THE NEW EMIR (SARAUTA) CHAPTER 3 BY NIMCYLUV - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

THE NEW EMIR (SARAUTA) CHAPTER 3 BY NIMCYLUV

THE NEW EMIR (SARAUTA) CHAPTER 3 BY NIMCYLUV

- - Post a Comment

 THE NEW EMIR (SARAUTA) CHAPTER 3 BY NIMCYLUV
Gaba ɗaya Fadawanne suka tsaya suna kallonsa cike da mamakin tsawar da yay masu,tsawar dako  Lil prince bai taɓa yi masu ita ba,tsawaya Prince yay tare da harɗe hannayensa yana jiran ƙarasuwar Saifu,Cikin taƙama da izza Saifu yake takawa zuwa gabansa,wata irin tafiya yake tamƙar ɗawisu ya zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa,yana ƙarasawa wajansu yaja ya tsaya kana yaja numfashi tare da lumshe idanunsa kana ya ware saman fuskar Kulsum wacce ke zube gabansu tana kuka tamkar ranta zai fita,taɓe baki yay tare da ɗauke kai daga kallonta,gyara tsaiwarsa yay tare dajan ma dai²cin gemunsa yace."Wannan fa?"ta tambaya yana mai ƙawar da kansa daga kallonsu tamkar bashine yay magana ba,daga bayansa yaji ance "nine ya kamata ka tambaya basu ba"juyawa yay ya kalli Lil prince wanda ya ƙarasa maganar cikin ɓacin rai,wani shegen murmushin gefen baki Saifu yay wanda ya haddasa lumawar beauty points ɗinsa tare da bayyanar gav teeth ɗinsa wacce take siririya,ɗauke kansa yay daga kallon Prince ba tare daya tankasa ba,gaba ɗaya hankalinsa ya mayar kan Fadawan yana jiran jin abinda zasu faɗa masa.Wani ƙwarjinsa ne ya ninku a idanun Fadawan jikinsu na rawa suka faɗi ƙasa tare da faɗin "Umarnine daga magajin Mai martaba,ya nemi ta fito da *Kuyanga Zarina* amma taƙi kuma an tabbatar da itane ta ɓoyeta"suka ƙare maganar suna kallon Kulsum,cikin kuka Kuslum ta shiga faɗin."tabbas ɗazu naga Zarina lkcn dana fitowa daga sashin wannan mutumin daga nan taje ɓangaren Zaitun a nan na fita na barsu"ta faɗa tana sharce majinar data silalo ta cikin hancin sbd tsabar kuka.Waro manyan idanunsa Saifu yay tare da juyasu kaɗan wanda hakan ba ƙaramin ƙyau suka ƙarawa fuskarsa ba,cikin zazzaƙar muryarsa mai ɗauke da nutsuwa yace "Ni!?"ya faɗa yana mai ɗan ɗaga muryarsa,domin bai fahimci yarinyar sa suke magana akanta ba,jinjina kai Kulsum tayi tace."eh! kai domin tun jiya muke nemanta bamu ganta ba,sbd ita baƙuwace a masarautar bilhas ba ko'ina ta sani ba,bayan gari ya waye nazu shiga sashinka domin kaima breakfast na haɗu da ita a hanya haka ya tabbatarmin da a wajanka ta ƙwana"Wani baƙin cikine ya kama Lil prince,babu abinda ya ɗaga masa hankali wai a wajansa ta ƙwana,gaba ɗaya ya ruɗe tsantsar kishinta ya bayyana a kan fuskarsa,tabbas sai yanzu ya tabbatar ba ƙaramin so ya kewa yarinyar ba,son da baiyi tunanin zaiwa wata ƴar mace irinsa ba,son daya kejin zai iyayin komai a kanta haka nan zai iya hqr da komai a kan ya mallaketa,kasa cewa komai sai numfashi daya shiga saukewa,Saifu kam sai yanzu ya fahimci yarinyar da suke magana a kai,to ina taje ina ta sani a wajan,mai yasa ma ya barta ta fita tana cikin hali na neman taimako,mai yasa ya kasa tausayinta bare har yayi tunanin taimakonta kamar yadda ta buƙata,shurun da yayine,yasa Fadawan ci gaba da jan Kulsum suka bar wajan.Taune laɓɓansa yay yana jin babu daɗi cikin ransa,tabbas bai nunata mata tausayi ba,kuma dukkan abinda ya sameta yana dasa hannu a ciki,dafashin da akai yasa ya buɗe sexcy eyes ɗinsa ya saukesu a kan fuskar Lil prince wanda yake tsaye gabansa yana fitar da numfashi,zame kafaɗarsa yay kana ya kalli Prince yace."Ka tsaya matsayinka na ɗan Sarkin Masarautar bilhas,shoulderna ba tsaranka bace gane ko?"ya faɗa yana ɗaga masa girarsa ta hango,baki Prince ya saki domin tunda yake babu wanda ya taɓa yi masa irin wannan maganar bare har yay tunanin muzuntashi gaban mutane,amma yau an wayi gare a cikin garinsa kuma masarautarsa wacce yake ta ƙama da ita,kuma a gabansa wani ƙato ya tsaya ya gaya masa magana ba tare daya ɗauki mataki ba,yana kallon Saifu yayi gaba yabarsa a wajan ba tare daya tanka saba.Wani baƙin ciki ne da kuma tsanar Saifu ne ya sauka cikin zuciyansa,kuma ya ɗauki alƙwari baƙanta ransa kamar yadda ya baƙanta masa nasa ran,sai yasa yayi ladamar abinda ya aiƙata masa a yanzu,saiya wulaƙantasa gaban jama'a haka nan saiya tuzartashi,sai ƙulla masa sharrin da bai iya ya shallaƙesa ba,da wannan tunanin ya juya ya nufi Fada ya ƙira wasu Fadawa a kansu suje su bincika masa ɗakin Zaitun ko Zarina na ciki,cikin rawar jiki suka kama hanya domin aiwarta da aiken na Lil prince,suna zuwa su kaga ƙofar a rufe nan suka shiga ƙoƙarin buɗewa abu ya gagara,abu kamar da wasa harya zama babba,saida Prince ya gaji da kansa yazu yana zuwa yasa aka kunce ƙofar,ana kunce ƙofar ya faɗa ciki,da sauri yaja da baya tare da juyawa waje yana fidda numfashi ya shiga nuna ɗakin da hannu ganin hakan yasa gaba ɗaya Fadawan suka shige cikin ɗakin,salatin suka shigayi ganin.
Ganinta yashe a ƙasa bakinta ya fashe jini na zuba ta jikinsa,da sauri suka ƙarasa cikin jarumta wani Bafade yaji ya taɓata tare da jijjigata yana kiran sunanta,amma shuru babu amsa nan suka tabbatar babu numfashi a jikinta domin harta fara kumbura,da hanzari suka fito da ita waje tare da rufeta da wani mayafinta,Lil prince gaba ɗaya brain ɗinsa tsayawa yayi da aiki yana tunanin abinda ya sameta daga jiya zuwa yau wanda yayi sanadiyar rasa ranta,juyawa yayi yabar wajan yana tunanin inda zaiga Zarina domin shi yanzu itane damuwarsa ba mutuwar Zaitun ba.Mai martaba yana zaune a Fada jikin shigarsa ta alfarma wacce take nuni da shiɗin tabbas Sarkine,sanye yake cikin Alƙyabba mai ruwan ƙwai,Kuyangunsa sai fifita suke masa tare dayi masa kirari wanda yake ƙarasashi girmankai da kuma jin shiɗin wanine,gefe guda kuma Captain Saifu tsaye a kansa yana danna waya daman duk sanda ya shigo harya fita ƙala baya cewa sai abu ya zama mai muhimmanci yake magana,cikin kiɗima Fadawan suka shigo cikin Fadar tare da zubewa a ƙasa suna yiwa  Mai martaba kirari,Sarkin Fadane yace "gaisheku bayi Mai martaba na godiya meke tafe daku?"ya ƙare maganar yana kallonsu,Numfashi suka sauke a tare kana ɗaya daga cikinsu yayi jarumtar faɗin "Tuba muke Mai martaba idan abinda zamu faɗa zai ɓata ranku,amma tabbas matsala ta fara faruwa cikin masarautar bilhas,wacce a tarihi ba'a taɓa samun irinta ba" ya ƙare maganar yana sadda kansa ƙasa alamar jinjina, Mai martaba jiyayi zuciyarsa ta bada sauti dam,domin baya burin ace a lkcn mulkinsa wani abu ya faru wanda ba'a saba ganinsa a cikin gidan Sarautar ba,Zubawa Fadawan idanu yayi ƙafin ya gyara zama yace "Eheem"hakan da yayi ya tabbatar masu yana buƙatar jin abinda ya faru,da Sauri Sarkin Fada yace "Ƙarya kuke ƴar ƴan talakawa babu wani abu dazai faru a wannan masarautar mai'adalci bada sanin Mai martaba,idan kuma aƙwai ku faɗa munajinku" cikin rawar murya da kuma tsoro wani bafade yace "munje sashin kuyangi domin neman Kuyanga Zarina,sai akace tana ɗakin Kugayan Zaitun,ba muyi ƙasa a guiwa ba,mu  kaje ɗakin amma abinda muka gani ha bamu tsoro domin gawar.."tarin da Saifu yayi ne ya dakatar dashi daga ƙarasa maganar.


