YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 3 BY HARUNA USMAN - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA  CHAPTER 3 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 3 BY HARUNA USMAN

- - Post a Comment

 YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA

CHAPTER 3 BY HARUNA USMAN

Www.bankinhausanovels.com.ng 


JIYA MUN TSAYA 

Yanzu ma abin da ya sa ya kawo ku wannan tsibiri shi ne don babu aljanin da zai iya zuwa nan sai wanda ke da jinin sarautar gidanmu a jikinsa. Kuma ya kawo ku nan din ne don kada wani abu ya taba ku. Niyyata ita ce in kashe ku in ya so duk abin da zai faru ya faru, amma da ya ke kuna da sauran shan ruwa, sai kika yi mini magana, kuma a cikin maganarki na ji kin ce mini kyakkyawa, to mu kuma matan aljanu babu girmamawar da ta fi ki cewa aljana tana da kyau. Duk wadda kika ce wa haka, to kin gama da ita.” Www.bankinhausanovels.com.ng 

Shaihi Ibrahim dai ya ci gaba da ba Idrisu labari cewa, da ‘yarsa ta ji jawabin aljanar nan sai ta sami makama, don irin dabi'ar dan Adam na dogon tunani. Sai ta ce 

ZAMU TASHI 


wa aljanar, “Ko kadan babu wasa ko yaudara cewa ke kyakkyawa ce, duk hassadar mai hassada sai dai ya yi a game da wani abin amma ba game da tantamar kyanki ba, don ni na tabbata irin ki a wannan duniyar sai an tona. 

Abin da nake so ki gane shi ne, ganin mu da kika yi a nan ba a son ranmu ba ne, a'a, dole aka yi mana don fin Karfi da kuma kasancewar babu yadda za mu yi. Ke kanki idan kin yi tunani za ki fahimci cewa babu abin da ya hada aljani da mutum. 

Shi wannan dan'uwa naki ba shi da imani, ki duba zuwa yau din nan mu hamsin da daya ne a nan, kuma har gobe in ta kama kawowa ya ke yi, garuruwa da Kasashenmu kowacce daban ne, wasu ‘ya'yan sarakuna ne, wasu na malamai, wasu kuma 'ya'yan talakawa ne da masu dukiya, duk an kamo mu ba,a son ranmu ba, aka raba mu da iyayenmu da ‘yan'uwanmu da samarinmu, kin ga an raba mu da jin dadi ke nan. 

To ke inda kika yi kuskure ke nan, ki ka riKa kashe ‘ya'yan mutane ba tare da hakkinsu ba. Kin ga wannan ba laifinsu ba ne don babu yadda za su iya da shi, laifin dan‘uwanki ne, in ma halakawa ne shi ya kamata ki kashe. Saboda haka ya ke kyakkyawar yarinyar aljanu, muna fata ki yi tunani mu zama Kawayenki ba abokan gaba ba.” Www.bankinhausanovels.com.ng Da aljana ta ji jawabin ‘yata, sai ta fara Kwalla sharshar. Bayan ta nisa sai ta ce, “Lallai kuna da gaskiya, babu shakka na cuci 'ya'yan mutane, na halaka su baa kan hakKinsu ba, duk a dalilin wannan mugun aljanin, amma babu komai, kwanansa sun kusa karewa.” 

Suna jin haka sai suka ce mata, “Ai yakan yi barci a nan, muna iya taruwa mu yi ta soka masa wuka har sai ya mutu.” 

Aljanar nan ta KyalKyace da dariya sannan ta ce, “Ku dai ‘yan Adam ba ku rabuwa da almara, ai shi wannan aljani in duk aljanun duniya da mutane sun taru ba za su iya masa ba. Ni ce zan taimake ku, kuma daga yau kun zama Kawayena, ke kuma ke ce babbar Kawata. Ni dai na yi muku alkawari duk ranar Asabar da ya ke ba ya zuwa nan zan rika zuwa. Kuma na dauki alkawarin ba zan sake kashe wata mace ba saboda wannan mugun aljani.” Bayan ta gama zayyana musu duk wadannan bayanai, sai kuma ta ce musu, “Zan yi iyakacin KoKarina in sato wani littafi da asirin rayuwarsa ke ciki, Shi ma kansa wannan aljani dan‘uwana bai taba ganin wannan littafi ba, don kuwa yana nan wurin wata kakarmu mai shekaru sama da dubu hudu. Kada ku yi mamaki na ce dubu hudu na shekaru, to ko kadan babu mamaki don mu aljanu ba mu mutuwa da sauri kamar ku mutane.” , 

