SIRADIN RAYUWA CHAPTER 3 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 3 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 3 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

- - Post a Comment

 SIRADIN RAYUWA CHAPTER 3 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMAZauna ki lissafa duka ƙannenki ki zabar musu kowa yasaka,yau fulani inajin juyen kayan drower ɗinsu sukayi....ki zaɓa na saida na saidawa,na bada na bayarwa,don ba shakka waɗan nan kaya yadda suke fes kamar ba'a sanyasu ba ƙaramin kuɗi zan samu dasu ba Allah mai gado" murmushi takuma saki wannan karon mai sauti,tana sake jinjina son kuɗi irin na umma luba,kayane masu asalin kyau daraja da tsada,wanda duk wanda ya kalla koda bakasan kuɗinsu ba amma kasani ba masu 

ƙarami ko matsakaicin kuɗi bane,tanajin umma luba naci gaba da sambatu gami da bata labarai,ta tsugunna tana duba su hauwa'u tana zaɓarwa kowa,duk da sauran tasan sun musu yawa amma haka ta ɗauka musu,tana kintatar zata bayar a maida musu dai dai jikinsu.

"Ana abu a masarautar KAISA,wani abunma sai jibi idan Allah yakaimu" takai ƙarshe tana sakin guɗa,da alamu dai cikin nishadi take yadda ya kamata.Sunan masarautar dataji ya fito daga bakin umma luba sai taji duka kayan sun fice mata arai,AFNAN itace abu na farko daya soma faɗo mata a rai,kenan kayan sjn fito ne daga gidansu?,wala'alla ba za'a rasa nata a ciki ba,sai taji kamar ta barwa umma luba kayan,amma hakan bazai yiwu ba,saboda niyyar alkhairi tayi a gareta,dole ya hade kansu ta bata leda babba ta saka ta mata godiya kana tafito.


Kamar yadda ta qudirta din bata koma gida ba sai data shiga makaranta ta bada haddar dake kanta,saboda bata son ta  rasa rana daya cikin ranakun zuwanta makaranta,musamman da a yanzu suke gab da kammala haddace qananun litattafan addini su tafi zuwa manyan,ba qaramin dadin karatun takeji qwarai da gaske,koda yaushe takan godewa Allah wanda bayan ya hanata wasu abubuwa na rayuwa amma bai hanata hasken ilimi da qaunarsa ba,ba ita ba koda qannenta a yanzu ba zaka kirasu jahilai ba ta fannin addini,tunda alhmdlh dukkaninsu suna zuwa makarantar Allo da safe,suje ta magariba bayan sallar magariba.A hanya take tunanin abinda zata siya musu suci,saboda tasan bata bar musu abincin dare ba,hakanan babu yaqinin za'a basu suci,taso siya musu wani abun amma duka abinda ta lissafa zaija kudine,sai taliyar hausa ta fado mata a rai,idan ta siya kuma akwai bata lokaci kafin dahuwarta,mai yiwuwa su qosa ko wasu daga cikinsu ma suyi bacci,saita wuce gida kawai tana fatan asamu sauran abincin sayarwa wajen umma katti,tunda ba'a rasata da saura.Tun daga soron gidan mamaki yacikata fal jiyo muryar mahaifinsu yana hira cikin walwala da dariya

"Allah hakimu,yau kuma wanne manzan rahamar aka saukar mana?" Tayiwa kanta tambayar zuciyarta cike fal da taraddi,ba zata iya tuna lokaci na qarshe data jishi cikin irin wannan yanayin cikin tsakar gidansu ba,idanma zata tuna din zata iya cewa tun aurenshi na qarshe da yayi suka rabu,da wannan tunanin ta qarasa kutsa kai cikin gidan.Bata sake daskarewa ba sai data ganshi tsakiyar yaran,ko ina farantai nashe nashe da shinkafa da miya kowa na kaiwa baka,data lura dakyau ma sai take ganin kamar tsokokin kaji saman abincin,a haka ta dinga takowa idanunta akai,tana jin tamkar mafarki take

"Ke meye hanka,kalli gabanki mana,idan kuma yunwa kikeji kije ki amshi naki abincin wajen kattime" muryar mahaifinta kenan dake magana yau cikin cikakkiyar isa sabida cikakken awo da cefanen da yake ganin yayi,maganar tashi taja hankalin 'yan uwanta kan shigowarta,dukka suka bar abincin sukayi wajenta,wasu suna mata sannu da zuwa,yayin da wasu keta faman nuna mata rasha da gwabar da yau suka samu a gidan nasu,wanda sun manta rabonsu da samun koda arziqin fara damai da gishiri bare miyar kaji,wasu daga cikinsu ma namam suketa tura mata taci,saita maida hannayensu cikin sanyin jiki,don ita sam abun bai mata ba,hakanan bai burgeta ba,suma don basu gama sanin ciwon kawunansu bane,ta tabbatar da walakin,hakanan akwai wata a qasa,cikin tattausar muryarta da take tsarin halittarta tace

"Na gode,maza kuzauna kuci"

"Kujimin ja'iran yara,yo itama da nata kason ai,banson kilbibi idan zaku zauna kuci ku zauna" baban nata yakuma fada,duk sai suka zauna sukaci gaba da cin abincinsu.Sai a sannan tadubi sashen da baban nata yake a ladabce tace

"Barka da wuni baba,an wuni lafiya"

"Lafiya lau,sai yanzu kike dawowa?" Ya fada kamar yana ganin takai dare da yawa,kai ta jijjiga kawai

"Eh....na tsaya makarantar dare ne"

"To madalla" ya amsa yana afa lomar shinkafa bakinsa,miqewa tayi zata wuce dakinsu,sai kuma ta fasa taga gwara tasoma sauke nauyin bashin kudin umma katti a kanta,saboda haka tasauya akalarta zuwa dakin nata,dai dai lokacin da baban nata ya qwalawa umman kira yana cewa

"Kattime....kinga...gwara ki fito ki sake abinki,kici kazarki kisha jar miya ki godewa Allah da budin daya kawo yau"

Wani mugun tsaki ta saki sanda bilkisu ke saka kai dakin

"Ka hutar da yawun bakinka,aiba saika fada ba abinci zancishi,tunda haƙƙina ne Allah ya ƙwata yabani yau,amma duk wani iyayinka da ɗigiminka na riga dana daɗe da haddacesu,jiya bayau bafa,nasan dai ƙarshen alawa qasa,to mu zuba mugani,Allah ya bada sa'a" ta qarashe zancan tana dukan cinya gamida zunkuda zamanta,da alama masifa tana cinta.Sallamar bilkisun ma sama sama ta amsa mata,bata bata dukka hankalinta ba sai dataji da biyan bashi tazo mata,saita maida kai sukayi lissafi ta cire mata kuɗinta,tasa hannu kuwa ta amshe abinta ta linke kana ta tura mata kwanon abinci har guda biyu,daya shinkafa daya miya

"Ga naki kason nan,yau Allah yayi babu kwanan yunwa" umma kattin ta fada tana sake gyara boyon kudinta,da kallo tabi kwanukan,ita sam ko daya abincin bai bata wani sha'awa ko armashin ci ba,saboda ba umma katti ba,ko ita tasoma shanshano abinda ke shirin faruwa cikin gidan,wata ƙila ma nan da wasu 'yan kwanaki masu zuwa

"Allah ya amfana" kawai ta fada tana ɗiban kwanukan tafice zuwa dakinsu,yaran na ganin fitowarta kuwa dukka suka bita daki sukabar baban anan,don dama ba wani sabo ko shaquwa bane tsakaninsa dasu.Kaya tacanxa ta ninke wadancan don sune nadan fitar sannan taxauna sosai tajawo kanukan tasoma budewa,dai dai lokacin da amina wadda itace qarama a cikinsu tace

"Yaaya yau abincin yayi dadi wallahi,hadda naman zakara irin na gidansu hasana" ta qarashe maganar alamun walwala da annashuwa na bayyana muraran saman fuskarta,sai murmushi ya subewa bilkisun,yayin da hauwa hannatu da umaima suka sanya dariya

"Wai kice aikin babba ne aminatu,zakara ne bama kaxa ba"sai a sannan maganar ta bawa yarinyar dariya itama

"Ku matso maza musake ci" hannatu ta zaro ido tana sha cikinta

"Ai yaaya duk cikinmu yau ba wanda baiyi mugun qoshi ba,ni har amai nake ji wallahi,saboda nayita cine ina hutawa,don bansan yaushe zamu sake qoshi haka ba" da qaramin murmushi mai dauke da tausayi take dubansu sannan tace

"Bakin da Allah ya tsaga ai baya hanashi abinci hannatu" daga haka taja abincin tana ci,jifa jifa suna hira tana tattambayarsu abubuwan da suka faru bayan bata nan,da yake haka dabi'arta take,idan tadawo cikin hikima a cikin hira take bugar cikinsu wasu abubuwan,wanda anan ne idan taji wani kuskure da wani yayi ko ba daidai ba saita gyara mishi kota tsawatar masa."Ya akayi ne hauwa kuluwa?" Bilkisu tafada sanda take gama cin abincin da tsakurarsa kawai tayi ta ture,saita sauke hannun daga tagumin datayi tana murmushi

"Yaaya,duk kin fimu kyau,sai nadinga ji dama nice ke" murmushi mai sauti ya subuce mata,har fararen jerarrun haqoranta suka bayyana

"Toh?,yau kuma hauwa'u"

"Nima yaaya,na dade ina gani,ko qawayena idan sukazo sai suyita kallonki,suce kamar ba gidanmu daya ba,waike kin fimu kyau,kalar 'yan gayu dake" hannatu tayi nata sharhin daya sanya bilkisu dariya dole,sai data tsagaita sannan tace

"Kuma duka masu kyaune hauwa'u,bakigama ke 'yar fillo bace,gashinki ma yafi nawa santsi dakyau,kema hannatu baki kallon mudubi?" Maganar saita dan jefa yarinyar cikin tunani

"Yaaya" takira sunan bilkisu a sanyaye wanda hakan yayi calling attention na bilkisun sosai

"Na'am" ta amsa mata da dukka hankalinta

"Da gaske ni 'yar fulani ce?,amma ban taba ganin mamana ko 'yan uwanmu ba,tunda mamana ta tafi ban sake ganinta ba,kodai bazan sake ganinta ba yaaya,ko itama mutuwa tayi kaman mamanki?" Shuru ya ratsa dakin,yarinyar na dubanta tana jiran amsa daga bakinta bilhaqqi,maganganun yarinyar sosai suka taba ranta,suka koma soso wani sashe maigirma na zuciyarta,tausayinta yasake ninkuwa a ranta.Kama hannun yarinyar tayi a tausashe sannan tace

