WA NAKE SO CHAPTER 11 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WA NAKE SO CHAPTER 11

WA NAKE SO CHAPTER 11

- - Post a Comment

 WA NAKE SO CHAPTER 11


Ganin yayi shiru kuma bata daina kallon sa ba yasa ya daura hannun sa a kaffadar ta ya dan girgiza ta a firgice ta dago tana kallon sa cikin tsoro.

"Me me... Kace Yaa AK?"+


Ta tambaya muryar ta na rawa daga gani a firgice take sosai. Hannun ta ya kama yana murzawa a hankali. Idon sa ya sa a cikin idon ta. Sannan yace

"Aysher! Ki dawo cikin nutsuwar ki,  ki saurare ni kiji."


Kai ta girgiza kawai hannun ta rike da nashi yace

"Aysher i love u. I really love u Aysher please don't say no!"

Kai ta hau girgizawa tana cire hannun ta daga nashi sannan ta saka a cikin kunnen ta tana karkada su alamar kamar a toshe yake. Sannan ta dago tana kallon sa da manyan idonun ta. Sai yaji ba zai iya jurar kallon idanun nata ba.

Kallon sa take babu ko kiftawa. Menene aibun Ya AK babu a yadda ta sanshi babu sam. Mutum ne mai saukin hali da hakuri ba ruwan sa. Yanzu duk yabo da koda wacce yake so ashe ita ce. Zuciyar ta ce ke bugawa da karfi da karfi wanda bata san ko na menene ba.


Tasha fada masa wacce yake son sa bazata ki shi ba sai da wani dalili shin ita me zata ce masa. Kallon sa ta cigaba dayi ko kiftawa batayi.


Ganin irin kallon da take masa sai yaji jikin sa yai sanyi. Zuciyar sa in banda bugawa shima ba abinda take. Hawaye ne ya fara fitowa a idon ta da sauri ya matsa gaba ta yana fadin

"Kiyi Hakuri Aysher in abinda na fada ya bata miki rai amman ban fada da wata manufa fa dan Allah ki daina kukan nan dan Allah na rokeki. Ba zan taba yafewa kai na ba in har zan saka ki kuka dan Allah ki daina kuka."


A zahirin gaskiya bata san kukan me take ba amman ni nafi zaton tana kukan wani abun ne dai. Handkerchief πŸ’ ya zaro a aljihun sa ya mika mata. Bata amsa ba wannan yasa ya fara goge mata da kan sa. Ganin yana gogewa wani na zubowa ne ya durkusa a gaban ta ya tallafe kumatun sa.

"Ki fadan me yasa ki kuka dan na gyara barakar da nayi dan Allah."


Mikewa tayi ta juya zata shiga gida da sauri ya mike ya kamo hannun ta. Juyowa tayi suna hada ido tai saurin yin kasa da kanta. Sakin ta yayi yace

"Ya zaki tafi ki barni cikin zulumi Aysher ai ko so nane bakya yi kya fadan ba ki tafi ki barni ba kika san halin da zan shiga in kika tafi kika barni baki fadan abinda ke cikin zuciya ki game dani ba."


"Yaa AK ka daina zaton wani abu negative a tattare dani. Na fada maka ba wata 'ya mace da zata kika sai da dalili to nima a gaskiya...."

Sai kuka ya kwace mata dan haka da gudu ta bar wajen tai cikin gida.


Da kallo ya bita sai kuma ya koma kan dakalin ya zauna yana zuba tagumi. Hakikanin gaskiya kan sa ya daure ya dau zafi. Zuciyar sa kuwa in banda bugawa ba abinda take.

"Hasbunallahu wani'imal wakil!"

Yake ta nanatawa a cikin zuciyar sa a hankali yaji ya samu nutsuwa jin ana kiran sallah yasa ya mike ya isa tap din dake harabar masallaci. Alwala yayi sannan ya nufi cikin masallacin ya hau jam'i aka tada sallah.*

Umma dake tsakar gida zaune taga Aisha ta shigo a guje tayi daki tana kuka. Ido ta zaro sai kuma ta mike tabi bayan ta da sauri. Akan katifar ta ta same ta tana kuka kamar ranta zai fita.

STORY CONTINUES BELOW

Zama Umma tayi ta dago ta tana kallon yadda take kukan bil hakki da gaskiya kukan take tana sauke ajiyar zuciya. Janyo ta tayi ta rumgume ta a hankali tana bubbuga bayan ta tana fadin

"Ki na fadin La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalimin. Sannan kina fadin Hasbunallahu wani'imal wakil!"


Haka Umma ta dinga nanatawa itama a hankali ta amsa tana fada take taji ta samu rangwami akan abunda take ji dan haka a hankali kukan ya tsaya sai ajiyar zuciya da take saukewa.


Jin ana kiran sallah yasa Umma tace

"Tashi kije kiyi alwala kizo kiyi sallah!"

Jiki a mace ta mike ta fita. Umma ta bita da kallon tausayi duk da bata san me yake damun ta ba amman daga yadda take wannan kukan babban abu ne dan Aisha bata taba irin wannan kukan ba.


Mikewa itama tayi ta fita ta dauro alwala sannan ta dawo ta tada sallah. Aisha ma daki ta koma ta tada sallah. Tana idar wa ta hade kai da gwiwa tana cigaba da sauke ajiyar zuciya.

Zuciyar ta ba wanda take kawo mata sai Yaa Muhammad ina ba zata iya amsar soyayyar Yaa AK ba saboda Yaa Muhammad shii ya fara fada mata yana son ta kuma ya cancanci ta soshi. Dole Yaa AK yayi hakuri ba zata iya ba. Amman kuma in tace Yaa AK yayi hakuri shikenan sun daina waya da zumunci abinda bata so kenan bata son ta daina ganin sa.

Sai ta tuna halin da take shiga in yai tafiya kai bama tafiya ba just kwana daya in basu hadu ba ji take kamar sun shekara basu hadu ba.

"Ya Allah!"


Ta fada tana dafe kan ta da yake sara mata saboda yadda tai kukan dan har a lokacin ma hawaye ne ke fitowa daga idanun ta.


Sallamar Umma ta ji dan haka da sauri ta hau goge hawayen nata tana amsa mata. Shigowa tayi ta zauna a gefen katifar ta sannan ta kura mata ido.

"Aisha!"


Umma ta kira sunan ta kasa dagowa tayi ta kalle ta sai dai amsawa da tayi tace

"Na'am!"


"A baya na tambaye ki damuwar ki amman sai kika ce baki da wata damuwa. Sai daga baya kika fada min wanda abin ya tsaya min a rai kullum dashi nake kwana nake tashi Aisha. Ina lura da canji daga gareki da yawa."

Sai tayi shiru. Can tace

"Ki fada min me yake faruwa kukan me kike yi?"


Shiru Aisha tayi. Umma tace

"Ni ban san meyasa kike boyen abubuwan da ya shafe ki ba amman ban sani ba ko dan bani na haife ki ba. Amman Aisha wallahi duk cikin yaran nan na gidan nan ba wanda nake so da kauna kamar ki. Ke macece dole a so ki kuma a saka miki ido akan duk abinda kike ciki. Dole na shiga tashin hankali dan ban taba ganin ki kina kuka irin haka ba in har kina so hankali na ya kwanta ki daure ki fada min me yake faruwa?"


Shiru tayi sai kuma ta dago tana kallom Umma a hankali ta hau bata labarin Yaa AK da yadda yake koya mata karatu ta boye mata dai  a inda suka hadu. Amman daga nan ba abinda ta boye mata na alakar su da abun da yazo mata dashi a yau.


"To ke menene na kukan? Ko bakya son sa ne?"

"Umma Yaa Muhammad kuma ma ni bana son sa."


Kallom ta Umma take tana mamakin ina wayon Aisha ya tafi. Lallai in abu yazo kan ka wani wayo baka da dabara taka guduwa ma suke yi.

Amman Yadda Umma ta fuskanta Aisha tafi so Yaa AK akan Yaa Muhammad domin a yadda ta fada mata bata boye komai da feeling din da take ji akan sa ba. Tana masa boyayyen so ne da bata san tana masa ba. Zuciyar ta ya kama. son sa ya gama shiga dukkan jikin ta da zuciyar ya wanda ya canja ya koma Kauna.


Ba zata ce bata son Yaa Muhammad ba amman tafi kawo shakuwa su ke dawainiyya da Aisha akan relation din su. Dan haka dole a sannu ta ganar da Aisha kome take ciki dan da matsala in har ta auri Yaa Muhammad dan tasan soyayyar Yaa AK shine a ranta fiye da nashi in kuwa haka ne to akwai matsala dan an cutar da ita an dangarar da ita.

Kamar yadda Abba yake fada ne bazai wa Aisha auren dole ba dan haka a bar ta ta auri wacce take so. Kuma auren wanda kake so shine samun kwanciyyar hankalin ko ma wanene.


STORY CONTINUES BELOW

Aisha ki tsaya ki nutsu ki zabi *Wanda kike so* aure zaki yi bana son kiyi aure kuma daga baya ki gane wani abu daga baya. Muhammad da nane amman in har kika samu wanda kika fi so fiye da Muhammad ba zan miki dole ba. Domin auren *wanda kike so* shi zai baki kwanciyyar hankali da nutsuwa. Dan haka Aisha ki tsaya ki nutsu ki duba kiga soyayyar wa ke cikin zuciyar ki."


Kai ta girgiza tace

"Umma ni Yaa Muhammad nake ao. Tayaya zan so wani bayan shi."


"Aisha kenan ki tsaya ki nutsu Kibi komai a hankali sannan kiyi istihara ki gane *Wa kike s?* amman da farko yanzu da kike cewa bakya son shi wannan din kin shirya rabuwa dashi. Kinsan ba zai yiyu kina da aure kina mu'amala da wanda ba muharamin ki ba ko? Kuma ko shi Yayan naki ba zai yadda ba. Kin fada in baki ganshi ba halin da kike shiga shin kina shiga makamancin haka akan Yayan naki? A yanzu shakuwar ku da Wannan har tana son tafi taki da Yayan naki domin shi lokacin da kuka shaku tin kuna yara ne shi kuma wannan da giman ki kuka shaku dashi? Aisha ba zamuyi miki dole ba kuma ki cire tunanin Yayan ku a dan mune ba wanda zamuyi wa dole a cikin ku. Muna son ku samu farin ciki da zabin ranku ne dan haka a wanda zamu ce dole sai ya auri dan uwan sa in yace baya so. Meyasa kike jin abubuwan da yawa akan Yaa AK din bayan a baya akan Yayan ki kike jin sa? Wadan nan tambayoyin ki zauna kiyiwa zuciyar ki kuma ki fada masa halin da kike ciki in da hali ki bashi dama anan zaki gane *wa kike so?* kinga har an fara kiran sallah isha'i ki mika komai ga Allah. Insha Allahu Allah zai iya miki."


