa tsoron Allah ne. In muje lahira me zasu fadawa mahallicin mu."


Shiru tayi tana goge kwalla. ta ce,

"Ina son Yaya ya zama mai mukami dan ta wannan hanyar ce kawai burin mu zai cika na biyawa al umma bukatun su sai dai ina tsoron ranar tashin alkiyama ya zama an tsada shi akan yadda ya gudanar da mulkin sa."


Sai ta kuma fashewa da Kuka.

"Baba akwai hadisin da ka karanta min wanda kake wa shugaba bawan al umma ne, to. Baba tayaya al umma suke zama bayin shugaba kenan sun juya hadisin basa amfani da su.

Baba in har ka bautawa al umma wai me zai rage mu da shi bayan ba dukiyar su bace.

Baba akwai ranar al kiyama fa. Ranar da za a yanke mana hukunci in munyi aiki na gari aljanna in munyi akasin haka wuta.

Baba mai yasa muke makancewa ne, muke makancewa akan hakan mudai kawai duniya duniya. Bayan duniyar nan ba dindin din bace, ta dan wani lokaci ne da mu inganta rayuwar su amman sai dai ku inganta duniyar mu bayan lahira ita ce matabbata.

Ina tsoron wa Yayanah haka Baba. Amman nasan waye Yayana kuma zan kasance mai masa nasiha akan harkar mulki Baba.

Zan kasance mai tinasar masa da abinda ya manta a koda yaushe tin kan ya kauce hanya.

Zan kasance mai sa masa tsoron duniya dan ya cire ta daga zuciyar sa.

zan cire masa sha'awar azurta kan sa da dukiyar talakawa.

Zan sa masa tunanin neman aljannar sa da wannan mulkin ta hanyar kyautatawa al umma da kula da kowa na karkashin sa."


Tai shiru tana ajiyar zuciya ta ce,

"To Baba su ina duk wadan nan tunanukan nasu ya tafi. Daga su har matan su da iyayen su.?"


Baba da Ummah da suka saki baki suna kallon Aisha suna mamakin irin kalaman dake fitowa daga bakin yarinya yar shekara goma sha.


Kai Baba ya jinjina ya ce,

"Gaskiya ne Aisha hakika ke yarinya ce wacce duniya bata gaban ki. Aisha ina alfahari dake kuma zan cigaba da alfahari dake a koda yaushe kuma zan cigaba da miki addu'a Allah ya biya miki duk kan bukatun ki, Allah ya jagoranci rayuwar ki Aishaa."


Ummah kuwa jikin ta taja Aisha tana dan bubbuga bayan ta har tai shiru.


Lokaci guda imani da tsoron Allah ya cika zukatan su ga tsoron danne hakkin al umma. A haka ta mike taiwa iyayen sai da safe ta shiga dakin ta.


Kan katifar ta yar karama ta haye tana addu'ar bacci. Ta jima tana tunanin rayuwa da tsara yadda zasu gudanar da rayuwar su ita da Yayan ta.

Ta hanyar taimakawa al umma da inganta rayuwar su. Sai da su Ummah suka shiga daki sannan kuma ta samu bacci ya dauke ta.*

Aliyu kuwa sam saboda rashin son hayaniya yasa bai cika bin didigin aiyukan da ake ba.


Shi dai a ganin sa ana aiki dan ana shigo masa da batun kuma yana sakin kudin aiki sosai.


In yaje gidan Gwamnati da safe yamma nayi yake komawa gida. Da ya koma zai gudanar da abinda yasa ba yi.


Wanka yake farayi yai alwala ya nufi massalaci bai fitowa sai bayan isha'i.


Da ya fito cikin gida yake wucewa ya danga news sannan ya dan sha abu mai sanyi ko dumi ya shiga daki.


Kamar yadda ya saba karfe ukun nan yake tashi yai ta sallah. Har sai karfe biyar yake fita. Massalacin da ya gina a gefen gidan sa nan zai zauna har karfe bakwai.


Daga nan zai shige gida yaje yai training din sa. Sannan yai wanka yaci abinci.


Sai karfe tara yake shiryawa ya nufi can gidan gwamnati ya fara gudanar da abubuwan da yasa a gabansa.


In ya samu time zai dan shiga cikin gidan da yake dan zama anan ne in Hajara na bukatar abu zata je ta fada masa.


Daga haka kuma yayo gidan sa. Haka kullum rayuwar sa take kuma shi bai yadda da wasu securityn sa ba dan a ganin sa takura masa sukeyi.


Dan haka kawai yake cewa su bar sa. Ko gidan sa na can basu sani ba iya kar su gidan gwamnati. Duk yadda suke son su rakashi ko su na kula dashi zai hana su.


Hajara kuwa sam bata damu da harkar mijin ba ita dai ta nemi kudi sai in tana bukatar sa amman sam bata san yadda zata kula da shi ko da cin sa ba ruwan ta bare damuwar sa. Ita dai kudi sai ko in tana bukatar wani abun shine fa zata neme shi amman in ba wannan sam bata wani lura ko kula dashi.


*

Aisha kuwa tin daga lokacin ta kara sakawa kan ta kaunar karatun ta dan tasan da shine kadai burin ta zai cika.


Ta sawa kan ta damuwar abinda gwamna yai wa mahaifin ta dan yana aiki karkashin sa shine zai kore shi.


A ranta ta dau niyar sai taje ta samu gwamna koma me zai mata ta fada masa gaskiya ko da zai kashe ta.


Da wannan irin tunannin kullum take kwana take tashi tin daga lokacin da taji abinda gwamna yai mata.


Wannan yasa ta kara tsanar sa fiye da tunanin mai karatu.

Kwance nake a falo ina sanye da purple kala siket sai riga fara mai dogun hannu. jikina sanye da hijab ash kala. Sallamar sa naji. Mikewa nayi a hankali na sauke ido na kan sa.+


Yana sanye da wando jeans sai ash kalar riga mai dogon hannu. In zan lura Yaa Fauwaz na son Ash kala sosai.


Fuskar sa tayi kyau sai tashin kamshin turare yake wanda kafin yazo wajena shi nake fara ji. Haka in yana gidan na dawo daga ckul kamshin sa nake fara ji.


Ko ina kitchen ya shigo to kamshin sa ke farai min sallama. Abinda nafi so kenan kamshi wannan yake kara sani jin son sa a rai na.


Kallon juna mukai dan ni a zato na yana fushi dani dan yau kwana biyu kenan da ya kawon zancen Fu'ad.


Bansan waya fada mai ba duk ya tashi hankalin sa. Dan a lokacin ni har na fidda rai watakila ma Yaa Fauwaz ya hakura da ni dan har da kuka na na sha.


