SIRADIN RAYUWA CHAPTER 19 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 19   BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 19 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

- - Post a Comment

 SIRADIN RAYUWA CHAPTER 19

 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA


Wani kallo tayi masa na tsiwa,wanda shi kuma ya jishi har jinin jikinsa

"Wace matar auren naka?,idan zaka farka daga wannan mummunan mafarkin naka ka farka,ada dai qaddara tasa na zama matarka,bada amincewata ba,ba kuma don ina sonka ko qaunarka ba,sai don......".       Gaba daya ya fincikota zuwa cikin jikinsa da hannunshi qwaya daya tal,ya kuma haura gadon dasu gaba daya ya turmusheta,bayan ya azq mata dukka nauyinsa,abinda bata zata ko tsammata ba,hakan yaso wucewa da numfashinta na wucin gadi.      Cikin sakanni qalilan dumin jikinsu ya gauraya,suka soma musayar numfashi duk da yadda nata numfashin yake mata wahalar jaa da kuma fitarwa saboda yadda yake a samanta ya aza mata nauyinsa,fuskarshi saitin nata,idanunshi da suka sauya launi cikin nata,duk da sun rage girma hakanan launinsu ya sauya,amma sai taji sun mata nauyi,wani yanayi can daya taba shudewa da dadewa memory dinsa yazo cikin qwaqwalwarta a take,saita birkice masa,ta soma tureshi da dukkan qarfinta,tana magana da qyar

"Ka dagani ko in maka ihu"

"Bismillah" yace da ita,alamun ya bata damar yin ihun,sai kawai ya sanya bakinsa saman dogon wuyanta,bayan ya saka hannunshi ya sauke jelar gashinta,ya soma aika mata da wasu saqonni da suka sanyata mutuwar wucin gadi cikin salo na babu zato bare tsammani.     Hankalinta ta maida jikinta cikin sauri,ganin yadda tsigar jikinta ta soma zubawa,saboda yadda ya canza waje daga wuyan nata zuwa kunnenta,tun tana tureshi harta soma gajiya,tun tana cewa zata masa ihu harta soma cewa zata masa Allah ya isa,amma baima nuna yasan tanayi ba.      Babban abun tsoron yadda taji jikinta na sauyawa,mood dinta yana canzawa zuwa wani yanayi mai wahalar fassarawa,duk da yadda zuciyarta take a zafafe amma hakan bai hana gangar jikinta amsar saqonshi ba.       Hankalinta ya sake tashi ganin yana nemam shiga wata gona ta daban,taji kamar sama zata rikito mata data tuna gidan babu uban kowa bare ta nemi maceci,sauran qarfin daya rage mata ta sanya dukka ta turashi,ya motsa,saidai bai sauka daga samanta ba,saidai kamar allura ta masa ko wata tunatarwa,donshikansanya soma manta a inda yake.      Ya tsaya cak da abinda yakeyi din,ya kifa kanshi saman qirjinta yana maida numfashi da sauri da sauri,yana kuma jin yadda itama take maida numfashin har qirjinta yana dagawa,sautin bugun zuciyarta ya fito muraran.     A hankali ya soma saita nutsuwarshi,baiso ya daga fuskarshi a haka ta ganshi a ayanayin da yake ciki,ita dinma bata sake wani yunquri ba,don da qyar take fusgar numfashinta,tana kuma son daidaita nutsuwarta,ta yadda zata iya masa qwaqwqwaran kashedi.     A hankali ya mirgina gefe sannan ya tashi ya zauna sosai na wasu sakanni,hakan ne ya bata damar gajin yadda ya yiwa rigarta,saita juya itama da sauri tayi rub da ciki,haushi da takaici gami da matsananciyar kunya tana kamata.      Tana jin takunsa amma ta kasa juyowa bare ta masa tsiwa ko jan kunnen da tayi niyya,taji tsaiwarsa bakin madubinta na minti kusan daya sannan taji ya nufi qofa,sai kuma ya dakata.      Ba tare daya juyo ba cikin wata shaqaqqiyar murya yace

"Ban zama lusari ba,ba kuma zan taba zama ba,sassaucina da sanyina ya ta'allaqa ne kan laifin da nasan mun aikata miki,har a yanzun ke matatace har a wajen Allah,ina da kishi matsananci,bazan lamunci shigar kowa gonata ba ko wucewarsa ta gefenta ba,duk wanda ya aikata hakan zai gane bani da dadi,nafi namijin goro daci,ki masa kashedi,ki kuma ja masa kunne da babbar murya cewar kada ya sake ya sake nuna ya taba saninki ko a hanya,indainyana son tsira da mutuncinsa da lafiyarsa,idan kuwa ke kika kulashi....to ban yafe ba koda ban gani ba" daga haka ya taka a nutse yayi gaba.     A zabure ta miqe da niyyar gaya masa cewar bai isa ba,kuma shi yasan da wani igiyar aurensa a kanta,ita batasan da wannan ba,saidai kallo na qarshe daya jefeta dashi,ya kuma ja qofar ya rufe shiya kashe bakinta murus,tsahon minti guda tana zaune saita koma ta kwanta rigingine tana jan tsaki.      Maimakon taji haushinsa sai ta soma jin haushin kanta lokacin da qamshin mayen turarensa ya soma buwayar hancinta,data bincika da kyau sai taji jikinta ke qamshin kamae ya fesa mata turaren ne,hatta da fatarta data shanshana qamshin take,hakanan bedsheet dinta,haushin kanta ya cikata,saita miqe ta zauna tana tuhumar kanta,ya akayi tayi sake haka har ya cimmata,me yasa sanda ya shigo bata shiga bandaki ta kulle ba?,wani dogon tsakin taja ta sauka daga gadon,ta isa bakin qofa ta murza muqulli sannan ta nufi bandaki,don ta tabbatar idan ba wanka tayi ba ba zata daina jin qamshin ba.      Ita kadai a toilet tana wanka amma taja tsaki yafi cikin kwando,takanji haushin kanta ya sake kamata idan ta tuna yadda ta ruski jikin sanda tazo yin tsarki

"Allah ya isa na" ta ambata qasa qasa,bata taba tsintar kanta a yanayi irin wannan ba sai yau,kuma duk silarshi.       Kayanta ta maida data fito,duk da sun yamutse,ta isa gaban mudubi ta kalli kanta,duk sai taji haushin rigar ya kamata,don haka ta zage zip din ta cireta ta cillata cikin kayan wanki,ta dauko wasu ta sanya.      Tana shirin barin gaban madubi taga qaramar takarda da bironta data yi rubutu dazun aje a gefe,saman takardar memory card ne akai,ta dauke memoryn ta warware takardar.      Lafiyayyen rubutu ne cikin tsari kamar haka

_banda a gidan wasu nake,wasunma dana shigo gidansu ba tare da izininsu ba,wanda hakan ya taka dokar addini,da yau saina kaiki duniyar da zaki gane shayi ruwa ne,ki kuma sake sako wasu twince din part two,amma ko a yanzun nasan na bar miki tambarin da zaki dinga shafawa,kina kuma tuna cewa kedin mallakin wani ce,mallakin abdul'azeez shi daya,kuma har duniya ta nade....,ga memorynki idan kina da buqata,wayarki kuma da layukanki kunyi sallama dasu,nama yi gwari da tuntuni ban rabaki da ita ba,don bansan gardin daya saya miki ba,nima na tafi da memory mai dadi a ruhina,duk da kin cakawa zuciyata mashi,kishinki zai iya halakani kafin safiya,karki kuma sake fita bada iznina ba._


           _yarimanki ne,uban 'ya'yanki kuma_      Yayyaga takardar ta hauyi tana masifa ita kadai

"Aikin banza aikin wofi,gwara ka nema matarka tun dare baiyi maka ba,don ban yarda da wannan tatsuniyar ba,kuma abinda kayin yanzun alhaki a kanka wallahi,baka isa kamin shamaki da yin mu'amala da duk wanda naga dama ba,wayata kuma dole a adawomin da abata,tunda ba wani ne ya siya min ba ehe" haka ta dinga masifa ita kadai cikin gidan,ta koma gadon ta kwanta bayan ta canza zanin gado,sadai bata dade da kwanciyar ba taji sam kwanciyar babu dadi,hakanan ta dinga tariyo mata abinda ya faru dazu,don haka ta kuma jan tsaki,sannan ta sauko daga gadon taja dankwalinta ta daura,tama fice daga dakin gaba daya zuwa falo,da niyyar daukar landline ta kira anty zuhriyya,don yadda takejinta sam a yanzun bata son fitar

"Kodai gargadinsa ne ya miki tasiri" wata zuciyar ta tambayeta,kamar ita da wani tace

"Haba,shi din banza,bai isa ba"Ta baiwa kanta da kanta amsa,tana isa wajen wayar ta zauna sannan ta janyota ta fara kiran.      Anty zuhriyya cewa tayi tayi zamanta ma kawai,sa biya su dauko yaran duka saisu dawo tare,hakan itama ya mata dai dai,saboda wata muguwar kasala da takeji,kuma hakanan taji fitar ta fice mata aka.       Har zata tashi sai kuma ta koma ta zauna ta kira assadiq,tambayar abinda ya samu wayarta ya fara yi,saita rufe masa kan cewa babu chargy ne,ta sanyata a chargy,sannan ta gaya mishi amincewarta na zuwanshi a goben.      Hira yake janta dashi,amma sai taji sam hiran bata mata dadi,don haka ta dauki uzuri ta aje wayar,sai kawai ta zame a nan ta kwanta,don gaba daya batason komawa cikin dakin,saboda qamshinsa da har yanzu bai bar dakin ba.      Anan dinma bawai ta tsira bane,haka abun ya dinga fado mata arai,ta dinga juyi tana canza kwanciya gami da jan tsaki ita kadai.      Tun a hanya yana tuqi yake jinsa cikin wani irin nishadi mara misaltuwa,kallo daya zaka yiwa fuskarsa ka karanci hakan,a lokacin ya dinga tuhumar kansa,mai yasa ma ha tsaya yana kallonta a baya bai mori lokaci irin wannan ba?.       Yanayin ya dawo masa da memory masu yawa da suka shude a wancan lokacin,ya tuna first night dinsu,wani irin baudadden first night,wanda ko a labaru shidai bai taba jin irin nasu ba,saiya saki murmushi,ya saka hannunsa guda daya da baya tuqi da shi ya shafi qirjinsa