Gaba ɗaya suka zuba masa idanu ganin da gske tarin yake,cikin sauri wani ya ɗauko gorar ruwa ya miƙa masa,bai amshi  ruwan ba,kana baice masu komai ba yasa kai ya fice daga cikin Fadar,gaba ɗaya sukabi bayansa da kallo hatta Mai martaba suna mamakin abinda yasa mood ɗinsa ya sauya lkc guda.


Saifu jiyayi zuciyarsa ta cunkushe gabansa ya faɗi ƙirjinsa ya bada wani sauti mai ɗauke da fargaba,jiyayi gaba ɗaya ya zama wani vry weak duk wani kuzari na jikinsa ya kau,babu a sannu tunaninta ya fara sauka cikin ƙwaƙwalwarsa,ina take ma yasa Prince yake nemanta,maita aikata garesa har haka,hannu yasa ya dafe kansa wanda ya soma juya masa,gawarwa suka gani wanda ya sasu tsorata,baidai ita bace domin yasan tabbas bata da lpa,wani zafi zuciyarsa tayi masa a karo na farko ya kasa taimako mace wanda hakan ba halinsa bane,bai san mene yasa ya kasa taimakonta ba,aduk lkcn da yayi tunanin zuwa gareta yana jin zuciyarsa na tsananta bugu fuskarta nayi masa ƙwarjini,yayi rayuwa a ƙasashe daban-daban amma bai taɓa cin ƙaro da macen data tsaya masa arai harya kejin fargabar zuwa gareta,sau biyu ya ganta amma yadda zuciyarsa ke matsa mata da tunaninsa saika ɗauka yayi shekara guda da saninta,ɗan ware manyan idanunsa yay wanda suka soma ƙanƙancewa sbd ciwon da kansa ke masa,a hankali gargasar jikinsa ta soma miƙewa wani sanyi ya fara ratsa ƙofofin jikinsa,ba tare daya san inda yake ɗura ƙafafunsa ba,a haka yake tafiya harya ƙarasu cikin kata faren lambun dake masarautar wanda ba kowa ne yake shigarsa ba,yana zuwa ya sami wata farar kujerar mai ƙyau da tsari wacce akaiwa ado da tambarin gidan sarautar,a ƙafe take ƙasan wata bishiyar guava,zama yayi tare tura duka hannayensa cikin ƙwantacciyar sumar kansa tare da hargitsata ya shiga fesar da wani zazzafan numfashi ta cikin bakinsa,cikin tattausar muryarsa wacce ta soma sauya kala yace “YES! I know her in my dream”.

Gaba ɗaya suka ɗauke kansu daga kallonsa kana sarkin fada yace "muna jinka waziri me kake cewa gawarwa kuka gani har kuka gigice?"numfashi Waziri ya sauke yace "ba gawar kowa bace face kuyanga Zaitun"da sauri Mai martaba ya ɗago kansa a rikice yace "What! Mene kuke faɗa Zaitun fa? Ko daren jiya mu...."sai kuma yay shuru mai ƙarasa abinda zaice,wani murmushi yayi mai ɗauke da ma'anoni mutuwarta shike tabbatar masa da aikinsa ya amso wajan boka,ƙara gyara zama yayi ya shafi  cikinsa,cikin ransa yace "nasan dole daki mutu"a zahiri kuma ya kalli waziri da sarkin fada yace "aje a nemi Fulanin sora da Kilishi da jakadiya suyi mata suttura"Waziri da sarkin fada suka miƙe tare da  nufar sashin Fulanin sora.A kishin giɗe suka zameta sai fita kuyangunta suke mata,tasha Alƙyabba tasu ta mata,gabanta kayan cimane kala² irinsu Dubulan,Alkaki,Bakilawa,Zuma,sai kuma dan ginsu fruit,suna zuwa suka zube gabanta tare da miƙa gaisuwarsu da kuma jinjinar ban girma,nan suka faɗa mata saƙon Mai martaba  saurin miƙewa tsaye tayi tare da rafka salati tace "ikon Allah jiya ta daɗe a nan gaba ɗayanta a rikice take ashe yarinyar nan alhine Ubangiji ya nuna mata mutuwarta,ikon Allah ya jiƙanta maza ka ɗauko gawarta zuwa nan sashin kana kuje ko faɗawa su Kilishi da jakadiya kada kuje wajan mai babban ɗakin itama ba lafiya gareta ba"Cikin gaggawa aka yiwa Zaitun wanka tare da shirya cikin likkafani,sannan akai waje da ita akai mata sallah kamar yadda addini ya kuyar,kana aka nufi da ita wata maƙabarta dake bayan gidan sarautar,abin mamaki dukkan kabarin da aka haƙa zai aga ruwa a cikinsa,daga ƙarshe aka sakata wani abin mamakin ana sakata acikin kabarin wani irin baƙin hayaƙi ya fito ta gabanta yay sama,gaba ɗaya wajan suka ɗauki salati,haka aka binneta sukai mata addu'a suka koma cikin masarauta.

Kamar a mafarki haka ta keji ana bugun ƙofar tamkar za'a ɓallata,a hankali ta shiga buɗe idanunta da sukai mata nauyin gske ga wani irin ciwo da kanta yake mata,miƙewa tayi zaune ta takure waje guda ta shiga rera kuka tare da kiran sunan Mom da sauran ƴan gidansu,tsagaitawa tayi da kukan jin bugun ƙofar ya ƙaro,a hankali ta lumshe idanunta cikin wata ajjiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi kana ta saki wata tattausan murmushi a lkcn da hawaye suka gangaro da  cikin idanunta,sosai ta rungome pillow ɗin dake kusanta,a hankali ƙyaƙƙyawar fuskarsa taci gaba da bayyana cikin eyes ball ɗinta,babu abinda yake ɗaukan hankali ya tafi da nutsuwarta ya dagula lissafinta irin faffaɗan ƙirjinsa wanda ya kasance a murɗe,a karo na biyu ta ƙara sakin murmushi,ƙara ta saki sabida fisgar da taji anyi mata,a kiɗime ta ɗaga jan idanunta ta sauke cikin na Lil prince,saurin ja baya tayi ganin idanunsa ya sauya jikinsa sai rawa yake,wani mugun murmushi yayi tare dayi mata rumfa,runtsa idanunta tayi sbd wani abu daya daki hancinta,ƙasa tayi sata gudu yayi saurin sanya mafa ya ta ɗeta ta faɗi ƙasa,kamar zautacce wanda ya rasa ƙwaƙwalwarsa ya nufi inda take tare da sanya hannunsa ya tura cikin..

Sumar kanta tare da jan long hair  ɗinta ya shiga janta har zuwa bakin bed ɗin,kuka ta saki tare da soma tirjewa amma dake ƙarfin namiji dana mace ba ɗaya bane tuni ya hankaɗata bisa makeken gadon tare dayin wani shu'umin murmushi yace "what the you thing tunanaki zaki ɓace min a gidan ubana kuma a masarautarmu? No! Beby kinyi kuskure kuma you pay for ur mistake know"yana faɗin hakan ya faɗa saman bed ɗin tare da fisgota ta faɗa jikinsa,wani kukan ta saki ta shiga ruƙansa akan ba zata sake ba,dukkan abinda yace za tayi,banda rawa babu abinda jikinta keyi wani tsoransa ya kamata dan gani take tamkar zai cuceta,musamman yadda take ganin rashin imani tattare dashi,zuba idanu yayi tare da dakatawa da abinda yake,a ƙaro na biyu ya gagara yin abinda yake sonyi mene yasa,mai yasa yake jin wani iri game da ita,kodai da gske sonta yake shine yasa ya kasa cutar da ita?idanunsa ya buɗe tare da murza ƙasan mararta wanda yake jin gashi ƙwance luff ga laushi ƙwanin sha'awa,kallonta yayi murya babu wasa yace "mene yasa kika ƙwana ɗakin wani,to daya lalataki gwamma ni na amshi budurcinki a banza tunda tallansa kike wa wani"ya ƙare maganar yana mirginata ƙasa,jikin tane ta ɗauki rawa wani tsoransa ya daɗa kamata,wai yau ita wani ke ƙoƙarin haɗa jiki da ita,tunda take babu wani namiji daya taɓa riƙe hannunta bare yayi tunanin aikata wani abu da ita,amma itane zai kallah yace tana tallan jikinta,God forbid da tayi irin wannan rayuwar ƙwara Allah ya ɗauki ranta,ta tsani zini haka nan ta tsani mai kusantarta,jin yana ƙoƙarin tura hannunsa zuwa samanta,yasa tayi sauri riƙe hannunsa tare da faɗin.


"Ubangiji yayi hani da abinda kake ƙoƙarin aikatawa gareni,dan Allah kada ka tuzarta rayuwata Prince,na roƙeka ka faɗin abinda kakeso nayi maka banda wannan abun"ta ƙare mgnar tana haɗa hannayenta waje guda alamar roƙo.