Har ga Allah ina son sa kuma ina son Fu'ad (chapter wadan nan da gaske ce true life ne soyayyar sai dai dan kari da zanyi akai. Amman duk wannan situation da zakuji sun shiga hakan ya faru da gaske.)


Zama yayi ya ce,

"Kin ganni ko? Na kasa hakura da rashin ganin ki."


Kai nayi kasa da shi. Ina dana sanin jefa wadan nan mutane biyu cikin wani hali.


Tin daga lokacin na fara tsoron ace ana son ka ka yadda ba dan kana son mutum ba sai dai dan kawai kayi na lokaci ne ya wuce.


Toni ga abinda ya faru dani na. Tin ba aje ko ina ba na fara jin son sa a rai na kamar zan mutu. Kuma fa bawai son Fu'ad ne din shima bana yi ba.


"Fateema dan Allah in kina min abinci bakya dan min barbade."

Duk da ina cikin wani hali na damuwa sai da na dago na dan harare shi.


Murmushi yayi ya ce,

"To kece duk yadda nake tunanin ki kin wuce nan. Ya Allah! Jifa yanzu na kasa hakura da ganin ki."

Ya dafe kan sa.


Kai na a kasa ban dago ba. Ya ce,

"Fateema kina so na."


Kai na gyada masa. Ya ce,

"Me zakiyi ki nunan haka."


"Ko yanzu ka aiko a daura mana aure."

Murmushi yayi ya ce,

"A rayuwata ban so yin aure yanzu ba na so sai na karo karatu amman ina ganin hakan bazai yiyu ba."


STORY CONTINUES BELOW

Shiru yayi ya ce,

"Da na fara service zan sa azo a tambayar min auren ki."


Wani sanyi na ji a lokacin sam ban kawo ya Fu'ad zai ji ba ko wani abu.


To ni nasan a zuciya ta na fison Yaa Fauwaz.

"Yunwah nake ji. Rabo na da abinci tin jiya naka sa ci."


Mikewa nayi da sauri nace

"Haba saboda me to?"


Nayi waje Kitchen naje na daura masa abinda yafi so wato dan wanke. Na soya manja muna da yaji na hado na kawo masa hade da lemo da ruwa.


Sai da yaci ya koshi sannan ya dawo kan kujerar da nake zaune da yake three sitter ce.


A gabana ya zauna muna fuskantar juna. Kasa nai da kai. Kai na ya dago ya zagaye face dina da hannun sa.


Ido na ya kalla ya ce,

"Idanun ki na burge ni. Ke dan Allah wai haka kika barni kuwa. Nayi soyayya kala kala amman ur own is different, yadda nake son ki yadda nake jin ki da komai ma."


Shiru mukai. Ya ce,

"Fada min kina son Fu'ad."


Shiru nayi bugun zuciya ta ya dadu. Ya ce,

"Oh My God please tell me!"


Kai na gyada masa. Dan murmushi yayi ya ce,

"Dis girl how can u love two person at thesame time. Is either kin fi son sa ko kin fi so na. Fadan dan Allah wa kika fi so?"


Da hannu na nuna shi. Kai ya dan daga yana tunani ya ce,

"Kai fa a gaban sa shima kice kinfi son sa."


"Haba dai I love u more than him, kai ma kasani."

Baki ya dan tabe ya kamo hannu na.


Kallon sa na tsaya yi. Kan kirjin sa ya dauran hannu nai saurin rintsa idanu na. murmushi yayi ya ce,

"Kinji yadda zuciya ta take bugawa ko?"


Kai na gyada dan naji sosai take bugawa. Ya ce,

"In har muna tare abinda nake ji kenan. Kuma duk bugun da zarai sai ta ambaci sunan ki."


Face dina ya dago yai min kiss a goshi ido na lumshe. Kallo na yayi ya kamo hannu na yai min a hannu.


Can ya ce,

"Bari Inje gun Mummy bana son nayi wani stupid abu anan."


Ya mike ya fita yana kallo na. Nima kallon nasa nake har ya fice. komawa nai na kwanta.


A zuciya ta ji nake ya zanyi, nasan ina son Fu'ad to amman kuma son Yaa Fauwaz daban yake nima ina jin sabon abubuwa in ina tare dashi wanda banji in muna tare da Fu'ad.


A can parlour kuwa Momy da Yaa Fauwaz ne ya sa mata daru wai sai ta ce ta bashi ni.


Momy ta ce,

"Fauwaz ina son ka sa Allah a ranka. Ka sani matar mutum kabarin sa kuma wani bai auren matar wani. Dan haka Indai Fateema matar ka ce ko mu dade ku mujima sai ta zama matar ka. And also kasan ance rabo ajali ko?"


Kai ya gyada ya ce,

"Momy ni ai ya zama ni kadai take kulawa please Momy"


Shiru Momy tayi ta ce,

"Kasan me kaje ka nemi soyayyar kanwar ka. Munan ba mai mata auren dole sai wanda take so. Dan haka kaje ka nema.

Bana son nasa magana akan al amarin nan Allah yayi wani abu ya faru kazo kana ganin kamar laifi na ne."


"Shikenan Momy amma Allah Momy ina son Fateema."

"Zan tayaka da addu'a."


Kai ya langwabe ya dawo daki in da nake. Ido na a lumshe ya sameni a hankali ya zauna daga inda ya tashi.


Ido na bude na kalle shi. Murmushi ya sakar min nima na mayar masa.

"Momy uwa ce ta gari tana kokarin kwantar min da hankali da na kawo mata wata matsala ta tana fuskan tata."


Murmushi kawai nayi. Hannu na ya kamo yana murzawa. Ya ce,

"Ina son ki Fateema."


Ido na lumshe. Kissing hannun nawa yayi. Haka muka yini tare sai magariba ya tafi.


Zuwan Yaa Fauwaz yasa sam bani da lokacin Fu'ad dan in yana nan bazan so yaga ina waya da wani ba haka nan in yana nan shima bazan so wani yazo ba.


Yaa Fauwaz da yazo kano dan yayi sati ko sati biyu sai gashi shine har month ko shirin tafiya bai yi.


A lokacin kuwa sosai Hankalin Fu'ad ya tashi dan sam Hankali na baya wajen sa.


Yakasa samo nutsuwa ta duk ya rame ya zama abin tausayi. In na zauna ina tunanin irin rayuwar da muke dashi nakan yi mamakin mai yaja hankali na ga Yaa Fauwaz.


Dan Fu'ad ma dan gayu ne, in kyau ne ma zai iya fin Yaa Fauwaz shima dan gata ne ta wajen iyaye da yan uwa. Ga ilimi both. Komai ya hada. Ya'yan yan uwa da yan ckul duk son sa suke amman shi ya kafe sai ni.

Yau ina gidan Yaa Zaharadeen dake a bayan unguwar mu yake. ina goye da Dan ta Sabir,  Fu'ad ya kira ni. Kan cewa yana hanya.