Daga nan fa sai ta shiga cikin 'yan matan nan suka sha kade-kade da’ raye-rayensu. In ka ga aljanar nan a cikinsu lallai za ka ga yadda Allah Ya yi ikonsa. Daidai goshin Magriba ta ce musu za ta koma, suka rabu suna kuka kamar sun yi shekaru tare, amma kafin ta tafi sai da ta gargade su da cewa kada ko da da wasa su kuskura su fada wa Sarkin aljanu cewa ta zo. Www.bankinhausanovels.com.ng Kafin ta tafi sai ta daga hannunta sama, sai ga wata Katuwar kwalbar turare, ta bude ta fesa duk a cikin gidan, sannan ta ce musu, “Abin da ya sa ni fesa wannan turare shi ne, don in ban fesa ba, yana zuwa zai ji Kanshin jikina. In kuma ya gane na zo, to ni na shiga uku ke nan.” Tana kammalawa sai ta yi dariya, kafin ta rufe baki sai hayaki ya turnuke ya tashi sama ya fita ta taga, ta tafi ke nan sai ranar Asabar. Wannan shi ne lamarin aljana. Amma lamarin ‘yata da sauran ‘yan mata bayan tafiyar aljana sai suka ci gaba da hirarsu, dare ya yi suka kwanta. Bayan wayewar gari da kuma daidaitar lokacin zuwan aljani, sai suka fara wake-wake da raye-raye. Can kuwa sai ga shi ya iso. Yana ganin su cikin wannan hali na farin ciki da " walwala, sai murna ta kama shi, su kuma ‘yan matan sai suka zagaye shi suna yi masa marhaban-lale, sannan Www.bankinhausanovels.com.ng  suka ci gaba da wakoKinsu. Bayan sun gaji sai suka dakata, aka yi ciye-ciye da tande-tande, aka sha ‘ya'yan itatuwa masu dadi. Babu shakka Sarkin aljanun nan yana cike da farin ciki, kuma ga ‘yata kusa da shi, komai ya ce nan da nan sai su tashi su yi masa. Wasu ‘yan matan kuma na tausa masa jikinsa. Duk suna yi masa haka ne don hila irin tasu ta mata, ba wai don suna son sa ba, don ka san su mata su ma kansu aljanun kansu ne. To bayan aljanin ya natsu, can sai ya cewa ‘yata, “Ni fa ina jin wani Kanshi ne kamar na aljani.” Sai ta ce masa, “Wace irin magana kake yi haka? Ka tara mu har hamsin da dori, sannan ka ce ba za ka ji Kanshi daban-daban ba? Kuma ka san mu mutane kowa Kanshin jikinsadabanne.” Sarkin aljanu ya amsa mata cewa, “E lallai kam kin yi gaskiya. Ni ma kuskure na yi.” A wannan rana ma kamar kullum, Sarkin aljanu ya yi murna da farin ciki mai tarin yawa. Da yamma lokacin tafiyarsa sai suka rera masa wata waka mai dan karen dadi har ya rude ya tafi yana begen su a cikin ransa. Bayan tafiyarsa sai suka taru wuri daya suna cewa, “Babu shakka za mu kama wannan mugun aljani a hannu, in ya san wata ai bai san wata ba, in shi aljani ne, to mu mutane ne, za mu ga wanda ya fi wani.” A haka har Juma'a ta kewayo, za su yi sallama da shi Www.bankinhausanovels.com.ng sai ranar Lahadi ke nan don ba zai zo ranar Asabar ba. Kafin su rabu duk sai 'yan matan nan suka fara 'yan koke-koke wai ba zai zo gobe ba, shi kuma da ya ga haka sai ya rude yana rarrashin su, can sai ‘yata ta tashi ta ce masa, “Ya kai rabin raina, wanda na fi so a cikin rayuwata, wai ku aljanu haka soyayyarku take ne? Ana ta buga soyayya babu sanin suna? Ko ni ban isa in san sunanka ba don ni ba aljana ba ce ‘yar'uwarku?” To su aljanu a irin tasu al'adar, in mace ta tambayi namiji sunansa, to wannan mata babu wanda take so a rayuwarta kamarsa. Da Sarkin aljanu ya ji yarinya ta tambaye shi sunansa sai ya sake dimaucewa, hankalinsa ya tashi, ya rude ya rasa halin da ya ke ciki don dadi, sai ya nisa ya ce mata, “Ya ke hasken rayuwata, ya ke abar Kaunata, sunana Sarki Sham'una dan Sarkin aljanu Damsalu.” Yarinyar nan tana jin haka sai nan take ta rera waka da sunansa, tana hadawa da sunanta sauran ‘yan matan suna amsawa. Sunan wannan ‘ya tawa Nur. Da Sarkin aljanu ya ji sunansa a cikin waka sai Kwalla shar-shar saboda murna. Ya daga hannunsa sama sai ga lu'ulu'u yana zuba kamar ruwan sama. Ya ce, “Ga kyauta nan irin tamu ta aljanu.” Nur ta ce, “Godiya muke ya Sarkin duniya. Amma ya kai wannan Sarki mene ne dalilin yin hawayenka>” Www.bankinhausanovels.com.ng