Kan Aisha a 'kasa ta kasa dagowa ta kalli Umma ma. Mikewa Umma tayi tace

"Bari naje nayi sallah!"


Sannan ta fice. Itama mikewa tayi ta tada sallar tana idar wa ta haye kalifar ta ta kwanta.

"Me maganganun Umma ke nuni akai ne? Umma na son tace ina son Yaa AK ne kome?"


Maganganun Umma ne suka dinga mata yawo aka amman ba wanda yafi tsaya mata sai wanda tace

"Kinsan bai zai yiyu kina da aure kina mu'amala da wanda ba muharamin ki ba ko? Kuma ko shi Yayan naki ba zai yadda ba. Kin fada min in baki ganshi ba halin da kike shiga shin kina shiga makamancin haka akan Yayan naki? Meyasa kike jin abubuwan da yawa akan Yaa AK din bayan a baya akan Yayan ki kike jin sa? "


Tuna wadan nan statement din na Umma yasa taji jikin ta yai sanyi. Tabbas haka ne

"In har ta auri Yaa Muhammad duk wata mu'amala ta tsaya tsakanin ta da Yaa AK shin zata iya hakan kuwa?"


Ido ta runtse tana mamakin yaushe har hakan ya zame mata jiki. Yaushe Yaa AK ya zama haka a rayuwar ta.

"Kwana daya in banga ka ba sai in shiga wani hali ina ga ina gidan miji na shin haka zan tai masa kunci ina tunanin wanin sa."


Juyi tayi akan katifa tana mai kara tuna kalmar Umma da take cewa

"Meyasa kike jin abubuwan da yawa akan Yaa AK din bayan a baya akan Yayan ki kike jin sa? "


Tabbas haka ne a baya in Yaa Muhammad ya tafi ta dinga kuka kenan da shiga mawuyacin hali wanda a yanzu bata fiya wani damuwa ko kuka da shiga wani haki ba. Sai in Yaa AK yai tafiya. Uhmm ai bama tafiya ba kwana daya aiki ya rike shi bai zo ba na ta damuwa da rasa nutsuwa takenan. Bayan nan ba wanda nake son gani kamar sa. Muryar sa na kwantar mara da hankali kalaman sa na sanyaya mata rai. A da fa duk Yaa Muhamamd take ji wa haka.


"Innalillahi wainna illahir rajiun! Allahu sahala illa ma ja'atahu sala wa anta taja ala iza shita sahala."

Abinda ta fada kenan tana lumshe idon ta dan yadda taji abubuwa na son cabe mata.


Wayar ta ce ta hau kara wannan yasa ta bude idon ta a hankali ta janyo wayar. Yaa Muhammad ne ke kira dan haka a hankali ta daga tai masa sallama. Amsawa yayi yana fadin

"Me yake damun kanwata?"


"Ba komai!"

"Hmm Aisha kenan amman kinsa daga jin muryar ki ba dai dai kike ba ko?"


"Bacci na fara!"

"Bacci tin yanzu tara ma fa vatai ba."


"Eh anjima zan tashi nayi karatu ne"

"Ok sai da safe to."


"Allah bamu alheri."

Tana kashe wayar ta fashe da kuka. Ta jima tana kuka a kwance ta kasa ko da tashi ne.


Umma ce ta shigo dakin hannun ta dauke da plate na abincin ta.

"Aisha!


Ta kira sunan ta idon ta tai saurin gogewa ta mike zaune.

"Ga abincin ki nan kici."


Ta ajiye ta fita. Duk da tana jin yunwa amman sai taji a lokacin bata jin wata yunwa. Janyo abuncin tayi tai one spoon sai kuma ta ture shi.

Mikewa tayi ta fita da plate din ta maida kitchen sannan ta shiga bandaki tayi alwala ta fito.


Kayan bacci ta saka ta hau kan katifar ta ta rufa da abin rufar ta.


*

Ana idar da sallah ya zauna a wajen sam ya kasa tashi ya rasa me yake masa dadi. Haka ya zauna ya dinga tufka da warwara har aka kira sallah isha'i aka kara tada jam'i ya mike yai sallah. Bayan ya idar yai shafa'i da wuturi sannan ya zauna yana addu'a Allah kawo masa mafita. Ya jima a masallacin dan sai takwas da rabi ya fita.

A hankali ya dinga tafiya kamar bai son tafiyar har ya karasa gidan sa. Yana shiga mai gadi ya mike yana fadin

"Barka da dawowa!"


"Yauwah!"

Ya fada yana shigewa ciki. A falon sa ya zauna yana dafe kan sa sai kuma can ya mike ya bude firij ya dauki ruwa yana bude murfin ya koma ya zauna yana kafa ruwan a bakin sa vai dire ba sai da ya shanye ta tas sannan ya mike ya saka a dustbin ya wuce bene inda dakin sa yake.


Yana shiga ya cire kayan sa ya nufi bandaki. Wanka yayi da ruwan dumi ya fito ya shirya cikin kayan baccin sa ya feshe jikin sa da turare. Kan gado ya zauna yana tunanin shin me reaction din Aisha yake nufi. Bata son sa ko yaya?


Wayar sa dake kan side duruwa ya mika hannu ya dauko. Kallon screem din wayar ya tsaya yi can ya shiga call log ya fara dialing number ta.

Tana kwance taji wayar ta na kara. Gaban ta taji ya yanke ya fadi tasan ko ba a fada mata ba Yaa AK ne dan ba mai kiran ta daga Yaa Muhammad sai shi. Yaa Muhammad kuma sunyi waya tace masa bacci zatai.

Wayar ta janyo ta tsaya kallon screem din wayar sunan sa ne ke yawo a screem din wayar kasa dauka tayi ta zubawa sunan ido kamar ranar ta fara gano. Zuciyar ta ne ya hau buga da karfi da karfi.


Ido ta lumshe lokacin da kiran ya yanke. Yana yankewa aka kara kira da sauri ta bude idon ta ta dauki wayar amman ta kasa dannan receive hannun ta sai rawa yake.


Kiran ne ya kara yankewa. Ajiyar zuciya ta sauke bata gama samun nutsuwa ba text ya shigo wayar da sauri ta dauki wayar tana bude text din Yaa AK ne dai dan haka cikin hanzari ta bude

_Aysher please pick the call i just want hear your voice. Muryar ki kadai zata sanyaya min zuciya ta dan Allah ki dauka ko na samu nutsuwa._

Ajiya zuciya ta sauke. Wayar ce tai kara daukar kara dan haka ta dannan receive πŸ“ž ta kai kunnen ta hadi da fadin

"Assalamu alaikum!"


Wata ajiyar zuciya ya sauke take yaji ya dan samu relief. Jin bai amsa ba ta kara fadin

"Assalamu Alaikum!"


Ido ya bude yana amsa sallamar da

"Wa'alaikum salam!"

Sai kuma sukai shiru.

Ajiya zuciya ta sauke. Wayar ce ta kara daukar kara dan haka ta dannan receive πŸ“ž ta kai kunnen ta hadi da fadin
"Assalamu alaikum!"+

Wata ajiyar zuciya ya sauke take yaji ya dan samu relief. Jin bai amsa ba ta kara fadin
"Assalamu Alaikum!"

Ido ya bude yana amsa sallamar da
"Wa'alaikum salam!"
Sai kuma sukai shiru. Shi yai karfin halin cewa
"Aysher are u there?"

"Uhmm!"
Kawai tace. Sai suka kara shiru yace
"Aysher bakya so na ko?"

Shiru tayi yace
"Please ki fadan me ke cikin zuciyar ki. Am Pleading πŸ™ talk to me and say what is in your mind please πŸ™ Aysher! Ba dole zan miki ki soni ba amman kiji tausayi na. Sonki ya gama shiga dukkan sassan jiki na ban da muradi da abin bege in ba son ki ba. Kullum fata na da tunani na kece ina son ki Aysher. Ban san lokacin da kika zaman jinin jiki na ba bugawar zuciya ta a ko da yaushe dake nake yin ta. Ban taba son wani abu a duniya kamar ki ba. Aysher ki fadan me kike ji a zuciyar ki game dani?"

Shiri tayi yace
"Tell me!"

"A ko da yaushe alheri nake ji akan ka Yaa AK. Abinda kazo min dashi ya girmi tunani na da hankali na. Na rasa samun mafita akan abun da kazo kin dashi Yaa AK. Zuciya ta ta kasa yanke min hukunci na rasa gane wane matsayi kake dashi a zuciya ta Yaa AK. Ba tin yau ba na fada maka kana da matsayi babba aguna wanda ban san irin sa ba."
Kuka ta saka tana fadin
"Na shiga rudani Umma ta sakan wani tunani da ban wanda ban taba yin sa ko kawo sa a rai na ba."

"Ki daina Kuka Aysher ban son jin kukan ki dan Allah ki daina kuka. Wanne tunani ne wannan Aysher?"
Ya tambaya a sanyaye dan kukan ta har cikin jikin sa yake jin sa.

"Uhmm!"
Sai kuma tayi shiru. Murmushi ya dan saki mai ciwo sannan yace
"Talk Aysher don't feel shy!"

"She remains me something i know but i forget it!"
"Me kenan!"

"My feeling,  my concern toward u!"
"As how?"

"Yaa AK kai shaida ne akan wasu abubuwa da yawa akan tsakanin mu. In kai tafiya ina shiga damuwa in rasa kwanciyyar hankali,  kwana daya in bangan ka ba ina rasa jin dadi all dis means what? I concern with u Yaa AK wanda is beyond As i says."
"What did you understand by it?"