Kasancewar tare muka zo da Yaa Fauwaz amman ya tafi kasancewar magariba tayi nace ina gidan Yaa Zaharadeen.


Ina sanye da daguwar riga Red kala wacce nai amfani da bakin mayafi nai kyau.


Ai kuwa can yazo ya same ni. A lolacin yana sanye da wani farin wando da jar riga yai kyau sai fidda kamshi yake. Amman kallo daya zakai masa kasan hankalin sa atashe yake.


Ya rame yayi baki duk yai kalar tausayi. Muna zaune a falon su bayana goye da Sabir muna dan hira.


Wayata ya amsa yana dube dube can ya shiga whatsapp tin da ya shiga kirjina ke dukan uku uku.


Chat din mu da Yaa Fauwaz ya shiga. Inna lillahi wainna illahir rajiun. Wallahi a lokacin ji nayi kamar ba laka a jikina. jikina yai sanyi ba kwari.


Abinda ya gani shi ya daga masa hankali ya ce,

"My me zan gani. Bazaki iya rayuwa ba shi ba. Innalillahi wainna illahir rajiun. Ya salam ni da nake da burin in rayuwa dake. Jifa My abinda kika rubuta ba kowa a zuciyar ki sai shi."


Idon sa ne ya fara zubar da ruwa, can kuma ya mike yana dafe kirjin sa da yai masa nauyi, Zubewa yayi a gun dan ya kasa tsayuwa. Inna illahi wainna illahir rajiun tashin hankali ba a sa masa rana.


Ni dai na hau cewa

"Dan Allah Fu'ad ka tashi."

Abinda na iya fada kenan dan baki na ya mutu ya riga ya kamani tsamo tsamo.


Ganin yaki tashi yasa na shiga na kira Anty Baby nace tazo Fu'ad ya fadi.


Nan na bata dan ta dan shima kokarin fadowa yake daga baya na dan jikina har rawa yake.


Fitowa mukai tare Anty Baby ta fara lallashin sa tana ya tashi sai da na taimaka masa ya mike sai ya fara magana ya ce,

"Anty Baby mene nake wanda Fateema bata so wallahi zan canja. Anty Baby kalli fa kalli abinda Fateema ta rubutawa Yaa Fauwaz wai bazata iya rayuwa ba shi. Shi kadai ne a zuciyar ta."


Kirjin sa ya buga ya ce,

"Ni kuma fa. Ya zanyi ni da Allah ya dauran soyayyar ta tin ina yaro nake fama da son ta. Inna lillahi wainna illahir raji'un."


Nidai ina gefe duk yadda Anty Baby taso ta ganar da Fu'ad ina idon sa ya rufe. Kasancewar nasan wace Momy kuma zata iya ganar dashi nace,

"Anty Baby bari kuje gun Momy."


"To Fateema."

na mike. Shima ya mike. Tafiya muke bame ce da dan uwan sa kala.

A lokacin Fu'ad idon sa ya rufe ko gaban sa baya gani. Na gane hakan ne lokacin da ya fada cikin wata kwata muna tafiya abinda kwatar yasan da ita amman ina bai lura da ita ba a lokacin.


Sannu nai masa muka karasa gida. A gate na debo ruwa na zuba masa har ya fita na shiga ciki.

Momy na gani zaune a falo. ta ce,

"Lafiya?"


"Nida Fu'ad ne bari dai ma shigo dashi gun ki yazo."

Mayafi ta dauka ta yafa sannan na fita na shigo da shi.

Muna shiga ya zauna a falo ni kuma nai shiru. A daki fargaba nake na rasa ya rayuwa ta zata kasance duk na rude ganin halin da Fu'ad ya shiga.+


A falo kuwa Fu'ad nacan yanai wa Momy kuka sosai shi yana so na ya zai yi.


Momy ta ce,

"Fu'ad ka kwantar da hankalin ka. Kamar yadda shima Fauwaz yake zuwa ya kawon damuwar sa har da kukan sa shima kai ma yau haka ne. Abinda na saba fada masa kai ma shi zan fada maka dan ban da abin fada yanzu.

Ka kwantar da hankalin ka. In Allah yayi Fateema matar kace ba mai aurar ta sai kai haka nan in akasin haka ne ba yadda zamuyi. Matar mutum kabarin sa. Kuma akace rabo ajali.

kasan rabo kan sa a mutu dan haka ka mika komai ga Allah dan Allah ka daina sa damuwa kaji."


Maganar da Momy tai masa ta dan sanyaya masa rai amman fa yana tsoron rasa ni.


A kalla sai da suka dauke awa daya suna magana dan ranar Dady baya gari sannan ya mike yai mata sallama.


Daki Momy ta shigo ta same ni na zuba tagumi. Zama tayi a gefe na ta ce,

"Kada kisa damuwa a ranki. Kije zai tafi."


Mikewa nayi nabi bayan sa. A compound na same shi. Na tsaya. ya ce,

"Zan tafi."


Kai na a kasa saboda nauyin sa da nake ji na ce,

"Kayi hakuri."


"Inyi hakuri da me? Fateema bakya sona ko?"

Kai na girgiza.


Wanda a zuciyata sam ni Yaa Fauwaz nake can tunani.

"Shikenan zan tafi sai da safe."


"Allah tashe mu lafiya."

Na rakashi har bakin gate sannan na dawo na shiga daki.


Tin daga lokacin kullum kowa da matsalar da zai kawon a gun sa. Daga in na kashe ta waccan sai kashe wannan ya tashi daga na magance sai na wannan ya tashi.


Bama Yaa Fauwaz da kullum muke tare sai yasa kullum yazo sai yai wa Momy zance na.


Haka nan kullum cikin kara so ya tabbatar da ina son sa yake. Ya kasa gamsuwa. Wanda ni kuma ina son sa har cikin rai na.


In yace zai hakura sai ya kasa haka dai ni kuma kullum cikin nuna masa ina son sa nake.


Abinda ya kawo tafiyar Yaa fauwaz ba komai bane dan zai je yai shirye shiryen tafiya service.


Wata rana muna zaune ya ce,

"Fateema kina son na zo kano service?"


Kai na gyada masa. Ya ce,

"Da gaske fa!"


Kai na gyada ya ce,

"Ok zanje nayi iya yi na a turon wajen ki."


murmushi yayi ya ce,

"Beauty murmushin kima daban yake."


STORY CONTINUES BELOW

A gaskiya Yaa Fauwaz ya iya soyayya sosai. Kana tare da shi kana manta komai sai son faran ta masa.


Ni mai shiru shiru sosai yake sani magana dan ko banyi ba zai nuna bacin rai wanda ni kuma ban son bacin ran sa.