"Mamanki bata mutu ba tana nan da ranta,kullum tana tunaninki kuma tanason ta ganki,amma wataran saidai kawai ki ganta tazo ganin hauwanta" murmushi ya kubcewa yarinyar,cike da nuna zumudi da kuma fata mai tarin yawa tace

"Da gaske anty?"kai ta jinjina mata alamun tabbatarwa

"Da gaske jidda" sai farinciki ya mamaye fuskarta.Da wannan hirar ranar suka kwanta,yayin da suka tadawa bilkisun tabo sosai cikin zuciyarta,don kowanne yanuna sha'awa dason ganin mahaifiyarsa,inama ace itama zata samu dama koda sau daya taga tata uwar,ta zanta da ita ko sau dayane kuwa?,tausayin yaran take wani lokaci fiye da kanta,don gwara ita tasan dukkan wanda yamutu haihata haihata shida dawowa doron duniya,amma sufa?,ta qyamaci halin mahaifinta dakan raba yaran da iyayensu yakuma kasa riqesu yadda yakamata,yayin da wasu daga cikinsu iyayen ne a karan kansu suke fushi saboda abinda mahaifinsu ya aikata su watsar da yaran.A daren ranar sai datayi kuka sosai kafin bacci yayi awon gaba da ita.☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️*MASARAUTAR KAISA*    Kamar yadda muka fada a baya babbar masarauta ce mai cike da iko mulki da wata cikakkiyar izza,tun shekarun masu tsaho da suka shude a baya har kawo yau,wanda tana gogayya da dukkan masarautun da suke maqwabtanta dama na nesa da ita,masarauta ce data cika ta tumbatsa da wani irin salo na mulki mai cike da adalci da qasaita na daban uwa uba kwarjini da daukaka da Allah yayi mata.Babbar masarauta ce wadda take da fadin qasa,tarin al'umma,kaisa garine da yayi iyaka da kano da jigawa,garine mai albarka noma da kiwo,hakanan al'ummar ciki na rayuwa ne qarqashin adalin sarkinsu maimartaba sarki Abdallah mu'az nuhu kaisa,wanda tun tale tale na kafuwar garin mulkin garin a hannunsu yake,shi kansa gadon gado yayi daga iyaye da kakanni.Gidan sarautar kaisa babban gidane wanda zaka iya kiranshi kai tsaye da gari guda,mai dauke da sassa sassa bisa tsari da fasali tun daga farkon gidan, gidajen ƙananun bayi da manyansu,bayi,masu qananun muqami da matsaikaita,securities na gidan wasu daga cikin dogarawa da sauran hadimai na gidan,haka tsarin yake daki daki har zuwa ainihin unguwar da matan sarki suke da iyalanshi da sauran makusanta.Sarki Abdallah adalin sarki ne wanda al'ummar garinsa kejin dadin mulkinsa qwarai da gaske,yana da tausayi ga talakawanshi,mutum ne mai sauqin kai duk da awasu al'amurran bashi da sauqi ko kadan,hakanan kaifi daya ne shi,magana daya yake babu canji,mutum ne mai qoqarin riqo da addini duk da cewa yayi karatun boko.mai zurfi,don kafin zamowarshi sarki ya riqe muqamai iri daban daban masu tarin yawa,tun daga qananu zuwa manya,don har ambassador ya tabayi,kafin daga bisani yadawo gida bayan Allah ya yiwa mahaifinsa rasuwa ya amshi sarautar garinsu.Sarki Abdallah nada matan aure hudu,ta hudun da ya aura bayan zamowarshi sariki ta rasu bayan ta haifi yarinya daya dashi,matarshi ta farko hajiya saratu ya aureta ne tun kafin zamowarshi sarki,a lokacin yana ministern mai na qasa,wanda basu jima sosai da ita ba don haihuwarta biyu Allah yayi haduwarshi da mayarsa ta biyu haj adama,wanda sun dan zauna zaman kishi lokaci maidan tsaho kafin Allah yasake yin aurenshi da Aishatulhumaira,a lokacin yana ambassador a qasar mali,diyar sarautar qasar itama kamar yadda yake.Tun haduwarshi da ita tashiga zuciyarsa qwarai da gaske takuma tafi dashi,saboda wani irin kyau da Allah yayiwa aishan,kowa yasan yadda kalar fatarsu da yanayin kyansu yake wanda yake dan zubi da na ethopian's,uwa uba jan aji da shan qamshinta wanda ya amsheta qwarai yakuma dace da matsayinta,wata irin mace ce da Allah ya zuba mata kwarjini da farinjinin manema,don shi kansa a sannan sai daya danci wuya kafin yasameta.Sai neman auren aishan yazama wani abu na daban wajen haj saratu da adama,tun daga sanda sukayi binciken kan wacece aishan hankalinsu yatashi qwarai da gaske,suka kasa sukuni saboda sunga cewa tako ina tafisu,sannan shi kansa mai gayya mai aikin sun fahimci kamar yana zumudin abun,duk da yadda yake qoqarin boyewa da dannewa,duk ta yadda zasu shiga a fasa abu ya faskara yaci tura,tilas daga qarshe dai suka shirya plan na tararshi gaba da gaba,suka sameshi a falo yana hutawa suka tada mishi maganar,yayi qoqarin fahimtar dasu da lallashinsu amma suka toge,daga qarshe ma suka sanya masa kuka hajiya saratu tace

"Kawai dai duka take takenka mun gane ,mun fahimci inda kasa gaba kuma mun fahimci me kake nufi,saboda Allah yabamu haihuwar 'ya'ya mata bamu haifan maka maza saboda kana sakaran ka amshi sarauta kana neman magaji tun yanzu,to ai muma bamu muka baiwa kanmu ba,kuma cikin daya haifi 'ya mace shi zai haifi da namiji" shuru yayi na mamakin kalamanta,sabodashi sam ko sau daya ma bai taba darsa wannan tunanin cikin ranshi ba,saboda babu wanda yasan gawar fari sai Allah,shi kanshi mai martaba a sannan yana nan da ranshi bai mutu ba bare yayi wani tunanin mulki.Idanu kawai ya zuba musu,suka dinga tashin hankali kala kala har akayi auren,yabar aisha a qasarsu saboda shima a sannan yana can yana aikinsa,sam ita aishan bata damu dasu ba,duk da tana da kishi tana kishin mijinta saboda yadda take sonshi amma ko zancansu bata masa,taja mutuncinta sosai,tun bata fahimci yadda suke kishi da ita ba harta gane,saboda haka tasan halin kowacce cikinsu duk daba qasa daya suke ba,kuma abdallah baya mata zancan kowacce cikinsu amma ta fahimci kowa,macace mai matuqar saurin gano abu,kaifin basira da hangen nesa,yanayin yadda abubuwa ke gudana idan yakoma can wajensu kawai ya isa ya bayyana mata komai.Basu sassauta kishinsu a kanta ba sai datayi haihuwar fari itama tasamu diya mace,kai kaga walwala da sakin jiki,harma suka yanke haj saratu zataje har can mali barka da taron suna,shi kansa yayi mamakin yadda suka sake din,amma bai kawo komai a ranshi ba donshi bai saka zancan haihuwar mata ko maza a wani babin ba,hasalima ya manta taqaddamar da sukayi dasu lokacin auren aishan,sai yayi murna sosai saboda yana tunanin sun sassauto ne saboda zuri'a da aka soma hadawa.
Haka kuwa akayi,ta shirya tsaf tayi siyayya ta alfarma suka tafi da duka yaran su hudu,nata biyu nimra da zunaira,sai na adama biyu Aafiya da afra.Gidansu aisha gida ne na karamci suma,saboda haka tasamu saukar girma data sake sanyata ta bambance aya da tsakuwa,bugu da qari duka yadda suke hasashe ashe abun yawuce hasashen nasu,don yadda taga anata hidimar bikin sunan jaririyar cikin gidan nasu,aishan 'yar gata ce gaba da baya.Tunda tazo suka gaisa aka kai mata yarinyar bata kuma bari sun hadu ba,saidai duk wani abu daya kamata ayiwa baqo dama wanda bai zama dole ba duka an yiwa saratun,takuma aiko aka mata godiyar kayan barka,saidai a jikinta taji cewa ba zuwan Allah tayi ba,to koma mene batajin zata bari kota yarda a cutar mata da diya,don tun sanda ta haifeta take mata mugun so.Yadda saratu tazo data tashi komawa saiya zaman gwiwa kusan a sanyaye,don ta ganewa kanta abubuwa masu yawa,ciki kuwa harda kyau da Allah ya yiwa yarinyar na daban,ga uwa uba gatan data gani ana nuna musu,koda ta dawo ta baiwa adama labari sai sukayi zugum,inda daga qarshe adaman ta katse tattaunawar tasu da cewa