"Zan qawata darenmu na farko da zamu sake rayawa fiye da tunaninki,na miki tanadin soyayyar da sai ta kusa zautaki ta kuma zauta tunaninki" ya furta haka shi daya cikin zuciyarsa,da wannan yanayin ya isa gida,kana kai tsaye ya wuce sassansa.       Toilet ya fada yayi wanka,sannan ya dawo ya fada saman gadonshi bayan ya fito,bai jima a duniyar tunani ba bacci yayi awon gaba dashi,baccin dake cike da wata irin nutsuwa daya jima bai sameta ba,baccin daya cika da.mafarkai,shida bilkisu cikin wata rayuwa mai dadi irinta ma'aurata,wajen da baikai ba a mafarkinsa sai daya kai,hakan ya sanya bayan ya farka dole ya sake wanka,zuciyarsa ta sake cika fal da shauqinta bege da wata iriyar zazzafar qauna,hakanan ya fito shi daya yana shawagi cikin wani lambunsa dake sassansa,yana jin zuciyarsa fayau,sai nishadi da soyayya da suka cikata maqil.      Bayan ya koma daki abun mamaki saiya tadda miscal din safwa jingim,tsaki yasha yana gyada kai ya aje wayar baibi ta kanta ba,ya rantse wannan karon zaka ga ainihin kalarsa da bata taba gani ba,zai saita musu tunani tunda su ya fuskanci basu dashi.¶¶¶¶¶¶¶¶¶    ¶¶¶¶¶   ¶¶¶¶¶¶¶       Tsaye take gaban mudubinta riqe da soson hoda da take shirin shafawa fuskarta amma ta kasa,saita buge da kallon kanta,ta rasa me yasa hakanan batajin wani karsashi a jikinta,farinciki ko dokin zuwan assadiq sam,bayan ita ta bashi iznin zuwan,komawa tayi saman kujera ta zauna riqe dai da soson

"Ko gargadinsa ke razanar dake?,ko don maganar da yayine kikeson ki fasa fita?" Zuciyarta ta tambayeta,saita kada kai da sauri

"Allah ya sawwaqe,shi din wa?" Tayi maganar tana fara shafa hodar a fuskarta.       Turare tadan dake fesawa kadan,sannan ta zura hijabinta mai hannu dark pink,wanda ya haskata sosai,ta zura slippers sannan ta fito.       Suna falo dukansu suna kallo,anty zuhriyya ta fita kitso tun daxun,daga ita saisu cikin gidan ta dubesu

"Najwa,akwai girki a kitchen,ki duba kafin na dawo"

"Tohm mami" ta amsa mata tana sake gyara zamanta saboda yadda kallon yayi mata dadi.      Amatu ce ta nace saita bita,hakanan badon taso ba ta barta suka fita tare.       Yana daga qofar gidan saman motarshi,cikin mamaki ta dubeshi

"Ya baka qaraso ciki ba?" Murmushi ya saki

"Nishadi nakeji yaukam,sai naji nafison zaman nan din,kona bude miki motata mu zaua ciki?" Wani kallo ta jefa masa mai kama da harara,saiya qyalqyale da dariya,don yasan kwanan zancan,ba abinda tafi tsana irin zance cikin mota,shi yasa shima ya tsokaneta da hakan.      Shirmen amatu ya tsaya biyewa har sukaci lokaci kafin ta shiga gida ya kuma saurareta

"To ya akayi?" Ya fada cikin murmushi yana dubanta,saita daga kai daga wasa da take da yatsunta tun daxu data fada duniyar tunani duk zaman hirarshi da amatu,murmushi kawai ta saki

"Kai za'a tambaya" gyara zamanshi yayi

"Kinsan meye?"

"Saika fada"

"Hajiya na bala'in son na kai mata ke ta ganki,tunda na soma mata zancanki itama kullum maganar kenan,ta matsu taga nayi aure,saboda na soma mata zancan rabi'a,har ta saka rai kuma taji shuru" murmushi tayi ta kada kai

"Lokacine,zamuje idan yayi".      Daidai lokacin anty zuhriyya ke dawowa daga gidan kitson ita da abeed,suka gaisa da assadiq,saidai yanayin fuskarta a yau ba kamar yadda suka saba gaisawa ba,hakanan tayi gaba tana dan binsu da kallo wanda hakan ya sanyawa bilkisu tsarguwa.       Tun safe yake fama da kanshi kan yadda yakejin matsanancin son ganinta,duk yadda yaso hana kanshi ya kasa,saboda haka daga masallaci da yayi sallar la'asar kawai yasaka cikin hadiman gidan mutum biyu suka daukoshia mota suka kawoshi.       Suna dosar unguwar farincikinsa na daduwa,yauma kota halin yaya yana jin saiya ganta koda bataso,saidai kuma me?,suna kusantar gidan fara'arsa tana raguwa,tun idanunsa na ganin masa kamar ba dai dai ba har ya tabbatar ita dince dai tsaye,tsaye tare da wani.      Wani bala'e'en wutar kishi ce ke ruruwa cikin ransa da zuciyarsa,lokaci daya kamanninsa suka canza,ya dinga furzar da huci,tun kafin su qarasa ya sanya suka faka motar,yayi shuru zaune a ciki yana kallonsu daga inda yake.      Da qyar ya iya daidaita numfashinsa sannan ya dakatar da hadimin dake yunqurin bude masa qofa,ya bude da kansa,qafafunsa ya soma zirowa kafin gangar jikinsa ya biyo baya,hannayensa zube cikin aljihunsa yake takawa zuwa inda suke tsaye,idanunsa a kansu harya cimmasu.       Sam basu ganshi ba,tana bashi amsar wata tambaya da yayi mata,wadda tambayar tayi matuqar bata dariya,sai suka hada idanu da ita.      Cak dariyar ta tsaya mata,gabanta yayi wani mummunan faduwa da batasan dalilin hakan ba,hakanan taji dukka gwiwoyinta sunyi sanyi,koda batasan fuskarshi sosai ba amma tasan cewa zallar bacin raine a saman fuskarsa.      Sauyawar yanayinsa ya sanya assadiq juyawa shima,suka hada idanu da yariman,saiya dan zuba mishi idanu,shahararren dan kasuwan da ya jima yana ganin tarin kama mai yawa tsakaninsa da yaran bilkisun,abu biyu ya  hanashi mata maganar koya tambayeta,abu na farko yana tsoron amsar da zaiji daga gareta,tace masa eh shine mahaifinsu amatu,wanda indai.hakan ya kasance,bayajin matar data taba mallakar mutum kamar azeez din zata soshi so na qauna har zuciyarta,ta kuma aureshi da zuciya daya,a ma'aunin cancanta da kaiwa mizani ko kusa ko alama bai isa ya hada kafada da yariman ba,tako wanne fanni ya mishi shal,babu bigiren da zaya iya tsaiwa ya hada qualitynsa da nashi,tun daga kyau,ilimi,zati cikar halitta da haiba,uwa uba dukiya da nasaba.      Abu na biyu kuma idan ya tuna tun asali,auren dole akayima bilkisu,wanda bayajin akwai macen da za'a aura mata mutum kamar abdul'azeez kaisa din ta kira auren da sunan auren dole,mutumin da tarin cincirindon 'yammata ke buri da fatar ya waiwaya ya dubesu koda sau daya ne,koda bada batun aure ba,koda iya friendship ne kawai amma basu samu wannan damar ba,sannan bayajin mutum kamarshi zai auri macen da baiso ko bata sonshi,saboda dama da Allah ya bashi na iya auren duk irin nau'in macen da yakeso,daga kowanne irin nau'in jinsi yare ko qabila,wadan nan tunane tunanen da yake yawanyi su suke gaya masa ba abinda ya hada bilkisunshi da shi,face kama kawai daga Allah,wadda ke nuna zallar qarfin ikonshi,isarshi qudirarsa da iradarsa,kamar yadda yaji ana cewa,kowanne dan adam akwai masu kama dashi a doron duniya mutum saba'in.        Kallo daya tak ya yiwa assadiq yasha jinin jikinsa,hakanan ya sake tsaida hankalinsa tsam,a hankali ya bude bakinsa cikin izza da qasaita yace

"Banason in cutar dakai,amma kada ka yarda ka qara minti biyar qofar gidan nan" yana kaiwa haka ya damqi hannun bilkisu yayi gaba.     Turje turje ta fara yi tana fadin ya sakar mata hannu,amma baiko waiwayeta ba har ya isa bakin motarsu,ya baiwa hadiman umarnin su fita subar mishi key din a jiki.      Haka kuwa akayi,ya sanyata a mazaunin kusa da driver ya rufeta,sannan ya zagaya daya set din ya zauna ya rufe sannan ya tashi motar da wani irin mugun gudu daya tsorata bilkisu ya fice daga layin.      Tafiya sukayi ta wajen mintina talatin kafin yaja wani wawan burki daya sake tsoratata,ba tare daya kashe motar ba ya waiwayo yana dubanta,ya zuba mata rinannu kuma narkakkun idanunshi,cikin jikinsa can qashinsa yakeji kamar zazzabi nason kamashi,yayin da yaketa controlling fushinsa,saboda baiso yayi abinda bai kamata ba,ko ya wuce gona da iri.      Dauke nata idanun tayi daga irin kallon da yake mata,cikin hade girar sama data qasa tace

