SIRADIN RAYUWA CHAPTER 8 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 8 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 8 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

- - Post a Comment

 SIRADIN RAYUWA CHAPTER 8 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

      Lokacin daya dawo dare yayi,saidai bawani dare can ba,a sannan sha biyu ne harda rabi,da muqullanshi daya saba amfani yabude gidan yabude yashigo,falon tsit babu kowa kamar yadda yakan tarar kullum idan yadawo,kai tsaye ya haura zuwa sama inda dakinshi yake.       Alwala yasoma yi kamar yadda yasaba zama da alwala akai akai haka ammi takoya mishi tun ba yanzun ba,yakuma saba yatashi da dabi'ar,alqawarin daya yiwa safwa yana cikin ranshi,mutum ne shi mai.matuqar kiyaye alqawari dakuma qoqarin cikashi,don haka yaja laptop dinshi yakunna.       Kiran safwa yasoma yi,wadda tajima gaban system din nata tana tsammanin kiranshi,harta soma kumbura jin shuru har yanzun bai kira ba,saidai idan ta tuna yana da cika alqawari sai kuma fushin nata ya sassauta,don haka yana kira ta daga.       Tarwai ta bayyana cikin screen din nashi,ta cika screen din gaba daya,tana kwance rub da ciki saman gadonta,sanye da wata lafiyayyar baqar riga ta wani yadi wadda ta haska fara tas din fatarta,gashinta na reto a kafadarta guda,fuskarta fes da madaidaiciyar kwalliya,labbanta sunata qyallin lipstick ta hasken screen system din.       Murmushi ta sakar masa tana kashe masa idanu daya,saiya lumshe idon nashi yana jin tsigar jikinsa na tashi,uwa uba yanayin kwanciyar da tayi din batayi masa ba,saboda ana ganin wuyanta zuwa qirjinta sosai,duk da basu bayyana ba gaba dayansu amma kana iya hango tudunsu

"Tashi sosai ki zauna" ya fada qasa qasa yana lashe busassun labbansa,murmushi takuma sakar masa,taji dadi ta sanyashi a yanayi,tana son taga yasauya saboda ita,anata ganin wannan kawai shine xai nuna ma'aunin qaunar da yake mata,hakanan zai bayyana adadin yadda ya matsu su zama mallakin juna kamar yadda itama ta matsu,tunda tasan bazai taba buda baki ya gaya mata yadda take da buqatar ji ba

"Meya faru da kwanciyata kuma?"

"Ki gyara kawai ko nayi cutting up kiran" tasanshi sarai zai aikata,don haka ta miqe zumbur tazauna tana tura baki gaba,saiya saki wani qaramin murmushi wanda iyakacinsa labbansa.       Bata iya wani dogon fushi da shi,don haka ba bata lokaci tasauko suka soma hirarsu,anan yayi realising lallai safwa batasan da zancan plan da ammi tayi na,saboda kusan rabin hirar tasu tayau tana nuna mishi yadda take bala'in kishinsa,daga qarshe ma ita yabarwa fagen yaxuba mata idanu yana kallon yadda labbanta da sukasha man lebe suke motsi.       Cikin jikinsa yaji tabbas akwai matsala idan sukaci gaba da zama a haka,don haka ya yanke shawarar samun abun mai zafi da zai rage masa abinda yasoma ji


       Yasake kallon agogon dake aiki qasan system din,dare ya riga da yayi,bai kyautu ya tashi sodangi ba yanzu,don haka ya sanya laptop din a sleep bayan ya nemi uzuri wajen safwa ya dantse kiran,yamiqe ya zura slippers dinshi yasauko qasan.      Dai dai lokacin da yunwa ta hanata sakat sakamakon qin fitowa da tayi taci abincin dare,har suka gama abinda suke suka tafi suka kwanta.       Don dole ta tashi da hanzari jin yadda hanjinta ke curewa waje daya,slippers dinta itama kawai ta zura tana tattare hannun rigar baccin jikinta,wadda take riga ce iya cinya mai dogon hannu da wandonta dogo na wani lallausan yadi ruwan hoda,kanta babu dankwali,sai gashinta jelarsa ke reto a bayanta yana kuma qyalli saboda mai da gyara da yasha,ta bude qofar dakin nata a hankali kamar wata barauniya,ta tsaya ta kasa kunne,sai data tabbatar bataji motsin komai ba sannan tasoma takawa a hankali zuwa kitchen din.      Cikin qaramin plate tazubo abincin kana ta dawo falo,tvn dake aikia falon wadda sun manta basu kashe ta ba taja hankalinta suna nuna wani shirin girke gike,saita tsaya gaban tvn da plate din a hannunta tana yafitar abincin kadan kadan tana ci,idanunta da dukka hankalinta yana kan tvn.       Taku biyu rak yayi ya hangi mutum gaban tv,abun sai yaso daure mishi kai gamida bashi mamaki,a hankali yake qarewa bayanta kallo,a jikinsa yakejin baquwa ce,don sam batayi yanayi ko zubin rakiya ba bare yace itace,duk da ba wani kallonta yake ba amma yasan ba ita bace

"Wow" bilkisu tadan fada cikin birgewa,saboda abinda cook din ta hada yayi matuqar burgeta yakuma bata sha'awa.        Sautin muryarta yasake tabbatar masa da zarginsa,saiya ci gaba da saukowa idanunshi a kanta.       Jin takun saukowa daga step ya sanya gabanta mummunar faduwa,ta soma zazzare idanu,babu abinda yazo ranta illa

"SHINE!" zuciyarta ta gaya mata da qarfi

"Wala'alla ma dakinki zashi" zuciyarta ta sake gaya mata,sakin kwanon hannun nata tayi da hanzari ba tare data shirya ba,a miliyan tayi dakinta kamar zata tashi sama batare datako waiwayo ba bare taga waye,wanda hakan ya baiwa sassan jikinta damar motsawa dakyau,bataci biriki ba sai data tabbatar ta isa dakin,kana ta sanya muqulli tarufe qofartata gam.      Mamaki ne yasanyashi tsaiwa yana kallonta gamida mamakin wacece wannan?,ganin baida amsa saiya tabe baki gamida dage kafadunsa yawuce zuwa kitchen donyin abinda yafito dashi.      Koda yakoma dimma hirar kadan suka qara ya bata haquri,ya qarasa shanye coffe dinsa kana yayi shirin kwanciya yakwanta,kafin bacci yadaukeshi yatuna abinda yafaru mintunan da suka wuce,saiya tabe baki gamida jan qaramin tsaki,idan bamai matsalar qwaqwalwa ba wazaiyi haka?,kawai daga jin taku saika yar da kwanon hannunka kahau gudu,sake gyara kwanciyarsa yayi yana jan tsaki gamida rufe idanunsa,ya aje komai gefe yanason bacci ya daukeshi.      ******    ******   ******   ****      Kimanin qarfe sha daya ne na safiyar ranar,su ukune zaune a falon nata saman dining suna karyawa,fulani aisha da yaranta uswa da sumaira.      Diyar uswa ce akan cinyarta tana bata farfesun nama a hankali yayin da suke taba hira wadda ta shafesu,daidai lokacin jakadiya ta qaraso,ta zube tana shaida mata saqon son ganinta da saudat(qanwar maimartaba mahaifiyar kamal) keson yi.      Kai ta gyada kana ta bada izinin ganinta,ta dauke idanunta ta maida kan yaran nata,sai ta yiwa sumaira inkiya data dauki sahla dake saman cinyarta,ita kuma ta miqe tana goge hannunta da tissue.     Cikin nutsuwa qasaita take saukowa daga wajen dining din zuwa ainihin falon,tana sane da zuwan saudat din gidan kimanin kwanaki hudu,amma bata nemeta ba kamar yadda ta nemi sauran abokan zamanta.       Tuntuni tasoma shaqar wani abu dangane kan saudatun,hakanan takejin sam takunta bai mata ba,tun kafin yau dama ba wani alaqa mai kyau bace can can tsakaninta da saudatun tunda aka aurota,hakanan jininsu bai hadu ba,hakan kuma baya rasa nasaba da aurotan da yayi a wata qasa,wanda a lokacin saudat din sam bataso hakan ba,akwai qawarta dataso hadashi da ita kamar kamar me,taji ba dadi sosai,don a sannan ita dayace ta rage mishi qanwa kuma abokiyar shawara,dama duka duka su ukune Allah ya baiwa sarki mu'az,Allah ya yiwa babbar yayarsun rasuwa,tabar yaro daya wanda yake hannun saudat din tana riqo.       Cikin qasaita shigo shan qamshi da kallon komai ɗai ɗai tashigo falon,don dukka cikin gidan babu sassan da yakai na fulani aisha kyau da tsaruwa da kayan ado na alfarma dake sake nusashe dakai cewa nan fa akeyin sarautar,don ita gada tayi daga fannin mahaifi dakuma miji,sarauta saidai ta nunawa wasu