Sarkin aljanu ya ce, “Ya ke rabin raina Nur, kin san mu aljanu ba ruwanmu da lissafin shekaru irin yadda ku mutane ku ke yi, amma da yake ni masani ne na irin wannan lissafin saboda irin gagarata sai in ce yau kimanin shekara dari hudu da hamsin da bakwai da wata biyar ke nan ban yi hawaye ba sai yau, ga shi kuwa na yi karo da mazaje da yawa a filayen yake-yake mabambanta, na kashe mazaje shahararru, na ga farin ciki da bakin ciki amma ba su taba sa ni Kwalla ba sai yau, dalili kuwa don tsananin son da nake yi miki.” Sai Nur ta ce, “Ya kai wannan kyakkyawan Sarki, babu shakka ina da abin da ke damu na.” Sarkin aljanu ya tambayeta, “Ke kuwa mene ke damun ki a wannan duniya alhali ina kusa da ke? Kan mutum nawa kike so? Ko kuwa kan aljan nawa kike so yanzu-yanzu a kawo su nan?” Nur ta ce, “A'a, ba kawunan aljanu ko mutane ke damu na ba, ni abin da ke damu na shi ne rayuwarka, don ka ce mini kana yake-yake da yawa. Ni kuwa kaicona ranar da za a kashe ka, ni ma ranar ba zan kwana da rai ba.” Sarkin aljanu Sham'‘una yana jin zancen yarinya Nur sai ya kece da dariya har yana Kyakyatawa. Bayan ya gama dariyarsa sai ya ce mata, “Kai, ku dai mutane kuna da ban dariya, shi ya sa kullum na zo nan sai na www.bankinhausanovels.com.ng koma cikin farin ciki, shi ya sa yanzu talakawana ke matukar jin dadina. Tun daga lokacin da kika zo nan har yanzu ban sa an yi wa wani aljani ukuba ba, don ina komawa fadata ne cike da farin ciki daga nan wurinki.” Ya ci gaba da cewa, “Ya ke kyakkyawa Nur, a yau lokaci ya Kure, yanzu ana can an fara zama a fadata.” Yarinya Nur ta tambaye shi, “Ya kai masoyina yaushe ne ake maka fadancin? Ga shi kullum a nan kake yini sai yammaci kake komawa?” Sai ya ce, “To ai mu aljanu baa mana fadanci da rana sai dai da dare, da rana kuma shiru. Ai kamar ku mutane ne da daddare shiru amma da rana ku yi ta hidima.” Sai ta ce, “E lallai gaskiyarka, ya kai Sarkin aljanu, lallai ya kamata ka tafi yanzu kada in rike wa talakawa Sarkinsu, don dole wani lokaci in riKa adalci in rika tuna cewa ba ni kadai ce da kai ba.” Yayi murmushi, ya ce, “E wannan kuma daidai ne.” Nan da nan ya yi sallama da su ya bace yana mai cike da annashuwa. Wannan shi ne lamarin ‘yan mata da Sarkin aljanu Sham'‘una. Yana tafiya sai suka shiga hira suna yaba wa yarinya Nur, saboda hikima da dabara da iya hilarta. Ranar Asabar 'yan matan nan suka shirya suna ta nishadi suna sa ran zuwan Kawarsu wato aljanar nan. Can kuwa sai suka ji wani Kanshin turare da ba su Www.bankinhausanovels.com.ng taba jin irin sa ba a wurin tare da waka mai sanyaya rai daga cikin irin wakoKin da sukan yi, can sai suka ga lokaci ya Bace, sai ga aljanar ta zo cike da farin ciki don wannan zuwan ta yi shi ne don Kawance ba mugunta ba. Kai irin kayan adon ma sai wanda ya gani. Tana bayyana sai suka tarbe ta da murna da farin ciki da nuna Kauna, bayan sun gaisa ta kawo ‘yan ciye-ciye masu dadi ta ba su. Da suka natsa sai suka shaida mata yadda ta kasance tsakanin su da Sarkin aljanu da kuma irin yadda ya saki jikinsa da su, har ma da yadda ya tambaye su labarin yana jin wani Kanshi na daban, da yadda suka shashantar da tambayarsa, har da yadda ya yi Kwalla. Bayan sun gama shaida mata sai ta ce musu, “Ai dama na gaya muku cewa shi wannan aljani fa duk cikin aljanu da wahala a sami wanda ya fi shi jarunta da saurin fahimtar abubuwa. Sai dai kuma namiji komai jaruntarsa mace ce maganin sa.” Suka ci gaba da gudanar da nishadinsu kamar yadda suka saba. Can zuwa La’asariyya sai suka shiga wani lambu da ke cikin gidan suna zagayawa suna tsinkar 'ya'yan itatuwa. Nur ce ta yi wa aljana magana, “Ya ke wannan kyakkyawar Kawa tamu, ga shi mun zama Kawaye kuma mun yarda da junanmu, mun bai wajuna Www.bankinhausanovels.com.ng amana da aminci, amma abin mamaki har yanzu ba mu san sunanki ba, saboda haka yanzu muna son sanin