"Ina kake shirin kaini,ka maidani inda ka daukoni,koka budemin na fita kaji ko?".      Shuru yayi mata kamar baxaiyi magana ba,sai daya tabbatar ya rage kaso mafi yawa ma fushin dake cinsa sannan ya bude baki,cikin murya mai sanyi kaman an sanyashi a ruwan qanqara,saidai kuma cikin fushi dake bayyane qarara cikin muryarshi yake cewa

"Bakisan ainihin waye azeez ba....nayi imani da hakan,kozan lamunci komai bazan lamunci wasa da izgilanci da igiyar aure na ba,kiyi komai saboda an taba ranki,amma banda wasa da martabar aurena....idan da naso,zan iya daukarki,na kaiki wani waje wanda ba wanda yasani,tunda kedin mallakina ce,amma bazanyi hakan ba,saboda aikata hakan kamar nayi amfani da qarfina ne maimakon neman yarda da aminci afuwa da kuma shafe laifuka da mantawa dasu,amma ki kiyaye,ki kiyayi aikata ire iren wadan nan abubuwan,na rantse daga yau duk wanda na sake kamawa yazo wajenki da sunan tadi sai na masa daurin da babu wanda ya isa ya fito dashi,sai nasa ya bata,bacewa ta har abada...." Sosai kalamansa sun shigeta,kuma daga yanayinsa ba shakka zai aikata sama da hakanma a kanta,to amma batason ta nuna mishi weekpoint dinta bare yaci gaba da amfani da hakan,saboda haka cikin tsiwa tace

"Saboda kuna da mulki?,kuna da kudi?,kuna da fada aji?,saboda kai wanine?" Bai amsa mata ba,hakanan bai fasa tada motar ba,illa dai kawai yayi wani qaramin murmushine na gefan baki,idanunsa na akan titi,yayi ribas din motar ya koma titin daya baro,sai a sannan yayi magana guda daya

"Lokaci ne....kibi a sannu 'yammata" yayi furucin yana qoqarin cooling mind dinsa,don ba qaramin zafi yakeji qirjinsa yana masa ba,kamar ana kara masa garwashi.      A qofar gidan ya sauketa,fit ta fice ba tare data waiwayoshi ba,ya bi takunta da kallo harta shige,sannan ya lumshe idanu yana jin yadda qirjinsa keci gaba da zafi,ya sake juya akalar motar a hankali ya fita a layin ya harba titi.      A bakin falo ta tadda anty zuhriyya tsaye,kamar dama tana dakon shigowarta ne tace

"Ina kikaje?,na aika qofar gida kizo akacemin baki nan,babu motar assadiq din kuma a wajen" duk sai ta dibibice,ta rasa yadda zatayi mata bayani kuma me zatace mata?.      "Ta dawo?" Ta jiyo muryar abbaa dake saukowa daga sama,saita waiwaya ta dubeshi

"Eh gata nan"

"Yauwa maigado,ki qarasa dakin baki kina da baqi" ya fada sanda yake qarasowa cikin falon riqe da wasu takardu.      "Baqi kuma?" Ta fada cikin ranta cikin mamaki,tabbas taga baqin wasu kyawawan motoci a harabar gidan,amma bata taba kawowa cewa baqinta bane,to baqi daga ina?,kuma su waye?,ganin babu wanda zata yiwa tambayar sai kawai ta juya ta fice zuwa dakin baqin ranta cike fal da wasi wasi.       A hankali ta shiga falon bakinta dauke da sallama,hakanan takejin wani irin nauyi ta kuma kasa daga idanunta ta kalli falon bare taga su waye a ciki har sai data iso ainihin falon.       Faduwar gaba taji saboda ganin fuskar dattijon wanda ke amsa sallamarta cikin sakin fuska dake cikin nadin farin rawani me ratsin gold,kwarjini da haibarsa sun cika falon gaba daya

"Maraba da 'yata bilkisu....maza qaraso nan" ya fada yana nuna mata daura dashi,ganin tana niyyar sulalewa ta zauna daga bakin qofar falon.     A hankali ta qaraso,sannan ta zame ta zauna a qasa kamar dazun kanta na kallon qasa,ta motsa labbanta da qyar wanda batasan me yasa tunda taga mutumin takejin wani irin nauyi ba tace

"Barka da warhaka"

"Barka kadai diyata,marhaban da surukata bilqisu" kasa amsa mishi tayi,sai gingirin da taji kanta yayi mata.      Shuru na wani sakanni sannan taji yayi gyaran murya sannan ya fara magana cike da dattako da kuma nutsuwa

"Sunana abdallah mu'az kaisa,mahaifi ga abdul'azeez...." Saiya dan dakata,yayin data sake daga kai a sace ta kalleshi,eh babu shakka,ga kama ta jini nan tsakaninsu,saita sake sadda kanta,yaci gaba da magana cikin hikima da nutsuwa

"Ya akaji da hidimar rayuwa,ina 'yan jikokina?" Gabanta yadan fadi,yasan dasu ne dama?,garin yaya?,waye ya gaya mishi gidan anty zuhriyya?

"Suna lafiya alhmdlh"

"Ma sha Allah"

"Amm....na samu labarin dukkan abinda ya faru tsakaninki da iyalina cikin satin daya gabata,a gaskiya ko a mafarki ban taba kawowa aisha ko abdul'azeez zasu aikata wani abu makamancin haka ba sam,sai gashi abun mamaki hakan ta faru,abun yayi matuqar girgizani da kuma daga min hankali,hakanan ya sakani cikin shakku da nazari..." Saiya dakata yana maida numfashi,da alamu abun yana tabashi sosai har yanzu cikin zuciyarsa

"Nazo da kaina wajenki diyata don na baki haquri,na kuma nemi gafararki.....karki dauka nazone a madadin abdul'azeez ko mahaifiyarsa,a'ah,nazo ne on behalf my self,nida kaina naga ya cancanci nima na baki haquri,saboda an cutatar da rayuwarki,an ruguxata ba bisa amincewa ko yardarki ba,an miki ta qarfi,kiyi haquri kiyi haquri ki kuma yafe ma masarautar kaisa gaba daya" wani irin kwarjini da nauyinsa takeji,da yake bata haqurin kamar zata nutse a wajen,indai har ta cika cikakkiyar yar adam,wadda ba butulu ba,ai bata da bakin magana sai godiya ga Allah,domin a yanzun ya mata komai,rashin cewa bata yafe din ba bataga me zai qareta dashi ba,don haka tace

"Ranka ya dade na yafe,Allah ya yafemu gaba daya" murmushi yadanyi sannan ya sake cewa

"Na gode qwarai da gaske....sannan akwai alfarma ta biyu da nakeso kiyimin,kada kice zaki duba wani abu ki tursasawa kanki wajen yin wannan alfarmar,a'ah....wannan zabinki ne,sai yadda kikace,ina mai neman alfarma a wajenki daki koma dakinki,kamar yadda abdul'azeez ya shaida min cewa ke matarsa ce,bayan ya maidaki gaban shaidu guda uku,mata biyu namiji daya,na kuma tabbatar da gaskiyar hakan....ina neman wannan alfarmar daga gareki ne domin kubutar da mutunciki da nasa da kuma na mahaifiyarsa da zaki taimaketa akan hakan" kanta ta daga da sauri ta kalleshi suka hada idanu,saitaji nauyi tayi maza ta sake duqad da kanta,alfarmar ta mata nauyi da yawa,har yaso ya fuskanci haka,saiya dora da cewa

"Kiyi haquri,ki kuma taimakemu,neman komawarki bawai yana nufin ki yafewa abdul'azeez ko aisha ba,kina iya ci gaba da hukuntasu ta yadda kikaso....sannan koda kin amince...zaki koma dakin nakine a duk sanda kikeso,igiyar aurenku ce banason a tsinkata kodon albarkacin albarkar yara har biyun da Allah ya baku,sa'annan shi kansa bazan shaida masa hakan ba,har sai kin gama hukuntashi son ranki,kin kuma gamsu a jiki da zuciyarki cewa hukuncin yayi miki.....don Allah diyata" ya furta yana dan zamowa kamar zai sauko qasa.       Sosai taji wani irin nauyi da kunya,da kuma tsoron kada fa ya sauko ya durqusa mata,mutumin da aqalla yama girmi mahaifinta bare ita,data tabbatar sa'ar autarsa afnan ce,don haka cikin firgici da sauri ta furta kalmar

"Na amince" ba tare data shiryawa fadar hakan ba.
      Tana iya jiyo ajiyar zuciyarsa,ya saki murmushi wanda ya bayyana sannan yace