"Bismillah" ammi tafada tana nuna mata daya daga cikin kujerun cikin nata salon qasaitar da isa,saida saudatun tazauna kana itama tayiwa kanta mazauni kan kujera maicin mutum biyu,kana ta dora qafarta daya saman daya idanunta kan saudat

"Matar dan uwana" ta fada kamar yadda ta saba kiranta dashi

"Maman kamal....yaushe a gari?" Ta fada a dake,saita dan yatsina fuska

"A qalla yau kwanana hudu cikin gidan nan,amma da mamaki idan kikace bakisan da zuwa na ba" hannayenta ta watsa kafin ta hadesu waje guda

"Ba abun mamaki bane,saboda kowanne mutum akwai irinsa,ba kasafai na fiya damuwa ko bibiyar al'amuran dake wakana cikin gida ba,indai lamarin bawai yajibanceni bane" wani duba ta mata tanason fahimtar meta fada din,magana ce cikin magana ko kuma magana tayi kanta tsaye ba tare da kowanne nufi ba?,saita gyada kai sa'an nan tace

"Haka ne" daidai lokacin da sumaira ke saukowa rungume da sahla,kana ta qaraso cikin girmamawa,fuskarta a sake kasancewarta maison jama'a fiye da kowa cikin 'ya'yanta,tazauna saman daya daga cikin kujerar tana gaida saudatu da suke kira da mom,gami da tambayarta 'yan uwanta yaran saudatun wato safna da safina

"Qalau" ta amsa a taqaice,daga bisani uswa ta sauko itama ta gaidata,saidai ita daga gaisuwar bata qara komai akai ba saima qoqarin miqewa da take don barin wajen,kasancewarta gwanar miskilanci ce itama kamar dan uwan nata abdul'azeez,dukka fulani aisha na ankare da yadda take amsa gaisuwar tasu,wanda tasha bamban da yadda take treating su walida qwarai

"Ke zonan,don uwarki me yasa ne baki da hali,kodon kinga mun aurar dake ne yasa kike ganin kanmu daya" ta fada cikin zafi zafi,kamar da biyu take maganar.      Uswa dake tafiya ta waiwayo kana tace

"Wa wai?,ni?" Wanda ita harga Allah bada wani abu tayi maganar ba,kusan nature dinta kenan

"Ban sani ba" ta amsa mata a gadarance.      Batace komai ba ta dawo din tasamu waje taxauna,saita soma fada mara dalili,ta inda take hawa bata nan take sauka ba,waita yaye kowa bata neman kowa.       Dukkan wani takunta da abinda fulani aisha ke nema ya gama bayyana kanshi,don haka saita shareta yadaga waya tasoma amsa kira,bata tsagaita ba har sai data gama taga yaran suna tashi suna wucewa ciki kana ta ajjiye.        "ƴan mexico ana can dai,ƙiri kiri an hana abdul'azeez dai rayuwa cikin ahalinsa,bayan bashi da wadanda suka fisu" saudatun ta fada kamar meyin fada,murmushi fulani aisha tasaki cikin nutsuwa tana aje wayar hannunta,kana ta daga idanun nata ta zubawa saudatu su.        "Komai na rayuwa ai lokacine,sau da dama wasu abubuwan sukan xama alkhairine a rayuwar dan adam,musamman nisantar wasu gurare da muhallai,karki damu innar abdul'azeez,akwai lokaci" sarai ta fahimci magana take gaya mata cikin magana,saita miqe tana tabe baki tana duban aishan da wani irin kallo

"Ni zan wuce,dama leqowa nayi mu gaisa,tunda ku baku neman kowa" murmushi tayi kamar babu wani cikin maganarta daya bata mata rai,kana ta miqe tana dubanta

"A haba,mukan nemi mutane mana,musamman wadanda mukasan muhimmancinsu me yawa ne cikin rayuwarmu,sa'an nan tarayyarmu dasu tana da wata fa'ida da alfanu,kamar dai ke" tasan gatse tayi mata sarai,takuma fahimci babu wani abun dazai kashe bakin aishan,don haka tayi gaba,zuciyarta cike fal da quluwarta,tare da ninka alwashin qudurinta cikin ranta.       Murmushi tasake sosai sanda saudatun tafita

"Kainuwa kenan......dashen Allah" tayiwa kanta da kanta kirari,kana takoma tazauna inda tatashi,tana ci gaba da wassafawa da qiyasta yadda abubuwa zasu ci gaba da wakana.       Rai a bace ta isa sashen adama,wanda har takai dukka barorin daketa faman miqa mata gaisuwa cikin girmamawa babu wanda ta amsawa ko mutum daya.

Bata tsaya an mata wani iso ba kamar sashen fulani aisha,kawai ta cusa kanta inda tasan xata samu fulani adaman,a sannan tana zaune ne ita diyarta Aafra,'yarta ta biyu wadda ayanzu haka kudin aurenta ke hannu,duk da ba'a sanya rana ba,tanason hadata ne da autarta ta aurar dasu lokaci daya.      Da sauri tazauna tana gyara zamanta ganin shigowar gaggawar da saudat din tayi mata tana duban yanayinta,gaidata afra keyi,maimakon ta amsa saita ce

"Bamu waje zamu gana da babarki" duban maman nata tayi kamar ba zata tashi ba,amma inkiyar da fulani adaman tayi mata ya sanyata miqewa tana tura baki,ta dauki wayarta tana gyara yafen mayafinta tafice.       Qaqqarfar ajiyar zuciya tasaki sanda take zama,cikin damuwa fulani adama tadubeta

"Wai lafiya kuwa saudat?"

"Inafa lafiya,har yanzu haqarmu ta gaza cimma ruwa,daga sassan aisha nake,komai nasu yana tafiya dai dai,da alama ma yadda suka tsara,babu alamun wani abu dake damuwarsu,akwai matsala fa adama,tabbas akwai matsala,wankin hula zaya kaimu dare".      Maganar itama ta sanya damuwa a ranta,saita sauke ajiyar zuciya cikin damuwar tace

"Yanzu babu wani abu kenan da xamu iya yi,ba shakka wannan babban abun kunya ne a wajenmu"

"Ina zuwa,akwai wani aiki dana sanya ayimin" saudat ta fada bayan ta zaro wayarta ta soma danne danne.        Dab da kiran zai katse muryar kamal ta bayyana

"Hey mom" ya fada da alamun muryarshi na nuna tafiya yakeyi a qasa

"Hey....kana ina ne?" Dan tsaki yaja yana yarfa hannu

"Ganinan a qasa,mom nayi nayi ki matsawa daddy ya siyamin mota amma kinqi,kullum saidai mu qare da aron ta wancan dan girman kan,haba da Allah bafa girmanmu bane,shi yasa kowacce beb ka taya sai kaga hankalinta na kanshi indai ta sanshi"

"Kaga dakata.....kaima kasan halin babanka sarai,bazai siya ba,shi yasa naketa fafutuka wannan lamarin ya tabbata komai yadawo hannunmu,bama mota ba har private jet zaka mallaka" dan tsalli yayi gamida sakin ihu,wanda qila da anan gida nigeria yake sai an tsaya kallonshi

"Wow mom....akwai kuwa latest news"

"Dama shi nakira ji....gayamin ya ake ciki"

"Yarima ya daina kwana a gida kwata kwata,kusanma sai ku kwana mu yini wani lokacinma sai yayi almost two to three days bamu ganshi ba,infact....dana lura dakyau ma sai na fuskanci da yawa daga cikin kayanshi basa gidan"

"Me hakan ke nufi kenan?" Tayiwa kamal tambayar,amma idanunta suna kan adama

"Well,ina tunanin kamar yasauya gida ne fa"

"Ina yakoma"

"Idn't know gaskiya mom,kinsanshi da tsare gida,bayason yawan tambaya ko sanya idanu"

"Dole kazama mai tambaya,kuma dole kazama dan sa idonsa koda bayaso,ya zama lallai ka binciko mana ainihin abinda yake faruwa,dakuma inda yakoma"

"Ohkey....i will do my best" daga haka ta katse wayar tana duban adama.      Babu wanda ya iya cewa dan uwanshi da komai,har tsahon wasu mintuna kafin adama ta magantu

"Tabbas aisha ta sauyawa abdul'azeez gida ne,kuma ina da yaqini da tabbacin akwai dalilin da yasanya tayi hakan,akwai abinda takeyi ko take shirin yi wanda take boyewa batason kowa yasani" kai saudat tajinjina cikin gamsuwa

"Hakane,nima na yarda da hasashenki....zan matsawa kamal har sai ya binciko mana komai cikin qaramin lokaci" tattaunawa sukaci gaba dayi a tsakaninsu ta yadda zasu bullowa komai harna tsahon wani lokaci.