Zare hannunsa yayi daga cikin rigarta,a hankali yasa hannu ya shafi gefen fuskarta yace "ki amince da aurena,shine zaisa ki kuɓuta daga gareni,ki soni tamkar yadda nake sonki,kana ki kiyaye haɗuwar da wannan banzan guy ɗin idan ba haka ba,dake dashi zan manna maku hauka,zai jawo maki lukutar masifa"ya ƙare maganar yana ɗaga murya,runtsa idanunta tayi domin ba taji zata iya abinda ya keso,sai dai a ace ta aikata zini gwamma ta amince buƙatarsa koda bata sonsa,daga baya ta kuyawa zuciyarta sonshi,tasan idan ta aureshi yana da haƙƙi a kanta sannan ubangiji bazai kamata da laifin komai ba,amma tayaya zata iya zama aure dashi bashi da bakusa yana da ƙyau dai² shi,amma bata san halinsa tana tsoro ace shiɗin ma nemin mata ne kamar yadda halinsa yake son bayyana a gareta yanzu,shurun da tayi ne yasa zuciyarsa halɓawa dan bazai juri rashin amince a gareta,sosai gangar jikinsa keson kasan cewa da ita,bai son aikata komai daga gareta yana son ya mallaketa as his wife,so dole ya ajjiye taurin kai da izzarsa ya tura mata sonsa,idan yazu yaje wajan wasu matan ya rage zafi,ƙara matsawa yayi jikinta tayi saurin janyewa kallonta yayi yace "ohh baki amince ba? Ok kishirya amsata a yau"yana faɗin hakan ya miƙe zai bar ɗankin tayi saurin faɗin "A'a na amince"jinjina kai yayi yace "good ki shirya zanzo zance anjima"yana faɗin hakan yasa kai ya fice a ɗakin.


Durƙushewa tayi wajan tana sakin kuka mai tsoma zuciya,wani baƙin ciki da ɗaci ta keji a ranta,amma babu inda za taje taji daɗi babu mai rarrashinta,babu wanda za taji ɗumin jikinsa bare ta samu nutsuwa,a hankali ta murza daimond ring ɗin hannunta ta kai masa sumba,kana ta ƙanƙame hannun a ƙirjinta,ta shiga sauke ajjiyar zuciya shine kaɗai ya rage mata shine abinda zata kallah taji daɗi.


Tana zaune wata Hadima ta shigo hannunta ɗauke da wata Alƙyabba mai sulɓi mara,zai kayan ƙwalliya dasu parfumes,tana zuwa ta ajjiye kayan gefen Zarina tace "Sannu Zarina ki daina kuka Allah yasa mutuwar itane hutu gareta tabbas munyi rashin Zaitun mace mai kirki ga hqr"ya ƙare zancen idanunta na kawo ruwa.


A kiɗime Zarina ta miƙe tsaye tare da kallon Hadimar cikin rashin fahimtar,dan ta gaza gane wacce Zaitun ɗince take magana akai,cikin tashin hankali ta shaƙi wuyan matar tare da faɗin"wacce Zaitun kike magana akai ba,badai ƴar uwata Zaitun kike fara ta rasu ba,dan Allah kice mafalkine ba gsky ba,dan Allah ki barni haka kada kisa zuciyata ta buga"ta ƙare maganar tana saki kuka tare da zubewa wajan,Cikin rarrashi Hadimar tace "Sai hqr ai dukkan mai rai mamaci ne,ita lkcn tane yayi yanzu"ta ƙare maganar tana rarrshin Zarina.


Shuru Zarina tayi gaba ɗaya tunaninta ne ya tsaya,mene yayi sanadiyar rasuwar Zaitun?,kenan dukkan maganar da sukai matsayin wasiya ce?tayaya zata ruguza Masarautar bilhas?sauri kallon ring ɗin hannunta tayi ganin yayi wani sheƙi,ganin kanta na juyawa sbd yawan tunani yasa ta takire waje guda,nayin yadda jikinta yake babu ƙwari ga  fever da ciwon kai dake jikinta yasa gaba ɗaya jikinta ya saki bacci yayi gaba da ita.
    *_Kogi_*
Wajan ƙwana biyar kenan da ɓatan Zarina,a washe garin data ɓata Abba ya dawo cikin tashin hankali ƙwana daya kenan dajin ɓatan ta,amma gaba ɗaya ga fita hayyacinsa,ya rafe sosai,dukkan inda suke tunanin ganinta sun bincika shuru babu ita babu mai kamarta,Mom kocin abinci sai Mamu ta  matsa mata ta keci,an maza taimako masallatai da makarantu sai saukar alkur'ani ake.


Tafiya suke su uku Mom Abba sai Mamu,ana haka wata goguwa mai ƙarfin gaske tazu ta rufesu gaba ɗayansu,gaba ɗaya suka tsorata Abba ne kawai mai dauriyar cikinsu gaba ɗaya ya rungomesu jikinsa ya shiga salati yana kallon ikon Allah,a hankali goguwar ta shiga riki ɗewa tana komawa wata siffa,cikin abinda baifi ƙiftawar idanu ba,goguwar ta rikiɗe ta koma wani jibgegen ƙaton baƙin dodo,wata dry dodon yayi kafin ya buɗe hannunsa saiga wata ƙyaƙƙywar rayinya ta faɗo,da sauri Mom ta ƙwala ƙara tare da faɗin
         “Zarina”
Da sauri Abba ya shigo bedroom ɗin jin yadda matar tasa ta saki ƙara,yana shiga ya gan ƙwance zufa sa yanko mata take,ga yadda take miƙa hannu tana son kama wani abu,numfashi ya saki yana mai jin tausayin kansu domin duk su biyun Zarina itane rauninsu,rashinta babbar illace ga zuciyoyinsu a hankali ya taka zuwa wajan bed ɗin da take ƙwance,yana suwa ya sanya hannunsa ya jawota jikinsa ya shiga tofa mata addu'a,kuka ta fashe dashi tare ƙanƙamesa,kanta ya shafa a hankali yace.

"ashe baza kiyi hqr ki yarda ta ƙaddara ba,kefa musulmace my dear hqr zamuyi mu amshi ƙaddararmu da hannu biyu muci gaba da addu'a Allah ya bayyana mana our luv Zarina insha Allah  Ubangiji zai kareta da kariyarsa"ta ƙare maganar yana bubbuga bayanta,kallonsa tayi da murya wacce taci kuka tace "amma my dear tayaya hankali na zai ƙwanta ina ganin Luv cikin ƙuncin rayuwa,wannan mafarkin da nayi ya tabbatarmin da Zarina bata cikin ƙwanciyar hankali,bata da nutsuwa wannan wacce iriyar lukutin tashin hankali ne,ina jin tsoro bansan wane hali ɗiyata ke ciki ba,gasu Sufyan wannan garin da sukaje ƙwantar da tarzoma ba'a iya samunsu ya rabb ka kawo mana mafita"ta ƙare maganar tana ƙara maƙalesa kamar ƙaramar yarinya.


"Ameen"shine abinda Abba yace kana ya laƙaci hancinta yace "rigimatu zanje guest room i have a specail quest ki kula da kanki"ya faɗa yana peak ɗin lips ɗinta,da kallo ta bishi kana ta miƙe ta nufi toilet domin yin alwalar sallar asar.

Abbana na fita ya isa guest room ɗinsa,da sassarfa ya ƙarasa ganin mutumin da baiyi tunanin gani ba,yana zuwa wajansa ya zube ƙasa sbd bashi girmansa,dry Al'mustapha yayi kana yasa hannu ya ɗaga Abba yace.

"haba Abdallah mekenan hakan saika saka na bar maka gidan ai"ya ƙare maganar yana murmushinsu na manya,cikin girmamawa Abba yace "Uncle ya hanya banyi tunanin ganinka ba,yaushe ka sauka daga Cameroon,ina yarona yaya yake?"Abba ya jera masa wannan tambayoyin cike da farin cikin ganinsa.

Murmushi Al'mustapha yayi tare da zaro wayarsa daga cikin aljihu yace "Lafia Allahamdullah,jiya na sauka wani aiki ya kawoni nan Kogi shine naga ya dace na shigo,Yaronka ya daɗe da sauka a Nigeria ai barima na kirasa najisa yau shuru"ya ƙare maganar yana dailing numbers.
*_Bilhas_*
Misalin ƙarfe 4 na yamma Hadima batul ta shirya Zarina cikin wani haɗaɗɗan lafawa mai ruwan milk sai green ɗin flowers a jikin lafaya kana ta yarfa mata wata light make up mai ƙyau,kana ta feshata da wani haɗaɗɗan parfume mai ƙamshi da kuma sanyi,ita dai Zarina da idanu kawai take kallon  Batul,amma ƙasan zuciyarta tana jin wani baƙin ciki da raɗaɗi sosai zuciyarta keta fasa,Hadima batul tana gamawa ta kalli Zarina tace.