"Alhmdlh,alhmdlh,ba shakka kin cika 'ya ta gari,kuma nagartacciyar uwa ga jikokina,na gode miki sosai bilkisu,na gode qwarai da gaske,ubangiji ya albarkaci rayuwarku,yadda aka miki katsalandan a rayuwarki ina roqar sarki Allah ya sake miki juyi da sauyin rayuwa mafi alkhairi" addu'a sosai ya dinga jerowa tana amsawa da amin,har zuciyarta tayi wani irin taushi,hawaye ya soma sauka saman fuskarta.       Sanda ta fita sai data turo.masa su amatu,sun jima a wajensa kafin su dawo cike da kyautuka.      Batasan iya dadewar da sukayi ba,saboda tunda ta dawo tana dakinta a kulle,kwance saman gado tana rusgar kuka,tana kuma tuhumar kanta,anya batayi kuskuren amincewa zata koma rayuwa cikin wadan nan ahalin ba?,ta kuma amince babu neman shawara ko yarda antyn tata wadda take kamar mahaifiya a wajenta,wadda ta tsaya tsayin daka,kai da fata wajen inganta rayuwarta,harta kawo bigiren da take kai a yanzu,uwa uba kuma mahaifinta,duk da shi ya kasance sila kuma dalilim afkuwar komai,amma a yanxun ai ya canza,iri sauyin da bata taba zata ba,kuma kusan yama fita jin ciwo duk sanda ya tuna yadda al'amuran suka gudana.       Ta fannin anty zuhriyya tana ankare da ita,ta kuma san kwanan zancen,don haka ta hana kowa rabar dakin da take,ta bata lokaci,tasan nan da wasu lokutta zata sauko komai zai daidaita,saboda ko a yanzun itama tafi mata sha'awar takoma gidan uban 'ya'yanta,amma har yanzu akwai jiqaqqiya tsakaninta da fulani,batajin zata barta haka.       Ganin har sallar isha'i bata fito ba ya sanya anty zuhriyyan ta nufi dakin nata,inda tabar duka yaran suna cin abincin dare,tayi knocking qofar,a sannan bilkisun na saman abun sallah,wanda tun sallar magariba bata tashi daga kai ba,tayi istihara yakai sau goma duka a waje daya,tana neman zabin Allah,sai taji ta samu nutsuwa 'yar kadan cikin zuciyarta.      Tashi tayi ta bude mata,ta shigo idanuta a kanta,kana ta samu gefan gadon bilkisun ta zauna kana tace

"Tunda baqonki ya tafi baki fito ba,hala lafiya lau?" Kanta a qasa tana murza tafin hannunta,tana jin wani nauyin anty zuhriyyan kan hukuncin data yanke ba tare da shawartarta ba,ta rasa ta inda zata soma gaya mata,sai taji qwalla ta cika idanunta

"Na aikata wani ganganci na saurin amincewa da alfarmar daya nema a wajena ba tare dana shawarci uwa a wajena ba,saboda girma da shekarunsa...." Murmushi mai sauti anty zuhriyya ta saki wanda ya baiwa bilkisu mamaki

"Kada ki damu daughter....qarshe dai kice kin amince zaki komawa aurenki ne....alhmdlh....hakanma kamar wani tarnaqine ga maqiya da zaki musu,kada ki damu,duk hukuncin da kika yanke ina bayanki dari bisa dari,matuqar babu cutarwa ko keta dokar Allah" wani wawan ajiyar zuciya ta sauke mai sauti a sarari,anty zuhriyya ta kalleta,can qasan ranta cikin sigar tsokana

"Daughter.....irin wannan ajiyar zuciya haka?,haka dama kikeson yarima?" Da sauri ta dubeta tana gwalalo idanu cikin mamaki

"So ummi....don Allah kibar fada,wallahi naji dadine da ranki bai baci ba" kaitake gyadawa tana gumtse dariya

"A'aha,ga abu a sarari na gani,soyayyace zallah..."

"Wallahi ban taba jin sonshi a raina ba ummi" ta fada kamar zata saki kuka,anty zuhriyyan ta tarbi numfashinta

"Meye na saurin shiga masallaci haka?yo in banda soyayya meya hana 7yrs idonki ya qyasa wani harki aureshi?,saida kika jira yarimanki"

"Ki yarda dani ummi...kin manta ban taba sanin fuskarsa ba....Allah ba qaunarsa"

"Shshshs!!!!" Anty zuhriyya tace dariyar da take boyewa tana qwace mata

"Bansan sakarya bace ke sai yau,uban yaran naki kike cewa baki qaunarsa baki taba qaunarsa ba?,tome zobensa yakeyi a wajensa?" Idanu ta sake fiddawa,sam ta mance dashi,ya akayi antyn ta gani

"Su amatu na ajewa" dariya sosai ta saka sannan ta dubi bilkisun da kyau

"Kina sonsa,baki sonsa yanzu ba wannan zancan akeyi ba,abinda na sani kawai shine,zamu qona ran abokan adawa....zan kuma soma gyaran diyata tun yanzun,zan soma shiryata komawa gidan uban 'ya'yanta" sosai bilkisu ta narke,gabanta na faduwa ta kalaman anty zuhriyyan

"Nifa anty bazan koma yanzu ba,saiya gane kurenshi,kuma ma idan na koma ai kamar yaci galaba a kaina" idanun ta zaro itama

"Gane kure kuma na nawa daughter?,har abada kuma koda kin koma koda baki koma ba kece kikaci galaba a kansu,kin gama dasu,tunda kika haifa musu yara,gasunan,duk wanda ya kallesu yaga masarautarsa KAISA zammm....so ki aje kome gefe ki fara karbar gyara daga wajena" daga haka ta miqe tana niyyar fita,sai bilkisun tace

"Zanje gobe naga baba"

"Allah ya kaimu" ta amsa mata tana qarasa ficewa daga dakin.      ¶¶¶¶¶¶¶   ¶¶¶¶¶   ¶¶¶¶¶¶¶


      Motoci biyu ta tanada domin yin mata rakiya,don tana da buqatar sirri,ba kowane takeson yasan inda zata da kuma abinda zai kaita ba,sai wasu motoci ukun da aka cika da kaya na alfarma iri iri,kayan qyale qyale na mata,saika rantse da Allah wani lefen 'yar gatan xa'a kai,kama daga tufafi,kayan kwalliya mayafai jakankuna takalma da sarqoqi harda gwalagwalai.       Cikin shiga ta alfarma ta nemi izinin fita wajen maimartaba,ya kuma bata izinin ba tare da yasan inda xata je ba,bare azeez wanda tun jiya daya dawo gidan yake kwance a sashensa cikin wani irin ciwo mara misaltuwa,ba tare da sanin kowa ba.        Tun safe data tashi ta kammala dukkan ayyukan da tasan tana yi cikin gidan,kana fa koma dakinta ta shirya tsaf cikin wata doguwar riga da aka mata dinki da shufom da duwatsun shuwarisky masu qyalqyali da daukar idanu,saita bada wani samfur na daban,ta kuma haskata sosai,hakanan tayi kyau kai bakace ita ta haife amatu da abdul ba,tsaf zaka mata kallon budurwa.        Tana fitowa falon tana lalubar atm dinta cikin jaka,don tana son ta yiwa babanta siyayya idan ta fitan kafin taje gidan,amatu ta kalleta

"Mami....nazo muje?"

"Babu da wanda xan fita,nima ba jimawa zanyi sosai ba,abinda ko wanka ma bakuyi ba,ku zauna bazan dade ba....,gidan daba baqonku bane,kusa ko yaushe kuna tafe.....ummi zan wuce"

"Saikin dawo,ki gaishesu,yauwa...,idan kin dawo ki tsaya don Allah ki tsaya a bawa road ki karbomin dinkunan nan wajen latif"

"In sha Allah" ta fada a gaggauce tana ficewa a falon.      Najwa anty zuhriyya ta kalla

"Yau kam da alama qazanta kukeji ko?" Najwan ta dubi anty zuhriyya

"Wlh yau bansan zubawa jikina ruwa"

"Kyaji dashi,tunda ke baki da niyya hada kan abeed amatu da abdul ki musu,duk sanda kikaso ke kyayi" waiwayawa tayi ta dubi abdul,kamar yadda ta zata din kuwa ya hade ranshi qyam,cikin dariya dariya tace

"Ummi kema kinsan ba'ayiwa abdul wanka tuntuni ya yaye kanshi" duban yaron tayi,yaro qarami sai manyance,shi Ala dole ba za'a jikinsa ba,shi yasa ya daina yarda ayi masa wanka

"Ku shiga tare idan kin gama musu ki hada masa nasa ruwan na daban yayi,ai babban mutum ne dama bai kamata anty najwa din ta dinga ganin jikinsa ba" dariya sukayi gaba daya,shima sai a sannan ya sassauta fuskarshi.        Ba'ayi minti biyar da shigar yaran ba mai gadi yayi knocking qofar falon,ta bashi izini ya tura qofar ya shigo,yana tsaye daga bakin qofar falon ya gaya mata saqon

"Hajiya....baqi kukayi cikin motoci,suna son a bude musu ne su shigo" tayi mamaki sosai,saboda iya saninta tasan basu da wani baqi,amma sai tace a bude musu su shigo din,ya amsa da to kana ya juya ya fice,saita miqe,ta isa window din dake can qarshe yana fuskantar harabar gidan,ta yaye labulen tana leqen masu shigowa.      Motocin da taga suna shigowa sai suka bata mamaki,saita saki labulen ta koma falo tana jiranjin su waye zasu shigo.      A hankali ta soma jin kamar banbadanci da kirari har zuwa qofar falonta,tana daga tsaye tana duban qofar falon,fulani ne akan gaba,sauran barorinta biye da ita.      Sosai anty zuhriyya ta zuba mata idanu,tana hango kamannin dake tsakaninta dasu amatu da kuma yarima azeez,cikin sakanni 'yan kadan kwanyarta ta gaya mata ko wacece matar.     Dukkan wani hade rai da bacin rai ta tattaro ta azawa fuskarta,ta kuma ci gaba da kallonsu har zuwa sanda suka gama shigowa 

"Su waye ku?" Ta fada kanta tsaye idanunta cikin na fulani

"Mu baqi ne daga masarautar kaisa....muna tafe ne tare da uwar gijiyarmu,amarya ga sarkin kaisa,mahaifiyar yarima abdul'azeez magajin sarki,wanda ya taba auren diyarku" wani kallon banza ta watsawa mai bayanin,sannan ta kuma sake maida idanunta ga wata dake kusa da ita

"Ba wannan dogon bayanin na buqaci ji daga gareku ba,wa kuke nema?,saboda babu wata alaqa data taba hadamu da wata masarauta ma balle ta qasar nan a iya namu sanin"