"Abin da yake dauren kai kenan. Amsoshi da yawa suna zuwa kaina amman ni basu nake so su zo ba."
"Kamar Yaa?"

"Uhmm ban yadda da amsar da zuciya ta take bani akan me yasa nake jin komai akan ka ba. Na dauka saboda taimakon da kake min da shakuwar da mukai ne amman kuma....?"
Dan murmushi ya saki dan ya gama gane komai Aisha na son sa amman ta kasa yadda da abinda zuciyar ta take fada mata akan tana son sa din. Ba tin yau ba ya lura da hakan amman ita bata gane ba.

Sai yaji saukin abinda yake ji game da ita dan haka sai yace
"Amman kuma me?"

Ido ta runtse tayi shiru.
"Dan Allah ki saki ranki muyi magana ta fahimta barin kashi a ciki baya maganin yunwa dan haka say it out zaki samu relief akan abinda yake damun ki da ranki. Ni yanzu ai na fito da abinda yake rai na. Ruwan kine ki amshi soyayya ta ruwan ki ne ki wofantar amman ni nasan na samu wani sassauci a cikin zuciya ta fiye da da danake boye miki abu. So please ki fada min kinji My queen!"

STORY CONTINUES BELOW
"Yaa AK I think i love u!"
Wani murmushi ya saki mai kayatar wa sannan yace
"Did you think or you feel?"

"Uhmm koma dai yaya ne!"
"No you have to choose one. Think or Feel!"

"Suna da wani bambanci ne?"
"Yes of caurse you too know it ai. But let me remember you. Think kina tunani while Feel kina ji. Anan i rather want you to say u feel than u think. Kuma ke kike jin abun dan haka kinfi ma kowa sanin what u are in!"

Shiru tayi tace
"Shikenan is ok! Yanzu ya za'ai menene aibu na da kike son ki 'ki amsar soyayya ta uhm?"

"Yaa AK is not that."
"Uhmm to menene?"

"Yaa Muhammad i have a special feel on him. He loves me and me t....."
Sai kuma tayi shiru. Yace
"Ehemm and you too love him ko?"

"Uhmm!"
"To ki fada min mana!"
Shiru tayi yace
"Aysher!"

"Uhmm!"
Ta fada. Yace
"Ki min magana!"

Wayar ta kashe sannan ta fara  rubuta masa sako. Tana cikin rubutawa ya kira amman taki dauka yana katsewa ta cigaba da rubuta masa sannan ta tura masa.

Yana zaune rike da waya yana kara dailing sakon ya shigo sai da ta kara katsewa sannan ya bude sakon
_Yaa AK kamar yadda na fada maka ba macen da zata kika sai da dalili to nima ina da dalili. Yaa Muhammad shine dalili na ba zan iya cewa ban son sa ba. Ina son sa._

Idon sa ne yai jajir jin Aisha na fadin tana son wani. Dan haka ya maida mata reply yace
_Naji uzurin ki amman ki fada min kina so na?_

_Na fada maka i feel something akan ka da na rasa menene shi. I feel i can't do without u but yaudarar kai na nake. Dan bazan taba kin Yaa Muhammad. Kuma i can't leave with two men_
Ta tura masa hawaye na zubowa a idon ta. Sam bata san ta rubuta ba ma dan abun da ta fada masa duk daga kasan zuciyar ta suke. Zuciyar ta ce kawai ke umartar ta akan tayi hakan.

Yana ganin sakon ya mike tsaye. Ya yadda Aisha na son sa to akan me take son sadaukar da rayuwar ta da farin cikin ta akan Yaa Muhammad.
"Saboda yayan tane sun shaku kuma ya raine ta."
Zuciyar sa ta bashi amsa. Ido ya runtse yana fadin
"Ina ma nine Yaa Muhammad din nan."

Wayar ya fara dannawa yana tura mata sako yace
_Yanzu me kika yanke to?_

Tana ganin sakon taji gaban ta ya fadi. Ba zata iya fada masa bata son sa ba kuma ba zata iya cewa Yaa Muhammad haka ba dan haka sai ta kashe wayar gaba daya dan tasan da yaga no reply zai kira ita kuma bata san me zata ce ba.

Ai kuwa ganin a dau lokaci ya kara tura mata
_Am waiting!, _
Amman not reply dan haka ya hau kiran wayar sai dai aka ce masa a kashe take. Kara redailing yayi amman amsar dai daya ce a kashe bai san.lokacin da yai cilli da wayar ba. Ya zura hannun sa cikin sumar kan sa tana yamutsa ta.

Kan gadon ya koma ya kwanta a ringine ranar kwana yai bai runtsa ba. Aisha ma kwana tayi tunani ta kasa bacci karatun ma da ta dauko zatai sam ta kasa sai tunanin Yaa AK take da wasu moment din da suka wuce tin daga haduwar su har kawo yau.
A kan kunnen su akai assalatu.*
**
***
****
*****
******
Zaune nake a falo sanye da dogon wando fari sai vest itama fara kai na sanye da hula baka wacce keyar ya daga saboda kai na dake a tsefe na saka masa ribon. Fuska ta babu kwalliya ko kadan daga kwalli sai man lebe amman nayi kyau fatata tayi fresh da ita. Sai tashin kamshin turare nake wanda irin wanda Fu'ad ke sanyawa ne.
Research nake a system dina gefe na cup ne da lemon kwalli na 5Alive. Dagowa nayi na tsiyayya sannan na dan yi sipping na ajiye ina cigaba da dannan system din gaba na.

STORY CONTINUES BELOW
Waya ta ce ta dau kara wannan yasa na dago Hajiyar Fu'ad ce dan haka cikin sauri na danna receive πŸ“ž na kai kunne na nayi sallama cikin nutsuwa.
"Assalamu alaikum!"

"Wa'alikum salam!"
Cikin ladabi kamar tana gaba na nace
"Ina yini Hajiya?"

"Lafiya lou ya kuke yasu Momyn taki?"
"Suna lafiya!"

"Madallah daman cewa nayi kwana biyu bari na kira mu gaisa."
Kai na girgiza saboda tina irin soyayya da Hajiyar Fu'ad ke min nace
"Wallahi Hajiya aiki ne yai mun yawa amman insha Allah zan shigo wannan weekend!"

"Amman kwana dai zaki min ko?"
Ta fada daga can bangaren shiru na danyi sai kuma nace
"Insha Allahu!"

"To Allah yayi albarka a gaishe min da Momyn sai anjima."
"Nagode Hajiya!"

Na kashe wayar Momy da ta tafi daga kitchen na dago na kalle ta nace
"Momy Hajiyar Fu'ad ce tace na gaishe ki!"

"Ina amsawa. Gaskiya mutanen nan suna da mutunci wallahi. Sun riki zumunci."
Kai na dauke nace.
"Wallahi fa ita ta kira ni fa wai kwana biyu. Nace dis weekend zan samu na shiga shine take fadin wai kwana zan mata."

Momy tace
"To me kika ce! Ba tin yau ba take son kije ki kwanar mata Fateema matar nan na son ki dan haka ni dai in zaki dau shawara ta ki kwanan mata ko taji dadi yadda take son kin nan kinji."

"Toh Momy."
Zama Momy tayi tace
"Ana ta aikin ne?

"Wallahi wai yaushe Yasmeen zata dawo ne?"
"Tace sai hutu ya kare!

"Har nan da one week gaskiya ta dawo haka taje tana cinyewa Mami kayan dadi ko da yake Baba Uwani ita ke cinyewa ba kanwa ta ba."
Momy tace
"Kya dai ji dashi aga mai kwadayi a cikin si."

Murmushi Fateema tayi ta sipping din lemon gaban ta. Wayar ta ce tai kara ta dauka Dr Ahmad ne wanda yake aiki a asibitin ta. Ta dauke shi tamkar uba saboda aboki ne ga Dadyn ta ma.

"Assalamu Alaikum!"
Ta fada!
"Wa'alaikum salam! Fateema kina ina ne? Dan Allah ki taho asibiti an kawo wata na nakuda kuma ta jima tana yi har ta galabaita gashi ni kadai ne a asibitin dan Dr Ibrahim da Dr Hauwa suna wani aikin.  Dr Auwal kuma kinga baya nan. Please ki taho yanzu!

Kan ya gama magana ma har ta shiga daki doguwar riga kawai ta zura a kan kayan jikin ta ta dauko keyn mota ta fito da sauri.
Momy da taga ta Fateema ta fito a guguce tace
"Lafiya dai ko?"

"Lafiya lou! Momy wata aka kawo tana nakuda ance ta galabaita sosai ina jin aiki za ai mata bari dai naje Momy."
"Zaki iya driving kuwa?"

"Momy zan iya."
"To Allah kiyaye ya bada sa'a!"

Da gudu ta fita dakin kan ta karasa wajen mota tace
"Buden gate dan Allah."

Tana shiga ta fice a guje daga gidan. Tafiya take tana sharara gudu kamar zata tashi sama tazo kan kwana bata lura ba sai kawai ji tayi ta bugi wata mota. Bata tsaya dubawa ba tayi reverse ta dau hanya.

Da kallo yabi motar ta ta a zafafe ya bi bayan ta amman duk yadda yaso ya kamo ta tayi masa nisa sai dai yana iya hango ta a haka har ta karasa layin asibitin tin daga nesa take dannawa mai gadi horn kan tazo har ya bude tana zuwa ko parking batai na kirki ba ta fita a motar ko key bata cire ba tayi ciki da gudu.

Kan mai gadi ya rufe gate din motar dake bin tata ta karaso shiga yayi yai parking yana bin motar da yake bi da kallo ba kowa a ciki.
Fitowa yayi daga cikin motar sa. Wani dogon matashi ne da baxai wuce thirty two ba, yana sanye cikin kananun kaya idonsa sanye da bakar spec, dogo ne shi din sosai, sannan shi ba baki ba kuma baxa a sa shi a jerin farare ba. Hannun sa ya zura a cikin alhijun wandon sa sannan ya karasa wajen mai gadi. Sallama yai masa suka gaisa sannan yace
"Please me motar nan nake nema!"

"Hajiya Fateema gaskiya yanzu ta shigo kuma da dukkan alamu emergency aka kira ta sai dai ka jira bari a samu ai maka booking din ganin ta Allah yasa bata da wanda zata gani yau."
Kallon mai gadin ya tsaya yi can ya ce
"Ok!