"Masha Allah Ubangiji yayi halitta a nan,Allah yasa ki zama silar gyara komai na wannan Masarautar mai Albarka"kallonta kawai Zarina tayi a zuciyarta tana son tambayarta wani abu game da Lil prince amma laɓɓanta sunyi mata nauyin gaske bata jin zata iya cewa wani abu a yadda ta keji zuciyarta na zafi,kama hannunta Batul tayi tare da janta zuwa waje suna tafe tace "Prince bashi da wata matsala ki amshesa matsayin miji za kiji daɗi,kinga idan kika zama Fulani nima kaina zan huta sai a ƴanta ni ko"ta ƙare maganar tana sakin dry,Zarina idanunta ta sauke a kan wata ƙyaƙƙyawar ƙofa wacce zata sadaka da wani sashi,sosai yanayin wajan yayi mata ƙyau a idanunta,musamman yanayin tsarin wajan da aka ƙawata da zallar a zurfa da goal,tsayawa tayi tare da ƙorawa wajan idanu,Batul itama kallon wajan tayi sannan tace "Hajia mai babban ɗaki kenan,mutuniyar arziƙi nan sashinta ne ba kowa ke zuwa ba,Allah sarki tana cikin halin damuwa,ba komai na sani game da ita ba,dana baki labari,amma ana tunanin kamar Mai martaba ne yasa aka....,"sauri toshe bakinta tayi sbd ba tayi tunanin maganar zata kufce mata ba,ajjiyar zuciya ta saki tace "wai Allah ya soni wannan baki nawa bashi da lunzami gaba ɗaya"ita dai Zarina bata kulata ba sai kallon sashin kawai take tare nanata sunan Mai babban ɗaki a ranta,tana son zuwa nan tabbas kuma dole na nemi mafita,amma tayaya?Murmushi tayi tace.
“Lil prince”
Ci gaba da tafiya suka har Hadima batul ta saki wata hanya ta nufi wani wajan da ban,sbd Prince yayi mata kashe din kana da sake tabi ta hanyar Fada,a dai² wata haɗaɗɗiyar ƙofa ta Ƙara ta tsaya,kana ta dubi Zarina tace.

"lambu kenan nan shine wajan da Prince yafiso dan haka maza shiga ciki yana zaman jiranki"tana faɗin hakan tayi saurin juyawa tabar wajan.

Zarina ji tayi gabanta ya faɗi,amma kuma son shiga wajan ya ɗarsu a zuciyarta musamman jin ta ambaci sunan lambu,wata iska mai daɗice ta fara ratsa jikinta,wani sanyi ya sauka cikin zuciyarta,a hankali ta lumshe idanunta tare da buɗe hancinta ta shiga shaƙar ƙamshin furannin wajan,wajan 5minutes ta ware eyes ball ɗinta ta zubasu cikin lambun wani murmushi ta saki ganin shuke² kala² a wajan ga yadda flowers keta kaɗawa sunyi green abin sha'awa ka sancewar yanayi ne na rani lkcn sanyi lkcn da ƴar ƴan marmari ke bozu tare da yaɗu,cikin shauƙin daya sameta ta ɗaga ƙarfta tare da tura kanta cikin lambun ta shiga ware manyan idanun tare da tunanin inda zata gansa,ganin ba taga kowa ba yasa ta ƙara tura kanta ciki tare da suma jujjuya kanta,can ta hangesa zaune akan wata babbar ladduma mai laushi ƙasan bishiyar gauva,sadda kanta ƙasa tayi ta shiga wasa da yatsunta.

Tunda ya zauna ƙasan bishiyar gauva yake tunanin wacce akace ta rasu,kasa samun nutsuwa yayi,duk wani tunani nasa ya tsaya,bawai ya damu da ita bane,A'a baya son ya zama silar rasuwarta domin ya gaza taimaka mata a lkcn data buƙaci hakan,lumshe idanunsa yayi tare ta shafa bear ɗinsa wanda yake dai² da fuskarsa,a hankali fuskarta ta fara bayyana lips ɗinta ya zuba idanu ta ciki idanunsa inda fuskarta take zuwar masa,ganin tana ta mamul² da laɓɓanta tamkar zata cinyesu gaba ɗaya ta jiƙasu da saliva,tsigar jikinsa ne ya tashi yanayinsa ya fara sauyawa,yana nan zaune aka kira sallar azhar,miƙewa yayi tare da fita zuwa sashinsa yayi wanka tare da sauya kaya,kana yayi alwala ya ɗauki ladduma tare da wayoyinsa,sai ya ɗauki vanillah da alkaki da cake,sbd ba komai yake iyaci ba,gaba ɗaya abinci mai damesa ba baya tsarinsa,jin jikinsa ya lafe tamkar zai haɗe da bayansa yasa ya ɗauki wannan,yana ɗauka ya rufe sashin ya ƙara dawowa cikin lambun a nan yayi sallar kana ya buɗe vanillah ya soma sha a hankali ya zubawa ring ɗin hannunsa idanu,yana mamaki yadda kullum yake ƙara sheƙi a ƴan ƙwana biyun nan,yana wajan aka kira asar a nan ya gabafatar sannan ya kira best friend ɗinsa suka gaisa,bayan sun gaisa ya kashe wayar ya lumshe idanunsa tare da shafar mararsa wacce take yi masa ciwo sama²,ji yayi zuciyarsa ta buga da ƙarfi gudunta ya ƙaro,ga wani sanyi dake ratsa cikin zuciyartasa wanda ya saukar masa sa kasala,tabbas tana kusansa banda ita babu wani wanda ya kejin wannan mood a kansa,a hankali ya buɗe fitinannun idanunsa tare da zubawa ƙofar wajan idanu,a tsaye ya ganta ta sunkuyar da kai,tana wasa da ƴan yatsunta,taɓe baki yayi tare da ɗauke idanunsa daga gareta,a hankali ya miƙe tsaye tare da zuba hannunsa cikin aljihu,cikin nutsuwar data gama ratsa jikinsa ya soma takawa zuwa inda take tsaye,jin numfashi na dokan fuskarta ga wani daddaɗan ƙamshi dake kawowa hancinta ziyara,a hankali ta lumshe idanunta tare da ƙara buɗe hancinta ta shiga shaƙar ƙamshin turaren dake jikinsa,zuba mata idanu yayi tare ƙurawa laɓɓanta idanu,a dai² lkcn wayarsa ta fara ringing taɓe baki yayi tare dajan siririn tsaki,wayar ya zaro a aljihunsa ganin sunan Abbunsa na yawo saman makeken screen ɗin wayarsa yasa cikin so da ƙauna yayi picking call,tare lumshe idanunsa cikin zazzaƙar muryarsa yace "Abbuna nayi kewarka harna gaji"ya ƙare maganar yana shafa cikinsa,saukar muryarsa cikin kunnanta yasa tayi sauri buɗe idanunta domin ta tabbatar wannan muryar bata Prince bace,idanunta ne ya sauka cikin nasa,wata harara ya watsa mata wacce tayi saurin sanyasa ta sunkuyar da kanta tare da juyawa zata bar wajan yayi saurin sanya tattausan hannunsa ya riƙe nata hannu haɗe da jawota zuwa gabansa.
Kafeta yayi da idanunsa wanda suke a lumshe, kafin ya ɗauke idanunsa daga gareta,hannunta ɗayan ya kama ya sanya wayarsa akai kana ya saka wayan a speaker,ɗan jan gefensa yay kafin ya ciji lips ɗinsa na ƙasa yace "Abbuna nine ka ɓoyewa zuwanka 9ja,nayi fushi"ya ƙare maganar yana murza tafin hannunta,wanda yake fidda gomi kaɗan² hakan yasa yaji daɗin riƙe hannunta,musamman yadda bai jin daɗin jikinsa daga jiya zuwa yau,lumshe idanunsa yayi yana sauraran abinda Abbunsa ke faɗa masa ta cikin wayan,ɗan turo bakinsa yayi gaba tare da girgiza kai alamar "A'a" tamkar daɗi na kusanshi,can ya saki tattausar murmushi ya ƙare matse hannunta dake cikin nasa wanda yasa ta saki ƙara sbd zafin da taji,idanunsa ya zuba mata tare da juya mata idanunsa ya ɗaga gira ɗaya alamar "mene?"sadda kanta tayi sbd wani ƙwarjini da yayi mata, ba tajin zata iyaci gaba da tsaiwa kusanshi sbd yadda zuciyarsa ke gudu ga wani ɓari da jikinta keyi,wani irin abu ya fara yi mata yawo cikin jiki,da dukkan alamu mood ɗinta ne ya fara sauyawa,hakan yasa ta fara ƙoƙarin ƙwace hannunta daga cikin nasa,jin yadda take ƙoƙarin ƙwace hannunta daga nashi yasa ya lumshe idanunsa,ba tayi aune ba taji ya jawota jikinsa tare da ɗura hannunsa a waist ɗinta,can ƙasan maƙoshi yace "Abbuna kace yau ziyara kayi daga saukarka,ok Allah ya bada lada"jinjina kai yayi tare da faɗin "ok kai gaidashi luv you bye"ya faɗa yana sakar masa sumba ta wayar kana ya ƙatse kiran tare da cillah wayan cikin aljihunsa,zazzafan numfashi ya fesar ta bakinsa kana ya zareta daga jikinsa tare da ɗauke hannunsa daga waist ɗinta,wasu minutes suka ƙwashe a haka kafin ya zubawa hannunta idanun tare da kama hannunta ya haɗa da nasa nan take wani haske mai ƙyalli da sheƙi ya bayyana wanda yayi sanadiyar rufewar idanunsa,a hankali ta shiga ɗaga zara-zaran eyes lashis ɗinta wanda suka sha maskara sukai ƙwance luff saman fuskarta,zuciyarta ce ta buga da ƙarfi sakamaƙon  ƙyaƙƙyawar fuskarsa data bayyana cikin eyes ball ɗinta,wani ƙwarjini da haibarsa ne suka cika idanunsa kasa jure kallonsa tayi sai sadda kanta ƙasa tare da zubawa hannunsa ido,sosai ta tsorata ganin the same ring ɗinta a hannunsa,ƙara zubawa ring ɗin idanu tayi cikin *AL'AJABI* ta ɗura hannunta saman yatsansa ta shiga murzawa,yadda take murza hannunsa yasa shi dawowa cikin hayyacinsa zare hannunsa yay daga cikin nata tare da janye jikinsa daga kusancin da sukai,ba tare daya ce mata komai ya juyawa zuwa inda laddumarsa take,yana zuwa ya ƙwashe komai nasa,cikin isa da gadara haɗi da izza ya bar cikin lambun,bayansa tabi da kallon dukkan yadda tasu ta ƙara ganin ƙyaƙƙyawar fuskarsa haɗi da ganin zoben hannunsa amma ta gagara yin hakan,a hankali wasu hawaye suka ziraro daga cikin idanunta,tabbas yana da banbancin da sauran mazan shiɗin gwarzone kuma jajirtacce mai aiki da iliminsa,amma halinsa ba kowa zai iya juresa ba,a ɗan tsaiwar da tayi dashi ta fahimci shiɗin mutum ne wanda mgn bata damesa ba,yana da miskilanci wanda yake ƙara masa ƙyau da ƙwarjini,sannan yana da waskiya sosai ta fashimci kallon da yake mata,amma data ɗaga idanu zai ɗauke kansa tare da haɗe rai ya wani taɓa fuska shi a dole baiyi wani abuba,tana nan a tsaye harya ɓacewa idanunta,wani murmushi ta saki tare da lumshe idanunta kana ta ware laɓɓanta tace 
     “HEART DREAM”
Ganinsa ya tayar mata da abubuwa kala² a zuciya,zuwa yanzu babu wanda take buri da ƙaunar gani sama dashi,kallo guda da tayi masa taji tana ƙauna da muradin zama dashi,sam miskilancinsa bai dameta ba,kanta ta samu da tambayar wanene shi a Masarautar bilhas ko shime yareema ne?idan har hakane tabbas suna da banbanci da Lil prince domin halayyarsu a fili ta banbanta,kujerar kusa da ita ta zaune wacce ta kasance ƙarƙashin bishiyar fasadabir,wanda yayi manyan-manya yay jaa sbd nunar da yayi,samun kanta tayi da sha'awar shan Fasadabir ɗin,a hankali ta miƙe tare da ɗaga hannunta ta cire guda ɗaya,soma juyashi tayi a hannunta ganin harya fara tsagewa sabida nuna,wajan kujerar ta koma ta zauna tare da soma shan Fasadabir ɗin har wani lumshe idanu take dan dani,wanda a zuciyarta kuma tunanin Saifudeen ne fal ranta.