Abu da yawa yana burge ni da Yaa Fauwaz. Shi mutum ne simple wanda duniya bata fiya damun sa ba. Dan shi bai son mace dan kyan ta. Dan ya nuna min pics din yan matan sa da yawa duk ba kyawawa bane.


Dan ni kadai ce kyakawa ma a ciki. Haka nan bai son yawan make up a cika fuska da kwalliyar nan, daga kwalli sai man lebe nake amfani da su wanda idan ya ganni yata zuzuta kyauna kuma ba wai dan dadin baki ba har ran sa haka yake.


Bai son mace mai iyayi da gwalli to nima kuwa rayuwata so simple na dauke ta. Wannan yasa na kara damke zuciyar sa yake sona fiya da yadda yaso ko wacce girlfriend din sa.


Yana son mace mai tsafta sai gashi anzo wajen dan tsafta sosai nake da ita dan yana jin jina min shi kansa.


Haka yana son mace wacce ta iya abinci sai kuma nima Allah yasa gwanace fa karshe wannan yasa yake kara girmama ni da kwadayin zama matar sa.


Sai ilimin addini wanda yake da son sa sosai. Sai gashi har yanzu da na sauke nayi hadda ban daina neman sa ba. Yana son samawa ya'yan sa uwa ta gari ko dan tarbiyar su dan uwa ita ce karfin tarbiyya duk da dai ance *tarbiyya na ga Allah* (my next buk insha Allah).


Duk da ni dashi muna sawa a ran mu dan mun hada jini shiyasa soyayyar juna mu ta dadu a zuciyar mu.


Tayaya mutum zai iya barin mace mai dukka wadan nan abubuwan bayan itama tana son sa.


Bata duba rashn ilimin nasa da wani abu nasa ba ta rungume shi hannu bibiyu dole shima ya soni kamar rayuwar sa.


Yakan yawan fadan best food da kalar sa. Wanda nake yawan masa su. Haka best kalar sa nakan yawan saka kaya masu kalar su.


Baki na nakan masa ado da wani pink man lebe wanda in na saka Yaa Fauwaz yai ta yabon lips dina kenan.


A yadda na gane Yaa Fauwaz mutum ne mai nunawa in abu yai masa. Nidai ina jin dadi dan kumai nayi zai yaban ya nuna jin dadin sa.

Haka ma Fu'ad namiji ne da ko wacce mace zatai burin samun sa a matsayin masoyi ko miji. Namiji ne mai son wahaltawa matar sa. Mutum mai saukin kai baka taba jin yai fada da wani kuma ko an bata masa rai yana jimawa kan ya dau zafi. Sai dai in aka kai shi bango. In kuwa yai zuciya da abu yayi kenan.


Haka Rayuwar mu ta dinga kasancewa. Duk da ina kwatan ta cusa Fu'ad a raina da nuna masa dukkan kulawa ta amman kuma son Yaa Fauwaz na kara daduwa a cikin zuciya ta.


Akwai lokacin da ban dauki wayar Fu'ad ba tin dare to har aka kwana haka da safe ya tafi ckul da kyar ya iya abinda ya kai shi. Ga shi ya kasa cin abinci.


Yana dawowa daga ckul wanka kawai yayi ya saka kaya yayo unguwar mu.

Naji tsoro da na ganshi dan so nasan Fu'ad na min shi.


Jiki har rawa yake yake fadan,

"Fateema me nai miki ne? Fateema ko abinci na kasa ci bare naji dadin rayuwa. wallahi Fateema kece rayuwa ta ki ka barni mutuwa zan yi."


Take kaunar Fu'ad dina ta dawo sabuwa a cikin rai na. Kitchen na mike na shiga na hado plate babba da kayan tea da duk abinda zai bukata na da abinci na kawo masa.


Zama nayi na ce,

"Kayi hakuri ba abinda kai min."


Na hada masa tea nace kasha ko cikin ka ya warware. Dan nasan Fu'ad yana da wata ulcer wacce ya zama chronic zan iya cewa kullun sai Fu'ad yayi ciwon ciki shi yasa ma kullum a kare zaka ganshi bai da kiba ko kadan.


Sai da yasha na hada masa abinci ya sha na dauko masa maganin ciwon ciki shima ya sha.


Sannan na zauna ina kwantar masa da hankali kan ya daina sa damuwa aran sa. Sosai ya sake mun jima dan har karfe goma muna tare.

STORY CONTINUES BELOW

Labarin soyayyar mu ni da Fu'ad abar so ce da burgewa. Dan mun fara soyayya tin bamu san mene so ba. Haka tin ina jin kunyar sa dan ko kallon sa ban iyawa har buya muke muna zance.


Duk da a lokacin ko mun hadu ba abinda nake iya fada masa sai dai shiru saboda kunya, tin ina shekara 10 muke tare yanzu shekarra mu 9 tare haka dai Har takai yana zuwa gidan mu. Tin sai shekara shekara yake zuwa har ya zamana sai sallah babba ko karama. Kai har takai ta kawo duk ranar lahadi yana gidan mu. Har ta kai ta kawo zai iya zuwa guna a koda yaushe.


Iya fahimtar juna da soyayya tsakani na da Fu'ad duk mun wuce wajen. Tin in yai magana na kasa amsa. In ya ce, nayi shiru na ce me zance. Har takai ta kawo ni da Fu'ad kowa na iya fadawa dan uwan sa damuwar sa.


Mene cikin so in ba tausayi da sadaukar da komai ga masoyi ba. To ban da haufi wallahi Fu'ad kome ne zai iya min dan samun farin cikina.


Sau da dama da muka hadu da Yaa Fauwaz ko in ce da muka fara soyayya Fu'ad kan yawan fada min.

"Fateema farin cikin ki shine nawa. Wallahi in har son Yaa Fauwaz shine farin ciki gareki zan sadaukar da soyayya ta gareshi. Nasan Yaa Fauwaz yana son ki to bazan dana sani ba dan nasan zai kula dake ko ba komai dan uwan ki ne bare kuma ga soyayya."


Ko kuma ya ce,

"Fateema in har kina son Yaa Fauwaz zan iya barin masa ke. Sai dai ki sani ina matukar kaunar ki."


To nima ba son sane bana yi ba ban san me zance yake damuna ba.


In muna hira yana fadan irin son da yake min da burin sa ga rayuwa wanda duk wanda yaji sai ya kara son wannan masoyin nasa dan yawancin komai na rayuwar sa ya sadaukar gareni ne. To in yana fadan wadan nan sai in ji dama Yaa Fauwaz ne ba dan wai Yaa Fauwaz baya fada min su ba kawai dai.


Lokaci da dama in yana nuna kulawar sa gareni nakan ji ina ma Yaa Fauwaz ne.