Wajen da ake bokking ya isa ya fada musu me ke tafe da mutumin sannan ya tafi ya barsu. Mai bada booking din ya kalle shi yace
" bana jin yau zata ga kowa dan yau tace bama zata shigo ba gaskiya sai dai gobe dan daga gani emergency ne ya shigo da ita kuma da ta gama zata fice."

"Yanzu babu yadda za ai na samu ganin ta yau."
"Gaskiya kayi hakuri sai dai gobe."

"Alright gobe by which time?"
"2:30-3:00pm!"

"Alright nagode sai gobe!"
"Aha!"

Ya juya ya shiga motar sa yana kara kallon motar Fateema fita yayi a asibitin.
Tana shiga ta nufi dakin da zata tadda doctoir Ahmad tana shiga yace
"Yauwah barka da zuwa."

Lab coat ta daura kawai ta nufi inda mai cikin take. Dubata tayi tace
"Ina ganin ba sai an mata operation ba."

"Kin duba condition din ta."
"Yes a saka mata oxgyen insha Allahu zata iya naga Baby yana kokarin fitowa da kansa."

Nan da nan akai mata connecting Fateema ta matsa tana bata kwarin gwiwa hadi da danna cikin nata a hankali a hankali sannu a hankali yaron yana pushing har kan sa ya leko wanna yasa Fateema ta karasa ta janyo yaron. Ai kuwa nan ya kwalla kara. Towel ta amsa ta saka yaron tana mai sakin murmushi sannan ta mikawa nurse dhi. Gun uwar takoma ta dubata sannan ta saka a gyara ta ta fice a dakin din.

Office din ta ta shiga ta gyara jikin ta sannan ta fito. A kofar office din ta ta samu Dr Ahmad yana ganin ta ya saki murmushi yace
"Gaskiya Dr kinyi kokari Allah kara basira."

Murmushi tayi tace
"Ai duk training naka ne nagode."

Ya ce
"Sai tafiya kenan?"
"Wallahi kasan yau ina hutu."

"Haka ne kuma min tarwatsa hutun mun fito dake ko?"
"No ba matsala ai ceto rai ne."

Tana karasawa wajen mota mijin matar ya taho da sauri kamar sai mata sujada ya hau yin godiya yana fadin
"Nagode Hajiya Allah kara dafawa ya shige gaba ya biya bukatun ki na akheri."

"Ba komai ka godewa Allah!"
Ta shiga mota ta bar asibitin ta kama hanyar gida. sai da ta shiga ta tuna  inda ta bugi mota dazu ta tuna dan haka tana shiga gida ta fito tana duba inda ta bige motar ta.

Waya ta dauka ta kira bakanike kan yazo ya dauka ya dawo mata da ita anjima dan tafi jin dadin hawar ta.

Key ta bar masa wajen mai gadi ta shige gida. Momy ta sama a falo ta mike da sauri tana fadin
"Yaa?"

"Alhamdulillah ta sauka lafiya ta samu baby boy!"
"Masha Allah. Allah kara lafiya."

"Amin. Bari na watsa ruwa nai sallah na fito."
"Ok!"Tana shiga ta watsa ruwa sannan ta daura alwala. Mai ta shafa sannan ta saka dogon siket baki da bodyhug ja. Ta saka jar hula akan ta. Sallah tayi ta jima tana addu'a sannan ta mike ta fito. Kitchen ta shiga ta debo cake a plate ta dauko lemo a cikin firij ta dawo gaban system din ta da ta fita ta barta dazu.+

Momy tace
"Abincin fa?"

"Na koshi!"
"Wai Fateema haka rayuwa zata tafi ace kin kauracewa abinci. Abinci in ba kiyi two to three spoon ba shikenan sai wadan nan kayan fulawar shiyasa gaki nan kullum sai dada karewa kike yi."

"Momy ai suma abincin ne!"
"Ba dai kamar abinci ni ban dauke shi a abinci ba kayan zakin gwara ma meat pie amman gaskiya ki canja tunani wannan ba abun bane mai kyau."

"Toh Momy!"
"Kullum maganar kenan to momy kuma ba gyarawa kike ba."

"Momy fa ina cin abinci."
"Cokali daya biyun shine cin abinci."

"To ayi hakuri!"
Kai Momy ta dauke Fateema ta fara ci tana aiki a system tana gamawa ta kai plate din.

Zama tayi tana kallon a system suna dan taba hira da Momy har akai la'asar ta koma ciki tai sallah.
Tana zaune akan daduma wajen biyar dan ta kasa tashi duk lokacin da ta haukan sallaya kasa tashi take bama in ta tuna da Fu'ad ta tayi masa addu'a kenan Allah kare shi ya tsare shi ya dawo dashi gida.
Dan kanta take zarga da tafiyar Fu'ad yaki dawowa. Momy ce ta shigo da sallama. Amsawa Fateema tayi tana dagowa. Keyn motar ta ta ajiye mata tace
"Me yasamu motar?"

"Uhmm dazu ne garin sauri na bude wallahi."
"Alah ya kiyaye."

"Amin!"
Ta fita. Itama mikewa tayi ta fito falo ta zauna. Aiki ta cigaba a system har akai magariba ta koma daki tayi sallah.

Tin da nayi sallah ban mike ba dan alkur'ani na dauko ma ina biyawa a hankali cikin kira'a mai dadin sauraro. Ban tashi ba sai da naji ana kiran sallah isha'i. Sallah na mike nayi. Nayi shafa'i sannan na zauna ina addu"a.

Takwas da rabi na fito falo. Momy na sama akan dining tana cin abinci gun dining din na karasa na zauna. Flask na bude naga farfesun kifi shi na diba ina ci har Momy ta gama ta bar wajen.

Kayan na kwashe na kai kitchen na tsaya na wanke na gyara kitchen din fes sannan na fito falo na zauna ina kallon TV da ake wani indian film.

"Gaskiya Momy gidan ba dadi ya kamata su Baba Uwani su dawo haka."
"Au ke da kika ce kada su dawo su zauna ko ba haka kika ce ba da zasu tafi."

"Da wasa nake am totally missing them da ba aiki tafiya zanyi nima na barki ke kadai. Bazan iya zama basu ba."
"In kikai aure ba."

Baki na turo. Momy tace
"Fateema lokaci fa naja dan haka ki cire Fu'ad a ranki nasan ba zaki rasa manema ba sai dai ki 'ki to ni dai abinda zance shine aure shine darajar ko wacce 'ya mace dan haka ki nutsu a cikin masu son ki ki fitar da daya."

Hawaye ne ya fara biyo kunci na. Momy ta bude baki tana kallo na dan duk lokacin da ta farai mata maganar aure abinda ke faruwa kenan sai na fara kuka. Daga haka kuma sai numfashin na ya fara daukewa.
"Ni bance kimin kuka ba bare ki tadan hankali dagani sai ke a gida kiyi abinda kika ga ya dace Allah bada sa'a!"

STORY CONTINUES BELOW
Ta fada tana mikewa ta bar daki kifa kai na nayi akan kujera ina sakin kuka hadi da dafe zuciya ta.

Shekara daya kenan rabo na da Fu'ad amman son sa bai taba dushashewa a zuciya ta ba. Duk wanda zai zo min sai naga bai kai Fu'ad ba. Fu'ad is perfect. Babu kamar sa. Kalaman sa hankalin sa da nutsuwar sa komai nasa daban ne. I miss him i will always miss him.

Ashe abinda yake fada min kenan da yace
"I miss you!"
Nakan ce
"Bayan muna tare!"

Sai kawai yai murmushi yace
"I will always miss u!"

Ashe what he means kenan. He means he will always miss me. To dan me ya tafi ya barni bayan zai ta kewa ta. Ko yanzu ina ransa. Kai na girgiza ina tuna abunda yace
"Ba zan taba mantawa dake ba. Ba zan taba cire ki a zuciya ta ba. Kece kadai wacce nake so da kauna."

Irin wadan nan kalaman nasa sam basa goguwa a zuciya ta. I really really love and missing him. I can't love anyone else than him. I love him so much.
Na jima ina kuka sannan na mike na kashe kayan kallo na wuce daku. Alwala nayi na hau kan sallaya ina sallah bayan na idar na dauki alkur'ani ina karantawa. Har karfe uku ina zaune a wajen ina karatu bayan na gama na mike na kara sallah. Ina idar wa na dauki carbi na fara jan.
"Hasbunallahu wani'imal wakil,  la'ihalalahu wahadahu lasharikalahu lahul mulku wa lahul handu wahu Alla kulli shai'in kadir. Lahaula wala kuwata illa billah,  salatin annabi da astagafurullah wa atubu ilaik."

Hakika kan nayi sallah asuba na samu sauki sosai a cikin zuciya ta dan haka ina idar da sallah na mike na fara gyara gidan. Ina gamawa na shige kitchen. Ina cikin feraye dankali Momy ta shigo.
Durkusawa nayi nace
"Ina kwana?"

"Lafiya lou Fateema kin tashi lafiya?"
Ta fada tana kallo na dan daga kallon ido na ma zaka san nasha kuka dan a kumbure suke kuma sun danyi ja.

"Lafiya lou!"
"Me kike dafawa ne?"

"Potatoe ball zanyi ne."
"Ok kawo na tayaki kada ki makara."

"No Momy barshi na karasa."
Duk yadda Momy taso ta amsa kin bata Fateema tayi. Dole Momy ta fita wanka tayi.

Karfe bakwai ta gama da komai ta saka akan dining. Wanka ta shiga tayi. Ta shirya cikin wata atamfa purple colour an mata zane da pink and milk kala. Dinkin riga da siket ne ya mata kyau ya zauna a jikin ta kamar dan jikin ta aka dinka.

Mayafi ta dauka milk da takalmi mai dan tudu milk sai jakar ta baka ta fito hannun ta rike da mayafi da jaka dayan kuma wayar ta.
Dakin Momy ta shiga ta tadda ta zaune a kan kujera.
"Momy ni na gama zan tafi."

"Kin karya ne?"
"Na diba za wuce dashi!"