Saifudeen cikin nutsuwa da kuzari haɗi da jarumta yaci gaba da tafiya a cikin masarautar,dukkan inda ya ratsa Barori da kuyangu haɗi Hadimai ne,kowa yana aikinsa,wasu an ƴantasu wasu kuma haryau bauta suke tamkar ba mutane ba,a haka yaci gaba da tafiya harya isa sashinsa yana shiga,ya ajjiye komai dake hannunsa a mazauninsa,zubewa yayi  akan italian bed ɗinta tare da jawo pillow ya rungome ya shiga sauke ajjiyar zuciyar kamar karamin ƙaramin yaron da yayi tsere,baisan meke damunsa ba a ƙwana biyunan,amma ya samu kansa dason fahimtar abinda ke faruwa a wannan masarautar,A ranar daya sauka ya sameta zata bar gidan sarautar kamar mahaukaciya,a karo na biyu yaga Fadawa najan Kulsum,abu na uku ga yadda Zaitun ta rasa ranta kuma ya tabbatar ba haka nan ta rasa ran nata ba,ko lkcn tane yayi babu shakka aƙwai silan rasuwan nata,babban tashin hankalin bai huce maganar da yaji Mai martaba ya nayi game da Mai babban ɗaki ba,wacce har yau ya kasa fahimtar wace Mai babban ɗakin,mai yasa ya keson aikata hakan gareta shine tambayar da yakewa kansa daga jiya zuwa yau amma ya kasa samun amsarta,kuma ya ɗaukarwa kansa alƙawari kare rayuwarta haka nan dole ya binciki wanne sashi ne nata daga cikin flats ɗin gidan sarautar.

Da wannan tunanin ya miƙe tare da faɗawa bathroom,ruwa mai zafi ya haɗa a cikin jakuzzi,ka sancewar yanayin garin aƙwai sanyi ga kuma iska mai ƙarfi dake kaɗawa tamkar za'ai ruwan sama,kayansa ya cire tare da ratayesu saman hanger kana ya shiga cikin jakuzzi'n,sannu a hankali yake shigewa jikin ruwan zafin tare da ware laps ɗinsa ruwa na ratsa mararsa dake masa ciwo,lumshe sexcy eyes ɗinsa yayi tare da sanya hannunsa ya shafi saman mararsa wacce ta ɗan kumbura,cije laɓɓansa yayi sbd zafi da raɗaɗin daya saukar masa,ƙara nutsewa yayi cikin ruwan sosai zafin ruwan yake ƙara masa kuzari,wata nauyayyiyar ajjiyar zuciya ya sauke kana ya murza zobensa cikin so da ƙauna ya manna masa kiss,zuwa yanzu yama manta da cewa ya ganta cikin lambu,daman burinsa bai huce ya tabbatar da lafiyarta ba,a yadda ya ganta tasha ado kamar wata gimbiya ko sarauniya yasan cewa tabbas ta samu lafiya,ya ɗauki lkc mai tsayi cikin ruwan kafi ya soma wankan yana kammalawa ya ɗauki bathrope ya sanya a jikinsa,kana yayi brush tare da ɗaura al'wala,domin haka tsarinsa yake baya taɓa zama babu al'alwa domin ita kanta kariyace ga mutum,yana gamawa ya fito tare da zama kan dressing mirrow ya juna handrayer  ya soma busar da somar kansa,yana kammalawa ya ɗauki body lotion mai ƙamshi da kuma daɗi a jiki ya soma shafawa chocolate naked body ɗinsa mai ɗaukar idanu,bayan ya kammala ne ya ɗauki body spary ya feshe jikinsa dashi,a ɗan gaggauce ya buɗe wadrope ya ɗauki uniform ɗinsa da wando da rigar haɗi da ficap ɗin ya sanya,wow amy colour ya haɗu da chocolate skin ga yadda sumar kansa ta ƙwanta har wuyansa luff sai sheƙi take,ta ƙara fiddo da asalin ƙyan na baƙin balarabe,sosai murɗaɗɗan jikinsa ya amshi kakakin sojoji,a wannan lkcn ko namijine ya kallesa sai zuciyarsa ta buga,balle ƴan mata masu ƙarancin shekaru irinsu Zarina wanda suke Adult,masu tashan balaga wanda yanzu ne lkcn da budurcinsu ke bayyana suke jin kansu tamkar wasu manya,wajan dressing mirrow'n ya dawo kana ya ɗauki turarensa Ohud mood ya goga a jikinsa,sannan ya ƙwashi wayoyinsa da key ɗin motarsa tare da rufe ƙofar sashin ya nufi hanyar Fada.


Dake yau zamane na sirri wanda Lil prince ya nema wajan Mai maryaba yasa babu mutane da yawa a Fada sai Mai martaba,Tiraki,Sarkin fada,waziri,Sai kuma Lil prince dake durƙushe gaban mahaifin nasa yana son ya bashi damar magana,sbd gaba ɗaya hankalinsa yayi kan Zarina kuma ya tabbatar yanxu Hadima Batul ta kaita lambu shi kawai take jira..

Gyara zama Mai martaba yayi kana yayi gyaran murya a hankali yace "muna sauraranka meke tafe dakai haka Magaji?"ya cilla masa tambayar yaname fahimtar yanayinsa,ƙara sunkuyar dakai Prince yayi cikin dakiya da kuma maida fargabar dake ransa yace.


"Allah ya ƙara maka lafiya da yawan rai daman ina neman kabani dama domin na fiddo da macen da nakeso na aura,domin ina son ajjiye iyali"ya ƙare maganar yana zubawa Mai martaba idanu.