Sai da takai ta kawo in muna zaune yana narkar min da zuciya har hawaye nake dan a lokacin zan fi so naji Yaa Fauwaz ne ke Fada min dadadan kalaman da yake fada min.


Shakuwa ta da Fu'ad gaskiya tayi kololowa dan har ina zanton so daman shakuwar muce yasa nake ganin kamar son sa nake amman ba shi nake so ba.


Haka nan muna tare da Yaa Fauwaz wanda yai wajen wata biyu zuwa uku.

A haka muka kara shakuwa mai tsanani da Yaa Fauwaz dan sai da yai watanni da kwanaki ya fara shirin tafiya.


Duk hankali na ya tashi. Dan na shaku da Yaa Fauwaz dan kullum muna tare kwana dai dai ne bai zuwa gidan mu.


Ranar da Yaa Fauwaz zai tafi kuwa kuka sosai nai ta shan sa. Dan da yazo na mike zan rakashi gate dan Yaa Kamal shi zai kai shi Airports


Muna tsaye a barandar falo ya kalli ni. Ya ce,

"Baby nah zan tafi. Baby na ki kular min da kan ki da amanar kan ki kar ki taba mantawa ina sonki."


Kasa nai da kai na hawaye na taruwa a ido na. Kai na ya dago yaga ido na taf da hawaye. Kai ya girgiza ya ce,

"Please Baby don't cry."


Ai kam kamar yace nai kuka na fashe masa da wani gigitacen kuka.

"Ya salam!"

Ya fada yana jawo ni jikin sa. Lallashina ya fara yana shafa bayana a hankali a hankali amman kamar kara min kaimi ake.


Lallai sai yau na san rabuwa da masoyi ba dadi. A da na sha rabuwa da Fu'ad wanda ko zaiyi tafi. Dan akwai lokacin da zai fara FUD nayi hawaye amman bai kai wannan ba. Na shiga damuwa amman bata kai wannan ba.


Har Momy sai da ta tausaya min ta ce,

"Kiyi hakuri daman sabo akewa kuka ko mutuwa akai ki daina kuka ai kuna tare da shi."


Sai dai nai shiru ni kadai nasan abinda nake ji. Ko da Yaa Fauwaz ya sauka ya kira ni nai masa ban gajiya.


*

Ya samu tarba daga Mamahn sa. Dan Shi kadai ne dan ta son duniya ta daura akan yaron nan nata haka nan Abban sa.


Sai da ya huta ya fito falo ya ci abincin da aka hada masa.

A ranar Mamahn sa taga pics din akan screem din waya ta. Kallon sa tayi ta ce,

"Wow 'ya ta ce akan wayar ka. Ah lallai kuna dasawa ko dai da wani abu a tsakanin kune."


Kai ya sosa ya ce,

"Mamah Fateema yarinya ce mai hankali da nutsuwa ga tarbiyya ga ilimi. Mamah ko wane namiji na kwarai zai so Fateema ba dan kyaun ta kawai ba sai dan dabi'un ta kuma nasan zai kwadayin ta koda yaran su. Mamah a gaskiya ina son Fateema."


Ya fada yana yin kasa da kai. Mamah ta ce,

"Kai Alhamdulilah Allah ya tabbatar da alheri ai haka ake so. Fateema kam yarinya ce ta gari wacce samun kamar ta za a sha wuya sai dai Allah ya baka ita zan fi kowa farin ciki."


Haka dai sukai ta hira ta da yabo na har Abbun sa ya zo shima aka zauna hirar da shi.


Tinda Yaa Fauwaz ya tafi sai kuma waya da chat kullum muna makale da juna.  Soyayyar mu sai gaba take. Sai dai na fada muku Yaa fauwaz akwai kishi to ta nan fa in ya tina da Fu'ad sai ya damu ya ce,

"Baby ni abinda bana so sharing dina da yake "


In ya fada haka sai dai nai murmushi kawai. In kuwa ya tina da hakan sai muyi kwana biyu yana dan fushi dani abinda yake damuna kenan.


Fu'ad kuwa rashin Yaa Fauwaz sosai yake samun time in zai zo guna dan da ina fargabar kar yazo ya samu Yaa Fauwaz duk suga kamar ina sane ne.


************************************************************************************************************************************

Tin daga ranar kullum sai Aisha taje gidan da Baba ya kwatanta mata anan yake aiki har aka kore shi.


Duk da in taje tana mamakin gini gidan dan bata taba ganin irin sa ba. Dan kyau yana da kyau ga gidan kato.


Kullum in taje sai tai ta sake saken yadda zata shiga gidan. Haka nan shima Aliyu kullum ya dawo yana ganin ta a kofar gidan tin bai lura da ita har ya fara lura da ita. Haka zai hau benen sa ya shiga barender yai ta kallon ta.


A ran sa ya ce,

"Me wannan yarinyar take zuwa yi to?"


Sai dai ya tabe baki ya daga kafada kawai yayi ciki. Amman yarinyar ta tsaya masa a rai.


Kullum ta zamar masa kamar TV da in ya dawo sai ya hau bene yai ta kallon ta har ta tafi.


Sosai al amarin yarinyar ke damun sa shi dai ba zai ce ga kamar ta ba dan baya kallon fuskar ta. Amman ta tsarin jiki tabbas ya yadda da cewa yarinya ce.


In bata zo ba duk sai ya shiga damuwa ya rasa dalili. Duk rashin son shiga sabgar mutane yau shi ke shiga damuwa akan rashin ganin yarinyar da shi bai san ta ba kuma bai san wacce ba.


Yakan ji haushin kan sa in ya tina akan me yake damuwa. Yau kamar kullum bayan ya baro gidan gwamnati ya karaso gida. Horn yayi mai gadi ya fito ya bude masa. Shiga yayi yai parking ya fito mai gadi na masa sannu da zuwa amman hannu kadai ya daga yai ciki.


Dakin sa ya shiga ya watsa ruwa ya fito. Ya sanya threequater wando na kakin sojoji. Sai riga fara mara nauyi. Barandar dakin ya shiga.

"Yau ma bata zo ba"

Ya fada a ran sa.

Har zai juya sai ya hango ta tare da Mai gadi suna magana. Yadda take magana duk da baji yake ba sai ya ji ta burge shi.


Ido ya kura musu ko zai ji me ke faru amman ina ya kasa. kallon su kawai ya tsaya yi har ta gama bayanan ta mai gadi yai magana sannan ta daga hannu tana nuna masa cewa gobe ma zan dawo.

STORY CONTINUES BELOW

Ta juya ta diba a guje tayi can. Wata ajiyar zuciya Aliyu ya sauke yana mai sakin murmushi a ransa yace,

"Zan so naji me suke fadi."


Haka ya koma daki cike da nishadi wanda bai san ko na menene ba.