"Koma meye dai mu godewa Allah data yiwo mu,don inda namijine kuma saita Allahu,sai abinda idanuwanmu suka gani kenan".Tafi tafi haka rayuwa ta dinga tafiya har zuwa sanda maimartaba ya kwanta ciwo,wanda ciwon nashi kusan shine silar daya sanya abdallah ajiye aikinsa na ambassador,yadawo gida gaba daya saboda shine babban danshi,wanda kuma sukagi shaquwa dashi fiye da kowa,wannan karon harda aisha itama tabiyo mijinta nigeria donta zauna dashi,a sannan dukka matan nashi ciki garesu,saidai akwai bambancin watanni,na saratu shine mai watanni bakwai,adama wata shida,yayin da aisha nata keda wata biyar,saboda tsayinta da yanayin shigarta yasama ba kowane ke lura dashi ba.A wannan zaman da sukayi tare da sake karantar kowa tsaf ciki da bai,haka suma sun sake fahimtar tazarar data musu a zuciyar mijin,katsam saiga al'ummar gidanma kusan suna neman komawa qarqashinta,kasancewarta mai budadden hannu,ba baya bace wajen kyauta,duk da tarin izza da qasaitarta,duk da bata cika sakin fuska ko faran faran da jama'a ba,amma duka wannan bai damu mutane ba,da yake yanzun kusan kowa yafi ga abun hannun dan uwanshi.A wannan lokacin tsakanin adama da da saratu kowa fafutukar ganin ya haifi da namiji yake a cikinsu,kudi suka dinga bararwa suna baiwa malamai na Allah daba na Allah ba ana abubuwa iri iri saboda su haifi namiji,gamida alqawura iri iri ga hadimansu na duk wanda yazama silar samun namiji a cikinsu zasu 'yantashi,masu 'yanci kuma zasu wadatashi,saboda kowacce tana ji a jikinta lokacine yayi da mijinsu zai karbi sarauta,wanda hakan ke nuna cewa abu na gab zuwa kansu.Amma a zahiri idan sun hadu kowacce fata takewa 'yar uwarta nako itace tasamu babu komai,saidai kowanne ta qarqashin qasa akwai hadimansa dake masa aiki a sashen kowaccensu ba tare da kowannensu yasani ba.Ta fannin aysha kuwa hankalinta a kwance yake,sabgarta kawai take da kula da mijinta,da kuna tayashi kulawa kan lalurar mahifinsa,sun tuttura mata sabbin fuska don su shiga jikinta kamarsu amma basu samu wannan damar ba,saboda halinta na dabanne ita,tana da matuqar wayo da takatsantsan,don haka ita basu da wani labari daya danganceta ko sassanta sai dan abinda ba'a rasa ba.Wata biyu da dawowarsu a safiyar wata asabar saratu ta haihu,tashiga tashin hankali da matuqar girgiza sanda unguwar zoman dake amsar haihuwarsu ta shaida mata diya mace tasamu,babu jimawa labari ya karade gidan,ranar sashin nata tamkar zaman makoki akeyi,saboda kowa yasan yadda ta qwallafa rai akan da miji kuma bata samu ba,dukkanin hadimanta ranar kaffa kaffa suka dinga yi,babu wani mai qwaqqwaran motsi ko dariyar kirki,a haka labari yasamu adama,tayi rawa tayi shewa tayi juyi gaban mutanen da take gani amintattun tane,wadanda sune suka kawo mata labarin,saidai batasan cewa sune makasan nata ba,kana ta umarci hadimanta maza su shirya abinci mai rai da motsi a kaiwa saratu,itama tana bisa hanya.Isar abincin da isarta sassan saratun ba wani tazara mai yawa,donta qagauta taje ta ganema idanunta

"Haka Allah yashirya,qaddararsa kenan" adaman ta fada cikin fuskar jimami sanda take zaune kusa da saratu wanda ke kashingide saman wata kujerar hutawa dake wani daki na musamman da aka kebe saboda hutawar.Nannauyar ajiyar zuciya saratun ta saki,kana a hankali ta dora idanunta kan adaman,tuni labarin abinda tayi ya rigata isowa,saboda haka tar take kallonta,saita miqe tazauna sosai sannan tace

"Qaddararmu ce gaba dayanmu halan" saita san dakata tana ci gaba da duban adama tana shaqar numfashi sannan ta dora

"kuma na rantse da sarkin da babu wani saishi,indai ni saratu uwar gida ga Abdallah bani nasoma haifa mishi ɗa namiji ba,babu matar da zata haifa ɗa namiji cikin gidan nan".Gaban adama yafadi tsoro yadan shigeta,kada fa yazamanto namiji ne a cikinta saratu ta aikata abinda zaisa yakoma mace,amma a zahiri saita dubeta duba na mamaki

"Tofa....kamar yaya,me kike nufi?" Sai data koma ta kashingida sannan ta bata amsa a taqaice

"Lokaci zai nuna" daga haka bata kuma tanka mata ba,saita aje mata yarinyar saitin qafafunta tamiqe tana cewa

"Lamarin ubangiji dai rubutacce ne,Allah ya qara lafiya,nina wuce" binta tayi da kallo,sai ta saki shu'umin murmushi

"Kinsan ubangiji ne adama?,muzuba mugani" ta fada cikin ranta,kana ta waiwaya tadubi yarinyar daketa bacci abinta batasan ma me ake ba,sai taji dama ta bude idanu ta ganta a matsayin d'a namiji ba mace ba,takirayi daya daga cikin barorinta tadauki 'yar ta maidata cikin gadonta.

Sanda abdallah yazo ganin ɗiyarsa ya amsheta hannu bibbiyu cikin farinciki kamar sauran haihuwar,ba tare da nuna wani abu har fili da zuciyarshi,abinda yadan sake kwantar mata da hankali kenan,duk da burin dake ruruwa cikin zuciyarta wutarshi bata ragu ba bare ta mutu,taji alwashin duk tsiya duk runtsi itace zata fara samawa abdallah magaji ta kowacce hanya,ba zata taba bari wata cikinsu ta karbi wannan kambun ba.


Aisha kam sai bayan kwanaki uku da haihuwar sannan ta taka taje cikin rakiyar hadimanta wanda kusan dukkaninsu amintattun tane,saboda an hadasu ne da ita tun daga masarautarsu,qalilan ne wadanda suke haifaffun masarautar kaisa.


Tajewa da jaririya kyautar saitin gwal sarqa dan kunne abun hannu harda zobe da awarwaro,tun daga ranar bata sake komawa ba.
Suna akayi kamar yadda aka saba gagarumi,yarinya taci sunan sa'adiyya mahaifiyar saratun suna kiranta da walida,hakanan taci gaba da rainon walida tana zuba idanu kan cikin adama da aisha.


Kwanaki arba'in darda doriyar takwas akai itama adama ta haife nata cikin bayan sallar la'asar,itadinma Allah ya nuna isarsa,buwayarsa da kuma ikonsa,tun la'asar akayi haihuwar amma dif babu labarin abinda ta haifa din,tana canbtana tantama da tunanin idanuwansu ne basuga dai dai ba amma namiji ne,sam bata ta wahalar da yarinyar tasha wanda ba'a samu ta fara kuka ba saida qyar,har sai bayan sallar magariba sannan komai ya tabbata.


Sosai tashiga rudu da tashin hankali itama,don dukka malamanta kowa ya tabbatar mata da cewa namiji ne zata haifa wannan karon,abu na farko data soma fada shine
"Tabbas ba shakka wannan surkullen saratu ne,kuma wallahi bataci banza ba,sai tasan dani take zancan".


Itama tuni labari ya dade da isar mata,tasa aka shirya lafiyayyen abinci aka aika sassan adaman kamar yadda itama tamata,sannan tashirya cikin tawagarta suka je barka
"marhaba lale,ashe abokiyar tagwaitakar walida ta iso..." Ta qarashe tana dariya dariyar da zata nuna maka hakan ba qaramin dadi yayi mata ba kenan.


Adaman na zaune a lokacin tanacin farfesun naman rago,saidai jinsa take kamar tana tauna plagyl tana hadiya ne,fuskarta kai kace dare biyu akeyi,maganar saratu yasa tazuba mata idanu,kana cikin kauri da kaushin murya tace
"Burinki yacika,amma kisani...komai nisan jifa qasa zai fado,hakanan na rantse da girman Allah kamar yadda kikaci alwashi nima naci....dukkanin wanda yayimin kan kara saina masa na itace" saman cinyarta ta isa tadora mata yarinyar tana sakin murmushi sannan tace
"Ga fili gamai doki nan....saura sukuwa" saita soma takawa tafice daga dakin tabaiwa barorinta dake can falon farko umarnin su aje saqon kayan barka suzo suwuce.


Wannan ma aishan kamar wancan karon,batazo na sai bayan kwana uku,itama ta bata kwatankwacin abinda ta baiwa walida tatafi.


Tun daga wannan ranat dangantaka tayi tsananin tsami tsakanin saratu da adama,aka shiga takun saqa naban mamaki,yiwa juna zagon qasa,da zamba iri iri.


Aisha na gefe batasanma sunayi ba,dama babu abinda zai hadata dasu,yanayin halayensu yasa ta sake takatsantsan da komai da kuma kowa,hatta da diyarta bata barinta ta qetare sashenta bare tayi nisan kiwo,saboda batajin zata iya dauka idan wani mummunan abu yasameta.


Sai dukka hankulansu ya karkata yakoma ga aishan sanda tashiga watan haihuwarta,kamar tunaninsu ne yazo daya,kowacce saita soma mata aike dake nuna tsantsar kulawa,bata taba cewa kada a karba ba,amma kome suka kawo din bata yarda ya rabi inda take.


Ziyara da suka shiga kawo.mata akai akai kuwa kai tsaye ta soketa ta dakatar dasu ba tare da shakka ko shayin gayawa kowaccensu ba kai tsaye,hakan yasake basu mamaki yakuma tabbatar musu aishan da halayenta na dabanne,kuma lallai jinin sarauta na yawo a jikinta koma bayansu da za'a iya cewa taka haye.


Yadda ta fahimci sunayin saiya sanya nata qaunar samun da namiji,sai taji tanason ta haifa da namijin taga yaya zasuyi?,tanason ita tazama mace tafarko da zata samarwa abdallanta magaji.


Kwana hamsin da biyar cikin dare naquda ta kamata ganga ganga,a lokacin kusan mafi yawan al'ummar gidan da suka damu da rashin lafiyar mai martaba har zuciyarsu kusan idanunsu biyu,cikinsu harda al'ummar sashenta,a daren abdallah yana can sassan maimartaba cikin dakinsa suna fama dashi saboda yadda ciwonsa yatashi ainun fiye da kowanne lokaci,saita kira mutum biyu cikin amintattunta suka kebe iyasu suna kula da ita.


Daidai lokacin data haifi ABDUL_AZEEZ bawan mabuwayi,a sannan mabuwayin ya nuna buwaya da ikonsa yadauki ran sarki mu'az nuhu.


Kaqqarfar ajiyar zuciya tasauke
Tana furta kalmar
"Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi tatimmus salihat".


Ita da kanta ta hana afitar da jinsin abinda ta haifa din tun cikin daren,sai zuwa wani lokaci data shirya susani din.


Sanarwar haihuwar abdul_azeez ta karade gidan hade da sanarwar mutuwar mai martaba,wanda hakan ya taimaka wajen janye hankalin mutane wajen son sanin me aka haifa?,wanda wannan yabata damar shiryawa sosai da tsara yadda zata fuskanci gaba,ta riga data sani haihuwar abdul'azeez zai iya zame mata wani babban qalubale a rayuwarta tsakanin abokan zamanta.


Abdallah bai samu shigowa ganinta ba sai bayan sallar magariba,tana zaune tana kallon yadda yaketa faman murmushi yana kissing yaron kamar zai maidashi ciki,duk da cewa yana cikin alhini da jajjaɓi na rashin da yayi amma fuskarshi ta nuna farinciki mara misali,hakan shike nuna shaidar cewa yanason magaji kamar yadda kowanne mutum keso,amma shi kansa baisan yana da wannan feelings din ba,saiyau feeling din ya bayyana kanshi da kanshi
"Allah kenan,mai kyauta yakuma amsa a duk lokacin da yaga dama,Allah ya amshi mai martaba sai gashi ya bani wani copy din" cikin tayashi alhini aisha ta girgiza kai
"Allah yayi mishi rahama,yasa can tafi nan"
"Amin don annabin rahama....amma wannan fa" saiya dakata yana sake jujjuya abdul'azeez a hannunshi,sai murmushi yasake kubce masa
"Dan somalia ne,aisha kinmin wayo,ku yadauko zam,dan da alama har kalar fatar ma,na tsira da minahil kenan?" Duk da yadda zuciyarta itama take babu dadi saboda rashin da sukayi saida murmushi ya kubce mata,sai daya tattofeshi da addu'a sosai kana yamiqa matashi ya mata sallama.