"Uwargijiyarmu ce tazo ta gana da tsohuwar surukarta domin samun sasanci" kubra mafi kusanci da fulani cikin hadiman ta fada,sake watsawa mai bayani na gaba kallon banza tayi sannan tace

"Kece zakiga bilkisun?,ko kece uwar gijiyar da kiketa rattabo bayani haka?,mu duka ahalinmu babu wata data taba rabar masarautar kaisa bare tayi auratayya da waninku,so ina tsammanin kun samu buguwar qwaqwalwa" zata sake bada amsa fulani ta daga musu hannu,gami da nuni da cewa dukkansu su fice,ba'a rufa wasu sakanni ba duka suka fice din kuwa,falon ya zamana daga ita sai anty zuhriyya.        "Na tattako da kaina nazo ne domin samun maslaha,da kuma gyara barakar dake tsakanin maimartaba dani kaina da kuma yarona...inason a wannan karon idan so samu ne.....ta shiga masarauta ta bayyana yafiyarta ga abdul'azeez dani kaina,na mata alqawarin bata dukkan abinda takeso,na mata tanadin rayuwa mai inganci,hakanan ko a yanzun ma da tarin alkhairi nake tafe,idanma tana buqatar ta sake koma masa ne a matsayin matarsa,a shirye nake akan hakan,matuqar komai zasu daidaita".     A kaikaice anty zuhriyya ke mata wani kallo,zuciyarta taxo iya wuya,wannan damar take nema babu shakka kuma gata tazo mata,idan har bata amayar da dukka abinda ke zuciyarta ba,idan har bata hana idanun fulani bacci ayau da zafafan maganganu masu quna ba tabbas ita din bata haifu cikin uwarta da ubanta ba,hakanan bata da rana a wajen bilkisu.

Matsalar guda daya kenan....bakya ganewa....kuma ban saka ran zaki gane ba,tunda har yanzu baki gane din ba,amma bari na baki wasu alamomi ko zaki gane din" sai anty zuhriyya ta gyara tsaiwarta tana harde hannayenta a qirji,tana kuma yiwa fulani wani irin kallo

"Hala sanda kuka shigo gidan nan idanunki a kulle suke,koda a bude suke toba shakka girman da munin abinda ke zuciyarki ya rufe miki idanu.....ki kalla gidan nan da kyau,tun daga waje zuwa ciki....mun miki kama da mabuqata?....koda munyi zubin mabuqata,ba shakka Allah ne ya yisu,kuma ya yisu a hakanne bawai don baya sonsu ba,ya yisu ne saboda jarrabawa da sanya rayuwar kowanne bawa bisa mizanin jarrabawa,kuma ya yisu a hakane badon masu kudi mulki ko sarauta sun kasance mafiya soyuwa a wajen Allah fiye dasu ba"      "Naji kina wasu maganganu,duk da bani da tabbacin cikin hayyacinki kike,to idan ba'a hayyacinki kike ba gwara ki koma daidai,dukka tatsuniyar da kika lissafa dai dai take da dawowar matacce duniya,a yanzu bilkisu ya muku nisa,hakanan ta tsere muku,kwatankwacin yadda sama ta yiwa qasa nisan taraza mai tarin yawa"

"Koda ace xaki hada dukkan abinda kika mallaka keda ahalinki kaffffff......baku da abin maida bilkisu cikinku saboda girma ko martabar wannan abun,mu MUTUNCI muka zaba,MARTABARMU tafi gaban komai,hakanan KIMARMU babu wani abu da za'a mata farashi ko a daidaita ta dashi,KUDI ba shine arziqi ba,DUKIYA ba itace wadatar zuci ba,hakanan ƘYALE ƘYALEN RAYUWA ba shine samun nutsuwa da kwanciyar hankali na,saboda haka shawara guda daya xan baki.....sawunki a likkafa ki fita salin alin ki koma inda kika fito,ke da dukka wani tarkace naki da kike masa kallon arziqi ko kuma dukiya,koda sawun tayar motocinku bana buqatar tozali dasu bayan gushewarku bare wani abu daban".      Mamaki mai dimbin yawa,al'ajabi data dinga jinsa kamar a mafarki su suka dinga mamayarta,a iya tarihin rayuwarta,babu wani wanda ya yaba tsayawa haka ya gasa mata maga ganu makamantan wannan,ta tashi tsahon rayuwarta ana mata biyayya,ta tashi tsayin rayuwarta ana girmamata,ta tashi tsahon rayuwarta ana kiyaye dokokinta da bacin ranta,amma yau sai ga wata halitta tana gaya mata magangun da bata taba jinsu da kunnenta a kanta ba tsayin rayuwar tata,cike da zallar mamaki tace

"Kinsan me kike fada kuwa?,shin kin riqe kuqa dawa kike magana?" Murmushin takaici anty zuhriyya ta saki,kana ta tako dab da fulanin ta tsaya a gabanta

"Kinci sa'a ban riqe sunarki ba,amma dai nasan cewa ina magana ne da wata uwa kuma mata ga sarkin qasata,mace mai yawan dagawa alfahari da kuma zallar zalunci danne haqqin marayu da rashin sanin darajar dan adam.....ki fitamin a gida tun labarin zuwanki baikai kunnen sarki abdallah mu'az ba,tun ban wargaza shirinki da yayi saura ba" gaba daya ta gama daureta da jijiyoyin jikinta,siffofin data siffantata dasu sai suka tsaya mata a rai,koda yaushe jama'arta kallon mai kyauta tausayi haqqin na qasa da ita suke mata,amma yau sai gashi an siffantata da siffofi mafiya qyamata a awajenta.      "Ummi....ni wannan nakeso anty najwa yau ta sakamin" 

"Nima wannan ummi don Allah...amma taqi wai saidai idan mami ta dawo" muryoyin amatu da abdurrahman da suka fito a guje a jere riqe da kayan a hannunsu ta karade falon kowa na saurin nunawa anty zuhriyya.         Cak idanunta suka sauka kan fuskokin da suka kusa sanyata shidewa,fuskoki guda biyu masu kama ta sak da sak da fuskar abdul'azeez dinta,ta wani sashen kuma tata fuskar take hange jikin tasun,sai take ganin kamar mafarki kamar almara,don haka ta soma matsawa gaba kadan don tagani abinda idanunta ke gane mata da gaske ne

"Kul!ahir dinki!" Ta tsinci muryar anty zuhriyya kamar mai bata umarni tana fadi

"Karki soma kusantar inda suke.....kamar yadda kika koresu tun suna gudan jini....,sun koru koruwa ta har abada,sun barranta daga kasancewa jininki,ina fata zaki hanzarta fita,don bamu buqatar gama nunfashinmu da naki" daga haka ta qarasa ta kama hannayensu zuwa ciki,suna waiwayen fulani tare da tunanin wacece ita?.       Wani irin gumi ne ya yanko mata,qafafunta taji sun matuqar sanyi kamar ba zasu iya daukar gangar jikinta ba,su waye wadan nan yaran masu tsananin kama da abdul'azeez

"Jikoki,yayan bilkisu da abdul'azeez" wani sashe na zuciyarta ya bata amsar tambayarta,mummunar faduwar gaba ga ziyarceta,tare da wani gumin da yafi na dazu dumi da jiqa sassan jiki,kada dai ace sune cikin data kore samuwarshi?,kada dai ace da gaskene,da gaskene abinda suka fadi,a sanda ta hana azeez ya mata bayani,a sanda ta kasa tsaiwa ta saurareshi?.       Wani irin mugun sarawa kanta yake,a matuqar salube jikinta taja qafafunta da qyar ta fice,tana jin sanda suka take mata baya suna binta da kirari harta isa bakin motar,ganin batace a sauke kayan ba ya sanya ba wanda yayi maganarsu,aka tada dukka motocin suka fice daga gidan.      Cikin motar riqe take da kanta,babu abinda ke mata kaikawo sai magangun anty zuhriyya,daga qarshe kuma fuskokin yaran su mata kutse cikin tunanin nata,gaba daya kwanyarta ta burkice,tana da buqatar qarin bayani,don haka ta shaidawa kubra,ta gayawa driver sassan yarima azeez zasu wuce kai tsaye,a kuma bincika a tabbatar mata yana nan kafin su isa din.        Har wani huci anty zuhriyya takeyi ita kadai,ranta a bace yake,wato yadda malam bilya ya zubda musu qima akan kudi har yanzu da wannan take kallonsu?,koda yake ko yanzun alhmdlh,ta fadi da yawa daga cikin abinda ke mata kaikawo a qirjinta,ko a yanzun ta rage wani nauyi da radadin.      Sam batayi niyyar shaidawa bilkisu ba,abbaa kawai tayi niyyar gayawa,don kada yaga jinkirin komawar bilkisu dakinta,don ta tabbatat ta gayawa bilkisu abinda ya faru za'a samu hutsancewarta ne kan komawar,ita kuma tafiso ta koma din,ko don yadda yarima yake binta,ta koma taga qarshen iko da iyawar aisha fulani!.         A hankali tayi sallama falon da yake mallakin mahaifin nata,ya daga kai yana amsa mata lokacin da yake shafawa qafafunsa man zafi,wadanda a yanzu kuma kusan suner rabin matsalarsa,don ko barcin kirki sai sunso suke barinsa yayi.      Murmushi dauke a fuskarsa yake maraba da bilkisun,kai bakace shine wannan malam bilya din ba,wanda a baya bai damu da kuka ko dariyarta ba.       Itama fuskarta dauke da murmushi ta qaraso cikin dakin,ta aje jakarta cikin sauri tana karbar kwalban man tana cewa

"Baba bari na samu ladan nima,naga hannunka bai kaiwa wani wajen" ta fada tana xama gabanshi ta soma shafa masa

"To ya zanyi,ita yanxu kaltume kafin ma ta samu damar zuwa ta shafamin na gaji da jira,hidima sun mata yawa,barin yanxun da take ita kadai" cikin salo tsokana bilkisun tace