"Ok Allah kiyaye!"
Ta fada ta mike suka fito tare. Har bakin kofa ta rako ta sannan tai mata addu'a Na amsa da Amin.
Mota na shiga na dago mata hannu sannan na fice. Tuki nake kamar bana son tukin dan yadda jiki yai matukar yin sanyi har na dau hanyar asibiti sai na juya motar na nufi gidan Fu'ad.

A kofar gida na tsaya ina kallon gidan sai kuma na tada mota na tafi dan key din gidan na office. A hankali na danna horn lokacin da nazo bakin gate din asibitin. Da sauri mai gadi ya bude gate din yana fadin
"Sannu da zuwa!"

"Yauwah Baba ina kwana?"
"Lafiya Alhamdulillah! An tashi lafiya?"

"Lafiya lou!"
Na fada ina jan motar na nufi gun parking dina. Wajen da ba mai parking sai ni kadai. Ina ajiyewa na fito. Wasu nurse ne guda biyu suka karaso suna fadin
"Ina kwana Dr fateema!"

"Lafiya lou kun tashi lafiya?"
"Alhamdulillah!"

Nayi ciki suka biyo baya na. Office din na shiga kamshin da nafi kauna naji a ciki dan haka sai naji wata nutsuwa ta saukar min. Gaban table dina na karasa na zauna. Hannu na na saka na dauki turaren dake ajiye akan table din. Bude shi nayi na shinshina sai kuma na lumshe ido. A hankali nace
"My i miss you with your Fragrance,  cool voice,  soft hand,  love look,  i miss everything in you."

STORY CONTINUES BELOW
Ajiye turaren nayi ina sauke ajiyar zuciya sai kuma na bude ido na a hankali. Dan flask din da na saka a cikin jaka ta na dauko daya na potatoe ball dayan kuma kunun alkama ne da na dama na zuba madara a ciki.

Agogon hannuna na duba naga 8:30am mikewa nayi na fita ta kofar baya. Cikin asibitin na nufa kai tsaye. Ina shiga na wuce dakin da aka kwantar da matar da na amshi haihuwar ta jiya.

Ina shiga na ganta zaune tana shan tea. Tana ganina ta saki murmushi tana fadin
"Ina kwana Dr?"

Gun Babyn na isa nima ina murmushi nace
"Lafiya lou ya jiki?"
"Naji sauki!"
Ido na na kan Babyn nace
"Allah kara sauki!"

Sai kuma nace
"Masha Allah! Baby tubarkallah."
Nai manna masa kiss a kumatu ina fadin
"Morning Baby!"

Maman ta dake sallah ta idar ta juyo tana fadin
"Ina kwana?"

Har kasa na durkusa na ce
"Ina kwana Mama?"
"Lafiya ya aiki?"

"Alhamdulillah."
"Mungode fa."

"Allah zamu godewa."
Kai ta gyada na karasa wajen mai jegon ina fadin
"Ba dai wata matsala ko?"

Kai ta gyada tace
"Babu komai alhamdulillah!"
"Masha Allah zamu gani zuwa afternoon in ba wata matsala sai a sallame ku."

"Mungode."
"Ba komai!"
Na fada ina maida Babyn. Sannan na juya nace
"Sai anjima."

"Allah yayi albarka ya biya bukatu ya rabaki da damuwa duniya da lahira."
Maman Mai jegon ta fada. Wani sanyi naji da tai min addu'ar dan haka na amsa da
"Amin nagode sosai."

Na fita a dakin. Office na koma nai walha sannan na fito.  Round nayi har zuwa sha biyu da rabi sannan na koma office. Kunun kadai na sha sannan na mike nai sallah. Ina zaune har aka kira azhar nayi sallah karfe biyu da rabi na koma kan table dina.

System nake dubawa ina ganin wadan dake son gani na. Na farko ne aka shigon dashi ya zauna ya fada abinda ke damin sa na bashi magani sannan na sallameshi.

Sai da na duba mutum hudu sannan aka ce sauran daya bai karaso ba. Karfe uku da kwata nurse ta shigo tace
"Hajiya yazo!"

"Ok cene ya shigo."
Na fada ina bude flask din gaba na. Fork na saka na dauki daya na kai baki na dan yunwa naji ina ji.
"Assalamu alaikum!"
Naji wata murya mai sanyi tayi sallama a cikin office din. Da sauri na dago karaf muka hada ido wata faduwar gaba naji ta ziyarce ni. Dan haka nai sauri dauke kai ina amsa sallamar tasa a hankali.

"Bismillah!"
Na fada ina nuna masa kujerar dake gaban table dina ganin bai motsa daga inda yake ba yasa na dago ina kallon sa.

Tsaye yake a inda yake idon sa kyar akai na. Dogone sosai sanye yaje da milk kalar gezna sai brown hula da takalmi da agogo. Idon sa sanye da farin glass. Yana dogon hancinsa da madaidaicin baki mai dauke da pink lilps.

Kwarjini yai mata dan haka tankara cewa
"Bismillah!"
Har lokacin bai motsa ba bare yasan tana yi ma.

Baki ta tabe ta mai da hankalin ta kan flask din gaban ta. Daya ta kara ci kawai taji kuma ba zata iya cin abu ana kallon ta ba. Firij din gefen ta ta bude ta dauko ruwa sannan ta bude ta sha kadan ta ajiye sauran akan table din gaban ta.

A sace ta dan kalle shi taga har lokacin yana tsaye bakin kofa yana bin ta kallon. Kamshin turaren sa kuwa duk uabcika office din. Jim tayi ta kasa zama ta mike tana daukar wayar ta ta nufi kofar da zata sada ta da cikin asibitin. Da kallo ya bita har ta fice sai kuma ya sauke a jiyar zuciya kujerun dake office dun ya samu daya ya zauna yana sakin ajiyar zuciya.
Tana fita ta nufi dakin mai jegon jiya dubata tayi taga ba wata matsala daga ita har Baby din dan haka ta basu sallama. Ta fito kenan ta hadu da Dr Auwal ya karaso suka gaisa tace
"Ashe ka dawo."

Yace
"Wallahi dawowar kenan kinsan na bar mara lafiya nazo na duba naji ance har kin sallame sa."

"Ok Alhaji Muktar ko? Ai yaji sauki sosai."
"To madallah nagode fa."
Murmushi kawai tayi ta wuce ya bita da kallo yana murmushi.

Office na koma ina shiga naga mutum zaune akan kujera sai da zuciya ta tabuga domin kuwa ba karamin tsoro ya ba ba dan ni na manta da yazo ma. Sai kuma na dake na wuce na zauna akan table dina ina aiki a cikin system.

Murmushi ya saki ya mike ya dawo gaban table dina. Ban dago ba sai kamshin sa da ya cika min hanci na.
"Dr Fateema ko ince Hajiya Fateema am i right?"

Dagowa nayi na kalle sa sai kuma na dauke kai nace
"How may i help you!"

Zama yayi yace
"Na zata babbar macece ashe you are young and cute also beauty!"

Bata san lokacin da ta saki murmushi ba tace
"Ko?"

"Yes! Jiya na biyo bayan ki kan na karaso kin shiga. Despite ban san wacece ke ba."
"How comes."

"Jiya kin bige min mota da ki tsaya ki ban hakuri sai ma kika janye jika bar wajen. Wannan yasa na biyo ki kan na karaso kin shigo ban san wacce ba na tambaye mai gadi yace min sunan ki Hajiya Fateema naso na ganki a jiya aka ce ba zan samu dama ba wannan yasa nace yau din zan dawo. A gaskiya ban zata haka zan ganki ba. Daga kallo daya kin sacen zuciya ta. Kin burge ni you are young and ...."
"Uhmm ya isa!"
Na fada ina kallon sa nace
"Da me kazo kai min!"

"Biya na zakiyi!"
"How much wil i pay u!"
Ta fada tana dannan wayar ta miko masa wayar tayi tace
"Put your account number and the amount am sorry. Ina sauri zan zo in amshi wani emergency issue ne na taho ga ceton rai ne shiyasa."

Amsar wayar yayi ya fita daga wajen yai dailing number sa yana ji tana kara sannan ya mika mata yace
"Nagode. Allah kiyaye gaba. But..."

Mikewa tayi tace
"Is ok please zanyi sallah!"
Tana fadar haka ta nufi kofar toulet ta shiga da kallo ya bita yana sakin murmushi ta burge shi sosai. Fita yayi shima dan bai son rasa jam'i. Sai da ya fita ya lura da motar ta da har an gyara ta daga bugewar da tayi jiya. Kai ya girgiza ya bar wajen ya tafi masallaci yana fitowa ya shiga mota ya nufi gidan sa.

Ina fitowa daga bandaki na ga baya office din tsaki kawai na saki na hau kan sallaya na tada sallah. Ina idar wa na mike na hau hada kaya na. Flask din da nazo dashi na fito dashi. Gun mai gadi na nufa na bashi ya juye sannan na koma mota na ajiye kaya na na tada motar na fice a asibitin. A hankali nake tafiya ina tuna dan rainin hankalin nan. Tsaki nayi ganin traffic πŸš₯ ta tsaida mu. waya ta na dauka ina duba message dan naga nawa ya dauka amma sai naga basuyo min alert ba. Account dina na duba naga ba adau ko kwandala ba. Baki na tabe na ajiye wayar ina kallon titi. A haka aka bamu hannu na tada motar nayi gidan mu da Fu'ad.

A bakin gate nayi parking sannan na shiga. Gidan na nan yadda yake dan ina yawan zuwa na gyara shi. A falo na zauna ina bin dakin da kallo kullum na shigo gidan sai na tuna rayuwar da mukai da Fu'ad.

Ba abinda nake mantawa kamar hadda haka nake ji. Momy taso a kwashe kaya amman na hana. Da tace ko su Hajiyar Fu'ad zasu yi amfani Hajiya ma tace a barmin shi kawai.

Zaga gidan nayi. 6:15pm na fito na rufe na koma mota ta. Gida na nufa kai tsaye kan na karasa har an kira magariba dan haka na kwashe kaya na nayi cikin gida.