*******    *****    *********      Tunda yatashi a safiyar yau gaba daya yaji bashi da sha'awar fita ko ina,don hatta da qasan gidan bai sauko ba bare mutanen gidan susan yana cikin gidan.      A samanshi yayi wankansa yadda yasaba,yashirya cikin kaya marasa nauyi dukka farare kamar yadda yawanci yafi son fararen kaya a shigarsa,yana da coffe maker ya hada coffe dinsa da wani sauran cake yasha,yagama dukka sabgoginsa a waya,kamar kiran ammi da maimartaba da sauran mutanen da yake da hulda dasu,yakira safwa ma suka dan kashe wasu lokuta kana ya katse wayar,ya debi litattafan makarantarshi,ya isa can quryar falonsa ya murda wata qaramar qofa saiga wani qawataccen balcony dan madaidaici da aka bullo dashi ta backyard na gidan,wajene da aka masa kwalliyar furanni daketa bawa wajen qamshi kala kala,tun daga qasa har jikin bangon wajen,sai kujerun hutawa guda uku da table,daga balcony din kana iya ganin backyard din fes.     A nutse ya isa kan daya daga cikin kujerun yazube litattafansa,kana yasoma tattakawa harya isa gaban qarfen da aka tokare balcony din dashi,dafe qarfen yayi yana qarewa backyard din kallo,kafin yadauke idanunshi ya cillasu cikin gine ginen da yake iya hangowa cikin unguwar.       Shuru unguwar take kamar kowanne lokaci,sai mutane tsilli tsilli dake wucewa,wanda yawanci a qasa suke tafiya da alama ba nisa zasuyi ba,wasu mata wasu maza,wasu mace da namiji wani lokaci da 'yan yaransu.       Ajiyar zuciya yasauke sannan yasake dawowa yazauna kan kujerar bayan ya kwashe litattafan ya azasu saman cinyarsa,yasoma budawa a hankali yana nazarin karatuttukan ciki.         Sosai karatun yake masa dadi,saboda yanayin wajen dakuma yadda yake sake fahimtar abinda yake karantawa sosai kamar ana bude qwaqwalwarsa ana zuba masa shi.      A hankali yasoma jin surutu,wanda da fari yayi qoqarin tokare hayaniyar don kada tashiga karatunshi ta bata mishi yanayin da yake jin dadinsa.      A hankali a hankali sai surutun yasoma yawa,yakuma so ya dameshi,hakan yasa yasoma mutsu mutsu yana yana gyara position na zamanshi ko xai daina jin hirar,saidai abanza, duk yadda ya gyara zaman baijin canjin muryoyin da yakeji.       "Bilkisu!" Yaji an qwala kira,hakanan yaji kamar an fusgi hankalinsa,saiya dauke kansa daga kallon littafin zuwa bangaren da yaji muryar tana fitowa.      Su biyune zaune saman wasu 'yan kujeru masu kyau da aka tanada a wajen saboda hutawa,sun tasa botiki kowa dai dai a gabansa suna faman wankin inner wears,sunata hira gami da dariya da alamu lokacin na musu dadi,kuma babu abinda hake damunsu,da alama sune suka isheshi da surutu kenan tun dazun.       Su biyu ne,rakiya da wata wadda baisan ko wacece ba,sanye take da doguwar riga na wani yadi mai sulbi da qyalli wanda kana masa kallo daya zakasan ya jibanci gidan sarauta,an masa dinkin doguwar riga,wadda daga sama ta kamata datayo saman cikinta kuma zuwa qasa ta bude sosai,hannunta gajere ne sosai don ko gwiwar hannu tsahonsa baikai ba,gashin kanta da yasha gyara shekaran jiya yana fake a ribbom,duk motsin da tayi sai jelarsa ta tayata motsawa,fuskarta akwai alamun nutsuwa da walwala,amma wacece ita?,ya tambayi kansa yana zuba mata idanunshi gamida sake karantar yanayinta

"Idan kun gama bilkisu ga abinci can na kammala" cewa mama sodangi dake qarasowa wajen tana dubansu.      Wannan karon baiji me ta fada ba,saidai fuskarta shimfide da murmushi take wa mama sodangin magana,bata qara minti daya ba maman ta juya tabar wajen,yayin da kuma sukaci gaba da aikinsu da kuma karadinsu,shi kuma yaci gaba da nazartarta.       Baisan adadin lokacin daya kwashe ba yana bibiyar lamarinsu,daga bisani ya farga,tamkar wanda aka tashi daga barci yayi firgigit,ya janye idanunshi daga kansu yana jan wani mugun tsaki,haushin kanshi sosai ya kamashi,baiga dalilin da xai sanyashi xama yana wannan abun ba,yaduba agogon dake maqale a wani saqo dake wajen,yasake jan tsaki haushi yana sake cikashi ganin lokacin daya narkar a banza,saiya tattare takardunsa kawai kana yawuce ciki,yasanya maqulli ya rufe qofar.        Kan gadonshi ya fada da qarfinsa cikin rub da ciki yana sauke qaqqarfar ajiyar zuciya,hakanan wata kasala tana lullubeshi,sai ya lumshe idanunsa yana furzar da iska daga bakinsa,surarta yadinga gani cikin duhuwar idanunsa tana masa yawo,sai yayi hanzarin bude idanun nasa gamida maida kwanciyarsa rigingine,ya kuma goye hannayensa a qirjinsa idanunsa suna kallon rufin dakin.       Wasa wasa saiga abun nason shiga tunaninsa,saiya miqe yasake zama sosai yana jan tsaki,babu shiri yatashi zumbur ya isa cupboard dinsa yasoma zaro.kayan da zai iya sanyawa,sam babu plan din fita a yanzu a tsarinsa,amma dole yafita,don baison yazauna yayita fama da tunanin da zai dameshi,ya shirya a gaggauce kana ya rufe saman yasauko yafice daga gidan gaba daya,bayan yadauki motarsa dake aje gaban gidan.       *******    *****    ********     Cikin madaukakin farinciki take takowa zuwa inda yake tsaye a filin sauka da tashin jiragen sama dake mexico,jinta take cikin wata duniya ta musamman,yau da kanta ta kawowa azeez din ziyara,abinda ta dade tana so tana kuma sanya rai.      Murmushine sosai kan fuskarta tana kallonshi,yayin da shima ita yake kallo,fuskarsa ta washe alamun akwai fara'a sosai shima bisa tashi fuskar,dab da zata qaraso inda yake tasoma sassarfa saboda yadda fa qagu ta ganshi,ji take kamar ta shekara bata ganshi din ba,ta taho da sauri da niyyar fadawa jikinsa,da hanzari yakauce yana mata murmushi kana ya kada dan yatsanshi manuni

"Nooo...." Saiya mata nuni da mutanen dake zirga zirga a wajen da idanunsa,kafadunta ta daga tana tabe baki gami da bata rai,cikin idn't care manner,baisan me yasa take daukan wasu abubuwan ba'a bakin komai ba,tsabar wayewa ce ko boko ne ya mata yawa oho bai sani ba,ko kuma sangarta ce da gata?,ita ba rayuwar waje tayi mai yawa ba bare yace abunne yashigeta,sam tana ganin don yayi hugging dinta ba wani komai bane,hakanan bata dauki kisses a tsakaninsu a bakin komai ba inda yana biye mata,tana ganin ai suna son juna kuma auren juna zasuyi,so ba wani abu bane don suna body contact,tunda ba maj gaba daya suke ba sun kame kansu,saidai sam shi bai yarda da wannan tsarin ba,tunda yasan kanshi,yasan matsalarsa yasan kuma yaya jikinsa yake,ko baya ga hakama shi abun baya burgeshi,yafison komai yazo a lokacin daya kamata yakuma dace,sai yafi bada armashi da ma'ana.       Har yabude mata motar tashiga tana zumburo baki,yasan don ya hanata ta rungumeshine yasa take wannan kumbure kumburen,saiya basar kamar bai lura ba,yasoma tunanin inda zai ajeta,daga bisani ya yanke ya tambayeta

"Ina madam takeso ayi mata masauki?" Cikin muryar dake nuna fushi tace

"Inda yallabai yake zaune mana" ya gane sarai inda take nufi,gidan da suke zaune shi dasu kamal da mutspha harma da jabir,bazai soma wannan gangancin ba,yaje yakaita cikinsu ya aje,ita kanta ziyarar tata banda tare da antynta sukazo qasar ta sauka a wani gari ita kuma tace zata qaraso ta kwanan musu ko dayane da yace ya yafe,baison yafadiwa antyn haka taga kamar ya gwasale mata 'yar 'yaruwarta ne,duk dashi wannan ba damuwarsa bane koda zata ji haushin,amma ita safwan a karan kanta ta jima tana masa nacin xata zo takanas daga nijeria zuwa mexico,shike dakatar da ita,sannan uwa uba yasan baya bata attention dinsa kan soyayyarsu yadda takeso saboda dalilansa da suka ta'allaqa da yanayinsa,dakuma yadda ita a karan kanta take mu'amalantarsa yana masa tsauri da yawa,dakuma jefashi cikin yanayi.        "Zabi wani wajen dai" saita dage kafada