Har ya fita yadawo ya dubeta
"Zan aiko da saqon da za'ayi masa amfani dashi,ki tabbata an masa amfanin dashi yadda yadace"
"In sha Allahu" ta fada 


Washegari kuwa sai gashi,wani rubutune mai garin magani da za'a masa wanka dashi akan towel,sai a shanya towel din yabushe,da wani irin man shafawa da za'a dinga shafe masa duk jikinsa duk dare idan zai kwanta,kobai fada ba tasan na tsarine,kuma taji dadin hakan sosai.


Duk da wannan rasuwa da akayi hakan bai hanasu son sanin me aisha ta haifa ba,duk da basu samu zuwa ganinta ba amma sunata faman aiki gami da leqo 'yan bugar ciki ko ince leqen asiri,saidai hadiman nata 'yan gaske ne,don har sukayi suka gama basu san me aka haifa din ba,har sai ranar bakwai din mutuwar mai martaba
A ranar ne akayi radin suna ba tare da wani shagali ba saboda mutuwar
Kuma a ranar ne aka nada Abdallah kan karagar mahaifinsa,yazama shine sarkin garin kaisa.


Ba qaramin girgiza zukatan maqiya sukayi ba sanda saqon radin sunan jariri yakai musu da sunan MUHAMMAD ABDUL'AZEEZ,don haj saratu saboda tsabar rudewa cewa tayi
"Abdul'azeez ko aziza?,anya kuwa kunji dakyau?" Tafada cikin razani da rudani tana duban barorin nata.


Dukkaninsu kawunansu suka sadda kamar sun aikata mata wani laifi,sannan daya daga cikinsu tace
"Ki yafemu ranki ya dade,tuba muke....amma ba shakka abdul'azeez shine sunan yaron" sauran duka suka jijjiga kai alamun hakane
"Zaku iya tafiya" tu buqaci su bata wuri,saboda yanzu babu abinda take da buqata sai kadaicewa.


To bangaren adama ma kusan haka abun yake,amma ta dake itama takuma shirya kyautatuttuka ta aika sassan saratun hade da saqo,wanda tace tana tayata murnar samun magaji,Allah ya rayashi.


Tunda taga saqon tasan cewa da biyu adaman ta aiko dashi,hakan kuwa ya qular da ita yakuma fusatata,amma dole ta danne a idanun mutane ta amsa takuma aika mata da saqon godiya.


Bayan nan haka tasake shirya kyaututtuka kala daban daban na alfarma masu yawan gaske ta aika sassan aisha,tace kyauta ce zuwa ga yarima abdul'azeez daga uwarshi,itama aishan ta karba,takuma bada tukuici mai tsoka,irin tukuicin dake nuna zallar isa da qasaita.


Murmushi adaman tayi sanda taga tukucin,tadinga kada qafa tana ayyanawa wala'alla aisha ta yaba shi yasa ta bada irin wannan tukucin haka,take wani shiri yafado mata aranta,ta tafa hannuwanta cikin nishadi ta kashingida tana tsara yadda komai zai gudana.


Tun haihuwar abdul'azeez take nuna mishi soyayya da qauna mai yawa,wani irin so takewa yaron,yashiga zuciyarta da yawa,har takan gaza tantance shida minahil wa tafiso.


Wani kwarjini da farinjini Allah yabashi tun daga quruciya,hakan yasa ta sake takatsantsan dakuma kaffa kaffa a kanshi,ko ina zai shiga akwai sanyawar idanu akanshi saboda tsaro,wannan yayi tasiri qwarai wajen rage hanqoran mafarautan rayuwarsa,yakuma takurasu tare ta qara musu qaimi wajen ganin sun aiwatar da qudurinsu.


Ta bangaren adama kuwa ta bada himma sosai don ganin ta nunawa duniya tana qaunar abdul'azez,haka tadinga qoqarin ganin ta jashi jikinta ta yadda komai zai tafar mata a sauqi,saidai babu wannan damar daga wajen ayshan,ita da abdul'azeez din saidai ta ganshi daga nesa,idan ma kuwa zata ganshi a kusa ta gaban idanun masu tsaronshi ne.


Tsakanin fulani adama da fulani saratu tun haihuwarsu ta uku babu wadda tasake koda batan wata,hakan yasanya zargin juna a tsakaninsu,kowacce tana ganin 'yar uwartace tayi mata wani abu,hakan yasanya dukkaninsu suka sanya aka rufe mahaifar juna ba tare da sun sani ba.


Bayan haihuwar abdul'azeez da shekara hudu aisha tasake haifan diya mace wadda taci sunan mahaifiyar mai martaba suna kiranta da uswa,bayan ita sai arifa sannan sumaira da huda auta.


Kusan a iya cewa aisha itace tauraruwar maimartaba ko ace giwarsa,tun asali bawai sai zuwa yanzu ba,badon komai ba saboda dukka cikin matanshi babu tamkarta wajen damuwa da lamuransa gamida nuna mishi qauna kulawa da soyayya,hakanan halinta dabanne cikin matanshi,duk da tana da kafiya jajircewa kan dukka abinda tasa gaba.


Idan taso abu tana sonshi ne da dukka zuciyarta,hakanan idan taqi abu tana qinsa ne da dukka zuciyarta,kaifi daya ce ita,ba'a fiya sauketa daga ra'ayinta ko sauya mata al'amura ba.


Baya ga mijinta da iyaye 'ya'yanta sune abu nabiyu da take so sosai a rayuwarta,cikin 'ya'yan kuma sai abdul'azeez tashi qaunar tafi takowa,tun lokacin da aka taba samun galabar cutar dashi sau biyu ta fidda duk wani qasaita izza da isarta,ta sake qaro rashin yarda da tsaron lafiyar yaran nata.


Sosai aka samun nasarar kwantar dashi kwanciyar da ba'aso har abada yatashi ba,saidai zakaran da Allah yanufa da cara,aishan macace data yarda da malamai wadanda zata biya kudi ayi mata sauka duk wata ko sati da addu'o'i kan tsaronta dana yaranta,duk da itadin bata damu can da saitayi da kanta ba,wannan shi yakawo sassaucin lamarin Allah yayanke masa ya tasheshi da wuri.


Tun a sannan tadaura dambar dukkan wanda bayason ganin abdul 'azeez a matsayin yarima saita hanashi bacci
Ta dora buri sosai bisa rayuwarshi
Tana qaunarshi da bashi kulawa fiye da kowa cikin yaranta
Zaka iya taba kowa ta daga maka qafa amma banda abdul'azeez
Zata iya daukan komai sabodashi,hakanan zata iya haqura da komai saboda abdul'azeez
Tayima rayuwarshi babban tanadi
Taci buri da alwashin saiya zama wani shima tamkar yadda mahaifinsa yazama kafin zamantowarshi sarki
Duk wanda yakwana yatashi cikin gidan yasan zallar qaunar da take masa
Saidai duk da wannan yasan wacece mahaifiyarshi sarai,yasan tsarinta yasan halayyarta ta kaifi daya ce!


A yanzu burinta nafarko shine abdul'azeez yayi karatu mai zurfi bakin rai bakin fama,wanda take hasashen shine mataki nafarko da zai soma zama wani haske mai kaifi a gareshi dazai nunawa duniya shi,sunansa yayi fice,yakuma shiga loko da saqo na duniya fiye da sunan mahaifinsa.


Yana da wannan ra'ayin,yana da burin haka,sai akwai abu guda daya tak daya kawo sauyawar ra'ayinsa da nata,burinta guda daya daya zama tarnaqi a rayuwar abdul'azeez,buri guda daya daya kawo sabanin ra'ayi tsakaninsa da ita,abu guda daya dayake neman dagula rayuwa da nutsuwarsa,duk da takan gaya masa
"Abd'azeez,kada kace zakaja da dukkan abinda na shimfida maka,dukkan abinda nakeyi inayine saboda kai,saboda 'yan uwanka,saboda kare suna da matsayi na masarautarku data mahaifina,ka ajiye naka da ra'ayin da burin,na maka alqawarin cewa AKWAI LOKACI!".


Dukkan wani qoqari da juriyarshi ya tattarata waje daya don ganin sun tafi doro daya bisa tsari da ra'ayin mahaifiyarsa,saidai koda yaushe qoqarin nasa yana neman gazawa,akaran kanshi bashi da yadda zaiyi da kanshi,da da akwai da babu makawa zai kasance kamar yadda takeso dinne,saboda babu abinda yake qauna a duniya sama da mahaifiyarsa shima,yadda tabashi qauna haka yake qaunarta koma fiye da hakan,zallar soyayya irin ta d'a da uwa.


Wannan shine taqaitaccen tarihi kan masarautar kaisa,duka sauran abubuwan da basu bayyana ba zasu bayyana kansu a nan gaba,muje zuwa.......🤙🏽🤙🏽

   A hankali tasauke labulen harabar tata wadda take iya ganin dukkan abinda ke kaikawo cikin gidan,duk data sauke labulen amma saitaci gaba da tsaiwa gabanshi duk kuwa da cewa bata iya hango abinda ke ci gaba da gudana saboda kauri da nuyin labulen,amma kuma kunnuwanta naci gaba da jiye mata bushe bushe da tashin algaita data mamaye ilahirin gidan gaba daya.