"To kodai bazawarar da na gano a bayan layinmu xanwa magana?" Daquwa ya watsa mata

"Uwariyo....yauni na xama kakanki maigado?,ai ni yanzu mace dayace a duniya inda tana nan xan iya zama da ita,kuma nake marmarin zama da ita,nakejin inama zan ganta,saidai ta yimin nisan da babu damar sake haduwa har sai na cimmata,maimunatu,mace ta gari da banga irinta ba kaf rayuwata,salihar mace da nake yaqinin biyayyar miji zata sadata da aljanna in sha Allahu,ina miki fata maigado,duk da kin debi da yawa daga cikin halayenta,amma ina miki fatan biyayyar miji da haquri koda kwatankwacin na maimunatu ne" ya tuna da mahifiyarta,kuma sosai abun ya taba ranta,saita sadda kai qasa,maganar da yayi kamar yasan lamarin dake tafe da ita.       "Kamar akwai magana a bakinki mai gado" ya fada yana dubanta,shuru tayi na wasu sakanni sannan tace

"Kayi haquri baba,nayi wani hukunci ne ba tare da na baka dama ko naji ta bakinka ba" bata boye masa dukkan yadda sukayi da maimartaba ba ta shaida masa,murmushi ya saki,ya tabbatar batasan saida ya soma ganinsa ba kafin ita

"Baki kuskure ba maigado,abinda kikayin shine dai dai,kuma yanzun dukkanmu bamu da wani sauran hukunci a kanki,dukan hukunci naki ne.....duk yadda zan soki bilkisu kona kare miki haqqi ko martabarki bazaikai naso ganinki a dakinki ba,cikin martaba da rufin asirin aure,saidai idan harke din hakan bai miki ba" shuru tayi tana nazari.      Muryar mahaifin nata ta katseta,magana yake mata cikin sanyin murya da lalama,gami da nasiha da kuma sake neman afuwarta kan abinda ya aikata mata.       Ta jima a wajen shi,har zuwa sanda lokacin da ya tabbatar da cewa ta nutsu a xuciyarta sannan ya rabu da ita ta shiga cikin gidan wajen 'yan uwanta    A ladabce sunusi sarkin sassan yarime ke amsawa fulani ke amsa mata cewa yariman yana ciki,yanason mata bayanin cewa kwanakin duka da suka biyo baya suma basuga wulgi ko duriyarsa ba,amma basu samu damar hakan ba harta wuce zuwa ciki.      A mamakance take bin ko ina na falukanshi da kallo,babu wata alama dake nuna mata cewa yana nan din,dukkan alamu sun nuna cewa kamar an dauki wasu kwanaki ba'ayi amfani da bangaren nasa ma gaba daya ba,ko wanne qwan lantarki na a kashe,ba abinda keyi sai ac da keta fidda uban sanyi,tanayi tana kashe wasu,wasu kuma tana rabuwa dasu,cike zuciyarta fal da mamaki,ta tsammaci ma bai qasar,donko sanda sunusi yace mata yana nan tayi mamakin jin hakan.      Bedroom na qarshe tayi nasarar samu a bude,an kara qofarshi,ta tura da sallama a bakinta ta shiga,idanunta na saman gadon dake nuna akwai mutum kwance.      Can qasa taji anyi magana,bisa dukkan alamu amsa sallamar akayi

"Abdul'azeez" ta kirayi sunanshi tana tsaye daga gefe,yadan motsa kadan,sannan bayan shudewar minti guda ya yaye bargon daya rufa a hankali ya miqe ya zauna,bayan ya jingina bayanshi da makarin gadon.     Cikin tashin hankali take kallonshi,kamar ba azeez dinta ba,gaba daya ya feɗe,hakanan ya rame ya zabge,fuskarshi har ta soma tara gashi wanda batasanshi dashi ba,cikin hanzari ta qarasa gefan gadon a rude tana furta

"Ya salamu ya Allah,me ya sameka?" Tana kallon yadda qirjinsa ke dagawa da kuma fitar numfashinsa.      Idanunsa a kulle,shi kadai yasan ya yakejin jikinsa yace

"Banajin dadi ne"

"Bakajin dadi ko baka da lafiya kwata kwata abdul'azeez!" Ta fada a dan zafafe sannan ta sake cewa

"Tun yaushe ne baka da lafiyar amma babu wanda ka shaidawa?,kazo ka kwata ka kulle kanka kai kadai?,so kake ka mutu?" Ta sake fada cikin fada

"Qaramin yarone kai abdul'azeez?" Ta kuma tambayarsa.     Kasa amsa mata yayi saboda wani radadi da yakeji,ta fuskanci hakan,don haka hannunta na rawa ta ciro wayarta ta soma laluben wata lamba ta kira,umarni take badawa kan maza maza a fidda mota cikin sirri xa'a fita da yarima zuwa a sibiti,ta gama wayar ta kashe,saita rasa me zatayi banda sannu da take masa,ranta gaba daya a jagule kuma a tashe,meya sameshi haka amma bata da masaniya,Allah ne yasan kwanaki nawa yayi a haka,wannan matsalar gaba daya ta shiga rayuwarta,ta canzata,ta hanata aiwatar da komai yadda ta saba,ta zuba mishi idanu tana kallon yadda yake kokawa da numfashinsa.       Safwa ta fado mata a rai,haushi takaicinta ita da mahaifiyarta ya qarar mata a rai,ta zabawa azeez safwa ne saboda ya samu gata da kulawa irin wadda safwan taga ana bata a gidansu,ta zabeta ne domin ta zame masa macen aljanna,macen da zata zamar masa nutsuwa da hutu,sai kuma gashi tunda akayi auren ba abinda aka tsinta a zaman nasu,hakanan babu abinda xa'a dorar.      Cikin mitina qalilan aka fita da azeez din zuwa babban asibitin kudi kuma mallakin likitan gidan,tunda ta gaya masa bata yarda a dubashi ko a kwantar dashi cikin asibitin gidan ba,don ta tabbatar dukkan wadanda suke musu bita da qulli,da kuma binsu da sharri idanuwansu na kansu,don haka ta gwammace ya xauna a sibitin likitan,cikin dakuna da aka tanada na musamman mafiya tsada a asibitin.       Taso shaidawa maimartaba kafin tafiyarsu,to amma tasan cewa yanzun yana zaman fada ne,ba lallai ta samu ganinsa ba,don haka ta yanke tafiya ta shaida masa daga baya,don gaba daya hankalinta ba'a kwance yake ba.       Yanayin yadda yaga jikin yariman ya sanya aka fara bashi taimakon gaggawa,daga qarshe suka qara masa da oxcygyn saboda yadda numfashin ya soma masa wahala.       Cikin mamaki likitan ke tambayar fulani meke damun yariman?,a iyaka binciken da sukayi basuga wani ciwo ba,illa damuwa data masa yawa,da kuma yawan tunani daya sanyawa ranshi,wanda hakan ke neman yin barazana ga lafiyar zuciyarsa.       Cike da mamaki take kada kai

"Ban sani ba likita,bansan me yasaka har haka cikin zuciyarsa ba"

"Nina sani" afnan wadda ta biyosu asibitin daga baya ta fada,waiwayowa fulani tayi tana kallonta cikin mamaki,kanta tsaye ta soma magana

"Bilkisu,bilkisu ce a ranshi,ita ya saka cikin zuciyarsa,itace kuma silar ciwonsa da samuwar sauqinsa" daga haka ta miqe abinta ta soma takawa zata fice,da fulanin da likitan da baisan tushen maganar ba gaba daya suka bita da kallo harta fice daga office din

"Anyway....koma meye damuwarsa ya kamata a kawo qarshenta indai anason ya samu lafiyar zuciyarsa" maganar likitan data dawo da ita hayyacinta kenan.       Ita kadai a dakin da aka kwantar dashi take kai kawo tana tuna maganar afnan cikin qwaqwalwarta

"Bilkisu,bilkisu?" Ta maimaita sunan a hankali,sannan ta daga kanta ta dubi yadda yake kwance yana bacci da taimakon iskar oxcygyn.        Tunda take dashi bazata iya tuna sanda ya kwanya ciwo ba har haka,ace har gaon asibiti,mutum ne shi mai jumurin ciwo kowanne iri ne,yakan yi harkokinsa alhalin baida cikakkiyar lafiya,a haka zaiyi harkokinsa harya gama ciwo na cinsa a tsaitsaye ya kuma warke abunsa.       Amma da gaske bilkisun ce?,indai kuwa ita dince kamar yadda afnan ta fada bai haqura ba kenan?,idan kuwa bai haqura ba shin akwai shekaru ko wasu abubuwa da zasu zo su sanyashi haqurar?,idan ciwon nan ya zama ajalinsa fa?,qatotuwar tambayar data rufto kwanyarta kenan,ta sanya jikinta ya soma rawa,ba shiri ta samu sit ta zauna tana kiran sunan Allah,sai taji a jikinta kamar zata rasa yariman ne,sai taji kamar lokacin rabuwarsu ne yazo,cikin sauri da rawar jiki ta jawo jakarta,ta fidda wayarta ta lalubi lambar mai martaba.       A dake ya amsa sallamarta kamar yadda yake mata a wadannan kwanakin,cikin sanyin jiki da sanyin murya tace

"Saqona bai iske ba halan Allah ya taimakeka"

"Ya iskeni mana,amma me zan muku?,Allah ya bashi lafiya,inajin ke kika zabarma rayuwarsa hakan aiko?,kinga kenan ai babu matsala,saidai nayi fata da addu'ar Allah ya taimaka" daga haka qita ya kashe wayar.       Cikin mamaki tayi saroro,sai wayar ta sulale daga hannunta,ta saka hannayenya biyu tana rufe bakinta dasu gamida furzar da zazzafar iska,wani abu ya dunqule mata a maqoshi,bata taba zaton rana makamanciyar wannan na zuwa ba tsakaninta dashi,saita miqe da sauri ta isa gaban gadon tana duban fuskarsa data fada,zancan mai martaba na dawo mata