"To daya gidan" kafadanshi yadaga,yana ganin can din babu matsala sai yace

"Alright". Ko kafin su isa gidan tuni ta warware daga fushin da takeyi dashi,don dama bata iya wani dogon fushi dashi.        Tana zaune gefan gadonta tana warware kalbar dake kanta,wadda rakiya tayi mata bayan tsefaffaen kan ya dameta,sallama cikin wata lallausar murya ta ratsa falon kana ta isketa har dakinta,sai tabar duk abinda take tana saurare ko zata sake jin wani abun bayan sallamar,bata sake jin komai ba face muryar rakiya cikin tsananin girmamawa tana fadin

"Barka da zuwa Allah ya taimakeka....barka da warhaka yarima"

"Yarima?" Ta tambayi kanta gabanta na wani mummunan faduwa da batasan dalili ba,indai zata san cewa yana gidan,indai kuma za'a ambaceshi ko yaya sai taji wannan fargabar da faduwar gaban,tamkar wadda akace gashinan shigowa saita rarumi dankwalinta tana rufe tsefaffen kanta,kana ta rarraba idanu cikin dakin,gabanta naci gaba da faduwa,zuciyarta na mata saqe saqe gamida raya mata abubuwa masu yawa.       "Tana madafa....bari nayi kiranta" tasake jiyo muryar ruqayya tana fada cikin sauri,duk da bataji me yace daga can sashen ba,amma tabbas mama sodangi ya buqaci gani,hakanan tasamu kanta da tashi cikin sanda ta isa bakin qofar dakin nata,ta sanya hannu da niyyar murza muqulli,wata zuciyar tace zai iya yiwuwa ajiyo qarar taba qofa,tunda cikin falon babu kowa

"Wow swerry,gidan nan yayimun fa" muryar safwa ta katse shurun da falon yadauka bayan wucewar rakiya

"Am so glad to hear this" ta sake jiyo lallausan muryar tana fada a taqaice,ci gaba tayi da tsaiwa hakanan ba tare da tasan dalili ba harta jiyo muryar mama sodangi na fitowa daga kitchen.       "Barka da dawowa" ta fada itama akwai alamu na ban girma a muryarsa,manyan idanunshi ya lumshe yana gyada kai kawai,yanayin yadda yake maganarshi idan baka sanshi ba zaka tsammaci yanga ce yakeyi,saidai hakanan yanayin halittarsa take

"Yauwa sodangi....ga baquwa nan,sunanta safwa,zatayi kwana biyu" cikin girmamawa tace

"Fulani ta shaidamin.....Allah ya baki nasara barka da zuwa" dan murmushi safwa tasaki dadi yana ratsata,tanason harkar da za'a dinga bata girmanta ana kuma kambamata,tunda tasan takai ayimata hakan,saita gyada kai kawai tana cewa

"Barka kadai sodangi,mun sameku lafiya?"

"Lafiya qalau gimbiya safwa" sunan yasake faranta mata rai,hakan yasa lokaci daya taji mama sodangi tayi mata a ranta.      Miqewa yayi don dama a hannun kujerar yake a zaune,sai safwan ta dubeshi da shagwabar nan tata

"Ina zuwa kuma?" Cikin sanyin muryar kamar yadda yasaba,kai bakace ya iya hargowa ba,shi yasa duk wanda yaganshi a sa'ilin da yake fada take daban mamaki,bazakace shi bane

"Zan qarasa schedules dina nayau" kafada ta maqe tana dubanshi

"Sam ba yarda ba,kamata yayi kayi cancel duk wani schedules naka har sai na koma,tunda kasani saboda kai nazo ai" tuni mama sodangi tajuya don komawa kitchen,don abun yadan mata nauyi,tunda bata taba ganin hakan ba,hasalima duk fadar safwa da ake yau tasoma ganinta.       Girarshi yadage sannan yace

"Really?"kawai saita sake mishi kukan shagwaba,kusan bataji me yace mata ba,amma taji takun hawanshi sama,kasa barin wajen tayi har zuwa sanda aka gyarawa safwa dakin da zata zauna,daganan bata sake jin komai ba,saita saki qofar takoma bakin gado tana sakin ajiyar zuciya a jejjere.        Dai dai lokacin karatunsu harda wasu mintuna akai taji anyi knocking qofar dakin,saita sake yin wuri wuri,duk da kusan awa biyu cif bata sake jin wannan muryar da take da yaqinin tashi bace,sai muryoyinsu rakiya da mama sodangi wani lokaci dana baquwarsu wadda da alama tacika tambaya dakuma surutu.       Shahadar quda kawai tayi tabada daman shigowa,rakiya ce a shirye tsaf riqe da litattafansu a hannunta,fuskarta qunshe da murmushi take duban bilkisu,zamansun tare dakuma shaquwarsu yasanya daga ita har rakiyan kowanne yake mance matsayin dan uwanshi a tsakaninsu,sukan kalli juna ne tamkar qawaye,sau tari mama sodangi ce kan jawa ma rakiya kunne kada ta mance matsayim bikisun,itakuma bilkisu sam hakan bai mata dadi,don ita bataga wani matsayi daban dake gareta ba,uwa uba ma ita tafi jin dadin mu'amalarsu a hakan dari bisa dari,rakiya a matsayin qawa kuma 'yaruwa,mama sodangi a matsayin uwa,hakan yafi gamsar da ita,tun suna takatsantsan da kiyayewa har suma suka saki,suka kuma dauketa a yadda takeso su dauketan

"Akramakillah.....hala yau bazamu samu darasi ko guda daya ba?" Wayarta da take browsing da ita ta sauke bayan ta kashe datar,baya ga kiran 'yan uwanta tana jin dadin wayar sosai,duk da cewa bata charting ko guda daya,amma ta zame mata wani dandali na daukar karatu,tasan ingantattun link na manyan malamai da take shiga tadauki karatu sannan tafito,ta qaru fiye da zatonta,takuma sake imani da cewa,ita waya yadda ka dauketa hakan take,kamar kwalba ce,asali a tsaftace take,idan kaso kazuba ruwa ko lemo,idan kaso kazuba giya,wannan kai ka gurbatata.       Cikin sanyin murya tace

"Rakiya bamu kadai bane bafa a gidan" murmushi ya subuce mata,tana mamakin yadda bilkisun take bala'in tsoron gamuwarta da yarima abdul'azeez,ko ita da take hidima cikin gidansu,take kuma qarqashin ikonsu tsoronta baikai wannan ba,abun nasu yana da matuqar daure kai,ance mata aure aka musu,amma dagashi har ita babu wanda yataba ganin wani?,batasan koshi ya taba ganinta ba(eh ya taba ganinta amma rakiyan bata sani ba),babu wanda ya taba hada inuwa da dan uwanshi,duk da batasan ainihin rayuwar aure gaba daya ba,amma ta tabbatar wannan ba shine aure ba.       "Dodon yafita tun dazu,babu kowa cikin gidan saimu" harararta tayi kadan kana tayi shuru  kamar bata yarda ba,sai kuma ta sauke ajiyar zuciya

"Muje" ta furta tana saukowa daga saman gadon,tazura slippers dinta tana ware dankwalin kanta 


      Kamar yadda tace din babu kowa cikin falon sai mama sodangi itama dake jiran fitowarta,ta gaida maman kamar yadda tasaba duk yammaci sannan tazauna suka fara karatun.        Sai data soma dajin kataratunsu na jiya sannan tadora musu da wani sabo bayan ta tabbatar sun fahimta wancan kuma yazauna yadda ya kamata.        Awa guda kacal sukaci a karatun aka bude qofar dakin da bilkisu tasan babu kowa a ciki,hakan yaja hankalinta don dama a tsorace take,ta daga kanta da hanzari tana duban qofar dakin,safwa ce ke fitowa,sanye da wasu riga da wando masu azabar kyau da suka amsheta,saidai sun bayyana duk wata sura ta jikinta,tashin qamshi take sosai,kanta yasha gyara,hakanan a fake yake da ribbom kalar kayanta,hakan yasake qawata kwalliyar tata.       Ido suka hada da bilkisu,suka kalli juna na wasu sakanni kafin bilkisun ta janye nata idanun,itama safwan ta janye tana qarasowa falon,gami da mamakin wacece wannan maikyau haka?,choculet beauty.       Saman kansu ta tsaya,alamun sangarta qarara suna bayyana tattare da ita,ta dubi mama sodangi

"Sodangi da Allah inason peppersoup din kifi,Allah yasa kuna da?"