*

Washe gari ma yana dawowa ya shige ciki ko wankan bai ba dan yana son yaje yaga ko ta zo. Yana hawa yaga karasowa ta.


Mai gadi ne ya mike ya karasa gun ta. Ta ce,

"Baba ina yini?"


"Lafiya lou! Yau ma daga makarantar baki koma gida ba ko?"

kai ta gyada sannan ta ce,

"Ai kasan na fada maka yau ma zan zo."


Aliyu dake sama kawai sai ji yayi yana son jin me suke fadi. Cikin azama ya sakko ya nufi bakin gate.


Daga dan baya ya tsaya yadda baza su ganshi ba. Muryar ta mai dadi da zaki ta doki kunnen sa ta ce,

"Baba na fada maka gun mai gidan nazo."


Mai gadin ya ce,

"To ai bai ce min zai yi bakuwa ba."


Ido ta zaro ta ce,

"Haba dai Ai ni ba bakuwa bace yasan ni ni yar uwar sa ce."


Dariya Mai gadin yayi ya ce,

"Ke din?"


Kallon sa tayi ta ce,

"Oh baka yadda ba ko?. To kira shi ka tambaye shi."


"A'ah ba sai anyi haka ba. Yanzu Yallabai ya dawo kiyi hakuri. Zan sanar masa ko gobe sai ki dawo kinji."


Kallon sa tayi ta ce,

"Ba damuwa. Ka sanar masa sai gobe."


Ta fada tana daga masa hannu. Shima dariya mai gadin yayi ya daga mata hannu.

Aliyu dake tsaye bai san sanda ya saki murmushi ba. Yana tsaye mai gadi ya shigo yana ganin sa ya zube yace,

"Ranka ya dade lafiya dai ko?"


Bai amsa ba sai cewa yayi

"Kabar ta gobe in tazo."


"Insha Allahu ranka ya dade."

Yai ciki ba tare da ya kara sauraran sa ba.

Shi kadai a ciki ya dinga jin kamar muryar yarinyar na masa magana. Sanyin ta da sakin ta da sautin duk sun tsaya masa a kai.


Ido ya rufe dan ya tino da surar ta amman ina ai ba kallon ta yai ba dan kusan ta juya masa baya ma.

Murmushi yayi ya mike ya shiga bayi ya sakarwa kan sa ruwa sai da ya fito ya kimtsa jin ana kiran sallah yasa ya nufi massalaci.


Sai bayan isha'i ta koma gidan. Zama yai yana shan fura yana kallon news har karfe tara sannan ya mike ya je yai wanka ya hau kan gadon sa.


Amman abin mamaki duk yai addu'oin sa amman sai ya kasa bacci yaji muryar yarinyar na ratsa dukkan jikin sa da zuciyar sa.

Ya jima tunanin yarinyar sannan bacci barawo ya dauke shi. Wanda har da mafarkan yarinyar wai tazo gun sa.


Zai iya cewa baya mafarki in ma yayi sai akan aiki in ya sa abu a gaba. To ana ne zaka ga ya yi mafarki.


Amman wai yau shine ke mafarkin wata yarinya. Wanka ya mike yayi ya dauro alwala dan har hudu ta gota. Sallah yayi ya jima kan sallaya har sai da yaji an kira sallah a massalaci sannan ya mike ya fita.


Sallah yayi dan sai karfe bakwai ya shiga gida. Dakin da kayan training nasa suke ya shiga ya dade har karfe tara sanna ya fito yai wanka.

Black tea kawai ya sha ya kimtsa cikin kakin sa wanda ya fito da shi ras. Take kwarjinin sa ya bayyana.


Wanka da turarukan sa yayi sannan ya mike ya fita bayan ya jima yana addu'a a kofar da zata sada shi da compound din gidan.


Yana fita mai gadi ya fara gaida shi sannan ya bude masa gate. Mota kawai ya shiga ya ja ta.


STORY CONTINUES BELOW

*

Aisha na komawa gida ta kosa taga gobe tayi. Ta rasa menene dalili amman tabbas dole ta hadu da wannan gwamnan ko dan ta fada masa gaskiya.

Dan haka Allah Allah take a tashi daga boko ta tafi isilamiyya. Duk da tasan dai ba dole ne ya barta ta shiga b

ba kullum haka yake yawan fada mata.


Haka tana dawowa ta shiga tai wanka. Ummah dai kallon ta take dan taga ko abinci bata kalla ba. Tana fitowa ta shige daki ta saka uniform din isilamiyya Ash kala.

Fitowa tayi rike da jaka. Kallon ta Ummah tayi ta ce,

"Wai saurin me kike haka. Kin dawo ko abinci baki ci ba."


Tsayawa tayi ta kalli Ummah ta ce,

"Wallahi wai yau Malam shehu ne yace muje da wuri saboda akwai haddar da zamu bashi."


Kallon ta Ummah tayi. Aisha tai saurin dukar da kai dan kar Ummah ta gane karya take. Ummah ta ce,

"Ai dai ke ci abinci tinda in kika tafi sai yamma gab da magariba zaki dawo fa."


Zama tayi ba dan taso ba haka ta dinga cin abincin. Tana gamawa ta mike. Ummah ta kalla ta ce,

"Ummah na tafi."


"To Yar gidan Yayan ta. Allah bada sa'a."

"Ameen!"


Ta fita. Kallon garin tayi lokacin baifi karfe biyu ba bayan sai biyu da rabi zuwa uku ake shiga.


Makarantar ta nufa ba kowa dan haka ta dau tsintsiya ta dinga share dukka makarantar sai da ta gama ta zauna ta fara muraja'a. Ta jima sannan aka fara taruwa.


Hauwa'u, yar abokin Baba makobtan su ta ce,

"Ai na biya miki Ummah ta ce kin taho."


"Wallahi yau aikin ladan nake so."

Murmushi tayi ta zauna suka fara muraja'a.


Haka tai ta Allah Allah a tashi. Har akai sallah la'asar sai gani tai kamar lokacin ma baya tafiya.


Karfe biyar da rabi ake tashi dan haka, ana tashi ta zillewa Hauwa'u kamar yadda take mata kwanan nan.


Gidan ta dosa tana Allah Yasa Mai gadi ya bar ta. Aliyu ma a gun aiki shima Duk ya kagu biyar tayi ya taho gida.


Biyar da minti arba'in da biyar ya karaso kafar gidan sa. A hankali yake driving amman sa . idon sa akan hanyar dabtake amman bai hange ta ba.


Ciki yayi yana fitowa kenan tana karasowa bakin gate din. Tsayawa kallon ta yayi. Kamar yadda ta saba haka ta rissina ta gaida Mai gadi cikin ladabi da biyayya.


Amsawa yayi cikin sakin fuska yana fadin

"sannu da zuwa ranki ya dade."