"Tuba nake ranki ya dade,Idan da sabo yaci ace kun saba da ire iren wadan nan abubuwan dake faruwa cikin gidan nan" saita sauke hannayenta daga goya kana ta waiwayo tana duban wadda ke tsaye a bayanta kanta na kallon qasa cikin nuna girmamawa
"Ko jikina bazai taba sabawa da wadan nan al'amuran ba bare zuciyata,mansura...ni kadai nasan yaya nakeji a zuciyata duk sadda yaran nan yadawo hutu gidan nan,idan yatafi kan cika da fata da burin yatafi kenan,ko duriyarsa banson a sake ji,amma.....kullum jiya iyau,komai ya faskara,aisha bansan da wadanne iri bokaye da matsafa take aiki ba" takai qarshen maganar tana dafe goshinta da hannu kana ta yarfar dashi
"Allah ya huci zuciyarki,tabbas wataran haqanmu zata cimma ruwa,tunda dukkan mai nema yana tare da samu" kai kawai ta kada,ba tare data amsa maganar tata ba tace
"An gama shirya dukka kyaututtukan da kayan ciye ciyen?"
"An gama ranki yadade" ta amsa mata tana rusunawa
"Shikenan.....kije,bayan wasu lokuta akai ace injini,ina masa barka da dawowa,sannan ina nan tafe in duba lafiyar dana" tafadi maganar tana jin dacinta har qasan zuciyarta,duk wannan abun tana yine saboda babu yadda zatayi,tana yine saboda tacimma wani buri nata wanda tasoma aiki akai,amma aysha ta dakatar da tafiyar lamarin ta hanyar turashi wata qasa uwa duniya waida sunan karatu,sai taja qwafa tana neman daya daga cikin kujerun alfarma dake mamaye da qaton falon tazauna.


_fulani saratu_


    Babbar haraba ce da aka qawatata da shuke shuke masu sanyaya rai da debe kewa,kashingide take saman wani tafkeken kilishi wanda aka qawata zamanshi da tuntu masu zanen gidan sarautar kaisa da wani yadi mai taushi,wanda duk da taushinsa zanen sarautar da rubutun jiki bai hanashi fitowa ba.


Ita daya ce zaune a wajen kamar yadda ta buqata takuma shaidawa barorinta bata buqatar kowa kadaici takeso tsahon mintuna talatin,saidai duk yadda taso tasamu hutu takuma katange kunnuwa da idanunta wajen jin duk wani sauti alama ko shaida na shigowar abdul'azeez cikin gidan ta gaza cimma gaci,sarewa da algaitar dake tashi saika rantse daura da itane bawai nesa da inda take ba.


Sake gyara kashingidar da har yanzu batajin dadinta tayi gamida jan wani dogon tsaki,bayan tadire tafurta a hankali
"Wannan wacce irin masifa ce!" Idanunta da zuciyarta taf da wasu al'amura da sukayi shekara da shekaru suna sukan ranta.


A hankali take takowa farfajiyar da mahaifiyartata take,duk da idan kadubi fuskarta zaka karanci damuwa qarara a cikinta,jin takunta yasanya fulani saratu daga kai tana duban inda take jiyo takun,ganin walida ce yasanyata maida kanta tana dakon isowarta
"Barka da warhaka mama" walida tafada bayan tazauna gefan kilishin da haj saratu ke zaune akai,bata amsata ba sai data koma tazauna sosai tasauke ajiyar zuciya idanunta kan walidan
"Barka kadai....ya akayi?" Kai tadan rausayar cikin nuna alhini kana ta hadiye wani abu sannan tace
"Mama....dama yau yarima zai daw....."hannu tadaga mata cikin katseta
"Dakata,bansan wani da irin wannan sunan ba,ki kirashi da sunan da mahaifinsa ya rada masa" kaitadan jinjina,tajima da sanin cewa mahaifiyarta bataso ko qaunar taji ankira abdul'azeez da wannan sunan ko misaqala zarratin
"Afuwa....abdul'azeez"shuru yaratsa nadan sakanni,tamkar ba zatace komai ba kana ta ƙuta tace
"Gashi kuwa idanunki sun ganemiki?" Wani busasheshen murmushi da babu armashi ko farinciki a cikinsa ko misƙala zarratin tasaki sannan taɗora
"Akullum aikin mahaifiyarsa kenan,rufe dawowarshi harsai ana yagobe ko randa zai dawo,koda yaushe aisha gani take itadin me wayo ce,bayan duk wayonta babu ruwan ƙaddara da wannan,hmmmm".


Sam walida bata bi takan zancanta,don ita duka waɗannan salon maganar tasu bata cika fahimtarsu ba,asalima basa gabanta
"Mama....kaman yadawo a lokacin da bamu shirya masa ba,yadawo a lokacin dabai dace ba" sosai tasanya ƙwayar idanunta cikin ta walidan,tana karantar rudewa ƙarara cikin idanun nata
"Me kike tsoro?"
"Makarantata,kada mai martaba yaqi yarda da maganar tafiyata karatu"
"Akan wanne dalili?" Ta jefa mata tambayar data sanyata ƙara zama
"Mama,kinsan kome maimartaba zaiyi wanda yashafemu sai yayi shawara da abdul'azeez,akowanne lokaci yakance idan babu shi nan gaba shine ubanmu,kuma kinfi kowa sanin yadda bayason wata cikinmu tafita wata ƙasa karatu,afnan kawai ta ishemu misali.....".


Kalaman walidan tamkar wani tuni ne ko fami a zuciyar haj saratu,saboda haka ta tsaida walidan
"Saboda shi abdul'azeez din shine uban kowa?,ko zamansa muke?,ko a ƙarƙashinsa muke?,wai tsoron ma me kikewa ƙaninki?,yaron da kika baiwa kwana hamsin harda doriya....to wannan karon kuwa bazan lamunta ba,abarmin yarana suyi karatu a duk inda sukeso kuma sukaga dama,saboda shima babu uban daya takurashi,asalima shida kansa ya zabi ƙasar dayafiso sannan yatafi,don haka zuwanki makaranta babu fashi indai ina raye,banason ma nasake jin wata magana kan wannan batun" sosai walidan taji dadi,cikin farinciki tadan rungume hajia saratun
"Allah ya qara miki lafiya da nisan kwana"
"Amin" ta amsa ciki ciki saboda bacin ran dake damunta,walidan tabude baki zata sake cewa wani abu wayarta dake saman cinyarta wadda ke jone da erpiece dake cikin kunnenta tadauki kida,saita saki mahaifiyar tata tahau duba kiran,kana tamiqe zumbur tana zura takalmanta
"Ki gayawa mabaruka akawomin ruwa da lemo" kaita gyada mata tayi gaba data amsa wayar.


A hankali jeron gwanon motocin suka dinga fakawa illa qwara daya data ci gaba da kutsa kai zuwa cikin gidan masarautar,wata iriyar mulmulallaiyar mota ce mai ruwan gold,'yar qarama ce wadda dududu bata da wani girman arziqi amma sai azabar kyau da tsada dakuma daukan hankalin mutane.


Bata tsaya ba harsai data isa qofar sassan fulani aisha kana ta tsaha cak,kamar qiftawar ido wani hadimi dake zaune gaban motar yayi wuf yafito,ya tsaya bakin qofar motar yayi qyam yana jira a bashi umarnin bude murfin motar.


Tsahon minti daya kafin ataba glass din motar wanda ya fidda sautin qwas sau daya,sautin na gama direwa a kunnensa yayi maza yabude yana cewa
"Gaba salamun baya salamun magaji ga mahaifinsa,taka lafiya cikin amincin Allah da kiyayewarsa,Allah ya kare mana kai,ya zamar maka jagora kuma majingina yarima kuma sarkin gobe"


Sautin kirarinsa yaqare daidai sanda yasanyo qafafunshi dake saye cikin takalmi half cover shoe irin na maza na zallar fata qirar qasar italy mai dan banzan kyau da daukar idanu,kafin wasu sakanni gangar jikinsa tabiyo bayan qafafun nashi,wasu shegun suit ne suka bayyana ash colour masu madaukakin kyau da jan hankali,sun zauna masa a jikinsa tamkar saboda shi aka qirqiresu,fuskarsa da hannayensa dake daure da wani tsadden agogon gwal sune abu na qarshe da suka fito,hasken ranar dake kwance saman sararin subhana ya haska kwantacciya kuma lafiyayyar fatarsa wankan tarwada,wani irin choculet colour skin wanda ko cikin wankan tarwadan ma bakowanw ke dace da irin nau'inta ba,nau'in fatar dake tsada wanda tsantsar hutu dajin dadi suka hadu suka qara mata ado da qawa da wani irin launi mai daukar idanu.


ƙawatacciyar fuska wadda komai nata ke bisa tsari mai qayatarwa,cikakken gashin idanu da madaidaicin gashin gira wanda qasansa wasu irin madaidaitan idanune wanda basu cika girma ba,hakanan sunfi gaban qananu,saidai wani irin shape ne dasu dake dake cike da kwarjini da maganadisu dakan narkar da zuciyar duk wanda ya zubawa su,musamman 'yammata da yaken dilmiyasu cikin kogin soyayyarsa cikin daqiqu qalilan,kyakkyawan hancinsa mai matsaho da tudu wanda ya ta qasanshi ya qawatu da gashin daya zagaye fuskarshi zuwa habarshi,wanda yasha gyara da wani irin salon aski mai qayatarwa,yakuma fidda kyawawan labbansa,wadanda suke Da surkin ja,daga cikin jerarrun haqora farare tas sun sake qawata fuskar tashi,sai dimple qwaya daga daga kumatunsa na hannun dama.


Miƙewa yayi sosai bayan yafito daga motar yana duban sassan mahaifiyar tasa,tsaiwar tasa ita ta bayyana yanayin tsari na jikinsa,yana da tsaho da murjajjen jiki,wanda murjewarsa yasake tasiri wajen boye adadin tsahonsa,faffadan qirji da kakkauran damtse duk da ya boye cikin rigarshi amma dukkan alamun qarfi da samartakarsa sun bayyana qarara a zahiri,duk kuwa da cewa bazai wuce shekara ashirin da biyar ba
(Lol,masu karatu zasuce wai wannan kyau haka,yawanci ko baka qimanta jarumin littafinka da wannan siffar ba kuda kanku haka kuke hasasoshi,beside ma novel din dukka yakan tafine bisa tafarki biyu,ilimantarwa da kuma nishadi).


A hankali yasoma takawa kai tsaye zuwa sassan fulani aisha,wanda a duba daya kacal da zaka masa ka tantance yadda jinin sarauta daga tsatso biyu na uwa da uba ke zagaya jininsa,yazauna masa kuma ya zame masa jiki,duk inda zaya gifta sai barori da hadiman dake sashen da wadanda wata sabga tashigo dasu dama 'yan ganin ƙwaƙwaf sun zube suna miƙa gaisuwa,kamar yadda yake a tsarinsa yakan ɗaga musu hannu ne kawai yawuce,a haka yadinga kutsa kai har zuwa cikin ainihin ginin dazai sadashi da falo nafarko na mahaifyar tashi.


Kyakkyawar macace hakimce saman ɗaya daga cikin kujerun alfarma royal dake kewaye da falon,ta zarta munzalin ƙuruciya hakanan batakai shekarun da za'a kirata da dattijuwa ba,duk da cewa ta tasamma shekara hamsin babu uku amma baka isa kace tana da waɗannan shekarun ba,mulki da tsananin hutu gamida jin daɗi sun wawashe kaso mai yawa na dukka hasashen da zaka iya yi mata na shekaru yaboye,saika tsammaci tana cikin shekararta ta talatin ko talatin da ɗaya zuwa da biyu ne.