"Eh akwai ranki yadade.....akwai"

"Ohkey" ta fada tana zagayawa saman kujerun  don ta zauna,da alama ta gama bada nata umarnin kenan,da niyyarta ta fada takoma cikin dakin,amma hakanan batasan meye yaja hankalinta ba taji ra'ayin xaman falon,saita zauna daga bayansu tadora qafarta daya saman dsya tana dan latsa wayarta,yayin da wani sashe na hankalinta yake kansu.      Tunda mama sodangi tabar falon zuwa kitchen don yin aikin safwan sai bilkisu take jinta incompatible,zaman sam bai mata ba,ta dinga tsarguwa tana jin kamar safwa na kallonta ne,uwa uba batasan wacece safwan ba,don haka ba tare da wani dogon sharhi ba ayau ko tambaya suka rufe da addu'a ta tattara tawuce daki.      Fuska safwa ta yamutse,don me ita ba zata kulata ba kamar kowa?,donme ba zata girmamata ba kamar saura?,wacece ita?,don taga tana da kyau

"Wacece waccan" safwa ta jehowa rakiya tambayar data rudata lokaci guda har tahau inda inda,wanda da safwan ta gogu da rayuwa yaci ta karanci wani abu

"Na.....'am....iyee?" Take gumi ya yanko mata,ta sanyata a tsaka mai wuya,batasan ainihin amsar da zata bata ba,sa'an nan tana ankare da gargadi dakuma jan kunnen mai qarfi da mama sodangi tayi mata koda safwan zata tambayeta wace bilkisu,kuskuren da tayi guda daya shine bata tambayi mama sodangin amsar Da zata baiwa safwa ba a duk lokacin data jefa mata tambayar ba kamar yanxu

"Yar uwata ce,tare mukazo" tasamu kanta da shirya wannan qaryar,baki safwa ta tabe tana kada kai

"Shine take acting kaman wata tsiya,baku shaida mata wacece ni ba?" Kai ta kada da sauri

"Bata sani ba Allah ya taimakeki,kiyi haquri,rashin sanine,tayi kuskure amma zan mata bayani,saidai duk da haka tana da matsala,bata magana mai tsaho,likita ya hanata" ita kanta yadda ta shirgo qaryar tabaiwa kanta da kanta mamaki,amma babu yadda ta iya,don shine kawai mafitar da zata kare kanta da bilkisun ma gaba daya.        Sai taji zuciyarta kuma tayi sanyi

"Barta kawai tunda lalura gareta,na tsammaci izza ce"

"Ko kadan ranki yadade" tasake fada da sauri,daga haka safwan bata sake cewa komai ba,saita maida kanta ga wayarta,rakiya kuma ta miqe tanufi kitchen tana sharce gumi.     Zaune yake kawai cikin motar bayan ya fakata daura da wani wajen wasan yara dake kusa da unguwarsu,ya jima zaune a ciki a yadda yake,bawai don yana wani abu ba ko kuma yana da abunda zaiyin ba,hakanan kawai baya son komawa gidan,ya tabbatar da cewa indai baiyi da gaske na safwa zata zo ne ta tafi bayan ta tayar masa da qaton tabon da yaketa qoqarin warkarwa amma abu ya gagara,tunda a halittarsa ne,jininsa ne haka babu yadda ya iya.      Sam bashi da sha'awar komawa yaci gaba da tu'ammali da magungunan,dalili kenan daya sanya yake gudun duk wani abu da zai sanya ya nemesu.      Wayarsa dake hannunsa tun dazun tadauki sauti,wanda hakan ke nuna kiranshi ake,da hanzari yaduba,sai yaga ammi ce,don haka yadan kwantar da kujerar da yake zaune akai ya jingina bayansa sannan yadaga

"Barka da warhaka ammi" gyaran murya tayi kadan sannan tace

"Yauwa....barka kadai,ya makaranta?"

"Alhmdlh ammi,ya maimartaba"

"Komai lafiya....azeez nace ba?"

"Na'an ammi"

"Meye dalilin da zaka sauke safwa a gidan da yarinyar nan take?,ina hankalinka yatafi?,ko so kake ka jawo mana matsala ehen?" Cikin kwantar da murya da girmamawa yace

"Babu komai ammi,babu abinda zai faru" shuru tadanyi na wasu sakanni sannan tace

"Ka tabbatar da abinda ka fada,idan ba haka ba..."

"Please ammi karki damu,ba abinda zai faru....in sha Allahu"

"Ina saka ran haka". Daga nan suka aje wannan maganar suka shiga wata kuma daban.       Shiga nan fita can,bashi ya isa gida ba saida dare yashiga yasoma danyin nisa,duk da daya batayi ba,yabude motar bayan ya fakata yakashe,yakulle sannan yanufi cikin gidan.       Bai tsammaci zai taddata a falon ba,saiya sameta zaune tana kallon tv,hannunta riqe da cup na lemo.lokaci lokaci tana kurba,duk tayi hakanne don kada bacci ya dauketa ba tare daya dawo ba bata sani ba.      Kai ta daga suka hada idanu,sosai ta bata rai,don bataji dadi ba,wuni taso suyi tare ta morewa zuwanta,amma ta lura kaman yana avoiding dinta ne,baison zamansu inuwa daya,bayan duka don shi tazo din.       Ya lura taji babu dadi sosai,don haka ya sakar mata murmushi wanda ya wanke dukkan wani bacin ranta tashun farko,saita saki ajiyar zuciya kawai tana lumshe idonta,lokaci guda kuma ta budesu akanshi,take tahau shagwabar tata data saba,yasamu daya daga cikin kujerun yadan dosana kamar yadda yasaba zama a falon,bai wani fiya zama harya sake koya dauki dogon lokaci ba.     Dole wannan karon yadan zauna da ita,yabiye mata,yadan jima duk asonshi na yaja ra'ayinta karta bishi samanshi,saidai ina sam bata yarda ba,cewa tayi saita rakashi tazauna tayi gadinsa har yayi bacci sannan tasauko,a yadda yasan sangartar safwa,yasan bataqi ya matsa mata ma gefan gadonsa ta kwanta ba,zatace tunda su sunsan babu wani abu tsakaninsu to ina ruwansu da wani,yadan dafe goshinsa da hannunsa yana ayyana yadda zaiyi da ita,saidai kafin ma yagama tunanin ita harta aje cup din hannunta tadauki key din daya shigo dashi da wayarsa tasoma haurawa saman,saiya bita da kallo kawai,babu yadda zaiyi da ita,iyaka idan sunje ya lallaba tasauko,don haka yamiqe yabi bayanta.       Dai dai lokacin da mama sodangi ke fitowa daga dakinsu,tunda taha safwa batayi bacci ba hakanan itama saita kasa,yanzun kuwa data ga tayi saman azeez din duka sai taji ranta a jagule,bata shakkar azeez amma tana sane da abinda yake damunshi,kuma babu wanda yafi qarfin shaidan sai wanda Allah ya kare,ita sam wannan ziyarar ta safwa batayi mata ma'ana ba,tayi mamakin duk tsantsenin fulani da kularta akan azeez data bari safwa tazo,kodon tana ganinta a tsakaninsu?,gaba daya saita kasa nutsuwa takoma tazauna tana kasa kunne taji saukowar safwan.       Ko a jikinta haka ta baje saman gadonshi tana masa hira,kamar yadda suka saba ba komai yake iya bude baki ya bata amsa ba,a hakanma yana qoqartawa duk don kada taga ya wulaqantata,haka yashiga wanka da kayan jikinsa yashirya a ciki sannan yafito.       Idanu tasa tana qare masa kallo,yadda kayan suka bala'in masa kyau,quruciyarsa qarara tasake bayyana,hakanan wannan sihirtaccen kyan nasa mai kashe gangar jiki da zuciya,shima kallonta yake hannayensa harde a qirji,yadda suka zubawa juna idanu yasa yasoma jin wasu abubuwa na yawo cikin jikinsa,yayi nisa wajen qoqarin yaqar abunda yake ji din,bai ankara ba yajita cikin jikinsa ta rungumeshi tana sakin qaqqarfar ajiyar zuciya,take qamshinta yasoma shiga hancinsa,gashinta dake fake yasoma gugar fuskarsa,tsigar jikinsa ta zuba,ya janyeta da sauri daga jikinsa,idanunsa na nuna zallar bacin rai

" meye haka safwa?"ya fada a kausashe,saita sake zuba masa idanu kafin daga bisani qwalla tacika idanunta,tajuya masa baya da sauri ganin suna niyyar gangarowa

"Saboda na rungumeka yarima shine kakemin tsawa haka?" Ta fada muryarta tana rawa,sai yayi qoqarin cooling kanshi,yasani wala'alla shine mutum na farko daya soma.mata tsawa a rayuwa,tunda yasan sarai irin gata da shagwabar da take gaban iyayenta

"Babu komai nagode,nina kawo kaina,ko kuma nace soyayyar da nake maka ta janyomin" saita soma takawa zata fita daga dakin,don harga Allah taji haushi sosai,a wajenta runguma ba komai bace,don hatta da mahaifinta takan iya rungumeshi,a wajenta da waccar da wannan duka daya ne,sannan idan kanason mutum ba komai bane hakan,tunda ba wani abu ka aikata da zai nuna a jikinka ba.       Karon farko daya kama tsintsiyar hannunta,wanda sai dayaji sosai ajikinsa,dukkan gabbansa suka amsa,ita kuma abinda ya sanyayar da ita kenan,saboda makamancin hakan bata taba faruwa ba a tsakaninsu.       Saman kujerar dake dakin ya ajeta,kana yazauna sosai a gabanta yana duban fuskarta