Murmushi tayi wanda ya kara fito da kyan ta. ta ce,

"Zan iya shiga."


Kai ya daga mata ya ce,

"Eh!"


Kallon sa ta tsaya yi duk yadda take son shiga kuma sai taji ta kasa. Kallon ta yayi ya ce,

"Ki shiga mana."


Kai ta daga ta kalli gidan sannan tai addu'a ta shiga. Duk abinda ake Aliyu na ganin ta.


Ita kam bata lura da shi ba. Cikin tafiyar ta a hankali ta fara tafiya site din masu aikin sa yaga ta nufa wannan yasa yai saurin yin inda take.


Kamo hannun ta yayi yayo kofar falon gidan da ita. cikin tsoro da firgici ta ce,

"Malam menene?"


Dariya taso ta bashi amman ya danne ya ce,

"Ina zaki?"


"Waye kai da zakai min wannan tambayar?"

Ta fada cikin isa.


Kallon ta yayi ta ce,

"Malam gun gwamna nazo a ina zan same shi."


Kallon ta ya tsaya yi ta ce,

"Wai baka ji nane."


"Ya Salam!"

Ya ambata dan a duniya zai ce bai taba tsurawa wata mace ido kamar yadda ya tsurawa Aisha ido ba.

Ko Hajara matar sa bazai ce ga kammanin ta ba. Kallon ta ya cigaba dayi.

Yarinya ce wacce bata fi shekara goma sha biyu zuwa uku ba. Tana da tsayi madai dai ci. Fara ce irin farin buzaye yan nijar.


Jikin ta a murke yake tana da diri mai kyau. Idanun ta manya ne, wanda bakin ciki yake bakikirin sai sheki yake haka idon ta kamar kwalla ta taru sai kwalli idon kayi.


Gashin girar ta gazar gazar a kwance kamar ta yanke ta tsara shi. Haka nan bakin ta dan karami pink kala. Gashin idon ta a cike suke gazar gazar dasu wanda suka karawa idon kyau.


Hannu ta tafa a dai dai idon sa wannan yasa ya dawo daga duniyar tunanin da kallon suffar ta da yake. Kasa yai da kai.

Kasa yai da kai ya ce,

"Wajen wa kika zo na tambaye ki?"+


Kai ta daga tana kallon gidan. Gidan ba laifi yai kyau ta fada a ranta.

Kallon ta yayi ya ce,

"Gidan ya miki ne?"


Kai ta gyada ta ce,

"Ba laifi duk da yau na soma shiga irin wadan nan gidan amman yai kyau. Wai meyasa masu kudi basa tsorin Allah. Ji gidan nan ka shiga cikin gari kaga inda wasu suke kwana."


Kallon ta ya tsaya yi ta ce,

"Wai kai lafiya?"


Murmushi yayi ya ce,

"Nima ina kallon gidan ne, kuma ina nazarin maganar da kike fadi."


Murmushi tayi ta ce,

"Wai meyasa kullum in nai magana sai mutane suna mamaki wasu kamar yadda kace kana nazarin magana ta haka suke fada. Akwai wani abu da na fada sabo a cikin magana ta ne."


Ajiyar zuciya ya sauke dan sautin maganar ta kadai na taba masa zuciyar sa. ya ce,

"Wasu mutunen suna da kaifin basira ta yadda har hakan yake girmewa shekarun su da wayon su to gare kin ma ina jin hakan ne duk da ban san shekarun ki ba."


Dariya tayi ta ce,

"Haka Yaa Muhammad yake yawan fada. Wai tunani na da hankali na yafi shekaru na. Ashe da gaske yake"


Kai ya gyada mata kawai ta ce,

"An ce min nan gidan gwamna ne?"


Kai ya gyada mata shima ta ce,

"Yana nan yanzu?"


Shiru yayi. Tsoron sanar mata yake ainihin gwamnan da bai san dame tazo ba. Ba wai cutarwa ba. Kai ya girgiza mata. Kallon sa ta yi da idanun ta masu birkita duk wani da namiji da ta kalla. Ta ce,

"Wai kai meyasa baka magana daga eh sai A'ah ko ka gyada kai. Ni ban so in baza kai min magana ba ka barni naje inda zani."


Mamaki ne ya kama shi dan zai ce tinda yake bai taba haduwa da namiji ko mace da ya kure shi da ido kuma yai mai magana ba shayin komai a ran sa ba.


Duk da ita ma da ta kalli idon sa taso ta firgita amman haka ta dake kasancewa Aisha akwai rashin tsoro.


"Gaskiya ne nan gidan gwamna ne sai dai ni ke zama a cikin sa yana zuwa amman ba kullum ba me zai miki da kike neman sa."


Wani kallo ta watsa masa ta ce,

"Ina ruwan ka da jin abinda zai min?"


Kai ya girgiza mata ta ce,

"To ya za ai na ganshi."


Murmushi yayi ya ce,

"Ganin gwamna ba abu ne mai sauki ba. Dan sai kin bi ta gun mutane da yawa har sai kinyi rubuta wasi'ka."


STORY CONTINUES BELOW

Ido ta zaro ta ce,

"Ganin san kawai?"


Kai ya gyada mata. ta ce,

"Ikon Allah yanzu mutum yana shugaban talakawa da masu ilimi da marasa ilimi amman har sai anyi wani rubutu yo in wanda yake son ganin sa bai iya ba fa ko kuma Wani abun fa shikenan kana son ganin shugaban ka ba hali."


Hannu ya harde a kirji ya zuba mata ido. Ya ce,

"Kinsan shugaba kuwa kowa zai iya kawo masa hari ko kisa ko cutar wa "


Wata yar dariya tayi ta ce,

"Ni kuwa nasan shugaba tinda nasan yadda Manzon Allah (SAW) ya gudanar da mulkin nasa. Shi in za a ganshi sai anyi duk wadan nan abubuwan ai da shi zamuyi koyi bada dabi'un wasu ba."


Kai ya jinjina ya ce,

"Eh haka ne."


Ta ce,

"To ni yanzu ban da halin ganin sa kenan.?"


"Kinga yanzu yamma tayi, gashi daga makaranta kike, Kije gida amman gobe kinga asabar ko da safe ne kizo ma san yadda zamuyi."

kallon sa tayi ta ce,

"Dan Allah zaka hadani da shi."


Kai ya gyada mata ya ce,

"Insha Allahu amman fada min me kike son fada masa."


Wani kallo tai masa ta ce,

"Ka bari in na fada masa in yaga zai iya sai ya fada maka."


Ta fara tafiya. Kallo ya bita da shi ya ce,

"Ba sallama!"


Juyowa tayi ta ce,

"Wai kai menene halakar ka da gwamna?"


"Dan uwa nane."