"Haka kika zabarwa rayuwarsa aiko?" Kai ta girgiza ta dora hannu saman kansa tana shafawa a hankali,kamar me neman amsar abinda ya dace tayi.        Ajiyar zuciya me qarfi mai martaba ya saka,bayan ya kashe wayar gaba daya sai yaji ya kasa nutsuwa,yanajin kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi a asibitin,amma dole ya dake ya kanne,harsai fulanin takai kanta da kanta inda yakeson taje din,harsai ta saitawa kanta hanya tukunna

"Allah ya bada lafiya,ya taqaita maka" yayiwa abdul'azeez din addua a fili can qasa yana jingina bayansa da dan gadon hutawar da yake kai,yana jin damuwa sosai cikin ranshi.        "Lafiya kuwa Allah ya taimakeka?" Ya tsinci sautin adama saman kanshi tana jeho masa tambayar,sam ya manta ya sanyata ta dauko mishi lemon tuffa a falo,sai ya miqa mata hannu yana amsar lemon ba tare daya amsa mata ba.      Bata haqura ba dai ta zauna daura dashi

"Kowa yaga fuskarka yasan kana cikin damuwa,idan don abinda yarima ga aikata ne saidai muce kayi haquri,kowanne bawa da jarrabarsa,dama ko cikin yaranka sai kaga Allah ya fitar maka da zakka a cikinsu,wani halinsa daban,shi yasa ba jinsi ake roqo ba da nagari,wasu matan sai suzo sufi mazan nagarta.....amfanin Allah ya baka yaran da yawa kenan,idan wani ya bata maka sai wani ya faranta maka aiko?".       Da mamaki saman fuskarshi ya sauke cup din yana dubanta

"Wani abun na gaya miki yarima yayi?" Sai tadan dirirce kadan

"Au...to ai na zaci abinda ya farune satittikan da suka gabata" bai sake cewa da ita komai.ba ya maida kofin bakinsa,wasu wasi fal ranshi yanata auna maganganu da ayyukan adaman cikin lokuttan nan,yayin da ita kuma tayi tsam da ranta,gefe guda na zuciyarta ya cika fal da haushi da takaici,duk yadda sukaso jin wani abu abun ya faskara,wani sashen kuma yana kwabarta na ta taka a hankali kada kwabarsu tayi ruwa,tunda tafi kowa sanin waye sarki abdallah din


       Ranar ranta a bace haka anty zuhriyya ta wuni,bilkisu nacan gida batasan meke faruwa ba,don a can ta wuni,koda ta dawo batace da ita komai ba,sai da abbaa ya dawo take shaida masa abinda ya farun.      Murmushi yayi kawai sannan yace

"Na lura da abubuwa masu yawa,me martaba ya boyewa matarsa komai ne,batasan meke faruwa ba,akwai kuma abinda yakeson aiwatarwa,kada ki saka wannan abun cikin lissafin damuwarki,mu jira lokaci,nasan abinda ya shirya din xai bayyana"

"Kamar me abban najwa?" Ta tambayeshi

"Karki gaggawa,ki jira ki gani" ya fada yana bude foodflask din abincin data aje masa yana duba meta dafa,yayin da ita kuma ta shiga zurfin tunani sosai.


   ¶¶¶¶¶¶¶   ¶¶¶¶¶   ¶¶¶¶¶¶      Yadda yake jin jiki a lokutan hakan yake samun kulawa daga wajen likitoci,sosai hankalin fulani yake a tashe kamar yadda hankalin me martaba yake,saidai shi ya danne ya kuma boye,bai bari kuma ta gane hakan ba.       Kamar wata safiya yana zaune dakinsa yana lazumi,saidai gaba daya hankalinsa da tunaninsa yana kan azeez din dake kwance a asibiti.        Daga bakin qofar mihrabin da yakan zauna yayi sallah da lazumi yaji sallamar afnan,yayi mamaki qwarai jinta a irin wannan lokacin,don bata taba zuwar masa haka ba,sai daya amsa sannan ya bata izinin qarasowa.      Cikin nutsuwa kuma a ladabce ta samu waje ta zauna,ta gaidashi ya amsa mata cikin kulawa,shiru tayi na wani dan lokaci har sai daya tambayeta sannan ta soma magana cikin sanyi

"Abby....zuwa nayi na roqeka alfarma,don girman Allah kayi haquri,ka yafewa ammi da ya azeez kuskuren da suka aikata ko ince ganganci,ka daure ka shiga lamarin ya azeez,wallahi sosai yakejin jiki a asibiti,ina kuma da yaqinin cewa,inda ace bilkisu na tare dashi bazai shiga wannan yanayin ba" shuru yayi yana dan murmushi na wasu sakanni,sannan ya bude baki a nutse yace

"Haqiqa abinda aisha ta aikata yayi mugun bani mamaki da kuma girgizani,din ban taba kawo mata aikata hakan ba,laifin kuma bana kowa bane face na mahaifiyarkin,na riga dana yafe musu,amma yafiyar ba yana nufin karna dauki mataki akai ba,lamarin azeez na riga dana shigeshi tuntuni,saidai nabar sauran damar hannun yarinyar da aka zalunta,amma su ban basu damar su sani ba,saboda inason su gama horuwa,na baiwa mamarki haske na yadda zata gyara kurenta amma har yanzun bata dau hasken ba bare ta gyara,bani da yadda zanyi,iyakata nayita zama na zuba ido naga randa zata dauki haske,ta kuma dauki matakin gyaran,wanda gyaranta shi kadaine zai qarasa kawo qarshen wadan nan matsalolin" fuskar afnan ta fadada fara'a da kuma haske,cikin zumudi tace

"Kana nufin abby ka dawo ma da ya azeez matarsa?" Kai ya gyada

"Hakane,ban kuma lamunci ki gayawa kowa ba kamar yadda nima ban shaidawa kowa,nayi hakanne kuma bisa wani dalili nawa" kai take gyadawa tana sarawa salo da hikima irin na mahaifinta,tabbas ya cika cikakken adalin shugaba kuma jagora,sai yanzu take sake gane abinda yasa jama'arsa ke masa son so

"Allah ya saka da alkhairi,ya kuma qara girma abbi,amma don Allah kaje kaga ya azeez" murmushi ya kuma saki sosai yana dubanta

"Kin taba ganin an shiga tsakanin hanta da jini,dole zanje,amma sai bayan wani lokaci dana diba"

"Hakanma muna godiya" ta fada tana murmushi.      Hira suka taba wadda suka dan jima basuyi irinta ba,kana daga bisani sukayi sallama,harta kusa fita daga wajen yakira sunanta

"Karki manta,bance ki gayawa kowa yadda mukayi ba"

"In sha Allahu abbi....amma abbi inason naje naganta anty bilkisun" kai ya gyada

"Babu laifi....ki miqa gaisuwata zuwa gareta" ran afnan fes ta fita daga wajen maimartaba,hakanan hankalinta akwance yake yanzun,tasan na zasu rasa nagartacciyar suruka irin bilkisun ba.  ¶¶¶¶¶¶¶   ¶¶¶¶¶   ¶¶¶¶¶¶¶     Cikin zumudi da farinciki take shiryawa,bayan ta samu dan rakiya a sirrance zuwa gidansu bilksun,ta kuma nema rakiyar mama sodangi itama a sirrance,bayan ta shaida mata dukan abinda ke faruwa,wanda hakan ya yima mama sodangi dadi matuqa,kamar ta taka rawa haka ta dinga ji.       Babu wani jinkiri suka gama shirinsu tsaf,suka kama hanya.       Dai dai lokacin da bilkisun ke zaune saman wasu kujeru dake farfajiyar gidan,hannunta riqe da wani dan qaram littafi tana dubawa bayan tashin anty zuhriyya yanzun nan zuwa cikin gida.       Tsiya tayi mata ta kuma yi mata tas kan taqi gado taqi mawanka,duk kayan gyaran data kawo mata sai taqi amfani dasu,tace gyara dole kuwa babu fashi,kodon ta rikita musu yarima,ta kuma sake qular da aisha babarshi,itakam komaima jinsa take kamar a mafarki,hatta da komawar duk data amsa amma jinta take kamar wasan yara.       Batasan yadda zuciyarta da gangar jikinta suka dauki abun ba,itadai gata nan ne dai kawai ta zubawa sarautar Allah idanu,taga yaya qaddararta zata kaya.       Karar dage gate yadanja hankalinta,ta daga kai ta kalli motar dake shigowa,sai kuma ta maida taci gaba da karatunta,hakan ya sanya har suka fito bataga su waye ba,sai dataji takun tafiya sannan ta kuma daga kanta.       Sosai gabanta ya fadi sanda tayi arba da mama sodangi da kuna afnan a tafe,ta miqe tsaye cikin wasu wasi tana kallonsu,mama sodangi bata ganta ba,afnan ce ta hangota,saitayi wajenta da sauri hannaye bude cikin nuna zallar farinciki da kuma hargowa irinta farinciki sanda ta sake tabbatarwa lallai bilkisu classmate dinta ce

"Billy bilya!" Ta ambaceta da sunan da akan kirata dashi wani lokaci.       Haka kawai saita samu kanta da subucewar murmushi kan fuskarta,itama ta bude hannayen nata dukka tana dariya,har afnan ta qaraso suka rungume junansu,kowanne zuciyarsa na farincikin ganin dan uwansa.       "Wayyo Allah na,ashe da gaske dai kece,har taraddadi nake kar naxo.na samu ba kedin da nake tunani bane,bilkisu ina kika boye haka?,meye labari?" Da mamakin yadda bakin afnan din ya bude take kallonta,cikin dariya tace