"Duba da girmanki kike wani kuka?,kin manta shekara biyu kawai.na baki zaki zauna gabana kina kuka?,oya share hawayen" murmushi ya kubce mata,saita sanya bayan hannunta tana goge qwallar data soma zubo mata,sai data gama tsaf sannan yace

"Akwai abubuwan da mu a idanunmu zamu dinga kallonsu ba komai bane,saida a addininmu haramunne kuma dole kowanne baligi da baliga su gujeshi,kamar yanzun,kebancewar da mukayi kadai ni dake musulunci ya hanata,kinsan dalili?"saita girgaza kai

"Saboda indai mace da namiji suka hadu a wani kebantaccen waje wanda daga shi sai ita,to ba shakka shaidanne na ukunsu matuqar ba ma'aurata bane su,i did'nt mean anything,nasan xakita tunanin abubuwa kala kala,to duka ba wannan bane....yanxu kinga dare yayi,bai kamata ace muna nan zaune a tare nida ke kadai ba,kije dakinki ki kwanta,i promise gobe xamu wuni tare" kalamansa sun wanke duk wani fushi da bacin ranta gaba daya,ba lafuzzan bakinsa ba,hatta da sound din azeez din mai taushine da wanke zuciya,ta jima bai zauna haka ya jera mata kalamai masu nuna kulawa da lallabawa haka ba,saboda tsabar miskilanci da jinin sarauta dake yawo a jininsa,shi yasa yau take jinta a duniyar sama tana yawo.       Salin alin ya rakata har qofar dakinta tashige,sai da yaga ta shiga sannan ya saki ajiyar zuciya,dai dai lokacin da mama sodangi itama ta maida qofarta tarufe tana sakin ajiyar zuciyar itama,ba shakka akwai matsala kuma za'a samu damuwa ita tasani,jikinta yana bata mawuyacine idan ba lokacin karbar qaddarar bilkisu bane nabiyu ya durfafota,kafin ta kwanta ta yankewa kanta shawara,shawarar da take fatan xata canza komai,ciki harda tunanin bilkisu dakuma rayuwar azeez gaba daya.


*******    *******    *******


      Washegari hakanan babu yadda ya iya ya kashewa safwa lokacinsa gaba daya,wuni gida sur,daga nan zuwa can,wuni yayi mata dadi qwarai fiye da dukkan wasu wuninnika na rayuwarta,tayi yadda takeso takasance da azeez din son ranta,wanda tsahon tarihin soyayyarsu basu taba kashe awanni haka masu yawa tare ba.       Saidai duk da hudubar da yayi mata daren jiya hakan bai sanya ta fasa tabashi ba,musamman idan taga wani abu daya burgeta ko yayi mata,hakan yasake takurashi da matsa mishi,ya fuskanci kusam dabi'arta ce haka,ta saba har batasan sanda takeyi ba,haka yadinga qoqarin kakkauce mata har zuwa sanda suka dawo gida.      A ranar kam yayi kwanan wahala qwarai,yasan kuma dalilin tashin ciwon nasa bai rasa nasaba da safwa din,shi yasa washegari da take shirin komawarta hakan ya masa dadi,duk da cewa bai nuna ba.      Tun safe take ziryar samanshi amma saita tadda qofar a rufe,tayi kiran wayoyinshi dukka a kashe,yana dakin kuma duk knocking din da takeyi yana jinta,yana sane yayi hakan,don baiso tashigo ta qarawa wuta fetur.      Data gaji take tambayar mama sodangi

"Ina tsammanin yafita ne,qila akwai wani uzuri daya fiddashi" wannan amsar da bilkisu taji ta bata ya sanyata jan tsaki,tana ziro qafafunta qasa da niyyar fitowa daga qunshen data yiwa kanta,cikin zuciyarta tana cewa

"Ashe bainan,inataso nafita amma nake zaune".      Riga ne a jikinta shirt mai gajeran hannu sosai,wanda hakan ya bayyana santala santalan hannayenta,iyakar rigar qugunta,sai wando high waisted wide leg daya dace sosai da rigar,baqar doguwar riga ta dora akai mai sulbi saqar wasar oman,tayi rolling da mayafin rigar,sai tayi wani kyau,kai kace baqar balarabiya ce.      Dai dai lokacin tasan dukka suna kitchen,don kusan dama da ita ake girkin,tasan lokacin kowanne abu,don haka can ta nufa kai tsaye.       Gab da zasu shiga sukayi kacibus da safwa tana fitowa,hannunta riqe da cup data cikoshi da fresh milk,bayan ta gama zirga zirgar neman azeez din.      Kallon juna sukayi,bilkisu ta rabata tawuce,yayin da safwa din ta bita da kallo harta shige,kana ta qarasa ficewa daga kitchen din,zuciyarta na raya mata bilkisun sam batayi kama da hadimai ba,batasan me yasa yarinyar ke tsaye mata ba,take kuma cika mata idanu.     "La la la,mama kika ce tare zamuyi,badon na shigo ba saidai acemin an gama?" Tafada tana duban qullin alkubus da mama sodangi ke bugawa zata turara

"Aina dauka yau hutun uwar dakin nawa ne yamotsa,tuba nake" murmushi tayi kawai tana hayewa saman wata kujera mai dogon mariqi tana duban rakiya dake qoqarin hada miyar alkubus din,mamakin inda suka samu kayayyakinmu na nigeria takeyi,saidai bata tambaya ba,don ba mutum ce ita mai bin qwaqwqwafi ba

"Ba amana" ta fada a taqaice tana jifan rakiya da hararar wasa,dariya tadan saki kana tace

"To ya zamuyi?,tunda so kike ki sake zama ta ɗaka ta ɗaka"

"Kul" mama sodangi tayi saurin kwabar rakiyar,sai ta sadda kai

"Afwa mama". Murmushi kawai bilkisun tayi,wani lokaci maman tana bata dariya,ita har yau wani girma take bata,bayan itadin bamai girma ko qima bace,saita sauko ta cire after dress din nata tana amsat bugun daga hannun maman

"So nake nakoya sosai,shi kadaine yafi wahalar dani a girki".       Suna tsaka da aikin safwa tasake shigowa zata aje cup din hannunta,hakanan idanunta suka dinga yawo kan bilkisu,saboda yadda dirinta da shape dinta suka bala'in fitowa ba,ba namiji ba ko.mace ta kalleta ba shakka zatasan cewa ba qaramin ajiya Allah yayi a wajen ba,sai a sannan tasake yarda,bawai tsaho kawai sirantaka ko farar fata ce zallar kyau ba,tunda ga choculet colour skin mai matsaikacin tsaho dauke da qirar data bata mamaki,bata mantawa kwanaki saida ta dinga amfani da supplement don ta fidda qirarta sosai kawai donta burge azeez dinta,tabi sassalkan gashinta da kallo,wanda bugun fulawar da take yahadu da santsin gashin yasanya daurin dankwalinta warewa,gashin duka ya bayyana.       Cikin sakan qasa da talatin sassanyan qamshinsa ya baibaye ilahirin kitchen din,kafin daga bisani lallausar muryarsa mai cike da kwarjini dakuma izza tabiyo baya da kyawawan lafuzza na sallama.     Dukkansu suka juya,banda bilkisu wadda cikin sakanni da basu wuce uku gudun zuciyarta ya ninku,kowacce gaba ta jikinta tadauki rawa,zuciyarta kuma take yanke ta gaya mata waye,sai taji kamar an kafeta,ko wuyanta ba zata iya motsawa ba bare ga juya,dana sani da nadamar abinda yafito da ita daga daki suka baibayeta,tanajin yadda mama sodangi da rakiya suke gaidashi cike da tsa tsar girmamawa yana amsawa cikin ginshira da isa ta sarakai.       Sam bai kula da mutum ba bayan wadanda sukayi magana dashi,har sai da safwa dake tsaye a bayanta tayi magana cikin shagwaba

"Hey dear....karkacemin kana cikim gidan nan?" A hankali yadauke idanunshi daga kanta,duk dabaisan wacece ba amma zuciyarsa ta gaya masa yarinyar rannan ce,abu guda daya tak dabai manta ba tsaho da sulbin gashinta da idanu sukan iya gani koda bilkisun na nesa dakai,wani abu yakeji yana tsirga masa,dalili kenan daya sanya ko cikakken kallo bai yiwa mace sai idan ta kama dolen dole

"Hey...." Ya amsa mata kwai a taqaice,yana sake qoqarin lanqwasa kansa da yiwa idanunshi shamaki wajen maida dubanshi ga halittar dake tsaye,ganin kamar yana gab da gaza hana idanunshi saiya juya zai fice,safwa ta rufa mishi baya,yayin da mama sodangi ke tambayarshi idan yana da buqatar wani abun yafadi akawo masa

"Ba abinda nake buqata" ya amsa mata ataqaice yana ficewa.       "Yarima yarima kenan

"Wai nikam mama,dama can haka yake,bayacin abincine waishi" dan dariya mama sodangi tayi

"Kin taba ganin mutumin da baya cin abinci?kawai dai mutum ne shi mai qa'ida tun yana yaro,hakanan yana da tsantsami,abu qalilan zai gani ya fasa cin abinci ,yana da tsari dakuma kalar abincin da yakeso,baya son qazanta ko kadan,shi yasa zakiga kamar baicin abinci,yana da zabi,ba kowanne yake ci ba"dukkaninsu babu wanda yalura da yanayin da bilkisu ke ciki ba.     Hannayenta ta zare daga cikin flour sannan ta yayibi after dinta da dankwalinta,tanason fita tana kuma tsoron kada ta samesu a falo,idanunta ta runtse kana ta saka kai,saidai cikin sa'a babu kowa a falon,hakan shi ya bata damar wucewa da sassarfa zuwa dakinta.