sunanki, amma fa in kin yarda.” Da aljana ta ji zancen yarinya Nur, sai ta yi dariya mai daukar hankalin wanda ya ga hakoranta, sai ta ce, “Ya ke Nur, ke da Kawayenki babu shakka kun san yanzu ina son ‘yan Adam. Na rantse da rana, a da mu aljanu ba mu da abokan gaba kamar ku mutane, don muna zaton ku miyagu ne, shi ma ya karfafa mini guiwa wurin kashe-kashen da na yi ta yi, ashe ba haka ba ne. _Yanzu na fi son ku fiye da 'yan'uwana aljanu, kuma yanzu zan iya sadaukar da kaina domin ku. Sunana Dailanu ‘yar Kailanu. Shi mahaifin Sham'una wato Damsalu shi ne yayan mahaifina.” Sai wata daga cikin ‘yan matan nan ta tambaya, “Ashe Sarkin aljanu dan'uwanki ne na kusa?” Dailanu ta ce, “Kwarai kuwa.” Dayamma tayi sai Dailanu ta ce musu za ta koma sai ranar Asabar. Tace, “Kuma nayi muku alkawari zan zo muku da littafin da asirin kurwar Sarki Sham'una ke ciki, Littafin yana nan a wurin kakarmu Bakayalu kuma babu wanda ya isa ya shiga ma’ajiyarta sai ni. In tana nan babu wanda zai tunkari wannan littafi. Ni ma abin da ya sa zan sami damar dauko shi don za ta yi wata ‘yar tafiya ne, kuma ni ce kawai a dakinta, saboda Www.bankinhausanovels.com.ng haka in akwai wadda ta iya karatu da rubutu daga cikin ku sai ta juyi bayanin ciki don in koma da shi. Ko kadan babu dama wannaan littafi ya kwana a waje. Kul! Wannan littafi ya kwana a nan, to kuwa kwananku ya Kare, ni kuma na shiga ukuba har abada.” Sai yarinya ‘yata Nur ta ce, “Babu shakka, akwai wadanda suka iya karatu da rubutu. Na tabbata za mu iya juye shi cikin lokaci komai yawan shafukansa kuwa.” A haka suka tsayar da shawara. Lokacin da Dailanu za ta tafi sai Nur ta ciro wani warwaro na zinare daga hannunta ta sa mata. Aljana ta yi murna mai tarin yawa, a Karshe dai ta koma tana begen wadannan Kawaye nata. Bayan tafiyarta sai suka zauna suna kewar ta, suna ambaton kyan halinta tare da labarin irin kyau da cikar halitta da Allah Ya yi mata, tare kuma da tausayawa game da wulakancin da Sarkin aljanu Sham'una ya yi mata. Washegari Sarki Sham'una ya zo, su kuma ‘yan mata suka ci gaba da abubuwan da suka saba. Da suka natsa sai ya kalli yarinya Nur ya ce mata, “Ya ke kyakkyawa, ranar Juma’‘a na ji kin ce wani abu game da tsoron da kike yi game da rayuwata.” Sai ya yi murmushi sannan ya kalli sauran 'yan matan yana mai ci gaba da bayani, Www.bankinhausanovels.com.ng “Ya ku wadannan ‘yan mata, ina so in sanar da ku cewa, tun can shekaru masu yawa da suka shude na gagari mazajen jarumai na aljanu. An dade aljanu suna shiri suna kawo mini hari ina wargaza rundunoninsu. A haka sai da na zo na gagari dukkan tarayyar aljanu. A cikin shahararrun aljanun da muka fafata sai wani Sarkin aljanu daga Yamma ne kawai ya dan wahalar da ni cikin shekarun da kasashenmu suka rika bugawa. Yanzu haka yana nan a cikin battar Karfe a kulle, ita kuma battar tana can karkashin tekun nan da babu wandakezuwa. | Www.bankinhausanovels.com.ng To ai ni Bata lokaci ne tunanin mutuwa a gare ni, don kuwa babu wanda ya san sirrin rayuwata sai wata tsohuwar kakata wadda ta san duk salon mugunta sannan kuma tana da tsananin mugun fushi, ko da mafarki babu wanda ke son ya kusanceta, kai in takaice muku labari ba wanda ya isa ya je wurinta daga ni sai wata yarinya ‘yar'uwata sunanta Dailanu. Ita wannan tsohuwa ita ce shugaba a wurin bautarmu, kuma a wurinta ne asirin rayuwata ya ke, kun san kuwa raina yana cikin garkuwa mai wuyar karyawa. Wannan shi ne kadan daga cikin labarina,dondazan _ tsaya ba ku labarin yake-yaKen da na buga ne, to da sai “mu yi shekara ba mu gama ba.” . Bayan Sarkin aljanu ya kammala wannan labari nasa Www.bankinhausanovels.com.ng sai Nur ta ce, “Ya kai wannan Sarki mai tsananin Karfi, lallai babu shakka ranka yana cikin katanga, katangar kuwa mai tsabagen Karfi, saboda haka yanzu hankalina ya kwanta kuma na yi murna mai yawan gaske.” 