Momy bata falo kuma daman ban sa ran ganin ta ba dan haka na shige dakina kawai. Wanka nayi nayo alwala na fito na saka doguwar riga na tada sallah. Har ya zamar min jiki dan in nai sallah magariba sai isha'i nake tashi awajen.
Sai takwas da rabi na fito falo. Momy na sama zaune tana kallo. Zama nayi a gefen ta nace
"Momy ya gida?"
"Alhamdulillah! Yaushe kika dawo."
"Na dawo ana kiran magariba na shiga nai sallah sai yanzu na fito."

"Ya aikin?"
"Alhamdulillah."

"To maza tashi kije kuci abinci dan ba zan yadda da cin kayan flour din nan ba kullum. Ni ramar ki damuna take."
Mikewa nayi dan nima yunwar nake ji tin kunun da nasha ne a ciki na. Kan dining na isa na bude flask daya naga tuwon semo ne miyar kuka da yaji naman kasuwa. Dayan kuma fried supegette ce da aka yanka hanta a ciki.

Tuwon na saka rabin malmala da aka kulla a leda sannan na zuba miyar na fara ci. Tas na cinye wanda na zuba na mike zan mai da kawon Momy takaraso wajen flask din tuwon Ta bude taga abinda na diba. Fuska ta hade tace
"Me kike ci kenan. Wai ke kam Fateema kina likita baki san illar rashin cin abinci ba.,"

Zama nayi nace
"Momy illar rashin cin kika ce ni kum ina ci ko yaya ne. Matsalar ka zauna baka ci ba shine!"

Tagumi Momy ta zuba tana kallo na nace
"Momy ba kyau fa."

'To ya zanyi Fateema ai ke kika saka ni yin tagumin. Ace mutum bashi da abinda ya tsana sai abinci anya kuwa?"
Murmushi na saki nace
"Momy ina ci fa ko a asibiti ina bayar wa a siyon kuma ina sha malt ko fresh yoo!"

"Haka kenan kullum sune abinci. Dan Allah kina cin abinci ko kya yi kumari kalli yadda kike dada karewa sai kace kudin guzuri haba Fateema."
Kai nayi kasa dashi nace
"Toh!"

Plate din hannu na ta amsa tace
Maza dauki rabin ki cinye. Ji yar mal malar amman ace itama sai an rage ko yaron yaye tai masa kadan bare ke."

Dauka nayi na saka ina fadin
"In cikina ya fashe ai shikenan!"

STORY CONTINUES BELOW

"Bama zai fashe ba dan wannan dan tuwon to masu ci da yawan ma bai fashe ba bare ke."
Ci na fara amman jin cikin na nake kamar zai fashe da kyar na karasa turawa na mike na wanke plate din.
A falo na samu Momy na dauki mayafi na yafa nace
"Bari na motsa jiki na ko abincin ya fada daga nan zan siyo chewinggum a wancan super market din dan wallahi ciki na kamar zai fashe."

"Sai ki dawo!"
Momy ta fada na fita a kafa nake tafi dan cikin ya sauka duk da ba wani nisa ne da shagon ba.

Doguwar riga ce a jiki na ash kala wacce akai mata layi layi da baki bata da shape a tsaye take kawai dan haka dan karamin mayafin ta na yafa wanda shima kalar rigar ne sak. Amman ya haska ni. Fuska ta ta fito ta ciki tai kyau da fresh. Waya ce kadai a hannu na sai ATM card dina.
A haka na karasa super market din. Na shiga na wuce na fara daukar chewing gum da sweet πŸͺ chorcholate 🍫 sai wasu biskir din. Duk na zuba a basket.
Mutumin dazu da yake office din ta shine a  jikin motar sa a kofar super market din. Sanye yake da ash kalar wando sai bakar riga mai gajeran hannu. Idon sa sanye da glass πŸ‘“ baki. Tun da zata shiga yake kallonta har ta shiga. Wannan yasa shima din shiga.
Kan ya karasa har ta gama da gun sweet ta wuce wajen turaruka bin bayan ta yayi, bai magana ba ta fara zabar wadan da take so. Kala kala ta dauka sannan ta dauki irin na Fu'ad. Juya shi ta farayi sannan ta saka a basket din hannun ta. Bayan ta gama ta tafi gun pad, ta duka ta dauki virony manya guda biyu.

"Assalamu alaikum!"
Akayi mata sallama. Jin muryar namiji yasa tai saurin dagowa  ido suka hada gabanta yayi mugun faduwa don rass ta ganesa.

Da sauri ta juya ta bar wajen. Da kallo ya bita yana murmushi sai kuma ya bita ya same ta tana daukar soap  yace
"Amman dai ai ba kyau ai maka sallama baka amsa ba ko. Ai addu'a nai miki ko ba zaki min ba kya amsa wacce nai miki ko?"

Bata juyo ba kuma bata amsa masa ba yace
"Ya kike ya aikin?"

Still bata kula shi ba. Gaban ta yasha yana murmushi yace
"Kin gane ni kuwa?"

"In na gane ka me zan maka? menene matsalar ka dani ne wai?"
"Haba Hajiya tah baki kala da masu saurin fushi ko fada ba. You are cool i see meyasa kike son canjawa daga yadda kike ehee?"

Juyawa tayi tana kallon wani side din gaban ta na bugawa da karfi.
"Shikenan amman babu fada me zai kawo gaba ehe? Ni dai ayi hakuri in na bata miki rai ne."

Still tayi a tsaye, bata juyo ba kuma bata ce komai ba. Murmushi yayi kawai ya wuce ya nufi hanyar fita daga mall din.
Baki ta tabe ta dan bishi da kallo ta gefen ido, bayan wasu sakwanni ta bi bayansa,  a gun counter ta same shi yana biyan kudin abun da ake masa parkaging a leda wannan yasa ta nufi wajen dayan counter duk da da mutane dan wajen da yake ba kowa sai shi kadai.

Ana xuwa kai na na daura kayan a gun. Yana gama lissafa mata yace
"15500!"

ATM din zan mika sai gani nayi ya mika masu nasa, juyawa nayi ina kallonsa ya saka masu pin dinsa, Hararar sa nayi sannan na fice ba tare da na dauki ledar tawa ba.

Suna cire kudinsu suka mayar masa card dinsa ya dauki ledar tawa ya fito kofar da sauri. Har na bar harabar wajen dan haka da sauri ya biyo ni kan nai aune sai ganin mutum nayi a gabana. ledan kayan nawa ya mikon yana fadin
"Kiyi hakuri in na bata miki dan na biya miki kudin amman ai ba kyau mai da hannun kyauta ba. A ido ba haka kike ba nai miki sallama baki amsa ba na miki ya aiki same sannan yanzu na biya miki kudi amman kin ki amsa dan Allah ba dan ni ba ki amsa nasan kinfi karfin sa amman na biya saboda shishigi irin nawa kiyi hakuri ki amsa ba zan kuma ba insha Allahu."

STORY CONTINUES BELOW

Tin da ya fara magana kai na a kasa yake in ban da faduwa ba abinda gaba na ke yi. Dagowa nayi a karo na farko naga yana kallo na kai na dauke dai dai lokacin da aka kira sa kenan. wayar ya zaro yana kallon screem din wayar tasa. Murmushi ya saki sannan ya danna receive πŸ“ž  ya kai kunnen sa shiru yayi sannan yace
"Am sorry dear gani nan yanzu zan karaso na tsaya siyar miki abinda kika ce kina so ne."

Ta gefen sa nabi zan shige sai yai saurin kamo hannu na sannan yace
"Ok sai na karaso!"

Hannu na na fincike ina hararar sa nace
"Menene haka?"
Hannu ya daga alamar ban hakuri sannan yace
"Kiyi hakuri gashi!"

Ya mikon ledojin nawa. Kallon kedar nayi yace
"Please!"

Hannu na saka na amsa sannan na juya zan tafi yace
"No thanks!"

Juyowa nayi a zafafe nace
"Ni na sakaka?"
"Ayi hakuri da wasa nake ina nufin ba sallama!"

Kai na dauke na wuce da sauri ya kara shan gaba na yana fadin
""Toh muje in ajiye ki a gida?"
Da sauri nace
"Bana so!"
Na yi gaba na barshi. bin na yayi da kallo yana murmushi, sai bayan da nayi nisa  sannan ya juya ya koma gun motar sa.
*
**
***
****
*****
******
Har asuba daga Aisha har Aliyu ba wanda ya runtsa a cikin su. Gwara Aliyu tin uku ya hau kan sallaya yana sallah yana mika rokan sa ga Allah akan ya shige masa gaba.

Aisha kuwa sai hudu da rabi ta mike ta dauro alwala sannan tazo ta shinfidsa sallaya tai sallah ta zauna tana addu'a da neman mafita. Karfe biyar ta mike ta kawo raka'atanil firij tana idar wa taji an tada sallah dan haka ta mike tayi sallah.

Bata koma ba dan exam suke da ita. Dan haka ta dauki littafin ta sai dai sam ba abinda take ganewa in banda tunanin Yaa AK da take. Littafin ta dire kawai ta zuba tagumi. Har karfe bakwai da rabi tana zaune tana tunanin da ta kasa gane.

Umma ce ta shigo dakin bayan ta gama hada abin kari har tayi wanke wanke. A bakin kofa ta tsaya tana kallon ta dan kuwa sam bata ma san ta shigo dakin ba. A hankali ta karaso ta zauna a gefen ta da sauri Aisha ta dago tana kallon Umma. Sai kuma tace
"Ina kwana?"

"Lafiya Alhamdulillah! Naga baki fito ba har yanzu kuma naga kuna da exam yau ko?"
"Yanzu zan fito karatu nagama ne."

Ta fada tana dauke littafin dake gefen ta.
"Kinga Aisha ki rufawa kan ki asiri da son sakawa kan ki damuwa. Ki mika komai ga Allah shi zai iya miki. In kika ce zaki sa damuwa zaki lalata abubuwa da yawa a rayuwar ki. Kina ganin jarabawa kike yazu haka zaki je kina yin tunani. Ki sani wannan ita ce damar ki ta karshe in kikai wasa da ita shikenan ki mai da hankali dan shine farin cikin Yayan ki da Yaya AKn naki. Ko kina son ki fadi jarabawar?"

Kai ta girgiza Umma tace
"To ki shiga hankalin ki. Tashi kije ki dibi ruwan kiyi wanka kizo ki shirya ku tafi."