"Mu qarasa ciki mana" saita juya sashen mama sodangi

"Mama....sannu da zuwa" ta furta a hankali,tana tuna wasu abubuwa da suka shude zamanin baya a rayuwarta,kai mama sodangin ta kada

"Bani amsawa,bayan an manta da nine a tsaye" dariya sukayi dukansu kana suka rankaya zuwa cikin gidan.       Ko daya a cikinsu anty zuhriyya bata gane ba tunda bata sansu ba,iyaka sun gaisa cikin mutunci,tasa najwa ta aje musu abunci da kayan motsa baki ta wuce ta barsu.        Hira sosai suka daka,tun daga labarin rayuwar makaranta,suns tuna yadda suka rayu,da yadda afnan din ta dinga qwarzabar billy,a nan wajen tace

"Kinsan wani abu?,alokacin fa burgeni kike,kawai so nake ki kulani muyi qawance,ke kuma kin qi,ni kuma inajin haushin na xubda daraja na fara zuwa wajenki,ina tsoron kada ki yarfani girmana ya zube,shi yasa nake miki haka" dariya sosai ta baiwa billy,ta karya wuya tana cewa

"Ni a sannan guguwar data taso rayuwata a gaba tasa bana ganin kowa sai ita,da kuma yadda zanyi na kawar da ita".     Sun dau lokaci sosai suna hirar,har sai da mama sodangi tace

"Kinga idan abinda ya kawoki dama kenan....ni matsa nayi abinda ya dameni" murmushi afnan tayi sannan ta tattara dukka hankalinta akan bilkisu

"Biko kashi na biyu muka sake zuwa yifa?" Bilkisu na dubanta ta tambayeta

"Bikon mefa?"

"Matar yayana" ta bata amsa kai tsaye tana dubanta,sai tadan matse fuska kadan sannan tace

"Awwnnn" daga haka kuma tayi shuru,tana tunsnin meya hana mahaifiyarsa sanya baki ne cikin maganar?,bayan itace qashin bayan komai?,sai wadanda bada su akayi ba keta zuwa,lallai ba shakka akwai matsala kuma akwai damuwa kenan.        "Bilkisu.....a matsayina na uwa ga yarima ba mahaifiya ba,bayan maimartaba nima gani nazo da kaina nema mishi afuwa a wajenki,don a yanxun bashi da ikon iya magana dake,yana gadon asibiti yana jiyya" waiwayowa tayi tana dubansu jin abinda sukace,sai afnan ta dage gira

"Yes...kin kwantar dashi,kuma komai.na iya faruwa da zuciyarsa....kima Allah kiyi haquri anty billy" ta qarashe fada tana hade hannayenta biyu waje daya.      Murmushin qarfin hali ta saki tana kama hannayen afnan kana ta sauke

"Bari....girman me martaba da darajarsa yafi gaban haka,ya riga ya roqa alfarma kuma na masa,so wannan ya riga da ya wuce"

"Indai da gaske ne to gaskiya ki tattara kayanaki ki tafi jinyar yayana" afnan ta fada tana langabewa cikin nuna alamun tausayi,dariya ce ta qwacewa bilkisun kana ta kada kai

"Bazai yuwu ba afnan,kiyi haquri" kamar zata saki kuka haka tayi,amma dole ta haqura,daga haka akalar hirar ta koma ga mama sodangi,ta soma tambayarta rakiya

"Rakiya ai tana gidan mijinta,yaranta biyu yanzu haka" murmushi ta saka tana mata fatan alkhairi,tare da tuna zaman shekara dayan da sukayi,zama me dadi a tsakaninsu,wanda sam ba zata mance dashi ba.        Suna tsaka da hirar dirvern gidan ya dawo dasu amatu daga tahfeez,ba afnan ba,hatta da mama sodangi sai data kusa narkewa a wajen saboda tsabar mamaki da wasuwasi,ai kafin kace meye tuni afnan ta isa wajen yaran tun kafin su qaraso ciki ta cafesu,basusan wacece ba,basusan dawan garin ba sai suka hau baza idanu,muryarta na rawa kamar zata saki kuka ta dubi bilkisu tace

"Don girman Allah kice wadan nan twince din ya yarima ne,kice nashine karkice aah" dariya da tausayin xallar soyayyar yaran data gani cikin idanunta ya kamata,murya can qasa ra furta

"Nakune" qatuwar ajiyar zuciya mama sodangi ta saki,ashe itama abinda takeson ji kenan,sai kuma dukka suka tattara duk wani attention nasu kan yaran.      Tun yaran suna baza idanu suna dari dari sai gasu sun sake,tana sake nanata musu ita din wace,kafin wani lokaci kuwa suka riqe radam a kansu,qarshe sai gasu suna qyaqyata dariya tare tana basu labarai ita da mama sodangi.      Ganin yaran ya hanasu tafiya da wuri har kusan sallar isha'i,koda suka tashi tafiya dinma kafewa afnan tayi da magiyar don Allah bilkisun ta bata su aro koda na iya yaune,gobe ta dawo mata dasu

"Kiyi haquri,bazai yuwu ba" tace da ita,hakanan jikinta a sanyaye ta saukesu suka wuce,bayan ta cika wayatta da hotunansu kamar ba gobe.      Cikin kwanaki biyu rak ta wanko hotunan,ta kuma cika sassan fulani dasu waje waje,wanda da ace wajene da kowa ke iya shiga ba shakka da.labari ya cika masarautar,randa fulanin ta soma gani ta jima tsaye tana qarewa yaran kallo,tun randa ta dora idanunta a kansu suka tsaye mata cikin xuciya da ruhi,taji wani abu mai kama da soyayya da qauna na ratsa zuciyarta,kwatankwacin yadda takeson mahaifin yaran,abu daya ya hanata kasa magana a kansu,duk da yadda kullum take kwana ta tashi dasu a ranta.      Batasan afnan na bayanya ba sai data yi gyaran murya,sai kawai tayi gaba ba tare data waiwayo ba,kamar ba kallon hotunan nasu ta tsaya yi ba,dariya ta kama afnan

"Uhmmm,ammi kenan,idanma zaki bi hanya tun wuri gwara kibi,saina taya abbi wannan yaqin wallahi".¶¶¶¶¶¶¶   ¶¶¶¶¶   ¶¶¶¶¶¶¶¶      Ko ina na jikinta rawa yake cikin tashin hankalin da bata taba riskar kanta a ciki ba,ba ita ba....dukkan wanda ke wajen hankalinsa a tashe yake,wasu daga ciki ma sun soma kuka,saboda yanayin da aka fita da yarima azeez.       Lambar mai martaba ta kira,tayi sa'a yana available,bugu uku ya daga

"Idan ma ba zaka zo ka ganshi ba,to na roqeka ka yafe masa,saboda yanayin daya shiga din,bamu da tabbacin samuwar ruhinsa......duk da cewa nice silar komai,dukka laifin yana wuyana a qa'ida....amma ina roqar masa afuwarka" kalamanta sunyi masifar daga mishi hankali,don haka bai iya maida mata amsa ba ya katse kiran,sannan ya bada umarni cikin gaggawa aka tada motoci ya nufi asibitin.       Fulani adama da fitar ta kasance kan idanunta saita jinjina kai,tana baiwa kamal umarnin bin ayarin motocin me martaba,yaga inda suka nufa,don sama bata yarda da yanayinsa a 'yan lokuttan nan ba,ta sakawa sauyawar mood dinshi ayar tambaya.       Yanayin daya samesu a ciki ya tabashi shima,tsahon awa guda kafin su maidoshi dakin,bisa qwararan dokikin banda hayaniya sam,hakan ya sanya maimartaba ya baiwa kowa umarnin komawa gida,abar mai jiyyar shi kadai,tunda akwai masu kula dashi,sai a sannan yake tambayar ina safwa?,ita ya kamata ta zauna dashi,tsananin bacin rai ya hana fulani bashi amsa,inda ace tana da iko ba shakka yau da ita da kanta zata sallami yarinyar,saboda ko kusa bata ga rana ko amfanin auren nasu ba.       Duk yadda yaso zuwa asibitin washegari bai samu dama ba,saboda baqin da masarautar tasu sukayi daga qasar jigawa,saidai ya samu bayanin cewa jikin nasa da sauqi sosai,don harma ya dan farka,hakan ya dan sake saka masa kwanciyar hankali.      Washegari ana idar da sallar asuba,gari yana yin shaa ya shirya zuwa sake dubashi ba tare da wasu mutane 'yan rakiya masu yawa ba.        Lokacin da ya tura qofar dakin saiya sameshi saman abun sallah,ya jingina bayanshi da bango,ya fada sosai ya qara haske,da alamar gyangyadi ne ya debeshi saboda tasirin allurai da ruwan da aketa saka mishi,wanda ciki akwai na bacci.       Saida ya tsaya ya gama qare masa kallo sannan ya saki murmushi,babu shakka ba'a cika baki a soyayya,hakanan babu wanda ya isa ya bugu qirji yace yafi qarfin soyayya,ko yace shidin jarumi ne a wannan fagen,ko wayeshi kuwa,bai taba ganin wani abu daya karya abdul'azeez din,ya cire masa dukkan wata jarumata tashi da qwarin gwiwa ba irin wannan lamarin,saiya ci gaba da takawa a hankali har yakai bakin daddumar ya xare takalmansa,sannan ya zauna a gabansa,kasancewar daddumar tana da yalwa,ya langwashe qafafunsa yana ci gaba da kallonshi,sannan a hankali ya saka hannunshi ya bugi cinyarsa........⁷³Post a Comment for "SIRADIN RAYUWA CHAPTER 19 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...