Jinjina kai Mai martaba yayi kafin yayi shuru alamar tunani,wajan sama da 5minutes kafin ya ɗago ya kalli prince yace "Muma zamu so hakan domin mutuncinmu ne zai ƙaro idanun jama'a ace yau Magaji zai ajjiye iyali Thank God,amma kafin nan ,zanso nasan wacece Fulani mai jiran gado?"ya ƙare maganar yana sakin murmushi alamar jin daɗi,Murmushin ƙarfin hali Prince yayi kana yace "Godiya  nake ya Abbana,daman ba wata bace face *Kuyanga Zarina* ita nake muradin ƙauna na kasance da ita *ABADAN DA'IMAN* ina fatan zaka bani damar hakan?"ya ƙarashe maganar kansa a ƙasa,Saifudeen dake bakin ƙofar yana ƙoƙarin shigowa yayi saurin tsaya tare da sanya hannu ya dafe saitin zuciyarsa,wani ɗan radaɗi da zafin da yaji tayi masane yasashi runtsa idanunsa,cikin narkakkiyar murya yace "Ya rabb help me"ya ƙare maganar yana jin gina bayansa da jikin ƙofar ya harɗe hannayensa a faffaɗan ƙirjinsa,ya zubawa Prince ƙanƙantattun idanunsa.
Mai martaba jin maganar  Prince yayi tamkar ruwan sama wanda ba'a shirya masa yake sauka,tabbas abinda Magaji ke nema babban abune,baya tunanin ƙalubalan dake gabansu,yasan cewa baza'a taɓa yadda Prince ya hau karagar mulki ba tare daya nuna shaidu guda uku wanda dasu ne aka lamunce munce a ɗana mutum as King of Bilhas,amma shi ya fahimci ba wanne a ransa ba,yaushe Prince ya faɗa soyayyarsa baiwarsa,ya manta cewa auren baiwarsa ya haramta a garesa,wata zuface ta shiga karyowa Mai martaba,wani huci ya fitar mai zafi,kana ya kalli Prince yace "Are you mad,ashe baka da tunani Magaji how baiwarka zata zama matarka kuma Fulanin bilhas you're vry stopid kama sauya wannan banzan tunanin naka mara amfani,idan ba haka ba...."sai kuma yayi shuru ya ƙarasa maganar sbd idanu huɗu da sukai da Saifudeen,maida hankalinsa yayi kan Prince yace "Get out!"ya ƙare maganar yana ɗan ɗaga murya,wani  baƙin ciki ne suka sauka zuciyar Prince sbd baiyi tunanin hakan ba,duk da cewa da wahala ya amince amma baiyi tunanin zai kasa amince masa ya samu abinda yake buƙata ba,a karon farko ya tambayi abu wajan Mai martaba amma ya kasa samu,cikin ɓacin rai ya miƙe tare da fice daga Fadar,tsayawa yayi wajan  Saifu tare dajan tsaki yace "YOU?"sai kuma ya jinjina kai tare da ficewa daga cikin Fadar,ko inda Lambun yake bai kallah ba sbd yadda ya kejin zuciyarsa babu daɗi,yana zuwa harabar gidan direct motar ya faɗa ya jata da wani irin gudu ya nufi N.S University.


Saifu dry ya kusa yi amma sbd dry baya tsarinsa infact ma bai saba yinta ba,yasa ya saki wani shu'umin murmushi tare dajan gemunsa ya shafi cikinsa,a hankali ya ƙarasa cikin Fadar tare da zama ya fuskanci Mai martaba kana ya sunkuyar dakai ƙasa ba tare da yace komai ba,Sarkin Fadane ya dubesa yace "Ɗan samari da alama kana son cewa wani abu ko?"Sarkin fada ya faɗa yana kallon Saifu,sai a lkcn Saifu ya buɗe gajiyayyun idanunsa ba tare daya kalli Sarki fada ba,yace "Barka da hutawa Mai martaba"ya ƙare maganar yana sauke numfashi sbd tsayi da maganar tayi masa,baya iya jure magana indai bada Abbunsa ba,Kallonsa Mai martaba yayi yana jinjina ƙarfin miskilancin Saifu,ɗauke wannan tunanin yayi daga ransa kana yace"Saifu ka shirya yau zaka zaɓi Maid mai kula da ɓangaranka"yana gama faɗin hakan ya tura Waziri yace"kaje kasa ayi shela dukkan Kuyangun da ma'a basu aiki ba su fito yanzu"da sauri waziri ya miƙe tare da nufar waje domin ai watar da abinda Mai martaba ya umarce shi.


Zarina ta daɗe zaune a wajan harta shanye Fasadabir ɗin dake hannunta,bayan ta kammala ne ta miƙe tsaye tare da soma zagayawa cikin lambun sbd gajiyar da tayi,cikin nutsuwa take zagayen lambun tana kallon yadda shukokin wajan tare da flowers dake kaɗawa a wajan,komai na wajan birgeta yake a hankali ta shiga tsakanin wasu manyan bishiyo sbd daddaɗar iskan wajan dake kaɗawa,ɗan juyawa tayi jin kayanta ya  riƙe wani abu,murmushi ta saki ganin wata tsuhuwar aƙwati tana isa ta zare kayanta,har zata huce sai kuma ta samu kanta da buɗe aƙwatin nan tayi arba da wata ƙyaƙƙyawar takubi haɗi da wata hular zallar azurfa sai sheƙi take,sosai take kallon takubin haɗi da hular wanda kana ganinsu kasan na musammane,samun kanta tayi dasun adanasu dan haka ta hangi wani rami mai zurfi tana zuwa ta ɗauki aƙwatin tare da sakata ciki,kana ta shiga maida ƙasa saida ta cike ramin tas ta baje ƙasar wajan,sannan ta zauna kan kujera tana sauke numfashin gajiya,ta daɗe a wajan sosai sannan ta fara jiyo shelan neman dukkan sabbin kuyangun masarautar,zuciyata ce ta buga da ƙarfin gaske wata fargaba da tsoro ya dirar mata a zuciya,da hanzari da miƙe tare komawa sashin da aka sauketa tana zuwa ta cire kayan jikinta tare da watsa ruwa tana gamawa ta nemi fararan kayanta ta sanya,jikinta na zubar da ruwa ta sanya flat shoe ɗinta ta nufi harabar masarautar domin amsa kira.


Lil prince's pov
Yana isa Universty'n babu inda ya tsaya sai office ɗin Yazeed yana zuwa yayi knoking nan aka bashi umarnin shiga,yana shiga ya nemi waje ya zaune akan wata duguwar sofa dake office ɗin,dry Murmushi Yazeed yayi cikin shaƙiyanci yace "banyi expecting  ganinka ba at this time hope dai lafiya"tsaki Lil prince ya saki cikin ɓacin rai yace "You stopid kada ka ɓatamin rai akan wanda Mai martaba yayi"da mamaki Yazeed ya saki pen ɗin dake hannunsa tare da kallon Prince yace "what wrong with you,do you know what are you try to say,Mai martaba ya ɓata maka rai how?"ya ƙare maganar da mamaki a kan fuskarsa,numfashi Prince ya sauke tare da cije leɓe kana ya dubi Yazeed yace "sabida kawai naje masa da burin ajjiye iyali ina buƙatar aure sbd na samu wacce na keso,na fahimci so yake naita bin yaran mutane kamar wani ɗan akuya shi bai gina rayuwarsa ni bai barni na gina tawa ba,dashi dani mu duka munsan abinda muke ba dai² bane,idan burinsa nabi ƴar ƴan mutane akan buƙatarsa why nima bazai barni nayi tarayya da wacce nake so ba"ya ƙare magana yana dukan pillow'n dake kusansa,jinjina kai Yazeed yayi yana mai jinjina lamarin yau Prince da kansa yake cewa yana son aure,tabbas Allah ne kaɗai yasan son daya kewa wacce yake burin aura banda haka aida baiyi wannan tunanin ba,kafin yayi magana an turo ƙofar office ɗin bakinta ɗauke da sallama,haɗe rai Yazeed yayi kana yace "ke lafiyanki zaki shigomin office without excuse? "ya faɗa yana cillawa Mema harara,zubewa Mema tayi gabansa tare da fashewa da kuka tace "Sir kaji tsoran Allah idan babu duniya aƙwai ƙiyama akan paper ɗinka na rasa damata ta wannan shekaran,tsawan shekara huɗu inayin past akan dukkan exam ɗin da nake,amma yau ka zama sanadin lalata burina da kuma farin cikina,akan wani banzan ƙudiri naka,lallai kayi nasara abinda baka sani ba shine aƙwai Allah kuma yana kallon  komai yana jin komai,sannan wannan tarin zunubin da kake aikatawa wa ƴan mata bazai barka ba,Allah ya isa ban yafe ba Ubangiji ya isarmi kuma ya sakamin cikin gaggawar da ikon Allah saika tuzarta ni Maryama Alhassan zan bar maka makaranta zanje ka wanda yake tsumayina domin aurena,nagode Allah da bai baka damar cin burinka a kaina ba,nabarka lafiya"tana faɗin hakan ta fice daga office ɗin zuciyarta nayi mata zafi,wani banzan kallo Yazeed ya watsa mata tare da faɗin "sakalya aƙwai irinki dubu kuma da bazata suke da ƙama"Prince kam damuwar dake ransa ta hanashi tanka masu,daga ƙarshema miƙewa yayi tare dayiwa Yazeed sallama ya fice daga cikin office ɗin,motarsa ya faɗa tare da ficewa daga cikin makarantar gaba ɗaya.**** ****
Tsaye suke gaba ɗaya sun jere tare dabin layi tamkar za'a raba masu wani abu,a hankali Saifudeen kebinsu da kallo dukkan wacce ya kalla sai yaga tsaftarta ba tayi masa ba,wata ma idan ya ganta sai taɓe baki tamkar yaga kashi,ahaka yayita tafiya harya huce kusan rabin kuyangun baiga wacce tayi masa ba.