Wankan tarwada ce itama amma saboda hutu yasa fatarta ke nemam juyewa zuwa fara irin farin nan mara haske sosai,duba daya zaka mata kaga izza mulki dakuma qasaita shimfide saman fuskarta.


Sanye take da wani lace na alfarma wanda aka yiwa dinki na manyan mata,wuyanta kunne hannuwa da yatsunta dukka kowanne akwai abun ado,fuskarta wadace take da fara'a,tun sanda kunnwanta suka jiyo mata sautin algaita na isowar shalelen nata fara'a taƙi barin fuskar tata,farincikinta ya gaza ɓuya.


"Salamu alaikum....Allah ya taimakeki,yabaki yawan rai,ina iya ƙarasowa?" Dayake cikin farinciki take ayau din dakanta ta amsa mata
"Bismillah lubabatu" cikin nutsuwa da girmamawa ta ƙaraso falon,wanda ba kowa ne yataba ƙetarashi ba,face ire irensu makusanta,kuma amintattun fulanin,fuskarta fadade da fara'a tazube a gabanta
"Allah ya qara miki lafiya tauraruwar mai martaba,hasken masarautar kaisa,uwa a wajen yariman kaisa....sarkin gobe da ikon Allah,Allah yayi,yarima ya qaraso lafiya,yana gab da shigowa nan,yana neman izini" murmushi yasube ma fulani aisha har saman lebanta,wanda ba kasafai suka fiya ganin hakan ba
"Albishir dinki lubabatu yayimin dadi,ko yaushe saqonki mai dadi ne,kije a bude miki store,kidauki dukkan abinda kikaga kinaso,ladan wannan albishir din naki...yarima kuma basai an masa iso ba,yana iya shigowa duk lokacin dayake da buqatar hakan,kice ina masa maraba" sosai tasake duqawa cikin madaukakin farinciki,tana ayyana iya abinda yau zata diba a store din
"Kinfi gaban haka Allah ya taimakeki,gado kikai ai ba taka haye bace,saqonki yanzun nan zai isa ga kunnen magajin mai martaba,godiya nake...godiya nake...." Hannu ta daga mata,don zuwa yanzu ta qagu kawai taga yaron nata,don haka umma luba tamiqe ta hanzari tafice.


"Assalamu alaikum warahmatullah" ya ambata cikin Muryarshi mai taushi,mai kuma cike da samartaka irin ta matashin da ilimi da mulki suke aiki a jikinsa,miqewa tayi tana murmushi idanunta bisa kanshi,tana jin qaunar yaron nata har cikin ranta
"Wa'alaikumussalam warahmatullah,maraba da yarima" murmushi yasake shima wanda yafidda ainihin kyansa,murmushi na daya daga cikin abubuwan dake masa kyau a dabi'unsa,saudai kash,shidin ba ma'abocin fara'a bane bare murmushin kansa,duk inda kaga murmushinsa to tabbas wajene mai muhimmanci,ko kuma wani muhimmin abune yafaru
"Allah ya qara miki lafiya da nisan kwana Ammi" yafada sanda yake isowa gabanta ya duqa saman gwiwoyinsa tamkar qaramin yaro,hannunta tasanya saman lallausar sumarshi tana cewa
"Alhmdlh,na godewa Allah daya sake kawomin kai gida hutu cikin qoshin lafiya,Allah yaci gaba da albarkatar rayuwarka"
"Amin ummina" ya amsa mata cike dajin dadi sannan tabashi umarnin tashi,yasamu daya daga cikin kujerun yayiwa kansa mazauni bayan tazauna.


Gaisawa suka sakeyi,tana karance dashi,yadda suka saba dai,saidai ta lura akwai dan sauyin yanayi tattare dashi,maganar da suka tabayi watannin baya tadawo mata akai,sai take fatan ba lamarin bane har yanzu cikin ranshi ya kasa barinsa ba kamar yadda ta umarceshi,saidai koma meye zata tabbatar data sake cire masa batun cikin ransa har zuwa lokacin data tanada.


"Kaje ka huta,bani kadai ba har 'yan uwanka na marmarin ganinka,muna da isashshen lokacin zama mu gana,har wata nawa?...." Ta tambayeshi tana dubanshi fuskarta na fidda murmushi,yana tsaye hannunshi guda cikin aljihunsa,saiyadan rusunar da idanunsa zuwa duban wani sashen kana ya amsa mata cikin sanyi
"Ba wata ba ba satittika ba ammi,i forever came back" yanayin fuskarta saiya soma sauyawa daga murmushi zuwa hade rai,wani kallo take masa wanda dama ya tsammaci sama da haka daga gareta
"Me kake cewa azeez?,kadawo kamar yaya?,bayan aqalla akwai shekara daya da wasu watanni a gabanka kafin kagama,kuma kafi kowa sani koda ka gama din bawai zaka dawomin bane yanzu,zaka dora da masters dinka har zuwa inda nake ganin lokaci yayi da zaka dawo kaci gaba da rayuwa cikinmu,karka soma,kada ka yarda kayi abinda zai bata tsarina koya batamin rai,kafin kowa sanina,kafi kuma kowa sanin tsarikana akanka,saboda haka karka soma yin duk wani abu da kasan zai wargatsa tsarina" dukkanin idanunshi yazuba mata da wani irin duba dayake nuna zallar buqatar a tausaya masa a fuskanceshi da nashi buqatun,saita dauke kanta daga dubanshi,saboda ita kanta tasan da idanunshi kadai yana iya karya lagonta,saboda wata baiwa ta musamman da Allah yayi masa cikin idanun,murya a narke hakanan a sanyaye yace
"Please ammi...listen tome" 
"Kawuce ka huta,koma meye daga baya ka sanar dani,amma kasani,bazan yadda da dukkan abinda zaici karo da tsarina ba" daga haka ta baiwa kubra daya daga cikin amintattunta umarnin shigowa
"Allah yabaki nasara....aikene daga sassan fulanin masanawa...."
"A hada da nata da nasu duka ayi yadda aka saba" ta katseta ba tare data bari ta qarashe bayanin nata ba.


Shuru ya ratsa falon har kubran tafice,sannan shima yasoma takawa a hankali yabi sawayenta yana furta
"Na barki lafiya",da ido tabishi harya gama ficewar,tasauke ajiyar zuciya tana lalubar kujera tazauna bayan tadauki wayarta dake daura da ita tasoma neman wani layi,tana jin tausayinsa yana ratsata,amma tilas takauda kai saboda anata ganin tsarinta shine tsari,kuma ko meye tanayi ne don ci gabansa da alfanunsa.


A hankali yatura qofar qawataccen falon nasa cikin wata iriyar kasala ta zuci da gangar jiki,falone na qarshe wanda daga shi sai dakin baccinsa,yalwatacce kuma qawataccen falo wanda komai dake cikinsa kalolin milk ne da gold,komai qanqantar abun kuwa,komai dake cikinsa yana alamta maka gidan da kake kuma sashen wanda kake ba tare daka bata baki wajen tambaya ba,sarauta zalla,komai nadauke da tambarin masarautar,hatta kuwa da kujerun dake falon,falone wanda yake gaba gaba cikin jerin manya kuma tsararrun faluka dake kafatanin gidan,wannan shine qiyasi da wadanda suka samu katarin taba shiga falon sukayi.


Iska yafesar mai zafi daga bakinsa yana kallon manya manyan hotunan dake maqale a falo,wanda bana kowa bane face nashi maimartaba da mahaifiyarsa fulani aisha,wani shi kadai,wani shida ita,wani shida mai martaba wani su ukun,hotunane da sukayi bala'in kyau suka kuma dace da yadda aka shiryasu,hatta da frames nasu suma milk ne da gold.

Gaban daya daga cikin hotunan ammin dake saqale ya qarasa ya isa gabanshi,sosai yazuba mishi yana kallonshi kai kace itace tsaye yana fatan ta karanci tsantsar gaskiyarsa takuma tausaya masa,ya rasa da wanne irin yare zai mata bayani tagane,duk daya fahimci ta gane inda yasa gaba,saidai bata da sha'awa ko niyyar yi masa abinda yake da muradi.


A qalla yashafe kusan mintuna goma ahaka,kana da kanshi ya lumshe kyawawan idanunshi sannan yabudesu,dai dai lokacin daya sauke ajiyar zuciya yasanya hannunshi yana sassauta daurin tie dinshi,kana ya zareshi ya jefar,yasoma rage duk wani kaya da yasan zai takura masa dake jikinsa,a haka ya isa bedroom dinsa yatura yashiga yazauna bakin zagayyen gadonshi yana cire sauran kayan da suka rage.


Sai daya gama cire sauran kayan da sukayi saura a jikinsa sannan yawuce toilet dinsa dake manne da dakin gadon.


Ya shafe a qalla kusan minti talatin sannan yabude qofar toilet din yafito daure da towel,gargasar jikinsa tayi luf saboda ruwa datasha sai sauran ruwan dake diga tun daga sumarshi zuwa qafarsa,a maimakon yazauna shafa mai saiya koma gefan gadon yasake zama,ya jawo locker dake manne da gadon yasoma laluben wani abu.


Mintina qalilan ya debo layukansa na qasar nan yasoma qoqarin cire nakan wayarshi ya sanyasu,bai kammala ba wani abu dake daga saman gadonshi yadanyi wuta gamida 'yar qararrawa,kai kawai ya daga ya kalli abun yamaida kansa ga abinda yakeyi,yasan wani ne ke falon farko yana jiransa,hakanan yakejin baison doguwar magana duk da dama haka halittarshi take,hakanan baison ganin kowa.


Yana gama hadawa yakunnata ya sanyata saman gadon yatafi gaban madubi yasoma shiryawa,nikam tsaiwa nayi ina kallon ikon Allah,kowacce gaba da irin nata man da turaren tamkar macen dake tashen budurci haka yadinga shafa kowanne a muhallinsa,yana cikin fesa body spray wayarshi tadauki tsuwwa,saiya dakata yana komawa da baya don ya duba waye yakirashin.


'Safwa' da manyan baqi shine sunan daya bayyana saman screen din wayar,saiya dauke kanshi yaci gaba da abinda yakeyi din ba tare daya daga ba,saboda yasani tariga da tasan tsarinshi,idan ta katse din ba zata sake kiranshi ba.