"Ok!"


Ta fada ta juya tana kara tafiya. Bin bayan ta yayi ya ce,

"Bakya son rakiya ta ne!"


Murmushi tayi ta ce,

"Zaka rakani gida."


Kai ya gyada mata.  Baki ta dan tabe ta ce,

"Muje!"


Yabi bayan ta. Mai gadi na ganin su ya karaso yana fadin

"Ranka ya dade barka da fitowa."


Hannu kadai ya daga masa. Kallon mai gadi tayi ta ce,

"Shi fa wannan haka yake kamar mai ciwon baki bai son magana "


Ido mai gadi ya zaro ya dan saci kallon Aliyu da ya dan saki murmushi har tai gaba sai ta juyo ta ce,

"Ka fada masa kar ya kara hanani zuwa cikin gidan nan."


Kai ya gyada mata. Ta kalle shi ta ce,

"Kai fada masa man."


Kallon mai gadi yayi wanda duk ya tsure ya ce,

"Kaji abinda ta fada ko?"


Da sauri ya gyada kai ya ce,

"Naji ranka ya dade ayi hakuri."


Suka fita tana fadin,

"To Baba sai gobe."


Kasa magana yayi har Aliyu ya bi bayan ta. Mamaki cike da bakin Mai gadi ya ce,

"To mene hadin sa da ita ko dai da gaske yar uwar sa ce."


Wajen zaman sa ya koma da tunani kala kala.  Sai da ya rakata har kan layin su  sannan ya tsaya ya ce,

"Ni zan koma sai goben."


"To nagode."

Ta fada tana falfalawa a guje. Kallo ya bita da shi yana murmushi.

A Haka ya koma yana tafiya a hankali yana jin dadin weather garin iskar yamma na busa shi. Kamar bai son tafiya haka yake tafiya kan ya karasa gida har an kira sallah magariba wannan yasa ya shige massalaci. Bai fito ba sai bayan sallah isha'i.


Gida ya nufa yai wanka ya dawo falo firij ya bude ya dauko fruit apple da banna da paw paw da aka yayanka masa.


Zama yayi ya fara kiran iyayen sa suka gaisa sannan ya kira Mamah nan ta bashi Maryama da ta cika shi da sururun ta.


Suna gama waya ya kunna TV dan kallon news amman abin mamaki duk ya kasa sai tunanin Aisha da muryar ta da suka dabaibaye masa zuciya da jikin sa.


Haka ya je yai wanka yai alwala ya kwanta amman abin mamaki sai gashi sai juyi yake ya kasa baccin. Ta shi yayi ya dauro alwala ya hau kan sallaya ya jima yana sallah sannan ya fara karatun alkur'ani sai wajen biyu ya kwanta amman karfe hudu a idon sa ya mike.


Yadda ya saba gudanar da komai haka ya gudanar har akai kiran sallah ya fita massalaci sai dai a ransa wannan yarinyar da bai san ta ba bai san sunan ta ba duk ta na cikin ran sa.


To mene hakan me hakan ke nufi ko dan dai yana son yaji mai zata fada masa ne.


Meyasa bai ce mata shine Gwamna ba. Wata zuciyar ta ce,

"Dan kana fargabar abinda zata fada dan wannan yarinyar ban san me tazo gare ni da shi ba."


Can ya ce,

"Amman me yasa ta tsaya a rai na."


Dan yadda take abubuwan ta da yadda take sani nishadi da dariya. Jarumtar ta da rashin tsoron ta na burge shi.


Daman a cikin mutane akwai wanda zai iya sa shi nishadi a da ya zata zama waje daya kadai yafi koma sa nishadi sai gashi haduwar sa da wannan yarinyar a jiya yaji ya fi jin nishadi fiye da duk yadda ya saba in ya kadaice.


Wani abu in ya tina yai murmushi wani ya girgiza kai, haka dai shi kadai.

In ya tuna yadda take tsare shi da idanun ta masu kyau sai ya lumshe ido yai murmushi ba tare da yasan yayi ba ma.


Zai ce in ba kanwar sa Maryam ba da take da surutu ba wacce ta taba tsare shi da surutu har ya biye mata bai gaji ba kuma bai ji haushi ba.


Haka ya gama tunani duk abinda zai yarinyar na ran sa ya rasa meyasa.

Sai da yai wanka ya zauna yana jiran zuwan ta karfe goma zai fita amman shine har karfe daya yana gida bai da shirin fita duk da yana da bakin da zaiyi yau amman bai da niyar fita.


Haka ya zauna a gida da tunani ya mike ya leka ko zai ga tazo amman ina komai kamar ta babu.


Da ya shirya zai fita sai da ya tambayi mai gadi ba wanda yazo neman sa.


Mai gadi ya ce,

"Babu ranka ya dade."


Ya fita acan ma duk hankalin sa na gida. haka ya gama abinda zai yi a gaugautai ya fita karfe hudu sai gashi a gidan sa.


Amman ba Aisha ba alamun ta. Mai gadi ya kira ya ce,

"Ba wanda yazo neman na?"


Mai gadi cikin ladabi da tsoro ya ce,

"Babu ranka ya dade ai ba mai zuwa neman ka."


Ya ce,

"Ok jeka."


Har ya tafi ya ce,

"Bai ga ko wani a kofar gida ba."


Nan ma ya ce,

"Ban gani ba ranka ya dade."


Haka ya shiga gida dan samun hutu amman duk ya kasa samu yau bai jin dadin zaman kadai cin Aisha kawai yake buri tazo ta sa shi nishadi da surutan ta.


Sai ya tina yadda take bashi umarni a ransa ya ce,

"Wannan yarinyar duk yadda akai tana da jini da sarauta."


Ido ya lumshe idanun ta ya gani yai saurin bude ido.

"Wai menene haka?"


Ya tambayi kansa dan shi ya kasa sukuni duk tunanin yarinyar ya dame shi abinda ko sunan yarinyar bai sani ba."


Haka ya yini daga ya leka barander ko zai hange ta sai ya koma falo ya kwanta ko abinci ya kasa ci duk da shi ba ma'abocin cin abinci bane in ba a gida yake ba.


Lokaci daya ya ji damuwa abinda in ba takura masa akai ko hayaniya ya shiga ko wani abu bai fiya jin haka ba.


Tin da yake bai taba shiga damuwa akan wata 'ya mace ba. To me hakan ke nufi.


*Ku bashi amsa readers. ni dai na ce.........  a'ah sai naji daga bakin ku tukkunna.*


*Ina son ganin comment da yawa*

Don't forget to vote

Godiya mai tarin yawa ga masoya littafai na hakika ina godiya da yadda kuke bibiyar labarin nan.


Muje zuwa.


Post a Comment for "WA NAKE SO CHAPTER 3"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...