Da ɗan sassarfa take da tafiya kanta a ƙasa zuciyarta na bugawa sabida lattin da tayi,yadda take tafiya tsakani da Allah a gareta sauri take,amma a zahiri wata irin tafiya take mai ɗaukan hankalin dukkan wanda yayi arba da ita,kanta a ƙasa take tafiya yadda take daka ƙafarta a hanzarce ya mawa ma dai² cin waist ɗinta damar juyawa cikin uniform ɗinta,can nesa da inda ya baro taja ta tsaya,wani murmushin gefen baki yayi tare da taune laɓɓansa,haka yaci gaba da takawa har zuwa ƙarshe baiga wacce tayi masa ba,bare har yayi tunanin cin abinda ta girka,Waziri ne yace "Duba da ƙyau yaro wannan sune sabbin kuyangunmu na wannan masarautar"baiko kalli inda waziri yake ba,yaja ya tsaya tare da lumshe idanunsa na wani lkc kana ya waresu a kanta,yadda take mamular laɓɓanta ya sashi saki tattausan murmushi,sosai tsoran dake kan fuskarta ya bayyana,gaba ɗaya ta hana kanta sukuni,cikin ya shafa kana ya gyara tsaiwarsa tare da haɗe ransa tamkar bai taɓa dry ba,cikin kausasshiyar murya mai daɗi wacce take nuni da wanda yayita umarni yake badawa yace "you the last person"a tsorace Zarina ta ɗaga idanunta ta saukeso a kansa,wani hawaye ne ya soma zubuwa daga cikin idanunta,kasa tamkashi tayi sbd wani irin ƙwarjini da yayi mata,wata tsawa Waziri yayi mata yace "ahir ɗinki ƴar talakawa maza jeki zuwa bauta"ya faɗa yana ƙara sauke mata wata tsawar,gaba jikin Zarina ya ɗauki rawa wani tsoro ya ƙara kamata a karo na biyu,kasa takawa tayi bare tayi tunanin zuwa inda yake tsaye,a hanzarce Waziri ya ɗaga wata ƙatuwar bulala zai shimfiɗa mata a baya yaji anyi saurin riƙe hannunsa tare da faɗin "No!..
Da sauri Waziri ya ɗaga kansa sama domin yaga wanda ya hanashi dokan Zarina,mamaki yayi ganin Saifu tsaye a gabansa yana danna waya, gaba ɗaya bama su yake kallo ba,yaushe har yazu wajan hartakai gaya riƙe masa hannu,hannunsa ya sauke ƙasa wanda yake ɗauke da bulalar kana ya kalli sauran Kuyangun yace.

"kowa ya koma masaukinsa kafin a ƙara nemanku"

Zarina wata sassanyar ajjiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi tare dayiwa Allah godiya domin ta gama tsorata kuma ta saddaƙar Waziri zai zabga mata wannan bulalar,akaro na biyu ta kuma sauke ajjiyar zuciya,a hankali ta ɗaga jiƙaƙƙun idanunta ta sauke a kansa,da sauri ya janye idanunsa daga gareta tare da haɗe fuskarsa tamkar bashi ba,sunkuyar da kanta ƙasa tayi ta shinga wasa da hannunta,gefe na zuciyarta kuma tana jin wata nutsuwa na ratsa zuciyarta da gangar jikinta,a dukkan lkcn da tayi arba dashi tana jin wani different feelings a kansa,tasha zama tayi tunanin mene hakan mene yasa take jin wannan yanayin game dashi amma ta gagara sanin dalili,tana son ƙara kallonsa amma sam ba zata juri ganin abinda take gani a cikin idanunsa ba,ɗan tsaki kaɗan yaja kafin ya sauke numfashi mai ƙarfin kaske,cikin nutsuwa ya juya tare da nufar wata haɗaɗɗiyar mota kirar ferari,har yayi nisa sai kuma ya tsaya,ba tare daya juyowa ba yace.


"follow me"yana faɗin hakan ya buɗe side ɗin drever tare da zama a ciki yana jiran ƙara suwarta,ta daɗe a tsaye kafin ta fara takawa zuwa wajan motar jiki a sanyaye ta buɗe side ɗin mai zaman banza ta zauna,lumshe idanunta tayi tare da cure jikinta waje guda ta shiga sauke ajjiyar zuciya,ba tare daya kulata ba yayiwa motar ke tare da fice daga cikin masarautar gaba ɗaya.


Kasan cewarsa ƙwararre a harkar dreving yasa cikin nutsuwa yake murza kan motar hankalinsa ƙwance,tym to tym yakan ɗan lumshe idanunsa sabida daddaɗar fresh air ɗin dake kaɗawa a kan titi wacce take bada wani sanyi na musamman,sanyi ne wanda baisa takura a jiki,hasalima saidai kaji nutsuwa tazu masa,ƙara lumshe idanunsa yayi tare dajan motar da gudu domin bai saba dreving a hankali ba,a zahirin gsky dreving kawai yake amma hankalinsa nakanta musamman yadda yake hangota ta gefen idanunsa ta cure waje guda tamkar maijin sanyi,bai taɓa waiting time a kan mace ba,bare har ya zauna yayi tunaninta,some time yanawa mace kallon mace mai rauni wanda damuwarsu ke bayyana a fili,tabbas mace abin tausayice duba da yadda maza ke amfani da rauninsu hatta kai ga sun cusa masu wani baƙin ciki da kuma ƙunci a zuciyarsu,yana jin tausayin mace baya da burin wulaƙanta mata,hakan yasa bai taɓa jin wani feeling akan kowa wacce mace, bare harya ɗarsawa zuciyarsa wani abu game da ita.
Amma yau an waye gari tunaninta ya tsaya masa a zuciya,yayinda yake jinta a dukkan wata gaba ta sassan jikinsa,yana jinta sosai a jikinta,bai san mene hakan ba,bai kuma san tayaya hakan ya kasance ba,bashi da burin yin wata soyayya ga wata macen bare under age like her yafi yadda cewa kawai tausayinta ya keji,amma kuma yawan tunaninta da yake na mene?wannan shine abinda ya faɗu masa a yanzu,a karo na biyu ya taɓe baki haɗi da cije lips ɗinsa na ƙasa,cikin zazzaƙar muryarsa mai sanyin gaske a bayyane yace.


"We have a the same ring that why i'm always think about her nothing else"

Tunawa da yayi tana cikin motar yasa shi haɗe ransa tamkar bashi yayi magana yanzu ba,hannunsa yasa a hankali tare da turashi cikin tulin sumar kansa ya hargitsa,cikin yanayin mood ɗin daya samu kansa ya sauke wata sassanyar ajjiyar zuciyar tare da fesar da wata zazzafar iska ta cikin bakinsa.


Dukkan yadda zuciyarta take muradi da kuma ƙwaɗayin ƙara ganin ƙyaƙƙyawar fuskarsa ta kasa bata dama sabida wani irin bugawa da ƙirjinta yake very past tamkar wacce ta shekara tana gudu,ƙara haɗe jikinta tayi waje guda tare tura fuskarta tsakiyar cinyoyinta,wasu taƙwayen hawaye ne suka shiga sauka daga cikin idanunta,da saurin ta sanya wani ta toshe bakinta dan ba taso ya fahimci halinda take cikin bare yayi tunanin wani abu a ransa,amma zamanta tare dashi tamkar takura ne da kuma hana sukune,a dukkan lkcn da sukayi kusa da juna tana ji tamkar su shekara a hakan,sabida sanyi da nutsuwar da take samu a garesa,amma ƙwarjinsa yake hanata sauke uwa uba kuma wani magaɗisu dake fituwa cikin idanunsa,ba zata iya jure haɗa idanu dashi,tabbas idan aka tilasta mata hakan tasa tamkar ace numfashinta ya ɗauke ne,tana tsaka da wannan tunanin taji yaja wani wawan birki wanda ya hadda bugewar kanta da jikin ƙofar motar.
Ƴar ƙara ta saki tare da saurin dage goshinta wanda taji yana mata zafi,a hankali ta ɗago kanta tare da runtsa idanunta da ƙarfi sbd yadda wajan ƙeyi mata zugi,ƙwaɓe fuska tayi tare da juya sleepyn eyes ɗinta,rau² tayi da idanu tare da haɗiye ƙwallan daya tarar mata a cikinsu,cikin muryarsa shagwaɓa tace.

"Auchhhii very hurt"ta faɗi maganar lkcn da take sanya hannunta saman goshinta tare daya tsuna fuskarta😟a lamun zafi,cikin juriya da kuma jarumta ta soma juyawa zuwa side ɗin da yake,wani numfashin wahala ta sauke ganin tuni yabar motar,dry ta bawa kanta ganin da gske tsoransa da gske,wani murmushin tayi sai kuma ta murguɗa baki cikin ranta tace.


"he acting like a king"ta faɗa tana leƙa kanta ta window'n motar sai a lkcn ta fashinci shopping yazu,whatever dai taji daɗin fituwarta dan kusan satin guda rabon ta fita waje,sai yau sosai yake ƙarewa gefen titi'n kallo da kuma yadda mutane ke harkokinsu babu wanda ya damu da wani,hakan kuma ya ƙara birgeta cikin ƙanƙanin lkcn ƙuncin dake zuciyarta ya kau,domin ita yarinya ce wacce bata ajjiye damuwa a cikin rant,ta yarda cewa Innallah ma'arsabirin dukkan tsanani yana tare da sauƙi,ta yarda cewa damuwa bata taɓa zama magani,kuma ƙaddara bata taɓa dauwama tana da nata lkcn,haka nan kuma dukkan rayuwan mutum tana tafiya ne da kalan nasa ƙaddara,kamar yadda tayi imanin cewa tata kalan ƙaddarar kene kuma ta shirya karɓarta da hannu bibbiyu,a ƙaro na wajan uku hawaye ya ƙara silɓiyowa ta cikin idanunta,cikin muryarta mai sanyi tace.