Saidai a wannan karon sabanin baya kiranne yasake shigowa,cikin mamaki yasake dubawa,ba ita bace sufyan ne,mutumin da yakeso ya kammala shiryawa yakirashi,babu bata lokaci yadaga wayar yakara a kunnenshi
"Thank god,yauna taki sa'a,ringing biyu kayi picking,'yan iskan yau basa kusa hala?" Yasan me yake nufi,kuma yaudin baijin wani jokes a kanshi irin wanda sukanyi lokaci lokaci a tsakaninsu,murya can qasa yace
"Kana ina?"
"Bansan wannan taqamar taka prince,ka dawo zaka fara kenan,nine maganinka,any way ina dab da shiga garin abuja ne yanzu"
"Oh shit!" Yafadi yana runtse idanunsa
"Hey friend,yaya dai?"
"Baida amfani tunda baka nan,see you later" daga haka ya katse kiran,ya cusa hannunsa guda saman sumar kanshi yana yamutsata,yana buqatar taimako,yana buqatar tallafi,yazama lallai yayi dukkan mai yiwuwa ammi ta fusakanci,ta gane matsalarshi,bayaso yakai ga fadawa ga halaka,yana qyamatar hakan matuqa da gaske,saiya nufi wardrobe dinsa yasoma binciken kayan da zai sanya da hanzari.


Falon dake manne da bedroom dinshi yadawo yazauna hannunshi riqe da wayarshi,yashafe aqalla awanni kan wayar da alama akwai abinda yakeyi kafin alamun dake bayyana anason ganinsa sushiga kadawa,karo na wajen biyar yana basarwa kafin daga bisani yatashi ya isa gaban cctv camera din dake nuna mishi duk wani sashe na gidan,ya fuskanci daga falo na uku ne,saiya shiga inda camera din falo na uku take,afnan ce tsaye bakin madannin qofar,fuskarta na nuna alamun qosawa,sanye take da doguwar riga wadda tabude daga qasa sosai tarufe har qafafunta,kanta yane da mayafi wanda iyakarsa wuyanta,tadan bubbuga qafa alamun gajiya da tsaiwar,saiya daga yabata izinin shigowa.


    "Yaaya....barka da warhaka" tafada cikin nuna farincikin ganinshi
"Ammi tace zaka shigo,amma shuru munata jira,an kawo maka abinci kace a dakatar,shine ta aikoni in gaya maka,ka qaraso sassanta acan xamuci abincin rana tare" kai ya kada mata kawai,wanda hakan yasa tadan bata rai
"Yaaya,har yanzu baka daina ba?,baka bani amsa bafa"
"Am coming" ya amsata a taqaice,idan dasabo sun saba da halin miskilancinsa,wanda tun usuli haka yake,duk da kuwa yadda ammi taso ta sauyashi,koda qannenshi ne yadinga sakewa dasu suna hira amma abun yaci tura,ba kowanne lokaci magana take damunsa ba,tasan ci gaba da tsaiwarta bashi da wani amfani saboda haka tajuya tafice cikin ranta tana mita
"Shi mutum Allahn daya yishi koyaushe kaman wani kurma ko bebe,bakinsa ko tsami bayayi,saikace mai ciwon kunne wanda bayajin me mutane ke fada bare ya amsa su" da wannan qananun mitocin tafice takoma zuwa nasu sassan.


    Zaune yake yana fuskantar ammin tashi cikin shigar qananun kaya da suka sake haska quruciya da kyansa,tazarar dake tsakaninsu dukka kayan abincine da abunsha nau'i daban daban
"Abdul'azeez" muryar amminsa ta ratsa dodon kunnenshi,wanda hakan yasa ya dakata daga shan tataccen ruwan inibi zalla da yaketa faman yi tun dazun,gaba daya jin cikinsa yake a cunkushe,bayajin sha'awar cin komai,saboda matsalar dake barazana da rayuwarsa yana jin tafi qarfin komai
"Ammi" ya amsa mata muryarsa a tausashe
"Matsalar dake gareka har tayi girman da zaka gaza cin abinci?" Ta qarshe maganar tana kafeshi da idanunta cikin son sake karantarsa,saiya ajjiye kofin hannunshi ya hade hannayen nasa waje daya,yana matuqar jin kunyar yin maganar da ita akoda yaushe,abu babu wani wanda zai masa maganin damuwar indai bai tsaya yabude baki yayi magana da itaba yadda yadace
"Hakan nada alaqa da cemin bazaka koma karatu ba?" Tasake jeho masa tambayar.


   Wani nauyi yaji yahau kanshi sosai yadda ta tsareshi da idanu,irin wannan maganar banda abokai ba zaka iya yinta da kowa ba,to amma ci gaba da shurunshi na nufin fadawarshi halaka,saboda duk duniya ita kadaice zata lamunce mishi yasamu mafita
"Kiyimin afuwa ammi,nayi qoqarin nabi tsarinki kamar yadda kika umarceni amma hakan yaci tura,kiyi haquri ammi ki fuskanceni,idan na aikata wani abu da yake ba dai dai ba tamkar na zubar da mutunci da qimar masarautar nan dama taku masarautar,sa'annan bamusan ta wacce fuska abokan adawa zasu bibiyemu ba,wala'alla dukka abinda zan aikata din yazama sun tonoshi,yazama wani makami da zasuyi amfani dashi,wanda zai ruguza duk wani shiri naki akaina ammi,ammi....kiyimin afuwa,kamar yadda nataba gaya miki a baya" saiya sake sadda kanshi yana jin nauyi
"Ina da buqatar aure ammi,idan kikayimin,na miki alqawari bazai dauke hankalina koda ya kadeni daga dukkan qudurin da kika tsara ba,komai zai tafi yadda kike muradi ammi na miki alqawari".


Shuru ne ya ratsa ilahirin falon kai kace babu wani sauran me rai sai na'urori,kowanne tsakaninshi da ita akwai abinda ke kaikawo cikin zuciyarsa,tasani tabbas abdul'azeez tun shekarun baya abinda yake da buqata kenan,tun baikai ga furta mata ba,amma sai tayi tunanin cusa masa ra'ayin karatu tuquru dason maidashi wani madaukaki zaisa ya manta da komai yabi tsarinta,tana ganin a yanzu abdul'azeez tayi quruciya da yawa,yayi qanqanta ace yayi aure,totally bama plan dinta kenan ba,hakan yaci karo da dukkan wani tsarinta,yayin da gefan abdul'azeez zuciyarsa ke cike da fata dakuma burin samun nasara a wannan karon,yanajin cewa indai yayi failing wannan karon to kuma babu wata sauran nasara da zai kuma saka ran samu,hakanan yana tsoron abinda zai biyo baya,bashi da tabbacin ci gaba da wanzuwa a bigiren da yake kai yanzu,komai na iya faruwa dashi,duk da ko sau daya baya yiwa kansa fatan haka
"Abdul'azeez!" Ta kirashi da wani tune dake nuna komai zata fada din daga zuciyarta take gaya masa,magana kaifi guda kamar yadda dabi'arta take!
"Kamar yadda nima na gaya maka a bayane,zancan yi maka aure a yanzu yaci karo da dukkan wani tsari nawa,hakanan zai iya zama silar rugujewar komai,zan maka aure abdul'azeez....amma ba yanzu ba,akwai lokaci,zan maka aure alokacin da duniya tasan waye yarima Abdul'azeez,zan maka aure lokacin daka zama irin mutumin da nakeso,zan maka aure asanda ka qarasa zama cikakken mutum mai raza da firgita zuciyar maqiya abokan gaba da abokan adawa,zan maka auren a lokacin aure na kece raini,irin auren da zai shiga bakunan al'umma,kamar yadda na zaba maka mata wadda tadace takumayi dai dai da yarima abdul'azeez,hakanan idan kayi haquri zan cika maka daya burin naka,amma ayanzu abdul'azeez....a karo na farko ni mahaifiyarka ina mai baka haquri daka dakatar da gudanuwar wannan tunanin a ranka,gaba daya ma abdul'azeez shekararka nawa,25 years fa?,kai kana ganin da wadan nan qananun shekarun naka zaka iya daukan duk wani responsibility na aure?,gefe daya ga goal dinmu da muke son muyi achieving duka at d same time?" Saita kada kai
"Taura biyu ba zata taba taunuwa abaki ba lokaci daya,kayi qoqarin cika dukkan wani buri nawa kagani abdul'azeez,babu abinda zaka nema ka rasa daga nan har zuwa lokacin da zaka bar duniya".


Shuru yakuma biyo baya,cikin qananun mintoci qwaqwalwarsa tayi masa bitar kalamanta,sai kawai yajanyo kwanon dake cike da alkubus yasoma zubawa,saboda yana ganin no way out kuma,abinda yafimishi yaci gaba da azumin tadawwu'i da yakeyi,duk da cewa wani lokaci yakan gamu da tasgaro da wahalhalu,daga lokacin dayayi buda baki zuwa wayewar gari,ci gaba tayi da nazartarsa saidai ta kasa fahimtar kowanne yanayi tattare dashi,hakan yake wasu lokutan idan yaso,duk yadda kaso ga karantarsa sai hakan ya maka wuya,tasauke boyayyar ajiyar zuciya cikin ranta tana fata da saka ran maganar tawuce a wajenshi ne.
"Zaka koma makaranta da zarar hutunka ya qare kamar yadda aka saba,banason mai martaba yasan komai,wannan tsarina,banason kuma yasan da zamansa" kai kawai yasake jinjina mata.


"Auta?,wa nake gani kamar auta?"kubra daya daga cikin amintattun fulani aisha ke fada dai dai sanda take shigowa farfajiyar dake hade da falon da abdul'azeez da mahaifiyarsa ke zaune,cikin waninirin hanzari ta janye kunnuwanta daga laben datayi musu,sannan cikin lokaci qanqani tayi qoqarin yanayinta na masu gaskiya
"Saqo nazo zan kawowa yarima daga sassan fulani adama,to nasamu kuma babu kowa ciknku,kuma ta jaddada min muhimmancin saqon,shi yasa nayi yunqurin neman iso da kaina"
"Saqo?,wanne irin saqo?" Kubra tafada tana jifanta da duban tuhuma,saita miqa mata wani farin yanki dake nannade da wani abu a ciki,kamar ba zata karba ba sai kuma tasa hannu ta amsa tana jifanta da wani kallo
"Kinfi kowa sanin cewa idan fulani na ganawa da yarima,a irin wannan lokacin haramunne ga kowanne cikinmu yarabi wajen sai wanda ta yarjewa,kada ki sake wannan kuskuren ko gangancin,saboda data ganki da kanta kinsan hukuncinki basai na fada ba,a sauka lafiya" tafada tana nuna mata hanya,cikin girmamawa tace
"Godiya nake" kana da hanzari ta wuce kubran,zuciyarta fal farinciki na samun nasarar da tayi kubra bata ganota ba,uwa uba yau tasan tana da gwaggwaban kyauta na iyakacin abinda kunnuwanta sukaji mata,duk da maganar data jin bata zama wata cikakkiya da za'a fahinta ba,amma matuqar akayi dogon nazari ana iya fahimtar wasu abubuwan.