Siyayya sosai azeez din yayiwa safwa,bawai don bata dashi ko tana buqata ba,a'ah,sai don kyautatawa dakuma amminsa daya tabbatar da cewa zataji dadin hakan,don ya fuskanci a rayuwa tana matuqar qaunar tarayyarsu da safwa din.       Shi da kanshi ya kaita airphort bayan ya siya mata ticket,sukayi sallama,sai a sannan hankalinsa yakwanta,saidai ta tafi ta barshi da tarin ciwukan da baisan lokacin warkewarsu ba.


*******    ******   ********     Karo na uku kenan data kawo mata wani abu cikin cup tace ta shanye,kuma wai ita kadai,don bata bari ko a gaban idon rakiya tabata,akwai yarda da aminci tsakaninsu,don haka babu wani zato ko kokwanto,barema dukkan abinda take batan akwai dandanon madara sosai da garɗin wasu abubuwa da batasan meye ba.       Tana tsaye saman kanta tana dubanta,har ga Allah tanayine saboda taimakon bilkisun,tana kuma yine cike da fata da kuma saka ran kome zaya faru bilkisun taci gaba da zama a matsayin da take dashi yanzu,wannan shine babban fata da burinta na komai ya canza.      Jikinta yana bata komai yana iya faruwa sa bilkisun cikin kwanakin,hakan yasanya hatta da ruwan wanka sabulu da turare nata na dabanne,wanda hakan yasake tsumata da sauya mata fata da odour na jikinta zuwa wani yanayi na musamman,duk da batasan manufar mama sodangin ba,amma canje canjen data qara gani akan nada yabata mamaki,saidai batayi magana ba,tayi shuru tana kallo.        Sai data shanye sannan mama sodangin tazauna a gefanta tana dubanta,cikin tausasawa tace da ita

"Ina fatan baki manta matsayinki cikin gidan nan ba,dakuma abinda yayi silar barowarki qasarki" wani mummunan faduwa gabanta yayi,kana ta daga kai tayi ta dubi mama sodangi cikin mamakin jin furucinta,ta tuna mata da wani babban abu da ita ta manta dashi ko tace ta shagala,wanda tasan yin hakan tamkar yaudarar ce tayiwa kanta,saita gyada mata kai a sanyaye

"Kome zaya faru bilkisu ki tareshi da kyakkyawan fatan zai sauya dukkan zuciyoyi da tunani zuwa bigiren alkhairi a taki rayuwar,kiyi haquri da dukkan.abinda ka iya faruwa,kome zanyi zanyine dominki bilkisu,zanyine don hakan yazama sila na wanzuwar abinda ba'a taba kawoshi cikin tsari da tunani ba" saita miqe ba tare data iya kallon idanuwan bilkisun ba,itama saita bita da kallo harta fice,bata iya gane komai cikin kalamanta ba,bata sani ba ko qwaqwalwarta ce tayi qanqanta da kalaman sun mata girman da bazata iya fasasu ba,daga bisani data gaji da qoqarin fassara komai saita watsar tashiga sabgarta.        Cikin kwana daya tal mama sodangin tasauya mata dukka kayan baccinta da nau'in wasu kaloli masu kyau tsada da daukan hankali,duk da basuyi mata ba ita a yadda takeso amma haka ta haqura,saboda tunawa kanta da tayi wacece ita?,karta zarme da yawa,itadin tamkar aikin kwangila ne ya kawota gidan,so zabe ko nuna ra'ayi duka ba nata bane.      Abu na biyu data lura dashi shine yadda mama sodangi ta maida musu lokuttan kwanciyarsu daga qarfe takwas na dare,sabanin da dasai tatafi daki ta kwanta ma tabarsu,musamman alokuttan datasan cewa yarima yana iya shigowa,shima duka bata damu ba,idan ta koma dakin taji batajin bacci sai ta dauki wayarta ta rage dare da ita har zuwa sanda zataji bacci,kusan kwanaki uku kenan hakan ma faruwa kafin mai afkuwa ta afku,mai afkuwar data sanya ta gane dalilin samun dukkan sauye sauyen data gani.
          *12:30 am*       Tun sanda tabar falon takoma dakinsu take kwance tana juyi daga farkon gadon zuwa qarshensa da wayarta a hannu tana browsing abubuwan da tasan zasu amfaneta,tun tanayi cikin marmari harta gaji bayanta ya qage,don haka ta aje wayar ta sauka daga gadon,mintuna wajen biyar takashe tsaye gaban ma'ajiyar kayanta dake lafke da kaya,wanda ita kanta batasan sanda ta tarasu ba,dukka mallakinta ne,hakanan lokaci lokaci takanji mama sodangi na waya da wata mace da take kira da fulani,wadda har yanzu batasan matsayin matar ba,duk da tajima tanajin sunanta bakin umma luba kafin mama sodangin,saidai tafi zargin ita ta asassasa dukkan wani abu dake gudana a yanzu cikin rayuwarta.       Takanji tana tambayarta me suke da buqata?,yaya zamansu yake,takanji ta aiko mata da kudi tace ayi siyayya,sukan aje mata sabulai mayuka suturu da taruruka masu dan karen tsada kyau da gyara jiki duk bayan wasu lokutta,saidai bata sani ba,ita fulanin ce ke bada umarnin ko a'ah,amma tafi tunanin ita dince,tunda sauyin bai faruwa yawancin lokaci sai bayan mama sodangi tayi waya da ita.      Bakinta ta tabe,ita sam a rayuwarta a baya bata san wani sanya kayan bacci ba,sai gashi lokaci daya an mata sabo dasu,hakanan ta zari daya daga cikinsu da takejin tafi kwanta mata,mai wani irin taushi da sulbi,ta cire kayan jikinta sannan ta sanyata,ta daure madaurin dake jikinta kana ta daga kai tana duban agogo.       Idanu ta zaro tana mamakin lokuttan data bata har haka akan waya,bacci takeson tayi amma qishirwa takeji sosai data sanya maqogaranta bushewa,dole tana da buqatar ruwa,don haka ta zura slipper mahadin kayan data gani a jiki,tabude qofar dakin a hankali ta durfafi kitchen,don tasan a canne kawai zata samu ruwa mai irin sanyin da takeso.
        Zaune yake a daya daga cikin corner din kitchen din,idanunsa aruntse,hannunsa daya riqe da cup na ruwa,yayin da dayan yafin hannunsa ya runtse qwayoyin yana tantama da tunanin yiwuwar shansu ko a'ah,yayima kanshi alqawarin yadaina sha tun a wancan lokacin,to amma yanayin daya samu kan nashi a yanzun bashi da wani solution idan ba shan zaiyi ba,hakanan rashin shan nasa baisan wanne irin sakamako zai haifar masa ba,wala'alla sai yafi nashan tablet din muni.       Takun daya soma ji yasanyashi bude idanunsa da suka kada suka canza launi zuwa bakin qofar,karon farko da yaga fuskarta sosai fiye da gani guda biyun da yayi mata a baya,a hankali take takawa zuwa inda fridge din yake,alamu sun nuna kamar tana tsoron wani abu ne,wala'alla daren daya soma yine,ci gaba yayi da qare mata kallo har zuwa sanda ta dauki ruwan taci gaba da takawa cikin sanda wanda tafi kama da yanga tabar kitchen din ba tare data lura da wanzuwarsa a wajen ba.      Sosai yasake rintse idanunsa kamar zai shigar dasu ciki,wani abu yana yawo sosai a jikinsa,ganin da yayi mata tamkar wani fami yasake zame masa,saiya kasa ci gaba da riqe kofin hannunsa,ya ajeshi gefansa hannunsa na rawa.       Ya kusa mintuna biyar kana yamiqe yana qoqarin daidaita kanshi yafice daga kitchen din,sanda ya iske falo saiya kasa ci gaba da tafiya zuwa samanshi