"nayi kewanki Mom ina fata baƙya ciki ƙunci da baƙin ciki kamar yadda nake,ina roƙan Allah ya haɗa fuskokinsu kafin ɗaukewar numfashinmu,i luv you Mom ina baƙin cikin ranshinki kusa dani,yaya yaran da basu da iyaye suke ji,yayane yaran da iyayensu suka haifa suka yar suke ji,ta rayuwa da Mom ɗinta na tsayin lkcn mai yawa amma ƙwana 7 kacal ta gagara samun sukuni sbd rashinta,Ya rabbi ka kawo mafita ka kawomin ranar da zan koma wa Mom na"ta ƙare maganar ta ƙara fidda wani kuka mara sauti.

Ta daɗe a wajan kafin ya dawo cikin motar mutane ɗauke da kaya a hannunsu,yana daga cikin motar ya buɗe masu bouth ɗin motar suka fara zuba masa kayan,suna gamawa ya zaro kusan 20k sabbi ƙal ya basu ƙyauta,bai tsaya jin godiyar da yake masu ba yaja motar a guje yabar wajan,jin shassheƙar kuka kusanshi ya sashi juyowa sai a lkcn ya manta tare sukazo wajan,shi mene yasa ma yazu da ita? Taɓe baki yayi a hankali ya kunna waƙar Atif aslam ya shiga bi cikin zazzaƙar muryarsa cikin nutsuwa da ƙwanancewa yake bin waƙar tare da shan vanillah yogourt ɗin dake hannunsa,a haka har suka ƙarasu cikin harabar masarautar bilhas,yana fitowa yayiwa wasu Hadimai nuni dasu ƙwashi kayansa sukai masa ciki,ana haka motar Lil prince tayi parking da ɗan saurin ya fito ganin Zarina wacce ya yini da tunaninta yau.


Sosai Saifu ya fahimci wajan Zarina zaizo hakan ya sashi saurin riƙe hannunta ba tare da tayi tunani ba,ya soma janta da ɗan saurin.


Wani baƙin ciki ne ya sauka zuciyar Lil prince cikin ɗaga murya yace.

"ohh hello!"ya ƙare maganar cikin ɗaga murya,tabbas yasan dashi yake hakan kuma baisa Saifu ya tsaya ba,saima ƙara tafiya yayi hankali ƙwance.


Da saurin Lil prince yasha gabansu idanunsa a rufe ya ɗaga hannu ya zabgawa Zarina Mari kana ya dubeta yace.


"ohh weldone beby you did again uhm u will pay for ur promise"ya faɗa yana jefa wata uwar harara,sannan ya juya kan Saifu tare da nunashi da hannu yace.

"You! Wai kai wanne power ma kake dashi a gidan sarautar nan da kakeson yin abinda kaga dama kuma a lkcn da kaso ehee answer me?"


Ɗauke kai Saifu yayi daga kallonsa na wani lkcn ya saki hannuta tare da hankaɗata zuwa ga Lil  Prince,kamar bazai magana ba sai kuma ya gyara tsaiwarsa tare da soma karkaɗa key ɗin hannunsa,cikin muryar isa da gadara yace.

"idan kai a matsayinka na ɗan sarki wanda suke ta ƙama da ƙarfin mulkinsu haɗi da dukiya ba kaji kunya ƙulla alaƙa da ita ba,to nikam bata tsarina bata gabana kallon baiwa nake mata tamkar yadda aka bani umarni na zaɓi maid,dalilin hakan yasa na ɗauke dan nima ta dingayi min bauta banda haka ko inuwa ɗaya bata isa na haɗa da ita ba,bare kayi wani banzan tunani kaga ni ban hanya na huce ban iya ciwon baki ba"ya ƙare maganar yana jan numfashi mai ƙarfin kanse sbd nauyin da maganar tayi masa,ya daɗe banyi magana mai tsayin haka ba sai yanzu shi yasa yaji maƙoshinsa nayi masa ƙirjinsa nayi masa raɗaɗi,ko ƙara kallonsu baiyi ba ya huce ta gabansu yana tako cike da kamala.


Wani banzan kallo Lil prince ya watsawa Saifu tare da faɗin "tabbas baka san mece Sarauta ba,baka san mene ƙarfin mulki ba,nayi Alƙawarin da ƙarfin mulkin da muke dashi saina a zabtar dakai saina baƙanta zuciyarka da kalalolin azaba mai raɗaɗi nayi alƙawarin kozan rasa komai nawa sai naga ƙarshenka da ƙarfin mulkina"ya faɗi hakan cikin baƙin ciki da ƙonan ran da Saifu ya cilla masa,sosai maganganun Saifun sukayi nasara a zuciyar Prince hakan yasa yaji babu abinda yafi tsana a yanzu sama da Saifu,juyowa yayi ya zuba mata ƙananan idanunsa wanda lkci guda suka ƙanƙance sbd ɓacin rai,cikin maganarsa wacce take nuni da umarni yace.

"After magrib kizo Lambu i want talk to you"yana faɗin hakan yasa kai ya shige hanyar da zata sadashi zuwa flat ɗinsa.

Tsaye suka bar Zarina zuciyarta nayi mata zafi da raɗaɗi,a karon farko ta ƙara tabbatarwa kanta shiɗin bamai damuwa ne da damuwar wani ba,tayi tunanin zai bata kariya zai kula da ita haka nan zai taimaketa sbd fuskar nagartattun mutane da yake da ita,sai dai tayi kuskure shiɗin nada banne kansa kawai ya sani bai damu da kowa ba kamar yadda taga alamu daga fuskarsa,lallai ta yadda ita ɗin bai wace sai dai hakan bazai saka ta yarda ya wulaƙanta ta ba,ya jefeta da maganganu masu baƙanta rai da kuma tarwatsa zuciya,zata nuna masa ita ƴar halak ce kamar yadda bai damu da ita ba haka nan itama bata damu dashi ba,zata ɓoye masa sannan za tayi nisa tashi zata hqr da son ganin fuskarsa da zuciyarta ke ƙwaɗayi,ji tayi a yanzu gaba ɗaya ya siri mata wata tsanarsa ta dirar mata a zuciya da zama dashi ƙwara zama da Lil prince zata koyawa zuciyarta sonshi duk da hakan abune mai matuƙar wahala a gareta.
Hannu tasa ta share hawayen dake ƙwance saman fuskarta kana ta fara tafiya cikin rashin kuzari da kuma sabon yanayin data samu kanta na ƙunci da baƙin ciki.


Saifu yana ƙarasawa flat ɗinsa direct bedroom ya shige yana kallon yadda suke jera masa kaya kamar yadda ya basu umarni,yana shiga ya soma cire uniform ɗinsa kana ya ajjiyesu jikin wadrope,bathroom ya shige yana zuwa ya sakarwa kansa shower.
Sanyin ruwan da yaji ya sauka tsaƙiyar kansa zuwa naked chocolate skin ɗinsa,ya sashi sauke ajjiyar zuciya tare da fesar da wani huci mai zafin gaske,a hankali jikinsa ya soma rawa idanunsa ya ƙanƙance tare dayin wani jaa tamkar an watsa masa barkono,yanayin yadda jikinsa ke rawa ya haddasa miƙewar jijiyoyin kansa wanda suka fito suka jera saman forehead ɗinsa,a hankali gagasar jikinsa ke miƙewa,hakan yasa fresh skin ɗinsa ƙarayin dark itama ta sauya kala,cike firgici da ficewar hayyaci yasa hannu ya hanrgitsa somar kansa gaba ɗaya ya birkice ya zama tamkar wanda akaiwa allurar hauka.A hankali ta tura ƙofar farlon a hankali kamar wacce ƙwai ya fashewa,cikin fargaba da tsoro da kuma yadda zuciyanta ke beating vry past ta tura kanta cikin parlon tare da soma juyawa idanunta kamar wacce ke neman wani abu,ganin babu kowa a parlour'n yasa ta ƙarasa shigewa cikin,sosai parlour'n yayi mata ƙyau musamman yadda a.c ke ratsa parlour'n ganin bata da wani tym yasa ta soma gyara parlour'n tana gamawa,ta gamawa ta nufi kicthen cikin ƙaramin lkcn ta shirya masa specail night food mara nauyi,bayan ta kammalawa ta goge komai na kicthen kana ta shirya masa wamers ɗin a kan table,miƙewa tayi tare da
(24) hamma cikin saurin tayi wanka a toilet ɗin data gani na parlour kana tayi alwala,cikin sauri ta fito tare da gabatar da sallah issahi,tana idarwa ta miƙe a can capert ɗin dake parlour'n lkc kaɗan bacci yayi gaba da ita ba tare data amsa kiran Lil prince ba.

Post a Comment for "THE NEW EMIR (SARAUTA) CHAPTER 3 BY NIMCYLUV"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...