"Toh Umma!"
Ta fada tana mikewa. Fita Umma tayi ita kuma ta cire kaya ta shiga bandaki. Wanka tayi ta fito ta shirya cikin kayan ta. Tana cikin saka safa Umma ta shigo hannun ta rike da cup din tea 🍡 da plate bread ne da kwai a ciki.

"Maza ki cinye ki fito ki tafi har takwas saura ku da zakuyi jarabawa tara da rabi ai kya je ki nutsu kan lokacin ko?"
Ta ajiye sannan ta fita.

Zama tayi ta fara ci sai kuma ta tsaya kallon waje daya tana tunani. Umma ce ganin Takwas tayi yasa ta fito ta shiga dakin.
"Aisha!"
Umma ta kira sunan ta tana rike haba.
"Haba Aisha yanzu baki sha ba har sai ya huce."

Dauka tayi ta kafa kai tana sha tana tura bread din da kwai. A haka ta cinye sannan ta mike ta dauki jakar ta tace
"Umma na tafi."

Kudin makaranta ta bata sannan ta fita. A hankali take tafiya sam bata da kuzari a haka ta karasa makaranta. Ko da take can bayan aji ta karasa ta zauna bata tashi ba sai da aka shigo yin jarabawar. Sit din ta ta isa ta zauna aka basu booklet kowa na rubuta sunan sa da exam number and serial number amman ita ta zubawa papper ido kawai. A haka aka fara passing question paper.

Shima har aka ajiye bata sani ba. Nan fa aka fara jarabawa amman sam Aisha ko biro bata daga ta nufin yin rubutu ba. Tunanin Yaa Muhammad da Yaa AK kawai take duk da na Yaa AK yafi yawa.

Wani lokaci ta tuna da Yaa Muhammad yake fadin
"Buri na a yanzu ki gama makaranta ki fito da sakamako mai kyau. Daga nan sai inda karfi na ya kare na ganin kin cigaba da karatu. Damin yin karatun ki zai taimakawa mutane da yawa ba mu kadai ba har al umma."

Sai kuma Yaa AK da yake fadin
"Aisha ina son naganki kin zama likitan nan yadda zaki na kin allura in ban da lafiya ko kina duba marasa lafiya. Duk da biyan ki za ai amman zaki samu lada domin kinyi abu mai kyau bare yadda zuciyar ki ke da kyan nan nasan zaki nemi lahirar ki da damar da zaki zamu. Dan haka ban da buri sai na inga yau kin gama jarabawa kin fito da result mai kyau na samar miki makaranta mai kyau. Ya Allah! Wa yaga Aisha ta gama karatun ta ta zama cikakkiyar likita. A duniya ina jin ba wanda zai fini jin dadi da farin ciki. zan ta miki addu'a Allah dafa miki kema kuma sai kin taimaka wajen bada goyan baya kiyi karatu ki kuma hada da addu'a!"

Hawaye ne ya zubo mata a idon ta. Dagowa tayi ta kalli yan ajin kowa ya mai da kai akan aikin sa ana ta rubutu dan haka itama sai ta maida kallon ta kan booklet πŸ“”  dinta da ko  A bata rubuta ba. sai kuma ta dauki biron ✒  hannunta ta daura akan paper πŸ“œ πŸ“” din ta. Sunan ta ta rubata with her serial and exam number. Question papper ta dauka tana dubawa. Nan ta fara answering objectives din wanda duk yawanci a cikin karatun da Yaa AK yai mata ne a jiya kan wannan abun ya faru.
Tana cikewa wani abun tana gani kamar a lokacin yai mata bayani dan haka tana fara essay din ta fara bayani kamar yadda yai mata. Sai da ta gama ta daga tana kara dubawa lokacin yan ajin har an fara fita dan haka tana gamawa ta mike tayi submitting sannan ta fita. Can bayan ajijuwan su ta karasa ta zauna tana tagumi.

"I do it just to makes both of u happy."
Ta fada hawaye na zubo mata.
"Why am i sad, crying,  😒 and disturben why?"
Ta tambayi zuciyar ta.

Zuciyar ta ce ta bata amsa tace
"Saboda kin saka wanda ke son ki cikin damuwa."

"This shows that am concern with his problem. Why i am Worries with his problem?"
Ta kara tambayar zuciyar ta.

"Is because you love him!"
"I love him!"
Ta mai maita abinda zuciyar ta ya fada mata.

"If i love him what about Yaa Muhammad. How can I loves two person at thesame time!"
Ta girgiza kai. Sannan tace
"Inpossible!"

Ta dafe kai. Sannan tace
"Wannan kenan yanuna bansan *wa nake so?* ba"

Ido ta lumshe sannan ta bude
"How comes..."
Sai kuma ta cije baki. sannan tace
"Tayaya hakan zai faru. Kenan ban san *Wa nake so?* ba. Ya Allahu!"

Ta fada tana rufe fuskar ta da tafin hannun ta. Hawaye ne ya fara zubowa a idon ta sannan ta mike a hankali ta bar wajen dan daman Exam kawai ta kawo su school din.

Shima sai da yayi raka'atanil firji sannan ya nufi masallaci acan yai sallah sai karfe shida ya fito yayo gidan. Yana shigowa yai wanka ya shirya cikin wata suit din sa maroon πŸ”Ί colour ya saka black  shoe πŸ‘ž sannan ya saka black watch ya fito hannun sa rike da waya yana daddanawa. Ko dining bai kalla ba ya fice a falon.+
Motar sa ya tada kawai ya fice a cikin gidan. Gidan gwamnati ya nufa kai tsaye yana shiga ya wuce inda office din sa yake. Fuskar nan a hade kamar me dan duk wanda ya gansa sai ya bashi hanya ya wuce dan ba karamin shiga hankalin su sukai ba ganin ba walwala ko kadan a fuskar shugaban nasu.
Zama yayi ya kawa aikin komai duk aiyukan dake gaban sa kasa su yayi ya zauna kawai yana tunanin Aisha. In Aisha ta ki yaya zai yi wannan shine abinda ke daga masa hankali.

Sam ya kasa sukuni komai ya kasayi in banda tunanin ta da abubuwa kala kala. Sam bai ci komai ba ya fito kuma ko yunwa bayaji.

Haka ya yini a office din bai aikin fari ba bare na baki. Duk masu appointment dashi ma in ance sun zo cewa yake acanja musu lokaci da ba zai iya ba.

Sosai tunanin da yake ya saukar masa da wani irin ciwon kai da bai taba yin irin sa ba. Ga wani zazzabi da yake ji. Jarumin Namiji kamar Aliyu lokaci daya ya karaya ya fara fidda rai  Ba shiri yana yin sallah la'asar ya bar gidan gwamnatin.

Gidan sa ya nufa kai tsaye yana parking ya fito yana ganin juwa. Tsayawa yayi a jikin motar sa ya dan ji dai dai sannan ya bude idon a hankali ya nufi cikin gidan.

Yana shiga vai zarce ko ina ba sai dakin sa. Yana shiga ya zare takalman sa ya hau kan gado ya rifa da bargo saboda sanyin da take ji.
Abun mamaki yake bashi sosai. Tun yana dan karamin sa ba abinda ya nema bai samu ba, ‘yan mata masu ji da kansu, ta fanni ilimi, kudi, kyau da komai, sai dai ya take ka wuce dan ko kallo basu isheshi ba.
   
   
Mai ya rasa a rayuwa Power, mulki, kudi, ilimi, mutumci, daraja, suna, duk uana da shi amma yau yana ji yana gani zai rasa *Burin ransa* ko kuwa yace *wacce yake so* Wannan shine ne na farko a rayuwar sa da ya  taba jin wani abu ya taba zuciyar sa, ya ji kaunar wani abu da son kasancewa da wani abu a rayuwar sa amma ya rasa wannan abun.

Yana ji ina gani Aisha zata fi karfin sa, bayan ya gama saka rai da ita ya gama kwallafa wa ransa son ta da son kasamcewa da ita. Yasan Allah shi ya jarabce sa da son Aisha dan ya zama Haske a gareshi kuma ya zama hasken domin canjin da Aisha tayi masa da taimaka.masan da tayi kadai ta zama *Hasken rayuwar sa.* ta haskaka masa rayuwa sosai ta yadda ba zai taba mantawa da ita ba.
Wani abin mamaki bai An kara ba sai hawaye masu dumi ya ji suna zubowa daga idonsa. Gaskiya ba zai iya tuna yaushe ya yi zubar hawaye a fuskarsa ba sai yau, Ji yake komai da yake da shi ya zama na banza in har bazai samu kasance da ita a  karkashin inuwa daya ba.
Yana son ya jure rashin ta amman meyasa yake kasa jure rashinta, zuciyata ta kasa, daga jiya zuwa yau kadai son ta ya dada ninkuwa a cikin zuciyar ta nesa ba kusa ba.

Shi da yafi karfin komai da komai a rayuwa amman ya kasa samun abu guda daya tal. Juyi yayi akan gafo yana jin zazzabi na kara rufar masa. Shi kadai yasan me yake ji a zuciya da jikin sa. Jin sa yake kamar maraya, duk da ya kasance dan dangi me uwa da uba mai gata. Ji yake kamar duniya gaba daya ta juya masa baya in har Aisha ba zata amshi soyayyar sa ba.

STORY CONTINUES BELOW
Idon sa da sukai masa zafi dan yadda kan sa ke ciwo ya lumshe ido yana tuno yanayinta, murmushinta, dariyarta, tsiwarta, fushinta, surutunta, tunaninta, hagen nesanta, kyakkyarwar zuciyarta.
   
"Dariyarki kadai ya ishi ni samun farin ciki da kwanciyyar hankali a dukkan rayuwarta,"
Ya fada a cikin zuciyar sa.
"Ina son murmushi ki mai mai kara min kwarin gwiwa. Aysher ba zan iya jure rashin mace irinki ba, kallon daya in na yi miki yana wanke dukkan wata matsalar rayuwata. In na rasa ki yaya zan yi"
Bakin sa yai saurin rufewa da hannu yana fadin
"Allah na tuba. Allah kada ka jarabce ni da rasa Aysher!"
Allah shi ya aiko Aisha cikin rayuwar sa dan ta canja masa rayuwa ta haskaka masa ta kuma ceto sa daga halaka. Hakika yana mai godiya da Allah da ya hada shi da Aisha.Lokaci guda Zara ta juya masa baya , shigowar Zara rayuwarsa ya canja abu da yawa a rayuwarsa.