Tsaye tayi tana nazarin yadda tasamu auta a tsaye bakin qofar,bata karanci wani abu ba,amma hakanan taji hankalinta bai kwanta da ita ba,saita jujjuyaa saqon kana taju tafice dashi,don tasan koda an isar dashi ga fulanin abinda zatayi shi zatace nata tayi itama.


Daidai lokacin da wayarta dake saman cinyarta tadauki tsuwwa,tamaida idanu tana kallon kiran uswa babbar diyarta da bata jima da aurarwa ba,wadda ke aure a masarautar kano dake shigowa wayarta,ta dauki wayartata daga saman cinyarta kana tasake cewa
"Maimartaba yana bahrain,dazun kafin isowarka suka tashi,yatafi taron sarakunan arewa,yace ka nemeshi da layinsa nacan" daga haka tadauki wayar uswa din.


"Zaka koma makaranta da zarar hutunka ya qare kamar yadda aka saba,banason mai martaba yasan komai,wannan tsarina,banason kuma yasan da zamansa" fulani adama tasake maimaita maganganun da auta ta gaya mata,ta jujjuyasu tana nazarinsu yafi sau shurin masaki,karo na wajen goma sannan tamiqe tasake tattaki hannayenta goye a bayanta,cikin murya mai amon sauti tafurta
"Nasani wallahi nasani,tabbas akwai wani boyayyen abu da aisha take boyewa,ba shakka nasan da wannan,babu yadda za'ayi ke daya tal kika haifi da namiji wanda babu ko shakka ayau mahaifinsa yarasu ko yayi murabus zai maye gurbinsa,amma ace kin turashi karatu wata uwa duniya,kin zareshi daga dukkan wata harka ta sarauta tamkar shidin agola ne ba jinin gidan ba,tabbas akwai abinda aisha kike shiryawa" saita waiwaya tadubi auta
"Inama ace kin samo gundarin jimlar cikakkiyarta,ba shakka da ayau kin karbi 'yanci" sosai furucin yabugi auta harya sanya jikinta tsuma,tazube gaba daya kan gwiwoyinta tana duban fulani adama
"Indai hakane....namiki alqawarin bankado miki dukkan wani shiri nasu muddin numfashina matuqar zan zama 'ya"
Kai fulani adaman ta jinjina tana fidda murmushi kana tamata nuni da tana iya tafiya.☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️


     Tamkar wadda aka bugewa gwiwoyi haka ta dinga qarasowa gaban gidan nasu idanunta qur kan gidan kamar wadda keson fahimatar yanayin gininsa don zana taswirarsa,duk wata yunwa da gajiyar tafiyar qasa data kwaso daga makarantar zuwa gidan tatafi babu ita,a yanzun fargaba kasala da mutuwar jiki su suka maye gurbin wadan nan.


     Masu aikin gini keta kwaso qasa daga ciki suna fiddota waje,wanda kana ganin yawan qasan zakasan cewar wani sashe na gidan aka buge yabada wannan qasar,mahaifinta na coge qofar gidan cikin 'yan aikin yana sake musu bayani da wassafa musu abinda yakeso suyi masa,da gaske ne kenan hasashenta na dab da zama gaskiya?.


Hankalinta yayi matuqar nisa cikin duniyar tunani,har ta manta da cewa tsaye take qofar gidan nasu,saida taji wani hannu dake cike da qasa yana tabata ana cewa
"Yaaya oyoyo" sannan hankalinta yadawo jikinta,saita waiwaya tana duban gefanta,umaimace,jikin nan yayi budu budu da qasa kai kace tayi birgima ne cikin yashi
"Ya haka umaima,meyasaki wasan qasa bayan na hanaku"
"Gini ake mana yaaya a gida,sabon gini,har cikin dakinmu ma" tayi maganar cikin zallar quruciya gamida nuna murnarta a fili,lallai quruci dangin hauka,batasan hakan me yake nufi ba shi yasata take wannan farinciki,to amma kuma mamakinta datace gini har a cikin dakinsu,kada dai ace abinda yatabayi shiya sake maimaitawa,cikin sauri taja hannun umaiman suka shige cikin gidan da saurinta.


Duk da wannan aikin ginin hakan bai hana umna katti sana'arta ba,saidai duba daya zaka yiwa fuskarta kasan yau koma me aka mata a cike take fam,a nutse tabi tsarin ginin da aka soma yiwa kwaskwarima da kallo
"Ina mahaifinta yasamu kudin yin gini?,bayan yau kwanaki biyu baisiyo koda qwayar hatsi ya kawo gidan ba?" Tayiwa kanta wannan tambayar,babu mai bata amsa,hakanan tambayar bata da wani cikakken amfani a wajenta,tunda bayau tasoma gani ba,kusan wannan shine karo na uku a iya girmanta bayan tayi wayo cikin abinda zata iya tunawa,banda abinda yafaru cikin quruciya
"Me kike ne haka akaina,idan zaki gaba gwara kiyi karki fado kaina,don wannan ba abun mamaki bane wajen ubanku mai halin 'yan bunsuraye,wanda bai ganin akuya ya qyale ba tare dayabi ba,tunda kikaga haka ai amsar dayace,yaga wata akuyar ne zaibita" maganganun umma katti masu matuqar muni da kaifi suka katse tunaninta,saita maida kanta ga umma kattin bayan ta janye baya,da alama tun dazun take neman hanyar fidda kalaman bakinta,amma abun yayi muni da yawa,idan bata duba 'ya'yanshi ba da wasunsu a sannan ke cikin gidan a qalla ya kamata ta duba masu siyen abincinta da maginan dake wajen,idan su ba baqi bane game da yadda sukan aibata junansu maginan da masu siyayyar fa?,saita janye hannun duka qannen nata zuwa dakin nasu da tunkafin ta qarasa ta fuskanci aiki yabi ta kansa.


   Ilai kuwa an kwakwashe kusan rabin dakin an bar musu dan ragowar filin da take da tabbacin ba qaramin quntata zasuyi ba yayi zamansu,tunda dukkaninsu qara girma sukeyi,wannan ne karo nabiyu daya taba datsar dakin nasu yaqara cikin gininsa duk sa'ilin daya tashi aure,cikin baqinciki take duban yadda kayansu sukayi budu budu da sumunti,tana tuna awanni shida baya kafin ta fita makaranta yadda suka hadu ita da qannen nata suka killace kayan da dakin tsaf gwanin sha'awa,amma idan ka kalleshi a yanzu ba zaka tsammaci haka ba.


    Saita nufi akwatinta da sauri tana addu'ar Allah yasa kudinta data adana musu suke jalauta rayuwarsu basu salwanta ba,tajawoshi tabude tahau dubawa.


Nannauyar ajiyar zuciya tasaki harda lumshe idanu lokacin data iskesu yadda suke
"Mai gado!,ke bilki!" Muryar mahaifinta dake kwada mata kiran mafarauta ya ratso dakin,da alama dab yake da isowa,sai tayi hanzarin cusa kudin tsakanin cinyoyinta,daidai lokacin daya qaraso din


"Au,kema baqinciki kike da raya sunnar da mahaifinki zaiyi?" Yajefa mata tambayar da batasan hawanta ba bare saukarta,bata da wata mafita illa girgiza kai alamun a'ah
"Yar nema,sai anyi magana saiki shiga kadawa mutane kai kamar namijin qadangare,to idan ba baqinciki kike ba kina ji ina qwala miki kira ki kasa bude baki ki amsa min?"
"Banji bane baba,kayi haquri" tafada cikin rauni da sanyin murya,yanayin yadda tayi maganar saiya tuna masa da mahaifiyarta maimunatu,sai jikinsa yadanyi sanyi,ya qaraso cikin dakin yana dubanta
"Kiyi haquri maigado,ina nema mana sauqine kinji?" Yafada cikin muryar lallashi,cikin mamaki ta daga kai tana dubanshi,sauqi kuma wanne iri?,bataga wani alamu na neman sauqi daga mahaifinta cikin rayuwar da suke ciki ba,ganin bata fahimta ba saiya sake cewa
"Eh,kinsan annabi yace idan kana cikin talauci kana da mace daya ka ta biyu,idan ka qaro baka rabu dashi ba ka qaro ta uku,idan ka qaro baka rabu dashi ba ka cike ta hudu" tamau kanta ya qulle,duk da tasani babanta yayi dogaro da wannan hadisin qaryar ne tunda dadewa yake aikata dukkan aure aurenshi,hadisin da bashi da tushe balle makama,hadisin da bashi da muhalli ko digo cikin addininmu,hadisin qaryar daya halakar da magidanta da dama,amma tana da yaqinin a yanzun bazai taba fahimtar bayaninta ba idan ma tace zata fahimtar dashi
"Don haka shi yasa naketa wannan abun ko Allah xaisa a dace....nadan ragi dakinku zan mata bandaki a cikin dakinta,saboda balaraba tacemin batason bandakin hadaka,kinsanta gwanar tsafta ce,Allah dai yakawota zaki ganewa idanunki" ya qarashe maganar yana washe baki kamar wanda aka yiwa albishir.


Itadai kanta na duqe a qasa takasa koda dagoshi saboda kunya da nauyi harya gama maganarshi yamiqe tsaye,saiya sanya hannunshi a aljihunsa yafiddo dari
"Ungo wannan ki riqe a hannunki keda qannenki kuci abinci,karki bari wancan baqar kadarar tagani don silaina yau bazai shiga hannunta ba 'yar baqinciki,nasan yadda kiketa dawainiya dasu,kedin diyar albarka ce,kinyo gadon halin uwarki,Allah yaqara miki himma,yabaki miji na aurar dake na huta,ko yaron nan yamiki magana zai fito maigado karki masa halin miskilancin nan naki na banza,ki bashi dama kinjiko?" Bata da wani xabi illa tace masa to,saboda ta qagu ma yafice din yabasu guri.


Ranar bazata fita aiki ba saboda umma luba ta gaya mata zatayi kwana biyu gidan sarki,don haka tazage ita da qannen nata suka gyara ragowar filin dakin daya rage musu suka goge simintin da tsumma.

Post a Comment for "SIRADIN RAYUWA CHAPTER 3 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...