Tana gama fada masa haka cikin murna sai ta barke da waka, tana yi tana hadawa da sunansa sauran suna amsawa. 

Yamma ta yi, wato lokacin tafiyarsa, sai ya yi sallama da su ya koma kamar kullum cike da farin ciki. Bayan bacewarsa sai suka zauna suna ta labari gami da tunani. 

Ran nan dai ‘yan matan nan cikin bakin ciki suka kwana, saboda jin irin kariyar da ran wannan mugun aljani ke ciki, amma kuma daga baya suka tattara lamarinsu zuwa ga Allah, suka ci gaba da roKon Sa da Ya Kwace su. Sarkin aljanu Sham'una ya ci gaba da zuwa har ranar Juma'a. A ranar Asabar wasu daga cikin Musulmin ‘yan matan nan suna zaune suna karanta wata sura daga cikin Alkur'ani mai girma, sai ga aljana Dailanu. Tana isowa ta ji karatun nan sai hankalinta ya tashi, ta rude jikinta ya yi sanyi, taji ba abin da take so kamar karatun, saboda haka sai ta sami wuri ta koma gefe ta zauna har sai da suka gama. Kafin su kammala sai ga aljana tana hawaye saboda irin firgicin da karatun ya jefa mata. Suna gamawa sai suka ga Dailanu ba kamar kullum ba Www.bankinhausanovels.com.ng Hmm labari fa nata tafiya kudai kuci gaba da kasancewa damu Www.bankinhausanovels.com.ng 

Post a Comment for "YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 3 BY HARUNA USMAN"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...