"Halal dinka ce,halal dinka ce" yaji wani sashe daga qwaqwalwarsa yana gaya masa tamkar wanda akewa magana atsakiyar kanshi.      Tabbas bashi da wata mafita,yakai irin stage din da idan ba allura zaiwa kanshi ba zaiyi wuya ya iya controlling kansa,ya riga da ya yiwa ammi alqawarin barin allurar dama magani gaba daya,kamar wanda mayen qarfe yake ja haka yadinga jinsa kamar ana fusgarsa zuwa cikin dakin,sannu a hankali har ya isa bakin qofar,yasa hannunshi saman handle din yamurza tabude ya sanya kanshi ciki.       Dai dai sanda qofar tabude bilkisu dake kwance tsakiyar gadonta tana sauraren bacci ya sureta tabude dukkanin idanunta cikin sauri da wata irin matsananciyar faduwar gaba,saidai bata iya ganin komai ba sakamakon duhun dake mamaye a dakin,wanda tuni dama takashe duk wata fitila ta dakin don tagama shirin baccinta.      "Waw.....waye?" Ta tambaya cikin tsananin tsoro,bai amsa mata ba yaci gaba da nufar direction din da yasan zai kaishi zuwa inda fitilar gefan gadon take,a nutse yadora hannunshi ya kunnata,wani qaramin haske da baikai yakawo ba ya bayyana,hasken da bai iya nuna maka zahirin fuskar wanda kuke magana dashi.        "Way....waye?" Ta sake tambaya cikin kakkarwar murya karo na biyu

"Abdul'azee" ya bata amsa da wata iriyar gajiyayyar murya,abdul'azeez?,tasake furta sunan can qasan zuciyarta,sunan data jima da haddaceshi qyam a qwaqwalwarta,sautin muryarsa da qamshin turarensa suka qarasa bayyana mata wayeshi,gaba daya jikinta yasaki yamutu,ya lumshe idanunta tanaji a jikinta koma meye a yau komai ya qare yazo qarshe,damar da take tunanin ta samu ko zata samu ta qare mata,tasan qaryarta,bata da bakin wata magana ko yunquri,anzo wajen da zatayi bautar da take tunanin ita aka kawota tayi,wasu zafafan hawaye suka biyo kuncinta,ta cure waje daya tana jin kaduwa da tsoro har cikin hanjinta,tanajin kamar ana mata bushara da cewar mala'ikan mutuwa ke isowa gareta.       Ba zata iya cewa ga yadda akayi ya kawo kanshi gareta ba,kamar yadda ba zata iya adar da yadda komai yasoma wakana ba saboda tsantsar tashin hankalin data shiga,yau cikin wata qasa cikin wani dare a cikin wani irin yanayi zata rasa 'yancinta da alfaharinta na diya mace,wanda tasan dama kamar an riga da anyi cinikinsa tun ba yau ba an biya iyayenta.       Abu uku xuwa hudu kawai zata iya tunawa,yanayin qamshinsa,addu'ar dataji yanayi tun afarko,muryarsa da bata tantance me yake fada ba,da kuma 'yar banzar azabar data ci,wanda shine abu na qarshe da bata sake sanin meke faruwa da ita ba harsai bayan wasu awanni data farka,ta fuskanci azabar data sha da kuma zallar tsoro da baqinciki suka hadu suka sumar da ita.       Lokacin data farka ta fuskanci akwai mutum kusa da ita,ta qanqanuwar fitilar gefan gadon take iya hango inuwarshi,saidai bata iya ganin fuskarshu,xaune daura da ita,da 'yar qaramar tazara a tsakaninsu,da alamu babu wani bacci daya iya daukanshi,idanunta ta maida ta rufe,saita fashe da kuka,kukan daya sanya abdul'azeez ya fahimci cewa ta farka bayan dukka taimakon gaggawar daya bata

"Am really sorry" ya furta a hankali yana jin zuciyarsa sam babu dadi,taji sarai abinda yafurta din da qaramar murya can qasa,tana jin sanda tamiqe ya soma takawa sannu a hankali yafice daga dakin ba tare da ya waiwayo ba.      Bai rufa minti biyar da fitar ba taji an kuma turo qofar,kana aka kunna makunni qwan dakin,haske ya mamayeshi,ta tsammaci shine don haka bata bude idanunta ba,hakanan bata fasa kukan da take ba

"Bilkisu" aka kira sunanta,a sannan ta fuskanci mama sodangi ce,saita bude idanun nata da suka kumbura suka mata nauyi ta dubi maman,fuskarta sam babu wata walwala ko digon fara'a,tasoma takowa inda bilkisun ke kwance,ita kuma tasake maida idanun nata tarufe,takuma dora kukanta daga inda ta tsaya.      Mama sodangin kusan ita ta gyarata tayi mata komai kana ta kakkabe mata dakin tacire zanin gadon ta sauya wani,ta barta tana sallah daga xaune itakuma tasake ficewa,daga yanayin yadda take aikin xaka tabbatar jikinta itama a mugun sanyaye yake,ga bilkisu kuwa hawaye sunqi barin idanuwanta,tana daga xaune take sallar don ba xata iya tsaiwa ba,koda ta idarma saita hada kanta da gwiwa tana kuma sakin wani tsumammen kukan,dukkan abinda yafaru da ita a daren jiyan yadinga tariyar kansa da kansa a kwanyarta.       Shi kadai yadinga sakin ajiyar zuciya qasan shower din idanunsa a rufe lokacin da ruwan ke sauka yana ratsa kowanne sashe na jikinsa,yana tuna dukkan abinda yafarun,wanda yake jinsa tamkar a mafarki,kamar ba shine abdul'azeez ba,yana feeling guilty ta wani sashe na zuciyarsa,yayin da wani sashen kuma yakejin he is innocence,matarsa ce,abinda yayin akwai tarin bambanci tsakaninsa da wanda shedan yakeso yayi,koma meye dai aure aurene,kuma matarsa ce,duk da har yanzu gulitiness din da yakeji a zuciyarsa yana nan,amma yanajin wani yanayi na daban a gangar jikin nasa da zuciyarsa gaba daya,duk wani nauyi daya dade saman zuciyarsa da gabbansa yanajin babu shi,yanajin kansa fresh,tamkar ranar amminsa ta haifeshi,yayin da wani irin happiness ke kutso yanayin da yake ji yana ratsashi,kallo daya zakawa fuskarsa ka karanci hakan,duk da cewa baisan hakan yana bayyana ba,da ire iren wadan nan tunane tunanen ya kammala tsarkake jikinsa sa'annan yayi wanka yafito.       Mama sodangin ce tasake shigowa dakin karo na biyu,dauke da kofi me cike da kakkauran tea sai zuba qamshin ganyan shayin ahmad tea yake,yana fidda turari,tayi sallama duk da bilkisu bata amsa ba,tasamu gefanta tazauna tana riqe da kofin,saita ajeshi gabanta sannan tace

"Ki daure ki saka wani abu cikin cikinki,likita nakan hanya,zata dubaki" ko motsawa bata iyayi ba bare ta daga kanta,lallashin duniya mama sodangi tayi mata amma bata iya motsi ba,ta sani koda ta kurba abune mawuyaci ya iya wucewa maqogoranta,a haka sukaci gaba da zama har sanda rakiya taturo qofar dakin ta shaida mata zuwan likita.      Dr huda,matashiyar likita,wadda qalla ta doshi shekara ashirin da bakwai,mutum mai haba haba da son jama'a,uwa uba fara'a,kusan ita ta hilaci bilkisu tasha shayin dakyau kafin tafara dubata,tanayi tana tsokanarta,saidai hakan bai rage komai cikin abinda take ji a zuciyarta ba,daga qarshe saita lumshe idanunta kawai tadaina ganin kowa saijin zantukansu.      Tayi mata dukkan abinda yadace,ta dubata dakyau ta bata magunguna,takuma fadiwa mama sodangi yadda zata mata treating wajen tawarke da wuri,baqinciki da kunya suka cikata,yanzu kowa ma sai yasan abinda yayi mata?,daga bisani tasa mama sodangi ta bata waje tace zasuyi magana da bilkisu

"Yi haquri ki bude idon ki kalleni" kasa yin yadda tace tayin tayi,saita zauna dab da ita ta kamo hannayenta

"Don Allah badon ni ba" dole ta budesu tana duban dr huda,saita sakar mata murmushi

"Hala kinwa ango gaddama ko?...." Bata da amsar bata illa shuru,saita sake murmushi tana dubanta

"Ba'a haka qanwata.....miji irin azeez kike jawa aji?" Da kallo dai tasake dubanta tana kuma sauraren maganganunta harta gama,ta dora da bata shawarwari,wadanda su da babu duka dayane a wajenta.      Saidai yadda ta jata a jiki da yadda tasan aikinta ya burge bilkisu,har taji tadan burgeta,taji inama ace itace dr huda,inama ace itace tasamu cikakkiyar damar kammala karatunta,tana sha'awar ta zama wata,saidai almakashin qaddara yasa kaifinsa yana daddatsa rayuwarta in to pieces,wannan abun daya faru yasanya take dukkan wata dama tata a rayuwa ta qare,duk wani buri nata ya rushe,babu wani sauran abinda yarage mata kuma.²⁸

Post a Comment for "SIRADIN RAYUWA CHAPTER 8 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...