*
Haka ya yini ya kwana da zazzabin washe gari ma sam bai je aiki ba a gida ya zauna wanda zaman ba abinda ya kara masa sai damuwa. Wayar sa gaba daya kashe ta yayi dan bai son a kara masa wata damuwar akan wacce yake ciki a lokacin.
*
Cikin sati daya ya rame dan ko fita yai ba abinda yake iyawa a office. Komai ya ajiye shi ya zubawa sarautar Allah ido.
Ciwo yake a tsatsaye tsatsaye wanda yake kara karar dashi. Dan wani ciwon kai ke damun sa sosai yake jin ciwon ga zuciyar sa da take damun sa da batun Aisha. Yana son Aisha amman bai son yai mata dole kuma farin cikin ta shi yake so. Dan haka ya kashe wayar sa dan bama ya son ya kira ta bare ta fama masa ciwon da yake fama dashi.
Amman yadda zuciyar sa ke damun sa da vatun ta idanun sa ke son ganun ta kunnuwan sa ke son jin muryar ta yasa yake jin kamar komai na duniyar an daura masa a kan sa. Sam bai da nutsuwa. Addu'ar yake azumin yake amman duk a banza dan bai jin wani sauki sai daduwar son ta a zuciyar sa.
Lokaci guda ya canja rayuwar sa da ta kowa da ya shafe shi kamar yadda Aisha ta canja masa rayuwa da tunani.

Sarki kam da mahaifiyarsa kullum suna cikin sa masa albarka, yayin da mahaifinsa ya tabbatar ya samawa talakawansa sarki adali, ya samu magaji tabbas ba mai gadonsa sai Aliyu ba. Don haka yakara yi wa Allah godiya da wannan canji da aka samu daga dansa.
Hajara kuwa sam bata damu da ganin canji daga mijin ta ba duk da tasan miskili ne mai zurfin ciki amman hakan bai sa ka kasa gane yana tattare da wata matsalar bane.

*
Aisha kuwa cikin kwana daya har ta rame ba ta da aikin yi sai tunani gaba daya ta kasa karatu dan ma washe gari basu da jarabawa amman jibi suna da ita amman littafin na hannu ta ita ta kasa ko da karanta kalma daya ne.
Umma sai nasiha take mata da bata kwarin gwiwa akan ta dage tayi karatu ko dan ta bawa mara 'da kunya kuma ta cikawa Yayan nata burin su da suke son suga ta gama karatu ta samu sakamako mai kyau.

*
*
Da yaya take iya yin jarabawar da kyar take iya rubuta abun arziku dan tunanin. In ba gani tayi an fara submitting bama ta lura har tai wani abun arziki.
Ta rame ta kara zama shiru shiru abun tausayi da ita in ka ganta. Umma kullum cikin addu'a da mata nasiha take.
Ta kira number sa har ta gaji gashi ita tsoton zuwa gidan sa ma take yi. Da taga ba madogara sai Allah kawai ta nufi gidan nasa amman A lokacin sai Mai gadi yace mata bai dawo ba.
"Da yaushe yake dawowa?"
"Gaskiya yanzu bai da lokacin dawowa har 12 na dare ma sai ki ganshi."
"Shikenan nagodr!"
Ta fada tana juyawa amman zuciyar ta ta kasa nutsuwa ko a wane hali yake duk ta damu ba kadan ba.

Zaune take a daki ta rasa me yake mata dadi littafi ne a hannun ta amman bata san me take tunani ba. Muryar Yaa Muhammad ta jiyo wannan yada ta mike da sauri. Ji tayi yana fadin
"Ina kanwata!"
STORY CONTINUES BELOW
Wannan yasa ta fita da gudu. Kusan cin karo sukai ta tsaya kallon sa shima kallon ta ya tsaya yi yana murmushi
"Yaya!"

Ta fada cike da mamaki ya ja hancin ta yace
"Bakya murna ne na koma?"

"No Yaya amman ai baka fada min zaka dawo ba ko?"
"Suprise nai miki kanwata."

"Sannu da zuwa bari in kawo maka ruwa ka shiga ka zauna."
Ta fada tana yin kitchen din su. Ruwa ta debo masa sannan ta zubo masa abinci.

A dakin sa ta same shi zaune akan dadduma. Ajiye masa tayi tace
"Ina zuwa."

Da sauri ta jyya kan ta fita yace
"Ina zaki?"
"Yanzu zan dawo ka ci abinci ka huta kar na dame ka’’

Ya yi murmushi, yace
"Ai abincin ba zai shiga ba in ba kya kusa, sannan ina so ki dame ni Aisha saboda na yi kewar ki da rashin surutun kin nan, zan matukar jin dadi in kin dame ni’’

Ta yi murmushi, tace
"To Yaya na in na soma damun ka sai ka gaji da ni ka kore ni’’
Ya yi dariya, yace
"A da ma bana korar ki bare a yanzu Aisha. Ba ranar da zan gaji dake har in kore ki."

Zama tayi tana fadin
"To kaci abincin!"
Kallon ta yake ba ko kiftawa yace
"Kanwata kinyi rashin lafiya ne?"

Kai ta girgixa tace
"Me ka gani?"
"Naga kin rame!'

"Karatun jarabawa ne kawai."
"Ayyah sorry gaskiya za a daina karatun nan in har zai na saka kanwata tana ramewa."

Tai murmushi tace
"Yanzu dai kaci abincin shiyasa nace zan fita ai ka hana nasan ba ci zakai ba zaka zauna surutu ne kawai."

"Iyeee ni ke surutun ko?"
Kai tayi kasa dashi. Yace
"Taho muci to."

Cikin ta ta shafa tace
"Ni kam na koshi."
Kallon ta yayi yace
"Nima haka!"

"Haba Yaya na please kaci ni ban jima daci ba."
"Da gaske?"
Kai ta gyada masa ya juya yayi bismillah ya fara ci tana zaune tana kallon sa a fili kallon sa take amman a zahirin gaskiya ba kallon sa take ba tunanin Yaa AK take shin yana ina ya aikin yaci abinci yana lafiya? Duk wadan nan sune tunanin da take yi kawai.

Kallon ta Yaa Muhammad yayi yaga gaba daya hankalin ta baya wajen sa wannan yasa ya ce,
"Kanwata!"

Bama tasan yana yi ba. Ya kara fadin
"Kanwata."
Da sauri ta dago ya kura mata ido yace
"Lafiya na lura kamar baki cikin nutsuwa? me ke damun ki?"
Ta yi murmushi, tace
"Ba komai Yayana‘’ 
Saurin kawar da zancen tayi dan tasan halin sa tace
"Nayi mamakin dawowar ka."

"Ko? Zuwan na me so nane!"
"Wacce me son ka!"

Kallon ta ya tsaya sai kuma yace
"Wata ce wacce nake so da kauna. Ban da kamar ta a duniya ita ce abokiyar rayuwa ta masoyiyar zuciya ta abar alfahari na."

"Wacece wannan Yaya na?"
"Kece Kanwata ke kadai nake so da kauna kanwata ban da kamar ki kanwata zan iya rasa rai na akan ki. Zuwan naki ne Kanwata nazo a saka ranar bikin mu da kin gama jarabawa."

'Kwarewa tayi saboda yadda taji maganar tasa har tsakar zuciyar ta a bazace. Ta sauri ya mika mata ruwa ta amsa ta fara sha. Tana gama sha ta lumshe ido. Yace
"Sannu Kanwata."

Ido ta bude ya sakar masa murmushi shima ya sakar mata. Yace
"Na dawo ne dan ke kawai kanwata. Ke kadai nake so da burin ki zama tawa ke kadai nake so. Ke kadai ce mai sona ina fatan nima ni kadai kike so da fatan zamowa mahadin rayuwar ki."

Gaban ta taji ya fadi wannan yasa tai kasa da kanta. Yai murmushi yace
"Tin kina karama nake son ki,  tin baki dan kanko ba har yanzu son ki bai ragu a zuciya ta. A yanzu kin girma, na lura tin daga lokacin kika canja kika zama shiru shiru. Aisha nazo ne na nemi auren ki wannan karon dan haka ina son ki fada min kina so na za ki aure ni?’’
   
Wata faduwar gaba taji ta same ta ta kara sunkuyar da kai ta kasa daga kai ta kalle sa saboda kunya, tsoro,  fargaba shiru tayi taki cewa komai. Yai murmushi ya ce,
"Dan Allah ki ban amsa Aisha rashin amsar zai sa na kawo wani abu a raina bana so na tauye miki hakkin ki farin cikin ki kadai nake so, ina son na ganki cikin kwanciyyar hankali da farin ciki ina son ki Aisha ki fada min kinji."

"Ni dai kunya nake ji!"
Ta fada kawai. Kallon ta ya tsaya yi sannan yace
"Kanwata kenan aure fa zamuyi!"

"Uhm uhmm Yaya ni dai ka bari!"
Ta fada tana rufe fuska da hannun ta.  Yai murmushi sannan yace
"T’o na bari kanwata."

Shiru sukai sai yace
"Ina Yaa AK!"
Tini ya famo mata mikin da take fama dashi. Dan haka take yanayin ta ya sauya duk yadda taso ta danne amman sai da ya gane.

"Lafiya kanwata meya faru?"
"Uhmm Yaya kwana da yawa ban...."
Sai kuma tayi shiru tana zare ido. Kallon ta ya tsaya yace
"Uhmm ina jin ki kwana da yawa baki me ba?"

"Uhmm daman baya nan ne ya bar garin."
Wata ajiyar zuciya ya sauke dan tin daga lokacin da ta fara bashi labarin malamin ta Yaa AK hankalin sa ya tashi bama da yaga bata da batu ko labari sai nashi. In kana son kaji surutun ta tabo maga Yaa AK wannan abu ya tsaya masa a rai bai dai nuna bane kawai.

Mikewa tay da sauri. Ya kalle ya yace
"Ina zaki kuma!"
"Bandaki!"
Ta fada tana fita kawai. Da kallo ya bita yana murmushi.

Post a Comment for "WA NAKE SO CHAPTER 11"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...